Kiyi hakuri kinji ikhlas, babu komai duk abinda yafaru dake daga Allah ne,
Bayan tafiyarki babu irin cikiyar da banyi ba amma Allah baisa ansameki ba, ko wanda ya ganki ma ba asamu ba"
Kallonsa tayi yana share kwalla daga idonsa,
"Abba haka Allah ya aiko, shekarata 5 ahali na lalura sai yanzu nasamu lafiya"
"Allah yasake baki lafiya ikhlas"
Amsawa tayi da "amin" daga nan suka cigaba da hira wacce ba arasa ba amma ikhlas ta boye masa maganar anyi mata fyade.
Sai da suka raba dare suna hira har wurin karfe 12 domin ko ada lokacin da tana gida kullum haka take zama atare dashi suyita hira har sai dare yayi nisa sannan takoma dakinta, yau dinma hakance ta faru sai da taji garin tsit sannan tayi masa sallama tatafi.
Dakinta ta koma tayi shirin bacci ta kwanta, Allah Sarki sabo turken wawa inji bahaushe nan kuma taji kewar elmustapha da ni'ima ta kamata tasan da tuni yanzu suna can tare ko ana hira ko kuma an kwanta,
Baccine mai mutukar dadi ya dauketa wanda bata shirya masa ba.
Washe gari tunda asuba ta tashi tana yin salla ta shiga kitchen domin dama tun da can haka ta saba itace take shiryawa mahaifinta abincin da zai ci,
Tana kitchen din tana soye soyenta yakumbo ta shigo afusace,
"Allah ya kawo mu kuma kin dawo zaku fara rabon girki keda matar gida sai kace wasu kishiyoyi, ohhh ni Hadiza ina ganin ikon Allah agidan nan, to bari kiji kina jina? Komai akwai muhallinsa wai an sakawa kuturu sarka ta cire, kibari kije naki gidan sai kiyi wannan ikon amma ba anan ba, shasha kin gama yawon barikinki kin dawo sai da kikaga duniya tayi miki atishawarar kuda sannnan zaki jawo jiki ki dawo dayake ke mayya ce, to ahir dinki"
Duk wadannan maganganun da yakumbo take yi ikhlas bata daga ido ta kalleta ba aikin gabanta kawai take yi har yakumbo ta karaci fadanta ta tafi bata koda kalleta ba,
Girki na alfarma ta shiryawa abbanta ta kinkima ta nufi bagarensa lokacin karfe 7 daidai, akan dining ta shirya masa ta juya ta fita zuwa dakinta,
Wanka tayi ta shirya ta fito cikin doguwar riga ruwan dorawa samfarin Arabian gown lokacin har karfe 8 tayi,
Falon abbanta ta koma yana zaune yasha farar shadda mai tsada yana cin abincin data dafa masa,
"Ikhlas sannu da kokari kinji, Allah yayi miki albarka"
Zama tayi akasa tafara gaisheshi, tana nan zaune har ya kammala cin abincin daidai lokacin hajiya Nafi ta shigo fuska ahade,
"Ikhlas zan fita babu komai ko?"
"Abba babu komai amma ina bukatar phone saboda ina son yin waya"
Murmushi yayi yana gyara babbar rigar jikinsa,
"Akwai waya sabuwa tana nan adakina maza shiga ki dauko, tana nan acikin drewar din gadona"
Mikewa tayi cikeda murna domin dama tana son ta kira elmustapha yau,
"Haba Alhaji, wayar nan fa nice nayi maka sautu nace maka wayata tana bani matsala idan ina yin magana ba afiya jiba har sai na daga murya, amma yanzu shine zaka dauka ka bawa yarka?"
"Haba hajiya nafisa kici girma mana kibarwa yarki"
"Bazata ci girman ba, akan me zata ci girma? Nace bazata ci girman ba, kai amadu kaji tsoron Allah, amadu kadaina fifita wannan yar taka akan matarka" yakumbo tafada tana daga bakin kofa atsaye,
"Ina ake yin haka ya tafi mata daraja in banda awajenka dayake kai sallamamme ne sun gama sabauta ka"
Batare da yayi magana ba ikhlas tafito rikeda kwalin wayar a hannunta ta wucesu zuwa dakinta domin harda sabon sim na etisalat ta dauko Wanda tagani ajiye acikin drewar din,
Fada da masifa yakumbo taci gaba dayi sai da tayi mai isarta sannan ta fice tabar falon.
Daki ta koma taje ta jona wayar a charge, takoma gadonta ta kwanta.
Bata tashi ba sai misalin karfe 12 narana, lokacin wayarta tayi full, sim din ta cire tasaka acikin wayar ta dauko number din elmustapha ta saka ta kira,
Ringing biyu ya daga da sallamarshi,
"Yaya barrister" tafada cikin siririyar muryarta,
"Ikhlas, kece?"
"Nice nan yaya, ina anty ni'ima?"
"Tana gida ikhlas ni ina office, yagida ya mutanen gida?"
"Lafiya lau suna gaisheka, idan ka koma gida ka gaida anty ni'ima"
"Zataji ikhlas zan kiraki anjima"
Kashe wayar tayi tana murmushi domin elmustapha yazama wani mutum mai muhimmanci acikin rayuwarta.
Tun daga wannan lokacin kullum cikin kiranta elmustapha yake safe da rana, yamma da daddare, sabon dake tsakaninsu ya sake karfafa har takai ga elmustapha furta mata kalmar so,
Murmushi tayi tashafi gashin kanta wanda ke kwance akan kafadarta,
"Yaya barrister kenan, babu maganar aure atsakaninmu, ni na daukeka a matsayin yaya dan uwa, bazan taba iya hada kishi da anty ni'ima ba domin tayi min halaccin da bazan manta da ita ba"
"Halaccin me tayi miki? Wallahi ikhlas ina sonki dagaske kuma so irin na aure"
"Bawai ki nayi ba, kawai dai kadauka kamar babu aure a tsakaninmu"
Tun daga nan yashiga yimata naci akan ta yarda ta soshi amma taki tace sam babu maganar aure a tsakaninsu ganin taki yarda yasashi hakura ya kyaleta ba dan yaso ba.
_*Ummi Shatu*_ππ»
[12/11, 6:24 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_22_
~~~ Haka zaman Ikhlas yaci gaba da kasancewa agidan mahaifin ta, gata iya gata abbanta yana nuna mata amma tana fuskantar tsana da kyama daga wurin yakumbo da hajiya Nafi,
Gatan da abbanta yake nuna mata ne ya sake hura wutar tsanarta a zuciyoyin su yakumbo, kullum ita ke shiryawa mahaifinta abincin da zai ci, gyaran dakinsa da duk wani abu da ya shafeshi itace keyi da haka har ta cika wata uku da dawowa.
Sanye take cikin riga da wando na Pakistan milk colour, tana sanye da hular roba baka, tunda ta tashi take aikin shiryawa abbanta abin karyawa,
Wani ciwon ciki taji yana turnuketa ba tare data shiryaba, aikin ta bari ta duka tana tafiya ahankali ta shiga dakinta,
Kan gadonta ta hau ta kwanta tana murkususu, wani irin amai take jin yana taso mata dakyar ta iya tashi da gudu ta fada toilet anan ta shiga kwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, amai take kwarawa sosai,
Tajima tana aman kafin ya lafa mata tasamu ta kuskure bakinta ta koma daki ta kwanta, lokaci kankani zazzabi ya lullubeta,
Jinta shiru da abbanta yayi yasashi kiran wayarta, lokacin tayi mutukar galabaita,
Dakyar ta iya daukar wayar ta kara a kunnenta,
"Yar abba har yanzu ba agama shirya abincin ba?"
Cikin muryar rashin lafiya tace "abba bani da lafiya"
"Na'am, iye? Ikhlas meya sameki? Bari nazo" wayar ya kashe cikin tashin hankali,
Ahanyarsa ta fitowa yayi kicibus da hajiya Nafi,
"Alhaji ina zaka kuma? Maganar da muka fara jiya nazo mu karasa"
"Hajiya Nafi ba yanzu ba sai wani lokacin, ikhlas ce babu lafiya"
Yana kaiwa nan yayi gaba hakan ya kular da hajiya Nafi ta nufi sashen yakumbo, tana zuwa tahau fada,
"Gaskiya yakumbo nafara gajiya da cin mutuncin da ake yimin agidan nan, Alhaji yafi bawa yarsa muhimmanci fiyeda ni gaskiya nagaji"
Mikewa yakumbo tayi daga kishingiden da take,
"Yana ina? Muje"
Fitowa sukayi suka nufi dakin ikhlas,
Lokacin da abban ikhlas yaje dakin nata tana kwance sai nishi take yi idonta ya rufe,
"Ikhlas, ikhlas, sannu meya sameki?" Yafada arude,
"Abba cikina ne yake ciwo da zazzabi"
"Bari nakira likita, ina zuwa"
Wayarsa ya dauka yafara neman dr dinshi wanda yake dubashi agida Nigeria,
Hajiya Nafi da yakumbo ne suka shigo kowacce fuskarta babu walwala,
Jin yana yin waya yasasu jiran ya gama,yana gamawa yakumbo tahau fada,
"Amadu yanzu kayi adalci kenan? Ka kyauta kenan? Matarka baka bata muhimmanci kamar yadda kake bawa yarka yanzu kayi daidai kenan?"
"Yakumbo yanzu kuma me nayi?"
"Au tambayata ma kake yi? Yayi maka kyau amadu"
Shigowar likita ce ta dakatar dasu, yana shigowa yafara bincikar ikhlas yana yimata yan gwaje gwaje,
Mintuna kadan ya dago yana kallonsu fuskarsa babu annuri,
"Um yallabai, nagama bincikena wanda ya kamata nayi, am sannan gaskiya Nagano yarinyar nan tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyar"
Ba abbanta ba hatta ita ikhlas din sai da tayi zumbur ta mike batare da tasani ba,
"Likita ciki? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
"Wallahi yallabai abinda nafada haka yake tabbas tana da ciki"
Wani kukan kura abba yayi yaje ya damketa, "ikhlas, ikhlas abin kunyar da kika jawo min kenan? Ashe dama wasikar da kika barmin cewar kin tafi yawon karuwanci dagaske kece kika rubuta? Ikhlas abinda zaki yimin kenan ina dan siyasa shahararre ki bata min suna?"
Tarin da ikhlas tafara saboda shakar da abbanta yayi mata ne ya sanya likitan yin saurin kai mata agaji ta hanyar banbare hannun abbanta daga wuyanta,
"Kabarni na kasheta likita, kabarni na kasheta tun kafin ta bata min takarata, ikhlas kin cuceni kin cuci kanki"
"Alhaji hakuri zakayi Dan Allah"
"Likita fita waje zan kiraka"
Fita dr yayi, yana fita hajiya Nafi da yakumbo suka marmatso kowacce fuskarta dauke da murmushin mugunta.
_*Ummi A'isha*_ππ»
[12/12, 2:18 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_23_
~~~ Cikin takaici da bakin ciki abbanta yake kallonta, bai san lokacin da ya kai mata wani wawan mariba, tuni taga hasken wuta ya gifta ta idanuwanta nan take idonta guda daya yajuye yayi ja ya kumbura,
Rikeshi hajiya Nafi tayi tana cewa "a'a Alhaji karka illatata"
"Ai gwanda ya illata ta kowa ya huta, yarinyar nan nema take ta bata masa suna agari" yakumbo tafada tana hararar ikhlas,
"Hajiya Nafi ikhlas tana neman tayi min sanadin da yan adawa zasu samu galaba akaina, labarin nan yana fita yan adawa zasu fara yimin yarfe wanda daga karshe zai janyo min rashin nasara azaben da za a gudanar"
"Kayi hakuri Alhaji yanzu kawai hanya mafi sauki ka kira likita ya zubar da cikin nan tun kafin zance ya yadu agari yan adawa su samu hanyar cin mutuncinka agidajen radiyon dake kasar nan"
Lekawa abba yayi ya kira dr, yafara yi masa bayanin azubar da cikin, ita dai ikhlas tana zaune akan gadonta tana gursheken kuka,
"Alhaji zubar da cikin nan akwai hatsari domin yakai wata biyar..!"
"Ya isa dr nidai kawai kayi abinda nasaka" abba yafada cikin tsawa,
Jiki na rawa dr ya debo wasu manyan kwayoyi guda takwas ya mikawa ikhlas,
Cikin kuka ta karbi magungunan, "hajiya Nafi Miko ruwa, miko ruwa"
Dasauri hajiya Nafi taje ta dauko robar ruwa tana murmushin jin dadi,
"Wannan yarinya baki yiwa kanki dabara ba, kin cuci kanki, koda yake banyi mamaki ba duba da irin takardar da kika bari kafin ki tafi yawon karuwancin" yakumbo tace da ita cikin isgili,
Shiru ikhlas tayi batace komai ba sai hawaye saboda tasan koda tayi magana abbanta ba saurararta zaiyi ba awannan lokacin,
Allura guda uku likita ya sake zuka ya nutsa mata, nan take taji jiri yana daukarta ga mararta ta turnuke da ciwo, babu shiri ta kwanta tafara murkususu,
"Gara ki mutu ma mu huta" hajiya nafi tafada acikin ranta,
"Dr dan Allah ka rike min sirrin nan bana son maganar nan tafita waje har yan adawa suji" abbanta yafara rokon dr,
"Kar kaji komai yallabai insha Allah babu wanda zaiji"
Ganin mutane bibbiyu ikhlas tafara sai kuma taji fitar wani abu daga jikinta, take jini ya balle kamar an bude fanfo,
Zaro ido dr yayi,
"Yallabai ina jin ansamu matsala"
"Likita babu damuwa muddin cikin zai fita toni bukatata ta biya"
"Wayyo abba, wayyo cikina" ikhlas tafada cikin nishi, babu wanda ya kulata acikinsu suka juya suka firfice daga dakin.
Falo sukaje suka zazzauna jigum yayinda yakumbo itada hajiya Nafi suka dage suna zuga abban ikhlas suna dada tunatar dashi wasikar da ikhlas din tabar masa tsawon shekaru 5 da suka gabata.
Kimanin awa daya suna zaune suna tatrauna maganar, dr ne yasake komawa dakin da ikhlas take ciki tana kwance bata ko motsi, iya tsorata dr ya tsorata nan take yafara bata taimakon gaggawa, gashi ta zubar da jini da yawa kuma hankalinta da alama baya jikinta,
Falo ya fita da sauri inda su yakumbo suke,
"Yallabai yarinyar nan tana bukatar ruwa da jini"
"Dr kaje ka samo duk abinda ake bukata nidai burina cikin nan yafita indai yafita zan iya kashe ko nawane"
Hannu yasa acikin aljihunsa ya ciro rafar yan dari biyar biyar ya mika masa,
Dasauri likitan ya fice domin zuwa samo jinin da ake bukata da ruwa,
"Wannan yarinya ta gama cin mutuncinmu" yakumbo tafada tana rike haba,
"Kanta taciwa mutunci amma baniba" abban ikhlas yafada ahargitse,
Cikin mintunan da basu wuce 20 ba dr ya dawo dauke da jini leda hudu da ruwa shima leda hudu ga magunguna cikin leda,
Dakin da ikhlas take ya shiga har lokacin bata motsi,
Ruwa ya daura mata ahannun damanta hannun hagun kuma ya daura mata jini,
Har jinin ya kare da ruwan aka sake daura wani bata dawo hayyacinta ba, gashi jini bai tsaya ba,
Yinin ranar sunyi shine cikin tashin hankali, misalin karfe 5 na yamma likitan yabar gidan da niyyar zai dawo da daddare, babu wanda ya sake komawa dakin da ikhlas take balle yaga halin da take ciki.
Karfe 6 ta bude idonta wanda ya ke dishi dishi, jinta tayi ajike, hakan ne yasata tuno da abinda yafaru da ita, wani rikitaccen kuka ta saki tana hadiyar dunkulen bakin cikin daya tokare mata makogaro,
Dakyar ta iya shiga bathroom gaba daya jikinta yagama jikewa da jini ga wani jinin da yake zuba guda guda manya manya,
Kuka kawai takeyi tana gyara jikinta, wanka tayi da ruwan zafi sannan tafito har lokacin jinin bai tsaya ba.
Komawa tayi ta kwanta tana kuka mai ban tausayi, karfe 9 sai ga abbanta da dr da su yakumbo sun shigo cikin dakin,
Rufe idonta tayi tamkar mai bacci,bincikarta dr yayi yajuyo yana duban su abbanta,
"Yallabai ni ina ganin ayi hakuri akarbi wannan kaddarar kawai domin idan muka matsa yarinyar nan tana iya rasa rayuwarta gaba daya"
"Dr ban fahimceka ba.." Abba yafada cikin rawar baki,
"Gaskiya Alhaji am sorry to say wallahi har yanzu cikin nan bai fitaba yana nan ajikinta gashi tasha wahala ba kadan ba"
"Likita babu ruwanmu da wahalar data sha kawai mu bukatarmu ka fitar da cikin jikinta kota halin yayane, waye yaturata taje tayi cikin, ba ita takai kanta ba" yakumbo tafada cikin masifa,
Sake runtse idanuwanta ikhlas tayi tana mai jin tausayin kanta tareda tsanar wanda yayi mata sanadin shiga cikin wannan kuncin.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/12, 2:18 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga K'awata KHADIJA SIDI_
_24_
~~~Wani irin bakin ciki take ji yana ratsa cikin zuciyarta,
"Wannan wacce irin masifa ce ta sameni? Daga fyade sai ciki, innalillah hakika bazan taba yafewa wanda yayi sanadiyyar shigata cikin wannan bakin cikin ba" tafadi hakan acikin ranta,
Hankalinta ne yadawo jikinta sakamakon jiyo muryar abbanta da tayi yana cewa,
"Likita ka sake bata wannan maganin mana irin na dazu ko zamu yi nasara cikin ya zube"
"A'a Alhaji yin haka komai zai iya faruwa saboda kaga shi wannan maganin aka'ida ba ashan fiyeda guda biyu ita kuma kaga har guda takwas nabata, over doze din yayi yawa gaskiya"
"To yanzu likita menene shawara?
"Yawwa ni ina ganin akyaleta yanzu ta huta zuwa nanda kwana biyu inyaso idan har lokacin cikin bai zubeba sai nasake bata wasu kwayoyin"
"To shikenan dr nagode"
"Yawwa sannan yanada kyau abata abinci taci"
"Hajiya Nafi kawo mata abinci"
Fita dukkaninsu suka yi daga cikin dakin hajiya Nafi tawuce kitchen ta zubowa ikhlas tuwon shinkafa miyar agushi, lokacin data shiga cikin dakin ikhlas ta tashi zaune tana tunani idonta yana zubar da kwalla,
"Ai bakiyi kuka ba tukunna har sai ubanki yayi miki korar kare daga gidan nan, yanda uwarki tabar gidan nan dole kema sai kin barshi wlhi"
Dagowa ikhlas tayi tana kallonta, hakika dama tunda jimawa tasan hajiya Nafi da yakumbo basa kaunarta amma wannan abin da yafaru ya sake tabbatar mata irin kiyayyar da suke yi mata, abincin hajiya Nafi ta gara mata ta juya tayi tafiyarta,tana cin abincin tana kuka har ta gama,daren ranar kuwa duk iya sata ta bacci haka yaganta ya kyale.
Kwananta biyu acikin mawuyacin hali na lalura domin har yau jinin dake zuba ajikinta bai tsaya ba, aranar dr yadawo,
Shida abbanta ne suka shigo cikin dakin da take, ganinsu yasata tashi zaune,
"Dr kaje ka dubata idan cikin yana nan har yanzu to kayi duk yanda zakayi ka fitar dashi da karfi"
Arazane ta dago ta kalli abbanta, "Abba na rokeka da girman Allah ku kyaleni haka ni nadauki kaddarar da Allah ya doro min, nasan abinda kake tsoro abba tsoron kar maganar nan tafita gari yan adawa suyi maka dariya kake, abba ka taimake ni ka sanar dani inda mahaifiyata take wacce ka rabani da ita tun ina yar shekara 5 aduniya, kasanar dani inda take zan tafi nabar maka gidanka ta yanda ma babu Wanda zai san abinda yafaru da yarka"
Kuka take wiwi kamar ranta zai fita,
"Dr wai me kake jirane? Kayi abinda na umarceka"
"Yallabai ka duba maganar da yarinyar nan take yi" Dr yafada,
Juya baya abba yayi "da narasa kujerata da nake nema gara kin tattara kin bar gidan nan tabbas, ikhlas yau zan fada miki inda mahaifiyarki take, mahaifiyarki tana jihar Borno acikin miduguri a unguwar zumar, indai kikaje nan to duk wanda kika tambaya gidan shuwa babu wanda bai sani ba domin duk unguwar gidansu ne kadai shuwa Arab"
Saukowa tayi daga kan gadon tana hawaye,"abba kayafe min dan Allah nasan nasaka bakin ciki amma kayi hakuri ka gafurceni, sannan nagode yau da sanar dani da kayi inda mahaifiyata take zanje zan nemeta ita da sauran yan uwana"
Ba karamin tausayi tabawa dr dinnan ba, kayan aikinsa ya hada yayiwa abbanta sallama ya fita,
Akwati ta jawo tafara loda kayanta aciki tanayi tana kuka har ta kammala taja akwatin bayan ta yafa mayafinta,
Rafar yan Dubu Dubu guda biyu abbanta ya watsa mata ya juya ya fice daga cikin dakin,
Akwatinta taja har zuwa falo tana share kwallar idonta, yakumbo tagani da hajiya Nafi tsaye suna kallonta,
"Allah ya raka taki gona dangin munafurci da bakin rai, irida maita" yakumbo tafada tana harararta,
"Allah yaraba lafiya, ayi rainon ciki da goyo lafiya sai munzo suna" hajiya Nafi tace da ita tana shewa,
Akwatinta taja ta kara Sauri tafice daga falon tana kuka, bata sake koda waiwaye ba har tabar gidan tafita gate ma'aikatan gidan da jami'an tsaro sai kallonta suke tana tafe tana kuka,
Abakin titin kofar gidansu tayi sa'a ta samu taxi nan ta saka jakarta aciki ta shiga tace da mai motar ya kaita tasha, har lokacin kukan bakin ciki da bacin rai take yi wanda ji take inama ta mutu ta huta da wannan takaicin rayuwar.
Tafiyar minti ishirince ta sadasu da tashar mota tana zuwa ta samu motar da zataje Borno dama motar ta cika yanzu mutum daya suke jira dan haka koda taje aka saka kayanta a motar shirin tafiya kawai driver din motar yayi nan da nan suka harba titi,
Kanta ta kwantar akan cinyoyinta tana kuka marar sauti sakamakon halin data samu kanta aciki, abbanta yana sonta yana kaunarta kuma yana nuna mata soyayya akoda yaushe amma yanzu ya juya mata baya sakamakon kaddarar data afka mata ya kasa hakuri ya rungumi kaddarar da Allah ya aiko musu domin yana gudun kada takararsa ta lalace.
_*Ummi Shatu*_ππ»
[12/13, 12:19 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata KHADIJA SIDI_
_25_
~~~Har suka bar Zaria suka kama hanyar Borno bata dago kanta ba tana sunkuye tana kuka gamida tsanar halin data samu kanta aciki,
Tunda suka dauki hanya basu tsaya ba har azahar tayi alokacin ne mai motar ya tsaya domin su gudanar da salla, cincin ta siya guda biyu manya wanda dakyar ma ta iya ci saboda tsananin bacin rai ita yanzu tunaninta daya shin tayaya zata fuskanci mahaifiyarta da wannan tashin hankali, agaskiya tasan bata yiwa mahaifiyarta adalci ba domin bataje mata da wani abu wanda zai sakata farin ciki ba sai ma sabaninsa.
Karfe 6 daidai na yamma suka shiga cikin garin Maiduguri, kwatancen da abbanta yayi mata tabi dan haka bata sha wata wahala ba tasamu mai taxi din da zai kaita har gidansu mahaifiyarta,
Banda faduwar gaba babu abinda ikhlas take yi musamman ma da taga sun shigo layin da zai sadasu da gidansu mahaifiyarta,
Adaidai kofar gidan mai taxi ya ajiyeta yana cewa,
"Yawwa mun karaso hajiya"
Kudinsa tabashi ta tsaya tana kallon gidan, babban gidane wanda yasha gini irin na zamani, tabbas dama ta dade da sanin mahaifiyarta yar babban gidace domin mahaifinta yana daya daga cikin manya manyan attajiran garin sannan yayyun mahaifiyarta suma dukkaninsu masu hannu da shuni ne,
Kinkimar jakarta tayi ta tasamma cikin gidan kirjinta yana dukan tara tara, tana shiga taga bangare bangare wanda zasu kai kusan guda biyar,na hannun damanta tabi ta shiga, wata yar dattijuwa ta hango fara sol kamar balarabiya tana alwala atsakar gida,
Da sallamarta ta shiga amma duk jikinta asanyaye yake,
Barin alwalar dattijuwar tayi ta dago ta zubawa ikhlas ido kafin tayi magana da karfi tana nunata,
"Ikhlas ko?" Matar tace da ita,
"Ehh" ikhlas ta mayar mata da amsa tana dan murmushi,
"Ikon Allah, yau kece agidan, zo muje, taho taho, lale lale"
Bin bayan dattijuwar ikhlas tayi zuwa wani bangare nagaba kadan da Wanda matar take ciki,
"Shigo ikhlas yau kece, shiyasa dama nake ta fadawa maman naki tayita hakuri duk daren dadewa zaki nemeta to yanzu ba gashi ba kinzo da kafarki"
Ita dai ikhlas binta kawai take har suka shiga cikin falo anan ta hango mahaifiyarta tana salla, jakarta ta ajiye ta samu wuri ta zauna tana bin falon da kallo,
"Zauna ina zuwa bari naje nadawo" dattijuwar tace da ita tareda ficewa daga cikin falon, tana nan zaune har mahaifiyar tata ta idar da sallar ta jiyo tana kallonta,
"Ikhlas" mahaifiyarta ta kira sunanta cikin mamaki,
"Na'am ammi...." Da sauri ta tashi ta karasa inda take zaune tafada jikinta tafara kukan farin ciki, rungumeta mahaifiyar tata tayi itama tana fitar da kwalla domin rabonta da yar tata tun tana yar shekara biyar aduniya,
"Ikhlas waye ya kawoki?",
"Ammi ni kadai nazo"
Sake rungume juna sukayi, amminta tana kankame da ita tamkar wata jaririya, hawaye kawai ikhlas take fitarwa hakika uwa itace gatan danta shiyasa duk Wanda ya rasa uwa dole yayi kuka,
"Tashi kiyi salla ikhlas sai kici abinci ko"
Janye jikinta tayi daga jikin ammi tana goge hawayen fuskarta,
Daukar mata jakar ammi tayi suka shiga cikin dakin baccinta, alwala tashiga toilet ta dauro tafito tazo tayi salla duk akan idon mahaifiyarta domin tana zaune abakin gado tana kallonta,
Godiyarta tafara kaiwa wurin ubangiji da yabata ikon ganawa da mahaifiyarta,Shafa addu'ar tayi ta tashi ta matsa kusa da ammi,
"Ina wuni ammi"
"Lafiya lau ikhlas, ya mutanen gida, kinzo lafiya, ina abban naki?"
"Lafiya lau ammi"
"Sannu da zuwa"
Mikewa tayi ta isa inda kwanukan abinci ke jere ta dauko mata kwano guda biyu tazo ta ajiye agabanta,
"Ga abinci kici"
Bude abincin tayi biskine aka dafashi wara wara ga miyar kuka agefe wacce tasha busasshen kifi da man shanu nasha nasha, take taji kwadayinta ya motsa abinku da mai ciki,
Bararrajewa tayi tafara kwasar abincin tana yiwa ammi hira gamida tambayar yayunta yan biyu Hassan da Hussain,
"Sai anjima zaki gansu dazu suka fita cikin gari"
"Ammi sun gama karatu?"
"Sun gama karatu mana ikhlas yanzu aiki suke nema"
"Allah yasa su samu ammi"
"Amin"
Tana kammala cin tuwon ammi ta kama hannunta suka fita tafara bin kofa kofa ta gidan tana shiga da ikhlas tana nuna musu ita, kowa sai mamaki yake na girman ikhlas lallai akwana atashi babu wuya, kowacce kofa dake gidan sai da suka shiga hakan yasake gajiyar da ikhlas dan haka koda suka dawo dakin ammi gadonta kawai ta haye ta kwanta tana jin wani farin ciki yana ratsata domin tuni ta dade da manta damuwar da take dauke da ita.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/13, 12:19 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata Khadija Sidi_
_26_
~~~Agefenta ammi ta zauna tafara matsa mata kafafunta tana cewa,
"Har yanzu kina yin wannan ciwon kafar ne kamar lokacin da kina yarinya?"
"Ammi ciwon kafa kuma?"
"Lokacin da kina yarinya kina yawan yin ciwon kafa dan har asibiti nake kaiki duk azatona sikila ce dake domin alokacin ma abbanki cewa yayi kasar waje zai fitar dake adubaki to kuma har nabar gidan bai fitar dake ba" share Yar kwallar data tarar mata agefen ido tayi bata bari ikhlas din tagani ba,
"Ammi yanzu dai banayi nawarke"
"To ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi sai kiji dadin jikinki"
"To ammi ki kyaleni na dan sake hutawa"
"To huta"
Cigaba da matsa mata kafarta ammi tayi har aka fara kiraye kirayen sallar isha,
Sai alokacin ikhlas ta mike tashiga bathroom tayi wanka tafito yanzu jinin dake fita a jikinta ya dan ragu sai dan digo take gani sabanin da wanda kamar an bude fanfo,
Mai ta zauna ta Shafa tana kallon ammi wacce ke salla agefenta,
Wasu riga da wando marassa nauyi ta dauko ta saka ta tashi domin yin sallar isha,
Tana cikin yin sallar ne ta jiyo sallamar yayunta yan biyu, sauri tayi ta sallame ta kwasa zuwa falo,
Kamarsu daya ba ataba banbancesu komai nasu iri dayane gasu kyawawa farare masu hanci, tamkar taje ta rungumesu take ji,
Su dinma tsayawa sukayi suna kallonta,
"Ammi wacece wannan?" Hussain ya tambaya yana kallonta,
"Nima ban santa ba" ammi ta bashi amsa cikin barkwanci,
"Hassan ka ganeta? Ikhlas ce kanwarmu, wallahi itace, kalli gefen goshinta inda ta ji ciwo da scissors lokacin da ammi tana koyon dinki"
"Wallahi itace kam" hassan yafada yana mika mata hannu, hannunsu ta kama tana murmushi sai kuma suka fara kuka gaba dayansu,
Ammi ce tayi karfin halin rarrashinsu har suka hakura sukayi shiru suka shiga hirar yaushe gamo? Sun dade tare suna hira har sai da karfe 2 nadare yayi sannan kowa ya hakura ya nufi makwa cinsa,ita dai ikhlas bayan ammi taje ta rungumeta ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
*
Abangaren Lamido kuwa tunda ya tafi kasar Kenya kullum cikin damun bash yake awaya ko ya gane masa pretty dinshi, amma koda yaushe amsar bash guda dayace,
"Ban ganta ba ni nama manta kamanninta"
Dafe kai Lamido yayi yana tunaninta acikin zuciyarsa shidai yasan ko zai manta wata ya mace to banda pretty domin tazama wani sashe na rayuwarsa,
Tsoron Baffa ne kawai ya hanashi dawowa gida domin yace bai yarda yazo gida ba har sai ya gama karatunsa wato shekaru uku kenan, dakyar ya samu yayi masa sassauci ya yarda yazo ganin gida idan yayi shekaru biyu acan,
"Pretty a ina zan dada ganinki? Idanuwana suna son ganinki koda kuwa acikin mafarkine, pretty wallahi ina sonki"
Kullum haka yake furtawa tamkar wani zararre hakanne ma yasa bash gama yarda da cewar Lamido ya samu tab'i a brain dinshi kuma ita wannan mahaukaciyar ba mutum bace aljana ce.
Wayarshi ya jawo yashiga kiran bash dama video call suke yi akullum,
"On top ya?" Bash yace dashi yana murmushi,
"Bash kasan dai maganar gizo kullum bata wuce ta koki, dan Allah bash ka taimakeni, wallahi ni idan nadawo gida yanzu raina in yayi dubu sai ya baci kasan dai irin fadan Baffa musamman ma akaina, nafi kowa laifi agidan nan"
"Lamido magana ta gaskiya wannan yarinyar ba sake ganinta zakayi ba dan haka kacire ran kara sake haduwa da ita acikin rayuwarka?"
"Dan Allah dakata min, waye ya fada maka bazan sake ganinta ba?" Lamido yafada azuciye domin shi mutumne mai zuciya da zafin rai,
"Saboda aljana ce, Lamido ko kaso ko ka ki wallahi sai nafada maka gaskiya, wannan yarinyar aljanace kawai ta zautar da kai ne,in banda haka tayaya daga haduwa da ita sau daya zaka mace asonta har kana ikirarin ka tsani kowacce mace sai ita kadai kake so"
"Kaga malam da Allah kar ka bata min rai, sai anjima"
Katse wayar Lamido yayi yana tsaki ransa duk yagama baci sam baya son yaji bash ya kira pretty da aljana saboda shi yasan ba aljana bace mutumce sannan shi kansa yana son ya cireta daga cikin zuciyar tasa amma hakan yaki yiyuwa domin tagama mamaye dukkan sansan hanyoyin jinin jikinsa.
_*Ummi A'isha*_ππ»
[12/14, 10:27 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_27_
~~~Kullum Lamido cikin tunanin prettyn shi yake duk yabi ya zauce domin shi kadai idan yana zaune sai kaji yana magana ahankali,
"Pretty dan Allah ki sake bayyana agareni wallahi ina sonki, wai baki san yanda sonki yake neman illata rayuwata bane"
Kullum cikin fadin haka yake gashi da farin jinin yanmata duk inda ya shiga mata na sonshi suna bibiyarshi amma wani lokacin yakan tuna hudubar bsffanshi wacce yayi masa lokacin da zai bar gida kan ya kula da kansa ya daina yawon bin mata ya daina shan kodin, hakan da yake tunowa ne wani lokacin sai yaji jikinsa yayi sanyi.
Haka lokaci yaci gaba da tafiya batare da Lamido yaji labarin pretty ba kamar yadda yake kiranta, kullum bash shawara yake bashi akan yayi hakuri ya cire yarinyar nan daga cikin zuciyarsa amma ya gagara, wani lokacin idan ya zauna shi kadai a bedroom dinsa sai ya dauko hotonta ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar surarta, Allah ya bata duk wata cikakkiyar sura da ake bukata awurin ya mace amma kuma sai ya gusar da hankalinta,
Tsintar kansa kawai yayi yana mai zubar mata da hawayen tausayi,
"Pretty da ace Allah zai sake hadani dake da zan aureki ahaka zan nuna miki gatan da ba ataba nunawa wata ya mace ba afadin duniyar nan kamar yadda SULTAN ya nunawa fatinshi, wallahi da sai kin zama tauraruwa acikin mata fiyeda yadda Lamin ya mayar da Junada acikin MACE GUDA DAYA TILO, zan soki ahaka zan rayu dake ahaka kuma zan nuna miki soyayya ahaka fin wacce umar faruk ya nunawa KAUSAR YAR AUTAR MATA,da sai kin zama abar kwatance kamar yadda jawad ya mayar da pherty acikin MARTABA TA,ke kadaice matar da naji ina son kasancewa da ita samada yadda Awwab ya kasance da Nihal cikin KWARYA TABI KWARYA, soyayyar da nake miki tafi wacce Hakeem yayiwa Ayshanshi cikin BIYAYYAR IYAYE, zan baki kulawa irin wacce Junior ya bawa jiddanshi cikin SANADIN GATA, domin na tabbatar ke bakiyi kamada Muhibbat din Yasir ba ta cikin AURE YAKIN MATA, tabbas kin fi sameenat iya tarairayar miji domin ita tsabagen sakacinta yasa zaid auro mata yar aikinta acikin RUWAN DARE, kullum addu'a ta Allah ya mallaka min ke na rayu dake kwatankwacin yadda Abbu ya rayu da bintinshi cikin WANI HASKE hakika kema haske ce agareni pretty"
Yafada yana share kwallar idonshi, haka rayuwarshi taci gaba da kasancewa har ya shafe kwanaki masu yawa a kasar Kenya, alokacin ya dan rage surutai akan pretty amma kuma sonta da kaunarta yana nan makale acan kasan zuciyarsa, gashi yaci gaba da hallayarshi ta shan kodin domin anashi ganin hakane kadai hanyar da zaibi wurin rage damuwar dake addabarshi, neman mata kuwa ba koda yaushe yake yiba sai dan jifa jifa amma wani abu da bai sani ba shine duk wadannan abubuwan da yake yi ana sanar da baffansa domin dama ya baza c.I.d akansa.
*
Tunda ikhlas ta koma wurin mahaifiyarta ta tsinci kanta acikin rayuwa mai dadi, kullum cikin tarairayarta ammi take itada yayunta da duk sauran mutanen gidan ga kakarta mahaifiyar ammi itama kullum suna tare Suna tsokanar juna irin wasan jika da kaka dan haka tuni ikhlas ta manta da wata aba wai ita damuwa, nan da nan ramar da tayi ta bace ta ciko tayi bul da ita.
Yau satinta uku da zuwa Suna zazzaune acikin falon ammi itada da yayunta hassan da Hussain da ammi, hira suke yi sosai ammi tana basu labarin irin rayuwar da suka yi da mahaifinsu da kuma uwar mijinta da kishiyarta har kawo sanadin data baro gidan,
Dukanninsu babu wanda bai ji tausayin ammi ba, kallon ikhlas ammi tayi,
"Ke kuma wacce irin rayuwa kikayi dasu? Dan nasan yakumbo bata kaunar jinina bazata taba sonki ba"
"Hakane ammi hakika yakumbo bata kaunarmu abbanmu kadai take so ban taba ganin uwar da take son danta amma bata son jininsa ba sai akan yakumbo...!". Labarin irin rayuwar da tayi tashiga sanar dasu har haukan da tayi da kuma abinda ya faru wanda yayi sanadiyyar tahowarta wurin ammi,
Kuka ammi take sosai, hankalinta idan yayi Dubu to duk ya baci, ba ita ba harta hassan da Hussain ma labarin ya girgizasu amma duk abinda yafi firgata su shine jin wai ikhlas tana dauke da juna biyu ahalin yanzu har na tsawon wata biyar.
"Ammi kiyi hakuri ki daina kuka,mu taru mu nemo mafuta acikin wannan al'amari kawai" Hussain yace da ita,
"Hussain wacce mafita kuma, nidai yakumbo da Nafi sun gama cutata kuma in Allah ya yarda sai Allah yayi min sakayya" ammi tafada cikin kuka,
"Ni anawa ganin idan dare yayi kawai mu dauki ikhlas mu kaita private hospital azubar da cikin nan domin wlhi haifeshi babbar tawayace acikin rayuwarta, idan ta haifi cikin nan mijin aure ma sai ta rasa" inji Hussain,
"A'a hussain, gaskiya wannan ba shawara bace saboda karfa muje garin gyaran gira mu rasa ido, ina nufin kar muje garin zubar da cikin nan mu rasata gaba daya" hassan yafada,
"To kana nufin barinta zamuyi ta haifi dan shege?" Hussain yafada cikin kufula domin dama shi mutumne marar hakuri ga zuciyar tsiya hassan yafishi hakuri,
"To akanta aka fara? Ba kaddara bace?" Hassan yabashi amsa,
"To wlhi bazai yiyuba bazata Haifi dan shege ba balle azo ana nunata da baki kuma shima dan azo ana yi masa gorin uba wata rana" hussain yafada yana huci,
"Yaya hussain dan Allah kar ku kaini wurin zubar da cikin nan wallahi zan iya mutuwa dan bakuga wahalar dana sha bane a Zaria lokacin da abba yasa azubar da cikin" ikhlas tafara rokonsa tana kuka,
Tashi hussain yayi afusace "zan tattakaki idan kika sake magana, haka kikeso mu zuba ido muna ji muna gani rayuwarki ta samu nakasa? Banza shashasha ana son ayi miki gata kina bujirewa"
Ammi na zaune tana kallonsu har lokacin bata iya cewa ko uffan ba.
_*Ummi Shatu*_ππ»
[12/14, 10:27 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_28_
~~~Jugum ammi tayi tana saurarensu ga kuma sautin kukan ikhlas wanda ya cika falon,
"Kaga hussain kayi hakuri ka mayar da wukar, yanzu me kakeso ayi?" Hassan ya dafashi yana tambayarsa,
"Zan kira dr za azubar da cikin nan kawai" hussain ya bashi amsa,
"To shikenan kirashi" inji hassan,
Tashi hussain yayi ya fita, sai alokacin ammi ta goge hawayen idonta tafara magana,
"Shi hussain yanada wata irin zuciya wlhi,idan ma an hanashi baji zaiyi ba ni bana son a salwantar min da rayuwar ya"
"Babu komai ammi bari dai muga zuwan dr din tukunna sai muji abinda zaice" hassan yace da ammi yana kallon ikhlas cikeda tausayawa,
"Ammi ni da yaya hussain ya barni, nahakura na dauki kaddara domin na tabbatar wannan jarrabawa ce daga Allah, nayi tawakkali kuma hakika Allah yana tare da masu tawakkali domin ya fada mana hakan acikin littafinsa mai tsarki acikin suratul D'alaq, yace
_"'Waman yatawakkal alal lahi fahuwa hazbuh, ma'ana duk wanda yayi tawakkali da Allah to Allah ya isar masa"'_
Dan haka abar maganar zubar da cikin nan haka dan Allah"
Jawota ammi tayi zuwa jikinta ta rungumeta,
"Babu komai ikhlas ni bazanyi miki irin yanda mahaifinki yayi miki ba wato na juya miki baya, a'a nima zan yi kokarin tayaki karbar kaddarar da Allah ya aiko miki, Allah yayi miki albarka, hakika da yawa daga cikin wadanda suke haduwa da kaddarar cikin shege har suke kashe Kansu to ba dan gudun abin kunya suke yin haka ba suna kashe Kansu ne sakamakon kyamata,tsana, cin zarafi da suke fuskanta daga magabatansu,alhalin kuma duk wanda ya kashe kansa to ya mutu kafiri, nikam bazan taba kyamatarki ba yata"
Rungume juna sukayi suna kuka, shi kansa hassan dake zaune shima kwallar yake yi,
Suna nan zaune hussain ya dawo shida wani likita dan tsamurmuri,
Nuna masa ikhlas hussain yayi, nan likitan ya matsa kusa da ita yafara dan duddubata har na tsawon minti goma kafin ya jiyo ga hussain,
"Hussain wannan cikin yawuce ace za a zubar dashi domin yayi kwari, idan kuma muka dage akan hakan to gaskiya zata iya rasa rayuwarta"
"Dr munir yanzu babu wata dabara da zaka iya yimana?"
Girgiza kai dr munir yayi, "wallahi babu hussain domin muna zubar da cikine idan yana wata daya, biyu ko uku amma muddin yakai wata hudu ma bama iya zubarwa saboda hakan zai haifar da matsala balle wannan wanda har yakai watanni shida babu kwana kadan"
"Ok, babu damuwa munir nagode"
Mikewa sukayi da likitan suka fita tare ammi tabisu da kallo,
Hussain ne ya dawo shida mahaifiyar ammi wato hajiya kakarsu,
Ganinsu jugum yasa hajiya cewa "meya sameku ne kamar masu zaman makoki?"
Hussain ne ya sanar da ita duk abinda yake faruwa nan tafara tafa hannu tana salati,
"Kanaji hussaini ita kaddara ana gudunta ne kafin ta zo amma da zarar tazo to hakuri ake yi arungumeta hannu bibbiyu, wannan abu kaddara ce kuma zamu karbeta Allah yasa mu samu sakamakonta gobe kiyama, yanzu abinda zai faru ai duk gidan nan babu wanda yasani ko? To zanbi duk na farfada musu cewar ikhlas babanta aure yayi mata akauye gashi yanzu mijin ya sakota shiyasa ta dawo nan"
"Yawwa hajiya, wannan shawarar tayi" hassan yafada yana murmushi,
"Lallai naka sai naka duk wanda zai rufa maka asiri bayan naka zai biyo" ikhlas tafada acikin zuciyarta,
"Haka yayi Allah ya rabasu lafiya, babu komai mu zamu riketa kuma zamu rike duk abinda zata Haifa zamu zame masa uba" hussain yafada yana goge kwallar data taru a idonsa,
"Allah yayi muku albarka yasake hada kanku"
Shine abinda ammi tafada kawai, fita hajiya tayi duk taje ta farfada agidan cewar ashe ikhlas ciki ne da ita mijinta ya sakota, tun daga lokacin kowa agidan yake bawa ikhlas kulawa gashi abinci kullum ana kawo mata daga kowanne bangare na gidan.
Yanzu ta saki jikinta hankalinta ya kwanta kuma ta murmure tayi kyau sosai, cikin jikinta kuwa sai dada girma yake tamkar wacce zata haifi yan biyu,
Cikinta yanada wata takwas yayunta hassan da hussain suka samu aiki a state government, murna wurinta ba acewa komai, salary dinsu na farko da suka dauka kayan baby's sukaje suka jibgo mata suka iyo mata siyayya mai tarin yawa hatta kayan wasan babyn sai da suka siyo.
Ammi itace take kaita asibiti awu ko hajiya kakarta,duk wanda yaga cikin nata sai ya sake kallonta domin kamar wacce zata haifi yan uku haka yake dan tsabar girma, kulawa sosai ammi da yayyunta suke bata wacce bata samuba daga mahaifinta.
Watan cikin tara da kwana goma ta tashi da nakuda awata ranar juma'a,
Hajiya ammi ta kira suka kira hussain suka dauketa zuwa wani private clinic, suna zuwa ko minti ishirin batayi ba ta haifo santalelen yaronta namiji kyakkyawa dashi fari sol kamar balarabe,
Tunda akayiwa yaron wanka taji nurses din na tambayar ina abban yaron domin suyi masa albishir, gashi sai yaba kyawun yaron nurse din suke tayi, babu abinda kake ji sai,
"Woww, beautiful boy"
"Ba ataba haifar kyakkyawan yaro a asibitin nan mai kyawun wannan yaron ba"
Hawaye tafara fitarwa, tunani take yi aranta yanzu idan yaron nan ya girma ya tambayeta ina mahaifinsa me zatace dashi? Sai tace masa fyade aka yi mata tasamu cikinsa?
Barkewa tayi da wani sabon kukan mai mutukar ban tausayi.
_*UMMI A'isha*_ππ»
[12/15, 9:53 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_29_
~~~Kuka taci gaba dayi ko kallon inda jaririn yake ba tayi ba,
Kawo mata jaririn nurses din suka yi suna ta yaba kyansa,
"Maman boy ga yaronki, kyakkyawa mai koshin lafiya gashi big" daya daga cikin nurses din tafada,
Bata jiyo ba kuma batayi magana ba sai uban kuka take yi marar sauti, agefenta suka kwantar mata dashi domin duk azatonsu bacci take yi kasancewar anyi mata allurar bacci,
Tana jinsu suka fita daga cikin dakin da take sunata yaba kyawun jaririn, har bacci ya dauketa bata juya ta kalli yaron ba tana jinsa dai yanata mutsul mutsul a inda aka kwantar dashi.
Baccin awa biyu tayi ta tashi lokacin jaririn yana kuka, bata juya ba amma tana jin kukan har cikin ranta,
Wata nurse ce ta shigo da Sauri tana tambayarta,
"Maman boy baki tashi bane? Ki tashi ki bawa boy abinci"
Kin juyowa tayi tai shiru hakan da tayi ya sanya nurse din tabata tana girgizata amma fur taki motsawa, suna cikin wannan dramar su ammi suka shigo itada hajiya da hussain,
"Yawwa gwanda da kuka zo, maman boy taki bawa jariri nono" nurse tace dasu tana kokarin fita daga cikin dakin,
"Haba ikhlas ya za ayi ki hana danki nono? Menene amfanin hakan?" Inji hajiya ta fada tana kokarin daukar yaron,
"Rashin hankali mana in banda rashin hankali shi jariri ina ruwansa yasanma abinda ya faru da har zaki huce akanshi?" Ammi tafada cikin fada,
Jin haka yasa ikhlas rushewa da wani sabon kukan mai sauti,
Rarrashinta hajiya da ammi suka fara yi,
"Yi hakuri ikhlas kinji, kika yi juriyar rainon cikinsa ma har kika haifeshi balle shayar dashi, kiyi hakuri ki karasa ladanki kinji" ammi tace da ita tareda dafa kafadarta,
"Ammi ban son ganinsa dan Allah kuje ku kaishi gidan marayu ko ku yar dashi.." Tafada tana kuka,
"A'a ikhlas ko daya ba za ayi haka ba, dayawa daga cikin yaran da suke tasowa babu tarbiya babu tausayi a zukatansu to wadanda akayi cikinsu aka kasa daukar kaddara aka jefar dasu ne, kuma da ace za arinka yin hakuri ana rungumar yaran ana basu kulawa to da sai kiga kilama sun zama silar taimakon addinin Allah" ammi tabata amsa tana kallonta cikeda tausayawa,
"Gashi kuwa kamar balarabe sai uban dogon hanci kamar in cire in kara anawa" hajiya tafada cikin barkwanci,
Ganin taki dagowa ya sanya hussain daka mata tsawa domin dama kawai ya tsaya yana kallonsu ne yaga iya gudun ruwanta,
"Ke....! Tashi ki karbeshi ki bashi nono ko nazo nayi bol dake, tashi nace"
Tashi tayi tana kuka har lokacin bata daina ba,
"Yi mata ahankali yan biyu, ai zata tashi" hajiya ta katseshi,
"Bazaki karbeshi ba, hajiya mika mata shi, karbeshi, banza shashasha, wannan wanne irin shirmene? Akansa zaki huce kome? Kefa kikace kin dauki kaddara to kuma sai ki gajiya tun daga yanzu?" Matsawa yayi kusa da ita ya sassauta murya,
"Nasan abinda kike yiwa kuka, tsoro kike kar ya girma ya tambayeki waye babanshi ko? To ni dinnan ni Hussain nine ubansa, zan zame masa gata zan reneshi tamkar dan da na haifa jinina, in dai ina raye to yaronki bazai taba kukan rashin uba ba nayi miki alqawari, ki saki ranki ki kwantar da hankalinki, ki kula da danki daga nan har zuwa lokacin da zaki yayeshi, zan dauki nauyin komai nasa na rayuwa nayi alkawari"
Dakyar ta mika hannu ta karbeshi daga hannun hajiya tana kuka tadorashi akan cinyarta tana kallonsa, hakika tasan ita kyakkyawa ce ta asali to amma bata taba ganin kyau irin na wannan yaron ba, yaro kamar ba'indiye, sumar kanshi kadai abar kallo ce gata sinkif ta sauko har goshinsa takusa rufe masa ido,
Feeding dinshi tafara yi amma ta daina kukan da take yi, zubawa yaron ido tayi tana jin wani irin sonshi yana ratsata,
"Wanne suna kike son asa masa?" Hussain ya tambayeta,
"Yaya da niyyata asaka masa ABDALLAH" tafada tana share kwallar idonta,
"Hakan ma yayi, bari naje na dawo"
Tare da ammi suka fita suka barta da hajiya,
Tunda ya kama nonon yana sha take kallonsa, lallai Allah babu yanda bai iyaba, kalli yaro kato dashi mai koshin lafiya, amma babu uba yanzu wasu ma'auratan kuma suna can sukuma suna neman haihuwar ido rufe amma basu samu ba,
Sai da yasha ya koshi sannan ta mikawa hajiya shi ta koma ta kwanta.
Ammi ce tadawo dauke da kaya niki niki su flasks din ruwan zafine dana abinci da kayan tea da sauran kayan bukata,
Take aka shirya jariri cikin kayan sa riga da wando farare sol,
Abinci ammi ta zuba mata ta hada mata tea mai kauri ta bata, tana gama ci ta koma ta kwanta, nan asibitin yafara karbar bakuncin yan gida domin duk sunzo ganin jariri, duk wanda ya karbeshi sai ya yaba kyansa dan haka ta dauri aniyar zata rinka yi masa addu'ar maganin baki.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/15, 9:53 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari ma tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_30_
~~~Da wannan tunanin tayi bacci ba ita ta farka ba sai misalin karfe 3 narana, lokacin data tashi hajiya ce kawai adakin tana kishingide itama tana dan baccin,
Gefenta ta kalla jarinrinta ne kwance shima amma kuma rabi ajikinta yake, hular kanshi tafara gyara masa tana kallon fuskarsa, idanuwansa manyane domin kusan ma sunfi nata girma,
"Abdallah" tafada ahankali,
Turo kofar dakin akayi aka shigo ammice da yayanta hassan suka shigo dauke da kaya,
Farfesun kajine ammi ta iyo mata ga kuma kayan marmari cikin yeluwar leda,
"Tunda kin tashi ai sai kici abincin ko?" Ammi tace da ita tana kokarin zuba mata farfesun,
"Woww,fine boy" hassan yafada lokacin da ya dauki yaron,
"Wannan yaron ai yafi uwarshi kyau" hassan ya sake fada,
"Ni cewa ma nayi zan cire hancinsa na lika anawa" hajiya dake kishingide agefe tafada tana dariya,
"To hajiya Kodai kina kamune?" Hassan ya tambayeta cikin zolaya,
Ita dai ikhlas tana zaune tana saurarensu tana cin farfesunta amma acikin ranta tana jin yan uwanta da mahaifiyarta sun gama yimata komai aduniya domin su basu koreta ba kamar yadda mahaifinta yayi mata afarko,gashi kowa sai murna yake da raha babu wanda zai ce danta bashida uba sai wanda ya sani.
Karfe 8 nadare aka sallamesu zuwa gida domin daga ita har babyn lafiyarsu lau babu wata matsala,
Suna isa gida ta samu kaya kaca kaca wanda yayunta suka siyo mata itada jaririnta alhalin kuma kafin ta haihu ma sun siyo mata wani.
Kula da ita ammi tafara yi itada abdallah har ranar radin suna anan aka radawa yaro suna abdallah, raguna biyu manya yayyunta suka siyo aka yankawa jaririn,
Komai awadace babu abinda ikhlas take nema ta rasa komai yayunta suna yi mata, irin kulawar da suke samuce tasaka yaron saurin girma, lokacin da sukayi arba'in kamar yayi wata biyu,
Ita kanta ikhlas din ta dan murmure tayi kalau fes da ita, hussain da hassan kullum cikin siyowa abdallah kayan sawa da kayan wasa suke yi daidai da rana daya basu taba kyamatarsa ba, haka sauran mutanen gidanma daga hannun wannan ya koma hannun wannan kasancewar babban gidane wuni zaiyi bata ganshi ba harma abin ya zame mata sabo,wani lokacin idan ammi tana tambayar ina abdallah sai tace,
"Ammi ni ina zan san inda yake? Kila yana kofar hajiya"
"Kullum dai ahaka kuke sai yabata agidan watarana" ammi tafada cikin wasa,
Dariya kawai ikhlas tayi,alokacin kuma barrister elmustapha ya fado mata domin rabonta dashi tun tana Zaria yanzu kuma ta sake sabon sim da sabuwar waya dan haka ta kirashi suka gaisa suka dan taba hira har yake sanar da ita ni'ima ta haihu watanni biyar da suka wuce sunan yarinyar ikhlas, murna tayi sosai tayi musu Allah ya raya, hakika ita kanta tasan elmustapha yana sonta to amma kuma ita bazata iya aurensa ba karewar so ma gashi har sunata ya sanyawa yarshi.
Rayuwarta haka taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali har abdallah ya cika wata goma lokacin yana yawonsa ko ina ga dankaren surutu shiyasa ta yayeshi, gashi yaron yana tsananin sonta koda yaushe yana makale ajikinta idan kuwa bai ganta ba to tamkar marar lafiya haka zai zama shiyasa itama bata nisa dashi kullum tana manne dashi, kayan wasanshi kuwa sai kace kamfani domin su hussain kullum cikin siyo masa suke,
Lokuta da dama sai ta zubawa abdallahn ido tayi ta kallonsa,yaron kama yake yi mata da larabawa wani lokacin ma har tambayar kanta take kodai balarabe ne yayi mata fyaden domin kyawun abdallah yayi yawa hatta hasken fatarshi ba irin nata bane yafita fari sosai domin shi har wani yellow yellow yake yi,
Dafarko kafin yayi wayo tana zama ta kunshe kanta adaki tayita kuka amma tunda yayi wayo sai ta daina domin akwai lokacin da yaganta tana kukan, jikinta yaje ya fada shima yafara kuka yana kankameta,
"Anty waye ya daceci kike kuka" shine tambayar da yayita yi mata shima yana kuka, rarrashin duniyar nan tayi masa akan yayi shiru amma yaki sanadiyyar kukan da yayi har zazzabi yayi ranar, tunda taga haka sai ta hakura ta daina kukan ta fawwalawa Allah lamarinta, sannan ta rungumi danta domin soyayya take nuna masa ako ina kuma agaban kowa har hajiya tana tsokanarta tana cewa ta futsare santa bata alkunya,
Ko bacci take yi da rana haka abdallah zai zo ya shige jikinta tare zasu yi baccin idan bathroom ta shiga to kofar bathroom din zai je ya tsaya yana gadinta har tafito, iya shakuwa sun shaku sosai,
Yanzu shirye shiryen bikin hassan da hussain yayunta suka fara yi wata mai zuwa,kudi mai yawa suka bata sukace tayi siyayyar hidimar biki ita da danta.
*
Lamido lamarinsa kullum sake ta'azzara yake yi domin babu abinda ya rage acikin halayyarsa, kullum cikin shan kodin yake da kula mata ganin abin yana nema yayi yawa ya sanya baffanshi shawartar inna cewar zai yiwa Lamido aure kwanan nan amma ya tagani, itama goyon baya tayi,dan haka Baffa ya kira bash yake tambayarsa wacce yarinya ce Lamido yake so bash yace su biyune akwai fadila akwai kuma ihsan kuma duk yan matansa ne tun kafin yabar kasar,
Bin gidajensu yaran Baffa yayi duk ya nemarwa Lamido aurensu aka saka ranar biki watanni biyu kacal (kaji Lamido dan gata, mata biyu alokaci daya),shi Lamido yana can Kenya bai san abinda ke faruwaba gashi kullum sai sunyi waya da yan gida amma babu wanda ya fada masa shirin da akeyi akansa ko bash bai sanar masa ba,
Sai da Baffa yagama komai harta gidan da matan zasu zauna Baffa ya samar masa an hada lefe na alfarma ankai biki ya taso gadan gadan sannan Baffa yace masa idan yagama exam yadawo gida lokacin shekararsa biyu babu watanni 3 acan,
Shi bai san ko menene ba dan haka yafara murna yahau shirin dawowa gida, pretty dinshi yaje yayiwa tsaraba ya sai mata zoben gold mai kyau ya siyo mata abin hannu shima na gold,
Aranar laraba da yamma jirginsu ya sauka a filin saukar jirage na sir ahmadu bello, yahade cikin blue din suits masu tsada wadanda suka karbeshi gashi zuwansa waje yasashi ya dada wayewa ya sake zama dan birni dan gayu _(classic guy)_,idonsa sanye da bakin gogle wanda ya sake fito da farar fuskarsa mai dauke da bakin saje akwance luf.
0 comments:
Post a Comment