~~~Ita kanta fatar jikinsa ta sauya ta sake zama fresh yana tafe yana shakar iska yana fesarwa har ya karasa saukowa daga matattakalar jirgin,
Bash ya hango tsaye yana kallonsa yana dariya, inda yake ya karasa ya bashi hannu suka rungume juna,
"Welcome on top" bash yafada suka rungume juna suna dariya,
"Bash baka cika alkawari ba amma tunda gashi nadawo to zan dubo pretty na da kaina"
Dariya bash yayi aranshi yana cewa "maganar pretty kuma ai ta kare"
Amma afili sai yace "ok to shiga mota dai mu tafi kawai"
Bude motar sukayi suka shisshiga suka bar airport din,amma bash sai dariya yake yi kasa kasa ta mugunta wanda shi lamido bai fahimta ba domin bashida masaniyar auren da baffanshi zai yi masa gashi har mata biyu ris,
Suna tafe suna hira har suka karasa gidansu lamido anan yaga gidan nasu yasha sabon fenti an sake gyarashi tsaf, amma sai bai kawo komai ba aranshi,
Yana shiga cikin gidan innarsa ta tareshi da murna amma baffanshi baya nan bai dawo ba, babu kunya yatafi yaje ya rungume innah amma ita duk kunya ta kamata duk da kasancewarshi dan auta akwai alkunya irin nasu na fulani,
Jan hannun bash yayi suka karasa cikin falo duk ma'aikatan gidan sai sannu da zuwa suke yi masa,kujera yasamu ya zauna yana murmushi,
"Innah komai na gidan nan ya sauya yazama sabo badai duk murnar zuwana ne yasa akayi haka ba"
"Murnar zuwanka ne mana autan Baffa" inna ta bashi amsa,
Abinci aka gabatar masa kala kala nan ya zauna ya kwashi girki shida bash suna ci suna hira har Baffa ya dawo, rungumeshi Lamido yaje yayi yana murna domin rabonsa dasu tun lokacin da ya tafi Kenya sai dai agaisa awaya.
Har dare suna tare da Baffa da Lamido sunata hira, misalin karfe 9 suna falon Baffa azaune baffa ya kalleshi yana murmushi yace,
"Lamido ka shirya karshen satin nan zan daura maka aure da yaran da kake zuwa wurinsu kafin ka tafi Kenya fadila da ihsan ina nufin ranar juma'a mai zuwa kaga saura kwana biyu kenan"
Wani irin abune ya tasowa Lamido ya gilma ta idanuwansa tuni ya daina gani yaga duhu ya mamaye fuskarsa,
"Baffa aure? Kuma aurenma har mata biyu?" Yafada muryarsa na rawa,
"Eh Lamido abinda nake so dakai kawai kayi biyayya"
Shiru Lamido yayi bai sake magana ba har baffa da innah suka gama yi masa yan nasihohin da zasu yi masa ya tashi ya nufi dakinsa,
Rigar jikinsa kawai ya cire yafada gado yafara juyi yama rasa abinda zaiyi sai kawai yafashe da kuka, shi dai babban burinsa arayuwa yanzu shine yaga ya nemo prettyn shi ya aura yayi rayuwa da ita ashe hakan bazai faruba, kuka yake kamar ba namiji ba sai da ya raba dare yana kuka sannan ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa ya fito yazo ya kwanta, baccin da baiyi ba kenan, da safe kuwa tashi yayi da zazzabi gashi idanuwansa sunyi ja sun kumbura kamar wanda aka buga awurin.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/16, 7:56 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga K'awata Khadija Sidi_
_32_
~~~Koda innah taganshi ahaka gigicewa tayi domin ba karamin kumbura idanuwanshi suka yi ba sakamakon kukan da ya kwana yana yi,
"Lamido meya sameka?" Tafada agigice,
"Innah ciwon ido nake" yabata amsa yana mai sake runtse idonshi saboda baya son taga hawayen da yake boyewa domin kwalla ta taru acikin idonsa,
"Kaje ka nemo magani maza"
"To innah"
Breakfast yadan cakula yasha ruwan tea empty yatashi saboda baya son hankalin innah ya tashi yasan muddin taga baici abinci ba to zata shiga damuwa,
Bakin face yasaka a fuskarshi ya rufe idanuwanshi ya dauki daya daga cikin motocin baffa ya fita,
Cikin gari ya shiga yaje ya tsaya agefen kasuwa daidai plaza dinnan da yayiwa mahaukaciyar nan fyade,
Kallon barandar da yaganta azaune yafara yi kwalla tana ciko idonsa, ya dauki lokaci mai tsawo acikin motar zaune yana kallon wurin kamar wani tababbe,
Jan motar yayi yanufi gida, abakin gate din gidan suka yi kicibus da bash yazo gidan,
Fitowa yayi ya rufe motar yanufi bash din,
"On top wannan face din fa sai kace sabon makaho"
Dan murmushi Lamido yayi ya mika ma bash hannu yana cewa,
"Ciwon ido nake yi kasan kuma zan iya shafawa wasu shiyasa na rufe"
"Ko kuma ka kwana kana kuka ba" bash yafada yana kallonshi
"Apolo nake yi"
"To Allah yabada lafiya, yanzu dai ga invitation cards can na bugo na rarraba suma amaren na kai musu nasu"
Shiru Lamido yayi shifa yama dade da mantawa da fadila da ihsan din domin rabonshi dasu tun yana sch a yola,
"Shikenan tunda ka gama rabawa, Allah ya saka da alkairi ni yanzu zazzabi nake ji zan shiga ciki"
"Allah yabaka lafiya domin gobe ne daurin aure fa kuma akwai dinner, akwai ladies night, akwai Polo day, akwai..."
"Dan Allah ya isa haka Allah ya kaimu goben" Lamido ya katseshi tareda yin gaba yabar shi awurin,dakinsa yakoma ya kwanta bayan yasakawa kofar key, lulluba yayi da bargo sakamakon zazzabin da yake ta rinjayarsa babu dadewa zazzabi mai zafi ya rufeshi tuni yafara suratai marassa dalili kamar yanda ya saba duk lokacin da yake zazzabi.
Shirye shiryen biki kam ya gama kankama sosai bash sai rabon katin gayyata yake yi amma duk wanda ya bawa katin indai abokinsu ne sai yayi mamakin jin cewa on top ne wai zaiyi aure kuma aurenma fadila da ihsan zai aura saboda duk sch dinsu kowa yasan soyayyarsa da yan matan biyu sukuma duk inda suka hadu sai sunyi fada akansa kwata kwata jininsu bai haduba gashi kuma zasu zama kishiyoyin gaske da rabon miji daya zasu aura.
Amare kam kowacce ta damu bash da tambayar ina lamido yake domin dukkaninsu suna son ganinsa,shidai bash kawai ce musu yake yana nan zuwa sabgogine suka yi masa yawa.
Kamar jiya Lamido yauma baiyi bacci ba gashi bashida lafiya zazzabine ajikinsa mai zafi, ganin zai mutu shi kadai adaki yasashi tashi ya tasamma bangaren innah, lokacin da yaje sashen nata acike yake da baki yan uwa,
Dakinta ya shiga ya sameta da yan uwanta sai hira ake yi kamar ba dare ba,innah na ganinsa tasan bashida lafiya, hannunsa ta kama ta fita dashi zuwa sashen baffa yan uwa sai tsokanarsa ake yi suna fadin,
"Kaga angon mata biyu alokaci daya, ayyuri yuri yuriririiiiiiiikiii..!"
Bai iya cemusu komai ba har suka fice,
"Lamido jikinne ko? Sannu"
Falon Baffa ta kaishi lokacin baffan yana zaune yana lissafa katan katan din goro da alawar da aka siyo yana warware na kowanne gida wanda za akai gidan amaren,
"Baffa kaga Lamido bashida lafiya" inna tafada tana zaunar dashi akan doguwar kujera,
"Assha sannu Lamido, um kawo masa abinci yaci sai yasha magani"
Cikin sauri innah ta nufi dining table ta zubo masa tuwo da miyar kubiya ta kawo, tashi yayi ya karbi tuwon yaci lauma biyar ya ajiye yasha paracetamol ya koma ya kwanta mintuna kadan bacci ya daukeshi.
Tunda yafara baccin nan bai tashi ba sai karfe 3:30 nadare, dakinsa ya koma ya yi wanka ya sake kwanciya sakamakon daren jiya baiyi bacciba yasa baccin saurin sake saceshi daga nan kuma bai farka ba sai da asuba,
Bayan dawowarsa daga masallaci ma kwanciyar ya sake yi dama tun jiya wayoyinsa duk ya kashesu saboda baya son damu,
Yana tsaka da bacci yaji ana tashinsa, tsaki yayi yadan juya kadan yatashi, yayanshi yagani rikeda kayan da zai saka,
"Haba Broz ya ina baccina kawai zaka zo ka katse min"
"Tashi Broz kayi wanka ka shirya ai daurin auren naka ya kusa, kaga na farkon a Numan za adaura na biyun kuma anan cikin Yola, to yanzu Numan zamu fara zuwa, ga kayanka wanda zaka sa"
Tashi yayi yana cije lebe ya shiga bathroom yayi wanka ya fito lokacin har Broz din nashi ya fita, agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi har yanzu akwai kumburi a idonshi ga ja, mai ya shafa yasha turare yasaka farar shaddar da yayanshi ya ajiye masa wacce tasha dinki, anan ya fito a angonshi sak, hular ma farace haka takalmin duk farare ne agogon hannunshi ne kawai na azurfa mai kyau, bakin face yasaka afuskarshi saboda tsaro.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/17, 7:36 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_33_
~~~Yana fitowa daga dakinsa yaga mutane nan mata suka shiga yin guda suna tafi,
Bash ne ya rankayo yazo ya kama hannunshi yana murmushi,
"Kayi kyau on top"
"Nagode" yafada atakaice tuni masu hotuna da video coverage suka fara aikinsu na haska Lamido,
Mota yaje ya shiga kirar _Lexus_, bash yajasu suka rankaya domin tafiya kauyen Numan wanda canne tushen su fadila.
Misalin karfe 12:30 aka daura auren Lamido da fadila akan sadaki naira dubu hamsin, daga nan kuma cikin garin yola suka dawo unguwarsu ihsan wanda gidansu ke Sultan Road lokacin karfe 1:30 dan haka ana idar da sallar juma'ah a babban masallacin dake kofar gidan aka fara daura aure, ita dinma sadakinta naira dubu hamsin kamar na fadila, bayan daurin auren Lamido gida yakoma bash ya mayar dashi gashi amaren suna son ganinshi domin kowacce sai waya take yiwa bash tana tambayarsa ina angonta dole sai hakuri ya basu fadila kam harda kukanta domin kawayenta da suka yi secondary sch tare sun zazzo kuma sunata son su ganshi, ta wuri daya taji sanyi da bash yace mata da daddare akwai dinner kuma Lamido zai halarci dinner din yanzun ma dan bashida lafiyane yana zazzabi.
Lamido kam yana komawa gida daki ya shige yayi kwanciyarsa yanzu kallon kowa yake yi bashida bakin yin magana, wuni guda adaki yayishi har mangaruba tayi alokacin bash yazo domin ya shirya su tafi dinner, dakyar ya iya shawo kan lamido ya yarda ya shirya ya hade cikin purple din shadda gezna mai kyau yar gasken, bai saka babbar rigar ba iya yar cikin kawai yasaka yasa hula yarufe idanuwansa da bakin face,
Agidan baya ya zauna bash yajashi,
"Ina zamu fara zuwa?" Bash ya tambayeshi,
"Oho kai kasani"
"To gidansu fadila ya kamata mu fara zuwa domin itace uwar gida"
Lamido najinshi bai tanka masa ba, gidansu fadilan suka wuce wanda ke IBB road, suna zuwa bash ya kirata tafito, tasha kwalliya tayi kyau cikin wani pink din material,
Gidan baya bash ya bude mata kusada lamido, shiga tayi ta zauna, lamido ko juyawa ya kalleta baiyi ba,
"Lamido ya jikin tafada muryarta na rawa,
Juyawa yayi ya matso da ita jikinsa domin nesa dashi ta zauna yagane dalilinta nayin haka tsoro takeji kar ya yarfata,
Hannunwanta yakama acikin nashi,
"Da sauki fadila ya hidimar biki?"
Ba karamin dadi taji ba jin ya dan sakar mata fuska,
"Mun godewa Allah"
Hannunta ya murza acikin nashi yana kallon fuskarta babu laifi itama kyakkyawa ce wannan dalilinne ma yasashi yin soyayya da ita domin shi duk yan matanshi kyawawa ne,
"Kin san ku biyu na aura keda ihsan ko?" Ya tambayeta yana gyara mata gashinta da aka yanko mata gaban goshinta ya zubo,
Kai ta daga masa "ehh nasani"
"Yawwa to shikenan Allah ya zaunar daku lafiya"
"Amin" ta amsa tana lumshe idanuwanta domin wani farin cikine yake ratsata,
Gidansu ihsan sukaje suna zuwa itama tafito cikin kwalliya tasha material golden colour komai nata golden ta saka,
Itama bayan bash ya bude mata ta shiga ta zauna suka saka lamido a tsakiya, ganin fadila jingine jikin lamido hannunta cikin nashi yasata juyar da kanta,
"My Lamido ya jikinka"
Hannunta itama ya kamo ya rike cikin nashi,
"Da sauki my ihsan, ya taro?"
"Alhamdulillah my lamido"
Daga nan bai sake magana ba amma kuma yana lura dasu kowacce sai hararar yar uwarta take yi gashi sunki koda kallon junane,shikam da sun san abinda ke ransa da basuyi haka ba domin duk cikinsu babu zabinshi.
Har sukaje hall din da za agudanar da dinner din babu wacce ta kalli wata, shidai haka ya lallaba aka shiga wurin dinner din, wurin ya tsaru sosai yasha decoration gashi ya cika dam da al'umma
Wurin da aka tanadar musu suka wuce sukaje suka zazzauna kawayen amaren sai fulawa suke watsa musu da turare mai kamshi suna feshesu dashi.
Dinner din tahadu amma shi lamido sam babu fara'a akan fuskarsa har aka tashi anan kuma fada yaso barkewa tsakanin fadila da ihsan akan hanyarsu ta komawa gida,
Wata tsawa lamido ya daka musu "kai ya isheku kar Ku sake kuyi min fada"
Dolensu suka yi shiru, har akaje aka sauke ihsan basu kara magana ba, bai kulata ba tafita daga motar, haka itama fadilan lokacin da aka ajiyeta bai kulata ba, ita yasan gobe za akai masa ita gidansa ita kuma ihsan sai jibi wato ranar lahadi.
Suna zuwa gida ya fita daga cikin motar ya wuce bedroom dinsa, zama yayi ya dafe kansa wanda ke tsananin ciwo da sara masa kamar zai fita yabar jikinsa,
Wayarsa ya kunna tuni sakonnin abokanshi suka shiga shigowa rututu wanda duk na tayin murna ne, bai samu damar iya mayar musu da reply ba sakamakon sakonnin sunyi yawan da hakan bazata samuba.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/17, 7:36 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a Zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_34_
~~~~Washe gari tunda safe Lamido ya fita, bakin wannan plaza din ya je ya tsaya amma yauma babu ita babu alamunta yau kam har cikin kasuwar ya shiga ya na dan duddubawa ko zai ganta amma shiru, kangon da yayi mata fyade aciki kuwa tuni an gineshi an mayar da shi shaguna,
Yajima yana kekkewayawa yana yawo amma maimakon yaganta ma sai sabbin mahaukata yake gani maza, glass din motar tashi ya sauke yafara mika musu kudi yan dari bibbiyu sababbi,
Gida ya koma ya shiga daki ya kulle kansa har azahar tayi yana nan akulle sai da bash yazo tukunna ya samu ya bude kofar bash ya shigo yana kallonsa kallon kurulla,
"Wai kai meke damunka, sai ka shigo daki ka rufe wayoyinka duk akashe mutum bazai sameka ba"
"Bana son adameni ne, bana son hayaniya i don't want any hustle and bastle"
"Suwaye zasu damekan, mu ko matanka?"
"Duk wanda kaga ya dace"
Kafin bash ya sake magana innah ta shigo dauke da flask din abinci da kunun shinkafa awani jug,
Fulatanci ta hau yi masa,
"Lamido meyake damunka ne baka son cin abinci, dan Allah ka karba kaci kaji"
"Innah zanci"
"Yawwa Lamido shiyasa ma idan ankawo amaren naka zan fada musu baka son cin abinci sai suna yi maka dure"
Dukkaninsu dariya suka saka banda Lamido wanda murmushi kawai yayi,
Ba don yaso ba haka ya dauki abincin ya danci shida bash suna gamawa suka fita salla ahanyarsu ta dawowa bash yake sanar dashi cewar ihsan itama yau za akawota amfasa goben,
Baice komai ba yawuce dakinsa domin yanzu idan akwai abinda yake kauna arayuwarsa to zaman dakine baya ga wannan baya bukatar komai.
Misalin karfe 9 nadare aka kai masa amarensa gidansa dake unguwar governor road, shikam yana gida akwance yana dan jin zazzabi sama sama dama ko kayansa ma sai bash ne ya hada masa yakai can gidansa ya saka masa a dakinsa,
Yana kwance yana aikin nasa na tunani bash ya shigo,
"Wai dama baka shirya ba?" Dan Allah on top kai muke jira"
Batare da yayi magana ba ya mike ya shiga toilet yayi wanka ya fito har lokacin bash yana tsaye yana jiransa, mai ya dan shafa ya gyara sumarshi da sajensa yasaka wani farin lallausan yadi mai kyau wanda yake kamar tissue marar kauri domin har ana iya hango farar singiletin daya saka aciki jar hula yasaka,
Turarensa mai mutukar dadi ya fesa na azhaar, jan hannunsa bash yayi suka fita, wurin innah ya shiga yayi mata sallama ya fito yashiga wurin baffanshi shima yayi masa sallama ya fito,
Cincirindon abokansu yagani wadanda zasu rakashi, yake ya rinka yi yana basu hannu suna gaisawa kowa sai murna yake tayashi,
Motar bash ya shiga suka dauki hanya anan yake fadawa bash cewar suna kaishi kawai su tafi baya bukatar su shigar dashi domin kanshi ciwo yake yi,
Bash bai ki ba suna zuwa gidan ya saukeshi yaje wurin abokan nasu yana yi musu jawabi,
Gidan kawai Lamido yake bi da kallo Wanda yake katon gaske yasha fenti pink pink milk milk, farfajiyar gidan ma badai girma ba gashi anyi shuke shuke, hasken wutar lantarki ya haskake ko ina,
Cikin gidan ya tasamma wanda yake babban falo ne na gaske wato general falo, sai kuma corridors wanda kowacce tana dashi tanan zaka bi kaje sashenta, shikuma nasa sashen yana ta opposite dasu amma kuma gidan sashe hudune hakan yasashi dan murmushi domin daya sashen sashen pretty dinshi ne sai dai yana jin tausayinta na zama da zatayi da kishiyoyi hakan zai kawo nakasu acikin kyakkyawar rayuwar da ya shirya bata.
Dakinsa yanufa wanda ajiki aka rubuta _master room_ ahankali ya bude ya shiga, dakin katone sosai yasha sha funutures masu tsada kirar Royal, komai na dakin ya dace dashi,
Kan gadonshi ya karasa ya zauna yana bin dakin da kallo, tashi yayi yaje ya rufe kofar da key yadawo kan gadon yayi tagumi yana tunanin da ace pretty dinshi aka kawo mishi gidan nan ai da yanzu yana tare da ita yana bata kulawa, yana shayar da ita ruwan soyayyarshi mai mutukar tsada,
Runtse idonshi yayi sai ga hawaye sharrr suna bin kumatunshi,
Hangosu kawai yake shida pretty acikin wani yanayi, kuka ya fara yi ka'in da na'in yama manta da cewar amarensa na can suna zaman jiransa,
Shiru shiru bai shigo ba gashi kuma kowacce sai kiran wayarsa take akashe nan duk hankulansu ya tashi,musamman ma fadila,
Agogo ta kalla karfe 12:30 nadare, wayarta ta dauka tana kuka takira babanta yana dagawa tace ita tsoro takeji har yanzu ita kadai ce agidan Lamido bai shigo ba, lallaminta babanta yayi yace bari yakira baffan lamidon,
Wayar ta kashe tana kuka, babanta suna gama waya da ita baffa ya kira yace har yanzu fa ango baije gidan ba yabar yarinya ita kadai acan,
Mamaki baffa yayi to ya akayi haka tunda 9 Lamido yayi musu sallama ya tafi, bai gama wannan mamakin ba Baban ihsan shima ya kirashi domin itama tayi waya gida tana kuka wai Lamido bai zo gidan ba, dole tasa baffa fita adaren ya dauki mota ya nufi gidan Lamido addu'arshi daya Allah yasa dai Lamido ba club yatafi ba ko gurin shashancinsa tunda ya kula kamar bai so wannan auren da akayi masa ba,
Wayar bash yake ta kira amma bai daga ba sai da ya kirashi wurin sau 10 sannan ya daga cikin magagin bacci,
"Baffa.."
"Kai bashir kuna ina ne?"
"Baffa ni ina gida Lamido kuma yana gidansa tun 9 na kaishi natafi"
"Ka tabbata?"
"Ehh Baffa"
Kashe wayar baffa yayi ya nufi gidan lamidon yana zuwa watchman ya bude masa ya shiga, gidan shiru tsit kamar babu kowa gashi babu hayaniya asalima unguwar sabuwar unguwace lallai dole amaren su shiga damuwa.
*_Ummi Aisha_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_35_
~~~Cikin gidan ya tasamma kai tsaye ya shiga babban falon tanan yabi ya shiga bangaren Lamido, yana zuwa yafara nocking,
Lamido dake kwance yana kuka yajiyo anfara bugun kofar dakinshi duk azotanshi daya daga cikin amaren ne dan haka ya share yaci gaba da kukan da yake,ankai kusan minti biyar ana bugun kofar amma yaki tashi kamar amafarki yajiyo muryar baffanshi yana kiransa,
"Lamido, Lamido, Lamido"
Tashi yayi arazane yakarasa bakin kofar ya tsaya dan ya tabbatar ai kuwa shi dinne, cikin hanzari yakama rigarsa ya goge fuskarsa ya bude kofar,
Baffa yagani tsaye yana kallonsa, hamnunshi baffa yakama suka koma cikin dakin,
Abakin gado suka zauna baffa ya zuba masa ido cikin tausayawa domin ya fahimci kuka yake yi kai duk yanda akayi akwai yarinyar da Lamido yake mutukar so sai yanzu ya gane wannan amaren da ya aura masa basune zabinsa ba basune burinsa ba kawai yayi masa biyayya ne,
"Lamido ya zaka zo ka zauna adaki bayan an rigada an kawo maka amarenka suna can suna jiranka" baffa yafada gamida kamo hannunsa,
"Baffa kainane yake ciwo"
"A'a lamido kafada min gaskiya, daga ganin fuskarka kuka kakeyi, ko kanada wacce kake so ne??
Shiru yayi babu amsa,.
"Nace akwai wacce kake so?"
Sai alokacin ya daga kai alamar ehh,
"To ai lamido duk wannan mai saukine, shiyasa ubangiji ya Baka damar ka auri mata har guda hudu, yanzu ga biyu zabina wanda na aura maka, nan gaba kaima Kanada damar da zaka auro guda biyu wadanda suka kasance zabinka, bazan hanaka ba lamido, duk lokacin da ka shirya ka Aurota ka kawota gidan ka"
Sai alokacin lamido yaji sanyi aranshi,
"To baffa nagode"
"Yawwa yanzu katashi kaje wurin iyalanka"
"To baffa"
"Yawwa Lamido kayi hakuri kar ka sake zubar da hawayenka kaji, idan matanka suka ganka kana kuka zasu ce ragon maza suka aura"baffa yafada cikin barkwanci,murmushi lamido yayi yana shafa sajenshi batare da yace komai ba,
Mikewa baffa yayi lamido yabi bayanshi ya rakashi har inda motarsa take ya shiga ya tafi, ciki lamido ya dawo ya dauki hularshi yasa ya nufi sashen fadila.
Ahankali Ya shiga cikin falon nata duk jikinsa babu kwari kamar anyi masa duka, falon yasha kayan alatu masu aji da matsayi, tsada da kuma haduwa, komai purple aka zuba tun daga kan kujeru har labulaye kai da duk sauran kayan ciki komai kalarsa purple,
Dakinta ya bude ahankali ya shiga, can tsakiyar gadonta ya hangota tana takure da alama kuka take yi,
Sallama yayi ahankali ya karasa kusa da ita bayan ya hau kan gadon,
Mayafin datake lullube dashi ya janye ya kamo habarta ya dago fuskarta, sanye take cikin jan lace mai tsada sai kyalli yake yi yasha stones ajiki,
"Am sorry my fadila..!" Yafada cikin sigar lallashi, bude idonta tayi ta kalleshi ba karamin kyau da haduwa yayiba acikin wannan daren, sai dai amma idonsa yayi ja,
"Lamido ya naga idonka yayi ja?" Ta tambayeshi a gigice,
"Ciwon ido nake yi ai fadila, banida lafiya"
"Ayya sorry my lamido" tafada kamar zata saka kuka,yan yatsunta ya kama yana kallon fuskarta,
"Kije kiyi alwala ki fito, ki sameni a babban falo nida ihsan"
"Tom" ta amsa ciki ciki sakamakon ambatar ihsan da taji yayi, mikewa yayi ya fita ya nufi part din ihsan wacce itama yasan tana can tana baza idanuwan ganinshi.
Falon ihsan ya shiga ita kuma komai nata coffee colour ne da ratsin milk ajiki, bedroom dinta ya kama ya shiga tana zaune agefen gado ta kifa kanta ajikin pillow,
Abayanta ya zauna ya rungumeta ta baya yana cewa "my ihsan badai har kinyi bacci ba?"
"Lamido ina ka shiga?" Ta tambayeshi tana shasshekar kuka,
"Kiyi hakuri ihsan akwai abinda ya tsayar dani kinji"
"Meya tsayar dakai awannan daren bayan kasan muna nan muna jiranka" tafada cikin kuka, hannunshi ya mika ya fara share mata hawayen fuskarta, cikin sigar lallashi yafara magana,
"Kiyi hakuri my ihsan,pls daina kukan ki tashi kiyi alwala muje muyi salla"
Sakinta yayi ta tashi ta shiga toilet dinta binta da kallo yayi tasha atamfa super yar gasken green colour,hakika yasan daga fadila har ihsan duk suna sonsa to amma shi matsalar shima yana da wacce yake so sai dai kawai yasha alwashin zai zauna dasu domin yiwa mahaifinshi biyayya,
Yana nan zaune ta fito ta dauki gyalenta, hannunta ya kama suka fita zuwa babban falon gidan inda fadila ke tsaye tana jiran fitowarsu.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata Khadija Sidi_
_36_
~~~Tun daga nesa suka fara aikawa da junansu harara musammam ma fadila wacce idonta kamar zai fado dan tsabar hararar da take aikawa ihsan,
Bai kula dasu ba, agaba ya tsaya sukuma suna bayanshi yajasu salla, raka'a biyu sukayi yai sallama, addu'o'i yayi musu afili da waje sannan ya jiyo yana kallonsu,
"Fadila, ihsan dan Allah na rokeku ku zauna lafiya banda tashin hankali sannan dukkaninku matana ne babu wacce tafi wata awurina, dan Allah banda fada domin bashida amfani"
Babu wacce tayi magana acikinsu dan haka yaci gaba,
"Fadila kece babba saboda kece uwar gida dan haka ki rike girmanki, ke kuma ihsan banda rashin kunya kibata girmanta, zaku rinka yin girki kwana bibbiyu, amma tare zaku rinka yi saboda bana son abinda zai rarraba kawunanku"
"Da dai kowa yayi girkinsa yafi" suka fada bakinsu har yana haduwa,
"To hakan ma babu matsala kowa ya rinka yin nashi girkin daban,yanzu dai zanyi kwana bakwai awurin fadila kafin sai nadawo dakinki ihsan kema nayi miki kwana bakwai daga nan kuma sai kufara kwana bibbiyu,akwai mai magana acikinku?"
Girgiza kai sukayi alamun babu, tashi yai yaje inda fridge yake girke ya dauko manya manyan robobin fresh milk guda uku ya kawo musu yasake komawa saman fridge din ya dauko wata leda mai kyalkyali,
Kajine duku duku guda uku aciki, anan ya baje musu suka dan tattaba domin daga shi har su babu wanda yayi wani cin kirki,
Bayan sun kammala ne suka tashi domin kowa yatafi dakinsa, tare suka jera suka fara raka ihsan dakinta sannan ya kamo hannun fadila suka wuce dakinta,
Rigar jikinshi kawai ya cire ya kwanta daga shi sai farin dogon wandon yadin dake jikinsa da farar vest, ita kam fadila wanka ta shiga ta sillo ta fito daure da towel da wani ta lullube kanta da jikinta, sai da ta zauna ta kyalkyale jikinta sannan ta dauko rigar baccinta ja tasaka taje kusa dashi ta kwanta.
Haka zamansu ya kasance har yagama yiwa fadila kwana bakwai dinta ya koma dakin ihsan nanma yayi kwana bakwai daga nan kuma suka fara rabon kwana,inda yake yiwa kowacce kwana bibbiyu.
Kasancewar hutunshi yana da dan yawa yasa zai dan jima akasar, kullum fadila da ihsan na zuwa sch kowacce a motarta take zuwa domin babu wacce ba akawota da mota daga gidansu ba,
Shikam lamido kullum ahanyar zuwa bakin kasuwa yake harma wurin ya zama wurin zuwansa domin kullum sai yaje,
Hankalinsa yanzu yadan kwanta sakamakon aurennan da yayi kuma yana kokarin bawa kowacce kulawa haka suma suna kula dashi domin dukkaninsu suna tsananin sonshi sai dai babu jituwa atsakaninsu kowacce ta tsani yar uwarta kamar zasuga hanjin cikin juna suke gashi dole sai sun hadu domin kitchen dinsu ma ahade yake guda daya ne for general.
Yanzu kam lamido ya daina shan kodin kuma ya daina neman mata domin tunda yayi aure yaji matan banza sun fita daga ransa kwata kwata, yar kulawar da yake samu tasashi yayi kalau dashi yasake yin kyau sosai amma babu wanda zai ganshi yace yanada mata biyu,
Watansu biyar da aure ya shirya komawa Kenya nan kuma baffanshi yace dole sai yatafi da daya daga cikin matansa, amma koda ya tuntubesu sai fadila tace da ita zai tafi ta yarda zata ajiye karatunta idan sun dawo sai taci gaba tunda yanzu saura shekara daya da rabi ta gama, shirye shiryen tafiya suka fara amma fa har lokacin lamido bai manta da mahaukaciyar nan ba tana nan acikin zuciyarshi kullum da ita yake kwana yake tashi.
Ranar alhamis da yamma jirginsu ya daga shida fadila suka bar Nigeria, tunda sukaje Kenya kuma suke fada da fadila saboda bata son motsa jikinta tafi son ayi mata komai tana daga kwance,
Wannan dalilinne yasa kullum basa zama lafiya da lamido domin shi mutumne mai kyankyami da tsantseni, kullum tana kwance tana bacci zai shirya ya tafi lectures yanda yatafi yabarta wani lokacin haka zai sake dawowa ya isketa ko wanka bata tashi tayi ba bare ta gyara musu dakin,
Ganin tasaba da kwanciya yasashi kullum sai yayi abubuwanshi sannan yake tafiya amma ba karamin dana sanin zuwa da ita yayiba domin da yasan haka zata yi masa to babu dalilin da zaisa ya taho da ita.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga kawata Khadija Sidi_
_37_
~~~Haka yaci gaba da hakuri yana zaune da ita gashi kullum cikin cin take away suke domin girkinma batayi,
Wannan dalilin yasa suka fara yar tsama, kamar kullum yauma shiryawa yayi cikin kananan kaya blue din t shirt da black din trouser yayi kyau sosai kamar wani dan indiya turaren black valvet ya dauka ya feshe jikinsa dashi, bai ko kalli inda fadila take ba ya dauki jakarshi yayi gaba,
Baki ta taba ta sake gyara kwanciyarta caraf idonta ya sauka akan wani hoto wanda ke boye abayan akwatunan kayan lamido, tashi tayi taje ta dauko hoton, hoton macene amma kuma hoton wani iri domin an zana matar kamar irin mutanen da dinnan, cillar da hoton tayi ta koma tayi kwanciyarta,
Lamido tunda ya fita bai dawo ba sai bayan sallar azahar yana shiga daki yaga hoton pretty akasa can akan katifa kuma fadila ce ke kwance tana bacci,
"Kai!" Yafada dakarfi,
"Fadila, waye yasaki fito min da wannan hoton? Iye?"
Firgigit fadila tayi ta tashi tana zare idanu tana kallonsa,
"Abayan can naganshi" tafada cikeda rashin damuwa,
"To shine zaki dauko min ki yarshi anan saboda baki san muhimmancin sa ba ko? To bari kiji wannan hoton yafi komai muhummanci acikin rayuwata, ina tsananin kaunarsa kuma ina sonsa karki kuskura ki sake taba min shi idan ba haka ba ranki zai iya baci.."
Daukar hoton yayi yana gogeshi da gefen rigarsa yaje ya mayar dashi wurin da yake dafarko a ajiye, duk fadila na zaune tana kallonsa, fita yayi daga dakin hakan yasata komawa tayi kwanciyarta tana taba baki
"Akan wannan banzan hoton zaka wani zo kana yimin fada, mtswww"
Tafada tareda jan tsaki ta sake gyara kwanciyarta.
*
Ikhlas taci gaba da rainon danta abdallah wanda ahalin yanzu har ya cika shekaru biyu daidai, wayo kuwa awurinsa kamar ba dan fari ba gashi tabarakalla kyakkyawan gaske,
Kamar yadda yayanta hussain yayi alqawari cewar zai zamewa abdallah uba to hakika yacika alqawarin domin daga ita har abdallah babu abinda suka nema suka rasa, gatan da abdallah yake samu kuwa wani mai ubanma baya samun rabinshi,
Rayuwarta kam yanzu sai godiya kuma tayi sa'a Allah ya dauke mata damuwar datake fama da ita ada, yanzu zuciyarta fes take.
Yau kam takama ranar laraba wanda bikin yayunta saura kwana 5 agudanar dashi, gida sai shirye shirye ake tayi, kwance take tana baccin rana,
Abdallah ne ya garzayo da gudu yazo ya dale jikinta yana jijjigata,
"Anty ki tashi muje ki siyo min kayan"
Tashi tayi tana rungume dashi ajikinta,
"Ohh abdallah badai zaka barni nayi baccin nan ba saida ka tasheni"
Shiryawa tayi shima ta shiryashi suka yiwa ammi sallama suka fita,taxi ta tsarar musu suka shiga suka nufi shopping complex,
Suna shiga layin kayan yara ta wuce domin zabowa abdalla kaya, hadaddun riga da wando ta zabo masa kala biyar ta koma wurin takalma tafara zaba,
"Anty turare fa?" Ya tambayeta yana nuna mata,
"Jeka ka zabo wanda kakeso guda daya to"
Dagudu ya kwasa ya tafi wurin turarurrukan, wani mutum yagani atsaye awurin turarukan shima yana dubawa,
Rungume mutumin yayi tabaya kamar Wanda ya sanshi yana cewa,
"Uncle nima zabar min guda daya antyna zata siya min"
Cikeda mamaki mutumin ya jiyo yana kallon abdallah,
"Wow, boy ina antyn naka?"
"Tana can tana zaba min kayan da zansa abikin uncle hussain da uncle hassan"
Kama hannunshi mutumin yayi ya dauka masa turaruka guda uku manya masu tsada,
Suna tafe suna hira har suka karasa wurinda ikhlas take,
Dagowa tayi tana kallon abdallah da mutumin,
"Abdallah a ina ka tsayane?"
"Agun uncle" yabata amsa yana nuna mata mutumin,
"Uncle..." Tafada cikin mamaki, kallon mutumin tayi farine dogo mai kyakkyawar fuska,
"Barka da yamma anty"
Yace da ita yana murmushi,
"Yawwa" tafada ahankali tana kamo hannun abdallah,
"Ya zaki kwace kanin naki bazaki barmin shiba?"
Murmushi tayi "Kanina ko Dana?"
"Haba anty ai duk son girmanki baki haifi wannan yaron ba?"
"Ko saboda me?"
"Saboda bakuyi kama ba ko kadan, kamarsa daban taki daban"
"Wannan shine kadai dalilin? Dama dolene yaro sai yayi kama da babarshi?"
"Kwarai kuwa"
"To kuma idan babanshi ya dauko fa?"
"Duk da haka dai baki haifi wannan yaron ba, ke yarinyace wacce ko auren fari ba ayi miki ba, ina tunanin ma yar makaranta ce"
Murmushi tayi tabishi da kallo,"to na yarda bani na haifeshi ba"
"Kin kosa da mahawarar kenan?"
"Hmm ba kosawa nayi ba, kawai dai nabar maka musunne na dauke ladan"
Jan hannun abdallah tayi domin subar wurin amma mutumin yayi caraf ya rike abdallah,
"Ya zaki rabamu bayan kin ganmu tare?" Sakar masa abdallah tayi takara gaba, tana tafe suna binta abaya ya dauki abdalla ya rikeshi akafadarsa,
Wurin biyan kudi taje ta cicciro kayan wanda duk na abdallahn ne babu nata,
Lissafi aka yi mata dubu 10,kafin tayi yunkurin biya har wannan mutumin ya biya,
Kasa magana tayi ta dauki kayan tafita ta tsaya awaje tana jiran fitowarsu, suna fitowa tafara yiwa mutumin godiya,
"Nagode madalla Allah ya saka da alkairi"
"Amin, shiga mota muje?"
"Ina zamuje?" Ta tambayeshi cikin mamaki,
"Anty gida, uncle zai kaimu gida"
Binsu tayi ta shiga motar amma abaya ta zauna bata shiga gaba ba sai dai amma sai kallonta ta mudubi yake yi duk motsin datayi sai taga sun hada ido ta cikin mirror.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_38_
~~~Tana jinsu shida abdallah sai rangada hirarsu suke kamar dama sun san juna, itace ke yimasa kwatance har suka je gidan,
Fitowa tayi tana jiran fitowar abdallah, tare da mutumin suka fito yana mikawa abdallah turarukan da ya sai masa guda uku,
"Antyn boy baki fada min sunanki ba"
"Kaima ai baka fada min sunanka ba"
"Sunana Abubakar Sadeeq"
"Sunana ikhlas"
Murmushi yayi "ashe mai ikhlasi ce matar tawa"
Murmushin itama tayi "nifa matar wanice kaga yarona nan"
"Nima mijin watane inada yara hudu uku maza daya mace"
Murmushi ta sake yi "ka dauka wasa nake ko? Baka san dagaske nice na haifeshi ba?"
"Gaskiya ban yarda dake ba"
"Shikenan tunda baka yarda ba nagode madallah da hidimar da kayiwa abdallah"
"Babu damuwa sai gani na biyu" yafada yana yiwa abdallah bye bye, ciki suka shiga suna zuwa abdallah ya Shiga gwada kayan yana murna sai bawa ammi labari yake cewar uncle dinsa ne ya siya masa.
Acikin satin su ikhlas suka sha hidimar bikin hassan da hussain wanda zasu zauna acikin unguwar domin tsakanin gidajensu da gidansu ammi ma gida dayane atsakani.
Tunda aka kammala bikin ikhlas take ramuwar baccin da bata samu tayi ba ga gajiyar biki data kwasa,
Tana falon ammi tana gogewa abdallah kayan sawarshi wurin sha biyun rana, ahankali ya lallabo yazo ya dale bayanta ya rungumeta, ammi na kwance tana kallonsu,
"Bawan Allah bari mana kar ka karya min bayana" ikhlas tace dashi tana gyarashi a bayanta,
"Uhm uhm anty ni bacci nake ji kizo muje muyi bacci"
"Abdallah baka ga aiki nake yiba haba bawan Allah"
Kwanciya yayi abayanta taci gaba da gugar ko minti biyu ba ayiba taji alamun yafara bacci, kashe iron din tayi ta mike dashi abayanta,
"Bawan Allah ka hanani gugar nan dai"
Dariya ammi tayi "kukam ai kunji jiki kamar jika da kaka idan kukai wani abun"
Batace komai ba tawuce dashi cikin daki taje suka kwanta, rungumeshi tayi har bacci ya dauketa, bata san lokacin da abdallah yatashi yafice ba.
Tana tsaka da bacci tajiyo maganar abdallah yana tashinta,
"Anty kitashi uncle din rannan yazo"
"Bari abdallah bacci nakeyi"
"Anty uncle din rannan ne yazo, kitashi"
Irin yanda yake jijjigata yasata ta tashi dole,
"Yanzu bawan Allah kullum bazaka barni nayi bacci ba daga nafara sai ka tashe ni?"
"Anty uncle ne yazo"
Tashi tayi taje ta dauko bakin hijabinta tasa ta kama hannunshi suka fita ammi bata falon da alama tana sashen hajiya,
A kofar gida ta sameshi atsaye yasha kwalliya cikin brown din yadi,
Tun daga nesa yake kallonta har ta karaso da sallama a bakinta,
"Nazo nemanki tun dazu ban ganki ba sai karamin kaninki naga" yanuna abdallah,
Kallonsa tayi "abdallah fa ba Kanina bane wallahi dana ne"
Cikin mamaki ya kalleta "wai kina nufin ke kika haifeshi?"
"Wallahi nice na haifeshi"
Binta yayi da kallo domin babu wanda zaiyi tunanin tayi aure balle har ace ta haifi yaro,
"Kenan kin taba aure?"
Shiru tayi bata amsa masa ba, dan haka yaci gaba,
"Uhm ikhlas wallahi nidai naganki ina sonki kuma zan aureki"
"Nagode da soyayyarka amma kacire maganar aure dan bazan aureka ba?"
"Ko menene dalili?"
"Wannan nabarwa kaina ni daya"
"Bazai yiyuba, dole akwai dalili kuma yana da kyau ki sanar min"
"Gaskiya bazan sanar dakai ba amma kayi hakuri bazan iya aurenka ba"
Hannun abdallah ta kama suka shige cikin gida tana jinsa yana kiranta amma bata waiwayoshi ba, gajiya yayi da tsaiwa ya tafi.
Kwana biyu da faruwar wannan sai gashi ya dawo wannan karon har cikin gida ya shiga har falon ammi,lokacin da ikhlas tafito taganshi tayi mutukar mamaki,
Tareda ammi tasamesu yana yi mata bayanin cewa yana son ikhlas kuma aurenta zaiyi, ammi kam cewa tayi yaje su daidaita Allah ya zabi abinda yafi alheri,
Hannun abdallah ya kama yace zasuje children's park and zoo domin yayi kallo,
Ammi bata hanasu ba amma tace itama ikhlas ta shirya sutafi tare ba abar yaro shi kadai ba,
Shiryawa ikhlas tayi ta danyi kwalliya tasa bakin material da farin mayafi suka fita.
Wuri suka samu Abubakar sadeeq ya shimfida musu darduma suka zauna bayan yayi musu oder din kayan sanyaya makoshi, shi kuwa abdallah yadade da bazama wurin da ya hango yara na wasa cikin nishadi da annashuwa.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_39_
~~~Zuba mata idanuwa Abubakar Sadeeq yayi yana kallonta yana nazari,
"Ikhlas meyasa bazaki aure niba, Kodai ban kasance daga cikin irin mazan da kike so ba?"
Girgiza kai tayi tana murmushi "bahaka bane"
"To yayane?"
"Ban shirya aure bane acikin rayuwata"
"Kamar ya? Bakiji dadi bane agidan mijinki nafarko ko kuma rasuwa yayi ke kuma kike tunanin ko bazaki samu wanda zai iya maye gurbinsa ba?"
Girgiza kai ta sake yi "Sam ni ban taba aure ba ma"
Kallonta yayi da mamaki "to tayaya kikace abdallah kece kika haifeshi,haba dama ina tantama, wallahi ina doubting domin duk wanda ya ganki yasan ke budurwa ce"
"Wallahi nice mahaifiyar abdallah, nice na haifeshi"
"Tayaya?"
"Na haifeshi ba tare da uba ba, ina nufin abdallah bashida uba, dan haka kaga ni ba irin matar da zaka aura bace"
Kallonta yayi har lokacin da mamaki atare dashi,
"Wannan ba shine dalilin da zaisa na fasa aurenki ba, kawai nidai ki sanar dani abinda yafaru dake har kika haifi abdallah nikuma nayi miki alqawarin zan aureki ahaka kuma zan rike ki amana zan rike abdalla kamar dan dana haifa acikina"
Zamanta ta gyara ta tankwashe kafafunta ta fuskanceshi ta fara magana,
"Ikhlas Ahmad Buzu shine asalin sunana, mahaifina dan kasar Nijar ne cikin babban birnin niyami, shi kadai iyayensa suka haifa,
Lokacin da ya zama saurayi sai ya shigo kasar Nigeria domin neman ilmi da kasuwanci, acikin garin Zaria ya zauna a hannun wani malami inda yake koyon karatun allo, to malamin nashi yana zuwa Maiduguri ta jihar Borno yawon fatauci, duk shekara tare suke zuwa da babana,
Akwana atashi har babana ya zama dan gari yana zuwa Maiduguri da kansa ya koma Zaria yawon kasuwanci, tsakaninsa da kasarsu ta nijar kuwa sai dai yaje ya gaida mahaifiyarsa ya kai mata abinda ya samu,
Lokacin da babana yafara samun budi sai yafara neman aure amma kuma ba abashi ba hakan yasashi barin Zaria ya koma Maiduguri acan ya hadu da mahaifiyata suka fara soyayya, itama mahaifinta babban malamine, ganin babana almajirin ilmine yasa mahaifinta bashi ita aka daura musu aure suka koma Zaria,
Tunda suka yi aure sai mahaifina yafara samun budi, babu dadewa ya zama hamshakin dan kasuwa wanda yayi suna a nahiyar kasar nan,
Nijar ya koma ya dauko mahaifiyarsa ya dawo da ita nan gidansa sai dai kwata kwata yakumbo mahaifiyarsa bata son mahaifiyata ta tsaneta,
Haka suke zaune tana gallaza mata, kullum maganarta bata wuce abbana ya kara aure ko yasamu magaji tunda ita ammi bata haihu ba, amma abbana baya cewa komai sai dai yace akwai sauran lokaci tunda har yanzu basuyi shekara goma da aure ba,
Ana cikin haka ammi ta samu juna biyu tunda yakumbo ta fahimta sai hankalinta ya tashi nan ta shiga makirci iri iri dan ganin ta raba ammi da cikin nan amma hakan bai samu ba, lokacin haihuwa nayi ammi ta haifo yaranta yan biyu maza murna wurin mahaifina ba acewa komai dan ba karamin dukiya ya salwantar ba awurin sha'anin bikin suna,
Ba adade da suna ba ya kwashesu zuwa kasa mai tsarki suda jariran domin gudanar da umarah, iya yakumbo kawai aka Bari agidan, hakan ya sata shiga damuwa dan haka kafin su dawo sai tatafi nijar ta dauko yar kanwarta Nafi ta kawo ta gidan koda su abba suka dawo sai ta shiga matsa masa akan lallai sai ya auri Nafi,
Dafarko ya bujire amma da ta shiga yin magani da asiri sai ya yarda aka daura auren dama bazawara ce aurenta hudu, tunda akayi auren abubuwa suka sauya,
Ammi zaman hakuri kawai take agidan domin yakumbo da Nafi sun tsaneta sun tsani yayanta, lokacin data yaye su hussain alokacin ta samu cikina ai nan jaraba ta tashi agidan saboda ita Nafi har yanzu bata samu juna biyu ba dama bata taba haihuwa ba,
Asiri babu wanda basayi har takai da abba yafara tsanar yayansa yan biyu wadanda da babu wanda yake so kamarsu, ko kusa dashi sukaje sai fada da duka da hantara gamida kwazazzaba, nan ammi ta shiga damuwa domin itama yanzu baya sassauta mata amma tasan ba yin kansa bane aikin asirine,
Cikin wannan halin ammi ta samu ta haifeni bayan tasha mutukar wuya domin ranar abba baya nan dan haka yakumbo da Nafi suka ki koda taimaka mata ne suna jinta tana kwalla musu kira babu wanda ya amsa tun safe take daki tana nakuda har dare sai sha dayan dare ta haihu alokacin ta tura hussain yaje ya kirawo mata makociyarta talatu wacce itace tazo tayi mata komai ta gyara jaririyar, duk da mahaifina yana cikin hali irin na asiri hakan bai hanashi murna da samun haihuwata ba.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/20, 8:43 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_
_40_
~~~Yayi murna sosai kuma yayi farin ciki ya kashe kudi domin hidimar suna, ranar suna aka sanya min suna ikhlas wannan shine sunan da mahaifiyata ta zabar min,
Nan fa yakumbo ta shiga maganganu saboda ba asaka sunata ba wannan dalilin ne yasata sake tsanar mahaifiyata da yayanta,makaranta ma da aka saka su Hussain ata kudi haka ta tada sababi tasaka abba adaki ta zazzageshi tace lallai lallai aciresu domin bazata zuba ido tana ganinsa yana watsa kudinsa ba alhalin ba gama haihuwa yayiba, ga Nafi nan itama haihuwa zata yiyyi nan gaba, da yake dane mai biyayya sai yabi maganarta domin baya yi mata musu.
Makirci da manakisa babu wacce ammi bata ganiba, ga sharri kala kala, ranar da bazan manta ba itace lokacin ina yar shekara biyar,
Yayuna sun tafi makaranta sai ammi tafita ta dora mana abinci tana girkin yakumbo da Nafi suka fito suketa zaginta amma bata ko daga ido ta kallesu ba har takusa kammala aikinta,
Tagama abincin kenan tazuba min ina ci, Nafi ta debo dakakken barkono ta watso ma ammi wannan yayi daidai da shigowar su hussain daga makaranta, ai hussain na ganin haka ya daka tsalle ya ballo reshen bishiyar umbrella din dake tsakar gidanmu ya nufi yakumbo da Nafi,
Yana zuwa ya hau jibgarsu dayake shi mutumne mai zafin rai da zuciya, duka sai da yayi musu lilis dakyar suka gudu daki,
Shikam hassan kallo ya tsaya yi saboda sam bashida fada, wannan dukan da hussain yayiwa su yakumbo shine sanadin da yasa yakumbo ta tursasa abba ya saki ammi kuma tace bazata bar su hussain ba sai dai tatafi da tsiyarta,
Nice kadai aka barni agidan domin abba yana mutukar sona yana ji dani saboda ina jin acikin magungunan da su yakumbo keyi basu samu wanda zai rabashi dani ba,
Fada maka irin bakar wahalar dana sha ahannun matar uba da yakumbo abin kamar bata bakine domin nasha wahala sai dai suna yin hakanne idan abba baya nan amma idan yana nan nuna min so suke yi,
Ahaka nayi primary private nagama har nayi secondary nanma na kammala lokacin nazama budurwa sosai ga gata da abbana yake nuna min domin lokacin ya shiga siyasa kuma yayi suna sannan ya samu karbuwa,
Dakina daban abba ya shirya min ya saka min kayan kyale kyale irin wanda duk wata budurwa zata bukata,
Shekarata daya da gama secondary abba ya kaini aikin hajji, acan na hadu da wani saurayi kamal Wanda dan gidan wani senator ne a abuja,
Muna dawowa gida kamal yafara zuwa wurina, hidima da kashe kudi yana yimin sosai, irin hirar da naji Nafi da yakumbo suna yi domin ganin sun cutar da abba ta hanyar zuba masa garin magani yasa nafara girkawa abbana abincinshi dakaina, nice nake dafa duk wani abu wanda zai ci,
Haduwarmu da kamal baifi da wata uku ba senator yazo gidanmu yakawo kudin aurena naira dubu dari biyar da kujerar hajji,
Ai wannan abu ba karamin daga hankalinsu Nafi yayiba take suka shiga kulle kullensu nikam ban san abinda ke faruwa ba,
Ranar lahdi da daddare lokacin abba yatafi abuja hajiya Nafi ta shigo har dakina tace zobene na azurfa aka kawo tallarsa wata kawarta data dawo daga dubai nima gashi ta dauka min idan abbana yadawo sai yabada kudin,
Batare da tunanin komai ba nakarba na ajiye akan mudubina, kin tafiya tayi tace nasaka tagani,
Dauka nayi nasaka dama daga wanka nafito, nadauko Pakistan dina riga da wando nasaka take naji wani irin nannauyan bacci yana daukana nan nakwanta awurin, tsakar dare natashi nafice nabar gida shikenan ban sake sanin inda hankalina yake ba,
Koda gari yawaye aka nemeni aka rasa, abba ma lokacin da yadawo ya tarar ana nemana hankalinsa ba karamin tashi yayiba,
Nan yabaza mutane nemana gidan radio da jaridu da gidajen tv duk cikiyata ake an manna hotuna na, abbana har cewa yayi duk wanda ya samoni zai bashi miliyan biyu amma shiru,
Adakina aka samu wata wasika wai nice na rubuta acewar su Nafi,
_Zuwa ga abbana abin sona, abba nasan zaka yi mamakin ganin wannan wasikar tawa to ba abin mamaki bane na rubutata ne domin nasanar dakai cewar natafi zan shiga duniya yawon karuwanci domin ta wannan hanyar ce kadai da zan iya rama abinda kayiwa mahaifiyata, zanje na iyo cikin shege nadawo gidanka domin ina son mutane su tsaneka sudaina yinka._
_Nabarka lafiya,_
_Daga yarka ikhlas_
Lokacin da abbana yaga wannan wasikar ba karamin bakin ciki yayiba amma sai su Nafi suka fita daga zargi bai zargesu ba saboda wasikar da yagani.
Labarin taci gaba da bashi har izuwa yau ta kare labarin tana kuka,
"To tayaya da mutuncinka zaka auri wacce tayi cikin shege ta haihu"
Murmushi sadeeq yayi yace,
"Ikhlas kenan, wannan bazai zama dalilin da zai saka naki aurenki ba, saboda kaddara ce ta afka miki bawai da ganganci kikayi ba, ni nayi alqawarin zan aureki ahaka nan bada dadewa ba, insha Allahu nan da wata biyu kina gidana a matsayin matata, sai dai na manta ban fada miki ba inada iyali, sunanta Suhaima da yaranmu Hudu, haydar, faruk, sayyid da kanwarsu Aysha,"
Murmushin karfin hali tayi tace "Allah ya rayasu"
"Amin, ni dan yolane mahaifina babban alkaline a yola, ina da yayu biyu daya mace daya namiji sannan inada junior brother guda daya"
Daga kai tayi alamar gamsuwa,
"Yakamata muje na mayar daku gida tunda yamma tayi kar ammi tayi fada"
Murmushi tayi ta mike tana kokarin nannade dardumar da suka zauna akai, shine yaje ya kamo hannun abdallah daga wurin da suke wasa shida yara,
Sai da ya biya dasu ta supermarket yayi musu siyayya sannan ya mayar dasu gida.
_Gaisuwai mai tarin yawa gareku dunbin masoyana masu karanta littafina, hakika ina alfahari daku kuma ina kaunarku aduk inda kuke._
0 comments:
Post a Comment