~~~Tun daga lokacin Abubakar sadiq ya mayar da gidansu ikhlas gida domin kullum sai yazo, yanzu agidan babu wanda bai sanshi ba, abdallah kuwa tamkar dan cikinsa domin kullum suna tare,
Ita kanta ikhlas din yanzu ta sake dashi ta amince masa duk da dai bataji tana tsananin sonshi ba amma zata aure shi domin halaccin da yayi mata,
Tamfatsetsiyar waya mai tsada ya siyo mata gashi duk abinda zata bukata yana siyowa ya kawo mata, nanfa yafara neman aurenta gadan gadan,
Ganin ba wani auren saurayi bane yasa su ammi yanke ranar auren sati uku, nanfa aka shiga shirye shiryen biki domin a yola zata zauna sannan yace bazai hada musu gida da matarshi ba kowa gidansa daban,
Yayunta sunyi rawar gani sosai wurin siya mata furniture's masu tsada hadaddu kirar royal,gyara kuwa na amare tashashi domin indai gyarane to gidan ta taras, gyaran jikin da akayi mata hatta fatarta sai da ta sauya tayi laushi lubus kamar ta jarirai,
Abubakar sadiq ya dage sosai wurin yi mata kayan lefe masu tsada komai irin wanda ake yiwa budurwa yayi mata,
Ranar juma'a da misalin karfe 2 na rana aka daurawa Abubakar da ikhlas aure acikin garin borno,
Aranar aka tafi da ita yola domin kaita gidanta, kuka itada abdallah dakyar aka rabasu domin Hussain yace ba zata tafi dashi ba sai dai ya rinka zuwar mata hutu.
Hanyar birnin yola aka dauka da ita tana tukunkune cikin katon mayafi sai kuka take yi aranta kuma tana jin girman Abubakar sadiq da kimarsa tana kara karuwa acikin zuciyarta domin yayi mata komai ya rufa mata asiri ya sota ya nuna mata kauna hakika ya zamar mata wajibi ta zauna dashi da gaskiya kuma ta kyautata masa,
Sai daf da sallar magrib suka samu suka shiga garin yola, kai tsaye gidanta dake unguwar senate roads aka dauka da ita domin ko sallar la'asar basu samu sunyi ba,
Suna zuwa gida ya cika da hayaniya dakinta kuwa jama'ar ta isa, sai dai abinda yake tayarwa da ikhlas hankali shine faduwar gaban datake tayi koda wanne lokaci,
Daurewa tayi tafita inda sadiq ke tsaye yana jiranta bayan sun gama waya,yana tsaye a bayan dakunanta yasha shadda ruwan kasa mai masifar kyau,
Hannunta yakama suka tasamma dakinsa,
"Muje kiyi salla ko?" Yace da ita yana duban fuskarta, kai ta daga suka shiga dakin nasa wanda ya tsaru mutuka,
Yana zaune yana kallonta tayi sallar ta idar,
"Yanzu kije kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta, gobe idan Allah ya kaimu gidanmu za a kaiku domin acan za ayi wunin biki sannan da yamma idan brother na yadawo akwai walima wacce za agabatar a Mubarak hotel",
Batare da tayi magana ba kawai ta mike zata fita, hannunta ya kamo wanda yasha kunshin jan lalle da baki wanda ba karamin kyau yayi mata ba, kyau kam ikhlas tayishi babu wanda zai ganta yace ba budurwa bace,
"Kunshin yayi kyau my.." Yafada yana sinsinar hannunta,
"Nagode" ta bashi amsa atakaice,
Dakyar ya saketa tafita ta koma dakinta Wanda yake cike da yan rakiya domin duk yan gidansu babu wanda baizo ba in banda ammi amma hatta matan Hussain da hassan duk sunzo,
Wanka ta shiga ta fito saboda jinta take agajiye sosai, tana gefen gado tana Shafa mai hajiya kakarta ta dubeta,
"Yarnan banga kinci komai bafa, ina jin rabonki da abinci yau kwana biyu kenan"
"Kibarta hajiya ai dura za muyi mata wallahi idan ta gama shiryawa" shamsiyya matar hassan tafada tana dariya,
"Angon zamu kira kawai yayi mata durar" farida matar Hussain ta cafke zancen, ita dai ikhlas tana zaune tana jinsu bata tanka ba domin ita kadai tasan irin faduwar gabar datake addabarta.
*
Zaman Lamido da fadila akasar Kenya haka yayita tafiya yau da dadi gobe babu amma kasancewar ita fadilan tana mutukar sonshi yasata fara dan gyara halinta tana yin abinda yake so,
Yau tunda suka tashi daga barci yafara yi mata albishir din gobe zasu tafi Nigeria amma bazai dawo da itaba shi kadai zai dawo,
Duk da haka tayi murna amma tasan zatayi missing dinshi hakan yasata langabe kai,
"My Lamido zanyi missing dinka idan ka dawo kabarni"
Hannunta ya rike yana kallon kyakkyawar fuskarta,
"Karki damu my fadila just three months kawai zanyi nadawo shikenan nagama, zamu kasance har abada tare"
Kiss tayi masa agoshi ta tashi ta shiga toilet,shiryawa sukayi suka fita domin yin siyayya, kaya sosai fadila ta dibarwa yan gidansu da kawayenta,
Shikam Lamido ihsan ya saiwa kayan shakatawa itada prettyn sa, sai ko brother dinshi da ya siyawa agogon silver mai kyau,
Kasancewar jirgin karfe bakwai suka bi yasasu sauka da wuri domin karfe 10 daidai na agogon Nigeria suka sauka, bash ne yaje daukosu, nan Lamido yafara tambayar bash tun acikin mota,
"Bash ya alkawarinmu? Ka samo min pretty din?"
Murtuke fuska fadila tayi jin an ambaci mace amma hakan bai damu lamido ba saima ci gaba da yayi da tambayar bash,
"Nifa wlhi nama manta da wata pretty dinka" bash yafada yana driving,
Tsaki Lamido yaja yashafa sumar kansa,
"Insha Allahu kuwa sai na nemota da kaina"
"Yafi maka dai" bash yabashi amsa,
Lamido bai sake magana ba har suka je gidansa, ihsan suka samu ta shirya musu kayan tarba kala kala iri iri amma kuma tsakaninta da fadila babu kallon arziki sai hararar juna suke yi kamar zasu kwancame da dambe,
Jikin Lamido ihsan taje ta shige tana murna,
"I missed you my Lamido.." Ihsan tafada tana rungume dashi,
"Me too my ihsan, ya studies?" Ya tambayeta yana shafar kumatunta,
"Kaga mai mata biyu angon fadila da ihsan dan gatan baffa" bash yafada cikin zolaya,
"Akwai ta ukun ma tana nan zuwa" Lamido yace dashi bayan ya zauna akan kujera,
Abincin da ihsan ta shirya musu ta fara zuzzuba musu, babu laifi tayi kokari kuma abincin yayi dadi amma fadila kamar adole take ci saboda sai wani yatsine yatsinen fuska take yi, ita kam ihsan bata kara bin ta kanta ba tana can jikin Lamido ta lafe sai ciyar da junansu abinci suke, abin nasu gwanin sha'awa shi kansa Lamido yana tsintar kansa cikin farin ciki idan ya kalli ihsan da fadila saboda dukkaninsu kyawawa ne na karshe hakika yasan ya yi sa'ar mata masu kyau presentable yanzu burinsa dayane ya mallaki pretty dinshi a matsayin mata.
_Masu karatu kuyi hakuri da wannan dan babu yawa, gaisuwa mai dunbin yawa agareki Ramlat Muhammad maska keda dukkanin masoyana masu sona, ummi Aisha tana sonku fiyeda yadda kuke sonta._
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/24, 7:40 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_42_*
~~~ Sai da ya huta sannan ya fita shida bash zuwa kasuwa, kayan da zai bawa brother dinshi gifts yaje ya siyo,
Lokacin da ya dawo gida har ihsan da fadila sun tafi gidan bikin dan haka bedroom dinshi ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito domin zuwa wurin bikin amma kuma gabansa sai faduwa yake bai san dalili ba,
Farar shadda yasaka da jar hula, dinkin iya gwiwa ne rigar,yayi kyau sosai, komai nasa mai kyaune, motarshi ya dauka ya fita zuwa gidan innah lokacin karfe 4 na yamma,
Dakyar ya samu ya ga innah saboda jama'ar da suka cika gidan shikuwa baffa baya nan, dangi sai tsokanarshi suke "kaga mai mata biyu, da wuri zaka tsufa"
Dariya kawai yake yi yayi gaba, acan gate ya hango brother dinshi dan haka ya karasa gareshi suka rungume juna,
"Broz ina ne wurin walimar ne?"
"Mubarak hotel ne Lamido, kaje nima yanzun nan zanzo, kaga sai ku gaisa da yayar taka"
Murmushi Lamido yayi "congrats broz"
Juyawa yayi ya hau motarsa yafita ya nufi wurin walimar,
Lokacin da yaje anfara gudanar da wa'azi amma amarya da ango basu karaso ba, zama yayi awurin da aka warewa maza nan ya ciro phone dinshi yafara chtn, mintuna kadan yaji mai wa'azin yana shelar cewar ango da amarya sun karaso zasu shigo yanzu,
Daga dara daran manyan fararen idanuwanshi yayi ya soma kallonsu, tasha jan leshi da lifaya ja an nannade mata jikinta baka ganin komai ajikinta sai fuskarta wacce tasha kwalliyar amare,
Mikewa tsaye yayi yana kallonta, ahankali ya murza idonshi ya bude domin gani yake kamar mafarki yake yi,
"Pretty..." Yafada ahankali muryarsa tana rawa, sai binta yake da kallo daga karshe dai ya tabbatar itace saboda bazai taba mance kamanninta ba,
Wani jiri ne yafara daukarsa babu shiri yafita daga cikin hall din, wani juyawa yaji kanshi yana yi ga wani irin ciwo da ya dauka,
Ahankali ya shiga motarsa ya fizgeta zuwa gidansa, gudu ya sharara mintuna kadan ya isa gidan, dakinsa yawuce ya rufe kofa ya kwanta akan gado,
Hotonta ya janyo yafara gani kawai sai ya fashe da kuka kamar wani karamin yaro,
Kuka yake wiwi kamar tababbe,
"Shikenan na rasata, narasaki pretty, narasaki" yafada yana kuka,hotonta ya rungume akirjinsa yana kuka sosai,
Har mangaruba tayi su fadila suka dawo bai bude kofar ba yana ciki yana kuka, kasancewar ihsan ce dashi yasata zuwa ta fara nocking din kofar tashi amma bai budeba,
Sarawar da kansa keyi masa yasashi dole yin shiru yabar kukan, nan take zazzabi ya rufeshi babu dadewa baccin wahala yayi gaba dashi bashi ya farka ba sai tsakar dare misalin karfe 3 daidai,
Kansa ya rike wanda yake jinsa yayi masa nauyi sosai, dakyar ya iya mikewa yaje toilet yayi alwala yazo yayi salla, ko tantama baya yi yasan jininsa yahau karshen hawa,
Wani sabon kukan yafara, kwana yayi yana kuka ciwon kai kuwa kamar kansa zai tsinke da azaba, sai da gari ya waye ihsan tazo tana buga kofar sannan ya tashi ya bude,
Kallo tabishi dashi duk fuskarsa ta kumbura idonsa kuwa ba acewa komai saboda jan da yayi bau,
"My Lamido meya sameka?" Ta tambayeshi tana shafar fuskarshi,
Murmushin yake yayi "bani da lafiya ihsan gashi harda ciwon ido"
"Ayya sorry naga fuskarka ta dan kumbura gashi idonka yayi ja da yawa"
Bakin gado yakoma ya zauna ya tura hoton pretty kasan gado da kafarshi gudun kar ihsan tagani, kusa dashi tazo ta zauna ta kama hannunshi duk ta damu,
"My Lamido na kawo maka tea?"
"Kawo min dan kadan"
Tashi tayi tafita, ahankali ya goge kwallar idonshi shikam yasan dole ciwon zuciya ya kamashi domin bazai iya sanarwa da yayansa cewa wacce yakeso ya aura ba,
Ihsan ce ta shigo dauke da kayan breakfast akan farantin silver, tea ta hada masa yana daga kwance kafaufunshi akasa yana kallon sama,
Jikinshi ta shiga ya tashi tafara bashi, dakyar yasha rabin cup domin jin shayin yake kamar madaci yake sha,
Ganin ya dade baya nan yasan cewar ihsan tana da bukatar kasancewa dashi, ahaka ya daure duk da baya cikin nutsuwarsa ya kulata,
Wanka yaje yayi yafito ya shirya cikin kananan kaya farar t shirt da bakin wando, bakin glass yasa afuskarsa yafita ya nufi gidan innarsa domin ya yanke shawar cewar nanda kwana biyu zai tafi Kenya,
Lokacin da yaje yan biki duk sun tattafi saura guntu, kebewa sukayi da inna ya sanar da ita zai koma Kenya jibi,
"Lamido lafiyarka kuwa? Naga kamar baka da lafiya" innah tace dashi tana duban fuskarshi,
"Ehh innah, ciwon kai nake yi da ciwon ido yanzu ma idan nafita sai naje asibiti naga likita"
"Kai Lamido kullum kai kenan a ciwon ido anya kuwa?"
"Eh inna lalura ce ai"
"To Allah yabaka lafiya"
Tashi yayi yanufi side din baffa yana shiga ya samesu tareda yayanshi sadiq,
"Ah broz baka je kun gaisa da yayar taka ba" yayanshi yafada yana murmushi,
"Zanje ai broz banida lafiya ne"
"Allah ya baka lafiya"
Zama yayi suka gaisa da baffa anan Lamido yake sanar masa da jibi zai koma, tashi yayi ya fita yashiga motarsa yana driving yana kuka, tabbas yasan indai ya sanarwa da yayanshi cewar matarsa itace farin cikinsa itace burinsa to yasan zai bar masa to amma baya son yayi hakan saboda baya son ya zamo daga cikin mutane masu son kansu,
Abakin kasuwa yayi packing, hannunshi yaduba wurin da ya rubuta sunanta gashi nan radau rubutun yayi baki kamar irin zanen nan na tatu wanda turawa suke yi,
Idonshi ya lumshe wasu hawayen suka sake bin kumatunsa,
Wurin da ya yimata fyade yafara kallowa acikin zuciyarsa, karar wayarshi ce ta dameshi, ahankali ya zarota daga aljihunsa, bash ne dan haka ya daga yana share hawayen fuskarsa,
"Hello bash"
"On top kana inane?" Bash ya tambayeshi,
"Ina bakin kasuwa"
"To bari nazo"
Kashe wayar yayi ya kifa kansa ajikin sitiyarin motar yana kuka, har bash yazo bai saniba sai da ya shigo cikin motar ya dafashi, dagowa yayi fuskarsa jagaf da hawaye kamar karamin yaro.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/24, 7:40 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_43_*
~~~Dagowa Lamido yayi yana kallonsa,
"Lamido kuka? Kuka fa kake kamar karamin yaro,meya faru?"
Rungume bash yayi yafashe da kuka "bash narasata,wallahi narasata har abada"
"Wacece? Taya akayi kasan ka rasata? Haba Lamido be a man mana amma ka zauna kana kuka kamar wani mace"
Hawayen fuskarsa yafara sharewa yana kallon bash,
"Lamido wa ka rasa?"
Shiru Lamido yayi domin baya son ya sanarwa da bash abinda yafaru, tambayar duniya bash yayi masa amma yaki fada masa gaskiyar abinda ya faru,
"Bash duk burina yanzu ya wargaje, shirina duk yagama baci, banida burin da ya wuce sai na pretty ashe ba rabona bace" yafada muryarsa adashe saboda kukan da yayi,
"Kayi hakuri Lamido, dan Allah kabar kukan nan, nayi maka alkawari zan tayaka burinka ya cika"
Kallon bash yayi yana murmushi mai ciwo,
"Bash ba zaka gane bane, muje ka ajiyeni agida"
Exchanging din wurin zama suka yi bash yafara driving yana jin tausayin Lamido,
Gidansa ya kaishi ya ajiyeshi yatafi, a falo ya iske ihsan tana kwance tana kallo, ita kuma fadila ta tafi ganin gida,
Tasowa ihsan tayi ta kamashi zuwa dakinsa kwanciya yayi ya rike kansa wanda ke faman yi masa zugi,
Wuni yayi a kwance ranar bai tashi ba sai dai idan zaiyi salla, ihsan duk tabi ta shiga damuwa domin tana tsananin sonshi jin ciwon take har cikin ranta,
Kayansa yasata ta shirya masa domin tafiyar wuri yake son yayi.
*
Abangaren ikhlas amarya kuwa tunda aka tashi daga walimar bikinta taji wani zazzabi yana shamayarta dan haka ana tashi Abubakar sadiq ya kama hannunta aka nufi gidanta da ita, suna zuwa yan uwanta suka fara yi mata sallama domin komawa borno,
Kuka kam ta shashi kamar ranta zai fita, dakyar sadiq ya iya rarrashinta ya samo mata abinci taci ta kwanta,
Kwananta biyu tana zazzabi Kafin ta samu ta warware, duk wata kulawa wacce mace take bukata awurin miji to sadiq yana bata ita gashi kwana bakwai zaiyi mata saboda itama bata taba aureba,
Babu laifi ta dan sake dashi saboda mutumne mai raha da faran faran, har ya gama yi mata kwana bakwai dinta ya koma gidan uwargidansa bai gundireta saboda yanda yake tarairayarta yana bata kulawa, kuma aranar ya kawo mata yaranshi domin su tayata zama ko zasu samu damar dauke mata kewar rashinsa,
Tana kitchen tana aiki ya shigo ahankali ya sadado yazo ya rufe mata fuskarta, murmushi tayi ta zame hannunshi tana dariya,
"Ai naganeka"
Juyo da ita yayi yana murmushi,
"Bawani nan"
"Sannu da zuwa, mu karasa falon"
Hannunta ya kama suka fita yana cewa "hotunan bikin nakawo miki an wankosu"
Zama tayi agefensa yafara zaro mata hotunan tana gani,
"Woww handsome" tafada ahankali daidai lokacin da tazo kan hoton Lamido kaninshi,
"Wannan hadadden gayen fa? Waye?" Ta tambayeshi tana kallonsa,
"Brother nane jiya ya koma kenya amma ya kusa dawowa ma gaba daya, ya akayi?"
"Gaskiya yafika kyau wallahi, nidai ban yarda ba kodai exchange za ayi? Tafada cikin tsokana,
"Ehh ayi nabar masa dama ai shine karami amma idan kin shirya zama da kishiyoyi saboda matanshi biyu kinga zaki zama ta uku sannan kuma zai karo ta hudu nan gaba"
Zubawa hoton ido tayi gabanta yana faduwa aranta tana yaba kyau irin na lamido gashi dan gayu na karshe,
"Dagaske matanshi biyu?" Ta tambayeshi,
"Wallahi dagaske"
"Um mudai ba haka muka so ba kanin miji yafi miji kyau, gashi wannan hausar tayi tasiri akanmu kanin mijinmu yafi mijinmu kyau"
Murmushi sadiq yayi yaja hannunta yana cewa, "bawani kyau da yafini kawai dai yafini rashin ji"
Tun daga lokacin ta shiga tsokanarshi cewar kaninshi yafishi kyau ita da tasan da wannan kanin nashi da tafasa auren shi ta auri kanin, murmushi kawai yake yi idan yaji ta fadi haka sai yace ai yanzun ma yaci girma ya barwa kanin nashi, kullum haka suke rayuwarsu cikin nishadi da girmama juna,abdallah kuwa kullum tana makale awaya dashi suna hira domin ba karamin missing dinshi tayi ba.
*
Da damuwa mai mutukar yawa Lamido yakoma kenya amma yakasa fadawa kowa damuwarsa, yana komawa yakoma harkar shaye shayen da yadaina, gashi wani irin ciwon kai yake fama dashi dolensa sai da ya ziyarci asibiti, koda likita ya dubashi jininsa yayi mugun hawa saboda damuwa da bacin ran dake addabarsa,
Yanke mu'amalarsa yayi da kowa domin tunda ya dawo baiyi waya da gida ba domin hatta bash sau daya suka yi waya ya cire sim din ya ajiye wayar, matanshi ne ma wani lokacin yana chtn dasu ta facebook idan ya bude system dinsa.
Haka rayuwa taci gaba da tafiyar masa cikin kunci da bacin rai har lokacin zana jarabawarsa ta karshe tayi, kullum cikin shan abun maye yake neman mata kuwa kamar beyi aure ba.
_*Ummi Shatu*_👌🏻
[12/24, 7:40 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_44_*
~~~Da haka Lamido ya samu ya kammala jarabawarsa amma ya dan rame yayi baki, aranar da yagama washe gari ya dawo Nigeria,
Murna wurin ihsan da fadila tamkar zasu cinyeshi, kowacce nuna masa soyayya take hakika ya tabbatar shi dan gatane,
Dawowarsa babu yanda yayansa baiyi dashi ba akan yaje su gaisa da ikhlas amma yaki zuwa,
Kullum yana rufe acikin daki sam baya walwala amma ahakan yana daurewa yabawa matanshi kulawa, ganin yanayin da yake ciki yasaka innah zaunarshi ta tambayeshi damuwarsa amma fur yaki sanar da ita, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin damuwa da bacin rai,
Ganin abun kullum gaba yake yasa baffanshi saka malamai aka fara yi masa rokon Allah,
Yadan samu sassauci acikin zuciyarsa amma damuwa kam har lokacin yana tattare da ita, ga tsananin ciwo da kanshi yake yi masa.
*
Zaman ikhlas da Abubakar sadiq abin gwanin ban sha'awa kullum cikin faranta ran junansu suke, watansu daya da aure ikhlas ta fara laulayi, koda sukaje asibiti gwajin farko likita yace tana dauke da juna biyu, murna wurin Abubakar sadiq abin ba acewa komai, wata sabuwar kulawa ya shiga bata alokacin yaje borno ya dauko mata abdallah domin yayi mata hutu amma Hussain dakyar ya bari aka taho dashi dan yayi mata sati biyu kacal, tunda abdallah yazo Abubakar sadiq yake fita dasu wuraren shakatawa har ya gama yi mata sati uku yatafi saboda kullum sai Hussain ya bugo waya yana cewa adawo dashi,
Gidan barrister elmustapha Abubakar sadiq ya kaita ta wunarwa ni'ima wacce tana nan dauke da yarta Ikhlas, wuni sukayi suna hira ita dai ni'ima duk kunyar abubuwan da ta yiwa ikhlas abaya yanzu take.
Cikin ikhlas yanada wata uku Abubakar sadiq ya samu sauyin wurin aiki inda aka mayar dashi bauchi alokacin ya shirya yaje yayi report ya dawo, dawowarsa da sati biyu ya shirya tafiya, rigima ikhlas ta saka masa adole sai ya tafi da ita, dakyar ya rarrasheta yace next time idan yazo tare zasu koma,
Rakashi tayi ta dawo tana murmushi, ko minti talatin ba ayiba da tafiyarsa kaninshi lamido yazo gidan idonsa jajur, wannan shine karo na farko da yazo gidan,
Tana dakinta tana nunke kayanta taji sallamarsa cikin daddadar muryarsa duk da mganarshi tana dan shigen kama da irin ta Abubakar sadiq amma ta lamido tafi dadi,
Hijab tasa ta fito tana amsa sallamar, sai da gabanta ya fadi lokacin da suka yi ido biyu domin ba karamin kyakkyawa bane ashe ganin da tayi masa ahoto kyansa bai bayyana ba,
"Am dama brother sadiq ne yace nazo mutafi tare dake" yafada ahankali yana kallonta,
"Yana ina? Lafiya? Ina zamuje"
"Lafiya lau, kizo muje yana can gidan uwar gidanshi"
Babu abinda ta dauka tabi bayanshi ko gidan bata rufeba domin jikinta yabata babu lafiya,
Motarshi suka shiga amma agidan baya ta zauna yatashi motar suka nufi titin asibitin makama,
Koda suka isa tuni harsu baffa da uwargidan Abubakar sadiq sun karaso, innah da uwargidan sai kuka suke ga yaranshi ma sunata kuka abin tausayi,
"Lafiya? Meya faru? Meya samu sadiq din?" Ikhlas ta tambaya agigice,
Rungumeta uwar gidanta tayi tana kuka "hatsari yayi,over taking akayi masa tifa tabi ta kansa, shikenan zamu rasaka..." Tafashe da wani sabon kukan,
Lamido ne ya mike yabi bayan likita domin za adebi jininsa akarawa sadiq,idanuwansa sunyi jajur daga gani hankalinsa atashe yake,
Wunin ranar ba abarsu sun shiga inda yake ba sai da daddare suka samu ganinsa, yana kwance ko ina na jikinsa an nannade da bandeji kansa ya kumbura mutukar kumbura kamar an hura,ko ina jini ya firfita ajikinsa,
"Sannu.. Sannu sadiq" ikhlas tafada tana kuka,
Hannun uwargidanshi ya kamo yarike ahankali yafara magana wacce ba aji har sai an kasa kunne,
"Allah yayi miki albarka, Allah ya raya mana yaranmu, kiyi hakuri zan tafi nabarki da nauyinsu akanki, kiyi hakuri ki basu tarbiya yadda ya kamata, Allah yayi miki albarka"
Rushewa da kuka uwargidan tayi tafita waje, hannun Lamido ya kamo ya kamo hannun ikhlas,
"Lamido kai Kanina ne hakika nasan zaka iya rike min amanar iyalina, ga ikhlas nan ka aureta ka riketa kabata kulawa da duk wani gata kamar ina raye, Lamido ka aureta saboda bana son ikhlas ta auri bare wanda ba jinina ba ina jin tausayin ikhlas saboda zan tafi nabarta daidai lokacin da take bukatata..." Take yafara wani tari mai ban tausayi,
"Tana dauke da juna biyu, nabar maka amanarsu itada abinda ke cikinta...." Iya abinda ya iya fada kenan tari mai sarke kirji yaci karfinsa take yafara aman jini, kuka wiwi ikhlas take rerawa dakyar innah ta kamata suka fita itama tana kukan,
Dawowa cikin dakin innah tayi nan tasamu Baffa Abubakar sadiq yana yi masa jawabi irin wanda yayiwa ikhlas da Lamido amma kuma yakasa fada sosai saboda tarin da yaci karfinsa, shi kansa sadiq din kuka yake yi sosai,
Lamido kam sarkin kuka tun dadewa hawaye suka balle masa, shigowar likita ne yasasu fita waje dukkaninsu suna fita suka iske yaran sadiq suna kuka suna cewa akaisu suga abbansu,
Wannan kadai ya isa saka mutum kuka, tsit wurin yayi baka jin komai sai kukansu, alokacin babban yayansu lamido da yayarsu suka karaso nan wuri ya sake barkewa da kuka,
Dare suka raba suna koke koke duk cikinsu babu wanda yayi bacci suna zaune suna jiran tsammani har asuba tayi alokacin Abubakar sadiq yayi shahada ya cika,
Likitan ne ya fito fuskarshi daukeda alhini ya shaida musu cewar Abubakar sadiq ya rasu,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" shine abinda kowannensu ya furta, nan kowa yafara kukan zuci wanda yafi nafili ciwo, lamidone suka shiga shida babban yayansu suka fito da gawar,
Gida dukkaninsu suka dunguma suka tafi, suna zuwa labari yafara yaduwa cewar Allah yayiwa Abubakar sadiq rasuwa nan gida yafara cika da yan uwa da abokan arziki, innah ko hawaye batayiba tana zaune rikeda cazbaha a hannunta,
Ita kuwa ikhlas hawayen ma har ya kafe tana kwance ajikin bango ta takure,
Tun asuba aka yi masa wanka aka shiryashi gari yana wayewa misalin karfe tara aka yi masa salla aka tafi kaishi bayan yan uwa sunje sunyi masa addu'a,
Ikhlas tana kwance ta rike kanta takasa koda motsi rabonta da abinci tun jiya da safe kafin sadiq yatafi, tana nan kwance yan gidansu suka zo daga Maiduguri lokacin karfe 12 narana,
Ko ruwa bata iya shaba innah tayi tayi da ita tasha koda tea ne amma takasa sha, tana daga kwance tana kallon kowa ciki harda matan lamido ihsan da fadila.
Misalin karfe 4 na yamma tana inda take a kwance innah tazo tana kiranta cewar tayi baki, tashi tayi ta fita jiri yana daukarta, ni'ima matar elmustapha tagani sunzo yi mata gaisuwa.
*_Ummi A'isha_*👌🏻
[12/24, 7:40 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_45_*
~~~Falo suka dawo ita da ni'iman ta nemi wuri ta zauna ko magana bata iya yi sai dai daga kai,
"Sannu ikhlas Allah yayi masa rahma,dazu barrister ya kirani yace nazo nayi miki gaisuwa kafin ya dawo shi baya nan yayi tafiya zuwa kaduna wurin wani case"
Daga kai ikhlas tayi bata iya yin magana ba, ni'iman ta dan jima kafin ta tashi zata tafi, bin bayanta ikhlas tayi dakyar ta rakata tsakar gida suna fita ta hangi lamido tsaye shida wani mutum wanda daga gani kanin mahaifinsu ne ko wa,
Binsa tayi da kallo shi dinma yanzu duk ya zama wani abun tausayi domin har yayi wata yar rama,
Daga inda take tayiwa ni'ima sallama ta juya ciki, dakin innah taje ta kwanta domin nan babu mutane sosai tana nan a kwance har mangaruba tayi, tashi tayi tai salla tana idarwa ta koma ta kwanta,
Muryar Lamido ta fara jiyowa yana yiwa innah magana suna dosowa cikin dakin,
"Innah zaman makokin nan fa duk bidi'a ce babu ita a koyarwar annabi, dan haka ana yin kwana uku kowa ya watse yatafi yaci gaba da harkokinsa" Lamido yafada kamar zaiyi kuka domin wannan mutuwar ta sadiq ta bugeshi mutuka,
"Haka baffah ma yace domin duk wani labarin duniya agidan mutuwa zakaji ana yinsa awurin karbar gaisuwa dan haka sai kaga maimakon asamu lada sai ayita daukar zunubi"
"Ai ana yin kwana uku wallahi kowa sai ya tafi.." Daidai lokacin suka shiga cikin dakin,
"A'a ikhlas dama kina nan?" Innah ta tambayeta, kai ikhlas ta daga, kallonta Lamido ya danyi duk bakinta yagama bushewa gashi tayi wani irin sanyi,
"Innah bata da lafiya ne??" Ya tambayi innah,
"Ehh to kasan mai juna biyu ba a rabashi da ciwo gashi kwata kwata bata ci abinci ba nidai ko ruwa banga tasaka acikinta ba..."
"Kuma shine take kwance??" Yafada arazane, da saurinsa ya fita mintuna kadan ya dawo hannunsa rikeda gwangwanin maltina,
Bude gwangwanin yayi batare da ya kalleta ba yace "tashi kisha malt"
Dakyar ta tashi saboda wani jiri take ji, karba tayi tana mamakinsa domin duk maganar da zai yi mata baya kallonta asalima gani take kamar dole yayansa marigayi yayi masa wurin bashi amanarta data abinda ke cikinta, domin sam kamar bashida ra'ayinta,
Sanyi karara maltina din dan haka ta daga tafara sha tana shanyewa ko ajiye gwangwanin bata yiba taji amai ya taho mata take tafara kwarara shi wanda har kan kafar Lamido sai data wanketa da aman,
"Sannu ikhlas, sannu,Lamido ko asibiti zakuje?" Inna ta fada arude,
"A'a bari zan kira likita" yabawa innah amsa yana satar kallon ikhlas wacce ke rike da cikinta tana yunkurin amai, wani tausayinta yake ji yana ratsashi,
Likita ya kira awaya minti kadan sai gashi nan yafara dubata jin fatarta tayi laushe tayi yaushi yasashi jona mata karin ruwa,
Tare suka fita da Lamido yafara shaida masa cewar adaina barinta tana zama da yunwa saboda abinda ke cikinta,
"Likita ina fata dai cikin lafiya yake?"
"Lafiya lau yake babu abinda ya sameshi amma akiyaye"
"Insha Allah dr"
Dawowa dakin da take yayi bayan ya sallami likitan, tana kwance bacci ya dauketa fuskarta tayi wani siyau,
Tausayinta yake ji sosai yadade atsaye kafin ya juya yafita daga dakin, gidansa ya wuce saboda su ihsan sun tafi tuni,
Wanka kawai yayi ya kwanta yadaga kanshi sama yana tunani, rayuwa kenan yanzu shikenan har sadiq yayi ya gama sai dai a ambaci sunanshi amma badai aganshi ba lallai rayuwar duniya yar kalilance,
Yana nan kwance yana tunani har dare yayi nisa domin kasa bacci yayi sai aikin tunani yake tayi ciki harda tunanin ikhlas ashe da rabon sai dan uwanshi ya aureta kafin shi ya mallaketa tunda gashi nan harda rabon juna biyu atsakani,
Juyi yayi ya rungume pillow yanzu bazai iya fassara yanda yake ji ba shin kishin dan uwanshi yake ji ko sabanin haka? Shidai yasan yana jin wani yanayi wanda yakasa ganeshi,
Har asuba tayi idonshi biyu, salla kawai yayi ya sake kwanciya har lokacin dai bai samu barcin ba hakan yasa idonshi yin dan ja kuma ya kumbura,
Karfe 7 daidai ya tafi gidan Baffa, lokacin an fara fitowa da tabirmi ana shimfidawa a rumfar da akayi a kofar gida,
Cikin gidan ya shiga ya nufi dakin innah yana gaggaisawa da jama'a, yana shiga ya samu ikhlas zaune tayi tagumi akan gadon innah, batare da ya kalleta ba yace,
"Kinci abinci?"
Dagowa tayi ta kalleshi yana sanye da blue din yadi harda hula,
"Ina kwana? Ya karin hakuri?" Tafada ahankali,
"Lafiya, alhamdulillah"
Kallonta ya sake yi "nace kinci abinci?"
Kai ta girgiza "waina da miya akayi nikuma kosai da koko nake so"
Batare da ya sake magana ba ya fita, wayarshi ya dauka yakira bash yafara tambayarshi a ina za asamu koko da kosai?
Wurin 8 bash ya kawo masa koko da kosai din, tashi yayi ya shiga cikin gidan har lokacin ikhlas tana dakin innah akwance bakinta ya bushe,
"Gashi, tashi kici" yafada bayan ya ajiye mata agabanta, mikewa tayi ta dauki kosan tafara ci sai da yaga taci kusan rabi sannan ya juya ya fita,
Bin bayanshi tayi da kallo aranta tana tunanin irin zaman da zasuyi dashi amatsayin ma'aurata domin zata cikawa sadiq burinsa na auren dan uwanshi kamar yadda yabar wasiyya sai dai taga alamun shi lamidon kamar yanada jijida kai da wulakanci ko kuma dan yaga yana da kyau ne?
Tabe baki tayi taci gaba da cin kosanta. Akwana atashi har Abubakar sadiq ya cika kwana uku da rasuwa hakan tasa aka daina zaman makoki kowa ya kama gabansa in banda Lamido da baffa sai bash, acikin gida kuwa iya innah ce kadai sai ikhlas da uwargidanta, domin ko matan Lamido ma ya hanasu zuwa yace suyi zamansu baya son zaman nan na munafurci,
Ranar da Abubakar sadiq ya cika kwana biyar aranar barrister elmustapha yadawo yazo yiwa ikhlas gaisuwa, kicin kicin Lamido yayi ya hade rai yatashi ya shiga cikin gida inda ikhlas take,
"Waye barrister elmustapha?" Ya tambayeta fuskarshi adaure,
"Dan uwana ne" tafada tana kokarin tashi,
"To kizo yazo yimiki ta'aziyya" yafada tareda fita daga cikin dakin,
Bin bayanshi tayi ta samesu awaje atsaye shida elmustapha din,
Yana tsaye yana kallonsu har suka gama gaisawa elmustapha yayi mata gaisuwa ya tafi sai lokacin shima yakoma wurinsu baffa ya zauna.
Ranar da akayi sadakar bakwai aranar kowacce ta koma gidanta, ita ikhlas itada hajiya kakarta zasu zauna zata tayata zama, lokacin da ta shiga gidanta kuka ta fashe dashi domin jin mutuwar tayi ta dawo mata sabuwa saboda gani take kamar zata ga Abubakar sadiq komai nashi gashi nan hatta agogon da yacire ranar da zai rasu gashi nan ajiye akan mirror,
Kuka ta wuni tanayi har yamma, lokacin Lamido yazo gidan ya isketa tana kukan, hajiya ce tayi masa bayanin abinda yafaru cewar tun dawowarsu take kukan nan,
Dakin ya shiga ya tattaro duka kayan sadiq din yafita dasu yasa a mota,
Dakyar hajiya ta samu ta sata tabar kukan ta shiga wanka tafito tazo ta kwanta hannunta rikeda carbi tana ja.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/25, 1:50 PM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_*46*_
~~~ Baccine yayi gaba da ita saboda ta jima bata yiba,tana nan tanata barci har hajiya ta shiga kitchen tayi musu dan wake tafito,
Firgigit ikhlas ta farka daga baccin da take saboda mafarkin da tafara da marigayi Abubakar sadiq,
"Ga abinci can nayi, sannan kina bacci makotanki na baya sun shigo yi miki gaisuwa"hajiya tace da ita,
"Hajiya bazan iya cin abincin nan ba saboda bana sha'awar cin komai yanzu gashi cikina ciwo yake yi" ikhlas tafada tana yamutsa fuska,
"Daurewa zakiyi kinji, daure"
Komawa tayi ta kwanta bata ci abincin ba taci gaba da jan carbinta.
Lamido koda ya kwashi wannan kayan gidan innah yaje ya bude tsohon dakinsa ya zuba kayan ya fito ya nufi gidanshi,
Lokacin da yaje gidan fadila ya samu a babban falo tana buga tv game tasha gayu cikin riga da wando jeans yayinda ihsan take cikin kitchen tana yin girki,
"Welcome my Lamido" fadila tafada tana kokarin kaucewa motocin da suke gabanta,
"Yawwa my fadila" yafada atakaice ya wuce dakinsa, ihsan ce ta fito daga cikin kitchen tawuce fadila tana tsaki, "mtswwwwwwww"
"Banda lokacin ki yarinya" fadila tafada,
"Aikin banza" ihsan tafada ta nufi dakin Lamido, tana shiga fadila na shiga ta jawo rigarta ta baya,
"Ke wa kika cewa banza? Ni sa'arkice?"
"Ba asaniba, sannu uwata karewar girma kenan"
Lamido yana cikin bathroom yana jinsu har yafito basu daina cacar baki ba,
"Ban taba sanin ku sokaye bane sai yau, anyi min rasuwa ko dadewa ba ayiba kunzo kuna yimin shouting aka baku barni da radadin mutuwar da dan uwana yayiba"
Fita fadila tayi ita kuma ihsan ta tsaya saboda itace dashi, tana nan tsaye har ya shirya yasaka kananan kaya bakar t shirt da jeans blue ya dauki key din motarshi zai fita,
"Darling ba zaka ci abinci ba?" Ta tambayeshi cikin tausayawa domin Lamido yanzu dolene yabaka tausayi saboda duk ya zama wani sanyi gashi ya dan rame kadan,
Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita, hannunshi ta riko cikin nata,
"Kayi hakuri insha Allah ba zamu sakeba, dan Allah ka cire damuwa aranka pls and pls.."
"Nagode my ihsan, bari naje gidan ikhlas nadawo zanje na dubota saboda bata da lafiya"
Kallonsa ihsan ta tsaya yi batare da tace komai ba har yafice daga cikin dakin,
Masallaci yafara zuwa yayi salla sannan yatafi gidan ikhlas din, lokacin da yashiga gidan ya samu hajiya tanata fama da ita akan ta tashi taci abinci amma taki tashi,
"Ke yanzu hakan zai yimiki dadi kinada lalura amma ba zakici komai ba?" Hajiya tafada cikin fada,
Lamidone ya shiga falon bakinsa dauke da sallama idanuwansa akan ikhlas wacce ke kwance akan tiles ta tasa kanta da pillow din kujera,
"Sannu da zuwa Lamido, lale" hajiya tafada,
"Yawwa sannu hajiya" Lamido yace da ita ahankali,
Zama yayi yana kallon ikhlas,
"Hajiya bata da lafiya ne?" Ya tambayi hajiya,
"Wai cikinta ne ke ciwo kuma taki cin abinci"
Tashi yayi ya isa inda take kwance ta juya musu baya,
"Meyasa ba zaki ci abinci ba?" Yafada yana kallonta,
"Cikina ne yake ciwo kuma bana son cin yaji"
"Sai me kike son ci?" Ya tambayeta yana kallon wani wuri,
"Doya da kwai irin wacce ake sayarwa a kasuwa"
Batare da ya sake magana ba ya juya ya fita yana yiwa hajiya magana,
"Hajiya bari naje nadawo"
"To to sai ka dawo,sai ka dawo"
Fita yayi aransa yana tunanin wani aiki sai me ciki, kasuwa ya shiga layin yan doya, nan ya samu ana soyawa fita yayi ya siyo mata cikin bakar leda,
Gidan ya koma ya isketa ta rako wasu mata wadanda suka je yi mata gaisuwa,
Wucesu yayi bai ko kallesu ba, wannan yana daya daga cikin banbancin halayyarsu da marigayi domin shi mutumne marar shariya da kyaliya gashi da faran faran sabanin Lamido wanda yake marar magana gashi da rashin fara'a sam baya son yiwa mutane magana ko kallonsu ma bai damu dayi ba,
Dawowa tayi daga rakiyar da tatafi tana tunanin halin Lamido wanda tafara ganewa,
"Gashi nan ya kawo miki doyar idan dagaske kike sai kici" hajiya tafada cikin mita,
Jan ledar doyar tayi ta zauna ta bude tafara dauka tana ci,
Yana zaune yana kallonta har ta ci da yawa sannan ta ture ledar ta kwanta awurin,
"Hajiya bari natafi zanje gidan suhaima itama na dubata, bari na rubuta miki no dina idan da wani abu sai ki kirani"
"To shikenan insha Allahu ma babu komai, madalla angode"
Batare da ya kalli wurin da ikhlas take kwance ba ya wuce ya fita,
Gidan suhaima yaje itama tana sanye cikin katon hijabi da carbi a hannunta ga mamanta nan da kanwarta wadanda suke tayata zama kasancewar mahaifinsu ya jima da rasuwa,
Da gudu su hydar da faruk suka taso suka rungumeshi suna cewa, "oyoyo uncle"
Rungumesu yayi sai kuma yaji kwalla ta cicciko masa idonshi, hannunshi yasa ya goge ya dauki karamar wato Aysha ya kama hannunsu faruk zuwa ciki,
Zama yayi suka fara gaggaisawa, tunda ya shigo Xahar kanwar suhaima ta kafeshi da ido kamarsu daya da sadiq marigayi amma yafishi kyau nesa ba kusa ba.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/25, 1:50 PM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_47_*
~~~Murmushi Xahar tayi taje ta dauko masa ruwa ta ajiye tana dan kakkawar da fuskarta alamun jin kunya,
Ya dan jima agidan kafin ya fito yayiwa suhaima sallama ya tafi, nan Xahar tafara santin kyawunsa tana fadawa yayarta, murmushi suhaima tayi tace,
"Ke kuwa Xahar me zakiyi dashi matanshi fa biyu sannan baya ji duk gidansu marigayi babu marar ji kamarsa neman mata, shaye shaye, duk halinsa babu na dauka"
"Kai anty wallahi nidai ya tafi dani yanada kyau sannan babu wanda ma zai ganshi yayi tunanin yayi aure balle har ace yanada mata biyu"
"Dan kyau kam Lamido yanada kyau domin duk cikin yayan innah yafi kowa kyau matsalarshi kawai baya ji tun kafin ayi masa aure yake bibiyar mata ke wannan dalilinne ma yasa akayi masa aure har mata biyu"
Mikewa Xahar tayi"nidai wallahi naganshi nayaba so babu ruwana da wani halinshi"
Daki ta wuce bata jira amsar da suhaimat zata bata ba.
Gida Lamido ya koma yaje ya zauna ya huta Sati dayan nan da baiyi aski ba har gashi ya dan taru a fuskarsa,
Zama yayi a tsakiyar matanshi kowacce tana bashi kulawa, yana nan tare dasu har dare sai alokacin yafita domin zuwa ganin ikhlas,
Tana kwance asaman kujera tana tunanin mijinta Lamido ya shiga cikin falon,
"Assalamu alaikum" yafada acan kasan makoshinsa,
Dagowa tayi tana amsa sallamar ahankali,
Zama yayi acan nesa da ita,
"Sannu da zuwa" tafada tana kokarin tashi zaune,
"Yawwa ya jiki?" Ya fada yana kallon screen din wayarsa,
"Da sauki" ta bashi amsa,
"Hello bash ina kajene? Ok mu hadu to" ta jiyoshi yana waya,
Yana nan zaune har hajiya tafito suka gaisa ya mike yafita yana yiwa hajiya sallama, tun daga ranar gidan ya zame masa wurin zuwa domin kullum sau hudu yake zuwa idan kuma bai samu dama ba yazo sau uku, bashida buri illa na yaga ikhlas ta samu lafiya kuma ta haihu lafiya,
Kullum cikin siya mata kayan makulashe yake da sauran kayan bukata wannan dalilinne ma yasa matanshi suka fara saka ido akai domin kullum ahanyar zuwa wurin ikhlas yake, yanzunma shiryawa yake yana kokarin fita fadila ta shigo dakin tana kallonshi,
"My Lamido ina zakaje?" Tafada a zuciye,
"Zanje nagano ikhlas ne" yafada cikin rashin damuwa,
"Amma naga dazun nan da yamma ka fita kace ganinta zakaje yanzu kuma kazo kana cewa sake zuwa ganinta zakayi, agaskiya mu mun kasa gane abinda kake nufi saboda kullum baka da wata magana sai tata, idan tausaya mata kake yi ai ba ita kadai aka mutu aka bari ba, ga anty suhaima nan asalima ita tafi cancanta daka tausayawa saboda ya tafi ya barta da marayu har guda hudu.." Ta karashe maganar zatayi kuka,
Tunda tafara maganar kallonta kawai yake har ta gama, batare da yace da ita komai ba ya juya ya fice, wani takaicine ya lullube fadila domin shi dama Lamido matsalarshi kenan sai kayi masa magana idan bata gamsheshi ba ko tanka maka bazai yi ba sai yayi banza dakai ko kuma yatashi yabar maka wurin,
Fita tayi tana kuka ta nufi dakinta tana sharar hawaye.
Kai tsaye gidan Lamido ya shiga tun daga kofar falon yake jiyo sautin radiyo ana sauraren wa'azi,
Shiga yayi ya iske hajiya sai bambami take yiwa ikhlas kan ta tashi taci abinci amma taki,
"Yawwa gwanda da kazo ni ina jin nakusa tafiya nabar gidan nan saboda yarinyar nan bata jin magana bata son cin abinci ko kadan alhalin mace mai ciki sai da abinci" hajiya tace dashi,
"Hajiya dauko abincin zata ci" yabata amsa tashi hajiya tayi ta fita tana fita ya karasa inda take,
"Tashi kici abincin nan, meyasa ke bakya gudarwa kanki matsala ne? So kike cikin jikinki ya samu matsala? To wallahi idan kika bari cikin nan ya samu matsala bazan yarda ba" yafada cikin kufula,
Kallon mamaki tabishi dashi tab irin wannan fada haka sai kace shi yayi cikin, to inaga kuma idan cikin nashine kenan Allah ne kadai yasan dokokin da zai kafa,
Hajiya ce ta dawo dauke da filet tazubo shinkafa ta da miya, zama yayi ya tisata agaba tafara cin abincin har taci rabi amma sam bata jin dadinsa,
Wani amai ne ya taho mata batare data shiryaba take ta amayar da abinda ke cikinta gaba daya,
Cikin tashin hankali Lamido yake kallonta har ta gama jirine ya dauketa ta fadi sharafff,
Cikin sauri ya isa kanta yana leka fuskarta.
*_Ummi A'isha_*👌🏻
[12/25, 1:50 PM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_48_*
~~~Cikin sauri ya isa kanta yana leka fuskarta,
"Ikhlas,ikhlas.." Hajiya ta kira sunanta cikin tashin hankali,
Ko motsi batayi ba ganin haka yasa lamido gigicewa,
Hannunshi yakai ya juyo fuskarta numfashinta gaba daya ya dauke,
Mikewa yayi tsaye ya zaro wayarsa yafara kiran dr,
Ruwan sanyi hajiya ta dauko tafara sheka mata amma shiru,
Suna nan tsaye har dr yazo,
"Ashigar da ita cikin daki" dr ya fada yana kallonsu,
"To ni ai ba iya daukarta zanyi ba" hajiya tafada adiririce, daukarta lamido yayi yai hanyar dakinta da ita, akan gadonta ya shimfidar da ita ya juyo yana kallon dr,
"Yarinyar nan cikin nan yana bata wahala abin tausayi" lamido yafada acikin ranshi,
Dubata dr yayi ya daura mata ruwa ya rubuta magunguna ya juyo yana kallon Lamido "meyasa bata cin abinci? Arinka bata abinci tana ci sannan ta rage damuwar da take damunta" likita yafada tare da fita,
"Ikhlas amma kina shan karin ruwa" hajiya tafadi tana kokarin zama akusa da ita,
"To ya za ayi hajiya sai hakuri kawai" lamido yabata amsa ya fita,
Chemist yaje ya siyo magungunan ya dawo, har lokacin ikhlas bata iya bude koda idanuwanta ba, zama yayi a falo yana jiran ta tashi,
Tafi awa daya tana bacci kafin ta tashi lokacin ruwan da aka daura mata ya kare,
"Sannu ikhlas, dan Allah ki cire damuwa aranki kinji" hajiya tace da ita,
Daga kai tayi ta shiga toilet tafito jiri na daukarta, komawa tayi ta kwanta tana haki kamar wacce tayi tseren gudu,
Tashi Lamido yayi yayiwa hajiya sallama ya tafi,
Zuciyarsa cike fal da tausayin abar sonshi ji yake kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa,
Lokacin da yaje gida fadila na zaune afalo tayi tagumi ta zubawa kofa ido tana ganinshi ta mike tsaye idonta jajur alamun tasha kuka ta more,
"Fadila lafiya kike zaune anan?" Ya tambayeta cikin kulawa,
Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da wani kukan, janta jikinsa yayi ya rungumeta, ahankali yake tafiya da ita tana jikinsa yana rarrashinta har zuwa cikin dakinta,
Agogon bangon dakin ya kalla karfe 11:30,zaunar da ita yayi agefen gadon ya sunkuya agabanta ya kamo hannayenta yafara rarrashinta,
"My fadila kiyi hakuri pls, karki yi fushi da mijinki kinji.." Yafada cikin sigar lallashi,
Mantar da ita bacin ran da take ciki yayi ta hanyar nuna mata soyayya, sai da ya tabbatar da yabata kyakkyawar kulawa sannan ya tashi ya fice daga cikin dakin ya tafi nashi,
Bathroom ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta nan kuma tunanin ikhlas ya addabeshi, juyi ya rinka yi har ya samu bacci ya daukeshi,
Washe gari ko breakfast baiyi ba ya fice ya tafi dubo ikhlas, lokacin da yaje ya ganta yasamu ta dan warware alamun sauki ya samu tana zaune afalo tana cin wainar shinkafa da miya,
Da sallama ya shiga cikin falon ya zauna akan kujera,
"Sannu da zuwa, ina kwana?" Tafada ahankali duk kunya ta kamata ta kasa sakewa taci wainar,
"Yajiki?" Ya tambayeta batare da ya kalleta ba,
"Da sauki" tabashi amsa ahankali,
Babu wanda ya sake magana acikinsu har hajiya ta fito daga cikin kitchen tana dauke da filet mai dauke da waina da miya aciki,
"Barka da zuwa, ga waina"
"Hajiya ina kwana? Ya mai jiki? Allah ya bata lafiya"
"Ah jiki yayi sauki, amin amin, ga waina"
Daukar filet din yayi yafara cin wainar yana sauraren maganar da hajiya take yiwa ikhlas,
"Ki dauko maganin kisha sarkin yan kin magani" hajiya tace da ikhlas cikin fada,
Dakyar ta mike ta shiga daki ta fito rike da ledar maganin tazo ta zauna sai yayyatsina fuska take yi da haka ta samu tasha maganin,
Lamido ya dan jima agidan kafin ya tafi ta gidan suhaima ya biya yaga yara sannan ya fito ya nufi gidan baffa acan ya kwashe lokuta masu yawa sai yamma sannan yabar gidan ya nufi gidansa.
Kasancewar yau girkin ihsan ne ya sanyashi samunta acikin falo tana zaune zaman jiranshi,
Kallonta yayi tasha kwalliya tayi kyau amma sai cika take tana batsewa,
"Darling yanzu ka kyauta kenan? Tun safe kabar gidan nan baka tashi dawowa ba sai yanzu" tafada tana zumburo masa baki,
"My ihsan ikhlas ce bata da lafiya shine naje na dubota"
Harararshi tayi ta dauke kanta, "kuma shine zaka tafi kaje ka zauna"
Murmushi yayi yakamo hannunta yana kallonta ya fuskanci daga fadila har ihsan din duk kishi suke da ikhlas, shi kansa baisan wanne irin zama zasuyi ba su ukun idan ya auri ikhlas,
"Ai dubiya ce ihsan kuma kinga yanzu babu wanda zai lura da ita sai ni"
Dagowa tayi ta kalleshi, "shikenan Allah ya bata lafiya" hannunshi ta rike ta rakashi dakinshi sannan ta fito.
*_Ummi A'isha_*👌🏻
[12/26, 9:30 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata KHADIJA SIDI_
*_49_*
~~~Kan gadonshi ya fada ya kwanta sai da ya shafe lokuta masu yawa sannan ya tashi ya shiga wanka ya fito yasa kayan bacci ya sake kwanciya,
Tunanin ikhlas ne ya mamaye ruhinsa wanda ya hanashi bacci, ganin ya kasa bacci ya sashi mikewa ya fita zuwa dakin ihsan,
Tana kwance tana sharar baccinta, bayanta yaje ya kwanta ya rungumeta.
Washe gari bai fita daga gida da wuriba kasancewar jiya bai samu bacciba adaren jiya, sai wurin 12 sannan ya fito da niyyar tafiya wurin ikhlas,
Ihsan tana kitchen tana aiki ita kuma fadila tana zaune a falon tana goge zannuwan gadonta,
Fitowa ihsan tayi hannunta rikeda ludayin miya tana kallonsa,
"Darling ina zaka kuma"
"Ihsan zanje na gano ikhlas ne"
"Har yanzu bata warke ba?" Tafada a kufule,
Batare da yabata amsaba yasa kai yafice, takaicine ya kama ihsan da fadila domin itama fadilan ranar girkinta haka yayi mata,
"Ihsan kiyi hakuri nima haka yayi min shekaran jiya, ban san daliliba yanzu gaba daya ya dauki kulawar duniya ya dorawa ikhlas da anyi magana kuma sai kiji yace wai amana aka bashi, ai ba ita kadai bace amana tunda ga anty suhaima nan ita da aka mutuma aka barta da marayu har guda hudu"
Jiyowa ihsan tayi idonta cikeda kwalla,
"Ki barshi fadila mu yanzu ya mayar damu wasu wawaye, idan kuma mutum yayi magana yafika fushi, jiyafa tun safe ya fita daga gidan nan amma bashi ya dawo ba sai dare, nidai wallahi bazan juri irin wannan wulakancin na on top ba"
"To idan bamuyi hakuri ba ya zamuyi ihsan? Kinfi kowa sanin on top idan muka zake da yawa wallahi mamaki zai bamu"
"Fadila idan ke zaki juri wannan cin mutuncin nasa wallahi nidai yanzu bazan jura ba, idan da yayi min najure lokacin bai aureni bane amma yanzu na zama matarsa inada hakkoki akansa ciki kuwa harda zamansa agida"
"Hakane ihsan kiyi hakuri nima nasha irin wannan takaicin shekaran jiya"
Juyawa ihsan tayi takoma cikin kitchen tana share kwallar da ta fara silalowa akan kuncinta.
Lokacin da Lamido ya fita ta kasuwa ya biya ya siyawa ikhlas kayan marmari irinsu lemo da ayaba da Apple, gidan ya shiga atsakar gida ya samu hajiya tana yin wanke wanke,
Gaisawa suka yi ya shiga ciki, afalo ya iske ikhlas din zaune ta gama cin abinci, kallonta ya danyi cikin nata har ya dan fito,
"Sannu da zuwa" tafada tana mai kokarin janyo hijabinta,
Ciki ciki ya amsa suka gaisa ya mika mata ledar da ya shigo da ita ya tambayeta koda abinda take bukata tace babu,
Mikewa yayi ya fita yayiwa hajiya sallama ya tafi, gidan suhaima yaje itama ya gaisheta, Xahar kanwarta sai shisshige masa take duk da bashida ra'ayin kula mace sai da ta makale masa har ya bata phone number dinshi amma ya fada mata yanada wacce zai sake aura nan da yan watanni, cewa tayi taji tagani kuma ta yarda,
Tun daga ranar suka fara soyayya sama sama shida xahar, batun ikhlas kuwa kullum cikin zuwa ganinta yake gashi bata rabuwa da rashin lafiya kullum cikin ciwo take, tausayinta ne yake kama Lamido duk lokacin da yaje ya ganta.
Irin kulawar da yake bawa ikhlas ne yasa yanzu bashida lokacin kowa sai nata hakanne ya sake kular da fadila da ihsan har suka kasa hakuri suka tunkareshi da maganar, kaca kaca yayi musu ya balbalesu da masifa yahau fushi dasu,
Gidan innah sukaje suka kai kararsa wurin baffa, kiransa baffa yayi yai masa nasiha yace ya zauna ya kula da matanshi ita kuma ikhlas idan yaje sau daya arana ma ya isa,
Gidanshi ya koma ya samu ihsan da fadila zaune afalo suna jiran zuwansa,
Zama yayi yana kallonsu,
"Fadila, ihsan kun bani mamaki da bazaku iya tayani rike amanar da dan uwana ya bar min ba, naji abinda kukaje kuka fadawa baffa, ni kuka kai kara ko?? Nagode"
Tashi yayi yabar falon batare da ya jira abinda zasu ceba, tabe baki fadila tayi yayinda ihsan taja dan guntun tsaki.
Kulawa iya kulawa yana bawa ikhlas yanzu cikinta ya girma ya fito sosai domin watanshi bakwai, alokacin Lamido ya tafi jahar yobe domin shiga camp, damuwa iya damuwa ya shiga domin gani yake babu wanda zai kular masa da ikhlas kamar yadda zai kula da ita,
Da damuwar halin da yatafi yabarta ya tafi, ita kuma ikhlas abdallah aka kawo mata hutu shida mahaifiyarta ammi domin suyi mata sati biyu,
Tunda su ammi suka zo kullum tana makale da abdalla suna hira gashi ya girma yadan zama saurayi, satinsu uku shida ammi suka tafi aranar da suka tafi aranar Lamido ya dawo yafito daga camp.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/26, 9:30 AM] Ummi A'isha👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga kawata KHADIJA SIDI_
_*50*_
~~~Wanka yayi ya shirya yaje yayi aski sannan ya wuce gidan baffa, innah Kadai ya samu agidan, zama yayi suka gaisa suka dan taba hira kafin yayi mata sallama ya nufi gidan suhaima, yana zuwa ya samu Xarah ta shirya masa kayan tarba irinsu snacks da dambun kifi ga lemuka kala kala,
Fitowa tayi tasha kwalliya sosai cikin blue din leshi mai kyau,
Zama tayi tana murmushi tana kallonshi yana zaune akan kujera ya karkace ya rausayar da kanshi yana latsa wayarshi, ba karamin kyau taga yayi mata ba hakika lamido shine irin mijin da ta dade tana addu'ar samu domin ya hadu ba karya,
"Sannu da zuwa ranka yadade" tafada ayangance,
"Yawwa Xarah ya gida?, ina mamansu sayyid ko bata nan?" Ya tambayeta yana kallon fuskar wayarshi,
"Tana nan kabari mu gama sai na kira maka ita" tafada idonta narai narai,
"Ai Xahar sauri nake yine shiyasa, ki kirata kawai mu gaisa na wuce"
Tashi xahar tayi badan tasoba taje ta kira suhaima, nan suka shigo da yaranta suna ganin lamido suka je suka makalkaleshi,
Kallon yaran yake yi cikeda tausayawa kusan duk lokacin da yagansu sai ya rinka jin kamar zaiyi kuka,
Gaisawa sukayi da suhaima yayi mata sallama bayan ya kwashi yaran domin yana son ya kaisu supermarket ya iyo musu siyayya,
Ganin zai tafi yasa xahar binshi tana cewa "nima zanyi rakiyar"
Bai bata amsaba ta shiga gaban motarshi ta zauna sukuma yaran suna baya,
Gidan ikhlas ya nufa, acikin mota yabar su xahar itada yaran ya shiga cikin gidan shi kadai,
Lokacin da yashiga gidan ikhlas tana zaune a falo daga ita sai vest baka ta daura zani asama tasaka katon cikinta agaba tana cin shinkafa da wake ga robar yaji da ta gishiri agefe tana dandana tana sakawa acikin shinkafar tana ci, gefe kuma hajiya ce zaune sai faman mita take yi,
"Ban taba ganin yarinya mai taurin kai ba kamar ke wannan yarinyar, kullum sai nayi miki fadan cin wannan gishirin amma kin ki ji ai shikenan"
Sallama yayi ya shiga idonshi akan ikhlas,
Tana jinsa tayi wuf ta fara neman hijabi amma babu kasancewar su biyune agidan daga ita sai hajiya shiyasa take zamanta yanda take so,
"Hajiya dan Allah taimakeni da hijabina" tafada kamar zata saka kuka saboda ta kasa tashi domin cikinta yayi nauyi sosai,
Tsayawa yayi bai karasa shigaba har sai da hajiya ta dauko mata hijabin ta saka ta rufe jikinta sannan ya shiga,
"A lale lale, barka da zuwa Lamido"hajiya tafada tana gyara daurin dan kwalin kanta,
Shiru ikhlas tayi tana suraren gaisawar da hajiya suke yi da Lamido,
Ido Lamido ya zubawa ikhlas nan yaga tayi kiba tayi suntum hatta kafafunta ma kamar an hura balo,
"Hajiya meya sameta? Lafiya kuwa take? Naga tayi kiba sosai" yafada yana dauke idonshi daga kallon ikhlas,
"Hawan jinine, jininta ne yahau sosai gashi likita ya hanata cin gishiri amma taki ji ka ganta nan kullum haka take sakashi agaba tayi ta ci kuma likita yace indai jininta bai sauka ba lokacin haihuwarta yayi to ita da jaririn zasu shiga wani hali",hajiya tafada cikin fada,
Kallon ikhlas yayi duk tabashi tausayi kamar yayi mata kuka,
"Hajiya debo min duk gishirin dake gidan nan"
Har hajiya tafita babu Wanda yacewa wani uffan tsakaninsa da ikhlas, tashi yayi yaje ya dauke na gabanta wanda ta ajiye,
"Dan Allah kabar min" tafada kamar zatayi hawaye,
"Ya za ayi likita ya hanaki abu amma ki dage kan sai kinyi, wato ke baki san illarsa ba ko? To ki bari idan kika haifar min yarona lafiya sai kije kici gaba da cin gishirinki idanma buhu zaki rinka cinyewa asati ni babu ruwana"
Dagowa tayi ta kalleshi tana mai jin mamakin kalaman da suka fito daga bakinsa wato shi bata ita yake ba ta danshi yake yi,
Hajiya ce ta shigo hannunta rike da ledar gishiri yeluwa,
"Ka ganshi duk na debo maka ko cikin cokali ban rageba"
"Hajiya dan Allah da maggi kawai zaku rinka yin girki"
"Ni dama bana son gishirin nan saboda hawan jini"
Mikewa Lamido yayi ya karbi ledar gishirin ya juya zai fita,
"Dan Allah ka kawo min ice cream" ikhlas tace dashi,
Girgiza kai yayi, "babu ice cream din da zan kawo miki domin lafiyar yarona bana son sanyi Ya kamashi"
Yana gama fadin haka ya juya ya fice,
Binshi da kallo ikhlas tayi har ya fice,
"Komai kace yaronka komai kace yaronka sai kace kaine kayi cikin sai kabari ka ajiye naka gudan jinin kafin ka nuna min iko" tafada acikin zuciyarta tareda gyara zamanta bayan ta tankwashe kafafunta dakyar.
0 comments:
Post a Comment