~~~Fita lamido yayi sai alokacin ya tuna da cewar ashe fa yabar Xahar dasu sayyid a mota,
Bata rai xahar tayi ta hade fuska ita adole taji haushin zaman da lamido yayi, bai ko kalleta ba ya shiga motar ya tayar yafara tuki,
"Haba Lamido kuma sai katafi kabarmu munata zaman jiranka alhalin ga zafin rana" xahar tace dashi kamar zata sa kuka,
Batare da ya kalleta ba yace,
"Ai da sai ku kunna ac"
Babu wanda ya sake magana acikinsu har suka tasamma supermarket din sai dai amma ita xahar sam bata ji dadin amsar da ya bata ba, shiru tayi ta kyaleshi saboda ta fuskanci shima yanaji da wulakanci,
Packing yayi a harabar supermarket din suka firfito suka shiga yana dauke da aysha akan kafadarshi kasancewar itace karama,
Cewa yaran yayi kowa ya dauki abinda yake so nan suka je suka ciko karamin basket da kayan ciye ciye,
Yana son ya daukawa iklas kayan zaki amma yana tsoron kar yaje ko masu ciki basa sha, wayarshi ya ciro yafara kiran dr yana dagawa ya tambayeshi,
"Dr dama tambayarka zanyi masu ciki suna shan zakine?"
Daga can bangaren dr yafara bashi amsa,
"Lamido mudai asonmu kar susha saboda idan sunzo haihuwa to dole ne sai sun zubar da wannan zakin"
"Ok to dr amma kamar ice cream fa?" Lamido ya sake tambayarsa,
"Ehh amma kar asha dayawa saboda shi ciki zafine dashi ta ciki to amma ba ason arinka shan sanyin da yawa gudun kada yaron ya samu matsala"
"Ok thank you dr"
Kashe wayar yayi yaje ya dauko ice cream kwaya daya karamar roba,
Wurin biyan kudi yaje shida yaran aka fara lissafi nan yaga ita xahar bata dauki komai ba saboda kunya, da kanshi yaje ya dauko wani turare dan 5000 yazo ya biya ya bata, nanfa dadi ya rufeta ganin lamido ya fara damuwa da ita,
Gida ya koma dasu ya ajiyesu ya juya ya nufi gidan ikhlas tana nan zaune daga ita sai zani iya kirji da hijab da alama daga wanka ta fito,
Da sallama ya shiga ya mika mata robar ice cream din,
Kallo tabishi dashi sannan ta sake kallon yar mitsitsiyar robar ice cream din da ya bata,
"Wannan ne ice cream din?" Ta tambayeshi cikin karfin hali,
"Ehh shine idan kuma kin raina ki bani kayana" yafada bayan ya juya ya fara tafiya,
"Ni ba rainawa nayi ba amma abinne da mamaki kamar wanda aka bawa sadaka?"
"Wannan dinma sai da na kira dr na tambayeshi badan haka ba da bazan kawo miki ba" yafada tareda karasa ficewa,
"Uhm kaji masu d'a komai kace d'anka komai d'anka" tafada aranta tareda bude robar ice cream din tafara diba tana sha.
Lamido kam wannan yar maganar da sukayi da ikhlas shine yasake tayar masa da dafin ciwon sonta,
Driving yake yana nishadi har ya karasa gida, ko agidan ma saida su ihsan da fadila suka gane yana cikin farin ciki.
Kullum yana hanyar gidan ikhlas gashi yafara service sai dai bai fiya fitaba koda yaushe yana gida,
Yau sam bai leka ikhlas ba tun safe har dare dan haka yana yin sallar isha ya tashi ya fita lokacin da yaje gidan kamar kullum ita da hajiya ya samu a tsakar gida sun shinfida tabarma ikhlas na kwance tana shan kankarar pure water ita kuma hajiya tana zaune,
Zama yayi suka fara gaisawa da hajiya yana kallon ikhlas,
"Meye wannan kike sha?"
Shiru tayi bata amsa masa ba ganin haka yasashi juyawa ga hajiya,
"Hajiya me naga tana sha?"
"Kankara mana, ai na hanata shan kankarar nan amma ikhlas taki ji ina jin so take ta haifo yaro mai limoniya, kullum cikin yi mata fada nake amma bata dauka"
Tashi yayi yaje ya mika mata hannu "bani nan"
Mika masa tayi tafara kokarin tashi zaune,
"Nifa dan bakuji zafin da nake jin cikina yana yimin bane" tafada tana kumburo baki,
"Fridge din ma daukeshi zanyi inyaso naga abinda zaki sha, ke kullum bakya jin magana daga an hanaki wancan sai ki koma wancan ki bari idan kika haihu sai ki zamar da kankarar abincinki kiga idan zamu yi miki magana"
Shiru tayi masa har ya karaci fadanshi ya tafi domin ta fuskanci shi ta lafiyar jaririnshi kawai yake bata ita ba, tun da ya hanata shan kankara suka shiga yar tsama dashi amma kullum yana zuwa gidan fiyeda sau biyu,
Watan cikinta tara da kwana biyu tafara nakuda nan hajiya ta kira lamido yazo suka tafi asibiti, duk hankalinshi ya gama tashi saboda ganin yanda ikhlas take yi,
Suna zuwa aka Shiga dakin haihuwa da ita, awarsu biyu da zuwa ta haihu amma kuma sai dai ta zubar da jini da yawa dan haka aka fara tunanin kara mata,
Ko jaririn bai tambaya ba ta lafiyar ikhlas yake yi,lab sukaje da dr din aka gwada jininsa aka diba domin karawa ikhlas,
Suna nan tsaye shida hajiya da innah aka fito musu da jaririn wanda yake fari sol mai kamada mahaifinshi sak,
Ai innah naganin jaririn sai ta fashe da kuka shi kansa lamido sai da yayi kwalla.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/26, 9:30 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_*52*_
~~~ Daukar jaririn lamido yayi yai masa addu'a ya mikawa hajiya shi ya juya ya fita,
Ba afito da ikhlas ba sai bayan awa daya sai alokacin su innah suka shiga ganinta, tayi jugum tana tunanin marigayi,
Sannu dukkaninsu suka hau yi mata har lamido ya shigo,
Dagowa tayi ta kalleshi jin ko sannu bai yi mata ba sai ma karbar jaririn da yayi ya rungume yana fara,a ita ta rasa gane kan wannan iko irin na lamido.
Zuwa dare aka sallamesu, kai tsaye gidan innah suka wuce, dakin kusa da na innah anan aka sakawa ikhlas kayanta dana jaririnta,
Komai wanda zasu bukata an siyo, lamido yana ajiyesu ya juya yanufi gidanshi acan yaje yana yiwa su fadila maganar haihuwar ikhlas,jin ya damesu da maganar yasasu jin haushi kowacce tasha kunu taki kulashi.
Tunda aka yi haihuwar yake zirga zirga har suna yazo, ana igobe suna yaje gidan, lokacin yan uwan ikhlas sun zazzo su matan yayunta dasu ammi da sauran matan gidan,
Afalo yasamu baffa da ikhlas suna maganar sunan da za asakawa yaron,
"Yawwa lamido dama kai muke jira na tambayeta sunan da za asakawa yaron tace abari kazo kaine babanshi" baffa yafada cikeda jin dadi,
Zama lamido yayi yana kallonta sai ciccije lebe take kamar marar lafiya,
"Baffa sunanshi Abubakar Saddiq sunan mahaifinshi"
"Yawwa to bakinku yazo daya da ita domin itama haka tace amma tace abari kazo aji"
Mikewa baffa yayi ya fita hakan yasa lamido matsawa inda take,
"Baki da lafiya ne?"
Kai ta daga masa
"Meyake damunki?"
"Ciwon ciki"
"Ko zamuje asibiti?"
Girgiza kai tayi alamun a,a,wucewa yayi ya fita ita kuma ta koma daki ta kwanta amma kuma ciwon sai karuwa yake ganin haka yasata daukar wayarta ta karbi wayar hajiya ta kwafi no din lamido ta kira,
Yana driving ta kirashi, sabuwar no yagani dan haka ya share, sai da ta kirashi sau uku baiyi picking ba, ganin haka yasata tura masa text massage,
Jin shigowar massage wayarshi yasashi dauka ya duba,
_Abban sadiq kazo ka kaini asibitin har yanzu cikin nawa bai daina ciwo ba._
Shine abinda yaga an rubuta, yana ganin sakon ya rude, da saurinshi ya koma gidan, yana zuwa ta fito suka tafi,
Asibitin data haihu ya kaita acan aka dubata aka bata magani suka dawo gida.
Washe gari da safe aka yi suna duk da cewar basuyi wani gayya ba amma dangi sun taru, matan lamido kuwa dakyar suka zo gidan sunan amma sai kumbure kumbure suke yi, haka taron sunan ya tashi lafiya lafiya.
Gidan yayi mata mutukar dadi saboda duk inda ta waiga danginta take gani tako ina,
Karfe 8:30 nadare suna zazzaune adakinta itada yan uwanta taji wayarta tafara ruri tana dubawa taga *ABBAN SADIQ* kamar yadda ta rubuta, ahankali ta daga wayar,
"Kawo min sadiq zan ganshi" taji yafada tun kafin ta yi magana,
"To amma yanzu wanka ake yi masa Bari ashiryashi sai na kawoshi" tabashi amsa tana satar kallon hajiya wacce take nannade sadiq a towel bayan tagama yi masa wanka da ruwa mai dumi,
"Waye yake nemansa?" Hajiya ta tambayeta tana jawo kayan kwalliyar sadiq din,
"Abbanshi ne" ikhlas tabata amsa,
Shiryashi akayi cikin kayan sanyi ikhlas ta daukeshi ta fita,
Yana zaune shi kadai acikin falon yasha kananan kaya wadanda suka yi mutukar amsarshi, brown din trouser da blue din t shirt mai gajeren hannu,
"Sannu da zuwa" tafada tana kokarin mika masa sadiq,
"Oyoyo saddiqu na" yafada batare da ya amsa mata ba ya karbi sadiq din,
"My boy ya ka wuni?" Yafada yana kamo yan yatsun jaririn yana sawa abakinshi,
Tsayawa tayi kawai tana kallonshi yanda ya daddage yana yiwa sadiq magana maganar da bai saniba,
Atishawa sadiq yafara jerewa har sai da yayi guda hudu,
"Alhamdulillah, sorry my boy,mura kake yi ko? Ni dama nasan dole kayi mura saboda kankarar da aka rinka dura maka lokacin da kana cikin ciki gashi yanzu ka fito duniyar ma amma baka huta ba sai wankan dare ake yi maka"
Dagowa yayi ya kalli ikhlas "dan Allah adaina yiwa yaron nan wanka da daddare"
"To" ta amsa masa atakaice,
Agogo ya kalla karfe tara daidai nadare,
"My boy inje in tafi ko? Sai da safe bye bye"
Mika mata shi yayi ya tashi ya fita, binsa da kallo ikhlas tayi,
"Ikon Allah baya karewa" tafada acikin zuciyarta,
Cikin dakinta ta koma inda yan uwanta suke zazzaune sunata shan hira,
"Sai yanzu yatafi?" Ammi ta tambayeta,
"Ehh dama danshi yazo gani" tafada tana kwantar da sadiq, kwanciyar itama tayi domin yin baccin.
Washe gari wurin misalin karfe 10 lamido yaje gidan daidai lokacin ana yiwa sadiq wanka sai kwala kuka yake yi,
Tunda ya shiga falo yake jiyo kukanshi nan yafara jin kukan har cikin ransa, kasa hakuri yayi ya leka dakin, hajiya yagani tana yiwa sadiq wanka ita kuma ikhlas tafito kenan itama daga wankan, da sauri taja baya ta koma cikin toilet din domin daga ita sai daurin kirji kanta babu dankwali kuma bata yafa komai ba,
"Hajiya meya sameshi yake kuka?"
"Wai wanka ake yi shine yayi kamar zai tsaga gidan nan dan ihu" hajiya ta bashi amsa,
Karbarshi yayi bayan hajiya ta nadeshi acikin towel,
"To ya isa zo muje" sabashi yayi akafada ya fita dashi yana jijjigashi.
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/26, 9:30 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_53_*
~~~Sai da ikhlas taji fitarsa sannan ta fito ta shirya, ganin shiru shiru bai dawo dashi ba ya sanyata dibar kayan da za asawa sadiq din tafita tabishi falo,suna zaune shida innah da sadiq akan cinyarshi yakama hannayenshi,
"Ga kayansa" ta mika masa,
"Ungo saka masa ki mikoshi" karbarsa tayi ta saka masa kayan ta mika masa shi tatafi,
Bai dawo dashi ba sai wurin 12 shidinma saboda tafiya zaiyi shiyasa,
Mika mata yaron yayi ya juya zai tafi,
"Abban sadiq.." Yaji ta kira shi, tsayawa yayi batare ya jiyo ba,
"Gobe zan kai sadiq allura a asibiti"
"Allah ya kaimu" yabata amsa tareda yin gaba sai dai har cikin ransa yana jin dadin wannan sunan da take kiranshi dashi,
Daki takoma inda su ammi suka gama shirinsu tsaf domin tafiya Maiduguri,
Lokacin da zasu tafi ikhlas harda kukanta, nan suka tafi suka barta daga ita sai hajiya kakarta.
Washe gari da safe lamido yaje daukarta domin kaita asibitin, ba karamin kyau tayi ba domin wata koriyar atamfa wax tasaka wacce tasha dinki mai kyau, farin mayafi tasaka da farin takalmi idan kaganta bata da maraba da amarya,
Gaban motar ta shiga ta zauna suka tafi, suna hanya wayarshi tafara ringing, dubawa yayi yaga xahar ce dan haka yaki picking, jin ta dameshi da kira yasashi dagawa,
"Hello zan kiraki anjima"
Taji yafada tareda katse wayar, ko wacece kuma oho ko kuma data daga cikin matanshi ne, ta raya hakan aranta, har sukaje asibitin babu wanda yayi magana acikinsu,
Bata wani jima ba tagama abinda ya kaita ta dawo wurin Lamido ya dauko hanyar dawo dasu gida, wayar ikhlas ce tafara kara dan haka ta lalubota acikin jaka, sunan elmustapha tagani nan ta dauka da fara'arta,
"Yayana nayi fushi ai tunda baka zo kaga danka ba" tafada tana murmushi,
"Yanzu gani nan ai zanzo na wanke laifina, kina gida?" Elmustapha ya bata amsa daga daya bangaren,
"Ehh, to sai kazo" tafada gamida katse wayar,
Hade rai lamido yayi, lokacin da suka karasa gida daidai lokacin elmustapha ya karaso ya fito ya tsaya ajikin motarshi,
"Bani yarona" lamido yafada gamida dauke sadiq daga kan cinyarta,
Tsayawa sororo ikhlas tayi tana kallonsa, shi wannan wai meye nufinsa ne? Yanda yake nuna mata gadara akan yaron nan ko shine ya haifeshi iyakaci kenan,
Bata gama tunanin da take yi ba taji ya balle murfin kofar yafita da sadiq akafadarsa,
Tashi tayi tafita ta nufi wurin elmustapha,
Murmushi yake aika mata yana kallonta,
"Maman boy rowar ganin boy din ake yimin ne?" Inji barrister elmustapha,
"Ni na isa? Daga asibiti muke ne kuma sadiq din muka kai"
"Ayya Allah ya bashi lafiya"
Gaisawa suka danyi suka taba yar hira sannan yayi mata sallama zai tafi, wata katuwar leda mai kyalli ya dauko wacce take cikeda kayan jariri iri iri,
Godiya sosai ikhlas tayi masa ta juya ta shiga cikin gida da ledar kayan a hannunta.
Lokacin da lamido ya shiga cikin gida duk ranshi abace yake domin yagama fuskantar inda elmustapha ya dosa yasan son ikhlas yake yi sai dai amma awannan karon shi bai shirya rabuwa da itaba shiyasa ma zaiyi duk iya yinsa naganin bata kufce masa ba,
Wurin baffa ya shiga ya sameshi shida innah zaune suna tattaunawa,
"Har kun dawo?" Inna ta tambayeshi,
"Ehh innah" yabata amsa tareda zama akan kujera,
"Baffa dama cewa nayi tunda maman yaron nan ta haihu sai ayi maganar daurin auren ko..?" Yafada cikin dakewa,
Murmushi baffa yayi yace "hakane lamido amma mu da bari mukayi har sai tayi arba'in tukunna"
"To shikenan baffa Allah ya kaimu"
"Amin amin" tashi yayi ya fita daidai lokacin ikhlas ta shigo dauke da kayan da elmustapha ya bata,
Binta yayi zuwa dakinta domin bata sadiq, ajiye kayan tayi awurin hajiya tana cewa "barrister elmustapha ne ya kawowa sadiq.."
Fita tayi domin karbo sadiq ahannun lamido, mika mata sadiq din yayi yace,
"Kar ki kuskura ki sakawa yarona wannan kayan da wancan mutumin ya kawo"
Yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa,
Tsayawa tayi tana kallonsa abin nasa ma abin dariya "lallai abban sadiq"
Tafada tareda shigewa dakinta. Haka taci gaba da kulawa da yaronta, lamido kuwa kullum yana gidan sannan duk wani nauyi na sadiq to a wuyansa yake da haka har sukayi arba'in alokacin suka fara shirye shiryen zuwa Maiduguri, kwanansu arba'in da shida suka tafi itada hajiya amma ita hajiya bazata dawoba,
Lamido bai so wannan tafiyar ba amma dolenshi babu yanda zaiyi, sai dai fa amma kullum cikin yiwa ikhlas waya yake yana tambayarta ya boy dinshi,
Tunda sukaje ammi da hajiya suka fara gyarata domin baffa yace tana komawa daura aurensu za ayi da lamido inyaso daga baya ta tare wannan shine burin lamido domin idan aka daura auren hankalinsa zai fi kwanciya ko bata tareba yasan dai mallakinsa ce,
Gyara iya gyara anyiwa ikhlas nan tayi kyau tafito fes tamkar budurwa, tunda taje kullum tana makale da abdalla wanda yanzu ya sake zama dan saurayi,
Satinta biyu ta shirya ta koma yola bayan tasha gyaran jiki dana gashi da kunshi samfarin na yan Sudan, ga wasu turarurruka da humra masu dadin kamshi da ammi ta hada mata baya ga turaren wuta mai dadi wanda yake sati kamshinsa bai fita ba.
_Gaisuwa mai tarin yawa gareki hawwaty da dukkan masoyan ruwan kashe...._
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/26, 5:13 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_*54*_
~~~ Sai wurin sallar magrib sannan ikhlas ta sauka,
Gajiya iya gajiya ta gaji sosai, dan haka koda takarasa gida salla kawai tayi taci abinci ta kwanta,amma ko minti biyar batayi ba da kwanciyar lamido ya kirata kan ta kawo masa yaronshi zai ganshi,
Tashi tayi tana zumbura baki tasa hijab ta fita,
Wai! Ai lamido naganinta yaji ya rikice saboda kyawun da yaga tayi masa, bai jima ba ya tafi ya nufi wurin baffa anan ya tayar da darun shidai nan da wani satin yake son adaura masa aure da ikhlas nan da watanni uku masu zuwa kuma sai ta tare,
Ganin ya damu yasa baffa amincewa amma da sharadin sai yaji ta bakin ikhlas din, washe gari Baffa ya sameta adaki da maganar, bata ki ba saboda tana son ta cikawa marigayi burinshi kamar yadda yabar mata wasiyya duk da tasan zata sha fama da lamido idan ya zama mijinta saboda sunada mabanbantan ra'ayi shida marigayi,
Acikin kwanaki uku kacal aka gama shirye shiryen bikin ikhlas da lamido, amma har yau bata ga idonshi ba,
Aranar juma'a aka daura auren, sai aranar yazo gidan yasha farin yadi kanshi babu hula, yanzu kam kansa tsaye zai shiga dakin domin ta zama mallakinsa,
Abakin gado ya sameta tana zaune tana shayar da sadiq, sai da ya shiga cikin dakin sannan yayi sallama, cikin sauri ta sauke rigarta ta janye sadiq,
Amsa sallamar tayi kanta akasa, hannu ya mika ya karbi sadiq yana mai bin hannunta da kallo saboda har lokacin kunshin hannunta yana nan bai goge ba,
Fita yayi da sadiq a hannunshi ya tasamma wurin innah, ajiyar zuciya ikhlas ta ajiye tana kallon kofa,
Bai jima awurin innah ba ya fito ya koma dakinta ya mayar mata da sadiq ya tafi gida,
Afalo ya iske fadila da ihsan kowa tana harkar gabanta,
Duk wanda yaganshi yasan yana cikeda farin ciki domin hakan ya kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskarsa,
Zama yayi a kujerar tsakiyarsu,
"My fadila my ihsan dama ina son magana daku,ina son sanar daku cewa yau nayi aure na karo muku abokiyar zama"
Kallo suka bishi dashi dukkaninsu kallo irin na mamaki,
"Aure fa? A ina?" Ihsan ta tambayeshi,
"Ehh, amma ba wata bakuwar fuska bace kun santa, ikhlas ce maman sadiq"
Shiru kowaccensu tayi domin dama sun dade da zargin sonta yake amma abin yazo musu da sauki saboda ganin yanda yaketa rawar jiki basu zaci bazawara ya aura ba har da d'a,
Jin basu yi magana ba yasashi mikewa ya wuce ciki,
Nannauyar ajiyar zuciya fadila ta ajiye ta kalli ihsan,
"To ihsan kin dai ji yanda yace so yanzu ya rage garemu musan abinyi"
"Kamar yaya fa?" Ihsan ta bukata,
"Ina nufin yanzu lokaci yayi Wanda zamu hade kanmu mubar fada mu ajiye kishi agefe mu tarairayi mijinmu cikin kissa mu rabashi da waccar tsohuwar domin idan ba haka muka yi ba to wallahi yan kallo zamu zama idan ta shigo cikin gidannan nan kuma kinga tafimu shekaru gashi ta taba aure kuma shima yana sonta domin da ace baya sonta da bazai aureta ba, dan haka muyi karatun ta nutsu mu nemi mafuta kar mu bari tafimu fada awurinsa"
Dagowa ihsan tayi ta dafa kafadar fadila "hakika wannan shawara taki tayi kuma naji dadinta, idan har tayi kuskuren shigowa gidan nan to sai tayi dana sani domin sai mun hanata sukuni sai mun hanata jin dadin zaman aure, zamu tanadi makirci da sharri kala kala agareta, hmmm balle ma abin zai zo mana da sauki tunda bazawara ce kinga ta cikin ruwan sauki zamu cinma burinmu na fitar da ita daga cikin gidan nan"
"Yawwa ihsan ashe kin fahinci inda na dosa, wallahi Lamido ya mace akanta irin mutuwar da bazai rayuba har abada, kigafa irin kulawar da yake bata sai kace ita tafi kowa" fadila tafada tana murmushin takaici,
"Kibarta zamuyi maganinta" inji ihsan, da wannan shawarar suka tsayar da matsaya,(kunji fa masu karatu fadila da ihsan yanzu an hade kai domin fitar da ikhlas).
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/26, 5:22 PM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_55_*
~~~Lamido na cikin dakinshi duk farin ciki yagama lullubeshi, wai yau shine ya zama mallakin pretty bayan ya jima da fitar da rai da samunta,
Wanka ya shiga yayi ya fito yafara shiryawa, yana tsaka da taje sumar kanshi ihsan ta shiga cikin dakin tana dan ciccin magani,
"Sai ina?" Tafada tana kallonshi,
"Zanje unguwa ne?" Yabata amsa,
"Yaushe amaryar tamu zata tare ne?" Ta sake tambayarsa,
"Sai nan da three months domin ina son sadiq ya danyi wayo kafin lokacin"
Tabe bakinta tayi ta juya ta fita tana murna aranta kuma fata take Allah yasa auren ya mutu kafin ta tare din,
Kananan kaya lamido yasha, jan wando da bakar t shirt an rubuta polo, jan takalmi sau ciki ya saka ya fito yana ta faman kamshin turare, yau ko abinci yakasa ci saboda tsabar murna,
Lokacin da ya fito su fadila suna zaune a falo suna kallo,
"Ni na fita" yafada gamida saka kai ya fice,
Babu wacce ta tanka masa har ya fice daga falon,
"Wurinta fa zai tafi" inji fadila,
"Nasani ai, yayita zuwa" ihsan tafada cikin jin haushi, nan suka cigaba da tattauna maganar kowaccensu ranta babu dadi.
Lamido na fita wurin bash ya wuce, akofar gidansu ya sameshi yana zaune akarkashin wata bishiya,
"Kaga sabon ango" bash yafada cikeda tsokana tareda mikawa lamido hannu,
Hannun bash ya kama yana murmushi "bash kaga wani ikon Allah ko? Wai ashe dai da rabon pretty matata tace.."
Kallonshi bash yayi cikeda mamaki "on top kar dai kace min dama itace matar da yayanka ya aura?"
"Wallahi bash itace, ai ban taba shiga tashin hankali da damuwa ba kamar wannan lokacin,ko kasan har bp dina sai da ya hau"
"Amma lamido meyasa kaki fada, meyasa kabar wannan sirrin acikin ranka kai kadai bayan kasan dan uwanka zai iya mallaka maka dukkan abinda ya mallaka,meyasa kaso cutar kanka? Meyasa za kayiwa kanka illa?" Bash yafada cikeda tausayin abokinshi,
"Bash sanin Broz zai iya mallaka min duk abinda ya mallaka shiyasa nayi shiru saboda bana son na shiga hakkinsa domin ban san irin son da shima yake yiwa ikhlas ba, sannan ka sani alokacin da na matsa sai na aureta to da zan iya mutuwa tunda gashi harda rabon yaro atsakaninsu,nasan ina son ikhlas soyayyar da bazan iya taba kwatantawa wata ya mace ba, to amma bana son kuma na takurawa dan uwana, dayake akwai rabon aure a tsakaninmu kaga sai Allah ya karbi rayuwarsa alokacin da bamu shirya rabuwa dashi ba nikuma sai Allah ya mallaka min ita alokacin da ban taba tsammani ba, lallai Allah ya cika mai hikima domin shine yake bawa mutum abinda yake so amma ba alokacin dashi mutumin yake soba"
Kwallace ta ciko masa ido yasa hannu ya goge yana murmushi,
"Ina tayaka murna on top Allah ya baku zaman lafiya" bash ya fada yana dafa kafadarsa,
"Amin bash nagode, bari nawuce"
"A'a mu wuce dai dan nima binka zanyi"
Tare suka shiga mota suka fita suka nufi gidan kallon ball.
Sai da akayi sallar magrib sannan Lamido ya nufi gidan baffa,
Dakin innah ya fara shiga suka gaisa sannan ya fito ya shiga dakin ikhlas, tana zaune ta goya sadiq tana goge kayan sawarshi ga waya a makale a kunnenta tanayi,
"Abdallah nace naji... Yawwa bawan Allah maza kagaida yaya Hussain kaji"
Sai da lamido yaji gabanshi yafadi rass wanda bai san dalili ba, wayar ta katse ta dago tana kallonshi,
"Abban sadiq sannu da zuwa" tafada cikin muryarta mai dadin gaske,
"Yawwa,sadiq bacci yake yi?" Ya fada yana shirin zama agefen gadonta,
"A'a idonshi biyu yanzu na goyashi" tafada ahankali,
"Miko min shi"
Tashi tayi ta sauko dashi ta mika masa, karbarshi yayi ya kwantar dashi akusa dashi ya sunkuya ya fara yi masa wasa, daga shi har sadiq din sai dariya suke faman kyakyatawa kamar wasu sabbin kamu,
Tana zaune tana gugarta tana sauraren lamido da sadiq, domin wani lokacin sai taji lamidon yana yiwa sadiq din magana sai kace babba,
"Saddiqu na bari naje salla ko? Ko zaka rakani?, yawwa saddiqu na yi zamanka naje na dawo, bye bye"
Mikewa yayi ya mika mata shi, "ungoshi naje nadawo"
Karbarshi tayi tabishi da kallo har yafice, murmushi tayi aranta tana raya cewa shima lamido har yau akwai kuruciya atare dashi saboda abubuwan da yake yi idan ya dauki sadiq,
Tana nan zaune tasamu ta kammala gugar ta kwantar da sadiq ta fara sallar isha, ko raka'a biyu bata kaiba taji sadiq ya fara kuka, sallarta taci gaba dayi, tana kaiwa raka'a ta uku lamido ya shigo,
"Sadiq meya sameka?" Jin bai daina kuka ba yasa lamido kallar wurin da take sallar,
"Kinga yi sallama ki yi feeding din yaron nan idan yayi shiru sai kiyi sallar.."
Sallarta taci gaba dayi shikuma sadiq sai kuka yake tsalawa, haushi ne ya kama lamido domin jin kukan yaron yake har cikin ranshi, zaman tahiya tayi tai sallama ta kuma mikewa domin gabatar da shafa'i da wutri,
Tashi lamido yayi yaje ya sha gabanta, "me zakiyi? Wallahi baki isaba babu sallar da zaki sake yi har sai kin bawa yaron nan nono yasha,kina ganin yaron yana ta faman kuka amma kin kyaleshi saboda rashin tausayi"
Kallonshi ikhlas keyi cikeda mamaki, "karbeshi ki bashi yasha" yasake fada yana mika mata yaron,
"Dan Allah abban sadiq kabarni na idar wallahi yanzu idan sadiq ya kama ban san lokacin da zai koshi ba, cine dashi kamar gara.."
Hijabinta ya fusge "wallahi a'a, ki karbeshi nan da 12 nadare idan ya koshi sai kiyi sallar, may be ma tun fitata yake kukan amma kika kyaleshi dan mugunta"
Karbar sadiq din tayi ta zauna har lokacin lamido yana tsaye akanta ya zuba mata ido yana son yaga tafara feeding din sadiq.
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/27, 7:44 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
_*56*_
~~~Maimakon tafara feeding dinshi sai tafara jijjigashi,
Kallonta ya tsaya yi, har tsawon minti biyu bata bashi nonon ba sai jijjigashi take gashi sai kuka sadiq din yake tsalawa,
"Wai meye haka ne? Kibawa yaro nono kin barshi sai kuka yake" Lamido yafada azuciye,
Nan dinma dai batayi wani yunkuri ba,
"Ko dama barin yaron nan kike yi da yunwa ne?"
Shiru tayi taci gaba da jijjigashi tana mamakin lamido domin nuna mata yake kamar yafita son sadiq ko yamanta cewar itace tayi dawainiyar cikinshi tayi nakudarsa?
"Wai lafiyarki kuwa?" Yafada cikin fad'a,
"Bari nabashi ruwa" tafada tana sabashi akafada, tsayawa lamido yayi domin ganin ikon Allah,
Ruwan ta dauka tabashi yaki sha idan ma ta saka masa fidar abaki sai ya ki bude bakin nashi,
"Yaron nan ba ruwa zaisha ba yunwa yakeji nafada miki amma kin hanashi abincin shi"
"To ka matsa daga kaina mana" tafada tareda jan hijabinta ta saka ta cusa sadiq cikin hijabin tafara kiciniyar shayar dashi,
Murmushi ne ya kwacewa lamido batare da ya shirya ba sai yanzu yagane nufinta nakin bawa sadiq abincinsa ashe kunya take ji, bata son yaga kirjinta,
"You kid your self yarinya" yafada aranshi,
"Ki fito da yaron nan yasha iska, ya zaki kunsheshi acikin hijabi baya shan iska?" Yafada yana kallonta,
"Da iska fa" tafada tana sake baza hijabin"
Juyawa yayi zai fita saboda yaga alamar indai yana nan bazata sake ta shayar da sadiq yanda ya kamata ba,
"To sai da safe" yafada tareda ficewa daga cikin dakin, fuskarshi dauke da murmushi yafice daga gidan domin ikhlas tabashi dariya sosai in banda ita ai ranar wanka ba aboye cibiya,yana tafe yana murmushi har yaje gida,
Kasancewar yau ranar girkin ihsan ne yasashi isketa afalo tasha sleeping dress tana jiranshi,
"My ihsan bakije kin kwanta ba?"
"Ai na tsammaci ko agidan amaryar zaka kwana yau" tafada cikin gatse,
Duk da ya gane magana ta fada masa amma sai ya share saboda baya son su rinka samun sabani da matanshi akan ikhlas,
"Wa? Ai yau ni nakine ke daya" yafada tareda jan hannunta zuwa dakinshi.
Washe gari agida ya wuni bai fita ko inaba yana gida shida ihsan ita kuma fadila ta tafi sch karatu,
Sai wurin 3 sannan ya fita, kai tsaye gidan baffa ya wuce, bai sameshi agida ba dan haka ya shiga wurin ikhlas,
Yauma kamar jiya sadiq na kwance akan gado sai kuka yake ita kuma tana toilet tana wanka,
"Yauma barinshi kikayi yana yin kukan? Ko baki gama wankan ba ki fito ki karbeshi, kinji?"
Shiru babu alamun fitowarta, yana nan tsaye yana jijjigashi ta fito daure da zani daurin kirji, yau danma Allah yasota bada towel ta shiga ba ai da tasha kunya,
Mika mata shi yayi yana bin gashin kanta da kallo wanda ke nannade wuri guda,
Karbar sadiq din tayi ta je bakin gado ta zauna sai dai takasa bashi yasha, sanin idan yana tsaye ba zata bawa sadiq nonon ba yasashi fita daga dakin ya nufi dakin innah amma sai ya tarar bata nan dan haka ya fito,
Lamido na fita ikhlas ta janye zanin tafara feeding din sadiq, tana tsaka da shayar dashi lamido ya shigo, kiciniyar janye bedsheet din dake shimfide akan gadon tafara yi domin rufe jikinta,
"Oh sorry" yafada tareda juya mata baya amma duk da haka hankalinta bai kwanta ba har sai da ta janyo hijab ta saka ta rufe kirjinta,
"Na shiga wurin innah na tarar da bata nan ina tatafi?" Ya tambayeta har lokacin bai jiyo ba ya juya mata baya,
"Gidan su sayyid ta tafi ganinsu" ta bashi amsa,
"Ok to ni natafi" fita yayi yatafi, shi lamarin ikhlas dariya yake bashi saboda yanda take boye boye sai kace wata budurwa, amma hakan ya burgeshi ganin yanda taketa boye mishi bata son yagani, shi da yake matsayin mijinta ma boye mishi take ballantana mutanen waje, agaskiya wannan abu ya burgeshi domin wasu matan ma a kasuwa ko acikin motar haya ko a asibiti ko agidan biki ko agidan suna haka zakaga sun yaye mayafi sun kwaye riga cikinsu awaje kirjinsu awaje suna shayar da yaro, (yan uwa mata yakamata mu kula),cikin gari ya shiga bai sake waiwayar gidan ba sai wurin 9 da yan mintuna bayan ya iyowa ikhlas yar siyayya,
Kayan marmari ya siyo mata da kilishi cikin takarda, ko dakin innah baiyi niyyar shigaba domin yasan kila yanzu ta kwanta dan haka ya saka mata nata siyayyar a kitchen,
Dakin ikhlas ya bude ya shiga amma duhu didim, tunani yafara to kodai bata nan,to amma ina zataje da daddaren nan sai dai watakila bacci tayi, wayarshi ya haska ya kunna fitilar dakin nan haske ya gauraye dakin, can tsakiyar gado ya hangota akwance itada sadiq, ledojin hannunshi ya ajiye ya karasa gaban gadon ya sunkuya inda suke kwance, tana sanye da sleeping dress mai santsi kalar hanta,rigar iya gwiwarta take mai dan siririn hannu ga sadiq kuma tana feeding dinshi sai bacci take,
Kirjinta ya kalla sai da yaji wani Yarr ajikinsa saboda yanda yaga kirjinta acike kamar bata taba shayarwa ba,tsayawa yayi ya zuba mata ido yana kallonta wanda hakan ya daukeshi tsawon lokaci batare da ya sani ba,
"Lallai dole aringa boye min ashe da dalili" yafada acikin zuciyarsa, bargo ya warware ya lullubesu yaje ya kashe musu wutar dakin ya fita,sai yanzu ya gane dalilinta na boye masa siffarta,
Tunaninta kawai ke damunshi da son kasancewa da ita sakamakon ganin kirjinta da yayi, har yaje gida bai daina ganin kyakkyawar surarta acikin idonsa ba.
Kamar wanda yasha kayan maye haka ya zama a kasalance duk jikinsa ya mutu, packing yayi ya fito ya nufi cikin gidan, koda yaje dukkaninsu basa falo da alama kowacce ta shige bedroom dinta,
Kayan da ya siyo musu ya ajiye akan dining ya wuce bedroom dinshi, wanka ya shiga yayi ya fito yasaka kayan bacci riga da wando iya cinya, kan gadonshi ya hau ya kwanta ya runtse idonshi sakamakon jin yanayin jikinsa ya fara sauyawa yasan ba komai ke dawainiya dashi ba face son kasancewa da ikhlas,
Kasa bacci yayi in banda juyi babu abinda yake yi, ganin lamarin yana neman ta'azzara yasashi tashi zaune, wayarshi ya dauka ya budo hotonta ita da sadiq wanda ya dauka batare da ta saniba,
Kallonta yake yi a hoton kamar zai cinyeta, agogo ya duba yanzu karfe 1 saura nadare yasan yanzu tana can tana baccinta cikin kwanciyar hankali amma shi ta barshi da aikin tunaninta.
_Fatan Alkairi gareku stylish bich da Hajja maman ihsan, ina addu'ar Allah ya raya mana baby ihsan_
*_Ummi A'isha_*ππ»
[12/30, 7:04 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_57_*
~~~Zuciyarshi ce taci gaba da harbawa da sauri da sauri, number dinta ya danna yafara kiranta,
Tana zaune tagama sakawa sadiq Pampers taji kararar waya, sai da gabanta ya fadi saboda duk zatonta ba kalau ba ganin abban sadiq na kiranta acikin daren nan,
"Hello abban sadiq" tafada lokacin data kara wayar a kunnenta,
Wani sanyi yaji ya ratsashi dalilin jin muryarta,
"Uhm ina sadiq?" Taji ya fada cikin kasalalliyar murya,
"Gashi nan yanzu ya gama kuka"
"Kuka kuma? Kukan me yake yi?"
"Kukan rigama.."
"Kodai barinshi kikayi da yunwa?" Ya sake tambayarta,
"A'a, kawai dai rigima ce salon ya hanamu bacci" tafada bayan ta kwantar da sadiq ajikinta,
"Yana da yawan kukane?"
"Sosai ma"
"Ai barinshi kikeyi da yunwa shiyasa yake miki kuka"
"A'a wallahi kawai dai kukan rigima ne sai kace wanda ya gado"
"Gado?" Ya tambayeta yana murmushi,
"Ehh" ta bashi amsa,
"To wa ya gado a kukan?" Ya tambayeta cikeda nishadi domin yau wani nishadi yake ji atare dashi,
"Kai ya gado" tabashi amsa tareda lumshe idanuwanta,
"Sai dai ke" ya mayar mata da amsa,
Murmushi tayi wanda har yana jiyoshi acikin kunnensa,
"Meya baki dariya?"
"Naji ne ai kace wai ni ya iyo a kuka"
"Ehh mana, kin san dai komai naki ya debo"
"Naka dai" tafada tana murmushi domin itama tafara jin dadin hirar da suke yi,
"To naji na yarda ni mai kukane lokacin da ina kamarshi"
"A'a ni ba haka nace ba"
"To me kikace? Uhm, fadi naji"
Jin alamun shigowar mutum yasashi juyawa dakyar, fadila yagani cikin night gown red mai kyau taci kwalliya kamar me shirin zuwa dinner,
Karasowa tayi cikin yauki tana kallonshi,
Ajikinshi ta zauna ta dora kanta akan kirjinshi,
"Bari na kyaleki kiyi bacci to,ki shafa min kan sadiq dina pls kinji, sai gobe"
Yafada tareda katse wayar ya maida hankalinsa ga fadila wacce tasha kunu,
"Kaida waye?"
"Nida matata ne" yafada yana shafa kanta, tabe baki tayi tana jin kishi yana shigarta,
Abangaren ikhlas kuwa bata so abban sadiq ya katse musu hirar da suke yiba, rungume sadiq tayi ta lumshe idonta tana mai jin wani yanayi agame da abban Sadig.
Washe gari da safe data tashi taga ajiya, mamakine ya kamata lokacin data ga abubuwan da suke ciki domin tasan abban sadiq ne ya kawo mata,
"To yaushe ya kawo min? Naga munyi waya dashi amma bai fada min ba" tafada acikin zuciyarta, tunowa tayi da cewar zataje gidan elmustapha yau saboda ni'ima bata da lafiya tana son zuwa dubata,
Wayarta ta dauko lokacin karfe 8:30 nasafe, abban sadiq tafara kira domin ta nemi izini,
Yana kwance yana bacci fadila na gefenshi wayar tafara vibration har zata tsinke sai fadila ta daga,
"Abban sadiq ina kwana?" Fadila tajiyo muryarta daga can,
"Bashi bane mayya jarababbiya, in banda ke jarababbiya ce da daddare baki kyaleshi ba da safe ma bazaki kyaleshi ba? Tsabar jarabar son namiji tun jiya kike like masa..."
Dif ikhlas ta katse wayar domin ta gaji da jin wadannan munanan kalaman na fadila, ranta taji ya dan sosu domin maganganun fadila masu zafine,
Bude ido lamido yayi ahankali yana kallon fadila,
"Meya faru?"
"Wata ce ta kiraka, ya za ayi ta kiraka da sassafen nan dan tsabar rashin adalci..."
Fautar wayar yayi ya duba sunan pretty dinshi yagani hakan yasashi tashi zaune ya dubi fadila,
"To meye damuwarki da wayata? Waya saki ki dauka? Ina ruwanki da wayar da ta iyo min? Kika sani ko yarona ne bashida lafiya ta kirani ta fada min"
"Oho muku dai idanma mutuwa yayi wannan kuma damuwarku..." Kafin ta karasa ya dauketa da mari, tashi tayi cikin takaici,
"Akan waccar banzar zaka mareni? Wallahi baka isaba, ni ba baiwa bace da zaka sakani agaba ka mareni ba, wallahi bazan yarda ba" tafada tareda fashewa da kuka,
Ihsan ce ta shigo dakin atsorace domin ta jiyo hayaniyarsu,
"Meyake faruwa?" Ihsan ta tambaya,
"Marina yayi akan wannan kucakar matar tashi ta kirani na daga"
Mikewa yayi yai kanta zai sake bata wani marin, cikin sauri ihsan ta shiga tsakani,
Tashi fadila tayi tana kuka taje ta rungume ihsan, "jiya raba dare suka yi suna waya ko dakina bai zoba sai nice na biyoshi nazo na sameshi yana waya da ita sannan yau sassafe ta kirashi awaya kuma ace bazan yi magana ba ina ji ina gani acuceni?"
"Wallahi bakiyi laifi ba fadila, ya za ace kina tare dashi wata ta kirashi? Agaskiya ba ayi mana adalci agidan nan kullum cikin zuwa ganinta ake sai munyi magana ace yar amanace to ai kowa ma dan amana ne, gaskiya mun gaji da wannan abun ehe gara kawai akawota gidan nan itama ta tare mu huta da wannan yawo da hankalin da ake yi mana" ihsan tafada tareda jan hannun fadila suka fice daga dakin,
Binsu yayi da kallon mamaki domin yagama ganewa kishin ikhlas suke yi sosai,
Komawa yayi ya kwanta ya fara kokarin nemanta awaya amma bata shiga ba wayar akashe take,
Wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya cikin farar t shirt da blue din wando,
Fita yayi daga gidan ya nufi gidan baffa, koda yaje agurguje ya shiga wurin baffa suka gaisa ya fito ya shiga cikin gidan, dakin ikhlas ya leka daga ita sai towel tana zaune agefen gado tana feeding din sadiq da alama daga wanka ta fito,
"Assalamu alaikum" yafada tareda kokarin shiga cikin dakin,neman abin da zata rufe jikinta dashi ta fara daga karshe data ga bata da mafita sai kawai ta janye sadiq din tajawo towel din ta rufe kirjinta nan kuwa sadiq ya callara kuka,
Kyaleshi tayi tafara amsa sallamar da lamido yayi,
"Meye haka?" Lamido ya fada yana kallonta,
Bata bashi amsa ba taci gaba da gyara towel din jikinta ga sadiq kuma yanata faman yin kuka,
"Bai koshi bafa" yafada idonshi akanta,
"Allah ya koshi" ta bashi amsa, murmushi yayi ya juya mata baya aranshi yana cewa "wanne darene wanda jemage bai ganiba?", dan murmushi ya sake yi mai kayatarwa domin har saida dimples dinshi suka bayyana batare da ya shirya ba, lebenshi nakasa ya dan lasa da harshenshi yana murmusawa,
"Hmmm kidaina wani boye boye saboda nariga da naga abinda kike boyewar"
Jin maganar tashi tayi tazo mata irin zuwan bazata,
*_Ummi Shatu_*ππ»
[12/30, 7:04 AM] Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_58_*
~~~Ahankali ta dago da kanta ta kalleshi,amma ta kasa magana saboda kunyar data gama rufeta wani irin nauyin lamido take ji marar misaltuwa amma takasa yarda da abinda yafada cewar yaga kirjinta, kanta ta sunkuyar cikeda kunya,
"Meya faru dazu kike yimin waya?" Tajiyo muryarshi yana sake yi mata magana,
"Am dama gidan ni'ima nake son zuwa zanje na dubo ta bata da lafiya"
"Yaushe?"
"Idan anjima"
"To ba yau ba"
Yana gama fadin haka ya fita daga cikin dakin, binshi tayi da kallo aranta tana jin mamakin wannan isar tashi lallai ta yarda maigida ko yaya yake akwai nuna iko,
Shiryawa tayi ta kwanta tunda ya hanata zuwa gidan ni'iman, tana nan akwance ta jiyoshi yana yiwa innah sallamar ya tafi, ko dakin nata bai dawoba ya wuce,
Innah ce ta shigo dakin nata ta karbi sadiq ta goyashi ta fita, wayarta ta dauka ta kira matar yayanta ta hadata da abdallah suka fara hira, kusan kullum katin wayarta yana karewa ne sanadiyyar hirarta da abdallah duk lokacin da tayi recharging to shi zata kira.
Misalin karfe uku na yamma tana daki tana yiwa sadiq wanka lamido ya shigo,dan satar kallonta yayi ya kalli yaronshi,
"Sadiq zaka rakani unguwa? Shirya maza ka rakani" yafada tareda ficewa,shirya Sadig tayi cikin blue din riga da wando fari ta saka masa farar safa da blue din takalmi, turare ta fesa masa,
Dagashi sama tayi tana dariya "zakaje wurin abba? Zaka raka abbanka unguwa ko? To zo na kaika abba"
Tana saukeshi taga lamido atsaye yana kallonta kur ko kiftawa ba yayi dan haka taji wata irin kunya ta kamata, mika masa sadiq tayi tana cike da jin kunya,
Karbarshi yayi "yawwa saddiqu na, kayi kyau my boy"
Har yakai bakin kofa yajiyo maganarta "iya sadiq ne zai yi rakiyar"
"Ehh" yabata amsa,
"Saboda me?"
"Saboda mata basa zuwa wurin"
"Akwai wurinda mata basa zuwa dama?"
"Da akwai"
"Inane?"
"Gidan kallon ball"
Dariya ta danyi yayinda shikuma lamido ya fice dauke da sadiq a kafadarsa.
Tunda suka fita gidan kallon ball yatafi shida bash basu baro wurin ba sai 9 lokacin har sadiq yayi bacci,
Ajiye bash yaje yayi a gida sannan ya nufi gidan innah,
Ikhlas na kwance ta zuba ido ta zuba ido amma shiru babu lamido babu alamarsa dan haka tayi shirin baccinta tayi kwanciyarta,
Har ta dan fara bacci sama sama taji shigowar lamido yana dauke da sadiq a kafadarshi yana bacci,
"Har kin fara bacci?"
"Abban sadiq sai yanzu?" Tafada tareda jan blanket ta rufe jikinta domin rigar bacci ne ajikinta kalarta pink marar duhu shara shara,
"Ehh shima har yayi bacci" kissing din sadiq yayi ya mika mata shi yana kallonta k'asa k'asa domin duk da cewa ta rufe rabin jikinta da bargo hakan bai hanashi hango kyakkyawar rigar baccin dake sanye ajikinta ba sannan ga yalwataccen gashin kanta nan mai mutukar shek'i da bak'i daure wuri guda kanta babu koda dan kwali,dakyar ya iya daurewa yayi controlling din kanshi ya daidaita nutsuwarshi ya dauke idonshi daga kanta ya juya ya fita,
Kwatar dashi tayi ajikinta ta koma ta kwanta tana tunanin al'amuran rayuwarta musamman ma mahaifinta wanda yayi watsi da rayuwarsu ita da yan uwanta domin rabonta dashi tun lokacin da ya koreta daga gidansa har yau bata sake jin labarinsa ba.
Washe gari da safe bayan ta shirya tsaf ta fita falo da sadig a hannunta, kan dining taje ta zubo ruwan zafi ta hada tea takoma falo ta zauna,
Zille zille sadiq yafara nan ta duka da niyyar ajiye cup din tea din amma cikin rashin sa'a sai sadiq ya shuri hannunta da kafarshi nan ruwan zafin ya zuba akafarshi,
Kuka ya cillara wanda har sai da innah ta fito daga dakinta tana tambayar meya sameshi,
Mikewa ikhlas tayi tana rike dashi,
"Wlhi innah konewa yayi da ruwan zafi"
"Konewa? A ina? Muga?"
Innah tafada agigice, karbarshi inna tayi ta duba kafar wacce tuni har wurin yayi ja ya tashi sosai,
"Wai wai haka wurin ya kumbura? Maza kira lamido yazo ya kaishi asibiti"
Agigice ikhlas ta dauko wayarta tafara kiranshi, yana kwance adakinshi shi kadai kasancewar yanzu ikhlas da fadila sun hade masa kai fushi suke dashi,
"Hello" yafada ahankali,
"Abban sadiq kazo ka kai sadiq asibiti"
"What" yafada da karfi tareda mikewa, ko wanka baiyi ba ya saka kaya ya fita.
Aguje yaje gidan yana yin packing ya fito a hanzarce ya shiga cikin gidan, afalo ya iske innah da ikhlas ga sadiq nan kuma a hannun innah sai tsaga kuka yake,
"Innah wai meya sameshi ne?" Yafada arude,
"Konewa yayi" innah ta bashi amsa,
"Konewa? Garin yaya"
"Tea ikhlas ta hada shine ya shureta da kafarsa tea din ya zuba a kafarsa"
Kamar wanda zai doketa haka yayi kanta yana yayyafa mata ruwan masifa,
"Wannan wanne irin sakaci ne? Ya za ayi ki dauko tea kuma ki ajiye akusa dashi, na fuskanci sam bakida kula akan yaron nan,you are very careless, yanzu ki duba kiga yanda yaron nan ya kone saboda tsabar sakacinki..."
Ikhlas ji tayi kamar ta fashe da kuka saboda tsabar takaici,
"Haba lamido ya zaka tisa yarinya agaba kayita yi mata fada haka.." Innah tafada tana kallonsa,
"Innah wallahi sakacinta ne.."
"Ba sakaci bane lamido domin babu wanda yafi uwa son danta, idan da ace tanada yanda zata yi da bata bar yaron nan ya kone ba da gara ita ruwan zafin ya konata, kabar wannan maganar ka karbeshi ka kaishi asibiti"
Bai kara magana ba ya karbeshi ya fita, wani chemist ya kaishi aka daye fatar aka yiwa wurin dressing da bandeji, jin kukan yaron yake kamar me,
Ita kam ikhlas tafiya lamido yayi yabarta da mamaki saboda yanda ya dage yake ta yi mata fada kamar zai daketa,
Ana gama yiwa sadiq dressing din ya daukeshi zuwa gidanshi, dakinsa ya wuce dashi ya kwantar dashi akan gado domin lokacin ya daina kukan,
Kayan jikinsa ya cire ya shiga wanka, yana bathroom yana wanka ihsan ta lek'o d'akin nan taga sadiq a kwance,
Tabe baki tayi ta juya tafita ta nufi dakin fadila,
"Kinga yau kuma abinda Nagani? Um yau ni naga sabon salo wai kiran salla da usir ko kin san wannan gayen d'an ikhlas yaje ya dauko yazo dashi cikin gidan nan?"
"Wai dagaske ko da wasa?" Fadila ta tambayeta,
"Wallahi dagaske, zama ki ganshi zo muje ki gani" jan hannun fadila ihsan tayi zuwa falo suka nemi wuri suka zauna suna jiran suga fitowar lamido.
Fitowa daga wankan lamido yayi ya shirya ya sa kaya yanayi yana yiwa sadiq wasa,farar t shirt mai dogon hannu ya saka da wando baki, turaren silver hummer ya feshe jikinsa dashi,
D'aukar sadiq yayi ya fita yana cewa sadiq "yarona ka gaji ko muje na kaika wurin momy" dorashi yayi akan kafad'arshi ya fita yana murmushi domin yana mutukar kaunar sadiq,
Su ihsan yagani afalo suna zaune kowacce ta dora daya akan daya fuska adaure ita kuwa fadila cingom take tauna ta turo dan kwalinta gaban goshi.
_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoyana ina miko gaisuwa gareku, daga karshe ina cikiyar k'awata BATOOL MAMMAN marubuciyar Al'adun wasu idan sakona ya sameki to ina gaisheki gaisuwa mai kima_.

[1/2, 10:23 AM] Itz Ummi A'ishaππ»: *RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
_Sak'on gaisuwa da fatan alkairi ga aminiyata cwt KAUSAR LUV,sannan ina mika sakon taya murna ga Besty PHERTYMAH XARAH bisa kammala kayataccen littafinta da tayi, Allah ya kara basira._
*_59_*
~~~ Ba tare da yako kallesu ba ya wuce yana yiwa sadiq hira domin yanda suke fushi dashi haka shima yake fushi dasu,
"Mtswwwww" ihsan taja dogon tsaki,
"Ai wallahi sai mun gyara masa zama acikin gidan nan daga shi har wacce yake shirin kawowa gidan" fadila tafada cikin jin haushi,shi dai Lamido bai San suna yi ba tafiyarsa yayi zuwa gidan baffa,
Babu kowa a falon dan haka ya wuce dakin ikhlas tana zaune akan gado cikeda damuwa, "woww!!! Handsome" tafada Acikin mind dinta daidai lokacin da idanuwanta suka hango mata kyakkyawan dressing din da lamido yayi ba karamin kyau yayiba domin yana ji da kyau da gayu, mika mata sadig yayi ya juya zai fita,
"Abban sadiq dan Allah kayi hakuri wallahi ba laifina bane" ya jiyo muryar ikhlas,
Juyowa yayi "shikenan ya wuce amma dan Allah ki rinka kulawa,ki bashi abincinshi yasha idan yagama ina falo ki kawo min shi"
Fita yayi yaje kan dining ya debi abincin da zai ci, zama yayi yaci yasha ruwa ya tashi ya koma falo ya zauna, yana zama ikhlas na fitowa,
Sadiq ta bashi ta juya zata tafi,
"Kinga dan jona min kayan kallon nan pls" yace da ita tareda fara yiwa sadiq wasa, harshen sadiq ya kama yana yi masa wasa shi kuma sadiq din sai dariya yake kyalkyalawa,
Tv ta jona masa ta juya ta koma dakinta ta kwanta, kwanciyarta babu dadewa bacci ya dauketa daga karshe ma bata san lokacin da lamido ya dawo da sadiq ba dan sai wurin 3 ta tashi taga sadiq akusa da ita shima yanata baccin.
Washe gari da azumi ikhlas ta tashi saboda ana binta azumi guda daya bata rama ba,
Akwance ta wuni tana bacci sai da yamma ta fito tana goye da sadiq, innah ta samu a falo ita da lamido suna hira, ai sadiq na ganin lamido ya fara tsalle yana murna kamar zai fado daga bayan ikhlas yanda yake yi kamar zai kunce zanin ya sauko abin har mamaki ya bawa ikhlas saboda ta fahimci sadiq yanzu ya gama gane lamido sosai,
Sauko dashi tayi ta mikawa lamido,
"Saddiqu na ka tashi daga baccin? To zo mu gaisa"
Tana jinshi ya takarkare yana ta yiwa sadiq din wasa, kitchen ta shiga ta fara gyara wake saboda alale take son yi,
Kunun shinkafa ta dama ta fito, iya innah ce kadai a falon da alama lamido ya fita da sadiq,
Kitchen ta sake shiga bayan an markado mata waken, alalanta ta shirya mai dadi wanda yasha alayyahu da dafaffiyar hanta,
Ana kiran salla ta gama, kayan ta diba takai dakinta bayan ta dibarwa innah nata,
Sanyayyen zobon data dama ta diba tasha kawai taje ta dauro alwala bayan tayi wanka saboda tana son taji karfin jikinta,
Doguwar riga marar nauyi mai hannun shimi ta saka tayi salla tana idarwa ta cire hijab dinta tajawo kwanon alalanta ta dauki filet ta saka zata fara ci kenan lamido ya shigo dauke da sadiq a kafadarsa,
Agefen gado ya kwantar dashi ya dawo gabanta ya zauna, flaks din gabanta ya fara bubbudawa yana gani,
"Babu tayi?" Yafada bayan ya langabe kanshi yana kallonta, rigar jikinta ba karamin kyau tayi mata ba, tayi mata caras sannan babu wanda zai ganta yace ta taba haihuwa,
"Bisimillah" ikhlas tace dashi cikin jin kunya, cup ya dauka ya tsiyayi kunun gyada yafara sha tareda tsareta da ido yana karewa surarta kallo,
Duk ikhlas tagama takura gashi takasa sakewa taci abincin da ta ci burin ci, duk yanda takai ga kwadayin alalan nan haka ta kyale tana cakularsa,
"Azumi kikayi?"
"Eh" ta bashi amsa a hankali,
"Azumin me? Ramuwa?"
Girgiza kai tayi alamar a'a,
"Ok ai na dauka ko baki cika ramadan din ba"
Shiru tayi bata cemasa komai ba amma da alama kunun nata yayi masa dadi domin har ya shanye mata rabi, ita dai alla alla take ya gama ya tafi domin ta samu ta sake taci abincinta,idonshi ya zubawa kyakkyawar fuskarta kurrr baya ko kiftawa amma ya lura sam ta kasa sakewa dashi domin abincin ma ta kasa ci saboda yana wurin,
Tashi yayi yai mata sallama ya tafi sai alokacin ta iya cin alalanta.
Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali kullum lamido yana gidan innah manne da sadiq, su kansu su fadila suma yanzu sun sauke abinda yake kansu sun shirya da lamido amma fa ta ciki na ciki,
Ikhlas na zaune adaki tana goge kayanta taji wayar ta na tsuwwa dauka tayi anan yake sanar da ita ta shirya anjima zai zo ya kaita gidan barrister elmustapha, kashe wayar tayi tana cewa "yau ka ga dama kenan zancen da tun sati uku da suka wuce na rinka binka ka kaini kaki"
Tashi tayi ta shirya ta saka atamfa ja da jan mayafi tasaka sarka da dan kunne golden,
Shirya sadiq tayi bayan ta gama shiryawa, blue din wando ta saka masa da pink din riga ta saka masa safa pink da blue din takalmi,
Tana kammala shiryawa lamido na shigowa, sallama taje ta yiwa inna ta fito suka tafi yana rikeda sadiq, ba karamin kyau yaga prettynshi tayi ba gaba daya ta tafi da tunaninsa,
"Yaushe zan zo mu tafi?" Ya tambayeta lokacin da suka karasa kofar gidan elmustspha,
"Sai da daddare" ta bashi amsa,
"No yamma dai"
Langabe kai tayi "dan Allah ka bari sai dare" tace dashi cikin shagwaba,
Mika mata sadiq yayi batare da yace komai ba, nan daddadan kamshin jikinta yakaiwa hancinsa ziyara wanda ya nemi rikitashi,bude kofar motar tayi ta fita ahankali tana dan murmushi wanda ita kanta bata san dalilinta na yinsa ba,kallonta ya rinka yi har ta bacewa ganinsa,sai da yaga shigarta gidan sannan ya tafi.
Tunda sukaje gidan bini bini sai Lamido ya kirata awaya ya tambayeta sadiq da haka har dare yayi sai wurin 8 yazo daukarta,
Perfect suya spot ya nufa dasu wato wurin sayar da kayan makulashe, packing yayi agefen titi ya jiyo yana kallonta,
"Me zan taho miki dashi?"
"Babu komai"
"Baki isaba dole sai kin fada wallahi"
Fuskarshi yakai saitin tata"uhm fadi ina jinki"
"Donote da meat pie ko fish pie.." Tafadi cikin jin kunya,
Kallon tsukakken bakinta yayi yanda take magana"ai wannan bakin Naki shine meat pie da donote din" yace da ita yana kashe mata idonshi daya,
Fita yayi daga cikin motar yabarta da murmushi akan fuskarta,
Tana nan zaune yaje ya dawo hannunshi dauke da ledoji guda 3 iri daya, biyu ya mika baya ya ajiye ita kuma ya ajiye mata daya akusa da ita, ledar tata ya buda ya dauki meat pie guda daya yafara ci yana driving,
Ido ta zuba masa tana kallonsa yayi kyau ainun kasancewar ya sake wanka ya sake shiga cikin yellow din riga da jan wando ga kyakkyawan sajenshi kwance akan fuskarshi sai sheki yake sannan duk taunar da yayi sai kumatunsa ya lotsa,
Ganin tanata kallonsa yasa lamido juyowa ya kalleta, "meye kiketa kallona ne ko baki baniba na baki kayanki?"
Daurewa tayi ta mika masa hannunta tana murmushi "bani kayana.."
Murmushi yayi maimakon ya bata sai ya kama hannunta ya rike cikin nashi,daga shi har ita wani yarrrr! Sukaji sakamakon wani bakon al'amari da ya ziyarcesu lokacin da hannuwansu suka hadu da juna,sunkuyar da kanta tayi tana jin yanda yake matsa yan yatsunta,
Ahankali yake juya hannunta mai mutukar laushi cikin nashi har sukaje gida amma ikhlas ta fuskanci duk kasala ta kamashi domin kamar dakyar yake yin tukin gashi idonshi yadan kad'a ya sake launi, sakin hannunta yayi ta dauki sadiq kasancewar yayi bacci,cikin kasala ya riko mayafinta nan ta jiyo tana kallonshi, matsawa yayi ya mannawa sadiq kiss a goshi,kallonshi ya mayar gareta sai da gabanta ya fadi sakamakon haduwar da kwayar idanuwansu suka yi,cikin azama ta sauke nata idon akasa domin bazata iya cigaba da kallonshi ba,hannunshi taji akan fuskarta yana shafar kumatunta ahankali ta lumshe idonta sakamakon jin bakinshi bisa nata,sakinta yayi dakyar ta fice ta shiga gida.
Tunda ta shiga gida takasa daina tunanin lamido da abinda yayi mata kasa bacci tayi sai juyi take tana aikin tunaninshi dakyar bacci barawo ya dauketa,shi kanshi lamidon shima hakace ta faru dashi domin shima ya kasa mancewa da yanayin da ya samu kanshi lokacin da yake tare da ikhlas.
Tunda haka ta faru tsakaninsu ikhlas take jin kunyarshi sam ta kasa hada ido dashi lamido ya ganeta sarai amma yayi biris da ita ya share ya nuna kamar bai fahimci abinda take nufiba alhalin ya gane domin ko magana yake mata bata taba daga ido ta kalleshi sai dai ta sunkuyar da kanta kasa gashi sai tayita kakkawar da kanta dan kar su hada ido,dariya al'amarin ikhlas yake bashi sai dai hakan yana burgeshi domin kunyar ikhlas ta dace da ita kuma tana yi mata kyau saboda ita kunya awurin mace ado ce.
Kwana biyu da faruwar wannan lamari inna ta shirya tatafi jimeta bikin yar yarta da ikhlas tayi niyyar tafiya amma lamido ya hana saboda lokacin sadiq bashida lafiya yana zazzabi,
Ikhlas na zaune takaicin duniya ya isheta lamido ya shigo shida sadiq,
"Wai damuwar me kike yi? Saboda inna bata nan? Kawai kibari zan zo na tayaki kwana" yafada cikeda tsokana yana dan kasalallen murmushi wanda ya kawata fuskarsa, bata kulashi ba ta dauki sadiq shikuma lamido ya fice,
Karfe 9 ta gama shirinta ta kwanta itada sadiq bayan tayi masa shirin bacci, har ta dan fara bacci taji shigowar lamido,tsayawa yayi yana kallonta ita da sadiq din, tana sanye cikin riga da wando dark blue masu tambarin fari ajiki amma rigar mai budadden kirji ce mai dan siririn hannu,
Abayanta yaje ya kwanta ahankali ya rungumeta ta baya,
"Abban sadiq baka tafi gida ba?" Ta tambayeshi domin ita bata zaci abinda yafada dazu cewar gaske ne ba,
"Yau zan tayaki kwana ne" ya mayar mata da amsa yana shakar ni'imtaccen kamshin dake tashi daga jikinta domin wani irin kamshine wanda gaba daya ya kasa gane kalar kamshin da jikinta yake fitarwa,shi kanshi shi dinma wani kayataccen kamshi ne mai dadin gaske yake fita daga jikinsa yana ratsa hancin ikhlas,
"Na yafe ka tafi wurin matanka" tafada tana lumshe idanuwanta,
Jiyo da ita yayi tana fuskantarshi wanda har tana iya jiyo saukar numfashinsa akan fuskarta,
"Duk basa nan sun tafi numan bikin kanwar fadila idan kuma baki son kwana dani ne sai naje na tafi na kwana ni kadai" yafada bayan yasaka hannuwanshi ya zagayeta ajikinshi,
Shiru tayi ta lumshe idanunta tana jin yanda ya shiga jikinta ya matseta duk motsin da zatayi ajikinsa ne bayan kuma ga fili nan da yawa abayanshi ya bari,
"Abban sadiq ka matseni fa" tace dashi ahankali,
Yana jinta ya rabu da ita daga karshe ya saka hannunshi jikinta yafara mika mata sakonni masu nauyin fada, cikin wani irin yanayi wanda bazai faduba suka shiga daga shi har ita wanda sun dade acikinsa kafin lamido ya iya barinta bacci mai dadi ya daukesu.
Can cikin dare yaji sadiq ya farka tashi yayi yaje ya daukeshi yabashi ruwa yasha ya maida shi ya kwantar ya koma jikin ikhlas ya kwanta,
Kiran asubar farko ta tashi tayi alwala tayi salla,lamido ta kalla wanda ke kwance yanata faman bacci,
Ganin 6 saura yasata zuwa ta fara tashinsa, juyi yayi ya bude Idonshi daya,
"Abban sadiq ka tashi kayi salla" ikhlas tace dashi ahankali idonta akasa, hannunta ya riko cikin nashi wanda har sai da taji wani irin yarr!,
Kamar meyin rada ya bude baki yace,
"Akwai ruwan zafine?"
Girgiza Kai tayi alamun babu, "to kije ki dafa min dan sai nayi wanka kafin nayi salla" yace da ita yana shafar hannunta da lallausan hannunshi,
"Wanka? Wanne irin wanka kuma?" Tafada ba tare data sani ba,
"Irin wankan da miji yake yi idan ya kwana a dakin matarshi" ya bata amsa bayan ya lumshe kyawawan sexy eyes dinshi.
_Masu karatu kuyi min uzuri na rashin ganin posting dina kullum wannan ya farune sakamakon yan abubuwan da ba za arasa ba na yau da kullum, gaisuwa mai tarin yawa agareku masu son ruwan kashe... Musamman ma mom sultan tareda zee gajou, nagode da soyayyarku._
[truncated by WhatsApp]
*RUWAN KASHE GOBARA...!*π₯
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
*_60_*
Its a dedicated ceremony,
an anniversary, but not wedding.
The easy way to tell is
its birthday.
Have a smile in all the way
& have a lovely birthday.
_HBD FIDO SODANGI KAWATA..!_, _SADY KAWATA_& _AUNTY A'ISHA (Maman Ansar)_.
~~~Juya masa baya tayi cikeda kunya domin ba karamin kunya yasata taji ba,hannunshi mai mutukar laushi taji yasaka ya kamo nata ahankali,
"Zan samu ruwan zafin?" Ta jiyo muryarshi mai dadi yana yi mata magana,
"Ehh" tabashi amsa a tausashe,tashi yayi yasaka hannuwanshi ya zagayeta,gaba daya jinta take yi acikin jikinshi wanda har ba zata iya wani kwakkwaran motsi ba sakamakon yadda ya matseta ajikinshi,
"Ba kayi salla ba fa abban sadiq" tafadi ahankali kamar me yin rada', sakinta yayi ahankali ya koma ya kwanta, ba tare data waiwayo ba ta juya ta fice daga cikin dakin ta nufi kitchen,
Ashana ta dauka ta kunna risho ta dora masa ruwan zafin,
"Agaskiya abban sadiq baka da kunya ko kadan wallahi"
Tafadi hakan tana murmushi, tana nan atsaye har ruwan ya tafasa ta juye acikin dan karamin bokiti ta dauka ta nufi cikin dakinta,
Akwance ta kuma samun lamido yasaka hannuwanshi ya zagaye sadig kanshi kuma akan pillow,
"Abban sadiq badai wani baccin ka sake komawa ba?" Ta tambayi kanta acikin zuciyarta,
Toilet ta shiga ta hada masa ruwan wankan ta fito, atsaye ta sameshi yagama cire kayan jikinshi ya rage daga shi sai gajeren wando dark blue,
Kanta akasa ta wuceshi ta koma falo ta kwanta akan doguwar kujera, shidai lamido kallonta kawai yake yi saboda yanda take jin kunyarshi abin yana burgeshi kuma yana kara wutar kaunarta acikin zuciyarsa,
Toilet ya shiga yayi wanka ya fito yazo ya shimfida abin salla,
Zama yayi yai addu'o'i bayan ya idar da sallar, kan gadon ya koma ya rungume sadiq ya koma wani baccin.
Wurin 7:30 ikhlas ta shiga dakin har lokacin dai bacci lamido suke yi shida sadiq, sadadawa tayi ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya ta saka doguwar riga ta atamfa kalar yeluwa ta dauki turare ta fesa,
Falo ta sake komawa ta zauna nan wayarta tafara neman agaji, tana dubawa taga yaya Hussain ne dan haka ta daga cikeda murna, gaisawa kawai suka yi ya hadata da abdallah suka fara hira,
Sun dade suna hira sannan suka yi sallama ta kashe wayar,
Kukan sadiq da tafara jiyowa ne yasata tashi ta nufi dakin, tana shiga taga lamido ya tashi yana shirin daukar sadiq din,
"Ina kika tafi kika bar yaro yana kuka?" Ya jefo mata wannan tambayar yana mai kallonta domin ba karamin kyau tayi masa ba, kwalliyarta ta tafi dashi dari bisa dari,
"Ina falo ne" ta bashi amsa tareda mika hannu ta amshi sadiq din,
"Abban sadiq ina kwana?" Tace dashi ahankali,
"Lafiya lau" ya amsa mata gamida kwanciya ya juya mata baya, falo ta fita ta zauna tafara feeding din sadiq,murmushi lamido yayi ya sake kwanciya yana mamakin ikhlas ganin har yanzu bata daina boye mishi abincin sadiq ba shi ya rasa wacce irin kunya gareta.
Sai da ta tabbatar da ya koshi sannan ta kwantar dashi taje ta dora ruwan zafi tazo tafara yi masa wanka,tana fara yi masa wankan yahau kuka,
Kawai sai ganin lamido tayi ya fito daga dakinta da sauri kamar wanda zai tashi sama,
"Wai kukan me wannan yaron yake yine?" Yafada cikin kunar rai domin yanzu a duniya idan akwai abinda ya fi tsana to kukan sadiq ne, yana mutukar kaunar yaron har cikin ranshi, yanda yake jin son yaron aranshi ji yake ko dan cikinshi ba lallai ya soshi haka ba,
"Wanka fa kawai ake yi masa shine yaketa wannan ihun" ikhlas ta bashi amsa cikeda mamakin lamido saboda lamarinshi yanzu mamaki yake bata kwata kwata bashida sauki indai akan sadiq ne,
"Kinga yi masa ahankali" kusa da bahon wankan sadiq din yaje ya tsaya yana kallonsu, shima sadiq din yana ganin lamido ya sake tsaga kuka yana son lamido ya daukeshi,
Ita dai ikhlas abin mamaki yake bata saboda yanda sadiq ya gane lamido,domin ko goyanshi tayi to yana ganin lamido zai fara mutsu mutsu yana kuka ala dole sai yaje wurinshi,
Hanzartawa tayi ta gama yi masa wankan ta sakashi cikin towel ta mikawa lamido shi, ai yana karbarshi taji sadiq yayi shiru ya daina kukan kamar ba shine da yaketa tsaga kuka ba kamar zai kashe musu dodon kunne,ita dai bata san irin soyayyar dake tsakanin lamido da sadiq ba wannan tabarwa Allah domin shine kadai yasan hakan,
Juyawa da sadiq lamido yayi zuwa cikin dakinta ya zauna a bakin gado ya dauki man shafawar sadiq yafara shafa masa yanayi yana yi masa wasa,
"Kaine sadiq? Kasan sunanka?... Saddiquna ko"
Cikin dakin ikhlas ta bisu ta samesu sunata aikin dariya,
"Dauko kayanshi asaka masa" Yace da ita,
Wurin kayan sadiq taje ta dauko masa bakar riga da brown din wando ta dauko safa da hula farare tazo ta karbeshi,
Da kuka tasamu ta shirya shi ta mikawa lamido shi, juyawa tayi zata fita har takai bakin kofa taji muryar lamido yana yi mata magana,
"Ina zakije?"
"Falo" ta bashi amsa,
"Me zakiyi?"
"Zama zanyi" ta mayar masa da amsa,
"To dawo nan ki zauna" yafada bayan ya juya ya rungume sadiq, juyowa tayi ta dawo cikin dakin taja stool din mudubi ta zauna tana kallon Lamido da sadiq sannan tana sauraron shirmen da suke yi sadiq yanata kyakyata dariya,
Bacci sadiq din ya koma dan haka lamido ya kwantar dashi ya juyo yana kallon ikhlas wacce ke zaune ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben dake hannunta wanda sam bata san a inda ta sameshi ba,
"Kinga" ya fadi ahankali, dagowa tayi ta kalleshi amma sai tayi saurin sunkuyar da kanta ta saukar da kwayar idanuwanta kasa, ita ta kasa ganewa lamido domin gaba daya yanzu ya sauya mata ya koma wani kala na daban. Tashi tayi ta matsa inda yake ta zauna a dan nesa dashi,
"Gani" tafadi ahankali,
"Ahakan zan fada miki maganar? Kalli fa yanda kika yi nesa dani sai kace wani abin zan yi miki"
"Kayi hakuri abban sadiq ba haka bane ina sone naje na dora mana breakfast.." Ta bashi amsa wanda har lokacin idanuwanta a kasa suke ta kasa kallonshi,
"Kibar wannan breakfast din kizo kiji abinda zan fada miki"
"Abban sadiq ka fada min ina daga nan ai zanji.."
"Shikenan idan ba zaki zo ba tashi ki tafi"
Ganin kamar ranshi ya dan baci ya sanyata matsawa kusa dashi,
"Kayi hakuri gani..!"
Juyawa yayi ya kalleta har lokacin kanta yana kasa tana wasa da yan yatsunta.
_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoyana masu kaunata, hakika ina kaunarku a duk inda kuke,fatan alkairi gareki momy na (maman A'isha),Allah ya baki kyakkyawar rayuwa cwt momma!._
0 comments:
Post a Comment