Murmushi ya danyi ya saka hannunshi ya dago da fuskarta,
"Kalleni..!" Yafadi ahankali, kasa kallonshi tayi ta lumshe idanuwanta,
"Ki kalleni..." Ya sake fada yana kallon kyakkyawar fuskarta,
Dan yatsanshi yasa akan lips dinta yana zagayawa,
"Kinyi kyau sai dai matsalar baki saka jan baki ba why?"
"Babu komai.." Ta bashi amsa,
"Ki rinka saka jan baki zaki fi kyau"
"To" ta bashi amsa har lokacin ta kasa kallon fuskarshi,
Sake matsawa jikinta yayi nan hancinshi yasoma aika masa da fitinannen kamshin dake tashi daga jikinta,
"Wanne turare kike sakawa?" Ya tambayeta yana mai sake shakar kamshin jikinta,
Shiru tayi bata amsa masa ba saboda ta fuskanci ya fara kokarin wuce gona da iri,
Hannunta ya kamo ya makale cikin nashi,
"Ya kika barni inata magana ni daya ne?" Nan dinma shirun ya sake ji tayi, idonshi ya sauke akan lips dinta wadanda suka kasance jajaye duk kuwa da cewar bata saka jan baki ba,amma duk da haka sunyi mutukar jan hankalinshi,
Babu zato taji yayi hugging dinta yafara kissing din bakinta, sunsunkuyar da kanta ta fara yi,gaba daya ta rasa yadda zata yi saboda kissing dinta yake yi ta kowanne sashe dake kan fuskarta zuwa wuyanta,
"Ki rinka saka jan baki da jagira...,ina son irin wannan kwalliyar ciki harda saka wannan abun na saman ido da kumatu,da irin wannan zane zanen da kuke yi a kafa me baki da red...!" Taji yana rada mata acikin kunnenta,
"Kinji..!" Ya sake rada mata, kai ta daga alamun ehh amma ta kasa magana dalilin yagama saukar mata da kasala,
"Kunyata kike ji ne?"
Ya tambayeta bayan ya tarairayota gaba daya ya dorata ajikinshi,
"Uhm...!?" Ya sake tambayarta,
"Na kasa gane wacce irin kunya Allah ya halicceki da ita bayan kuma naji ana cewa idan mace tayi aure ta haihu to kunyarta na raguwa ba kamar lokacin da tana budurwa ba, hakane?"
Girgiza masa kai tayi alamun a'a,
"To yayane?" Ya tambayeta yana kallon idonta wanda sam taki dagasu ta kalleshi,
"Ai kunya bata karewa..." Tace dashi cikin yar karamar muryarta,
"Sai yaushe? Ya tambayeta yana sinsina wuyanta,
"Abban sadiq...." Tafada gamida rike hannunshi,
"Shhhhhh" yace da ita bayan ya dora dan yatsanshi akan lips dinta,
Dolenta tayi shiru ta rike maganar da tayi niyyar yi ta rabu dashi yaci gaba da juyata son ranshi.
Bude idonta tayi ta kalleshi yana kwance ajikinta ya rungumeta tamkar wanda zai koma cikin cikinta,
"Abban sadiq zanje na hada breakfast.." Ta fadi cikeda jin kunyarshi,
"Yunwa kike jine??" Ya tambayeta,
Girgiza masa kai tayi alamun a'a,
"To ni kinga yunwa nake ji sosai..."
Lumshe idonta tayi domin ta gane abinda yake nufi amma ita kuma bazata bari hakan ta kasance agidan surukai ba,
"Kinji abinda nace?"
"Uhm naji" ta bashi amsa,
"To ya za ayi?" Ya sake tambayarta,
"Babu" ta bashi amsa,
"Haba? Rowa zaki yimin?"
"Abban sadiq rana fa tayi wallahi kalli agogo ka gani...!" Ta fada a shagwabance,
"To idan kina son na iya hakura kidaina yimin wannan shagwabar"
Shiru tayi masa bata sake magana ba, matsawa yayi daga jikinta yaje ya rungume sadiq wanda ke kwance agefe,
Tashi tayi da dan kwalinta a hannunta ta fita tana kokarin tufke gashin kanta wuri daya ta nufi kitchen fuskarta dauke da murmushi,
"Ohh abban sadiq kenan.. Rigima taki karewa?" Ta fada acikin zuciyarta tana murmushi,
"To ni yanzu ma me zan dafa ne?" ta tambayi kanta,
Doya ta fere ta soyata da kwai tayi yar sos mai dauke da kwai da hanta aciki,
Acikin flask ta zuzzuba ta dauka ta kai falo, hijabinta ta saka ta dauki na baffa ta nufi sashensa yana zaune da jaridar weekly trust a hannunshi yana karantawa idonshi sanye da farin medical glass,
Har kasa ta tsugunna ta gaishe da baffa ta tashi zata tafi,
"Ikhlas motar Lamido nagani ne awaje?"
Ta jiyo baffa yana tambayarta, ras gabanta ya fadi,
"Ehhh baffa motarshi ce tun safe ya kawota ya ajiye"
"To idan yazo gidan ki turo min shi"
"To baffa" tafada tareda juyawa tayi gaba gabanta sai faman faduwa yake domin bata son baffa ya gano lamido agidan ya kwana.
Dakinta ta shiga ta tsaya tana kallon lamido wanda ke kwance yana bacci yana rungume da sadiq,
Ba karamin kyau taga yayi mata ba domin har acikin barcin ma sai da beautiful points dinshi suka bayyana,
Agefenshi taje ta zauna tana kallonsa akaro nafarko domin bata taba samun damar karewa siffarshi kalloba,
Tun daga kan dan yatsan shi har zuwa gashin kanshi duk sun tafi da tunaninta, hannunshi kuwa gashine zara zara ajiki,
"Handsome.." Ta fadi ahankali gamida mika hannunta ta shafo gashin hannunshi ahankali ta yadda ba zaiji ba,
Fuskar sadiq ta kalla ta kalli fuskar lamido,
"Allah wasa wasa yaron nan yana kama da abbanshi"
Karar wayar lamido ce ta katse mata zancen zucin da takeyi, mika hannu tayi ta daukota daga kan bed side drewar dinta,
Ras gabanta ya fadi saboda ganin sunan wacce take kiransa,
"Xahar wacece kuma xahar?" Ta tambayi kanta,
A saitin kanshi ta tsaya nan ya bude idonshi daya ya kalleta,
"Menene? Idan ina bacci ba atsayawa akaina"
"Waya ake yi maka" ta fada tareda mika masa wayar,
Screen din wayar ya kalla ganin xahar ce me kiran yasashi yin dan guntun tsaki ya tura wayar karkashin pillow, nan wayar taci gaba da kara domin xahar bata fasa kiranshi ba, ita dai ikhlas tana tsaye tana kallonshi,
Zaune ya tashi ya jawo wayar ya kara ajikin kunnenshi,
"Hello xahar ya akayi ne? Bacci nake fa" yayi magana ahankali,
"Sorry abban sadiq" xahar ta fada daga daya bangaren hakan da ta fadane yasashi murmushi domin sai yaji kamar ikhlas ce tayi maganar saboda itace take kiranshi da wannan sunan,
"Babu damuwa meya faru?" Ya tambayeta yana murmushi,
"Kwana biyune ban ganka ba gashi idanuwana suna bukatar ganin beautiful face dinka" xahar ta bashi amsa cikin shagwaba,
"To zan shigo anjima" yafada yana mai satar kallon ikhlas wacce ke tsaye ta zubawa fuskarshi ido,
"To sai kazo ina nan ina jiranka" ya jiyo xahar tafada cikeda murna,
"Ok bye" yace da ita tareda kashe wayar,
Wani abune ya fara ratsa zuciyar ikhlas wanda bazata iya tantance ko menene ba amma tafi tunanin kishine,
"Kishi kuma? To ni me ya hadani da kishin abban sadiq..?" Ta tambayi kanta acikin zuciyarta,
"Saboda mijinki ne" wata zuciyar ta bata amsa,
"To amma akan me zanyi kishinsa bayan matanshi biyu nice ta uku kuma nasan sauran matan sonsu yake shiyasa ya aure su sabanin ni da ya aureni domin cikawa dan uwanshi burinshi" take taji wani bakin ciki da kunci ya rufeta ya lullube zuciyarta,
Hannunta taji lamido ya kama yana kokarin zaunar da ita akan jikinshi,
"Tunanin me kike yi?" Ya tambayeta yana mai kallon idanuwanta wadanda suke mutukar burgeshi domin kalarsu daban suke dana sauran mata,
Ajiye kwayar idonta tayi akasa tana son tambayarshi wacece wacce ta kirashi awaya kuma me zaije yi awurinta sannan menene matsayinta agareshi? Amma kuma sai taji ta kasa tambayar tashi domin nauyinshi take ji,
Karar wayarshi ne ta sake katse mata tunanin da take yi,
"Hello fadila" taji yafada yana shafar gashin girarta wanda yake kwance lif,
"My fadila ai ina son kiranki rigani kawai kikayi, ya hidimar biki?" Yafadi tamkar me yin rada,
Shiru ikhlas tayi tana jinshi amma aranta ji take kamar ta fashe da kuka amma wata zuciyar hanata take tana cewa "dama tunda kika auri mai mata har biyu ai kin san dole sai kinyi hakuri"
Ji tayi ya kwantar da kanta akan kirjinsa yana shafa fuskarta, shagala tayi ta ma manta da batun wayar da yake yi domin har ya kammala bata sani ba har sai da taji ya sunkuyo da fuskarshi saitin tata yana kallonta,
"Bacci kikayi?" Taji ya tambayeta ahankali,idanuwanta ta bude ta yi saurin kokarin tashi daga jikinsa, hannunta ya rike yana murmushi,
"Ina zaki je?"
"Nagama hada breakfast tun dazu fa"
Mikewa yayi yana rike da hannunta amma ita duk ta gama takura,
Tana baya yana gaba har sukaje falon ta tsugunna tafara zuba mishi abincin,
"Kar ki hada min tea bazan sha ba wannan ya isa" yace da ita yana kallonta,
"To" ta amsa mishi a takaice,
Daukar abincin tayi ta mika mishi ta koma nesa dashi ta zauna, tana kallonshi yafara ci har ya kammala ya mike,
"Bari naje gida nayi wanka"
"To, baffa yace yana nemanka"
"Ok bari naje"
Tana kallonshi ya wuce ya shiga dakinta ya dauko wayoyinshi ya fito ya wuce kallonshi tayi ta yi har ya fice daga falon,
Zama ta koma tayi aranta tana tunanin to Kodai lamido wani auren zai sake yi? Dakyar ta samu ta yakice wannan tunanin daga ranta.
Har yamma tayi shiru lamido bai dawo ba har akayi sallar magrib nan kuma hankalin ikhlas ya tattara ya koma kanshi domin shirun yayi yawa,
Wayarshi ta kira gabanta yanata faduwa,
"Hello" taji ya fada lokacin da ya dauki wayar,
"Abban sadiq mun jika shiru shikuma sadiq yanata nemanka.."
"Gani nan zuwa" yafada gamida tsinke wayar,
Tana zaune a falo tasha ado cikin pink din leshi dinkin fitet tana feeding din sadiq, ba karamin kyau tayi ba amma bata ga shigowarshi ba,
Rankwafawa yayi agabanta yana cewa,
"Saddiqu na abinci ake..." Tun kafin ya karasa ikhlas ta zabura ta janye sadiq ta saki rigarta,
"Me yake damunki ne?" Ya fada yana kallonta,
Shiru tayi tana kallonsa amma ta kasa magana, "ni narasa me kike boyewa bayan nafada miki cewar na dade da ganin abinda kiketa boye min"
Sunkuyar da kanta tayi, "karfa ki manta jiya..."
"Gashi" ta katseshi ta hanyar mika mishi sadiq,
Karbarshi yayi ya juya dashi zai fita fuskarshi dauke da murmushi domin lamarin ikhlas dariya yake sakashi ko bai shirya ba, mikewa ikhlas tayi tabi bayanshi tana rikeda mayafinta a hannu domin yin rakiya amma sai satar kallon lamido take domin yayi mutukar yi mata kyau saboda bakar riga ya saka da blue din wando abinka da farar fata nan yafito fes dashi,lumshe idonta tayi tana jin kamar taje ta rungumeshi "you look soo fine handsome" ta fadi hakan acikin ranta,amma afili sai tace dashi,
"Abban sadiq ina ka shigane baka zo kaci abinci ba alhalin kuma yanzu kai gwauro ne balle nace kaci awurin..."
Katseta yayi ta hanyar cewa,
"Nine gwauron? Me mata uku ai baza a kirashi da gwauro ba domin idan wasu basa nan to wata tana nan danma dai kin hanani angoncewa"
Murmushi tayi tana gyarawa sadiq kwanciyarshi akan cinyarta amma duk yasata taji kunya saboda maganar da ya fada dan haka tayi gaggawar kawar da zancen ta hanyar cewa,
"To meyasa baka zo kaci abincin ba?"
"Na koshine wallahi, tun abincin da kika bani da safe har yanzu jina nake a koshe may be da daddare ma ruwan lipton kawai zan sha"
Murmushi tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi wacce take kyalli tamkar mudubi.
Daukarsu yayi ya fita dasu cikin gari sune har wani hadadden store inda lamido ya fita ya siyo musu kayan makulashe ya hado da ice cream kwallo daya,
"Abban sadiq ya naga ice cream din guda daya? Kai bazaka sha bane?"
"Kece dai ba zaki shaba amma ni zan sha" yabata amsa tareda tashin motar ya fara driving,
"Saboda me kace haka?"
"Saboda bana son sanyi ya harbi sadiq saboda duk abinda kika ci shima ajiki zai samu"
"Tabb" ta fadi gamida budewa ice cream din tafara sha, packing yayi a gefen titi ya dauki sadiq ya mika shi kujerar baya ya kwantar ya dawo mazauninshi ya juya yana kallonta,
"Miko min abuna" ya ce da ita tareda mika mata hannunshi, ganin bata da niyyar bashi ya sashi matsawa jikinta ya matseta, kokawa suka fara yafara kokarin kwatar robar ice cream din amma ikhlas ta boye a bayanta, kujerar da take kai ya kwantar ya koma yaci gaba da kokarin kwacewa ice cream din,
A hannunta ta debo ta shafa masa a fuska tana dariya hakan ya sashi shima debowa ya fara shafe mata fuskarta dashi,
"Abban sadiq kabari wlh akwai sanyi.." Ta fada tana kare fuskarta tana dariya,
"Amma shine ni zaki Shafa min bayan kin san cewa akwai sanyin?"
Matsawa yayi jikinta sosai yasaka harshensa akan fuskarta yafara lashe mata ice cream din da ya shafa mata.
_Gaisuwa mai tarin yawa agareki Sameerat (Dr meerath) naga sakonki nagode kwarai da gaske._
_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/6, 8:31 PM] Itz Ummi Shatu👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
_*62*_
_Yabo da jinjina gareku Hawy nah & my AG tawa ni daya, tareda yan matan Lamido Faty B~B & my lovely namesake Ummi A'isha._
~~~Murmushi tayi ta rike hannunshi tafara kokarin dakatar dashi amma bai barta ba har sai da ya gama lashe ice cream din fuskarta gaba daya,
"Ki goge min abinda kika Shafa min a fuska.." Yafada yana rikeda ita,
Kafada ta make alamun tak'i, idanuwanshi ya rufe ya fara yar kara kadan,
"Washh idona... Samomin ruwa na wanke fuskata.."
Ai ikhlas najin haka ta rude bata san lokacin da ta makalkaleshi ba takai bakinta kan fuskarshi ba ta soma lashe masa ice cream din dake fuskarshi,
Lasar fuskarshi take babu kakkautawa har sai da ta gama lashe ice cream din tsaf,
"Abban sadiq ya fita ko akwai saura?" Ta tambayeshi tana girgiza shi,
Bude idonshi yayi yana kallonta ta cikin hasken street light din data haskesu, tsura mata ido yayi sai kuma ta ga ya kwashe da dariya yana kallonta,
Ta ganeshi sarai cewar wayo yayi mata dama can babu wani abunda ya shiga cikin idonshi,
Juyawa tayi ta soma kokarin sauka daga jikinshi tana cikeda kunya,
"Menene abin kunya kuma bayan kin riga da kin gama lasar min fuska.." Yafada tareda rikota,
"Ga ice cream din kasha" ta mika masa guntun na cikin robar wanda ya rage,
"Sha ki bani" ya mayar mata dashi yana yi mata wani irin shu'umin murmushi,
Girgiza kai tayi ta sake mika mishi, murmushi ya dan saki ya kalli kwayar idanuwanta, hakika yau ya yarda babu abinda yafi rayuwa da masoyi dadi domin shi ya tabbatar da hakan saboda wani irin shauki yau yake ji atare dashi sanadiyyar yana tare da abar sonshi prettynshi, karba robar yayi yana mai cigaba da kallon fuskarta ita kuma duk kunya ta gama cikata,
"Nasha na rage miki?"
"A'a ka shanye"
Hannunshi yasa ya shafi fuskarshi wanda duk dankon ice cream ya gama baibayeta,
"Fuskata danko..."
Kafin ya rufe bakinshi tuni ikhlas ta sake fakar idonshi ta debo ta zuba masa a fuska, nan ta shiga shafe masa fuskarshi dashi,
Kokawa suka shiga yi yana rirrike hannunta amma bata daina shafa masa ba,
"Yau dai ice cream dinnan ahaka zamu shanyeshi ko?"
Yace da ita gamida saka hannunshi ya debo ya yaba mata, "Abban Sadig wallahi zanyi mura.."
"Za muyi dai tunda haka kika zaba"
"Allah dagaske nake"
"To zo in lashe miki, kawo fuskarki..."
Sai da ya lashe ice cream din tsaf sannan ya dago da kanta yana cewa,
"Saura ni..., kinji"
Cike da kunyarshi tasa harshenta ta soma lasar fuskarshi har ta gama idonta arufe,
Sakinta yayi ya tashi ya koma kujerar zamanshi yana murmushin farin ciki,
"Mu koma gida ko? Amma pls rakani mu fara zuwa wani wuri"
Batayi magana ba ta mika hannunta sit din baya ta dauko sadiq wanda keta faman bacci,
Ita kanta ikhlas din yau wani nishadi takeji bata taba sanin haka lamido yake ba sai yau da yafara nuna mata irin salon soyayyarshi,
Titin gidanshi ya dauka dasu ya juyo yana kallonta,
"Banji kince komai ba"
"Game da mefa?" Ta bukata batare data kalleshi ba,
"Bakiga inda na dosa bane? Bakya tsoron tanan nakaiki dakinki",
Murmushi tayi ta dan saci kallonshi kadan,
"Ai nasan ba Zaka yimin haka ba"
Murmushi shi dinma yayi "waye ya fada miki? Tab ai ni banki ace na daukoki kenan ba daga nan sai gidana"
Daidai lokacin suka karasa kofar gidan nashi, awaje yayi packing ya bude motar zai fita,
"Ko zaki rakani?"
"A'a"
"Saboda me? Tsoro kikeyi? Shikenan bari naje na fito"
Kallo ta bishi dashi har ya shige cikin gidan, murmushi ta saki sam bata zaci haka lamido yake da iya soyayyaba sai tsakanin jiya zuwa yau da suka zauna awuri guda, ita da kallon murdadden namiji take yi masa marar sanin yanda soyayya take ashe abin ba haka bane, jinginar da kanta tayi ajikin kujerar motar tana murmushi,
Batare da taga tahowarsa ba kawai sai shigowarsa cikin motar taji, tashin motar yayi ya juya ya nufi gidan Baffa dasu.
Lokacin da suka isa gidan a kafada ta dauki sadiq ta nufi cikin gida shikuma lamido ya wuce masallaci,
Yana fitowa daga salla ya shiga gidan nan ya isketa itama tana sallar ta kwantar da sadiq a gabanta,
Daukar sadiq yayi zuwa kan gado ya dorashi akan ruwan cikinshi ya fara yi masa wasa. Tana idar da sallar ta mike tana ninke abin sallar,
"Zuba min ruwa zanyi wanka, fuskata danko take yi har yanzu" lamido yace da ita yana kallonta,
"Tom" ta bashi amsa ta shige cikin toilet ta hada mishi ruwan ta fito, sadiq ta dauka ta fita dashi falo tabar lamido yana shirin shiga wanka,
Abinda suka shigo dashi na makulashe su ta bude ta fara ci, tana nan zaune lamido ya fito daga shi sai t shirt dark brown da boxer iya cinyarshi,
Akusa da ita ya zauna ya fara cin abinda take ci,
"Sadiq kai ka koshi ko?"
Murmushi tayi "uhm"
"Dama uhm zakice tunda kina barinshi da yunwa"
Murmushi tayi ta mike ta nufi cikin daki, wanka ta shiga tayi wanda tun tana cikin toilet din taji kukan sadiq ya yawaita danma a hannun lamido yake, hanzartawa tayi ta gama ta fito daure da zani daurin kirji da towel karami wanda ta rufe jikinta dashi,
"Ungo shi" lamido ya fada yana dan harararta saboda tabar sadiq yana kuka,
Karbarshi tayi ta zauna tafara shayar dashi bayan ta sakashi acikin towel din ta lullubeshi, tari ya fara yi alamun ya kware ai nan lamido yace bai san zance ba ya matsa kusa da ita ya yaye towel din yana fadin,
"Wallahi ba zaki cutar min da yaro inaji ina gani ba"
Dolenta babu yanda ta iya haka taci gaba da feeding din sadiq lamido yana tsaye yana kallonsu har sai da ya tabbatar da cewar ya koshi sannan ya karbeshi yaje ya haye gado ya kwanta ya rungumeshi,
Gaban mirror taje ta dan gyara fuskarta tasha turare kala kala ta je ta dauko kayan baccinta sai da ta waiwaya ta tabbatar da cewa lamido baya ganinta sannan ta saka kayan wanda suka kasance riga da wando milk colour masu laushi,
Bayanshi taje ta kwanta tana kallon sumar kanshi,
"Abban sadiq idan ka tashi yin kitso na iya" tafada ahankali, sadiq ya kwantar ya juya gareta ya rungumeta,
"Gobe zanje nayi aski ai, yau da naje wurin Baffa yace ya kamata na rage sumar nan"
Murmushi tayi "ai tashen samartaka kake yi shiyasa"
Murmushi yayi ya sake shigewa cikin jikinta "tunda kin iya kitson to yimin naji"
Hannuwanta ta nutsa cikin sumar tashi ta soma shafawa ahankali can taji ya rike hannunta,
"Bari da zafi fa"
"Kai abban sadiq ashe da kai mace ne da anga me kukan kitso" tafada tana murmushi, juyawa yayi da ita ya zame hular kanta,
"Tunda kema kanki a tsefe yake bari inyi miki kitson kiji idan babu zafi"
Idanuwanta ta rufe ta fara sauraron kalar sakon da yake son aika mata dashi.
Sun dade basu runtsa ba har wurin karfe 2:30 nadare, karfe 6 ikhlas ta tashi tayi salla ta tashi lamido, tashi yayi yana hamma,
Toilet ya shiga sai da yayi wanka sannan ya fito da gajeren wando a jikinsa,
Kayansa ya saka yayi salla ya koma ya kwanta.
Ta bayanshi ta je ta kwanta take wani bacci yayi awon gaba da ita nan ta murgina ta rungume lamido acikin baccin batare da ta saniba, juyowa yayi ya sake rungumeta yana mai kallon kyakkyawar fuskarta, tunda ya kura mata ido bai iya daina kallonta ba har sai da ta farka,
Hamma tayi ta bude idonta nan suka hada ido da lamido yana yi mata wani kayataccen murmushi, kunya ce ta kamata saboda ganin yanda ta rungumeshi kamar tana tsoron kar wani ya kwace mata shi,
"Abban sadiq.., ina sadiq yake?" Ta tambayeshi tana zaro idanuwanta,
"Gashi can a bayana, me zaki yi mishi bayan kin zo kin rungume mijinki kin manta dashi, sai yanzu kika tuna dashi?"
Ya fad'i hakan yana kallon kwayar idonta,
Saukar da idonta k'asa tayi cikeda kunya nan tafara kokarin tashi lamido yayi saurin riketa,
"Ina zakije kuma?"
"Wanka zanyi" ta bashi amsa har lokacin idonta yana kasa,
"Wanne irin wanka?" Ya bukata yana lumshe mata idanuwanshi,
"Normal wanka" ta bashi amsa cikeda kunya domin ta gano inda tambayar tashi ta dosa,
"Ni kuwa kinga...." Hannunta takai kan bakinshi da sauri ta rufe masa baki,
"Please abban sadiq ya isa dan Allah.." Tace dashi bayan ta langabar da kanta cikeda kunya,
"Au kar na fada? Bakya son kiji damuwata? Shikenan tunda hakane" yace da ita cikin kalar tausayi,
"Nifa ba haka bane" ta fada a shagwabance,
"To yaya ne fada min...!" Ya fadi hakan yana matsa yan yatsunta,
"Please kabarni naje nayi wankan" ta sake fadi idonta yana kallon kasa,
"Nifa ba wani abu zance ba dama cewa zanyi ni kuwa tun ranar da na fara kwana a cikin dakin nan sai nayi wanka sannan nake yin salla.." Ya fada ahankali kamar me yin rada, kanta ta kawar daga barin da yake ta soma kokarin tashi ba tare da ta bashi amsa ba,
Sakinta yayi ya juya ya rungume sadiq.
Zani ta dauka ta shiga toilet tayi wanka sai da ta leko ta tabbatar da cewa lamido bacci yake sannan ta lallaba ta fito ta shirya agurguje cikin jan material mai laushi, kwalliya ta dan yiwa fuskarta ciki harda saka jan janbaki, turaruka masu dadi ta fesa ta fita zuwa kitchen,
Ruwan zafi kawai ta dafa ta soya kwai ta dauka ta kai falo daidai lokacin lamido ya fito da sadiq a hannunshi,
Bata kalleshi ba ta dauki breakfast din baffa ta tafi ta kai masa ta dawo, karbar sadiq tayi domin yi mishi wanka amma duk motsin da zatayi idon lamido na kanta saboda tayi asalin yi mishi kyau.
_Sakon gaisuwa gareku ummu Nura & maman inteesar, Allah ya raya muku yaranku._
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/6, 8:31 PM] Itz Ummi Shatu👌🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_
*_63_*
_Sakon fatan alkhairi gareki Rukayyat Ahmad (mrs Mansur I yelwa) nagode miki dayawa._
~~~Yana zaune yana kallonta ta gama yiwa sadiq wanka ta shiryashi cikin jar riga da bakin wando ta fesa masa turare ta nufi wurin lamido dashi tana cewa,
"Zakaje ka gaida abba? In kaika wurin abbanka ko..?"
Mikawa lamido shi tayi wanda ke kwance akan doguwar kujera amma da alama ba kalau ba domin taga jikinshi yayi la'asar sannan duk girman idanuwanshi yanzu sun dawo kanana gashi sunyi wata kala,
Karbar sadiq yayi gamida riko hannunta, "yaushe zaki tare ne?"
Kallonshi tayi da mamaki "tarewa kuma? Basu innah sunce sai nan da watanni ukuba?"
Murmushi yayi wanda bai shirya yinshi ba, "gaskiya bazan iyaba, bazan jure ba, kifara shiryawa nanda sati biyu zaki tare"
Dagowa tayi ta kalleshi amma yanayin data ganshi aciki ya tabbatar mata cewar da gaske yake abinda yafa babu alamun wasa,
"Abban sadiq kabari mu kara koda wata dayane saboda kaga sadiq har yanzu.."
"Har yanzu me?" Sassauta muryarsa yayi yasake matse hannunta cikin nashi,
"Kina sone in mutu ko me?? Wallahi ina bukatarki akusa dani, i need you...! Yau dinnan zanje na samu baffa na fada masa, sassauci daya zan iya yi miki shine zan baki nan da sati uku kigama shirinki sai ki tare"
Yana gama fadin haka ya saki hannunta ya mike zaune yana rikeda sadiq a jikinshi,
Tsugunnawa tayi ta hada masa tea ta mika masa sannan ta ajiye masa sauran kayan agabanshi, tashi tayi ta shiga daki tana mamakin lamido saboda ita aganinta tunda yanada mata har guda biyu ai bazai wani damu da batun tarewarta ba,
Dakin tabi ta gyara ta fesa room freshener,tana kokarin fita lamido ya shigo,
"Hada min ruwa zanyi wanka" yace da ita ahankali,
"To" ta fada gamida juyawa ta shiga cikin bathroom din ta zuba mishi ruwan wankan ta fito,.
Falo ta fita ta zauna tahada tea tana sha, tana nan zaune ya fito rikeda waya a makale a kunnenshi yana magana,
"Nan da karfe nawa zaku karaso..? Ok sai kunzo"
Katse wayar yayi ya juyo yana kallon ikhlas wacce itama shi take kallo domin adon da yayi ba karamin kyau yayi mishi ba sannan ya fito dashi mutuka,
"Innah ce tace sun taho sun ma kusa karasowa"
"To Allah ya kawosu lafiya" ta fadi ahankali, juyawa yayi zai fita tayi saurin tsayar dashi,
"Abban sadiq dama akwai maganar da nake son muyi dakai.."
Dawowa yayi ya zauna yana saurarenta,
"Ina jinki"
"Uhm dama akwai wata islamiyya a unguwarmu ta da,marigayi ya karbo min foam din makarantar yace zan fara zuwa idan na gama cikewa to kuma sai ya rasu kafin nakai ga kammala cike foam din.."
"Wacce irice makarantar?" Ya tambayeta,
"Islamiyya ce ta matan aure kullum ake zuwa karfe 2 ataso karfe hudu saboda diploma ce ta Arabic"
"To zaki shiga amma ba yanzu ba sai bayan kin tare tukunna" mikewa yayi ya fita daga falon nan tabi bayanshi da kallo.
Misalin karfe 12 narana innah ta karaso tun daga wannan lokacin kuma ikhlas bata ga lamido ba sai duk taji ta shiga damuwa, karfe 9 tagama shirin bacci ta kwanta amma ga mamakinta sai ta kasa baccin domin kewar mijinta itace ta fara addabarta, juyi tayi ta rungume sadiq tana shakar kamshin turaren da lamido ya bar mata akan pillownta,
Tashi tayi taje ta bude drewar din kayanta ta dauko kayan baccinshi wanda ya kwana dasu adaren jiya,
Rungume kayan tayi tana jin kamar zatayi kuka, lallai rashin masoyi abune mai nauyin gaske domin ita sai yau ta tabbatar da hakan,
Kayan ta saka akan fuskarta tana shakar kamshin da suke fitarwa, ahankali ta mika hannunta kan bedside drewar dinta ta dauko wayarta, sakon text massage take son tura masa amma kuma ta rasa wacce kalma zata yi amfani da ita wurin bayyanar masa da irin yanda tayi rashinsa a wannan daren,
Daurewa tayi ta rubuta _I miss you abban sadiq_ ta tura masa, yana kofar falon gidan yana kokarin shigowa yaga sakon nata, murmushi yayi yasaka kai ya shiga,
Ahankali ya kama kofar dakin nata ya bude ya shiga ya lalubi makunnar wutar dakin ya kunna,
Duk wannan hidimar bata san yanayi ba domin idonta arufe yake ta lullube fuskarta da kayan baccinshi,
"Allah sarki my pretty ashe kema zakiyi missing dina adaren yau kamar yadda nima na tabbatar da zanyi missing dinki" yafadi hakan acikin ranshi,
Ahankali ya karasa kan gadon ta bayanta ya zauna ya dafata ya mika fuskarshi saitin tata, hannunshi yasa ya fara zare kayan baccin nashi wanda ta rufe fuskarta dasu,
Tsorata tayi ta zabura zata mike, cikin sauri ya dakatar da ita,
"Ina zakije? Nine fa" taji muryarshi yana yi mata magana, take ta dawo cikin hayyacinta sai kuma kunya tafara shigarta domin yazo ya kamata tana lullube da kayanshi,
"Meyasa kike da zurfin ciki? Meyasa kike son cutar da kanki? Ni nasan kinada bukatata kamar yadda nake bukatarki dan haka ki yarda ki tare lokaci kusa.."
Shiru tayi ta kasa koda motsi, juyawa yayi da ita zuwa kan jikinshi, "bakice komai ba"
Nan dinma shirun tayi masa, "uhmmm" ya sake fada ahankali, sanin ba zata iya yi masa magana ba saboda tana jin kunya yasashi rabuwa da ita ya dagota zuwa jikinshi ya rungumeta, wani irin sanyi yaji yana ratsa zuciyarshi, bakinta taji ya fara laluba da nashi,
Sun dade cikin wani irin yanayi kafin lamido ya kwantar da ita ya rada mata a kunneta "natafi sai da safe"
Bata iya bashi amsaba har ya tashi ya fita daga cikin dakin bayan ya kashe mata hasken dakin, juyawa tayi ta sake rungume kayan baccinshi tana murmushi da tunaninshi ta samu tayi bacci marar dadi domin sam bata ji dadinshi ba.
Washe gari lokacin da lamido yazo gidan wurin baffa yaje yace masa yana son ikhlas ta tare nanda sati uku, nan innah ta tada fada tace ba yanzu ba domin har yanzu sadiq bai gama yin kwariba dan haka ya bari sai nan da watanni uku kamar yadda akayi yarjejeniya dashi.Tashi yayi ya fita ranshi a bace ko cikin gidan bai shiga ba,
Tun daga ranar ya fara zarya agidan domin kusan kullum sai yaje gidan fiyeda sau hudu wani lokacin kuma har karfe 11 nadare yake kaiwa ganin abin yana neman yayi yawa yasa baffa kiran ikhlas yace tafara duk wani shiri wanda zatayi domin nanda sati uku zata tare agidanta,
Ba karamin murna lamido yayiba nan rawar kai ya karu kamar zaiyi me dan murna wanda har sai da su ihsan da fadila suka ji takaici, bash kuwa tsokanarshi ya shiga yi yana cewa shida yake da mata biyu kyawawa agida duk yanmata meye nashi na zumudi akan bazawara, duka lamido ya kaiwa bash yace,
"Bash baka san wacece ikhlas ba shiyasa, abin sirrine ba zaka ganeba"
Dariya bash yayi "wannan haka yake on top".
Gidan baffa sukaje bash yayi dropping dinshi ya wuce, cikin gidan ya shiga ya iske ikhlas a falo tana goye da sadiq yana bacci anan ta sanar masa cewar tana son zuwa Maiduguri kafin ta tare, da kyar ya yarda ya barta, dan haka ranar talata da safe ta shirya ta tafi amma ba ita ta isa gidaba sai daf da sallar magrib,
Tun da taje aka fara yi mata gyaran jiki irin na amare da sauran gyare gyare wadanda baza arasa ba, lokacin da taga abdalla sai da tayi mamaki domin ba karamin girma yayiba gashi kuma yana yi mata kama da wani Wanda ta kasa gane ko waye,
"Abdallah ka dada zama saurayi" tafadi tana dariya,
"Anty zaki tafi ki bar mana sadiq ko?" Abdallah yafadi yana murmushin da har sai da kumatunsa suka lotsa,ras ikhlas taji gabanta ya harba amma kuma ta gagara tuno wanda abdallah yake yi mata kama dashi,
"A'a abdallah bazan bar muku sadiq ba sai dai kai kazo mu tafi dakai"
Makale kafada yayi yace "ni bazanje ba awurin uncle Hussain zan zauna"
"Kaji ja'iri to dakai zasu tafi" ammi ta fadi tana dariya, sallamar yaya Hussain ce ta katse musu hirarsu,
Zama sukayi suka gaisa anan yake sanarwa da ikhlas cewa yabawa farida matarsa kudi wanda suka hada shida hassan gobe suje kasuwa itada farida su siyo duk abubuwan da take bukata domin tsofaffin kayanta kwasosu za ayi akawowa ammi itama tasaka adakinta, godiya sosai ikhlas tayi washe gari sukaje kasuwa itada farida nan suka fara jidar kaya masu tsada da kyau wanda ita dai ikhlas tsayawa kawai tayi tana kallon farida domin duk abinda ta nuna tana so daukoshi farida take ta biya kudin, bata san adadin yawan kudin da su Hussain suka bayar ba,
Sai yamma lis suka koma gida lokacin sun kammala siyayyar sun siyo dukkan abinda ya kamata, cigaba da gyaran jikin ikhlas akayi har ya rage saura kwana uku ta tafi yola wanda aranar da ta koma awashegarin ranar zata tare,
"Ina son kwalliya ciki harda irin wannan zanen da kuke yi a hannu da kafa.." Maganar lamido ce ta dawo cikin kunnuwanta hakan ta sata zuwa aka yaryada mata jan kunshi mai hadida baki wanda ya kama atafin hannunta da tafin kafarta radau,
Turaren wuta dana jiki da humra masu kamshin gaske aka harhada mata bayaga su kwalacca da sauran kayan kamshi,batun lamido kuwa tun ranar data bar yola yake faman kiranta awaya, kowanne lokaci cikin yi mata waya yake har ranar da zata dawo.
Tun asuba suka fita itada hajiya da matan yayunta ga kuma motar kayanta wanda yayunta suka sake mata, suna zuwa gidanta suka wuce dasu da motar kayanta bayan sun sauketa a gidan baffa, bata dade da sauka ba ta fita ta tafi saloon lokacin data dawo ta samu ni'iman elmustapha tazo gidan tana jiranta, yan kafi kuwa sai dare suka dawo bayan sun shirya mata dakinta da falonta tsaf, kitchen ne dai guda dayane ahade wanda nasune su duka ukun amma kowacce ta shirya kayanta agefe daya,sannan tunda sukaje gidan gaisuwa ce kadai ta hadasu dasu fadila da ihsan daga wannan kowacce shigewa dakinta tayi taki fitowa har suka gama jeren,
Adaren sukaje tsohon gidanta suka tattaro mata duk wani abu wanda zata bukata sauran kuma aka loda a mota domin tafiya dashi maiduguri,lokacin da suka je gidan saida ikhlas tayi kuka saboda tunowa da marigayi da tayi,
Sai wurin karfe 12 sannan suka samu damar yin shirin bacci,
"Kai mutuniyata kinga dakinki kuwa?? Komai ya hadu wallahi sannan ke din kanki ma kinyi kyau sosai, wallahi ina jin idan lamido ya ganki zaucewa zaiyi" farida tace da ikhlas tana dariya,
"Ai ni idanma akwai abinda yafi zaucewa zanso lamido yayi indai akaina ne" ikhlas ta fada acikin zuciyarta, amma afili cewa tayi,
"Dagaske? Bani labarin gidan dan Allah"
Kwanciya farida tayi tana cewa "kibari gobe idan kinje zaki gani ni yanzu ki kyaleni bacci zanyi domin nagaji"
Kwanciyar itama ikhlas tayi fuskarta dauke fa murmushi tana tunanin gobe iyanzu tasan tana tare da lamido a kusa da ita.
_Gaisuwa mai tarin yawa agareki Fiddausi Zurmi,kwana biyu kin b'ace idan sakona ya riskeki ina gaisuwa._
*_Ummi A'isha_*👌🏻
*RUWAN KASHE GOBARA..!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
*_64_*
http://aishaummi.blogspot.com
~~~ Daren ranar daga Lamido har ikhlas baccinsu ragagge ne domin doki,
Lamido kam juyi yake tayi ya kasa bacci har ihsan ta fahimta dan haka ta mike daga kwancen da take,
"On top wai meye haka?" Ta fadi ranta abace,
"Mefa?" Ya tambayeta yana basarwa,hakan da yayi ya sake kular da ita,
"Kazo ka kwanta sai wani juyi kake kana yin tsaki kamar dole nayi maka zuwa dakin nawa" ta fadi a kule,
"Yi hakuri my ihsan.. Na kasa yin baccinne shiyasa"
Hannunta ya kamo ya kwantar da ita akusa dashi ya fara lallashinta.
Washe garin ranar tunda gari ya waye ikhlas tafara harhada dukkanin kayayyakinta wuri guda,
"Kidai bi ahankali kar zumudi yasa ki mance kayanki masu amfani" Farida tace da ikhlas cikin tsokana,
"Zumudin me? Kin jita" ikhlas ta mayar mata da amsa tana mai kokarin rufe akwatinta,
"Ahaf kuma dai" farida ta fada tana dariya,
Sallamar ni'ima ce ta katse musu hirar da sukeyi, nan dakin ya hargitse da hirarsu,kaya sosai ni'ima ta kawowa ikhlas ciki harda cake cikin karamin bokiti da meat pie da pepe chicken wanda tace shine gudun mowarta, wunin ranar abin gwanin ban sha'awa domin ikhlas tana cikeda farin ciki da nishadi.
Da misalin karfe 8:30 aka dunguma domin raka ikhlas dakin mijinta, mota dayace bash ya tuko yazo daukarsu kasancewar babu yan rakiyar da yawa domin daga Farida sai hajiya kakar ikhlas sai ni'ima matar barrister elmustapha,
Lokacin da suka isa gidan tsit kakeji baka jin motsin komai in banda karar na'urorin sanyaya daki wadanda suke amfani da wutar lantarki,
Suna daf da shiga falon gidanne suka yi kicibus da ihsan tareda fadila sun rako kawayensu wanda da alama tafiya zasuyi,
"Barkanku da zuwa" fadila da ihsan suka fada atare tare da yin gaba,
"Yawwa dai sannunmu" Farida ta fada tana rikeda sadiq a kafadarta wanda ke faman yin bacci,
Da addu'a a bakin ikhlas ta saka kafarta ta dama lokacin da zasu shiga falonta, har cikin dakinta suka shigar da ita ta zauna abakin gado sannan Farida ta karasa ta kwantar da sadiq agefe,
Zama sukayi sunata yaba irin kyawun da dakin nata yayi gashi komai ya tsaru iya tsaruwa,
"Ku tashi mu tafi ba dogon zama zamu yi ba" ni'ima tace dasu,
Hannun ni'ima ikhlas ta rike "haba anty ni'ima daga zuwa?"
"Kin jita kamar gaske, alla alla take yifa mu tafi" Farida tace tana dariya,
"Kuna inane? Ku fito mu tafi mana" suka jiyo muryar hajiya daga falo,
Mikewa suka yi suka fita suna cewa "to amarya Allah yabada zaman lafiya"
Shiru ikhlas tayi tafara bin dakin da kallo hakika komai yayi,tashi tayi ta leka falon wanda yasha kaya masu kyau kalar blue da baki, murmushi tayi tana jin son yan uwanta da kaunarsu yana ratsata domin sune suka yi mata wannan hidimar wacce bazata taba iya biyansu ba sai dai tayita yi musu addu'a,
Kasancewar wunin ranar bata ci abinci ba yasa taji cikinta yafara kugi hakan ya sanyata tashi taje ta bude snacks din da ni'ima ta kawo mata, meat pie ta debo da pepe chicken tazo ta zauna ta fara ci tanayi tana tunanin ina lamido ya shiga kuwa domin rabonta dashi tun kafin ta tafi yola,
Tashi tayi ta isa gaban fridge ta buda, cike ta ganshi da kayan jika makoshi kala kala,robar juice ta dauko guda daya tazo ta zauna ta bude ta fara sha,
Karar bude kofa taji hakan ya sanyata waiwaya, lamido ta gani sanye cikin yellow din t shirt mai layi layin baki ajiki da bakin wando, yayi kyau sosai yasha aski, fuskarshi dauke da murmushi amma daga gani daga bacci yatashi, bakinshi dauke da sallama ya shiga ikhlas ta amsa mashi tana murmushi.
Akusa da ita ya zauna yana murmushi,
"Bakya nemana ko? Tun rana kaina yake ciwo nasha magani na kwanta sai daf da magrib natashi na rama sallolin da ake bina nasake kwanciya sai yanzu na tashi nayi sallar isha nayi wanka na fito"
Kallonshi tayi cikeda kulawa, "ayya sannu ai ban saniba"
"Amma da kika jini shiru meyasa ba zaki nemeni kiji ba?" Ya tambayeta yana lumshe mata manyan idanunshi,
"Kayi hakuri.."
Hannu ya saka cikin filet din da take cin meat pie da pepe chicken din ya dauki daya ya fara ci,
"Nima yunwa nake ji saboda rabona da abinci tun rana"
Dagowa tayi ta kalleshi, "tsaya to na karo maka"
Daukar filet din tayi ta nufi cikin bedroom dinta binta da kallo yayi tayi kyau sosai tana sanye cikin material baki mai santsi dinkin riga da skirt gaba daya ya bayyanar da kyakkyawar surarta gashi tasha kunshi ja da baki bayada kwalliyar da fuskarta tasha irin wacce ake yiwa amare,
Bai fargaba yaji har ta dawo ta ajiye masa filet din akan dan karamin stool din dake ajiye agabanshi,
"Abban sadiq gashi" tace dashi tareda nufar wurin Adana kayan sanyi nan ta dauko masa ruwa da juice ta dawo,
"Wannan naman yayi dadi.." Ya fada yana kallonta,
"Abban sadiq banda santi dai" tace dashi tana murmushi,
"Babu wani santi dagaske yayi dadi ki ajiye min gobe dashi zanyi breakfast"
"To shikenan zan ajiye maka"
Tana nan zaune har ya kammala ya fara bin falon nata da kallo domin ba karamin tsaruwa yayiba gashi sai wani kamshine mai dadi yake tashi,
"Muje naga cikin bedroom din naki" yafada hadida kama hannunta ta mike tsaye suka tasamma cikin dakin, agefen gadonta ya zauna ya kwanta yana kallonta,
"Dakin naki yayi kyau sosai.."
"Nagode" ta amsa masa tana wasa da yan yatsun hannunta,
"Dauko sadiq mu tafi dakina" ya fada bayan ya tashi zaune, make kafada tayi alamun a'a,
"Ba zamuje dakin nawaba?" Ya tambayeta, gyada kai tayi alamun ehh,
"Anan kikeso mu kwana?" Ya sake tambayarta, daga masa kai ta sakeyi,
"Yau me ya samu bakin naki ne? Kin dai san cewar yunwa nakeji sosai ko?"
Kanta ta sunkuyar kasa tana murmushi,
"To zo naga meya samu bakin naki yau yaki magana" ya mike tsaye ya isa gareta ya kamo hannunta zuwa bakin gadon,zaunar da ita yayi a jikinshi yana shakar daddadan kamshin da jikinta yake fitarwa,
"Ikhy baby.." Ya fada ahanakali yana rikeda hannunta yana kallon zanen kunshin da aka yi mata,
"Ban san dunbin farin cikin da nake cikiba ayau sai dai kawai zaki fahimci hakan da kanki, ki tashi kiyi alwala muyi salla ko?"
Ba tare data tayi magana ba tafara shirin tashi tsaye, mikar da ita yayi ya kama hannunta zuwa cikin bathroom din wanda har ciki ya bita ya kunna fanfo yayi mata alwalar ya rikota akan kafadarshi suka dawo cikin dakin,
Sallah suka gabatar raka'a biyu tareda addu'o'in samun zaman lafiya,
Kallonta lamido yayi da murmushi akan kumatunshi "wai me kika bawa sadiq ne yaketa wannan baccin?"
"Ni babu abinda na bashi" ta fada kanta na kasa,
"Ok yaro ya gane yau babanshi angone shiyasa.."
Shiru tayi masa tana murmushi, tashi yayi yaje ya janyo dan karamin gadon sadiq ya daukeshi ya sakashi aciki ya koma gaban mirror ya tsaya yafara shafe jikinshi da dadadan turaruka masu kamshin gaske, gaban gadon ya koma ya kwanta yana kallon ikhlas, da hannu ya fara yafitota dakyar ta iya tashi ta isa gareshi saboda kunya.
Daren ranar daga shi har ita sunyi rayuwa mai dadi wanda basu taba tsintar Kansu aciki ba sai a lokacin, sai dai abinda ya daurewa ikhlas kai shine kukan da suka dade sunayi itada lamido Wanda bata san dalilin faruwar hakan ba,
Har gari ya waye lamido na dakinta duk inda ta juya yana rungume da ita wani irin zazzafan sonta ne yaji yana dada shigarsa, tare suka yi wanka suka yi salla suka koma suka kwanta.
Wani zazzabi ne ya fara rufe ikhlas nan jikinta ya fara zafi gashi sadiq ya tashi ya fara kuka, daukoshi lamido yayi yazo inda take kwance ta lulluba da bargo,
"Pretty dan daure ki bashi yasha sai na kaishi gidan innah tunda baki da lafiya" ya fadi cikin tausayawa,
Daurewa tayi ta tashi ta amsheshi ta shayar dashi har sai da ya koshi, nan kuma yafara bangalawa Lamido dariya yana son yayi masa wasa,
Hannu lamido yasa ya taba jikinta, nan yajishi zafi zau,
"Bari na kaishi nadawo"
Bata iya bashi amsaba sai daga masa kai da tayi, fita yayi da sadiq a hannunshi yaje bedroom dinshi ya dauko key din mota ya fita,
Lokacin da yaje gidan innah samunta yayi a falo tana shisshirya wasu litattafai na baffa acikin jaka,
Mika mata sadiq yayi bayan sun gaisa "innah gashi mamansa ce bata da lafiya"
Karbarshi innah tayi nan taji shima lamidon jikinshi zafi zau alamun zazzabin "lamido, kaima ai zazzabin kake yi ga jikinka nan naji da zafi..." Inna tace dashi tana sake tabashi,
"Ehh wlh innah nima zazzabin nake ji"
"To Allah ya sawwake, ka gaishe da mutanen gidan"
"Zasu ji innah"
Ko wurin baffa bai shigaba ya fice daga gidan jikinshi rau dan zafi, yayi niyyar yaje chemist ya siyo musu magani amma yaji bazai iyaba saboda zazzabin jikinshi karuwa yake wanda dakyar ma yake tukin.
A galabaice ya karasa gida yafita daga cikin motar yana rungume da hannayenshi a kirjinshi alamun yana jin sanyi, baiji motsin kowa ba da alama daga ihsan har fadila babu wacce ta fito,
Bedroom din ikhlas ya shiga nan ya sameta akundundune cikin bargo kamar yadda ya tafi ya barta, bayanta yaje ya kwanta ya rungumeta bayan ya lulluba da bargon,
Dama zazzabin kamar jira yake ya kwanta take ya rufeshi gaba daya ruf, kuka lamido ya fara da surutai saboda zafin zazzabin (hmm masu karatu kun san dai lamido da surutu marar kan gado idan yana zazzabi),
Rungume ikhlas yayi ya fara yi mata surutai "pretty wallahi ina sonki, ke kadaice macen da zuciyata take so, nafara sonki tun kina mahaukaciya lokacin dana ganki a bakin plaza, bazan iya controlling din kaina bane lokacin shiyasa har nayi miki fyade, tun daga lokacin nashiga halin damuwa har dawowa nayi adaren bayan na tafi amma ban gankiba, pretty nasha wahala akan sonki, sonki ya wahalar dani ya azabtar dani,tun daga ranar da nayi miki fyade ban sake samun farin ciki ba sai daren jiya, nasha bakin ciki da kunci kala kala adalilin rashinki musamman ma da na rasaki, kwatsam ban tashi ganinki ba sai a matsayin matar yayana wallahi pretty ji nayi kamar na mutu nabar duniya saboda tashin hankali domin rayuwata duk nagama tsarata ne tare dake" tunda yafara maganar yake kuka har kawo iyanzu.
Kumatunta ya kamo da hannuwanshi wadanda suka dau zafi ga kuma hawaye yana bin kumatunshi, "Dan Allah pretty karki sake rabuwa dani, kar ki sake guje min, idan kika gujewa rayuwata wallahi mutuwa zanyi saboda i can't do without you, you are the part and parcels of my life...".
_Gaisuwa gareki yayarmu Anty Hajiya, badan kar nayi karya ba da sai nace kin fi kowa son ruwan kashe gobara.. Domin har mafarkinshi kike...!_
_Masoya ku rinka yi mana uzuri kudaina saurin fusata da yin fushi alokacin da kuka ga kun yi mana magana bamu amsaku ba,kun san dan'Adam ajizine sannan kar mu manta cewar annabi Muhammad (S. A. W) yayi hani da saurin fushi, muna sonku acikin ko wanne yanayi domin da bazarku muke rawa._
*_Ummi A'isha_*👌🏻
*RUWAN KASHE GOBARA..!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
_*65*_
http://aishaummi.blogspot.com
_Fatan alkairi gareku yan group din anty ybk (musha karatu) ko shakka babu kunfi kowanne group son ruwan kashe gobara..wannan shafin nakune musamman._
~~~Gaba d'aya ikhlas jin maganganun da Lamido yake yi mata take kamar acikin mafarki,maganar da yaci gaba dayi ce ta katse mata tunaninta,
"Pretty wannan zoben dake hannunki zobe nane, nine nan na sanya miki shi saboda nasan zan sake haduwa dake har mu rayu tare a matsayin ma'aurata mata da miji, i love you pretty... I love you,... I love you..!"
Duk da cewar jikinta babu karfi amma hakan bai hanata zabura ta mike zaune ba, hankadeshi tayi wanda saura k'iris yakai k'asa,
Jikinshi zafi zau ya d'ago yana kallonta "pretty kar kiyi min haka, wallahi zan iya shiga mummunan hali muddin kika juya min baya.."
"Sai dai ka mutu dan indai nice to nagama zaman aure dakai..."
Lamido najin haka bai san lokacin da ya zabura ya mik'e ba,
"Idan mun rabu muyi yaya da yaronmu? Haba pretty kiyi nazar..."
Hannu ta d'aga ta katseshi, "wanne yaron? Wallahi ko cikine ajikina sai na b'arar dashi ballantana yaron da ya fito duniya..."
"Cikin nawa zaki b'arar pretty?" Ya tambayeta cikin tashin hankali,
"Kwarai kuwa dan bazan haihu dakai ba balle har wata rana azo ana yiwa d'ana gorin ubanshi mazinacine ba..."
Ras ras lamido yaji gabanshi ya harba tab lallai indai hakane akwai aiki ja agabanshi, kafin ya farga har ikhlas ta dira daga kan gadon ta nufi wurinda kayan sawarta suke nan ta bude drewar din tafara kwaso kayan tana watsa su kan gado, cikin sauri lamido ya bi bayanta ya fara kokarin rirriketa,
"Pretty dan Allah kiyi hakuri amma kar ki tafi ki barni, kiyi min duk wani hukunci da kika ga ya dace dani amma karki tafi ki barni..."
"Akan me zanci gaba da zama da mazinaci irinka wanda ya kasa hadiye kwalamarsa ya afkawa mahaukaciya, ahaka kake son in zauna dakai? Kana bin yaran mutane kana lalatawa ciki harda mahaukata, wallahi da nasan haka halinka yake da ban yarda an daura mana aure da kaiba, macuci azzalumi, marar tausayi marar tsoron Allah, mazinaci kawai.." Duk wadannan maganganun tana yinsu ne yayinda hawaye yake bin kumatunta, shima lamidon hakan take domin shima hawayen yake sonyi sai dai a wannan karon yayi juriyar hanasu zubowa fuskarshi sai dai acikin zuciyarsa suke kwarara, amma idanuwanshi sun hadu sun kad'a sunyi jajajur,
"Naji koma dame zaki kirani ki kirani dashi sai dai karki manta ita kaddara ba a tab'a iya guje mata,abinda ya faru tsakanina dake kaddarace rubutacciya.."
Toshe kunnuwanta tayi da hannuwanta guda biyu "kaddara? Kaddara fa kace? Kar ka sake yimin magana saboda yanzu bana son jin maganarka ka fice min daga cikin daki, ban son ganinka, i hate you...!"
Arazane ya nufeta yana zuwa tafara ja da baya "karka tabani, karka kuskura ka tabani da k'azamin jikinka, wallahi da ace nasan kai mazinacine da ban bari kazamin jikinka ya shafi nawaba.."
Duk da wad'annan mugayen kalaman da take jifanshi dashi bai hanashi dosarta ba, ja da baya take har ta isa gaban mirror,
"Wallahi indai baka rabu daniba sai na kashe ka ko na kashe kaina domin na tsaneka.."
Kwalbar turare ta dauko ta bugi bango da ita take kwalbar ta fashe turaren ciki ya tsiyaye,
"Da inci gaba da zama da kai gara na kashe kaina na mutu.."
"Ikhlass.. Dan Allah kar kiyi min haka"
Inda take ya karasa ya riketa yana kokarin kwace kwalbar, yana jin kwalbar ta yanke shi a hannu amma haka ya daure yaci gaba da kokarin kwacewa saboda ya lura ikhlas zata iya aikata abinda tace gashi da alamar bata cikin hankalinta yanzu,
Kokawa suke sosai, wata irin fusga tayi take ta yankeshi a goshinsa kafin wani lokaci har jini ya b'ata masa fuska, amma bai barta ba har sai da ya kwace kwalbar,
"Ka fita min daga cikin daki mugu kawai azzalumi macuci, mazinaci.."
Ba tare da ya sake bi ta kanta ba yasa kai ya fita, key din kofar falon ya zare ya rufeta ta ciki ya tafi da key din domin baya son ta tafi,ko fadanne gara ta zauna suyi tayi har ranar da zata hakura amma kalmar data fada cewar ta tsaneshi tafi komai razanashi domin baya son ta tsaneshi,
Bedroom dinshi ya shiga ya watsa kwalbar acikin dustbin ya shiga toilet ya wanke fuskarshi, ga hannunshi duk ya yanyanke,
Kan gado yaje ya kwanta take kuma maganganun da ikhlas ta fada masa suka fara dawowa cikin kwakwalwarshi wanda yake jinsu tamkar saukar aradu,
Wani zazzafan zazzabine ya sake rufeshi mai hadeda ciwon kai, nan yafara kukan zuci wanda yafi na fili ciwo amma ga hawaye nan suna faman sintiri akan kumatunsa.
A b'angaren ikhlash kuwa lokacin da lamido ya fita ya barta wani kuka mai ratsa zuciya ta fashe dashi ta fad'a kan gado ta kwanta taci gaba da kukan da takeyi amma har cikin ranta wani irin tsanar lamido taji yana shigarta,sannan ga wani zazzabi mai zafi da yake saukar mata ajikinta,
Zanin gadonta ta damke da hannuwanta tana kukan bakin ciki, take abubuwan da suka faru acikin rayuwarta suka fara dawo mata cikin kwanyarta tiryan tiryan, tun daga kan korar karen da abbanta yayi mata har zuwa kan auranta da lamido, haba sai yanzu ta gano tsantsar kamar da abdallah yake yi da lamido wanda abaya ta kasa fahimtar hakan sai yanzu,
"Bazan zauna dakai ba saboda na tsaneka, na tsaneka lamido, babu abinda zai Sa naci gaba da rayuwa da mutumin da bai dauki sab'on Allah a matsayin komai ba, Allah ne kadai yasan yawan matan da kayiwa fyade bazan zauna dakai ba bare abinda kayiwa yaran wasu nima ayiwa yarana.., Bazan taba yafe maka ba" tafada bayan ta sake fashewa da kuka,
Kamar wacce aka tsikara sai kuma ta mike zunbur ta dauki hijabinta ta nufi kofar fita,tana zuwa taji kofar a kulle k'yam ko ba afad'a mata ba tasan lamido ne ya rufeta aciki saboda kar ta tafi,
Bugun k'ofar ta fara yi da hannunta kamar zata b'alle ta gashi k'ofar k'ark'arfa ce ba irin wacce zata budu a dad'in rai bace, dukan k'ofar taci gaba dayi da hannunta wanda take jin zafin had'uwar kofar da hannunta yana shigarta tamkar hannunta zai cire dan rad'ad'i amma hakan baisa ta hak'ura ba sai ma k'ara k'aimi da tayi wurin cigaba da bugun,
Lamido yana kwance yana jinta amma ya kasa tashi domin zazzabine ajikinsa sosai ga wata hajijiya da yaji tana d'aukarshi, jin bugun k'ofar da ikhlas take yi yak'i k'arewa gashi yana tsoron kar taje taji ciwo a hannunta garin bugun k'ofar hakan yasashi tashi da k'yar ya d'auki key din bedroom din nata ya fita, yana tafe yana had'a hanya kamar wanda yasha abin maye,
Bud'e k'ofar yayi take ta yunk'uro zata fito nan yayi saurin tare bakin k'ofar ta yanda bazata iya wucewa ba,
Ciki ta koma bayan ta sake fashewa da wani sabon kukan, rufe k'ofar yayi ya bita cikin dakin, akan gadonta ya sameta a kwance tana gunjin kuka, ta bayanta ya k'arasa ya zauna ya kai hannunshi da niyyar kamo hannunta domin jikinshi ya bashi taji ciwo ajikin hannun saboda gashi nan har ya kumbure,
Cikeda masifa fuskarta dauke da bala'i ta tashi zaune, "karka kuskura ka tab'ani da k'azamin hannunka wanda kaje ka gama yawon bin mata dashi..." Tafad'i hakan idonta cikin nashi domin yanzu kunyar dake tsakaninsu tuni ta saka k'afa tayi fatali da ita,
Idonshi jajur a k'ank'ance yake kallonta gaba d'aya ma ya rasa abinda zai ce mata amma kuma zuciyarsa jinta yake yi kamar ana had'a mishi wuta aciki dan zafi,
"Ikhlas naji nayarda da duk abinda zaki kirani dashi,amma dan Allah kar ki nemi illata kanki idan kika yi haka to tamkar kina neman illata rayuwata ne.." Yace da ita yayinda hawaye ke sauka akan kumatunshi,
"Sai me dan na illata rayuwarka? Ai ayanda nake jin zuciyata ahalin yanzu zan iya kasheka domin a duniya idan akwai wanda nafi tsana to kaine.."
Kallon k'wayar idonta kawai yake yi yana hadiyar bakin cikin da take kunsa masa,bai sake magana ba amma duk da haka saida ya mik'e yaje inda take, zabura tayi yayi saurin saka k'afarshi tayi tutub'e ta fad'a jikinshi,
Wani ihu ta saka domin ita yanzu bata son jikinta yana shafar nashi, matseta yayi gam gam ajikinshi ya kamo hannuwanta yana dubawa domin shi ayanzu nema yake jin wani irin zazzafan sonta yana ratsashi domin daren jiya darene wanda bashida na biyunshi acikin rayuwarshi,
Ganin hannuwan nata yayi duka biyun sun kumbura sunyi ja, kallo yabi hannun nata dashi hawaye yana zuba daga idonshi domin yau ga abinda yake so amma kuma babu damar nishad'antuwa dashi saboda ba acikin kwanciyar hankali yake ba,
"Ka sakeni ka daina yunk'urin tab'ani na fad'a maka na tsaneka na tsaneka.."
Muryar ikhlas ta katse masa tunaninshi, cikin sauri ya saketa ya mik'e, yana kallonta ta fad'a kan gado taci gaba da rusar kuka Wanda jin kukan yake yi har cikin zuciyarshi amma kuma zuciyarshi ta fara bashi shawarar indai sakin ikhlas shine farin cikin rayuwarta da burinta to ya kamata ya saketa domin ta samu farin cikin saboda bashida burin da ya wuce na yaganta cikin farin ciki.
_Gaisuwa mai tarin yawa agareku, soo fine, hassanatou, mom salma, ummi sadauki, zainab Abdul, maman humy,ummsaheed, ummu Aliyu,maman fahad & Rashidat makama, nagode da kaunarku agareni._
_*Ummi Shatu*_👌🏻
*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
aishaummi.blogspot.com
_*66*_
~~~Ba tare da ya jiyo ya kalleta ba ya juya zai fita, cikin azama ikhlas tayi kukan kura ta bi bayanshi tareda kamoshi ta baya,
"Babu inda zakaje har sai ka rubuta min takardar sakina ka bani saboda na fada maka bazan zauna dakai ba, i hate you..."
Ayanda yake tsaye ahaka ya ci gaba da tsayuwar ba tareda ya juyo ba amma acikin zuciyarshi tunani yake yi wannan wacce irin masifa ce take kokarin kunno kai a tsakaninshi da ikhlas? Bayan sai da yagama shan wahala akanta yanzu kuma lokaci yayi wanda yake ganin zai samu farin ciki da daddad'ar rayuwa sai kawai fitina ta b'ullo musu?
Dafe goshinshi yayi da hannunshi "ohhh God..!" Ya fad'i ahankali,
"Ka sakeni nace maka,wallahi idan baka sakeni ba zan iya illata ka na illata kaina.." Muryar ikhlas ta katse masa tunaninshi,
Girgiza shi tafara yi da karfinta, "ka sakeni nace.."
Juyawa yayi ya b'anb'are hannunta daga jikinshi ya juya yayi saurin ficewa daga cikin d'akin,
Da gudu ta taso amma kafin tazo tuni yayi nasarar rufe k'ofar dakin, bedroom dinshi ya koma yaje ya d'auko key din motarshi ya fice daga gidan,
Wani chemist yaje aka yi masa dressing din ciwon da yaji,ya siyo maganin zazzab'i dana ciwon kai sannan ya siyowa ikhlas maganin ciwon da taji garin bugun k'ofa,
Kallo daya zaka yi masa ka gane yayi bankwana da kwanciyar hankali, yana driving yana goge kwallar dake taruwa acikin idonshi da haka ya k'arasa gidan, lokacin da yaje sai da yayi ta maza sannan ya samu nasarar tsayar da hawayen idonshi, jiki babu k'wari ya fito daga cikin motar ya nufi cikin gidan, bedroom din ihsan ya lek'a babu kowa aciki gashi iya falonne kawai a bud'e duk yadda aka yi ta tafi makaranta, d'akin fadila ya zarce itama bata nan anan ya tabbatar da cewar itama makarantar ta tafi domin duk dakunansu a kulle suke,
D'akinshi yaje ya zauna ya dafe kansa yayi tagumi domin gaba d'aya duniyar tayi masa zafi ji yake yi kamar ya barta ya huta,
"Kodai na saki yarinyar nanne kamar yadda ta buk'ata??" Ya tambayi zuciyarshi,
"Amma kuwa da ka zama ragon namiji indai ka saketa akan wannan d'an k'aramin haukan da tayi,kenan ma ba sonta kake yi idan har ka iya sakinta, ka manta wahalar da kasha a dalilin rashinta? Ita fa dama soyayya ta k'unshi farin ciki da sab'anin haka amma indai aka jajurce to daga k'arshe za ayi achieving abunda ake so" wata zuciyar ta bashi amsa, mikewa yayi cike da k'warin gwiwa domin yanzu yaji ajikinsa zai iya jure kowacce irin bak'ar magana wacce ikhlas zata fad'a masa,sannan zai iya zama da ita ko acikin wanne irin haline.
D'akin nata ya bud'e ya shiga, tana zaune dab'as a k'asa ta d'ora kanta akan gado har lokacin kuka take yi ga hannuwanta sun yi suntum saboda tsabar kumburin da suka yi,
"Pretty..." Ya kira sunanta ahankali bayan ya tsugunna agabanta,
Ko kallonshi bata yiba taci gaba da kukan da takeyi,
"Kiyi hakuri ki daina kukan nan, bari na kawo miki abinci kici ga magani nan sai kisha" ya karashe maganar kamar wanda yake koyonta,
Nan dinma shiru tayi masa, tashi yayi ya fita zuwa kitchen anan kuma ya tsaya yayi sororo domin bai san ta inda zai faraba kasancewar babu abinda ya iya dafawa abu daya yasan zai iya shine soya kwai da dafa ruwan zafi domin wannan dama ko lokacin da yana school yana yi,
Gas ya kunna ya fasa kwai guda hud'u ya yanka albasa harda tumatur yasa maggi da curry ya soya, saukewa yayi ya tafasa ruwa kad'an ya zuba a cup yasa lipton da sauran kayan had'a tea ya kinkima ya nufi d'akin ikhlas,
Tana nan a inda ya barta amma yanzu ta daina kukan saboda wani irin zazzabi da ya saukar mata ga ciwon kai kamar kanta zai rabe gida biyu dan haka dolenta ta hakura tayi shiru, shi kanshi lamido shima zazzabinne ajikinshi kawai daurewa yake yi,
Agabanta ya ajiye kayan ya daga kai yana kallonta, "ga abinci na kawo miki, dan Allah ki daure kici.."
Tana jinshi bata kulashi ba, ledar maganin ya bude ya ciro maganin ciwon hannun da ya siyo mata wanda ya kasance na shafawa, hannunta ya kamo ahankali wanda yake zafi zau, maganin ya bude ya fara lakuta yana shafa mata, bin tafin hannunta yake da kallo saboda yanda kunshin hannun nata yayi kyau sosai gashi ya fito radau,
Ko motsi batayi ba har yayi ya gama, "ikhlas nasan nayi miki ba daidai ba amma kiyi min afuwa, wallahi bazan iya rabuwa dake ba domin kece rayuwata you are my life, i can't survive without you,ina yi miki son da ni kaina ban san adadinshi ba"
Hannunshi ya mik'a mata yana nuna mata"kalli hannuna kiga yanda na tsagashi da reza na rubuta sunanki saboda tsananin son da nake yi miki, wallahi bazan iya sakinki ba pretty da ace zan iya to da nayi mutukar yin hakan zai haifar miki da farin ciki, amma karki manta da wasiyyar da dan uwana ya bar miki ta cewar karki auri wani idan bani ba, shin zaki yi watsi da wasiyyar da ya bar miki ne?"
Sanin bazata amsaba yasashi tashi ya fice, yana fita ta koma kan gado ta kwanta ta tukunkuna cikin bargo tana hawaye domin tunowa da tayi da wasiyyar da Abubakar sadiq ya bar mata, ita shaf da ta mance ma da wannan maganar sai yanzu, indai hakane kuwa to dole ta hakura taci gaba da zama da lamido domin cikawa Abubakar sadiq burinshi.
Shima Lamido yana fita daga dakin ikhlas dakinshi ya koma ya kwanta bayan ya lulluba acikin bargo sakamakon zazzabin da yaketa faman damunshi.
Daga shi har ita akwance suka wuni sai dai idan lokacin salla yayi su tashi suyi su koma su kwanta, har magrib tayi kowannensu yana kwance babu abinda yaci, sai misalin karfe shida sannan lamido ya tashi yayi wanka yayi salla yanzu kam yaji saukin zazzabin dake damunshi,
Tashi yayi ya fita afalo ya iske fadila da ihsan suna zaune suna hira yayinda fadila ke cin indomie da dafaffen kwai,
"Ango sai yanzu aka samu damar fitowa?" Ihsan tace dashi tana kallon goshinsa ganinshi nannad'e da bandeji,
"Ni ai nazata ko sai ka gama kwana ukun naka a dakin amarya sannan zaka fito" fadila ta fada tana murmushi,
A kusa da fadila ya zauna yana murmushi, "ni kaina da banyi niyyar fitowar ba har sai nagama kwana ukun" ya mayarwa da fadila amsa tareda karbar spoon din hannunta ya debi indomie din da take ci yafara ci,
"Darling ya naga goshinka da bandeji? Ciwo kaji?" Ihsan ta tambayeshi,
"Ehh wallahi" ya bata amsa,
"Garin yaya? Kai da kake tareda amarya ai bai kamata kaji ciwo ba" fadila tace dashi tana d'agawa ihsan gira,
"Naje gidan innane zan kai mata sadiq shine na buge"
Ya basu amsa yana cigaba da zukulkular abincin fadila,
"Ayya sorry" suka ce dashi atare,
"Kodai asake dafa maka wani indomie din?" Ihsan ta tambayeshi tana murmushi,
"No wannan ya isa" ya bata amsa, yana nan zaune sunata zolayarshi har ya cinye abincin ya mike,
"Bari naje na dauko sadiq daga gidan innah"
"Adawo lafiya" fadila ta amsa mishi amma ihsan ko sake kallonshi bata yiba har ya fice daga falon, yana fita suka fara gulmarshi,
"Jishi kamar wani marar lafiya dan Allah" inji ihsan,
"Bashida lafiya mana ai daga gani kin san akwai dalili, bakiga idonshi yayi jaba, ke nidai ina jin on top ba kalau ba"
"Koma meye shi ya jiyo badai yanata rawar kai dan yayi sabuwar amarya ba"
"Hmmm rabu dashi damuwarsu ce dashi da ita" fadila ta fadi tana turo dan kwalinta gaban goshi,
"Muna nan zai dawo garemu" inji ihsan,
Tashi fadila tayi "bari naje na cire kayannan na dawo"
"To sai kin dawo nima kitchen zan shiga na dafa lipton",wucewa fadila tayi ita kuma ihsan ta shiga kitchen.
Lamido yana fita gidan innah yaje, samunta yayi goye da sadiq yanata bacci ita kuma tana zaune tana jijjigashi,
"Innah sai ke kadai? Gashi sadiq dinma naga bacci yake yi"
"Ni kadaice lamido, ai tun yamma yake baccin nan sai dai Allah yasa kar ya hanaku bacci anjima" innah tace dashi tana murmushi,
"Amin dan maman tashi bata da lafiya"
Sauko da sadiq innah tayi ta mikawa lamido tana cewa "Allah ya bata lafiya"
"Amin" ya amsa tareda tashi ya fita, a gaban motarshi ya kwantar da sadiq ya nufi gida dashi,
Gabanshi ne yafara faduwa lokacin da ya nufi dakin ikhlas domin bai san irin karbar da zata yiwa sadiq dashi ba, akan abin salla ya sameta zaune ta idar da salla tana addu'a,zama yayi agefen gadonta yana rungume da sadiq, nan idonshi yakai kan tea da soyayyen kwan da ya soya mata da safe amma ko tabashi bata yiba,
Kwantar da sadiq yayi yana kallonta,
"Ga sadiq nan ya dawo amma dan Allah na rokeki karki barshi da yunwa.."
Ko niyyar bashi amsa bata dashi ganin haka ya sanyashi tashi ya fita ya koma dakinshi ya kwanta.
Har dare ya tsala idonshi biyu ya kasa bacci ganin haka yasashi fita ya nufi dakin ikhlas, baiyi mamakin ganinta ido biyuba,
"Waye?" Ya jiyota tana fada daga cikin bedroom dinta,
"Nine" ya bata amsa gamida kwanciya akan doguwar kujerar cikin falon, bata sake magana ba ta gyara kwanciyarta ta kwanta tana ji sadiq ya fara kuka tayi biris dashi domin laifin abbanshi ya shafeshi shima,
Tashi lamido yayi ya shiga cikin dakin saboda jin kukan yake yi har cikin ranshi, samunta yayi ta juyawa sadiq din baya ta barshi yana kuka, saka hannu yayi ya daukeshi,
"Ikhlas kar ki hukunta wannan yaron da laifina domin shi bashida laifi ko kadan"
Kyaleshi tayi ya Karaci maganganunshi ya gama ya fita da sadiq din a hannunshi yana jijjigashi,mintuna kadan ya koma baccin dan haka ya sake mayar dashi kusa da ita ya kwantar.
Daga lamido har ikhlas yanda suka ga rana haka suka ga dare har asuba tayi, dakin ya leka ya sameta zaune da kayan bacci tana feeding din sadiq, juyawa yayi da baya ya fita domin baya son ta ganshi ta cire sadiq daga jikinta.
_Gaisuwa gareku Queen Bilqees, Teeemarh luv & Indon k'auye_
_Ina cikiyar momy Halamcy idan sakona ya sameki to ina nemanki da gaggawa._
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
aishaummi.blogspot.com
*_68_*
~~~Bin bayanshi da kallo tayi tana nazarin maganganun da ya fad'a mata, wato shima yanzu laifinta yake gani kenan maimakon yaga laifin kansa, girgiza kai tayi ta yi dan karamin tsaki ta d'auki sadiq ta rungumeshi,
Kuka take son yi amma ta gagara saboda dalilin da ko ita kanta bata sani ba, tana nan rungume dashi har ya farka dan haka ta tashi zaune tayi feeding dinshi sannan ta d'aukeshi zuwa bathroom tayi mishi wanka tazo ta shiryashi tana yi tana tunanin abdallah domin kwana biyu bata samu sunyi doguwar hira dashi ba gashi kowanne lokaci sai taji ya fado cikin ranta sannan kuma sai yanzu ne take ganin matsananciyar kamar dake tsakaninshi da lamido domin hatta kwayar idon yaron irinta lamido ce sak, har yan yatsunshi da farcenshi duk irin na lamido ne, jar riga da blue din wando ta saka masa ta daukeshi ta goyashi ta fita zuwa kitchen akaro na farko,
Tunda ta fito take bin tsakar gidan da kallo domin bata san yanda yakeba, babban falo ta shiga saboda ta cikinshi kitchen din yake,fadila ce azaune taci gayu sosai cikin pink din shadda tana yin karin kumallo, babu wanda ya kula wani ikhlas ta shiga kitchen din, ganin kayanta tayi jere a gefe daya da sauran kayan amfaninta irinsu gas,fridge da makamantansu, can bari daya kuma store ne cike da kayan abinci aciki,
Gas ta kunna ta dora jalop din taliya da dankali, babu bata lokaci tayi ta gama ta sauke ta zuba acikin food flask ta dauka ta nufi dakinta, lokacin da ta fito fadila bata nan ta tashi hakan yasata tabe baki aranta tana tunanin ko wacece wannan kuma?
Daf da zata shiga dakinta ta hango ihsan itama zata fita tana rike da lecture notes da key din mota sai shan kamshi take yi,
Dakinta ta bude ta shiga ta zauna a falo ta kunna kallo wanda sam ba dadinshi take ji ba kawai dai tana yine maganin zama shiru.
Har dare yayi bata kara jin labarin lamido ba sai da ta fita zataje kitchen domin dumama taliyar da ta dafa da rana, a falo ta ganshi shida ihsan da fadila yana zaune a tsakiyarsu suna kallo, kamar ta juya ta fasa zuwa sai kawai tayi fuska taje ta wuce ta shiga cikin kitchen, tunda lamido ya ganta hankalinshi da nutsuwarshi suka tattara suka koma kanta,
"Darling baka gabatar mana da amaryar ba fa" ihsan tace dashi tana jingina ajikinshi,
"To ba gata can kun ganta ba" ya bata amsa,
"Ehh amma duk da haka ai ana gabatar da amarya kuma itama ana gabatar mata da wadanda tazo ta samu" fadila ta saka baki hannunta rike da remote tana kokarin canja channel,
"Sai kuyi kuma.." Ya basu amsa yana murmushi,
"Kenan dai nufinka ba zaka gabatar damu awurunta ba, itama ba zaka gabatar da ita awurinmu ba?" Ihsan ta sake tambayarshi tana makale hannunta cikin nashi,
Kafin ya bata amsa har ikhlas ta fito daga cikin kitchen din hannunta rike da food flask, wucesu tayi ta shige, binta da kallo lamido yayi aranshi yana yaba irin shigar da tayi domin wata bakar atamfa tasaka mai ratsin yellow ajiki dinkin doguwar rigane ta sama ya tsuke ta kasa kuma ya baje dan haka ba karamin kyau tayi ba gashi dai ba wani kwalliya tayiwa fuskarta ba amma duk da hakan tayi masa kyau,daurewa yayi ya yakice tunaninta daga ruhinshi yaci gaba da hira dasu fadila har 10 tayi sai lokacin suka yi sallama kowa ya tashi ya tafi dakinshi.
Bedroom dinshi ya shiga yayi wanka ya yi kwanciyarshi ya dauki waya ya kira Xahar, ita kanta Xahar sai da abin ya bata mamaki domin lamido bai fiya kiranta ba sai dai ita ta kirashi,
"Ranka ya dade.." Ta fadi cikin yanga,
"Yakike?" Ya tambayeta bayan ya lumshe idonshi yana hakanto kyakkyawar surarta domin itama ta hadu babu karya amma da bai gane hakan ba har sai yanzu da yafara kulata kulawa kuma wacce zata kaishi har ga aurenta, hira suka ci gaba dayi da ita sosai har 11, kashe wayar yayi bayan sunyi sallama ya juya kanshi yana kallon sama ya fara tunani kuma,yasan abinda yayiwa ikhlas abune mai ciwo amma kuma tunda har ya fito fili ya bata hakuri ai ya kamata tayi hakurin ta yafe mishi su rungumi dansu su rikeshi su zauna lafiya amma maimakon haka ma sai gaba da fushi da ta dauka dashi wanda ko kadan bai bata masa rai ba kamar yanda tabar sadiq ya fadi yaji ciwo, wannan abu yayi mutukar kular dashi shiyasa ma shima yanzu ya dauki aniyar nuna mata kuskurenta.
Ikhlas na kwance a daki bayan tayi shirin bacci, shiru shiru taji lamido bai shigoba saboda taga kwana biyun nan da suka samu sabani a falonta yake kwana domin yasan bazata bari ya kwana acikin dakinta akan gadonta ba, amma kuma yau ko falon bai zoba,
"Me wannan gayen yake nufi? Nufinshi kenan nice zan bishi dakinshi? Tab lallai ashe zamu shekara ahaka" ta fadi hakan acikin zuciyarta,
Tana nan kwance tanata sake sake acikin zuciyarta har dare yayi sosai bata san ma lokacin da bacci ya kwasheta ba sai da asuba tayi sannan ta farka,
Alwala tayi tai salla ta dauko alqur'aninta ta bude ta karanta abinda ya sawwaka sannan ta tashi ta koma ta kwanta, tunda kuma ta koma bacci ba ita ta tashi ba sai 9 nan dinma kukan sadiq ne ya tasheta, zaune ta tashi ta daukeshi,
Ta saitin window dinta ta jiyo maganar lamido shida fadila da alama duk fita zasuyi,
Wani takaicine ya lullubeta wato ma fita zaiyi amma ko yazo yaga yanda suka kwana suka tashi itada sadiq,
"Hmm yayi kyau" ta fada ahankali tareda tashi da sadiq ajikinta ta nufi bathroom.
Wuni guda gidan shiru tsit babu kowa aciki sai ita kadai hakan yasata shiga cikin damuwa,har sai da yamma tayi sannan ta fara jiyo motsin matan gidan alamun sun dawo,
Bata fita ba har magrib sai da tayi salla sannan ta fita ta nufi kitchen, lamido ta gani cikin kananan kaya riga t shirt fara da boxer baki yana kwance akan doguwar kujera ya dora kanshi akan cinyar ihsan tana wasa da sumar kanshi,
D'auke kanta tayi tai kamar bata gansu ba ta wucewarta cikin kitchen amma kuma zuciyarta jinta tayi tai mata wani irin nauyi ga zafi da ta fara,
Tana shiga cikin kitchen taga fadila tsaye tana soya cheaps, wurin kayanta ta wuce ta kunna wuta ta dora tukunya, tana tsaye tana grating din kayan miya fadila ta kammala aikinta ta wuce ta fita, kamar ikhlas zata fashe da kuka haka taji amma ta daure ta kammala dafa indomie din ta dauka ta fita,
A falon ta sake tarar dasu dukansu suna cin cheaps din da fadila ta hada musu, dauke kanta tayi ta wuce a zuciyarta tana jin ita kadai Lamido ya ware saboda yana son yayi mata rashin mutumci acikin gidanshi,
Tana shiga dakinta ta ajiye food flask din ta zauna sai hawaye sharrrr! Hawaye ne suka ci gaba sauka akan kumatunta har na tsawon wani lokaci. Dakyar ta iya cin abincin tayi salla tayi wanka tayi shirin bacci ta kwanta.
Haka suka ci gaba da zama har na tsawon wani lokaci, duk ranar girkinta lamido bama ya dawowa gidan da wuri domin ranar ne yake zuwa hira wurin xahar, idan kuma ba ranar girkinta bane to bata jin duriyarshi sai dai idan ta fita falo su hadu.
Jin zaman gidan tayi ya isheta domin kullum ita kadaice take wuni agidan sai weekend su fadila da ihsan ke zama, shi kanshi lamidon shima ba zaman yake yi ba domin sunata shirye shiryen kammala service dinsu ga ginin company dinshi wanda baffa ke gina mishi da ake son ayi agama domin fara aiki,
Tana zaune a dakinta tana kallo taji alamun ya dawo dan haka ta mike ta nufi falo, yana zaune shi kadai da laptop agabanshi yana latsawa,yayi tsananin kyau cikin farar riga jersey da dan karamin wandonta iya cinyarshi,
"Abban sadiq wurinka nazo" tace dashi fuskarta babu walwala,
"Ina jinki" yabata amsa ba tareda ya dago ya kalleta ba,
"Maganar makarantar islamiyya dinnan da muka yi dakai, ina son zan fara zuwa"
"Ba yanzu ba" ya mayar mata da amsa idonshi akan laptop dinshi,
"Wanne irin ba yanzu ba? Kullum ni kadai nake wuni agidan nan sauran matanka gasu nan ka barsu suna fita makaranta amma sai ni yanzu dan nace zan shiga islamiyya zakace bazan jeba?" Ta fada cikin bacin rai,
D'an murmushi yayi kadan sannan yace "idan akan fadila da ihsan kike magana to ni banine na nemar musu makaranta ba, asalima a makarantar na gansu har nafara sonsu na auresu, dan haka yanzu bazan hanasu karatunsu ba..."
Juyawa tayi ta tafi ba tare da ta sake magana ba amma kuma maganarshi ta yi mugun kona mata rai mussamman ma kalmar da ya fada wai asalima a makarantar ya gansu har ya fara sonsu, tsaki tayi ta gyara kwanciyarta zuciyarta na yi mata radadi, dama ko bai fadi haka ba ai tasan yana sonsu kuma dan yana sonsu ya auresu har yake zaune dasu.
Lokacin da ikhlas ta tafi lamido kasa samun nutsuwa yayi domin baya son yayi mata abinda zata rinka ganin kamar mijinta na baya yafishi sonta duk da yasan duk abubuwan da suke faruwa laifinta ne domin itace tayi mishi abinda har ya kasa hakuri ya fara fushin shima, rufe laptop dinshi yayi yai shiru, rabonshi da dakinta tun lokacin da ya mayar mata da sadiq washe garin ranar da ya fadi yayi targade yanzu kimanin wurin sati shida kenan.
_Fatan alkairi agareki Xarah (the writer of Deemah),nagode miki sosai this page is for you my dear!_
*_Ummi A'isha_*👌🏻
*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
aishaummi.blogspot.com
*_71_*
~~~Shiru dukkaninsu suka yi in banda ikhlas wacce ta fashe da kuka harda shassheka,
"To kuma menene abin kuka? Keda Allah ya rufa miki asiri, dama wannan addu'ar muka dade muna yi miki domin kada wannan yaron ya girma wata rana ya nemi ki nuna masa ubanshi ki kasa.." Hajiya tace da ita tana kokarin karasa shigowa cikin dakin,
"Ki daina kuka ikhlas wannan abun kiyi farin ciki ne domin yanzu hankalinki zai fi kwanciya.." Ammi ta fada tana kallonsu,
"Ammi baki san fa irin wulakancin da yayita yimin ba kawai saboda na nuna mishi bacin raina akan abinda yayi min" ikhlas ta fada cikin gurshekin kuka,
"To da waye yace miki ki nuna masa bacin rai? Ai bacin rai ya kare tunda har Allah ya rufa miki asiri uban wannan yaron ya bayyana.." Hajiya ta sake fada,
"Dan Allah hajiya ya isa haka... Ya za ayi ku rinka goyon bayanshi? Nifa akan wannan maganar wallahi ko kotune sai muje dashi domin a kwato mata hakkinta kuma bazata koma gidanshi ba har sai ya gane kuskurenshi.." Yaya Hussain ya fada cikin fada
"Adai yi hakuri abi komai a sannu" ammi tace da Hussain cikin sigar rarrashi,
"Ai wallahi sai ya gane kuskurensa sannan kuma bai isa mun bashi abdallah ba sai dai yayi duk abinda zaiyi,kuma wallahi indai ba itace tace zata koma ba to dole sai ya saketa" Hussain ya sake fadi tareda ficewa fuuuuu cikin fushi,
"Dadina da Hussain akwai zuciya da zafin rai" hassan ya fadi,
"Barshi yayita yi dan me da masifar tsiya" inji hajiya,
"Allah dai ya kyauta" ammi ta fadi amma acikin zuciyarta murna ce fal wacce ita kadaice tasan dalilinta.
Karfe 5 daidai lamido ya dawo gida, fadila da ihsan ya iske a falo suka yi mishi sannu da zuwa ya wuce dakinshi,
Wanka yayi ya fito ya koma falo inda fadila ta shirya girki domin ranar girkinta ne, zama yayi yaci abincin ya tashi ya fita salla, lokacin da ya dawo daga salla zama yayi a falo ya fara kallon ball har lokacin sallar isha yayi, masallaci ya koma yayi salla ya dawo ya sake zama a falo, harsu ihsan suka gama zamansu suka tashi shi yana nan a zaune sai da 9 tayi sannan ya tashi ya nufi dakinshi kamar wanda aka cewa ya dawo sai ya dawo da baya ya nufi dakin ikhlas domin yau sam baiyi ido hudu da itaba kuma baiji koda kukan sadiq ba,
Dakin nata ya bude ya shiga nan ya ganshi duhu dindim babu alamar haske, fitila ya kunna ya shiga cikin dakin rasss! Zuciyarshi ta harba domin dakin wayam babu ita babu sadiq,
Toilet ya bude ya leka nan dinma hakan take babu kowa, cikin sauri ya fita daga dakin har yana yin tuntube,
"Ina pretty ta tafi?" Ya tambayi kanshi bayan ya zaro wayarshi daga cikin aljihunsa, dakin ihsan ya nufa a sukwane ga waya kuma yana kiran innah,
Ko sallama babu ya fada dakin Ihsan, fitowarta kenan daga wanka tana daure da towel "my ihsan yau kinga maman sadiq agidan nan?" Ya tambayi ihsan arude,
Girgiza masa kai tayi "gaskiya yau ban ganta ba kwata kwata jiya dai mun hadu a falo zata shiga kitchen"
Juyawa yayi da sauri ya fita yana magana "ko ina innahn ma ta shiga? Inata yi mata waya taki dauka.."
D'akin fadila ya tasamma yana shiga yayi karo da ita itama tana kokarin fitowa,
"Fadila yau kinga ikhlas acikin gidan nan?"
"Ban ganta ba, lafiya?" Fadila ta bashi amsa, batare da ya mayar mata da amsaba ya juya yayi waje, wurin mai gadi yaje ya fara tambayarshi da yaushe ikhlas ta fita, nan maigadi yace tun safe ta fita da katon akwati,
Motarshi ya nufa ba tare da yace komai ba ya daukota a zabure ya fita, gidan barrister elmustapha ya je ya tura aka yi masa sallama dashi ya fito bayan sun gaisa ya tambayeshi ko ikhlas tazo?
Cikeda mamaki elmustapha yace "lafiya? Nidai yau banji ni'ima tace ikhlas tazo gidan nan ba"
"Shikenan sai da safe nagode"
Motar tashi ya koma ya shiga ya figeta ya nufi gidan innah yasan duk yanda akayi ikhlas can ta tafi, yana zuwa ya shiga ciki jikinshi har rawa yake yi,
"Innah ina ikhlas take?" Ya jefawa innah wannan tambayar daidai lokacin da ya shiga cikin dakinta,
"Ikhlas kuma? Ai ikhlas yau bata zo gidan nan ba lamido, ko wani abune ya faru?" Innah ta tambayeshi hankalinta atashe,
"Innah ikhlas bata gidana, ban san inda ta shiga ba" lamido yace da innah idonshi cikeda kwalla,
"To ka kirata awaya mana"
"Wallahi innah ko na kirata ba dauka zatayi ba"
"Ka kirata dai kaji"
Wayarshi ya zaro ya fara kiranta amma shiru shiru bata dauka ba harta katse yasake kira nanma shiru taki dauka da haka har sai da yayi mata miss called fiyeda goma,
Text massage yaga ta turo mishi kamar haka:-
_Kadaina kirana haka domin bacci zanyi nasan abinda zaka tambayeni bai wuce a ina nake ba, to ina Maiduguri gidanmu cikin gatana inda ake sona ake kaunata,Lamido ko kai kadaine autan maza to na hakura dakai bazan sake zaman aure da kaiba, idan ka samu dama kana iya turo min da takardar sakina.._
Ai lamido yana gama karanta sakon nan hankalinshi ya tashi kololuwar tashi take kwallar idonshi ta zubo akan kumatunshi,
"Innah kinji wai tana Maiduguri, wai bazata dawo ba sai dai na saketa..." Ya fada kamar Zararre,
"Fada kuka yi ko me? Menene ya hadaku?" Innah ta jero masa wadannan tambayoyin ajere, jikinshi ne ya fara rawa domin ya zama dole ya fadawa innah saboda ranar wanka ba a boyon cibi,
"Innah wallahi fushi take dani tun lokacin da na fada mata gaskiyar cewa nine mutumin da ya....." Shiru yayi kasa karasawa,
"Yayi mata me?" Innah ta tambayeshi cikin kaguwa,
"Innah ki yafe min nasan da lokacin da ina dan makaranta nayi rashin ji iri iri amma wallahi innah yanzu na tuba, wallahi yanzu bana aikata ko wanne irin laifi, tun lokacin da kuka yimin aure wallahi na shiryu amma innah ki taimaka min domin ikhlas itace rayuwata wallahi bazan iya rayuwa ba sai da ita..."
"To ai lamido ni na kasa gane inda maganar taka ta dosa"
"Innah fyade nayi mata tun shekaru wurin shida da suka wuce amma wallahi bada niyya nayi b...."
Tun kafin ya karasa innah ta daukeshi da mari har guda biyu ajere, rike kuncinshi yayi ya daga ido yana kallon innah domin tun tasowarshi innah bata taba marinshi ba sai yau,
"Akan wannan ne dama zaka zo ka sameni kana yimin surutu? Ka fice min daga daki ka bani wuri, ai gara kar ta dawo din domin indai hakane to baka da halin kwarai shashasha kawai, fice min daga daki" innah tafada cikin tsawa, juyawa yayi ya fita yana hawaye ya nufi dakin baffa,
Yana kishingide akan darduma yana jan carbi, tunda baffa yaganshi yasan ba lafiya ba dan haka ya mike zaune yana kallonshi,
"Lamido lafiya?"
"Baffa dan Allah dan annabi ka taimakeni, kada ka juya min baya kamar yadda innah tayi min, wallahi ina sonta itace ratuwata bazan iya rayuwa babu itaba.."
Dafashi baffa yayi "wacece?"
"Wacece kuwa banda matarsa ikhlas wacce yayiwa fyade saboda shi cikakken marar imani ne, shine kuma yanzu zai kwaso jiki yazo yace wai muje mu dawo masa da ita, to bari kaji ko zaka mutu ikhlas ba dawowa gidanka zatayi ba, hakan da tayi yayi daidai domin babu amfanin zama da fasiki idan ba ahali irin na lalura ba" innah dake bakin kofa ta fada tana huci,
A furgice baffa ya kalli innah "ban gane abinda kike nufiba? Kun sani a duhu"
"Gashi nan yayi maka bayani da bakinshi abinda ya faru.."
"Lamido wai me yake faruwa ne?" Baffa ya sake tambayarshi,
"Baffa wallahi ba laifina bane kaddara ce tasa har nayiwa ikhlas fyade..." Lamido ya fada yana kuka,
Cikin fushi baffa yake kallonshi "kuma to mu yanzu me kazo muyi maka?"
"Zuwa yayi muje mu dawo masa da ita mana saboda tatafi gidansu tace bazata zauna da fasiki ba" innah ta bawa baffa amsa ranta abace,
"Ni zanje na dawo maka da ita? To saurara kaji sai dai ka mutu amma zaman aure da wannan yarinyar kun gamashi, ni ba mutumin banza bane kuma bazaka mayar dani wofi ba dan da ace ma tun farko nasan ka aikata haka to da ban bari ka aureta ba amma yanzu ka jira takardar sammaci dan na tabbata yan uwanta ba zasu kyaleka sai sun gurfanar dakai agaban kotu" baffa ya fada cikin fushi tareda mikewa zai tafi, kafarshi lamido ya rike yana kuka,
"Baffa dan Allah kuyi min afuwa ku yafe min domin abinda ya faru kaddara ce..."
Fincike kafarshi baffa yayi ya kada kai ya fice daga falon innah ta mara masa baya suka bar lamido durkushe anan yana aikin kuka,
Mikewa yayi kanshi yana wani irin ciwo ga juyawa da yake yi, ko ba afada masa ba yasan hawan jininsa ne ya tashi domin yana dashi kuma ata sanadiyyar ikhlas ya hadu dashi,
Motarshi yaje ya shiga zuciyarshi sai bugawa take yi da karfi,ga hajijiya dake daukarshi, wayarshi ya dauka ya kira bash anan ya zayyana masa dukkan abinda ya faru, sosai bash ya jinjima lamarin acikin ranshi,
Kashe wayar lamido yayi ya finciki motarshi ya nufi gida, ikon Allah ne kadai ya kaishi gida domin titin ganinshi yake yi bibbiyu kamar wanda yasha kayan maye,
Yana zuwa ya shiga cikin dakinshi ya kwanta, kamar wanda ciwon ke jira yana kwanciya zazzabi ya kawo masa ziyara baya ga ciwon kai da ya sarke shi, juyi ya fara yi akan gado nan kuma ya fara amai har ya gangaro kasa daga kan gadon, wani azababben ciwon ciki da ciwon kirjine ya sako masa kai daga nan bai sake sanin halinda yake cikiba.
Fadila ce ta shiga cikin dakin nashi cikin shirin bacci nan tayi ido hudu dashi yashe akasa acikin amai bakinshi yana fitar da wani farin kumfa kamar wadda yaci guba, agigice ta ruga da gudu zuwa dakin ihsan wacce ita tuni tayi bacci ma,
"Ihsan, ihsan tashi, kitashi lamido zai mutu"
Zabura ihsan tayi ta diro daga kan gado domin jin abin tayi kamar a mafarki, tare suka sake runtuma zuwa dakin lamido, ganinshi yasa ihsan rudewa,
"Mun shiga uku me yaci?" Ihsan ta fada arude,
"Fadila dauki wayarshi ki kira koma wanene azo akaishi asibiti domin wallahi ni bazan iya driving acikin Daren nan ba"
Arude fadila ta dauki wayarshi ta yi dialling ita bata ma san kowa ta kiraba ashe bash ta kira domin shine mutum na karshe da suka yi waya, yana dauka ta fashe da kuka tana cewa "dan Allah ka taimaka mana kazo mu kai lamido asibiti kar ya mutu..."
Ai afirgice bash ya diro daga kan gadonshi, mintina kadan ya karaso gidan, su ihsan sai kuka suke yi sun sakashi agaba sun kasa koda tabashi, babu wata wata bash ya daukeshi a kafadarshi yayi waje dashi, hijabansu suka debo kawai suka bi bayan bash sunma manta da cewar kayan bacci ne kawai ajikinsu.
Wani dan karamin asibiti suka kaishi amma bash ba karamin gudu yayi ba kafin su isa abibitin, su ihsan kuwa sai faman kuka suketa yi kamar ransu zai fita,
Wasu nurses ne suka taimakawa bash suka shigar da Lamido wani dan daki wanda za a dubashi aciki, hankalin bash ba karamin tashi yayi ba domin ganin halin da lamido yake ciki,daya daga cikin nurse din da suka shigar da lamido ne ta fito tana kallonsu arude,
"Am sorry to say ina tunanin fa patient din da kuka kawo tuni ya dade da rigamu gidan gaskiya saboda guba yaci....".
0 comments:
Post a Comment