*CHAPTER 11*
ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana
fadar. a a dan Allah ka yi hakuri Malam kar ka kashe shi.鈥� 掳
Malam ya goce yana fadar, 鈥榃allahi yau sai dai akwashi
gawa'rsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.鈥�
Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi鈥檜 da duka kamar Wani
zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin hankali su
suka hana Rabi'u komai saidai kare kansa da yake, sai da
yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike ya yi
waje
Hayaniyar su ce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta
tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake
faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana
dukan Rabi鈥檜 ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta
motsa
鈥� Rabi鈥檜 ya ruga malam ya bi shi har
, 鈥淪ai na kashe ka la鈥檃nan nan Allah, Allah ya isa tsakanina
da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin *gidan nan, kai
cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka
munafukin Allah.鈥�
Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa 鈥榶an zummokaransa
ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, 鈥淜a san inda dare
ya yi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa
ka hadu da mummunan hatsarin da za a kasa gane ka,
Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah ya yi maka
wanda . ya fi shi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta,
Allah ya daga maka hakali ya hana nutsuwa a duk inda ka
ke鈥�
Laure ta fito tana fadar, 鈥淒on Allah Malam ka shigo gida
haka nan tun'da dai ka kore shi ka ga har 鈥� mutane sun fara
taruwa.鈥� '
Malam Bala ya dawo gidan ya ci gaba da 'zazzaga masifa
tamkar wanda ba ya cikin hankalin shi, Saude dai na kallon
su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata
mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba
Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana
neman Rabi鈥檜 can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar
gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya
hada kan shi da gwiwa da 鈥榶an kullin tsummokaransa a
gaban shi.
Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake
tana kiran sunan shi, Rabi鈥檜 ya yi saurin dagowa yana
kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da
hawaYe, ya yi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. '
Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da 'wani irin
kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi鈥檜
ya samu da kyar ya iya tsaida nasa
kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba
tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba.
鈥淪aude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Ki yi
hakuni na san Ubang鈥榠ji na sane da mu ba mancewa ya yi
da mu ba, kuma shi ya san yanda zai yi da mu, tashin
hankalina Saude a yanzu daya ne ' yanda zan tafi in bar ki
ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki
fuskanta bayan bana nan, ban sani ba.鈥�
Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, 鈥楧ole zan
tafi', dole zan bar garin nan Saude ki yi hakuri ki rungumi
rayuwa a duk yanda ta zo miki kar ki yarda ki sabawa
Ubangiji a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0
kishiyar hakan. Na 鈥� san insha Allahu Ubangiji ba zai bar
rayuwarki ta lalace ba." 鈥�
Yasa'hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi 鈥榶an, dari
biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya
raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, 鈥淕a. wannanki riqe
a hannunki kiyi amfani dasu insha Allahu zaki rinqa samun
aikena a duk inda na shiga a fadin
duniyar nan.鈥�
Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar,
鈥淎llah ya hada fuskokin mu da alheri."
Saude ta yi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin
kuka mai daga hankali.
鈥淒on Allah kada ka tafi ka bar ni Yaya wallahi mutuwa zan
yi idan ka tafi Wayyo Yayana!鈥� Ta qara fashewa da wani
gunjin kukan.
Rabi鈥檜 ya dafa ta yana kallon idanuwanta kafin ya ce, 鈥淜i yi
haquri Saude ni kaina ba dan na so ba zan tafi inbarkiba,da
zaiyiwu da dole dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne
tunda ke macece amma na
yi miki alkawarin duk inda make a duniya ina tare
da.... Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda
kukan da ya kwace masa shi ma. Ya zame hannayenta
daga jikinsa yana fadar, 鈥淚n har kina sona da gaske Saude
kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida ni na tafl sai
wata rana.鈥�
Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar
hawayen da ke zuba daga idanuwanshi kamar an kunna
famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka tun
iya karfinta. Rabi鈥檜 na jin ta amma bai waiwayo ba saboda
yanda yake jin zuciyarshi na
Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba
jama鈥檃 da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda
Saude ta duka ba ta sake tashi a gun ba, tun tana kukanta
iya karfinta har muryarta ta disashe. ~
Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga
gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana,
amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana' kuka, ba ta
ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina鈥� tana dagowa ta
ga Inna Laure, ta mike ta 鈥� kwasa da gudu ta nufi hanyar
gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ' Tana shiga cikin gidan ma
nan ma Malam ya dora mata da na shi dukan yana zaginta
tare da yi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu
alamun ' tausayawa鈥� a fuskarta ita ma ta hau zaginta tana
fadin
* 鈥溾€橸ar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna
tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.鈥�
Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu
tsummokaran kayan 鈥榊ar Baba wadanda ta gama da su ta
watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada
mata yanda za ta sanya sannan ta 鈥� dora mata tallar
wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta tice daga gidan tana
matsar kwallah.
Haka ta je tallar ta dawo ba taci komai ba, sai kukan da
take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki
alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wurin ranar
yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za ta ga Yayanta
amma k0 mai kama da shi bata gani ba haka ta karaci
yawon tallar ta ta dawo da yamma likis.
Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman
kujera 鈥榶ar tsugunne taya ni gulma suna
hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da
baki tana fadar.
鈥淜in gan ta nan fa dillalliya, wan: ai aikatau ga wannan ai
tallar cc kawai ta dacc da ita.鈥�
Dillaliya ta ce, 鈥淗aba dai a ganin ki dai, amma in da ni ce da
wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai."
Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna
Laure cinikinta ta mike ta wucc dakinta.
Tana jin Inna Laure na fadar, 鈥淗mm! Dillaliya kenan ai ni
duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, to shi kuwa k0
miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi
don har na fara tunanin in zuba masa shinkafar Bera a
abinci 鈥榶a ci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe.
Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na 'ga yarinyar jinin ya
zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai da na
shiga daki na yi ta dariyar qeta yanda na ga Malam na
sharar 鈥榶ar kwalla.鈥�
I
Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo
diilaliya na fadin
鈥淜e wai ba zaki saro gyada ki soya mata ta rinqa zama
kofar gida ba na ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za
ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da daddare.鈥�
Laure ta ce 鈥淎i k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje
鈥榊ar Kutungu da kaina in siyo mai kyau
in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata
Akwai ki da bada shawara mai kyau.
Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuquki
wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da
mai lallashin ta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda
rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa
Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta
yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata
a. duniya, ba su da kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta
sake rushewa da wani sabon kukan lokacin da ta tuna da
lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan
kwalliya. *
Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan ya ga ta shiga
damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen
nata, ga shi yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya
ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan
za 鈥�
tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shi ba
yanzu, wala ya mutu k0 ya yi rai. Shin k0 yana a wane hali
yanzun ma?
鈥淲ai k0 ba da ke nake ba ne Saude kina ji ina ta faman
kiran ki?鈥�
Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta
goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi
Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, 鈥溾€橸ar iska duk uban
me kike ina kiran ki kin yi min shiru?鈥�
Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da
suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki
tana fadin.
鈥淜e dai kya kai su in kaya ne wuce ki ki dora mini sanwar
tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki
wanke mini su.鈥�
Saude ta yi saurin dagowa ta kalle ta, Laure ta ce,
鈥淏akallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin
isa.鈥�
Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta
taba yin wanki ba, don kayanta ma kale daya ne, duk wani
wankin gidan Rabi鈥檜 ne ke yinsa. To ta inn ma za ta fara?
Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan
ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan
Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama
aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga
mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman
numfarfashi.
Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al鈥檃mura sun
karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar
gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu
hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare.
Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar
kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun
girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara
dagulewa take tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum
a wurinta jiya ta fi yau.
Tun tafiyar Rabi鈥檜 bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara
samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara
biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan rashinsa
wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta
ta kwanta ta yi barci, qunci da wahalhalun rayuwa sun yi
mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin
rayuwar da take ciki.
Musamman abubuwan da 鈥榊ar Baba ke mata ya na
damunta, ko'dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a
lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma 鈥榊ar Baba na
da shekara sha biyar, amma tafi Saude garin jiki, saboda ita
irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan
gaBoBin nan.
Don ita Saude 鈥榶ar siririya ce sosai, kamar a hure ta 'ta fadi,
sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa 鈥榊ar Baba gajeriya ce
mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da wadatar na
shanu, ba laifi 'ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci
da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware
ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya.
鈥榊ar Baba har tafi mahaifiyarta wurin鈥榬ashin mutunci da
rashin tausayi ga gadara da ' rashin kunya da tsinannan
surutu, kamar aku, ga shi' Inna Laure da Malam Bala sun
dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka
samu yana kanta.
Shi yasa 鈥榊ar Baba ta tashi da kwalliya 鈥榶ar gayu ce sosai,
suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na
fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma
idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau.
Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana
gab kawowa kofar gidansu ta hango wata qaramar mota
Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a
lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da
wasu 鈥榶an uwa masu 'mashin' ma balle mota
Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon
motar, ta zo daf da ita ne ta ga an bude an fito. 鈥榊ar Baba
ce da wani saurayi suka fito daga
gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan
ledojin nan na shopping.
Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke
Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side ga su
daban-daban, wato wari da wari, wani ya fi wani. Hakan
yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya
takalman duk sun sha faci da Leda.
Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu
tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin
na fadar, 鈥榃annan kuma wace ce?鈥�
鈥榊ar Baba tabe fuska kafin ta ce 鈥溾€橸ar talla ce gidanmu take
tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?鈥�
Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce 鈥淎鈥檃, haka kawai amma
dai gaskiya kazama ce, wallahi bakijiba data wuceni
harzuciyata saida ta tashi. "
Daidai nan Saude ta shige cikin gidan tana jin zuciyarta na
mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin
tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta sannan ta dauki
abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne
ke bi yabe
yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna
ta soma cin dumaman tuwon.
鈥榊ar Baba ta shigo niki~niki da ledoji Inna Laure da ke
zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar.
鈥淥yoyo! Ga 鈥榶ata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka
farauto mana
鈥榊ar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye
ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin mayafinta mai
kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna,
gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo
waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta
k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take.
Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala-
kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace,
daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na
manyan mata.
Bakin Laure ya Ki rufuwa鈥榯a dubi ,鈥榊ar Baba taha fadar,
鈥淲annan kuma ina ki ka same shi 鈥榊ar Baba, dan wane ne a
garin nan?鈥�
鈥榊ar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace,
鈥淲allahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi
na dawo daga makaranta.鈥�
Laure ta rafka guda kafin ta ce, 鈥淒a kyau 鈥榶ata tauraruwa
cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki
dan anan dai haihuwa ta yi rana, Ki dai tsaya ki nutsu ki
dage ki shake mana wuyan duk wanda ki
Kikeso in ja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa
daurin huhun goro
鈥榊ar Baba ta sa dariya tana fadar, 鈥淜ai shi yasa nake son ki
Laure.鈥� 鈥�
Ta mike tsaye tana fadar, 鈥淗mm! Gaskiya wani abu na ci
min tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar
mini da aji a gaban samarina.鈥�
Laure ta zaro ido 鈥淲ace yarinyar?鈥�
鈥榊ar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, 鈥榊o wace ce in ban
da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta
wallahi da ta wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya
nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali
ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar
matalauta.鈥�
Laure ta ce, 鈥淎i waccan mai kama da igiyar shanyar ni
kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni
za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.鈥�
鈥榊ar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune
kamar mai rawar taBa-kaka.
Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu
sunada bakinda 鈥檢asu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa
sanin kayanta a duniya kala uku ne sumana Laure ne data
gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai
da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun
wanka k0
na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta
siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi
wanki tadiba aciki tayi wanka.
Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man
shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata
shekaru uku kenan da suka wuce da 鈥榶an kwanaki. Ta
mayar da 鈥榶ar kwallar da ta ciko mata ido ta ci gaba da cin
tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata
tsaye a qahon zuciya.
Da rana Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa
bokitin alalarta a gaba tana kallon jama鈥檃 na ta kai wa da
kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take
yana faman tsangala kafa da shanyayyan hannunsa guda
can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda
ya shanye
Saude ta Kara hade fuska dan a duniya idan akwai wanda
ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijo dan a
Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani
qarami. Yaro
Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana
' faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta
daukc kanta ta ci gaba da kallon wani waje. Garba
ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. 鈥渟annu
da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?鈥� Saude ta jiyo muryar
nan kamar an kunna injin
markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana
Lol i relly feel unhappy for rabiu
[1/17, 7:54 AM] A A Dboy: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[1/19, 5:11 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
*CHAPTER 12*
kallon shi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk ya yi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a cikin saba, saboda tsabar qazanta da kurar duniya da ya sha. Saude ta dame zuciyarta ta amsa masa don k0 kadan ba tajin za ta iya yi masa wulaqanci saboda girman shekarunsa dan ya yi jika da ita.
Garba ya Kara watso haqoran nan wadanda su kai kore fatau kamar gansa-kuka yana fadar, 鈥淗aba Saude na ga alamar kamar ba ki san magana dani, ki yi hakuri ni masoyinki ne ba makiyinki ba kuma ni aurenki zanyi bawai wasa zaikawoni wurinkiba yanzu haka idankika amince min mahaifinki kawai zan nema a yi magana.鈥�
Saude ta watsa masa wani kallo mai kama da harara ta zumburo baki kafin ta ce, 鈥淣i fa ba anre zan yi ba yanzu
Ya yaqe baki yana fadar, 鈥淗aba Saude ke yanzu idan bakiyi aureba saime zakiyi?idan ki ka amince: ki鈥榢a aure ni, killa ceki zan yi a鈥榞idana, kin gama zuwa talla idan ma kina tunanin matana hudu ne to a shirye nake dana saki daya daga cikinsu Ya kikacene Saude?鈥� 鈥� Haushi ya kamata ta mike afusace tadauki bokitin tallarta ta yi gaba ta bar shi nan zaune
Garba Gurgu ya yi dariya yana girgiza kai yana fadar鈥� 鈥淵aro yaro ne.鈥� Ya mike yana cangala qafa shi ma ya yi gaba abin sa.
Bayan Saude ta gama tallarta da yamma likis ta koma gida a gajiye ta samu ta ci abinci ta yi sallar Magariba, sannan ta dauki tallar dare ta fita kofar gida ta zauna da 鈥榶ar fitilar aci-balbal.
Kamar daga sama ta hango shi tsangal-tsangal haushi ya cunkusheta ta bade fuska a zuciyarta ta kudiri aniyar idan ya sake ya zo inda take sai ta cire kunyarsa daga idanuwanta ta yi masa rashin kuunya tunda ta lura bai san girmansa ta gani ba ta daga masa kafa ba
Da mamakinta sai ta ga ya yi wa kofar gidansu tsinke, ta saki baki da idanuwa tana kallon shi, ta ga ya kira wani yaro ya tura shi cikin gidansu. Yaron bai jima ba ya fito tana kallon su can sai ta ga mahaifinta ya flto sun tsaya suna gaisawa, gabanta ya yi 鈥檓ata mummunar faduwa hankalinta ya yi masifar tashi ba dai Garba wurin mahaifinta ya zoba.
Wayyo Allah na shiga uku! Abin da ta iya fada kenan wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a kuncinta tana kallon yanda mahaifinta ke ta faman
washe bakivyasa hannu ya karBi kudin da Garba Gurgu ya ba shi, sannan suka sake yin musabaha, sannan ya shiga gida shi kuma ya wuce abinsa ba
tare da ya kalli inda take ba. Saude ta ta kwashi kayan tallarta ta nufi cikin gida. A tsakar gida ta samu mahaifin nata na fadawa
鈥淟aure kin ga wani abun murna k0 wai mutumin nan Garba Gurgu ke son Saude
Laure ta rangada kuda ta ce, 鈥淜ai amma abun ya yi min dadi wallahi, ka ga sai a hada su su duka da 鈥榊ar Baba. don ita ma ta ce yaron nan mai zuwa wurinta da jar motar nan ya ce zai turo ai maganar aure
Malam Bala ya ce, 鈥淎i ko haka za ai dama ni na amsa masa, yanzu haka ya ce jibi za a kawo kayan nagani-inaso yanzu haka har kudi ya ba ni kin gansu dubu biyu. Kai gaskiya mutumin nan yana da mutunci.鈥�
Laure ta ce鈥淭o, ai sai ka tsakuro mini nawa tunda ba kai kadai keda diyar ba
Malam ya ce, 鈥淜efa tsiyarki ke nan duk abin ki ai kya bari' na mutu sannan ki rufe ni ai k0?鈥�
Ya ja tsaki ya cimimiya kwarar dubu guda ya cilla mata ya juya zai tafi ya ga Saude tsaye rungume da kayan tallarta hawaye sun gama bata mata fuska.
Malam ya ce, 鈥淜e kuma fa lafiya?鈥�
Cikin muryar kuka Saude ta ce 鈥淜a yi haquri Baba don Allah wallahi bana san shi ba zan iya aurensa ba, sabo...
Malam ya katse ta ta hanyar fadar, 鈥淜e dalla Saurara mini kin jiki Ba kya son shi sai wa ki ke so?鈥�
Saude ta yi shiru tana faman shashshekar kuka Malam ya sake fadar 鈥淣a ce idan ba kya son shi, sai ubanwa kike so?Munafukar Allah,nankikaso ki jibge mana kita zama kitsufa a tasha kina talla, tunda kebaki da tunani ko Allah yataimaka kemaya kawo miki dauki, tunda ki ka tashi akwai bakon takalmin da ya taBa zuwa wurin ki da sunan so, iye?
Amma shi ne har kina da bakin magana. Shekarar ki nawa yanzu a duniya? Kin zauna kin jibge babu mai taya ki kek0 kishin kanki ba kya yi, kina kallon 鈥榶ar uwarki kullum wannan ya shiga wannan ya fita, harda masu motoci, amma saboda rashin kishin kai ba ki taba damuwa ba.鈥� mts! Ya wuce yana fadar.
鈥淚dankinada wandakikeso to saikituro shi ai lokaci bai qure miki ba daga nan har ranar daurin aurenki
Wani irin kuka ya Kara kwacewa Saude, ta aje kayan tallar ta yi dakinta da gudunta tana. wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Laure ta ja tsaki tatattara kayanta tana fadar, 鈥淜e
dai kya kai su idan kaya ne dan bakin ciki sai dai ya kashe ki don na gaba ya riga ya yi gaba har abada ba zaki iya kamo taba.鈥�
Saude ta sha kukanta har ta godewa Allah bata . da mai lallashinta haka ta kwanta har bacci barawo ya sure ta. Haka ta farka yau idanuwanta duk sun 鈥� kumbura sun yi jawur saboda kukan da ta sha jiya. Haka ta je tallanta ta dawo jikinta ba kuzari kana ganinta ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Ta yi zaman daBaro kan sumuntin tsakar dakin, don
kuwa dakin bai da arzikin k0 qaramar tabarma
Saude ta jingina da bangon dakin ta rafka wani ; uban tagumi ko tunanin me take? Oho 鈥榊ar Baba ta dago labulen tana mata wani shakakken kallo kafin
ta ce
鈥淚dan kin gama tagumin sai ki fito ga kayana na ki hado ki wanke mini. 鈥�
Saude ta dago da jajayen idanuwanta tana 芦 kallonta, haushi da baKin ciki suka turnuqe mata zuciya, tuni dama batun yau ba take jin takaicin abin da 鈥榊ar Baba ke mata ba sai ka ce ita ce babbar, ita ma kuma ita ce karamar.
鈥榊ar Baba ta ce, 鈥淜i ka tsaya kina kallona da wasu kananan idanuwanki can masu kama da na kwarkwata kixo ki min wanki na ce
Takaici ya kuma turnuke Saude cikin fusata ta ce, 鈥淲ai 鈥榊ar Baba me ki ka dauke ni ne jakar ki ko
kuma me? Karfa ki manta a girme na girme ki,amma ki rinka! yi min abu kamar wata yar da ki ka haifa. Ai ba 鈥榶ar wanki ki ka aje ba, da ki ka
dama can da ina miki Inna ce ke sani, amma ke baki isakisani inmiki wanki ba鈥� 鈥�
鈥榊ar Baba ta ce 鈥楨h, lallai wuyanki ya isa yanka, har ni ki ke gayawa magana yau k0 Saude dan kin ga Laure ba ta nan lallai za ki san kin yi da diya ba shegiya ba, za ki gani.鈥� Ta juya ta yi gaba.
Saude ta ja tsaki ta IaIIaBa ta kwanta ta ci gaba da nazarin abindayadameta. Bata ankaraba saidaita ji saukar kayan wanki a jikinta ta zbaura ta mike tana kallon mai wannan aikin.
0000000000
鈥淲ato kenan har鈥� yar iska ce har kin yi girman da 鈥榊ar Baba za ta sanya ki ki mata abu ki zage ta ki ce ba zakiyi ba.
鈥� To yau sai na ga uban da ya ,tsaya miki ki dauke su maza ki je ki wanke mata, ki shanya ki zauna su *bushe ki linke ki kai mata daki, tantiriya marar kunya, ai na godewa Allah morewa ta dama na ga rayuwarki ta wulakanta, kuma na yi nasara, in dai ina numfashi kin auri Garba Gurgu kin gama, bankadaddiya yanda na ga bayan uwarki da wannan
takadarin ke ma sai na ga naki. 鈥�
" Ta ja tsaki ta wuce tana fadar. 鈥淢unafukar banza!鈥� .
Wasu irin hawaye masu dumi suka zubo daga idanuwan Saude tasa bayan hannunta ta goge sannan ta' shiga tattara kayan wankin ta wuce tsakar gidan,
Ta. wanke su gaba daya abun bakin cikinta har da bireziya da dan paint, saboda kawai tsabar raini da wulakanci. Rayuwa kenan.
Kamar yanda mahaifinta ya ce za a. kawo kayan nagani-inaso, haka kuwa aka yi Garba Gurku ya aiko mata da kaya cikin Gari ya yi zafi, dinkakkiyar atamfa ce ta roba riga da zani sai dakakkiyar abaya kwaya daya, sai takalmin roba shi ma guda daya da sinqin sabulu guda da Katuwar 鈥檏walbar mai dangwali-yaBa, sai naira dubu a sama.
Laure ta dauki naira duban sannan. ta mikawa Saude kayan don ba abin da ya yi mata a cikin kayan. Wasu irin hawaye masu zafi suka ziraro daga idanuwanta tasa hannu ta karBi kayan ta wuce daki 鈥� da su.
Tana shiga ta wurgar da su tsakar dakin ta durkushe tana raira wani sabon kukan mai cin zuciya. Tabbas tana cikin halin da ya kamata a tausaya mata,Yayanta ya ringa yi mata gizo cikin idanuwanta ko wane hali yake yanzu? Saude ta sha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru
Abu wasa-wasa lokaci ya ci gaba da tafiya, Garba Gurgu ya ci gaba da yi wa Saude hidima, idan abun kirki ne sai Laure ta rike, idan kuma ta gajam tagajan ne sannan za ta ba ta, ita k0 ba ta taba kallon kayan ba don yanda ta tsani mai kayan haka su ma kayan ta tsane su.
鈥� Ranar: wata Laraba Saude ta dawo daga tallar safe, misalin qarfe daya na rana, Laure tace yau ba tallar rana ta je ta shirya za ta je ta dubo 鈥榶ar Garba Gurgu da ta haihu ta dawo gida wanka jiya ya zo ya gayawa Malarn. .
Wani bakin ciki ya tokarewa Saude wuya, ta rasa ma abin da za ta ce saboda takaici, ta wuce dakinta ta yi kwanciyarta, har aka soma kiran sallar La鈥檃sar, Laure ta ji shiru ta leko dakin nata ta ganta a kwance idonta biyu k0 motsin kirki ba ta yi.
Laure ta dauki sallallami tana fadar, 鈥淵anzu zuwa ki ka ki ka kwanta dan kin raina mutane, ya yi miki dadi sosai wallahi. To sai ki fito ki shirya in ga ubandaya isa ya hanaki kije dubiyannan ki ciro cikin kayan da yake kawo miki ki sanya kin ji na gaya miki鈥� Tana gama fada ta juya ta wuce abinta.
Wasu irin hawayen bakin ciki suka zirarowa Saude ta yunkura ta mike jikinta ba kwari, ta fito ta janyo ruwa cikin rijiya ta dauko sabulu guda cikin kayan nasa da ya kawo mata ta nufi bandaki ta yo wankanta wanda rabon da ta yi irinsa ba za ta iya tuna shekarar ba.
Tana gamawa ta fito ta nufi dakinta ta janyo mai ta shafawa fatar jikinta, ta zazzaga farar hoda a hannunta tamurzawa fuskarta, ta bude ledar da kayan ke ciki kala uku .ne daga wata atamfa 鈥榶ar
roba sai wani yadi mai santsi an yi masa dinkin riga da wanda, sai wani leshi marun an masa dinkin jaka tsaye.
Saude ta dauko shi ta saka ta Ciro takalmin robar
ta sanya ta kawo milk din hijabin da ke cikin kayan
ta sanya, sannan ta fltO zuciyarta na faman suya. A lokacin Laure da 鈥榊ar Baba na zaune gaban murhu
ana ta faman soyen kaji da sanrayin ta ya kawo
Saude ta dubi Laure da idanuwanta wadanda suke san zubar da hawaye ta ce, 鈥楴a fito.鈥�
Laure ta dago tana kallonta, alamun mamaki bayyane a fuskarta qarara, wanda har ta gaza danne shi a zuciyarta sai da ta furta.
鈥淪aude ke ce haka? Dube ta 鈥榊ar Baba ki ga abun mamaki.鈥�
鈥� Kallo daya 鈥榊ar Baba ta yi mata ta dauke kanta tare da jan tsaki, Laure ta kada kai kafin ta ce, 鈥淭o sai ki tafi k0 wa ki ke jira?鈥�
Haka Saude ta kama hanya jikinta a sanyaye ta yi. gaba. 鈥�
鈥� Gidan Garba Gnrgu yana can qasan unguwarsu ta baya, haka Saude ta taka~ da qafa. Gidan qaton gida ne ginin qasa,~rabin katangar duk ta zube a Kasa
wanda aka sa buhu aka zagaye. Saude tasa qafarta cikin dogon zauren wanda aka fito da Katuwar kwata ta tsakiyarsa har tsakar gidan,
gaban ta ne ya shiga faduwa lokacin da ta sa qafa cikin soron gidan, ba ta san irin tarbar da za a yi mata ba, ta san mugunta ce kawai ta sa Laure ta ce ta
zo gidan ba wani abu ba. Saude ta yi sallama a tsakar gidan wanda yake a hargitse sai ka rantse da Allah bai鈥檛aBa ganin Shara
ba ga wasu manyan tukwane da murahu a tsakiyar tsakar gidan ko鈥檌na komatsai ne a tsakar gidan ba masaka tsinke, ga yara nan suna ta faman tsalletsallensu a tsakargidan sai ka ce ba su taba ganin ruwa ba a rayuwarsu saboda tsabar Kazanta.
Saude ta Kara daga murya tana sallama sannan matan da ke ta faman zirga-zirga suka ankara da ita aka amsa mata tare da . yi mata maraba, jikinta a sanyaye ta qarasa cikin, gidan tana danne fargabar zuciyarta.
Daya daga cikin matan ta janyo kujera 鈥榶ar tsugunne ta miqa mata ta zauna suka shiga gaisawa, wasu su biyu babu riga a jikinsu sun saki nonuwa a waje sai ka ce silifas suna ta harkokin su babu abin da ya dame su, sai Karamar su ce keda daurin qirji. Kai da gani ka san an yi masu kisan Kuli, an kashesu ko kadan baza akirasu da mata ba.
Saude ta qakaro wani murmushi wanda iyakarsa saman laBBanta kafin ta ce, 鈥淣a zo ganin jariri ne.鈥�
Babbar cikin su ta ce, 鈥淎u! Ni dai na ce ba mu. ,
waye ki ba, suna daka ki shiga ki gan su.鈥�
mu kishi da jikannu wallahi, ba ta yiwuwa da sake an bawa mai kaza qafa鈥�
A daidai nan Saude ta fito tana qokarin sa takalmanta ta ji matar na fadar, 鈥淢unafuka ashe Ieken asiri ki ka zo in dai gidan Malam ne ki shigo kema ki zauna, sannu a hankali za ki koma yanda muke 鈥�
Sauran matan dai babu wadda ta tanka, harkar gabansu kawai suke. Saude ta sa takalminta dai ta yi waje, tana jin Garba ya biyo ta yana fadar.
鈥淭saya Saudatu ki ga dakin ki.鈥�
Bata tsaya kulashiba tayi gaba da hanzarinta sai sauritake dankokadan batasan ta hada ido dashi, munin shi da qazantar shi kadai ta isa tasa ta tsane shi, to balle ga shi tsohon najadu ga nakasa kai shi dai abun ya yi masa yawa.
Bata ankaraba tanata tafia cikin sauri tana zancen zuci, ba ta ji horn din da ake faman kwarara mata ba, saidai taji an hankadata gefe hankalin Hamid ya yi masifar tashi, ya yi saurin yin fakin din motarsa ya fito a guje: ya nufo inda take yana kokarin daga ta, Saude ta yi saurin mikewa dan gudun karya tabata shimaya dago da niyar yabata hakuri, su kai four eyes, ido hudu, wanda ya
haifarwa Hamid da bugun zuciya mai tsanani.
Cikin tsoro da rudewa Saude ta soma ba shi hakuri, kallonta yake ido cikin ido wani abu na faman zarya a cikin kirjin sa muryarsa a sanyaye ya ce.鈥�
Ai nine zanbaki hakuri nidana kadeki kiyi haquri wallahi ban lura da keba ne.鈥�
Saude ta kada masa kai sannan ta wuce shi abin
ta.
Hamid ya yi saurin bin ta yana fadar, 鈥楧on Allah dan tsaya mana 鈥榶anmata.鈥�
Saude ta waigo tana 鈥� kallonsa, ya dan gyara tsayuwarsa kafin ya ce 鈥楧on Allah idan ba za ki damu ba ki fada mini sunan ki.鈥� .
鈥淪aude.鈥� Ta ba shi amsa a taqaice.
Ya girgiza kai yana fadar, 鈥淣a鈥檃m Saudat, don Allah idan ba za ki damu ba kimin kwatancen gidanku
Saude ta waro ido tana kallon shi, alamun mamaki bayyane a fuskarta ta kasa ma magana, ya danyi murmusa kafin ya ce, 鈥淜i yi hakuri kar kice na fiya shishshigi da yawa;鈥�
' Saude ta dauke kanta kafin ta ce, 鈥淟afiya dai ko?
鈥� 鈥淟afiya kawai dai ina so inxo in Kara duba kine don ban sani ba ko wani abu ya same ki.鈥�
Saude ta wuce shi tana fadar, 鈥淣i babu abin da ya same ni.鈥� Hamid ya yi tsaye yana kallon tafiyarta hatta kusa Bacewa ganinsa, ya ja wani taqaitaccen murmushi
murmushi mai sauti tabbas yau zuciyarsa ta samu abinda takeso,zaicigabada binta harya samu ya samo kanta. Ya juya ya shiga motarsa ya bi ta a baya harkofar gidansu ya rakota batasanai ba, sannan ya koma abin sa.
Saude nashiga gida, Laure ta bitada kallo kafin ta ce, 鈥榃ai kin je gidan nasu kuwa?鈥�
Saude ta daga mata kai alamar eh laure ta yatsina fuska kafin tace 鈥淎mma abinda mamakine da akace min amaryarsa mugun kishine da ita aina dauka sai sun karya miki qafar baya.鈥� Ta ja tsaki mts!
鈥淪ai ki wuce kafin tallar yamma ta qarisa
Saude ta wuce dakinta simi-simi ba tare da ta sake tankawa ba. Tana shiga daki ta kwanta, wani irin abu ya tokare mata zuciya, ta lumshe idanuwanta fuskar mutumin nan ce ke mata gizo, har yanzu hancinta baidaina shakar kamshin turarensa ba mai sanyin kamshi.
Dama yace yanasonta tabbas da saitayi kukan dadi. Makaskanciya irin ta a ce irin wannan namijin yasota aidakamar wuya wai gurguwada auren nesa. K0 鈥榊ar Baba da ta fita komai ba ta samu kamarsa ba, ballantana ita mafi kaskanciya mai tsananin rauni Taja wani gwauron numfashi tare da
saurin kawar da abin dake zuciyarta, don ta san k0 a mafarkinta hakan ba zai taba samuwa ba.
Washe gari Saude ta dawo daga tallar safen ta, sannan ta dauro alwala ta yi sallah; sannan ta fita鈥� tsakar gida ta zauna, Laure ta sauke alalar aka zazzage mata a bokiti ta dauka ta fice abin ta.
Hanyarta ta kullum yau ma ta ita ta bi idonta na saman hanya ta wuce ta qofar gidan Alhaji Bashir, Hamid da ke zaune saman teburin maigadi ya ga tahowartaya zabura ya mike, ya dubi Malam maigadi yana fadar.
鈥淚na zuwa Baba bari in dawo.鈥� Bai jira abinda zai ce ba ya yi saurin bin ta dan kar ta Bace masa.
Saude ta tsinci muryarshi na fadar. 鈥淎ssalamu Alaikum. 鈥� Ta waigo tana kallon shi da mamaki a fuskarta ta
kasa bude baki balle ta iya furta wani abu, Hamid ya yi murmushi kafin ya ce, 鈥淩uwan zuma ne ni ba madaci ba na kasance mai began ki tun a lokacin da na soma ganin ki ba wai sha katafi ba, mene na tunanin a kan hakan?鈥�
Saude ta fara nutsuwa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wadda ta qawatu da dogon hanci da yalwatattun idanuwa wata nutsuwa 'ta dirar .mata muryarta a sanyaye ta ce, 鈥淶aBina ba tsakanin zuma k0 madaci ba ne, kyakkyawan zabina shi ne yawaita ayyuka, masu kyau da gujewa munanan dabi鈥檜 na kasance mai zurfin tunani da. Kwakwalwa ba da zuciya鈥� ba, me ye tunanin ka a kan hakan?鈥�
Hamid ya dan saurara kafin ya ce, 鈥淚kon Allah ga .shi nima yanzu haka Dady jirana yake, amma ba damuwa, ki fada masa zuwana gobe insha Allahu
zan dawo.鈥�
Saude ta amsa da to, sannan ya juya ya tafi ta raka shi da idanuwanta.
Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya. Mamaki da al鈥榓jabi su suka dabaibaye zuciyar Saude, har yanzu bata fidda ranta da cewa mafarki take ba, za ta iya farkawa a kowane irin lokaci. Ba
Washe gari Saude ta dauki tallar wainar .ta. Bayan ta siyar karfe sha daya da 鈥榶an mintuna ta dawo, Laure ta hada' ta da sanwar alala duk da matsananciyar ranar da ake kwalawa haka ta zauna a tsakar gidan gaban murhun sai gumi ke tsiyaya a jikinta.
Tamkar daga sama yaro ya shigo ya yi sallama, Saude ta amsa tana kallon shi, ya ce, 鈥淲ai' ana sallama da Malam in ji wani mutum a waje.鈥� Saude ta nuna masa dakin Laure da hannu tana fadar.
' 鈥淪higa can ka fada masu.鈥�
Yaron ya wuce ita kuma ta ci gaba da abin da take, yaron bai yi minti biyar da fita ba Malam Bala ya fito cikin shirin tafiya masallaci kasancewar yau
Juma鈥� a bai fita kasuwa da wuri yasa kai ya fice Tsawon wasu mintina da suka haura goma zuwasha
biyu sannan鈥� ya dawo gida yana faman Kwalawa
Laure kira鈥� . 鈥淟aurel Laurel! Laure!!! Wai kina ina ne nake ta
faman kira kin yi shiru
Ta hankado labule ta fito tana fadar, 鈥淲ai ya akai ne, ka keta faman kwala min kira sai ka ce yaki?鈥�
Malam Bala ya yi kwafa, 鈥淎mma dai ai kin san ruwa baya tsami banza, kin san dai daga jin kiran鈥� nan kin san da walaki.鈥� Laure ta ce 鈥楾o mu gani a qasa
Ya ce, 鈥楾abarma zaki ba ni dan gidan Alhaji' Bashir ne yazo wai wurin 鈥榶ata yana son a bashi izinin turo iyayensa maganar aurenta.鈥�
Inna Laure ta zaro qananan idanuwanta haqoran nan suka yo gaba sai ka ce kamfanin cokula ta ce 鈥淜ai don Allah yana ina? 鈥�
Malam ya ce, 鈥淵ana waje
鈥淎鈥檃 bari a kai masa tabarmar.鈥� Ta juya daa 鈥榟anzarinta ta nufi daki ta janyo masa tabarma bayan qaure ta fito fana fadar.
鈥淕a shi Malam ka shimfida masa a soro gatanan zuwa.鈥� Ya amsa ya juya da hanzarinsa har yana tuntube
Inna Laure ta nufi dakinta can kurya kan gado bonanza ta shiga inda 鈥榶ar Baba ke kwance tana faman sheka baccinta Inna Laure ta shiga tashinta.鈥� 鈥榊ar Baba ta bude ido da kyar cikin magagin barci. 鈥� 鈥�
Ki tashi da alla kin ji aikhairi yazo mana har 鈥� cikin gida, da rana tsaka.鈥�
IKilima ta ja wani鈥� tsaki ta juya daya barin ta ci gaba da baccinta, Inna Laure ta Kara bubbuga ta Ta zabura a fusace.
鈥淲ai mene ne don Allah za ki dame ni kawai ina baccina
Inna Laure ta ce, 鈥淜i tashi banza arziki ne ya zo mana da qafafuwansa dan gidan Alhaji Bashir yaron nan ya z0 wai neman auren ki tashi banza, banza ki shirya.鈥�
鈥榊ar, Baba ta zabaura ta tashi zaune idanuwanta a warwaje tana fadar, 鈥淜ai Laure don Allah da gaske ki ke?鈥�
Laure tace, 鈥楢鈥檃 ai sai ki tashi ki gani da idon ki yana soro shi da Babanki.鈥�
IKilima ta buga wani uban tsalle ta dire daga kan gadon, saboda doki, ta kwasa da gudu zata fita Laure ta yi saurin riqo ta.
鈥淜e da Allah tsaya haka za ki je sai ka ce wadda ta tabu, ai sai ki ja ya ce ya fasa, maza ki shirya da Allah karya gaji da jira. 鈥�
鈥榊ar Baba ta dan nutsu kafin ta ce, 鈥淏a za ki gane bane Laure yaron ya hadu yanda ba ki tsammani kyakkyawa ne, kuma dan gayu, daga qasar waje fa ya dawo ya kammala digiri dinsa. Laure idan na aure shi wallahi na gama more miji, ai duk samarina
korarsu zanyi "Ta dan yi shiru kadan kafin ta ce
鈥淭o wai ma me zan sanya?鈥� Laure ta ce, 鈥淜i sa wannan shaddar taki sabuwar
Ginznar nan tana yi miki kyau sosai.鈥�
鈥榊ar Baba ta kada kai alamar ta game, sannan ta juya ta bude akwatinta ta Ciro shaddar dinkin riga da siket ne ya sha aiki matuka, ta saka kayan wadanda suka dame ta matuka komai na jikinta ya flto. 鈥�
Ta zauna ta yi kwalliyarta sosai ta kawo dankwalinta ta 'kafa daurin鈥榥an mai suna ture-kaga tsiya, sannan ta saka dan kunne da sarka, ta mike ta janyo wani dan ficicin gyalenta mai kama da matacin koko saboda shara sharansa ta yafa, ta saka takalminta mai tudun dunduniya ta saka, ta dauko wata gingimemiyar jaka saikace waddazatabiki ta rataya a kafadarta, ta juyo tana kallon Laure tana wani murza idanuwa.
鈥淭oya kika ganni?鈥濃€�
Laure ta ce, 鈥淜in hadu qarshe 鈥榶ata ai shi yasa nake qara son ki, dan kuwa kyan ki daban yake dana sauran mata shi yasa kullum sai an mana sallama.鈥�
IKilima ta sheke da dariyar jin dadi na kwarzantawar da Lauren ta yi mata ' Malam ya hankado labule 鈥淲ai me take Jira ne har
yanzun kunsam jirafa bashi da dadi
Inna Laure ta ce, 鈥淎i ga ta nan fitowa Malam, ya yi hakuri. 鈥� Malam Bala ya saki labulen ya juya
鈥榊ar Baba ta dubi Laure ni鈥淣a tafi Laure.鈥�
鈥淎鈥檃 mu je in taka miki.鈥� Laure ta fada tana yake hakora.
A tare suka fito, Saude na durkushe a gaban murhu sai faman hawaye take saboda hayakin da ya turnuke ta, har ba ta iya ganin gabanta sai sharbar' mijina take.
Suna isowa inda take Laure ta dube ta, 鈥楾o 鈥榶ar iska munafuka wutar ce ba za ki hura ba k0 so ki ke alalan ta jike a cikin ruwa, annamimiya munafuka.鈥� Ta duma mata wani uban kulli wanda ya sa ta yunkurin amai ta zabura ta mike tana faman sosa inda ta 'maka mata dundun. .
Ta ce 鈥榃allahi Inna itatuwan ne danyu sun ki su kama.鈥�
Inna Laure ta haure ta da kafa, 鈥楰an ubanki ke da danyun yanzu dan kina munafuka wadannan itacen' sune danyun,to idan ma kinbarta tayi danya dan kanki,danni yaddah kika fita da ita haka zaki saida ta ko ta kwabo ban ce ki dawo da ita gidan nan ba, wuta kuma kar ki hura ki yi shekaru dubu anan
Saude ta surce majina tare da goge ruwan hawayen da ke zuba daga idanuwanta, ta duke. ta ci gaba da hura wutar da baki, amma illahirin zuciyarta
LOL YA abin yake NE GUN WA HAMID YAZO IKILIMA KO SAUDE
MUCi GABA Dakasancewa DA ADmin Dboy DONJIN yadda WANNAN TAQADDAMA ZATACI gaba DA KASANCEWA
[1/19, 5:11 PM] I love my mum: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[12:17PM, 02/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: [1/19, 5:14 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
*CHAPTER 13*
a cunkushe take saboda duk abin da ake tana jin 鈥榊ar Baba ta tabe: baki ta wucc soron gidan, Saude ta tsaya da hura wutar tana kallonta idonta ya ciko da hawayce
Hamid yana zaune a barin tabarma yana karkada kafafuwansa ya yi irin zaman nan na masu cin tuwo, 鈥榊ar Baba ta jingina da bangon soro ta kafe shi da ido cikin ido tana wani murmurtsa idanu.
Hamid ya tsaya yana qare mata kallo cike da mamamki ya ce, 鈥淜e kuma fa wace ce?鈥�
鈥榊ar Baba ta鈥榶i wani qasaitaccen murmushi irin na gogaggun yan duniya kafin ta ce 鈥淎i ni ce iKilima wadda aka fi kira da 鈥榊ar Baba, da alama baka gane ni ba ko?鈥� Ta Kara jan wani munafukin murmushi tana fadar.
鈥淜owa ma idan nasa kayan nan haka yake fade: beganeni:ba ashe dama haka nake da kyau hummml Kayan suna mini kyau sosai.鈥�
Wani takaici da haushi suka kama Hamid cikin takaici ya ce, 鈥淜e da Allah saurara kin ji bana can shirme da sakarci kin, Saudat na ce a kira mini ita nake nema ba wai keba kin gane? 鈥�
鈥榊ar Baba ta ji tamkar ya watsa mata ruwan zafi a zuciya cikin Bacin rai ta ce, 鈥淎i ba ita Baba ya ce kana nema ba ni ya ce kana nema
Hamid ya dan sassauta murya, 鈥淜in ga kiyi hakuri don Allah ki je ki kira mini ita ta sanda zuwana please ban san ku biyu bane a gidan."
鈥榊ar Baba ta waro ido tana kallon shi bakinta na fadar, 鈥淜utumar... wallahi ba zan je ba har ma ta isa in kula ta 鈥榶ar tallan gidan namu ba zan jeba wallahi, sai dai ka daskare a nan.鈥�
Ta juya za ta tafi Hamid ya yi wani murmushin takaici ya zura hannu cikin aljihu ya ciro kudi鈥� yan dan biyar biyar sababbi dal guda hudu ya miqa mata.
鈥楢n shi ga wannan ladan kiran nata idan ba za ki kira ta don Allah ba. 鈥�
鈥榊ar Baba ta sa hannu ta fizge kudin tana fadar, 鈥淎i raba mugu da makami ibada ne鈥� Ta juya ta yi cikin gida.
Laure ta tarye ta tana fadar, 鈥榊a akai ne?"
鈥榊at Baba ta fashe da kuka tana fadar, 鈥淲ai Laure wai ba ni yake so ba, wai SAUDE yakeso.鈥�
Laure ta ja wata ashariya 鈥楰an habbm.... Bake yake soba uwar wa yake so?鈥�
鈥� 鈥淵ar Baba ta nuna' mata kudin da ya 'ba ta, 鈥淜in gama waiyabani inkiramasa ita
Laure tace daukomin mayafina naje na sameshi 鈥榊ar Baba ta kwasa da gudunta ta dauko mata mayafinta ta baza saman kafada ta nufi soron kamar an hankada ta.
Hamid yana zaune hmnunsa riqe da qatuwar
wayarsa yana wasa da ita, yana ganinta ya fadada fuskarsa da fara鈥檃.
鈥淪annu da fitowa Umma barka da rana.鈥� Inna Laure ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa
sannan ta gyara tsayuwarta tana fadar, 鈥淜ai ne bakon Saude?鈥�
Ya dan sunkuyar da kai qasa alamun kunya kafin
ya ce 鈥淓h nine Umma.鈥�
Laure ta kuma gyara mayafinta mai kama da an kwato shi daga bakin kura ta ce 鈥淭o Saude dai da ka ke ganinta shegiya ce 鈥榶ar gaba da Fatiha, ce yarnan da ka gani kuwa ni ce mahaifiyarta nina haife ta da cikina, kuma ka san an cewa shi dan gado sai ya zarta to Saude kuwa har tace ban iya ba, dan wurin gantali da yawon bariki gari gari babu inda Saude bata zaga' ba. Kai in taqaice maka har cikin shege sai da ta yi.鈥�
Wani irin abu ya dakarwa Hamid zuciya mai zafin gaske ya samu da kyar Ya iya hadiye shi kafin ya iya fadar, 鈥淎mma Umma da mamaki a gaskiya ba zan Boye miki ba Saude ba ta yi wa rayuwarta adalci ba sululu kenan macijin sari ka noqe
Ki yi hakuri Umma insha Allahu ba zan guje mataba don wannan qaddarar ta fada nayi
miki aIqawarin auranta a hakan in ceto rayuwarta.鈥�
Laure ta ce, 鈥淎鈥檃 ahir!.Dinka karka fara don ba zaka taba iya ceto Saude ba saboda kin Allah irinna yarinyarnan ya wuce tunanin ka鈥� Laure ta sa kukan munafurci har da su fyace majina.
Hamid yana kallonta saidata gaji dankanta ta dan sassauta ta ci gaba da fadar, 鈥楧an nan shu鈥檜mancin Saude yana ci min zuciya wai yarinyar hartasan tanemi mace 鈥榶ar uwarta,bacin mazan datakebi yandakasan karyar mazahaka take.
Na zubarwa Saude ciki yakai biyar a asibiti har sun haddace mu, sun gaji idan mukaje ma yanzu kararmu sukace zasuyi wai saboda zubdawa Saude cikin da muke yakai iyaka.鈥�
Hamid ya ce鈥淒uk wannan ba matsala ba ce Umma, wallahi ahakan insha Allahu indai saude mai shiryuwa ce sai na shiryar da ita.鈥�
Inna Laure tace, 鈥淜ai malam,Saude bazata taba shiryuwa ba saboda ba ta tsoron Allah k0 kadan babu Allah a ranta.鈥�
Hamid ya ce 鈥淎i Umma Islamiyya zan sanya ta insha Allahu kekanki saikinyi mamakin yanda zata shiryu ta nutsu.鈥�
Inna Laure tace鈥淒annan kenan bakasan Saude ba har yanzu, ai kwakwalwarta a dode take ba
ta daukar komai ba ka da abin da Saude ke iya dauka ballentana harta iya haddace shi.鈥�
Ya ce, 鈥淎i Umma babu abin da yafi qarfin addu鈥檃, sai mu taya ta da addu鈥檃 insha Allahu za mu yi nasara amma ni ina son ta kuma wallahi aurenta zanyu
Inna Laure ta harzuka cikin haushi ta ce 鈥淭okai baza,a auramaka itadinba 鈥榶atadaicetonayi mata miji koka tashi kabarnan yanzunnan wallahi k0 in maka ihu kwarto, dan iska kai ana gwada maka Annabi kana rintse ido.鈥�
Hamid ya mike ya ajiye mata bandir din yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya ce, 鈥淶an tafi Umma ga wannan a sai sabulu zan dawo sati mai zuwa da fatan za ki sauko daga dokin qiyayyar da kika hau, na gode
Ya juya ya fice daga soron ya bar Laure tsaye dakam tamkar wadda aka kafe sai zazzare na mujiya take a kan kudin, wani abu na yi mata zarya a zuciya ta duke ta suri kudin ta yi cikin gida tana kwalawa Saude .kira Sande da take duke gaban murhu ta yunkura da niyartatashi, amma ina dukanda Laure ta soma
kai mata yasa ta duke babu shiri, Laure ta janyo
bakin wuta tana faman dukanta sai ka cc yaqi fidi
take. 鈥淵au sai na kashe ki har lahira in ga ta
soyayya, ke nan har kin isa wani ya ce yana son ki a hakan. To idan ma farar fatar ce ta janyo shi yau
sai na lalata ta.鈥� Tun Saude na ihu har ta soma Kokarin kwatar
kanta, 鈥榊ar Baba ta tare ta tana fadar, 鈥楲aure fuskar za ki toya ki lalata mata ita mu ga ta kyau da iyayi.鈥�
Saude .ta sa wata irin kururuwa, ta kwace daga hannun 鈥榊ar Baba ta yi dakinta ta maida qofa ta rufe, tana jin Laure na fadar k0 ta bude ko ta cin nawa dakin wuta amma ba ta motsa ba.
Kuka take sosai kamar ranta zai flta, dan Laure duk ta tattaya mata jiki da bakin wuta abin ka ga jar fata duk jikinta ya yi jawur. Ai kuwa nan ta sulale Kasa ta zauna tana faman kukanta.
Tabbas ya zame mata wajibi ta cirewa zuciyana kwadayin wata rayuwa mai dadi, dan ta tabbatarwa kanta Inna Laure ba za ta taBa barinta
ba, tasa hannu tana sharar kwalla. Inna Laure ta sake bubbuga qofar tana fadar,
鈥淪ai ki flto ki daukar mini talla ta in ba haka ba in karya kyauran in shigo.鈥�
Yadda ta ke dukan kyauren da Karfinta ya tabbatarwa Saude za ta iya ma abin da ya fi hakan, ta ta miKe tana kallon kayan jikinta, tun leshin da ta saka ne ta je gidan Garba Gurgu ne a jikinta, har yanzu ga shi Laure duk ta qona shi. Ta dauki hijabinta ta sanya ta bude kofar ta fito, Laure ta kai mata wani duka tana fadar.
鈥溾€橸ar iska munafuka!鈥�
Ta watsa mata kayan hannunta, 鈥楰arbi maza ki canza kayan jikin ki duk wani abu da ki ka san na kwalliya ne a cikin dakin nan ki ki miqo mini shi yau sai na ga qaryar soyayya ai dai sai da kyan aka soyayyar ko to zan gani.鈥�
Saude ta amsa ta koma dakin, wata kodaddiyar atamfa ce riga da zani ba dankwali, rigar sai a hada irinta mutum hudu su shiga ciki ga ta duk ta yage saboda tsufa. Sai zanin Jaka tsaye ya yi matukar shan jiki ya sha gamun baki har wuri hudu, ga shi babu dankwali 'sai wata abaya, hawaye suka ciko a idanuwan ta tausayin kanta ya kamata ta cire kayan jikinta ta sanya wadanda ta ba tan, sannan ta tattara komai na cikin dakin ta fito da shi.
Laure ta kwashe tana fadar 鈥淢unafukar banza, kuma wallahi ki sake in ji labarin kin tsaya kin saurari matsiyacin yaron nan na rantse da Allah sai
na lahira ya fi ki jin dadi, 鈥榶ar iska tambadaddiya.鈥� Ta sa qafa ta haure ta sannan ta wuce
Saude ta dauki bokitin tallarta tasa kai ta fita, tana faman sharar kwalla. Rayuwa kenan ita dai ta san ba ta daga cikin wadanda sukai sa鈥檃r rayuwa a duniya.
Tana tafe tana sharar kwalla tana zancen zuci, ba ta ankara ba sai dai ta ga mutum a gabanta, wani irin kallo yake mata mai cike da mamaki muryarsa a sarkake ya ce Lafiya Saudat, wace irin shiga ce wannan laflyarki qalau kuwa?鈥�
' Saude tasa hannunta guda tana goge hawayenta, ta soma magana cikin kuka.
鈥淟afiyata lau don Allah ka yi hakuri ka flta daga rayuwata na roqeka.鈥�
Hamid ya girgiza kai yana fadar, 鈥淚mpossible, wallahi abin da ba zai taBa yiwuwa ba kenan, sai dai idan har son ki zunubi neto na ratayawa kaina alhakinsa, amma ba zan taBa barin ki ba.鈥�
Saude ta tsaya da kukanta tana kallon shi kafin
ta ce, 鈥楳e yasa ba xaka rabu da ni ba, k0 kana san jefa zuciyata ne cikin bala鈥檌n da ba zan iya flta ba? . Wannan kukan da ka ga ina yi duk ta dalilinka ne.鈥� Hamid ya ce 鈥淣a ji na dauka, amma don. Allah ki yi hakuri ki bani kadan daga cikin labarin ki ni
nayi miki alkawarin taimaka miki da duk wata gudun mawar da kike buqata."
Hawayen da suka tsaya da zuba daga idanuwan saude suka Ci gaba da zubowa tana sharBar majina kana ta fara magana.
鈥淜amar yanda ka sani sunana Saude, tunda na . tasona bude idanuwana na ganni tare da Yayana,shine uwata shi ne ubana shine komai nawa. Bai barin nayi kuka , kullum burin shi ya samamin farin ciki da gatan da na rasa a rayuwa,
Ni kuwa burina kullum in matsa masa in sanya shi yimin abinda baidai konyinsa
Hamid ya ce, 鈥淭o yanzu yana ina shi Yayan naki?
鈥� Saude ta Kara rushewa da kuka kafinn ta ce . an raba ni da shi, su suka raba ni da Yayana.鈥�
Ya ce, 鈥楽u waye?鈥�
Muryarta na rawa cikin kuka ta ce, 鈥淏aba da inna Laure.鈥�
Hamid ya ja wani numfashi mai nauyi yana jin yanda take ta faman kuka da shashsheka tausayinta mai tsanani ya shige shi, muryar shi a sanyaye yake magana.
鈥淚na mahaiflyarki da mahaifinki su ke?"
Saude ta ce, 鈥淏an san inda mahaifiyata take ba,
Ban taBa ganinta ba, wannan kuma da ka gani shi
ne mahaifina, Inna Laure kuma matarsa ce 鈥榶ar Baba ita kuma qanwata ce
Hamid ya sake sauke wani nannauyan numfashi ya fahimci yarinyar tana cikin matsala, ya zuba mata idanuwansa farare tas cikin sanyin muryarsa ya ce, 鈥淜i yi hakuri Saudat na fahimci irin abin da ki keji a zuciyarki, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu na yi miki alqawarin taimaka miki da dukkanin karfina in dai ina raye sai na daga darajarki a duniya, sai kuma na wanzar da murmushi a idanuwan da Yaya ya bari cikin hawaye.鈥�
Ya dan qara numfasawa kafin ya ce 鈥淜i je
" 'lallar ki dawo, zan zo da daddare in same ki wurin tallarki za mu yi magana, amma don Allah ki daina kukan nan haka nan kin ji?鈥�
Saude ta daga masa kai tana goge hawayen da
ke fuskarta, ya dan tsura mata ido da murmushi a kumatunsa ya ce, 鈥淭o dan yi murmushi mana beauty
*Dukda batasan abindayace ba,ammatayi murmushin kuma kalmar beauty din ta yi mata鈥� dadin sauraro a kunne. Sai da ya ga tafiyarta
sannan shima ya juya ya tafi zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa.
Da yamma likis Saude ta dawo daga wurin tallarta Laure ta jibgo uban wanki, sannan tace ta ' dora sanwar tuwan dare. Saude ta duka a gun ta yi kukanta har ta gaji sannan ta ja ruwa ta dora sanwar ta dawo ta ci gaba da wankin.
Ana gama sallar Magariba Malam Bala ya dawo gidan, Laure ta shimfida masa tabarma a
tsakar gida ta kawo masa fura da mafici ta zauna gefensa.
Malam Bala ya bude furar ya soma sha, sannan
ya dubi Laure yana fadar, 鈥淲ai ya suka yi da yaron nan ne Laure?鈥�
Ta taBe baki tare da furta, 鈥淯hmm! Malam kenan, ai yaron dan iska ne takadari kana ganinsa kamar na kirki suna hira da 鈥榊ar Baba ya nemi taushe ta cikin zaure Allah ya rufa asiri yarinyar nan ta yi ihu, na kwaso da gudu na raka shi da bakin wuta har waje, mutane na ta bani hakuri suna fadar in kyale shi ai ni鈥檞annan abu ya ci min zuciya wallahi har kuka na yi.
Yanzu dan kawai an gan mu talakawa matsiyata shine za a shigo har cikin gida a ci zarafin mu. Kai Malam wannan abu da me ya yi kama?鈥� .
Tunda ta fara zancen 鈥榶a鈥檡an cikin Saude suka fara juyawa wani irin gumi ya shiga tsatstsafo
mata, take juwa ta kwashe ta, sai dai ta ganta zaune a gefen bokiti.
Malam da tunda ta fara zancen ya hau sallallami, ai sai ya rufe furar yana fadar, 鈥淲ai harni za a ciwa mutunci a garin nan Laure na rantse miki da Allah sai na yi kararsa kotu, kuma ta addinin Musulunci.鈥�
Laure ta ce 鈥楢a, Malam abin ai duk bai kai na kotu ba wurin mahaifinsa za ka gobe tunda sassafe ka kai qararsa ka ce ya jawa dansa kunne ga abin da ya yi maka in ba haka ba za ka sa hukuma ta
(shiga tsakaninku.鈥�
Bakin ciki ya cika malam Bala ya zabura ya
mike ya suri buta ya nufi bandaki.
Laure ta tabe baki ta raka shi da harara a zuciyarta tana fadar sauna kawai. Ta yunkura ta mike ta dubi Saude da ke 'zaunc ta ce, 鈥淭oke kuma tsohuwar munafuka kin zauna kin kasa kunne kina sauraran jama鈥榓 sai ki tashi ki dauki tallar gyadar ki tafl idan kin dawo kin qarasa wankin tunda cinikin na yauzu ne."
Saude ta lallaba ta mike tana jin tamkar za ta
fadi ta dauki tallar ta ficee, kuka maya gagareta idanuwanta sun yashee babu komai cikin zuciyarta sai duhu. ' 鈥楰0 minti goma bata yi da zama ba ta hango shi ya nufo inda take; yau sanye yake cikin manyan kaya, 鈥榥a wani lallausan yadi milk colouz; mai hasken gaske dukda a'cikin duhu ne amma bata kasa ganin shekin yadin ba, kansa yana sanye da hula baka yasa bakin takalmi a Kafafuwansa, tun kafin ya Karaso kamshin tuiarensa ya daki hancin Saude ta lumshe idanuwanta, sai a lokacin wasu
hawaye suka tarar mata 鈥� Hamid ya yi mata sallama tare da durKusawa gabanta, muryarsa a sanyaye ya ce 鈥淪annunki yan matana barka da Kokari.鈥� '
Saude ta bude idanuwanta tana kallonsa. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka ziraro 鈥� 鈥� Hamid ya mike tsaye ya ciro farin hankicif
Dinsa daga cikin aljihu ya miqa mata, Saude ta girgiza masa kai don ta san k0 rike hankicif dinma kadai ta yi sai ya yi dauda, to balle ta goge fuska dashi wai sunan wani wai shi 鈥�
Danduwala.
. Hamid ya sake mika mata hankicif. din yana fadar :鈥榃allahi sai kin goge garama ki karBa kawai鈥� 鈥�
' Jim yanda ya yi saurin rantsuwar ne yasa Saude
ta amsa ta goge hawayen, ya ce, 鈥淭o bani abuna鈥�
Ta yi wani dan taqaitaccen murmushin da bai , wuce kan labbanta ba ta ya qara goge fuskar shi da shi sannan ya saka a aljihu yana fadar.
鈥淲annan tafiyar yau ba ta ki ba ce wurin Baba nazo don haka ni kin ga taflyata."
Bai jira abin da za ta ceba ya juya ya tafi abinsa zuciyar Saude ta qarasa karyewa ta kifa kanta saman kayan tallar tana rera wani irin kuka mai cin zuciya. .
Hamid ya karasa Kofar gidan da qarfin zuciyarsa ya aiki yaro ya yi masa sallama da Malam Bala. Yaron bai jima da fitowa ba ya ce ga 鈥� shi nan zuwa, sai ga Malam Bala ya fito da alama masallaci za shi saboda an fara kiran sallar Isha鈥檌, yana ganin Hamid a qofar gidansa ya ja ya tsaya yana fadar.
鈥淢alam laflya?鈥�
Hamid ya durKusa har qasa yana gaishe shi. Malam Bala ya ce鈥淜ai dakata ban san rashin kunya ka ji har ni za ka dauka mutumin banza da WOfl, to ka je komai ka yi dan kanka ka, Allah ya isa tsakanina da kai, duk da ka gan ni talaka ina da wadatar zuci.鈥�
Mamaki ya kashe Hamid ya dago yana kallon
Malam muryar shi cike da rudani ya ce Don girman Allah ka yi hakuri Baba wallahi ban san abin
da nyi ba wanda kake fadarsa a yanzu芦 Malam Bala ya ce 鈥楢i dama ba zaka san abin da kake; fada a kansa ba, tunda ka ci idon dan akuya ' amma abin da nake so da kai anan shi ne ka tashi ka ba ni Wuri kar in sake ganin ka gifta k0 qofar gidan nan, kuma zanje in samu mahaifin naka ya yi maka tsakani da鈥� ya yana mutumin banza kawai鈥� Yana gama fada ya juya zai tafi, Hamid na kiran 鈥� Baba don Allah ka saurare ni, amma bai kula shi ba , ya yi gaba Wani abu ya tsaya zuciyar Hamid, ya lallaba . 鈥� 鈥榶a mike jikinsa ya yi masa masifar sanyi ya nufi 鈥� inda Sande take zaune tana faman raira kukanta. 鈥� 鈥� 芦 Tausayinta ya lullube shi ya kura mata ido ' na wani dan lokaci kafin ya soma magana muryarsa a ' sanyaye ya ce鈥淏a zan hana ki kiyi kuka ba Saudat, 芦 dan zubar hawayenki ya zama dole na fahimci abin da aka shirya mana, amma don Allah ki yi haquri kamar yadda na dauki alkawari鈥檔 taimaka miki ba . zan fasa ba Saudat da yardar Allah sai na ga rayuwarki ta inganta, kar ma Wannan abun ya dame ki ki yi hakuri kinji share hawayen ki karma ki Jawa kan ki
. ciwon kai鈥� ' Ya samu ya lallasheta ta yi shiru sannan ya tafi zuciyarsa na faman saqe-sake 鈥�
Washe gari da sanyin saflya Malam Bala ya shirya ya nufi gidan Alhaji Bashir saboda yanda Laure ke ta faman ingiza shi. A kofar gidansa ya same shi zaune saman mota da News paper a hannunsa yana dubawa.
Malam ya yi masa sallama, Alhaji Bashir ya dago tare da amsa masa cikin sakin fuska ya miqa
. masa hannu su kai musabaha. Malam Bala ya ce
鈥楧ama Alhaji wajen ka nazo.鈥�
Alhaji Bashir ya ce, 鈥楾o mu shiga daga ciki k0?鈥�
鈥淎鈥檃 daga nan ma ya isa, Kara na kawo maka.鈥�
Alhaji Bashir ya ce, 鈥楰ara kuma tawa?鈥�
Ya ce 鈥楧anka Hamid na kawo maka qararsa ka ja masa kunne dan kuwa ya shiga har cikin gidana zai keta mini haddin鈥� ya shi yasa na zo wurinka na kawo maka kashedinsa, don kar naje in dauki mataki kaga anatare babu dadi,don haka nazowurinka kai masa kashedi da iyalina.鈥�
Alhaji Bashir da ya nutsu yana kallonsa mamaki ya dabaibayeshi muryar shi a sanyaye ya ce, 鈥淟allai ka haifi yaro ba ka haifl halinsa ba, don Allah ka yi haquri Malam in dai nina haifi Hamid ya gama bi k0 ta gefen gidanka kayi haKuri don Allah, don Annabi.鈥�
Malam ya ce, 鈥淭o ni dai kashedi na kawo maka
ka ja masa kunne.鈥�
Alhaji Bashir ya ce, 鈥業nsha Allahu.鈥� Sannan ya juya ya Lafi buzun-buzun.
Alhaji Bashir ya sauke wani gwauron numfashi, sannan ya yunqura ya nufl cikin gidan zuciyarsa a cunkushe ya shiga falon gidan, babu kowa a falon sai Hajiya Hanifa tana tsaye tana goge-gogenta a falon, yana shigowa ta tsaya da aikin da take tana kallon maigidan nata bakinta na fad'ar.
鈥淟atiya dai k0 Alhaji?鈥�
Muryarshi ba dadi ya ce, 鈥淚na yaron nan yake?鈥�
Hajiya Hanifa ta ce, 鈥淵ana dakinsa ka san ai bai farka ba yanzu.鈥� Alhaji Bashir ya ce tado mini shi maza-maza.
Jikin Hajiya Hanifa na rawa ta nufi kofar dakin Hamid din. ta kwankwasa masa yana kwance nannad鈥榚 cikin bargo yana Sheqa barcinsa, saboda rashin baccin da ya samu jiya.
Ya bude idanuwansa tare da yunkurawa ya mike, yazo ya bude kofar, Hajiya ta dube shi kafin ta ce 鈥淜a je Abbanka na falo yana jiran ka Ya amsa da. to, sannan ya juya ya koma ciki ya nufi bandaki ya wanko bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya dauko jallabiyarsa ya sanya ya fito
Alhaji Bashir yana tsaye inda yake har Hamid ya qaraso yana qokarin dukawa ya gaishe da mahaifin nasa, ya ji saukar wani gigitaccen mari ya ratsa .
Kunnensa ya dago da sauri yana kallon sa, cikin Bacin rai Aihaji Bashlr ya soma fada鈥淣i zaka dauka dan iska k0 Hamid dama abinda. ka koyo kenan a qasar wajen da na tura ka. Ni zaka jawa; abin fada a cikin garin nan. To baka isaba., maza ka tattara yanaka-yanaka ka koma Kaduna, yau
ba sai gobe ba ka je ka kula da kamfanina tunda aikin gwamnatin bai zama dole ba, ba zaka zauna nan ka ja mini abun kunya ba, dama shi yasa da aka ce ka je ka nemi yarinyar nan Zainab kaqi saboda ba ka gaji da barbada ba, ka yi daidai ka kyauta tashi ka ba ni wuri.鈥� Jikin Hamid ya yi matukar yin sanyi ya miqe a sanyaye tare da fadar, 鈥淎 yi h akuri." Ya juya ya koma dakinsa ya kwanta, tunani ya addabi zuciyarsa 鈥榶a rasa hanyar da zai bi ya taimaki yarinyar nan, ya 鈥� lusmhe idanuwansa yana jin wani abu na masa
yawo.
Ya san fushin mahaifinsa yana fushi da shi ya yi kwana uku, tabbas kuma dole ya tafi Kaduna tunda ran mahaifin nasa ya Baci, ya lallaBa ya mike ya cire jallabiyar da ke jikinsa ya fada bandakin da ke cikin dakinsa.
Saude ta dawo daga tallan safenta ta iske Laure Zaune itada Malam Bala suna tattauna magana!
Hamid, ta a jiye bokitin wainar ta 'bama Laure kudin, ta karba tana kirgawa sannan ta ,dubeta tana fadar.
鈥淛eki ga wake can ki kai markaden alala.鈥�
Saude ta amsa da to, sannan ta wuce Malam Bala ya dubi Laure yana fadar, 鈥淜in ga na ma mance, Malam Garba ya fada min za"a kawo kayan sa ranar yarinyar nan gobe
Laure ta cc, 鈥淎i garama a gaggauta Malam mu kawar da yaran nan mu huta.鈥� 鈥�
Iya abin da da Saude 鈥檛a ji kenan 鈥檛a fice tana jin tamkar za ta kifa saboda tashin hankali da fargaba. Haka ta je ta kai markadan ta dawo ta dafa alalar duk Laure na zaune tana kallonta, ta gama ta zauna ta Kirga mata a bokiti, sannan ta dauka ta tafi
Hamid da ke kokarun sanya jakarsa a mota ya hango ta ya rufe motar da sauri 鈥� ya nufo ta da murmushi a fuskarsa ya ce, 鈥淩anki shi dade barka da
fitowa.鈥� Saude ta waigo tana kallonsa kafin ta gaishe shi
da dakusasshiyar muryarta. Hamid yargyara tsayuwa yana fadar. 鈥淒ama ke nake jira ki taho mu yi magana da tun dazu na Hamid ya ce 鈥楰inga wannan fitowar wallahi Kaduna zan tafi yanzu yanzun nan mahaifina ya tura ni amma karki damu kwana uku kaWai zan yi in
dawo saboda maganar ki, akwai wata hukumar kula da haqkin mata zanje ofiss din su a kan maganar ki
Saude ta daga masa kai alamar eh ya yasa hannu cikin aljihu ya Ciro kudi masu yawa 鈥榶an yan naira dari biyar biyar guda ashirin ya miqa mata yana fadar 鈥楪a wannan ki riqe ki yi amfani da su kafin in dawo.鈥�
Saude ta zaro idonta wadanda suka ciko da hawaye, ta girgiza masa kai alamar a鈥檃, Hamid ya hade fuska yana kallonta ya ce 鈥淜arbi na ce mana me ye haka?鈥� 鈥�
Ganin yanda ya hade fuska yasa Saude ta sa hannu ta karBa tana fadar, 鈥淣a gode.鈥� Ya zaro wata waya cikin aljihunsa 鈥榶ar qarama mai kyau ya mika mata.
鈥淕a wannan ki riqe ta hannun ki zan rinka kiran ki mu yi magana.鈥�
Saude ta karBa ya juya yana fadar, 鈥淪ai na dawo.鈥� Saude ta juya da niyar taflya su kai ido hudu
da 鈥榊ar Baba tana tsaye tana kallon su, suna hada ido 鈥榊ar Baba ta ja kwafa tana kada kai ta wuce 'Hankalin Saude ya yi masifar tashi wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta ta ji tamkar ta zubar da kudin saboda firgita, cikin tsoro ta je tallar yau ta dawo cike da tsoron irin hukuncin da za ai mata. Haka ta shigo gidan 鈥榯ana faman sanda kamar munafuka a tsakar gida ta samu Laure da dillaliya
suna zaune. Ita iyan tana kan tabarma, ita kuwa dillaliya tana kan kujera 鈥榶ar tsugunne. Saude ta durkusa tana gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Laure kudin tallar nata, ta karBa ta sake mika mata hannu.
鈥淏a ni sauran wanda kwarton naki ya baki
Jikin Saude na rawa ta ciro kudin da wayar ta mika mata, Laure ta shiga jujjuya wayar a hannunta da kudin tana taBe baki ta dubi dillaliya tana fadar.
鈥淒uba ki ga fa.鈥�
Dillaliya ta karba tana gani, ta dago tana kallon Laure tana fadar, 鈥淎mma ni sai nake ganin kamar wata banza ce ta sauko muku daga sama, kawai ki yi kwance-kwance kinada abun duniya idan ma yaudara ce ta kawo sa ke dai me ya dame ki ita ta jiyo.鈥�
Laure ta ce, 鈥淗mm! Dillaliya kenan ba zaki gane ba yaron fa da gaske aurenta zai yi ba wai da wasa ba.鈥�
Dillaliya ta dan yi shiru kafin ta ce, 鈥淭o yanzu ya ki ke ganin za a yi?鈥�
Laure ta ce, 鈥淕askiya na fara tsora ta da lamarin nan karfa danhakin dakaraina yazo yatsone maka ido. Shi yasa na kira ki kawai ki dauke ta ki tafi da ita AIKATAU cikin gidaje har zuwa lokacin bikinta shekara guda za a sanya ranar daurin aurenta sai ki taho da ita kawai kin ga na yi maganin takadaranci k0 ba haka ba?鈥� Dillaliya ta ce, 鈥淎I ko kin kawo shawara Laure, Abuja ma zan tafi da ita gidan wani sabon dan Majalisa, mai tashen kudi, wata kawata ce ta yi min maganar kai masu ma鈥檃ikata gidan, don haka ta shirya gobe zan zo in dauke ta da sassafe mu tafl, duk wata
kina da dubunki biyar zan rinka karBo miki na albashinta.鈥�
Dadi ya kama Laure ta ce 鈥淎llah ya kai mu Kawata, tun Asuba ma zan tasheta.鈥�
Dillaliya ta ce, 鈥淎mma kina ganin ba za mu samu matsala da mahaifinta ba?鈥�
Laure ta ja wani gajeran tsaki tana fadar, 鈥淜e kuma da sokawa zance wuqa kike wannan qotan wake san ya shi a lissafi ai sai yanda na yi da shi.鈥�
Dillaliya ta ce 鈥淭o shi kenan babu matsala 鈥榶ar
uwa. 鈥� . Duk labarinsu Saude tana jiyo su daga daki tana zaune saman simintin dakin kanta na jingine da bango, wasu irin hawaye ne masu zafin gaske kebin kuncinta. Wayyo duniya ita dai ta san ta zo duniya a rashin sa鈥檃. Haka ta ci gaba da rera kukanta babu mai鈥榣allashinta.
Washe gari Karfe takwas kamar yanda dillaliya ta
fada ta zo cikin shirinta Laure ta tiso qeyar Saude a
gaba, ta hada ta da dilla'iyar tana faman zuba mata kashedi.
鈥楰l kulada aikin da za,a baki kuma banda dan hali, dan wallahi kika sake ki ka yo abin da za a koroki ki ka dawo min lokacin dawowarki bai yi ba wallahi saina shake ki kin mutu kin ji na fada miki, kuma kinsan zan iya
Ta zaro naira dubu cikin kudin da Hamid ya ba ta, 鈥渨anda ta kwace, ta mikawa dillaliya tana fadar.
鈥淕a wannan kiyi kudin mota.鈥� Dillaliya ta karBa ta tisa Saude gaba suka tafi.
Sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu damar zirarowa daga idanuwanta, tana ji tana gani suka nufa tasha cikin鈥� yar qaramar motar nan Kurkura.
Suna sauka dillaliya ta kama masu motar Abuja suka 鈥� hau, dama. saura mutum uku, aka samu wani namiji
yakarasa cikon na ukun direbaya dauhanyar Abuja.
ALHAMDULILLAHI MASHA ALLAH _
Sai mucewa matafiya Allah ya kaisu lafiya. .
Mu hadu a littafi na biyu
Donjim yaddah wannan lbrn zaici gaba da kaYAwa
[1/19, 5:14 PM] I love my mum: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[1/22, 10:28 AM] I love my mum: *YAR TALLA*
BOOK 2
*CHAPTER 14*
TUNda suka fara tafiyar Saude ke raira
kukanta, a hankali har sai da suka kusa
kawowa Suleja, sannan wani bacci mai
nauyi ya dauketa Ba ita ta farka ba sai da ta ji
Dillaliya na tayar da ita, Saude ta bude ido ta ga har
sun kawo tasha, mutane na ta fita, sannan ita ma ta bi ayarin masu fitan
Tun da suka sauka tasha Saude keta faman zare na-mujiya, ta zo garin da ba nata ba, za ta iya rantsewa tunda take ko gidan Mutum Daya bata taBa zuwa ba, to balle ta tsallaka Kano k0 wani garin da ke kusa鈥� da su, amma yau ga ta cikin 鈥楢buja tsamo-tsamo. Ikon Allah. .
Dillaliya ta tsaida musu tasi tasha suka shiga, Saude dai na biye da ita da idanuwa sai faman waige-waigen idanuwa take. A hankali ta ga sun shigo cikin rukunin wata unguwa wadda kai tsaye za a kira ta da G. R.A
Unguwar shiru ba ka Jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka ga manyan shuke shuke da suka sa titin unguwar tsakiya, kowane gida ka kalla ka san na wani kusan ne, gaba daya babu gidan da bana wani babban mutum ba a unguwar.
Saude na cikin kallon jerin gidajen ta ji Dillaliya na fadar.
鈥淣an za ka ajiyemu.鈥�
A hankali Saude tabi kofar gidan da aka ajiye su
din, wanda za ta iya rantsewa tunda suka taho gidaje
kadan ne suka kai shi kyau da tsaruwa. Saude ta zuro qafafuwanta ta fito kamar yanda ta ga Dillaliya ta yi, ta tsaya ta biya mai tasi din sannan ta yi gaba Saude ta bi bayanta. Kai tsaye katafaren gate din gidan suka nufa makeken gaske mai kama da Kofar shiga gari, ga wasu manya-manyan shuke-shuke da suka zagaye gidan gaba daya. Dillaliya ta tsaya tana latsa wata 鈥榶ar karamar na鈥檜ra da ke like a bangon gidan. ' Wani irin tsoro da faduwar gaba suka bugi Saude anya kuwa, ba tahowa akai da ita a saida ita ba, don tana da yakinin wannan ba gida bane sai dai k0 wata ma鈥檃ikata ta sarrafa naman mutane Ba ta gama tunanin ba ta ji qarar tura gate din take ta yi ido hudu da wasu manya-manyan qarti har hudu, bakikkirin da su majiya qarfi, sun bude qofar, suna qokarin shiga suka ga wata bakar mota
yar dunkulalliya mai daukar hankali ta ratsa ta
shiga cikin gate din
Dillaliya ta janyo hannun Saude da niyar su shiga, qartin nan suka yo kansu da wata irin masifaffiyar tsawa wadda tasa 鈥榶an cikin Saude
juyawa gaba dayansu,fitsari ya fara kwace mata a wando, ita kanta Dillaliyar ta firgita, don cikin rawar murya take fadar.
鈥淜u yi hakuri wurin matar gidan muka zo ni ce wadda na taBa zuwa da Hajiya Kande, wan,,,,,,
鈥淪hut up! I don 鈥檛 speak Hausa.鈥� ,
Tuni 鈥榶an cikin Dillaliya suka juya, .don ita dai k0 zo in kashe ki da Turanci ba ta sani ba, ido ya ' raina fata ta dubi Saude tana fadar.
' 鈥� 鈥淢e suke cewa?鈥�
Cikin muryar kuka Saude ta ce, 鈥淏an sani ba nima.鈥�
Dillaliya ta harzuka 鈥淵anzu ashe duk makarantar da ki ke zuwa asarar kudin tara kawai ake baki san komai ba?鈥� 鈥�
Saude dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mutanen nan suka maida kofa suka rufe suka bar su nan tsaye,
Dillaliya na ta faman saukewa Saude kwandon masifa, don ba ta iya Turanci ba. Kunji fa rashin鈥� kunya.
A hankali motar da ta shigo cikin gidan mai bakin gilas' ta faka a qatuwar harabar da aka tanada dan ajiye motoci, aka bude gidan direba da hanzari, wata 鈥榶ar budurwa ta fito cikin shigar suite baqaqe da gani ba zata wuce shekara talatin ba
, Tana fitowa ta bude gidan bayan motar tare da ja gefe ta kama, wata kyakkyawar mace ta fito, mai
masifar kyau kai ka ce Balarabiya ce k0 Baturiya saboda tsananin kyau da hasken fata Tana sanye cikin shigar wani danyen leshi mai kyan gaske, wanda tsadarsa ta tasamma dubu dari da wani abu, an yi masa dinkin riga da siket matsatstsu irin dinkin matan manya na Legas, dan qaramin mayafi ne saman kafadarta wanda ta dora shi kawai ta yi a gefen kafadarta, kanta an kafa mata wani masifaffen dauri mai kama da daurin inji, qafar nan tana sanye cikin wani masifaffen takalmi mai tsinin gaske da 鈥榶ar Karamar post din su a hannunta Idonta na sanye da wani qaton bakin gilas wanda: ya mamaye rabin fuskarta. A, Kai tsaye za ka lye. kiranta da 鈥榝irst Lady鈥� saboda haduwarta. Tana fitowa daga motar ta dubi yarinyar
鈥檇a ke tsaye, cikin wata irin murya mai kama da rada rada ta soma magana cikin harshen turanci.
鈥渏eki shigo da su.鈥�
Yarinyar ta amsa da 鈥榦key Tare da juyawa da sauri ta wuce ita kuma ta nufi cikin gidan nata tana wani irin taku, da wata irin faskekiyar waya a 'hannunta. ;
Dillaliya da ta gaji da ruwan bala鈥檌 sai kuma ta yi shiru tana tunanin mafita, can dabara ta fado mata ta
Ciro 鈥榶ar qaramar wayarta baby Nokia ta lallatsa lambar Hajiya Kande ta kara a kunne; tun kafin ta
soma magana ta ji an bude wata qaramar kofa yarinyar. Tace come and enter
Dudda Dillaliya ba ta san abin da ta ceba, amma ta fahimta ta hanyar yi masu nuni da hannu da yarinyar ta yi, don haka ta zabaura ko kallon Saude ba tayiba tayiciki, don haka itama tamike da sauri ta bi ta
Kan Saude ya yi masifar daurewa lokacin
da ta shiga cikin harabar gidan, gabanta ya shiga wata rugurguza da bugawa mai tsanani, yarinyar ta yi masu jagora har zuwa wani qaton ginin bane hawa hudu, wanda tamkar da gilas kawai aka yi shi, dama da hagu duk iri daya ne, suka nufi Bangaren dama suka tattaka wata matattakala wadda ba tafi hawa shida ba, sannan suka ratsa ta wata Kofa mai fadi, anan ma mace ce tsaye qikam kamar an kafe ta, tana sanye ita ma da bakaken suita jikinta, sai da ta sa wata 鈥榶ar na鈥檜ra ta daddana a jikinsu sannan suka 鈥� wuce cikin kofar da za ta sada ka da qaton falon gidan. Saude ta bi matar da kallo a zuciyarta tana fadar, ikon Allah yanzu ita kuma wannan aikinta kenan鈥�
Kamshin rom freshner da turaren wuta dan Maiduguri shi ya dakar masu hanci su duka hakan ya tabbatar masu da sun iso falon, qaton gaske wanda aka zagaye da kujeru saiti uku, kuma kowane
kalarsa. Kai batun ma in tsaya in, labarta muku haduwar falon duk wani bata lokaci_ne na barwa mai karatu ya yi image dinsa a zuciyarsa.鈥榊arinyar wadda zan iya kira da Ingozi ta yi禄 masu nuni da cikin falon suka tafi suka zauna dirshan a 鈥榪asan kafet din duk da kujerun da ke zube kamar a cikin store. Yarinyar ta juya ta tafi abinta tabar. su nan
zazzaune kamar masu zaman gaisuwa,; sai :rarraba
idanuwa suke ba Sauden ba na Dillaliyar ba, wadda sai ka ce ba ta taBa zuwa ba.
Tun suna tsammanin fitowarta har .suka soma . cire rai da za ta fito, don sun share fiye da awa biyar a zazzaune suna zare namujiya, sanyin AC sai kada su yake suna faman karkarwa. Tuni sun gama鈥檉idda rai da fitowarta, ga gajiya ga wata~ masifaffiyar yunwar da ke kwakwalarsu, sai faman gyangyadin gajiya suke. , Kamshin turarenta shi ya farkar dasu; gaba daya Suka wartsake suna daidata nutsuwarsu,. idanuwan Sande na zube a kan matar wadda ta nufo inda suke tana lallatsa faskekiyar wayar da ke-hannunta,*Allah mai halitta abin da Saude ta iya fada kenan a zuciyarta, saboda yanda ta ga tsabagen kyau kwance a jikin matar, wadda ba za a kira ta da doguwa ba ba kuma gajeriya ba ce, sai dai a kira ta da tsaka-tsaki. Ba ta da qiba sosai, amma kuma ba 鈥榮iriri ba ce sosai dai tana da jiki daidai-daidai.
1page is missing
A yanzu ma takalmi ne mai tsini a kafarta, sai dai babu gilas yanzu a fuskar tata.
Ta karaso cikin falon ta fada kan kujera ta dora kafa daya kan daya ba tare da ta dago ta kallesuba
idonta na kan wayar hannunta ta rinka amsa: masu gaisuwar da suke ta faman kwarara mata
Duk azaton Saude za ta basu hakurin shanyar dasu da ta yi amma sai taga kwata-kwata ma hankalinta baya kansu yana kan wayar dake hannunta ne
falon ya dan dauki shiru, Dillaliya na nazarin ko ta fara. Maganane
Cak matar ta mike wadda ba zata haura shekara talatinba
ba, muryar nan tatat kamar mai rada ta soma magana.
鈥楰i yi hakuri baiwar Allah ina da abin yi yanzu haka kikaga nazo nazauna dan insaurareki dama na lura kamar akwai wani important issue ne shi yasa na ce aje a shigo da ku, yanzu banida lokaci inada apointment da karfe sha daya.鈥� Tana maganar tana taflya. 鈥�
Dillaliya ta fara bada hakuri cikin rawar murya tana fadar, 鈥淜i yi hakuri ranki shi dade, wailahi na dan saurara ne ki fara magana kada in fara kiga kamar na yi rashin da鈥檃 a gabanki, dama ba wani
abu ba ne yar aikin da kika ce kina so CE na kawo miki guda tun wancan watan鈥� lokacin da mukazo ni
Da Hajiya Kande taya ku murnar cin nasarar lashe zabe kika ce kina san yar aiki guda mai nutsuwa za ki Kara shi ne na tsaya na binciko miki na kawo miki
Matar ta dan dakata daga tafiyar da take ta waigo a hankali, ta daura dara-daran idanuwanta kan Saude tana qare mata kallo sama da Kasa, tamkar wadda ta ga wani abun kyama a tare da ita, ta dauke kanta tana 鈥� latsa wayarta cikin rashin kulawa ta ce, 鈥淚s okey. 鈥�
Ta dan karkace tasa hannunta saman hannun
kujerar ta janyo sai ga wata 鈥榶ar loka, shake da kudi bandir-bandir yan 鈥� dubu-dubu, ta zaro masu yawa ba tare da ta Kirga ba ta cillawa Dillaliya tana fadar, 鈥淜i hau mota, sai da safe.鈥� 鈥� Ba tare da ta~ saurari godiyarta ba ta yi gaba abin ta, dad'i ya kashe Dillaliya ta tashi jiki na Bari. tana fadar, 鈥淜e kuwa kin yi nasara Saude, da ta dauke ki don Hajiya Kande ce min ta yi ta kawo mata yara 鈥榶an mata sun fi guda talatin tana cewa ba su yi mata ba, don haka saiki kula ni dai kin ga tafiya ta.鈥�
Ta mike ta bar Saude na zare namujiya, zuciyarta na faman kaiwa da kawowa, a yanzu ma kukan ya gagare ta' saboda tashin hankalin da take ciki yanzu ya fi gaban kwatance, tunaninta daya yanzu wace irin rayuwa ce za ta yi a gidan da ba ta san kowa ba?
Wane irin鈥� qalubale ne yanzu kuma za ta fuskanta? ' Ta Iumshe idanuwanta Kirjinta na barazanar 鈥�
fashewa, ga鈥� bacci, ga yunwa, ga gajia, ga uwa-uba fargaba da tashin hankali da suka鈥� dabaibaye zuciyarta. Tana nan zaune tana muzurai ta ga wata dattijuwar mace ta shigo falon sai dai ita da ganinta Bahaushiya ce wadda shekarunta ba zasu wuce
arba鈥檌n ba. Ta dubi Saude cike da kulawa kafin tace, 鈥淜i taso muje in nuna miki masaukin ki.鈥�
Saude ta yunkura ta mike tana jin tamkar za ta. kifa saboda rashin kuzari. Ta wata hanya ta ga sun bi ta cikin falon sai ga su sun flto wani Karamin bedroom shi daya, ba wasu karikitai a cikinsa sosai, 鈥� karamin gado ne kwara guda mai kyan gaske kwanciyar mutum guda, sai wardrobe dinsa a gefe, shi kenan sai kafet da ke malale a dakin mai laushi.
Matar ta juya ta dubi Saude tana fadar, 鈥楴an shi ne dakin da Hajiya ta ce a sauke ki da fatan za kiyi . farin ciki, don gaba daya ma鈥檃ikatan .gidan nan masaukinsu a waje yake sai ga ki ke daga ~zuwan ki anwareki, natayaki murna." 鈥�
Saude dai ba ta ce komai ba don ita abin da ke cikin zuciyarta yafi gaban wannan. Ta zauna gefen gadon wanda ya sha lallausar shimfida ta ci. gaba da bin dakin da kallo, wanda take ganinsa 鈥榯amkar wata
aljannar duniya. Matar ta sa kai ta fice saboda ganin hankalin Saude baya kanta.
Ba ta jima da fita ba sai ga ta ta dawo hannunta riqe da plate da ke rufe, tare da pure water ta ajiyewa Saude ta juya ta fice. Jikin Saude har rawa yake wurin saukowa ta bude plate din, ta kafe idanuwanta saman abincin. Shinkafa ce jaloup babu ko wadatar kayan miya a cikinta. Saude ta sa cokali ta soma ci, sai dai bakinta ya gaya mata dan ba ta yi tunanin
shinkafar za ta yi dadi a yanda ta ganta ba.
Hannu ba ka hannu kwarya haka ta rinqa cin abinci, lokaci guda ta kawar da shi, sannan ta dauki ruwan ta fasa ta shanye shi tas. Tana sauke ledar ta saki wata鈥� nannauyar gyatsa, idonta ya soma lumshewa ta yunkura ta haye kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya wani barci mai nauyi ya dauke ta.
Ba ta sake motsawa ba sai lokacin da ta jiyo ana ta kiraye-kirayen sallar Asuba, ta yunkua ta mike tana faman zazzare idanuwa can ta hango wata kofa jikinta na rawa ta nufe ta, ta bude ta tsaya sororo 鈥� tana kallo; 'an qawata wurin da kayan qawata bandaki. 鈥� ' 鈥� Da sauri Saude ta maida ta rufe dan ita a zatonta wani dakin hutawa ne, ta dawo ta zauna tana san yin
sallah amma ba ta san inda za ta kama ruwa ba, balle
, ta dauro alwala. Da ta gaji da zama ne ta koma ta
kwanta. 鈥� Sai dai a yanzu ba barci take ba. idonta biyu, tana kwance tana tunani, wai ita ce yau a kwance saman
lallausan gado irin wannan, ko a mafarkinta bata taba tunanin hakan ba. Fargabarta guda yanzu yanda ta ga matar gidan da ganinta tasan bata da mutunci, dan tunkan su hadu wani irin tsoranta ya mamaye zuciyarta鈥� Tana nan kwance tana juyinta, ita kanta ba ta san awannin da ta kwashe ba, ta ji motsin ana shigowa dakin ta yunqura ta tashi zaune tana kallon mai shigowar.
Matar Jiya ce ta shigo da sallamar ta, a yanzu ma hannunta na dauke da plate da cup a sama sai ruwa guda daya a dayan hannun ta ajiye, Saude da ke kan gado ta amsa mata sallamar ta tare da gaishe ta, ita kuma matar ta dan zuba mata idanuwanta kafin ta ce鈥淵au dai kin yi kwanciyar kadaici k0 ya ki ka ji gidan namu?鈥�
Sande ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba, matar ta Kara gyara zama tana fadar, 鈥淜in ga dai matar gidan sai kin yi takatsantsan dan ba ta da kirki, yanzu dubi duk dukiyar mai gidan nan amma abincin su daban na masu aiki daban.
Haushi ya kama Saude a duniya ita akwai ta da surutu da naci amma ba ta iya gulma ba, dan haka cikin qosawa ta dubi matar tana fadar, 鈥楧on Allah inane bayan gida in je in kama ruwa har yanzu ban samu na yi sallah ba 鈥�
Matar ta ce, 鈥榃ane bayan gida kuma bacin wancan.鈥�
, Saude ta waro ido tana fadar, 鈥淵anxu wancan kewaye ne?鈥� Matar ta yi murmushi tare da fadar,
鈥淭aso muje in nuna miki yanda za ki yi amfani da 'su
Saude ta yunkura ta mike ta bi bayan matar. Daya bayan daya ta rinqa nuna mata yanda ake amfani da komai da yake kwanyar tata a bude: take, a
take: ta dauka, don haka suka fito, matar ta tafi ita
kuma ta haye saman gadon ta janyo plate din ta bude, soyayyan dankalin turawa ne da kwai sai ruwan tea dan tsururu mai kama da fitsarin godiya. Dadi ya kama Saude yau za ta yi karin kumallon 鈥榶an gayu. Ta tisa dankalin tana ci tana faman santi a zuciyarta yanzu dama wannan shi ne rayuwar da masu aiki ke yi a gidajen da aka kai su aikatau? A gaskiya suna morewa don ita in dai za ta rinka samun abinci mai rai da motsi irin haka, to ai ba aikin da za,a sata a ,ciki batayiba bayan ta kammala sannan ta kwashe kayan ta ajiye gefe ta mike ta nufl bandakin ta dauro alwala ta tayi sallarta. Tana gammawa ta kishingida saman kafet din aiko nannauyan barci ya dauketa saiji tayi matarnan tazo tana tashinta ki tashi hajia nason ganinki
A falo yanzu nan da minti biyar Hajiya zata sauko ta ki gana da ita.鈥�
鈥榊an cikin Saude su kai wata masifar juyawa, alamun tsoronta ya bayyana a fili qarara. Matar ta-yi murmushi ta mike tana fadar.
鈥淗ajiya na da matukar kwarjini a idanuwan kowa, ki dake ki fltO yanzu dan kar ta riga ki fitowa ki samu matsala.鈥�
Ba ta jira abin da Saude za ta ce ba ta juya ta fice, ta yunkura da hanzarinta ta nufi bandaki ta wanko fuskarta da bakinta jikinta sai faman rawa yake tamkar wadda za ta gana da Azara鈥檌lu ta fito falon, Wanda yake tas-tas tamkar ba a shigwarsa saboda tsabar gyara.
Saude ta raba daga qasa ta zauna zuciyarta na barazanar fashewa, don ta san yau za ta wuni anan ba ta fito ba. Sai dai da mamakinta ba ta kai minti biyar da zama ba ta jiyo Kamshin turarenta mai kwantar da hankali, zuciyar Saude ta tsananta bugawa da sauri-sauri, tamkar ana buga ganga, da Kyar ta iya daga kai kadan ta dan saci kallonta.
Sanye take da wata dakekiyar shadda baka 鈥榶ar Mali, dinkin riga da siket sun bala鈥檌n kama ta, an yi mata aiki da jan zare da fari da kuma kore, kwalliyar nan da gani ta kanti ce, tun daga hannuwanta zuwa qafafuwanta da wuyanta gwala-gwalai ne sai daukar ido suke takalmi ne baki mai masifar tsini a Kafarta.
A yanzu idanuwanta rufe suke da baKin gilas din da . ya mamaye mata fuska,鈥榙a makullin mota rike a hannunta tana kadawa, ta qaraso ta zauna saman daya daga cikin kujerun da ke baje a falon ta dora
Qafa daya kan daya tana kadawa Saude ta zube tamkar mai shirin yi mata sujjada. Asma ta taBe baki tana yatsina fuska tamkar wadda
ta ga abun Kyama ta daga mata hannu.
鈥淵a isa bana san yawan gaisuwa, ya ya sunan ki?鈥� . ~ Muryarta na rawa ta ce, 鈥淪ande.鈥�
Ta yamutsa fuska tamkar ba .za ta sake magana ba can ta ja fasali kafin ta ce, 鈥淢alama Saudat na san dai kin san nan k0 gidan waye a qasar nan aka kawo ki ba ki da bukatar sai na maimaita miki?鈥�
, Ta dan yi shiru tamkar wadda maganar ke mata 鈥� wahala kafin ta ci gaba, 鈥淎 dan jiya zuwa yau nasa a , dan yi mini binciken ki a bugi cikin ki dan a fahimci idan kina da yawan surutu. Is oke zuciyata ta nutsu da na dauke ki aiki, ni dai ba mazauniya ba ce 鈥榶ar siya ce ba ni da time din kaina ma ballantana na wani, kullum cikin sabgogina nake;
Don haka na ce a samo mini yarinya mai nutsuwa wadda _zata kula da maigidana. za ki tsaya 鈥榶ar aiki a sashin maigidan, idan ki ka gaza kula da shi kuma zaki fuskanci fushina. Aikin ki shine zaki rinqa kula da abincinsa, abin shansa,
gyaran sashinsa, wurin hutawarsa. Ki nutsu ki fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so akwai lokutan da baya san magana, ki nutsu ki fahimta kar ki kuskura ki rinKa cika shi da yawan
magana, baya san yawan kallo koda yaushe yana bukatar abu mai sanyi kusa da shi Yana cin abinci sau hudu a rana, yana shan fruits
da daddare around 12:am kuma yana shan coffee, yana tashi daga barci qarfe bakwai, yana motsa jiki a lokacin da ya farka yana gamawa zai sha tea, sannan ya tafl ya watsa ruwa. Yana karyawa da misalin
Qarfe goma na safe.
鈥� Wannan shi ne tsarinsa, da fatan za ki kula, duk yan aikin da na daukar masa rashin fahimtarsa ne da basayi kesa inakorarsu. Ayanzu kece damata ta qarshe daga ke idan ki ka kasa kula da shi ba ' buKatar a Kara kawo masa wata, don haka ki tsaya ki nutsu ki fahimce shi ban san sakarci, idan kin yi aiki irin yanda yake so ni zan rinqa biyanki nera dubu ashirin duk wata. Da fatan kin fahimta?鈥�
Saude ta daga mata kai a sanyaye, amma . a kasan zuciyarta ta yi masifar karaya, don ta san ba ma zata iya ba yaudarar kanta kawai ta yi da ta amsa. '
Asma ta yunkura ta mike ta dubi matar da ke tsaye wadda da alama ita ce ma鈥檃ikaciyar sashinta, tace 鈥淜i ba ta kayan ta saka, aikinta zai fara daga
[1/22, 10:28 AM] I love my mum: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[12:17PM, 02/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: [1/24, 9:31 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 15*
gobe qarfe biyar na yamma, ina da taro a Hotel sai na
dawo." Ta juya ta fice abin ta babu maganar mayafi
Matar ta mikawa Saude wata leda tana fadar, 鈥淲adannan
su ne kayan da za ki saka.鈥�
Saude tasa hannu ta karbi kayan jikinta a sanyaye.
Matar ta yi wani takaitaccen murmushi tana fadar, 鈥淵a na
ga farawa da iyawa har kin yi la鈥檃sar, haba Saudat kar ki
karaya mana ki batawa Hajiya rai kin dauke ni matsayin
Auntynki ki yarda da abin da zan fada miki, ki sawa zuciyar
ki za ki iya abin da aka saki da kuruciyar ki ai babu abin da
zai gagare ki-Maigidan 鈥榤utum ne mai saukin kai yanayin
rayuwarsa irin ta Turawa ce idan dai ki ka nutsu komai zai
zo miki da sauki, kin ji?鈥�
Saude ta daga mata kai alamar eh sannan ta karbi kayan ta
koma Bangarenta ta fada kan gadonta da. kayan zuciyarta
na barazanar
fashewa.
Tsawon Iokaci ta dauka tana saka da warwara, , sannan ta
yunkura ta tashi zaune ta zazzage kayan daga 鈥榗ikin ledar
tana daddagawa. Suite ce baKaKe riga da siket sai ta cikin
fara, ta tsaya tana kallon
kayan sun burge ta sosai, ta linke su ta maida a leda.
Ta yunkura ta sauka daga kan gadon ta janyo abincin da
Aunty ta kawo mata ta bude
Tuwon shinkafa ne da miyar agushi, Saude ta zauna ta ci
abincinta sosai ta gama ta mike tayo alwala ta dawo ta yi
sallah sannan ta koma ta
kwanta.
Sai dai fargabar da ke zuciyarta babu abin da ya canza
yinin yau haka ta yi shi, ba kuzari a jikinta tana tsoron abin
da zai iya faruwa idan ta kasa yin abinda Asma ta sanya ta
ba ta san irin hukuncin da za ta yanke mata ba qila ma ta
iya kashe ta kawai.
'Zuciyarta ta kara tsinkewa wasu irin hawaye masu zafi
suka taru a idanuwanta, watakila ajali ne ya kawo ta gidan,
tasa hannu ta goge 鈥榶ar kwallyar da ta tarar mata ta juya
daga gefen da take ta lumshe idanuwanta, amma ba barci
take ba.
Washe gari Saude na zaune a qasa gefen gadonta, tana
tunanin da ya zame mata jiki, zuciyarta ta lula duniyar
tunanin Hamid da irin kulawar da ya. ba ta a rayuwa. K0 a
yanzu ba ta fidda rantaba tana ji a jikinta za ta koma gida ta
same shi, tana ji a jikinta shi ne mijin da zai aureta su yi
rayuwarsu cikin kulawa da Kauna.
Aunty ta turo kofa ta shigo tare da sallama, Saude ta bude
idanuwanta tana amsawa. Aunty ta tsaya daga bakin kofa
tana fadar, 鈥淵a na gan ki anan zaune, k0 kin manta ne yau
ne ranar da aikin ki zai soma?鈥�
Saude ta kalli tace Na sani Aunnty ba ta ce sai Karfe
biyar ba?鈥�
Annty ta yi wani takaitaccen murmushi kafin ta ce 鈥淵allaBai
ya yi tafiya zuwa qasar China sati ukun da suka wuce, don
haka yanzn za ki tashi ki fara gyara masa Bangaren shi ki
zauna har ya iso.鈥� Ta wurgowa Saude makullai tana fadar,
鈥淯ngo
wannan sune makullan bangaren sa.鈥�
Saude ta cafe lokacin da bugun zuciyarta ya tsananta,
Annnty ta juya tana fadar, 鈥淜i tashi ki shirya ina falo ina
jiran ki na raka ki Bangaren nasa.鈥�
Saude ta taKarKare ta mike ta nufi bandaki ta dade a tsaye
zuciyarta na faman kaiwada komowa, sannan ta daure ta
watso ruwan ta fito, ta zauna bakin gadonta ta ciro kayan
daga cikin ledarsu ta sanya kamar yanda Aunty ta nuna
mata, ta mike tsaye siket din bai Karasa isowa kasa ba ya
dai wuce gwiwoyinta, sannan ta janyo hijabinta ta sanya
sannan ta kawo takalmin da ke cikin kayan ta saka wanda
yake sawu-ciki, sannan ta fito ta samu Aunty zaune tana
jiranta tana fitowa suka jera suka fita. ~ '
Gaba daya suka fita daga wannan shashin, suka . nufi daya
Bangaren wanda ke hagu. Aunty ta karBi makullin ta bude
sashin suka shiga, komai na sashin irin na wancan ne, babu
abin da ya bambanta. Aunty ta mika mata makullin tana
fadar.
鈥淕a shi ki goge komai ki gyara,idan kin gama. Ki zauna har
ya iso, da ya iso ki karbi jakarsa ki kawo masa abu mai
sanyi kin ji?鈥� Saude ta daga mata kai ' alamar eh.
Sannan ta juya ta tafi ta bar ta tsaye tana faman bin
katafaran falon da kallo. To ta ina ma za ta fara? Ita dai a
iya ganinta ba ta ga abin da ya yi datti ba, ta taBe baki
sannan ta fara takawa saman matattakalar 鈥� 鈥� benen ta
shiga cikin falon, kai tsaye wani qaton falo ne ta fara shiga
wanda, har yafi na farkon haduwa da tsaruwa.
Idanun Saude suka sauka saman wani makeken hoto
wanda yake jingine a kasan gefen bango, ta danci gaba da
bin hoton da kallo. Wani kyakkyawan namiji ne ajin qarshe
wanda shekarunsa ba zasu鈥� wuce talatin da biyar ba, kallo
daya za kai masa ka tabbatar ya hadu tamkar wani
Balarabe, yana rungume da Asma sunyi murmushi'su duka,
sun yi * masifar kyau, dama duk kyan Asma bata kai
mutumin ba, duk da yana namiji, don shi kalar kyansa yafi
kama da na Larabawa saika rantse Balaraben Saudiyya ne
Saude ta wuce a hankali ta shiga zagaye falukan sashin da
bedroom din dake ciki, ita kanta tana ,tausayin kanta
saboda sashi~sashin dake ciki sun kai
goma, haka ta dauko mofa da tsintsiya da tawul da .bokiti
ta fito ta shiga gyaran sashin,鈥�
Sai da ta gyara ko鈥檌na da ina ta goge tare da kunna bona
bonar da ke falukan kowacce ta zuba turaren 'wuta a ciki,
sannan ta dauki room fresner ta dinga feffesawa a ko鈥檌na
da ina, ta Kara gudun A.C sannan ta rurrufe ko鈥檌na kamar
yanda Aunty ta fada mata, ta dawo falon qasa ta zauna
gefen kujera tana faman zare na mujiya, sanyin A.C na
ratsa ta. A take tamkar ta kwanta saboda tsabar gajiyar da
ta yi.
Misalin Karfe biyar da 鈥榶an mintina Saude ta ji an turo Kofar
falon ta zabura ta tashi tsaye kirjinta na wani masifar
bugawa da qarfl da qarfi. Shi daya ne ya shigo yana sanye
cikin shigar Kananan kaya, sai wani yaro da ke bayansa
wanda ke sanya da suit, yana rataye da irin jakar
ma鈥檃ikata.
Ahmad ya tsaya yana watsa mata wani irin kallo
wanda ya Kara hautsina mata鈥� yan hanji, muryarta da rawa
ta fara fadar, 鈥楽annu da zuwa
鈥� Shut up! You are very stupid, get the hell out of here
Jikin Saude ya hau Bari ko鈥檌na na jikinta rawa yake ga shi
dai ba ta san tsiyar da ya fada ba, amma yanda ya kwatsa
mata tsawa, ya tabbatar mata da korarta yake don haka jiki
na Bari ta gifta zata wuce, Ahmad ya kara daka mata
tsawa.
鈥淲ait, na ce ki tsaya.鈥�
Saude ta ja ta tsaya, sai faman kyarma, take, don yanda ta
ga tsantsar Bacin ransa ta tabbatar zai iya
kai mata duka cikin bacin rai yace hope baki dai hau min
sama ba?"
Saude ta yi shiru tana faman rawar murya, yaja wani dogon
tsaki ya wuce ciki, jikin ta yana rawa ta wucc, sai faman
harde qafafuwa taka , har tabar falon.
A tsaye ta samu Asma sanye da wata doguwar riga milk
colour, ta dora dan qaramin mayafi saman kanta wanda ya
tsaya iya wuyanta, gilas dinta yau a hannu yake tare da
makullin mota da alama fita za ta yi. 鈥�
Saude na shigowa ta tsaya tana kallonta, cikin tsantsar
takaici take kallonta, jikinta ya qara yin la鈥檃sar tana shirin
dukawa ta gaishe ta ta ji saukar wani mahaukacin mari' har
sau biyu, dama da hagu,
* wanda yasa sai da ta kifa cikin takaici Asma ke fadar.
鈥淎she ke dakikiya ce ban sani ba sakarya, jaka ce keba?
Dube ki, dubi abinda da ke jikin ki, yanzu da wannan bakin
abun ki ka shigar masa ne? Oh! Kin gama dani, amma kin ci
sa鈥檃rsa da ya kyale ki da kin gane baki da wayo, don na
tabbatar yau k0
' ruwa ba zai iya hadiya ba.鈥� Ta ja tsaki mts! Ta juya ta dubi
Aunty wadda ke芦 tsaye tace, 鈥淩abi maza Id debo mata
kayan shafawa da turarurruka, ta cire wannan bakin abin ta
shirya, ki tabbatar ta koma ta ba shi hakuri, Wallahi
idan ki ka sake yaqi amincewa da ke zama 鈥榶ar aikinsa na
rantse miki sai kin fuskanci fushina kin ji na rantse.鈥�
Ta'Karasa maganar da karfi, sannan ta juya ta yi gaba abin
ta.
Wasu irin hawaye masu zafl suka biyo kuncin Saude, wayyo
Allah wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki?
Au'nty ta dafa ta muryarta a . sanyaye. .
鈥渢ace kizo mu je, kada dan wannan abun
ya razanar dak茅, na san za ki iya yin abin da ma yafi wanda
aka saka ki, idan dai har kin sawa ranki zakiyi, za ki yi
Saudat, please zo muje.鈥� Saude dai ba ta tanka mata ba ta
juya ta bi ' bayanta suka nufi wani sashi daban, ta tura wata
'禄 kofa sai ga su sun fada wani dan falo irin na ' Sauden. 鈥�
Aunty ta bud鈥榚 wata loka da ke jikin bango sai ga kayan
kwalliya kamar su ci kansu, ta dauko leda ta dibar mata
masu yawa, tun daga man shafawa, sabulan wanka, kayan
kwalliya har da turarurmka, sannan ta bude wardrobe ta
ciro dan qaramin hijabin nan mai tsayawa iya wuya wato
himar kalar ja ta
mika mata tana fadar
鈥淜i yi sauri ki je ki gyara ki tafi, dan na san yanzu haka
akwai abubuwa da dama da yake buqata.鈥� Saude ta karBa
ta fice jikinta amace.
Sai data sake wani wankan sannan ta fito ta shafa mai a
jikinta ta kawo wata 鈥榶ar qaramar powder fara ta shafawa
fuskana, ta sa man lice a bakinta, sannan ta mike ta mayar
da kayan jikinta, ta dauki qaramin hijabin ta rufe kanta.
Wani irin abu ya cunkushe mata zuciya, tunda take a duniya
bata taba irin wannan shigar ba ace kana dan Musulmi
amma ka flta a haka, kai duniya! Takaicin kanta ya kamata,
k0 tsayawa ta dubi kanta ba ta iya ba ta dauki turare ta fesa
guri uku kawai sannan ta fice zuciyarta na faman kai kawo.
Tsoronta ya qara tsananta lokacin da ta iso bakin sashin
nasa ta daure ta yi ta maza ta sa kai cikin falon cike da
fargaba. Turus! Ta ja ta tsaya 鈥榶ar sallamar da take shirin yi
ta makale mata a makoshi,
wani irin tsoro da fargaba mai tsanani suka dirar
mata Kwance yake tsakiyar falon saman kafet ya yi
daidai. daga shi sai gajeran wando ba k0 singlet jikinsa, ya
yi matashi da hannayensa fuskarshi na kallon sama,
idanuwan shi a lumshe suke kamar mai barci.
Saude ta runtse: idanuwanta ba 鈥檛ana shirin ta juya da sauri
ta-芦koma sai kuma ta tuna
Da
maganar Asma da take fadi鈥淲allahi idan kika sake
Yaqi amincewa dake a matsayin yar aikinsa sai kin fuskanci
fushina. "
[1/24, 9:31 AM] A A Dboy: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[1/24, 10:13 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 16*
Saude ta ja ta tsaya tare da juyowa , muryarta na rawa ta
sake yin wata sallamar, Ahmad ya bude idanuwansa
wadanda suka kada sukai jawur, yana kallonta, kallon da ke
tabbatar da tsananin tsananta cikin idanuwansa ya sake
she idanuwansa kafin ya soma magana tamkar wanda yake
sanyin rada.
鈥淏a cewa nayi kar ki bari in sake hada hanya da ke ba?
Okay ba kiji ba kenan, shi ne ki ka dawo k0?鈥�
Muryar Saude na rawar disko ta ce
hajia ce tace min Ba ta qarasa fadar abin da za ta ce ba ya
zabura a
Qufule yana fadar, 鈥淲uce ki bar falon nan,鈥榠dan kuwa ki
ka bari raina ya baci za ki hadu da abin da baki yi tunani
ba. Gate out! 鈥� 鈥榊an cikin Saude suka Kara Juyawa, wannan
shi ne gaba kura baya hayaki, wasu irin hawaye suka biyo
kuncinta ta durqusa a gabansa cikin kuka tana 鈥� fadar, 鈥淒on
Allah don Annabi ka鈥榶i min rai ka yi haquri wallahi idan na
koma na ce mata ka kore ni kasheni za ta yi don Allah ka yi
hakuri 鈥� . Ahmad鈥檡a tsaya yana kallonta tsawon lokaci yana
jin tamkar ya shake ta saboda takaici, don a duniya idan
akwai abin da ya tsana鈥榯o bayan kuka
Ne k0 cikin film baya Kaunar ya. ga ana kuka, '
Ya ja tsaki mts! Tare da fadar 鈥淭ashi na ji ya ishe ni haka.鈥�
Muryarta a raunane ta ce 鈥淣a gode. 鈥�* Bai tanka mata ba
ya juya ya koma kan kujera ya yi kwanciyarsa abinsa
tsawon Iokaci babu wanda ya
Tanka can dai Saude da ta lura idan za su kwana a haka
bai damu ba sai ta mike ta dan matsa kusa da shi kadan ta
durkusa tana fadar, 鈥楰o kwai abin da ka ke buqata in kawo
maka?鈥�
Ahmad ya dan tsura mata ido= kadan, kamar wadda ta
zage shi sannan ya juya tare da kada mata yatsun hannun
shi ba tare da ya yi鈥� magana ba, zuciyar Saude ta Kara
tsurewa, don ta lura mutumin ya tsane ta da wuya idan
kuma zai bata mazaunin mai aikin nasa.
Kwalla ta cika mata idanuwa cikin muryar kuka ta soma
magana, 鈥淒on Allah to in kawo maka wani abu mai sanyi.鈥� "
鈥�
鈥淣a ce miki a鈥� a, a鈥檃 shin wai k0 dole ne?鈥� Yanda yake mata
maganar ya firgita ta, saura kadan da ta fadi saboda
razana. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka
samu damar biyo kuncinta.
' Ahmad ya ja wani gajeran tsaki yana fadar, 鈥淥h! My God,
jeki kawo mini koma meye zaki kawo, k0 baki Jiba?鈥� Ya
fada a harzuke
Saude ta mike a razane ta nufi gurin firij din ta , bude,
lemuka ne kale-kale sun fi kada ashirin jikinta sai rawa yake
ta rasa wane za ta dauko masa, can idonta ya sauka kan
fresh milk ta kwali, tasa hannu ta dauko masa tare da kofi
na tankaran guda mai gindin turmi ta rufe firij din ta nufo
inda yake. Ta durkusa a gabansa tasa hannu ta gage
hawayen da ke zuba a idanuwanta sannan ta balle murfin
ta tsiyaya masa fiye da rabin kofi din, ta miqa masa, ba
musu ya sa hannu ya karba
Saude ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya, wadda ta
janyo hankalinn Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuwansa
kadan sannan ya dauke kansa. Ta yunkura ta mike tana
fadar, 鈥楽ai da safe.鈥�
K0 uffan baice mata ba har ta fice Kai tsaye dakinta ta nufa
ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin abin da ya faru
dazu ya rinqa dawo mata ita kanta ta ba kanta tausayi dan
zama tare da miskilin mutum irin wannan ba Karamin aiki
ba ne, shin k0 yaci abincin ma ko k0 haka nan ya kwanta?
Allahu 鈥楢'a lamu.
Ta daga kanta tana kallon agogon dake manne a bangon
dakin karfe goma da鈥� yan mintina, ta qara ' juyawa sosai a
kan gadon, dan to san saura 鈥榶an mintina lokacin shan
coffee dinsa ya yi, yanzu dan kawai zai sha wani coffee har
sai wani ya je ya
hado masa saboda san kai kawai irin na masu kudi
1page is missing
Saude ta zabura ta durgusa tana gaida shi, k0 inda take bai
kalla ba ballantana ta sa ran zai amsa, don haka taja
bakinta ta tsuke tana kakllonsa ya isa gaban firiji ya bude ya
dauko robar ruwa guda, ya murde murfin ya daga sama
yana kwararawa cikinsa ya sha ya kusan rabi sannan ya
ajiye ya waigo da niyar wucewa. Saude ta yi saurin
sunkuyar da kanta ta ci gaba da abin da take, don tsoron
kar ya 鈥� kama ta tana kallonsa. '
Bai kula ta kanta ba ya haye sama abinsa. Saude ta girgiza
kai a zuciyarta tana mamakin miskilanci irin nasa, don har
ma ya zarce matar tasa , ' tunda ita duk abin da kai za ta yi
magana, amma shi sai dai ya kore ka. Ta girgiza kai ta ja
gefen kafet ta zauna tana muzurai; ,
Da misalin Karfe goma saura minti biyar Ahmad ya sauko
daga sama kamshin turarensa ya mamaye falon gaba daya,
Saude ta dan dago a hankali ta saci kallonSa sanye yake da
wani yadi mai laushin gaske sky blue, ya sha aiki da farin
zare. Yadin mai Sharashara ne hakan ne yasa akan iya
hango farar singlet dinsa da short nirker din da ke jikinsa,
farar fatar . nan ta yi wani luwai-luwai kamar jikin Jariri. *
* Ya ja ya zauna kan kujera da waya rike a 'kunnensa yana
magana cikin harshen Turanci, Saude ta yunknra ta mike ta
fita daga falon ta bi wata 鈥榶ar kwana da ke gefe sai ga ta ta
Bude qaton dakin dafa .
abinci wanda ma鈥榓ikata ke ciki, harsu uku duka mutum
daya ne Bahaushiya a cikinsu. To su wai me yasa ba sa son
daukar Musulmai zalla aiki ne?
Ba ta da mai amsa mata wannan tambayan, don 鈥� haka ta
karb0 break din yallaBai din sannan ta fito. A bakin kofa su
kai karo da Aunty ta zo daukar wa Hajiya nata suka gaisa,
sannan ta wuce, ta nufi falon nasa. : :
Yana zaune kamar yanda ta bar shi har yanzu bai gama
wayar ba, Saude ta dora tiren kayan abincin saman dinning
table sannan ta koma can gefe nesa da shi ta zauna tana
jiransa ya gama wayar amma da alama bai da niyar
gamawa har wani kashe murya yake yana zuba shagwaBa,
sai. kace wani qaramin yaro, duk kunya ta ishe ta, ji take
tamkar ta zuba da gudu, don duk da ba ta. san abinda yake
cewa ba, ' amma zuciyarta ta ba ta da matarsa yake wayar
Ashe dama yana dariya irin haka? Lallai k0 da wa yake
wayar nan, to an jiKa ta a shanye Ba ta ankara ba tana
duniyar tunani sai dai ta ji muryarsa na fadar, 鈥淜awo
abincin nan
Saude ta zabura har tana neman faduwa ta mike, ta nufi
dining din ta dauko kayan karyawar tazo ta gabansa ya
nuna mata kan kafet din ta aje masa anan sannan ta koma
ta zauna
Ya watsa mata wani kalla mai, kama da harara kafin ya ce,
鈥淲aye kika ajiye ya yi serving din. "
Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai
ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, 鈥淣a ce
waye zai zuzzuba abincin?鈥�
. Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, 鈥淵anzu zan zuba.鈥�
Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan
ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa.
Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da
takaici ya ce, 鈥淵anzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin
tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali
mts!鈥� Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din,
sannan ya soma sha.
Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba
masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta鈥� ce,
鈥淎bincin kamar yaya za a zuba?鈥�
Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka
mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki
plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da
miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da
kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa,
wato~ papper chicking, sai
gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora
saman plate, wato sandwich.
Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba
masa farfesun naman a plate din sai ta debi
yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman
ta rufe.
鈥淏ai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali
har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka
tilastawa sai ya kalle ta ya ce, 鈥淭ashi kawo mini morning
fresh
鈥榊an hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani
abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a
dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? 鈥�
Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan
ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya
tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to
k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan
qashi a kasa. 鈥�
Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko
鈥榶ar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi,
ta durkusa tare da fadar, 鈥淕a ta.鈥�
Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani
mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu
ya ja tsaki mts! Yana fadar. 鈥�
鈥淜e jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba
ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta
shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?鈥�
Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, 鈥淜ai Allah dai ya
wadaran dakikin mutum stuppid girl ni
Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.鈥�
Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka ciko da
hawaye muryarta na rawa tace, 鈥淜a yi hakuri don Allah. 鈥�
Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki
鈥淢ts!鈥� 鈥�
Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta
cikeda tsanarta ya ce, 鈥淜i fadawa Madam, ina da meeting
yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa
gobe komai kr nan mu hadu ta network.鈥�
Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a
tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo
kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji
ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka
cire ni daga' wannan rayuwar qangin鈥� bautar da rashin
galihu.鈥� A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya,
sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta
share 鈥檋awayenta.
Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa
yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda
yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike
ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar
ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko鈥檌na ta yi
turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC
鈥�
a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can
Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren
wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da.
kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a
sanyaye ta ce 鈥淵allaBa鈥榠 ya ce鈥淎 fadawa Madam ba zai
dawo ba sai gobe
Aunty ta ce, 鈥淭o ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.鈥�
Saude ta dan yi jim cike da tsoro.
Aunty ta katse mata tunanin da fadar, 鈥淜ije mana Saudat
tunanin me ki keyi haka?鈥�
Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan
ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na
farko kenan da ta fara hawa saman. 鈥� Haka kawai ta tsinci
gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya
dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai
ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni鈥檌mar da Ubangiji
ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama鈥�
har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo
hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara
matsawa tare da yin wata sallamar.
Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata
dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi
tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa
tantance ta, ta ji saukar
wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu.
Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta
ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, 鈥淵ou
are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo
ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi
ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?鈥�
Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take,
hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta
ce 鈥淜i yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi
tafiya sai zuwa gobe da yamma za..
鈥楽o What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni
duk inda nake ki fada mini, iye?鈥� Ta ja wani dogon tsaki mts!
Kafin ta ce, 鈥淒a alla gate out on my parlour鈥� Ta sake kwatsa
mata tsawa, 鈥淚 say
gate out k0 ba kya jine?鈥� saude ta zabura ta mike ta bi
hanyar da take nuna
mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana
fadar, 鈥楽tupld kawai.鈥� Sannan
ta juya ta koma ciki abin ta.
Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada
kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo
Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta
samu kanta a ciki me cike da qaskanci
da wulaqanci ni Saude? Kuka take 鈥榮osai bata da mai
lallashinta. Rayuwa kenan.
,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,,
Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da
rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da
bambanci, 鈥檚auqin鈥� ta ma tun a gida ta riga ta saba da
wahala.
Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara
falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya,
wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. 鈥�
Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan
wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin
鈥榶an kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun
masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan
kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce
abinsa yana fadar.
鈥淜i biyo ni da robar ruwa mai sanyi.鈥�
Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye
lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda
tare da kofi guda daya tabi bayansa
A qaton filin wasan鈥� dake gefen lambun gidanta鈥� same shi
yana ta faman tika kwallo shi daya, duk
ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta
hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _
raya mata wasu abubuwa da dama cike t脿ke da mamakin
Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi
masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum
ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum
irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa
na fadar.
鈥淲ai ke k0 kurma ce ne?鈥�
Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta
durkusa鈥� gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, 鈥淕a ni.鈥�
Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, 鈥淗ankalin ki yana ina
ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki
ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali?
Tunanin me ki ke鈥�?鈥� 鈥�
' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif鈥榯a ta ya鈥榳uce yana
sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da
tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta
dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba.
Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake
gaban na鈥檜rar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa,
Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, 鈥淒on
Allah don Annabi
YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba
zan Kara ba.鈥�
nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya
dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi
mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba
abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike
da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan.
鈥� Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala
ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko鈥檌na
sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen
falukan da kujerun鈥�
Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran
wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake.
Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi
biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai
kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa
ba yabo ba fallasa yace 鈥淜ije ki sanar da kuku yau ina da
baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk
abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba
ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba.
Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da
sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a
falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe
ta zauna.
Ya鈥榶i wayarsa ya gama sannan ya matso inda
~ take ya鈥� mika mata wani key yana fadar, 鈥淜arbi
wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan
sauke bakin nawa.鈥�
Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita
kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun
ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne
in ba wanda ya saba ba.
鈥檇on ko wancan karan da za ta shigo falon nasa 鈥檃nty ce ta鈥�
bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin
* .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta
~samu ta bude kofar sannan ta shiga.
Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji
kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani
dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka 芦san odar
waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye
gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba
wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta
goge ko鈥檌na da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba
dayansu 鈥渢ayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala
sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da
turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin.
gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya
falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni鈥檌ma. .
鈥� Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi
saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, 鈥淪annu da fitowa
YallaBai an kammala.鈥� Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana
bin falon da
kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya
burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa,
tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba
sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum.
Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi
gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba.
Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito
yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa.
Ba tare da ya qaraso inda take ba ya ja. ya tsaya
hannayensa zube cikin aljihu, cikin sanyayyar muryarsa ya
ce, 鈥淎kwai katon din lemma da , robobin ruwa da aka kawo
suna cikin鈥� kanta, za mu shiga meeting karfe sha daya, kin
ga yanzu Saura minti goma ina so sha daya da rabi ki
dauko lemu da ,ruwa kizo ki jajjera a gaban kowacce
kujera, lemo daya robar ruwa guda. Akwai meat pie an
nadeshi guda biyu cikin tissue sai ki ajiyewa kowacce kujera
guda'a gaban teburinta. Ina fatan kin gane?鈥�
鈥� Saude. Ta daga masa kai alamar eh ya ce 鈥淥key, kuma
idan za ki shiga ban da surutu, ban ce ki yi wa kowa
magana ba da akwai kayan da zaki karba ki canza.鈥� Oya
ban san wasting din time je ki.鈥� 鈥� 鈥� Saude ta lallaBa ta mike
ta fice abin ta tana jinjina girman wadannan bakin a
wurinsa.
Tana shiga'Aunty ta miko mata leda ta karba ta nufi ciki, ta
watso ruwa ta flto. A tsaitsaye ta shirya duk da yanzu ta
dan nutsu ta shafa hoda da dan mai
鈥榓 labbanta, ta sawa idanuwanta kwalli, tunda ta lura bakin
kunya ne za a yi, ta zazzage kayan daga ledar Suit ne irin
na jikinta, amma na yanzu wando ne da siket ba, kuma
bakake neba sai rigar.cikin ce mai kalar jini,鈥� harda belt irin
ta mata. Mamaki ya. kama Saude shin k0 sun manta ita
diyar Musulmai ce ba arniya ba?
Taja ta zauna gefen gadon tana mamakin yanda za ta ratsa
mutanen nan da wadannan kayan, ta dafe kai tana jin
tamkar ta zabga da gudu. Bugun agogon dakin yasa ta yi
saurin dago kai qarfe sha daya daidai ta buga, Saude ta yi
saurin miqewa ta saka kayan wanda suka zauna mata a jiki
cif da cif tamkar
dama an auna ta, ta saka bakin takalmin kayan sawuciki
bakake marasa tudu
Ta janyo karamar himarta ta saka, wadda take ganin ta yi
mata qankanta nesa ba kusa ba,
bayan da ta Karasa ta fice da hanzarinta, tana faman rawar
jiki, sai kace angon kare
Karfe sha daya da rabi daidai ta dauki katon din lemo guda
da katan din faro tan nufi falon taron wanda take jiyo sautin
magana sama-sama a yi da
Hausa a yi da Turanci.
Saude na shiga ta ji tamkar ta zabga da gudu, saboda
yanda ta ga mutane sun kai ashirin Turawa bakar fata, shi
kuwa uban gayyar yana zaune a kujerar da ke tsakiyarsu,
da abun magana a gefen teburinsa, tsoro ya kama ta abin
ka da bagidajen mutum ta samu ta yi ta maza, ta shiga
zabga sallama, babu wanda ya amsa a cikinsu, mamaki ya
kama ta to su kuma wadannan wane irin mutanene da ba su
amsa sallama? Ta sa kai ta shiga tana faman muzurai
kamar wata marar gaskiya. 鈥�
Ta durkusa 鈥淚na kwananku?" Babu wanda ya . kalli inda take
ma balle ya san abin da鈥� take hankalinsu na kan jawabin
Dr., wani irin abu ya yi wa Saude tsaye a Kahon zuciya, don
ita a ganinta su ma sun yi niyar ci mata fuska ne. Don haka
ta shiga jera ruwa da lemon kamar yanda ya fada mata, ta
koma ta Kara dauko wasu sannan ta qarasa jerawa ta
koma ta dauko meat pie din su ma ta jejjera. Tana gamawa
ta tsaya gaban Dr. wanda ke dan rubuce鈥� rubuce a saman
wani Karamin littafl, sannan ta dan rissina.
YallaBai a kawo maka abincin ka nan ko sai ka
fito zakaci Wani irin kunya da haushi da takaici suka taruma
Dr Ahmad ya ji tamkar qasa ta tsage ya shiga ciki. Jin ya
yi. shiru yasa Saude tunanin k0 bai ji bane ta sake
maimaitawa. 鈥淵allabai nan za a kawo ma abincin ko,,,,,,,,
Tunkafin ta karasa rufe baki Dr. Ahmad ya rufe matashi
da鈥檞ani zazzafan marin daya rudarda ita, ya nuna mata
hanya.
鈥榞et out stupid girl Bace' min da gani bagidajiya kawai.鈥�
Saude ta dafe kunci cike da kaduwa ta juya simisimi ta fice
Tana fitowa daga falon tamkar wadda aka zungura ta fashe
da kuka mai ban tausayi, ta kifa kanta akan kujera tana
kukan ta babu mai lallashinta, ita kanta bata san tsawon
lokacin da ta dauka ba sai dai ta jiyo motsin mutane alamar
za a tito.
Ta zabura ta boye: bayan kujera tana jin su s脿ida suka
gama fita gaba daya, sannan ta fito cike da tsoro. Kai da _
ganinta kasan tana鈥榗ikin tashin hankali dan bata san irin
hukuncin da zai yanke mata ba yau, duk da bata ga
laifinda鈥榯ayi鈥檓asa ba, ammata lura ya dau zafi da * ita ta
qara fashewa da kuka Ya Allah Ka fidda ni tausayin kanta
ya kama ta.
Ita dai batayi sa,ar zuwa duniya ba tunda tazo batasan
masoyanta ba duk inda ta shiga da.
0 comments:
Post a Comment