*CHAPTER 17*
masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya
taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna
mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so
ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da
take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma
kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta
hadu da Hamid dibta kuIlum addu鈥檃rta kenan musamman
idan ta zo kwanciya bacci.
鈥淲ayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka
Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne
ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi
Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi
hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya
tsaya cak yana kallonta ya ma rasa
me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa
lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa
da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan
abinci a gun 芦
Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata 鈥榶ar
siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa,
wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar
farar fatar da hutu ya jika, hankalin
Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~
鈥榃ayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana
kuka, 鈥榃allahi ba da gangan na ajiyeba
Na rantse da Allah 鈥� ya runtse.idanuwansa ba tare da yace
da ita komie ba 鈥渢a rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan
abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita ya
鈥榶i karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi
yanda ta ga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire
himar din 禄 kanta tasa hakori 鈥漷a"yaga shi ta yagi kadan ta
daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar
yana kallonta yanda tabi ta gigicc ta rude fada take, 鈥楽annu
Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita
hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya'sake lumshe
idanuwansa sbaoda radadin da qafar kemasa yce 鈥楧auko
min wayata in kira likita. 鈥� .Hankalin, Saude ya: qara "tashi
da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma 'ne. Ta. sake
rushewa da :kuka ita ko yau ta san hukuncinta mai girmane
taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa, ita ta
zauna daga gefe tana 'kallonsa
Hankalin ta ya kara tashi tsoronta daya kada 鈥� jininsa ya
qare, don ta ji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zai yi,
ta sa hannu ta gage hawayenta cikin muryar kuka ta 鈥渃e鈥淜0
in kawo 鈥榤aka gishiri ka barbada tunda jinin yaqi tsayawa?鈥�
Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma?
Saude ta qara marairaicewa 鈥淒on Allah in kawo maka kada
jinin ka ya qare.鈥� Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya
narkar da zuciyarsa ya ji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake
langwaBe kai 鈥淚n kawo?鈥�-. Bai san lokacin da ya daga mata
kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka
ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalin鈥�
yan matan zamani 鈥�
Meke son faruwa da ni ne? Ya tambayi kansa. Tambayar da
ba shi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta
durkusa ta mika mesa gishirin, ya lusmhe idanuwansa ba
tare da ya yi magana ba, ta ce, 鈥淚n barbada maka?" '
Ya daga mata kai alamar eh, ta durkusa ta 鈥� 鈥榳arware
danrin' sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman
ya Bantale, bai san lokacin da
ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. 禄 鈥�
Saude ta watsar da gishirin cikin鈥� ta rike qafar tana fadar,
鈥淵i hakuri don Allah鈥榙a zafi ko?鈥�
Ya girgiza mata kai alamar a鈥檃, ita kanta ta san ya fada ne
kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar
bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai
crce ta a gidan. '
Wani irin鈥� tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta
'jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya
narkar da zuciyarsa, ya ji tamkar yasa hannu . ya shafi
gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulani鈥�: ta
daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe
idanuwansa a hankali. ;*A haka har likitan yazo ya same su,
ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya
amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna
yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi
ya ce 鈥楾sautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .鈥�
Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya
Janyo yar akwatin鈥榮a ta duba marasa lafiya, 鈥� saude ta miqe
da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . 鈥�
Yace ina zaki kuma
Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka ta ce,
鈥淶an fita ne ba zan iya kallo ba.鈥�
Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yaf8 komai
daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta
fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau,
wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a
da.
Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon
ta yi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai ka ce
munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna
tana fadar 鈥淎鈥� a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da
zuwa, ina wuni?" Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai
kama da
harara, kafin ta ce鈥淚na ne gidan naku? Lallai samun
wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan
, ya zama naku, kai gaskiya ne, an zo birni an asha jar
'miya ai dole a mance mafari.
To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a
Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci
unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da
buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki
same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya
mazaunai ake ke da
matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin
To ki sani kin kusa komawa gida,'dan an sa ranar auren ki
wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana
nan yana jiran ki."
Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta ji 鈥� tamkar
ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin
hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin
kuka mai ban tausayi.
Dillaliya ta鈥� tabe baki tana fadar, 鈥淜uka kama yanzu鈥� ki ka
fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan
don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo
wannan nataccen saurayin ki Hamid ya ce a kawo miki.鈥�
Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike
mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki
na rawa.
Dillaliya鈥� ta ce, 鈥淗ar na shiga mota ya zo da kansa har
tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,鈥� ke
kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo
ba.
Saude dai jujuya takardar kawai take, tana jin wata irin
soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da
ita ba shi ya mantar da ita kukan da take.
Ta mike cike da dokin san ganin abin da ke cikin *鈥榓mbulan
din, Dillaliya ta dube ta, 鈥楪idan wa za ki ai ba mu gama ba,
kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko鈥榢ina nufin haka
nan ki ka zauna ki ka
saki baki da ciki kina ta kwasar dadi ke da ki ka iya cin
dadi.鈥�
Cikin sanyin jiki Saude ta ce 鈥楰i yi hakuri Dillaliya wallahi
ban ajiye komai ba, tunda na zo babu abin da aka ba ni.鈥�
Dillaliya ta cce鈥淜e dalla tashi' can har sai an ba ki keba ki
iya 鈥榶an tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi
sake dashiki tattaraki boyeba
Saude ta ce 鈥淪ubhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?鈥�
Dillaliya ta ce 鈥淜e gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin
Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin
sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi 鈥�
Wani inn takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata
yanzu idan鈥� yar tace ta sanya ta? Cikin sanyin muryarta ta
ce, 鈥淏ari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su 鈥榊ar
Baba da Inna Laure da Baba na gode
Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa 鈥淚dan ubanki ya
ba ni kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su ba,
munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin
Kasa za a turbune ta sai mu ga qarshen jin dadi da kyau.".
Saude dai ba ta kula ta ba ta fice abin ta, tan shiga
bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman
Dirshan ta balle ambul脿n din ta zazzago abinda ke ciki
Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar
qaramar wayar saluka
Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara
zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar
takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama
rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman
rubutun ya burgeta ta dauki zoben nabazurfa dan sirir tana
jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan
yatsanta qarmi na hagu
Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin
takardar
Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana
lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta
gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira
sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa
Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na
kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba
amman zuci yarta ya bata hamid ne don haka hannunta na
kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama
Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar
muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da
sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana
Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa
yanxu saqona yaxo gareki hakane?
Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace
hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka
mance daniba yaya hamid?
Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa
dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata
gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana
fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat
bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a
rayuwa na miki wannan alqawarin
Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid
Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace
gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ?
Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat
nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh
saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda
aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin
abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike
ganin za,ayi don muna cikin matsala fa
Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an
fada mini
Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ?
Cikin kidima saude tace ina?
Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba
Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo
Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai
tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji birina kafin satin duk
yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat
ina tsoron in rasaki
Saude taja鈥榥umfashi kafin ta ce, 鈥淚nsha Allahu Yaya Hamid
duk yanda zan yi kafin satin zan yi ba za ka rasa ni ba da
yardar Allah.鈥�
' Dadi Ya kama Hamid nan ya ci gaba da jan ta da hira, su
kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka
jiyo ana kiran sallar Magariba.鈥�
Hamid ya ce 鈥淟ah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci
lokaci har haka, bari in je in yi sallah zan kira ki zuwa dare
kin ji sweaty na?鈥�
Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin
dadi ya cika masa zuciya. Ta murgina ta sake mirginawa
cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta
cikin irin wannan farin cikin ba 鈥� 鈥� 鈥溾€�
Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta,
ta ji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta
kara a kunne tare da rairo sallama
Hamid ya amsa tare da gaishe ta, ta amsa ba sai dai ta
maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya
nisa kafin ya ce鈥淜in san me wai ashe jiya yayanki yazo
gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?鈥�
Cikin zakuwa Saude ta ce, 鈥楰ai don Allah Yaya hamid yanzu
yana ina don Allah?鈥� ~
Hamid ya ce鈥淣ima abin da yasa na baro Kaduna ke nan
cikin daren na zo Katsina, amma sai na samu wai matar
gidanku ta sa mahaifinku ya yi masa korar kare, suka dinga
watso masa kaya waje cikin daren ya bar Katsina, amma ya
barma maqotanku saqo baki
Saudat ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take
tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki
Hamid ya ce, 鈥淎i kuma nifa ba wai na fada miki ba ne don ki
tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu
wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na
yarda da Kaunar da ke tsakanin ku na san in har yana da
rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri
don Allah kin ji?" Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya
kashe wayarsa.
Saudc ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya
dama she Yaya Rabi鈥檜 yana raye? Ashe 鈥榙ama bai mance
da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a
Lol labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta
wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada
tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya
tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba
gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara donjin ci gaban
wannan qaya taccen labarin idan naga comment sosai
zanci gaba anjima idan kuma kukaqi to sai gobe kenan
naku har kullum
Admin Dboy馃
[1/25, 9:29 AM] A A Dboy: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[1/25, 10:39 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 18*
1page is missing
Gaban Ahmad ya yi wata mummunar faduwa cikin sanyin
jiki yace, 鈥淟afiya kuwa me ke damun kine? Tamkar ba zata
tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin
tsayawa, sai da ya sake鈥� maimaita mata tambayar, sannan
ta samu ta tsaida
, kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan
Tace
鈥淵allaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa
dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum ba na
ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum
take neman rugujewa ne saboda wahala?鈥� YallaBai shin .....
鈥�
Kuka ya ci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta ta ci gaba
da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar
Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo
kamshin turaren da ke fatar shi.
Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta 鈥楽audat Wanda ya sa
ta dago kanta da sauri don bata taBa
zaton ya san sunan ta ba, kuma yau ne karo na farko da ya
taBa kiran sunan nata. Ya ci gaba da magana, 鈥楽audat k0
me rayuwa ta
' bada hakuri aka a karba, ki karBa' duk abin da rayuwa ta
zo miki da shi ki rungume shi, sai ki ga Ubangiji ya taimake
ki a duk inda ki ke, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba
sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.鈥� Ya
fada da siririyar 禄 murya, ta dago da jajayen idanuwanta
tana kallon ,
shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen:
鈥淜i daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin
ba ki tanadi mai share miki shi ba.鈥�
Saude ta鈥� yi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da
nauyi, ya dan razana tare da fadar 鈥淥h am sorry Ya mike ya
ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta
soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya
mayar aljihu, sannan ya ce
鈥淭ashi mu je ciki, kin ci abinci kuwa?鈥�
Shiru ta yi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu
ta mike, suka nufi falon kai tsaye
Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka
鈥榖a Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan
gwan'gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da
~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani
Qaramin plate wanda ya ji dafaffen kwai da madara
' ga shi ya dauki sanyi.
Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta,
sannan ya ja gefe ya zauna saman kafet din yana'
fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da ta ci, ba musu ta
sa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa
hadawa tana ci. Cake din * ya yi mata wani masifar dadi
don sai ta ce tunda take 鈥� ba ta taba cin abu mai dadinsa ba
ita kanta ta yi
mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi ta yi
don ba ta saba cin irin shi ba.
Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da ta ji babu wuri a
cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana
gamawa ta mike da niyar tattara
kayan, ya daga mata hannu.
鈥淏ar shi kawai za a tattara.鈥� Kallon shi kawai ta yi sai dai ta
gaza magana.
Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, 鈥淜ije kawai ki
huta', kin'ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?鈥� '
Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi
hartakai bakinkofa tajiyakira sunanta ta' waigo tana
kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai
ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, 鈥淧lease kar ki sake
yin kukan nan don Allah.鈥�
Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, 鈥淜in yi alkawari?鈥�
Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice
A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da
tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da
kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da
yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai
imani. _ ' .
Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss 鈥� call biyar
ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, 鈥� Allah Sarki
soyayya. Ta ajiye wayar karkashin
Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo
mata tamkar yanzu 鈥榮uka yin ta, ta yi wani 鈥漨urmushi tare
da yin wani juyi
. Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad
da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa,
saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana
dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce
gwiwarsa sai
bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da 鈥� 鈥漡aishe
shi.鈥�
Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa
mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda
ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare
falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki,
karaf su kai ido hudu, 鈥榞aba daya idanuwansa da
hankalinsaya tattara su a 鈥榢anta.~
鈥� 鈥橲aude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin
basarwa irin ta gogaggun maza ya鈥� yi
mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita
dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta
iya haka ta ajiye bonar din ta nufl
: ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _
鈥淕a ni鈥� Yalla Bai.鈥�. Idonsa na' kanta kamar mai san
karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce鈥淵a kamata a
tsaya da aikin
nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin
yunwa ba ne?鈥� Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna
tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki
Saudat ta sunkuyar da kanta qasa鈥� tana kallon yatsun
hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai
tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya
kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe
idanuwansa komai yake tunani? Oho.
Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye
masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, 鈥楪a
abincin. 鈥�
Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan
kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar
wani karamin yaro ya ce, 鈥淶ubo mana. 鈥� Saude ta yi saurin
kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa
ya hana,
don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta
zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, 鈥楶late
guda za ki zuba mana.鈥� Ba ta musa ba ta dauki saving
spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar
nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba
su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba
wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a
gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki
kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa 鈥榗okula
ta miqa masa.
Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan
murmushi a fuskarsa ya ce, 鈥淪annu.鈥� Ba ta amsa ba saboda
yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun,
kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da
plate din a gabanta shi
ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban
Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi
saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a鈥檃. Dr. ya
hade fuska tare da fadar.
鈥淜arbi mana meye haka?鈥� Yanda ya yi maganar cikin tsawa
ya sa ta saurin mika hannu ta karBa.
Ya ce 鈥淭o sa hannu mu ci maza.鈥� Ta yi saurin kallonsa
idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya
girgiza kai cikin damuwa ya ce 鈥淎bincin ne ba zaki ci ba shi
ne za ki yi kuka?鈥�
Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a鈥� a Ya kada kai cike
da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya
lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~
Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me
ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar
da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta
tsoro. Ji take tamkar ta mike ta
bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude
idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin
take cikin sanyayyar muryarsa ya ce 鈥淣a takura ki k0? Ki yi
hakuri kina iya tafiya kawai. 鈥� 鈥� Gaban Saude ya yi wata irin
masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce鈥淜a yi haquri dan
Allah 鈥� Ya dauke kansa kafinn ya ce 鈥淎ini banyi fushi ba.鈥� 鈥� .
. Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta
Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -.
yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin
da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana 鈥� fadar
鈥淜a yi hakuri yanzu ai zan ci.鈥�
A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da
idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da
saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya
dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa
cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata
kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin
nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire
nasa.鈥� a
Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar
ya aka yi? Shiru tayi 鈥渢a kwashe kayan ta dawo ta gyara
wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune
yanacikin karant
jaridarsa, ta dan durkusa. _ 鈥淶an tafi Yallabai ko akwai wani
abin da~ ka ke so?鈥� '
Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya
ce, 鈥淢e yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa ki ka
kasa sakin jiki?鈥� Saude ta yi shiru ba tare da ta iya cewa
komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna
ina san mu yi magana.鈥� Ba musu ta samu gefen kujerar da
yake zaune ta zauna a saman kafet. Dr. Ya wurgar da
jaridar kan kujera tare da gyara zama ~sosai ya harde
yatsun hannunsa guri guda sannan ya kira sunanta.
鈥� 鈥淪audat, kiyi hakuri da takura ki da nake ki daure ki ba ni
labarin ki ina san in ji labarin ki na damu da in san wace ce
ke kuma me ye dalilin kawo ki aikatau maimakon a inganta
rayuwarki da ilimi k0 dan ke ma ki amfanar da wasu a
gaba?鈥�
Saude ta yi shiru tana tunanin dan abin data sani a cikin
rayuwarta, idonta ya ciko da kwalla-ta dago tana kallon shi
da sarqaqkiyar muryarta ta ce
鈥淵allaBai babu komai a cikin rayuwaba sai duhu, . babu abu
guda na haske a cikinta, idan ma na samu
to ya suBuce mini. ban san komai a cikin rayuwata
ba sai wahala da. Qaskanci, haka rayuwar tawa ke tafiya...
鈥� Kukan da take riqewa ya soma kwace mata, ta sa
hannu tana goge hawayen kafin ta ci gaba 鈥� 鈥淣i dai nasan
ance an haifeni ne a gafin Katsina, kuma na bude idona a
cikinta, don haka na
ci gaba da rayuwa a yanda tazo mini a ciki, "tunda nayi
wayo na ganni a: gabana Yayana Rabi鈥檜 sai mahaifina
Malam Bala, sai kishiyar mahaifiyata Inna Laure da yarta
iKilima wadda ake ce mata 鈥榊ar Baba.鈥� 禄 A nan ta Iabarta
masa gaba dayan labarin rayuwarta har ya zuwa yanzu.
Tana gamawa ta kifa kanta a saman cinyarta tana kuka.
Tausayinta ya qara kama Dr Ahmad wanda yake jin tamkar
ya". zubar mata da hawaye, ya tausayawa halin da ta 鈥�
tsinci rayuwarta tun tana yar karamarta har girma ta
mallaki hankalinta, amma Inna Laure ba za ta bar ta haka
ba wannan wace irin macece? 鈥� ; Ya kira sunan ta cike da
damuwa ya ce.鈥淜i yi hakuri Saudat insha Allahu sai kin
yi,alfahari da rayuwarki ni zan maye miki gurbin Yaya
Rabi鈥檜 da kuma Hamid in dai ina numfashi. Saudat sai kin yi
鈥� dariya da farin ciki kamar kowace mace, ki kwantar鈥漝a
hankalin ki ki daina kuka haka kinji?鈥� 鈥� _ Kai kawai ta daga
masa alamar eh ya zaro ~ hankicif cikin aljihunsa ya mika
mata ta karBa ta鈥� share hawayenta sannan ta mika masa ya
karba kafin yace, 鈥淵anzu ki tafi kije Ki kwanta daga masa
alamar eh? Ya ce to shi kenan,鈥榢idab bani lokaci zan danyi
tunani a kan matsalarki kafin. in 鈥� samar miki mafita da
fatan鈥榙ai ba zaki yi fushi da;
Duk abinda rayuwa ta sake baki ba zaki karba da hannu
biyu
Saude ta daga masa kai alamar eh yace to allah ya kaimu
Jin yayi shiru yasa ta miqe ta nufi hanyar fita har takai
bakin korar taji ya kira sunanta ta waigo tana kallonsa yace
ki kawomin coffe yau da daddare kai kawai ta daga masa ta
juya ta fice abinta koda ta koma bangarenta ruwa kawai ta
watsa ta koma ta kwanta a binta wani barci ya dauketa ba
ita ta farkaba saida wayarta ta dameta da qara tasa hannu
ta dauka cikin magagin barci jin muryar hamid yasata
saurin watstsakewa daga baccin suka shiga hira sunfi awa
biyu a haka sannan sukai sallama da niyyar zai qara kira
zuwa anjima misalin qarfe goma daidai saude ta fito daga
bangarenta ta fita kai tsaye kichin ta nufa ta dauko flasks
din coffe da qananun kofinan da yakesha dasu ta nufi
bangarensa dasu saidai tun kafin ta qarisa ta hango
bangaren nasa dun dum babu alamar hasken wuta tsoro ya
kamata gashi bata taho da wayartaba ballentana ta haska
kuma babu damar ta koma
Wayyo allah taji tamkar ta fashe da kuka
Taja ta tsaya cak tana tunanin abinyi tun kafin ta
Qarasa nazarin taji wani haske mai Karfi ya taso da saukar
ruwan sama mai Karfi ai bata san lokacin data kwasa da
gudu ba ta yi Bangaren nasa, ba ga shi duk ta jike Tamkar
daga sama ta ji ta yi tuntuBe da wani abu ta fasa wata
uwar qara ta saki kayan ta kwasa a guje, karaf sukai kicibis
ta da mutum, ta sake kwala wani qara mai qarfi cikin
dabara ya rungume ta sosai a jikinsa yasa hannu ya kunna
wutar falon. Amma har a lokacin 鈥� ihu take tana, zullon
kwacewa, hannu yasa ya
tallabo qeyarta ya juyo da fuskarta saitin tasa su kai
ido hudu. Sai Alokacin ta tsaya da ihun ta saki wata _
. ' nannauyar ajiyar zuciya cikin muryar kuka ta ce 鈥榃allahi
ka tsorata ni na zata, na zata... 鈥檚ai kuma tayi
Shiru Yanda take maganar a shagWaBe ya barge shi har bai
san lakacin da ya saki wani murmushi ba yasa dan
yatsunsa ya lakace mata hanci yan fadar, . 鈥淵ou ar so
beautiful Ya lumshe idanuwansa tare da mata wani
murmushi,wadda ta tsaya iya makoshinsa kawai
' Sai a lokacin Saude ta lura da irin rikon da ya yi mata ta yi
saurin zame jikinta da na shi a kunya ce saboda yanda
ruwan. ya jika kayanta duk suka mammanne a jikinta
tamkar ba ta sa komai ba ta juya da gudunta ta bar falon
tana ji yana kiranta amma ba ta tsaya ba, haka ta koma
sashin nata cikin ruwan. '
Tana shiga ta hada kanta da bangon falon tana jin tamkar
qasa ta tsage ta shige ciki, saboda kunya da nauyi. Ai k0
ba za ta sake yarda su hadu ,ba duk rintsi kai dole ma in
bar gidan. nan, wannan abun " kunya har ina, musamman
idan鈥� matar gidan ta samu labari ai ita ta san ta kade har
ganyen ta. Kunya ta isheta tarinqa jin tamkar tarusheda
kuka.
Ta samu ta yi ta maza ta cire kayan ta dauko tsohon
zaninta ta yi daurin Kirji da shi ta haye kan 鈥� gadonta ta ja
bargo ta kwanta. Amma sai me? Da ta rufe ido sai ta ga
tamkar ga Dr. Ahmad nan zai rungume ta, ta zabura ta
tashi zaune tana muzurai, ga qamshin turarensa da ya
mamaye ta, ta yi wani gajeran murmushi tare da komawa
ta 鈥榢wanta: ta runtse idanuwanta a haka bacci mai nauyi ya
dauke ta. Washe gari tunda ta farka take zaune tana san
zuwa wurin aikin nata, amma kunya ta hana ta, ji 鈥� take ba
za ta iya sake hada ido da shi ba, don haka ta
gidan.
Ita kanta ba ta san ta dan lokaci ba sai da ta soma jin
cikinta na kukan yunwa, ta daga kanta ta kalli agogo. Sha
daya da mintina, tana shirin tashi zaune ta ji an turo Kofa
an shigo. Ta yi saurin tashi tana fadar, 鈥淪annu Aunty.".
Ta amsa da 鈥淵auwa Saudat laflyadai ki kek0?鈥� Saude ta ce
鈥淭o da sauqi dai kaina neke dan 鈥漜iwo.鈥� 鈥� .
Ta ce, 鈥楢yya, Allah Sarki kije Hajiya na neman ki tana falo.鈥�
Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa, ta ce, 鈥楲afiya
dai k0 Aunty? Allah yasa ba wani laifl na yi ba.
鈥� Aunty ta ce 鈥淭o laflya, YallaBai ne ya aiko kiranki.鈥� _
Hankalin Saude ya Kara tashi alamun tsoro ya . bayyana
karara a fuskarta, ta mike jiki amace tana fadar, 鈥淕a ni nan
zuwa.鈥�
Cikin sanyin jiki ta canza kayan jikinta sannan ta fito
zuciyarta na faman bugun dardari. harta qarasa .falon ta
hango鈥橝sma, tsaye riqe da Kugu, tana sanye da wasu
riga鈥榙a siket sari tare da 'mayafinsu tamkar wata
.Ba鈥檌ndiya, takalmin nan mai shegen tsini a qafarta.
A danyi nesa da ita Saude ta tsaye ta durkusa tare 鈥� da
fadar, 鈥業na kwana Haj iya.鈥� .
Asma ta watso mata wani razanannan kallo kafin ta ce
鈥楽hut up ke nan har marar kunya ce wace ce ke? Uban
waye uban ki a garin nan da har za kiqi zuwa aiki saboda jin
dadi har Dr. ya aiko kiran ki, me ki ke ji da shi a cikin gidan
nan? Me ki ka taka'?
, Banza sakarya jaka鈥� yar qauye.
Yau k0 rashin lafiya ki ke dole za ki sanar in ba daibakisan
inda kankiyake ba, tunda an ajiye miki wayar tarho da za ki
iya kira da ita ki sanar, amma ke isasshiya kin yi shiru abin
ki wato idan ana so a neme kito ki -sani wannan shi ne
laifinki na biyu cikin manyan laifukan da ki ka aikata a gidan
nan duk ran daki kikai na uku,kisani aranar鈥漽akikarbi
takardar sallamar ki kinji na fada miki鈥� Tana gama fada ta
juya ta haye sama a zafafe
Jikin Saude ya yi sanyi matuqa, ta lallaba ta mike ta fice
zuciyarta a cunkushe da baKin cikin yanda aka wulaqanta
ta ba tare da an saurari uzurinta ba.
Rayuwa kenan ,
Haka ta sa kai ta shiga falon tare da sallamar鈥檛a, tsaye yake
tsakiyar falon ya goya hannayensa a baya yana jin
sallamarta ya yi saurin waigowa ya nufo ta da hanzarinsa
Lafiya Saudat me ya same ki? Ba dai ruwan jiya
, neya saki zazzaBi ba?鈥�
Saude ta girgiza kai alamar a鈥� a, sannan ta durkusa tana
gaishe shi, bai iya amsawa ba 鈥� ya sake jefo mata wata
tambayar
鈥楤an yarda ba Saudat idan lafiyarki qalau me yasa yau ba ki
zoba?"
Saudat ta Kara dukar da kanta qasa tare da fadar, 鈥榢aina ne
yake ciwo kadan shi ya sanya.鈥�
Dr. ya ce ni dai na sani, :nasan baki da da lfy Saudat bari in
kira likita ya duba ki, kin ci abinci ' 鈥� kuwa? .
Da sauri ta ce ai na warke.
Dr ya. girgiza mata kai a鈥檃 Saudat ban san wasa da lafiya,
taso ki ci abincin kafin yaz0.
Ganin yana shirin riko hannunta yasa tayi saurin tashi da
kanta ta bi shi ya nuna mata tsakiyar kafet ta' zauna sannan
ya nufi dining ya dauko kayan abincin ya kawo mata, yau da
kan shi ya zuzzuba mata ya tura mata a gabanta tare da
fadar. ,
鈥楧on Allah ki daure ki ci.鈥�
Kai kawai ta daga masa, sannan ya wuce ya dauki wayarsa
ya kira likitansa. Yana cikin wayar ne Asma ta sawo kai
falon tana wani taku sai ka ce wadda take filin. gasar iya
taflya, Dr. ya zuba mata idanuwansa cike da tuhuma. 鈥�
Karaf idonta ya sauka kan Saude wadda tuni hanjin cikinta
ya shiga juyawa saboda tsananin
firgita da tashin hankali, Asma ta ja ta tsaya tana ,fadar.
鈥淢e nake gani haka Dr? 鈥榊ar aikin ce kecin abinci a faod
flask dinka, kam babban ....... 鈥�
Kai jama,a akwai rikici fa sai kunjini agaba donjin yaddah
zataci gaba da kayawa naku har kullum admin Dboy馃
[1/25, 10:39 AM] A A Dboy: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[12:17PM, 02/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 19*
鈥淢e nake gani haka Dr? 鈥榊ar aikin ce ke cin abinci a food
flask dinka, kam babban ....... 鈥�
Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar ya ce
鈥淭o k0 rai ya yi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a baki ba
k0? Ya yi mata tambayar cike da 鈥� isa da gadara. _
鈥� Asma ta qara shaqa kafin ta ce 鈥楬mm! Dr. kenan amma
dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa
kai girma ka yi bak0? A. Zo a iske yar aikin ka na cin abinci
a kwanan ka,
鈥榶ar aikin ma 鈥榶ar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci ya yi
masu daurin .....
Dr. yayi saurin daga mata hannu 鈥榶a isa haka Asma, kin
sanni sarai ban san cin fuska don Allah tunda ban aika miki
da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.鈥�
' Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da
sassauta mur'ya ta ce 鈥榊anzu Dr saboda 鈥榶ar aikin ka ka ke
cimin fuska haka?鈥� 鈥� Ya ce 鈥楢mma kin sani Sarai ba a gaya
mini yanda zan yi ko?鈥� Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta
bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda 鈥�
lomar abinci ta yi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza
hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da ta
Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar.
鈥淜i nutsu ki ci abincin ki sosai ga likita nan zuwa.鈥�
Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro
cikin kuka ta ce, 鈥榃ayyo Allah na ka ja mini Allah kadai ya
san abin da za ta yi mini yau na
banu na lalace! 鈥�
Dr. yace 鈥楰uka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin
kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. 鈥�
Saude ta Kara rushewa da kuka, 鈥榃allahi gida zan tafi鈥�
Dariya ta kama Dr. ya ce, 鈥楢she matsoraciya ceke lallai
Saudat na tabbata da Asma ta ji haushin ki da k0 sama da
qasa za ta hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san
halina ne sarai don haka ba ta damu da ke ba ta kaina za ta
dauki matakin don haka ki ma kwantar da hankalin ki ki ci
abincin ki 鈥�
Saude ta ture abincin tare da fadar, 鈥楴a qoshi.鈥�
鈥淢e? Ai wannan ne baki isa ba k0 ki dauka ki cinyc shi ko
yanzun nan in kira ta ince kin cetazo ta kwashe kwanukan
kin gama.鈥�
Saudc ta yi saurin waro ido waje tare da janyo
abincin da saurinta ta ci gaba da ci, ya yi dariya a ,
zuciyarsa sosai ya ce matsoraciya.
Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai
tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa
ya je ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a
kan ta rinka shan magungunan, sannan ya ba ta ta tafi
Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan
na jiranta. ' .
Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye
magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa
faman ruri tun dazu ta ci gaba da wayarta.
Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr.
tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita
take saboda wayar da su kai da Hamid jiya da
daddare
Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya
irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana
kallon Saude wadda ke durkushe tana 'goge goge
鈥� . Jikinta ya ba ta tamkar ana kallonta, don haka ta yi
鈥榮aurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde
hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude ta
yi saurin durkushewa tana masa sannu
da fltowa, bai amsa mata. 鈥檅a鈥� sai ma ya sake gyara
tsayuwarsa. 鈥淢e yasa baki san hutawa?鈥�
Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce 鈥楢i aikina ne shi
yasa.鈥�
Dr. yadan dauke kai kafin yace, 鈥楢i kin kusa barinsa, saki
wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.鈥�
Bai jira abin da za ta ce ba ya yi gaba abinsa,
Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita?
Ba dai korarta za su yi ba? Da sauri ta zabura ta bi
bayansa.
. Hadaddan wurinn shakatawa ne wanda aka kashewa
dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban
sha鈥檃wa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon
roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya
dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da
ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya
daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba ta ji ya fizgo
hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin
harshen turanci.
Mutuwar tsaye ta yi don tana bala鈥檌n tsoron sa sosai, don
ma yana dan Karami, sai ta ga ya 鈥檉adi' Kasa alarnar
gaisuwa. Dr. ya yi dariya yana kallonta ya ce 鈥淎na gaishe
kifa?鈥� Kallonsu kawai take bata 鈥� iya yin magana ba, birin ya
mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen
murna. ' ,
Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.鈥� qaton lilo
na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a
fuskarsa ya ce 鈥淚n hau za ki jujjuya ni鈥�?鈥� 鈥楧uk da
haushin riKon da ya yi mata ya kama ta sai da ta yi dariya
saboda yanda ya yi maganar.
Ya ce, 鈥極koy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya
ki.鈥� Tun kafin ta yi wani yunkuri ta ji ya sure ta ok ya dora
saman lilon.
Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba
daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na
kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da
ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana
sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana
zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya ta yasa ta bude
idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa.
鈥楧on Allah don Annabi ka sauko da ni.鈥�
Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, 鈥楾o sauko tunda
ba kya so.鈥�
Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata
bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata
hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya
yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. 鈥�
Saude ta yi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya ja ta
da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar
Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da
ita shi ma ya zauna, suka
sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude ta bi abin . da aka
dora' saman tebur din da kallo, wanda a kai 鈥�
鈥� rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko
ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da
fadar.
鈥淜arba mana.鈥�
Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din.
Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, 鈥榯saya tsaya waya
fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake'a take
bakauyiya ai bari ake sai an tafl.鈥� Yana maganar cike da
zolaya. .
Saude ta zumBuro baki" jin ya kira ta da bakauyiya, dariya
ta kama shi ya ce, 鈥楢鈥檃 鈥榶anmata ashe kin iya fushi irin
haka?鈥�
Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Ya ce, ' 鈥榃ai fushin
ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa
wuyana.鈥�
Dariya ta kubce mata yanda ya yi maganar a ladafce sai
kace ba YallaBai din da ta sani ba, ganin dariyarta yasa ya
mikc yana fadar
鈥淭aso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.鈥� 鈥�
Saudeta tashi ta mika masa gift din da ya bata, 鈥榶a dan
zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce
鈥楧a shi za ki tafi kyauta ce daga gare鈥� ni.鈥� Yana gama fada
ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za
tace ba.
Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta
komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta
saunan ta iya wage murya tana fadar, 鈥淣a gode kwarai.鈥�
Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba
ya Bace abinsa, ita ma ta yi gaba cike da zullumin
abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan
gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro
wani
kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a
jikinsa. Saude ta bi hoton wayar da kallo kai da gani ka san
ta yi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta 鈥楢llahumma
arzuquni" tasa hannunta ta bude kwalin.
Gabanta ya yi wata mummunar faduwa ta yi 鈥� masifar firgita
ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana
jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko
da kudl aka hada ta ba za ta iya kunnata ba.
Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni
Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye
suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake
ya jaza mata bala鈥檌n da ba zata iya dauka ba, yanzu
tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan?
Motsin taflyar da ta ji ne ya sa ta zabura ta maida
wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana
faman鈥榤uzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka
gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu
ta janyo ledar tana duddubawa.
Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da
mayuka, ta ajiye鈥� leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan
gari ya waye ta je ta maida
masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin
hankali da bala鈥檌n da ba za ta iya dauka. Ba
Dole nema ta runtse ido ta fada masa鈥� ya fita daga
rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana
nufin ba ta san mutuncin kanta bane da wannan tunanin
bacci barawo ya sace ta.
Washe gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu
kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace-
aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana
sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta
Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga
matattakalar yana fadar, 鈥淶o. nan Saudat." *
A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin
girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa' a tsanake
sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin
dagowa tana kallonsa, ya qara鈥榞yara tsayuwarsa tare da
maimaita mata tambayar.
鈥淣a ce laflya ba ki bude kyautar da nayi miki ba
Ko baki iya bane?鈥� Ya karasa maganar cike da tuhuma. ;
Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin
nutsuwa ta soma magana.
鈥淜ayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai na
ga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi'
tunanin maido maka, amma ka yi hakuri
Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman
hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce
鈥楧ama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa
cancanta ce to ke kuw kin ' wuce wadda a kai miki kinfi
qarfin hakan.
Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata
dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan
shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha
Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar
hawaye, kin fahimta?鈥�
Saude ta girgiza masa kai tana fadar, 鈥楢鈥檃 Yallabai yin
hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi
ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya,
na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da
shi zata dauki kowane irin mataki a kaina,
Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, 'Ko
kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum 鈥漚binda
Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji
don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai
tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma
akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke
alkawarin da na dauka.鈥�
Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka ta ce, 鈥楴a
san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata
qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. 鈥�
Dr. Ahmad ya ce, 鈥楬akan ma ba za ta kasancewa ba Saudat
ki daina ma fada.鈥�
Saude ta ce, 鈥業dan ya kasance fa?鈥�
Shiru ya yi yana kallonta Saude ta yunkura ta mike
hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar
zubowa cikin kuka ta ce, 鈥榋an bar gidan nan dole zan bar
shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa
kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi
kukan rashina, babu ba ni da shi.... Kuka ya ci Karfinta
sosai.
Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta
cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana.
鈥楧uk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu
inda za ki shiga ki layance min. Ina tare da ke Saudat har:
sai na ga kin yi dariya sai na ga rayuwarki ta inganta kin
samu farin ciki mai dorewa
na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da
hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.鈥�
Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga鈥� mata kai
yana fadar, "Tabbas kisa ido kiyi
kalio.鈥� 鈥榊a juya a sukwane ya fICe daga falon ya bar ta
nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata,
tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba
lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta
yi musu mummunan zargin da zai鈥榮a ta yanke mata hukunci
daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har
ta hango irin bala鈥� in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa
aikinta tas ta bro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a
kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza
mata Kwakwalwa. 鈥淲ai Saudat me ke damun ki ne shin k0
kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin
ki kwance yake tun yaushe nake fama da ke kina gocewa.
Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fad'a mini in fidda
raina kawai, amma don me za 鈥榢i ta yi min yawo da hankali
ki ce yau ki ce goba, idan kin san ba zaki iya fitowa daga
gidan ba ki 'fad'a mini ni in zo da kaina in dauke鈥榢i.鈥� 'Saudat
ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba,
ta ma rasa ta indaza ta fara, don . haka ta kwantar da
murya ta ba shi hakuri tare da yin .
masa alkawarin duk rintsi gobe za ta gudu ta bare 鈥� Abujar.
禄 ,
Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya yanzu
hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya
taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata
al鈥檃muran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da
wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai
da ta harhada kayanta tsab na barin garin. .
Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci
qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake
dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina.
Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana
bacci, don haka ta mike da hanzarinta za ta shiga bandaki
ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. '
Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar,
鈥楾o yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma ba ki samu damar
ba? .
Saude ta sauke numfashi tare da fadar, 鈥楴ina fada maka
Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi,
saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don
Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da
zai faru.鈥�
Ya ce, 鈥楬mm! Saudat kenan na lura ba ki san irin son da
nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi
yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a
rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan
ki dani please; 鈥�
Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda
yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya
ta ce, 鈥淜ayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin
yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu 鈥榶an
awanni zan maka kyakkyawan albishir.鈥�
. Hamid ya ce Allah yasa ki gaggauta kin ji?鈥�
鈥檒nsha Allahu.鈥� Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe
wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi.
wata mummunar bugawa.
A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura
mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya
tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat ta ji.tamkar ta
kurma ihu saboda tsaba: tsor da kaduwa duk ta
dabarbarce,.
, Dr. Ahmad ya take a hankali har zuwa gabanta ya mika:
mata hannu, 鈥淏a ni wayar.鈥�
Ba musu ta miqa鈥� masa wayar hannunta na rawa. Ya ce,
鈥榤iqo min har da waccan da na baki.鈥� Jikinta na faman bari
ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe
abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba
Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan
wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a
kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare鈥� ka
, Asma. ta fado kamar an an jefo ta, ' ' Saude ta Zabura ta
miqe a tsorace tana kallonta,
Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta
durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta
bakinta sai kyarma yake wurin fadin
鈥業n...ina... ina wuni
Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga
zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta
kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta
juyatafice batare datace uffan 鈥榖a.
Saude ta yi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta
yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai 鈥榳uya,
don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a
tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai
muzurai kawai take yi.
' Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, 鈥� tabbas
idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce
kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin Dr. Ahmad.
Qokon ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta
iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita
dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri,
ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta
nufi Gangaren nasa.
Sallamar da take shirin yi ta makale a
makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya
wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da
bayansa take saboda ya bada
baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi
marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi
mata mummunan zargi.
Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da
jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude
ta durkusa a gabansa muryarta a sanyayc ta ce 鈥楧on Allah
ka yi hakuri Yalla6ai wallahi ba...
Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi
taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar
muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana.
鈥淚n yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya
baci ne don na kama ki kina kula maza?鈥� Ya girgiza kai.
鈥淜0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar
nan samarinn ki neba zai rage ni da 鈥� komai ba, illah dai
kawai na tausayawa rayuwarki da ke qoKarin rugujewa, ke
yarinya ce Saudat ba za ki gane waye da namiji ba sai ran
da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci
irin wautar da ki kai a baya.
Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi
rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda
yasa na dauka zuciyarki shararriya ce
babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar
da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta
kai ki ta baro ki.鈥� Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza
kai, sannan ya mika mata wayarta.
鈥淯ngo ga wayarki.鈥�
Hankalin Saude ya qara masifar tashi ba ta san lokacin da
idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar
su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki
kafin ya ce 鈥楰ukan me za ki kuma Saudat ai na dauka
firgicin ki鈥榥a raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai na
ce na bar ki da shi, to me ye kuma abin kuka?鈥�
Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi
tsayawa ta soma magana cikin kuka. 鈥淜a yi hakuri wallahi
ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.鈥�
Nan ta kwashe labari ta ba shi tun daga sakon da ya aiko
Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. ya ja
numfashi kafin ya ce 鈥楽aude kenan, a dan labarin da ki ka
ba ni na fahimci kina son Hamid shin haka ne?鈥�
Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse
aka, ta rasa abin da za tace masa ma.
Dr. ya sake cewa, 鈥楧a ke nake magana fa Saudat kin mini
shiru
Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, ya yi mata masifar
kwarjinin da ba za ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin da
ke zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita
mata tambayar a karo na uku, ba ta
san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza
masa kai, alamar a鈥檃.
Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara
donjin yaddah zataci gaba da kayawa
[1/27, 10:11 AM] A A Dboy: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[1/28, 12:05 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
*CHAPTER 20*
Dr Ahmad ya ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce 鈥淜i je zan neme ki.鈥�
Saude ta share hawayenta ta mike a sanyaye tafi Dr. Ahmad ya bi ta da rinannun idanuwansa wanda sukai jawur.
Saude tana shiga dakinta ta fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai sauti, ita kanta ba za ta iya misalta tashin hankalin da take ciki ba, zuciyarta na wurin Hamid ta san dole ya neme ta tunda ta sanar da shi yau za ta bar gidan, shin idan ya kira ta bai same ta 鈥榖a wane irin zargi zai mata? Kila ma ya rabu da ita. Wayyo ni Allah na! Ta Kara rushewa da wani sabon kukan. Yinin ranar haka ta yi shi babu wata walwala a tare da ita.
. Da yamma liqis Dr. Ahmad ya aiko aka kira ta, don haka ta wanke fuska ta murza mai da hoda, duk wai don karya gane kukan data sha, sannan ta fice.
Da sallamarta ta shiga falon nasa, yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon, ya harde tamkar wani basaraken Balarabe, shigar ta manyan kayan ta yi masa masifar kyau ta Kara fitowa da cikar kamalarsa da kwarjininsa.
Saude ta durqusa dan nesa da shi kadan kafin ta ce, 鈥楽annu dahutawa YallaBai.鈥�
Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuWansa kafin yace, 鈥楳e ya samu idanuwan ki Saudat, kuka ki ka rinka yi tun tafiyar ki k0?"
Da sauri ta girgiza masa kai alamar a, a 鈥楬mmm! Saudat kenan me yaSa kike san boye mini damuwarki alhalin duk wani motsin ki sai zuciyata ta fassara mini shi Ya girgiza kai tare da fadar 鈥楾ashi mu je ki min rakiya cikin gari.鈥� ,
_ Da hanzarinta ta yi saurin daga kai tana kallonsa Dr ya mike; tare da fadar kar ki ce komai biyo ni kawai. Saude ta mike. jikinta a sanyaye tana shirin fashewa da kuka yana kallonta bai kula taba ya yi gaba abin sa.
鈥� Saude ta bi shi tana matsar kwallarta ita dai so yake kawai ya jaza mata tashin hankalin da ba za ta iya dauka ba kawai. Suna fitowa harabar gidan ta samu masu tsaron lafiyarsa wadanda suke a lungu da sake na gidan sun nufo sa, wasu kuma sun nifi wurin motocinsa wadanda yake fita da su
Dr. Ahmad ya daga masu hannu kawai ya nufi wata shareriyar Jeep mai qofa takwas fara mai bakin gilas, daya daga cikin masu gadin nasa ya take da gudu ya bude masa kofar baya '
Dr Ahmad ya juya yana kallon Saude wadda ke tanya tamkar鈥� yar kaciya, ya yi mata nuni da hannu alamar ta shiga ta ji tamkar ya dora mata dukkanin tashin hankalin duniya ta ja ta tsaya cikin
tsananin kidima
Dr Ahmad ya dan matsa daf da ita muryarsa Kasa
kasa ya ce 鈥榋a ki shiga k0 k0 sai na dauke ki na shiga dake da kaina?鈥� .
Ganin yanda ya matso ta ya tabbalar mata zai iya yin abin da ya fada din don haka ta janyo dauriyar duk duniyar nan ta dorawa kanta, ta taka a sanyaye ta 鈥� shiga motar, tana zama shi ma鈥榶a shigo aka maido masu kofar aka kulle
Saude ta ji ta yi mutuwar zaune idan ta ce bata cikin tsananin rudu da kaduwa ta san ta yaudari kanta. Ta lumshe idanuwanta tana sauraren bugun zuciyarta ta san ita yau tata ta Kare ba abin da zai hana Asma na samun labari tasa bindiga ta. Harbeta
Shiru babu wanda ya yi magana a cikinsu. Sai Dr. Ahmad neya dan mika hannun shi ya latsa gefen motar, sai ga wasu hadaddun labulaye sun zagaye motar , ya mika hannu ya bude na鈥檜ra mai KwaKwalwa (Computer) din da ke gabansa wadda ke jikin motar ya kunna, sannu a hankali ta kama tamkar talabijin din bango.
Ya koma ya jingina ya ci gaba da latselatsensa ba tare da ya kalli inda take zaune ba, kowa da abin da
yake sakawa a zuciyarsa.
Ba ta san sun iso ba sai dai ta ji an bude masu qofar, Dr. ya rufe computer din ba tare da ya kalle ta ba ya ce 鈥楩ito mu je. 鈥� Bai tsaya ba ya sa kai ya fito don haka ita ma ta ziro qafafuwanta ta fito tana kallon harabar wurin da suka shigo.
wurin gyaran jiki ne wanda ya amsa sunansa a cikin garin Abuja daga sama an yi rubum da manyan ..
baki a jikin wani karfe ANNURI beauty QUEEN rubUTun ya bada hasken
鈥� Dr Ahmad ya yi gaba Saude na biye dashi har suka iso cikin masu take masa baya daya yayi saurin isa ya bude musu qatuwar kofar ta gilas tareda gaishe
suka shiga qaton wurin mai kamar an gina shi da' zallan gilasai Da kyar Saude ke dosana kafarta鈥� dan gudun kar ta fasa gilas din
Suna shiga ciki su kabi wata qofa mai kama da ofis,鈥� Dr. ya tsaya gaban wata mata cikin Harshen turanci su kai magana sannan ta miqa masa wata yar lakarda ya yi wani dan rubuce rubuce ya miqa. mata itasa hannu, 鈥� sannan ta mike ta yi masa nuni da wani kujerar dake gefe da dan tebur dinta guda a gabanta; wanda aka dora News paper a sama, ta kawo masa lemu da cake sannan taja hannun Saude. .
鈥淐ome and enter my frnd Saude ta ce ikon Allah ai ke kika san shi
Tasa hannunta cikin na Saude suka shiga cikin wani qaton wuri nena gaske wanda aka zubama duk wani" injin 鈥� k0 wata na鈥檜ra ta gyaran jiki 鈥楳atar ta kira wata babbar mace Bahaushiya wadda ba zata wuce shekara arba in ba ta nuna mata Saude su
Sukai kai magana cikin harshen turanci da matar ta mikawa Saude鈥榟annu da murmushi a fuskarta tana fadar.
鈥淵ou are welcome my sis. '
Saude ta yi sukuti tana kallonsu cike da takaicin turancin banzan da suke mata. K0 matar ta lura ne? Oho ta canja harshe zuwa Hausa.
鈥淪annu da zuwa 鈥榶ar uwa mu je k0?鈥�
Ba musu Saude ta bi ta suka nufl Bangaren gyaran gashi, ta zauna a kai mata gyaran gashi sosai sannan suka wuce Bangaren gyaran jiki, inda a kai mata dilka da halwa lokaci guda, daga nan a kai mata gyaran qafa
da na akaifa. Tun kafin a qarasa dama Saude ta gama tsurewa da
tsabar kyan da ta gani kwance a jikinta, ita kanta ba ta taBa sanin haka ta hadu ba sai yau, don k0 Indiya sai
haka, saboda idan baka san ta ba aka ce maka Ba鈥檌ndiyace ba yanda za ai kai musu. '
Ita kanta ta san sun ci lokaci, don k0 da ba ta duba agogo ba ta san dare ya ja sosai. Ana gamawa suka fltO inda Dr. Ahmad ke zaune rike da jarida yana dubawa suna Karasowa ya ajiye jaridar ya mike yana kallonta tamkar wadda ta fado daga sama, lokaci guda kuma ya lumshe idanuwansa ya bude ya juya ya koma wurin 鈥榶ar Baturiyar nan wadda ke ta latse-latse cikin computer ya mika mata A.T.M dinsa tasa ta cire kudin sannan suka flto daga wurin.
Ita dai Saude kallonsa kawai take, amma tambayoyi ne cike fal da cikinta, wanda ta tabbatar ba *
ta da mai amsa mata su sai shi kadai. Suna mota wanda suka shiga kamar dazu direba ya ja su suka fice daga 禄 harabar wurin Saude ta lalubo duk wani karfin halinta kafin ta iya bude baki ta kira sunansa.
鈥淵allaBaii鈥� ,.
Dr. Ahmad ya dago da idanuwansa daga saman wayarsa yana kallonta kan ya ce, 鈥榊a dai Sande?"
鈥溾€� Ta dan sha Jinin jikinta kafin ta ce 鈥業na so in dan 鈥� yi wata鈥� yar tambaya.鈥� ce
Dr ya dauke kansa daga kanta kafin yace, 鈥楾un 禄 kafin ki yi tambayar na san abin da za ki tambaya don haka ki yi haquri ki hadiye zan ba ki amsa da kaina 鈥� idan lokaci ya yi.-鈥�
Za ta sake magana ya daga mata hannu, hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke a dole, ta bar zuciyarta na faman鈥� dukan tara-tara. Suna isowa gidan ta .kwasa da sauri da niyar ta riga shi shiga gidan, Dr. ya yi saurin tsayar da
ita ta hanyar kiran sunanta, ta ja ta tsaya cak 鈥� Da kansa ya Karaso har inda take ya daidaita tsayuwarsa a gabanta kafin ya soma magana, 鈥楰i shirya gobe da safe za mu fita.鈥�
Saude ta yi saurin dago da fuskarta tana kalloh shi shi ma ya zuba mata idanuwan nasa wanda babu alamar fargaba a cikinsu,idanuwanta suka kawo kwalla cikin muryar kuka ta soma magana.
鈥淣i wallahi ,ba zan je ba na gane so kawai ka ke ka jaza min bala鈥檌n da ba zan iya dauka ba na rantse da . Allah babu inda zani .... 鈥� Ta Kara rushewa da kuka.
鈥淒on Allah don Annabi ka taimake ni kar ka jaza min bala鈥榠n matarka don Allah...鈥�
Dr. Ahmad ya yi wani murmushi wanda ya tsaya iya laBbansa kawai kafin ya ce, 鈥楢she kina da baki haka? Da kyau. To ki dai shirya鈥� fita gobe koma me ye zai faru ai kina iya daukarsa idan kuma ba ki zoba to ki tabbatar ni da kaina zan shigo in dauke ki kin san kuma zan iya, don haka sai da safe.鈥� .
Ya juya ya yi gaba ya bar ta tana masa rakiya da kallon da ke cike da mamakinta karara, don a yanzu hawayen ma sun daina zuba. Mamaki da fargaba suka kashe ta, ita kanta ba ta san tsawon lokacin da ta dauka a tsaye ba, don sai da ta yi da gaske sannan ta iya jan qafafuwanta ta yi gaba.
Tunane-tunane da damuwa yau su suka hana Saude barci da wuri, shekarunta sun yi Karancin da za ta iya yankewa kanta hukunci, da ta gaji da tunanin sai ta kifa kanta samaun filo ta shiga kuka mai sauti, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru don kanta, babu wanda ya lallashe ta, sai ajiyar zuciyar da take ajewa akai akai. A' haka barci barawo ya sure ta ba tare da ta sani ba. '
Tun da garin Allah ya waye Saude ke zaune saman gadonta ta zuba uban tagumi da hannuwa bibbiyu, kana kallonta za ka tabbatar da tsantsar damuwarta, ba 芦 ta ankara ba taji an turo kofa za a shigo. ,
Gabanta ya yi mummunar faduwa ta zabura ta miKe tana faman muzurai don duk a zatonta Dr. Ne
Aunty ta turo Kofa ta shigo da sallamarta Saude ta ja wata ajiyar zuciya sannan ta koma ta zauna Aunty ta 鈥� 鈥榙ube ta da kulawa kafin ta ce, 鈥淟afiya kuwa Saudat?"
鈥� Saude ta dake kafin ta 'ce, 鈥楳e kika gani Aunty?鈥� 鈥楴a ga duk kin yi wani wurjanjan ne kamar ba kya cikin hayyacin ki.鈥� '
Saude ta girgiza kai 鈥楢鈥檃 lafiya ta qalau kawai dai
.tunani me.鈥� ~ Aunty ta dan zuba mata ido kafin ta ce, 鈥楰ai Saudat ban yarda da ke ba jeki gaban madubi ki kalli 鈥� kanki da kyau, ki ga yanda kika koma, wannan kyan da daukewar lokaci guda na mene ne?鈥�
Gaban Saude ya kara mummunar bugawa duk ta dabarbarce ta rasa abun fada. '
Aunty ta girgiza kai tana wani murmushi wanda 鈥榖ai kai zuciyarta ba ta ce, 鈥楽audat ke nan ni ba tun yauwa ba na fara zargin ki, sai dai a yau na kara . tabbatar da zargina, Saudat gyaran jiki ki kaJe,鈥�
Gaban Saudat ya Kara wata mummunar bugawa a 鈥� karo na biyu, idanuwan nan suka yo warwaje . Aunty ta ce鈥淗mmm! Saudat kenan me yasa ki ke
Kokarin yaudarar kan 'kine? Me yasa ki ke nema ki dorawa zuciyarki wahala ne? Shin Saudat kin yi tunanin wannan kyan naki zai iya daukar hankalin maigidan nan ne? K0 kusa wallahi k0 da wasa don Yallabai ya wuce duk wani tunaninki 鈥� ki Don idan har kyau na daukarsa to duk inda ake Zuwa auro: kyakkyawar mace a fadin duniyar nan:
'yana da kudin da zai iya aurarta ke k0 siyowa ake yi yana da kudin siyan ta.
Saude duk yanda baki tunani ba Yallabai ya wuce da sanin ki nasan YallaBai tun kafin ya auri Asma鈥檜 asalina 鈥榶ar aikin gidan su ce. Saudat wallahi . wallahi yar gidan shugaban Kasa har falon Hajiyarsa ta zo nemansa, amma ya fice ya bar mata gidan bai kula ta kanta ba. Saudat duk yanda ki ke ganin YallaBai ya wuce 鈥檔an, don jin kansa da mazantakarsa ya wuce yanda kike ganinsa a cikin gidan nan, don ni kaina ba zan iya kirga yawan 鈥榶an matan da ya yi ba tsakanin Abuja da sauran jahohinnan ba. Saudat ina guje miki daukar Dala da Gwauron Dutse aka, don idan ki ka bari Asma鈥檜 ta samu labari ina mai tabbatar miki sai kin raina kanki.
Don k0 da ki ke ganin kamar ba su damu da juna ba, to wallahi suna son junansu don kuwa auren soyayya su kai kamar za su cinye junansu. 鈥�
Asalin Asma 鈥榶ar asalin nan Abuja ce mahaifinta shi ne Ministan kudi na Nigeria a lokacin kafin ya sauka daga kujerar. Mahaifinta abokin mahaifin Yallabai ne ba zan taba mantawa ba sun taba zuwa gaishe da mahaifin Yallabai da Asma da mahaifinta da mahaifiyarta a lokacin shi mahaifin Yallabai yayi yar rashin lafiya.
Anan ne suka hadu da Asma da Yallabai, tun farkon soyayyarsu sun 鈥榯iffita qasashe masu yawa,
Soyayyarsu ta dauki tsawon lokaci kafin a tsaida maganar aurensu A lokacin ne kuma iyayensu suka sanya su harkar Siyasa Cikin sati biyu a kai bikinsu aka gama cikin ma 鈥檃ikatan da aka bai wa Asma Hajiyar Yallabai ta 鈥� hada masu dani na dawa gidansu da zama.
A lokacin basa wannan kasa basa wancan kasa cikin wata guda ba baifi su zauna nigeria sau biyu ba Daga baya ne kuma aka fara kamfen to sannan ne suka zauna aka fara yaqin neman zabe ita da shi duka kowa yana neman tasa kujerar shi yana neman dan majalisar tarayyar Abuja, kuma cikin ikon Allah kowa ya samu.
To a lokacin ne fa kowa ya kama gabansa, haduwa ma sai ta yi masu wuya suna cikin gida daya, amman sai suyi wata wani lokacin basu hadu ba, sai dai k0 cikin dare, amma idan wannan yana Nigeria to shi wannan ya bar kasar,idan wannan ya dawo to wannan ya tafi wurin meeting. Haka dai abin ya ci gaba da kasancewa
Kafin zuwan ki Asma ta samarwa YallaBai 鈥榶an ' aikin da zasu rinka kula da shi sun fi biyar duka an karesu kowacce da tata matsalar har zuwa kanki Saudat da ki ke ganin Asma ba qaramar mai arziki ' bace duk yanda ki ke tunanin rashin mutuncinta ya
wuce nan musamman a kan mijinta鈥� Don tana da masifaffen kishin da ba ki tunani zata iya yin komai a kansa, don haka Shawara 鈥榥ake baki
Don ina sonki saude ki kama kanki tun kafin
Yallabai ya lura da takun ki, idan kunne yaji Ta tabe baki tare da juyawa ta fice
Saude ta saki wata ajiyar zuciya mai qarfi shin in ban da abun Aunty ma ita ko giyar wake ta sha ai ba ta fara hada kanta da YallaBai ba, balle da hankalinta .dama abin da take gudu kenan mummunan zargi, shin yanzu ma idan suka sami labarin fitarsu jiya ya kenan? Ta girgiza kai cike da fargaba ta yunkura ta mike don tsoron kar ya zo da kansa ya Kara jaza mata wani zargin, ta zura takalmanta sannan tafi ta nufi bangaren nasa. :
Tana shigowa falon shi kuma yana saukowa daga
matattakalar benan, sanye yake da shigar qananan kaya, koriyar riga da bakin wando sai takalmin qafarsa 鈥� na fata, yau babu gilas a fuskarsa don haka kana ganin fararen idanuwansa fat masu kama da farar takarda, sumar kannan tasa ta sha gyara sai sheki take hannunsa na rike da makullin mota. , Saude ta durkusa a qasa jikinta a sanyaye tana gaishe shi. Dr. Ahmad ya amsa mata cike da kulawa kafin ya ce, 鈥楽audat ya na ga kamar kina cikin damuwa laflya dai k0?鈥� '
Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai Dr. Ahmad ya Kara matsowa daf da ita ya sa hannu ya mikar da ita tsaye cikin raunanniyar muryarsa ya ce,鈥� 鈥淏an yarda da babu komai ba Saudat, ki fada mini me .ke damun "ki, ?" Ya yi tambayar yana nuna kansa,鈥� , Saude ta girgiza masa kai alamar a鈥檃. 鈥�
Ya CE to waye?" Idonta ya kawa kwalla ta yi
shiru ba tare da ta yi magana ba, dan tana motsa ~ bakinta kuka ne zai kubce mata
Zuciyar Dr ta cika da tausayi muryarsaa sanyaye ya ce 鈥濃€楽audat kina cikin damuwa na fahimci yanda ki ke ji a tawa zuciyar kiyi hakuri insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe Taso muje Saudat.
Ta yi saurin kallonsa da idanuwanta dake cike taf 鈥榙a kwalla tana qokarin yin magana ya dora danyatsansa saman labbanta alamar ta yi shiru kar ta ce komai, sannan ya yi gaba abin sa. Saude ta lallaba ta mike ta bi shi tana goge kwallarta.
Yau da kan shi ya ja motar cikin wata qaramar mota 鈥榶ar dunkulalliya mai鈥� kofa biyu wato sport car, iya shigar mutum biyu ce mai bakin gilas irin wanda duk nacin ka ba ka isa ka gane wanda ke ciki ba.
_ Kai tsaye wurin da suka je jiya ta ga sun nufa ita 鈥榙ai kallonsa kawai take kamar jiya haka suka shiga ya' yi rubuce~rubucensa aka shiga da ita wajen 'Washing and dressing. > 鈥� Cikin awannin da ba su fi uku ba aka gama mata 鈥� kwailiyarta tsab cikin wasu hadaddun kaya . ready made riga da siket English wears bakin siket da falmaran mai jinin kart. Falmaran din ya kawo mata 鈥榟ar kusan kugu mai dogon hannu sai bakin siririn gyale wanda aka nade mata tamkar nadin Larabawa ya tsaya iya wuyanta Gyaran gashin da , akai mata ya zubo ta gefen fuskarta ya sauka har
fadarta; Rigar ta ciki ta kamata sosai surarta dukta bayyana ta bi ta lafe jikinta, falmarar din mai budaddan gaba ce hakan yasa babu abin da ta rufe
. Takalmin kalar baqi ne mai mai tsini sai jakarsu 鈥榶ar Post mai dan girma. Suna鈥� gama mata suka sa camera suna mata hotuna dan su~kan sun san ta yi masifar haduwa k0 gasar sarauniyar Indiya zata iya kyan da zata yi kenan. Ni kaina dai marubuciyar ban san Saude ta hadu haka ba sai yau, lol ta koma tamkar wata jugunanniyar hadaddiya wayayya classical.
Shi kan shi uban gayyar duk yanda ya so daurewa sai da ya tofa ,
鈥淜ai Saudat wannan cinyewar fa haka? Dama haka ki keda kyau ko dai idona gizo yake min wallahi am so suprise
Saudat dai iyakar ta ido, sannan ya biya kudin suka fito
A mota ma sai dai ya dubeta, 鈥淜in san wallahi kin yi kyau gaskiya Momy za ta yaba da ke
Saudat ta yi saurin kallonsa, 鈥楳omy kuma?鈥�
Ya daga mata kai 鈥淚ta fa dan yau yawo zamu sha tun daga gidan sister Farida har gidan Uncle B da 鈥� gidanmu inda aka haife ni yau za ki ga Momyna da Dad dina ai za ki yi farin ciki ko?鈥濃€�
A sanyaye Saude ta daga masa kai amman zuciyarta cike take da zargi da kuma dumbin fargaba '
Tafiya su kai mai nisa sosai kafin su iso Maitama, Dr. ya ja ya tsaya a bakin gate din wani gida wanda ya ke zagaye da manyan furanni masu kyan gaske ya yi horn ,maigadi ya bude sannan ya cinna hancin motar cikin gate din gidan.
Ya samu wuri ya yi fakin ya dubi Saude fito mu je ranki shi dade k0 sai na fita na bude miki? Saude ta yi saurin watsa masa wani kallo mai kama da harara.
Ya yi wata dariya harda kyalkyalawa kafin ya ce 鈥榃annan kallon fa yallabai ne fa.鈥� Saude ta yi saurin turo kofar ta fito tana gunkuni irin na shagwababbun yara Dr. ya fltO daga motar yana zolayarta. Maigadi ya kwaso da gudu ya nufo su ya zube gaban Dr. yana kwasar gaisuwa, ya Ciro kudi masu yawa ya mika masa ya shiga godiya tare da kirari. Dr. ya dubi Saude 鈥楳u je鈥� Ba musu ta juya ta bi shi suka nufl cikin gidan. .
Ita dai ta gama saduda duk yanda Allah ya yi da ita mai kyau ne ta riga ta fidda rai da rayuwar gaba daya. A bakin qofar falon suka tsaya yana Kwankwasa qofar, can ta ji wata murya na fadar, 鈥淲ho is knocking?鈥�
鈥淏rother. 鈥滵aga can suka ji ta fasa wata uwar Kara da takun gudunta. Dr. ya murmusa ya kalli Saude tsakiyar ido ta yi saurin janye idanuwanta. Tana bude qofar ta yi wani tsalle ta fada jikinsa tana dariya, Saude ta saki ido da bakl tana kallon su. Ikon Allah su kuma haka tasu dabi鈥榓r take?
,ckin dariya take fadar. Woo my my bros; ,nayi kewarka.鈥�
鈥楧r: Ya yi dariya tare da janye ta daga jikinsa yana nuna mata Saude tare da fadar 鈥淵ou see her did Is my Saudat
' Da sauri ta maida hankalinta kan Saudat, ta sake juyowa tana kallon shi tana fadar, 鈥淎re you sure?鈥� '
Ya yi wani takaitaccen murmushi yana fadar, yes am sure my sis.鈥� "
Ta yi wani tsallen murna ta dafo Saudat tana fadar 鈥淲ow my bross wallahi na ji dadi sosai, Saudat 鈥� sannu da zuwa mu shigo don Allah.鈥� 鈥� 鈥�* Saude dai kallon su kawai take tana dafeda . kafadarta har cikin falon, tsararran gaske wanda ya ji kayan alatu na more rayuwa iri-iri Da kanta ta zaunar da ita tana fadar. 鈥榋auna nan my sis, da me dame ki ke so a kawo miki yanzu, tun daga snacks, lemo abinci, fruits, duk komi ki fada don wallahi naji dadin zuwanki my bross na gode fa.鈥� Murmushi kawai ya yi mata, ta Kara jawo Saude a jikinta 鈥楴a ce don Allah ki saki jikinki munfa riga
Mun zama daya yanzu dan na san nan ba da dadewa ba ' zaki shigo cikinmu haka ne? 鈥�
Saude da ke jin manganun tamkar saukar markade ta yi tamaza ta daga mata kai. Faridat ta ce 鈥楪ud ai dana sani.鈥� Ta dubi Dr kai kuma fa yaya me ka keso k0 , ,
duk kun bani zabi? Ya ce a a karki wahalar da kan ki dan yanzu haka gidan Uncle B za muje daga nan za mu wuce gidansu Dad, don haka kl kawo mana lemo kawai
Faridat ta bata fuska ta hau diredire tana fadar, wallahi ban yarda ba Allah
Dr. ya yi wata qasaitacciyar dariya kafin ya cc, 鈥榃ai ke har yau ba za ki girma ba k0 kin manta ke ki ka aje Affan da Ummy ta?鈥�
Dariya ta yi ta juya ta bi wata hanya cikin falon nata, tana fita Saudat ta yi saurin kallonsa tana shirin yin magana ya yi saurin daga mata hannu alamar ta yi shiru, a dole ta ja bakinta ta tsuke
Gaba daya falon ya dauki shiru sai dai kukan A.C da talabijin din da ke ta faman haukanta ita kadai. Ba tafi minti goma ba sai ga ta ta dawo dauke da wani qaton tire ta ajiye saman tebur, lemukan kwali ne guda hudu sai kofuna masu kyau sai robobin Faro biyu, sai fruits kala-kala sai wani tangaran din da aka zuba dambun mama a ciki, sai daya plate din hadaddan chips din dankalin turawa ne. Farida ta dube su.
鈥淒on Allah kuba ni minti goma zuwa sha biyar k0 dan wani abu ne marar nauyi in girka muku.鈥�
Dr ya ce鈥楰in san Allah sauri muke wannan ma is okay. 鈥� Ya tashi ya matso inda Saude take zaune da
muryarshi qasa-qasa yace, 鈥楾unanin me ki ke Madam鈥�? Kallonshi kawai ta yi ba ta tanka ba.
Faridat ta yi murmushi tana fadar, 鈥榃allahi Yaya '
ka yi zabe: kuma mai kunya, amma Bufullatana ceko?鈥�* Murmushi ya yi tare da fadar, 鈥楤ana san sa ido fa.鈥� . Ta yi dariya tana fadar, 鈥楢i dan Safwan baya nan ne 鈥� wallahi daka sha tsiya, ya tafi ya dauko su Affan daga makaranta, amma don Allah yaushe za ku dawo don . gaskiya ni dai wannan zuwan ba nawa bane
Dr. yace鈥楽ai ki tambayi Madam din dan in gobe ta ce in dawo da ita kin san zan iya.鈥�
Farida ta yi. saurin riko hannun Saudat tana fadar, 鈥楧on Allah don Annabi ki taimaka Anty Saudat ki dawo kin ga dai ni yanzu qanwar ki ce
Yanda ta yi maganar ya tilastawa Saudat yin dariyar da ba ta shirya ba, har da Kyakyatawa a haka Farida ta ja ta jikinta har ta samu ta saki jikinta da ita sosai kamar sun dade da haduwa, kasancewar Farida mai shegen surutu ga barkwancin tsiya da iya bada labari.
Inda suka bambanta da Dr kenan ita tafi shi Magana shi kuma bai da magana sosai; amma kamar su daya kamar an tsaga kara, har wajen tsawon kana ganin su ka ga 鈥榶an gida 鈥榙aya. .. ~ Da wayo da wayo sai Dr ya yi da gaske sannan suka samu suka bar gidan Farida, ta hadowa Saudat ~ kayayyaki cike da wata qatuwar jaka mai girma Kirkinta ya bawa Saudat mamamki, kwata-kwata ba ruwanta da Jin kai k0 miskilanci irin na Dr
Suna cikin mota sun dau hanya Saude ta dube shi da alamun damuwa karara a fuskana tace
' 鈥淶uciyata na cikin duhu kuma a cike take da
sarkakarkun al鈥檃mura masu rikitarwa ina cikin rudani 鈥� don Allah ka fidda zuciyata cikin duhun da take ciki ka fada min me yasa kai wa 鈥榶ar uwarka Karya a kaina, k0 shi ma hakan duk yana cikin taimakon nawa鈥榥e?"
Dr. ya yi wani? murmushi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, 鈥楰amar kin sani duk yana ciki, kuma daga yau deel din namu zai Kare da fatan kin gane?鈥� Ba鈥榯a ce
masa komai ba ta yi shiru zuciyarta na kaiwa da , kawowa
Katon gate ne ta ga sun tinkara katafaren gaske 鈥� mai kama da鈥� qofar shiga gari.. Saude ta saki hanci da ido tana kallon gate din yayin da shi kuma yake faman horn, masu gadi biyu ne suka bude kofar Sannan suka 鈥榮higa katafarea gidan ya sauke gilas din motar: yana ; gaisawa da masu gadin sannan ya wuce.
Kai tsaye Katuwar rumfar da aka tanada dan ajiye , motoci ya nufa ya faka motar tsakanin motecin da su kai jerin gwano a cikin rumfar Dr. ya bude motar yana . kallon Saude ya ce,鈥� 鈥榊au ga ki har gidansu YallaBan
ki, da fatan kin yi farin ciki.鈥� . Kallon shi kawai ta yi ta juya ta bude murfin motar ' ta fito, shi ma ya fito yana fadar 鈥淎鈥檃 ba ki yi farin cikin ba kenan? Lallai yarinya aiko zaki fadawa Momy Ya yi gaba ta bi bayansa
Ma鈥檃ikatan gidan da ke ta faman aikace-aikacens
u, , 鈥� mai ban ruwa nayi mai aske fulawoyi suna ganinsu .suka nufo su suka zube suna kwasar gaisuwa, ita dai ' Saude ta gaza amsawa duk kunya ma ta ishe ta, yanda suke ta faman kiranta da Hajiya, a zuciyarta ta ce Allah Sarki ai duk mu ne dan ta san da sun san wacc 鈥檆e ita da ba su gaishe ta ba. ' Suna wucewa Dr. ya dube ta ba walwala'a fuskarsa ya ce, 鈥楧uk wanda ya gaida ke ki rinKa amsawa, don za su dauka wulaqanci gare ki. 鈥�
Ba ta ce masa komai ba ta ga sun nufl wata Katuwar kofa ya tura suka shiga cikin katafaren falon. Ne
Babu kowa a cikin falon sai 鈥榶an aiki guda biyo suna ta faman goge-goge suna shigowa suka zube suna kwasar gaisuwa, Dr. ya nunawa Saude wurin zama * sannan ya nufl wata kofa, 鈥榶an aikin kuma suka fice suka bar Saude na ta faman zazzare namujiya a cikin
falon. . Tsawon mintinan da suka kai goma
, sannan ya tito hannun shi sarke dana wata magidanciyar mace dan ba za a kira ta da tsohuwa ba, saboda a qalla shekarunta ba zasu wuce arba鈥檌n da _ 鈥榶an kai ba. Tun kafin su qaraso Saude ta yi saurin鈥�
saukowa Kasa daga saman kujerar da take sama, matar
ta wage baki har hakoranta suka bayyana wanda aka likawa hakorin Makka, ta ture Dr. wanda ke rabe da . kafadarta ta riqo Saude tana fadar. 鈥�
鈥� 鈥楰ai ni sakar ni ka ji tunda baka gaji'ya sannun ki da zuwa Saudatu zauna nan kinji
Ta zauna tare da ita saman kujera, tana amsa gaisuwar da Saude ke mata cikin sarkewar murya
Momy ta dubi Dr. tana fadar, 鈥楰ai sai ka cemin amaryar taka Bafullatana ce gaskiya nayi murna saki jikin ki Saudat mu gaisa ki dauke ni tamkar
mahaifiyarki kinji ko?鈥� Kai kawai ta daga mata
Momy ta yi murmushi cike da jin dadi tana fadar,
' 鈥楢llah Sarki je ka kira Dad dinka na san yana Bangarensa yana jiran ka Dr ya mike da zumudinsa ya fice.
Yau dai Saude ta ga ikon Allah ta ga inda soyayyar da da mahaifa take yanda suka rinka nan nan da ita tamkar zasu goya ta don Dad din na zuwa Dr cewa ya yi sai an yi siyan baki
* Kamar wasa dattijon yace 鈥楢u! Kace gaisuwa da neman iri ku ka zo.鈥�
Dr, ya ce, 鈥淓h Dad ba komai
鈥渄ad yace To amaryar taka za ta je Saudiyya?"
Dr yace eh
鈥淶a ta Dady 鈥� ~ yace
鈥楾o an biya, mata.鈥� *
Dr ya ce, 鈥楢i bai isaba Dad wallahi inafa son ta da yawa
" Dad ya ce, 鈥楾o ka hau sama ka dauko mata makullin
Motar da nayi niyyar yi mata takwuici.鈥� ; musamman sbd ita nasa aka kawo motar daga london jiyannan kuma aka iso da ita maza jeka dauko mata makullin a sama
Lol jama,a asha karatu lfy
[1/28, 12:05 PM] I love my mum: 馃摎馃摎DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100馃摎馃摎
[12:17PM, 02/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: [1/28, 12:10 PM] I love my mum: *YAR TALL*
*CHAPTER 21*
Dr yayi wani tsallen murna yana fadin kai thank u very much dad ya sumbaceshi kamar wani yaro momy tace 鈥渢unda dad dinka kadai ya siyi bakin don sai ta zage ta yi magana har sai mun ce ya isa haka.
Dr. ya ce, 鈥榃lh A a Saura ke Momy.鈥�
Dariya suka sa masa Momy ta ce 鈥楢i kyauta ta tsakanina da ita ne babu mai ji bare ya gani.鈥�
~ Dad ya ce, 鈥楢i kuma bamu yarda da wannan wayon ba mu gani a qasa.鈥�
Momy ta ce, 鈥楢i tsakanin 鈥榶a da uwa babu mai shiga don ni yanzu na bar maka wannan da baya girma yau na dawo nan. "
Dad ya ce 鈥楤a komai ai dama tare muke koya kaya kace my son?鈥� Dr. ya ce 鈥楢i k0 dai Dad fada mata mu dai mu
gani a qasa ; Hajiya ta ce, 鈥楬ummm! Kan ku ake ji "Ta janyo
hannun Saude tana saka mata wani zobe tare da abun hannunsa, sannan ta bude sarkar ta sanya mata da kanta ta cire mayafinta tasa mata yan kunnanyen
Masu shegen kyau. * Dr ya kaure da tafi鈥� yana fadar 鈥楰ai Mamy
gaskiya baki ya siyu." Dad ya ce, 鈥楽ai ku taso muje mu yi lunch
Gaba daya ba musu duka suka mike hannun momy sarqe dana Saudat, Dad kuwa yana dafe da kafadar Dr suka nuf1 dinning area
A tare suka ci suka sha ana ta barkwanci basu suka bar gidan ba sai bayan sallar Magariba. Zuwa Saudat. gidansu Dr. Ahmad yau ya Kara mata darasi a rayuwa iyayensa sun nuna mata qauna tamkar zasu goya ta abin daya karayar mata da zuciya wanda ya sa ta kuka mai cin zuciya
鈥� Dr Ahmad da ke tuqi ya dago ya kalle ta kadan sai a lokacin ya lura da kukan da take ya maida kan shi saman. titi muryarshi a sanyaye ya ce, 鈥淜ukan me ki ke kuma?鈥�
Tamkar bazata tankamasaba, saidatayi dakyar ta iya tsayar da kukan nata kafin ta ce, 鈥楧ole ne inyi kuka Yallabai ta yanda kai , wa iyayenka qarya don kawai ka cimma wata manufa ta 鈥� ka, ni dama na sani tun fakro ka tsane ni kana san ka 鈥榢ore ni amma ka rasa hanyar da zaka bi kar Hajiya ta bata ranta, amma ni da ka bi ta ni ba sai kabi ta wannan hanyar ba ta nuna kana sona ba, don hanya ce ta tarwatsa rayuwata wallahi, idan daga nan ka sauke ni ba za ka qara ganina a gidanka ba har abadan 鈥� abada" 鈥�
Ta qarasa maganar tare da qara rushewa da wani sabon kukan 鈥�
Dr ya taka birki tare da sauka daga saman Iitin ya . koma gefe ya_faka motar ya kunna fitilar dake cikin
Motar ya jirkito yana kallonta gaba daya ya tattara duk _ wata nutsuwarsa a kanta, cikin sanyin muryarsa ya kira Sunanta.
鈥淪aude kenan wallahi tallahi tunda nake ban taba tunanin tarwatsa rayuwarki ba kullum fatana shine in ga rayuwarki ta inganta dubi idanuwana Saudat kalleni don Allah.鈥� Ya fada. tare da riKo hannunta wanda ya tilasta mata kallon nasa.
Tayi saurin sauke idanuwanta saboda wani irin kwarjinin dayi mata ga alamun damuwa nan bayyane kwayar idanunsa Dr yaci gaba da fadin
鈥淜i kalle ni sosai Saudat idan har kin san abin da ake nufi da. so to zuciyata na dauke da dumbin soyayyarki da qaunarki', kuma duk abin da ki ka ji ina fada da gaske nake a shirye nake da auren ki a kowane
Yanayi.鈥� Saude ta yi saurin dagowa a razane tana kallon shi,
tsabar rudu da kadauwar da ta yi ya yi bala鈥檌n firgitar da ita, a nutse yake kallonta ba tare da ya sake magana ba cak kukan Saude ya tsaya ta soma magana tana kallon tsabar idanuwansa, cike da kaduwa ga muryar har ta soma: disashewa saboda kukan da ta yi cikin sarqakKiyar murya ta soma fadar.
鈥淒an Allah don Annabi ka rufa mini asiri kar ka Sake furta wannan kalmar wadda za ta. zamo makamin rugujewar rayuwata wallahi ka fi qarfina ta kowace
fuska, kai ba sa an aurena bane karkama klsake fada" don Allah don Annabi."
Dr. ya lumshe idanuwansa ya harde a tsanakke ya soma magana 鈥楤a kya sona kenan Saude Juyo ki kalle ni ki fada mini ba kya sona, fadi kawai
Saude ta ji tamkar yana buga lugudan tashin hankali a zuciyarta ta runtse idanuwanta tana jin tamkar zuciyarta za ta yi bindiga.
Dr. ya sassauta murya tamkar mai shirin鈥榝ashewa da kuka ya ce 鈥楽audat wallahi ina son ki, so kuma irin na gaskiya wanda babu wasa a cikinsa, kuma wallahi a shirye nake da na fuskanci kowace 'irin jarabawa ce a kanki, ki amince min don Allah inamai tabbar miki ba za ki yi nadamar damqa mini zuciyarki ba. 鈥�
Shi yasa na fara kai ki wurin鈥� iyayena kafin in furta abin da ke zuciyata,鈥� duk da ba su san wace ce ke ba, amma abun zai zo da sauki don gari na wayewa gobe zan mai da ke Katsina idan kuma kin amince na nemi auren ki 鈥�
Cikin kuka Saude ta ce 鈥楾a yaya zan mince in je fa rayuwata cikin matsala? Wace ce ni da zan iya kishi da matarka? 鈥榊ar wace ce ni a qasar nan da zan so miji kamar ka? Yallabai kafi karfina kai ba sa an aurena ba ne wallahi.鈥�
Dr ya ce鈥楴i ba wannan na tambayeki ba Saudat ' shi aure sa a da sa a ne? Wa ya fada miki? Ai shi aure cancanta ce kawai, Kuma da ki ke maganar kishi da Asma, wace ce ita, ta isa ta hana abin da Allah ya鈥�
Qaddara. Saude nina ganki kuma nace ina so kuma mutum ko aljan bai isa ya. hana ni sonki ba har sai idan kece kika
ce ba kya sona, kuma insha Allahu na san ba za ki fada
ba, haka ne?鈥�
Ya yi maganar tare da matsar yatsun hannunta wadanda ke cikin hannunsa, Saude ta runtse idonta tana jin wani abu na yi mata kai komo a zuciya. To k0 shi ne son? Ta tambayi kanta.
Dr. ya girgiza ta tare da fadar, 鈥楤ude idon ki Saudat ki kalli masoyin ki ki furta abin da ke 鈥� zuciyarki, shin kina sona za ki aure ni?鈥�
Shiru ya ratsa wurin ta kasa cewa uffan. Dr. cikin sarkewar murya ya ce, 鈥楧on Allah ki yi magana ki ce wani abu, please Saudat. 鈥�
Kunya da nauyinsa suka dabaibaye ta ta samu ta duke da qyar kafin ta iya magana cikin wata likitacciyar murya ta ce, 鈥楾o ka sake ni in fada.鈥�
鈥� Da sauri ya saki hannun nata yana fadar, 鈥楴a saki fadi."
Saudat ta dan yi jim tana tunanin abin da zai iya Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar muryana ta soma magana.
鈥淵allabai ni ba sonka ne ba na yi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen da ta same ka ballantana makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ce cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa ko ya yake.鈥�
Cikin farin ciki Dr. ya ce, 鈥楬aba Saudat ai matukar ina 鈥渃iki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai
dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a 鈥� zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.鈥�
Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, 鈥榯asa tafin hannu ta rufe fuskarta, Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasa mota hanya suka cigaba da tafiya
禄 tare da waninsu ya sake magana ba.
Horn din da ta ji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso Cinna hancin motar cikin gate din gidan ya yi daidai da bugawar zuciyar Sanue dif zuciyar ta ** tsaya da aiki a take.
Ina ga k0 Asma ce za ta fito, Saude ta ji muryar Dr na fada wanda ba ta ma fahimtar me yake fada ba saboda tsabar rudu da kaduwa da take ciki.
Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr ya ji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso.
. Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare da ya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar
鈥淪aukar yaushe My dear.鈥�
,, Turus ya ja ya tsaya saboda k0 kallon shi ba ta yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr ya yi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura ta yi matukar 鈥� 'firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa a 鈥� sanyaye yabi bayan ta
Tana qarasawa gaban motar ta ja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, 鈥楤ani key da motar." Ta fada cike da gadara.
Dr. ya ja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko鈥檌n kula ya ce, 鈥楤a zan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?鈥�
Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki ta ce, 鈥榖a zaka bayar ba ni ka ke fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zan yi mamaki ba tunda ka dauki 鈥榶ar iska kun flta kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole za ka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. .
Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da kowace. karuwa don sai na sa ka yi nadamar da baza ta taBa qarewa ba wallahi, dan ba irin Asma ake wa irin wannan tozarcin da wulakantar ' ba a cikin gidanta, mayaudari, munafuki kawai.鈥� Tana maganar tana kwance dankwalin kanta.
Ta hau daura damara a qugunta tamkar mai shirin shiga filin dambe ta durkusa ta kwashi duwarwatsun da aka baza a harabar gidan ta hau jefa su a gilas din motar tana fadar.
鈥淲allahi yau sai dai k0 ni ko ke a gidan nan 鈥榶ar iska wallahi sai na yi ajalin ki, karuwar banza."
Dr. da ke tsaye ya yi saurin rike ta yana fadar, 鈥榃ai me ye haka Asma kina da hankali kuwa ki ke abu kamar ba. educated ba, wannan ai hauka ne ki ke da
RaShin hankali a gaban mutanen da suke a qarkashin ki wannan ai kanki kike jawa abin fadi a duniya.鈥�
Asma ta kwace daga riwon da ya yi mata tana haki ta ce 鈥楰ai da alla ni rufe min ba ki kai har wani mutunci ne ka 'sani bacin wanda ka zubarwa kanka a bainar jama鈥檃, ai idan akwai wani sakarai marar hankali to bayan ka yake, mutumin da ya maida 鈥榶an aikin gidansa abokan cin garinsa, ai sai yanzu na fahimci abin da ke korar duk 鈥榶an aikin da na kawo maka, kuma wallahi ba zan taBa rufa maka asiri bu sai duniya ta san abin da ka aikata, kuma yarinyar nan yau sai na halaka ta.
Bai ankara ba ta rarumi wata qatuwar adda wadda ake aske fulawowi da ita, ta sauke madubin motar, wanda ya yi daidai ta fasa qara Saude wadda ke zaune a gaban motar.
Dr. ya yi saurin rike Asma yana fadar, 鈥榃ai ke wace inn mahaukaciya ce wallahi za ki jawa kan ki aikin dana sani, dan na rantse da Allah idan ki ka kashe yarinyar mutane wallahi sai na yi shari鈥檃 da ke
Da sauri ta kalle shi bakinta a sake cikin sarkewar murya take fadar, 鈥榋a kai shari鈥檃 da ni Ahmad akan karuwar? Lallai kam da na nuna maka kai Karamin dan bariki ne. To bari in kashe ta sai kai qarar tawa."
Dr. ya qara rike ta gam kafin ya ce 鈥淎sma ya kamata ki shiga hankalin kifa dan kin sani sarai ba zan lamunci wannan haukan naki ba, don ban ga abin da a kai ba, wanda zai sanya ki wannan jakancin ba idan mun fita da Saudat sai me 鈥榶ar aikina ce ina da
Right din fita da ita mu yi siyayyar abin da ake buqata. dan me za ki nemi tarwatsa mini tunani haka kawai?"
Asma ta girgiza kai, 鈥楲allai Ahmad ka cika dan akuya yanzu a kan karuwar ne ka ke kirana da jaka, lallai kam ana yi, kun tafi siyayya ne shi yasa ku ka . tafi ku biyu babu k0 da direba, kuma ta zauna a gaban
掳 mota. Kai gaskiya ne ai na ga hakan, amma sai dai abin daka manta k0 ranar da ka fara ganina a duniya da hakorana talatin ka gan ni cur, ballantana ka maida ni
. Karamar yarinya, wadda ba ta san abin da take ba.
Kuma wallahi tallahi na rantse maka da Allah sai na yi ajalin 鈥榶ar iskar yarinyar nan jaka sakarya
daqikiya ballagaza wadda iyayenta suka sadaukar da ita saboda abun duniya, wallahi daga yau ta gama karuwanci da kowa.鈥�
Dr. ya cc, 鈥楬mmm! Asma kenan kina ba ni mamaki yanzu har iyayenta sun miki laifi dan sun Sadaukar da 鈥榶arsu ta zo ta yi miki abin da ki ka gaza Min a rayuwar auren ki ashe har sun miki laifi?"
ldanuwanta a warwaje ta soma fadin, 鈥楤an gane ba? Dama na dauke ta aiki ne don ta maye gurbina?鈥�
Cikin rashin damuwa ya ce 鈥淵es k0 kin dauka 鈥榓binci shi ne kawai matsalata ni ba mutum bane? Dole
kwai wani abun da nake buqata bayan wannan, dole 鈥�
lna buqatar kulawa ta mace, sai dai bata gurbatacciyar hanya wadda take haramun ba, don sanin kanki ne ni Ba mazinaci ba ne shi ya鈥榮a na yanke hukuncin auran Saudat don na ji dadin maye gaba dayan gurbin '
naki wanda sabgogin yau da kallum suka saki ka "watsar.鈥�
Cikin tsananin firgita da razana Asma ta kwace daga rikon da ya yi mata tana fadar, 鈥楰utumar ubannan Kai karya ka ke wallahi tallahi karya ka ke Ahmad ba ka isa ba na rantse maka da Allah babu 鈥榶ar matsiyatan da ta isa ta shigo cikin gidan nan batare da na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne.鈥�
Dr. Ahmad ya ce Ai ko sai dai kada a Kara; domin zuciyar Ahmad ta riga ta yi nisan da mai rai ba zai gane iya adadin gudunta ba, kuma ina mai tabbatar miki k0 da malaman da ke Barno da Nijar. malamanki ne ba ki isa ki hana wannan lamarin ba. Da fatan kin gane Asma ta hau ja da baya da baya tana fadar 鈥楴i. .ni Ahmad wallahi qaryarka ta sha karya wallahi ba ka isa , ba Ta durkusa tana kokarin daukar addar daya yar a 鈥� 鈥榪asa, wadda ya kwace daga hannunta.
鈥� Dr ya kalle ta yana fadar, 鈥榃allahi idan ki ka matsa kusa da motar can a bakin auren ki 鈥�
Yaja wani dogon tsaki ya juya ya yi gaba ya bar ta ' ta fasa wani gunjin kuka ta durkushe a gun Dr ya fada motarsa sai dai ganin halin da Saude ,ke ciki ya daga masa hankali kuma ya ga madifar" dauriyarta don gilas din motar da ya fashe sai da ya yanki goshinta, jini ya zuba sosai duk ya bata mata fuska, hankalin sa ya tashi ya tayar da鈥� motar ya fice
daga gidan ba tare daya sake kallon inda asma take
ba, ya nufi asibiti da ita. Suna zuwa kuwa aka karbe ta akai mata dresin
din ciwon aka rubuta mata magunguna, sannan suka baro asibitin. A cikinsu babu mai magana kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Can Dr. ya dan waigo
ya kalli Saudat sannan ya maida kallonsa a kan titi cikin sanyayyar muryarsa ya ce.
鈥淒on Allah don Annabi ki yi haquri Saudat kada dan wannan abun ya daga miki hankali k0 kadan, ni daina ce ina son ki kuma ni zan zauna da ke ba Asma ba. To insha Allahu na yi miki alqawarin farin ciki da jin dadin rayuwa a duk inda suke zan nemo miki su, fatana ki鈥� rayu cikin farin ciki da walwala, kar ma abin datayi dinnnan yadameki kinji?"
鈥� Kai kawai ta daga masa alamar eh, amma qasan zuciyarta cike yake da tsabar rudani da tsoro. Dr. ya ~ tsaya 鈥楪idan Abinci鈥� ya yi take away sannan ya dawo suka wuce. Kai tsaye daki ya kama a wani hadaddan hotel mai tsadar gaske kwana daya, ya ba ta makullin dakin mai lamba 12, sannan ya ajiye mata ledar take away din ya gwargwada mata komai a cikin dakin Wanda yake da qaton falo da bedroom sai bandaki da dan wurin hutawa.
Sannan ya dube ta a nutse, 鈥淒afatan dai babu wata matsala?鈥�
Saude da kc tsaye tana kallon shi ta sunkuyar dakai qasa muryarta a sanyaye ta ce, 鈥淏abu.鈥�
Dr. ya ce 鈥極key zan wuce mu jeki rufe dakin ki tabbatar kin kulle sosai sai Zuwa da safe,,insha Allahu zan dawo sai mu wuce Katsinan a tare kin ji ko?鈥� "
, Saude ta dago da idanuwanta wadanda suka ciko da kwalla ta daga masa kai, Dr. ya dan tsura mata idanuwa jikinsa a sanyaye ya ce 鈥楽audat hawaye nake gani a idanuaki me ye kuma?鈥�
Saude ta sadda idanuwanta tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce uffan ba Dr Ahmad ya Kara matsowa daf da ita cikin sanyayyar muryar shi ya kira sunanta
鈥淪audat me yasa ki ke san tayar min da hankali ne?
'Me yasa ba kya son ganin nutsuwa ta? Kinfi son ki
ganni a firgice ne, iye Saudat?鈥� Kai kawai ta girgiza masa ba tare da ta kalle shi ba Ya ce, 鈥楾o meye? Ba kya san in tafl ne in zauna tare
. da ke. " Da sauri ta daga masa kai don kuwa abin dake
zuciyarta kenan, don gani take tamkar idan ya tafi ba zata sake ganinsa ba.
Ya yi murmushi wanda ya bayyanar da haqoransa kana ya ce 鈥淜i sha kurumin ki My dear insha Allahu babu abindazai faru kedai kiyanida addua kawai kinji?鈥� . 鈥�
A hankali ta daga masa kai ya ce 鈥榊auwa ko ke fa, 鈥� kikwanta ki hutakinji, kiyibarci mai dadi saida safe. 鈥漎a ja mata hanci yana dariya sannan ya fice.
Saude t maida qofar ta rufe ta koma ta jingina da ; kyauren idanuwanta a lumshe zuciyarta na bijiro mata 鈥� d wata irin matsananciyar soyayyar Dr. Ahmad wanda take jin a yanzu tamkar ta bishi ta zauna a tare da shi, farin cikinta da fargabarta ba zasu musaltu ba. Farin cikinta dai shi ne ta samu namiji daya tamkar da goma ajin duk wata isasshiyar mace. Fargabarta kuwa itace. Shin kuwa zai iya auren ta don ita ta san ya riga yafi qarfinta ta kowace fuska, to idan ma ya ' aureta ta ya za ta yi da matarsa Asma, don yau ta ga. bala,in da: take fada mata.
A hankali ta ja Kafafuwanta ta nufi bedroom din; kai tsaye bandaki ta nufa ta dauro alwala ta fito ta yi sallar isha,i sannan ta tashi ta haye saman鈥� madaidaicin gadon da ya sha shimflda ta alfarma ta zauna ta jawo take away din da ya ajiye mata ta bude ta ci abin da za ta iya ci saunan ta kwanta, ba dan tana jin barci ba sai dan ta samarwa gangar jikinta hutu
Tunda {a kwanta ba ita ta farka ba sai Karfe shida saura 鈥榶an mintina, ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin data dauka tana barcin, don haka ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta zauna tana lazimi tsawon lokaci sai da ta gaji don kan ta ta mike ta koma ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin gida da irin abin da za ta iya fuskanta a can din. Rayuwarta ta baya a gidan ta dawo mata tare da tunanin masoyinta Hamid, har yau har gobe tana jin son shi a zuciyarta,鈥渟aboda shi ne mutum na farko da ta
Tara so a rayuwarta kuma shi ne mutum na farko da ya fara burin taimaka mata
Kwankwasa kofar da ake ne ya sa ta saurin tashi ta taje ta bude qofar, Dr. ya shigo yana sany茅 da shigar wani sabon yadi milk colour, mai laushin gaske an yi masa aikin hannu a jikin rigar Yana .sanye da hula sai takalminsa na fata
'idonsa na sanye da siririn farin gilas, gaba daya kamshin turarensa ya mamaye falon.
Saude ta durkusa tana gaishe shi cike" da girmamawa, Dr. ya amsa yana fadar, 鈥楧aga yin knock sai ki bade kofa ba tare da kin tambayi k0 waye ba baki san nan batel bane? Komai na iya faruwa fa.鈥�
Muryarta a sanyay茅 ta ce, 鈥楢i na san kai ne
Dr. ya ce ya a kai ki ka sani? Ta dan yi jim kafin tace ai ka ce min zaka zo da safe. Ya dan yi wani murmushi kafin ya ce ashe ba ki da mantuwa kinsan in bayan dana manta ban nuna miki yanda za ki yi
kisa a kawo miki break ba da ba zan zo nan ba sai wurin sha biyu da wani abu
Ya ja ya zauna tare da tura mata katuwar jakar da ke hannunsa ya ce duba ki ga kayan nan idan sun miki saikisa yanzu sai mu tafi.鈥� Saude ta zauna saman * kafet tare da janyo ledar gabanta ta shiga bubbudewa a ~ sanyaye 鈥�
Dogon wando ne baki irin mai kama qafafuwan nan an masa adon pink color sai rigarsa
禄 Shima ma pink mai adon baki, rigar mai yankakke wanda ake kira da v neck
Rigar mai dongon harnu ce,,,sai wata duguwar riga har qasa itama pink cclour ita ma mai dogon hannu, tana da yankakken gaba sai siririn mayafinta.
~ Ta ajiye kayan ta janyo wani qaton kwali ta bude鈥� takalmi ne a ciki baki da 鈥榶ar qaramar pose irin wadda ake makalawa a hannu, 鈥榶ar qarama, sannan ta Ciro wata 鈥榶ar jaka, saitin kayan shafawa ne a ciki hade da sabulu da turare kayan sun bala鈥檌n
Burge ta har cikin ranta, shi kan shi ya fahimci hakan 鈥�
a idanuwanta, don haka muryar shi a sanyaye ya ce. 鈥淪un yi kyau k0?鈥� Murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ha, ya
*mike tareda fadar kije ki shirya dame zakikarya ?
Me za,a kawo miki?鈥�
Saude ta sunkuyar da kanta tare da fadar, 鈥楰omai aka kawo min."
Cikin zolaya ya ce, 鈥楤a dai komai ba k0 zaki ci shinkafa da miyar kwadi?鈥�
Da sauri ta kalle shi ido waje, ya yi wani siririn murmushi kafin ya ce 鈥榊e鈥檚 nan ba abin da ba sa dafawa har miyar dodon kodi.鈥� Saude ta Bata fuska
tamkar zatayi amai tace 鈥楴idai a,a 鈥� Ya yi wata dariya irin wadda ba ta taba sanin ya iya ta ba da alama yanda ta yi maganar cikin shagwaba ya. yi masifar barge sa tare da daukar _ hankalinsa, ya matso daf da ita yana kallonta da
ya ce, 鈥楧an qara鈥� maimaitawa mu ji please. 鈥�
Kunya ta kama ta ta juya da sauri ta yi ciki ta bar shi nan tsaye harde da hannu a qirji yana kallonta
har ta bacewa ganinsa, ya yi wani murmushi tare da
鈥榣umshc idanuwansa 鈥�
Saude na shiga bedroom din ta fada saman gadon dakin ta rungume filo cike da murna haka kawai ta ji wani irin farin, ciki ya baibaye ta, ta lumshe idanuwanta tana mai son tuno wani abu can
鈥� kamar wadda aka tsikara ta zabura ta mike da gudugudunta ta fada bandaki ta watso ruwa a gurguje ta
鈥榙auro alwala ta fito ta yi nafila raka鈥檃 biyu tare da roKon Ubangiji ya kare ta daga sharrin Inna Laure, don tanaji ajikinta wannan karon idan akahanata auren Dr. mutuwa kaWai za ta yi.
Tana gama addu鈥� o 鈥檌nta ta mike ta janyo 鈥榶ar jakar kayan shafawar ta fito da su ta mutsa mai lotion a jikinta, sannan ta shafa hoda ta sa abun
鈥� gyaran gira ta gyara girarta, har ta soma sai da ta sa
. maskara ta gyara ta, sannan tasa brown eye a girarta ta bi bakinta da sassaiikan jan baki pink colour; sai ka rantse da Allah kalar lebanta ne haka.
Saude ta mike ta janyo kayan ta saka dogon 搂
' wandon: wanda ya kama ta tsam-tsam sannan ta
鈥濃€� kawo rigar ta sanya, wadda ta bi illahirin jikinta ta ta
lafe, Saunan ta kawo dogUwar rigar ta dora ta
* Warwar茅 gashin kanta ta Kara daure shi sosai, ta yi masa tamkar gamma a baya, ya zama tuntu sannan ta 禄 鈥� kawo gyalen rigar ta yi kamar rawani da shi.
Ta Ciro takalmin mai tsini ta saka, ta dauko pose din ta saka sarkar da mahaifiyar Dr. ta ba ta a ciki saboda rigar ba a hada ta da sarka sai dai ta bar dan
kunnen a kunnenta tare da abin hannu da zobe
Ta dauki turaren ta faffesa ko鈥檌na na jikinta,
saunan ta tsaya gaban madubi tana qararewa kanta kalla, Barakallahu! Masha Allahu ni dai abin da zan 鈥� iya cewa kenan don a gaskiya na san Saude ta hadu qarshe, ita kanta ba ta san tana da wannan kyan haka ba Masha Allah.
Ta fito daga dakin cikin nutsuwarta, Dr Ahmad dake zaune saman kujera yasa kayan abincin a gabansa bai san lokacin da. ya mike ba yana kallonta, hatta qaraso gabansa ta durkusa a gabansa.
鈥淪annu da hutawa YallaBai."
Dr鈥� Ahmad ya koma ya zauna jiki a sanyaye sannan ya amsa da yauwa sannu Saudat, kin sha kyau wallahi irin wannan haduwa haka.
Murmushi kawai ta yi, Dr ya dake dan karya bada: kansa yace Bismillah maza ki karya mu tafi tana murmushi ta janyo tiren kayan abincin ta bude tea flask, ne sai kayan hadinsa, . *. sannan soyayyan kwai da agada, sai wani kwanon
tangarab shi; kuma farfesun zallar tsokar kaza ne
' Saude ta dauki kofi 鈥檊uda biyu ta hada masu
ruwan tea din sannan, ta miqa masa DR : ya tsaya yana kallonta kafin ya ce 鈥榃aya fada miki ban 'karya ba?", 鈥� Murmushi kawai ta yi tare da qara mika masa kofi din, yasa hannu ya karBa ya hada da kofin da hannunta ya riKe yana Kokarin ya hada ido da ita, yana muryarshi a sanyaye ya ce Thank you. 鈥�
Saude ta zame hannunta ji take tamkar ta zabga da gudu, ta. yi ta maza ta dake ta dauki kofin din tea din ta soma tsotsa tamkar wadda babu makoshi a bakinta.
Duk abin da take Dr yana kallonta bai ce mata
Kala ba, ta yi ta tsatsar abincin, sai da ta gama sannan ya mike ya dauki makullin motarsa ya dube
ta鈥楳uje ko?鈥�
Da to kawai ta amsa ya yi gaba sannan ta bi shi a baya, ya tsaya ya yi 鈥榶an abin da zai yi cikin hotel din sannan ya fito suka shiga mota suka dauki hanya kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa. Dr. ya miqe. hannu ya kunna masu karatun Alkur鈥榓ni mai ginna.
Don haka Saude ta koma jikin makarin kujerar ta" 鈥� kwanta ta. lumshe idanuwanta tana sauraron karatun,鈥� zuciyarta kuwa ta harba zuwa gida, fargaba mai~
tsanani ta shige ta tana tsoron makircin Inna Laure 鈥� tana tsoron abin da zai iya zuwa. ya dawo.
= hanya. Babu mai magana a cikinsu kowa da abin da鈥�
A haka barci barawo ya sace ta, ba ita ta farka ba sai da ta ji yana tayar da ita an kusa zuwa Welcom to Katsma, saude ta yi firgigit ta bude idanuwanta wanda hakan ya yi daidai da bugawar zuciyarta.
Innalillalhi鈥� ta yi saurin fada da qarfinta.
Dr ya yi saurin kallonta da hanzarinsa yana , fad'ar lafiya? Ta鈥� dan ja numfashi kafin ta ce, 鈥榃allahi ji na yi gabana ya yanke ya fadi, Dr. ya' juyo ya dan kalle ta kafin ya maida kallonsa kan titi ya ce, 鈥楰i rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihirrajiun
. insha Allahu ko ma me ye zai zo miki da
sauki.鈥�
Saude ta amsa da to, sannan ta nuna masa kwanar unguwarsu kafin a qarasa welcome to Katsina, haka ta rinka nuna masa hanya har suka iso kofa: gidan nasu, gaban Saude ya Kara wata muguwar bugawa .. ganin manyan rumfuna a kakkafe a kofar gidan da ' 鈥榶an tsirarun mutane a ciki.
Saude ta dafe kirji, 鈥榃ayyo Allah na k0 dai Baba ne ya rasu?鈥�
Dr ya yi saurin kallon Kofar gidan kafin ya ce
"A a ba mutuwa ba ce, dan ga hunhun goro can a gefe鈥� 芦 Saude ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce, 鈥業na Jin ko鈥� yar Baba aka daurawa aure yau.鈥� *
" Dr; ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali kafin ya ce, 鈥榃atakila, ki shiga ki gani sai鈥榢i min sallama da Baban.
Saude ta amsa da to tare da bude murfin motar ta fice.
Tun kafin ta fito dama hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kan hadaddiyar motar ta Dr wadda ta dauke illahirin hankaiinsu, duk da ba za ka ; iya ganin wanda ke ciki ba saboda bakin gilas din da 鈥榢e gare ta
Saude na fitowa daga motar kallo ya koma kanta, sai ka ce ba mutum 鈥榶ar uwarsu ba, mutanen dake zazzaune a rumfar ba za su wuce goma ba tun daga nesa ta dan gane mutum uku mahaifinta neda 鈥� kuma qannansa guda biyu, sauran kuwa ba ta san k0 su waye ba * .
Saude ta qaraso ta durqusa har kasa ta gaishe ' su, tamkar za su kwanta mata suke amsawa, saboda 鈥� tsabar girmamawa; amma ban da mahaifinta wanda ya Kara kafe ta da idanuwansa muryarsa a sanyaye yace, 鈥淲ace ce wannan kamar Saude?鈥�
Saude ta ce, 鈥楴i ce Baba.鈥�
innalillahi 鈥橸anzu Saude ke ce ki ka koma haka? Ina Dillaliyar da suka tafl _ ; dauko ki dazu?鈥� . Gaban Saude ya fadi cikin sanyin jikinta ta ce, = 鈥淎i kobasu kai ga zuwa ba, Allah yasa dai lafiya?鈥�
Malam Bala ya ce, 鈥榊anzu dai tashi ki shiga Ciki u 鈥� Kawu Isiya ya ce 鈥榃ai wace Saudan ce ka ke fada ban fa game ba?鈥�
Malam Bala ya ce, 鈥楽aude dai wadda aka tura a dauko a can Habuja amarya ita.鈥� 鈥�
Kawu Hamisu ya ce, 鈥楾o wancan mai motar fa da ya kawo ta?鈥�
Ba ta saurari abin da ya ce masu ba ta yi cikin gidan abin ta da sallamarta, mutane ne ke ta kujibakujibarsu an cika tsakar gidan nasu鈥榤akil da mata, an girke manyan tukwane da murahu Sai faman tuKin ' tuwo da sanwar miy茅 ake, kana gani k0 ba a fada maka ba ka san hidima ake.
Sude ta gaishe su sannan ta wuce dakin Inna Laure wanda shi ma yake cik茅 da jama鈥檃, duk gungun matan ~ da Saude ta gani kafin ta gaishe su su sun gaishe ta, ana fadar sannu da zuwa Hajiya, ba ta damu ba don a鈥� lokacin burinta kawai ta ji hidimar me aka a gidan nasu. ' '
Ta "samu ta kutsa dakin Laure ta gaishe da jama鈥檃r sannah ta wuce har bakin鈥� gadonta inda take zaune ita ~ da 鈥榊ar Baba an 鈥榮ha ankon shadda an kashe dauri sai faman zufa ake. 鈥�
Saude "ta~ qaraso har bakin gadon inda Inna Laure inna laure ce ta fara fadar 鈥楽annu da zuwa Hajiya kar dai ince. harda ke aka taho kun ji Saqon bazata haka, sai aka ce muku an daurawa yarinya aure yau din nan.鈥� .
,Saude ta . durkushe a bakin gadon muryarta a sanyaye ta soma fadar, 鈥楤ikin wa ake Inna Laure?" 鈥� . Gaban Laure ya yi wata masifaffiyar faduwa 鈥檞anda ya ja mata wata muguwar zabura daga ita har 鈥� 鈥榊ar Baban. Inna Laure ta mike tsaye tana gyara daurin zani tana fadar.
鈥淢e nake gani haka me zan gani Saude ke ce ki ka koma tsohuwar karuwa haka? Innalillahi wa鈥檌nna 鈥� ilaihir raji鈥檔n! Jama鈥檃 ku taya ni figa yan uwar kishiya ta zama zakara. Saude mu za ki zubarwa da mutunci a gari mu za ki jawa abun kunya abun fada, wayyo ni . ' Allah naga ta kaina 鈥� .Sai ta fashe da kuka ta fadi qasa. Sumammiya jama,a sukayo kanta suna fadin a taimko da ruwa laure tayi dogon suma
鈥榊ar Baba ta kalli Saude sama da qasa ta
watsar ta ja wani uban tsaki tana fadar, 鈥楢ikin banza ai
. dai dadin abun da ba a san. asalin balbela ba da sai
ta ce daga Masar take, kuma duk rigar qadangare bai
isa ya zama kada ba a Kadangaren nan dai na shi zai
zauna. .
Idan kina jin dadi ne kin tafi birni kin goge to babu
, abin da gogewar ta ki zata 鈥榯a Kare domin yau dinnan
za a wuce gidan Garba Gurgu don tuni an daura auren, 鈥�
ki da shi a safiyar yau kuma wallahi tallahi wani abu
鈥� idan ya samu mahaiflyata sai na dauki fansa a kanki
munafuka kawai.鈥� . 鈥� Tunda 鈥榊ar Baba ta furta daurin auren nata Saude
ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da gurnan,ji
take numfashinta na wani sam -samA kamar zai dauke.
Ta rushe' da wani irin kuka mai daga hakali, ta zabura ta yo waje a guje tamkar marar hankli ta tsallake mutanen da ke waje da gudunta tana jin mahaifinta na kwala mata kira, amma ba ta tsaya ba
Dr Ahmad wanda ya gaji da zaman motar ya fito ya jiggina da motar yana latselatsen wayarsa ya ganta
Ta fallo a; guje hankalinsa ya yi masifar tashi ya nufe ta yana qokarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunji kuka
ya rikice cikin tsananin rudani' ya riko ta yana fadar, 鈥淢e ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne, ki fada min?鈥�
Sande ta. Qara rushewa da wani kukan ba tare da ta saurara ba鈥� ta shiga qakarin fadar, 鈥楴a mutu.. na mutu... na lalace... YallaBai.., an daura min aure yau..鈥�
鈥榠nnalillahi wa 鈥檌nna ilaihirrajiun
Abin da Dr. Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar.
芦 ALHAMDULILLAHI
Wohoho jama nasan da yawanku kunyi missing din laure to mun dawo qauye ya abin zai kasancene da DR AHMAD wai INA YAYAN SAUDE SHINE MASOYIN SAUDE HAMID FUSHI YAYI YA HAQURA DA ITA KO YAYA SHIN WA ME ZAI FARUNE IDAN SU DILLALIYA DA ASMA AKA HADU YA AUREN SAUDE DA GARBA GURGU ZAI KASANCE wadannan amsoshin tambayoyin naku na cikin YAR TALLA BOOK3 WANDA ZAMU FARA GOBE AMMAN IDAN NAGA COMMENT SOSAI
0 comments:
Post a Comment