Murmushi kawai ta yi, Dr. Ahmad ya gyara zama
kafin ya ce
鈥淲allahi Saudat farin cikina a yau ba zai misaltu
ba, duk yadda zan kwatanta miki ba zaki gane ba,
don Allah ina Momy dinmu in sa ta cikin
idanuwana ko na ji sanyi, wallahi ba kiji da na ji
muryartaba sai na ji kamar da Mom dina nake
magana, wallahi na ji ina qaunarta ni ma鈥�.
Saudat ta yi murmushi tana amsa sallamar
Momy wadda suka shigo cikin falon, Alhaji Ashiru
ya amsa.
鈥淎鈥榓 wa nake gani yau a gidan namu, wai.
Ahmad kai ne da kanka?" Dr Ahmad ya zabura ya
miqe tare da washe bakiyana fadar 鈥�
Lah wai Daddy da ma nan ne gidanka na
Katsinan ashe?鈥� Alhaji Ashiru ya ce鈥淎i k0 dai nan
ne ai shi Alhajinka ya sani, don har ya ya taBa
zuwa Dr Ahmad ya ce, 鈥淚kon Allah ashe gidan
Daddyna nazo . ~ Ya durqusa yana gaishe su,
duka dadi ya
cika su don haka cikin fara鈥� a suke amsawa.
Alhaji Ashiru ya juya yana kallon Dr Mariya ya ce
鈥淭o ai ke wannan tuwona maina ke nan, wannan
dan Yaya Alhaji ne babban wanmu wanda , aka yi
wa aure tun last four years, bai taBa zuwa鈥� gidan
nan ba tunda muka yi aure, kullum in nayi
magana sai ya ce kishi yake taya Hajiya, to yau
ga
' shi har cikin falonki tasa ta kawo shi, don haka
kema sai ki Juya kambunki". 鈥� Dr. Ahmad yana
murmushi ya ce.
鈥淟ah wallahi kawu ba haka bane kasan abubuwan
ne sai a hankali, amma dai tuba nake ai yanzu
zan rinqa zuwa鈥� . .
Dr Mariya ta ce 鈥淎i dama :zaka rinka . zuwa
mana tunda yanzu taka ta kawo ka鈥� .
' Duka suka sa dariya ban da Saudat wadda
tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa
ba,
. sai ta koma ita ce sarakuwar. su kuwa hira ce
sosai 鈥渟uka Barke har Shukura ta shigo aka dasa
da ita, sai
lokacin ne Saudat ke dan sa baki kadan~kadan
har
sai da aka kira sallah, sannan suka fice suka tafi
. don sauke farali. Suna dawowa Momy tasa
Mairo
ta kawo abinci aka da dasa wata hirar a nan
suka"
tsaida ranar zuwa qauye sati mai zuwa don
tsaida , maganar auren.
Dr. Ahmad bai bar gidan ba, sai qarfe goma na
dare, Saudat ta yo masa rakiya har bakin gate,
鈥檡a tsaya yana kallonta muryarsa a sanyaye ya
ce
鈥淵au zan yi bacci har da munshari Saudat na
tabbatar a wannan karon zan mallaki abin da
zuciyata keso, lallai na yarda babu abin daya fi
qarfin Ubangiji k0 ba haka ba my dear"; ,
Saudat da ke faman wasa da 鈥榶an yatsun
hannunta ta yi murmushi kawai ba tare da ta
tanka masa ba, Dr. Ahmad ya bi ta da kallo
gabadaya idanuwanta na saman yatsun hannu
nata, ya miqa hannunsa ya riko duka hannayen
ya janyo 鈥� ta gabansa.
Da sauri ta waro idanuwa tana kallonsa, ya sakar
mata murmushi tare da hure mata idanuwa' da
sauri ta idanuwanta tana murmushi qasa-qasa 鈥� 鈥�
ya ce. * . 鈥淜i bari sai kin koma gida kin kwanta
sannan ki bude kin ji? Alkawari?鈥�
鈥�' Ta daga masa kai alamar ta yarda sannan . ya.
sakar mata wani siririn murmushi kafin yace
'Sida safe, ki kular min da
kanki, bacci mai dadi". . Ya shafi kanta daidai
lokacin da ta ke
Qokarin juyawa don haka ta qara sauri yana
kallonta harta bace ya sauke wata nannauyar鈥�
ajikyar zuciya sannan ya juya ya fice. _ .Bacci ya
kaurace wa idanuwan Saudat, ji ta鈥�
ke tamkar' ta taka rawar murna duk ta damu
Shukura da juye~juye, sai faman juya takardar da
鈥榶asa mata ahannunta take koda batasan meye
ya rubuce ba, amma ta san cheque ne na banki,
don
haka yau zuciyarta fes ta kwanta. Tun da gari ya
waye suka hau shirin tafiya
Qauye, Shukura ta shirya cikin wasu riga da siket
na wani swiss鈥� lace mai shegen kyau da tsada,
dinkin ya bi jikinta ya hau kalar fatarta
kasancewar leshin light blue mai adonda "ruwan
qasa-kasa, gashin nan ya sha gyara an daure shi
a gefen kunne sannan ta nada daurin kallabinta
mai suna touch Iight irin na 鈥榶an matan yanzu. .
Gyalenta da takalminta duk farare ne, sai
鈥榙ankunne da sarka na gwal tare da abin
hannunsa ta yi kyau sosai kasancewarta dama .
kyakkyawarce ajin farko 鈥� Saudat kuwa riga da
siket neta saka dark
brown mai adon yardin gwal a jik; irin na Indiya
.ta gyafa gashin kanta ta daure shi a baya ta
saki jelarsa' a gadon bayanta sannan ta nada
gyalen _ kayan saman kanta ta sake shi bai rufe
kwallliyar kayan ba, siririn dankunnenta na gwal
da abin 鈥� hannu wanda mahaiflyar Dr. Tasa ba
tasa abin wuyan ba saboda rigar kayan ta rufe
har wuyanta ta kawo takalminta golden mai
tsinin dunduniya ba qaramin kyau ta yi ba, yar'
indiya sak!
Sannan suka fito falo inda Momy da Alhaji ke
jiransu, Saudat ta bi Momynta da kallo wadda ke
sanye da riga da siket na atamfa sai ta dora '
baqar doguwar riga a sama mai adon jajayen
fulawoyi irin mai tsukakken hannun nan ce
Ta鈥� daura kallabin atamfar a kanta sannan ta
dora kallabin rigar a kan nata, ta saka takalmi da
jaka jajaye, hannunta da kunnenta da wuyanta
ma gwal ne mai tsadar gaske. Haka su Nabil da
Nabila sun hade cikin 鈥榶an kanti kamar ~ 鈥� ba"
yan Nageria ba. 鈥� .
' Dadi ya cilka Saudat, wai nan duk yan uwanta
ne da mahaifiyarta, wayyo rayuwa ke nan, sai da
suka gaisa da Momy da Alhaji sannan ta bawa
Momy cheque din da Dr Ahmad ya bata Momy ta
warware tana dubawa tare da zare ido, ta ce
鈥淜ai wannan kudin Sunyi 鈥測awa is too much, ya
yi yawa abin duba ka gani Alhaji five ,
Hundred thousand fa鈥�.
鈥� Alhaji ya ce 鈥淭a gode kwarai ai kyautar soyayya
ba ta yawa; ki bude mata account kawai ki zuba
mata a ciki
. Hajiya ta amsa da, 鈥淭o鈥�. Sannan suka mike
suka nufi tebur suka karya gabadaya sannan
suka fice su shiga wata Katuwar
motar Alhaji suka tafi humer jeep baka mai kyan
gaske, shi ya ja su da kansa, har zuwa cikin
Dandagoro. Jefi-jefl akan taBa hira inda Saudat
saurarensu kawai take, amma z'uciyarta 鈥� ta
shiga duniyar tumani da sake-sake ganin
al鈥檃muran ta ke tamkar a cikin mafarkinta suke ,
Faruwa jira kawai take ta farka a kowane
lokaci_ba.
. 鈥楢LHAMDU LILLAHI Masha Allah.
Mu hadu a littafl na HUDU kuma na karshe ldan
mai kowa mai komaI ya kai mu
NAKU HAR KULUM A,,I,,S
TABA KA LASHE
kadan daga cikin yar tallah book4
Dukkansu suka fito suka shga gidan saudat na
riqe da hannun nabiLa shikura na gefenta sai
nabil a gefen momy alhaji ashiru ya zauna yana
jiransu a mota sallamar da sukene ta janyo
hankalin inna laure take kuryar daki tana tattara
komatsai tayo tsakar gidan tana fadar marabanku
sannunku dai
Turus taja ta tsaya gamida dafe kirji cikin tashin
hankali da kyarmar murya ta soma magana su
waye ku daga ina?
Momy ta gyara tsayuwa gamida cewa ikon allah
abin da mamaki idanni baki ganeniba ai ina
tunanin wannan yarkice kya ganeta tayi maganar
tana nuna saude inna laure ta fadi qasa jabar
kamar an tile kayan wanki tana kwalama malam
bala kira malam bala ya fito daga kewaye a
gigice hannunsa riqe da buta yana fadin kai laure
wannan irin ihu haka ai saikisa juwa ta kwasheni
in fadi babu gaira babu dalili
Inna laure ta dinga nuna masa momy tana fadin
malam dubamin ka gani wacece nake gani kamar
maria
Cikinfirgici malam bala ya siki butar ta fadi facal
yayo kansu yana fadin wacce mariyar kike nufi
鈥榊AR TALLA- BOOK4
CHAPTER29
ZUciyar Saudat ta shiga duniyar tunani da sake-
sake ganin al鈥檃muran ta ke
tamkar a cikin mafarkinta suke faruwa, kuma har
yanzu ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane
ba lokaci. Minti sha biyar ya kawo su har kofar
gidan Malam Bala, inda Saude ke nuna masa
hanya har suka iso, ya faka motarsa a qofar
tsohon gidan.
Dukkansu suka fito suka nufi gidan, Saudat na
rike da hannun Nabila, Shukura na gefenta, sai
Nabil a gefen Momy, Alhaji Ashiru ya zauna ya
jira su a mota.
Sallamar da suke ce ta janyo hankalin Inna Laure
da ke quryardaki tana tattara komatsai, ta yo
tsakar 'gidan tana fadar, 鈥淢arabanku; sannunku
da...鈥�
Turus taja ta tsaya tare da dafe qirji cikin
tsananin tashin hankali da kyarmar murya ta
soma fadar. 鈥淪u wayr ku, daga ina?鈥�
Momy ta gyara tsayuwa kafin tace 鈥淚kon Allah
abin da mamaki, idan ni ba ki gane ni ba, ai ina
tunanin wannan 鈥榶arki cr kya gane ta?鈥�
Ta yi maganar tana nuna Saudat.
Inna Laure ta fadi qasa jaBar kamar an tile kayan
wanki tana kwalla wa Malam Bala kira, dukkansu
suka yi tsaye suna kallonta.
Malam Bala ya fito daga kewaye a gigice,
hannunsa rike da buta yana fadar. 鈥淜ai Laure
wannan irin ihu haka ai sai ki sa juwa ta kwashe
ni in fadi ba gaira ba dalili鈥�.
Inna Laure ta rinka nuna masa inda Momy ta鈥� ke
tana fadar. 鈥淢alam duba min ka gani, wace ce
wannan Kamar Mariya鈥�. ?
Malam Bala ya ajiye butar ya nufo inda suke
yana fadar, 鈥淲acce Mariyar ki ke nufi?鈥�
Yana qarasowa inda suke yaja ya tsaya, suna
kallon-kallo shi da Momy, alamun firgici da
kaduwa sun bayyana cikin idanunsa.
Dr. Mariya ta yi mmmushi kafin ta ce 鈥淜allona da
ka ke tamkar wadda ta fado daga sama, na san
ba :zai rasa nasaba da ganin ba-zatar da nayi
maka ba a lokacin da daga kai har matarka ku ka
saki jiki da na bar muku duniyar shi yasa. ku ka
wofintar da rayuwar bayin Allah, ku ka
gallazamusu, kuka cuta musu don kawai ba su da
kowa, amma me ya sa ku ka manta cewa, duk
abin da kuke Ubangiji na nan Yana kallonku,
kuma duk daren dadewa sai ya saka wa mai
haqqi hakkinsa,
musamman ma bayin Allah wadanda basu da
alhakin kowa?鈥�
Kuka cuta musu, ku' ka gallaza musu kuka
tozarta rayuwarsu daga qarshe ma ku ka
tarwatsa " . min su kowa ya kama gabansa don
kawai ka tsani
, uawarsu a kan Iaifin daba bata ji ba ba ta gani
ba; wannan shi ne sakamakon soyayyar da
Kaunar da na maka? Lallai da haka shi ne
鈥榮akamakon . soyayya to da ba ta yi rana ba,
Sai dai da yake Allah ba azzalumin bawansa
bane, sai dai idan shi bawan ya zalunci' kansa,
sai 'ga shi bai bar rayuwata ta tozarta ba kamar
yadda kai kaso, Ya daga daraja ta a duniya, Ya
kuma cika min burina tahanyar azurtanida ilimida
nagartaccen miji Wanda ya fi ka komai a rayuwa,
Ya kuma sake ba ni wasu 鈥榶a鈥檡an, sannan daga
karshe Ya hada ni da 鈥榶ata gudan jinina, tabbas
babu abin da zance da Ubangiji sai godiya. . 鈥� '
Abu daya ya kawo ni wurinkn shi ne ka sanar
dani inda dana yake in kuma ba haka ba wallahi
sai na zauna kotu da kai, don sai ka bani鈥榙ana,
cutarwar da kayi musu kuma wannan kai da
Allah, Shi zai yi hisabi a tsakaninku,
-don haka ka sanar dani inda dana yake
. Tsananin firgici da kaduwa su suka girgiza 鈥�
zuciyar Malam Bala 鈥� har ya ji qafafuwansa na
Kokarin gaza daukarsa; ya matsa jikin bango'ya
jingina'yana faman maida numfashi a wahalce"
Laure da ke durqushe a kasa ta zabura ta mike
tsaye cike da qarfin zuciya ta cire kallabin kanta
taci damara kamar irin鈥榮abbin mahaukatan nan ta
soma magana tana tafa hannaye鈥淜am babban
abin da malam ya hana, mu za ki gwada wa
qaryar arziki tsohuwar karuwa, kin je kin yo hayar
kaya shi ne za ki zoki mana bariki? To qarya ki
ke, wallahi idan kin fasa zuwa kotun kin raina
Allahn da
ya halicce ki, ke wanda ma ya ba ki hakuri Allah
ya tsine masa, mu din nan sai dai mu ga bayanku
ba dai ku ku ga bayanmu ba
. Dr. Mariya 'ta yi wani qasaitaccen murmushi, ta
cire gilashin da ke manne a fuskarta tana kallon
Laure kafin ta ce, 鈥楢i ita da ma . tabarmar kunya
da hauka a ke nade ta, don haka
ban kuma kasa dake ba ballantana har ki kwasa".
Ta juya kan Malam Bala ta ci gaba da fadar,
鈥淶an tafi Malam, na ba ka nan da sati guda ka
nemo min inda dana yake kafin in dauki mataki,
ga kuma Saude a hannuna Allah ya jefo min
daga sama don haka na rungumi abuna, zan
dawo rana irin ta yau don karbar dana, na barku
lafiya鈥�.
Inna Laure ta yi caraf ta damke hannun Saude
tana fadar, 鈥淲allahi babu inda za ki je da ita, nan
zaki barta a gidan ubanta, don mijinta yazo yace
shi bai sake ta ba, dole kuma'ta koma gidan
mijinta Yanzu-Yanzun nan鈥�.
Ido waje Saude ke kallonta' gabanta na. Faman
bugawa da sauri da sauri, Momy kuwa dariya tayi
cikin ajikafin tace 鈥淜adadai ace shirme da鈥�
jahilcin' naki har ya fara taba kwakwalwarki? Ai
k0 shi uban da ya haifi Saude bai isa ya hana in
tafi da ita ba ballantana karabiti鈥�. Kamarki ba
1nn Laure ta Kara hayayyakowa tare dA
cukwikwiyo rigar Sauden
Malam Bala yace 鈥淪ake ta su tafi鈥� .
Ta juya tana kallonsa a kidime tana fadar
鈥淲allahi babu inda za ta Malam,Dan duk garinnan
banga ubandaya isa yasa ta tafi da ita ba ,Na ce
ki sake ta k0?鈥� Malam Bala ya fadi a harzuke
fuskarsa dauke da tsananin bacin ran da bata
taba ganin irinsa ba a tare dashi A dole ta saketa
din zuciyarta na barazanar tarwatsewa ta rasa
inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta
durkushe a Kasa ta rusa wani irin kuka mai ta
hankali.
~ 鈥� Momy da Shukura suka tasa Saude a gaba
鈥榮uka fice batareda sunsake bitakantaba. Suna
ficewa daga gidan Malam Bala yaja yan
qafafuwansa ya nufi: hanyar dakinsa, bai ko
kula: Laure ba, abin da ya qara firgitata ke nan
Kara .kidimewa zuciyarta cike da firgicin tonon
asirinta.
Suna fitowa daga gidan suka shiga mota, Alhaji
Ashiru ya ce, 鈥淲ai har kun yi me?鈥�
鈥淢omy ta ce, 鈥淢un tafi kawai Alhaji鈥�.
Ya dan waro ido kafin ya ce 鈥淎mma na za ta za
ku yi min magana da shi ko da fitowa ce ya yi
mu gaisa, k0 ba ku samu mahaifin nata bane?鈥�
Momy ta kwantar da kanta a kan makarin kujerar
kafin ta ce 鈥淢anta da su kawai鈥楢lhaji, muje ai sai
da mutunci ake zumunci鈥�.
Bai ce komai ba ya yi wa motar key, Momy ta
ce, 鈥淪audat ta nuna musu gidan iyayen Hamid.
Saudat ta鈥檃msa da to jikinta a sanyaye, zuciyarta
cike da kasala.
A Kofar gidan su Hamid maigadi ya sanar musu
iyayen nasa sun yi tafiya zuwa Zaria, sai dai
Hamid din shi kadai, Momy ta ce ya yi musu
magana da shi. Maigadin ya juya ya nufi cikin
gidan, bai jima ba ya dawo ya sanar da su yana
zuwa. Suna nan zaunc cikin mota daga鈥� gate din
gidan, yana sanye da wani farin yadi mai sheki
ya daura wa wuyan hannunsa wata tsadaddiyar
agogo baka, mai kyan gaske ya dora farin gilashi
saman dogon hancinsa da makullin mota a
hannunsa, da
alama fita zai yi. Kai tsaye wurin motar tasu ya
nufo idonsa a kan Momy tun kafin ya ida
Karasowa
鈥� yana isowa ya rusuna ya gaida Daddy, sannan
ya gaishe ta yana fadin, 鈥淒octar kece a
gidanmu?鈥� ~ 鈥楧r Mariya ta fadada fara'arta kafin
ta ce 鈥淎iko nice da kaina Malam Hamid, ai dole
ne ma 鈥� inzo ko dan qaunar da ka nuna wa
Saudat ya zame min wajibi inzo in yi maka
godiya, kuma in maka albishir da cewa Saudat
yata ce nice mahaifiyarta nina haife ta da cikina"
Hamid ya waro idanuwa waje yana fadar, 鈥淵arki
kuma DR? Kina nufin dama kece mahaifiyarta鈥�?鈥� ,
Momy ta amsa da, 鈥淭abbas nina haife ta da dan
uwanta Rabi u鈥�. ~ Wani irin dukulallen farin ciki
daki zuciyar Hamid. ya daga hannunsa sama
yanA yiwa Allah godiya. Saudat kuwa kallonsa
kawai ta ke a . zuciyarta tana jinjina ma soyayyar
da bawannan 禄ke mata 鈥� 鈥� Momy鈥� ta ce 鈥淶a mu
tafi Malam Hamid, da fatan zumunci mai Karfi?
zai shiga tsakaninmu鈥� 芦 Hamid ya amsa da
鈥渋nsha ,Allah"鈥� Amma idansa na kan Saudat
wadda ke ta faman haske shi
鈥� da lallausan murmushi 鈥� Yace 鈥淢amy ki bani
adireshinku insha Allahu dana dawo daga tafiya
zanzo
Babu musu Momy ta ba shi dan qaramin card din
da ke cikin jakarta wanda ke dauke da adireshin
gidan da lambar gidan, sannan Dady ya ja motar
suka tafi Saudat na daga masa hannu har suka
Bace wa ganinsa. Wani irin abu ya caki zuciyar
Hamid, ya sa dan yatsansa ya lakace 鈥榶ar
guntuwar kwallar da ta taso masa, shi da ya sani
Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son
da
ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce
ta zama haka? Rayuwa kenan.
Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka
Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don
ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy
ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu
Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci.
Bayan sallar la鈥� asar kuma Shukura ta koma gida
saboda gobe tana da lecture a school.
Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar
alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil
da Nabila tana kallonsu suna home work da aka
ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon
kafadarta na rataye da katuwar jaka, 鈥榮ai rigar
likitoci sagale a dayan hannun da alama
dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka
zabura suka nufe ta a guje
suna fadar, 鈥淥yoyo my Momy, welcome".
Ita ma da fara鈥榓 a kan fuskarta ta rungume yaran
a jikinta tana shafar kawunnansu.
Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy
ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta:
鈥榙a mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye
kicin ta nufa ta jero kulolin鈥� .abinci a babban
faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi
ta nufo falon, inda ta samu鈥� . Momy har ta yi wa
kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon,
yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. 鈥�
Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta
soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa.
Momy ta rike farantin tana fadar.
鈥淏arshi kawai Saudat, kije falon waje
Hamid nanan ya zo zaku gaisa鈥� . . Saudat ta
washe baki tana fadar. ' ~ 鈥淜ai Momy, ashe bai
mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da
dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi
da ya ce 鈥榓 * washegari zai zo?鈥�
Momy ta ce 鈥淎h to, ni kaina da na ganshi a
yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya
garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je
kar yaga an barshi shi kadai.
_ 鈥� Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta
ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka
takalminta flat Shoe shi ma fari
A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade
hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke
jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil
ne wanda .aka yi musu a harabar wurin
shakatawa da
ke cikin park dukkansu sun yi matukar
kyau tamkar 鈥榶a鈥檡an da ke rayuwa cikin dusar
qankara.
Saudat ta qaraso cikin falon da 鈥榶ar siririyan
sallamarta, bakinta na dauke da murmushi.
Hamid ya yi saurin waigowa yana kallon mai
shigowarr tare da amsa mata sallamar Saudat ta
tsaya dan nesa da shi tana fadar, 鈥淪audatu ya
tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita
tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa鈥�. .
Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda
kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta,
girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi ya
fi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar
alfarmar da ke jikinta. Ba komai bane a jikinta,
illa wani tsadadden code lace dark blue mai
ratsin fad-fad a jiki, dinkin riga da siket, kalar
leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka
dinkin ya yi matukar kwantawa a jikinta. Yafi
mayafin da ta yi
Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da
sigarta ta nutsattsiyar budurwa.
: Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana
fadar, 鈥淎llah ya huci zuciyar Saudat, wai kin ga
yadda kika ka koma kuwa?鈥� 鈥�
鈥� 鈥� Saudat ta yi murmushi har da sunkuyawa ta
zauna tana fuskantar katon teburin da aka
qawata
da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~
鈥� ' 鈥� Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta
da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira
sunanta .
鈥淪audat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai .
misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa '
mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a
zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a
ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke
nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri sai
da nazo ki yarda da ni don Allah kyakkyawata".
Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin
yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani
zautaccce, shi ma 鈥榶ar dariyar ya yi yana sosa
qeya alamar ya danji kunya shi ma.
A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai
cikin falon da鈥� yar siririyar sallamarsa, waddai ta
makale amakoshi. * '
Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ' inda
yake Wani razanannen kallo ya watsa mata ta
cikin siririn farin gilashin da ke manne a
fuskarsa,
Lokaci guda ya dauke kansa tamkar allah bai
ajiye 鈥�
Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin
gidan.
Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da
maida hankalinta inda Hamid yake
Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . 鈥淲annan
shi ne abokin takarar tawa kenan?鈥�
Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan
wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid
yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani
sarai ba za ta iya hada soyayyar Dr. Ahmad da
ta kowa a zuciyarta ba.
Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a
cikin aljihunsa yana kallonta da fararen
idanunsa.
Saudat ta yi qasa da idanunta ta kasa hada ido
da Hamid din sai kawau ta tsinci kanta da jin
matukar nauyinsa.
Hamid ya yi wani malalacin murmushi
Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na
dan sarqewa ya ce 鈥淭sananin son da nake miki
Saudat, da dumbin qaunarki da ke zuciyata ba
zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat na yi
miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na
tabaa so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin
da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo
gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da
Kausar 鈥榶ar qanin mahaifina
'Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja鈥�
ban鈥� sonta, banida muhallin da zan iya
:ajiyeta a a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na
dawo. A yanzu haka mahaifina ya yi fushi , , don
haka mahaifiyata ta ba ni shawara na tafi
Kaduna Wurin matata, wannan ne 鈥� kadai abin
dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu鈥� haka
tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa
daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na
wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har
kin ji zaki iya aurena a yadda nake a 鈥� yanxu na
ba ki sati daya ki yi shawara duk abin da 鈥� kika
鈥漼anke zan dawo sai ki sanar dani鈥�.
鈥�' Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata
cebaa ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya
dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice
abinsa. Saudat ta mike jikinta a kasale ta 鈥� nufi
qofar shiga babban falon gidan. Ba ta ankara ba
sai dai ta ji sun yi karo yana qokarin fitowa ita
tana qokarin shiga, ta yi saurin ja da baya tare da
dafe goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya
dauke kai da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat
ta yi saurin rufa masa baya tana ' kiransa baida
alamar tsaya ba balle harya .saurar茅 ta hakan ya
sa ta Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa.
'Don Allah ka tsaya ka saurareni
Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka. Dr.
Ahmad yasa ya tsaya a gabanta yas鈥榟annayensa
a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta
langwabar da kai ' 鈥淒on Allah kar ka horar dain
da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba鈥� . . Dr
Ahmad ya watsa mata harara kafin yace鈥淚dan
har ni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke
kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki
kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa
maganar tare da sa hannu yana ture ta daga
gabansa
Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ' son
fashewa da kuka ta ce 鈥淗aba don Allah yallaBai,
Yaya Hamid ne fa ba wani ba鈥�.
Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo,
鈥淥key, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji
baneba k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba
ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce鈥�.
Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda
ta ke rarrashinsa yana qars botsarewa. ta juya
da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki.
Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda 鈥� zafin da
zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai
dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi
yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya
' iya haka ya juya ya fice daga falon
YAR. TALLAH
CHAPTER30
Saudat'na Shiga falon taga Momy zaune
hannunta rike da waya da alamar. magana ta
gama tana shirin giftata. ta wuce, Momy ta rika ,
hannunta. saudat ta waigo da sauri tana kallonta,
'don haka ta dawo ta raBa ta zauna zuciyarta
babu "dadi. ,
~ Momy ta kira sunanta, 鈥淪audat dan rigimar nan
naki ba zai miki haqurin ki fara karatu ba, naga
alamar rigimamme ne na gaske, don haka nayi
tunanin a tsaida magana kawai in yaso ko a
gidanki kya yi karatunki idan kina da rabo har
gaba da sakandire sai ki wuce a gidanki don haka
yanzu zabi yana wurin ki shin tsakanin Hamid da
shi Ahmad din waye kike jin kina so a cikinsu鈥�
Saudat ta dago a sanyaye ta dubi Momy
kafin ta ce, 鈥淒uk ina sonsu鈥�. Momy tayi wata
tatacciyar dariya ta ce,
鈥淭o idan kina sonsu duka Saudat wa ki ke son
aura
A ciki kuma?鈥�
Saudat ta yi shiru zuciyarta naci gaba da
' harbawa, ta. sani sarai soyayyarta a yanzu
tanaga
鈥� wurin Dr.鈥� Ahmad, to amma ta juya wa Hamid
baya 鈥�
' anya ta yi wa soyayyar da ya yi mata adalci?
To shi kuma Dr din fa?
鈥� 鈥� 鈥� Momy ta katse mata tunanin da cewa
. 鈥淜i yi tunani da kyau Saudat, duka mutanen biyu
duk suna qaunarki amma ni a nawa gamin
Ahmad shi ne wanda ya cancanta ki aura, amma
ki yi tunani da zuciyarki".
Saudat ta dago kai tana kallon Momy zuciyarta
na faman harbawa ta ce 鈥淢omy na zabi Dr din in
har ke ma ya yi miki
Momy ta dora hannu saman kafadarta ta dafa ta
tana fadar, 鈥淗akan shi yafi cancanta
Saudat, tashi kije Allah ya yi miki albarka".
Saudat ta amsa da, 鈥淎min鈥�. Sannan ta mike cikin
sanyin jiki ta nufi dakinta, ta fada kan gadonta a
rufda ciki ta dafe kanta da hannaye biyu tamkar
mai shirin kurma ihu, ta lumshe idanu tana jin
zuciyarta na bugawa da qarfl, tamkar za ta ballo
Kirjinta ta flto waje. Sai dai ta samu taimakon
wata dunkulalliyar damuwa da ta tokare ta ta
hana ta baro kirjin harta fito fili, tana so ta ji
halin da Dr. Ahmad yake ciki, amma kuma tasan
babu dama.
Tana nan kwance har aka kira sallar magriba don
haka ta miqe ta nufi bandaki ta dauro alwalla ta
fito ta nufi kan sallayarta ta zura dogon hija鈥榖inta
ta tayar da sallah, tana gamawa ta kishingida a
saman sallayar ta Iumshe idanunta tamkar mai
jin bacci, amma babu komai a zuciyana sai
dumbin damuwa. .
Ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula ta ji an
kwalla kiran sallar isha鈥橧, a dole ta mike don ba
鈥� da farali.
., saida ta gama sallar harta mike ba, zata Kara
kudundunewa akan sallayar tamkar mai jin 鈥�
sanyi, inda rai da zuciya keta aikin rarrabe
tsakanin Aya da tsakuwa anya dana dauki Dr.
Ahmad ta bar Hamid ta'yi wa soyayya adalci? 鈥� 鈥�
Ba ta ji shigowar Nabila ba, sai dai ta ji ta dafa
ta tana fadar, 鈥淎unty kizo inji Ya鈥榶a yana falo
yana jiranki鈥� ' Saudat ta yi saurin tashi zaune
tare da rike hannun Nabilar tana fadar, 鈥淲ane
falon Nabila?鈥�
鈥� 鈥淔alon Daddy da baki鈥�. Ta ba ta amsa. 禄 Saudat
ta dan yi jim tamkar mai nazarin wani abu
tamkar kuma wadda aka tsikara ta zabura ta
mike ta shuri takalmanta ta fice ta nufi falon da
yake ta sa kai ta shiga tare da 鈥榶ar siririyar
sallamarta, ba don Allah ya yi ta ita din mai ji
bace sosai daba yadda za a yi ta iya jin amsa
sallamar da ya yi a can qasan makoshi irin ta
wanda damuwa ta galabaitar da shi. 鈥� Jikin
Saudat ya yi sanyi matuqa, ta zubawa fararen
idanunsa ido, yana zaune saman kujera ya ,
tallabe kansa da hannaye biyu ya zuba wa kaifet
ido. Jikinta a mace ta IallaBa ta zauna. saman
kujerar da ke gefenta, ta kasa dauke idonta a
kansa. sawon mintuna biyar falon tsit baka jin
motsin komai a ciki sai iskar A. C zaman shirun
ya fara damunta tana son kawar da shirun, amma
kuma bata san k0 ta Wacce hanya zata biba, to
k0 hakuri zata ba shi? Idan ma hakurin ne ta ya
ya za ta ba shi? K0 Shukura za ta kira ta bashi
kan wayar ta
"lallasar mata shi..
' Ba ta ankara ba sai dai ta ganshi a durkushe a
gabanta, kirjinta ya yi wani mummunar bugawa
saboda yadda yawa Kafafuwanta, ta yi saurin ja
da baya cikin kujerar, hakan ya yi daidai da riqo
hannuwanta duka biyun da ya yi, tare da kiran
sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya wadda
ta tilasta mata dago kanta ta kalle shi, gabanta
ya yi wani mummunar faduwa, fararen idanun
nan nasa tamkar an watsa barkono, gabadaya ya
birice, ya canza tamkar ba shi ba ne wannan
tsayayyen daktan jarumi mai razanar da ita ba.
Ta runtse idonta da karfi saboda wani irin abu da
ta ji yana tsurga mata zuciya.
Dr. Ahmad ya kira sunanta da wata irin
dakusasshiyar murya, 鈥淪audat ki bude idonki ki
kalle ni don Allah, kar ki tsane ni wallahi ina
sonki, irin son da duk duniya babu mai yi miki
kwatankwacinsa. ,
Saudat ki taBa zuciyata za kiji ki saurari zuciyata
zakiji, ki kalli zuciyata za ki game irin guguwar da
ke binne a cikinta, Saudat ina sonki
son da zan iya salwantar da rayuwata a kanki, ..
wallahi Saudat ina cikin fargaba tunda na bar
gidan '
Karkiji yaddah zuciyata kr cikin baqin ciki a dole
na dauro alwala na zauna ina ta ambaton Allah
Saudat na yi sa鈥� a bakin .cikin ya gushe, amma
damuwar da nake ciki ba ta barni ba har a
lokacin nan na kasa runtsawa, gani nake
zuciyarki na wurin鈥� Hamid; da alama kuma za ki
iya barina ki 鈥� koma gare shi a kowane lokaci,
wannan tunanin ne ya tilasta min dawowa Saudat
don in sanarda ke cewa, idan har kika kuskuren
juyawa zuciyata baya, to tabbas鈥� a ranar zakiji
mummunan labari ~cewa na rasu, don ba zan iya
rayuwa ba matukar
babu ke a tare danibs
Shirun da Saudat ta ji ne ya tilasta. mata bude
idanunta tare da kallon inda ta ke sa ran' yana
zaune, amma da mamakinta tuni har ya kai bakin
kofa, ba ta san lokacin da ta mike ba, tare da
kiran sunansa.
Ya waigo da sauri tare da daga mata hannu.
Karki ce komai Saudat soyayya ta zarce duk
yaddaki ke tunaninta, don soyayya gamon jini 鈥�
ce ba wai gamma gambiza ba, so haduwar
zuciyane ba wai tilasta shi akeyi ba Kuma
linzamin so ' hankaline ba wai son rai ba. Saudar
kar ki tilasta wa kanki ki soni don kawai kina
tunanin ya kamata ki so ni, ba zan kasance mai
son raiba na tilasta miki
aurena ba alhalin ba nine a zuciyarki ba. Tun
ranar da na soma sonki na kasance bani da. wani
buri da
Daya wuce son nagana dauwar dafarinciki
鈥� zuciyarki, na dandana miki zaqin rayuwar da ba
ki taBa dandana ta. Va
Kuma kp a yanzu haka abin yake Saudat, dolene
na baki farin cikinki k0 da hakan yana nufin
rugujewar tawa rayuwar dole zan ba ki shi, kuma
na yi miki alkawarin sadaukar wa Hamid da
soyayyata matukar shi ne farin cikin rayuwarki鈥�,
Saudat taji wani abu ya tsarga mata zuciya mai
kama da tsinin mashi, hawayen da suka tarar
mata a idanu tun dazu suka samu damar biyo
kuncinta, kuka nena gaske ya kwace mata,
Wanda ta rasa dalilin yinsa.
Dr. Ahmad ya yi saurin nufo ta, jikinsa na.
kyarma yana Kokarin riko ta, ta yi saurin ja da
baya
tare da fadar 鈥淜arka taBa ni don Allah na rokeka,
idan鈥� har son da nayi maka bai gamsarda dodon
kunnenka ba don Allah ka fadamin kalaman da
zan yi amfani da su don su gamsar da kai, ni dai
in har na san abin da so yake nufi, to saboda kai
'ne in har dai abin da nakeji a zuciyata shine so,
to YallaBai na soka, so kuma kai kadai irin wanda
ba zai taBa Karewa ba har abada" Shi 鈥榢uma
hamid din fa ya zaki yi da shi Saudat? Yana
sonki kamaryadda nake sonki, babu wani dalili da
zaisa ki amince da daya daga
acikinmu don kawai kina ganin rashin
kyaumtawar ki guje masa Saudat ni na fadada
bakina na aminca miki ki zaba wa 'zuciyarki abin
da take so, k0 da 鈥� kuwa hakan yana nufin bani
za ki zaBa ba, kuma hakan ba zai sa na karya
alkawarin dana dauka ba, na daukaka darajarki da
duk.......
鈥淵a isa don Allah ya isa haka!鈥� Saudat ta yi
maganar muryarta a sanyaye cikin kuka ta ci
gaba da fadar, 鈥淒on Allah ka kyale ni haka, idan
na ce ban so Hamid ba YallaBai karya nake, sai
dai ina
so ka gane abu guda shine, irin son da nake wa
Hamid ba shi nake maka ba, sonka a cikin
zuciyata ya sha bamban da irin nasa, don kuwa
ka san shi murmushi yafi dariya. _
Abu guda kawai na sani shine, ba zan iya rayuwa
ba inba tare da kai ba, idan har ina da rabon
samun farin ciki da 鈥� jin dadi a rayuwata to kai ne
farin cikina, kai ne jin dadin rayuwata鈥�.
Da sauri ya nufe ta tamkar 鈥榸ai kamo ta, sai ka
ce wani zautacce, muryarsa harsarkewa ta ke
Wurin fadar, 鈥淒a gaske Saudat kin amince za kl 鈥�
zama tawa? Za ki kasance da ni yanzu da har
abada? Saudat don Allah ki amince ki zama tawa
ni . kadai, wallahi a yanzu kece farin cikina, ke
kadai kika ragemin, kin amince min na turo da
鈥� da sadakinki gobe, ki fada min Saudat, ke nake
saurare鈥�. Kai kawai ta iya daga masa ba tare da
ta bar
zuciyarta ta yi wani dogon tunani ba
Farin cikinsa ba zai misaltu ba a lokacin ita kanta
Saudat ta tabbatar da hakan saboda yadda ta ga
ya dawo cikin nutsuwarsa lokaci guda ya koma
kan kujera ya zauna tare da sauke wata
nannauyar ajiyar zuciya. Ya jingina kansa akan
makarin kujerar yana sauke numfashi cikin
nutsuwa, idonsa na kan Saudat wadda ta kasa
zama.
Dr. Ahmad ya qakaro wani dan murmushi kafin
ya ce, 鈥淜in min tsaye akai kina kallona k0 so ki
ke ki gano munina ne?鈥�
Saudat ta yi saurin janye idanunta a kunyace tare
da鈥� yar dariyarta Kasa~qasa.
Dr. Ahmad ya dan. kishingida kadan a kan kujcrar
yana fadar, 鈥渏eki samo min dan wani abu in ci
kada yunwa ta san yadda ta yi dani
A, dan sanyaye Saudat ta kalle shi, shi ma
'idanunsa a kanta suke adole ta juya ta nufl kofa
don kwarjininsa ba zai barta ta furta abin da ke
bakinta ba. Kai tsaye kicin ta nufa ta soma
dawainiyar sama masa can abin da ta san zai iya
ci, sai dai babu komai akicin din sai sauran
farfesun dare wanda ya ji kayan yaji, don haka ta
zubaruwa a kettle ta kawo garin citta da karunfari
da ganyen
ta zuba, sannan ta jona a wuta 鈥� Tana nan tsaye
harya tafasa sannan ta juye masa鈥渢a dora saman
tire ta dora kofi daya tare da cokalin shan tea,
sannan ta dora kular farfesun tasa filet da
madaidaicin spoon sannan ta bude tirij ta dauko
cake manya guda biyu ta dora a gefe, sannan ta
dauka ta shiga falon da yake da sallamarta har a
lokacin yana nan a kishingidensa; . Saudat ta
durkusa a gabansa ta zuba masa tare da
tsiyaya鈥檓asa ruwan zafl a kofi ta sa masa lipton
da coffe tare da madara da sukari kadan ta juya
ta miqa masa ya sa hannu ya karBa, bakinsa
dauke da murmushi ya ce 鈥淣a gode kwarai鈥�
Murmushi kawai ta yi ta mike ta koma kujerarda
ke fuskantarsa ta zauna.
Tana kallonsa sai da ya cinye komai ita kanta ta
yi mamakin irin yunwar da ya kwaso, shi .kansa
ya lura da irin kallon da ta ke masa. Ya mike
tsaye da dan murmushinsa yana kallon agogon
dake daure a hannunsa, ya ce 鈥淣i zan wuce, idan
har kallona da ki ke me cike da tuhuma ya
wadatar da ke Murmushi kawai ta yi, ta mike
tana tattara, kayan daya ci abincin, ya dan
mirgina kai 鈥�
鈥濃€榠dan kin shiga gida ki sanar da Momy
manya zasuzo gobe insha Allahu misalin qarfe
hudu na yamma鈥�
Allah ya kai mu鈥� amsa a takaice tare da bin
gefensa za ta wuce saboda kwarjininsa da takrjin
ya cika mata falon. Shi kansa ya lura da hakan,
cikin zolaya ya ce. 鈥淏a sallama kuma Madam ko
har na angwance tun yanzu ne?鈥� Ba ta juyo ba
ta yi gaba abinta saboda dariyar da ta ji yana
mata, ta tabbatar zolayarta yake son yi, don haka
ta yi cikin gida abinta. Washegari misalin karfe
sha daya na 鈥榮afe; Saudat na kwance a falonta
saman kafet ta' yi matashi da filon kujera tana
kallon wa'azin Shekh
Ja鈥檃far da aka sanyo na Sunna T.V mai taken鈥�
鈥楽uffatus salatun nabiyi'. '
A Kasan zuciyarta kuma tunani ne barkatai, tun
jiya data yi mafarkin Yaya Rabi鈥榰鈥� ta kasa
nutsuwa, tunanin dan uwan nata ya addabi '
zuciyarta k0 karyawa ta kasa yi, burinta bai wuce
na ta koma Dandagoro bA don ta karb saqon da
Hamid ya sanar da ita Yaya Rabi鈥� u ya bada
makotansu a ajiye mata, ta san gidan ba zai
wuce gidan Inna mai danwake ba, don gidanta ne
ke manne da nasu, kuma nan ne kadai gidan da
suk茅 ' shiga ita da Yaya Rabi u alokacin suna tare
Bataji shigoWar Momy a falon ba, sai dai鈥� ta ji ta
dafa ta tana fadar, 鈥淏acci ne k0 kuma dogon
tunani?鈥�
鈥溾€� Saudat ta yunkum ta tashi zaune tana kallon ,
mahaifiyar tata wadda ke kokarin zama a kan
kujera, ta ja remote ta rage sautin akwatin
talabijin
鈥� din tana fadar.
鈥� 鈥淵anzu Alhaji ke sanar da ni yau za su je wurin
Babanki don nema wa Ahmad aurenki, ni dai cewa
ma, na yi,,kawai a kyale shi aCi gaba da
,hidima a nan, Alhaji ya ce ba zai yiwu ba, dole a
ba
shi hakkinsa a matsayinsa na mahaifi.
* Ya ki ke ganin za a bullo wa tsarin bikin, don
rana kawai za akira ban da asabar din gobe ta
sama za a daura auren, kin ga dole musan abin
da za a shirya don kar IOkaci ya qure mana. Ki
min lissafin duk abin duk abinda kike so, don zan
tura a Dubai . za a hadp komai鈥� ,. .
' Saudat ta sunkuyar da kanta tana wasa da
yatsu. Momy ta kafa mata idanu muryarta a
saayaye ta ce, 鈥淪audat lafiyarki kuwa, me ke
damunki?鈥�
鈥� A hankali ta d鈥榓go kanta ta kalli mahaifiyar '
Kata da idanunta, wadanda suka ciko da kwalla,
ta ,
hadiye dunkulalliyar damuwar da ta 鈥榯okare mata
.
zuciya, kafin tace 鈥淢omy yanzu shi kenan Yaya
Rabiu ya bace kenan har abada?鈥�
YAR. TALLAH
CHAPTER31
Momy taja wani gWauron numfashi kafin tace
鈥淚nji wa ya fada miki Saudat? Ni naji a jikina
Rabi,u yana raya, kuma yanzu haka na_ baza 鈥�
*cigiyar鈥榮a tun daga gidajen talabijin, radiyo,
mujallu da kuma jaridu tare da ofisoshin jami,an :
tsaro insha Allahu Saudat zai bayyan, ki
kwantarda hankalinki kinji Saudat ta daga mata
kai kafin ta ce, 鈥淭un *鈥� ina Abuja Hamid ya sanar
da ni Yaya Rabi鈥� uv ya ba da sako a makwabta a
bani nasan gidan Inna mai danwake ne shine
nakeson inje inkarbo Momy ta ce, 鈥淎鈥榓 ba zan iya
barinki ki je ba, sai dai inwa Alhaji magana ya sa
k0 direba ne yaje ya karbo miki hakan ya yi
miki?" 鈥� Kai kawai Saudat ta iya daga mata
alamar eh. 鈥� . ' Tace 鈥淥kay lissafo min abubuwan
da ki ke *bukata, kodai kin bani wuqa da nama
ne? . Saudat ta amsh da, 鈥淓h Momy鈥�. Dariya
Momy ta yi kafin ta ce 鈥榃annan fillancin naki ya
yi鈥� yawa Saudat, anya kuwa?鈥� 鈥� 鈥� Dariya kawai
Saudat ta yi mahaifiyar tata ta fita ta barta ,
Misalin karfe budu na yamma Shukura taxo , 鈥�
gidan da鈥� yar qaramar jakar kayanta, dadi ya
cika' Saudat don kwana biyun da tayi babu ita
ba鈥� " 'qaramin kewarta tayiba
Shukura ta sauke jakana a kan gado tana
fadar 鈥淎marya kin sha kamshi, wannan fara arfa
duk ta murnar amarcin ne?鈥� Saudat ta waro ido
cikin dariya ta ce鈥淜ai _
don Allah meye na zolaya kuma? 鈥� 鈥�
' Shukura ta fadakan gadon tare da rungume ta
tana fadar, 鈥淏a wani nan zolaya, gaskiya na fada鈥�
' Saudat ta tabe baki ta zauna a kan kujera tana
fadar, 鈥淎i da ma Hausawa sunce idan baka
iya sharri ba ka koyi kage鈥� .,
Shukura ta ce, 鈥淏a wani nan, haka nan ki ke nuna
wa Momy kauyanci amma irinku sululu kasau
kunfi kowa iya shege
Saudat ta yi dariya tana fadar, 鈥淵au kuma da
mita ki kaxo gidan kenan?鈥�
Shukura ta ce 鈥淎i dole in miki iya shege, don
Momy ta kira ni wai na tattaro na taho mu zauna
don ta lura kina bukatar huduba ta, ni kuwa
Tasan ba wani nan k0 karya na fada?"
Saudat ta mike tayi hanyar鈥榝ita daga falon tana
fadar, 鈥淣i ban iya abin da kika iyaba鈥�. 1
Shukura ta tuntsure da dariya don ta san ta
Qular da ita.
, Washegari da safe suna zaune a falo Shukura na
karanta wa Saudat wani littafin Hausa mai suna
KADANGARUN BARIKI, Momy ta turo
Ta turo .Kofar ta shigo tare da fadar, 鈥淭o sai ku
tashi ku shirya yanzu maza direba ya kai ku
gidan Maman 鈥� Sumayya maida tsohuwa
yarinya鈥� . ' ' Shukura ta zabura tana fadar, 鈥淲ow
Momy! Da gaske?鈥� . 鈥� Momy ta yi murmushi tare
da Juyawa tana fadar, 鈥淎鈥檃 da wasa鈥�. , ~
Shukura ta dafe Saudat tana fadar, 鈥淜ai . amma
wallahi Momy tanaji dake Saudat, lallai zaki rudar
da DR wai baki taba jin labarin Maman Sumayya
a Abuja ba?" Saudat ta girgiza mata kai a
hankali, don ita 鈥� dai ba ta fahinci inda maganar
tasu ta dosa ba. , Shukura ta ce, 鈥淟allai, da
mamaki don a * fadin Nigeria babu jihar da sunan
matar nan bai , zaga ba, kaya ta ke siyarwa 鈥榶an
gaskr, tun daga kan, gyaran gashi, gyaran fata,
sabulluka zuwa mayukan gyaran fata, kayan
manyan mata kuwa wannan daga qasashen
Larabawa ta ke hada su. Ke dai bari 鈥� mu je za ki
gane wa idonki鈥� Saudat ta ce, 鈥淚ta kuma amarya
har wani . gyara na daban ake mata.鈥� , Shukura
ta yi wani takaitaccrn murmushi kafin ta ce 鈥淚n
ban da abinki Saudat, idan akwai . macen da ta
ke bukatar gyara a bayan amarya ta ke ko kuma
macen da ta haihu ita amarya ana bukatar 鈥�
komai nata ya xama na musamman ne tun ba ke
da"
Zakiyi aure gidan kishiyaba, ya kamata ta ko鈥檌na ,
mijinki' ya san da bambanci, tun daga tafukan ,
hannunki, labbanki, fatar鈥� jikinki, da kuma
fuskarki, sai kuma can ainahin wanda wannan
kuma aikin manyan mata ne musamman idan
auren na Soyayya ne
Abin da dai nake so ki gane shi ne ranar bikin
kowace mace to awurinta wannan babban ra'na
ce da babu irinta a rayuwarta, musamman idan
auren na soyayya ne.
A ranar daurin aurenki kowa burinsa ya ga irin
kwalliyar da zaki yi, kek0 da 鈥榶an gidanku ne suna
son qare miki kallo a wannan ranar, shi yasa
wasu matan tsabagen son gyaran jiki har gyaran
鈥榮ai yazo ya yi yawa, ya feSo musu 'da quraje a
fuska k0 da ba bata da wadannan kurajen a da.
Don
haka a matsayinki na aMarya ya kamata ki kula
da kanki, akwai sirrikan abubuwan da ke gyara
amare na farko a matsayinki na amarya ana
bukatarki da yawan sham ruwa sirrin hakan shi
ne, kar jikinki ya yankwane. Sannan ana bukatar
amarya da cin 鈥測a yan itatuwa hakan zai taimaka
wa fatar jikinta matuka, 鈥� sannan ana bukata:
amarya da ta yawaita sham , kankana, ita ma za
ta taimaka mata matuka wurin gyaran fatar
jikinta, haka kuma cin ganye irin su. latas da
kabeji, suma za su taimaka kwarai.
Ta yinkura ta nufi bandaki tana fadar 鈥淏ari in fara
watso ruwa mu shirya tun
kafin Momy ta sake biyo mu鈥� . Ta zame kayan
jikinta ta shige bandakin don
watsa wa jikinta ruwa. lko sai mai tsaga ido Allah
Almusawwiru, mai yadda Ya so, tabbas na yarda
komai nufi ne na Ubangiji, kuma al鈥檃marin aure
tamkar layin . kasuwa ne idan layi yazo kanka k0
bakaso sai an maka, kamar yadda arziki bai isa
ya guje wa 鈥榤ai shiba, haka shi ma rai bai isa
yaqi mai shi ba, haka matar mutum ba ta isa ta
guje鈥榤asa ba k0 ana 鈥� ha-maza ha-mata, auren
da Ubangiji ya qaddara to fa sai an daura shi duk
tsananin wuya, kuma duk dadi don duk nisan dare
gari zai wayr. Hakan ce kuma ta kasance don yau
ita ta kasance ranar juma'ar da za a daura auren
Saudat a asabar
In ka duba gidan Dr. Mariya acike yake da yan
uwa da abokan arziki na kusa da na nesa, don 鈥� a
ranar ne za a yi kamu, wanda Dr. Mariya ta
shirya . Biki ne ake ba wai na wasa ba, don kudi
ta ke kashrwa tamkar tana tsinto su
mafiyawancin abubuwan da ake yin amfani dasu
a wurin bikin duk
daga qasashen waje ta bada saqonsu aka taho
mata鈥� 鈥� dasu
DukvWanda ya 鈥漵an Saudat kuwa yancu鈥� idan*
ya ganta da wuya idan zai iya ganeta Cikin sati
~daya ta yi wani fitinannan haske, don har wani
.yalo-鈥榶alo ta ke, fatar jikinta ta yi wani luwai-
luwai
鈥檚ai sheki ta ke tare da daukar ido tamkar jikin
tarwada, cikia lokaci guda ta rikide tamkar wadda
aka Kara wa kyau da fari.
Kodayake irin manyan kudin da Dr. Mariya
ta saki wurin gyara 鈥榶ar tata sun isa ace ta
maf1 ; haka. don k0 gyaran jiki sau uku aka mata
arana, safe da yamma da kuma lokacin kwanciya
bacci, don daidai da Kunshi daga Abuja ta dauko
mai zanen da ta yi musu, gyaran gashi ne aka yi
musu 鈥� a babban wurin gyaran gashin da ke G. R
A,abinka da ma da mai abin don haka gashin ya
isa saukowa , har tsakiyar bayanta, ga wani baKi
da sheqi da yake na musamman. Haka dinkunan
fitar .biki duk a Lagos ta ba da aka dinko mata
wasu kuma a -. Dubai sai shaddojin ne ta bada
aka dinkosu a Maradi. Yanzu haka Saudat ce da
Shukura baje a falo suna duba kayan fitar kamun
da za su sanya a yau, Momy ta turo kofa ta
shigo da sallamarta, ta ' tsaya daga bakin kofa
jikinta a sanyaye ta ce
鈥淒ireba Ya daWO yanzu鈥� amma har yau dai mai .
danwake ba ta dawo ba, sai dai maigidanta ya
鈥檛abbatarda cewa, duk abin da ak茅 ciki ba za ta
rana ita yau ba tare da ta dawo ba" 鈥�
Cikin nutsuwa Saudat ke kallon mahaifiyar tata,
cikin sanyin jiki da sanyin murya ta amsa da,
鈥淎llah ya kai mu Momy, Allah Ubangiji ya
bayyana mana shi ma kafin lokacin鈥� .
, Momy ta amsa da,鈥淎min鈥�. Kafin ta dau wani
nannauyan numfashi tana kallon Shukura ta *
ce 鈥淵a kamata fa ku yi azamar shiryawadon Karfe
hudu daidai za a fara kamun鈥�.
Shukura ta amsa, 鈥淚nsha Allahu Momy
yanzu za mu shirya鈥�. ' ' Momy ta juya ta fice
Shukura kuma ta mike tana fadar, 鈥淭ashi鈥� yar
uwa ki fara shafawa jikinki ruwan lallen nan kafin
in fito daga wanka鈥�
K0 motsi Saudat ba ta yi ba ballantana ta sa ran
amsawarta, hakan ya sa Shukura waigowa ta
dubi inda Saudat ta ke, tare da fadar,鈥淟afiya dai
Saudat. " "
A hankali ta dago kanta tana kallon Shukura kafin
ta ce, 鈥淏abu komai鈥�.
" Shukura ta girgiza kai, 鈥淎鈥檃 ban yarda ba
Saudat, na lura damuwar fan uwanki na damunki
amma ya kamata ki yi wa Momy uzuri, saboda
yadda ta ke iya bakin qokarinta bai kamata ki
Kara , daga mata hankali da damuwarki ba. Kina
kallo tun 鈥�. ranar daki kace mata yayanki ya鈥�
bada sako
gidan mai danwake a ajiye miki Momy kullum sai
ta tayar da direba ya je gidan, amma har yau ba
a yi nasarar sa'mun mai danwaken ba, tunda an
ce ta je
garinsu Ki kara haquri don Allah Saudat, insha
Allah zaki ga sako mai dadi wurin mai danwake
da
zarar ta dawo tashi ki rage kayan jikinki in taya ki
shafa
鈥� Ba musu Saudat_ ta yun kura ta mike don ta
sani haquri ya zame mata dole, k0 da ba a ba ta
ba ita. ta ba wa kanta tunda dai babu wanda ya
san inda Rabi鈥� un yake. Shi kansa Dr. Ahmad din
yanzu iya kokarinsa yake mata a kan鈥� cigiyar dan
uwan nata' saboda yadda ya ga ta damu a
kansa. , 鈥� Da taimakon Shukura da kuma na
matar da 鈥� . Momy ta dauko mai kwalliyar amare,
aka gyara amarya Saudat cikin wani tsadadden
cotton lace mai laushin gaske kalar dark pink an
qawata shi da bakaken fulawoyi da wasu
qananun duwarwatsu, masu kama da yarfin gwal,
daurin kallabin da aka kafa mata duk wanda ya
kalla ya san daurin鈥榮hago ne don ba irin wanda
muka sabayi bane gashin 鈥� nan nata an saki
kadan gefen fuskarta sauran kuma an nade shi an
saki jelarsa a kan gadon bayanta inda
aka kawata wuyanta da kunnenta zuwa yatsun
hannunta da tsadaddun gwala-gwalai Sannan
suka dora ta a kan bakin takalmi mai
matsanancin tsini sai ka ce wadda ta hau tsani
sai yar qaramar jakarsu wadda ba ta wuce
girman tafin hannuba
Amarya kam ta fita batun bayyana irin
kyawun da ta yi ma bata lokaci ne, don k0
lokacin .da ta ke zama a kan kujerar da aka
tanada
' don amarya, saf ta zauna tamkar mutum-
mutumi, ko ace aljana don kyau, kai ka zata zana
ta aka yi ba 鈥� wai mutum bace
鈥淎na kiran sallar magriba aka tashi daga kamun,
a lokacin ne kuma Dr. Ahmad da abokansa ' '
suka iso gidan cikin tsadaddun motocinsu, don
haka gidan ya kara rikicewa, Shukura ta shiga
busy
don ganin ta karrama angwayen da abubuwan
ciye ciye da tande-tande.
Saudat kuwa duk kunya da nauyin Dr Ahmad ne
ya hana ta sakewa da kyar Shukura ta samu ta je
ta gaishe shi shima sai da ta yi da gaske a
lokacin da ta shiga falon da aka sauke su gogan
nata yana kishingide saman doguwar kujera
abokansa sun sa shi a gaba suna ta hayaniyarsu,
' inda shi kuma yake ta faman kallonsu yana cin ,
tuffa apple.
Saudat ta ji tamkar ta nutse a lokacin da suka
hada idanu, sai taga ma tamkar shima kara masa
kyau akayi, farin yadin neke jikinsa ya Kawatar Da
kyar ta yi ta-maza suka gaisa da abokan nasa
sarakan surutu kamar zasu hadiyeta
Kowa burinsa ya fadi albarkacin " bakinsa ita dai
ta gaza tofawa sabuda kwarjinin da angon nata
da ya cika falon, ji take duk girman dakin ya yi
mata kadan, sauqinta ma daya Shukura da ta
tare ma rigimar domin don kuwa ita
wurin dan banzan surutu ba 鈥榙aga baya ba. Dr.
Ahmad wanda tunda ta shigo falon bai * ,tanka
ba har sai da ya lura zolayar abokan nasa za
鈥� ta iya nutsar da Saudat cikin qasa don kunya, ~
sannan ya yunqura ya mike a kasale tamkar
wanda aka yi wa dukan tsiya.
, Ya nufi inda amaryar tasa ta ke nutse cikin
kujera ya sa hannu ya tayar da ita tsaye yana
fadar, 鈥渢aso mu bar nan Madam kada su samin
ke ciwon kai
Kamar jira suke suka yi kansa, amma bai kula
suba yana rike da hannunta suka fice daga falon
kai , tsaye harabar waje suka nufa, ya jawo musu
wasu fararen kujerun roba suka zauna cikin
rumfar da aka tanada don hutawa
Dr Ahmad ya yi wani murmushi mai kama
鈥� 'da dariya lokacin da yake Kokarin lallai sai ya
hada , ido da ita amma ta Ki yarda shi dariya ma
ta ba shi, ya tallabe kuncinsa yana fadar, 鈥淥h ni
Ahmad na ga ta kaina, haka zamu yi dake
kenan?鈥�
Ya Kara sa dariya, 鈥淟allai yarinya aiki ya , ganki
bama kadan ba, amma fa kin yi kyau don鈥� lokacin
da ki ka shigo falon sai da nayi suman wucin
gadi har wani kishi na ji ya yunkuro min yadda na
ga kartan nan na kallonki shi ya sa na harna
.gaza magana
, Duk yadda zuciyar Saudat ta ke cike da
alkunyarsa sai da dariya ta kwace mata jin yadda
ya kira wayayyun abokansa da qartai, Dr. Ahmad
ya kafe ta da manyan idanunsa yadda ta ke
dariyar 鈥� tata cikih nutsuwa
kallon da yake mata ya sa a dole ta gimtse
dariyarta, hakan ya yi daidai da sauke wani
gwauron numfashin da ya yi tare da lumshe
manyan fararen idanunsa ya shafi sumar qeyarsa
yana kallon farar moter da take shigowa cikin
gate din 鈥檊idan a dan nesa da su kadan aka faka
motar daga ita har shi idonsu na kan motar.
Zuciyar Saudat ta yi wata mummunar bugawa
lokacin da mutumin da ke cikin motar ya fito shi
da wata zukekiyar mace kai tsaye inda suke
zaune suka nufo har a lokacin kirjin Saudat
bugawa yake ta gaza k0 da kwakkwaran motsi.
鈥淗amid dinne k0? 鈥�
, Dr. Ahmad ya watso mata tambayar yana .
kallonta Kai kawai ta iya daga masa don a
lokacin har sun qaraso cikin sallamarsu inda
Hamid ya
miqawa Dr Ahmad barin fuskarsa 鈥榙auice da fara
a suka yi musabaha Hamid na riqe da hannun '
Dr Ahmad ya taya shi murna tare da yi masa
fatan aikhairi cikin sanyin jiki, Saudat ta gaishe
shi amma ga mamakinta har a lokacin da fara,a
akan fuskarsa ya amsa mata a. tare da yi mata
fatan aikhairi ya nuna zukekiyar macen dake
tsaye " wadda akalla shekarunta ba zasu haura
ashirin da daya ba . Yac茅, 鈥淕a Kausar nan
takanas 'muka taho鈥� tare don ta taya ni murnar
aurenki, ita ce amaryar ' tawa鈥�. Ya juya kan
Kausar din, 鈥淜ausar ga Saudat 鈥� Da鈥� fara鈥檃 a
fuskarta ta miqa wa Saudat hannu suka' yi
musabiha cikin sigar zolaya ta dubi Dr. Ahmad
tana fadar, 鈥淕odiya mara: adadi, .ka taimake ni
tunda ka kasa鈥� angona don da yanzu Kausar ta
shiga cikin jerin sahun matan da za ayiwa kishiya
a wannan watan,na gode 鈥� Dariya suka yi su
dukkansu ganin yadda Dr. '"鈥� Ahmad ya Saki
fuska babu alamar damuwa a yanayinsa ya sa
Saudat ta saki jiki ta mike ta riko hannun Kausar
tana fadar, 鈥淏ismillah鈥� yar uwa mu
shiga daga ciki mu gaisa sosai " Dr Ahmad ya
mike shi ma tare da miqa wa Hamid hannu yana
fadae 鈥淣i ma abokina. mu shiga
daga ciki gida na kula abin yar wariyar launin
jinci ce鈥�. , Duka dariya suka sa suka rankaya
suka nufi
cikin gidan
Zuciyar Saudat fes, ba qaramin dadi tajiba
Ganin yadda Dr. Ahmad ya karBi Hamid din cike
da 鈥� farin ciki. Ba Karamin mamaki鈥� ta yi ba
yadda Hamid ya samu labarin aurenta, kodayake
auren da kullum sanarwa ake a gidajen tal'abijin
da radiyo lallai ita kanta ta san ba Karamin
matsayi Hamid yake da shi a Zuciyarta ba, har
cikin ranta ta ji Kausar ta kwanta mata don
kawai tana matar Hamid hatta rasa inda鈥檢a
ta_saka ta, ta kawo mata wannan ta' kawo
wancan har sai da Kausar ta dakatar da ita, ita
kuma Shukura ta ci gaba da dawainiya da Hamid
din. ' . Ba su suka bar gidan ba sai qarfe goma
na
dare don sai da suka gaisa da Momy da Alhaji .
Ashiru sannan suka tafi a cewar gobe Hamid zai
maido , Kausar gaskiya su duka sun yaba da 鈥�
matar Hamid din don ba qaramar kyakkyawar
mace ya samu ba, wayayyiya kuma yar boko. 鈥�
Ba Saudat ba hatta Momy da Shukura sunyi _
mamakin irin makudan鈥� kudin da Hamid din ya
baiwa Saudat wai ta. siyi abin da ta ke So, tunda
鈥榖ai _ samuya siya mata komai ba. Lallai Hamid
ya
dauka Saudat da muhimmanci a rayuwarsa, haka
da ma al鈥檃marin Ubangiji yake
.Washegari ita ta kama ranar asabar da misalin
qarfe daya na rana aka daura auren " Saudat da
angonta Dr Ahmad Mukhtar ; daurin aure ne
wanda ya tara manyan mutane kala daban-daban
tun daga gida Najeriya har zuwa sauran
Kasashen qetara abbas daurin auren ya kafa
tarihi a cikin Dandagoro 鈥�
Motoci suka dauki amarya da tawagarta zuwa
gidan mahaifinta da ke Dandagoro don wai a can
ne za,a dauki amarya, kamar yadda Alhaji Ashiru
ya bukata ba don ran Momy yasoba ta amince
Haka manyan motoci suka kwashi amare aka nufi
gidan mahaifinta, amarya鈥� Saudat dake lullube
'cikin mayafl Kirjinta ya shiga dukan tara-tara
don ba tasan irin tarbar da dandazon Jama,ar
zasu samu a gidan nasu ba. Haka suka shiga
cikin
gidan mahaifiyar Shukura da DR murja qawar
Momy na riqe da amarya har cikin gidan. Inna
Laure da ke durkushe bakin murhu na ganinsu ta
zabura ta mike tsaye tamkar sabon kamun hauka
' : Fuskar nan tata dukta gauraye da majina da '
hawaye saboda hayakin wuta ciki kaduwa take
fadar, 鈥淲annan dandazon haka fa sai kace na
masu zuwa yaqi na menene?
' Dr Murja tace鈥淎u maigidan naki bai
Fada miki bane? To amarya ce aka kawo gidan
ubanta a dauke ta a ciki鈥�.
鈥� Kida a ruwa mai tada haukan dodo tana
fadar haka Inna Laure ta yo kanta da masifa, 鈥�
鈥楢maryar ukan abun uba za a kawo gidan ubanta,
k0 ita uwar amaryar bata sanar muku ba 鈥榶ar
tata ruwa biyu bace? Ai ba ta da uba don haka
an dai daura aure a gidan nan amma babu dan
iskan da ya isa ya-shigo min gida don a ci min
zarafi
Mahaiflyar Shukura ta kwantar da murya ta ce,
鈥淗aba baiwar Allah meye kuma abin cin fuska
don' dai kawai dan zaman da za a yi wanda bai
=wuce na minti talatin ba?鈥�
Ai kamar jira ta ke ta koma kanta, 鈥淜e rufe mani
baki kin ji tsohuwar banza, ai da ma garin 'banza
a farau-farau din wofi yake qarewa, gida dai nawa
ne, kuma dole ku bar min abuna in ba haka
"ba'wallahi sai in cinna wa gidan wuta mu hadu
mu duka mu qone za ku fita k0 kuwa ba zaku fita
ba?鈥� Ai kafin wani ya ba ta amsa ta kwaso itacen
da ke cikin wuta ta yo kansu * *鈥� Malam Bala da
ke kokarin shigowa cikin gidan ya yi wani kukan
kura ya yi kanta ya rike ta ta 'baya, hakan ya
sata fasa wani razanannen ihu tana kokawar
kwacewa, ya murde hannunta ya na cewa
[8:43AM, 06/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: YAR. TALLAH
CHAPTER32
Complete
Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana
tirje~tirje da zuba ~ munanan ashariya ya danna
ta dakinta ya kulle, ko,a haka aka barta ya ishe
ta azaba saboda tsananin zafin da ake
kwararawa a garin ga shi dakin ba shi da tagar
shan iska k0 kadan 鈥� Malam Bala ya nufo su
yana basu hakuri akan abin da Inna Laure ta yi
musu, ita kuwa Saudat idonta na kan mahaifinta,
za ta iya cewa tunda take da shi ba ta taBa
ganinsa ya yi irin kayan da ya yi ba, saboda
tsadadden yadin da ke jikinsa wanda aka yi wa
dinkin yar ciki da babbar riga, kayan sun sha
aikin hannu.
Dr.Murja ce ta ja mayafin Saudat ta rufe mata
fuska, wanda haukan da Inna Laure keyi ya sa ta
budewaba tare datasani ba
Malam Bala ya kwasa ya nufi dakinsa yana yana
raWar jiki, sai ga shi ya dawo dauke da manyan
tabarmi shi da kansa ya shimfida mnsu a tsakar
gidan suka zazzuna shi 鈥榢uma ya juya ya gita
baifi minti sha biyar ba sai ga shi ya dawn do.
wasu almajirai dauke da ledojin pure water dana
kwalayen 鈥� ,lemuka katan-katan鈥� aka jibga musu,
ita dai Saudat ta cika da mamakin abin da kr
faruwa sun kwashe mintina talatin a gidan
sannan angwaye suka zo daukar amaryarsu don
haka Shukura da mahaifiyarta suka tasa Saudat a
gaba
har zuwa zaure inda mahaifinta yake don ta roqi
gafararsa.
Saudat ta durkusa a gabansa jikinta ya yi sanyi
ba ta san abin da za tace da mahaifin nata ba,
abubuwan da suka faru ne a baya suke dawo
mata cikin zuciya, tamkar a yanzu ne suke
faruwa.
Tamkar Malam Bala ya san abin da ta ke tunani,
sai ga shi yana furta, 鈥淒on Allah don Annabi
Saude ki yi hakuri ki yafe min duk abin da na yi
miki wanda ki ka sani da wanda ma ba ki sani
ba. Na san na zalunce ku sai dai~ na san sharrin
shaidan ne, don Allah don Annabi ki yafe min
kafin na mutu wallahi ban san abin da-zan cr da
Ubangijina ba, tabbas na ga ishara a rayuwata,
kuma na yarda zakaran da Allah ya da chara k0
ana muzuru ana shawo sai ya yi, Saude ki yafr
min don Allah don Annabin rahma
鈥渟unyi mamakin yadda kuka ya ci qarfinsa ba
suboda tun yana maganar muryarsa ke rawa, ba
karamin鈥� sanyi jikin Saudat ya yi ba jin kukan
dattijon. nata don haka ba tareda zuciyarta ta
qara tuna mata komai ba ta ce 鈥淜a yi hakuri
Baba, ni
ban rike ka da komai ba, wallahi na yafe maka鈥�
Cikin kuka Malam Bala yace 鈥榃allahi ni 鈥� ba kiyi
min komai ba Saude, inma kinmin ba yafe
miki Allah Ubangiji ya yi miki albarka, Ya ba ku
zaman lafiya da zuri鈥� a dayyaba Saudat bata iya
amsawaba, sai dai Momyn
Shukura ce ta amsa sannan ta kama Saudat ta
mike suka rankaya aka nufi mota da amarya ,
Masu kai amarya suka dunguma a motoci, amma
abin mamaki sai ga wasu daga cikin jama鈥� ar ,
unguwar cikin masu rakiyar amarya babu goro 鈥�
ballantana katin gayyata
Har motocin daukar amarya zata dags Malam
Bala ya kwaso da sassarfa yana daga musu 鈥�
hannu, suka tsaya ya nufi motar da Saudat
ke鈥榗iki, ta taga ya mikamata wani Kunshi a baKar
leda. Ta karBa cike da girmamawa, sannan
motocin , suka rankaya da amarya sai garin
Abuja, alqawarin, Allah ya cika, don karfe biyu na
rana a gidanta ya yi mata wanda yake a unguwar
鈥榶an majalissu.
Saudat ba ta kasa gane gidan ba duk da kuwa
canje-canjen da ya qara samu, haka suka
rankaya Zuwa bangaren amarya, sai dai mucr
barakallahu fihi, masha Allah don Dr.禄 Mariya ta
murza naira wurin fiddo da 鈥榶ar tata don haka鈥�
tsarin gidan zuwa tsarin kayan ya qawatar da
falukan da aka zuba suka yi dace da juna, don
komai an sa shi cikin tsari, don haka duk wanda
ya je kai amarya sai da ya firgiga wai ahakan ma
donyawancinsu sun saba shiga irin gidajen amma
鈥榶an Dandagoro
kuwa sai ga su darshe a kan marbles suna ta
faman zare na mujiya, Shukura dai na rike da
amarya, Saudat wadda ta ke jinta tamkar a
saman gajimare wasu daga cikin dangin ango ne
krta faman dawainiya da su tun daga abubuwan
ci zuwa na sha harna tande-tande irinsu dambun
shinkafa dambun nama, shinkafar kaza, soyayyun
kaji, farfcsun kaji, donut, meatpie spring roll, fried
rice, hadadden salad chips din kwai da dankalin
Turawa, fruits kala-kala har da wanda ba su taBa
gani ba da sauran kwalayrn lemuka da robobin
ruwa masu sanyin gaske.
Saudat dai da ke cikin mayafi tana jin karadin
Farida qanwar Ahmad don ta fi kowa kai wa da
kawo wa an agama sallar la鈥檃sar motoci suka
kwashe 鈥榶an kai amaryar don dawo da su gida
bayan an cika su da sha tara ta arziki.
Sai a lokacin kuka ya zo wa Saudat ganin duk za
su watse su barta, Shukura ce ta rungume ta tare
da yi mata rada, sai ga ta tana kuka da dariya,
lokaci guda duka suka rankaya suka tafi suka bar
Farida rungume da Saudat kowa ya watse
Su Farida da wasu ma 鈥檃ikatane ke ta faman
gyare-gyaren gida, sai ga shi cikin dan lokaci
Bangaren nata ya zama very need, babu abin da
ke
fita a cikinsa sai qamshin room freshner mai
sanyin
Farida ta dawo bedroom din da Saudat ke ciki ta
zauna gefenta cike da kulawa ta ce 鈥淎unty
Saudat ki shiga bandaki ki watso ruwa sai ki
dauro alwala don lokacin sallar magriba ya yi鈥�:
Saudat ta Ki k0 motsawa haka kawai take jin
gabanta na faduwa ba ta da wani kuzari.
鈥� Faridat ta yi murmushi tana fadar, 鈥淗o Aunty
anya wannan dari-darin da ki ke a cikin * gidanki
zai fisshe ki kuwa?鈥�
Ta Kara murmusawa, 鈥淭o yi hakuri dai muje na
raka ki ki watso ruwan鈥� .
Ta sa hannu ta riko Saudat din don haka ta
sauko daga kan gadon tana Kokarin bin qofar fita,
Farida ta ce, 鈥淚na za ki kuma? Ki shiga bandaki
din nan mana dama don kar a Bata. mikine ya sa
na ce su shiga wancan bandakin da ke dayan
falon鈥�. ' Saudat ta dan yi sororo don ita dai 鈥榓 iya
ganinta ba ta ga wata鈥� kofar bandaki ba don
tsakanin falo ma da bedroom gilas ne ya raba 鈥�
tsakaninsu, don haka duk cikin falon babu wata
alamar kofa.
, Faridat ta mike ta nufi wurin gilas din ta danna鈥�
yar wata alama sai ga shi ya raba kansa biyu ya
fidda wata鈥� yar hanya wadda ta zarce har cikin .
bandaki Farida ta shiga ciki, don haka itama: _
Saudat ta bi bayanta. Farida ta gwada mata.
yadda
Zatayi amfani da komai na bandakin sannan ta
fita dan ta samu damar watso ruwan ' Tana
fitowa ta samu Faridat ta qara gyara gadon har
ta ciro mata kayan da zata saka don haka
Saudat ta nufi inda sallaya ta ke ta yi sallar
magriba ta zauna, har lokacin isha ya shigo
sannan ta yi sallar tare da shafa鈥� i da wutiri
wadda Momy ta . koya mata tare da wasu daga
cikin ayyuka na addinin musulunci tana idarwa ta
mike ta nufi kan gado inda Farida ta ajiye mata
kayan da za ta saka, wasu lallausan yadi ne
kalar baki mai taushin gaske wanda aka kawata
shi da wasu fararen duwarwatsu masu haske.
Saudat ta saka yadin a jikinta Wanda aka yi'wa
dinkin riga da siket yadin ya bi jikinta ya lafe a
farar fatarta. Farida ta shigo tare da 鈥榶ar siririyar
-sallamarta hannunta na rike da wani
madaidaicin faranti da ke dauke da 鈥榶an wasu
kananan kwanuka ns tangaram. Ganin Saudat ya
sa ta ta saki murmushi, 鈥淵auwa Aunty Saudat k0
ke fa? Ki dan yi make up k0 ya ya ne Murmushi
kawai Saudat ta yi ta nufl gaban ,dressing mirro
ta ja kujera ta zauna tana kallon gaban madubin
.wanda ke shake taf da kayan x kwalliya irin na
wayayyun mata da suka san kansu.
Body lotion kawai .Saudat ta dauka ta murjawa
jikinta, sannan ta murza wa fuskarta wata yar
karamar hoda wadda ta ida fito da tsabar kyawun
fuskarta, sannan ta shafa wa laBBanta wetlips
gloss, sai da ta Kara gyara gashin kanta ta dame
shi da farin ribbon kwara guda ta sake shi a baya,
sannan ta yi sassaukan daurin kallabi a kanta
wanda ya Kara fito da ita, ta dauki 鈥榶an qananan
鈥榶an kunnayenta da sarqa na diamond ta maqala
a kunnenta ta 'saka 鈥榶ar qaramar sarqa ta dauki
turarenta body spray ta mammatsa a鈥� gaBObin
jikinta, ita kanta ta san ta yi kyau irin wanda ke
nutsar da zuciyar maigida, ta juyo ta nufo inda
Faridat ke tsaye tana tattara 鈥榶an komatsanta.
Muryar Saudat na rawa ta soma fadar,鈥渋na kuma
za ki je don Allah : naga kin yi lullubi kina tattara
jaka?鈥�
Faridat ta mike tana kallonta da murmushi a
kan fuskarta, 鈥淢aigida ya yi kira Saudat, amma fa
kin yi kyau sosai, nasan yayana zai yaba don
Allah kada dai a yi masa rowa". Tayi maganar
tana dariya tare da shafar beauty point din
Saudat din ta juya a gurguje ta fice tana fadar,
鈥淒on Allah ki ci abin da na hado miki, please
Auntyna".
Saudat da ke tsaye ta bita * da , idanunta masu
kama da madara harta ta fice ba
yadda ta iya haka ta sadakas ta koma da baya ta
zauna a kan gadon nata wanda kr fitar da ,
sassanyan Kamshin bed freshner Ta miKa hannu
ta janyo tiren da Faridat ta ajiye mata ta soma
dudduba abin da ke cikin鈥� yan kwanukan da
kofinan, na farko gasasshen nama ne wanda ya ji
kayan yaji, sai na biyu wani' irin nama ne Wanda
aka yi wa 'wata irin dahuwa mai danko, sai' kofi
na farko tsumin markadaddun 鈥榶a'yan itatuwa ne,
dayan kuma danyar madarar shanu ce , mai kyau.
鈥� Duk da ba ta fahimci amfanin abubuwan a gare
ta ba, ta daure ta ci sosai kamar yadda Faridar
ta roKa. Ta dauki tiren ta fice da shi ta mayar da
shi a kicin da ke falonta na biyu, ta tsaya tana
kallon kicin din, komai na ciki tsab.tsab gwanin
kyau, ko falon wani mai kudin sai haka, don haka
maimakon ta bar kayan a haka, sai ta soma tara
ruwa ta wanke 鈥檚u cike da sha鈥檃war komai na
kicin din Ba ta ji motsin shigoWar mutum a kicin
din ba sai dai ta ji an rungumo kwankwasonta ta
baya. * 鈥� Ta fasa wata razananniyar Kara tare da
juyowa hakan ya ba shi damar rungume ta .
gabadaya a jikinsa tare da lalubar kunnceta cikin
鈥� sanyin muryarsa ya soma rada mata 鈥榶an
guntayrn ~kalmomin da ta rinka jinsu tamkar a.
cikin mafarkinta.
Cikin sanyin jiki ta soma Kokarin zame鈥� jikinta
hakan ya sa shi rike hannayenta duka biyun
'yana fadar, 鈥淪auara tsaya ki ji, bakinki kawai za
ki ara min just minti biyar kawai鈥�
Wani kallo ta watsa masa a razane tare da fizge
hannunta za ta tsere ya yi'saurin damko ta yana
dariya ya ce 鈥淜e da wasa fa nake miki, wallahi a
gajiye ma nake ba kiji gaBobina ba gaskiya na
samu Saudat da wahala, mu tafl ki taya ni na
watsa ruwa鈥�.
Duk yadda ta so ta kwace abin ya faskara
saboda irin kyakkyawan rikon da ya yi mata a
dole ta bi shi. 鈥�
Kai tsaye dakin baccinta ya nufa da ita, ya dire ta
a kan gadonta yana fadar, 鈥淶auna nan, bari na
watso ruwan na flto鈥� '
Ba ta tanka masa ba ya juya ya nufl wurin shiga
bandaki ya latsa ya shige _ ita dai kallonsa kawai
ta ke amma da
shawararta yabima da bai cire baqin yadin da ke
jikinsa ba, don ba Karamin kyau ya yi masa ba
abinka ga farar fata. Ta lumshe idonta ta bude
lokaci guda tare da komawa. da baya ta kwanta a
kan gadon, hakan ya yi daidai da shigowar Asma
鈥檆ikin dakin. Kirjin鈥� Saudat ya yi wata. mummunar
bugawa tamkar saukar aradu, don dama tun dazu
ta kasa nutsuwa tunda ta fahinci a gidan Asma
aka
kawo ta
Asma ta shigo falon sosai tana kallon Saudat . ta
kada kai tare da maida murfin kofar ta rufe tare
da murza key, abin da ya ida firgitar da Saudat ke
nan ta tashi zaune cikin matukar rudani tana
kallon Asma wadda ta jingina bayanta da kyauren
shigowar tana kallon Saudat bakinta dauke da
wani malalacin murmushi mai cike da mugunta,
sannan ta soma nufo inda Saudat din take zaune
Cikin tsananin firgici da rashin sanin abin yi
Saudat ta soma ja da baya. Asma ta ja ta tsaya
tana fadar, 鈥淚na za ki je 鈥榶an mata? Da ma kin
tsaya don kashe ki zan yi wannan shi ne
huquncin kuskuren da ki ka aikata '
wannan ranar ta yau za ta zamo darasi ga
sauran 鈥榶an aikin da ke kokarin auren mazan
iyayen
gidansu. Wallahi yau zan kashe ki kuma na kashe
banza, duk duniyar nan babu wanda ya isa ya bi 鈥�
miki hakki鈥�.
鈥� Kafin Saudat ta yi wani yunkuri tuni har A鈥榮ma
ta禄 kai mata cafka tana kokarin Shakar wuyanta
kamar wadda ta sha wani abin maye, kira ' ta ke,
鈥淵anzu zan kasheki sai dai yazo ya tarar da
gawarki; amma ba dai ke ba don Asma tafi karfin
鈥� 鈥� ta. hada miji da kaskantacciya, wulakantacciya
~ matalauciya wadda ta yi gadon ;siya da
talauci鈥�.
Kokawa ce ta kaure tsakaninsu, Asma na qokarin
kama makasar Saudat,鈥� ita kuma Saudat na
qokarin kwatar kanta sai dai qarfin badaya ba
don Asma tafi Karfln Saudat k0 daga yanayin jiki
ma tafita qiba, tunda ita har yanzu ba ta da
Kwari kamar a kama a karya, don haka Asma ta
samu nasarar kayar da ita ta janyo filon da ke
kan gadon abin da ya jazawa Saudat kurma wani
uba-uban ihu kenan, sai dai za mu iya cewa
ihunka banza, kururuwarka wofl don kuwa babu
wanda zai iya juyo ta.
Tana qokarin danne fuskar Saudat da filo, ita
kuma tana kokarin kwatar kanta tana ihu, a haka
Dr. Ahmad ya fito daga bandaki yana dame da
tawul da wani dan karami a hannunsa yana tsane
jikinsa, idonsa da kunnensa suka yi mummunan
gani da ji cikin kidima ya yi kukan kura ya dira
inda suke, ya fincike Asma da
Qarfinsa, amma har a lokacin ba ta daina boren
sai ta cafko Saudat ba.
Abin da ya sa shi kifa mata wani zazzafan marin
da ya sa ta dafe kunci kenan cikin tsananin
kidima don har wata wuta ta ga ta gifta mata
cikin tsananin takaici da zafin zuciya ta ke kallon
Dr, din da idanunta da suka ciko da hawaye
jikinta ya yi sanyi matuka ta soma magana cikin
mury茅r kuka.
, 鈥淎hmad ni ka mara? Ni ka mara saboda wannan
abun? Lallai ka tsokano wa kanka tsuliyar dodo
dan na鈥� rantse maka da Allah sai na halaka
yarinyar鈥� nan, sai na ga bayanta, sai na kawar da
ita daga doron qasa. Kai in ban da ma asiri ya
rufe _maka idanu wannan har mace ce wadda za
ka 'wulakanta ni a kanta鈥�.
Ta ja kwafa tana girgiza kai, 鈥淭abbas sai ka yi
dana sanin abin da ka aikata min banza, butulu,
mayaudari ai da ma duk dadinka da jaki watarana
sai ya yi maka tutsu don da ma dan halas ne
kadai ke maida halarci. . .鈥�
鈥淪hut up! You are very stupid, get out! Sakarar
banza na ceki bar nan鈥�.
Duk Dr. Ahmad ne鈥� ke maganar cikin
tsananin fushi tare da nuna mata hanyar fita. _
Tsananin baqin ciki da takaici suka sa Asma yin
wani malalacin murmushi tana kallonsa cike da 鈥�
qunar zuciya ta girgiza kai ' 鈥� ba zan yi mamakin
duk abin da ke fitowa daga bakinkaba Ahmad,
amma ina so ka sani na shirya daukar dukkanin
tashin hankalin da ka ke ganinka iya kuma ni din
nan wallahi sai na sa ka zubar da hawaye, sai
kayi nadamar sanina a rayuwarka.. 鈥淚t is enough
Asma I say get out!!鈥� Ganin yadda idanunsa suka
birkice ta san
komai zai iya faruwa idan har ya yi irin wannan
fushin don haka ta ja kwafa ba tare data sake .
magana ba ta bude qofarta fice tana murza
yatsunta alamar za ya gani ke nan. Tana fita ya
maida Kofar ya kulle sannan ya nufo inda Saudat
ta ke kwance tana faman shesshekar kukanta.
Dr. Ahmad ya zauna bakin gadon tare da
janyo ta jikinsa ya rungume ta sosai da鈥榶ar
sanyayyar muryarsa ya soma lallashinta, 鈥淵a isa
haka nan Saudat, kada kanki yazo yana ciwo, ki
yi haquri kinji, duk abin da ta fada karya ta ke ba
za ta iya ba鈥�.
Saudat ta dago kanta da sauri tana kallonsa
cikin idanunta da ke zubar da hawaye ta ce
鈥淵anzu abin da ta yi bai tabbatar maka da zata
iya aikata abin da ta fada din ba?鈥�
Dr. ya Kara rungumrta, 鈥淜i kwantar da ,
hankalinki zan Kara ja mata kunne sosai kin ji
k0?鈥�
Ba ta iya ce masa komai ba sai ma ta mayar da
kanta a kirjinsa tana kukanta kasa-qasa, Dr. ya
tallafo kanta da hannunsa ya soma bin fuskarta
yana lasar hawayen da suka Bata mata fuska, a
hankali ya soma zarcewa har zuwa kan Wuyanta
da鈥� Kirjinta ya rinka bin gabobin jikinta har zuwa鈥�
tsakiyar kanta yana sinsinar lallausan gashin
kanta wanda ya sha gyafa, sai daukar ido yake.
Saudat ta tSinci kanta cikin wani irin yanayi 鈥�
wanda bata taba tsintar kanta a cikinsa ba
tsawon
rayuwarta, ita kuka shi kuka duka an rasa mai
rarrashin wani, kiran sallar farko shi ya dawo da
Dr daga duniyar rudanin da ya shiga, iya jarunta
da hakuri Saudat ta yi shi, sai dai duk yadda ta
zata abin ya wuce tunaninta. Ta yi kuka har
muryarta ta dusashe don ta azabtu ta kuma sha
wahalar da ba zata misaltu ha, shi kansa ya rude
ganin yadda ya wahalar da ita, don haka ya sure
ta ya nufi bandaki da ita da kansa ya tara ruwa
masu dumi a bahu ya gasa mata jikinta, sannan
ya sa ta dauki niyya ta yi wankan janaba, ya
taimaka mata suka flto daga bandakin kai tsaye
saman gadonta ta haye, saboda yadda jikinta ke
faman kwankwatsa. Cike da tausayawa ya raBa
gefenta Ya shiga mammatsa mata jiki yana
rarrashinta da kalamai masu dadi, har ya samu
bacci ya yi awon gaba da ita, sannan ya mike ya
nufi bandaki ya yo wankansa ya dauro alwala
yazo ya zura jallabiyarsa sannan ya fito inda
shimfidar sallarsa ta ke ya rinka. jera nafilfilu, ,
sai da ya ji ana kiran sallar asuba sannan ya
sallama ya yi addu,o in da zai yi na godiya ga
Allah, ya maida sallar asuba. Yana gamawa ya
mike ya nufi inda Saudat ke kwance tana kukanta
yana son tayar da ita. amma yana tsoron ya
tsokano wa kansa rigima ba yadda ya iya a dole
ya tayar da ita din yadda ya . zata kuwa hakan
ya kasance don tana farkawa kuka 鈥�
ta sa masa ya samu ya rarrashe ta da
taimakonsa ta dauro alwala ta yi sallar sannan Dr
ya sure ta suka koma kan gadon suka kwanta
yana rarrashinta tare da rirrike ta tamkar tsoka
daya a miya
Karfe sha daya daidai Saudat ta farka daga
baccin da ya kwashe ta, ta bude idanunta sosai
babu Dr. a gadon don haka ta lallaBa ta mike ta
nufi bandaki don watso ruwa, sai da ta tara
rowan dumi ta gasa jikinta sosai sannan ta yi
wankanta sosai ta fito ta ja kujerar dake gaban
madubi ta
zauna. Ta janyo lotion ta murza wa jikinta, ta
dauki
kayan kwalliya ta yi 鈥榶ar sassaukar kwalliyarta, ta
qara gyara gashin kanta wanda ta cude da
mayuka masu laushi, ta sa ribbon kwara daya ta
daure gashin kanta ta fesa masa hair freshner, ta
mike ta nufi wurin wardrof ta bude ta ciro wani
swiss lace mai sulBi irin mai rawa-rawa kalar
jinin kare maroon an masa adon' fulawa light
pink dinkin riga da siket, Saudat ta saka kayan a
jikinta wanda suka .dace da kalar farar fatarta.
鈥淒inkin ya hau jikinta matuka ta nufi gaban
madubi ta kafa daurin kallabinta sannan ta saka
dankunne da sarka fashion kalar pink ta dauki
body spray ta bi jikinta ta mammatsa ta nufi
cover
din ,da aka tanada dan ajiye takalma ta soma
tunanin kalar da za tasaka.
鈥� Dr. Ahmad ya turo qofar ya shigo da sallamarsa,
Saudat taji tamkar ta aza da gudu don idan
akwai wanda ta ke jin kunyarsa to bai wuce Dr鈥�.
Ba a yanxu, shi kuwa kai tsaye inda ta ke ya nufa
fuskarsa dauke da fara鈥檃 yana fadar, 鈥淜ai babyna
wannan kyan fa duk nawa ne?鈥�
Ya ida maganar tasa tare da dora kansa a
kan bayanta yana sunsunar kamshinta.
. Saudat ta yi saurin zamewa za ta ruga ya sa
dogon hannunsa ya riko ta yana dariya, tare da
fadar, 鈥淟allai yarinya kina tunanin za ki iya tsere
min ke nan?鈥� *
Saudat ta sa tafukan hannayenta ta rufe
Fuskarta da su tana jin tamkar Kasa ta tsage ta
shige
ciki, Dr. ya sa hakoransa ya cizar mata 鈥榶an
yatsu
abin da ya sa ta saurin bude fuskar tare da 鈥榶ar
siririyar Kararta cikin shagwaBa kenan ya lakace
mata hanci yana fadar, 鈥淢arowaciya Allah da kin
Kara hana ni kallon kwalliyarki sai na cinye miki
bak8鈥� 鈥� Saudat ta yi rau-rau da idanu tana kallon
inda ya cizar mata. Ya yi saurin rike hannun yana
fadar, 鈥淎yya
'am sorry dazafi ko?鈥�
Ba ta tanka masa ba ta zame hannayenta zata
wuceshi ya yi saurin. cimmata yana fadar, ' '
鈥淭uba nake 鈥榶an matana mu je ki karya kin ji鈥�.
Bai saurari abin da za ta ce ba ya riqo ta suka
nufi kicin, ya zaunar da ita a kan daya daga cikin
kujerun da suka zagaye Katon dinning table din
glass, ya cr鈥淶auna a nan yan matana, me za a
kawo miko?鈥�
Saudat ta dago tana kallonsa sai a lokacin ta
lura da shigar da ke jikinsa, baqin wando ne jeans
da Karamar T.Shirt sai apron da ya daura fara
tare da zungureriyar farar hula irin ta kuku,
Saudat ta yi murmushi ta ma rasa abin da za ta
ce masa.
Ya dan matso daf da' ita, 鈥淚na jinki Madam, me
za kici?鈥� 鈥�
Saudat ta dauke kanta tana fadar, 鈥淣i fa da ,
kaina nake son in girka鈥�.
, Shi ma ya kwaikwayi maganar tata ta hanyar
fadar, 鈥淭o ai ni ma tuni na hada miki wani special
girki wanda zai gargade miki kunnuwa鈥�
Dariya Saudat ta sa sosai, saboda salon da ya yi
maganar da shi, shi kuma ya dauki faranti da
serving spoon ya bubbude food flask din da ke
saman tebur din ya kalle ta, 鈥淢e za a. zuba wa
, Hajiyar , akWai soyayyar agada plantain, akwai
pizza akwai soyayyen kwai, akwai sandwich tare
da
Lol ga asma ga saude akwai rikicifa
[9:08AM, 07/02/2017] 馃檰馃徏鈥嶁檪@lh@ji馃檰馃徏鈥嶁檪: YAR. TALLA
CHAPTER 33
da soyayycn kifi gasassun kaji a side kuma
tafasasshen ruwan zafi ne me zan zubo wa
gimbiyar tawa?鈥�
鈥� Saudat ta yi murmushi tana kallonsa ya riqe
_ ludayin zuba abincin sai ka rantse wani
kwararren
. kuku nr ta lumshe idanunta ta bude lokaci guda
tare da fad'ar, 鈥淣i dai kunu nake son sha鈥�. . 鈥�
Dr.ya ware ido cikin firgici yana fadar, 鈥� 鈥溾€楰unu
kuma baby? Karfa kice min an karBi 'takardun
ajiya ta jiya har an yi min sing?鈥� 禄 . Saudat ta
zumburo baki tana fadar, 鈥淣i dai *wallahi bana
so鈥�. 鈥� Ya langwaBe kai yana鈥榢waikwayonta, 鈥淣i
dai wlh baba so鈥�. Dariya ta Kwace wa Saudat
harda kyalkyalawa, duk yadda ta ke Jin nauyin Dr
sai da
ya kangarar mata da idanu, har ba ta san lokaCin
da .
. ta saki jiki da shi ba a dolenta. Sun yi break
dinsu sosai don da ya lura ma 芦Saudat
tsattsakuran abincin take mikewa ya yi tsam
ya janya ta jikinsa ya zaunar da ita ya shiga ba
ta
鈥� abincin da kansa
Tun tana turjewa har ta gaji ta saki jikinta, saida
ya tabbatar ta qoshi sannan ya kyale ta ya ja "
hannunta suka mike suka nufi falo inda suka baje
.inda yaketa Koqarin ya ga ta saki jiki da shi 鈥�
Karfe biyar na yamma taga ya yi shirin; fita
zucayarta ta yi mata wani iri ta zuba masa idanu
ba tare da ta iya tankawa ba Dr yana lura da
yadda yanayinta ya sauya lolkaci guda, amma sai
ya mika mata hannu, 鈥淭aso mu je Madam in
zazzagaya dake kiga Bangarenki ki kuma gaisa
da ' ma,ai katanki鈥� ' Ba musu Saudat ta mika
masa hannun nata ya janyo ta suka fice daga
falon sai da suka ratsa 'faluka kusan hudu
sannan suka hau matattakalar .bene suka sauka
falon qasa; sannan suka koma falon da ya鈥� fi
kowane girma a cikin gidan, a cikinsa kuma ke
da Bangaren ma鈥檃ikatan har su'uku 鈥榶an mata
biyu dattijuwa guda, sai kicin wanda yakr ta
' ,waje, nan kuma akwai mutum biyu masu girki
kwararru mace da namiji. Sai da ya zagaya da ita
ta ko鈥檌na na Gangarenta wanda tsarinsa ya yi
matukar burge Saudat komai na ciki ya yi mata,
musamman wuraren shakatawa da wurin
hutawarta. Suna gama zagayen gidan ya ja ta
waje har inda harabar motocinsa suke da sunan
rakiya, ai ' suna isa wurin motarsa ta tubure sai
ya tafi da ita ' Dr ya riko hannunta yana fadar,
鈥淭saya kiji bafa dadewa zanyi ba, just minti
talatin na dawo su Momy kawai zan je in gaisar,
insha Allahu ba zan jimaba
Saudat ta kWantar da murya kafin tace 鈥淎llah ya
kiyaye鈥� hanya Dr ya dan zuba idanu kafin ya ce
Kinmin izini da gaske har cikin zuciyarki na tafi
karfa sai na dawo in fuskanci fushinki鈥� 鈥� ' Saudat
ta dan yi dariya tana fadar, 鈥淗aba ni na isa? Ai
sai鈥�
Bangazar da akai kai mata ce ta katse maganar
da take qokarin yi, ta yi taga-taga ta fada 鈥榑 kan
motar da ke gabanta, kanta ya bugi motar,
Saudat ta dafe goshi ta waigo tana ganin mai
,wannan aikin, ba ta yi mamakin ganin Asma ba
wadda ta sha gaban Dr; har jikinsu na gugar
juna.
Saudat ta ji wani irin abu ya dakar mata zuciya
tamkar saukar guduma, musamman yadda taga
ya kafe ta da fararen idanunsa ba ya k0 son
kiftawa, yana kallon yadda take magana cikin
kissa da gadara
鈥淶an yi magana da kai?鈥�
Ya mantar da tasa muryar kasan tata, 鈥淭o ga shi
kuma fita zan yi yanzu a yi haquri sai na 鈥� dawo鈥�.
, .
Ta watso masa wani fari mai kama da harara '
sannan ta juya a fusace ta nufi inda sabuwar 鈥�
motarta ta ke mai baqin gilashi 鈥渢a fada
mazaunin dircba tare da dagawa escort
Dinta hannu ; ta ja abinta a guje ta fice
DR Ahmad ya yi wani dan gajeran murmushl tare
da kallon inda Saudat take wadda . tsabar takaici
yasa ta wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta,
Dr. ya yi saurin janyo ta jikinsa yana fadar, "Am
sorry tawan baki dai ji ciwo ba ko?鈥�
r Saudat: ta watsa masa wani kallo mai cike da
tuhuma kafin tace 鈥淎u ban ji ciwo bama zakace
. bayan kana kallon abin da tayimin
, Ya ce, 鈥淭o me zan ce mata Saudat? Ta yi
tayine don ta Bata min rai, ke kuma ta sa ki
Bata kwalliyarki to da na nuna mata ban damu
ba ai ga shi ta tafi k0, kuma ke don ina tsaye sai
ki ce ba za
ki iya rama wa kanki fada ba sai dole nina rama
miki Ai sai kuma na zama marar adalci a
tsakaninku k0 ba kya so na zama adali ne?鈥�
Saudat ta zame jikinta cike da da haushi ta
Nufi hanyar bangarenta. *
Dr ya girgiza kai a zuciyarsa yana fadar, 鈥淢ata
ke nan鈥�
鈥榙aniel ya bude masa gidan baya na motarsa, ya
shiga sannan ya rufeshi kuma ya shiga gida
gaba mazaunin direba ya ja shi suka tafi
Waiwaye adon tafiya Inji Malam Bahaushe bari
mu waiwaya baya muji shin wane ne Dr
Ahmad Muktar? Profassor Mukhtar L Kabir
shahararren dan boko ne, kuma fan kasuwa da
sunansa ya kewaye
Najeriya, kuma muhimmi a cikin lamarin da yawa
na shidda a cikin masu kudin qasar nan. Bai taba
rike wani mukami na siyasa ba amma kuma yana
daga cikin masu fada a ji a harkar siyasa da
mulki don yana tare da manya-manyan 鈥榶an
siyasa tun daga na qasar nan har zuwa qasashcn
qetare. Ahmad shi dan dansa na farko, sai da
aka kwashe shekaru goma sannan aka yi masa
kanwa Farida
kuma daga su ba a sake haihuwa ba, tun tasowar
Ahmad mahaifinsa ya so ya yi karatun boko mai
zurfin gaske don haka yana kammala firamare ya
tura shi qasar America a can ya yi sakandire
dinsa ya hada doctoring degree dinsa a kan abin
da ya shafi harkar siyasa da mulki. Yana
kammalawa ya ce ya tsaya iya nan, duk da
mahaifinsa bai so ba a dole ya kyale shi
kasancewarsa na dan gaban goshi.
' Dr. Ahmad bai fara harkar siyasa ba sai da ' ya
hadu da Asma don ita ce ma ta cusa masa
ra鈥檃yin yin siyasar amma shi ya yi karatunsa ne
ba don yana ra鈥檃yin yin mulkin siyasar ba amma
saboda' ita shi ma ya tsunduma kan harkar
siyasar wanda a yanzu ta rage saura 鈥榶an
watanni su sauka kuma ya yi alkawarin yana
sauka ba zai sake komawa ba don bai ga abin da
yake nema ba da zai
dora wa kansa wahala ba, a matsayinsa na dan
majalissar dokoki ta tarayyar Abuja, amma fa inji
shi saboda a ganinsa mulki wahala ne, kuma
bala鈥橧 鈥� ba kadan ba ga wanda ya kasa tsaida
gaskiya da amana Wannan kenan .
K0 da Saudat ta koma sashinta kai tsaye
b茅droom dinta ta nufa ta fada kan gadonta ta
kwanta zuciyarta cike da haushin abin da
Daktanta ya yi mata, da taimakon sanyayyen
sanyin air conditioner wani nannauyan bacci ya
yi awon gaba da ita. *
Ba ita ta farka ba sai qarfe bakwai da rabi da
yan mintina ta yi saurin saukowa daga kan gadon
zuciyarta na mamakin yadda har ta bari ta yi
baccin yamma ga shi har magruba ta kubce
mata. Cikin gaggawa ta dauro alwala ta fito ta yi
sallar magriba da isha tare da shafa鈥橧 da wuturi
sannan ta tsaya gaban madubi daga tsaye ta yi
鈥榶ar kwaliyarta marar nauyi, sannan ta nufi gaban
wardrobe ta ciro kayanta ta saka English west
riga da siket. ~
Fara: shirt silk sai dogon siket dinta baki irin mai
fadin nan yana da adon fararen fulawowi ta
warware gashinta ta daureshi da farin ribbon
'Kwara guda sannan ta makala wa kunnenta鈥� yar:
鈥� Karamar barima ta gwal ta yi kyau sosai, ta
koma. tamkar irin yan matan turawan ta zira
silifas na fata, sannan ta fito falonta ta tsaya
gaban talabijin din da ke girke gaban bango tana
canza channels
.鈥滵r. Ahmad ya shigo da sallama Saudat ta amsa
ba tare da ta juya
* ta kalli inda; yakeba ya shigo cikin falon ya dire
katuWar lrdar dake hannunsa mai dauke da'
tambarin Alshukur shoppin mall ya fada kan
kujerada alamun gajiya a tace da shi ya mika wa
Saudat hannu, 鈥楥ome on my baby, wallahi I am
"鈥� very tired zo in ji duminki kusa da ni ko na
wartsake" . Saudat ta waigo ta dan kalle shi
kamar ta share shi sai dai girman da yake da shi
a cikin idanununta baza su barta ba, don haka ta
nufi inda yake ta zauna kujerar da ke nesa da
tasa tare da fadar, 鈥淪annu da zuwa鈥�
Dr ya tsare ta da narkakkun idanunsa wanda
ya tilastta wa Saudat kallon kafet ya koma ya
jingina bayansa da makarin kujerar tare da fadar
.鈥淶o ki duba ledojin nan ki ga abin da ke ciki鈥�.
. Saudat ta mike ta :nufi gefensa ta durkusa kan
kafet tare da janyo ledar daya ta shigo da ita, ta
bude kwalaye ne har guda biyu, manya sai dai
daya yafi daya girma ta dan dago tana kallonsa
yace
鈥淏ude mana Bare kwalayen鈥� .tayi Saudat ta
gyara zama sannan ta soma bue qaramin kwalin
sai ga razananniyar 鈥� waya
iphone6plux kwance a cikin kwalin ta ajiye a
gefe
ta bude babban kwalin sai ga wata Yar qaramar
abu mai kamar komfuta ta daago tana kallonsa
da niyyar ta . yi magana ya katse ta ta hanyar
saukowa dagakan '
鈥� kujerar ya zauna gefenta ya karbi yar abar ya
Kunna yace鈥淲annan da kike gani sunanta ipad
kamar camputer yake zaki iya shiga yanar gizo
da komai _ Ta ciki nasa an zuba miki abubuwa
da yawa a ciki Wanda zai bude miki Kwakwalwa,
kuma zai rage 'dinga debe Niki kewa idan har
bana nan tunda ldan kinga ni din ba mazauni
bane cikin watan man da wuya inyi kwana hudu
a gida, saboda abubuwan da ke kaina ;NASA
milki kudi a ciki nayi miki saitin komai a . yanzu
zan fara koya miki yadda ake amfani da ita,. : Sai
kuma wayar da nayi miki alqawari gata ' nan
akwai akwai sabon sim a ciki na hada Saka miki
kudi a ciki, akwai lambar Momyn Shukura a ciki
idan za id kira su鈥�. ' Ya zura hannu cikin aljihu
sai ga key din mota ya miqa mata, 鈥淲annan
kuma makullin鈥� . 鈥榤ota ne saboda ko watarana za
ki ji sha awar' 鈥� yin tuki da kanki, saboda zuwa
makarantar dana
sai miki form din shiga makarantar social .
development Abuja, karatune zakiyi nayan
watanni zaki zama basic illetrate wata hudu
zakiyi ki gama ki amshi certificate dinki sannan
ki tafi ki karanci
social welfare wata Tara , sai ki Kara karBar
certificate wanda shi zai ba ki damar ki tafi
jami鈥檃 ki hada difloma in kina da bukata ma har
digin鈥� dinki sai ki hada da fatan za ki maida
hankali don ke maki zama wani abu watarana鈥�.
Tsabar jin dadi da murna Saudat har ta rasa . ta
yadda zata iya furtawa wani Abu idonta ya ciko
da kwalla idan akwai abin da take q auna a
rayuwarta bai wuce karatu b a, ashe kuwa
Ubangiji zai cika mata burinta, tamkar za ta yi
kuka ta fara zayyano masa godiya. Ya daga mata
hannu, 鈥淵a ishe ni haka Saudat, ban miki don ki
gode min ba, Ubangiji za ki gode ma wa don Shi
ne Ya kwato miki, kuma idan kina sha鈥榓war shiga
islamiyya to ita ma ki shirya ranar asabar mai
zuwa in kai ki Da鈥檃wa akwai sashin matan aure
sai ki rinka zuwa ranar asabar da lahadi da safe
kawai, taso mu je in gwada miki motarki".
Ya riko hannunta ya mikar da ita ba tare da ya
sake bari ta fadi abin da ta ke son fada ba suka
nufi harabar waje
Ganin shirgegiyar motar da Saudat ta yi sabuwa
dal ba karamin daga mata hankali ya yi ba, don
ba irin motocin da ta saba gani bane a kan titi,
ta qara wa motar kallomai suna Expedition baka
mai bakin gilashi wadda ta mamaye wurin
tsayuwar motoci uku ta鈥� maida kallonta kan Dr.
tana fadar Ni yanzu ya za a yi ' in iya jan wannan
matar Yallabai? Tayi girma sai ai ta mamaye titi
gaba daya ' Dr, ya tuntsure da dariya yana fadar,
鈥淏akauya sai kawai Expedition ta mamaye titi,
saboda tsabar shirmenki? Muje ciki daga gobe
zan
.fara koya miki tukin k0 don na ci dariya"
Saudat ta bata fuska ba tare da ta yi magana ba,
ya ja ta suka nufl sashinta yana Kara zolayarta,
wurin koya mata ipad din ma sai da ya ci dariya
saboda qauyancinta don Saudat dai ko a waya ba
komai ta iya ba, to bare ta fahinci ipad cikin
sauki ' ta ida qulewa ne ta yi zuciya ta yi ciki
abinta, yana kiranta ta Ki kula shi don haka shi
ma ya tattara ya 鈥� biyo ta da tarkacenta .
Washegari tunda safe Dr. ya bar gidan saboda
meeting din da ke gare shi, don haka Saudat ta
sha baccinta sai wurin azahar sannan ta shirya
ta fito donta 鈥榢arya kai tsaye dinning saidata
wuce falo uku sannan ta isa don nan ne inda Dr
ya sanar da ita ' kuku zai rinka shirya abinci, ta
zauna ta karya , sannan ta koma falonta ta dauki
ipad ta soma latse
鈥� latse, sai da ta gaji ta rufe ta dauki waya ta
danna lambar Mammy wadda suka kWashe fiye
da mintina talatin '鈥� sannan ta kashe ta kira
Shukura, itama sun dade
suna hira kafin su yi sailama, tana mamakin k0
鈥渒atin nawa ne maigidan ya loda mata? ,Har
bayan sallar isha Dr bai shigo gidan ba, harta
fara tunanin k0 lafiya, hakan yasa ta sa鈥� waya ta
kira' shi, a daidai lokacin da yake shigowa gidan
ya ce , 鈥淪higowata kcenan Madam, na gaji sosai
ki sameni a Bangarena don Allah鈥�.
0 comments:
Post a Comment