_Bismillahirrah manirrahim_
*JAN HANKALI/HANNUNKA MAI SANDA...*
_Wannan labari k'irk'irarren labari ne, banyishi don wani/wata ba, nayishi ne don ilimintarwa, nishadantar ga dukkan mabiya littattafaina...kuma ban yarda wani ko wata su juya mun labari ba zuwa wata siga ba tareda izini na ba, yin hakan ba karamin laifi bane saboda haka a kiyaye._
*SADAUKARWA*
_Kacokam wannan labari sadaukarwa ne ga dukkan masoyan ANEESAH na fili da na boye, kai harma da makiyana na saudaukar dashi a gareku...lolx._
_Am back wit anoda mavilous, hot n short love story...bear wit urz ANEELURV_
1
Zama tayi cikin bata fuska ba tare da ta kalli inda yake ba...muje...abinda ya fito daga bakinta kenan.
Murmushin bakin ciki da takaici ya sakar mata tareda gada kansa, ya fizgi motan shima ba dan ya so hakan ba.
Afreef ya danna kida wakar brandy easy true yana tashi a hankali, amma rigimar da Amal takeyi masa ya hanashi ya saurari wakan cikin natsuwa.
Tsawa ya daka mata da keee!!!...na hadaki da Allah amal ki barni naji da abinda dady yayimun kinki ki rabu dani, wai danme kika rainani haka?, ko dan kinga ina bin umarnin mahaifina ba tareda gardama ba ko nuna masa bacin rai?
Ohon maka...ta murguda masa baki tayi shiru, kasan cewar duk rashin kunyanta matsoraciya ce sosai.
Da haka suka isa yayi parcking yana jira ta fita amma tayi zamanta a motan tareda harde hannayenta.
Harara ya galla mata..bazaki fita kije ba ko shima saina shigar dake ciki?
To wai yaya Areef duk ka bi ka tsaneni wai ni nace dole sai ka....kaf ya buge bakinta..abeg get out of ma car! Ya fada in a serious tone.
Da sauri ta bude murfin motan ta fice tana kukan shagwaba har ta shige cikin gidan.
Dogon tsoki ya jaa tareda kwantar da kansa kan stiry yana maida wani huci mai zafin gaske, jin yanda yakejin yarinyar a ransa amma sam an bi an dagula masa lissafi ta fita a ransa cikin kan kanin lokaci.....
*** *** *** *** ***
Gidane kaya taccen gaske wanda ya kunshi zuria biyu a cikinsa, wato zuri'ar Alh Yusuf 'Doguru, kyakkyawan dattijon dayayi kaurin suna a nahiyar africa baki daya, yanada mata daya wato hajiya Rakiya da yaransu guda biyu, Abdul'ahad da Abdallah sune kadai Allah ya azurtasu da su, inda sukayi karatun arabi da boko cikin kulawa mai tarin yawa ga mahaifannasu, har suka girma suka mallaki hankalin kansu har suka mallaki iyalan kamsu.
_ABDUL'AHAD YUSUF 'DOGURU(AYUD1)_
Babban d'a ga Alh Yusuf Doguru, kyakkawan gaske ne dogo fari sal dan shekara 41, wanda yayi karatunsa a kasar germany inda ya karanta Electircal engineering yanzu haka yana da campany kansa a jihar katsina, yanada mata daya mai suna Maryam, Allah ya azurtasu da yara hudu, Areefullah, Arfat, Ayman, Adnan....
_ABDALLAH YUSUF 'DOGURU(AYUD2)_
'Da ne na biyu kuma auta a wajen Alh yusuf, kyakkyawa ne shima daidai gwargwado ya biyo mahaifiyarsu hajiya Rakiya, bashida hayaniya ko kadan kasa daya sukayi karatunsu shida dan uwansa Abdul'ahad, saidai shi lowyer ne, yana da shekara 39 a duniya, matarsa daya maimunatu, haka Allah ya azurtasu da yara uku, Amal, Affan, Afraz...
Rayuwa ce mai tsantsar dadi da nuna kulawar juna a tsakanin zuri'ar, kasan cewar Alh Yusuf 'Doguru tuni ya amsa kiransa wajen mahaliccinsa, sai mahaifiyarsu ta rage wato hajiya Rakiya, wacce yar asalin kasar sudan ce, mace mai halin dattako da nuna so ga dukka al ummar ba, batada kalmar da wuce ta furta a kowane irin lokaci irin 'Da na kowa ne..., hakan yasa take jin surukkanta tamkar ita ta haifesu.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
2
Hakan yasa basuda wani buri irin suga sun hada kan zuri'arsu waje daya.
Areef da Amal sun tashi ne a wajen kakarsu hajiya Rakiya, kasan cewar babu kowa kusa da ita.
Sangarta sakata jin dadi babu irin wanda basa gani wajen hajiya mama, saidai hakan yana konawa dadynsu Abdul'ahad rai dan baya so, a kullum yana nunawa mama cewar bai dace ba ana yi masu haka duk da cewar basune yara kana na awajen su ba akwai arfat ga ayman da affana.
To miye naka aciki nidai banida buri dabya wuce ma inga ranar auren yaran nan.
Hummmm...yaja dogon numfashi to shikenan mama ni zan wuce office dama na biyu mugaisa inji idan babu wata matsala.
Babu kam, saidai inaso a bawa areef mota saboda sudinga tafiya makaranta da amal wadansu lokuttan suna makara dan basu cika samun adaidaita anan layin ba sai sun taka da kafafunsu.
To zamuyi shawara da Abdallah, ya mike...ni sai nadawo, ya fice fuskansa ba yabo ba fallasa.
*** *** *** *** ***
Yaya Areef yau fa akwai gist..ta nufo kusa dashi ta sunkuya zata masa rada yayi saurin dakatar da ita, kasancewar bai cika son wasa da ita ba wai kar raini ya shiga tsakaninsu.
Miye ina jinki cikin hantara...
Hmmm...babu komai ta juya guiwa a sanyayaye...tana yi masa wani irin kallo
Kallonta yake shima nan take tausayinta ya kamashi kuma sai yaji bai kyauta ba sam yanda yayi mata.
Zo mana yar kanwata kin fasa bani gist dinne?, ya fada cikin dabarbarcewa.
Kai ta kada masa alamu a'a barshi kawai ta shige dakinta ta fada a gado tafara matsar kwalla tareda yan sake sake...wani meyasa yaya Areef yake mun haka ne?, meyasa baya son jana ajikinsa a matsayina na kanwarshi?, tambayoyin da tacigaba da nanatawa kenan a zuciyarta wanda takasa gano amsoshinsu.
Dakin ya bita yayi tsaye yana kallonta, wanda batasan ma ya shigo ba, cikin muryar tausayi ya ce Amal...Amal...kizo hajiya mama tana kiranki.
Kallonsa ma batayi ba balle tasan yana wajen.
_AREEFULLAH AYUD1_
Shine sunan da aka fi sanin dan matashin saurayin mai jini ajika da shi, kyakkyawan matashi son kowa kin wanda yarasa wanda bai wuce shekaru 23 a duniya ba, idanunsa kadai zaka kalla kasan cewa guy din dan soyayya ne, miskiline na gidan gaba, saidai kuma yanada hakuri sosai hakan yasa mahaifiyarsa take ji dashi sosai, yana karatu a KATSINA ISLAMIC UNIVERSITY(AL-QALAM), inda a yanzu yana shekarsa ta karshe a fagen karatunsa, kasancewar yarone mai hazaka da maida hankali ga karatunsa.
_AMAL ABDALLAH AYUD2_
Yar kyakkyawa kuma matashiyar yarinya moderate chocolate colour yar kimanin shekara 20 a duniya, Amal yarinya ce mai natsuwa da hakuri, wacce take bama soyayya a hakkinta a duk inda ta bayyana, tanada hakuri daidai gwargwado kuma tanason danginta, tana karatu a KATSINA ISLAMIC UNIVERSITY(AL-QALAM) in da take a 300L, komai kusan tare sukeyi da yayanta Areef, hakan yasa take jinsa a ranta fiye da sauran yan uwansu.
Hajiya mama uwace da idan ta kafa doka acikin zuriarta bbu wanda ya isa ya karya ta, wannan yasa su Abdul'ahad suke tsoron kiran conference meeting idan ta bukaci hakan
To yau ma ta bukaci hakan kuma tamkar akwai wata akasa ko mene ne?
Fira suke da yan jikokin nata sunata raha...
Areef wai ba wani motsi ne?, hajiya mama ta tambayeshi cikin zolaya.
Dariya Amal tayi tace..ah touh hajiya mama tayani gani yayan namu yafara tsufa dai...ta masa gwalo a boye.
Nan take yayi burning face...hajiya mama kin ganta ko?, ni wlh yarinyar nan ta rainani wlh.
Bawani raini kabani ansar abinda na tabayeka mana.
Keyarsa ya sosa yace wit tym grany zakiji.
To shikenan zan kira iyayenka anjima zansa meeting kanka.
Ido ya zaro yace haba ma grany karmuyi haka dake zan fada maki kome kenan anjima.
Da haka dai suka kammala firarsu Amal bata sake cewa komai ba saboda tsoro...lolx
Ki biyoni a hankali pl coz am sick, am just managing saboda beloved fans nawa, herat yhu all💕
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
3
Kwance take a dakinta babu abinda takeyi sai yan juye juye, tunani ne yake ratsa mata brain, dadynta yasa ta agaba sai ta fitar da mijin aure...ni muhibba ina zan saka raina ni banida saurayi kuma ban san ina zan same shi ba, ta fa da aranta..damn!!! Gabanta ya fadi, don ta tuna da tsohuwar kawarta da ta manta da ita tasan bazata kasa bata shawara ba.
Wayarta ta lalubo kasan pilo ta danna tareda scrolling contact nata, kai tsaye tayi dialing number sunan Friendy(Amerhl) ya bayyana a saman screen din wayarta...nan take kuwa bugu daya zuwa biyu sai ya shiga...huh...ta hura iska mai zafi daga bakinta.
Dauka tayi tareda kanga wayan a kunnenta..hlo
Hi kawata..
Dayan ban garen tace pls huz on d line..dajin fuskanta a daure yake, dan bataga dalilin da zaisa muhibbah tasake nemanta ba bayan abinda ya hadasu abaya.
Hmmm...Amerhl kar dai kice bakida no na kuma u cant even recognise ma voice?..ta fada guiwa a sanyaya.
Bani da shi ban gane mai mgn ba, idan bazaki fadan ba lets hang off pls.
Uhm...sunana MUHIBBAT S. SAULAWA, ina fatan kin ganeni kuma zaki yafemun abinda namiki pls.
Ohhh ur wlcm, Amal tafada arainace.
Pls kawata kina gida ne i wanna talk to u pls..
Bana gida pls..
Kawai ta kashe wayan ta tareda jan dogon tsoki.
Hmmm muhibba kin raina kanki dayawa tukuna ba, AMAL AYUD tafiki iskanci, ta cije lebenta tareda maida earpiece dake kunnenta tana jin kira'ar shureim.
*** *** *** *** ***
Yau ma kamar kullum suka hadu don zuwa gaisheda mahaifiyar taso, saidai su Afraz, Ayman, Affan da Adnan sun ki zama gida sai anje dasu.
Haka kuwa Maryam tace lallai bazai bar mata kayan rashin ji ba, kasancewar yau friday ranar baki ce a gidan, yaki ya amince kuwa, dole ta fara kwantar da kai tana... Alh kayi hakuri ka kaisu suje mika gaisuwa suma, to ya na iya muje.
Arfat da fito da gudunta kalabar kanta tana tsalle a wuyanta dady...dadyyyy..dan Allah zanje ina Alh Abdul'ahad har ya fidda kan motarsa daga gidan...haka ta koma tana rusa kuka saboda taso ganin aunty Amal akwai labarin da takeson bata.
Yi hakri mana ke ba babba bace?, kibari zansa idi driver yakai zuwa anjima...thank yhu momy tareda kissing fore head na mahaifiyar tata tana murmushi tashige dakinta.
Sallama sukayi baki dayansu tareda yan tsalle tsalle irin na yara, oyoyo Aunty babba, sukayo kanta baki dayansu, sunan da kannen nata suke kiranta da shi kenan, ta makalesu suna dariya sai Adnan yanemi yin kuka...
Aahh...lilin aunty dont cry jor zi na maka shan gulu ta kama hannunsa zaiyi bori a kasa ta cafeshi sama, sanna duk su dadynsu da Abbah suna gefe suna dariya kallon drama...
Juyowa tayi tace aw.. Tareda dafe bakinta, dady ur wlcm ina yininku..cikin jin kunya.
A'a ba komai auntyn yara kina lafiya,
Lafiya kalau Abbah
Sai a lokacin hajiya mama tafito tasha ado da daurinta irin nasu na tsaffi sai badada kanshi takeyi, ga kunshi ansa yar kafar tayi jawur kasancewar tsohuwar fara ce tas ga tsafta da iya daukar wanka.
Manyan mutane sannunku da zuwa, sunan da take kiransu a jimlace kenan idan yan wasan nata suna bisa kai.
Yauwa mama barka da fitowa.
Anan suka fara gabatar da gaisuwa da neman albarka ga dattijuwar mahaifiyar tasu.
Amal kuwa tuni ta shige daki da iyalan rigimar nata.
Yau ma kama kamar kullum muhibbah bata daddara ba ta sake kiran Amal saidai tahadu da rashin sa'a wayoyinta kaf a kashe suke, ta kira yafi a kirga amma baya shiga.. Dogon numfashi taja tace ni muhibbah nayiwa kawata laifi ya Allah kasa ta hakura, Amal nasan ba halinki bane wulakanta wani dan adam, laifinane da nakaiki makura, Amal ki ya femani ki saurari abinda zanzo maki dashi.
Abu kamar wasa saiga hawaye suna kwarara a kumatun muhibbah.
_MUHIBBAT S. SAULAWA_
Matashiyar yarinya yar kimanin shekara 21 a duniya, yar asalin garin gombe, kuma kawace ga Amal Ayud1, wanda babu wanda baisansu tare ba har yakaiga zumunci ya kullu a tsakanin iyayensu, muhibbat mahaifiyarta Allah ya mata rasuwa, sai mahaifinta yarage mata kuma ita kadai Allah ya azurta su da ita, tana da kyau daidai gwargwado, kuma ga halayyar kirki, saidai farat daya kawaye suka juya mata tunaninta, hakan yasa suka fara samun sabani da aminiyarta Amal wacce suka fi kiranta da sunan mahaifinta wato AYUD1.
Shin kowane irin abune ya hadasu haka take neman yafiyarta?
Saiku biyoni...
Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
4
Tsaye take bakin hanya tana neman dan adaidaita sahun da zai mikata gidansu Amal, amma bata samu ba, sai ta yanke shawarar ta sake kiranta don jin yaya ta yafe mata ko haryanzu tana kan bakarta gudun kar taje gidansu taci mutuncinta dan Amal akwai masifa.
Bakin kwalbati taja tunga tareda zama ta fiddo wayanta ajaka, sunan dai yana nan bata canja shi ba friendy Amerhl shine ya bayana kan screen din wayar, bugu daya kuwa tashiga.
Ana kiranki ko ba a daukan waya agabana sistoh...abinda Areef ya fada kenan, kasancewar suna bisa hanyarsu ta zuwa yiwa Arfat registration na umyuk da tasamu.
Murmushi tayi tace...yaya kenan wane waya ne bazan dauka a gabanka ba ai inajin sai ta Mr Right dina...ta kara sa maganar tana kallon idanunsa don ganin wane reaction zai bayar.
Nan take kuwa ya daure fuska yace okey..a takaice.
Wayar bata daina ringing ba haka ta dauka dan kar yayanta yayi tunanin maganarta gaskiya ne.
A kunne ta kanga tare da yin sallama.
Wa alaikissalam daya ban garen muhibbat ta amsa Damn!...gabanta yake faduwa dan taji Amal acikin sanyin murya.
Friendy ina jinki lafiya dai kuwa?.Abinda Amal tace kenan.
Dadi ya rufe muhibbat cikin zakuwa tace haba friendy inata kiranki baki picking ba inaso inzo na kawo maki ziyara na gaisheda hajiya mama.
Lolx...nikuwa bana gida yanzu ina hanya zamuje yiwa lili reg, sunan da take kiran Arfat dashi kenan kasancewar su biyu ne yan mata acikin zuriar biyu.
Oryt to ba damuwa bara na koma gida anjima zan shigo.
No problem muhibbat, thank yhu.
Sukayi hanging call din.
Wata harara ya watsa mata nan take jikinta yayi sanyi ta fara magana adabarbarce.
Yaya Areef watz wrong?
Bai kalleta ba.
Am talking to yhu yaya me yafaru ne?
Abeg Amal babu fa.
Shikuwa zuciyanshi ya fara raya mashi Amal kuwa tana da saurayi da har take kira Mr Right?
Tambayar da yayiwa kansa kuma bai samu amsarta ba.
Da haka har suka isa sch din.
*** *** *** *** ***
Taruwa sukayi baki dayansu a babban falon gidan Hajiya Rakiya, kamar yanda marigayi Alh Yusuf 'Doguru yakeyi duk lokacin da dama tasami don guda narda comfrence meeting, yau ma haka hajiya mama ta bukaci hakan.
Maimunatau da maryam wato mataye waje Alh Abdallah Da Alh Abdul'ahad suna zaune daga kasan kujera gefen hajiya mama kawunansu sunkuye a kasa dan suna matukar girmama dattijuwar, hakan yasa akullum suke kara shiga ranta takejin tamkar itace mahaifiyarsu ta a sali.
Arfat da Amal kuwa suna gefe suma, babu abinda Amal takeyi sai chat abinda yake konawa Areef rai kenan idan ta rungumi waya bataji bata gani.
Sauran yara Afraz, Ayman, Affan suna kan three sitter zaune suna game, sai auta adnan yana kan cinyar dadynsa.
Bayan sallama da gudanar da adduoi ga marigayi shugaban wannan zuria ba ki daya, taro ya fara kamar haka.
To amatsayina na mahaifiyarku Abdallah da Abdul'ahad na nemi wannan taro ne akan mutum biyu...
Damn!..gaban Areef ya fadi tareda dago kai ya kalli hajiya mama yana kada mata kai.
Dariya taso kufcewa dattijuwar ta maida ita tacigaba da cewa...ya kamata Areef da Amal ace a wannan lokacin sun fidda abokan rayuwarsu to amma na tambayesu baki dayansu babu wanda yabani wata amsa da zan gamsu da ita shiyasa nakeso ku mazaje kusa baki.
Tabbas mama nima inason yin wannan maganar tuni, Abinda Abdul'ahad yace kenan...ni a shawarata idan basu fitar ba inada shaawar a hadasu aure kawai don kara dankon zumunci a tsakaninmu kinga sai zuriarmu ta kara habaka.
Kwarai yaya AYUD1, ni iyakar shawarata kenan ma ahadasu din kawai zaifi.
Amal batasan wai nar da ake toyawa ba dan hankalinta baya gunsu, shikuwa Areef yaji dadin wannan taro saida kuma kash.. Amal ta karya masa guiwa da take maganar Mr Right dan dama shi tuni yake jinta aransa.
Hajiya mama tace to kai Areef kaine babba saikaje ta tuntubi Amak yanda kukayi saika sanar dani.
Baice komai ba dai, haka suka kulle taron da addua kowa ya watse sannan amal ta farga da antashi an barta cikin mamaki.
Huh....watz going on dere?
Hajiya mamaaaa......ta kwala mata kira cikin razana.
Areef ya fito daga dakinsa a razane yana mata kallon kin raina mutane ma.
Yaya ina su dady?
Kin dawo hayacinki kenan...ya watsa mata harara ya koma inda yafito.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
5
Guiwa a sanyaya ta koma dakinta.
Tana tambayar kanta wai meke damunta har ayi meeting a gama batasan an watse ba?
Uhm...ai shikenan kome kenan nayi wa hajiya mama dabara don ta sanar dani...ta fada tareda daga kafadunta.
Bacci ya gagaresa babu abinda yakeyi sai safa da marwa a tsakiyar dakin nasa...inason Amal kwarai da gaske, to amma anya batada wani saurayin boye da bamu san dashi ba?, but i wil find out saina yi yanda zan shiga zuciyar Amal, zan daina mata fada zan dinga janyota a jiki na don musaba miye da da...ya fada kan gadonsa tareda runtse idanunsa.
Dunuyar tunanin shiga sabuwar rayuwa ya fada shida Amal dinsa yashige har barcci yayi awon gaba da shi.
*** *** *** *** ***
Kan diny suke suna break fast, jikinta ya bata idonsa a kanta yake, tayi saurin dagowa sukayi four eyes sai ta maida kanta kasa taji kunyarsa ta kamata...
Dariya Hajiya mama tayi tace...toni bari zan shiga ciki Amal ki mikomun nawa break fast din a daki zanyi.
Meyasa hajiya mama?..tayi saurin tambayarta.
Tunda dai nace haka ayi mun yanda nakeso.
Kiyi maza ki mata karta hau mana bori kinsan asalinta yar bori ce...Areef ya fada tareda tuntsurewa da dariya.
Haka sukayi dariya baki dayansu tashige tareda bin bayanta da kayan karya kumallon a hannunta.
Kafin ta dawo Areef ya dawo kusada kujerar Amal ya zauna tareda daddafe kansa tamkar mai ciwon kai.
A'ah...yaya meke faruwa ne?
Ya dago kansa idanunsa sun fara kadawa alamar damuwa ta bayyana karara a fuskarsa...babu komai Amal
To yaya naga kadawo nan kuma ka dafe kanka pls meye ne tell me...ta zauna kan tata kujerar ta maida kaf hankalinta akansa.
Mamakin yanda ta damu da jin damuwarsa ya kamashi, Amal kinason jin komiye?
Yes offcourse Big bro..but muyi break fast first kaji yunwa nakeji.
Ni na koshi damuwana itace yunwana, warwarewarta itace break fast dina.
Huh...to nima na ajiye am all ears dear...takarkade kunnunwanta...tana murmushi.
Toh...Amal jiya anyi meeting akan nida ke, su dady sunce suna son hadamu aure, ni kuma naga kamar kina da wan.....ta dakatar da shi tace.
Haba yaya shine damuwarka?, dama ai muna son junanmu ko?
Ido ya sa mata yanda take ta zayyana bayanai babu ji babu gani kamar dama jira takeyi..
Hakane Amal, amma ai nasan bazaki rasa wanda kikeso bako?
Yaya babu wanda nakeso kaine Mr Right adin ai.
Are yhu serious?
Yes ma'am kawai abinda nakeso dakai nasanka da yan matan tsiya nikuma banida hakuri kasani.
Haba babe dont say dat da wuri haka mana.
To shikenan yanzu damuwa ta tafi ko?
Lets eat somthing sai muje mushirya ina da lecture by 12:00pm yau kuma kawata zatazo muhibbat.
Okey...ya watsa mata wani irin kallon da batayi tunanin yayanta yasan logon ba..
Huuummmmm....ta maida dogon numfashi tace...lallai!!!
*** *** *** *** ***
Alhaji inada magana pls...
To gashi har na shirya zan fita ake kokarin tsaidani kuma maimunatu?
A'a ba wani dogon magana bane dama akan meeting na jiya da akayi gidan mama.
To akwai matsala ne?
A'a dama ina ganin da anbar Amal ta fidda wanda takeso ina ganin kamar hakan zaifi, saboda wlh Alh ina gudun auren zumunci balle wanda aka hada basu suka hada kansu ba.
Kallon mamaki ya maida mata yace toooo tanan kika bullo kuma?
To kibari inna dawo zamuyi magana kinji ko a matsayinki na mahaifiyarta, amma kisawa ranki aikin gama ya gama tunda abinda yayanda AYUD1 yake ra'ayi kenan nima haka kuma mahaifiyarmu ma haka...yasakai ya ficewarsa.
Hmmmm...zaka dawo kasameni, ni ban yarda da wannan hadin ba, bazaiyi ace kullum kune da shawara ba mu iyayen yaran bazaku bamu hakkin mu ba...tashige daki ranta a bace.
0 comments:
Post a Comment