Kwance take a daki banda murgine murgine babu abinda takeyi, kasancewar fadawa kogin da babu hanyar billewa da tayi.
Soyayyar Areef ta yi mata katutu a cikin zuciyarta, wannan shi ake kira son maso wani, ka koshi ga kwanan yunwa.
Wayarta ta dauko ta dannan contact na Amal kai tsaye ya shiga bugu daya kuwa ta ci sa a tayi picking...
Hlo kawata kin isa gida lfy?
Hmmm.. Lafiya kalau, saida nakira sannan zaki tambayeni?
Laaa dan Allah kiyi hakuri wlh kina fita yaya Areef ya dawo ya tafi da dukkan hankalina saida na tabbatar da na gama yi masa komai sannan hankalina ya dawo mun am really srry dear.
Hmmn...Ta saki murmushn takaici wanda ya so ya bayyana a fuskarta kasancewar ba haka taso ba, dan ta so ace ta hadu da wannan yaya Areef don ta tantance ko shine zuciyarta tayi kamun da babu kifi aciki.
Yadai kinyi shiru S. Saulawa?..Amal ta fada cikin mamaki.
Duk a lokacin Areef yayiwa Amal kurui dan ya kasa gane inda wayar ta dosa.
Kawai hanging tayi don muhibbat takasa cewa komai...lallai kam.
Abinda ya fita a bakin Amal kenan.
Me yafaru ne babe?
Nothing much durlin kawai muhibbat ce tazo dazu take neman diverting wa kanta masifa.
Tooo...ko ita ce ta shigo dazu tym na fita ana jirana ina sauri.
Damn!..kaine take magana kun hadu kenan tana tambayarka ina gida kuwa? Ta tambayeshi a cikin razana!
Eh nine baby akwai damuwa ne?
Huh...babu!..ta daure fuska, anan take kishinta ya bayyana kansa a fili.
Pls babe karki barni a duhu mana ki fada mun watz going on?
Babu fa pls!
Hmmmmmm!..numfashi ya sauke mai zafi dan kansa har ya fara juyawa, kasancewar zubi da tsarin yarinyar da ya hadu da ita ya tabbatar dan ta haddasa makirci a tsakanin ma aurata ma abune kan kane a wajenta dan da ganinta shu'umar yarinyace...ya fada a ransa tareda dafe kansa.
Amal mikewa tayi ta shige dakinta tasa key.
Kuka tashiga rerawa dan tana ganin muhibbat zata zame mata masifa arayuwarta, meyasa muhibbat ta dawo cikin rayuwarta a lokacin da tasamu damar kulawa da nuna tsantsar kauna wa yayanta Areef?...haka taci gaba da kuka har bacci yayi awon gaba da ita.
Haka ya mike ya koma bangarensa, inda ya rasa me mashi dadi, kasancewar baya son inda zai samu wata yar tangarda a tsakaninsa da Amal dinsa, wayarsa ya lalubo ya kira ya kira amma taki picking, he just decided to text her, haka ya fara tura mata zafafan messages masu ratsa zuciya da tausayawa wanda ya rubutasu.
Duk a wannan lokacin bata san me akeyi ba don tayi nisa cikin barcinta.
*** *** *** *** ***
Fira sukeyi tsakanin yaya da kani wato AYUD1 da AYUD2 a kofar gidan mahaifinnasu wato marigayi Alh Yusuf 'Doguru har magrib suna tattaunawa dan gane da wasu 'yan matsaltsalu dake kokarin tasowa a tsakanin gidajen nasu guda biyu.
Yaya ina ganin kar muyi saurin fadawa mama wannan matsalar da kasan halin mata yanzu sai ta kawo mana cikas akan hadin auren yaran nan da muke kokarin yi.
No bazata kawo ba, ai ita tabada umarnin akan a yi hadin auren don kara donkon zumunci a tsakanin mu, so ina ganin mu fada matan shi zaifi ko ya kagani?
To babu damuwa muje muyi sallah in yaso sai mu shiga cikin gidan.
Suka mike baki dayanzu don dauro alwala su gabatar da sallar magrib.
Ko wace matsala ce suke magana akai?
Toh sai ku biyu dan guntun alkalamin tsohuwar marubuciyar...lolx
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
12
Sun idar da Sallah a masallacin kofar gidan nasu, kai tsaye cikin gidan suka isa tare da sallama.
Hajiya mama da ke kishingide tana shan fruits, yayinda Amal ke gefenta tana bata labari akan rayuwarsu ta yarinta ita da Areef.
Wa alaikussalam Hajiya mama ta amsa tareda tashi zaune.
Daddy, Abbah sannunku da zuwa, Inayini.
A'ah Amal yauwa, lafiya klau Abdul'ahad ya amsata cike da kulawa.
Mikewa tayi zata fice tabar falon Dadyn nata ya dakatar da ita, no dawo ki zauna.
To yaya akayi ne saraki?...hajiya mama ta tambaya.
A'a mama ba wani abu bane kawai munzo ne game da maganar su shiyasa.
Ohh yanzu naji magana, dama ina so in kiraku inji baku zo kunji wane mataki suke ciki ba.
Amal kanta sunkuye a kasa tanata murza yan yatsun kafarta.
Amal...Abdul'ahad ya kira sunanta.
Na'am Abbah...ta amsa ba tare da ta dago kai ta kalleshi ba.
Jeki kira Areef kuzo nan.
Damn...gabanta ya fadi dan tasan ita fushi takeyi da yayan nata.
To Abbah...ta mike jiki ba kwari.
Daf da kofar dakinsa ta isa inda tayi nocking sau daya amma bai bude, sai ma ya koma ya kwanta a rigingine yana kallon sama.
Nocking ta sakeyi..yace waye ne?
Ni ce...ta amsa kasa kasa.
Kasancewar tunaninta ya kwana yanayi bai san lokacin da yayi zumbur ya mike ba zuwa bakin kofan dan yajiwo zazzakar muryar da yawa kwana yana begenta...bude wa yayi ya ganta ya tsaye tana kallon kasa.
Amal....ya kira sunanta cikin san yayyar murya tareda tausayi.
Dago kanta tayi ta kalleshi.. Huh...haka ka rame cikin kwana daya?
Kurui sukayiwa juna kasancewar kasa gani bakin zaren.
Amal miye matsalan wai dan Allah?..ya tambayeta cikin sarkakkiyar murya.
Babu...shine abinda kawai ta iya fada masa...kazo su dady suna kiranka.
Huh...dady???
Meyafaru ne Amal?
Dont knw, ance na kiraka muzo tare.
Anan take jikinsa yasake yin sanyi...yace Amal karki yarda arabamu, wlh ina sonki i duly loves yhu beloyond expectations pls.
Juyawa tayi zata tafi ya sake dakatar da da ita.
Hope kinji abinda na fada maki?
Kai kawai ta iya daga masa alamar Eh ta wuce.
*** *** *** *** ***
Hajiya mama, Ayud1, Ayud2, Areef da kuma Amal sun hallar a cikin main falon nasu inda suka saba haduwa don comfrence meeting, inda Hajiya mama tayi sallama tareda yiwa iyalan nata kyakkyawan fatan alkhairi kamar yanda ta saba akowane lokaci, sannan taba yarannata damar gabatar da abinda suke tafe dashi.
Inda Abdul'ahad yafara da cewa...to mama abinda muke tafe dashi shine, na farko mahaifiyar Areef itace ta takura akan ita lallai bata amince da hadin auren zumunci ba a tsakanin Areef da Amal, sannan tana nuna cewa lallai sai an bata hakkinta amatsayinta na uwa agareshi, so abinne ya isheni duk da kuwa na tsaya tsayin daka akan bata isa ta dakatar da hukuncin da mahaifiyata ta yanke ba.
Damn...damn gaban Areef ya fadi dana Amal inda sukayi saurin kallon junansu, Areef yaso ya bude baki yace wani abu zuciyarsa tayi saurin dakatar dashi.
Wannan haka yake mama, to amma munzo mu tabbatar da shin Areef da Amal sun amincewa junansu na zama ma aurata ko kuwa?, idan hakan bai samu ba gudun samun matsala zamu ba kowannensu damar fitar da wanda suke so su aura...abinda Abdallah ya fada kenan mahaifin Amal.
Sam wannan maganar da kukeyi shirmece, wannan auren idan har kunga baiyiwu ba to babu raina ko kuma Allah bai amince ba, amma lallai sati mai zuwa inaso kuzo a fidda ranar aurensu saboda yara sun riga sun amincewa junansu kuma suna kaunar junansu.. Hajiya mama ranta ya soma baci sannan tacigaba da cewa...na tabbatar idan kukayi kokarin raba yaran nan yanzu zaku cutar da su da rayuwarsu..
Ta maida kallonta ga Areef da Amal wanda kallon juna sukeyi babu ko kyafta idanunsu...ta nunawa iyayennasu su tace ku kalla kuma ku duba kuga ramewa da sukayi kuma duk magana daya ce ta shiga sabuwar rayuwa irin ta masoya wacce basu saba ba.
Baki dayan su AYUD suka maida kallonsu ga yaran nasu, inda har a wannan lokacin su Areef ba su san me ake ciki ba.
Abdallah yace Areef....!
A razane suka firgita tare da sunkuyar da kawunansu kasa bayan sakwanni da suka gama isar wa junansu.
Kunya ce ta kama su sosai.
Hajiya mama tace ina fata kungani da idonku, to tabbas maimuna bata isa ta raba wannan hadin ba kaje ka fada mata wannan injini.
To mama insha Allahu babu matsala, mu zamu koma kome kenan zamuyi waya.
To madallah.
Suka wuce
Dady ku gaida gida abinda Afreef ya iya cewa kenan.
Kusada hajiya mama suka koma suka zauna banda kissing nata babu abinda sukeyi suna dariya.
Hajiya mama wlh muna sonki Allahu yabar mana ke.
Duk da dattijuwar matar bata damu da wasa da jika ba amma su Amal sun koya mata dole, dariya sukeyi sosai tamkar babu wata damuwa a tare dasu ganin kamar sun kashe boss, wanda ba anan gizo ke sakarsa ba don Amal ta manta muhibbat nacen tana nata zagon kasan.
Muje zuwa...
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
13
Sallama kakeji tundaga bakin get tamkar sabuwar zuwa a cikin gidan, ko miye dalilinta na yin hakan oho.
Karasawa tayi dafda bakin main falo har a wannan lokacin doguwar sallamar takeyi..inda Areef yake zaune shi kadai a falon ya amsa da wa alaikissalam waye ne?
Alhamdulillah!..ya fito bakinta tareda dafe kirjinta, kai tsaye ta kutsa cikin ido hudu sukayi da kyakkyawan matashin saurayin da yayi mata katutu cikin zuciyarta ya hanata sukuni tun haduwarsu ta farko, sauri takesonyi ko yanka tamkar an manna mata magnet tsakaninta dashi tayi saurin karasa kusa dashi tareda durkusawa daf dashi, sannu dai..shine abinda ya fito bakinshi cikin mamaki yana binta da kallo.
Yauwa sannu ta fada cikin sigar rausaya da kwarkwasa...pls Amal fa?
Ya nade kafafunsa saman kujera yace tana kitchen kijirata..ya mafada tareda daure fuska.
Okey...ammm pls ko kaine yaya Areef dinmu ne?
No am nt d one..ya mike ya nufi haryan kitchen din.
Baki ta rike tace...lallai inada sauran aiki anan kenan...tabdijan!
Cikin kitchen din ya same ta inda take ta yin hidimar dafa masu indomie, kasancewar hajiya mama tayi tafiya.
Har kaso kabani tsoro wlh.. Mene kake ta fushi haka ko yunwar ce ta soma wahalarmun da babyna?
Hmmm..ya harde hannayensa yana mata wani irin kallo.
Yaya watz wrong?
Kinyi bakuwa...ya fada fuska a daure.
What?! Bakuwa kuma?, aini banida wacce takirani da sunan zatazo wajena.
To kije kigani...ni zan wuce dakina idan kin kammala pls let me knw.
Olryt, but tell me me ya tabamun mr right dina?
Babu komai...yasa kai ya fice.
Bayansa ta biyo inda ta yaradda Muhibbat ta cire mayafinta tasha kananan kaya sun kame jikinta sosai ta maida kallonta ga album dake gefen sitter da take akai.
Fuuuuu.. Areef ya wuce ta inda takema bai kalla ba.
Amal mamaki ya kamata...muhibbat??!..yau kuma zuwa babu sanarwa?
Kawata...kinganni kamar daga sama halan?
Wlh anguwar nazo nace bara nayi suprising naki, ko ban kyauta ba?
Uhmnn.. Ba yabo ba fallasa ta amsa da eh kin kyauta kam, amma kinsan nafiso idan za a zo wajena asanar dani ko?.
Hakane am srry friendy.
Okey bara na kawo maki abinsha.
No da ma kin barshi wlh, hajiya mama fa?
Bata nan wlh taje dubiya
Eyyah...wai yayanmu wannan ko kuwa?, naga ajinsa yayi yawa kawata.
Hmmmn...muhibbat!. Kinsan wani abu?, banaso wani abu ya hadani dake akan mijin da zan aura, shigowarki me kika yi masa ne na kasa gane kansa?, kirike abinda yake tsakanina dake, kuma kisani tsakanina da ke AMINTAKA itace jigon tarayyarmu, kar kiyarda musake samun wata baraka atsakaninmu dan ina mai tabbatar maki yanda kikamun akan mubeen wlh tawa sai tafi taki zafi, ina daga maki ne na dan wani lokaci.. Tohm!, ta kara maganar cikin daurewar fuska, alamar tafara yimata shishshigi dayawa.
Toooo....aini bansan shine yayan naki bafa, yi hakuri, ki kirashi mugaisa mana nabashi hakuri pls.
Hmmmm kina daukan abin da wasa muhibbat try me pls wlh zaki gani, zan koma kitchen dan aiki yasani.
Uhm...okey kigama ina jiranki, inaso muyi mgn ne dake.
Amal ta mike ba tareda ta ce mata uffan ba ta shige kitchen ranta abace da wannan naci na muhibbat
*** *** *** *** ***
Daki ya shiga yana ta tunanin wannan masifa da naci na wannan yarinya da me yayi kama..safa da marwa yakeyi a tsakiyar dakin yana tunanin gane manufar wannan yarinya yakasa.
Haka ya gaji ya koma ya kwanta kan resting chair dake gefen gadonsa idanunsa sunyi jawur.
Urs Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
14
Haka ta kammala dafa masa indomie kai tsaye dakinsa ta wuce don kai masa, amma ta taradda ya fice baya gidan baki daya.
A'ah... Wai meke faruwa ne?, kodai yaya Areef baya son tarayya ta da muhibbat ne?..tambayoyin da takasa gane amsarsu, tagaji da tsayuwa ta koma ciki, inda har a wannan lokacin muhibbat tana zaune tana 'yan latse latsen waya.
Amal ta dawo ta zauna daf da muhibbat tareda kura mata manyan idanuwanta tace...muhibbat...!
Sannan ta dawo da hankalinta gareta ta amsa da na'am kawata.
Muhibbat na rokeki da kifita a rayuwata, abinda kikeso dai nayi maki shi yafiya kikace kuma na yafe maki so what next?
Ummmm...nothing much dear kawai dai yayanki yamun kamun da na gaza kwace kaina wlh.
Idonta ta fiddo dasu waje tace kina hauka muhibbat ko kanki ya kwance ne, pls kitashi kibar gidan nan tun kafin wani mummunan al amari ya shiga tsakanina dake...haka ta rufe idonta ta fara zazzagawa muhibbat rashin mutunci, amma ko a jikinta...ta dauki mayafinta zata wuce...to Amal Ayud, zan tafi kuma zan bar rayuwarki amma Areef baki isa ki rabani dashi ba saina auri Areef kuma Areef zai soni kisa ido kiyi kallo ta fice ba tareda taji komai daga bakin Amal ba.
Kasa ta zube tana rera kuka mai tsuma zuciya, wanda babu mai rarrashinta.
Haka ya shigo ba tasani ba, kai tsaye gabanta ya durkusa tareda kamo lallausan hannayenta ya runtse a hannunsa, ta dago kai ta kalleshi yayinda hawayenta suka kasa tsagaita kwararowa saman kumatunta.
Idanunta sun kumburo sunyi jawur tana kallon yayanta wanda tasan hes very innocent guy wanda tasan bazai so ya zalunci soyayyarsu ba...
Kallonta shima yakeyi ya kasa furta komai sai tsantsar damuwa dake bayyane ta kyakkyawar fuskar tasa..
Yaya Areef...ta kira sunansa cikin shashshekar kuka.
Na'am Amal mene ne damuwan pls...ya fada cikin sarkewar murya.
Yaya Karka yarda wata mace ta rubbaceka ta rabani dakai kaji..
Hmmm...Amal ina sonki bazan so soyayya ta dake ta samu wata matsala ba, da yardar Allah komai zai zo karshe kinji...share hawayenki pls...ya zaro handchie daga cikin aljihun sa yafara goge mata kumatunta...inda kamshin turaren handchie ya doki hancinta.
Sai taji tamkar ya sa ya yaye mata dukkan damuwarta.
Wani san yanyan murmushi ta mayar masa mai tattare da sakwanni.
Tace...i trust yhu ma man...i love yhu wit all ma hrt.
Thanks for d love ma baby...n i trust yhu too.. Ya mayar mata tareda zare yan yatsunsa daga cikin nata gudun kar hajiya mama ta dawo ta samesu haka.
To yaya bakaci indomie ba, wani za a dafa ko yaya?
No am okey babe zuwa anjima dai.
Ta zumbura baki zatayi sabon kuka..yayi saurin dakatar da ita...no pls wlh nakoshi yanzu.
To na yarda amma promise me zuwa anjima zaka ci dayawa.
Yeah i promised yhu..n kema kimun al kawarin babu ke babu waccen jakan yarinyar da take dagula mana tunani.
Nama ka alkawari wlh danni tuni na yanke wannan decision din insha Allah...i cant take it any more naganka cikin yanayin da bazan iya controlling naka ba.
Murmushi yayi yasa hannu ya lakuci dogon hancinta yace i love yhu babe.
Tayi dariya tareda sunkuyar da kanta kasa kunya duk ta rufeta.
*** *** *** *** ***
Gidan Abdul'ahad ya rikice, inda maimuna mahaifiyar Areef tace lallai bata aminta da auren zumunci ba..
To nidai ga hukuncin dana yake kuma hajiya mama ta yanke saboda haka saiki hakuri...ya mike zai fita taja wo bakin rigarsa tace to wlh tallahi Alh dole Areef ya dawo gidan nan da zama nagaji wlh da wannan abubuwan da ake mani, ni ban isa nace ga yanda nakeso nayi da Areef ba.
Mamaki ya gama kamashi ganin yanda maimuna ta canja cikin kankanin lokaci...hmmmm to sakarni zan fita, dan wannan hayaniyar bazan iya daukar ta ba, saboda nidai kinsan ban iya hayaniya ba kuma ban tashi naga gidanmu anayi ba ya fizge bakin rigarsa ya tafiyarsa.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
15
Barci ya gagareta, tunanin hanyar da zata fiye mata sauki takeyi dan ganin ta mallaki Areef takeyi...kwatsam ta tuna da wata kawar Amal wato nebo dinsu Amal mai suna salma, akwai ranar da Amal ta ba muhibbat no dinta tace ta kira mata ita so tayi saving no dinta.
Kai tsaye ta lalubo wayar ta da ke karkashin pilo tashiga scrolling contact nata saiga sunan salma a ciki, bata jira wata wata ba ta danna kira bugu daya kuwa salma ta dauka tareda kanga wa a kunnenta...hlo
Hi...pls salma ce?
Eh nice..wake mgn?
Laa baki gane ni ba?, Muhibbat kawar Amal.
Ahhhh ashe ana jinku manyan gari..to ya kike.
Uhm...lafiya klau wlh, dan Allah salma nakira Amal no dinta duka basa shiga, nakira ta hajiya mama itama akashe nace bara naji ko akwai ta wanda kike da wanda zan sameta urgently pls.
Ohhh shiyasa ma kika kirani kenan.. No wlh ba haka bane ina son muyi mgn da ita ne kan sch kinsan mun koma hutu n muna a final year namu.
Eyyah...all d best dear, bara na duba maki no yayanta Areef bazan rasashi ba.
Huh...Alhmdlh ta fada cikin zakuwa tace yauwa bani salma.
Sukayi hanging call din, cikin seconds saika text na contact din Areef ya shigo mata.
Dadi kasheta kamar ta yi ihu.
Bata jira wata wata ba duk da kuwa dare ya farayi kusan after 11:00pm amma bai dame ta ba kai tsaye tayi dialing no din ya shiga...ya dade bai daga ba har ya kusa yankewa sannan yayi picking tareda daukan yin shiru, kasancewar baisan no ba.
Itama shirun tayi sannan ta yi gyaran murya...cikin kisisina tace.. Hello yaya inayini.
Damn!...gabansa ya fadi...nan take ya daure fuska tamkar tana ganinsa ya amsa da lfy...pls huz on d line?
Shiru ta danyi na wani lokaci...kasancewar zazzakar muryar guy din mai tafiya da imanin duk wani mai saurarenta data dokin dodon kunnenta, a take taji waji yarrrrrrrr...ajikinta...ta sauke doguwar ajiyar zuciya tace...
Ayya yaya Areef kanwar ce wacce kake nunawa tsantsar tsana da babu gaira babu dalili.
Pls wake mgn ya fada in a serious tone!
Toooh maida wukan yallabai...muhibbat ce inason magana da kai ne.
Banida lokaci pls, and am warning yhu daga yau karki kuma yin gigin kirana idan ba haka ba zan sa abaki kashin tsiya dan am not ur class yauwa..ya katse wayar ba tareda ya jira jin amsarta ba.
Mamaki ya rufeta yabarta sagale da waya a hannu...hmmm lallai Areef ni mace ce kuma nasan hanyoyi daban daban da zan iya mallakarka cikin ruwan sanyi, ka kwantar da hankalinka...ta fada tareda cije gefen lebenta.
*** *** *** *** ***
Ranshi a bace ya yi sallama tare da fada cikin dakin mahaifiyar tasa kai tsaye..
Mama ina yini?
A'ah...Abdul'ahad lafiya kuwa?..
Mama maimuna ta hanani sukuni akan maganar yaran nan narasa inda zansa kaina.
Nan take ran hajiya mama yayi matukar baci, dan kuwa tasan kaf yaranta babu mai hakuri AYUD1 muddin kaga bacin ransa ti ankaishi makura..zama ta gyara tace...lallai ita maimunar ce takeyin hakan?
Yanzu tace Areef ya koma gida da zama..na fada mata bata isa ba, abune idan Allah ya kaddara za a yishi babu wanda ya isa ya dakatar dashi.
Abinda nake so dakai, gobe ku tattaro kaf matayenku kuzo inason magana ta karshe da ku dan gane da hidimar auren yaran nan, dan bazaiyiwu ba wlh, aure babu fashi...tashi ka koma kafin yaran ma suzo suganka cikin wannan bacin ran kayi hakuri, zanyi maganin abun...haka ya tashi jiki babu kwari ya fice
Zance banzq kawai...ni har ta isa nace ga yanda nakeson ayi ace ba haka ba nida jikokina kuma wadanda na rika tun da aka yayesu, sam bata isa...haka tacigaba da fada ita kadai, karshe ta janyo yar karamar radio ta takunna tareda kishingidawa.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
_Thanks alot for d warm prayers Alhmdlh am getting much more beta Allah yabar zumunci ameen_
0 comments:
Post a Comment