ASALIN LABARI
Muhibbat S. Saulawa da Amal yan matane masu aji da kokari a cikin frnds nasu shigar su ta sha ban ban.
Hakan yasa komai nasu yazama iri daya haline kowa da irin nasa.
Zaune suke a lecture all suna jiran azo ayi masu lecture saiga mubeen wato saurayin muhibbat wanda a duk duniya bata hada kowa da shi ba.
Baby kana nan ashe?
Abinda muhibba tafara cewa kenan
Shikuwa gogan hankalinsa yana kan Amal dan tagama tafiya da rayuwarsa
Amal kuwa babu abinda takeyi banda playing game na temple run2.
Hmmmmm...taja dogon numfashi, ina magana tunanin me kakeyi wai.
Au...am srry durlin wlh kinga kawarki ta iya game haka?
Harara ta wurga masa.
To ya ake ciki lemmi see ur phone, muje na taka maku mana ance baza ayi lecture bafa.
Okey lets go, ta mike tareda mika masa waya.
Friending muje.
Anan Amal ta juyo har tasan ba su kadai bane.
Damn!...gabansa ya fadi...naka takaina ina muhibba ta samu wannan zukekiyar yarinyar yar cas abinta?, aikuwa sai na san yanda na mallaki ya rinyar nan kutttt....ya fada a ransa.
Wani irin kallon raini Amal ta mayar masa ganin kallon maita ta yake tayi mata.
Tayi saurin yin gaba muhibba mu hadu a bus stop don yayanah yakusa karasowa wannan shiriritar badani ba.
Muhibbat bataji dadin yanda Amal tayiwa Mubeen dinta ba amma a haka ta amsa ta da to ba damuwa sai mun hade.
Suna cen suna magana mubeen har ya dauki number Amal a wayar shi yana yan latse latse kamar yanda ya saba yi idan wayar babynsa muhibbat tazo hannunsa.
Kuma jin sunanta da kawarta ta ambata yakara bashi damar lalubo contact nata a saukake.
Areef yayi parcking daf da bus stop inda ya hango fuskarta a murtuke, yayi saurin danna mata hon.
A firgice ta dago kanta inda sukayi wa juna dariya ta taso zuwa wajen motan.
*** *** *** *** ***
Tafiya sukeyi ita dai hankalinta akan waya yake kullum.
Wai Amal meyasa kike da bama wayarki muhimmanci ne wai?
Yaya game nake fa ba komai ba ta fada cikin shagwaba.
Hmmmm...toni wlh abin yafara bai haushi fa.
Am srry big broz na ajiye.
Tana ajiye wayan kiran muhibbat ya shigo sunan S. Saulawa ya bayyana a saman screen din wayar.
Kallonta Areef yayi kawai ya maida hankalinsa ga tukin da yakeyi.
Anan ta tsargu kodai yayanta sonta yakeyi ya kasa furtawa wannan tsananin nasa yayi yawa fa.
Muhibbat da nacin kira sai da tasake kira ganin ba a dauki kiranta na farko ba.
Nifa ban hanaki picking calls ba kiyi abinki...ya fada ko kallonta baiyi ba.
A tsorace tadauka...ya akayi ne muhibbat nifa na tafi gida yaya Areef yazo.
Daga dayan ban garen tace aw...yau kuma 'yar tafiya ce babu sallama in ba za a ragemun hanya ba?
To ai naga kina tare da saurayinki kar na takuraku shiyasa kawata.
Ba komai sai goben kenan ko?
Eh Allah ya kaimu.
Sukayi hanging ta ajiye wayan...tana yi masa wani kallo taga yanda yayanta ya murtuke fuska.
Yaya Areef...wlh idan ka daure fuska bakayin kyau..
To naji wazan burge ma idan nayi kyan?
Ohhhhh....zata yi dariya tayi saurin dafe bakinta.
Da haka har suka isa gida.
*** *** *** *** ***
Kai tsaye bath room ta fada dan watsa ruwa ta gabatar da sallah la'asar.
Bayan ta idar da sallah taji wayarta ta fara ringing tayi saurin dubawa ko mamanta ce, sai taci karo da sabuwar number.
Dauka tayi tareda kangawa a kunnenta ba tareda tace komai ba.
Amincin Allah ya tabbata agareki ya ke ma'abociyar kyau...
Abin mamaki muryar da ta doshi dodon kunnenta kamar ta saurayin muhibbat da suka hadu da shi dazu.
Tare dakai ta mai da mashi cikin mamaki...
Amal sunana mubeen, so da kaunarki ya hanani sukuni tun lokacin da nayi arangama da kyakkawar fuskarki dazu wallahi amal ina sonki kuma aurenki zanyi ki taimaka kibani hadin kai karki wahalar da zuciya mai aminci da karamci a tattare da ke.
Kana haukane?, kai wane irin mutum ne?, ina kasamu number na?, dakata malam am warning yhu for first n last tym karka sake kirana kuma kar kasake tunkarana da irin wannan shirmen da hankali bazai iya dauka ba, ni 'yar halak ce nasan mutumci, nakuma san Aminci..kuma na iya rikon Amana kuma na san yarda wadanda bazasu saka ni na aikata hauka da sakarci irin naka ba kaji ko!!!...ta kashe wayarta tareda wurgata saman gado ta koma ta kwanta saman prayer mat ranta a bace..wanda ita kanta tayi mamakin irin kalaman da ta fadawa mubeen mahaukaci.
Da haka har bacci yayi awon gaba da ita.
To daga wannan lokacin mubeen ya dinga yiwa muhibbat wulakanci, gashi ta dauki son duniya ta dora masa.
Wata rana suna zaune suna karatu da Amal da Muhibbat, sai muhibbat ta dauki wayar Amal tana kallon pics, duk a wannan lokacin Amal bata taba yarda kawarta taga pic na yayanta Areef ba, kasancewar mata halin su sai su, wannan yasa ma tayi masa folder dinsa tareda saka passward a jiki.
Waike friendy mesa wannan folder naki kullum a rufe halan baki da gaskiya?
Dariya Amal tayi saida wushiryarta ta bayyana...tace to ke kuma ina ruwanki, kiga iya wanda zaki gani mana.
To naji ga wayanki...hannu tasa zata karba suna cikin haka kwatsam number mubeen ta bayyana saman screen din wayar Amal...incoming call...huh!
Wani irin kallo muhibbat takeyiwa Amal alamar lallai kin cika mayaudariya...
Tambayarta ta soma yayinda ta sakar mata wayar.
Amal????
Number mubeen a wayanki?
Miye hadinki da mubeen Amal?
Kallon banza Amal ta mayar mata da shi tareda dogon tsoki...
Muhibbat kinfi sanin halina fiye da na kowa, kin san cewa ni ba ajin chewingum boys bace irinki, and banida tym na cin Amana dan nasan daraja da muhimmanci na AMINTAKA...kije kiyi tunani na barki da wannan..ta mike.
Muhibbat ba ta tsaya saura rartaba ta bi gabanta don yaga rigar mutuncinta a gaban mutane wanda hakan yasa mutane suka farga suka gane cewa Amal yarinya ce mai natsuwa, hankali da sanin ya kamata.
Haka sukayi rabuwar baran baran da muhibbat.
Bayan ta shiga adaidaita sahu ta isa gida, ta dauki waya da kanta taso kiran mubeen ta ci mutuncinsa sai kuma wata zuciya tace mata kibarsu da haka kawai...nan take tayi diverting number din ranta a bace ta shige bath room dan watsa ruwa.
*** *** *** *** ***
Yau ma kamar kullum muhibbat tacigaba da kiran Amal a waya saboda tana son zuwa gidansu don neman yafiya da afuwarta akan abinda ya faru abaya.
Kasancewar Amal yarinya ce mai saukin kai bata ba muhibbat wahala ba nan da nan ta sauka ta kuma bata damar zuwa yau.
Kiran ta sakeyi don wayarta a silent take saida hajiya mama ta kula tace...
Amal bakiga wayarki tana haske bane?
Ohhh....Ban kula ba hajiya mama...tana magana tana kallon Areef dan akowane lokaci tayi magana saitaga kamar batayi daidai ba ita dai Allah yasa mata tsoronsa duk da kuwa akwai tsokana akanta.
Daukar wayar tayi tasa a kunnenta...hello kawata kina lafiya?
Haba kawata ina taso nazo na ganki amma kinata mun yawo da hankali ko?
A'a ba haka bane wlh ban kula ba ma da kiranki...kin taho ne?
A'a amma idan ance in taho ai sai na taho yanzu yanzu.
Sukayi dariya baki dayansu.
Ehh mana kitaho.
Oryt am ma way.
Tahm ina jiran babbar bakuwa.
Ta kashe wayan.
Hajiya mama muhibbat ce kawata zatazo.
Haba...ashe tana nan kwana biyu andaina mana zancenta kuwa.
Eh wlh tana nan, yau ma zatazo ai.
To Allah kawota lafiya.
Ameeen hajiya mamarmu.
Ta mike tsaye daga ita sai wani tight sket dogo mai tsaga abaya da waya yar karamar riga wacce idan ta daga hannayenta sama cibiyarta zata bayyana...tashinta keda wuya kuwa kular kanta ta fadi kasa ta sunkuya ta dauka...
Duk a wannan lokacin idon Areef yana kanta.
Daga hannunta tayi sama don mayarda hularta anan kuwa satin cikinta da cibiyarta suka bayyana huh....
Saurin saddakansa yayi kasa yace subhanallah...wanda ya bayyana a fili ba tareda yasan hakan ya faru ba.
Waigowa tayi ta kallesa duk sai taji ta tsargu cikin sauri ta shige dakinta.
Ita kuwa yar dattijuwar dayake tsohon hannu ce wajen kwama mediacal glass don karatun jaridu tuni ta maida hankalin ga wata sabuwar mujallah dairly trust ta wannan makon.
Kansa a sunkuye haka ya mike jiki babu kwari, don bai taba ganin Amal haka, azuciyarsa kuwa babu abinda yake ji face lallai dolensa ya habbasa don ganin ya mallaki yarinyar nan in ba haka ba kuwa zaiyiwa kansa sakiyar da ba ruwa.
Lallai Areef ya fada tsundum a soyayyar da baisan hanyar fitar ta ba, dalili kuwa bashida tabbas idan Amal batada wani saurayin boye.
Shawara ya yanke akan ya zaunar da ita ya gabatar da kansa gareta.
Gari ya waye...ya shirya tsaf cikin fari jeans tareda sky blue t-shet ya taje gashin kansa inda ya kwanta yana ta salki gwanin burgewa, spray na sure ya dauko ya fesa, sannan ya nufi bangaren hajiya mama dan isar da gaisuwa.
Assalamu alaikum.. Yayi sallama tare da zama a gefen gadon dakin nata kasancewar sallar walha da ya tarad tanayi.
Shiru yayi na dan wani lokaci sannan yaji ta amsa kasa kasa alamar ta idar da sallahn.
Hajiya mama ina kwana.
Lafiya klau babban angon hajiya Rakiya.
Dariya yayi tareda sosa keya yace.. Yau ba naki bane angon na Amal ne.
Dariya tayi sosai sannan tace...to Alhmdlh Areefullah har kun daidaita kanku da wuri haka?, kai madallah madallah naji dadi wlh..
A'a dakata hajjaju...sunkuyawa yayi yayi mata rada..inda ta tuntsure da dariya tace.. Lallai ashe ma ba namijin bane abun duk burga ce.
Dariya yayi yace ba komai zan zama namijin ai very soon ya mike yana kakkabe jikinsa.. Bara naje da zafi na kar ma ki gogan tsufa yau kanwata taga nayi mata tsufa tace bazatayi ba...ya fice yana dariya
Dariyar tabishi da ita itama dan kuwa yanayin acting na yaran yana matukar burgeta hakan yasa akullum bata da wata kewa sai in sunje sch kafin su dawo.
*** *** *** *** ***
Rigin gine take tana latse latsen waya kamar yan da tasaba akowane lokaci, babu abinda takeyi sai chat da friends nata murmushi kawai takeyi wanda yasake kayatar da kyawun fuskarta.
Tun yana yin sanda har takai ga ya karasa tura murfin kofan ya bude ya tsaya cak tareda harde hannayensa yana kallonta shima yana mayar da murmushin gamida sauke ajiyar zuciya.
Amal.....ya kira sunanta cikin siririyar murya cikin yanayin tausayawa.
Firgita tayi dan jin kiran tayi tamkar cikin rada...kasancewar ta matsoraciya.
Tozali tayi da yayanta a bakin kofa ta nemi ta boye wayan ta a karkashin pilo ya daure fuska yace bani wayan nan.. Ya mika hannu.
Tabe baki tayi zatayi kuka tace yaya dan Allah wlh babu....ya daga hannu tare da rufe bakinsa alamar baya son jin komai...just give me d phone.
Kallon sa takeyi cikin alamar tambaya me tayiwa yayanta haka wai yake neman takura mata wai abu yakai har cikin dakinta??
Wayar ta mika masa nan take hawaye suka fara sauka a kumatunta.
Jikinsa yaji yayi sanyi ya sa hannu ya karba sannan yace...Amal...
Naam yaya...ta amsa kanta a sunkuye.
Amal meyasa kike bama waya matukar muhimmanci fiye da komai a rayuwarki?
Yaya tana debemun kewa ne
Ohhh mu da hajiya mama bamuda amfani kenan?
Saurin dago kai tayi ta kallesa tace a'a yaya kuna da shi mana...
To meyasa mu bakyayin fira damu, ko bamu iya firar da zamu saki murmushi bane?
A'a yaya, am sorry pls bazan kuma ba.
Ba laifi kikayi ba Amal amma ni kiris ya hana nace kinyi mani laifin ma.
Damn!...gabanta ya fado tace me nayi yaya Areef?
Kinyi mani sata Amal meyasa idan kina son abu bazaki iya tambayana ba kawai sai da na duba naga babu meyasa Amal why?!
Kyawawan idanunta ta fito da su waje tace...nashiga uku yaya me na daukar maka wlh yaya ban taba daukar maka abu without ur permission ba kasan halina ba tun yanzu ba yaya me na dauka wlh bani bace ba dan Allah kayi hakuri kasake dubawa....kuka yaso yaci karfinta.
Matsowa yasakeyi kusa da ita zuciyarshi kana kallon yanda rigar sa take bugawa da karfinta tamkar zatawo waje yace pls..Amal stop it bana son kuka kinji...kinyi mun sata kin sace zuciyana bayan baki sanar dani kina so ba meyasa Amal?, naji ina sonki sosai Amal ina son na aureki Amal ke yar uwata ce ta jini karki juyan bayan i duly loves yhu pls kinji..
Anan ta dago kanta ta yi masa wani kall wanda ya tabbatar masa da cewa 'accepted', duk da kuwa har alokacin idanunta basu daina ambaliyar zubar hawayen ba har sun fara kumbura da yin ja, nan take ta zube kasa kukanta ya tsagaita taji wani irin sanyi a ranta.
Ji yake tamkar ya rungumuta sai dai ina...bazai iya ba gudun aikata abinda bai dace ba.
Sunkuyawa yayi yazaro handchie a aljihunshi yana share mata hawayen ta kallonsa takeyi sosai anan tasake tabbatr da kyawun yayanta sosai.
Hannunta ya kama tareda damka mata wayarta yace Amal arage bama waya muhimmanci kinji, and am really sorry pls.
Kai ta gada masa alamr to.
Ya mike zai fita sai kuma ya juyo ya sake dubanta sukayi four eyez tayi sauri maida kanta kasa ya fice.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
9
Nan fa akeyinta, tun daga ranar amal takasa sakewa kunyar yayanta Areef takeji sosai, inda hajiya mama ta gano hakan kamar tayi masu magana sai kuma ta fasa.
Yau ma kamar kullum Amal ta hada masu break fast inda suke yar sauri sauri saboda lecture da take dashi, shi kuma Areef yau take final a wajensa don ya kammala komai defense zai kaishi na project.
Zugum tayi takasa cin komai haka tasa hannu ta rike musk din wato cup na shantin.
Ya ya Amal ko bakijin dadi yau naga kuzarin naki sai a hankali.
Nima dai kamar nayi wannan tambayar hajiya mama.
Babu komai hajiya mama wallahi nagaji da zuwa sch dinnan da zan samu kwanciyana zanyima.
Dariya sukayi hajiya mama tace to sannu alankosa.
Yauwa ban sanar daku ba yau fa akwai baki gidannan, iyayenku zasuzo dukansu.
Damn...gaban Amal ya fadi don kuwa tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki.
Shikuwa gogan haka dama yakeso.
Allah ya kawosu lafiya ya fada a takaice tareda mikewa Amal muje idan u are certisfied pls ana jirana.
Bata bashi ansa ba ta mike tare da dauko hijabinta da hand bag nata...hajiya mama we are going sai na maki tsara ba...sukayi dariya suka fice ba tareda sun jira ansarta ba.
*** *** *** *** ***
Gida ya cika kamar kullum, inda mahaifin Areef ya gabatar da komai a idon kowa gameda kyaututtukan da ya bama Amal da Areef tareda keys na mota guda daya sabuwa kirar formatic fara tas wacce gilashinta bazai baka damar ganin wanda yake a ciki ba wato thint, sunyi godiya da nuna farin cikinsu sosai inda shi kuma Alh Abdallah mahaifi ga Amal yayiwa Areef kyauta ta Upper wato takardar samun aiki a karkashin wani babban kamfaninsa inda ya daukeshi a matsayin General manager...huh dadi ya rufesu, babu abinda Hajiya mama takeyi sai zunduma wa yaran nata da zuriar baki daya albarka, kasancewar yanda basu da kyashi da jin zafin yiwa nasu da duk wani majiyi karfi a rayuwa, bugu da kari hajiya mama kema ga wannan inji Abdallah...wrapper ne na kudi wanda ni kaina mai rubutu bazan iya kiyasta ko nawane bane ya mika mata, albarka kam sunshata.
Matansu suna gefe maryam kanta a sunkuye tana ta cewa ameen angode cikin natsuwa da girmama wa, maimuna kuwa tun anan hajiya mama ta fara gane cewa lallai halayyarta tacanja don bakin ciki ya bayyana karara a fuskarta banda gatsine babu abinda takeyi da raba ido.
Ran Abdul'ahad ya yi matukar baci, yaso ya tanka sai kuma yayi tunanin a cikin mutane bai kamata ya mata haka ba.
Haka hajiya mama taso tace wani abu sai tayi mata uzuri don bata taba ganin haka daga gareta ba.
Yara kuwa sunacen suna duduma a back yard.
Arfat tana dakin auntyn ta Amal tana jiran su gama taron dan kuwa she really missed her.
Sun kulle taronsu da addua sukayi sallama kowa yaja iyalinsa zasu tafi arfat tace ita lallai tunda weekend ne abarta wajen aunty Amal...duk da ummansu bataso hakan ba dole aka barta kuwa tunda hajiya mama tasa baki.
*** *** *** *** ***
Muhibbat S. Saulawa itace mai adaidaita ya sauke a daidai bakin get din gidan hajiya Rakiya wato hajiya mamarsu Amal, ta sallameshi ya juya ya tafi.
Kai tsaye gidan ta shige suka gaisa da baba mai gadi ta wuce ciki, bakinsa ya rike dan tsohon don tun a yanayin shigarta zaka gane lallai idonta ya bude ba kamar yanda yasanta ba.
Karo taci da kyakkyawan saurayin yana waya yana kulle dakinsa dan baimasan da akwai wani a bayansa....damn gabanta ne yayi mugun baci dan bata taba ganin saurayi dan gayu kuma mai kyau irinsa ba, huh...bakinta yana kyarma tayi saurin ce masa sannu.
Ya juyo tareda soka wayarsa aljihu yauwa sannu ya watsa mata harara, a ransa yace ke kuma fa?, badai kece kawar Amal dina ba?, dan yau banji ance zakizo ba.
Tayi tsaye bata sake ce masa komai ba taga kamar ya shiga dogon tunani a tunaninta burgeshi tayi, rausaya da yan girgije girje ta fara yi duk dan ta burgeshi a hakan tace...dan Allah Amal fa?.
Mtsw yaja tsoki ya nufi parckinh area ya tayar da mota ya fice abinsa.
Lallai saina mallaki gayen nan koma waye shi dan yayi mani karshe...ta kutsa kai cikin gidan tareda doguwar sallama.
Hajiya mama dake falo ita kadai tana karatun alkur'ani ta tarad, muhibbat ta zauna kasa gefenta ta gaisheta cikin ladabi hajiya mama muhibbat ce kawar Amal...tana wasa da 'yan yatsun hannunta.
Eyyah...ban ganeki ba ai, kinyi girma kin bar kawarki ta tsaya wasa, kishiga tana ciki.
Kunya ta kamata sosai tace tohm ta mike ta nufi dakin Amal kai tsaye.
Nocking tayi ta tura kofan ba tareda ta jiya an bata damar shigowa ba.
What..suprise?!
Amal dake kwance da dan mini sket da yar body hug baka tana gyaran yalwataccen gashinta ta fada cikin mamaki...muhibbat?, wai kece ko am dreaming?.
Jeki wanke fuskanki saiki sake tabbatarwa ai mara kirki, kin bani wahala wlh friendy haba mana.
To ba wannan ba bara na kawo maki dan drink sai ki cigaba da naki korafin...ta mike tareda janyo hijab dinta tasaka ta nufi kitchen.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
10
Drinks kala kala ta zube mata a kan hand tray tareda cup takoma ta zauna.
Ur highly wlcm kawata.
Uhmm...thank yhu.
To kisha mana
No ba wannan ba Amal kafin nafara ce maki komai pls kuna da kyakkyawan saurayi a nan gidan dama ban taba sani ba?
Dariya Amal tayi tace waye kyakkyawan saurayi kuma kodai kinyi gamo ne kawata?
Abeg joke apart, wlh nashigo naci karo dashi yana niyyan fita, ya tafi da imanin zuciyana fa am serious.
Damn!!!... Gaban Amal ya fadi, kar dai ace muhibbat yayanta Areef take nufi, dan muhibbat basu taba haduwa face to face da Areef ba...lallai ta fada ciki ciki.
Yaya akwai matsala kawata?..muhibbat ta tambaya a razane
No manta kawai..dan banma gane wa kike nufi ba, d only thing bamuda wani guy a gidan nan banda wanda ya wuce yayanah Areef kuma my husband to be insha Allah...ta fada a takaice.
Tirkashi...abinda muhibbat ta fada kenan...dan jikinta yayi sanyi, kar dai ace nazo neman sasanci kuma musake komawa ruwa da aminiyata ta fada a ranta.
Shiru wajen ya dauka na dan wani lokaci sannan Amal ta ce...wai mene ne kawata kike ta kirana a lokuttan baya i thought ma kinyi aure fa.
Huh.. Aure fa kikace friendy to wa zan aura?
Dariya Amal tayi ta ban mamaki tace...ai kinfi dan dakon tasha sanin wanda zaki aura.
Hmmmm...waye shi to Amal??
Ya wuce wanda kika yi mani rashin mutunci akansa wanda bansan hawa ba bankuma san sauka ba.
Hmmmm...tasake jan dogon numfashi tace...Amal...mubeen kike magana kuma tuni muka rabu da mubeen baran baran dan tuni na gano bakin zaren mubeen mayau darine, ma ha inci ne shi yarabani dake, ke kawar kirkice, mai amana da sanin darajar ta AMINTAKA... kiyi hakuri akan abubuwan da suka faru a baya Amal kinsan zuciya bata da kashi wlh bansan ni da kaina zan iya aikata maki abinda nayi maki ba a school dan Allah kiyafe mun kawara.
Murmushi ta sakar mata wanda ya sake bayyanar da double dimples nata da kyawun fuskarta tace.. Muhibbat nu ban rikeki ba ban kuma ce bazan iya yafe maki ba, amma kinsan mezai faru?
Tayi saurin kada kanta, tace to abinda kika shigo gidan nan da shi yanzu, shi zaisa bazan iya kowa AMINTAKA...tsakanina dake ba, gudun shu'umanci irin na 'ya mace dan bazan boye maki ba wlh muhibbat tsoronki nake.
Idonta ta fiddo waje tare da dafe kirjinta....haba Amal me nayi maki kuma shigowata a gidan ki dubi girman Allah kiyi hakuri kawata.
Dariya taso kufcewa Amal tace wai ma muhibbat, duk ina sauran frnds naki da nakejin labarin kinyi duk kin barsu kin dawo mun ne saboda sake sakani cikin sabuwar rayuwa ko kuwa?
A'a ni yanzu banida frnds wlh kedin dai kece.
To ba damuwa, Amma kinsan wani abu?
A'a sai kin fada.
Saurayin da kike magana yayanah ne Areefullah, wanda kuma zan aura nan kusa ba da dadewa ba, ina so kisawa ranki in har shine babu ke babu wata alaka tsakaninki dashi dan nima aknsa babu abinda bazan iyayi ba.
Huh.. Wannan shine concrete warning...ta fada ciki ciki...
Yeah!!!...abinda amal tace kenan.
Suka cigaba da firarsu ta bayan rabuwa har kusan magrib, suka yi sallah inda muhibbat tayiwa hajiya mama sallama ta wuce gida.
Wanda taso ace Areef ya dawo gida kafin ta tafi sukasake hadu dan ta tabbatar da idan shine yayan Amal da take cewa fiancy nata.
*** *** *** *** ***
Arfat ce kwance kan cinyar auntynta Amal tana yi mata kalaba, suna ta firarsu ta bayan rabuwa kasancewar yanzu duk weekend a gidan hajiya mama arfat takeyinsa, inda take jan hankalinta akan ta maida hankalinta kan karatunta...Arfat karki sake ki yarda da yin AMINTAKA da kawa guda daya tilo ki kasance kowa naki ne cikin course mate naki amma banda mutumin banza, ban kuma ce kizama available ba.
Dariya arfat tayi tace to aunty babba.
Yauwa, kedai kizama classy lady u knw i mean.
Yeah aunty.
Da haka har ta gama mata suna firarsu gwanin burgewa.
_MONDAY 17th SEP 2018_
Yaune rana ta farko da Areef yayi shirin fara zuwa office, inda yayi shiga ta black suit wit white neck tile, yayi kyau matukar gaske, kai tsaye main falo ya isa don yiwa su hajiya mama sallama zai fita office.
Amal ya ci karo da ita daga ita sai yar rigar bacci tana ta kai kawo a diny area don shirya break fast, kuma duk saurinta na kafin yayanta ya fito ne tasan tagama har ta shiga wanka.
Huh...a razane tace wayyo yaya har ka fito ne?
Eh mana ko na koma?..ya fada yana kashe mata ido.
A'a ai idan nace ka koma to zan makarar dakai danace ka koma wlh.
Nooo ur wish is ma command babe bara nakoma.. Ya juya sukayi four eyez da hajiya mama tana dariya, tace yau kuma anzama rakumi da akala?
Dariya shima ya mayar mata yace good morning ma..uwargida ta.
Bawani uwar gida ni ban yar da ba.
Suka dara baki dayansu. Amal ta umarci Areef da yazo ya karya kumallo kafin ya fita.
Ya makara amma babu yanda ya iya dolensa ya zauna ya dan yi kadan.
Tana gefensa duk da shes nt comfortable da zama haka da yar riga nyty haka ta daure, kallon mai shiga zuciya ta yi masa tace...are yhu okey?
Yes dear.
Okey muje na taka maka.
Brief case nashi ta daukar masa suka fice zuwa parcking area.
Saurin dakatar da ita yayi yace koma daga nan ko kin manta yanda kike.
Kunya ta kamata dan sam ta manta a guje ta koma ciki tana dariya.
0 comments:
Post a Comment