0️⃣1️⃣
*Bismillahi rahamanin Rahim*
,,,,Zaune yake cikin office dinsa saman table dinsa kuwa ciki take da takardu aiki yake Amma kamar ba zasu kare ba, Dan tsaki yaja sannan ya dauko robar ruwan dake gefen shi yasha rike kanshi yayi Dan bakaramar ciwo take masa ba,karar bude kofar da yaji,hakan baisa ya dago ba Dan yasan duk duniya mutum daya ne yake shiga office dinsa Kai tsaye.
Shiru sukayi nadan mintina sannan yadago Kai ya kalle shi yadanyi murmushi sannna yace"wannan Kuma kowa yataba shi yazo zai sauke akaina oho, afili Kuma yace" kazauna Mana abok... tsawar da ya daka Masa shiya hanashi karasa maganar yanuna shi da hannun Yana cewa"
karka kara kirana da abokin ka,bazanta ba kasancewa aboki ga maci Amana ba,bana fatan kasancewa aboki ga Mai tsansar butulci,bana fatan kasancewa aboki ga mutumin da yake mance alkairai,
Nakasa yarda wai yau Kaine kake juyawa AISHA~LABBEBAH baya,bayan Duk alkairan ta agare k...
Shidinma tsawa yadaka Masa cikin bacin Rai Dan sosai maganar shi ta mugun Bata mishi Rai idon sa kuwa harta sauya saboda tsananin bacin rai yace,"kasani sadiq duk duniya Kai ne mutum na farko da zaka'iya duban fuskata kafadamin duk abinda kake so batare da na nuna maka matsayi na ba.
kasancewar ka aminina tun yaranta,Amma Kuma kasani hakan bawai Yana nufin baka damar fadan duk abinda yazo bakinka bane.
Sannan zancan AISHA~LABIBBA kasan cewa naso aisha kai shidane akan haka,tabbas aisha tayimin abubuwa dayawa duk A* SANADIN Soyaya* Kuma inaso kasaka aranka har duniya ta tashi bazan taba mancewa da aisha ba Kuma nafada mata ba sau daya ba basau biyu ba duk lokacin da take niman wani taimako ta nemeni Zan Mata ko wani iri ne,zancan aure na da itah ne babu bazan iyah auran taba get that in to har heard.
yakare ke maganar da buga hannun shi saman table dinsa karar saidai ta firgita sadiq,cike da ma'maki yake kallon shi sannan yace,"kamar yanda kace bazaka iyah auran AISHA ba Raihan Haka Nima bazan'iya yin abota da kaiba sannan zancan idan tana niman taimako zaka taimaka mata to mun gode 🙏🙏bama bukata,sannan ka rubuta ka ije wallahi saikayi nadamar abinda ka aikata asannan Kuma lokaci ya kure maka sai wani lokaci.
Yana kaiwa daidai Nan yasa Kai yafita.
Rikicewa iya rikicewa Raihan yayi dasauri yabi bayan sadiq Yana Kiran shi Amma Ina tuni haryaja motar sa yabar harabar company din.shiru Raihan yayi sannan yakoma yadaiko key din motar sa shima yafita daga company din.bai tsaya ko inah ba sai kofar gidan su AISHA Yana zuwa saukowa yayi daga motar yashiga gidan kasan cewar yasan itah kadaice take rayuwa acikin gida Yana shiga ya kwalla mata kira.
Cikin sauri ta fito Dan ko amafarki taji wannan muryar to babu shakka tasan ma'mallakin ta,tana fitowa yabita da kallon uku saura kwata yace,"ki yanzu Aisha sai yaushe Zaki San (annabi)ya fako?saiyaushi Zaki gani cewan Raihan dinda kika sani daban Dana yanzu?sai yaushe Zaki gane cewan nafi karfin ki?sai yaushe Zaki San cewa inda Yan aiki na suke kwana yafinan sau dari?yafadi haka tare da nuna gidan.
To bara kiji Abu na karshi dazan kara jaddada Miki shine babu Ni babu ke kidauka baki taba ganin Raihan ba Kai bakima tabajin maikalar sunan ba ,sannan kinyi nasarar rabanida aminina sadiq Amma kisani saina kuntata rayuwar ki saina hukuntaki.
Yana kaiwa Nan yajuya Yana rufe hanci alamar wari yakeji agidan duk da kamshin turaran wuta dake tashi acikin gidan cikin saure Tasha gaban shi tana kuka tsananin kuka duk idonta sun kumbura da alamu ta dade tana aikin kukan tace"Dan ALLAH Raihan karkamin haka karka manta da alkawarin da muka daukar wa juna,yanzu harzaka iyah mancewa da labibar ka?nicefa labibar raiha...
Saukar marin da tajine yahanata karasa maganar cike da mamaki take binshi da kallo Wai yau itace Raihan muradin zuciyar ta yamara.
Cikin daga murya yanuna ta Yana cewa,"inah Mai tabbatar miki duk Randa kika sake hada kazamar sunan ki danawa wallahi saina mugun Saba miki,cikin bacin Rai yasakai yafita daga gidan.
Itah kuwa sugunnawa tayi agurin tana kuka Saida tayi Mai isarta sannan ta tashi ta shiga ciki jiri na diban ta.
****
Shikuwa sadiq Yana fita gidan shi yanufa Yana zuwa yazauna Yana tunanin butulci irin na Dan Adam Dan shidai ko amafarki aka fada mishi cewa Raihan zaijuyawa Aisha baya to babu shakka zaice a a,Amma saigashe yau ba mafarki yake ba Amma hakan na faruwa,tashi yayi ya fara safa da marwa Dan samarwa kanshi mafita,Haka dai yadauki kusan Rabin awa Yana Abu daya sai daga baya ya dauki makullin motar sa yafita.
Yana fita bai nufi ko inah ba sai gidan su AISHA Yana zuwa shima yashiga da sallama ya shiga gidan jin anyi shiru ba'a amsa ba yasa yadan tsaya Dan baisan awani yanayi zaiganta ba jin shirun yayi yawa yasa shi karasawa da sauri saidai me zaigani🙄
*Thanks alot friends inah alfahari daku domin kunkasance kuna bibiyar Al"amarina ,to inah fata Zaku karbi wannan sabon liltafinin nawa da hannu bibbiyu.love you all*
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
chaptar*0️⃣5️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,, Cikin ikon Allah labiba bata wani ji ciwo mai tsanani ba,hakan yasa da aka tambaye ta sunan garin su babu bata lokaci tace,"Kaduna kuma ta faɗa sunan unguwar su, koda mutanan anguwar suka same labarin abinda yafaru,tuni hankalin kowa ya tashi Dan kowa yasan irin dattakwan da iyayan labiba suke dashi.
Cikin kankanin lokacin aka sadasu da gidan suna gaskiya saidai muce ALLAH yajikan su.
Sosai mutuwar iyayan labiba ya tabi kowa dan irin kukan da labiba take akullum,idan kaga raihan saika rantse iyayan sane suka rasu.
Bayan anyi sadakar arba'i labiba taci gabada zuwa makaranta saidai tsoro da take yawan jine yasa bata samun isansan barci gashi ita kaďai ce a gidan,ganin haka yasa tanime anema mata masu haya dansu ďebe mata kewa, sannan kuɗin data karba ta rinka biyan kuɗin makarantar ta, harzuwa lokacin da yan uwanta zasu shigo garin.
Cikin kwanaki kalilan kuwa aka samu ƴan haya, dubu goma shabiyu suka biya na shekara, haka zamansu yakasance gwanin sha'awa dan sosai malam audu da matar sa luba suke kula da ita sosai.
Lokacin da aka biya labiba kuďin hayan nata Tana zaune ta saka kuɗin agaba tana tunanin abinda zatayi dasu, cikin sauri ta tashi jikin ta har rawa yake tafita daga gidan, bata isaya ko ina ba, sai gidan su raihan,tana zuwa ta tarar da sadiya wacce take kiranta Inna sadiya tace, "sannu da aiki Inna "
Cikin zaro ido tace, "wani aiki kika bani? Eye nace, "wani aiki kika bani,da kike min sannu?
Muryarta har rawa yake tace, "k..k..kiyi hakuri Inna.
"munafuka kullum cikin bada hakuri kamar dangin maroka,mekike Nima?
"Inna dama bawani abu bane kuɗine na kawo wa ya raihan,cikin sauri sadiya ta mike har zaninta nan kwancewa,murmushi tayi tace, "haba yar abarka ai saiki faɗamin tun farko zauna bara nakira shi, ciki sauri ta nufi ɗakin raihan, tana tsaye sai gasu sunfito tare saidai, Sam babu walwala afuskar raihan ganin hakan yasa labiba tasha jinin jikin ta.
Sunkuyar da kanta akasa tayi tace, "ya raihan ina kwana?
,"Lafiya lau ya akayi?
Kuɗin dake cikin hijabin ta tafitar tace, "ya raihan gashi ka biya kuɗin jam ɗin ka dashi.
Ido ya tsare ta dashi yace, "ainah kika samu kuɗi?
Cikin sauri Inna sadiya tasa hannu ta kwace kuɗin,duk kansu kallon ta suke cike da mamaki tace, "me kuma haka yarinya ta kawo maka kudi maimakon ka karba kayi godiya, amma saika tsareta da wasu tambayoyi marasa ma'ana.
Murmushi tayi ta Kalli labiba tace, "karkiyi fushi kinji 'yar abarka "
Murmushin karfi Hali kawai tayi tace, "to sai anjima inna.
,"To sai anjima.
Cikin sauri tabar gidan hartana harɗe kafa.
Bin bayanta raihan yayi harta Kai bakin kofar gida zata shiga taji anfisgo ta, cike da mamaki ta juya tana kallon sa, gabaki ɗaya kamannin sa sun sauya idanuwan sa sunyi ja.
Murmushi tayi tace, "ya raihan make damun ka?
tsawa ya daka mata yace, "labiba ina kika samu kuɗ? Waya baki kuďi? Aikin me kikayi kika samu kuďi?
Dariya ta fashe dashi dansai yanzu ta gane dalilin ďaure fuskar tasa,saida tayi Mai isarsa sannan ta kalle shi tace ,"kwantar da hankalin ka ya raihan kuďin haya nane fa.
Shikansa baisan lokacin da dariya ya kubce masa ba, danshi baima San yanada tsananin kishi ba sai yau.
Kallon ta yayi yace, "shine kika kwasu kuďin kika kawo min?
Ďaure Fuska tayi tace, "to sai mee?
,"saiki rike saboda Al'amarin yau da kullum.
,"nidai yaya jeka anjima zamu haɗu,bata jira jin abinda zai faďa ba tayi cikin gida da gudu.
Murmushi kawai yayi ya koma gida ,yana shiga yatarar innan sa Tana kirga kuɗin da labiba ta kawo.
Cikin sauri ya kwashe kuɗin ya shige ciki, Dariya tayi tace, "jairin yaro dakace baka so.
Raihan yana shiga ciki ya kirga kuďin,dubu bakwai ne,girgiza Kai yayi yace, "IN SHA ALLAH labiba kece uwar 'ya'yana,zanyi karatu zanneme kuɗi ko domin na taimaka miki.
Washa gari tun safe raihan yaje yayi register din jam.
Cike da farin ciki ya dawo gida daidai lokacin malam sule yashigo ganin yanda ɗansa tilo yake farin ciki sosai shima yayi farin ciki ,saidai lokacin da raihan yafada masa dalilin farin cikin nasa saiya tsanci kansa da tsanan Hali irinna Inna sadiya, shiru yayi ya shige ɗaki.
Cikin nasara raihan ya zana jarabawar sa,sosai sukayi farin ciki ganin raihan yafito da sakamako Mai kyau,saidai ba'anan gizo ke tsaka ba,inda zasu samu kuďi domin raihan ya cigaba da karatu.
Kullum cikin tunani labiba take wani lokacin har kasa barci take tsabar tunani,wata rana tunda safe ta tashi ta shirya ta nufi gidan Mai anguwa,sosai ganin labiba da sanyin safiya haka yabashi mamaki ,bayan sun gaisa ta sunkuyar da kanta tace, "baba dama bawani abu bane yakawo ni, sonake nasayar da wani bangare na gonar da ake yiwa baba noma kafin ya rasu.
Shirune ne yaɗan ratsa gurin ďaga bisani yace ,"shin labiba meza kiyi da kuɗi da har kike soki sayar da fili?
Shiru tayi dantasan tana faɗa masa tofa babu abinda zaisa ya yarda.
Ganin hakan yasa yace, "shikenan tashi kije gobe ki dawo.
Da fara'ar ta tayi masa godiya ta wuce zuciyar ta falda farin cikin faranta ran masoyinta da zatayi.
Haka kuwa akayi Washa gari tun safe ta nufi gidan Mai anguwa,shiɗinma dama ita yake jira Dan haka tana zuwa ya Mika mata tsabar kuɗi har naira 3,0000,cike da mamaki ta karbi kuďin tayi masa godiya.
Bayan sallar isha da farin ciki raihan yataho gun labiba,ita dinma da fara'ar ta tafito,bayan sunsha hirar su irinta masoya ya Mike yace,"RAI'ISH tashi ki shiga gida dare yayi.
Yatsine Fuska tayi tace, "tun yanzu?
,"Eh gaskiya kinga dare yayi.
Kamu hannun sa tayi Wanda aiya tsayin rayuwar su wannan ce Karo na farko da suka taba rike hannun juna, da mamaki raihan yake kallon ta,ita kuwa murmushi tayi tace, "zan rokeka wata alfarma yaya dafatan zakayi min
?
,"zanyi miki RAI'ISH nayi miki alkawari"
,"inason kayi min alkawarin bazaka taba rabuwa Dani ba, kayi min alkawarin kasancewa dani harkarshan rayuwar ka, kayi min alkawarin babu wacce zata Zama matar raihan saini labiba.
Shiru yayi naďan lokaci sannan yakama hannun ta ya damke yana kallon fuskar ta yace, "nayi miki alkawari labiba.
Mika masa ledar kuɗin tayi tace, "ina niman alfarmar karka buɗi harsai katafi gida.
Bata jira jin abinda zai faɗa ba tayi cikin gida.
Tsawan lokaci ya kwashe tsaye akofar gidan yana nazarin maganar, ganin tsayuwar bata da amfani yasa ya nufi gida.
Yana shiga ɗaki ya warware ledar,mikewa tsaye yayi lokacin da yayi arba da kuɗin,harya mike zai fita dan nunawa iyayansa saiya hangi wata farar takarda ta faďo daga cikin ledar, cikin sauri ya ďauka danganin abinda ke ciki,wasikace kamar haka"
*Daga taka labiba,ina soka sani nabaka kyautar kuɗin daka gani acikin wannan ledar, kayi amfani dashi Dan biyan kuɗin makarantar ka, kuma karkayi gigin dawowa dashi dan wallahi wallahi bazan karba ba,ina sonka RAI'ISH.*
Lokacin daya gama karantawa gabaki ďaya hawaye yagama wake masa Fuska, Zama yayi agurin yana tunanin irin halalcin da labiba tayi masa a rayuwa kuma wai *duk asanadin soyaya* Shikam bashida abinda zai ceda soyaya sai godiya, gabaki ɗaya MA kasa fita yayi yasanar da iyayan nasa.
Da asuba bayan sun dawo daga massalaci yake sanar da iyayan nasa irin kyautar da labiba tayi masa, sosai ran malam sule ya baci ta inda yake shiga batanan yake fita ba, ita kuwa Inna sadiya harda take rawa,saidai har yanzu tananan da kuďirin aurar da raihan wa 'yar Mai kuďi,acewar ta labiba bata da wani mamura........
*Love you all*
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
chaptar*0️⃣6️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,,,,Cikin nasara raihan yafara zuwa makaranta, yaune ranar sata farko dan haka cikin sauri yake gudanar da shirinsa,saida ya gama tsaf, sannan yayiwa innar da sallama, samun nasara tayi masa sannan ya fice.
Yana fita yaci karo da labiba tana laɓe akofar gidan,murmushi suka sakarwa juna cike da tsansar kauna,kallon sa tayi tace ina kwana ya raihan "
"Lafiya kalau yakike ?
"Lafiya kalau nake ,dama zuwa nayi na ganka kafin katafi.
,"aikuwa kin kyauta .
Salama sukayi kowa ya kama gabansa, raihan yana shiga cikin makarantar sauke ajiyar zuciya yayi yace, "Alhamdullah yaudai ALLAH yacika min burina na farko arayuwa ta.
Gindin bishiya yasamu ya sauna kasancewar lokacin lecture dinsu baiba, yana zaune yaji anyi masa sallama,amsawa yayi da mamaki afuskar sa,murmushi sadiq yayi yace, "sunana sadiq yaune ranata tafarko acikin makarantar nan,koma daga yanayin dana ganka nasan kaima haka?
Murmushi raihan yayi yace," haka ne.
Tun daga ranar abota Mai karfi yashiga tsakanin Raihan da sadiq, tun raihan yana ɗan basarwa harya ware,ganin yanda sadiq yake da natsuwa da rikon addini .
Labarin labiba sosai sadiq ke Shanta gun raihan tun yana jin daɗin ta harya koma yana jin haushi,daga zarar raihan ya fara tuni sadiq zaisan hanyar da zaibi dan ganin An canza akalar zancan.
Wata rana bayan sun fito daga lecture raihan yace, "gaskiya sadiq bakada kirki kullum Nike zaryan zuwa gidan ku,amma Kai shiru.
Murmushi sadiq yayi yace,"to naji tunda yanzun mun gama sai muji ai.
Murmushin jin daɗi raihan yayi sannan suka nufi gidan nasu.
Bayan sun gaisa da iyayan sa suka nufi gidan su labiba, cike da zumuɗin ganin hasken idaniyan ta tafito tsaf da ita.
Aikuwa tana fitowa suka haɗa ido, kasa ɗauke idanuwansa daga kanta Sadiq yayi dan gabaki ɗaya ta tafi da duk kannin imanin sa.
Gaishe shi take, amma gabaki ɗaya bai masan tanayi ba,cike da mamaki raihan yaɗan dungure shi yana tambayar sa,murmushi yayi haɗe da Sosa Kai yace, "hmm kaidai bari,gaisawa sukayi cikin girmama.
Hira suka shigayi saidai Sam sadiq hankalinsa Baya gurin asalima idan za'atambaye shi abinda suke cewa tofa baisan abinda zaice ba, ganin tunanin ta naneman dagula masa lilsafi yasa yace,"raihan zan tafi gida.
Da murmushi ta kalle shi tace, "haba ya sadiq tun yanzu zaka tafi?komawa yayi ya zauna yace, "yanda kikace kanwata.
Dariya duk kansu sukayi ganin yanda ya koma ya zauna babu musu.
Lokacin da sadiq ya koma gida gabaki ɗaya kasa sukuni yayi, duk lokacin daya ratsa idanuwan sa ita kawai yake gani tana mishi wannan murmushin nata Mai narkar da zuciyar da akayi domin ta.
Banda murmushi babu abinda zaka iya gani afuskar sadiq ,har garin ALLAH ya waye sadiq ko ritsawa baiyi ba.
Sadiq na tashi bai tsaya koina ba sai gidan su raihan, sosai raihan yayi mamakin ganin sadiq da sanyin safeya haka, koda ya tambaye shi cewa yayi, "kaine fa kullum Kake min korafin rashin zuwana gidan ku, yanzu nazo kuma yazama Abin magana.
Murmushi raihan yayi yace ,"a a nifa bance komai ba,inbanda abinka ainan ma gidan kune.
Shiryawa Raihan yayi yace, "to sarkin tunani saika tashi mu tafi,jin haka yasa ya miki cikin sauri Dan duk tunanin sa gidan su labiba zasu tafi kafin sutafi makaranta.
Ganin hanyar da raihan yabi batayi kamada tasu labiba ba yasa yace, "aboki waiya labarin RAI'ISH dinka ne?
Murmushin jin daɗi raihan yayi dan aduniya bashida abinso da kauna kamar yaji ana labarin labiba,hnmm kaidai bari naso muje can kafin mutafi amma gudun karkace na bat....
Cikin sauri sadiq ya janyo hannun sa yace, "mu.. mu..mutafi mana saboda ni zaka ki zuwa gurin masoyiyar ka akan wani dalili?
Kasa magana raihan yayi ganin yanda sadiq harwani rawa bakinsa keyi,kallon da raihan yake masa yasa yagane yayi katobara cikin dabara yace, "indai zuwana gidan ku shizai dinga hanaka zuwa gun RAI'ISH to wallahi bazan kara, zuwa ba, cikin sauri yafara tafiya yana addu'ar ALLAH yasa raihan bai fahimci komai ba.
Fisgo hannun sa raihan yayi yace, "haba aminina bafa abinda Kake tunani bane,to shikenan kayi hakuri mutafi na ganta sai mutafi ko?
Murmushi sadiq yayi yace, "ko kaifa"
Suna isa suka aika ayi kiran labiba,cikin mintina Kalilan saigata ta fito sanye da hijab,fuskarta babu kwaliya amma tayi kyau sosai.
Gaisuwa sukayi cikin girmamawa sannan suka shiga hirar su irinta masoya,shikuwa Sadiq komawa can nisa dasu yayi yana kallon yanayin da take wasa da kwayar idanuwan ta,lumshe su take cikin kwarewa,dafe kansa yayi yace, "Kai wannan yarinyar zata kasheni da soyayar ta.
Cikin sauri ya dake bakin sa yace, "wai menake shirin aikatawa ne? Wannan fa budurwar aminina ne, shin hakan da nakeyi yayi daidai kenan?"a a ba daidai bane,dan idan Nine akayiwa haka baxanji daɗi ba,cikin sauri yabar gurin batare da yayi musu sallama ba,.
Sukuwa basuma San yatafi ba, saida labiba ta Kalli gurin taga bayanan cikin sauri ta dubi sahibin nata tace, "ya raihan abokinka yatafi.
Mamaki sosai raihan yayi ganin babu sadiq agurin Dan haka cikin sauri sukayi sallama ya nufi makarantar.koda yatafi makarantar duk inda yasan zaiga sadiq duk yaduba amma babu shi.
Cike da damuwa ya koma gida, shakuwa sadiq yana barin gurin gida yanufa saboda wani irin matsanan cin ciwon Kai dake damunsa.
Yana shiga gida ya tarar da mummy zaune afalo hannun ta rike da liltafi da alamu karatu take.
Gaisheta yayi ya shige cikin ɗakin sa,sosai mummy ta fahimci akwai matsala atattare da ɗannata ,hakan yasa tanufi ɗakin nasa hannun ta rike da cup cike da ruwan sanyi.
Aikuwa tana shiga ta sameshi zaune abakin gadon sa sai share hawaye yake,cikin sauri ta isa gare shi, Sam ganin ta baisa ya daina hawayan da yake ji kamar bazata taba tsayawa adanuwan saba, saboda yanda yake jin kaunar labiba na ratsa cikin jijiyoyin jikin sa.
Da kyar mummy ta samu sadiq ya tsagaita da kukan da yake, rike hannun ta yayi yace, "wallahi mummy mutuwa zanyi mummy ki taimake ni,mummy labiba labiba nake so,dakatar dashi tayi tace, "kwantar da hankalinka ka faɗamin damuwar ka,wacece labiba?
Sanda ya gama bata labarin zare hannun tayi daga nashi fuskar ta kuwa tuni harta canza laune magana tayi masa da muryar da kana jinta kasan babu wasa acikin ta tace, "ban koyar dakai cin amana ba ALLAH shaida ne, sannan kasani baza'ataba haɗabaki dani ayi cin amana ba,koda kuwa rashin yarinyar yana nufin rasa rayuwar ka, wallahi bazaka taba auran taba.
Tashi tayi ta fice daga ɗakin rai abace,sosai maganar mahaifiyar sa takara rikirketa tunanin sa,wani irin jiri yake gani daga zaune tashi yayi da nufin zuwa gunta yabata hakuri,yana kaiwa bakin kofar ɗakin sa ya faɗi.
Da gudu mummy tayi kansa tana girgishi haɗe da kiran sunan sa, amma ina tuni ya daɗe da sumewa cikin sauri aka ɗauke shi sai asibiti koda likita ya duba shi yaga jinin sa ya hau sosai, faɗa yashiga yiwa mummy,ita kuwa banda hakuri babu abinda take bashi, koda abba yazo sosai shima yaji mamaki rashin lafiyar nashi.
Raihan kuwa da damuwar rashin ganin sadiq ya kwana shiyasa tun safe ya tashi ya shirya yanufi gidan su,mamaki yayi sosai lokacin daya ji rashin lafiyar sa, koda raihan yazo asabitin sadiq lumshe idanuwan sa yayi kamar yana barci, dan ganin sa na iya tayar masa da ciwan sa.
Raihan yaɗan daɗe sosai asibitin ,sannan yayiwa mummy sallama da alkawarin Dawowa anjima shida labiba.
Yana fita sadiq ya buɗe idanuwan sa,da mamaki mummy tace, "kenan dama ba barci Kake ba"
Nod da Kai kawai yayi hawaye na gangara ta gefen fuskarsa ,cikin sauri mummy ta karasa gunsa tace, "haba mana bafa asan namiji da saurin karaya ba, inaso ka dauka komai mukaddari ne daga ALLAH,kuma kowa yanada irin tasa kaddaran, dan haka nake so ka dauka irin take kaddaran kenan.
Murmushin karfi Hali yayi yace, "IN SHA ALLAH mummy nayi miki alkawarin bazan sake saka damuwar ta a raina ba,murmushi mummy tayi tace," that my lovely son.
Karfe 4pm raihan da labiba suka shigo cikin asabitin bakin su ɗauke da sallama, har cikin zuciyar sa yaji shigar Muryarta, da sauri ya buɗe idanuwan sa, da murmushi ya amsa sallamar.
Kujerar dake gurin ta zauna tana masa sannu,amsawa yayi idanuwan sa ker kanta,musabaha sukayi da raihan.
shagwaɓe Fuska tayi wacce ta Zama ɗabi'arta tace", ya sadiq shine katafi babu ko sallama?kasan halinda nashiga lokacin da danaji rashin lafiyar ka kuwa?waro ido tayi tana jiran jin amsar sa, shikuwa girgiza Kai yayi alamu a a, "Gyaďa Kai tayi tace, ""Hmm ALLAH dai yasa ba sanyin anguwar mune yasakar maka zazzabi ba?
Sosai duk kansu suke kallon ta cike da mamaki Dan bata fiya magana Mai tsayi haka ba,,"kiyi hakuri gani nayi kuna tsaka da soyayar ku Karna katsa ku.
,"Dan ALLAH karkace haka, AI lafiyar ka tafi komai.
Sosai maganar ta yayi masa daɗi,dan haka ya tashi yazauna sukasha hira,koda likitan ya shigo yasamu sadiq sai Hira yake harda Dariya,hakan yasa yace, "zasu iya tafiya gobe,godiya sadiq yayi masa, lokacin da raihan da labiba zasu tafi sosai sadiq yaji babu daɗi,amma babu yanda yaiya haka yanaji yana gani suka tafi.
Koda mummy ta dawo ta sameshi garau hakan yasa ta gane labiba tazo asibitin.
Washa gari kuwa likita ya sallame su haɗe da shawarwari.
Ko'awa ɗaya agidan baiyi ba,ya nufi gidan su raihan,farin ciki sosai raihan yayi daya ganshi,tashi sukayi suka nufi gidan su labiba.
Da haka shakuwa Mai karfi yashiga tsakanin labiba da sadiq koda yaushe suna tare su uku,tun Abin yana damun sadiq harya basar Dan yasan har'abadan bazai taba samun labiba ba.
Lokacin da labiba ta zana jarabawar ta,sosai suka tayata farin ciki, lokacin su kuma suna 3000 level,lokacin komai ya kwancewa raihan Dan babu kuɗi hannun sa sasoi yashiga damuwa,gashi bayaso labiba tasan halinda Yake ciki.
aikin gonar da yake danyi yana samun kuɗi tuni ya daina zuwa saboda zirgazirgar makaranta,gashi suna da projet da zasuyi, amma babu kuɗi cikin kankanin lokacin gabaki ɗaya raihan yafita daga haiyacin sa, tambayar duniyar nan labiba da Sadiq sunyi masa,amma amsar ɗaya ce,"babu komai.
Haka suka hakura suka zuba masa Ido,cikin sa'a labiba ta rubuta jam dinta,ganin nasarar da tasamu bakaramar farin ciki yasakata ba Dan haka cikin sauri ta nufi gidan su, raihan,tana zuwa kuwa bata samu Inna sadiya ba Dan haka ta shiga cikin ɗakin sa, tsayawa tayi kamar andasata sakamakon Shigowa da tayi ta samu raihan yana kuka harda jiyar zuciya.
Ďago Kai kawai yayi ya ganta tsaye hannun ta rike da takardar jam dinta, share hawaye yayi yanufi inda take tsaye,dakatar dashi tayi cikin sauri hawaye na zuba tace, "karka karaso raihan ,ashe dama banida wani matsayi agunka?ashe dama ba'abakin komai nake agunka ba? Nagode sosai da irin take halalcin daka nuna min.
Ƙokarin tsayar da ita yake, amma ina tana fita Tana share hawaye,tana kaiwa bakin kofar suka haɗu da sadiq,ganin ta ahaka bakaramar tayar masa da hankalin yayi ba....
Suna haka saiga raihan yafito yana sharce zufa,idanuwansa ya sauke ana labiba yana son karantar yanayin da take ciki......
( *S A J CE* 😍😍)
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
chaptar*0️⃣7️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,,,,,Da gudunta ta bar gidan,kallon kallo suka tsaya suna wa juna kafin Daga bisani suka shige ɗaki,har zuwa lokacin babu Wanda yayi wa ɗan uwansa magana,cikin dakiya Sadiq yake tambayar raihan abinda yafaru.
Ganin bashida wata sauran dabara yasa ya zaiyana masa duk abinda ke faruwa harda ɗaukar dawainiyar karatunsa da labiba take.
Sosai ya tausaya wa labiba rashin iyayanta da tayi nandanan yaji sonta da kaunarta na kara ruruwa acikin zuciyar sa.
Tashi sukayi suka tafi gidan dan bata hakuri amma Sam labiba ta kenkeshi ido tace, "baxata fito ba,haka Suka hakura suka tafi, ranar haka zukatan mutum uku suka kasance cikin kuncin rashin ganin walwalar ɗaya daga cikin su .
Garin ALLAH na wayewa labiba ta kunsa kuɗin da zatayi register makaranta ta aikawa raihan dasu,haɗe da gargadin karya dawo dasu,lokacin da yaga kuɗin farin cikin abu biyu yayi, na farko zaibiya kuďin project ɗinda zasuyi, na biyu kuma yasan ta sauko kenan tunda gashi harta aiko masa da sako.
Lokacin da raihan yanunawa Sadiq kuɗin data bashi sosai yayi mamaki, amma dai yayi shiru dan bayason yana musu shishigi acikin Al'amuran su.
Bayan suntashi ɗaga makaranta suka nufi gidan su labiba suna zuwa akace musu tafita,tambayar yaron yayi inda tatafi,"nima bansani ba amma cewa akayi Mai anguwa yake kiranta.
Jan hannun Sadiq yayi suka nufi gidan Mai anguwa,suna zuwa suka tarar da labiba zaune agaban Mai anguwa sai share hawaye take, cikin sauri suka karasa gunta,tambayar ta abinda ke faruwa raihan yayi .
Aitana ganin sa taji zuciyarta ta karye cikin kuka tace, "ya raihan kaji wai wannan gonar ta baba,waiwasu mutane sunzo sunce tasu ce,kawai sun baiwa baba amanarta ne kafin suje sudawo kasancewarsu 'yan Gabon.
Kallon Mai anguwa yayi ya bukaci jin komai abakinsa,abinda ta faɗa dai shine Mai anguwa yakara nanata masa.
Wani irin gumene yaji tana saukar Mai lokacin daya tunawa dayayi kuɗin da labiba ta
Bashi,tafaɗa masa cewa kuɗin Rabin gonar ta tsayar,to yanzo ina zasu samu kuɗi da zasu biya su.
Maganar maigari ce ta dawo dashi cikin haiyacin sa,yace,"to labiba kindai San kinzo kin bukaci asayar miki da Rabin gonar ko?babu musu na ɗauki kuɗi na baki,to yanzu yaya zamuyi da masu gonar kasancewar ansiyar musu da Rabin gona.
Ɗago Kai tayi hawaye na zarya tace, "duk yanda kace haka za'ayi.
Murmushi Mai anguwa yayi yace, "shikenan zamu duba gidan da kike ciki idan takai yawan kuɗinsu saimu sayar dashi, idan kuma yafi saimu San yanda za'ayi.
To kawai tace, raihan kuwa tashi yayi cikin fushi da nufin yin magana, cikin sauri labiba ta girgiza masa Kai, haka yanaji yana gani ta hanashi magana,tashi sukayi suka nufi gida,sadiq kuwa kasa magana yayi ko menene dalilin sa oho.
Suna isa gida raihan yashiga bata hakuri dan yasan saboda shine rayuwa take niman juya mata Baya, ita kuwa daidai da minti ɗaya batayi dana sanin taimaka masa da tayi ba, damuwar ta ɗaya ce,yanda za'ayi ta shiga makaranta.
Murmushi tayi lokacin data tuna da raihan ɗinta yayi makaranta kuma IN SHA ALLAH shine wanda zata aura,tasan sunayin Aure zai saka ta a makaranta,
Dan haka ta kwantar da hankalin ta, Washa gari ranar kuwa Mai gari da wasu mutane suka zo suka duba gidan.
Kallon labiba yayi yace, "mun gode ALLAH anduba kuma antabbatar da kuɗin ɗakuna biyu da ake haya acikin su zasu isa biyan bashin,dan haka yanzu ɗakin da kike ciki yanzu ita ka ɗaice mallakin ki, Dan haka saiki kula, godiya sosai tayi masa sannan suka tafi.
Koda raihan da Sadiq suka zo tafaďa musu yanda akayi sosai suma hankalinsu ya kwanta,dan Sadiq harya fara nima mata gida.
Rana bata karya saidai uwar ɗiya taji kunya,yauce ranar da sadiq da raihan suka kammala karatunsu afannin kasuwanci,karamar liyafa aka haɗa musu awajan makarantar,ranar kuwa bakaramar daga akayi da labiba ba Dan cewa tayi babu inda zata tafi, da kyar aka samu Tashirya zasu tafi.
Har sunyi nisa ta duba kunna ta taji babu ɗankunnei ɗaya,marairace Fuska tayi tace, "Dan ALLAH ya raihan kayi hakuri wallahi na mance bansaka ɗankunai na guda ɗaya ba .
Kallon ta yayi sannan yaduba agogon dake ɗaure ahannun sa ganin idan yace, "zai koma sosai zai bata lokaci, Dan haka yacire kuɗi yabata yace, "kiyi sauri kizo kisame ni kinji?
Nod dakai kawai tayi,sauri take kamar wacce zata tafi aikin haji, tana fitowa bakin hanya ta tari Mai adaidaita, shiga tayi ta zauna Tana tunanin yanda Zata shiga cikin ɗinbin Jama'a waigowar da zatayi ta hango mutane atare gawasu motoci duk glass din motar Suta fashe,hakannan ta tsinci kanta dason ganin abinda yafaru, Dan haka cikin sauri ta tsayar da mai adaidaitar.
Biyanshi tayi cikin sauri ta sallaka Titin, wata mata tagani akwance duk jikinta jini numfashinta sai kaiwa da komawa yake,ga ɗiyar ta can agefe sai faman tsalla kuka take, cikin sauri ta rinka ratsa cikin mutane,ruwa tagani kusa da matar cikin sauri ta buɗe gorar ruwan,daga kan matar tayi ta dura mata ruwan,cikin ikon ALLAH numfashin matar yafara sauka Ahankali.
Ganin haka yasa ta buɗi bakin matar ta hura mata iska, tari matar tashigayi cikin ikon ALLAH numfashin ta yadaidaita ,suna cikin haka saiga motar asibiti ta iso cikin sauri aka ɗauke matar aka sakata cikin motar, duban matar tayi saitaga Tana ɗaga mata hannu alamar tazo ,babu gardama ta nufi gunta, da kyar matar ta buɗe baki tace, "Dan ALLAH ko zaki iya taimaka min ki rikemin yarinya ta zuwa asibitin?
Murmushi labiba tayi tace, "babu damuwa cikin sauri ta karbi yarinyar daga hannun mai'katan asabitin suka shiga cikin motar, hannun matar sakale dana labiba harsuka isa asibiti,cikin sauri aka shigar da ita ɗakin taimakon gaggawa.
Wasa da yarinyar labiba tashiga Yi samtama mance da inda zata tafi,suna zaune saiga wani mutum Mai cikar zati yashigo cikin inda suke zaune kana ganinsa zaka gane wannan yaci kuɗi ya kwanta akansu yayi facaka dasu.
Yarinyar tana ganinsa tashiga Mika masa hannu kallon mutumin tayi wanda shima ita yake kallo,ganin batada niyyar bashi 'yarshi hakan yasa yamika hannun ya ɗauke ta,tuni zuciyar labiba yabata mijin matar ne kuma uba ga yarinyar.
Gaisheshi tayi cikin girmamawa,kallon ta yake dan natsuwar ta taburge shi,amsawa yayi sannan yayi mata godiya da irin taimakon datayi wa iyalansa.
Murmushi tayi tace, "babu komai
aiyiwa kaine"
,"To shikenan muje ki ganta ko"
Ɗakin huta da aka shigar da ita suka nufa,murmushi tayi lokacin da taga labiba, godiya sosai tayi mata sannan tace,"tafaɗi duk abinda take so IN SHA ALLAH sukuma zasuyi mata,kama daga nima mata aiki, kuɗi,makaranta,ko kasuwanci.
Nazari tashigayi dan gabaki ɗaya arikece take, wata zuciyar ce Tashaga bata shawarar karbar aiki idan yaso saita baiwa raihan,cikin sauri tace, "aiki nakiso asama min, saidai bani zanyi ba, Danni ban karasa karatuna ba.
Cike da mamaki hajiya tace, "to wanine wanda kike so asamama aikin?
Murmushi tayi tace, "ya raihan,jin yanda takira shida yaya hakan yasa basuyi wani dogon bincike ba, suka bata complimentry cad,
Cike da farin ciki ta isa gida,raihan tagani akofar gidan su fuskarnan tasa kamar an aiko masa da sakon mutuwa,tsayuwa tayi tana kallon sa dansai yanzu ta tuna da inda zata tafi ta haɗu da wannan baiwar ALLAH,murmushi tayi ta nufo inda yake buɗe baki tayi da niyyar magana.
Daka mata tsawa yayi har sanda complimentary cad dinda ke hannun ta yafaɗi,atare suka Kai hannun Dan ɗauka cikin zafin nama yarigata dauka, karanta sunan yayi , Waro ido yayi yace, "labiba Aina kikasan alhaji Mustafa Bello algaita ?
shiru tayi dan tsabar farin ciki ma baibari ta karanta sunan dake jikin takardar ba.
Shirun datayi ne yakara harzuka shi,
Yace, "wato abinda zaki min kenan ko? labiba bin maza kike koma yanzu Ashe?
Fashewa da kuka tayi jin yanda ya fassara maganar cikin kankanin lokaci ta shaidda masa,labarin yanda akayi ta san shi da alkawarin nima masa aikin da tayi tana gamawa ta shige cikin gida da gudu dan sam bataji daɗin yanda ya zargeta da bin maza ba.
Kasa motsi raihan yayi jin inda ake niman yakai takardun sa abashi aiki, kuma duk ta dalilin ta gashi yabata mata rai ta hanya jifanta da mummunar kalma kash....
*Love you all*
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_
https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial
*T. W. A✍🏻*
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*chaptar*0️⃣8️⃣
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*
,,,,,Farin ciki sosai sadiq yayi lokacin da raihan ya faɗa masa batun aikin.
Ranar da zaitafi gun alhaji Mustafa bello algaita,shirinsa Mai kyau yayi labiba harda masa rakiya dan tuni suka shirya.
Lokacin daya isa company nin sosai yayi mamaki ganin girman company,yana shiga kuwa cikin girmamawa aka karbe shi,da farin ciki ya iyaso gida,ranar Inna sadiya harda rawa tsabar murna.
Cikin ikon ALLAH sadiq ma a company ya samu aiki cikin nasara suka fara aiki, kasan cewar su hazikai haɗi da tsansar ilimi hakan yasa sukayi ta samun karin girma.
Lokacin da inna sadiya taga raihan yataka mukamin da take fatan ganin ya taka, tuni ta fara hure masa kunne,tun yana basar wa harya fara ɗauka,akullum takan Cemasa ,"yaron nan inaso kabuɗe idanuwan ka kasani yanzu kafi karfin wata labiba, kaduba yawan matan dasuke zuwa gidannan danyin kamun kafa dani, kyau, Sura, duk babu wacce labiba ta taka kafarta,dan haka tun wuri ka faɗa mata ta nime inda dare yayi mata.
Labiba kuwa kullum idan tayiwa raihan zancan auran su saiya ce, "haba saurin mekike,nifa nake ne RAI'ISH nakine mallakar ki, da haka yake samu yarufe mata baki, yaudai tagaji da abinda raihan yake mata Dan yanzu sai yayi sati bai zo gunta ba.
Ɗaukar wayar daya saya mata tayi takira Sadiq, daidai lokacin suna tare da raihan, da murmushi ya Kalli raihan yace, "RAI'ISH dinka ce Kekira fa"shareshi raihan yayi kamar baiji abinda yake faɗa ba, ganin wayar Tana niman yankewa yasa yayi sauri ya ɗauka,da sallama ta fara, sosai muryar ta yadaki kirjinsa lumshe ido yayi sannan ya amsa, gaisuwa sukayi sannan yace, "RAI'ISH yanaji muryar ki kamar baki da lafiya?
Cikin sauri tace, "a a ya Sadiq lafiya ta kalau, kawai dai dama sonake muyi wata magana dakai bansani ba ko kanada lokaci?
,"Eh yanzu dai aiki nake amma IN SHA ALLAH idan Natashi zanbiya ta gidan ku, duk maganar da yake idanuwan sa alumshe take shiyasa bansan lokacin da raihan yafita ba,da mamaki yake kiran sunan raihan amma shiru babu shi babu labarin sa.
Labiba kuwa fashewa da kuka tayi dan sosai halin raihan yake damun ta,bayan sallar isha kuwa saiga Sadiq, da farin ciki ta tarbe shi, lokacin data faɗa masa halinda ake ciki game da raihan sosai Abin yabashi mamaki dan shi shaidane kan irin soyayar dake tsakanin labiba da raihan.
Sallama yayi mata da alkawarin zaiyi masa magana.
Washa gari yana zaune a office dinsa saiga raihan yashigo hannun sa sarke dana wata yarinya wacce kallo ɗaya zakayi mata kaji kana da bukatar amai, duk jikinta Tasha Blechin ga wani gashin doki data Kara agashin ta, janbaki kuwa kamar wata maiya, gajeruwa ce saidai bacan ba,gata da kananun ido Kai bata da wani tsari.
Mikawa Sadiq hannun tayi tace, "Hy am zakkiya.
Wani irin kallo ya watsa mata wanda saida tayi saurin janye hannun ta, kallon raihan yayi yace, "wannan fa?
Murmushi raihan yayi yace, "zakkiya sunan ta matar da zan aura kenan, cikin fusata Sadiq ya miki yace, "wasa Kake ko raihan?
Murtuke Fuska raihan yayi dan dama ɗaurawa kawai yake da irin walakancin da sadiq yake masa akan wata labiba yace,"na taba yin makamanciyar wannan wasa da kaine?"wani irin Dariya Sadiq ya kece dashi harda dukan table din dake gaban sa, ganin yanda sadiq ya mayar dasu mahaukata hakan yasa raihan yaja zakkiya suka fita sai wani nannarkewa ajikin sa take.
Zama Sadiq yayi yama rasa abinda zaiyi, farin ciki zaiyi ko bakin ciki? Shikansa shaida ne kan yanda labiba take mattukar son raihan Dan haka babu wani dalilin dazaisa yayi farin cikin rabuwar su.
Tashi yayi yanufi gida shi kansa yarasa wani yanayi yake ciki.
Ita kuwa labiba ganin kwanaki sai ja suke, amma babu labarin raihan,hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa gidansu ɗanta duba ko lafiya.
Tana zuwa kofar gidan taci Karo da raihan da zakkiya suna fitowa daga cikin gidan,tsayawa sukayi suna kallon juna daga bisani raihan yaja tsaki ya ja zakkiya zasu wuce, cikin sauri labiba tasha gabansa da mamaki take kallon sa tace,"rai'ish baka ganni bane?
Muryar Inna sadiya sukaji daga bayan su tana cewa, "idan yaganki sai mee nace sai akayi yaya?
Sunkuyar da Kai labiba tayi tace, "kiyi hakuri Inna,"
Munafukar yarinya sai anyi magana tashiga bada hakuri kamar agidan su aka halaci hakurin, to bara kiji wallahi kuda wasa kika kara tako kafarki cikin gidannan saina Saba miki, yo inbanda abinki wani sakaran namiji ne zai Auri Mai zamar kanta,ɗago Kai labiba tayi cikin sauri jin abinda Inna sadiya take faɗa, matsowa gabanta tayi tace, "kin tsareni da ido koba haka bane?
Nod dakai kawai labiba tayi hawaye na zarya akuncin ta.haka
Tanaji Tana gani suka wuce suka barta anan, zakkiya kuwa harda gwalo tayi mata.
Da gudu labiba ta nufi gida kuka take da iya karfi ta duk inda ta wuce sai ankalle ta,zata shiga gida kenan suka haɗu da Mai anguwa tsayar da ita yayi yace, "labiba lafiya make faruwa?
Cikin kuka tace, "baba raihan ne wai bazai Aure niba, tana gama faɗan haka ta shige gida da gudu, murmushi Mai anguwa yayi yace, "hmmm dama ance ta yaro kyau take bata karko, na daɗe da sanin wannan ranar Tana nan zuwa, shiyasa nayi dabara na karbe komai ahannun ki,sai lokacin daya dace nabaki zan mika miki duk abinda kika mallaka labiba.
Ware ido nayi nace, "lailai Mai anguwan nan akwaika da farin dabara.
Kuka sosai labiba tayi har saida tagode ALLAH,babu irin hakuri da Inna Mairo bata bata ba, amma Sam saida tayi ya isheta sannan ta share hawayan ta,kiran Sadiq tayi ta shaida masa abinda ke faruwa sosai Abin yabashi mattukar mamaki dan duk tunanin sa raihan wasa yake.
Dubashi a office yayi akace yafita ,yana fita bai tsaya ko ina ba sai gidan su labiba, yanda yaga fuskarta sosai sadiq ya tausaya mata, hakuri yabata yace karta damu komai zaiyi daidai da yardar ALLAH.
Lokacin da Inna sadiya ta faɗawa malam sule maganar zuwa gidan su zakkiya nema masa Aure, sosai malam sule yayi mate faɗa kiran raihan yayi dan yaji ko mahaifiyar sa dole tayi masa, saidai buɗe baki yayi lokacin da yaji abinda raihan yake faɗa masa...
[6/13, 14:37] Safnah: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*DUK A SANADIN SOYAYA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
0 comments:
Post a Comment