,,,,,,, Da mamaki mummy tace, "kamar ya alhaji bangane ba?
Murmushi yayi ganin yanda duk yanayin su yacanza lokaci ɗaya,"wato hajiya nadaɗe ina tunanin mijin da zan aurewa ilham mai addini da rikon amana, domin ina tsoron kar rayuwarta tagaiyara .
" kullum banada fatan daya wuce ganin ranar auran ilham ko domin na sauke nauyin amanar dake kaina wanda na ɗaukar wa mahaifinta wanda kima kinsan da ita.
"tun ba yau ba naso na aurawa sadiq ilham, amma nayi tunanin kila ita ilham ɗin tana da wanda take so kartaga an tauye mata hakkin ta, to Ashe ALLAH cikin ikon sa itama tana sonsa.
Babu wanda yayi magana acikin su kowa da abinda yake tunani, Hafsah kuwa gabaki ɗaya tausayin yayan nata ne ya dabai baye ta, domin tasan tsananin sonda yake wa labiba.
ita kuwa mummy duk laifin ta kwashe ta ɗaura akanta ne ganin tun bayau ba sadiq yake mata maganar labiba, amma Sam taki bashi Fuska gashi tanaji tana gani za'a haɗashi da wacce Baya so, kuma babu halin magana ace ta goyi bayan ɗanta .
Gyara Zama tayi tace, "amm inaga yakamata aji ta bakin shi sadiq ɗin idan shima yana ra'ayin...
Ďaga mata hannu alhaji yayi ranshi abace yace, "ke Karki kawo mum shashancin ku irin na mata, zancan auran sa da ilham ɗinne harsai anji ra'ayin sa? To bara kiji wallahi ko yanaso ko Baya so sai anyi bakin nan da izinin ALLAH idan kuwa kikaga ba'ayi ba tofa ilham ce tace tafasa, amma muddun tana sonsa aura kamar anyi angama zancan banza, tashi yayi yafita yana maganganu.
Yana fita Hafsah ta fashe da kuka, tsawa mummy tayi mata tace, "Dan ALLAH fice min aɗaki Karki karamin damuwa ki barni naji da Wanda ke kaina .
Tana fita ta haɗu da labiba duk idanuwan ta sun kumbura sharce mijina Hafsah tayi tace, "aunty labiba fita zakiyi ne?
"a a tafiya zanyi Hafsah gidan mu zan koma, tafiya zanyi ko hakan zai kawo daidai tuwa atsakanin ku, naji duk abinda abba yace, "Hafsah ki Sani ALLAH ya jarabce ni da son yaya Sadiq asanda banyi zatto ba, sai gashi zuciya ta kamu banyi amuba ,gashi kuma Zamu rabu alokacin da banshiryawa Hakan ba,kukane mai karfi yaci karfinta.
"inama yaya kana nan kaji yanda aunty labiba take furta yanda take ji a game dakai nasan dasai kafi kowa murna da farin cikin jin wannan babbar albishir ɗin,amm kash ilham ta ɗauki almakashi mai karfi ta datse soyayar ku, kuka itama take aka rasa mai rarrashin wani acikin su,ahaka mummy ta fito ta same su hakan kuwa yayi daidai da shigowar sadiq.
Da mamaki duk suke kallon su mummy MA daurewa kawai take, amma tabbas tasan ta cuci ɗan nata ,"ke Hafsah menene haka sai koke koke kuke kun mayar da gidan kamar gidan mutuwa faɗan sadiq cikin dakiya.
Da gudu Hafsah ta faɗa jikin sa Tana cewa, "yaya albishirin ka?
Kallon ta yake ganin kuka take sosai amma take masa albishir,daurewa yayi yace, "goro amma kafin ki faɗa min saikin daina kuka kinji autar mummy.
Share hawayan ta tayi sannan tace, "yau aunty labiba da bakin ta yafaɗa min cewa tana sonka da Kai kawai zata iya rayuwa.
Da gudu labiba ta shige ɗakin Don Sam batasan cewa abinda Hafsah zata faɗa masa ba kenan.
Kasa magana yayi Don sosai maganar ta daki kirjinsa shikenan ALLAH yacika masa burin sa, maganar da Hafsah take shiya dakatar dashi daga zancan zucin da yake, "yaya Sadiq amma abba yace bakada mata aduniyar nan sama da aunty ilham shiyasa ma aunty labiba ta fitar da akwatinta wai zata tafi cikin daran nan.
Da gudu ya isa gaban mummy bakinsa har rawa yake yace, "mummy da gaski ne abinda Hafsah take faɗa ? "da gaskene abba dake bayan sa ya amsa yana karasowa inda suke "Eh dagaskine ilham zaka aura IN SHA ALLAH kuma yanzu daga gidan dangin mahaifiyar ta dake garin nan nake mun tsayar da rana nanda sati ɗaya rak.
Basuyi auni ba saijin karar faɗuwar mutum sukaji da dugu duk sukayo kansa banda abba da yayi shigewar sa ɗaki , cikin daran aka nufi asibiti da sadiq Don cito ransa.
Koda suka tafi basu wani sha wahala ba kasancewar sunyi waya tun kafin su isa, saida suka kwashe awa uku akansa kafin yadawo daidai ,kuka babu irin wacce labiba batayi ba tun mummy na kwantar mata da hankali harta hakura ta barta ganin da alama kukan ba ɗaya bani, suna zaune Dr yafito da sauri suka nufi gunsa, sharce zufar fuskarsa yayi yace, "hajiya anyi sa'a ya farfo saida ahalin da ake ciki sakamakon jin wani abu wanda baiyi zatto ba,na firgici ko akasain hakan ya janyo masa muguwar bugun zuciya mai tsanani idan badan kun hanzarta zuwa asibiti ba da ina Mai tabbatar miki komai na iya faruwa,amma yanzu cikin yardar ALLAH komai yadawo daidai barci yake.
Godiya mummy tayi masa,sannan suka zauna jiran tashinsa.
****
Bayan fitar su kuwa da gudu ilham tafito da niyyar binsu, daka mata tsawa abba yayi yace, "ina zaki tafi cikin daran nan?
"abba asibiti.
"maza koma ciki idan kika saki kafarki yataka asibitin nan sainayi kasa kasa dake shashasha Mara zuciya, sannan ki shirya idan akwai wani abinda zakuyi na mata keda kawayan ki kije ku fara shiri IN SHA ALLAH sati mai zuwa zan ɗaura auran ki da sadiq.
Wani tsalle ilham tayi Tana godiya ga ALLAH daya nuna mata wannan rana sosai take farin ciki shafta mance abba na zaune agaban ta, shikuwa kallon ta yake yana tuno yayan sa aduk lokacin da yake farin ciki tofa Baya iya boyewa ko agaban waye saiya nuna.
Haɗa ido sukayi da abba cikin sauri da kunyar da ita kanta batasan tana da ita ba saiyau ta shige cikin ɗaki .
Tashi abba yayi yanufi nashi ɗakin yau jinsa yake wasai ko babu komai zai cikawa ɗan uwansa alkawarin daya ɗaukar masa.
***
Raihan kuwa saida yayi kwana biyar sannan aka sallame shi ,yaɗan samu sauki daidai misali,gidan ta Inna sadiya ta tafi dashi tana bashi kulawa sosai baya zuwa ko ina gurin aiki MA sai aika musu da sakon rashin lafiyar yayi,sosai kuwa suka jajanta masa,tun Randa aka sanar da abba akwai asiri ajikin raihan kullum saiya amso ruwar Addu'a ana bashi yana sha sauran kuma yana wanka dashi.
Cikin ikon ALLAH kuwa sosai suke ganin waraka Don zuwa yanzu ya daina zaburar da yake yawan Yi.
***
Tun ranar da zakiya ta tafi asibiti bata kara zuwa ba har aka sallame shi, ranar data tafi aka tabbatar mata da ansallami shi, wani ubun ashariya ta kunduma ta fito bata isaya ko ina ba sai gidan inna sadiya....
" babu ko sallama ta shigo gidan, lokacin Inna sadiya tasaka shi agaba yasha kokon data dama masa, ganin zazkiya yasa ta Mike tana gyara ɗaurin zanin ta cike da masifa tace"uban me yakawo ki gida na?
Kallon gidan zazkiya tayi sannna ta kwashe da Dariya "har wannan gida ne?
"hmmm tsohowa akwai bukatar akaiki asibiti ayi miki wankin ido domin kuwa da alama cutar makanta taziyar ce ki....
Marin da raihan ya ɗauke ta dashi shiya dakatar da ita daga furta abinda tayi niyya, cike da mamaki take kallon sa, batayi wata wata ba ta ɗauke Inna sadiya da mari har sau biyu,aikuwa Anna raihan ya rufita da mahaukaciyar duka Inna sadiya na tsaye tana kallon sa, daidai lokacin abba yashigo da gudu ya shiga tsakanin su, zuwa lokacin kuwa zakiya ta jigata ko motsi bata iyawa da alama ta daɗe da sumewa, amma ina raihan ko Lura da hakan baiyi ba.
Cikin sauri Abba Y'a ɗebo ruwa ya watsa mata, sauke ajiyar zuciya tayi Ahankali take buɗe idonta harta buɗe gabaki ɗaya kuka Mai cin rai tafashe dashi da kyar ta miƙe zata fita, Juyowa tayi tace, "lailai kin aikata babbar kuskuri rayuwar ki da harkika sa ɗanki yayiwa y'ar alhaji danko irin wanna dukar...... saina shayar dake ruwar azabar da baki taba jin makamanciyar irin taba aduniyar nan.
Cikin ɗaga murya raihan yace, "kafin ki shayar da mahaifiya ta bara na shayar dake, nufota yayi da gudu tabar cikin gidan abba kuwa tsare gabansa yayi yace, "kafin ka shayar da ita inaso kafara shayar Dani,Buɗe baki yayi yace, "sannna kitafi nasakeki saki uku.
Kyawawan mari abba yayi masa amma yanda kasan bashi aka Mara ba, karshe MA rike Hannun abba yayi yana ta Marin kansa yana hawaye yana cewa, "Abb ka mareni abba nacancanci fiye da haka,,,, abba nayi mata butulci abba nasan kaɗan Kenan nafara gani.....
, domin kuwa inada tabbacin hakin labiba bazai daina bibiyata ba har karshan rayuwa ta.
Rungume shi abba yayi ganin kamar ba'a cikin haiyacin sa yake ba, yace, "ka daina faɗan haka raihan Bakayi mata komai ba itace MA ta zulumce
ka .
Zame jiki sa raihan yayi yace, "abba wallahi batayi min komai ba abba Zoka zauna nabaka labari,,,,,,
duk maganar da yake haryanzu cikin zubda hawaye yake, ganin haka yasa abba yazauna yace, "raihan kanaso na saurare ka?
"Eh Abba.
"to kayi shiru ka share hawayan ka, cikin sauri raihan yashiga share hawayan sa Abin tausayi, Zama yayi ya Faɗawa abba duk abinda yafaru tun daga farko har karshe, Abin mamaki hawaye nagani suna kwaranya afuskar abba,,,
,kallon Inna sadiya yayi wanda tunda aka fara maganar itama take zubda hawaye yace,"bantaba yin dana sanin saninki arayuwa taba sai yau, kin cuceni halima kin gurbata rayuwar ɗa ɗaya tilo da ALLAH yabani, halima wani irin halicci ne banyi miki ba?
"Mena aikata miki haka?
Kuka sosai Inna sadiya take Don tuni dana sanin abinda ta aikata yake damun ta saidai sanin babu hanyar gyarawa yasa ta zubawa sarautar ALLAH ido.....
Sosai Inna sadiya take kuka kamar ranta zai fita dana Sanin abinda tayiwa ɗanta gudan jinin ta take, tashi tayi tazo har gaban abba, rusunawa tayi akan gwaiwowinta bibbiyu tace, "kayi hakuri kamin aikin gafara nasan na aikata babbar kuskure, amma ina niman alfarmar adubi ALLAH amin gafara.
Ganin yanda Inna sadiya take kuka take niman gafara yasa raihan ya ɗagata yana share mata hawaye yace, "Inna indai nine wallahi nayefe miki duniya da lahira,ki daina kuka IN SHA ALLAH abba ma zai yafe miki kinji Inna?
Nod dakai kawai tayi tashige ɗakin ta zuciyar ta cike da dana Sani.
Zama kusa da abba raihan yayi yace, "Dan ALLAH abba karka kullaci Inna akan wannan maganar, IN SHA ALLAH labiba zata dawo gummu nayi maka alkawarin haka.
Ďago Kan sa abba yayi cikin sauri yace, "kayi min alkawari?
Murmushi raihan yayi yace, "IN SHA ALLAH.
"indai kuwa kamin haka ina Mai tabbatar maka har inkoma GA mahalilci na zankasance mai alfaharin kasancewar ka gudan jinina.
Tashi raihan yayi donyi wanka Sam baiga tazama ba.
Cikin mintina kalilan ya kammala shirinsa cikin shadda ruwar madara anyi mata ɗinkin zamani takalmin da hula Ya ɗauko baki yasaka wow nace lokacin da nayi ido biyu dashi,murmushi yayi yace, "aunty SAFNAH nayi kyau kuwa? Haɗa Fuska nayi nace, "gaskiya bansani ba kasanfa gabaki ɗaya fushi Muke dakai Don haka bazance komai ba, tsayawa yayi yana kallon na yace shikenan bara naje gun *aunty farida da teema gabs* nasan su zasu faɗa min lol😂 😂 😂
Fita yayi bayan yayi wa Inna Salama wani irin nisha&i yake ji kamar anbashi auran labiba,bai zarce ko ina ba sai gidan su sadiq Don yin duk wacce za'ayi Don wallahi babu wanda ya isa yayi masa shamaki tsakanin sa da abar kaunar sa.
*******
Gabaki ɗayan su babu Mai cewa da ďɗan uwan sa kala harsaida sukaji yafara salati, cikin sauri duk suka isa gunsa, babu abinda bakin sa ke ambata sai labiba, kallon labiba mummy tayi tace, "ki amsa kozai ɗanji daɗi sannu kaji ɗannan.
"yaya Sadiq ina jinka.
"labiba dan ALLAh Karki gujeni kisani babu abinda bazan iyaba idan hakan zaisa na mallaki ki amatsayin Matata, babu abinda bazanyi ba duk asanadin soyayar da nake miki wallahi kece macen da zan iya Zama da ita amatsayin mata labiba kice kina sona kozan samu saukin abinda nake ji.
Waigawa tayi taga babu kowa aɗakin Ashe duk sun fita Zama tayi kusa dashi tace,"yaya Sadiq nima inajin sonka fiye da yanda Kake jin sona, amma kasani bin iyaye tamkar bin ALLAH da Manzon sane Dan ALLAH ka daina damuwa, idan ALLAH yanufa ni matar kace kasani babu makawa, amma inaso kafin natafi kamin alkawarin yin biyayya ga duk zabin da iyayanka sukayi maka kaji YAYA sadiq?
Wani irin nauyi yaji akirjin sa jiyake kamar idan yabuɗe baki ya amsa mata bukatar ta lallai mutuwa kawai zaiyi,rike kirjinsa yayi da karfi kankace me tuni jini yafara fita ta hanci da kunnan sa.
Wani irin gigitatciyar kara labiba ta kwala tana kiran mummy,da gudu mummy tashigo ganin halin da yake ciki yasa tafita da gudu har takalminta na zamewa kiran Dr kawai take.
*ALLAH sarki uwa mabada mama uwa mahaifiya babu irinki aduk faɗin duniyar nan, shin da akwai Wanda zai iya jure Zafin fitar ɗa daga cikin mahaifiyar sa, sama da uwa Kuwa?kai babu ALLAH kasakawa iyayanmu mata da mafificiyar alkairi yasa aljanna tazama makomar kowacce uwa afaɗin duniyar nan rjf mother* 🙏🙏😭😭😭
Cikin sauri dr suka cika akansa Don ceto ransa, mummy banda kuka babu abinda take kiran abba tayi dakamar bazai ɗauka ba ganin kiran yaki karewa yasa ya ɗauka ,kukan tane yacika masa sa dodon kunne cikin sauri yacire wayar daga kunnan sa, yanda take magana kaɗai yaisa shaida maka ba'acikin haiyacin ta take ba, katse wayar yayi yaɗauki makullin motar sa yanufi asibitin duk da kuwa 11pm daidai alokacin.
Yana isa asibitin da gudu mummy ta rungume shi tana kuka kamar ranta zanfita tace, "alhaji idan harzaka iya tuna halalcin danayi maka arayuwa tun daga auran mu harzuwa yau, idan zaka iya tuna cewa duk tsayin shekarun nan da muka ɗauka bantaba yimaka gardama akan duk wani abu da kake ganin shine daidai akan yaran nan ba,dan ALLAH kabar sadiq yazabi wacce yake so ya zauna da ita amatsayin mata ,Tana kaiwa nan tasake shi takoma can gefe tana sauke jiyar zuciya.
Sosai yaji tausayin ta lokaci ɗaya yayi dana sanin abinda ya aikata musamman yanda yaga Dr sai fita suke suna komuwa duk akan sadiq, rike kansa yayi saboda wani irin Sara masa da yake,kujerar dake gefinsa yasamu yazauna yana tunanin mafita.
Sai kusan 2am Dr suka fito daga ɗakin kusan su rai biyar kowa ka kalla acikin su kasan bakaramar jigata sukayi ba, cikin sauri Abba yanufi gunsu , ɗaya daga cikin Dr faɗa sosai yashiga yiwa abba kamar zai dake shi Sam baiyi LA'akari da yawan shekarun Saba.
Abba banda hakuri babu abinda yake bayarwa,haka suka kwana cikin zulumin rashin farkawar sadiq , 7am abba yaja motar sa bai tsaya ko inaba sai unguwar su labiba, yana zuwa bai zance koina ba sai kofar gidan mai auguwa ,Tarba mai kyau akayi masa sannan mai unguwa yake tambayar sa labiba.
Murmushi yayi yace, "lafiyar ta kalau ai zancan tama nazo maka, tiryan tiryan abba Ya kwashe komai dake faruwa yafaɗa masa, sosai mai anguwa yayi masa nasiha da nuna masa kuskuran daya tafka, nandai abba yanime alfarmar yana so aɗaura auran labiba da Sadiq alokacin domin yana ganin hakan shine kawai zai kawo samuwar zaman lafiya.
Sosai mai anguwa yayi farin ciki da hakan, cikin kankanin lokaci mai anguwa ya Tara dattijawan unguwar aka ɗaura auran labiba da Sadiq,saidai muce ALLAH yabada Zama lafiya.
Cike da murna da farin ciki abba yanufi asibiti, daidai lokacin sadiq ya farfado Dr suna kara dubashi Don gani babu wata matsalar data sake bulluwa.
Ganin yanda yake farin ciki yasa mummy ta matso gunsa tace, "alhaji lafiya naga kamar kana cikin farin ciki ?
Murmushi yayi yace, " hmm Kedai bari nayi abinda nake ganin yafi dacewa damune.
"kamar me kenan ?
"ALLAH cikin ikon sa yanzu aka ɗaura auran sadiq da labiba.
Ďago Kai labiba da Hafsah sukayi lokaci ɗaya jin abinda abba yake faɗa ,da gudu Hafsah ta rungume abba tana mai nuna tsansar farin ciki ta,labiba kuwa fashewa da kuka tayi Wanda ita kanta bazata iyacewa ga dalilin Saba ,matsowa gunta mummy tayi tace, "Meyasa kike kuka maimakon nuna godiyar ki ga ALLAH daya nuna miki wannan rana labiba Kodai kin daina son sane?
Girgiza Kai tayi tana sunne kanta cikin hijabin ta, da gudu Hafsah ta shiga cikin ɗakin duk da kuwa cike take da dr, amma ko kallon su batayi ba, rike hannun Sadiq tayi Wanda kallo ɗaya zakayi masa kasan yana jin jiki tace, "bro katashi ciwan ka ya warke bro kabuɗe idon ka, " anɗaura auran ka da labiba yanzu abba yadawo bro kana jina?
Buɗe idonsa yake Ahankali harya buɗe su akanta kara maimaita masa maganar tayi, wani irin fisga yayi mata yana cewa, "da gaske kike Lil sis? Da gaske kike yanzu labiba tazama Matata?
Nod dakai tayi hawaye nabin kuncin ta, Zara ruwan dake hannun sa yayi duk da ƙoƙarin da dr suke Don Ya tsaya, amma ina sai fisge jikin sa yake, ganin haka yasa Hafsah ta fita ta kira abba, daka masa tsawa abba yayi yace, "me haka maza koma kazauna ko kuma nasa awarware auran.
Da sauri sadiq yakoma Ya kwanta yana jin yanda zuciyar sa ke bugawa da karfi.
Mayar masa da drp ɗin Dr yayi, sannan suka fita suna tsokanar sa ganin yanda Komai ya Zama normal cikin kankanin lokaci,bayan fitar su shafe fuskar sa abba yayi idon sa cike da hawaye ganin yanda ɗan nasa yakoma lokaci ɗaya yace, "ka gafarta min nasan nine sanadiyar kasan cewar ka cikin wannan halinka gafarta min .
Zama Sadiq yayi yace, "Kai Ubane agareni, nine yakamata na nime gafarar ka akan bijire maka danayi kayafe min Abba,share masa hawaye abba yayi yace, "maza daina kuka Aure ne anrigada an ɗaura saika kwantar da hankalin ka kuma ni Bakayi min komai ba, idan makayi min to nayefe maka ALLAH yayi muku abarka.
"Ameen abba.
Tashi abba yayi yana fita Ya umarci labiba data shiga suyi magana, cike da kunya tashiga ɗakin tana jinta kamar wata sabuwar halilta,wani irin kayatatciyar murmushi sadiq ya aika mata dashi yana jin inama babu ruwa ajikin sa dafa babu abinda zaisa yakasa tashi ya rungume abinsa......
*Tofa muje zuwa muji yanda zata Kaya tsakanin sadiq da ilham, wani Hali raihan zai shiga bayan yaji ɗaurin Auren labiba da Sadiq aminin sa?*
*Ku biyo ni donjin yanda zata kasance taku har kullum*
_Jawabi_ 💐
[6/13, 14:39] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*
*STORY*
*&*
*WRITING*
*By*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
2⃣2⃣➖2⃣3⃣
*Bismillahi rahamanin rahim*
,,,,,, Cikin kwana biyu aka sallame su daga asibiti idan kaga sadiq bazaka taba cewa yayi ciwo ba, domin kuwa har wani y'ar kiba yayi, Gida suka nufa gabaki ɗayan su.
Ilham kuwa Shirinta take tsaf tayi wani irin kyau da cika tun daga ranar da abba yayi mata albishir bata kuma Zama agida ba, kullum tana cikin kaiwa da komuwa,cike da farin ciki ilham tafito, Zama tayi agefe, gaishe su tayi,sannan tayi masa yajiki?
Amsawa yayi da fara'ar sa abinda yabata mamaki kenan nandanan taji wani irin farin ciki yamamaye ta, tashi tayi da niyyar Shaga ɗaki, kiran ta abba yayi.
Da ladabi ta amsa kanta akasa tace,"
Na'am abba.
"Samu guri ki zauna .
Komawa tayi ta zauna kamar yanda ya umarce ta gyara murya abba yayi yace, "aiya sanina duk kanku nan kuna karkashin iko Nane,don haka inada damar da zanyanke hukuci kuma dole abita koda anaso ko akasin hakan.
"Dake zanfara ilham, inaso kisani kin aikata babbar kuskuri wanda banyi zatton zaki iya aikatawa ba bisaga LA'akari da irin tarbiyar dana ɗauraku akai,ALLAH shine shaida na koyar dake yanda zaki kaunaci mutane da girmama su aduk halinda kika tarar dasu, amma tun ba'aje ko inaba kin baɗamin kasa a ido hakan da kikayi min kin kyauta kenan?
Kasa tayi da kanta batare data furta komai ba, "Don haka yanzu inaso kibawa yayanki hakuri sannan kibawa labiba.
"gyara Zama tayi tace, "kayi hakuri yaya IN SHA ALLAH hakan bazata kuma faruwa ba, aunty labiba kema kiyi hakuri shairin zuciya ce.
Komai ya wuce duk sukayi mata sannan abba yaci gaba, "Alhamdullah bayan haka inaso na shaida miki an ɗaura auran sadiq da labiba yau kwana biyu kenan da faruwa hakan, rike kirjin ta tayi cikin sauri jin yanda ta buga lokaci ɗaya , tsaf abba yana Lura da yanayin data shiga cigaba da magana yayi batare daya kuma kallon inda take ba, "kuma hakan danayi bayana nufin fasa auran kida shi bane, kamar yanda kikaji nafaɗa IN SHA ALLAH ranar juma'a za'a ɗaura auran ki dashi,ina fata zakuyi zaman lafiya da juna, kuri ke juna da amana idan kuka min wannan alfarmar lailai zanyi alfahari daku.
Shiru falon yayi kowa da abinda yake sakawa aransa can abba yace, " ko kana da ja akan hukuncin dana yanke?
Cikin sauri sadiq ya ɗago Kai harbakin sa na rawa yace, "duk abinda ka yanke banida ja akai IN SHA ALLAH zanyi biyayya ga duk kannin umarnin ka.
"to Alhamdullah sannan inaso ka ɗauki labiba ka kaita gidan idan da wani abu datake da burin Yi sai tayi, za'akawo kayan lefe IN SHA ALLAH ranar juma'a kuma zata tare.
Ahaka kowa ya tashi donyin ɗan abinda baza'a rasaba, akwatin ta labiba ta ɗauko suka nufi anguwar su, amota gabaki ɗaya kasa sakewa tayi sai wani boye Fuska take, sadiq kuwa jiyake kamar anbashi kyautar gidan aljanna, gefe gudu kuwa tanadin azabar iri iri dazai ganawa ilham yake, da wannan tunanin suka iso kofar gidan.
Da mamaki duk suke kallon kofar gidan ganin wani makeken gida da aka Gina mai kyau da tsari harda get,juya motar sadiq yayi zuwa gidan mai anguwa, cikin farin ciki mai anguwa ya tarbesu, Zama sukayi aka kawo musu ruwa sadiq ne kawai ya iya SHA amma labiba akage take taji dalilin da yasa aka sayar mata da gida.
Murmushi Mai anguwa yayi jin tambayar da labiba tayi masa miƙewa yayi mintana biyu tsakani sai gashi yadawo hannun sa dauke da wata bakar jakka ,Zama yayi sannan yamika mata,kallon sa take cike da mamaki.
Gyara Zama yayi yace, "da farko inamai baki hakuri kan maganar dana faɗa miki dangane da gida da gonar da mahaifinki yabari, idan baki mance ba nafaɗa miki cewa gonar banashi bane gonar wasu baturar ne suka bashi amanar kula musu dashi, to azahirin gaskiya nafaɗa miki haka ne kasancewar naga kina shirin tafka babbar kuskure,gona da gida dai gonar mahaifinki ne, kuma tun daga Randa yabar gidan duniya nashiga kula miki da gonar cikin gaskiya da rikon amana, har zuwa yau da kike da company na kanki, Mai ɗauke da sunan ki, cike yake da ma'aikata ɗari biyu da ɗori,gida kuma naki ne duk bayanan da kike da bukata sani yana ciki zaki iya dubawa .
Sannan wannan bawan ALLAH da kika taimakawa matar shi shekarun Baya harda taimakon sa kika Kai matsayin da kike ayanzu.
Tunda mai Unguwa yafara magana labiba take kuka harya Kai karshe, rasa bakin da zata gode masa tayi, suna cikin haka suka fara jiyo hayaniyar mutane maso kuka nayi, gabaki ɗaya gurin ya hautsune, fita duk kansu sukayi Don ganin abinda ke faruwa ido biyu labiba tayi da gwagwonta Larai da gudu ta faɗa jikin ta, kuka suke sosai aka rasa wanda zai Bawa wani hakuri atsakanin su.
Lokaci mai tsayi suka ɗauka ahaka daga Baya mai anguwa yayi musu bayani duk abinda yafaru da halin da aka ciki ,sosai suka tausaya wa labiba sannna sukayi wa mai unguwa godiya akan ɗawainiyar da yayi da labiba ,nandai aka shiga gaisuwa da jajantawa juna, ciki da farin ciki suka nufi gidan da ayanzu yakasance mallakin labiba, shirin auran suka fara gadan gadan, cikin kankanin lokaci suka gama siyan duk abinda zasu siya na ɗaki .
Biki sosai yayi armashi, Amare sunsha gyara sosai, idan bawai kasan labiba bane idan ka ganta bazaka taba gane taba.
Ranar kuwa karamar hauka raihan yayi Don faɗa yarinka Yi da mutane gabaki ɗaya idan kaganshi zaka ɗauka zautatce ne,saida Inna sadiya ta keto cikin mutane tana kuka ta janye shi sai gida, agida MA saida abba yasa aka kulle shi aɗaki ,gabaki ɗayan rana labiba da kuka ta yini duk yanda akayi tayi shiru fir tanuna batasan zancan ba, saida aka kira sadiq aka faɗa masa, zuwa yayi har cikin gidan ya janye ta zuwa wani karamin ɗakin dake cikin gidan, rarrashinta yake amma kamar ana kara tunzura ta, ganin tana neman caza masa Kai yasa ya haɗa bakin su guri ɗaya .
Kiciniyar kwatar kanta take amma ina wani irin kissing ɗinta yake with fashion ,gabaki ɗaya jikin ta rawa yake yana sakin ta kallon ta yake ganin yanda idonta yacanza kala,murmushi yayi yace, "kina son kari ne?
Girgiza Kai tayi hawaye na zuba, "yace maza share hawayan ki ,cikin sauri tashiga share hawaye,da gudu ta koma cikin gida toilet ta shiga ta tsaya gaban mirro tana taba bakin ta murmushi tayi tace, "lailai akwai babar matsala.
****
Ilham kuwa tana cike da bakin cikin kasancewar labiba amatsayin kishiryar ta, haka dangin mahaifiyar ta suka rinka zugata,aikuwa tsaf ta hau ta zauna.
Sadiq kuwa ɗan kibewar da sukayi gabaki ɗaya jiyayi ilahirin jikin sa gabaki ɗaya ya mutu wani irin sha'awace mai karfi ke fisgar sa, ɗaukar motarsa yayi bai tsaya ko inaba sai gidan sa watsa ruwa yayi ya kwanta sauran abokansa MA haka suka hakura suka wuce batare da sunga Ango ba
Sai kusan 4 sadiq yafito daga gidan, yanufi family house duk hankalinsa nakan amarya sa, koda ya isa jama'a harsun fara watse wa, shiga yayi ya gaisar da mummy da sauran jama'ar dake gurin, bai tsaya bata lokaci ba yafita ganin yanda duk suka sakoshi gaba da zolaya.
Labiba kuwa tana can cikin dangi anata barkwanci, kiran Sadiq ne yashigo wayar ta cikin sauri ta ɗaga tare da mikewa ta shige ɗakin ta, shiru tayi Batace komai ba shima haka, saican yace, "princess har yanzu kukan kike?
"a a.
"to shikenan IN SHA ALLAH yanzu za'a kawo miki kayan da zaki saka na dinner da za'a tafi, amma Dan ALLAH banda irin wanna kwalliyar da akeyi wacce take mayar da fuskarku kamar ta aljannai kinji tawan?
"IN SHA ALLAH.
****
Misalin shida motoci ne suke jiro reras acikin gidan aka kwashe masu zuwa aka tafi dasu, da kansa sadiq yaje ya ɗauko labiba, kuda suka iso gurin tuni ilham ta daɗe da zuwa Dan haka bakaramin baƙanta mata rai zuwa ɗauko labiba da Sadiq yayi ba, hannun sa sarke da juna suka fito daga motar har zuwa inda ilham take ,Murtuke Fuska sadiq yayi ganin yanda take bin labiba da muguwar harara,ita kuwa murmushi ne sosai akan fuskar ta.
,"malama idan kin gama Harare hararan zaki iya zuwa ki samemu aciki yana gama faɗan haka yayi gaba, ganin da gaske yake yasa tayi saurin riko hannun sa, ahaka suka shiga ciki sai wani no noke masa take.
So sai gurin ya kayatu haka aka tashi kowa cike da farin ciki ,wanna karan a motar sa yabɗauke su saida yafara sauke ilham tukunna sannna yanufi gida da labiba, batare da bata lokaci ba ya sauke ta,wanka labiba tayi dan nanda ɗan lokaci za'azo ďaukar amarya, Shirinta saftayi cikin farar shadda doguwar Riga, ahaka aka zo aka ɗauke ta sai gidan sadiq tayi kuka sosai na rashin iyayan ta.
Gidane mai masifar kyau part biyu ne agidan da alama komai na cikin gidan iri ɗaya ne, domin harda peint iri ɗaya ne, basu wani zauna ba sukayi mata sallama da fatan zaman lafiya mai ɗaure wa ,bayan fitan su aka shigo da ilham, tana zaune taji shigowar sa, gyara gyalanta tayi daidai lokacin yashigo da Murmushin sa, Zama yayi kusa da ita yace,"amarya ta.
Gara gyara zamanta tayi Tana murmushi kasa kasa, hannun sa yakai zai yaye gyalan cikin sauri ta rike gam,hayewa gadon yayi suka shiga Kiciniya rike da gyalan, Basu Ankara ba sukaji an banko kofar cike da firgici suka juya suna kallon kofar ,ilham ce da kawayan ta duk kansu hannun su rike da zabga zabgan bulala.
Waro ido yayi gabaki ɗaya yama kasa furta ko kalma ɗaya , ilham kuwa gabaki ɗaya jikin ta banda rawa babu abinda yake, Sam batayi tsammanin ganin saba.
Mikewa yayi Aida gudu suka bar gidan, ilham hartana faɗi da gudu suka shiga ilham harda saka key akofar, kuka tafashe dashi tana cewa kingani ko sha'awa wallahi saida nace kar muje kikace muje gashi yanzu yagammu yakike so nayi yanzu?
" wacce ake cewa sha'awa cike da masifa tace, "malama Karki yarda ki ɗauran laifin akaina, danace muje janki Naye koda kafarki kika tafi?
cikin kuka tace, "haka MA zaki ce ko?shikenan,ɗaya daga cikin sune tazo tace me kuma Abin faɗa anan? kuskure ne munyita gabaki ɗaya Dan haka babu lokacin faɗa ku matso kuji yanda za'ayi, haɗa kansu sukayi sukayi kuskus wanda ni kaina banji abinda suke faɗa ba saidai kawai ganin su nayi sun fashe da Dariya, cikin sauri suka bar gidan ilham kuwa zuciyar ta Fes tayi wanka ta kwanta .
Sosai hankalin labiba yatashi tunina kawai take da sunzo babu sadiq ALLAH kaɗai yasan abinda zasuyi mata ,gabaki ɗaya jikin ta ya ɗauki rawa, Shikansa sadiq Abin bakaramar mamaki yabashi ba, haka yashiga rarrashinta da ƙyar yasamu natsuwar ta yadawo, wanka sukayi sannna yasa tayi alwala, tunda taji haka gabaki ɗaya jikin ta yayi sanyi, yalura da hakan amma sai ya basar Don bayaso takawo masa warge.
Salla raka'a biyu sukayi sannan yayi mata Addu'a kamar yanda muslumci ta tanada,ciro mata night dress ɗinta yayi ya miƙa mata fuskarsa babu yabo babu lallasa ,cike da kunya ta karba toilet tashiga ta canza kayan,hijabinta ta ɗauko ta ɗaura asaman kayan, koda tafito babu komai ajikin sa sai boxes ,rintsa idonta tayi, murmushi yayi cikin zuciyar sa yace zaki Sani ne.
Cikin sanɗa taƙarasa kamar wacce zatayi Sata haka takarasa ta kwanta Ahankali tana ratsa ido dan karya ji motsin ta, saida ta kwanta harda Addu'a ta hura akowani kusurwa sannna ta kwanta,saida yaji kamar taɗan fara barci sannna ya matso tare da janye zanin gadon data rufa dashi
.
hannun sa yasa yafara yawo dashi a saman fuskar ta ,cikin barci taji kamar ana shafarta cikin sauri ta buɗe ido zatayi ihu yayi saurin haɗa bakin su guri ďaya, hannu yasa yakunna hutar ďakin, ganin shine yasa tasauke jiyar zuciya tare da kwakari janye bakin ta, ina babu dama domin kuwa kissing ďinta yake cikin kwarewa har yana lumshe ido.
*Ni kuwa ina ganin haka nafita da gudu don kuwa nasan tabbas yau sadiq bazaiji rarrashi ba*
Saida yasamu natsuwa sosoi sannan yakalli fuskarta wanda tuni idonta suka kafe guri ɗaya kiran sunan ta yayi yaji shiru nanfa hankalinsa yayi masifar tashi, ruwa yadebo yashafa mata afuskar amma ina, cikin kankanin lokaci sadiq yanime fita daga haiyacin sa, kaya ya saka mata shima ya saka tashi, cikin sauri ya ɗauke ta sai asibiti....
*Always remember SAFNAH ALIYU JAWABI will always love you*
💐. *Jawabi ce* 💐
[6/13, 14:39] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
❄❄❄❄❄❄❄
*STORY*
*&*
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
2⃣4⃣➖2⃣5⃣
*Bismillahi rahamanin rahim*
,,,,,, Gudu kawai yake cikin mintina kalilan suka isa asibitin, cikin gaggawa aka nufi emergency room da ita duba time yayi yaga kusan 1am dukka kansa yayi da hannun sa Yana cewa, "why sadiq menene Abin sauri?
"" maybe wannan bashine lokacin daya dace ba, Innalillahi wa'innailaihi raji'un ALLAH kataimake ni,kusan awa dr suka kwashe kanta sannna suka samu suka tsayar da jinin bayan anyi mata ɗinki har biyu,rike baki nayi nace ,"lailai sadiq kayi barna.
Fitowa Dr fauziya tayi Tana sharce zufa da sauri yanufi gunta yace, "Dr dafatan ansamu nasara?
Nuna masa tayi daya sameta a office ɗinta , Kujerar dake fuskantar ta yaja yazauna yace, "ina sauraron ki Dr.
Saida ta gyara zaman glass dake fuskarta tayi tace, "kaine mijinta?
Shiru yayi gabaki ɗaya yama rasa abinda zai faɗa saican Ya haɗu kuzarin sa yace, "nine Dr ina fatan lafiya daiko?
"Eh lafiyar kenan saidai kasani kayi babbar kuskure waye faɗa maka haka ake Bida mace?
"wallahi kuskure aka samu Dr, amma yanzu Dan ALLAH kifaɗamin halin da take ciki kodon Nasamu natsuwa Dan ALLAH.
Hmmm tayi sanna tace, "kwantar da hankalin ka cikin yardar ALLAH mun Shawo kan Al'amarin saidai Dan ALLAH adinga kulawa gudun samun matsala, wannan bawani abu bane kasancewar ta sabon shiga shiyasa akan takasance IN SHA ALLAH koda wani lokaci daga yanzu zata iya farkawa.
Godiya yayi mata sannna yanufi ɗakin da take kwance,yana shiga ta farka, kura masa ido tayi Tana ƙokarin tuno abinda yafaru ,cikin sauri ta ɗauke idonta daga kansa tuno abinda yayi mata, cikin sauri yakarasa inda take yariko hannun ta cikin sauri ta shiga Kiciniyar kwacewa, amma ina karfi ba ɗaya ba,riketa yayi gam yana cewa.
"kiyi hakuri ruhi na kisani banyi domin cutar da keba,dan ALLAH Karki juyan Baya kice komai nawa Inna sonki fiye da kaina labiba na sakar miki linzamin rayuwata kijata ki kaita duk inda kike so, amma kimin alfarma Karki rabu Dani wallahi kece duniya ta.
Juyowa tayi ga mamakin ta sai ganin hawaye tayi wani na korar wani, cikin sauri ta tashi zaune itama rikeshi tayi Tana hawaye Dan sosai take jin zafin akasarta tace, "koda abinda kayi min yafi haka muni kasani bazan taba iya rayuwa babu kaiba ,zanyi maka komai duk asanadin soyaya.
Rungume ta yayi yana sunbatar ta tako ina,janye jikin ta tayi tace, "banfa warke ba, cikin wasa yace, "a a Dr tace idan nayi ma hakan zaisa ki warke da wuri, "a a nifa bance ba karka kaini.
Cikin sauri duk suka juya Dr ce atasaye tana kallon su cike da burgewa tace, "ke kuma amarya haka ake saiki bige da doguwar suma?com on Karki bada mata kizama jaruma agun mijinki Karki bari kizama lusara,aduk lokacin da yake ƙokarin faranta ranki kema kiyi ƙokarin faranta ran nasa kinga kenan kum faranta ran juna,,,,,,
"Karki tsaya ki sake jiki miji yayi miki komai a a ƙwaƙarta kema kina nuna irin nake salon kina duk abinda yake da bukata kina bashi bazaki gaji da wure ba balle ayi maganar jin ciwo irin haka Dan ALLAH mata kiyaye.
Tana gama faɗan haka tafice tabar labiba da rufe Fuska Don sosai taji kunya.
*****
Zakiya kuwa tunda tafita daga gidan tanufi gida zuciyar ta ke azallalar ta data ɗauki fansar abinda Inna sadiya da raihan sukayi mata, koda tafaɗawa mummyn ta sosai ranta yabaci, cikin izza da nuna isa tace, "wallahi yayi kaɗan ya wulakanta min Y'a saina shayar dasu maɗacin da harsu mutu bazasu daina jin ɗacin Saba, ki kwantar da hankalin ki gobe zamuje gumau karamar hukumar bauchi garin *yar yaddiko* akwai wani atsabibin boka Zamu tafi gurin sa Dani yake zancan.
****
Raihan kuwa haka ya kwana yana kuka da faɗa faɗe cikin kwana ɗaya gabaki ɗaya yagama fita daga haiyacin sa idan kaganshi saiya baka tausayi, Inna sadiya kuwa tayi nadama yafi dubu, gashi malam yaɗauke mata huta koda Gaishi shi tayi Baya amsawa itama gabaki ɗaya tafita daga haiyacin ta, bayan sati ɗaya Inna sadiya tana zaune yafito yayi wanka yasaka kayan sa Alhamdullah yau bakamar kullum ba.
Zama yayi kusa da ita bakin sa ɗauke da sallama, amsawa tayi tace, "Alhamdullah ALLAH Nagode maka, kallon raihan tayi tace,"ɗan nan ina Kara jadada rokona agunka Dan ALLAH kayi... Cikin sauri yarike hannun ta yace, "umma ke uwace nasan duk abinda kikayi kinyi ne Don samawa ɗanki farin ciki ne, nasan bazaki taba yin wani abu Don cutar da niba,don haka Karki damu komai yawuce duk Dan Adam yana da tasa irin jarabawar nikuma kalar tawa kenan.
Share hawayan sa yayi yace, "umma ina rokon wata alfarma agunki narigada nayi magana da abba kuma ya aminci Don haka yanzu ke kaɗaice nake jiran amincewar ki.
"ina jinka ɗannan faɗi bukatun ka ina sauraron ka.
Gyara Zama yayi yace "Legos Nike so nakoma da aiki na,inaso nabuɗe sabon babin rayuwa ta acan,inso namance da rayuwar danayi abaya inaso nayi move on Dan ALLAH umma karkice a a.
"hmm babu komai ɗannan na amince indai hakan zai sakaka cikin farin ciki to na aminci ALLAH yatsare gabanka da bayan ka, IN SHA ALLAH bazaka taba tabewa ba, duk abinda kataba saiya Zama alkairi agare ka da duk wanda yake kusa dakai.
" kasani duk da ALLAH kai kaɗai yanufa zai Haifa, amma inajinka tamkar rai goma domin baka taba bijirewa umarnina ba, ALLAH yayi maka abarka tashi katafi naji anfara kiran Sallah.
Tashi yayi yanufi masallaci yadaɗe yana Addu'a da niman Yafiyar ubangiji sannna yanufi compney ɗinsu , transfa yanime amishi zuwa reshansu na legos cikin sa'a kuwa batare da daukar lokaci ba aka tura shi can,ana Washa gari zai tafi yana kwance aɗakin sa acikin gida dake tun faruwa wanna abun a family house yake kwana, hannun sa hoton labiba ne banda hawaye babu abinda ke ɗiga saman hoton.
Yana kwance yaji tari yasarke shi, aikuwa yashigayi babu kama hannun yaro ,tun yana kwance harya zauna karshe durkusawa yayi yana tari haɗe da gudan jini, dangwalo jinin yayi lokacin tarin ya tsaya yace, "tabbas nasan sonki da kaunar ki su zasu sama ajalina labiba , idan kuwa haka ne ina Maraba da irin wannan rana duk asanadin soyaya.
Komawa yayi ya kwanta yayi lamo, sai barci barawo ne yayi awan gaba dashi.
Washa gari kuwa ya kama hanyar legos Ransa da gangan jikin sa cike da begen labiba Abin kauna.
*******
Ilham tashi tayi Don yin fitsare saijin tashin mota tayi cikin sauri ta leka ta window Don ganin ko barayi ne, ware ido tayi ganin yanda sadiq ya ɗauki labiba da alamu mai afkuwa ya afku,wani irin tsoro da kuma bakin kishi ne yahadu ya tsaya mata a makwogwaro, cikin sauri tayi ajiyar zuciya jin yanda numfashinta ke barazanar ɗauke wa, da hanzari ta ɗauki ruwa ta kafa abaki bata cire ba saida ta shanye.
Fashewa tayi da kuka tana maijin tsananin kiyyayar labiba kasan zuciyar ta.
******
Washa gari kuwa aka sallame su, sai
nannan yake da ita wani irin sonta yaji yana ratsa jijiyoyin jikin sa, suna zaune yana bata magani tace, "mijina ina jiye maka Faɗawa fushi ALLAH kasani duk abinda Kake yana jida kuma ganin ka.
Kallon ta yake gabaki ɗaya yarasa inda zancanta yadosa yace, " haka ne Nagode da tunatarwar ki, amma kozansan abinda kike magana akai.
"kanta tsaye tace, "kasani mu biyu ka aura Nida ÿar uwar ka ilham kuma sanin kankane zaman ka take inada tabbacin baka duba lafiyar taba tun jiya da aka kawo ta gidan ka amatsayin mata ba kanwa ba.
Shiru yayi harya buɗe baki da niyyar magana sallmar ta dasu kaji ne yadakar dashi daga faɗan abinda zai faɗa ,cikin sauri labiba ta yunkura zata Mike daga kwanciyar da tayi ajikin sa bayan yagama bata abincin ,cikin sauri yariko ta kallon sa tayi, alamu yayi mata data koma ta kwanta, ganin babu alamar wasa yasa tayi saurin komawa ta kwanta, zuciyar ta babu daɗi Sam bataso taga ana wulakanta mutum ,duk zuba mata ido babu wanda yace komai acikin su.
Rusunawa tayi hawaye nabin kuncin ta batare data furta komai ba, ganin tana bata musu lokaci yasa sadiq cikin fusata yace, "waye sa'anki anan tashi kitafi tukan Nabi takanki kizo kinsaka mutane agaba kina kuka maza bace Minda gani sakarya kawai.
cikin sauri labiba ta rufe masa baki tana girgiza Kai tace.
Cikin kuka ilham tace "Dan ALLAH yaya kayi hakuri wallahi shirin shaiɗan ne kuma nayi alkawarin Zama da aunty labiba lafiya babu wani tashin hankali dazakaji ta bangare na, aunty labiba kema kiyi hakuri dan ALLAH, Kara fashewa da kuka tayi zuciyar ta kuwa kamar zata tarwatse haka take jinta sabar tsanar labiba.
Tashi labiba tayi ta rungume ta tana share mata hawaye tace, "babu komai aunty ilham nikam bakiyi min komai ba, "Nagode yaya Bakace komai ba.
Murmushi sadiq yayi dan sosai yaji daɗin abinda ilham tayi, zuwa inda suke yayi ya haɗasu da kirjinsa yana cewa, "idan kukayi min wannan kunyi min komai arayuwa, kuma zanyi alfahari daku, maza daina kuka na yafe miki dama can bakiyi min komai ba, jeki sashinki ina zuwa.
Cikin sauri tafita har tana harďe hanya, Zama tayi afalon ta tana shike dariya cike da makirci, tsagaitawa da dariyar ta tayi Tana cewa, "lailai kin kasance sakarya acikin mutane labiba dahar kika amince da nadamar da kika gani saman fuskata, dazaki ga tsansar kiyyar ki dake kunshe cikin zuciya ta dako kaďan bakiyi gigin shiga rayuwa ta ba, a sannu zansaka ki nadamar auran Y'a sadiq dakika Yi, sake fashewa da Dariya tayi ta shige cikin bedroom ďinta ....
Duk asanadin soyaya
By
SAFNAH ALIYU JAWABI
Bismillahi rahamanin rahim
Murmushin labiba tayi tace, "hmmm sai yanzu hankalina ya kwanta .
Saka hannun sa yayi cikin sumar ta yana wasa dashi yace, " matsoraciya,rike hannun sa tayi cikin wasa ta gatsa masa cizo aikuwa nan yashiga mata cakulkuli tana zulewa,tsayar dashi tayi tace, "honey tashi kaje ilham tana jiran ka.
Buɗe baki yayi jin sunan data kirashi dashi yace, "a a lailai sumar jiya karyace tunda gashi har ancanza min suna .
Da sauri tatashi tanufi dakin ta cike da jin haushin kanta.
Murmushi kawai sadiq yayi yanufi sashin ilham,da Salama yashigo gidan cikin sauri tafito Faɗawa jikin sa tayi Tana kuka,ɗago fuskarta yayi yace, "menene Abin kuka ilham? Nafaɗa miki idan nine wallahi komai ya wuce aguna saidai akiyaye duk abinda zai Zama fitina, kinbin umarnina kuwa zai iya haifar da abinda rai bazai soba .
"IN SHA ALLAH ya'ya zanyi iya bakin kwakarina.
Janye ta yake sonyi daga cikin sa amma sai wani shishige masa take, ganin haka yasa yace, "muzauna ko?
Zama yayi ita kuma tana kwance kan cinyar sa,da gudu Hafsah ta faɗa ɗakin tana cewa, "bro kana ina gani nazoo,turus tayi Tana kallon sa cike da mamakin ganin ilham akan cinyar sa, juyawa tayi da niyyar komawa, cikin sauri ya tashi yazo inda take idonta sun kaɗa sunyi ja.
"Lil sis ya haka kin shigo kuma zaki koma bakiga ilham bane?
Tora baki tayi tace, "naganta mana bro mezan mata?
Murmushi yayi yace, "a a bangane ba ilham ɗinki Cefa?
Tasowa ilham tayi rike mata hannu tace, "haba sis duk fushin ne haka bazaki yafewa sis ba.
Murmushi tayi tace, "nikam bakimin komai ba .
Yazaki ce banmiki komai ba gashi kinzo zaki tafi ko Gaisawa bamuyi ba.
"kiyi hakuri sauri nake ne amma IN SHA ALLAH gobe zanzo.
"to shikenan ALLAH yakaimu.
Fita sukayi harda sadiq ɗin, suna kaiwa tsakiyar gidan Hafsah ta fashe da kuka Tana cewa, 'yaya dama haka halin maza yake?
"Mekuma yafaru Sis?
Bagashi harka fara cin amanar aunty labiba ba, kaida kanuna baka kaunar aunty ilham shine daga kawo ta harda wani kwanciya ajikin ka, ALLAH saiya saka wa aunty labiba.
da gudu ta nufi motar da tazo aciki,tana shiga suka fice daga gidan,gabaki ɗaya kasa motsi daga gurin sadiq yayi yana mamakin girman soyayar dake tsakanin labiba da ha.
Hafsah kuwa tana zuwa gida cikin ɗakinta tashiga tarufe kofar Faɗawa gado tayi Tana kuka daukar wayar ta tayi layin labiba takira tana ɗagawa taji yanda take ajiyar zuciya, murmushi tayi Don sadiq yafaɗa mata yanda sukayi tace, "Lil sis kamar kuka kike ko?
Shan mijina tayi tace, "aunty labiba wallahi bro cin amanar ki yake, ina cewa yayi baya son aunty ilham?to wallahi karya ne kisan yanda nasame su kuwa?
Gyara murya tayi tace, "Lil sis Karki damu yayanki adalin mijine kuma yanaso ya gyara tsakanin sa da mahalilcin sane, ko kinaso ALLAH yayi fushi da shine?
Girgiza Kai tayi kamar tana ganin ta.
"Yauwa sannan ilham da kanta tazo tanime yafiya akan abinda tayi mana,bakya so muma ALLAH yayafe mana ne idan muka Saba masa ?
"inaso saidai wallahi aunty kiyi taka tsansan da aunty ilham jikina yana bani akwai abinda take kullawa.
Dariya labiba tayi tace, "inaso kowani musulmi ya kyautata zato, Dan haka muyi mata zaton alkairi koda kuwa ba hakan bane aranta.
"to shikenan aunty zanzo gobe idan mummy tabari.
"saikin zo Nagode.
Sauke a jiyar zuciya tayi Tana Mai zurfafa tunani akan maganar Hafsah Don tabbas biri yayi kama da mutum ,amma IN SHA ALLAH bazata taba samun nasara ba.
*******
Ilham kuwa kamar ta kurma ihu haka taji, "waini kam ko asiri labiba tayiwa Hafsah ne?
Hmmm koma me zamu gani domin wallahi hatta mummy saina rabata ďa Y'a sadiq.
******
Raihan kuwa koda ya sauka a garin legos hotel yakama ya kwana Washa gari kuwa ya bazama niman gidan da zai zauna na wani lokaci, batare da wani wahala ba yasame 2bedroom mai madaidaicin kyau,cike da kwarewa yafara aiki cikin kankanin lokaci yasaba da mutan gurin ,Abu ɗaya ke damun sa yawan tarin da yake kwanan nan Abin yafara tsananta.
Koda yatafi asibiti aka tabbatar masa da zuciyar sane ta kumbara Don haka dole yarage tunani gudun Faɗawa halaka.
Godiya yayiwa Dr sannan yanufi gida, Shidai kam yasan rayuwar sa batada wani amfani agare shi tunda labiba tayi nisa dashi.
*****
Zakkiya da mummyn ta kuwa tun 6am suka bar garin Kaduna zuwa gumau, koda suka sauka tasha tafiya suke babu kama hannun yaro daji mai mugun nisa suka shiga tun zakkiya tana daurewa har Abin ya isheta Zama tayi agurin rike da bayan ta tace, "mom wai haryanzu ba'azo ba?
"dallah can malalaciya banza kitashi mutafi mun kusa.
Tashi tayi da kyar tana gunguni har suka isa,wani irin gurnani suka fara jiyuwa ,cike da tsoro zakkiya ta rike hannun mom jikin ta na kirma, shafe bayan ta mom tayi tace, "shegiya ga tsoro ga mugun aiki.
Suna tsaye saiga wani dunkulan haske ya baiyana agaban su, Ahankali hasken ke rikeɗa zuwa wani kasurgumin kato suffar sa Abin tsoro, idanuwan sa kwala kwala, gashin giran sa kuwa harya haɗe da sumar kansa tsabar yawa, bakinsa wangajeje.
Rusunawa sukayi agabansa cike da girmama mom tace, "kaine bokan dakafi kowani Boka afaɗin duniyar nan, nazo da kokon barata ka agazamin.
Wangale bakinsa yayi idonsa nakan zakkiya yace,, "tabbas kinzo inda za'ashare miki kukan ki, tare hannun sa yayi saiga wani dunkulalliyar Abu ya baiyana Mika min yayi,hannuna narawa nakarba.
Murmushi yayi mai kama da kuka yace, "yarinya ki kwantar da hankalin ki indai raihan ne kin gama samun sa, saidai kisani duk wani abu da kike Yi dole saikin daina, kama daga sallah azumi da duk wani abu daya dangance ibadar ALLAH.
"sannan wannan Abun dana baki acikin rijiyar dake gifen gidan da raihan yake zaki saka ina Mai tabbatar miki zaki SHA mamaki.
Jinjina lamarin tayi tace, "babu damuwa zanyi duk abinda Kace.
Tashi sukayi suka nufi gida zuciyar ta fes jitake kamar ta taka rawa Don murna.
*****
Sadiq kuwa sosai suke dirje soyaya cike da aminci,zaune suke ilham da labiba suna Hira sashin labiba,da sallama Hafsah tashigo gidan tana kwalla kiran sunan labiba, da sauri ta Mike suka rungume juna, cike da murnar ganin juna Hafsah tace, "Kaikai aunty labiba kinga yanda kika kara kyau da haske kuwa? Kanne ido tayi tace, "Kodai Kodai?
Duka takai mata cikin wasa tace, "ke kam taya kike gani Abu cikin sauri, daka tsalle tayi tace, "Dan ALLAH aunty labiba kinada ciki?
Nod dakai tayi Sam tama mance da wanzuwar ilham agurin sai tashinta kawai tagani cikin sauri ta fita daga gidan.
Kallon juna sukayi musamman tun bayau ba talura da yanda ilham take kulla mata shairi, ALLAH ne kawai yake fitar da ita.
Hira sukayi har yamma sannan ta tafi gida da murna take Faɗawa mummy abinda ke faruwa.
Murna sosai mummy tayi da fatan saukar ta lafiya.
Ilham kuwa sai safa da marwa take gabaki ɗaya jitake kamar zata zauce, hawaye kebin fuskarta wani na korar wani, daukar key ɗin motar ta yayi tanufi gidan sha'awa kozata samu mafita Don wallahi bazata tsaya tana kallon labiba ta rigata haihuwa agidan nan....
*SAFNAH ALIYU JAWABI ce*
[6/13, 14:39] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
*By*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*DEDICATED TO YOU MASOYI ABIN AL'FAHARI* ❤❤
2⃣6⃣➖2⃣7⃣
*Bismillahi rahamanin rahim*
,,,,,,, Da kuka tashiga gida da sauri sha'awa wacce yanzu take zaman zawarci gidan su tatari ilham cike da nuna tausayawa tace, "Yi hakuri ba kuka zaki yiba wallahi ɗaura ɗamarar yaki zakiyi Don ƙwatarwa kanki yanci yarinya.
Cikin kuka tace, "Toni Ya zanyi kindai san babu abinda banyi ba danganin tabar gidan, amma gabaki ɗaya abin ya faskara saima guzurin cike da take da.
Shiru sha'awa tayi can tace, "Nasamu mana mafita saidai bansani ba ko zaki iya.
Bakinta har rawa yake tace, "wallahi kuwa zan iya sha'awa ki gaggauta faɗamin , kinji Dan ALLAH.
"Na farko dole saikin San yanda akayi kika samu ciki cikin kankanin lokaci, bayan haka zanbaki wani magani saiki zuba mata acikin Abin SHA, cikin zaizube kinga kenan naki ɗan zairiga nata fitowa duniya idan mata kuma samun wani kenan, koya kika gani?
"to gaskiya shawarar ki tayi saidai kisani bafa kullum Ya sadiq yake nuna bukatar sa akaina ba,idan kuma na nuna mai share zancan yake ko kuma yace, "yawan sex yana kawo mutuwar jiki da sauri,toda hakan zancan zaibi ruwa.
Murmushin mugunta sha'awa tayi tace, "to basai ki nime wani yayi miki ba ya'isa yace banashi bane?
Gabaki ɗaya jin ilham ya ɗake zufa kawai take jin abinda sha'awa tace ,da mamaki take kallon ta tace kina nufin nayi zina da Aure na? Hmm haba haba ina bazan iya ba.
"To shikenan naga dama bani Nakira kiba, kekizo da kafarki ,Don haka idan kina ganin shawarar dana baki baiyi ba saiki nima wata,nikam iya inda nasan zan iya taimaka miki kenan
Murmushi tayi ta ɗauki Jakarta tace, "Karki damu shawarar ki tana kan hanya zankira ki awaya saimu tsara yanda Abin zai kasance, kinga baima San nafita ba karya dawo baiganni ba, cikin sauri tafita daga gidan.
Sha'awa kuwa Dariya ta saki harda rike ciki tace, "hmmm lailai ilham baki sanni ba, wallahi tun daga Randa nayi ido hudu da sadiq naji duk duniya babu namiji daya dace Dani sama dashi, kuma na ɗauki alwashin kawar dake nashiga kuma na zauna da uwar gidan sa lafiya, Dan nagane Hakan kawai shine mafita Dani kike zancan.
*******
Wasa wasa lamarin raihan yayi nisa takai duk tarin dayayi sai gudan jini yafaɗo, gabaki ɗaya yarame saidai duk yanda yake jin jikin hakan baisa tafaɗawa Inna sadiya ba, haka kuma bandaina tunanin labiba ba.
Ranar da jikin ya motsa sosai saida aka dangana da asibiti badan ransa yaso hakan ba ganin babu yanda ya iya yasa kawai ya hakura.
Sosai Dr yake masa faɗa lokacin da aka samu yadawo daidai, kallon Dr yayi hawaye nagangara yace, "Dr babu bukatar shan magani ko kuma daina tunani, domin kuwa itace komai nawa, itace duniya ta kaga kuwa daina tunanin ta tamkar barin duniyar ne gabaki ɗayan ta.
Gyara zaman glass ɗinsa Dr yayi yace, "wacece ita?
Shiru yayi can yashiga bashi labarin labiba, Dr ya tausaya masa sosai yace, "tabbas raihan kayi kuskure saidai kasani ba laifin kabane haka ALLAH ya hukunta bakada tsime baka da dabara dole sai hakan tafaru, kayi tawakkali IN SHA ALLAH komai zai wuce.
Murmushi raihan yayi Don yaji sanyi da wata irin natsuwa sun shige shi lokaci ɗaya yace, "Nagode Dr kuma IN SHA ALLAH zanyi amfani da shawarar ka,fita daga dakin Dr yayi baya yaduba yanayin saukar ruwa dake sakale ahannun sa.
******
Wata tsohuwar rijiyar dake gefen gidan su raihan zakkiya taje ta jefa wannan dunkulalliyar abinda Boka yabata, Cike da farin ciki ta zauna tana jiran zuwan raihan ko kuma kira,amma Abin mamaki harna tsawan sati shiru Kake ji babu labari,sosai hankalin zakkiya yatashi, cike da masifa take Faɗawa mom abinda ke faruwa.
Kallon ta mom tayi tace, "ki kwantar da hankalin ki zakkiya bara Nakira shi naji yanda za'ayi, ɗaga Waya tayi ta kira Boka, yana ɗagawa yafashe da Dariya yana cewa, "ki turota tazo ita kaɗai akwai abinda zanbata.
Baijira amsar taba ya katse kiran yana lasar baki yana tuno yanda yaga mazaunan ta ke kaɗawa .
Faɗa mata yanda sukayi da Boka tayi, cike da zakkuwa zakkiya tace, "mom bazan iya zuwa yanzu ba?
Harara ta aika mata dashi tace,"saiki tashi ki tafi ai kina gani ranar MA sammako mukayi amma sai kusan magrib muka dawo gidan nan, shine ke zaki tafi da tsakiyar ranar nan.
Bubbuga kafarta zakkiya tayi ta shiga ciki.
Murmushi mom tayi tace, "zakkiya sarkin rigima.
*****
Washa garin ranar kuwa zakkiya ta nufi gumau, koda ta isa gurin ta iske shi yana zama jiranta, washe bakinsa yayi yace, "ki Sani raihan Baya garin da kike, yana can Lagos can yake aiki yanzu Don haka tabbas aikin ki bazai yuba sai ainda yake zaune.
Dafe kanta tayi tace, "yanzu to menene Abinyi?kuma ta ina zanfara niman shi agarin Lagos boka?
Karki damu wannan karamin aiki ne saidai kisani akwai abinda zaki bamu kafin nan aikin ki yaci.
Batare da tunanin komai ba tace, "wallahi zan bayar koma menene?
Dariya boka ya kece dashi Wanda saida ilahirin dajin ya amsa sannan yace, "kince zaki iya ?
"zan iya Boka taimaka min.
Tashi yayi ya nuna mata data biyu shi, kan wani makeken dutse yakaita, cike da mamaki take kallon gurin, Don Sam inda suke da daji ne sosai, da mamaki take kallon sa zata buɗe baki tayi magana yace "kina magana anan mutuwa zakiyi Don haka kwanta.
Kallon dutsan tayi Wanda duk jikin sa akwai tsini aranta tace, "Kai anan zan kwanta? Tabɗi jam.
Daka mata tsawa boka yayi yace, "kina batamin lokaci.
Jikin ta na rawa ta kwanta, ga mamakin ta sai ganin boka tayi yana ƙwakarin kwance Zariya wandon sa, gashi babu damar tambayar sa,mamaki bai Kare ba saida zakkiya taga Boka yayi tumbur yana kusanto ta, cikin sauri ta rintsa idonta ganin katuwar abinsa kamar hamma.
Matsowa yayi inda take, take taji wani irin wari mai tayar da hankali Ya dake hancin ta,buɗe idonta tayi cikin sauri kafin tayi wani yunkuri tuni Boka Yasaka hannu cikin rigarta, hannun sa har bari yake lokacin daya isa ga dukiyar Fulanin ta,matsasu yake da karfi kamar ALLAH ya aiko shi.
Tuni idanuwan zakkiya suka shiga zubda hawayan dana Sani Mara amfani day ashige ta lokaci ɗaya .
batayi auni ba saijin shigar boka jikin ta tayi, wani irin ihu ta kwalla wanda shi kansa bokan saida yaɗan razana, amma ya dake ,zungurarta yake yana sambatu da kiran sunan ifiritai kala kala.
Tun zakkiya Tana ganuwa har ta sume, kusan awa Shida ya kwashe asamanta ,koda yatashi zakkiya ta daɗe aduniyar suman mu, wani kwarya ya ɗauko cike da ruwa kalar jini ya watsa mata.
AFirgice ta farka ganinta kwance awannan gurin na farko yasa ta tashi aikuwa kamar antura ta haka takoma ta faɗi gabaki ɗaya kafarta bazai iya daukar taba.
Kuka ta fashe dashi tana cewa, "ALLAH ya isa tsakanina dakai mugu azzalumi wallahi sai kaga karshan ka.
Dariya yayi yace, "tabbas kin tafka babban kuskuran da agabaki ɗayan rayuwar ki bazaki samu damar gyarawa ba.
"Tashi kitafi sannan daga yanzu kifara kirga ranakun mutuwar ki,yana gama faɗan haka ya bace bat.
Kuka zakkiya take kamar ranta zai fita, da rurrufe ta isa bakin titi,dakyar ta miki tatare mai adaidaita yakaita Tasha.
*****
Zaune suke ilham da sha'awa sai Dariya sha'awa take mata ganin sai wani rurrufe fuskarta take,murmushi sha'awa tayi tace "kunyar mee kike ji ilham?
Dariya tayi tace ,"wallahi wani irin nake ji ne.
"wani iri kuma? a a ko kaɗan Karki damu aiyanzu aka soma, amma dai kinji daɗi ba?
Duka takai mata cikin wasa tace, "kekam sha'awa saidai abarki,nikam bara natafi gida.
*****
Zaune labiba take hannun ta ɗauke da cup kunun gyaɗa take SHA,da sallamar ta ilham tashigo tace, "a a aunty labiba kece Abin yazo inji mai tsoron wanka.
Murmushi kawai tayi tace, "kin dawo? Yasu mummy?
Zama tayi kusa da ita tace, "lafiya kalau Sunce gaishe ku.
"muna amsawa.
Duba cup din ilham tayi tace, "wallahi yunwa nake ji aunty labiba baki dafa komai ba?
Akwai saidai fatan doya nayi bansani bako zaki ci,?
"zanci Dan ALLAH ɗebomin.
Tashi tayi ta nufi kitchen .
Tana shiga ilham ta fito da garin maganin da sha'awa ta bata ta zuba acikin cup ɗin, cikin sauri ta mayar ta girgiza.
Zama tayi ta Mika mata abincin, fara ci tayi Tana kallon yanda labiba take shan kunan gyaďar mai cike da garin magani....
Cokali hudu tayi tafara jin wani masifaffiyar ciwon Mara, tun tana daure wa harta fara salati jin yanda bayanta ya amsa lokaci ɗaya .
Kallon ta ilham tayi tace, "lafiya aunty labiba meke damunki?
Nuna mata cikin ta tayi Tana yarfe hannu alamar tana cikin matsanan cin Hali, cikin nuna ko inkula ilham tace, "sannu bara naje naɗan watsa ruwa na kwanta ALLAH ya sauwake,binta da kallon mamaki labiba tayi Tana aiyana wani abin aranta ganin yanda ilham ta nuna halin ko inkula.
Ďaga Kai tayi tace, "ilham ko zaki taimaka ki kira min Y'a sadiq Dan ALLAH "
Wani mugun kallo ta aika mata dashi sannan tace, "hmmm kinga nikam bana da kuɗi awaya bare na kira miki shi.
Wani irin ihu labiba tayi ganin jini na zuba ta kasarta,ilhma kuwa dawowa tayi ta tsaya akanta tana dariyar mugunta tace, "tabbas na daɗe ina miki kallon sakarya, amma ban tabbatarwa kaina ba sai yau, waike tunanin ki harkin Kai macan da zatayi girki naci?
"Hmmm gaskiya kam kin tabbata shashasha, to kisani wallahi koda Nakira miki Y'a sadiq babu abinda zai iya tsinana miki, Kai koda kuwa asibitin duniyar nan za'a zaga dake inama tabbatar miki bazaki rayu ba,domin kuwa maganin zubda ciki na zuba miki,sannan kaɗan akace na zuba Idanna zuba dayawa tabbas mutuwa zakiyi,ganin babu wani amfani da rayuwar ki take tsinana min shiyasa na zuba dukka,don haka tun yanzu kifara niman yafiyata akan cin amanata da kikayi.
Wani irin mahaukaciyar duka sadiq ya rufeta dashi tamkar mahaukacin zaki, dukanta yake haɗa da naushi ,bakinta da hancinta gabaki ɗaya jini suke zubarwa,da kyar labiba ta jamasa Riga Tana masa nuni da jinin dake kara yawa,tura ilham cikin ɗaki yayi wanda gabaki ɗaya kamar Ma bata numfashi haka ta koma ya kulle yajefa 🔑 cikin aljihu.
Da gudu yafita da ita daga gidan, number Hafsah yakira yace, "tasame su a asibiti labiba ba lafiya,aikuwa arikice Hafsah tayi waje tana kiran driver,cikin mintina ta isa asibitin rike hannun Sadiq tayi tace, "yaya Tana ina aunty labiba Tana ina bro?
Rarrashinta yake saiga likita yafito,da sauri suka isa gunsa, "Dr ina fatan dai anyi nasara?
Share zufa Dr yayi yace, "Alhamdullah saidai gaskiya tana da bukatar jini domin ta zubda jini sosai, kuma mun samu nasara ɗan baifita ba, saidai Dan ALLAH adinga kulawa.
Murmushi jin daɗi Hafsah tayi tace ,"IN SHA ALLAH.
Zuwa sadiq yayi aka ɗinba jinin sa aka saka mata saida yaga komai ya daidaita sannan yanufi gida, ɗakin daya kulle ta aciki yashiga, haryanzu tana nan yanda yabarta, ruwa Mai Kankana ya ɗauko ya watsa mata, sauke nannauyar jiyar zuciya tayi, sannan ta fashe da kuka Mai ban tausayi.
"ilham.
Ďago Kai kawai tayi Don Sam bama zata iya buɗe baki ba tsabar yanda take jin nauyin ta, "lailai kin kasance daga cikin azzaluman mutane, kin kasance Daga cikin mutane masu Fuska biyu, ALLAH ya isa tsakanina dake kije idan duniyar nanne ina Mai tabbatar miki ta isheki Riga da wando, akarshe ina Mai farin cikin sanar dake na sakike1 nasakike 2 nasakike 3 bana bukatar Zama da maci amana arayuwa ta ,yana kaiwa nan yayi ficewarsa yabarta tana kuka kamar ranta zai fita,dana sani Mara amfani ke cinta.
*****
Sadiq yana fita bai tsaya ko inaba sai Airport visa yashiga nima musu cikin sa'a kuwa yasamu na England zai tashi karfe 6pm da farin ciki ya koma asibiti, koda yaji tuni mummy ta iso gaisheta yayi Ya nime guri ya zauna baice dasu komai ba, ganin haka yasa Hafsah ta nufi gurinsa Ďago Kanshi tayi aikuwa hawaye ke gangara wani na korar wani ,share masa tayi tace ,"bro make faruwa?
Shiru yayi kamar bazai amsaba Candai yace, "guba aka bata, jiki na rawa mummy ta riko hannun sa kana ganin ta kasan afirgice take tace, "Waya min haka? Wani makiyi ne yake son ganin Baya na?domin kuwa nasan da wani Abu yasame labiba tabbas mutuwa zakayi koda kuwa baka mutu ba tofa babu wanda zai Kara gane kanka.
Jin maganar mummy yasa ya Mike cikin sauri hawaye bai daina zuba ba yace,"nagode wa ALLAH dayasa kika fahimci haka mummy wallahi bazan iya rayuwa Mai inganci batare da labiba ba, Don haka yasa nasaki ilham sakin da bazata taba dawowa..cikin sauri mummy tasa hannu ta bigi bakin sa har saida yafashe, dangolo jinin yayi yace, "mummy Na yarda da duk hukuncin da zakimin, amma kisani narigada na yanke hukunci nayi mata sakin da bazata taba dawowa ba har abadan.
Janyo yar yawon dake makkale mummy tayi ta Rufeshi da duka baji ba gani ,cikin sauri Hafsah ta shiga rokon mummy aikuwa haɗawa da Hafsah mummy tayi duk yanda sadiq yaso dukan ya daina taba jikin hafsa ina saida bayanta yafarfashe.
Bata daina dukan suba suma basuyi ƙwakarin hanata ba, kuma babu Mai magana ko ihun niman taimako acikin su, labiba kuwa cikin barcin ta taji kamar ana magana ana kuka buɗe idonta tayi cikin sauri aikuwa tabbas mummy ce ke dukan ya sadiq da Hafsah , durowa tayi daga kan gadon da gudu tanufi mummy da karfi ta fisge yar yawon tana Huci.
Ďago ido mummy tayi Don ganin wani mai karfi halinne ya karbi bulalar, aikuwa suka haďa ido da labiba wanda tuni idanuwanta sun canza kala, "mummy kiyi hakuri kawai tace ta sunkuyar da kanta, gabaki daya jikin mummy yayi sanyi ganin yaranta da take mutuwar so akwance kamar kayan Wanki duk jikin su afarfashe kuma wai itace tayi musu hakan.
Da sauri ta fita aɗakin tayi gida.
Labiba kuwa da sauri ta rungume Hafsah ganin itace bata motsi kiran sunanta take amma ina shiru, da gudu ta fita ta kira likita ,sosai abinda likita yagani ya bashi mamakin yaushe hakan tafaru basu sani ba ?ganin babu wani amfanin da sanin zaiyi mishi yasa yashiga duba Hafsah cikin kwarewa.
Sharce zufa yayi yace, "bawani abu bane suma tayi amma IN SHA ALLAH nanda zuwa anjima zata farka IN SHA ALLAH .
Godiya sukayi masa bayan yaduba sadiq yatabbatar baisamu matsalar komai ba yafita, cikin karfin Hali sadiq ya nufi gadon da Hafsah take kwance lokaci lokaci take sauke jiyar zuciya, rungume ta yayi yana zubda hawaye, fita yayi daga ɗakin bai tsaya ko inaba sai Airport visa yashiga nimar wa Hafsah da kyar yasamu hamdala yayi yakoma asibitin bayan yayi musu tekeway na abinci.
Zaune yasame labiba tayi tagume kamar baitace bata da lafiya ba, Sam itakam tamance batada lafiya da sallama yashiga ɗakin , cikin sauri ta Mike rungume shi tayi Tana kuka tace, "hubby kafaɗa min abinda ke faruwa?
Bubbuga bayanta yayi yace, "shhh karkiyi kuka kinsan bakida lafiya ko?
"oya ga abinci ki ɗauka kici,yajikin nata?
"Da sauki harma ta farka.
"OK maza kici akwai inda zamu tafi.
To kawai tace batare data tambaye shi inda zasu tafi ba, Tana gama cin abinci ya ɗauki ta suka fita daga asibitin,gida suka huce itadai labiba kallon sa kawai take sai harhaɗa kayan su yake,daurewa tayi tace, "hubby tafiya zamuyi nee?
"Eh kawai yace ya cigaba da haɗa kayan, cikin mintina kalilan yagama harhaɗa kayan suka fita, baizarce da ita koina ba sai gidan mai anguwa, farin ciki sosai mai anguwa yayi daya GA yanda labiba ta Kara kyau tayi haske,sunkuyar da kansa sadiq yayi yace, "dama sallama mukazo muyi maka zamu tayi Hutu England .
Ďago Kai labiba tayi cikin sauri jin abinda sadiq yace.
Mai anguwa kuwa washe bakinsa yayi yace, "a a kace mutan England zasuyi baki?"to ALLAH yadawo daku lafiya.
Duk suka amsa da Ameen,basu wani jima ba kasancewar duk hankalin su yana ga Hafsah dake asibiti.
Koda suka kamo hanya sotake ta tambaye shi ganin yanda yayi kicin kicin da Fuska yasa tayi shiru.
Suna shiga suka iske Hafsah ta farka tana zaune abakin gado,murmushi tayi masa shima ya mayar mata sannan tace ,"bro mummy fa?
"Shhh Lil banson wani magana yanzu yakike jin jikin naki?
"Dasauki kaifa yana ka?
"Hmm nasan kina jin yunwa ko? "labiba tashi ki taimaka mata ta ɗan kuskure baki tazo taci abinci mutafi.
"To kawai tace suka nufi toilet,bayan ta gama cin abincin sadiq da likita suka shigo atare Don tunda ta fara cin abinci yafita, sake duba jikin labiba yayi ahaɗe da yar tambayoyi saida ta tambatar masa da babu abinda ke mata ciwo sannan ya rubuta mata magunguna.
Hafsah ma haka sannan ya rubuta musu takardar sallama,basu fita daga asibitin ba sai kusan 5pm Don haka daga nan sadiq bai tsaya ko inaba sai Airport basu daɗe da isowa ba aka suma kira,Hafsah sai binsu da ido take takasa tambayar abinda ke faruwa ganin itama labiba shiru tayi.
Sadiq kuwa gudun MA karsu tambaye shi yasa yahaɗa girar sama data kasa fuskarnan kamar bai taba Dariya ba,sunaji suna gani suka shiga jirgi kasancewar shigar jirgin labiba nafarko kenan aikuwa gabaki ɗaya kallo ɗaya zakayi mata kasan atsorace take, ganin haka yasa yazauna kusa da ita Hafsah kuma tana bayan su tuni idanuwanta sun fara zubda hawaye.
Sarai yana ganin ta yabasar, daidai lokacin da jirgin zai tashi labiba ta kankame sadiq jikin ta narawa, Kara rungume ta yayi yana shafar bayan ta, harsaida jirgin ya daidaita asararin samaniya sannan ya duba yaga Ashe hartayi barci.
******
Jiki asanyaye ilham tanufi shashinta ta ɗauki duk abinda tasan zata bukata, bata tsaya koina ba sai gida,da kuka tashigo gidan daidai lokacin mummy ta dawo tana zaune afalo, cikin sauri ta Mike ta rungume ilham ganin haka yasa ta Kara fashewa da kuka Mai sauti.
Rarrashinta mummy take Tana cewa, "ki daina kuka ilham wallahi bazan taba bari wani yaci mutumcin kiba bare kuma ace ɗan dana Haifa aciki na yayi miki na barshi, jiki ciki ki kwanta bara abban ku yadawo wallahi sainayi maganin wannan yaron harmu zaiwa haka hmmm.
Farin ciki fal cikin ilham ta shiga tsohon ɗakin su, saidai wani shashi na zuciyar ta tana nadamar abinda ta aikata.
******
Zakkiya kuwa Abin duniya yataro yayi mata yawa, wani irin ruwa Mai muguwar Wari ke fita ta kasarta wanda warin sa kaɗai ya'isa saka mutum amai, kwance take aɗakin ta yi ɗaiɗai tsirara daga ita sai bra ko ɗankampai bashi ajikin ta, sallamar hibba ne yasa ta mike zaune tana cewa, "wallahi baki da kirki shine kika share ni ko?
Gabaki ɗaya hankalin hibba Baya gun maganar da zakkiya take mata sakamakon ganin wani katon ka dangare dake kwakarin fitowa daga kasarta kansa jazir, wani uwar ihu tayi ta fita daga ɗakin tana kiran sunan ammin zakkiya.
Hankali tashe zakkiya ta leka Don ganin abinda hibba take wa ihu haka aikuwa da gudu ta sauko tana kururuwar niman taimako ga kadangaren yana Rito ajikin ta aikuwa tsabar ruɗewa sumewa tayi agurin kamar gawa,sai asannan kadangaran yasamu damar fita....
Wallahi bansan Mezance ba am really sorry
*Love you all*
0 comments:
Post a Comment