,,,,,, Da gudu ammi ta nufo gunta tana jijigata haɗa da kiran sunan ta, cikin mintina kalilan suka kaita asibiti babu irin gwaje gwajan daba yiba amma, ba'agano musabbabin abinda ke damunta ba, sosai hankalin alhaji danko yayi masifar tashi ganin halinda yarsa take ciki aikuwa babu bata lokaci ya baro Dubai Don zuwa inda diyarsa take.
Koda yazo Abubawa sunkara rincaɓewa, domin kuwa wani irin kakkaurar ruwa Mai ɗoyin gaske ke fita ta kowani kofa najikin ta, sosai hankalin yan uwa da abokin arziki ya tashi.
Batare da bata lokaci ba alhaji danko yasa aka fitar da ita kasar Dubai Don acewar sa Dr basu Eya aiki bane, bangaran Drs ɗin kuwa sosai sukayi farin cikin haka Don wallahi sosai warin ke matsifar damun su.
Koda suka tafi maganar dai ɗaya ce, babu abinda ke damunta, amma taurin Kai irinna alhaji danko kin amincewa yayi daga nan ya dauki ta sai china, suma dai abinda suka gani kenan, amma ganin yanda yaruɗe yasa sukayi ta cinye masa Y'an kuɗinsa har saida sukaga yana niman komawa karkaf yasa suka fita suka faɗa masa gaskiya, aikuwa rashin hankalin da alhaji danko yayi musu asibitin saida sukayi dana sanin amsar aikin tun farko.
Ganin yanda yake niman Tara musu jama'a yasa suka kira jamian tsaro suka fita dasu harda Mara lafiyar wajan asibitin sannan sukayi musu gargaɗi da karda su kuskura sushiga asibitin.
Aikuwa ranan amminta tayi kuka kamar ranta zai fita gashi bazata iya Faɗawa alhaji asalin abinda yafaru ba, Don ko shakka babu Sakinta zaiyi itakuwa bata Shiryawa hakan ba.
Hakaa tanaji tana gani tayi shiru(wannan shi akae kira self-respect hahaha) gida suka dawo babu shiri aka shiga yinna gida.
Kwanan su bakwai da dawowa cikin dare zakkiya ta tayar da kowa gidan sakamakon yanda take jin zafin ciwon Feye dana ko yaushe , duk suka fito aruɗe cikin kuka tace, "please daddy forgive me wallahi it wasn't my fault it was mummy that took me to he's place daddy and now see what had happened, please daddy forgive me.
Gabaki ɗaya kan alhaji danko ya ɗaure gabaki ɗaya yakasa gani abinda take magana Kai , tsugunnawa yayi a gabanta yace," kiyi shiru baby kimin bayani akai mee kike maganar wai?
Aikuwa zakkiya bata rage komai ba ranar saida tafaɗa wa kowa ta yanda suke less da hibba harda yanda ta rinka Yi gidan raihan da zuwa gida boka harda amfani da ita dayayi .
Salati abba yayi yace, "kin cuceni kin salwantar Minda rayuwar ƴa,baxance dake komai ba amma kije nasaki ki Saki uku, wata uwar kara mummy ta kwallah tana kuka.
Wani irin Mika zakkiya take Tana jujjuya kanta, da sauri daddy yakaraso gunta yana kiran sunan ta, amma ina cikin mintina uku zakkiya ta amsa kiran ubangijin ta ,ranar daddy da mummy sunyi kuka kamar ransu zai fita.
Washa gari aka ɗauki gawar zakkiya aka sadata da gidanta na gaskiya.
Saida kowa ya watse sannan daddy yatafi har gidan Inna sadiya, zuwansa yayi daidai da saukowar raihan daga motar data ɗauko shi daga airport Don saukowar sa kenan.
Da fara'a daddy yamika masa hannu sukayi musabaha sannan yace, "dama kuwa kamar kasan gurinka nazo, wato akwai abubuwa da suka faru tsakanin ka da zakkiya lokacin bana kasar wanda wallahi nasan duk laifin nane, domin kuwa ban tsaya agida na baiwa iyalina lokacina ba bare ayi maganar tarbiyantar da gudan jinina.
"amma ina rokon ka daka yafewa zakkiya kozata samu dacewa da rahamar ubangijin ta, Don yau kwananta bakwai da Rasuwa.
Gabaki ɗaya jikin raihan rawa yake kamar mazari sosai mutuwar zakkiya ta dake shi, share hawayan sa yayi yace, "wallahi bansani ba ALLAH yajikan ta yasa mutuwa tazam Hutu agare ta, nikam nariga na yafe mata tun tuni abba.
Sosai daddy yayi masa godiya sannan yanufi gida zuciyar sa cike da farin ciki ki ,ko babu komai ya sauke wani babban hakki akansa.
*****
Raihan kuwa yana shiga gida bayan angaisa yake shaida masu mutuwar zakkiya sosai Inna sadiya take kuka Tana tuna ranar databar gidan nasu,
Saida raihan yaci abinci sannan yanufi gidan sa dake malali Don duba aikin gidan da ake masa Don anan yake son saka matar sa, Wanda auran su sati mai zuwa.
Sosai ginin yayi masa kyau aransa yake tunanin inama labiba ce agida nan, cikin sauri yabigi bakin sa yana cewa, "astagafurllah matar mutum ce.
"""""""""
Har jirgi ya sauka labiba bata buɗe idonta ba, murmushi sadiq yayi yasaka bakin sa akunnan ta, yace, "hy Sleeping Beauty tashi mun iso, kasancewar bata da nauyi barci yasa ta miki zaune tana murza idonta, murmushi yayi ya riko hannun su suka fita daga jirgin.
Cap yanemar musu suka saka kayan su a cike,gyar murya yayi yace,"akaisu hotel mafi kusa.
Aikuwa haɗaɗɗiyar hotel aka kaisu, ɗaki biyu sadiq yasa abasu,ɗaya nashi ɗaya nasu ,saida ya tabbarar sunci abinci sannan yanufi nashi ɗakin , zaune Hafsah take ta haɗa kaida kafa tana shashakar kuka.
Da sauri labiba tashiga tambayar ta dalilin kukan nata,ɗago kai tayi duk idanuwanta sunyi ja tace, "yanzu saboda ALLAH aunty labiba harda haɗin bakinki Y'a sadiq zai bijirewa umarnin iyayansa? sannan yayi musu kaura Don kawai yana ganin sunyi masa badaidai ba??
Gabaki ɗaya labiba ta kasa fahimtar inda maganar ta dosa tace, "ban fahimci abinda kika nufi ba?
Ganin da gaske labiba batasan abinda yafaru ba yasa tafaɗa mata komai harda dukan da mummy tayi musu.
Sosai hankalin labiba yayi mugun tashi,rarashin Hafsah tayi tare da daukar mata alkawari shawo kansa su koma gida.
Ko daya dawo kuka labiba ta fashe masa dashi tana cewa,"shin harka mance hakkin iyaye akan yayansu?shin yanzun mummy bata isa tayi maka hukunci akan abinda take ganin kayi badaidai ba? Shikenan tunda haka kazabar wa kanka,saidai kasani wallahi badani za'ayi wannan mugun aikin ba,tana kaiwa nan tafita tashige ɗakin su, key tasa ta kulle yanda bazai iya Shigowa ba.
Abu kamar wasa Washa gari babu irin magiyar da baiyi ba kanta buɗe kofar koda abinci nesu karba suci,amma Sam babu wacce tayi masa magana bare yasa rain zasu buɗe kofar.
Sosai yashiga damuwa, labiba kuwa dama akwai snacks da drinks acikin Jakarta shitabawa Hafsah taci saida ta tabbatar takoshi sannna itama taci, duk da Abin na damunta amma tasan wannan ne kaɗai hanyar da zatayi amfani dashi Dan ganin ta gyara kuskuran da sukayi.
Washa gari da Abin yadamu sadiq Zama yayi akofar dakin gabaki ɗaya yarasa abinda ke masa daɗi , kiran sunta yayi yace, "labiba Don ALLAH kibuɗe kofar nan na yarda ki hukuntani ta kowace hanya amma Don ALLAH banda wannan,wallahi ina cikin wani Hali ki taimaki hubbyn ki Don ALLAH.
Murmushin Hafsah tayi tazo har gaban labiba tace, "aiyi hakuri aunty labiba daga jin muryar bro wallahi nasan bakaramar nadama yayi ba, yanzu ki tambaye shi yaushe zamu koma idan yafaɗa mana sai mubuɗe.
Tashi labiba tayi Tana share hawayen daya gangaro mata Don kuwa sosai tayi ƙewar mijinta don dai bata da yanda zatayi nee.
Shikuwa yana zaune yaji alamar za'abude kofar cikin sauri yamike yana kallo kofar harta buɗe , sauke jiyar zuciya sukayi atare, Marairaice Fuska yayi sabanin ita data ɗaure kamar bata taba Dariya ba tace, "yaushe zamu koma gun mummy?
Baki narawa yace, "wallahi ko yanzu kika so mutafi Zamu tafi nidai ina rokon adaina yin fushi dani sosai yake kasheni.
"tambayar dana maka daban amsar da Kake bani Daban shikenan tunda baxaka faɗa ba,tura kofar tayi kamar zata rufe cikin sauri sadiq yace ,"Karki rufe gobe Zama tafi gobe goben nan.
Matsa masa tayi yashige ciki, Hafsah kuwa Matse dariyar ta tayi ganin yanda sadiq yake kwantar dakai yana bawa labiba hakuri, ita kuwa sai basarwa take.
Washa gari tunda Misalin karfe 8am suka bar England,sosai Hafsah taji takara bawa labiba wani gurbi acikin zuciyar ta,kuma ta Kara tabbatar wa kanta sadiq bazai iya rayuwa Mai inganci batare da labiba ba....
******
Ranar da aka fara shagalin bakin raihan akaro na biyu MA saida yayi kuka batare da sanin kowa ba, ganin hakan bashida amfani yasa ya watsake tare da mikewa ALLAH duk kannin lamuran sa, sosai kuwa akasha biki bayan anɗaura aka Sada amarya da gidanta saidai fatan zaman lafiya mai ɗaure wa.
*****
Mummy kuwa tun tana saka ran dawowar Hafsah hardai ta ɗaga Waya takira ta,ga mamakin ta gabaki ɗaya nunbarta bata shiga haka tayita gwadawa amma ina number bata shiga har dare.
Aikuwa ganin zaman bazai fisheta ba yasa ta zari gyale sai asibiti, koda tashiga wasu mutane tagani akwance ,rike baki tayi tace, "Kenan MA an salame su shine babu wanda yakira ni yafaɗa min,kenan Hafsah a can gidan zata kwana aikuwa wallahi bata isa ba, gidan zantafi na ɗauko ta karda wancan mayar ta lashe mata zuciya kamar yanda ta lashawa yayar ta.
Cikin mintina kalilan ta isa gidan, tun akofar get mai gadin yasanar da ita sunyi tafiya, cike da mamaki tace, "sun faɗa maka inda zasu tafi nee??
"a a hajiya saidai nagansu da kaya dayawa da dukkannin alamu zasu daɗe a can.
Wani irin gume mummy taji ya karyo mata, murmushi tayi Wanda akecewa kafi kuka ciwo tayi mishi godiya tafita daga gidan.
Adaddafe ta isa gida domin kuwa hankalinta yayi mummunar tashi, Tana zama alham tafito daga ɗakinta hannun ta rike da waya ,ganin mummy azaune yasa ta karaso da sauri, Zama tayi kusa da mummy tace, "mummy kin dawo?
"Eh kawai tace tayi shiru.
sake gyara Zama tayi tace, "mummy yakukayi? Kuma ina Hafsah take? Ko a can zata kwana?
Rike kanta mummy tayi jin yanda yake barazanar tarwatsewa ta dakawa ilham tsawa tace, "don Allah bacemin da gani duk ba dalilin ki bane gashi yarana suna niman juyamin Baya wanda hakan bai taba faruwa ba, ke kanki shaida ce duk abinda nasaka su Wala Wanda yayi daidai da ra'ayinsu ko kuma akasin haka, babu wanda yataba ɗaga Kai yace hakan baiyi mishi ba,amma gashi saboda gyara talgen wani nawa yayi ruwa,tashi tayi tashige ɗakin ta tana share hawaye da bakin zanin ta.
Mikewa ilham tayi ta shiga zarya aɗakin , can tace,"tabde jam wallahi bazata Sabo ba domin kuwa inada tabbacin zuwa yanzu ina ɗauki da cikin Najib, to Yabzanyi na shiga uku bara na kira sha'awa naji yanda zamuyi,cikin sauri tashige ɗakin ta.
kiran sha'awa tayi ta faɗa mata duk abinda ke faruwa, Murmushin mugunta sha'awa tayi tace, "kekam Karki damu badai kin tabbatar da kina ɗauke da cikin Najib ajikin kiba?
bakin ilham har rawa yake tace ,"tabbas hakane domin inajin yanayin ajiki na amma IN SHA ALLAH gobe zantafi asibiti Don kara tabbatarwa ,sallama sukayi sannna ilham ta kwanta tana nazarin yanda Abin zai kasance.
******
Yanda mummy taga safe haka taga dare domin kuwa salloli tayi Tana Mai miki rokonta gun mai sammai daya Kare mata da ya'yanta cikin kariyar sa, koda gari yawaya gabaki ɗaya fuskarta tayi jawur kasancewar ta farar mace duk da shakaru sunja hakan bai Hana farin fatarta fitowa ba,fitowa falo tayi ta zauna tana Jan Casbi,ilham kuwa kwalliyar ta taci tafito tana yar wake waken ta, Ďago Kai da mummy zatayi suka haďa ido da ilham cikin sauri ilham taja ta tsaya gabaki ɗaya jikin ta rawa yake Sam batayi tsammanin ganin mummy afalon ba.
Kallon ta mummy tayi tace, "ya kika ja kika tsaya ina fita zakiyi? Sannan har wakar tazo karshe?hmmn gaskiyar hausawa da sukace mutum mugun icce ko ka mutu sai anɗaure ka,don haka jeki abinki.
Kai akasa ilham taja ta wuce, dondai kawai zuwa asibitin yana da mahimmanci ne, shiyasa amma wallahi data fasa.
Tana fita mummy tayi salati tace dama haka mutumin duniya yake ,ni Inanan ina fushi akan ansake ta saki irinna walakancin asha ita ko ajikin ta.
*******
Koda sadiq suka sauko a airport gabaki ɗaya jiyayi jikinsa yayi sanyi taya zai fuskanci mahaifiyar sa? da Wani ido zai kalle ta bayan yanuna bata isa tayi masa hukunci ba.
Ganin yanda yake tafiya duk jikin sa amace yasa labiba tayi saurin karasowa inda yake, haɗa hannuwan su guri guda tayi tace, "karka damu ka kwantar da hankalin ka, karkayi shakkar fuskantar iyayanka Don basu hakuri, ina Mai tabbatar maka wannan itace kawai hanya mafi sauki.
Janyota jikinsa yayi ya bata sidehug yace, 'keɗin fitila ce dake haskaka lungu da sako na rayuwa ta, ina sonki ina fata ALLAH yasauke ki lafiya ya rabaki da abinda ke cikin ki cikin sauki kamar kinyi barci kin tashi .
Dariya tayi tace, "Ameen.
Hafsah dake bayan su kuwa tayi Dariya tace, "hmmm lailai kam wannan shine wasan kwaikwayo.
Duk kansu Dariya sukayi, harsun tsayar da cap zasu shiga sadiq yaji anriko masa Riga ta Baya, cikin sauri yajuya Don ganin wanine wannan, da mamaki sosai fuskarsa lokacin daya GA wata mace, rike da rigarsa.
Ganin yanda yake kallon ta yasa ta tayi saurin cire hannun ta ajikin sa, kallon lafiya yake mata gane hakan datayi ne yasa tayi saurin Mika masa wata farar takarda tana Murmushi ,tsayawa yayi yana kallon takardar ganin bashida niyyar Karba yasa ta zagaya ta gefen da Hafsah da labiba suke tsaya suna kallon ikon ALLAH.
ije takardar tayi acinyar labiba Tana cewa, "kawata ki duba Don ganin abinda ke ciki ina Mai tabbatar miki zaiyi muku amfani keda mijinki,tana kaiwa nan tajuya tayi tafiyar ta, duk kansu binta da kallo sukayi suna mamakin ta,tambaya kowa kewa kansa daga ina take kuma menene acikin wannan takardar da hartake ikiraran su duba zai amfanar dasu.
Da mamaki duk suka isa gida batare da sun duba takardar ba, suna sauka daga cap ɗin suka nufi cikin gidan harzasu Shiga sadiq yaja ya tsaya sosai yake Jinjina laifin dayayi,lailai ALLAH yayi mishi gata daya bashi labiba amatsayin Matar auran sa .
Mummy tana zaune tana duba takardar da ilham ta kawo maka wanda yake nuni da tana ɗauke da jaririyar ciki, duk da tayi murna amma Sam zuciyar ta taki aminta da cikin ita kanta batasan dalili ba.
Sallamar taji anayi kuma tabbas muryar Hafsah ce, bata gama tantance abinda tajiyo ba Hafsah ta shiga da gudu ta rungume mummy, mummy kuwa gabaki ɗaya takasa koda kwakwarar motsi domin kuwa duk wata gabba na jikin ta yasake ,kuka Hafsah ta fashe dashi jin mummy bata Yi magana ba sosai hakan yaɗaga mata hankali, kuka take Tana cewa,"kiyi hakuri ki yafe mana mummy wallahi bamuyi hakan Don bakanta miki Raiba Don ALLAH kiyi hakuri.
Sauke jiyar zuciya mummy tayi ta Ďago ta daga jikin ta tace ,"bakumin komai ba idanma akwai wacce tayi laifin tofa nice, "Don ALLAH ku gafartawa mummyn ki.
Cikin sauri sadiq ya karaso gunta rike mata hannu yayi yace, "mummy mu mukayi miki laifi Don ALLAH ki gafarta mana.
Share hawayan daya gangaro mata tayi tace, "babu komai na yafe muku ALLAH yayi muku abarka yasa ku gama da duniya lafiya.
Rungume ta duk sukayi suna murmushi, labiba kuwa tsayawa tayi daga gefe tana Mai farin cikin sake ganin farin ciki da annashuwa acikin wannan ahalin.
Saukowar ilham tayi daidai da zuwan mummy daidai inda labiba take tsaye, rike hannun ta tayi tace, "ke ɗin Abin alfahari nega kowa domin kuwa Hafsah ta sanar Dani duk abinda yafaru, ina Kara godiya ga ALLAH dayasa kika zama suruka kuma uwa ga jikokina.
"Mummy kamar kin manta da sabon jikan naki dake zuwa koo?
Duk ɗagowa sukayi cike da mamakin furucin ilham, itakuwa saukowa take cike da izza ta tsaya agaban mummy riko hannun mummy tayi ta saitashi daidai cikin ta tace,"kin mance da dan dangi nee tsohowa?
Wani irin gigitatciyar mari sadiq yayi mata bata gama hucewa ba Hafsah ta Kara mata wani ,mummy ma kara mata tayi sannna tace ,"bara na faɗa miki koda kike ikrarin kina ɗauke da juna biyu kuma kika ce na ɗana ne wallahi kwata kwata banjishi ajiki naba Don haka dole aje aduba.
Dariya ilham tayi tace, "hmmm ko zaki faɗamin dalilin ki, ko kuma wani shaida da zainuna cewa ba ɗansa bane? " ku kuma kina tantamar irin tarbiyar da kika bani ne? To ki sani duk wata rawa bin ƙiɗa take, idan nayi ba daidai ba, tofa ƙidanki na biyo.
"Wata murya sukaji daga waje tana cewa"Tabbas nice shaida domin Kuwa nasan komai.
Duk kallon ta suke cike da mamaki, musamman ilham wanda Toni taji wani irin zawo na neman zubo Mata..
*Karku damu kunji auran raihan daga sama ko? Ku biyu ni donjin yanda al'amarin ta kasance bayan fitarsa daga office ɗin dr*
🏝Jawabi ce yar mutan suleja 🏝
[6/13, 14:39] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄
💐
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
3⃣0⃣➖3⃣1⃣
*STORY*
*&*
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Wannan naku ne angel ɗita eesha da fulani*❤❤❤
*Bismillahi rahamanin Rahim*
,,,,,, Karasa Shigowa sha'awa tayi Tana sanye da doguwar Rigar atamfa tayi kyau babu laifi,zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun dake Zagaye da falon.
"duk kansu idonsu na kanta suna jira suji abinda zata ce.
Sha'awa kuwa murmushi tayi tace, "nasan duk kanku zuciyar ku tana cike da son jin karin bayani akan abinda nafaɗa ko? "To karku damu domin kuwa wannan dake tsaye ta nuna ilham wacce tuni gumee yagama wanke mata Fuska"to tafini sanin komai, "malama kiyi musu bayani.
"cikin sauri ilham ta isa inda sha'awa take tace, "Don ALLAH sha'awa Karki min haka kindai san amintar dake tsakanina dake baici ace kin saka Minda haka bak...
Fisgarta sadiq yayi har saida ta hantsila ,Nunata da hannu yayi yace, "wallahi nakara jin bakin ki saina shayar dake mamaki .
Kallon sha'awa yayi rai abace yace, "ke kuma ki gaggauta faɗin abinda kikace kinfi kowa Sani Tunkafin na kira miki police idan muka je can kinga zaki Yi bayani yanda yadace.
Murmushi sha'awa tayi domin kuwa tasan bama sai anji canba zata faɗa tunda dama abinda tazoyi kenan gyara Zama tayi tace, "da farko dai kafin nafara magana inaso ku warware wannan farar takardar dana baku ɗazu.
Aikuwa cikin sauri labiba ta ɗauko ta Mikawa Sadiq, buɗewa yake zuciyarsa tana tsananta bugawa tsoransa ɗaya baisan abinda takardar ta kunsa ba, buɗewa yayi ya fara karanta kamar haka, "
*Ni sha'awa na yanke hukuncin tonawa kawata ilham asiri dangane da cikin dake jikin ta, tabbas kinyi kuskuran yarda Dani dahar kika faɗamin abinda kika aikatawa mijinki na sunna,wata zina da auran shi akanki, Don haka na yanke hukuncin faɗa masa domin kar laifinki ya shafeni,tabbas sadiq ilham tana da ciki saidai fa wallahi wallahi cikin bashida wata halaka dakai, kawai tayi hakanne Don tana ganin hakan shizaisa ka sota feye da yanda Kake son labiba ,domin kuwa duk atunanin ta cikin jikin labiba ya zube,idan kuma baka yarda ba toka tuntubi wannan lambar dake jikin takardar saina jika* ....
Sauke jiyar zuciya sadiq yayi yace, "menene zai bamu tabbacin abinda kika faɗa gaskiya ne???
Murmushi tayi haɗe da fari da ido tace," saboda ina tare da mamallakin cikin, jin abinda sha'awa tafaɗa yasa ilham ta miki cikin sauri ta shako wuyar sha'awa, saida gyar aka kwaci sha'awa ahannun ilham, tuni idanuwan sha'awa sun canza kala, sadiq kuwa gabaki ɗaya ya rude ganin za'ayi Kisan Kai acikin gidan su, da gudu ya dauko mata ruwa yabata Tasha sai sannu yake mata duk da kuwa tarin ya tsaya, kallon ilham tayi tayi mata nuni da ido data Kalli yanda sadiq yaruɗe akanta,sosai ilham ta Kara Kuluwa domin sai yanzu ta gane dalilin sha'awa na jefeta cikin wannan hallakar.
Gyara murya mummy tayi wacce tun ɗazu take kallon Abin kamar amafarki tace, "zaki iya nuna mana wanda kika ikrarin shine mamallakin cikin?
Gyarar muryarta tayi yanda Najib zai iya jiyota, aikuwa cikin second sai gashi yashigo, sanye yake da jins an tsatsaga shi, Askin kansa kuwa yanda dai kukasan gayu suke Yi, tsaye yatsaya yana karewa kowa kallo, kallon sa sha'awa tayi tace, "kafaɗa musu yanda Abin yakasance.
Batare da shakka ko tsoro ba yashiga zaiyana musu yanda Abin yakasance tun daga farko,tashi ilham tayi jikin ta na rawa ta tsaya gabansa tace, "Allah ya'isa tsakanina daku, tabbas nasan wannan cikin bana yaya sadiq bane, amma kune kuka bani shawarar aikata haka Don haka na barku da fitowar rana zuwa faduwar ta ALLAH saiya nuna muku kuskuran k....
Wani lafiyayyiyar mari Najib ya haskata dashi harsaida bakinta yafashe, nuna ta yayi yace, "kika kuma yimin ALLAH YA isa wallahi saina canza miki kamannu ,lokacin da kika kawo kanki guna kin faɗamin cewar kina da Aure ne da harzaki min Allah ya'isa??
"to bara kiji inada tabbacin cikin jikin ki bazai wuce wata ɗaya da sati ɗaya ba Don haka na baki nanda wata bakwai ki kawo min jaririya ta ko jariri na.
Gabaki ɗaya rain sadiq yayi mummunar baci daga hannun sa yayi da niyyar Marin sa yaji anrike masa hannun sa cikin da mamaki yajuya Don ganin wanine daddy yagani yana tsayayar da hawaye yace, "karka ta bashi sadiq kabarshi duk abinda Kagani ka dauka kaddaran muce....
" tafaru kuma babu yanda zamuyi da ita, juyawa yayi ya kalli Najib yace, "tabbas naso ɗaukar babbar mataki akanka, amma jin cewa bata faɗa maka ita matar Aure bace yasa na sasauta hukuncin da nayi niyyar aiwatar akanka,kaje na barka da ALLAH.
"Ke kuma da kika kawo mana wannan zancan idan da saka hannun ki aciki kema kije mun barki da Wanda ya halilce ki, idan kuma babu to mun gode ALLAH yasaka miki da mafificin alkairi.
Yana kaiwa nan yashige ɗakinsa, rufe kofar dama dawowar sa kenan daga tafiya, yana shiga ya fashe da kuka, gabaki ɗaya sai sambatu yake wanda kana ji kasan ba'acikin haiyacin sa yake faɗansu ba,cewa yake, "yaya ka gafarta min nayi maka alkawari kuma na kasa cikawa, wallahi ALLAH yana shaida yanda nabawa yarana tarbiya haka na baiwa ilham, amma ga abinda tayi, yaya ka kafarta min.
Kuka sosai yake cikin kankanin lokaci zazzabi mai zafe ya rufe shi, duk yanda mummy taso ya bude kofa amma ina tuni yama daɗe da sumewa batare da sunsan hakan ba.
***
Sha'awa da Najib kuwa fita daga gidan sukayi jikin su duk amace, basu taba tunanin haka Abin zai tafi ba sosai abinda daddy Ya faɗa da kuma addu'ar da yayi,sosai yayi mugun tabar su ,sanann sunada tabbacin addu'ar zata bisu domin kuwa sune suka daurata ahanya sukayi mata gadar zare ta afka.
Gabaki ɗaya abin duniya yayi wa sadiq yawa duk kansu cike da tsansar damuwa suke sakamakon rashin buɗe kofar da daddy yayi,can dai mummy tace to koza'a karya kofar ne domin kuwa shirun yayi yawa.
Fita sadiq yayi yayiwa mai gadi magana aikuwa cikin mintina kalilan suka karya kofar ganin yanda daddy yake kokawa da numfashin sa yasa gabaki ɗaya hankalin su yatashi mattuka ,da sauri aka nufi asibiti dashi.
Ilham kuwa tana ganin sun fita itama ta fita bata tsaya ko inaba sai gidan sadiq , ɗakin ta tashiga ta ɗauko ɗayar kullin maganin da ta zubawa labiba, batare da tunanin komai ba tazuba acikin cup haɗe da zuba ruwa ta kaɗa ta juye abakin ta.
Bairo da takarda ta ɗauka ta Yi rubutu na kusan mintina uku Tana gamawa ta ije tafara wani irin Mika, rike
Cikin ta tayi Tana karanto duk kannin addu'ar data zoo bakin ta, cikin kankanin lokaci jini yace Salamu alaikum ganin haka yasa hankalin ilham yayi masifar tashi kashe kanta fa zatayi koya makomarta?
Tuna hukuncin da ALLAH ya tana darwa duk wanda ya kashe kansa da kansa , ihu ta farayi tana kiran sunan mai gadi, Mai gadi yana zaune yaji kamar anakiran sunan sa,dake yaga shigar ilham hakanne ya tabbatar masa da cewa lailai ita ke kiransa .
Da saurinsa yashaga gidan afalo yaganta kwance cikin jini da alama MA ta Sumee.
Ganin haka yasa yafita da gudu ya ɗauko wayar sa yayi yakira Sadiq ringin ďaya ya ɗaga, aikuwa batare da bata lokaci ba ya zaiyanawa sadiq abinda ke faruwa.
Cikin kankanin lokaci sadiq ya iso gidan batare da bata lokaci ba yanufi asibiti da ita, daidai lokacin Dr dake duba daddy yafito, da sauri mummy tanufo gunsa saidai yanda ta ganshi gabaki ɗaya jikin ta yayi sanyi ,gabaki ɗaya acikin su anrasa Wanda zai fara yiwa wani magana acikin su,candai mummy ta tabude baki tace, "Dr ya ji..kin..nasa?
"Hmmm hajiya abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki kituna cewa duk kannin mai rai mammaci nee ,ni dake duk bamu isa mu kaucewa hakan ba, Don haka nakeso kiyi hakuri alhaji ALLAH daya bamu aronsa ya karbe abun sa.
Wani irin kuka ne ya kubucewa mummy kuka take mai taba zuciyar duk wani mai sauraro, saida tayi mai isarta dr yana rarrashin ta sannan ta Share hawayan ta tace, "babu damuwa ALLAH yajikan alhaji yasa ya huta, bara na Faɗawa yayansa suna wancan gurin dake ankawo yar uwarsu itama bata jin daɗi .
Allah ya sauwake yayi mata sannan ya wuce ,ita kuwa mummy dakin da aka kwantar da ilham ta nufa zuciyar ta namata wani irin radaɗi.
Da sallama tashiga, ilham na ganinta tafara miki miki tana kiran sunan ta, cewa take, "mummy ki gafarta min duk da nasan bancancanci yafiya agunku ba, amma Don ALLAH ku gafartamin kozan samu sasaucin abinda nake ji.
Kama hannun Sadiq da labiba tayi tace, "nasan na zulumce ku Aɗan zaman da mukayi atare, amma ina Mai kara jaddada rokona agunku daku gafarta mi.. Bata karasa maganar ba harshanta ya karye gashi dai azahiri magana take, amma babu mejin abinda take faɗa , fita sadiq zaiyi Don kiran Dr, amma tayi saurin riko masa hannun Dan har yana jin zafin rokon datayi masa, can dai yaji tasasauta riko kuma ta daina fisge fisgen da take yi.
Taba fuskarta yayi yaji wani irin sanyi haka yashiga taba jikin ta, amma yanda yaji fuskarta haka duk jikin nata yake, kiran sunanta yashiga Yi yana jijigata.
Labiba kuwa matsowa gunsa tayi ta rike masa hannu Tana girgiza masa Kai hawaye kuwa kamar wasu ke korar wasu, kallon ta yake kamar bai fahimci abinda take nufiba, ganin haka yasa mummy ta janyo zanin dake jikin ta ta lullube mata jikin ta zuwa Kai.
Sai alokacin sadiq ya fahimci Ashe mutuwa tayi, wani irin kuka ne yakubce musu lokaci ɗaya musamman mummy wace dama tazo ta faďa musu mutuwar daddyn su ,sai kuma tazo ta tarar da wannan.
Rungume Hafsah tayi tace, "shikenan kunyi rashin mutane biyu lokaci ɗaya , Ya ALLAH kabamu dangana da juriya bisa wannan jarabawar dakayi mana.
Duk zuba mata ido sukayi kowa da tunanin da kekai kawo acikin zuciyar sa, Ďago Kai mummy tayi tace, "kuyi hakuri ALLAH yafimu sanin dalilin hakan daddy ALLAH yayi mishi Rasuwa dama abinda nazoo faɗa muku kenan.
Share hawayan sa sadiq yayi yanufi ďakin da aka kwantar da daddy, ganinsa yayi kwance kamar ka kira shi ya amsa, share hawayan daya gangaro masa yayi yace, "be a man sadiq yanzu ba lokacin kuka bane.
Fita daga ɗakin yayi yashiga kiran dangi da abokin arziki yana faɗa musu, kankace mee asibitin ya cika da mutane ,nan danan aka kwashe su aka nufi gida dasu aka suturce musu jikin su, sannan aka sadasu da gisansu na gaskiya saidai fatan dacewa ga duk kannin su, mukuma allah yayi mana kyakyawar karshe ......
🏝. *Taku SAFNAH ALIYU JAWABI* 🏝
[6/13, 14:39] Safnah: ❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANAƊIN SOYAYA*
❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
*By*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
3⃣2⃣➖3⃣3⃣
*Bismillahi rahamanin rahim*
,,, Sosai jama'a suka tausayawa wannan ahalin ganin yanda mutuwa tayi musu shigar bazata.
Koda maman ilham tazo tayi kukan mutuwar ƴar ta gudan jinin ta sosai.
Saidai gabaki ɗaya mummy tayi wasu sadiq gargaɗin karda wanda yafaɗi maso dalilin rasuwar nata, don haka duk wanda yazo saidai ace masa zazzaɓi ne kawai, yayi daidai da ajali.
Gidan cike take da masu zuwa ta'aziya ciki kuwa harda raihan, domin sosai mutuwar alhajin sadiq yataba mishi zuciya, da Misalin karfe uku na yamma suka shigo gidan shida amarya sa, sadiq yaji ɗadin ganin abokin nashi cikin kwanciyar hankali, bayan sun danyi gaishe gaishe tare da jajanta mishi kan rashin dayayi suka shiga cikin gidan Dan gaishe da mummy.
Sun tarar da ita cikin mutane tana karbar gaisuwa, fitowarsu kenan daga kitchen hannun Hafsah rike da jug mai ɗauke da kunu data damawa labiba, domin yanzu abinda take ci kenan kawai ya zauna.
Jin muryar sa tayi wacce har duniya ta naɗe bazata taba mance amonta ba,, cikin sauri taja ta tsaya, kurawa juna ido sukayi kamar yau suka fara ganin juna.
Lura da yanda yanayin ta gabaki ɗaya ya canza yasa ta janye mata hannu suka karasa shiga falon, kan labiba akasa harsuka karasa, Zama tayi amma gabaki ɗaya jikinta yayi sanyi.
Abangaran raihan kuwa sosai yayi mamakin canzawar labiba, ta Kara kiba, fatarta tayi kyau, karamin cikin dake jikin ta yayi mata kyau mattuka.
Gaisawa sukayi sama sama sannan raihan yace, "gimbiya labiba baidai har yanzu fushi aka Dani bako?
Ɗago Kai tayi cikin sauri don Sam bata tsammaci zuwan tambayar ba,sunkuyar da Kai tayi tace, "a a wallahi nikam ban rike kaba,nandai suka nimi yafiyar juna har yake sanar dasu mutuwar zakkiya sosai suka jajanta masa.
Sunɗan jima kafin sutafi da alkawarin sabonta abotar su.
Bayan kwana biyu sadiq da labiba sukayi shiri Don zuwa dubo compney ɗinta dan sosai akwai tsare tsaren da suke son Yi.
Suna isa kuwa suka shiga gabatar da abinda ya kawo su, cikin kankanin lokaci suka gama abinda yakai su, har zasu shiga mota raihan ya iso,sosai sukayi mamakin ganin sa Don kuwa babu wanda yafaɗa masa zasu zo, Gaisawa akayi cike da farin cikin sake ganin juna.
Har zasu shiga mota raihan yaja hannun Sadiq suka koma gefe ,murmushi sadiq yayi yace, "duk inda kaji kira tofa ansamu Don haka inajira naji dumus.
Murmushi shima yayi yace, "azahiri gaskiya kasan cewar bandaɗe dayin Aure ba, amma wallahi tunda naga Hafsah naji ta cikemin gurbin dana rasa,wallahi ina sonta mattuka Don ALLAH aboki.
Mamaki da farin ciki ne suka rufe sadiq, farin cikin sa ɗaya , shine wato tunda raihan yazo musu gaisuwar rasuwa gabaki ɗaya yarasa sukuni Don jiyake raihan yana iya kwace masa mata duba da yarda suke kallon juna wancan ranar, mamakin sa kuwa itace yanda gani daya harya kamu da son Hafsah .
Tuni zufa yafara karyu wa raihan ganin yanda sadiq yayi shiru, kama hannun sa yayi yace, "wallahi abokina nayi maka alkawarin rike maka kanwar ka da amana, Don ALLAH karkace a a tuni idonsa sun cika da kwalla.
Dariya Sadiq yake harda rike ciki yace,"Kai yanzu akan Hafsah Kake son yin kuka?kai amma wallahi kabada maza haba dai.
Murmushi raihan yayi yace, "bazaka gane bane aboki.
"to shikenan ALLAH yashige mana gaba, amma kasani bazanyi wa kanwata auran dole ba, idan taji ta amince zata Aure ka shikenan nikam bana da matsala tunda nazama yayar ka.
"Yauwa kuma baka bani labarin yadda lokaci ɗaya kawai mukaji labarin aure babu sanarwa ba.
Murmushi yayi yace, "kaima ka koyi son jin gulma ko?
Dariya yayi yace, "nidai ina sauraron ka.
*FLASH BACK*
B
ayan fitar raihan daga asibitin gida ya nufa, yana kara nazarin shawarwarin da dr ya bashi.
Cikin ikon ALLAH kuwa daya dukkufa shan magungunar daya bashi, cikin ƙanƙanin lokaci allah ya kawo waraka cikin lamarin sa, koda ya koma asibiti, dr sosai yaji daɗin ganin yanda jikin raihan yayi sauƙi.
Suna cikin magana sukaji anyi sallama, amsawa duk sukayi, cike da natsuwa ta ƙaraso ciki, rusunawa tayi har ƙasa ta gaishe su.
Amsawa raihan yayi batare daya ko kalli fuskar taba, miƙawa dr mas'ud abinci tayi, murmushi yayi yace"autar mum sai yanzu kika yi ra'ayin kawomin abincin?
Bubuga ƙafa tayi irin taso ta shagwaɓanɓun yara tace, "wallahi nidai bro kayi kayi aure na huta da wannan jigilar.
Murmushi kawai yayi yace, "shikenan jeki.
Aikuwa kamar dama jira take, nan danan tayi musu sallama ta tafi.
Tun daga wannan lokaci aminta mai tsanani ya shiga tsakanin raihan da mas'ud.
Lokaci zuwa lokaci raihan yakan ziyarci gidan su mas'ud.
Hauwa kuwa tun daga ranar data ga raihan taji duk duniya babu wacce take so sama da raihan, tun tana ɓoyewa harta fito ta bai yanawa ɗan uwan ta, da farko yaso nuna rashin amincewar sa, amma ganin yanda ta tashi hankalin ta hakan yasa yayi karfin hali ya sanarwa raihan, duk da sam baya jin zai taba karɓar wata soyaya kuma, amma ƙima da darajar mas'ud yasa ya aminci, duk da baya jin ɗigon sonta acikin zuciyar sa.
*Back to story*
Sauke ajiyar zuciya raihan yayi yace, "kaji yadda abin yakasance.
"Tofa kace dai aure ne yakaika Lagos abokina?
,,,, Dukan wasa raihan yakai masa, haka suka cigaba da tattauna yanda Abin zai kasance, ganin kamar ma sun mance dasu yasa Hafsah taje har gurin tace, "yaya Kodai mutafi nee??
"a a kujera ni ganinan.
Wani irin kallo Hafsah ta Lura raihan yana aika mata dashi, basarwa tayi kamar Ma bata ganshi ba, tayi gaba.
Kallon ta yake har saida sadiq ya tabe shi yana cewa,"malam Kadda ka kayarmin da kanwa. "nikuma Matata ba.
Dariya duk sukayi suka shiga mota kowa ya kama gabansa .
Koda raihan yatafi gida Addu'a ya dukkufa Yi Don samun shiga agun Hafsah har saida matar sata fahimci akwai abinda ke damun mijinta, yana zaune yayi tagume ta shigo cikin Shigarta mai daukar hankali Ta zauna kusa dashi, cire masa tagumin tayi tace,"honey Lfy make damunka?
Shiru yayi ita kuwa hakan yasa ta fara hawaye Don sosai canza mata dayayi yana mugun damun ta, ganin haka yasa ya warware mata daga biri har wutsiya.
Share hawayan ta tayi ta riko hannun sa tace, "karka damu IN SHA ALLAH zaka samu Hafsah, saidai Don ALLAH kayi kwakari kamanta adalci tsakanin mu.
Shima rike hannun ta yayi yace, "IN SHA ALLAH bazaki taba samun matsala daga gare niba.
"shikenan yanzu muje mu shirya Don babu bata lokaci zamu tafi gidan,sosai yayi godiya ga ALLAH daya bashi mata mai tsantsar tarbiya da hakuri.
******
Hafsah kuwa tunda sadiq yafaɗa mata abinda raihan ya faɗa mishi shikenan tashiga wasan boya dashi ,Don ita dai wallahi bazata taba auran mai mata ba, labiba ma tasa baki duk da dai farko dataji maganar sosai ranta ya baci, saidai tayi ta sallar dare tana addu'ar ALLAH yakawo mata agaji akan lamarin, cikin ikon ALLAH kuwa yanzu babu abinda take ji game da auran nasu duk da dai har yanzu Hafsah bata amince ba.
Yauma kamar kullum tunda safe suka iso gidan, suna zuwa labiba ta shiga dakin Hafsah lokacin kuwa tana toilet, jin muryar labiba yasa tace, "ya Salam wai duk saurin danake Yi karsu zo su sameni agida saida suka shammaceni Waiyo ALLAH.
Haka kuwa babu yanda ta iya ta fito Tana murmushi wanda Dagani Kansan kawai ankirkire tane.
Murmushi itama labiba tayi tace, "hmmm wato har gudun mu kike ko?
"a a akanmee? wallahi ko ɗaya kawai dai muna samun sabani ne.
"hmmm shikenan dama nazo ne Don muji amsar ki kindai san kece kika ce abaki lokaci ko?
Tasowa tayi ta zauna kusa da labiba idonta ya cika taf da hawaye tace,"yanzu aunty labiba kema kin yarda na Aure raihan mutumin da kike so fiye da Tunanin mai tunani, shine kika sona aura?
"mutumin daya azabtar da rayuwar ki, so kike nima ya azabtar dani? Mutumin da yake da mata bakya tunanin Insha wahala agurin ta?
Kamar Daga sama sukaji anacewa ,'aa wallahi indai nice babu abinda zanyi miki ki kwantar da hankalin ki, indai gida ne muna miki Maraba Nida baby.
Duk kansu kallon ta suke cike da mamaki Sam basu taba zatton ganin ta a wannan lokacin ba .
Da murmushi afuskar ta takaraso Zama tayi itama abakin gadon tace, "idan yarasa ki wallahi gidana tarwatsewa zaiyi ki taimaka,ga mamakin su hawaye takeyi sosai.
Duk gabaki ɗaya anrasa wanda zai rarrashe ta haka suka barta tayi tayi ,Candai labiba ta ɗago tace, "ki daina kuka IN SHA ALLAH komai zai zo cikin sauki.
AJiyar zuciya tayi tace, "aunty labiba bakisan matsalar dana fuskanta adalilin kiba, Don haka bana fatan sake fuskantar wani a dalilin Hafsah ,shiyasa nake rokon ki Aure mijina ina Mai tabbar miki wallahi ba zakiyi dana sani ba.
Tausayi sosai tabawa Hafsah ganin yanda take kuka zaka fahimci daga cikin zuciyar ta take fitowa, ajiyar zuciya Hafsah tayi tace, "shikenan na amince ALLAH ya tabbatar da alkairi tana gama faɗan haka ta shige toilet ta rufe kanta.
Rufe bakin ta tayi ta fashe da kuka Tana jin wani irin yanayi mai wuyar fasarawa , ita dai bazata ce bata son raihan ba, kawai dai tana jin babu daɗi ne idan ta tuna matsayin shi agun aunty labiba, shin tayi mata halalci kuwa.
Sukuwa da farin ciki suka sauka kasa Don sanar da mazajansu wanda tun ɗazu suke saka idon ganin su da kuma jin abinda suke addu'ar ji.
Koda suka faɗa musu kuwa suma farin ciki sukayi musamman mummy.
Cikin yar kwanaki kalilan maganar Aure ta Kankama har ansaka rana nanda wata ɗaya .
Sosai duk kansu suke shiga shirye shiryan bikin, gabaki ɗaya tsarin gida sadiq yasa aka sauya aka Gina masa shashinsa agefen na mummy Don bazata iya Zama ita kaɗai cikin gidan ba, kuma dama bai kamata abarta ita kaɗai ba.
Kankace mee tuni gida ya ɗau haske, labiba kuwa ciki yayi girma shiyasa koda bikin yazo duk inda zata tafi sadiq yana makkale da ita Don bayaso ta wahalar masa da Dan jariri,mutane kuwa sai Dariya suke masa ganin yanda ya mace akan labiba da abinda ke cikin ta.
Ansha shagalin biki sosai biki yayi biki anyi wasa da naira, Inna sadiya da abba sunyi murna sosai lokacin da suka haɗu da labiba suka roketa yafiya,itama da farin ciki ta amshe su.
*Kuyi hakuri wallahi ban cika shiga event na harkokin biki bane, shiyasa bansan yanda ake gudanar dasu ba Don haka kuyi hakuri please*🙏🙏🙏
Sosai gidan hafsah ya tsaro Don koni saida naji sha'warar gidan ,saidai fatan zaman Lfy mai ɗaurewa.
*Bayan wasu watanni*
Labiba nagani rike ahannun Sadiq sai yarfe hannu take alamar tana cikin wani Hali Waro ido nayi nace what kece har anzo gurin to ALLAH yaraba lafiya.
Cikin awa ɗaya labiba ta santalo ɗanta namiji mai kama da sadiq sak,sosai wannan ahalin suka shiga farin ciki Mara misaltuwa .
Koda ranar suna tazo Hafsah ce ta zabar masa suna sunan mahaifinsu aka saka mishi wato YUNUSA amma zasuna kiransa Amman.
Kyauta sosai labiba ta samu harda yan mai duguri saida suka halalci sunan.
Hafsah kuwa Cikinta yayi girma sosai,bayan sunan Amman da wata shida itama ta haifo diyarta mace aka saka mata sunan mummy.
Haka rayuwa ta cigaba da garawa soyaya mai karfi da shakuwa ke kara samun gurbi a zuciyoyin wannan ahalin, saidai fatan ALLAH yakawar da shaiďan atsakanina su.
*****
Sha'awa kuwa tunda suka fita da Najib daga cikin gidan mummy suka fara soyaya.
Ashe Najib yana ɗauke da cutar HIV Ahankali ciwon ke cin jikin su batare da sanin Suba, wata rana sha'awa tana zaune agida wata mata masu gwajin cutar suka shiga gidan batare da wata damuwa ba sha'awa ta bata hannun ta aka zuke jinin ta aka fara gwadawa.
Yanayin kallon da matar take bin sha'awa dashi yasa gabaki ɗaya taji ta tsargu,kallon ta tayi tace, "ke lafiya?
Murmushi matar tayi tace, "lafiya kalau saidai inaso kisani itafa cuta ba mutuwa bace Don ha... Marin da sha'awa tayi mata tayi daidai da shigowar Najib cikin gidan Dan dama aɗakin sa wani lokacin take kwana,to yauma hakance ta kasance.
Da sauri ya karaso gurin yace,"lafiya me kuma haka wacece wannan?
Kallon matar sama da kasa tayi tace,"kaji min yar iska wai inada cutar HIV.
Waro ido yayi yace, "mee ne h... I.. V?cikin sauri ya zauna ya Mikawa matar hannun sa waita gwada shi.
ALLAH sarki matar bataye fushi ba ta zuke jinin sa.
Tana gwadawa shima ya nuna akwai aikuwa tunawa da irin Marin da Tasha shiyasa ta tashi tsaye tace,"Don ALLAH ina toilet?
Nuna mata toilet yake gabaki ɗaya hankalinsa Baya kanta aikuwa da gudu ta fita daga gidan saida ta tabbatar tayi dan nisa sannan tace, "wallahi kaima kana dashi.
Jin haka yasa Najib Ya shake wuyar rigar sha'awa ya Matse ta da bango har saida ta Kai kasa Don gabaki ɗaya kafafunta bazasu iya daukar taba , gabaki ɗaya idanuwan ta sun firfito, ganin da gaske kasheta zaiyi yasa ta rarumi wakar dake kusa da ita ta daba masa aciki.
Da sauri ya sake ta tafadi kasa Tana tari, ganin irin illar data mai yasan zaiyi wuya ya rayu hankan yasa ya ɗauki wukar ya caka mata abaya, Tana juyawa ya daba mata akirji.
Ita kuwa cikin azama da azabar fitar rai da take ji yasa ta janyo abinsa ta rike harsaida ta rabashi da jikin sa, nanda nan rai yayi halinsa baiko Shura ba.
Itama haka.
Gabaki ɗaya duk sukayi mutuwar guzuma, saidai muce ALLAH yasa muyi kyakyawar karshe.
*Ni kuwa nace, dama hakki wata bari?*
*indai duniya ce duk abinda ka shuƙa tabbas zaka girba daidai da yadda ka shuƙa ta, ALLAH yasa muyi ƙarko mai kyau*
*Bissalma anan na kawo karshan wannan liltafin mai suna duk asanadin soyaya, ALLAH yasa abinda muka gani a ciki ya amfanar damu, ALLAH yasa mufi kafin zuciyar mu, ina kara Mika godiya ta ga ,ummu21,maryambinji,rrahinaabduolkadree,da dai sauran su ina godiya mattuka, da fatan sake jina asabon liltafi na mai suna AMJAD*.
*Bissalma*
0 comments:
Post a Comment