*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 1*
Wasu yara ne ke wasa su uku,,, yaran bazasu wuce shekara goma sha uku ba zuwa sha hud'u .'Dayar ce mai suna Fatima ta dubi 'yan uwan wasanta Maryam da Fadila,,, tace "Maryam ya kamata muje gida yanzu fa,, mun dad'e sosai muna wasa gashi rana ta fara fitowa ".Fadila tayi charab ta chafke maganar tana hararar Fatima,, sannan tace "ke idan kin gaji da yin wasa ne mu bamu gaji ba,, saboda haka ga hanya nan ki wuce zuwa gida babu wanda ya tareki ".Fatima ta dubi Fadila duba na rashin son fad'a,, tace "haba Fadila dad'ina dake akwai saurin fushi,, ni dama wasa kawai nakeyi muku na fad'i haka ne saboda kada a nememu arasa a gida "."To wa ne aiki ne zamuyi idan muka koma gida,, nidai gaskiya ban gaji da yin wasa ba ".Cewar Fadila cikeda rashin son maganar.
Sai asannan ne Maryam ta dubi Fadila tace "ya isa Fadila abar maganar,, kada abin ya zamar muku fad'a a tsakaninku muji kunya. Amma ai gaskiya Fatima ta ke fad'a ba k'arya ba ".Fatima tace "k'yaleta Maryam ai ya riga ya wuce adaina tunawa "."To shikenan babu komai ai ".Cewar Maryam dayake ita yarinya ce nutsattsiya mara son magana sosai,, sunyi shiru dukansu na tsawon lokaci,,, can dai Fadila ta katse musu shurun tace "ku zo mu fara 'yar chahu muna gamawa muyi gida ko,, amma nice ta farko ".Fatima da Maryam suka gyara zamansu domin suji dad'in wasar,, Fatima tace "ni ce ta biyu "."Ni kuma ta uku ".Inji Maryam cikeda natsuwa da kwanciyar hankali.
Suna tsakar wasarsu cikeda matuk'ar jin dad'i da nishad'i sosai,,,daga ganin yadda sukeyin wasar suna cikin walwala da farin ciki. Sun jima sosai suna wasa can dai suna batun tashi gidajensu,,,,saiga Iya Gwamma tazo wucewa zuwa gidanta. Ta zo zata wuce ne sai kuma ta dawo baya wurinsu Maryam,,, suna ganinta suka durk'usa su uku suna cewa "Iya ina kwana,, ya gida?.Lafiya k'alau 'yan uku masu kamada juna,, kuma 'yan matan gobe mi kukeyi anan ne? ".
Suka had'a baki wurin cewa "wasa mukeyi Iya Gwamma,, mi zamuyi miki Iyarmune ko wani abu kikeso mu siyo miki ne?".Iya Gwamma ta tsura musu idanu na wani lokaci tana kallonsu,, irin kallon na k'urilla da bai dace ba. Baki da hanci ta saki tana musu kallon kwad'ayi,,, da k'urilla nason cimma wani buri nata. Can dai da k'yar ta daure ta b'oye damuwarta da kwad'ayinta,,tace "muje gidana in baku kud'i ku siyomin biredi da madara shagon Mande ".
Fadila tayi saurin cewa "to Iya su Fatima ku tashi muje gidan Iya mu amshi kud'i,, mu siyo mata biredi da madara ".Maryam da Fatima jikinsu duk yayi mugun sanyi tsoro da fargaba ya bayyana a cikin zuk'atansu,, su kansu basu so zuwa ba amma babu yadda suka iya. Kamar suce basu zuwa ba amma ba zasu iya kallon tsabar idon Iya Gwamma ba,, suce ba zasu iya ba saboda ko banza tayi jikoki dasu. Can dai Fatima ta tattaro dauriya tace "to Fadila, Maryam tashi muje mana kinyi shiru lafiya dai? ".Maryam itama ta mik'e tsaye tace "Lafiya k'alau Fatima ".Tana kakkab'e jikinta da yayi k'asa saboda wasa,, su ma su Fatima suka kakkab'e jikinsu,, Iya Gwamma ta dubesu tace "ku wuce muje zuwa gidan na gaji da tsayuwa ".
Suka ce "to Iya ".Iya Gwamma ta sasu agaba suna tafiya,, ita kuma ta tsaya abayansu tana k'are musu kallon k'urilla tasa lasar baki da fitar da halshe,,, su Maryam suna tafiya suna fira cikeda matuk'ar jin tsoro da fargaba akan abinda kan iya faruwa dasu. Saboda maganar gaskiya da sunsan Iya Gwamma ce zata biyo ta inda suke,,, da tuni sun cikama bujensu ko zanensu iska. Domin Iya Gwamma ta shahara wurin maita da kuma sata a cikin unguwarsu,,, babu wanda baisan da zamanta ba sannan babu inda sunanta baije ba akan ita *MAYYA CE*.
**********************
*****Acan gidansu Maryam kuwa Mama Sa'ima ce zaune da yayan Maryam mai suna Mubarak,,,, suna firarsu ta tsakanin uwa da d'a. Yaya Mubarak ne ya dubi Mama Sa'ima yace "Mama tun d'azu muna fira banga giftawar yarinyar nan Maryam ba,, wai ina taje ne kuma? ".
"Hmmm Mubarak sun fita tun d'azu itada su Fatima,, gashi yanxu har azahar tayi basu dawo ba ".Inji Mama Sa'ima fuskarta tana bayyanar da damuwa.
Saida gaban Mubarak ya buga da k'arfi,, ya bada rasssss! Sannan ya tattaro natsuwarsa wuri d'aya,,, domin kada ya tashi hankalin mahaifiyarsa. Ya dubeta duba na natsuwa ya tausasa halshensa,, yace "Mama ki kwantar da hankalinki Insha Allahu suna waje suna wasa,,, kuma yanzu nan zanje ince su dawo gida hakanan. Ai wasan ya isa yau sai kuma gobe ".
"Da kako k'yauta Mubarak kayi sauri kaje kace ta dawo gida hakanan,,, saboda ina tsoron kada Alhaji ya dawo bai sameta gida ba. Nasan ni zai azama fad'a ni kuma ban aiketa ba wurin yin wasan banza ba ".Cewar Mama Sa'ima cikeda damuwa da tsoro..
Mubarak ya dubi uwar yace "ki daina damuwa Mama yanzu nan zan turo k'eyarsu,, insha Allahu Alhaji ma bazai san ta fita ba ".
Uwar tace "to Allah yasa tun can ka fara dukan shegiya domin Maryam agaskiya batajin magana,, kullum ina gaya mata idan ta fita wasa ta daina kaiwa azahar bata dawo gida ba. Amma tayi kunnen uwar shaggu da maganata saboda tana son babanku ya sani gaba ya cimin mutunci,,, wallahi yau kam sai jikinta ya gaya mata zata yabama aya zak'inta ".Ta fad'a cike da jin haushin Maryam.
Mubarak ya mik'e tsaye sannan ya dubi mahaifiyarsa,, cikeda lallashi yace "kiyi hak'uri Mama Maryam bazata koma dad'ewa awaje ba,,, yanzu zanje in korosu su dawo gida wlh amma dan Allah kada ki duketa Mamanmu ".
"Naji bazan duketa ba ,,, saboda kai ka haifarmin 'yar ko Mubarak ".Inji Mama Sa'ima cikeda sababi da masifa.
Mubarak ya sassauta murya yace "ba haka bane Mamanmu,, ganin nayi bugu baya magani sai dai addu'a da nasiha Allah ubangiji ya shirya mana zuri'armu. Kuma ya huci zuciyarki yake mahaifiyata,, kiyita hak'uri damu wata rana sai labari ".
Jikin Mama Sa'ima yayi matuk'ar sanyi akan maganar Mubarak,,hak'ik'a tasan duk abinda ya fad'a gaskiya ne babu k'arya acikin maganarsa. Kuma tasan Mubarak yaro ne mai natsuwa da iya kalamai masu dad'i da kwantar da hankali ga mai sauraronsa,, sannan yanada kaifin tunani da hangen nesa,, Mama Sa'ima ta numfasa tace "na hak'ura Mubarak Allah ubangiji yayi muku albarka,,, sannan ya shirya mini ku shirin addinin musulunci ".
"Amin Mamanmu,, toni zan wuce yanzu ".Cewar Mubarak.
Maman tace "Allah ya kiyaye hanya Mubarak yasa kayi saurin ganosu ".
Mubarak yace "Amin ".
Yaja k'ofar gidan ya bud'e tareda da fita,,, domin ya koro su Maryam su dawo gida hakanan..
**********************
Su Maryam suna tafiya suna fira har sukazo bakin k'ofar gidan Iya Gwamma,,, sukaja suka tsaya suna jiran harta iso dayake sun fi ta saurin yin tafiya kunsan abu da tsohuwa. Suka zauna suna hutawa can saiga Iya Gwamma ta iso tasa makulli ta bud'e musu k'ofar gidan,,, ta umurcesu dasu shiga cikin gidan dayake yara ne sosai babu wanda yasan ciwon kansa. Suka kutsa kai zuwa cikin gidan tareda Iya Gwamma,, suna shiga babu kowa cikin gidan sai komattsai da raggad'ud'an Iya Gwamma. Babu abinda ke tashi cikin gidan sai k'amshi soyen nama da k'arnin jini,,, dayake su Maryam yara ne babu abinda suka fahimta gameda Iya Gwamma .
Iya Gwamma ta tura ganbun d'akinta ta shiga cikin d'akin,,, ta d'an jima sosai sannan ta fito da kud'i ga hannunta d'ari uku da hamshin. Taba Fatima kud'in tana shafar hannun Fatima da wayo da wayo,,, tace "gashi ku siyomin biredi na d'ari da hamshin madara ta naira d'ari,,, inada sugar da bonbita naira d'arin da ya rage ku d'auka na baku "..
Fatima tace "mun gode Iya amma da kinbar kud'inki,,, ki k'ara ki sayi wani abu ".
Iya Gwamma tazo wurin kan Maryam tana shafa cikin dabararsu ta mayyu,, tace "Ayya 'yar nan k'yautace na baku kuma ba'a maida hannun k'yauta baya ".
"dallah rufe mana baki! Munce kibar kud'inki amma kinzo kinata damunmu da surutunki na banza,, bamu son kud'inki ko ana amsar k'yauta dole ne "Inji Fadila cikeda fitsara da tsiwa.
Iya Gwamma ta dubeta cike da tsananin mamakin rashin tsoronta,, ta bugi Fadila da wasa tace "amma yarinyar nan bakida kunya,, kinsan koni wa cece nayi fa jikanya dake yarinya".
Fadila itama ta dunk'ule hannunta cikeda rashin kunya,,, tayima Iya Gwamma mugun bugu a bayanta. Saida Iya Gwamma ta zabura da k'arfi! Tana mamakin k'arfin hali da rashin tsoro irin na Fadila. Fadila ta harari Iya tace "ina ruwana da kin yi jikanya dani tsohuwa,,, sannan sanin koke wa cece bayada wani amfani gareni! ".Tana murgud'a bakinta.
Hak'ik'a Fatima da Maryam sunyi matuk'ar jin tsoro da firgita! Akan abinda Fadila tayima Iya Gwamma,,, babu abinda jikinsu keyi sai makarkatar tsoro da fargaba. Can dai cikeda masifar tsoro suka had'a baki wurin cewa "dan Allah Iya kiyi hak'uri wallahi haka Fadila take da tsiwa ".
Iya Gwamma idanunta sukayi jawur saboda b'acin rai zuciyarta sai tafasa takeyi akan bak'in ciki,,, jijiyoyin kanta sukayi rud'u rud'u akan b'acin rai. Can tayi ajiyar zuciya na bak'in ciki ta daure tace "babu komai yaran nan amma ta sani taci alfarmarku,,, da wallahi bazata sake yima wani rashin kunya ba,,,amma ta je duniya ce zata ga abinda zai biyo baya! "".
"Mtsss aikin banza! Babu abinda zan gani sai alkhairin Allah,, kurwata kur! Kici kanki kisha bak'in ruwa ".Cewar Fadila tana tofar da yawu,, cikeda masifa da bala'i. Su Maryam ne sukaja hannunta da k'arfi suna bata hak'uri,, suka nufi hanyar zuwa shagon Mande suna tafiya Fadila tana ta masifa da bala'i,,, haka suka kama bata baki suna lallashinta. Suna isa shagon Mande dole tayi shiru suka siye abinda ya kaisu sannan suka juyo zuwa gidan Iya Gwamma.
Suna dawowa suka ba Iya Gwamma aikenta,, sannan su Fatima suka k'ara bata hak'uri akan abinda ya faru. Ta nuna musu babu komai ai tareda yi musu godiya sosai. Sannan sukayi juyawarsu zuwa gidajensu. Bayan fitarsu ne Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta harda fad'uwa k'asa akan makirci,, can tace '"hak'ik'a Fadila kin kawo kanki gidan mutuwa! Sai kinsan kinyi mini rashin kunya. Ko 'yan uwanki da basuyi min komai ba,,, bazan tab'a k'yalesuba balantana ke mara mutunci,, zakiyi nadamar abinda kika yimin a rayuwarki! "Hhhhhhhh haka dai Iya Gwamma ta cigaba da surutunta na son ganin bayansu Maryam..........
_More comment more typing_
_Mugirat Musa_đ
,
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 2*
***Iya Gwamma ce ta kama surutunta na hauka,, mai cikeda bak'in ciki da b'acin rai akan abinda Fadila tayi mata. Can naga Iya Gwamma ta shiga cikin wani d'akin da yake gefen d'akinta da take barci da saka kayayyakinta,, tana shiga ciki ta fito da wata k'warya cikeda jinin mutane. Ta samu wuri saman tabarma ta zauna tanata sambatu da maganganu irin na masu sihiri da tsafi,,, ta jima tanayi saiga rugugin tsawa da hayak'i! Suna bayyana ruwan jinin dake cikin k'warya suna chanza kala daga ja zuwa kore-kore. Nan da nan naga ruwan jini sun fara tururin tafasa,, kamar an azashi saman wuta. Nayi duba zuwa ga idanun Iya Gwamma sunyi jawur kamar barkono,, ga jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta chanza,, ko'ina a cikin jikinta gashi ya k'ara tsawo zago -zago kamar k'aho,,, bakinta babu abinda ke fitowa sai wuta mai mugun zafi. Can naga tayi wasu d'alamisai na tsafi saiga photonsu Maryam su uku ya bayyana a cikin k'warya,, suna tafiya zuwa gidajensu. Iya Gwamma tayi duba cikin k'waryar jini da idanunta jawur kamar kan jaki,,, tace" saina kasheku! Saina cinye namanku d'anye yara! Zan nuna muku ba'a yima mayyu rashin kunya akwana lafiya,,, hhhhh na kama kurwarsu ni Gwamma jikar mayya d'iyar *MAYYA* .Saina banbance muku atsakanin aya da tsakuwa,,, k'ananan marasa kunya kawai daku! ".
Haka dai ta cigaba dayin sambatunta,, tana tofe -tofe a cikin k'warya. Saiga inwar kurwarsu Fadila ta bayyana a cikin k'warya,, Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta da kuma farin ciki mara misaltuwa na cikar burinta....
**********************
Su Fadila suna tafiya suna firarsu cikeda walwala,, kamar babu abinda ya faru dasu agidan Iya Gwamma. Basu jima sosai ba suka had'u da yaya Mubarak,, bayan sun kawo wajen garkar gidajensu. Yaya Mubarak ya dubesu cikeda matuk'ar mamaki yace "Yara manyan gobe ina kuka shiga ne,, tun d'azu nake zagayar gari nemanku ".
Maryam da Fatima suka sunkuyar da kansu cikeda fargabar da irin amsar da zasu bashi,,, tsoro da fargaba ne ya bayyana k'arara akan fuskokinsu. Su biyu ne suka dubi Fadila domin sunsanta wurin rashin tsoro da dauriya,, da iya tsara k'arya da gaskiya akan lamarin rayuwa. Fadila ce ta numfasa tareda k'yafta musu idanu akan su saki jikinsu,, kada yayi saurin gano abinda zata furta k'arya ne. Su Maryam suka gyad'a mata kai alamar to,, duk da yake babu abinda sukeyi sai wuru -wuru da idanunsu alamun rashin gaskiya duk ya bayyana a fuskokinsu.
Fadila ce tayi murmushi mai k'ayartar da fuskarta tace "yaya Mubarak wasa mukaje gidan k'awarmu Hassana,, shiyasa ne kayi nemanmu baka ganmu ba ".
Mubarak yayi shiru na minti biyu yana nazarin maganar Fadila,, amma acikin zuciyarsa ko kad'an bai aminta da maganarta ba. Domin kuwa kallon d'aya yayi musu ya gane basuda gaskiya,, amma dayake shi ma d'an zamani ne ya nisa sannan yace "Ok ba matsala amma dan Allah ku daina dad'ewa awaje,, wurin yin wasa domin kuwa yanzu zamanin nan namu ya lalace. Akwai abubuwa da yawa da zasu iya cutar daku wanda bana fatar haka,, saboda zuciyata bazata iya d'aukar hakan ba ".
Fatima taja dogon numfashi tace "insha Allahu yaya zamu kiyaye maganarka,, ai domin muje gidansu Hassana ne yasa muka dad'e sosai".
"haka ne gaskiya yaya Mubarak ai da tun d'azu mun dawo gida ".Cewar Maryam.
Mubarak yace "to 'yan k'annena na yarda daku nasan ba zakuyi abinda za'a ce Allah yayi wadaran da halinku ba,, saboda haka ku wuce zuwa gida ".
Fadila tace "zamu kiyaye yayanmu karka damu ".
"Allah yasa da gaske kukeyi ".Inji Mubarak.
"Amin Yayanmu ".Cewar Fatima da Maryam atare cikeda sanyin jiki. Yaya Mubarak saida ya raka Fatima da Fadila har bakin k'ofar gidansu,, dayake gidansu d'aya baban Fatima shine yayan baban Fadila. Bayan yah Mubarak yaga shigewarsu cikin gidansu,, yazo yaja hannun Maryam yana yimata nasiha tareda maganganu masu lurassuwa cikin hikima da iya magana..
**********************
Mubarak ne da Maryam suka shigo cikin gidan,, tareda da furta sallama a bakinsu. Mama Sa'ima ta amsa musu yayinda take k'ok'arin kwashe sharar da ta kammala yanzu nan,,, tasa parker ta kwashe sharar tana zubawa cikin kwandon shara. Alokacin ne Mubarak da Maryam suka k'araso cikin tsakar gida,, suka samu wuri suka zauna saman tabarma. Mubarak ya dubi Mama Sa'ima yace "sannu da aiki Mamanmu "."Yauwa Mubarak".Inji Mamansu bayan ta fito daga wurin kwandon zuba shara,, ta zauna kusaga Maryam ta harareta tace "sannu Maryam sarkin yawo,, Mubarak gidan uban wa kagansu? ".
Maryam ta sunkuyar da kanta cikeda matuk'ar tsoro da fargaba! Tace "Mama dan Allah kiyi hak'uri gidansu Hassana mukaje wasa ".
"tabbas haka suka gayamin Mama,,,tayi ba dai-dai ba ayi mata hak'uri bata sakewa ".Cewar Mubarak.
Mama Sa'ima tace "naji Mubarak amma wallahi Maryam ki kiyayeni ! Inba rainin wayo da hankali ba,,, ki fita daga cikin gidan nan tun safe baki dawo cikin gidan nan ba sai yanzu bayan azahar. Saboda bak'yajin maganata to zan gayama babanki nasan shi ,,,zakijin maganarsa saboda kinajin tsoronsa mara jin magana kawai ".
Maryam ta fara zubarda hawaye ,,,muryarta tana rawa tace "na tuba Mama ki rufamin asiri kada ki gayama baba,,,,wayyo wayyo Allah! Wayyo kaina wallahi Allah bana k'arawa komi kikace shi zanyi Mama. Yaya Mubarak ka taimaka ka k'ara bata hak'uri kaji ".
Yaya Mubarak ya dubeta cikin tausayawa da k'aunar k'anwarsa,,, yasa hannu ya jawota ya rungumeta a jikinsa yana lallashinta. Yace "ya isa ya isa Maryam share hawayenki Mama zata hak'ura kinji,, kuma idan Allah ya yarda bazan bari ta gayama Alhaji abinda ke faruwa ba ".
"To Yaya ".Cewar Maryam tana shessheka tana ajiyar zuciya,, saboda kukan da tayi.
"to tashi uwar son jiki kije kiyi wanka sannan kici abinci,,, nidake ne a cikin gidan nan matuk'ar kikace bazakiji maganata ba,,,,sai rayuwarki tayi matuk'ar b'aci sosai wawuya wadda bata san ciwon kanta ba"..Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar b'acin rai sosai.
Maryam ta mik'e tsaye tayi hanyar zuwa d'aki domin tayi wanka,,, sannan taci abincinta..
Alokacin ne Mubarak ya k'ara cewa "Mama ayita hak'uri k'urciya ne wata rana zata daina,,, sannan nima zan k'ara saka mata idanu sosai ".
"hmmm haka ne Mubarak amma zamanin nan abin tsoro ne,,, ya zama dole mutum ya k'ara lura da d'iyansa. Saboda mayyu sunyi yawa a cikin mutane sosai kowa ka gani yaci magani ne domin yayi kud'i,, ko ya cimma wani buri nashi wurin bid'ar abin duniya sai mutum ya zama maye kowa ya kama gudunsa,,, kuma ba ko'ina ake amso maganin ba illa wurin bokaye da 'yan bori. Mutane sun manta da cewa babu mai talautawa da azurtawa idan ba Allah kad'ai ba. Sun manta da cewa babu mai iya ba mutum abinda Allah bai bashi,,, da ace wani bawa yana iya azurtar da d'an uwansa da ya fara azurtar da kanshi kafin kuzo neman taimako wurinsa. Ba'aganshi walak'ance cikin k'azanta da datti ba ".Inji Mama Sa'ima.
Mubarak yace "haka ne gaskiya Mama Allah ubangiji ya bamu ikon bin gaskiya da kuma gyarawa,, wad'anda suka b'ace Allah ya daidaitasu akan hanyar gaskiya ".
Mama tace "Amin summa amin Mubarak ".
Suka cigaba da firarsu cike da tsananin jin dad'i da nishad'i sosai,, sunyi nisa cikin fira ne saiga sallamar Alhaji Suleiman ya shigo cikin gidan. Suka amsa masa Mubarak ya gaidashi tare da yi mishi sannu da zuwa,,, ya amsa mishi fuskarshi cikeda fara'a da murna sosai. Mama Sa'ima itama tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata,, ta amshi kayan da ke hannunsa suka shige cikin parlourn d'akinsu.
Mubarak ya jima sosai yana tunani akan al'amarin rayuwa,, sannan daga baya shima ya shige cikin d'akinsa. Ya shiga cikin toilet yayi wanka sannan ya sanya singlet da guntun wando domin shan iska,, ya kunna vedio ya sanya American film ya fara kallonshi cikeda natsuwa da kwanciyar hankali....
*Ku biyoni sannu domin jin ko wa cece Iya Gwamma,,, da kuma jin tushen labarin*.
_Share&Comments_
~Muje zuwa~
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 3*
**Yaya Mubarak yayi nisa sosai a cikin kallon American film d'in da yakeyi,, ko k'wakk'waran motsi bayayi sosai saboda yadda ya mayar da hankalinshi kacokam a wurin kallon vedio. Da gani babu tambaya kasan yanajin dad'in kallonshi,,, hankali kwance yake gudanar da komai nashi..
Ab'angarensu Mama sa'ima kuwa suna shiga cikin d'akin,,, ta taya Alhaji cire kayan jikinsa. Bayan ta gama cire masa kayan tas ta barshi da singlet da guntun wando,, sannan ta ja hannunsa kamar yaro k'arami ta kaishi cikin toilet tareda had'a mishi ruwan wanka,, bayan ta gama duk abinda ya kamata ta fito ta bar Alhaji domin yayi wankansa. Tana fitowa ta k'ara gyare bedroom d'in tareda sa ma d'akin room freshner mai k'amshin dad'i matuk'a,,,, sannan ta fitoma Alhaji jalabiya fara da zai saka a cikin gida tareda da feshe jalabiyar da perform mai k'amshi,, sannan ta samu wuri ta zauna a cikin d'akin tana jiran fitowar uban 'ya'yanta..
Bayan minti goma sha biyar saiga Alhaji ya fito daga wanka,, yazo kusaga Mama Sa'ima. Tana ganinshi tayi murmushi sannan ta d'auko lotion mai k'amshi ta fara shafa masasannu sannu cikeda nuna matuk'ar kulawa ga mijinta. Babu abinda Alhaji yakeyi sai lumshe idanu ma'ana yana jin dad'in yadda take bashi kulawa,, bayan ta kamalla shafa mishi mai neta d'auko jalabiyarsa ta sa mishi,, tana gama sa mishi suka zauna a tare suna fuskantar junansu. Alhaji Suleiman ya dubeta duba mai cikeda k'auna da son matarsa yace "Ummu Maryam Allah ubangiji yayi miki albarka hak'ik'a ke mace ce ta gari mai biyayya ga mijinta,, ina alfahari da kasancewarki matata uwar 'ya'yana,,,nasan nayi dace da farin cikin rayuwata mai sona kuma mai son farin cikina,, da gudun b'acin raina banda tamkarki a cikin zuciyata ".
Alal hak'ik'a kalaman Alhaji Suleiman sunyi matuk'ar sanya Mama Sa'ima cikin tsananin nishad'i da farin ciki sosai,,, sunbi jini da jijiyoyin jikinta suna shawagi a cikin zuciyarta. Ta dubi Alhaji cikeda matuk'ar nishad'i sosai tace "Amin ya Alhajina kasani biyayya ya zama wajibi agareni nayi maka muddin ina numfashi a doron k'asa,,, kaine silar farin cikina hasken idaniyata,,, idan ban faranta maka ba waye zan farantawa aljannata tana k'ark'ashin tafin k'afarka fa mijina,,, idan ka d'aga k'afa in shiga idan ka take shikenan! Taya zanyi sakaci har na tab'e Abban Mubarak,, ina matuk'ar alfahari da kai Alhajina ".
Alhaji ya rik'o hannunta yana murmushin jin dad'i,, sannan yace "haka ne matata idan har miji ke d'agama matarsa k'afa ta shiga aljanna,, to ni tawa k'afar a d'age take matata kuma insha Allahu zaki shigeta ".
"Ina godiya Alhajina,, to ya kasuwar? ina fatar ana samun ciniki sosai ".Inji Mama Sa'ima..
Alhaji Suleiman yace "lafiya k'alau Alhmdlilah,, agaskiya ana samu ciniki sosai ".
Mama Sa'ima tace "masha Allah komai yayi k'yau matuk'a,,, dama haka ake son ji Allah ubangiji ya k'ara taimakawa ya bada sa'a da nasara "..
Alhaji yace "Amin amin Ummu Maryam,, ina yaran nan suke ne Mubarak da Maryam d'in? ".
"hmm Mubarak yana d'akinsa Maryam kuma na barota ta gama cin abinci zata kwanta,,, kasan yaran idan suna gida kodayaushe suna cikin d'aki shiyasa ba'a sanin suna nan ko basa nan ".Cewar Mama Sa'ima..
Alhaji yace "haka ne musamman Mubarak akwai shi da son zama cikin d'aki kamar mace,,, shiyasa ma bai fiye son zaman shago ba,,, Maryam ko taso zaman d'aki ai ita mace ce gidan wani zataje ".
Mama Sa'ima tace "ai zai saba da zaman shago saboda namiji dole ya fita ya nemo,, Maryam kuma ai lamarinta sai addu'a saboda akwaita da rashin ji wallahi ".
Alhaji ya harareta da wasa cikin tsokana yace "a'aaa kada ki sanyama 'yata ido barta tayi rashin jinta,,, ai komai yanada lokacinsa addu'a dai zamu dinga yi akan Allah ubangiji ya shirya mana yaranmu "..
"kunfi kusa kodayake bakason a ce ga laifin Maryam,, addu'a takobin mumini ce Allah ya shirya mana zuri'armu ".Inji Mama Sa'ima.
Alhaji yace "Amin yanzu dai naji magana ba'a dinga takurawa 'yata ba,, ana cewa tayi kaza kaza ba "..
Mama tace "kaidai ka sani da dad'in bakinka ".
Yace "harda ke kinsan inada mana "..
Mama tace "nasan mi? ".
Alhaji yace "inada dad'in baki mana,, kuma har kin yaba ".
Mama tace "rashin aikin yi dai ".Tana murmushi sosai..
"da ni dake bamuda aiki yi ba ".Fad'ar Alhaji yana dariya sosai..
Mama kauda kanta tayi gefe guda,, tana ta dariya sosai mai cikeda matuk'ar farin ciki da walwala,, Alhaji shi ma yana tayata dariya tareda da jifanta da kallon soyayya da k'auna...
*********************
***Agidansu Fatima kuwa suna isa cikin gidan sukayi sallama,, aka amsa musu suka samu uwayensu zaune wuri d'aya suna fira cikin farin ciki da nishad'i. Su Fatima suka samu wuri kusaga iyayensu saman tabarma suka zauna,, bayan sun zauna ne sukayi shiru basu ce komai ba saboda sunsan sunyi laifi...
Iyayen nasu sai firarsu sukeyi kamar basu gansu ba,, can dai Fatima da yake batada hak'urin yunwa ta bud'i baki da k'yar tace "Umma yunwa nakeji fa,, tun safe rabon dana koma saka wani abu cikin bakina ".
Mahaifiyar Fatima mai suna Nusaiba ta banka mata wata uwar harara,, sannan ta bud'i baki tace "to sabon salo inda kukaje ne baku ci abinci ba,, na aikeki yawon gantali da sakarci ne ? Da zaki zo kina damuna yunwa kikeji yau naga bak'ar munafuka,,, salon ubanki yaji yace ina miki horon yunwa ko,, Fatima Fatima! Ki fita daga cikin idona mai yawon sakarci da wawanci ".
Mama Nafisa mahaifiyar Fadila ta harari su Fadila,, tace "k'yaleta Nusaiba ai gara ita tayi magana,, wannan mai taurin kunne _(ta nuna Fadila)_ ko magana batayi ba saboda tasan batada gaskiya,,,gameda shegen yawon nan saina saka ki cikin turmi nayi miki dakan tankwan d'an bashirwa! Munafuka 'yar iskar yarinya ".
"Ni banga dalilin yawon banza ba miye kuka nema kuka rasa ne? Saboda Allah salon ku jawo ma kanku wani mugun abu! Ga mayyu a garin nan kamar tsaki,,, saboda haka zamu d'auki mataki akanku tunda bakujin magana ".Inji Umma Nusaiba.
Mommy Nafisa tace "mataki ya wuce musa Fadil ya basu matsiyacin kashi idan suka koma,, saboda naga sun raina Nabila basajin tsoronta kwata kwata,,,ni wlh idan rayuwata ta b'aci ina iya yi muku mugun bugun walak'anci da halaka,, saboda naga lalama batayi muku musamman ke Fadila mai kunne roba ".
Umma Nusaiba tace "ba wani Fadila aiko ba ita kad'ai zakiyima fad'a ba,,, ko Fatima ba baya ba wurin rashin jin magana ba,,,mu samesu rana d'aya mu basu kashin k'warai ko zasuyi hankali "..
Mommy Nafisa tace "naji amma ai tafita rashin jin magana,, amma nasan maganinsu ".
"babu wani ta fi ta duk d'aya suke ".Inji Ummu Nusaiba.
Fatima ce ta tattaro dauriya,, tareda marairaice fuskarta tace "Mommy,, Umma dan girman Allah kuyi hak'uri Insha Allahu bazamu sake ba,, dama gidansu Hassana ne mukaje shiyasa muka jima sosai bamu dawo ba ".
"munsan munyi kuskure ayi mana afuwa,,, bazamu k'ara aikata kwatankwacin haka ba ".Inji Fadila..
Mommy Nafisa taja mugun tsoki mtssss! Saboda ita akwaita da saurin d'aukar zafi da wuri,, ta juyar da kanta wani gefe domin kada suga fuskarta. Umma Nusaiba ce taja dogon numfashi tace "komai ya wuce yarana ubangiji Allah ya k'ara shiryaku,, Nafisa baki ce komai ba ".
Mommy Nafisa tace "ai kin riga kin gama magana Nusaiba,,, nima na hak'ura Allah ubangiji yayi musu albarka ".
Su Fadila sukace "amin mun gode sosai Iyayenmu ".Suka mik'e tsaye atare suka nufi cikin d'aki domin suyi wanka suci abincin rana,, iyayen mata suka cigaba da firarsu cike da walwala da annashuwa mara misaltuwa..
*ASALIN LABARI*
Maryam 'ya ce ga Alhaji Suleiman da Hajiya Sa'ima,, asalinsu 'yan nijar ne kasuwanci ne ya kawosu Nigeria acikin garin Gumi Zamfara state. Suleiman da Sa'ima 'yan uwan juna ne domin kuwa auren zumunci akayi,, sun taso ne tun suna yara suna matuk'ar k'aunar junansu fiye da yadda kuke tunani. Sun taso gidan mutunci masu nagarta da son zumunci,,,a familynsu sun kasance sunada had'in kai da kuma k'aunar juna babu gulma ko hassada da nuna k'yashi. Komai nasu a had'e yake abin burgewa da sha'awa matuk'a,, idan ka shiga cikin gidan da yake babban gida ne ba zaka iya gane wani banbamci ba,, saboda ba zaka iya gane wannan d'an wa ne ba ko d'an wance ce ba saboda had'in kai da zumunta,,, hak'ik'a famili ne mai matuk'ar k'aunar juna da yarda da 'yan uwa...
Sun had'a auren Suleiman da Sa'ima domin zumuncinsu ya k'ara k'arko,, masha Allah akayi dace ko su yara ne masu biyayya da k'aunar juna. Sun bada had'in kai cikin tafiyar da rayuwar aurensu cike da aminta da juna da zaman lafiya na hak'ik'a,, kowanensu yana k'ok'ari wurin ganin ya farantama d'an uwansa tareda k'yautatawa juna domin samun farin ciki da annashuwa mai d'orewa har abada ....
_Share &Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 4*
Domin samun farin ciki da annashuwa mai d'orewa har abada,,, zamansu zama ne na fahimtar juna da amana,, tausayi da tsananin shak'uwa a tsakaninsu. Dukansu suna k'ok'ari wajen ganin sun sauke hak'k'in dake bisa kansu na auratayya,, Suleiman ya kasance mutum ne mai sauk'in kai da tausayin na k'asa dashi bayada rowa ko k'yashi ko kad'an. Yanada son bayarda k'yauta da taimako gashi kuma mai tsananin biyayya da ladabi ga mahaifansa,, haka itama Sa'ima mace ce wadda batada matsala a rayuwarta,, tanada kirki da k'yakk'yawan d'abi'u tanada son mutane da yawan fara'a. Haka take kowa nata ne babu ruwanta da shiga sabgar daba ta taba,,,, shiyasa lamarin aurensu yazo da sauk'i matuk'a saboda shi bayada matsala hakama Sa'ima batada wata matsala..
Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar aurensu cike da jin dad'i da farin ciki mara misaltuwa,,, kowanensu yasan abinda ya dace ya kamata zaman lafiya ya wanzu a cikin gidan aurensu. Babu abinda sukeyi sai sunyi shawara tare su kashe tare su binne tare babu mai jin sirrinsu,, Alhaji Suleiman kasuwanci yakeyi tun anan nijar kafin harakar ta bunk'asa sosai .Itama Sa'ima tana saisuwa su kayan miya cikin gida irinsu,, maggi star racco,, daddawa,, maggi ajino motto,, gishiri,, kanwa,, sabulun wanka da wanki,, k'uli -k'uli,, tankwa da dai sauran kayayyakin miya..
Sunyi wata biyu da yin aurensu saiga ciki ya bayyana a jikin Sa'ima,, sunje asibiti an auna wata d'aya da satittikka zo kuga murna da farin ciki a fuskokin wad'annan bayin Allah. Bayan sunje gida suka sanarda 'yan uwa da abokan arzik'i duk wanda suka fad'ama sai yayi murna da farin ciki sosai,,, zo kuga farin ciki da nishad'i a cikin zuciyar iyayensu Alhaji Suleiman. Haka dai Sa'ima ta cigaba da samun kulawa ta musamman ta b'angare biyu iyayenta dana mijinta,, duk abinda take so shi akeyi mata na daga abubuwan ci da abinci mai gina garkuwar jiki,, haka abubuwan ke tafiya cikeda matuk'ar kulawa da tarairaiyarta. Shima kanshi uban gayya wata kulawa ya k'ara bata yana shagwab'ata da tarairaiyarta hundred percent,,, haka dai Sa'ima ta cigaba da rainon cikinta da bashi kulawa fiye da tunanin mai karatu,,, kwanaki suka cigaba da tafiya suna zama watanni..
Watanni takwas sukazo alokacin ne bayan sallar asuba,, ciwon nak'uda ya kama Sa'ima tun tana nishi hmhmhmhm hmhmhmhm hmhmhmhm babu wanda yaji,, har tazo ta fara kiran sunan mahaifiyar Suleiman. Inna ta shek'o da gudu ta taimaka mata tana mata addu'a harta santalo santalelen d'anta,, k'yakk'yawa son kowa k'in wanda ya rasa. Bayan Innar Suleiman ta gyarata ta kuma gyara ko'ina sai k'amshi yake tashi ,, can ta shiga cikin gida ta sanarwa kowa da kowa. Zo kuga yadda ake tururuwa zuwa ganin sabon jariri sabon jini,, haka dai mutanen unguwa suka cigaba da zuwa ganin jariri tareda yi mata barka da haihuwa,,, haka dai suka cigaba da zuwa dubiyar Sa'ima...
Sati yana zagayowa ranar suna yaro yaci suna Mubarak,, hak'ik'a 'yan uwa da abokan arzik'i sunyi matuk'ar k'ok'ari wurin ganin sun fitar da Sa'ima kunya,, anyi mata abin arzik'i k'warai da wadata raguna biyu manya -manya aka yanka da tinkiya d'aya. Haka dai akayi bikin cikin rufin asiri da wadatar zuci,, bayan maraice tayi kowa ya kama gabansa ya wuce zuwa gida..
*********************
Bayan shekaru biyar da haihuwar Mubarak,, Alhaji Suleiman ya kwaso iyalinsa daga mahaifarsa nijar ya dawo Nigeria zamfara state cikin garin Gumi. Ya cigaba da kasuwancinsa cikeda kwanciyar hankali,, itama matarsa ya bata jari domin ta cigaba da sana'arta da takeyi acan nijar..
Garin Gumi gari ne mai tarihi da d'umbin albarka,, sunayin kasuwanci da kiwo amma ba sosai ba babbar sana'arsu shine noman k'warya. Itace sana'ar da mafi akasari da 'yan garin keyi da kiwo amma ba sosai ba,, garin ba za'a kirashi k'auye sosai ba kuma ba za'a kirashi birni ba yana dai tsaka tsakiya. Mutanen garin mutane ne masu addini da tsoron Allah,, komai nasu zad sha'awa suke gudanar dashi...
**Anan garin ne Mama Sa'ima ta haifi Maryam atsakaninsu da Mubarak akwai tazarar shekaru shida,,, zo kuga murna alokacin da Mubarak yaga ya samu k'anwa fara tass k'yakk'yawar gaske ta bugawa a mujalla,,, hak'ik'a Allah yayi halitta a nan domin kuwa kallo d'aya zakayima jaririya ka gano sai anyi k'yakk'yawar mace abar kwatance da kallo cikin mutane. Haka dai Mama Sa'ima ta cigaba da rainon Maryam itada Mubarak,, shima Alhaji Suleiman Allah ya d'ora masa tsananin k'aunar iyalinsa wato yaranshi,, komai yi musu yakeyi gwargwadon iyawarsa domin samun farin cikinsu da walwalarsu....
Fatima 'ya ce ga Malam Nura da Nusaiba,, kuma yaya ne ga Nazifi mahaifin Fadila da mahaifiyarta Nafisa. Nura da Nazifi sun kasance 'yan uwan juna uwarsu d'aya ubansu d'aya,,, sun kasance 'yan asalin jahar kebbi amma sun dad'e cikin garin Gumi sosai tun kafin su fara tara iyali sosai,,, babbar sana'ar da suka dogara da ita shine noman k'warya da ita suke ci suna rufama junansu asiri. Ahaka suke d'aukar nauyin iyalinsu cikeda zafin nema da wadatar zuci,,, shiyasa ake son mutum mai zuciyar neman na kanshi domin kada mutum ya dogara ga wani. Zuri'arsu zuri'a ce mai had'in kai da zumunta,, tareda da matuk'ar kulawa da kuma soyayya da juna. Kan mazan a had'e yake babu wani munafurci ko gulma,,, hakama matansu sunada had'in kai matuk'a d'aya batayin abu saida shawarwarin junansu. Duk abinda suka yanke shawara shi sukeyi tare shiyasa ko yaransu Fatima,, Fadila,, Nabila da Fadil kansu yake a had'e cikeda matuk'ar tausayin juna da girmamawa..
Familinsu family ne masu matuk'ar k'aunar juna,, da fahimtar juna haka suke tafiyar da rayuwar aurensu cikeda zaman lafiya da soyayya..
***Iya Gwamma 'yar asalin Gumi ce gaba da baya,,, 'ya ce ga Malam Mamman da Ina Talatu tanada k'ane guda mai suna Lawwali ita Iya Gwamma. Inna Talatu mayya ce da taci magani a wurin wani babban boka mai suna LOK'ORO,, boka LOK'ORO shahararren boka ne da ya shahara a cikin garin Gumi da kewayenta. Sunanshi ya bazama ko'ina a jahar zamfara da k'auyukanta ,,,yana bada magani ne ga wad'anda suke son suyi kud'i sosai ko wani cimma burinsu na duniya. Babban matsafi ne dake aiki da bak'ak'en aljannu da dodonni,, ya shahara wurin mugunta da kashe rayuka na mutane harda aljannu. Bayan Inna Talatu ta amshi magani domin ta zamo mai arzik'i to kwatsam! Bata zamo mai kud'i ba ta rikid'a ta zama k'usurgumar MAYYA wadda nan da nan ta fara cin naman mutanen unguwa da na k'etaren gari,,, tun tanayi a b'oye mutane basu sani ba har yazo ya bayyana afili kowa ya gano ita mayya ce. Nan da nan mutanen gari da wad'anda take mu'amala dasu suka fara gudunta domin ceton ransu dana iyalinsu,,,ko'ina ka gani anyi gungu a majalisu babu abinda suke fad'a idan ba Inna Talatu *MAYYA CE* cin naman mutane takeyi da satar kurwa! Harda yaranta su Gwamma ake tarewa a hanya ake ce musu d'iyan mayya kunyi hasara,, Gwamma kuwa kashi takeyima yaran mutane idan ko warinta ne saisu kacame da dambe sosai. Ta samu yaro tayi masa mugun cizo sai jini ya fito tasa halshenta ta lashe jinin ta had'iye mak'wat kamar mayya ,,,tabar yaron nan kwance k'asa yana kukan ciwo wiwiwihhh.
Lawwali yana gefe guda yana kallon yadda take dukan yaron mutane kamar ta samu jaki,,, shi dai babu ruwanshi saboda yanada matuk'ar natsuwa da sanyin hali. Bayason hayaniya ko tashin hankali ko kad'an idan ka ganshi kana cewa ba Inna Talatu ce ta haifeshi ba,,, saboda natsuwarsa da hankalinsa..
Gwamma ce take kakkab'e jikinta da k'asa bayan ta gama chasa d'an mutane,,, ta juyo ta dubi Lawwali tana harararshi tace "shege raggon namiji kanajin ana zagin mahaifiyarmu amma kayi shiru,, sai dai ka koma gefe kana kallona ina fad'a,,, Allah yayi wadaran naka ya lalace! Wawan banza mai zuciyar kare ".
"yaya Gwamma kiyi hak'uri ni banyi shiru ba ne domin in b'ata miki rai ba,, nayi shiru ne saboda aganina fad'a baya kawo maslaha a cikin wannan lamari,,, kuma ai duk abinda suka fad'a ai gaskiya ne saboda Innarmu ta aikata maita! ".Inji Lawwali cikeda rashin son tashin hankali.
Gwamma ta zaburo mai da k'arfi cikeda jin haushin maganarsa,,, tace "Innarmu ce mayya saboda bakada hankali,, lallai Lawwali anyi tsinannen yaro d'an banza! Yanzu nan zanci ubanka ".
"Eh mana na fad'a ai gaskiya d'aci gareta k'arya kuma tanada matuk'ar dad'in d'and'ano mai zak'i yaya Gwamma ".Cewar Lawwali cikin jin haushin maganar Gwamma.
Nan da nan cikeda matuk'ar zafin nama da jin bak'in cikin maganar Lawwali,,, aiko Gwamma bata tsaya b'ata lokaci ba ta kwashe Lawwali da wani mugun mari mai matuk'ar zafi da rad'ad'i tareda gigita rayuwar d'an Adam! Ai saboda k'arfin marin saida Lawwali ya wintsilo k'asa da k'arfi,,, saida bakinshi ya fashe da jini jinshi da ganinshi suka d'auke na wucin gadi..
Yana kwance k'asa Gwamma ta nuna shi da yatsa cikeda zafin rai da tafasar zuciya tace "ina yi maka gargad'i da kada ka kuskura ka k'ara aibata mahaifiyarmu,,, idan ana zaginta kana kallo kana k'yalewa toni bazan k'yale ba,,, duk wanda ya nemi da ya zagi uwata to sai inda k'arfina ya k'are ciki kuwa harda kai da muke ciki d'aya,, wallahi wallahi! Akan mahaifiyata zan iya kashe rai har lahira!!! Kuma duk wanda ya shiga cikin gonata saina afka mishi koda kuwa kaine Lawwali,, yaron banza mara kishin uwarsa ".
Nan taja jikinta tabar Lawwali kwance a k'asa yana kukan rad'ad'in marin da tayi masa mai zafi sosai,,, ta kama hanyar zuwa gidansu babu abinda Lawwali keyi sai zubar da hawayen bak'in ciki da takaicin abinda Gwamma tayi masa,, kuma yasan ya fita gaskiya a cikin wannan lamari yasa hannu ya share jinin dake fita daga cikin bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya.....
_Share&Comments_
*I luv you my fans more more*
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*MAYYA CE*
đ„đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„đ„
đ„đ„đ„
đ„đ„
đ„
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍đ»
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 5*
Yasa hannu ya share jinin dake fita daga bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya,, idan banda rad'ad'i da ciwo babu abinda zuciyarsa keyi saboda marin ya shigeshi sosai matuk'a. Dak'yar Lawwali ya mik'e tsaye yana shafa kuncinsa da yake yi masa zafi da rad'ad'i,,, ya kakkab'e jikinsa daya b'aci da k'asa ga shatin hannun Gwamma nan ya fito b'aro b'aro a fuskarsa,,, haka dai yaja k'afafunsa yana tafiya dak'yar domin ya nufi gidansu...
Gwamma ce naga harta iso gidansu ta afka cikin gidan ba tare da sallama ba,, Inna Talatu ce da Malam Mamman ta iske ya dawo gida domin yayi wani mantuwa a gidan,,, ya dubi Inna Talatu yace "Talatu baki ga wata bak'ar leda ba dana yi mantuwa da ita ba,, ta mutane ce idan kin gani ki mik'omin sauri nakeyi zan wuce ".Inna Talatu ta harari Malam Mamman sannan ta buga tsoki mtsssss tace "maganar banza kenan Mamman mi zanyi da bak'ar ledarka idan na gani,, ko kuwa ni na sakaka yin mantuwa ne? Da har zaka zo kana damuna da surutunka na banza da yofi! "."Kinga Talatu ba haka ba ne ai tambaya baya zama laifi,, daga tambaya sai masifa wai miyasa rayuwarki yanzu ta chanza ne? Idan wani abu nayi miki ya kamata ki sanar dani in gyara kuskurena mu fahimci juna,, batare da wasu sun jimu ba ".Inji Malam Mamman cikeda lalama,,, yana dibe dibe ko zai gano inda ya ajiye ledarsa da ya manta,,, Inna Talatu ta k'ara hasala sosai tace "babu abinda ka yimin Mamman tambaya ce kawai bana so,, domin ni tambaya b'atamin rai takeyi da ka shigo cikin gidan nan ya kamata ka bani ajiyar ledar,, amma baka bani ba ka ajiye da kanka sai yanzu da baka gani ba kake neman takuramin da tambayar munafurci,, to ka diba inda ka ajiye kada ka dameni da tambayarka "."Allah ubangiji ya huci zuciyarki Talatu nasan nayi ba dai -dai ba amma kiyi hak'uri kinji ".Cewar Malam Mamman bayan ya shige cikin d'akin yana cigaba da bincikensa..
"da hak'uri ta mutu sadakar nawa ka bani tsohon banza bak'in munafiki! ".Cewar Inna Talatu cikeda bala'i da masifa.
Tun d'azu Gwamma tana tsaye babu abinda tace,, illa kallonsu da takeyi uwarta tana zagin ubanta. Sai alokacin ne Gwamma ta bud'i baki tace "Inna na dawo fa naga tun d'azu baki lura dani ba,, kinata surutunki ".
"To d'iyar k'warai sannu da zuwa ya gajiyar hanya,, ina kika baro k'anenki ne? ".Inna Talatu ta fad'a yayinda take dube dube ko zata hango Lawwali a bayan Gwamma..
Gwamma taja numfashi tace "lafiya k'alau na dawo Inna Lawwali kuwa na baroshi a bayana kan hanya ".Saiga Malam Mamman ya fito daga cikin d'aki rik'e da ledarshi a hannunsa,, alamar kenan yaga ledar ya dubi Gwamma da Inna Talatu yace "aaa Gwamma kin dawo ko ".
"Eh na dawo baba ".Cewar Gwamma.
Malam Mamman yace "to yayi k'yau Allah ubangiji yayi muku albarka ".
Tace "Amin baba ".
Malam Mamman yace "to ni Talatu zan wuce can kasuwa naga ledar da na tambaye ki,, kika yimin bak'ar magana wadda babu dad'in ji balantana saurare kamar ni ba mijinki ba ne ".
"to tunda ka gani ka isa barka kada ka gayamin maganar da batada dad'i,, inko rama wallahi domin ba tsoronka nakeji ba! ".Inji Inna Talatu MAYYA.
Malam Mamman yace "ai nasan bakijin tsoro na Allah ubangiji ya shiryeki Talatu! Rayuwarki tanada matsala sosai wlh,, ni inada aikin yi na barki lafiya masifaffar banza ".Yana fad'in wannan maganar yasa kai yayi tafiyarsa zuwa kasuwa,, batare da ya tsaya ya saurarin irin martanin da zata mayar mishi ba..
"kaine masifaffe ba ni ba ai wannan rainin wayo ne,,, daga kawai kaga ina maka shiru-shiru sai raini da walak'anci ya shigo,, wallahi bazan tab'a barin ka gayamin magana ba dad'i ba amma ba komai zanyi maganinka! ".Cewar Inna Talatu tana d'aga murya k'warai ta yadda wanda yake bakin garka,,, zai iya jiyo muryarta.
Sai asannan ne Gwamma ta iya bud'a baki tace "kiyi hak'uri Inna wannan abin bai kawo kallo ba,,, kuma bai dace ba kina d'aga murya sosai har na waje suna jinki ".
Inna Talatu tace "haka ne d'iyar albarka rayuwata ce ta b'aci sosai wlh,, shiyasa ki kaga inata fad'a amma yanzu tunda kinsa baki na daina fa,, mi ya faru ne naga kamar bakinki yanada magana ?".
"ke dai bari Inna ayau Lawwali yayi masifar b'ata min rai da bani takaici ".Cewar Gwamma.
Inna Talatu tace "mi yayi miki ne har ya b'ata miki rai ne? ".
Gwamma ta kwashe labarin duk irin fad'an da takeyi da yaran mutane da suke kiran Inna Talatu mayya,,, da kuma marin da tayima Lawwali da kuma maganganun da sukayi,, babu abinda ta b'oyewa Inna Talatu komai ta gaya mata..
Inna Talatu taja dogon numfashi tareda huci mai zafi,, sannan tace "yanzu Lawwali ni yake zagi harda kirana da mayya,, yau ko wa yayi masa tsaye saina halakashi! Nayi masa mugun bugu sosai wlh,,, yadda idan yaji ana zagina ko baiyi fad'a ba bazai saka bakinsa ba waishi mara kuny....
Inna Talatu bata k'arasa maganar da take sonyi ba,, saiga sallamar Lawwali yayi sannan ya shigo cikin gidan da fasasshen bakinsa. Inna Talatu ta jawo hannunsa kamar abin arzik'i tana k'ara shafe masa jikinsa da jinin dake fita daga cikin bakinsa..
Sannan ta tambayeshi kamar batasan komai ba tace "Lawwali uban waye ya fasa maka baki harda jini,, wa ye ya mareka harda shatin yatsu? Ka gayamin yau ko ni ko maishi mutuwa kad'ai ke rabamu wlh ".
Lawwali yace yana zubar da hawayen takaici "Inna Yaya Gwamma ce ta mareni saida na fad'i k'asa,, sannan ta dinga zagina babu iyaka ".
"ita Gwamman to naji mi kayi mata ne data mareka? ".Inji Inna Talatu.
"haka kawai ne banyi mata komai ba ".Cewar Lawwali.
Inna Talatu ta harzuk'a da hasala sosai,,, batayi wata wata ba ta kwashe Lawwali da matsiyacin mari biyu masu k'yau,,, ta ka mashi tana ta kashi kamar ta samu jaki. Babu abinda Lawwali keyi sai kuwwa yana kuka domin ya samu agaji cikin gaggawa,,, saboda ba k'aramin duka Inna Talatu takeyi masa cikeda matuk'ar takaicinsa da zafin rai tana cewa "da kai za'a had'a baki ana zagina ko ana cemin mayya baka damu ba,, saboda bakasan zafina ba amma 'yar uwarka da tasan zafina shi ne za kace mata ai gaskiya yaran suke fad'a domin na aikata maita! Yanzu saboda munafurci na tambayeka kace bakayi mata komai ba ,,,yau saina kasheka in kashe banza! ".Haka dai Inna Talatu ta kama dukan Lawwali sosai tana zaginsa..
Babu abinda Lawwali keyi sai kukan bak'in ciki da zafin duka,, yana cewa "na tuba na tuba Inna,, Inna bazan sake ba wallahi sharrin shed'an ne ki ya femin zan mutu zan mutu! ".Nan ya fad'i k'asa ya some duk da haka bata daina dukansa ba,,, sai da tayi masa lilis da duka sannan daga baya ta gano cewa ya suma,, taje ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi ta watsa mishi a jikinsa. Gwamma dai tana zaune tana kallon duk abinda ke faruwa hankalinta kwance,, can yaja dogon numfashi ya tashi zaune yana kuka duk gaba d'aya jikinsa yayi rud'u rud'u akan duka,,, Inna Talatu tace "gobe ma ka k'ara da sai naci namanka d'anye wlh! Kuma yau duk ubanda ya d'aure maka gindi ba za kaci abincin dare ba,, mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa! ".Tana gama fad'in maganganunta taja hannun Gwamma sukayi shigewarsu d'aki.
Lawwali yaja jikinsa sannu ya shige cikin d'akin da babu komai sai tarkacen kayayyakin aikin gida,, ya samu wata tsohuwar tabarma data yakuce akan tsufa ya kwanta. To haka abin ya kasance kuwa domin Inna Talatu hanama Lawwali tayi abincin dare da yunwa ya kwana,, mahaifinsa kuma baisan abinda yake faruwa ba a cikin gidan ba..
*********************
Da misalin k'arfe 12:00am na dare ne Inna Talatu ta tashi sannu a hankali,, tana dubawa ko Malam Mamman da Gwamma sunyi nisa cikin barcinsu. Ai kuwa taci sa'a babu abinda sukeyi sai minshari da gurnani na barci,, ta lab'ab'a sannu a hankali ta fito waje tareda zare sakatar gidan..
Tana fitowa waje ne duk unguwar tsit ta ke kowa yayi barci babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye dana wasu halittu,, ga wata irin sansanyar iska da ta ke busowa mai dad'in gaske. Sai da Inna Talatu ta dubi yamma gabas,,, kudu da arewa sannan ta duba kowace hanya babu kowa,,, sannan naga ta kama wata hanya siririya wadda ta nufi cikin daji,, tana ta tafiya har ta kawo wurin wata bishiya nan da nan naga ta cire tufafinta ta koma zindir haihuwar uwarta. Tana cire tufafinta ta isa wani wuri inda babu abinda ke tashi sai wuta wal wal wal,, wai ashe wurin 'yan uwanta mayyu ta zo domin suyi bugun wuta..
Wasar bugun wuta shi ne abinda mayyu keyi da daddare musamman alokacin zafi,, zindir haihuwar uwarsu sukeyi tareda canza kamanninsu ,, suna taruwa a cikin daji suna wasar bugun wuta shi ne su kama zagayar dajin gari bakinsu da hammatarsu sai fitar da wuta sukeyi wal wal wal zad tsoro!,, zasu jima sosai sunayi sannan daga baya kowa ya kama gabansa.
Suna gamawa ne Inna Talatu taje wurin bushiyar da ta aje kayanta ta d'auka ta sanya ta nufi gidan mijinta,, tana cikin tafiya kawai gani nayi ta girgiza da k'arfi! Ta rikid'a ta koma karya mai k'wala k'walan ido da halshenta ya kai tsawon igiyar shanya,, bakinta sai feso wuta yakeyi jawur tana kukan karnuka ohww ohww ohww babu dad'in saurare da ji hayak'i bak'i kawai ke fita daga cikin jikin karyar.
Ta kusa kawowa gida ta had'u da Lado zaiyi fitsari,,, komai na kayan cikinsa tana gani kamar irinsu hanji,, hanta ,, zuciya da duk wani abu da ku ka san d'an Adam ya keda haka suke ganin komai na mu kamar yadda ku ka ga skeleton,,, ai kuwa babu b'ata lokaci tasa halshenta mai kamar igiya ta jawoshi sai da tayi sama da shi ta koma tayi k'asa dashi,, sannan ta bugashi a k'asa cikeda maita. Lado babu abinda yakeyi sai kuwwar neman agaji amma ina dare ne kuwwarka banza.
Babu wanda zai jishi balantana ya kawo masa agajin gaggawa,, haka kawai yaji kamar an tsinke mishi jijiyoyin jikinsa saida Inna Talatu tayi masa azaba da mugunta iri iri daban daban sannan tayi wani mugun sihiri,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ta ga me wurin tana zagayesu na wani lokaci,, saiga wani farin abu mai surkin ja ya bayyana a tafin hannun Inna Talatu,,, yana bayyana ta karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri abin ya zama fa ra ta tura cikin jakarta ashe kurwar Lado ce ta mayar fa ra ta nufi gida da saurinta.
Tana shiga cikin gidan ta girgiza ta sake rikid'a ta koma mutum,,, sannan ta lallab'a sannu a hankali ta kwanta domin kada wani daga cikin d'iyanta ko mijinta su ganta.....
0 comments:
Post a Comment