Inna Talatu ta nemi Lawwali sama da k'asa ta rasa a cikin gidan,,, nan da nan hankalinta yayi k'ololuwar tashi cikin kid'ima da fargaba,, haka dai ta daure ta cigaba da harakokinta na cin naman mutane,, Gwamma itama ba baya wurin kamun inwar kurwar mutane tana cinyewa d'anye ba babu tausayi ko rahama acikin zuciyarta ko kad'an,,,mutane sai k'ara tsoracewa da katsewa akan lamarin mayyu sukeyi...
**Inna Talatu ce da Gwamma zaune suna tattaunawa akan yau,,, wa ne gari zasuje kamun inwar kurwar mutane suje can batare da b'ata lokaci ba,, Inna Talatu ce ta dubi Gwamma tace "Gwamma har yanzu bakijin labarin ina Lawwali yaje ya b'oye ba,, acikin garin nan wai?".Gwamma ta karkace baki tace "Inna ayau da dare da naje kamun inwar kurwar mutane,,, na ganshi acan gidan baba Labbo yana b'oya saboda kada ki ganshi wai ".Inna Talatu ta bushe da dariya sosai tace "hmm to ai ko ya gudu ya b'oye can bai tsira ba,, saboda idan inason inci naman jikinsa abu ne mafi sauk'i a wajena ".
Gwamma tace "nima naga wautarshi Inna ai kamun inwar Lawwali shan ruwa ma yafisa wuya sosai,, abinda ya aikata rashin wayo ne babba ".
Inna Talatu tace "yaje yayi tayi fa sannan ina son inja miki kunne ki rik'e wannan haraka ta maita hannu bibbiyu,,, saboda muddin kinayinta babu mai rainaki cikin mutane kowa shakkunki zai dinga yi,,, domin inason ki shahara da gunguma fiyedani inason duniya tasan da zamanki ".
Gwamma tace "zanyi iya bakin k'ok'arina kuma zan kasance mai biyayya ga boka LOK'ORO ,,har sai burinmu ya cika Inna bana wasa a cikin wannan sana'ar gado wato maita !"
"zaki ko shahara sosai da zama gagararriya acikin mutane da aljannu,,, babu wanda ya isa ya tab'aki ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar farin ciki da murna sosai..
Gwamma tace "naji dad'i sosai Inna dazan shahara a duniya ".
Inna Talatu tace "ba zakiji dad'i sosai ba sai nan gaba kad'an,, idan shahararki ta bayyana a cikin wannan gari ".
Gwamma tace "to Innata ta kaina".
Haka dai suka cigaba da shawarwari ta yadda zasu b'ullowa al'amarin kamun inwar kurwar mutane,, da kuma yadda zasu gudanar da komai cikin sauk'i....
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
**Abubuwa da dama sun faru acikin wad'annan shekarun da suka wuce,, ciki kuwa harda kamun kurwar mutane dasu Inna Talatu keyi suna cinyewa,, domin abin nasu yayi tsamari sosai sun hana shak'at da jin dad'i a cikin gari,, mutum bayada halin ya fito daga cikin gidansa ya dad'e yana a cikin kasuwa face sun kamesa,, ganin sun addabi rayuwar mutane yasa kowa yake addu'ar Allah ubangiji ya kawo k'arshen Inna Talatu MAYYA.
Saboda har yanzu basusan Gwamma ta zama k'usurgumar *MAYYA CE* shahararra a wurin mugunta da cin naman mutane,, domin ayanzu tanada shekara goma sha takwas Lawwali kuwa sha shida,, tamafi Inna Talatu mugunta saboda ita har naman aljannu ci takeyi saboda ta shahara da gunguma akan maita! Tana alak'a da dodanni wurin abokanka,,, batada tsoro ko shakku uban kowa duk abinda takeso shi takeyi.
Ganin da mutane sukayi kashe rayukan da akeyi agarin nan yayi yawa,, yasa dole suka fara takon sak'a da Inna Talatu sukayita d'ana mata tarko tana tsalkewa,,, domin duk abinda sukeyi tana ganinsu cikin tsafinta,,, ganin abinda suke mata yayi yawa sosai.
Yasa dole wata rana da misalin k'arfe 10:00am na safe,,, bayan sunyi karin safe itada Gwamma tace mata zataje can wurin boka LOK'ORO,, ta tsaya ta fake gida yanzu zataje ta dawo,,, Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo.
Inna Talatu ta shirya sannan ta saka kai tayi wucewarta zuwa wurin boka LOK'ORO..
********************
Inna Talatu ta girgiza ta rikid'a ta koma kaza sannan ta kama hanyar zuwa cikin k'usurgumin daji mai duwatsu,, dajin da boka LOK'ORO ke rayuwa acikinsa na tsawon shekaru,,, tana isa inda yake ta girgiza sannan ta rikid'a zuwa siffarta ta ainahi,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ce ta ratso kusa gareta tana girgizawa da zagayarta na wani lokaci kad'an,, can dai komai ya tsaya cak guguwar ta daina yawo ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma boka LOK'ORO,, idanunsa sunyi jawur kamar barkono jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u halittar yanayin jikinsa duk ya chanza,, ya bud'i baki yace mata "nasan mi yake tafe dake Talatu,, amma ki sake gayamin da bakinki saboda wak'a abakin mai ita yafi dad'i ".
"ya maigirma boka LOK'ORO abubuwa da dama sun faru acikin wannan lokacin,,, mutane yanzu so suke su kasheni har abada,, sunyi d'anamin tarkuna har sun gaji ina tsallakewa,, ka sanardani ta yadda zan k'ara kare kaina".Inji Inna Talatu cikeda matuk'ar sanyin jiki.
Tana gama fad'in wannan maganar boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya sosai,, wanda sanadiyyar hakan saida k'asa ta kama rawa yace"Talatu babu wani taimakon dazanyi miki domin alk'alami ya riga ya bushe,, mutuwarki ta kusantoki! Ajalinki yana zuwa agareki kwananki ya kusa k'arewa ".
Hankalin Inna Talatu ya d'unguma sosai zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi da k'arfi,, rayuwarta idan har tayi dubu to ta b'aci sosai,, ta d'ago idanunta jawur tace "boka LOK'ORO wa ye zai kasheni sannan ya zamo ajalina? ".
"Sala mafarauci k'anen baban Lado shine zai kasheki! Amma ba'a cikin sauk'i zai kasheki ba 'yarki Gwamma itama ta kashesa,,, sannan abin yazo ya zamar musu gaba mai tsananin gaske itada Ummaru d'an Sala mafarauci,,kinga kuwa bakida damuwa domin ak'alla ko kinyi k'aranci kinci naman mutane fiyeda dubu 'yarki Gwamma taci d'ari ".Inji boka LOK'ORO yana dariyar mugunta da rashin tausayi!.
Inna Talatu ta bushe da dariya sosai sannan tace "hak'ik'a nayi matuk'ar farin ciki da wannan maganar taka boka LOK'ORO,,, aini burina ya cika koda ya kasheni saboda 'yata ta zamo shahararriyar *MAYYA CE* gagararriya acikin mutane da aljannu,, saboda haka banida fargaba ko shakku akanta ".
Boka LOK'ORO yace mata "tabbas haka ne Talatu ,,,ki tafi zuwa gidanki na barki lafiya ".
Yana gama fad'ar wannan magana ya b'ace b'at kamar bai tab'a wanzuwa a wurin ba,,, Inna Talatu tana ganin boka LOK'ORO ya tafi itama ta rikid'a ta zamo kaza ta k'ara gaba domin zuwa gida...
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Inna Talatu ta koma gidanta ta cigaba da harakokinta itada Gwamma,, amma bata sanarda ita abinda boka LOK'ORO yace ba na gameda da mutuwarta ba,, saboda kada ta tayar mata da hankali.
Haka dai suka cigaba da rayuwarsu ta cin naman mutane da aljannu,,, cikeda matuk'ar kwanciyar hankali.
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan kwana biyu da faruwar magana atsakanin Inna Talatu da boka LOK'ORO,, bayan sun tashi da safe ne sun karya Inna Talatu tace ma Gwamma zataje daji domin ta d'ebo ganyayyakin da zata had'a wani magani,, Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo,, Inna Talatu ta shirya tayi cikin k'urgumin daji Gwamma tana ganin ta fita itama tayi wurin kamun inwar kurwar mutane da satar kayan jama'a har cikin gida.
Inna Talatu ce ta shigo k'usurgumin daji mai duhu da yawan itatuwa,, yanada manyan duwatsu babu abinda ke tashi cikin dajin sai kukan tsuntsaye dana namun daji daga ganin halittar dajin kasan ba za'a rasa k'wamak'wanmai acikinsa ba.
Inna Talatu ta falfala da wani azababban gudu tana hawa saman wannan icce ta sauka tahau wancan bishiya,, haka dai ta kama yawo acikin dajin cikin tsafi da sihiri harta kallama had'a ganyayyakin da suka kawota,, ta juyo ta kama hanyar zuwa gida tana tafiya tana wak'e wak'enta.
Tayi nisa da tafiya kenan kwatsam! Sai taga Sala mafarauci agabanta kamar an jefosa,, hannunsa rik'eda kwari da bakansa ga kuma kibiyar halbi a d'ayan hannunsa,, jikkarsa ce goye abayansa ya kamo namun daji irinsu,, kura,, damo,, zomo da maciji.
Inna Talatu taja tayi tsaye turus gabanta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri,, ta daure ta dubesa da jajayen idanunta b'acin rai k'arara ya bayyana akan fuskarta tace "kai Sala mafarauci lafiya ka taremin hanya,, mi kake nufi ne dani wai? ".
Sala mafarauci yace "kasheki zanyi Talatu saboda na dad'e ina d'ana miki tarko kina tsallakewa,, kin addabi mutanen gari da cin namansu saboda rashin imaninki ko jariri baki bari ba,, yau zan kawo k'arshen rayuwarki da zaluncinki! Ayau komai naki zai zama tarihi ".
"k'aryarka tasha k'arya Sala mafarauci ayau kaine zaka zama gawa bani ba,, sai dai uwarka ta haifi wani d'an idan tana raye amma ba kaiba,, ayau zaka d'and'ani d'acin mutuwa kwanciyar kabari shine yafi dacewa dakai a yanzu babu b'ata lokaci ".Inji Talatu cikeda matuk'ar tashin hankali da bala'i!.
Sala mafarauci yace "lallai kuwa ayau zakiyi nadamar duk abinda kika aikata saina banbance miki tsakanin k'arya da gaskiya! ".
Yana rufe bakinsa suka afkawa juna da azababban fad'a mai cike da rikitarwa da tashin hankali! Sara da suka kawai suke kaima juna cikin matuk'ar juriya da zafin nama.
Sala mafarauci yayita amfani da kwari da bakansa yana kaimata hari tana kaucewa,, sannan ya sareta da takobi ta kauce ya sari iska,,, kibiyarsa ya jefa mata ta kama kallon kibiyar da idanunta,, siririn haske ya bugi kibiyar ta juya domin ta chake Sala mafarauci ya kauce cikin zafin nama da juriya,, haka itama tayita jefo masa abubuwan sihiri irinsu wuta,, mashi,, wukake k'anana yana tsallake tarkonta.
Sun dad'e sosai suna azabtar da juna duk sun yiwa juna rauni sosai,, jini sai zuba yakeyi daga jikinsu akan fad'a,, amma duk da hakan basu daina ba Sala mafarauci ganin yayi Inna Talatu MAYYA tana batun kashesa a banza da yofi! Dole ya k'ara tattaro dauriya da hakurinsa ya sake afka mata cikin zafin nama ya sanya takobinsa yana ya sare mata kai ,,ai kuwa yana sare kan Inna Talatu jini ya kama bulbulowa kamar teku mai ambaliyar ruwa.
Wani irin rugugin tsawa ne ya bayyana dajin ya kama rawa da girgiza komai na cikinsa ya kama da wuta!,, Namun daji da tsuntsaye suka kama gudu domin ceton ransu,, alal hak'ik'a Sala mafarauci yaga abin mamaki da al'ajabi akan mutuwar Inna Talatu,, yasa hannunsa ya d'auki kan Inna Talatu da ya rabuda gangar jikinta yasa acikin jikkarsa ,,,yana sakawa wani k'aramin rami ya bayyana akusa da jinin jikin Inna Talatu,,, abin mamaki jinin ya dinga shiga cikin ramin har ya k'are tsab sannan gangar jikin Inna Talatu ta k'ara matsawa agefen bakin ramin.
Jinin yana k'are shiga ramin,,, ramin ya rufe kansa kamar bai tab'a bayyana a wurin ba,, Sala mafarauci ya juya zuwa hanyar zuwa gida yana tafiya yana tangad'i kamar mashayi,,, ga jinin Inna Talatu duk yayi masa faca faca a jiki ga wani zafi da rad'ad'in ciwon da taji masa sosai, akafarsa ta dama harta zaftari namansa babba yana shillo,,, dak'yar da bala'in dauriya ya kawo gidansa yana kawowa bakin garka ya fad'i k'asa rikcham ya some.
*Ab'angaren Gwamma kuwa bayan ta tafi wurin sace sacenta da kuma kamun inwar kurwar mutane,,, ta jima sosai a wurin kamun kurwar mutane sannan daga baya ta dawo gida tayi wanka tana jiran dawowar Inna Talatu.
Tana, zaune taji gabanta ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai zuciyarta tana yi mata k'una da tafasa sosai,,, haka kawai taji hawaye sun zubo daga idanunta jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta chanza kammani,, safa da marwa kawai takeyi a cikin d'akin ita kanta ta rasa dalilin dayasa hankalinta yayi matuk'ar tashi sosai,, zuciyarta tana yi mata suya da tafasa sosai .......
_Share&Comments_
*Muje zuwa*💗
[6/28, 4:34 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 17*
Zuciyarta ta kama tafasa da k'una sosai,, hakan ne ya tabbatarwa Gwamma akwai mugun abun da zai faru marasa k'yau ko ya faru ,,,hankalinta ya sake tashi ta dubi agogo bango ganin har Inna Talatu MAYYA ta zarce kusan awa biyar awaje,,, bata dawo gida ba gashi ita kad'ai cikin gidan babu mai shigowa ko lek'owa ganin mahaifiyarta ta jima sosai a waje,,, yasa ta yanke shawarar bari ta bita can inda taje ta nemota ta dawo gida,,, sai da Gwamma tasa tsintsiya ta k'ara sharen gidan sannan tayi musu girki domin tarbon dawowar mahaifiyarta,,, tana kamalla komai da komai ta sake wanka ta shirya cikin tufafinta masu dama dama,,tana shiryawa ta d'aga hannunta sama tana sambatu na tsafi da sihiri ta jima sosai tanayi,,,, saiga wani bak'in abu ya bayyana yana zagayarta can naga ya shige cikin jikinta ta rikid'a ta koma tsuntsuwa fara tass,,, tana komawa tsuntsuwar ta fito filin gida ta bud'e fikafikkanta ta tashi sama ta lulluk'a a cikin sararin samaniya tana ta matsiyacin gudu kamar aljana..
**********************
**Ab'angaren Sala mafarauci kuma bayan ya fad'i k'asa abakin k'ofar gidansa ya suma,,, duk jikinsa jinin Inna Talatu ne da kuma mugun raunin da taji masa hak'ik'a ya zubar da jini fiyeda kima,, ya dad'e kwance a k'asa babu wanda ya gifto can saiga Ummaru d'ansa da yayansa Labaran baban marigayi Lado sunzo bakin k'ofar gidan zasu shiga ciki,,, suna kawowa suka iske Sala mafarauci cikin jini kwance a k'asa ya suma,, sukaja suka tsaya,, baba Labaran ne yace "Subahanillah Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Sala ne akwance cikin jini Ummaru,, ko namun daji ne sukayi masa haka amma bamu sani ba ".Ummaru yace "anyah kuwa baba namun daji basu tab'a yima babana ba wannan mugun ta'addanci ba,, akwai dai abinda yake faruwa dashi "."wannan abu ko da yayi masa rauni sosai agaskiya koma miye bayada imani ko kad'an,, Allah ubangiji dai yasa shi farfad'o daga suman da yayi ".Inji baba Labaran,, Ummaru yace "amin baba ai komai yayi zafi maganinsa Allah,,, Allah ubangiji ya bashi lafiya ".Baba Labaran yace "amin yanzu abinda za'a yi shine mu kamashi mu ida shigardashi cikin gida,, kada mutane su fara taruwa suna yad'a maganganun gulma da jita jita ".Ummaru yace "to baba maganarka haka take mutane lamarinsu sai Allah "."ai shine saboda kasan mutanen garin nan akwai shegen munafurci da gulma ce gulma ce ".Cewar baba Labaran.
Ummaru ya kama hannuwa baba Labaran ya kama k'afafuwansa,,, suka ciccib'esa dak'yar suka shigardashi cikin gida suna nishi mai d'aukeda wahala,, suna shigowa baba Labaran ya kira Innar Ummaru da sauri ta fito daga cikin d'akinta,,, ya umurceta ta kawo tabarma a shimfid'a ma Sala mafarauci akwantar dashi,, jikinta yana rawa zuciyarta tana fad'uwa rasss saboda ganin halin da mijinta yake ciki na ciwo sosai,,, yasa tayi sauri ta d'auko tabarma da filo aka kwantar da Sala mafarauci samanta,, sannan aka aza kansa saman filo.
Inna Ummaru mai suna Yashe ta bud'i baki dak'yar cikin rashin kwanciyar hankali tace "yaya Labaran mi ya sami Sala,, a ina kuka tsintoshi? ".Baba Labaran ya dubeta duba na fahimta yace "kwantar da hankalinki Yashe anan muka tsinceshi bakin k'ofar gidan nan,, kwance a k'asa cikin ciwo ".Ummaru ya dubi mahaifiyarsa ganin irin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta,, dole yasa ya tausasa halshensa yace "eh ba wani babban abu bane Inna,,, rauni ne kawai yakeda ajikinsa kuma Insha Allahu zai warke ".Inna Yashe tace "Allah ya bashi lafiya ".Baba Labaran yace "amin Ummaru tashi ka shigar masa da jikkarsa cikin d'akin,, sannan kafin ka shigarda da ita fito da namun daji daya kamo saboda kada su lalace a banza,, wanda ya kamata asaisuwa sai asaisuwa wanda ya dace aci sai a ci".Inna Yashe tace "haka ne gaskiya ".To baba ".Cewar Ummaru alokacin ne ya mik'e tsaye yana fito da duk naman da Sala mafarauci ya kamo,, bayan ya gama fissuwa hmmmm yaji akwai abinda ya rage mai nauyi dunk'ulalle kamar k'wallo,, yana tab'awa yaji kamar kan wata dabba haka ne yasa ya fitar dakan Inna Talatu batare da yasan ko miye ba,,, yana fitarwa dukkansu idanunsu ya sauka ga kan Inna Talatu MAYYA,, ai saida suka zabura da k'arfi! Hankalinsu ya d'unguma sosai ita Inna Yashe fitsari ta saki a tsaye tareda rik'e bangon d'akinta 😂😂,,,su baba Labaran kuwa jikinsu sai rawa yakeyi da makarkatar tsoro,,, saboda shi yasan har abada bazai tab'a mantawa da Inna Talatu MAYYA ba domin jikinsa da zuciyarsa sun bashi itace sanadiyyar mutuwar Lado da sauran mutanen da ake kashewa! Ummaru ne yayi saurin mayarda kan Inna Talatu acikin jikka sannan yasa acikin d'akin Babansa ya kullesa aciki.
Sannan Ummaru ya dubesu yace "ina ganin kamar wannan abin bana damuwa bane,,, karku damu idan baba ya farfad'o zai sanardamu duk abinda ake ciki ko mike faruwa ".Baba Labaran ya dubesu yace "wannan abin haka yake amma akwai ban mamaki da al'ajabi acikinsa ".Inna Yashe dake wuru wuru da idanu alamar tsoro tace "muyi dai hak'uri har lokacin da Sala ya farfad'o zamuji duk abinda mukeson ji ".
"tabbas haka ne amma indai shi ya kashe Talatu MAYYA da kansa dole ne yaji jiki sosai,,, kuma Sala ya cika babban jarumi ".Inji baba Labaran.
Ummaru yace "babu shakka baba ne ya kashe Talatu mayya,,, shikenan mun rabuda azzaluma macuciya mai cin naman mutane ".
Inna Yashe tace "haka ne gaskiya maganarka Ummaru ".
Baba Labaran ne ya umurci Ummaru daya d'ebo ruwa a cikin randa masu sanyi,,, Ummaru yaje ya d'ebo ruwan ya kawo masa,,, yana kawon ruwan baba Labaran yayi doguwar addu'a acikin ruwan sannan ya watsawa Sala mafarauci ruwan ajikinsa.
Bayan jimawa kad'an sai naga Sala mafarauci yaja numfashi mai tsawo ya farfad'o daga suman da yayi,,, farin ciki da murna ya bayyana a zuk'atansu,,, shima kallonsu kawai yakeyi ya kasa magana akan rad'ad'i da zafin ciwo..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
**Tsuntsuwar da Gwamma ta zama ta kama falfala gudu bata sauka a ko'ina ba sai cikin k'usurgumin dajin da aka kashe Inna Talatu,,, tana sauka ak'asa cikin dajin ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma Gwamma,,, tana shiga cikin dajin lungu da sak'o gabas da yamma kudu da arewa tana neman Talatu MAYYA. Ta jima sosai tana nemanta harta galabaita akan yawo cikin dajin gashi hankalinta duk ya k'ara tashi,,, jikinta yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan neman mahaifiyarta,, saida ta sake dawowa baya sannan taci karo da gawa kwance ak'asa duk naman jikinta tsutsotsi ne da tsuntsaye da namun daji sun yakuce naman,,, sunyi guntu guntu dashi wani mugun wari da d'oyi kawai ke fita daga cikin naman Inna Talatu.
Gwamma bata gane Innarta bace Talatu ba saida ta tsaya tana nazari da kallon gawar da k'yau,,, cikin natsuwa da yawan kallon gawar can taga guntun zanen Inna Talatu ak'asa yasshe,, ta duk'a har k'asa ta d'auko guntun zanen Inna Talatu sannan ta d'ebi jinin da yake ga naman tana karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri ,,,,tana tayin wasu surutai marasa dad'in saurare da ji,,, ta jima tanayi saiga rugugin tsawa da hayak'i sun bayyana dajin gaba d'aya ya kama girgiza da tsawace tsawace mai muni! Jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye zago zago,,, idanunta sunyi jawur kamar barkono can dai duk abinda ya faru a tsakanin Inna Talatu MAYYA da Sala mafarauci ya bayyana tana ganin komai,,, daga farkon fad'ansu har K'arshensa inda ya kashe mata mahaifiya..
Tana ganin abinda ya samu mahaifiyarta ta fasa gigitacciyar k'ara da kuwwa! Dajin gaba d'aya ya amsa kuwwarta wani irin mahaukacin kuka ne takeyi mai cikeda tashin hankali da bak'in cikin rayuwa,,, jikinta gaba d'aya bak'in hayak'i ne ke fita bakinta da kunnenta kumfa suke fitowa saboda b'acin rai k'arara dake cikin fuskarta,,, kammaninta gaba d'aya ta rikid'e zuwa babbar dodanniya! Ta bud'i baki dak'yar tace "na rantse da rayuwar mahaifiyata na rantse da boka LOK'ORO,, kuma na rantse da gadon maita da tsafi! Sala mafarauci kajama kanka masifa da bala'i,,, kajama kanka mutuwa wlh saina kasheka na kashe duk zuri'arka!Saina d'auki fansar jinin mahaifiyata duk mutane garin Gumi kaja musu bala'i da tashin hankali !Saina kashe duka mutanen gari baki d'aya ".
Haka dai ta kama kururuwa da kuwwa mai cikeda tashin hankali da k'uncin rayuwa! Sannan daga baya ta dawo tsuntsuwa ta tashi sama cikin sararin samaniya tana masifar gudu harna tashin hankali,,,,, ta kamayin masifaffen gudu mai cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa!.
**********************
**Ab'angaren Lawwali bayan ya gudu ya koma gidan baba Labbo da kuma matarsa Inna Tani,,, bayan ya koma gidan baba Labbo ya had'ashi da d'iyansa Ila da Sagiru yana koya musu aikin noma da kasuwanci,,, komai na gidan cikin kwanciyar hankali da natsuwa suke yinsa basu nunawa Lawwali banbanci ko kad'an,, hankalin Lawwali ya kwanta sosai har haske da k'iba ya k'ara yi,,, duk abinda suke buk'ata shi sukeci iyaka gwargwado suna cin mai k'yau susha mai k'yau cikin rufin asiri da wadatar zuci ,,,komai tare sukeyi shida su Sagiru suna tsananin k'aunar Lawwali da tausaya masa saboda irin muguwar uwa da Allah ya bashi mara tsoron Allah da mugunta iri iri daban daban.
**Wata rana ne Inna Tani tana zaune da baba Labbo suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da fahimta sosai ,,,,Inna Tani ce ta dubi baba Labbo tace "agaskiya maigida ina matuk'ar tausayawa rayuwar Lawwali,, yanada halayyar k'warai da sanyin zuciya sannan gashi Allah ya had'asu da muguwar uwa MAYYA ".
"hmm Allah ya dai karemu daga shairin mugayen mutane,, amma lamarin Talatu kam sai a hankali duk ta rikita mutanen gari sai kashesu takeyi,, harda d'an uwana mijinta ta kashe saboda kada yayi mata kishiya! ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar bak'in ciki da jimamin mutuwar Malam Mamman.
Inna Tani ta nisa sannan tace "ai ganin akan irin abubuwan da Inna Talatu keyi ne yasa Lawwali ya gudu ya barta itada Gwamma su kad'ai aciki gida,,, Talatu kam tayi nisa bata jin kira saidai kayi hak'uri na kashe yaya Mamman da tayi,,, amma agaskiya ba zata tab'a k'arshe mai k'yau ba saitayi mutuwar walak'anci da tozarci! ".......
_Share&Comments_
*ku cigaba da bina fans*
[6/28, 4:35 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 18*
Malam Labbo ya dubi Inna Tani yace mata "idan banyi hak'uri ba mi zanyi mata Tani,, ni kaina idan nayi mata wata maganar banza tana iya kasheni a banza da yofi! Ni wallahi tsoronta nakeji kamar ciwon ajali,,, saboda nasan wadda rashin imani da rashin tausayi yasa ta kashe mijinta akan *KISHIN JAHILCI* da hauka,,, to babu shakka uban kowa tana iya kashewa batare da wani fargaba ko tsoro ba,,, domin mayyu da kike ganinsu basuda d'igon imani da tausayi ko kad'an a cikin zuciyarsu ".
Inna Tani ta bushe da dariya sosai sannan tace "ashe dai maigida kana tsoron mutuwa wallahi! Nida so nayi ka tareta kace mata miyasa ta kashe maka d'an uwa,,, ka dai gane ka irin tsorata ta d'in nan kace zaka had'ata da hukuma ".😁😁
"wa! Ni idan kikaga an kaini cikin kabari kaini akayi bani nakai kaina ba,,, so kike ina zuwa ta dubeni da shegunan idanunta jawur kamar wuta ta kame mini kurwa ta lak'umeni aini duk abinda tayi alhakin mutane na nan bisan wuyanta,,, saboda haka ki rufamin asiri babu ruwana duk abinda zatayi taje tayi tayi duniya ce wanda baizo bama jiransa take ".Inji Labbo cikeda matuk'ar tsoron al'amarin Inna Talatu MAYYA.
Inna Talatu ta sake fashewa da dariyar k'eta harda rik'e ciki takeyi akan dariya,,, sai ta dubi Labbo sannan ta fashe da wata dariyar mugunta.
Can dai ta daure ta tsayar da dariyar ta karkace baki tace "kaini wasa nakeyi maka taya zance kaje mahalaka da hankalina,, halan so nake in zama bazawara ai nasan ko maza masu tashe da k'arfi da mazantaka tsoron tunkarar mayyu sukeyi,, balantana kaida ka kwana biyu Allah ya sawwak'a in tura uban 'ya'yana wurin annobar gari mai cin naman mutane ".
Labbo yace "aike bakisan wani abu ba,,, idan kikaga yadda maza da mata yara da manya suke gudu in suka hango mayyu yadda zasu cikama buje ko wandonsu iska da gudu,, to sai cikinki yayi ciwo akan dariya wlh ai ni abin na d'aure min kai yadda suke rikid'a su koma kowace irin halittar suka gadama ".
"ina ni ina tsayawa dariya kowa yanata kansa,, to kai maigida miye abin mamaki bayan kowa yasan tsafi da sihiri ne sukeyi suna komawa kowace irin halitta,, inda ma Gwamma kaje ka dawo da ita nan kada uwar ta koya mata mummunan dabi'a da halinta ".Inji Inna Tani tana dariyar mugunta k'asa k'asa kada Labbo ya jiyota.
Labbo ya harareta yace "ina ni ina raba uwa da d'iyarta babu ruwana wlh,, ai tasan da zamana tayi zamanta wurin mahaifiyarta amma ke na baki iznin ki fita kije ki dawo da ita wannan gida ".
Inna Tani tace "hmmmm wai mutuwa kenan! Ni ko uwatace ke maita gudunta zanyi saboda in tsira da raina da lafiyata,,aini saboda tsorana ko muryar mayya naji saina saki fitsari a cikin wando 😂balantana har nakai kaina mahalaka ".
"to shine saboda kin mayardani wawa kike cewa inje ina ruwanki,, ai d'an uwana ne ta kashe ba naki ba to nabarta ga Allah ubangijin talikkai shi zaiyi mana hisabi a tsakaninmu ".Cewar Labbo ya muzurai da idanu alamar tsoro..
Inna Tani tace "kaini wasa nakeyi maka ai duk abinda zai cutar dakai sai inda k'arfina ya k'are,, bawai ince kaje gidan mutuwa ba ".
Labbo yayi murmushi yace "ai nasan wasa kike yimin matata,, uwar yarana banda tamkarki a cikin zuciyata ".Yana wani kashe mata idanu alamar soyayya. 😂
Inna Tani tayi masa kallon so tace "su Labbo kenan an tunada tsohuwar soyayyar da mukayi tunda dad'ewa sosai ".
"na tuna uwargida ran gida ".Inji Labbo.
Suka fashe da dariya tareda kallon juna suna murmushi,, daga ganin yadda suke gudanar da rayuwar aurensu akwai soyayya da k'auna mai k'arfi a tsakaninsu,,, firarsu kawai sukeyi cikeda matuk'ar farin ciki da kwanciyar hankali.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
**Abangaren Sala mafarauci yana farfa'dowa daga suman da yayi,, Inna Yashe ta kawo masa ruwa da abinci da magani ya fara cin abinci sannu a hankali,, cikin yanayi na ciwo sosai baba Labaran da Ummaru suna zaune gefe suna kallonsa cikeda matuk'ar tausayawa sosai.
Ya cigaba da cin abinci bayan ya d'anci mai dama sannan yasha ruwa tareda maganin,, ya aje kofin gefe yana jan numfashi dak'yar,, su duka sukayi masa sannu ya amsa,, baba Labaran yaje ya d'auko garin magani na gargajiya Inna Yashe ta shafe duka jikin Sala mafarauci dashi maganin,, da maganin ya fara yi masa rad'ad'i da zafi sai naga Sala mafarauci yana runtse idanu tareda cije baki yana nishi sannu sannu.
Zuwa wani lokaci sai naga maganin duk ya game jikinsa gaba d'aya yana ratsa sassan jikinsa,, ga wani irin zufa dake tsiyaya cikin jikinsa can yaja doguwar ajiyar zuciya sannan yace "hmmm yau naga mutuwa ga filin wuri naga tashin hankalin da ban tab'a ganin irinsa a rayuwata ba,, nasha azaba da bak'ar wuyar da ban tab'a shan taba a cikin rayuwata,, lallai mayyu annoba ne kuma guba ne cikin al'ummarmu saboda suna kashemu a banza sannan su cinye namanmu a yofi,,, ban tab'a zaton rashin imani da rashin tausayin mayyu yakai haka ba sai yanzu da naga mutuwa a filin wuri k'iri k'iri ".
Baba Labaran yaja doguwar ajiyar zuciya sannan yace "hak'ik'a yau k'anena kaga tashin hankali,, kuma Allah yasa kanada tsawon rai domin Talatu ko cikin mayyu ba k'aramar mayya bace ba,,, sannan duk ta zamo shahararriyar *MAYYA CE* wadda ta gagari mutane da dama acikin wannan gari namu mai tarin albarka ".
Ummaru yace "abin ba'a cewa komai amma gaskiya sharrin mayyu da muguntarsu ya wuce tunanin duk wani d'an Adam,,, sabodasu sun riga sun fita daga cikin mutane sun zama mayyu haka suke ganin komai na jikin mutane,, kamar dai yadda kukasan k'warangwal (skeleton),, wasu ma idan suka kama mutum idan ya gagaresu aljannu suke mik'awa kurwarsa su kashesa! Saboda haka baba ka auna babban arzik'i da ka dawo da ranka ".
"mun godewa Allah ubangiji da ya bashi ikon kasheta da kuma dawowa da rai,, duk da yake shegiyar annobar duk ta jimasa raunika da yawa ga jini sai zuba yakeyi a d'azu ajikinsa ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da farin cikin mutuwar Talatu k'usurgumar mayya.
Baba Labaran yace "haka ne gaskiya maganarki mun gode Allah da farin cikin dawowarsa a raye gida,, amma muna son ka bamu labarin irin gwagwarmayar da kasha wurin kashe wannan mayyar Talatu ".
Sala mafarauci ya gyad'a kansa yace "yanzu kuwa zan baku labarin yadda abin ya kasance "......Ya kawo labarin komai duk abinda ya faru daga farko har k'arshe ya gaya musu,,, bai b'oye musu komai ba na irin abubuwan da suka faru a tsakaninsu da Inna Talatu,,, da kuma irin tsafe tsafen da ta kamayi tana rikid'a ta koma mutum,,, haka dai ya sanardasu komi bai b'oye ba..
Suka had'a baki wurin cewa "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! "...
Haka dai suka cigaba da tattaunawa akan lamarin mayyu,,, da kuma irin cutarwar da sukeyi acikin al'ummar musulmai baki d'aya..
*Allah ubangiji ya kiyayemu*..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan faruwar mutuwar Inna Talatu MAYYA duk labarin komai,,, da irin kisan walak'anci da Sala mafarauci yayi mata ya bazu ko'ina a cikin garin Gumi,,, ko'ina lungu da sak'o acikin garin kowa ka gani fuskarsa tana bayyanar da tsananin farin ciki da nishad'i mara misaltuwa.
Majalisar samari da ta dattijawa sai murna sukeyi suna mayarda labarin abinda ya faru ,,, saboda farin ciki da murna ji sukeyi kamar su goya Sala mafarauci abayansu,, sarki da dogaransa da kansu sukaje har gidan Sala mafarauci sukayi masa godiya tareda da bashi babbar k'yauta,, ya amsa yana cikin farin ciki da nishad'i sosai domin yanzu kam yaji sauk'i sosai a jikinsa,, sukayi masa sallama tareda musabaha da junansu cikin girmamawa,,, suka wuce zuwa gida..
Tsuntsuwar bata sauka a ko'ina ba sai a cikin k'usurgumin dajin da boka LOK'ORO yake zaune,,, tana sauka ak'asa ta koma ainahin siffarta Gwamma,,, ta iske har boka LOK'ORO ya bayyana yana jiranta.
Ta dubesa da idanunta jawur kamar barkono,, b'acin rai da bak'in ciki ne suka bayyana k'arara akan fuskarta,,, ga hawaye yab'e yab'e a fuskarta tace "boka LOK'ORO ya kashemin mahaifiyata ya zanyi da rayuwata boka?,,, na zamo marainiya banida uwa banida uba wallahi wallahi duk wanda yakeda sa hannu ko yayi farin ciki da mutuwar mahaifiyata,, duk saina kashesu! Gaba d'ayansu in yaso kowa ya d'and'ani zafin mutuwa da rashin uwa,,,gasu can sai walima sukeyi suna murna da farin cikin mutuwar Talatu MAYYA ".
Boka LOK'ORO yace "kiyi hak'uri Gwamma zaki d'auki fansar jinin mahaifiyarki,, yanzu nan zan k'ara miki k'arfin tsafi da sihiri wanda zaki iya yak'ar kowane mahaluki a cikin duniya! ".
"ina son ka bani k'arfin sihirin da babu wanda zanji tsoronsa a cikin wannan duniyar mai cikeda bak'in ciki ".Inji Gwamma tana zubarda hawayen bak'in ciki da k'uncin mutuwar mahaifiyarta!.
Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya mai cikeda rugugin tsawa da bak'in hayak'i! Yace "yanzu kuwa zan baki sihirin da zaki kashe kowa kici naman kowa yadda kike so,,, sannan idan kika kashe Sala mafarauci ya mutu Ummaru d'ansa zaiyita farautarki kamar yadda sukeyin farautar namun daji! Saboda haka kiyi taka tsan- tsan da Ummaru domin shima hatsabibin yaro ne da zai gaji ubansa a farauta ".Yana gama fad'ar wannan magana ya dinga feso mata wani irin abu mai tsananin haske,,, shi kuma abin ya kama shiga cikin jikinta sosai yana kuma zagayarta da sauri da sauri!.
Hasken saida ya shige cikin jikinta tsab sannan komai ya dawo dai dai,,, "ki tafi gida Gwamma ki kashe duk wanda kike ra'ayi babu wanda ya isa ya hana ki sai Ummaru d'an Sala mafarauci,, saboda haka ki bishi a hankali sannu ki samu ki kawardashi a doron k'asa kafin ya zamo ajalinki! ".Yana kawo k'arshen maganarsa ya b'ace b'at kamar bai tab'a sauka a wurin ba.
"to mai girma boka LOK'ORO zanyi biyayya agareka matuk'ar ina raye,, sannan zanyi taka tsan- tsan da Ummaru d'an babban mak'iyina a duniya,, na rantse da girman tsafina saina kashe duka dangin Sala mafarauci muddin ina raye a cikin duniya! ".Inji Gwamma tana gama fad'ar wannan kalmar ta rikid'a ta koma tsuntsuwa,,, ta tashi sama tana masifaffen gudu a cikin gajimare,, tun ana hango tsuntsuwar har ya zamana ko hangota ba'ayi ta riga ta b'ace a cikin sararin samaniya..........
_Share&Comments_💜
[6/28, 6:03 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 19*
Ta b'ace a cikin sararin samaniya tana masifaffen gudu harna tashin hankali,,, ta jima sosai tana gudu sannan ta kawo gida ta sauka a saman roofing na gidan,, sannan ta sauko a cikin tsakiyar gidan wanda ya zamo mallakinta ayanzu,,, bada jimawa ba ta rikid'a zuwa ainahin siffarta Gwamma tana mai bak'in ciki da takaicin yadda aka kashe mata mahaifiya zama guda,,, ta nufi randar ta d'ebo ruwa tayi wanka fes.
Sannan ta gama shiryawa taci abincin da ta girka tunda safe,,, sannan ta nufi wurin inda take aje kurwa mutane kusaga randa ta d'auko fa ru (grasshoppers) kusan shidda ta lak'umesu a cikin bakinta,, batareda ta tsaya gasawa ba aiko tana cinyesu duka sai wata irin kuwwa da kururuwar mutane kawai yake tashi! Gwamma ta rufe kunnuwanta domin kada ta kurumce ga wata irin iska da guguwa mai k'arfi dake zagayar gidan sosai,,, hankalinta kwance dayake tasan babu abinda zai iya tunkararta da fad'a ayanzu,,,bayan komai ya lafa ta tashi daga inda take zaune tanata huci da bak'in rai akan yanzu ta rasa kowa nata idan ba Lawwali ba,,, tasha alwashin koda zatayi yawo tsirara sai taga bayan dangin Sala mafarauci da zuri'arsu baki d'aya,,,saboda ya sanyata cikin bak'in cikin da har abada ba zata tab'a warkewa ba idan har bata kashesa ba,,, bata huce takaici ba sannan kuma masu murna da farin ciki da kuma masu yin walima akan mutuwar mahaifiyarta saita kashe musu mata ko d'iya,,, domin su d'and'ani irin kwatankwacin zafi da rad'ad'in da ta jiya a cikin zuciyarta,,,,bazata tab'a yafewa duk wanda yakeda sa hannun acikin mutuwar Inna Talatu MAYYA ba,,,,shiyasa yanzu taji zuciyarta tana k'una da tafasa sosai wani irin zugi da rad'ad'i ne zuciyarta,,, ga wani turirin bak'in ciki daya dafe mata kan zuciya wani abu takeji yana tokare mata saman k'irji kamar an aza mata dutse babba.
Can dai ta kwanta saman gadon Ummanta tana zubar da hawayen bak'in ciki da na rashin uwa,, ga wani zogi da zuciyarta keyi saboda damuwa,, haka dai tayi shiru tana tunanin rayuwarsu ta can baya itada mahaifiyarta Inna Talatu da mahaifinta Malam Mamman...
**********************
**Acan cikin gari kuwa bayan mutanen sun gama yin walima da cin abincin walimar ,,,kowa ya watse tareda kama gabansa,, saboda yanzu mutane sun saki jikinsu sai murna sukeyi da mutuwar Talatu MAYYA,, wasu ma har gidan Sala mafarauci suke zuwa suna yi masa gaisuwar ya jiki dana ban girma sannan ya d'auko kan Inna Talatu da ya fille ya nuna musu ,, saboda tsananin jarumtakar daya nuna da kuma k'ok'arin da yayi wurin kashe k'usurgumar mayya gagararriya irin Inna Talatu,,, wadda akan shahararta ba kowa ke iya fad'a mata maganar banza ba..
Ganin maitar tayi sauk'i k'warai bayan mutuwar Inna Talatu MAYYA,, yasa mutane suka saki jikinsu kowa ya cigaba da sha'aninsa da kuma kulada iyalinsa,,, kodayaushe mutum zai iya fitowa acikin tsakar dare batare da fargaba ba ko shakku ba,,, idan kaga yadda mutane suka dawo cikin natsuwarsu da walwalarsu sai kayi mamaki sosai,,, mutane suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikeda matuk'ar kwanciyar hankali da kuma gudanar da kasuwancinsu..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SATI GUDA*
Bayan sati d'aya da mutuwar Inna Talatu MAYYA,, Gwamma ta wartsake ta share maganar kashe Sala mafarauci saboda batason ayi saurin gano ta zamo shahararriyar mayya,,, domin tasan hakan ne zai iya tona mata asiri da wuri yasa mutane su ganota cewa ita d'in mayya ce,,, saboda haka ne taba zuciyarta hak'uri da dangana tana kula da duk wani motsi na Sala mafarauci,,, duk inda ya shiga akan idanun Gwamma yake tana hankalce dashi da duk wani motsinsa,, idan tari Sala mafarauci yayi akan idon Gwamma idan abinci yakeci akan idonta ne,, in tak'aice muku babu wani motsin da zaiyi ba'a kan idanun Gwamma ba..
**Washe gari da safe misalin k'arfe 9:30am na safe,, Gwamma ta tashi tunda tayi sallar asuba ta share gidan gaba d'aya tsab sannan ta aza ruwan zafi asaman murhu ta d'ibi na wanka,, sauran ta barsu domin ta had'a shayi mai kauri.
Bayan ta shiga wanka ne ta fito ta sanya doguwar rigarta,, sannan tazo kitchen ta juye sauran ruwan zafinta a kofi tana juyewa ta shige cikin d'akinta,, ta d'auko kayan shayi da biredi ta had'a shayinta mai kauri tana sha da biredi,, haka dai ta cigaba da cin abincinta cikin natsuwa harta kammala,, tana gamawa taje wurin murhun wuta ta d'auko fara biyar ta cinyesu zama guda,, saida kuwwar mutane da kururuwarsu ta bayyana na tsawon lokaci,, bayan komai ya lafa ta fito bakin k'ofar d'akinta ta shimfid'a tabarma ta zauna shiru tana nazari da tunanin lamarin duniya da zamantakewar rayuwa gaba d'aya..
Can dai da jimawa saiga sallamar baba Labbo ya shigo har cikin gidan batare da wani shamaki ba,, Gwamma ta tsura mishi jajayen idanunta tun kafin ya k'araso kusa gareta yana k'arasowa ya samu wuri ya zauna kusa ga Gwamma,, yana kallonta yana mai tsananin jin tausayinta saboda gata marainiya kuma d'iya mace ita kad'ai acikin gidan,,, dak'yar ta bud'i baki ta gaidashi ba domin ranta yaso ba ya amsa mata cikin sakin fuska da walwala.
Sannan ya dubeta cikin tausayawa da k'aunarta amatsayinta na d'iyar yayansa yace "Gwamma ya mukaji da hak'uri na rashin da mukayi? ".
Gwamma ta kauda kanta cikeda matuk'ar takaici da jin haushinsa,, tace "mun gode Allah ya zamuyi duk abinda Allah yayi mai k'yau ne ".
"haka ne 'yata inason kiyi hak'uri ki maida komai ba komai ba,,, Allah ubangiji da ya baki su yaya Mamman da Talatu amatsayin iyayenki shine zai chanza miki da sauyi mafi alkhairi,, sannan ki sani dukkan mai rai mamaci ne kowa lokacinsa ne kawai yake jira,, burinmu dai Allah yasa mu cika da imani muna musulmai ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar tausayi da lallashi.
Nasihar nan da yakeyi mata saida taji an fama mata tsohon ciwon da ya riga yayi mata k'urji acikin ciki,,, ta d'ago rinannun idanunta jawur dasu tace "haka yake baba ".
Baba Labbo yace "saboda haka amatsayina na babanki k'ane ga mahaifinki Mamman,,nake umurtarki da ki dawo gidana da zama saboda bai dace ba kina yarinya budurwa kina zaman kanki ke d'aya acikin gida,,, bak'ya tsoron kada wani abu na cutarwa yazo ya cutardake ko yayi miki wata illa,, sannan akwai matasa masu shiga har cikin gidan mutane suna musu fyad'e da k'arfi da yaji,,, saboda haka ki tashi yanzu ki kwaso kayanki bazan bar gidan nan ba sai k'afata k'afarki ".
"to baba yanzu zan shiga cikin d'akin in had'o kayana saimu wuce zuwa gidanka ".Cewar Gwamma.
Baba Labbo yace "ina jiranki d'iyar albarka shiga ki had'o kayanki ".
Tace "to baba ".Ta tashi sannu kamar abin arzik'i ta shige cikin d'akinta,, tana shiga bada jimawa ba ta rikid'a ta koma macijiya mai kai biyu idanunta jawur kamar wuta bakin nan nata wargajeje gudan k'ato,,, macijiyar tayi zuruf zuruf ta fito wurin baba Labbo,, baba Labbo bai hankalta da macijiyar ba saida yaji ana lasar masa tafin k'afafuwa,,, naji yana cewa "wai wa ne irin k'waro ne ke lasarmin k'afafuwa ",,,yana gama magana yana juyowa idanunsa ya sauka akan macijiya,, ai kuwa ya zabura da k'arfi! Yana kuwwa sosai da kururuwar neman agajin mutane,, itama macijiyar tana ganin zai shek'a da gudu ta bisa da gudu tana fitar da halshenta.
Ai kuwa yana ganin ta biyosa ya k'ara gudu tareda k'ara rikicewa! Yana hawayen ganin mutuwa k'iri k'iri,,, ya kama zagayar filin gida saboda tsananin rikicewa da d'imaucewa! Babu abinda yakeyi sai zubar da hawayen tsoro,, macijiyar ta kama binsa harda hawa takeyi saman jikinsa tana k'ara tsoratardashi,, can naga baba Labbo ya buga wata gigitacciyar k'ara da kuwwa mai ban tsoro!.
Saiga kashi da fitsari tsuluttt tsuluttt tsuluttt sun fito daga cikin wandon baba Labbo,, ashe wai zawo yakeyi amma da yake yana cikin tsoro ne da firgici baisan yayi ba,, ya cigaba da zagayar gidan yana kukan bak'in ciki da takaici can ya bud'i baki yace"na tuba dan Allah kiyi hak'uri bansan Inna Talatu tabar miki mai gadinki bane,, nasha aradu bazan koma dawowa cikin gidan nan ba har abada,,, sai yaga macijiyar ta bushe da mahaukaciyar dariya tace "idan ka sake dawowa acikin gidan nan saboda ka tafi da Gwamma,, saina kasheka har abada! "."bazan ma koma dawowa ba kiyimin rai banason in mutu yanzu inbar iyalina ".Inji baba Labbo sai wari da d'oyin kashi da fitsari yakeyi. "Naji! Naji tsohon munafiki fita ka bani wuri,, kafin in chanza ra'ayina in kasheka a banza ".Cewar macijiyar cikeda matuk'ar hasala sosai,, ai kuwa baba Labbo ya shek'a da gudu saida ya buge kansa abango gidan ya fad'i k'asa d'immm! Sannan ya tashi da sauri ya falfala da gudun bala'i yana fesa zawo da fitsari,, babu abinda ke tashi sai b'urr b'urr b'urr yana gudun ceton ransa.
Tun yana gudun ceton ransa har ya kawo gungu samari ya wucesu da gudu,, suna lafiya lafiya Malam Labbo amma ina yayi nisa bayajin kira ganin haka ne yasa samarin suma kowa ya cikawa wandonsa iska suka shek'a da gudu ,,,suna biyar bayan Labbo.
Suna gudu har suka iso majalisar dattijawa suna firarsu cikin natsuwa ,,su Labbo sukayo cikinsu da gudu harda take cikin wani daga cikinsu sukayi yana kuwwa da k'arfi da kuka ,,,dattijawa suka runtuma da gudu da babbar rigunansu harda wanda aka takawa ciki shima ya mik'e zumbur ya kama gudu da k'aton cikinsa kamar k'warya.
Haka dai suka kama gudu nan kamar ransu zai fita,, kowane daga cikinsu ka duba bakin rai bakin fama yake gudu!. Nishinsu da sawun takalminsu kawai ne ke tashi ruduuu ruduuu d'iiiiiiiiii.
Maigari ne zaune da dogarawansa da sauran mutanen gari suna fira,, ga kwanonin tuwo nan da miya aje agefe rufe sannan ga ruwan yamin da aka kawowa Maigari domin ya kaiwa awakin matarsa,,, suna tsaka da firarsu saiga su Labbo da samari,, dattijawa sun shek'o da gudu sunyo cikinsu aikuwa aka d'unguje Maigari ya fad'a cikin kwanon tuwo shida wani dogarinsa,, ga hula da rawanin maigari agefe sai kuwwar zafin ciwo da neman agaji sukeyi shida dogarinsa,, d'ayan kuma ya fad'a cikin miya duk jikinsa ya b'aci sosai da ruwan miya shima sai kuwwa yakeyi yana murza idanu da laluben hanya saboda duk miyar ya shige masa acikin idanu.
Saura mutum uku suka fad'a cikin ruwan yami suna iyo dayake irin babbar roban nance wadda ke iya d'aukar mutane kusan hud'u,, sunsha ruwan yami sunyi tsamo tsamo suna kuwwar neman ceto da agajin gaggawa,, robar da taji nauyin bala'i ta fashe fasss suka kasa tashi a k'asa sai kuwwa sukeyi,, wad'anda suka tsere ko waiwayo su basayi sunata kansu! Wad'anda suka fad'a cikin ruwan yami suka tashi dak'yar suka kama Maigari duk ya k'one a hannu da fuska sai kuka yakeyi,, suka shigardashi cikin gidansa dayake a k'ofar gidan suke zama,, sauran kuwa daga baya mutanen gari ne suka ciccib'esu suka kai kowa gidansa..
**********************
Macijiyar ta koma mutum wato ainahin siffarta Gwamma sannan ta sake rikid'a ta koma kaza,,, ta fito daga cikin gidanta ta nufi gidan Sala mafarauci,, tana tafiya sannu sannu a hankali harta kawo bakin k'ofar gidan ta kalli k'ofar da idanunta wani farin haske ne ya fito daga idanunta ya bugi k'ofar ta bud'e kanta tayi zuruf zuruf ta shige cikin gidan Sala mafarauci da saurinta.........
_Share&Comments_
[7/2, 7:36 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 20*
Ta shige cikin gidan Sala mafarauci da saurinta,, tana shiga bata tsaya b'ata lokaci ba sai cikin d'akin Sala mafarauci da Inna Yashe sunata barcin rana,, ashe kafin taxo itace tayi amfani da tsafinta ta sanyasu barcin rana,,, batareda b'ata lokaci ba Gwamma ta kamayin wasu surutai na tsafi ba'a jima saiga wata irin mahaukaciyar guguwa da k'arfi! Tana zagayarsu Inna Yashe na tsawon lokaci can naga guguwar gaba d'ayanta ta shige cikin jikinsu kaf,,, tana gama shigewa Gwamma mayya tayi amfani da sihiranta ta b'ace a cikin gidan baki d'aya kamar wani halitta bai tab'a wanzuwa a cikin gidan ba,,, ta barsu nan kwance suna barcin sihiri da tsafi..
Bayan wasu awanni saiga sallamar baba Labaran da Ummaru atare suka shigo cikin gidan,, bawai tare suke ba baba Labaran ya had'u da Ummaru ne a hanyar dawowa gida shine yace bari ya biyosa saboda ya k'ara ganin yadda jikin d'an uwansa yayi sauk'i sosai,, suna zuwa sukayi sallama basu amsa ba baba Labaran ya umurci Ummaru daya shiga cikin d'akin yaga shin lafiya,,, Ummaru bai tsaya wasa ba ya shiga yana shiga ya tayar dasu daga barci yana cewa "baba lafiyarku k'alau kukeyin barcin rana? ".Suka kalli juna Sala mafarauci da Inna Yashe sunajin maganarsa amma sun kasa mayarda martani,, ganin haka ne yasa Ummaru ya sake tambayarsu sukayi shiru,, dalilin haka da sukayi ne yasa hankalin Ummaru ya d'unguma gabansa ya dinga bugawa da k'arfi dummmmm! Yaji wani irin d'aci da zafi a cikin zuciyarsa ga wani abu ya tokare masa mai nauyi a k'irjinsa,, can dai ya tattaro dauriya da hak'urinsa ya fito bakin k'ofa ya kira baba Labaran yace "masa baba kazo kaga wani abu ".To Ummaru ".Inji baba Labaran tareda shigowa cikin d'akin,, yana shiga shima saida gabansa ya bada rasssss! Yace "Sala lafiya naga kunyi shiru ne? ".Babu amsa ai kuwa baba Labaran da Ummaru suka dubi juna cikin tsoro da fargaba akan rashin maganarsu Inna Yashe.
Babu b'ata lokaci suka ga naman sassan jikin Sala mafarauci ya fara rabuwa filla filla,, kamar yadda kukasan ake raba sassan naman kaza idan za'a dafa misali k'afa daban kai daban bayanta da fiffikenta daban,, suka tsorace da rikicewa babu abinda ke tashi kuwwa da kururuwar Sala mafarauci cikeda matuk'ar zafi da rad'ad'in mutuwa,, ga jini sai bulbulowa yakeyi kamar an yanke sa! Ummaru da baba Labaran suka fashe da wani irin matsiyacin kuka mai cikeda bak'in ciki da tashin hankali ,, ga Sala mafarauci da Inna Yashe suna cikin mayuwacin hali amma basuda ikon taimakonsu! Sala ya sake buga gigitacciyar k'ara namansa ya rabu ga kansa agefen d'aki sai hawaye suke fitowa daga cikin idanunsa! Inna Yashe itama ta buga wata irin kuwwa tana fisge -fisge da soshe soshe can ta fad'i k'asa d'immmmm naman jikinta ya rabu filla -filla kamar yadda na Sala mafarauci yayi,, abin babu k'yawon gani d'akin gaba d'aya ya garwaye da jininsu Inna Yashe!.
Baba Labaran da Ummaru suka rungume juna akan tsananin tashin hankali da firgicewa! Babu abinda sukeyi sai zubar hawayen bak'in ciki,,, sun rud'e sun d'imauce basu tab'a ganin tashin hankali ba kwatankwacin wannan ba,,, zuciyarsu sai rad'ad'i takeyi da tafasa sun kasa cewa komai balantana suje neman agajin mutane ko taimako akan rikicewa da gigicewa! Bayan sassan naman jikinsu Inna Yashe ya gama yin filla -filla kwatsam sai suka ga tsutsotsi k'anana suna yawo a cikin jinin da sassan jikinsu Sala mafarauci,, can taga tsutsotsin suna shiga cikin wata k'wara d'aya tsutsar ita kuma tana rikid'a tana k'ara girma,, suna gama shigewa gaba d'aya tsutsar ta koma guda wargajejiyar k'atanya,, tayi amfani da bakinta ta kama shan jinin da cin namansu Inna Yashe tana k'ara zama k'atuwa!Taci naman taci taci saida ta cinye naman da kuma shanye jinin kaf baki d'aya! Sannan ta dubisu baba Labaran ta dinga feso musu wuta tana bugunsu gefen hagu da dama tayi musu lik'is da matsiyacin duka,, babu abinda ke tashi sai kuwwarsu da kukansu idan zasu gudu tayi amfani da tsafinta ta mayardasu cikin d'akin, haka dai ta cigaba da gana musu azaba da uk'uba iri iri daban daban na tsananin zalunci da rashin tausayi! Idanunta sunyi jawur kamar barkono jijiyoyin tsutsar ya tashi rud'u rud'u acikin fuskar tsutsar ana hango fuskar Gwamma mayya yana yawo,, amma su basu lura ba saboda tashin hankali da bala'i! Kunsan jikin wanda ya kwana biyu basa d'aya dana tsoho sai naga baba Labaran ya kama shure shuren mutuwa! Yana kururuwar zafin ciwo gashi ji yakeyi kamar ana soka masa allura ko wuk'a a cikin jikinsa,, nan da nan naman jikinsa ya daskare yana yin gunduwa gunduwa ya mutu dis batare da b'ata lokaci ba!.
Ummaru yana ganin abinda ya faru da baba Labaran ya buga kuwwa da gigitacciyar k'ara da k'arfi! Ya tunkaro tsutsar domin yayi mata kisan gillah,, tsutsar tana ganin ya nufota ta hura masa wani abu acikin fuska ya shiga cikin idanunsa yana fara lalube tayi amfani da sihiranta ta jujiyashi a sama! Sannan ta nunasa da yatsa yaje ya bugi bangon d'akin gauuuuuu! Ya fad'i k'asa d'immmmm kansa ya fashe da jini sannan ya suma.
Tsutsar tana ganin irin rashin imani da zaluncin data aikata,, ta bushe da mahaukaciyar dariya tareda rikid'a zuwa ainahin siffarta Gwamma! Ta dubi Ummaru tareda da nunasa da yatsa tace"yanzu muka fara wasar ni da kai na rantse da jinin mahaifiyata baxan tab'a barin kaji dad'i a cikin rayuwarka ba! Kafin ka zamo ajalina saina cusa maka bak'in cikin da har abada ba zaka tab'a mantawa dani a rayuwarka ba! Zuri'arku saina kassarasu baki d'aya munafiki azzalumin ubanka Sala ya ja maka ,,,saboda haka ni babu ruwana da kowa laifin Sala mafarauci ya shafesa! ".
Tana gama fad'in wannan maganar ta girgiza sannan ta rikid'a,,, ta b'ace b'at daga cikin gidan Sala mafarauci,,, suui suuu suuuu kawai kakeji alokacin da ta b'ace.
Tana barin gidan saida taje gidajen mutane tana kashe musu mata da d'iya,,,,,,amma fa wad'anda sukayi walimar murna na mutuwar Inna Talatu MAYYA da kuma wad'anda sukayi farin ciki sosai akan mutuwarta! Duk saida ta bisu gida gida tana kashe d'iya da mata,, wannan ta kashe matarsa wannan ta kashe masa wancan ta kashe masa d'iya haka dai ta kamayi saida ta kashe kusan mutum ishirin gamidasu Sala mafarauci ishirin da uku! Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Wannan masifa tayi yawa sosai,,, bayan ta kamalla kashe duk wanda ya dace ya d'and'ani zafin mutuwa! Ta b'ace b'at ta koma gidanta ko nace na iyayena,,, tana komawa gidan tayi wanka sannan ta dawo ta shirya domin ta kwanta kawai sai ganin mutum zaune tayi a saman gadonta yayi kwance rashe rashe,,, kallonta kawai yakeyi yana lasar baki dak'yar ta bud'a baki tace "wai Sule miyasa bakajin magana ne? Kace kana sona nace maka bana sonka to mi ye na bibiyata aduk inda naje ,,,,miyasa bakada lura ne kai aganinka iyayenka zasu bari ka aureni bayan sun san ni d'iyar mayya ce ".
"nidai nace ina sonki ba iyayena ba sannan nine zan zauna dake ba wasu ba,,, mi ye nayi miki kika tsaneni ko ganina bak'ya sonyi inzo wurinki? Ina sonki sosai babu wanda ya isa ya rabani dake Gwamma ni koda kece mayyar ba mahaifiyarki ba ina sonki a hakan ".Cewar Sule cikeda matuk'ar lallashi da dad'in baki.
Kalaman Sule sunyi matuk'ar tasiri a zuciyar Gwamma jikinta duk yayi mugun sanyi sosai,,, can ta nisa tace "bazaka tab'a gane matsalar tarayyarka dani sai nan gaba kad'an Sule,, ni nan da kake ganina rayuwata tana cikin matuk'ar hatsari akodayaushe akowane lokaci za'a iya kasheni! Amma ba komai na yarda da soyayyarka Sule na aminta ".
Sule yayi murmushi yace "nagode sosai da kika amshi soyayyata hannu bibbiyu ina sonki aduk yadda kike,,, sannan ai mutuwa dole ce kowa lokacinsa yake jira ".Ya fad'a shi bai gane inda maganar Gwamma ta dosa ba,, na cewa akwai lokacin da zaizo akasheta ba.
Gwamma tace "babu damuwa Sule duk yadda kace haka za'a yi saboda bazaka tab'a gane manufar maganata ba ".
Yace mata "aiko ni nake gane inda maganarki ya dosa saboda k'auna da soyayyar da nake miki daban yake a cikin zuciyata ".
"da gaske na kuwa gode da soyayyarka agareni Sule ".Tace tareda d'auko man shafi ta fara shafawa a jikinta tana shafawa Sule ya matso kusa gareta gab da gab sunajin numfashin juna yace "babu godiya a tsakaninmu masoyiyata,, ya amshi manshafin daga hannunta ya cigaba da shafa mata jikinta tareda tab'a duk wasu gab'ob'i da sassan jikinta 'har wani lumshe idanu takeyi akan dad'i sosai sannan b'ata tsintsar kanta cikin irin wannan yanayi ba ya bita da shafe shafe duk ya kashe mata jiki,,, ai dayake tsakanin baligi namiji da baliga mace idan suka keb'e a tsakaninsu na uku d'insu shed'an ne nan da nan yasa hannunsa ya jaye mata zane suka afkawa juna suna lashe lashe da kisses,, ina ganin sun sun fita cikin hayyacinsu naja k'afafuna nayi waje naja musu k'ofa.
Bayan wasu mintuna kad'an na jiyo ihu da kururuwar Gwamma tana kuka mai cike da zafi da rad'ad'in zama cikakkar mace,, hmmmm aikin gama ya gama Sule ya kwashi gararsa da jin d'adi.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Baba Labbo ne ya shigo aguje cikin gidansa da gudun bala'i duk jikinsa yayi faca faca da zawo da fitsari,,, yana shigowa ya d'unguje Inna Tani da sauri ya afka cikin d'akinsa garaffff garaffff garaffff ya rufe,, Inna Tani ta wintsilo k'asa bakinta ya fashe d'immmmm ta tashi tsaye tana share d'an jinin da ya fito daga cikin bakinta,,
Inna Tani ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai harda rik'e ciki akan dariya tace "maigida lafiyarka k'alau kuwa,, ka fito waje ka gayamin abinda ya faru dakai bayan kaje d'auko Gwamma,, ko acan ne aka baka tsoro ne? ".Tace tanata k'yalk'yalar dariya sosai........
0 comments:
Post a Comment