Shukrah ta gama shirin kwanciyarta ta hau gado ta kwanta bash ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa cki-cki a dole fushi take ya karasa kan gadon inda take kwance yana murmushi yace
" my wife fushi kike dani"
Ko uffan bata CE masa ta kirkiro wani guntun murmushi
"Am sorry kiyi hakuri "
"Uhmm..ba komai"
"Sure"
"Uhmm"
"Toh ki danyi murmushi mana"
Hakan kuwa ta sake masa murmushi yana dariya yace
"Daz my wife, tashi mu ci abinci toh"
"Na koshi"
"Pls mana " ya marairece hmmm bash akwai iya salo..lolx
Nan ta tashi ta xauna nama ne da exotic mai sanyi ya CE shi xai shiga wanka ta fara ci daga nan ya wuce dakinsa ya watsa ruwa tare da sa kayan baccinsa ya dawo ya sameta a inda ya barta.
Yana lallabata tana ci tana yauki๐๐ kamar bata so har Suka gama Suka kora da juice nasu se kuma Suka dawo falo ya kunna musu wani series film *walking death* suna kallo.
Shuairat kuwa 11pmta tashi daga bacci dama tun suna hira ita ta shige daki ta kwanta . falo ta nufa don yunwa take ji sai kuwa tayi saa foil pepa ta gani tana budewa taga nama a ciki nan ta hau ci se da ya isheta ta sha ruwa sannan ta koma dakinta xama tayi a carpet saboda bata jin bacci ta rasa me zatayi sai ta kunna data dinta watsap ta shiga mssgs Suka fara shigowa new number ta gani an tura mata hi"
Ta shiga ta ga num na online
"Helo!
Babu bata lokaci aka mata rply da
"Hw u"
"Fine alhamdulillh n u"
"Same"
"Eyya waye ne"
"New friend dinki ne princess maimah daga grp din gidan gyara "
"Aw Ayya am Ayshah"
"Nice meeting u"
"U too "
"Will like 2b ur kawa idan baxaki damu bah"
"Aww..really ! Naji dadi sosai u r welcm"
"Tnx ya gida yasu mum n ya yayanki da amaryarsa "
"Lfynsu lau..amma nayi fushi bakizo auren bruh bah"
"Eyya sory wllhi bana Adamawa ne daz y"
"Ok wane gari kike"
"Ina kd"
"Wow..daz gud"
"Ki ban labari toh" shuairat tayi murmushi tana jin dadin chat nasu da alama dai princess bata da girman kai sai tayi rply
"Me ya hana princess bacci ko dai tunanin prince ne๐
"๐๐laaahh...wa ya gaya miki? Nayi bacci fah ynxu na farka shiyasa"
"Aww...just like me wllhi"
"Baxaki ban labari ba koh"
"Toh princess wane irin labari kike so"
"Ur love story"
"Lolx...wllhi ban taba yin soyayya bah "
"Ar u serious Ayshah? Nima haka wllhi"
"Meyasa toh"
"Babu fah kawai ban taba bah kuma Wanda nake so din yayi aure"
"Allah sarki๐ฅ naki tausayin ki sorry"
"๐๐tnx"
"Amma ya akayi kika bari yayi aure ko kun bata ne?
"๐is a long story"
"Ok hard luck"
"Tnx" haka Suka cigaba da hira har 1 sannan Suka rabu kowacce ta kwanta .
Asuba ta gari first lady๐๐ผ๐๐ผ
Love u all๐๐๐
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*32*
By *Reefat yahya*
Da safe shukrah ta hada lafiyayyen brkfast ta ajiyewa maigidan nata ta chaba ado ckn atamfa ya'r holland tayi kyau sosai bangaren su mama ta je ta gaishesu suna falo sabida baba kullum se ya kalli news na safe ta ajiye musu brkfast sannan ta shige dakin shuairat bacci takeyi ckn kwanciyar hnkli shukrah ta kai mata duka nan kuwa ta bude ido tare da Jan tsaki ta koma baccinta wani dukan ta sake kai mata a baya aikuwa taja bargo ta gyara kwanciya
"Ke baxakije aiki bane"
Firgigit ta tashi xaune kwata2 ta manta yau xata koma bakin aikinta ban gida ta fada tayi wanka bayan ta fito shukrah bata nan ta shirya kanta ckn material tYi kyau sosai ta fito falo bayan sun gaisa da iyayen nata ta wuce bangaren shukrah.
Suna kari da mijinta ckn so da kulawa ta shigo tare da sallama ta gaida su sannan ta nemi wajen xama abinci ta deba iya cin ta tana ci suna hira bayN sun gama tare Suka fita da Yayan nata ya ajiyeta a wajen aikinsu.
************
Mr President tare da tawagarsa Suka sauko daga ckn jirgi ga jamaa nan birjik ana ta daukansu hotuna daga nan Suka shiga motocin da aka tanada musu Suka dau hanyar villa.
Bayan ya huta ya bada umarnin cewa bazai ga kowa ba se xuwa gobe saboda yana bukatar Hutu. Ckn gida ya wuce bangaren yaransa bodyguards na binsa a baya ga bash kuma a gefe ya iso dab da falon sauran sun tsaya amma banda bash , tare Suka shiga katafaren falon tare da sallama umaima tana kwance tana chat sultan kuma yana buga game . suna ganin mahaifin nasu Suka ruga a guje Suka shige jikinsa ya rungumesu gam gam gwanin tausayi yaran daga gani ansan cewa kadaici da maraici na addabarsu sun kai minti2 a rungume da juna sannan Suka sake shi yana murmushi yace
"My sultan ya kake"
"Lfy dad I miss u"
"I miss u more my sultan ya jikin sisy"
"Dad bansan meya sameta ba kullum se tayi kuka"
Mr President ya juya yana kallonta ta sunkuyar da kai bash ma ita yake kallo.a hnkli ya rike hannunta ya fara magana
"My baby me yake damunki"
"Ba komai dad"
"No tell me pls"
Sai kawai ta fashe da kuka nan ya jawota jikinsa ya fara rarrashinta dakyar ta bar kukan Suka xauna a kujera daya ya fara jansu da labari suna kwance a jikinsa.
Duk sanda umaima ta daga kai sai sun hada ido da bash , mr President ya kira iyayensa a waya ya hadasu sun Dade suna hira grandpa ya shaida musu yana nan tafe nan ba da dadewa bah haka Suka Dade a falon yana ta basu labarin China sosai ya cire mata radadin da take ji ya rage mata damuwanta , bash kuwa hnklinsa yayi nisa yana son ya gano matsalar umaima Amma ya kasa tuna komai.
Bayan tsawon lokaci mr President ya musu sallama ya tafi bash kuwa ya xauna yace magana xaiyi da umaima.
"Umaima ki gaya min me yake damunki"
"Babu"
"Umaima look at me"
Ta daga kanta idanunta Suka fada ckn nasa tayi saurin kawar da nata
"Umaima dama baki daukeni a bakin komai ba daz y kike boyemin damuwarki"
"Ba haka bane bash"
"No! Nagane matsayi na tnx"
Yana gama fadin haka ya tashi ya fara tafiya se kuma ta fara kuka cak! Ya tsaya ya juya yana kallonta haka nan sultan ma ita yake kallo "ya ilahi me yake damun yarinyar nan ne"
Ya taka yaxo ya sunguna a gabanta yace
"4Allah's sake umaima ya kike so a miki? Ki fadi matsalarki kin kasa fada kullum se kuka"
Tayi shiru batace komai bah
" pls ki daure ki gaya wa dad dinki tunda ni baxaki iya gayamin bah, kuma ki rage yawan tunani kar ya jawo miki prblm pls"
"Nagode" ta furta a hnkli daga nan bash ya tashi ya tafi tabi bayansa da kallo Allah Sarki bash baisan ma tana yi bah ita kanta takanyi mamakin irin son da takewa bash Wanda bata San yaushe ta fara shi bah haka nan bata San ranar dainawa bah.
Ita dai tayi imanin cewa tana sonshi Amma ko xata mutu ne baxata taba furta mishi bah, kuma bata tunanin cewa xata so wani mahaluki a duniya bayan basheer bah.maybe ita ma auren xumunci xaa mata cos ita kam basheer kawai take so a rayuwarta.
Allah Sarki umaima๐ฅ๐ฅ
Muje xuwa love u all ๐๐๐
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*33*
By *Reefat yahya*
Shuairat tana xaune a ofishinsu bodyguards Suka shigo Suka sanar da ita cewa mr President na bukatar ganinta ba tare da bata lokaci ba Suka fice tare.
Yana xaune a dakin hutawarsa ta shigo tare da sallama ya amsa ba tare da kalleta bah yana rike da wani Dan karamin cup black coffee ne a ciki yana sha a hnkli , waje ta samu ta xauna shiru sukayi babu Wanda yayi magana har tsawon minti 10 shuairat CE ta gaji da xaman nasu tace
"Mr president ka aika a kirani ina aiki n u din say anytin"
"My first lady yaushe xaki koyi gaisuwa ne? Ko baki iya respecting magabatanki"
Wani irin kunya ne ya lullubeta amma bata son ya gane hakan tayi gyaran murya tmkar Mara gaskiya tace
"Emm...uhmmm sorry about dat actually...
"Is ok! Neva mind , anyway na kira ne saboda ina son sanin hukuncin da kika yanke ko kuma in CE shawarar da kikayi batun maganar da mukayi som few weeks ago"
Ya tare numfashimta tare da kura mata ido
"Mr president I don't knw wat to say about it"
"Look Ayshah lokaci yana tafiya ya kamata ki fito fili ki gaya min cos my dad is on his way soon kuma xancen auren ne xe kawo shi"
Shiru sukayi kowanne da tunanin da yake yi ckn sanyin murya shuairat tace
"Mr president idan nace baxan aure ka bah wat will b d outcome"
Murmushi yayi yana girgiza kai yace
"Funny girl! Me a ciki ? Kawqi ki fito ki gayawa yan jarida da sauran jamaa cewa karya kikayi tun da can ba abunda yake tsakanin mu kinyi hakan ne....
" mr President ya xakayi da ...
Hannu ya daga mata yace
"Don't worry about me, kawai ki fito ki gaya musu gaskiyan idan xaa cireni akan mulkin ma fine I don't kia n xanyi tunani akan abunda xan sanar wa mahaifina so kada ki sa damuwa a ranki"
Ta rintse ido ya ilahi wannan wace irin jaraba CE? Shin ya xatayi? Ta amince da auren ko kuwa ? Toh idan ta fito ta fadi gskiya tabbas jamaa xasu mata kallon mutuniyar banxa daga ita har mr President yanxu me abun yi? Muryan mr President ne ya katse mata tunani
"Ayshah u don't have to worry about me"
"About u? Mr President dis is about us ya shafeni ka gane koh?
Murmushi yayi yace
"Nasan ma kina son auren kina wani nokewa pls feel free Ayshah"
Ta daga idanunta Suka fada ckn nasa ta murguda masa baki tare da cewa
"Meyasa xan so auren tsoho ? Kawai de kai kafi bukatar auren ba ni bah"
Tana gama fadin haka ta juya tabar masa falon yana murmushi shi kadai.
A waje Suka ci karo da umaima kallon kallo Suka tsaya yi daga karshe shuairat tasa kai xata wuce umaima ta fisge hannunta da karfi
"Ina xaki je munafukar karuwa kawai kin xo kin like wa mahaifina daga ganin arxiki koh"
Wani shuumin murmushi shuairat ta sakar mata tare da cewa
"Karuwancin ma iyawa ne wata idan tayi ta samu kudi wata idan tace xatayi duka xata sha"
Hannu umaima ta daga da niyyar Marin shuairat cas ta cafke hannun tana murmushi ta nunata da yatsa
" yarinya kinyi kadan wannan fuskar ba kowane mahaluki bane xe iya taba shi ba kingane koh, n don't 4get saura kankanin lokaci na xame miki uwa "
"Har abada Baxaki taba xama matsayin uwa a gareni bah"
Nan kuwa umaima ta fara hawayen jin an ambaci sunan uwa ta tuna da mahaifiyarta shuairat ta sake mata hannu ta juya xata tafi umaima ta sake Jan gyalenta da karfi ta juya suna fuskantar juna tace
"Ke umaima kike ko wa ki shiga taitayinki ni ba Saar yinki bane da mahaifinki nake dealing ba da ke ba , so ki kiyaye"
Bash ne ya hangosu ckn Sauri yaxo ya shiga tsakaninsu umaima ta fashe da kuka dai2 nan mr President ya fito don ganin meke faruwa shuairat ta juya ta kakkabe gyalen ta fara tafiya sai kuma ta juya ckn gadara tace
"Mr president I tink ya'r ka bata da tarbiya yana da kyau ka sanar da ita cewa aurenmu yana nan xuwa bada dadewa bah xan dawo gidan nan da xama she shul learn how to respect me "
Mr President da bash baki Suka bude suna kallon shuairat wacce ta wuce direct gun mota aka bude mata ta shiga umaima kuwa ta fashe da sabon kukan bakin ciki dad nata ya juya xai mata magana ta daga masa hannu alamar cewa bata bukatar jin komi daga garesa , wani dogon numfashi yaja sun hada ido da bash ya masa nuni da ido akan yaje ya mata magana hakan kuwa akayi umaima ta koma bangarenta bash yabi ta baya.
๐๐๐lov u all
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*34*
By *Reefat yahya*
Ta xauna dirshan a kasa wani irin bakin ciki take ji bash ne ya shigo yana mata murmushi ta kawar da fuskarta gefe handkerchief ya fara mika mata ta karba ta share hawayen sannan ya tashi ya bude fridge ya dauko mata ruwa mai sanyi nan ma batayi gardama ba ta karbi goran ta shanye tana sauke numfashi a hnkli nan kuwa taji hnklinta ya kwanta
"Umaima kiyi hakuri I know hw u feel"
"Hakurin me xanyi basheer? Nasan laifi na ne ni nafara nemanta da fada but...
Kuka ta fara yi bash ya cije lebe yana tunani halinsu iri daya da shuairat se saurin hawaye ga Neman magana koda yake mata ma dukkansu suna son kuka
"Bash baxan jure ganin dad da wata bah a matsayin matar da xai aura, it always reminds me of my mom"
"But umaima ya xakiyi? Allah ne ya kaddara hakan y not kiyi hakuri ki xuba musu ido"
"But na kasa bash! I can't baxan jure ganinsu bah wai ma dad har soyayya yake da wannan yarinyar?
"Umaima...
"No bash! Kasan me yake bata min rai? Tun ynxu fah idan ta fadi Abu dad baya tsallakewa idan sunyi aure fah?
"Umaima don't worry kiyi hakuri komi xai daidaita , nide ki rage yawan fushin da kike yi pls kuma ki daina disrespecting din dad naki pls"
"Ok "
"Pls promise me dat baxaki kara fushi da dad bah"
"Ok I promise"
"_gud girl daz y I like u"
Murmushi take ita kadai tasan abunda take ji, haka bash ya xauna yana debe mata kewa daga karshe ya mata sallama ya tafi.waya ta cire ta kira wata yar mamanta bayan sun gaisa take shaida mata cewa dad nasu xeyi aure haka anty kadi ta bata hakuri akan cewa ta kwantar da hnklinta dama dole wata ran xeyi aure ko ba ynxu ba.
***********
Shuairat CE tare da shukrah suna xaune suna hira a falon shukrah ya shigo tare da sallama shukrah ta karbe jakan hannunsa shuairat ma ta masa sannu da dawowa yace
"Baby I don't like wat u did today"
"Yaya ba laifina bane"
"I know but da kin kyaleta kawai"
"Haba yaya ya xaayi...
"Baby kada ki manta aure xakiyi ki koma a gidan bai dace Ku fara samun matsala tun ynxu bah"
"Yaya kasan baxan taba barinta ta mare ni ba koh"
"Yes na sani kuma ki rage nuna gadara da iko a gaban mr President he deserve som respect , duk da bansan limit na soyayyarku bah"
Shiru sukayi suna kallon kallo shukrah CE ta fito daga ckn daki tana kallon halin da suke ciki tace
"Lfy? Meke faruwa?
"Ba komai bash ya bata amsa sannan ya tashi tayi shigewarsa daki ya barsu ta juya gun shuairat tace
"Bestie menene?
"Ki tamabayi mijinki "
Nan itama ta fice ta koma bangarensu dakinta ta shiga ta fada gado ta rike kanta
"Ya Allah Kaine gata na ka xabamin mafi alheri tsakanina da mr President " ta lumshe idonta nan ta fara tuna fuskar mr President farine Sol dogo mai matsakaicin jiki yana da saje da dimple gashin kansa baki mai laushi yana da shanyanyun idanu farare gashi nan so cool bai iya fada bah baya son hayaniya duk abunda tayi se ido kawai yake xuba mata baxai furta komai bah
"He is too young 4his age"
ta furta a hnkli se kuma tayi murmushi .
Hmmmmm *Reefat* tace
"Shuairat ar u in love???
Hmmmm muje xuwa
๐๐๐๐
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*35*
By *Reefat yahya*
Alh Mohammed mahaifin mr President ne yake saukowa daga benen jirgi ga nan jamaa da dama ciki kuwa harda mr President ga yan jarida birjik se daukansa hotuna suke mr President ya karasa ya rungumi mahaifin nasa ckn farin ciki ya rike shi a kafada suna dariya Suka wuce filin motocin da aka tanada musu convoy na motocin Suka dau hanyar xuwa gidan mr President.
"Daddy nah I miss u so..much"
"I missed u too my boy"
Suna dariya bash ma yaso yin dariya Amma ya danne sarai mr President ya gane hakan se ya juya gun mahaifin nasa yace
"Daddy kaga wai kirani boy shine yake basu dariya"
Mahaifin nasa ya juya yana murmushi ya kalli bangaren da bash yake a gaban mota yace
"Yes! He is my boy cos shi kadai Allah ya bani kuma har ynxu ganin karamin yaro nake masa"
Murmushi sukayi haka Suka kasance har Suka karasa gida.
Umaima da sultan Suka fito da gudu Suka fada jikin kakan nasu yana dariyar jin dadi ya rungumesu sosai yaran na basa tausayi musamman idan ya tuna irin shakuwarsu da mahaifiyar tasu bayan sun shige katafaren falon mr President nan masu aiki Suka cika dinning da abinci kala2 ga yan xuwa barka da xuwa nan birjik bayan jamaa sun da tsagaita ne Suka wuce dinning table don cin abinci.
Mr President yana xaune kusa da mahaifinsa umaima kuwa tana gefen bangarensa na hagu sultan ne gefenta anyi serving dinsu kowa ya fara cin nasa, Alh Mohammed ne ya fara magana
"Son am so happy batun auren nan naka ka farantamin rai sosai"
Mr President ya fara tari daga nan ya dau ruwa yana kurba a hnkli sun hada ido da umaima ta kawar da fuska gefe.ya cigaba da cewa
"Dama naxo ne xancen auren naku , gobe xanje mu gana da iyayenta mu sa rana"
"Daddy y not...
"Boy bana son musu pls"
"Ok daddy Allah ya tabbatar da alkairi "
"Yawwa haka nake son ji.ynxu in banda abinka shkru nawa da rasuwar matarka amma ka kasa samun wata ko don yaran nan naka baka tunanin suna bukatar wacce xata debe musu kewa da rashin mahaifiyarsu?
Se ynxu umaima ta sa baki
"Granny mu bamu da matsala idan sultan ne kuwa yana da nannies masu kula dashi ba sai ya auro wata ya kawo bah"
"Oho! Ynxu nagane me yake hanaka aure wato wannn ja'irar ya'r taka ce bata son kayi aure koh? Toh karya kike umaima aure kam dole sai yayi kuma nan ba da dadewa bah"
"Daddy pls..
"Rufemin baki, baka da abunda xaka gaya min.Amma ka bani mamaki wallahi "
"Daddy plsss...
Fuu..umaima ta tashi ta bar falon ta tafi bangarenta Alh Mohammed ya juya yana kallon Dan nasa yace
"Boy! Irin tarbiyar yaranka kenan? Gaskiya nayi mamakin ganin haka a ckn gidanka son.kai kadai Allah ya bamu mun dauka son duniya mun dora a kanka amma hakan bai hanamu baka tarbiya mai kyau bah but y?
"Daddy am sorry wllhi umaima bata jin magana na ban....
"Quiet! Boy...kai ka haifeta ko ita ta haifo ka? Which one? Tell me!
"Daddy am sorry"
Mr President ya marairaice tmkar xeyi kuka nan kuwa mahaifin nasa yaji tausayinsa yasan sarai Suleiman be iya fada bah he is too cool shiyasa umaima take yin abunda ta ga dama can yace
"Ok son! Gobe insha Allah xan gana da mahaifin yarinyar xaa saka ranar aurenku nan ba da jimawa bah, aurenka na fari ni na xaba maka matar da ka aure n dis tym ka kawo wacce kake so dole xan jajirce don ganin na cika maka burinka.Allah ya bada xaman lfy insha Allah wannan yarinyar xata xame mana alkairi xata kawo farinciki a rayuwarka believe me son"
Yana magana yana kallonsa bayan ya gama ya tashi yayi shigewarsa dakin da ya saba sauka duk lokacin da ya kawo musu xiyara.sultan yabi bayan kakan nasa aka bar mr President shi kadai a xaune yasa abinci a gaba yana tuna kalaman mahaifinsa "shin da gaske Aysha xata kawo farinciki a rayuwarsa? How? Meyasa daddy ya fadi haka?
Hmmmmm..... Ya xata kaya tsakaninsu?
Muje xuwa
๐๐๐
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*36*
By *Reefat yahya*
Mr President ne xaune a falonsa yayi nisa ckn tunani bash ya shigo tare da sallama
"Mr president sir!
Firgigit ya motsa a hnkli yace
"Ehmm...basheer pls ina son ka kai daddy na gidansu Ayshah Bello"
Jim bash ya tsaya yayi shiru se kuma yace
"Ok sir!
Daga nan yayi waje wayarsa ya fitar yayi dialing din numbar mama ckn kankanin lokaci ta daga tare da sallama
"Mama ya gajiya"
"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh, dama mahaifin mr President ne zaizo Neman auren baby ynxu haka xamu taho tare shine nace bari na sanar daku"
"Tohh! Ikon Allah , dama shuairat ta daidaita da shugabankasa shine bata gaya mana bah?
"Mama kada ki sa damuwa a ranki kawai ki sanar da baba gamu nan xuwa yanxu"
Ya katse wayar a dai2 nan daddy ya fito yasha many an kaya se uban qamshi ke tashi bash ya fara soshe 2 kamar Mara gaskiya daga nan aka bude musu mota Suka dau hanyar kubuwa xuwa gidansu shuairat. Bash ya turawa matarsa text akan ta tanadi kayan motsa baki danginsu snacks da fruits se kuma lemuka masu sanyi ya sanar da ita gasu nan a hanya yana tare da manyan baki.
Baba da mama suna xaune a falo mamakin alamarin sukeyi domin basu taba tunanin cewa mr President xe auri ya'rsu bah suna nan xaune suka ji dirar motoci a kofar gidan bash ne ya sauka da sunan zeyi sallama don a basu ixinin shiga ya tura kofar gidan a hnkli yasa kai a ciki (basu San cewa gidansu bane lol) bayan kankanin lokaci ya fito ya shaidawa daddy ya fito nan Suka shiga har falon baba yana xaune shi kadai daga nan bash ya bar musu falon...
Bayan sun gaisa nan Suka fara hira tamkar sun Dade da sanin juna daddy ya shaidawa baba kan cewa shi Dan jahar Adamawa ne haka nan shima ya gaya masa shi Dan Adamawa ne sosai sunyi hira harda dariya tamkar sun saba da juna tun asali
Shukrah CE ta shigo tare da sallama ckn ntswa ta gabatar da kayan motsa baki bayan sun gaisa ta sa kai ta fice ta koma bangarenta bayan wani Dan lokaci mama ta fito Suka gaisa da daddy sannan ta koma ckn daki daga nan daddy ya gabatar da bukatarsa na Neman auren shuairat baba yayi shiru can kuma yace
"Alh da zaka bani lokaci zan...
"Haba Alh bello ai anzama daya, kuma yaran nan suna son juna tunda sun fito fili sun bayyana hakan.kuma shi yaron matarsa ta Dade da rasuwa munyi iya bakin kokarinmu ya kara aure amma Sam yaki, don haka ina rokonka ka taimaka ka bamu ya'rka tunda de sun daidaita suna kaunar juna"
"Alh Muhammad bawai zan hanaku bane, kasan shaanin yara"
"Haba Alh..Suleiman fah ba yaro mana shekarunsa 40 da doriya na tabbata xai rike ya'rka bisa gaskiya da amana , nidai burina ka amince mu sanya musu albarka kuma in son samu ne a daura auren nan da sati 2 masu xuwa"
"Ahhh..abun ma da wuri haka ne?
"Ehh mana..burina shine ka amince batun wani shiri koma menene bai taso bah ba se ansiya mata komai ba ni xanyi kayan daki da duk wani abunda zaa bukata na auren"
"Haba Alh Muhammad bazaayi haka bah"
"Alh bello bazaka gane farinciki da nake ciki bah, Suleiman shi kadai Allah ya bani a duniya burina shine naga ya tara min jikoki dayawa se kuma Allah ya kaddara matarsa ta haifi yara2 ta bar duniya.don haka nake son ayi wannan auren da wuri ko Allah zaisa da rabo a ciki"
Baba yayi shiru yana naxarin kalaman daddy
"Kayi shiru Alh bello, kada ka manta yanxu mun xama yan uwan juna fah " ya fada yana dariya baba yace
"Shikenan Allah ya tabbatar da alheri ya basu zuria ta gari masu albarka"
"Ameen yanzu naji magana! Nagode sosai ALh bello Allah yabar xumunci ya saka da alheri" nan ya xare bundir na yan dubu sabbi fil har bandur 3 ya ajiye a gaban baba
"Me wannan Alh Muhammad? Kaga abunda bana so kenan, ni ban nemi koda sisi ba daga gareku don Allah ka maida shi kuma auren nasu idan yazo bana son almubazzaranci a kimanta komi a yishi dai2 gwargwado nasan kuna da kudi amma ni bana son hakan"
"Alh Bello jahar mu daya da kai kasan al-adunmu na Adamawa idan anzo Neman aure da goro ake xuwa , nikuma ban siyeshi ba saboda ina marmarin xuwa don haka wannan kudin goron Neman aurene ba komai bah"
"Nasan da hakan Amma na yafe"
"Aa'a bazamuyi haka da kai bah alada CE dole sai anyi , batun almubazzaranci kuma insha Allah bazaayi bah na maka alkawarin hakan"
Baba ya xare bandir daya ya maida sauran yace
"Allah yayi albarka ya sanya alheri nagode"
"Sauran kudin fah Alh"
"No! Wannan ma yayi yawa kawai bana son gardama ne"
"Toh nagode sosai Alh bello se a fara shirin daurin aure nagode sosai"
Nan sukayi musabaha baba ya rakashi har bakin mota sukayi sallama driver ya ja a yayinda bash yake zaune a gefe Suka dau hanyar gidan mr President.
Hmmmmmm.muje xuwa
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*37*
By *Reefat yahya*
Shuairat tana xaune a ofishinsu ta buga uban tagumi wayarta CE ta hau ruri numban mama ta gani ckn mamaki ta daga sabida mama bata taba kiranta ba muddin tana wajen aiki
"Hello mamana"
"Baby kizo gida yanxu"
"Lfy dai koh?
"Kizo ina jiranki"
Ta kashe wayar tayi jugum se kuma ta tashi ta fara harhada takardunta bayan ta gama tayiwa Sarah sallama akan cewa ana nemanta a gida carab Suka hada ido da Mahmud yayi sauri kauda fuskarsa gefe taku biyu tayi ta karasa inda yake
"Mahmud ina son yin magana da kai"
"Sorry am busy"
"I knw but maganar is very important"
Ba gardama ya tashi Suka fita waje
"Mahmud wane laifi nayi to deserve dis?
"Bangane bah ! Wani Abu ne ya faru?
"Mahmud pls ka gaya min me namaka plss...
"Shuairat baki min komai bah"yana gama fadin haka ya juya ya koma ciki ya barta nan tsaye tsaki taja ckn jin haushin kanta wato ma har wani rigima yake mata mtswww...
Nan ta tare taxi ta kama hanyar gida.
Mama CE zaune a dakinta tayi shiru tana tunannin kalaman aminiyarta Hajiya mairo
"Amina ki godewa Allah da irin kyautar da ya baki ki kwantar da hankalinki , ai wannan shine arxiki na binka kana gudunsa idan ba haka ba waye xaiki amincewa da auren shugabankasa? Kawai ki nusar da shuairat ki gyarata sosai ki koya mata dabarun xama da miji ba wani batun ya tsufah ki manta da zancen shekaru ki tashi tsaye ki nemawa ya'rki hanyar da xatabi ta zauna da mijinta lfy wannan shine abunda ya dace kiyi tagumi ko tunani ba naki bane"....shuairat CE ta katse mata tunani ta shigo tare da sallama ta fada jikinta tana juyi
"Oh mama! Kin tsoratani I tot wani Abu ne ya sameki tank God u ar fine"
Murmushi mama tayi tace
"Lfy ta kalau na kiraki ne ina son muyi magana"
"Go ahead ina jinki"
"Dazun nan mahaifin shugabankasa ya bar nan, ya zo Neman aurenki"
Dumm...xuciyarta ta buga nan ta tashi xaune
"Waat? Neman aurena? Me baba yace masa?
"Me zai fada kuwa an saka ranan auren nan da...
"No! Mama it can't b nikam baxan auri tsoho bah"
"Aww really? Bazaki auri tsoho ba kika fito gaban dubban jamaa kika bayyana cewa kuna soyayya? Kiyi amfani da hankalinki shuairat ke fa kika amince masa ya turo iyayensa me kika maida mu?
"Haba..mama kinfa San komai akan alamarin nan na gaya miki yanda abun ya faru kuma wllhi bamu taba wani xancen soyayya dashi bah ..ni ..ni"
Se kuma ta fara kuka
Mama ta tabe baki tace
"Kanki ake ji yarinya da can wani ne ya turaki kika CE kuna kaunar junanku? Ko a wancan lokacin baki San shi tsoho bane se yanxu? Bazaki maidamu mutanen banza bah bari kiji gara ma ki saita kanki kisan abunda kikeyi"
Nan mama ta tashi ta bar mata dakin shuairat ta nemi hawayen ta rasa๐๐ da can ta dauka mama xata rarrasheta ne aikuwa ta tashi ta nufi bangaren shukrah a falo ta sameta tana buga game
"Yadai mutuniyar"
"Mtswww...wato kina xaune ckn kwanciyar hnkli baki damu da halin da nake ciki ba koh"
"Me ya faru bestie" shukrah ta fada a yayinda take ajiye wayar hannunta ta gyara xama
Shuairat ta tura baki tace
"Kina ji wai daddyn mr President yaxo neman aure nah"
"๐ณ๐ณkai ...dama shine yaxo gun baba dazun nan?
"Mstsww...ke ana serious kina wani mtsww
"Yi hakuri bestie dama kina soyayya da mr President ne baki taba gaya min bah"
"Allah na! Shukrah! Haba try to understand mana haaa da muna son juna xan damune ?๐๐
"Okkk...calmdown n tell me meyake faruwa"
Nan shuairat ta kwashe labarin kaf ta gaya mata murmushi shukrah tayi tace
"Trust me kuna son junanku just dat Baku fahimci hakan bane but wit tym...
"Hey hang it girl! Ar u kidding me? Ya zan fara soyayya da tsoho ne ..yurk! U know I can't "
"Babe baki gane ....
"Pls bestie stop it! Shi tsoho ne bai San me ake cewa love bah n shima ya gaya min bai taba yi bah"
"Tsoho? Ya kai 80 ne?
"Ahh..haba he is 40+"
"Hmmm bestie he is still young u can handle it, waima lemmi ask u salman khan na Indian film shekarunsa nawa?
"40+"
"Wat of sharukh khan?
"40+"
"Akshay kumar fah?
"๐๐๐ shima haka"
"Me zasu nunawa mr President? Kyau? Ilimi ko arziki? Hey girl wake up! Mata nawa suke neman mutanen da basu kai mr President bah? About 1000+ n duk fadin duniya babu macen da zata ki auren mr President but y bestie? Kiyi aiki da brain naki pls ke da kanki kika CE he is so cool..meyafi hakan toh namiji kyakkyawa ga ilimi ga hankali ga tausayi ga arixizi ga ga ...komai ya tara me laifinsa? N tell me ke din kintaba son wani namiji? Maza nawa Suka so ki Amma baki sauraresu bah kinga kenan Allah ne ya hadaku shi bai taba soyayya ba kema haka kiyi tunani akai shuairat u can do it u can handle it after all u ar a lady ni kaina ke kika koyamin wasu abubuwa da dama y not kiyi amfani da su? Ki zauna da kyau kiyi tunani"
Daga nan shukrah ta tashi ta shige kitchen ta bar shuairat da dogon tunani akan kalamanta...
Hmmmmm
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*38*
By *Reefat yahya*
Mr President tare da daddy da sultan suna cin abincin dare a dinning table na bangaren mr President umaima kuwa taki xuwa a dole wai tana fushi daddy ne ya fara magana
"Boy u ar lucky wallhi surukinka mutumin kirki after ol Dan Adamawa ne"
"๐ณ ..uhmmm ehh dad namanta ne ban gaya maka cewa shi Dan Adamawa ne ba "
Lallai shi da bai taba xuwa gidan surukan nasa bah ina zai San halayensu...
"Boy kana ji nah"
"Ehh..ina jinka daddy"
" idan na koma zanyi magana da momsin ka batun hada lefe xatayi magana da sakeena ya'r wanta wacce take business na kaya zaa hada komai a kawo daga nan sai a kai gidan nasu koh"
"Ok daddy nagode but da nace kudi zan bata ta siya da kanta"
"No! Mu zamu siya komai kuma babanta yace baya son almubazzaranci saboda haka komai dai2 gwargwado zaayi"
"Ok daddy nagode Allah ya kara tsawon rai "
"Ameen! Auren naku nan da 3weeks ne"
๐ณ๐ณwani tari ne yaxo masa wani bugun xuciya yaji...damm
"Boy ar u ok!
"Ehm..umm.am ok daddy am am fine"
Gub...gub haka xuciyarsa ya cigaba da bugawa innalillahi kawai yake maimaitawa can yaji muryan daddynsa na cewa
"Sultan tashi muje muyi hiranmu koh kasan gobe jirgin 7 zanbi insha Allah"
Daga nan Suka tafi aka barshi shi kadai nan ya fada duniyar tunani ....yanxu da gaske aure zaiyi? Ya zasu kaya da umaima? Ya zaman nasu zai kasance? Shuairat zata zauna lafiya ta rike masa sultan ? Anya xai iya kallonta a matsayin mata? Wace irin rayuwa zasu yi? Hmmm lallai yana da babban aiki a gabansa...haka dai ya cigaba da tunane tunanensa..
****************
Shuairat CE xaune a gaban dressing mirror tayi jugum tana tunani wai ynxu da gaske aure zatayi? Mr President xata aura? Ze iya bata romantic lyf da ta Dade tana mafarkin samu? Zai iya kallonta a matsayin matarsa? Zata iya zama da umaima da sultan? Ya rayuwarta zai kasance? Ya.....
Bude kofar dakin da akayi ne ya dawo da ita daga kogin tunanin da take mama CE rike da waya a hannunta ta mika mata
"Hajiya mairo xata miki magana"
"Ok" nan ta sa hannu ta karba ta kara a kunne tare da sallama
"Ina yini anti"
"Lfy my baby ya kike ya aiki"
"Lfy alhamdulillh"
"Baby nah magana xamuyi ta fahimtar juna"
"Ok anti ina jinki"
"Mama ta gaya min halin da kike ciki Amma ina son ki kwantar da hankalinki ki gane cewa aure nufi ne na Allah kuma matar mutum kabarinsa ki daure ki amince da zabin da Allah ya miki alkairi ne insha Allah, ki sake ranki ki cigaba da activities dinki kinji?
"Ok anti nagode"
"Ki kwantar da hankalinki munyi magana da yayanki zai sama miki ticket ki bi flight gobe kixo Kano gida kinji"
"Ok anti tnxx"
"Yawwa my baby takkia sai na ganki koh"
"Ok anti bye"daga nan ta mikawa mama wayar ta kashe ta juya suna fuskantar juna mama tace
"Ki shirya kayanki gobe jirgin safe zaki bi ki tafi Kano "
"Ok mama "
"Batun events kuma walimah kadai ya wadatar ko kuwa akwai program da zaki yi"
"Walima is ok "
"Toh shikenan ki fara shirya kayanki yanxu"
"Ok toh" daga nan mama ta bar dakin shuairat ta hada kayanata kala10 a travelling bag bayan ta gama se ta shiga watsap mssgs Suka shigo dama ta kwana2 bata shiga bah. Mssg din princess maimah ta gani
"Hi dear fren ya kike
"Fyn " ta mata reply tana online dat tym se ta tura
"Wia have u bin shiru 2days"
"Ina nan just busy ya gida n evrtin"
"Fine alhamdulillh kawai gt a little prblm wit dad ne"
"๐ณur dad? Haba y?
Nan ta gaya mata abunda ya hadasu shuairat tace
"Haba kawa ba kyau fushi da iyaye"
"Ok tanx xan kiyaye next tym"
murmushi princess tayi a dayan bangaren a xuciya tace she is just like her bro.haka Suka cigaba da chat nasu har na tsawon lokaci sannan sukayi sallama.
Ku biyoni....๐๐๐๐๐
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*39*
By *Reefat yahya*
A airport mr President yayi sallama da mahaifinsa yana rike da hannun sultan suna dagawa daddy hannu har sun juya xasu tafi daddy ya sake dawowa gun mr President yace
"Boy is gud kaje ka gaida surukinka"
"Ok daddy xan samu lokaci"
"No! Son xanso ace yau xaka je"
"Ok insha Allah zanje"
"Ok gud na tafi sai munyi waya"
"Safe trip a gaisheda momsi"
"Ok zata ji" daga nan mr President ya ja hannun sultan Suka shiga mota Suka kama hanyar gida.
Da yamma misalin karfe 4:30 mr President yasha manyan kaya se qamshin turare ke tashi an jera motoci bash na gidan gaba tare da driver a yayinda mr President ke xaune a gidan baya hannunsa rike da magazine yana karantawa , a kofar gidansu shuairat akayi parking na motocin dama can baba ya San da xuwan surukin nasa batare da bata lokaciba Suka shiga ckn gidan bodyguards Suka tsaya a waje bash na gaba mr President na biye dashi.baba na xaune a falo Suka shigo tare da sallama bayan sun gaisa an jerawa mr President kayan marmari iri2 Amma ko ruwa bai iya ya sha bah saboda kunyan baba yake ji, basuyi wani dogon hira bah shiru Suka yi tamkar babu kowa a falon chan baba ya daure yace
"Duk da naji cewa kana kaunar ya'ta amma don Allah ina rokonka ka riketa bisa gaskiya da amana bana son wani Abu ya sameta"
"Insha Allah baba na dau alkawarin kula da ita babu abunda zai taba ta "
"Nagode! Allah ya Baku zaman lafiya da zuria mai albarka"
"Ameen" mr President ya amsa ckn jin kunya daga nan mama ta fito Suka gaisa ta koma ciki ta barsu, haka nan sukayi sallama mr President ya tafi sannan bash ya shigo da bandir din kudade ya ajiyewa baba shi kuma se fada yakeyi wai akan me bash xe karbi kudin bai sauraresa ba yayi ficewarsa saboda ana jiransa a waje xasu koma gidan mr President.
*******************
Shuairat CE zaune a dakin da aka sauketa a can Kano ta ajiye kazar da ta sha hadin magunguna a gaba ta rasa ya xata fara cinsa gashi ta taba ta jishi ba dadi anti mairo CE ta shigo tare da sallama
"Lalala..baby har yanxu baki cinye bah? Gaskiya xamu bata dake"
ta tura baki tare da yatsina fuska tace
"Allah anti ba dadi bazan iya ci bah"
"Baby ki daure haka ki ci if not xamu bata oya ..now "
Haka tasa shuairat a gaba dole ta cinyeshi tass tana maida numfashi dakyar.bayan ta huta kadan mai gyaran jiki ta fara tata aikin haka Suka yini ranar gaba daya se gyarata ake yi har dare bata huta bah wani hadin tsimi aka bata dole ta shanye.
Misalin 9:00pm ta watsa ruwa tayi shirin bacci kenan ta kwanta a gado dama dakin ita kadai CE a ciki ta bude data mssgs na watsapp dinta Suka fara shigowa se kuma wayar ta fara ringing sabuwar num ne kuma special har ya kusan tsinkewa sannan ya daga ta kara a kunne tare da sallama
"Hey reporter ina kika je ? Wato baki xaman gida koh?
"Pls who is on d line?
"Baki ban amsa bah"
"Mr president?
"Baki xaman gida ina kike xuwa?
"Mr president ko kamanta cewa am a reporter so I have....
"Luk Ayshah daga yau nayi banning duk fitanki har xuwa ranar daurin auren"
"Aww..da gaske?
"Tambaya kike? Dont u have som respect?
"Umm..am sorry"
Shiru sukayi dukkansu biyu kowannensu ya rasa abun fada daga karshe ya kashe wayar.daga can bangarensa tunani yake meyasa ma ya kirata? Kuma idan tana fita ma meyasa zai damu? Daya bangaren xuciyarsa yace of coz matata tace dole na damu, no! I don't have too" shiii...ya sunkuyar da kai yana tunani ya kasa samun amsa ko daya.shuairat ma haka abun ya kasance mata ta kurawa wayar ido tana tunani daga karshe ta share maganar kawai ta shiga watsapp dinta Suka fara chatting da princess maimah da kuma shukrah.
Ku biyoni....
Love u all ๐๐๐
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*40*
BY *Reefat yahya*
Bayan sati daya aka kawo lefen shuairat mata biyu ne kacal Suka xo anyi musu kyakkyawar tarba an karbesu ckn mutunci akwati set 2 ne cike makil da kaya masu kyau Wanda bazan iya siffantasu ba sai dai masu karatu su kimanta da kansu๐ daga karshe sukayi sallama Suka tafi bayan an cikasu da snacks da drinks kala2.shukrah kam se santin kayan take xubawa aikuwa tayi snapping ta tura a instagram da watsapp cewa ga kayan lefen aminiyarta amma bata bayyana cewa mr President ne xai aureta. Shuairat ma ta yaba da kayan sunyi kyau ba karya , shirye shiryen biki ake Amma mr President ya hana duk wasu programs da zaayi ciki kuwa har fansan amarya yace bayaso sabida yasan yan gulma zasu cika wajen shuairat CE zatayi walima shikenan.
****************
"Umaima lfynki kuwa? Yarinya kin dau karan tsana kika dora akan mahaifinki bayan kinsan Allah ne ya hallata masa auren kin isa ki hana ne?
"Wllhi anti khady wannan cin amana ne yanxu shekaru nawa ne da rasuwar mom amma har ya manta da ita? Se kuma ta cigaba da kukanta anti khady ta sake baki tana kallonta sannan ta cigaba da cewa
"Nidai baxan goyi bayanki ba umaima wannan ai rashin gaskiya CE , Allah ya halasta masa auren mata 4 ke kice baki so yayi auren? So kike ya kare rayuwarsa haka?
"Anti kinga yarinyar karamace fah wllhi tun bata shigo ba ya daina kulamu kuma...
"Ki bude kunnuwanki kiji abunda zan gaya miki, ki tashi ki koma ki bawa mahaifinki hakuri ki rungumi kaddara ki xauna lafiya da matarsa Allah ne ya kaddara baki isa ki hana bah "
"Gaskiya nikam baxan iya bah, ynxu dama duk son da yakewa mom ya...
"Dakata umaima bari kiji labarin da baki taba ji bah, dad da mom dinku auren xumunci aka hadasu dad naku ba shi ya nemi auren mom naku bah biyayyace ta sa ya amince ya aurota har Suka xauna tsawon xaman da sukayi.dad dinku bai taba yin soyayya a rayuwarsa bah kuma....
"Wait..an..anti kina nufin duk xaman da sukayi babu soyayya a tsakaninsu?
"Bansani ba umaima Allah shine masani nidai nasan dad mutumin kirki ne yana da kara sosai har gobe baraa sami yaro mai biyayya irinsa bah a duk fadin danginmu"
Shiru umaima tayi tana tunani kanta ya kulle kwakwalwarta ya to she anti kady CE ta dafata a kafada tace
"Kiyi hakuri ya'ta nasan kina taya mom naki kishi but koda ace tana raye itama bata da ikon hana wannan auren kiyi hakuri ki shirya ki koma gun mahifinki"
"Zan koma amma ba yanxu bah, sai bayan bikin nasu "
"Shikenan xan kira dad na fada masa kada ya tada hankalinsa gun nemanki "
"Ok anti nagode"
Haka ta cigaba da xubda hawaye tana jin wani radadi a ckn xuciyarta.
*********
Shuairat CE a gaban dressing mirror tana kallon kanta tabbas ta canza ba kadan bah fatar jikinta se sheki yake ga gashin kanta da ya sha gyara se kuma dadaddan qamshin da yake tashi a jikinta murmushi tayi a yayinda ta cigaba da kallon fuskarta tana admiring din kanta lallai mr President yayi dace๐๐tunaninsa ne ya fado mata a rai fuskarsa ta hango , kyakkyawan karshene ita kanta tasan da hakan kuma yana da karamin ruwa idan bakasan shrkarunsa xaka CE Dan shekara 32 ne ta lumshe ido tana tuna farkon haduwarsu yana magana so cool yana da class sosai kuma yana da tausayi musamman idan ta tuna ranar da ya share mata hawaye lokacin da take kuka, shin zata iya soyayya dashi? Anya kuwa? Hmmmm ko kadan bata taba mafarkin cewa taxa auri babban mutum kamarsa bah sai kuma rayuwarta na baya ya fara dawo mata a kwakwalwa.....
Muje xuwa....
*Reefat*
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*41*
By *Reefat yahya*
*wacece shuairat*???
Alh Bello mamman hafaffen garin maiha ne na jahar Adamawa su hudu ne a gun iyayensu Ahmadu Salihu bello da kuma zainabu a can garin maiha aka haifesu duka amma shi bello ya koma garin mubi da xama gun wan mahaifinsa a can yayi primary da secondary sannan ya wuce jamia ta bayero Kano a can ya karanta bangaren education, bayan ya gama ya dawo gida a Yola yayi bautar kasa a wannan lokacin ne ya hadu da Fatima ya'r layinsu mahaifinta ne limamin unguwarsu a can karamar hukumar maiha ta jihar Adamawa.
Bayan ya gama bautar kasa akayi aurensu da Fatima shi kuma ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary na technical school a can mubi.Bello da Fatima suna son juna sosai kullum suna cike da begen juma haka Suka xauna ckn rufin asiri , sun share sama da shekara 6 Allah bai basu haihuwa bah amma duk da haka bello bai taba nuna damuwarsa bah, Fatima tayi2 ya kara aure yaki sauraranta har ta gaji don kanta ta daina kawo masa xancen.kwatsam Allah ya bata ciki sunyi murna sosai hKa Suka kasance ckn farin ciki har Allah yasa ckn ya cika wata9 da yan kwanaki Fatima ta haifi kyakkyawan danta fari tas babu inda ya bar fuskarta cki kuwa har hasken fata saboda Fatima fara CE sosai, ranar suna yaro yaci suna Basheer.
Haka Suka cigaba da rainonsa har ya girma yayi wayo aka sashi makarantar firamari har ya gama Allah be kara basu wani rabon bah , basheer ya gama primary ya shiga secondary har ya kai ss1 sannan Allah ya bawa Fatima wani ckn batun murna kam baa magana basheer duk yafi xumudi akan cikin kullum hirarsa be wuce xancen a haifa masa kanwa ya'r kyakkyawa.
Bayan wata9 ciff Fatima ta haifi kyakkyawar ya'rta wacce tayi kama da bello tamkar anyi kaki an tofar yarinyar baka CE Amma ba sosai bah tana da Dan hasken fatA , haka aka saka mata suna Aisha ana kiranta shuairat.
Shuairat ta tashi ckn gata gaba da baya koina sonta ake musamman yayanta basheer baya barin kowa ya taba ta, a wannan lokacin Alh bello yana koyarwa a jamiar federal university of technology Yola. Daga kan shuairat haihuwa ta tsaya musu cak da wannan lokacin ko bari Fatima bata sake yi bah, haka Suka rungumi yara biyun da da Allah ya basu.bash ya gama secondary dakyar ya yarda ya tafi jamia wai shi baya son ya tafi ya bar kanwarsa dakyar aka lallabashi ya tafi jamiar Ahmadu bello zaria bayan ya kammala ya dawo yayi bautar kasa sai kuma aka daukesa aiki da state security service , shekaru sun gabata Alh bello yayi retire ya koma gida yana hutawa se kuma dansa ya samu canjin aiki xuwa fadar shugabankasa a wannan lokacin ne shuairat take Jin karshe a federal polytechnic dake can mubi har ta samu ta kammala inda ta karanta bangaren mass communication...
Wannan kenan shine takaitaccen tarihin rayuwarta.
A hnkli ta ja wani gauron numfashi kamar a mafarki take ganin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwarta "ikon Allah kenan"
ta furta a hankali ynxu matsalarta shine ya xata fara nunawa mr President so? Anya zai kulata kuwa? Wane irin zama zatayi da umaima? Tabbas tana da aiki a gaba idan batayi da gaske ba xata fuskanci matsala a gidan wayarta ta hau ruri sunan shukrah ta gani nan ta daga
"Matar Yayan"
"Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida"
"Lallai sai dai idan baa kashe din bah , ya kike ya gidan"
"Lfy lau yaushe zaki dawo"
"Umm..kinyi missing dina ne "
"Bani kadai ba harda angon mah"
"Bangane bah"
"Ehh..mana wai dama baki gaya mishi zakiyi tafiya bane?
"Y? Meyasa xan gaya masa?
"Hmm...dazu ya tura bodyguards wai yana son ganinki"
"Uhmm..yayi kyau"
"Munafuka kina so kina nokewa"
"Ehh..sai akayi yaya"
"Nidai ki dawo da wuri kan a buga mana news paper cewa mr President yana Kano"
"Wannan kuma maysalrku "
"Uhmmm..in tayi tsami ma ji"
"Babu abunda zakuji"
"Se anjima toh "
"Ok bye sai na kira "
"Ok takkia"
Tare Suka katse wayar shuairat tayi jugum tana tunani lfy mr President yake Neman ganinta?
Oho!
Nima nace oho! Ku biyoni
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*42*
By *Reefat yahya*
A bangaren mr President kuwa yana xaune a dakinsa yayi shiru yana tunani anya zasu zauna lfy da yarinyar nan? Ta fiye takama da nuna isa, ysushe sukayi waya amma taki ta sanar dashi cewa tayi tafiya?.mtsww meyasa ya nemi ganinta ma? Lols Reefat tace cos u miss her preety face" wayarsa ya cire yana son kiranta sau 2 yana dialing sai kuma ya fasa a karo na ukun ne yayi ta maza ya kira har ya kusan katsewa sannan ta daya ckn sanyin murya tace
"Ur excellency"
Haka kurum yaji dadin sunan da tayi adressin nasa da shi wani murmushi ne ya subuce a fuskarsa
"My stubborn first lady! Ya kike"
Murmushi tayi da jin sunan stubborn ta gane abunda yake nufi
"Am sorry ur excellency nayi tafiya ba tare da na sanar maka ba"
"Is ok! Zaki iya yin duk abinda kike so as of now b4 ki shigo gidana"
"Don't worry a gidanka ma abunda naga dama zanyi cos am d first lady"
maganar ya sashi dariya sosai yace
"Well..we shall c! Anyway dama ina son ganinki ne saboda ina son sanin programs naki da kuma amount da kike bukata"
"Ur excellency ka kwantar da hankalinka bana bukatar komi iyayena xasu min idan ma akwai bukatar hakan"
"Nasan da haka but is my duty ..anyway zan tura miki 2mil kiyi shopping idan akwai bai isa ba let me know"
"๐ณ2wat? No! No! Me zanyi da 2milion? Walima CE zanyi fah n olredy iyayena sun riga sun tanada komi na walimar so no need pls"
"Bana son jayayya sai anjima"
Nan ya katse waya shuairat ta kurawa wayar ido tana nanatawa 2mil ? Hmmm lallai ma ai wannan almubazzaranci ne.mr president kuwa ya tsinci kansa ckn wani farin ciki haka kawai yana murmushi yana lumshe ido daga nan ya kira bash ya shaida masa yana bukatar account number din shuairat.
***********\\
Jirgin yamma Suka bi sai gasu nan a Abj shuairat ta kara haske fatar jikinta ta murje tayi kyau sosai duk Wanda ya daga ido ya kalleta dole ya kara kallonta a karo na biyu. Bash ne yazo daukansu ita da anti mairo da diyarta Sadiya wacce take saar shuairat daga nan Suka kama hanyar gida .
Gidansu a cike yake makil da jamaa babu masaka tsinke saboda saura 4days daurin auren shuairat , bangaren shukrah ta shiga a yayinda haj mairo ta wuce gun aminiyar tata ga danginsu nan birjik mutanen Adamawa kyawawa dasu falon shukrah a cike makil da jamaa ta sa kai tare da sallama shewa Suka fara yi wata ya'r kawun shuairat me suna Ummi ta tashi Suka rungumi juna da shuairat se ihu suke sai ga shukrah ma ta fito ta Ruga a guje Suka rungumi juna ta kalli shuairat tayi wani guntun dariya tace
"Gaskiya ne mata a gidan Dr Suleiman Muhammad first ladyn Nigeria da kanta, kasar ta kusa ta dawo hannunmu sai yanda muka juya ta"
Aikuwa sauran yan matan Suka fara shewa
"Aiyuriri ...mata a gidan shugabankasa Allah ya bar mana ke"
Dakyar shuairat ta samu ta shige dakin yayanta ita da shukrah da Ummi da kuma Sadiya.shukrah ta kawo musu lafiyayyen abinci ita da Sadiya Suka ci sukayi nak sannan aka baje a gado aka fara xuba shukrah tace
"Bestie kawaye nawa kika zaba"
"Ummi da Sadiya da maimuna ya'r anti luba sai kuma Hafsat mubi"
"Ok! Dama mr President ne ya turo yayanki yazo ya tambaya kuma tym din layinki baya shiga""
"Ok na kashe wayar ne tym da zamu tashi"
" mr President fah yana ji dake yarinya ! Kinga kalan zirga -zirgan da yan gidansa suke?
"Allah ko"
"Ehh ..mana wllhi ki rike tsohon nan da kyau don na lura yana sonki sosai"
Gaba daya Suka kwace da dariya Ummi tace
"Wa ya gaya muku shi tsoho ne? He is just 40 somtin ne fah "
Sadiya tace
"Gaskiya kam! Kimanta da zancen wani tsoho ki fito ki nuna masa so zalla Ku zauna lfy ya fiye miki wllhi, kuma kinga yana da wata shu'umar ya' mai shgen girman kai kada ki kuskura ki bari ta rainaki wllhi"
Shuairat tayi murmushi tace
"_ina nake da lokacin ta"
Mama CE tayi sallama a bakin kofar dakin shuairat ta ruga a guje ta bude ta fada a jikinta tana dariya
"Mama na I miss u"
"Ba wani u miss me bayan kinzo kinyi zamanki a nan baki nemi gani na bah"
"Wllhi Bahaka bane! Naga mutane sunyi yawa ne"
Daga nan tabi bayan Maman nata sukayi ckn gida.
Love u my fans๐๐
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*43*
By *Reefat yahya*
Karfe 4pm harabar city garden ya cika makil da manyan motoci kala2 idan ka duba can ciki bangaren da akayi decoration kuwa xaka bude baki ne galala tsantsan haduwar filin nikam xan iya cewa tunda nake ban taba ganin hadadden decoration irin haka ba๐๐๐ dama ansan city garden waje ne mai kyau kuma babu hayaniya se kukan tsuntsaye ga kuma flowers masu kyaun gaske anyi arranging kujeru kowane table kujeru hudu na zagaye dashi an rufesu da kyalle masu kyau colors daban2 wato multi color kenan haka nan bangaren da amarya zata zauna tare da kawayenta ma multi color ne abun de sai Wanda ya gani.
Idan ka duba kujerun sun cika da jamaa dangin mr President yan uwan marigayiya matarsa zainab dangin Maman shuairat da kuma dangin babanta ko ina dai manyan mata ne ansha ado na kece raini ga yan Adamawa kyawawa sun kara haska wajen both dangin ango da na amarya duka fulanin Adamawa ne idan kaga mummuna dai yan ganyan sodi ne๐๐ a dayan bangaren kuwa invited guest ne ga matan ~gidan gyara~ ~Nisaul jannah~ ~professional writters~ ~Hausa novel grp~ ~dangin juna~ ~qasaitattun mata~ da dai sauransu.idan ka duba wani bangaren kuwa *adda bena*CE da *m jabo* *pherty* *Maman shakur* *khaleesat haidar* *miemie bee* *Ummi Aysha* da sauran online writers nima a can na xauna ina watsa rubutu na. Yan gidan TV radio da news papers duk sun hallara ana daukan live a kowane tashar TV idan ka kunna xaa hasko maka walimar Aysha (shuairat) bello matar mr President๐, nayi rubutu har na gaji sai na taba miemie nace "amarya baxata zo bane" ta watsa min harara tace "tsiyata dake kenan rashin hakuri"๐ daga nan naja bakina nayi shuru wani dadaddan qamshi ne ya buga hanci na ina daga kai na hango shuairat tare da tawagarta๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Mutuwar xaune nayi *halamcy* CE ta saka hannu ta tare min baki na Wanda saura kiris ya fada kasa...hmmm kawai na ajiye Biro na nace baxan iya siffanta irin wannan kyawun bah sai Ku jira *afrah* idan ta gama da jumaiya se ta siffanta muku kyaun da shuairat tayi.๐๐๐Amarya da kawayenta Suka sauna a filin da aka tanada musu nan kuwa yan jarida Suka fara daukansu hoto wal...wal hasken kamera kawai nake gani sai kuma aka bude taro da adua nan malama Maryam ta fara gabatar da waazi akan hakkin aure da rayuwar aure a musulunci.haka aka cigaba da taron masu video recording nayi masu daukan hoto nayi ga yan jarida iri2 ga reportrs din tambari magazine ga JF ma sun tura Mahmud Wanda kansa me kallon kasa yana jin wani radadi har ckn ransa .Karfe 6pm aka raba souvenirs iri2 har da kayan makeups a ciki abinci kuwa dama table by table aka raba daga nan akayi adua sannan kowa ya fara shirin komawa gida a yayinda wasu sukaje daukan pix tare da amarya dakyar ta samu hanya wannan ma don bodyguards ne.
๐๐๐
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*44*
By *Reefat yahya*
Yau aka daura auren Ayshat bello maiha tare da Alh Suleiman Muhammad mayo ( PhD) akan sadaki naira 100k jamaa da dama Suka halarci daurin auren manyan kusocin gwamnati tare da manyan sarakuna ta kasashe daban-daban ga mutane dai talaka da masu arziki , yan jarida suna nan birjik an daura aure lfy aka watse daga nan villa Suka wuce akayi hadadden reception kowa ya ci ya sha sannan aka watse ango de furkarsa na dauke da murmushi .
A can bangaren amarya kuwa ta sha kwalliya ckn wata hadaddiyar shadda masu kyau da tsada ga gwalagwalai carkaf a kunne da wuyarta tayi kyau tmkar a saceta a gudu tana zaune a bangaren shukrah tare da kawayenta.ta buga wani uban tagumi shukrah CE ta shugo tare da sallama
"Amarya bakya laifi ko kin kashe sultan lolz"
"Hmmm...lallai mah rufa min asiri kan a jiki"
"Tashi muje an tura camera man yazo ana ta daukar hotuna"
"Kuje Ku dauka nikam na gaji"
"Haba ranki shi Dade, kinsan gobe war haka fah ganinki sai da ticket ki tashi muje muyi last card pls"
"Mttsww...me wani na cewa last card sai kace mutuwa zanyi"
Su Ummi suna mata dariya haka Suka fita akayi ta daukan hotuna da yan uwa da abokan arziki.
Tun Karfe 5 shuairat ta shiga wanka tare da anti mairo har magrib suna ckn bayi shiru kawai kake ji na so zuwa in gano me ya sukeyi acan Amma ba dama haka na hakura na zuba ido.by 7 Suka fito amarya sai qamshi take tmkar anyi barin turare dakin mama Suka wuce ta saka wasu atamfa ya'r super mai uban kyau da tsada batayi wani makeup bah dakin babanta aka kaita ya mata nasiha sosai tAna kuka Suka koma dakin mama a can aka kawo mata dafaffiyar kaza ta sha hadi sosai dole ta cinyeshi Tass sabida anti mairo ta sata a gaba, mama CE ta shigo haj mairo tace
"Mutuniyar idan akwai abunda zaki gaya mata kiyi sauri cos ance by 8 zamu wuce da ita gidan mijin nata"
Mama ta sunkuyar da kai tace "ba komi duk abunda ya dace ki sanar da ita " daga nan ta tashi ta tafi haj mairo ta kara fesheta da turare sannan Suka wuce bangaren yayanta baya nan Mr president ya kirashi haka suka zauna ckn shiri by8 Suka ji tsayuwar motoci . duk yanda shuairat taso ganin mamanta don suyi sallama abun ya gagara firr mama taki fitowa haka Suka hakura yan raka amarya Suka shirya Suka fito shuairat kam se kuka take anti mairo na bata hakuri daga nan akayi mota da ita.
Motocine masu kyau se sheki sukeyi gasu nan birjik sai Wanda ka zaba daga nan Suka dau hanyar villa.
Bayan sun iso gidan aka wuce wani dankareren building upstairs ne mai kyau gaskiya bazan bata lokacina ina zayyana muku tsaruwar ginin bah kawai de kunsan gdn shugabankasa kam๐๐karshen kyawu kenan. Yan rakiyar amarya sun zaga building din ko ina suna ta yabawa , an nuna musu dakunan daga nan anti mairo ta sallami kowa ya rage daga ita sai kawayen amarya da wata yar mama se kuma kanwar baban su shuairat. Dangin ango sun shigo wasu mata kyawawa su 6 Suka shigo musu maraba tare da ajiye musu abinci mai rai da lfy sannan Suka tafi. Kawayenta daki daban aka ware musu ita amaryar kuwa da anti mairo zata kwana, bayan sunyi shirin kwanciya Karfe 11pm anti mairo ta ajiye shuairat ta fara mata nasiha..
"Baby kiyi hkri bansan ko kina son mijinki koma yaya ne ki daure ki fara sonshi ki koyawa kanki yanda zaki so shi , haka nan shima ki koya masa sonki ki dasa sonki a ckn zuciyarsa Ku zauna lfy.yi nayi bari na bari kuyi hkri da juna wannan shine zaman aure, bauta ne ya kawoki ba wani Abu ba aljannarki kika zo nema kiyi kokari ki kasance mai faranta ran mijinki.ki zauna lfy da kowa ki mutunta kowa nashi ki daraja iyayensa ki girmamasu ki kula da dukiyarsa da ya'yansa, fada da umaima ba naki bane ki kame girmanki kada raini ya shiga tsakaninku...haka dai anti mairo ta cigaba da mata nasiha masu ratsa jiki daga karshe Suka kwanta.
๐๐๐lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*45*
By *Reefat yahya*
Da misalin Karfe 9 na safe masu aiki sun gama gyara komai na gidan sai qamshin air freshener ke tashi an jera abinci kala-kala a dinning table.building din dakuna 4 a sama da babban falo a tsakiya da dinning table mai kujeru6 sai kuma dakuna 3 a kasa da kitchen da kuma dinning mai kujeru 10 ga wani tangamemen falo da kujeru duma2 har set 4 kai kayan more rayuwa dai an narkasu a wanga falon.
Shuairat tayi wanka tayi ado ckn wani uban leshi Wanda zai kai 100k golden n lemon green da milk color ta saka yan kunnen gold mai tsadan gaske tayi kyau sosai tana tsaye a gaban dressing mirror tana kallon kanta yanda ta chanza tayi kyau sosai, anti mairo ta shigo dakin itama ckn uban kwalliyarta tana murmushi tace
"Wow my baby is looking gorgeous kinyi kyau sosai I wish Mr president zai ganki yanzun nan"
"Tnx anti" ta fada tana murmushi anti mairo ta rike hannunta Suka bar dakin sai kuma ga sauran yan uwan nata sun fito kowacce ckn ado na alfarma tare da kawayenta anti mairo na gaba tana rike da hannun shuairat Suka fito sai zuba gaisuwa ake musu wani Dan building Suka nufa me karen kyau .
Sun shigo tare da sallama wani makeken falo ne a cike makil da jamaa mata zalla gasu nan birjik kowacce tasha ado tana ji da kanta ckn faraa aka karbesu daga nan aka fara gaisuwa.
Bayan kowa ya nitsu anti mairo ta fara magana
"Ga ya'rmu nan mun kawo muku sai Ku riketa da amana idan tayi abunda ba dai2 bah a nusar da ita ko kuma a sanar damu saboda karama ce , Allah ya basu zaman lfy da zuria dayyiba"
Gaba daya falon aka amsa da ameen .sai ynxu na lura da wata dattijuwa mai kyaun gaske kamarsu daya da Mr president tunda aka shigo da shuairat se murmushi take a hnkli ta fara magana
"Insha Allahu zamu riketa hannu2 Allah ya basu zaman lfy da ya'ya nagari"
"Ameen" aka sake amsawa daga nan aka kai shuairat kusa da wannan matar Suka gaisa ta rike hannun shuairat cike da so tace "ya'ta Allah ya miki albarka kiyi hkri nasan zaku zauna lfy insha Allah "
Bayan wani lokaci kowacce tana Dan tufa albarkacin bakinta tare da musu fatan alheri daga nan aka fara daukansu hotuna sai kuma kyaututtukan da shuairat ta samu na ban mamaki wato turamen zani ne da lesuna sai kuma kdade mai dumbin yawa kai sunga abun arzki kam daga karshe Suka koma bangaren ta.kowa yana yabawa dangin Mr president da irin karamcin su.
Wani bodyguard ne ya shigo ya sanar dasu cewa Mr president na son ganin shuairat tayi shiru bata CE komai bah anti mairo CE ta jawota xuwa daki ta kara fesa mata turarurruka iri2 sannan ta kara powder da lipstick tace mata
"Saura kije kina wani nokewa , feel free mijinki ne"
Murmushi kawai shuairat tayi tana mamaki halaye irin na anti mairo daga nan ta sauka zuwa kasa inda bodyguard din yake jiranta daga nan Suka wuce ckn mota ya kaita bangaren Mr president.
Sau daya ta taba zuwa amma yau taga komai ya canza mata an sake fenti da furniture's da komi a bakin kofa bodyguard din ya tsaya ta karasa.
Bata sameshi a falon farko bah don haka ta wuce personal falonsa ta shigo tare da sallama yana zaune ckn manyan kaya yayi kyau sosai ko don ta kwana2 bata ganshi bane oho ya amsa ba tare da ya daga fuskarsa bah yana danna waya da alama wani yake son kira ta nemi waje ta zauna suna fuskantar juna. Shiru sukayi sai kuma ta tuna cewa ynxu itace kasa dashi nan kuwa a hnkli ta furta
"Ina kwana ur xcelency"
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata duk da cewa baya kallonta sannan ya amsa ckn wani salon ji da kai
"My first lady kin tashi lfy"
"Lfy alhamdulillh"
"Hw was ur nite ya bakunta"
"Lfy kalau"
"Daz grt, dama na kiraki ne ina son jin nawa zaa sallami frenz naki"
Shiru kake ji ta rasa me zata gaya masa yaji shirun yayi yawa don haka ya daga ido ๐ณ๐ณ๐ณ masha Allah haka ya furta a ckn zuciyarsa dama yarinyar nan haka take da kyau? Wow..she luks soo...btiful" carab Suka hada ido a dai dai lokacinda shuairat ta daga kanta , kowannensu yayi saurin dauke kai zuciyoyinsu ne ke harbawa.Mr president ya daure yace
"Kinyi shiru"
"Uhmm...gskiya nima bansani bah just give dem...
"No first lady! I hate dat word "bansani bah" ki gayamin pls"
Nan ma tayi shiru sai kuma ta tashi ya bita da ido har ta kai bakin kofa yace
"Ina zakije kuma muna magana"
"Uhm...zanje gun anti mairo ne"
"Zakije ki tambayeta nawa ya dace ?
Murmushi yayi yana tunani shi kadai cewa lallai akwai yaranta a tattare da ita
"Ok dawo ki zauna tunda baki sani bah lemmi tink on my own" ba gardama ta koma ta zauna yana danna waya can ya kara a kunne yace
"Ka tura sakon da na baka jiya ?
Ok yes ka hada duka ka basu a ckn gida "
Daga nan ya kashe wayar ya maida kallonsa gareta sun kurawa juna ido can shuairat ta kauda fuskarta yana Murmushi sannan ya fara magana
"Aysha ynxu idan aka baki mukamin first lady haka zaki dinga yi?
Ta daga kai ckn rashin fahimta yace
"Yes! Wat I min is dai komi sai kin tambaya ? Bazakiyi on ur own bah?
Ta zumbura baki tace
"Ni...ni nace a bani first lady ne dama"
A hnkli ya taka xuwa gabanta ya sunguna idanunsa a kanta suna fuskntar juna shuairat ta sunkuyar da kai tana wasa da warwaronta yasa hannu ya daga habarta Suka kurawa juna ido yace
" ke matata CE dole zaki koyi yanda zaki gudanar da wasu harkokin on ur own , u have to fight Aysha"
Bash ne tare da wani bodyguard Suka shigo tare da sallama ganin halin da Suka tarar da ogan nasu a ciki ne yasa Suka bar wajen shuairat kuwa kunyane ya kamata haka nan Mr president ma nan da nan ya tashi ya koma kujerar da yake da ya zauna ya dannawa bash kira a waya Suka shigo Suka sanar dashi cewa yayi baki daga England nan ya tashi Suka fita tare shuairat kuwa bodyguard Suka rakata ta koma bangaren ta.
๐๐๐๐๐ผ๐lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*46*
By *Reefat yahya*
Ta shigo bangarenta kawayenta suna mata tsiya Hafsat tace
"Ohhh shuairat an kasa hakuri a jira mu koma mana"
Ummi tayi dariya tace
"Gane min hanya dai da ana nokewa wai tsoho zaa aura ba zancen love gashi nan tun baaje ko ina bah an fara lumewa"
Suka fashe da dariya Suka shewa anti mairo ta shigo tana dariya tace
"Rabu dasu baby nah love kam kowa ma yana yi sai Wanda bai samu bah , Ku kuwa Ku tashi Ku tattara mu bar musu gida ynxun nan"
Suna dariya se kuma Suka hau godiya abun arzikin da Mr president ya aiko musu kowacce an bata kaya lace super da kuma Holland se kudi 120k shuairat kam mamaki ne karara a fuskarta sai kuma ta share zancen haka nan su haj mairo ma an basu kudade Masu yawa daga nan ta sake Jan kunnen shuairat akan zaman da zatayi a gidan tare da koya mata wasu dabarun sarrafa miji Wanda ba sai na fada bah๐ nan sukayi sallama shuairat ta fara hawaye haj mairo tace kul..karki bata kwalliyanki daga nan motoci Suka kwace su sai gida aka bar amarya daga ita sai halayenta sai kuma masu aiki.
Sama ta haura sai ynxu ta samu damar karyawa tea ta hada sannan ta Debi chips kadan da kwai ta zauna ta cinye tas sannan ta dawo falo ta kunna TV MBC ta kama tana kallon film din "triple X" yan uwan Mr president ne Suka shigo sun Dan taba hira daga nan Suka shaida mata cewa yau zasu wuce Adamawa wasu kuma Kano wasu kd da kuma Lagos, cin-cin doughnut da cake ta diba musu da turarurruka masu yawa ta basu suna godiya Suka tafi. Haka masu aikin Suka shigo Suka gabatar da Kansu nan ma ta kawo musu abubuwa iri2 suna yaba mata Suka koma bakin aikinsu.
A can bangaren Mr president kuwa wasu turawa ne Suka zo tayashi murnan auren da yayi maza 3 da mata 2 dukkansu manyan mutane ne masu fada a ji a can kasar England daga fadar sarauniya Suka zo don haka Suka nemi ganin amaryar tasa Mr president ya daga waya bayan ya Dan fita daga dakin da aka sauke bakin nasa layin shuairat ya kira ringing 2 ta daga
"Hello ur xcelency"
Wani yarr...yaji a jikinsa dakyar ya saita kansa yace
"Ki shirya baki nayi kuma turawa ne suna son ganinki"
"Eyya...Mr president y not su bari xuwa dare Allah na gaji ynxu bacci zanyi"
Tayi maganan ne ckn wani salon shagwaba murmushi yayi shi kadai yasan ma'anar yace
"Ok sorry ki huta zuwa daren sai ki shirya koh"
"Ok tnk u my dear"
Nan ta kashe wayar ya tsaya Jim...tmkar mai tuna wani Abu sai kuma ya nanata kalamanta na karshe "tnk u my dear" nan ya sake yin murmushi haka nan tun jiya yake jin kansa ckn wani nishadi daga nan ya koma gun bakin nasa ya basu hakuri cewa amaryar tasa tana tare da baki sai zuwa dare zasu gan ta haka Suka cigaba da hirarsu.
Bash da john suna zaune a waje John ya juya ya kalli bash yace
"Aboki Mr president fah ya fada tarkon son yarinyar nan ba kadan bah"
"Me ka gani john?
"Haba ...kana ganin yanda muka samesu dazun"
"Hmmm...next tym zamu hana kowa zuwa bangaren Mr president sai da izininsa cos yanzu yana da iyali bai dace ana shiga anyhw bah"
"Yes haka zamu yi"
Daga nan sukayi shiru shi kansa bash yana mamakin kalan soyayyar kanwar tasa da Mr president hmmm...mata kenan zasu maida tsoho yaro.
Shuairat kuwa tana zaune a falo har bacci yayi awon gaba da ita se bayan azahar ta farka tayi sallah sannan ta fada wanka, wani material pitch color ta saka dinkin buba da zani ta saka danyar gwal mai kyau ta fesa turare se qamshi ke tashi. Dinning ta wuce masu aiki suna tsaye a gefe aka zuba mata rice n chicken ta fara ci a hnkli tmkar bata so sai wani yauki take. wata mata ta shigo tare da wani Dan yaro nan kuwa ta gane sultan ne nan ta sake fuska tana faraa sun karasa falon ta musu tayin abinci matar ta jawo kujera ta zauna shuairat ta rike hannun yaron tace
"Boy zo mu ci tare" ba musu sultan ya karasa gunta ta daurashi a kafa nan ta fara bashi a baki suna ci suna hira masu aiki kam se yaba halayenta suke nan da nan anty khady ma taji son shuairat ya shige ta don ba haka tayi tsammanin ganinta bah ta dauka shuairat irin matan nan ne masu girman kai da wulakanta mutane.sunyi hira sosai bayan anty khady ta damka mata amanar sultan nan kuwa ta karba ckn jin dadi Suka rabu akan anti kadi xata koma yau.
Haka shuairat ta kasance tare da sultan tana biye masa duk abunda yake so shi zatayi sunyi game sunyi kallo sunyi karatu haka Suka kasance har lokacin sallan la'asar nan ma tare sukayi sallar shuairat ta masa wanka ta canza masa kaya sannan Suka tafi bangaren momsi( Maman Mr president )
Love u alll๐๐
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ๐NI DA SHUGABAN KASA๐
*47*
By *Reefat yahya*
Sun shigo falon tana tare da wasu mata su 2 nan shuairat ta gaishe su sannan ta zauna a gefe momsi kuwa wani irin dadi taji don anty khady ta shaida mata komai fuskarta dauke da murmushi ta fara Jan shuairat da hira tana tambayarta ko ta taba zuwan mayo belwa can Adamawa haka dai Suka cigaba da hira shuairat ta sake kadan suna hira sultan kuwa yana makale da ita, aka kawo musu fruits da drinks dakyar shuairat ta dau apple kwaya1 tana ci wannan ma saida momsi ta bata rai ne ta nuna mata cewa ta dauka nan gidan su ne ta daina jin kunya ta sake jikinta nan ne shuairat take tmbayar ina umaima aikuwa momsi ta zayyana mata daga biri har wutsiya sannan ta Dora da nasiha kan cewa tayi hkri da halayen da zata fuskanta gun umaimA haka dai Suka cigaba da hira har magrib sannan ta koma bangaren ta tare da sultan , bayan sunyi magrib da isha ta dibawa sultan abinci yaci ya koshi ta kunna masa cartoon yana kallo har yayi bacci nan ta daukesa ta kaisa dakin barcinta daga nan ta fada wanka.tana fitowa ta tsara wani uban kwalliya sannan ta fito da wani hadaddiyar dinner gown silver da duwatsu a jiki sai shinning suke ta sanya rigar mai dogon hannu pencil hand ya dame hannunta haka nan rigar dai-dai da jikinta ta saka wasu English diamond mai uban kyau ta daura wani red net daurin step har 6 tayi kyau sosai ta saka takalmin Vinci red color ta rike clutch purse din shima red ga red lipstick tayi kyau sosai woow....ta fesa turaren laylatul sahr da musk- almudhakkr se kuma far away , bleu feeling, diable bleue, to nyt , mekako Miami, Cuba , touch me da kuma esabella Curie.☺☺☺ turare 10...hmmmm qamshi kam baa magana ita kanta tasan ta hadu sosai.wayar intercom na dakin ne ya fara ruri ta daga wata mai aiki CE take sanar da ita cewa Mr president ya turo mota yana bukatar ganinta nan ta ajiye wayar ta kurawa fyskarta ido a ckn mirror tace
"Wow...yarinya kinyi kyau but hakan ya dace ta fita ne ko ta yafa gyale? Ahhh....turawa ne bata son su mata kallon bakauyiya don haka red net din ta dauko wani ta yafa sannan ta daurashi ta baya tayi kyau sosai๐๐๐๐.
A hnkli take takawa har ta fito falon ba kowa duk masu aikin sun koma bangaren su sai masu gadi a waje ta Tarar da bodyguard din ๐ณ๐ณ๐ณgaba daya Suka zuba mata ido dakyar ya saita kansa ya bude mata gidan baya ta shige daga nan ya ja motar .
Bangaren saukan baki sukayi parking ya bude mata kofa ta fito tana takun kasaita ta hadu da yayanta yana fitowa murmushi ta sakar masa sannan ta wuce ya tsaya galala yana kallonta har ta bace masa da gani yana tsaye yana mamaki shi kadai. Suna zaune a dinning area da alama ita ake jira Mr president ne yake fuskantar kofa tana shigowa ya kasa dauke idonsa a kanta tmkar a mafarki haka ya ganta kurrr ya ajiye ido ya kasa motsi tana murmushi ta karasa kusa dashi ta mika masa hannu nan ya tashi yana rike da hannunta gaba dayawa turawan sun shagala da kallonta basu taba ganin bakin fata kyakkyawa irin shuairat bah.Mr President ne ya katse musu tunani ta hanyar cewa
"Pls meet my wife mrs Suleiman"
Murmushi shuairat ta sakan musu sannan tace
"Hello everyone" tare da mikawa matan hannu sun gaisa ckn faraa sannan Mr president ya jawo kujera kusa da nasa nan ta zauna tare da cewa
"Tnk u Darling"
Ckn wani tsiga tana fari da ido Mr president kam se kallonta yake tmkar wata sabuwar hallita nan shuairat ta fara musu barka da xuwa tare da basu hakurin rashin xuwanta akan lokaci, haka nan ta sace zukatansu hira sosai sukeyi ckn harshen turanci Mr president in banda murmushi babu abunda yake shuairat ta bashi mamaki sosai nan da nan Suka fito da wayoyinsu aka fara daukan selfie an dauketa tare da Mr president ma sunyi kyau sosai nan aka fara turawa a instagram da Facebook ana taya Mr president murna. Daga karshe Suka gabatar da kyaututtukansu diamonds golds da dalolin amurka shuairat de tasha kyaututtuka da dama har wajen 12 sannan kowannensu ya koma masaukin sa shuairat ta tashi zata tafi Mr president ya rike hannunta sai kuma ya rungumeta gam a jiki, mutuwar tsaye tayi ta kasa motsawa Sun share minti 3 ckn wannan hali dai2 nan john ya shigo don kulle kofa aikuwa a 360 yabar bangaren ya tsaya a waje ya rike kai yana maida numfashi . Mr president ya motsa bakinsa a hnkli yace
"Allah ya miki albarka nagode sosai ki fitar dani kunya tnx much Allah ya biyaki"
"Amee..men" dakyar ta amsa daga nan ya sake ta yace
"
"Muje ki kwanta dare yayi"
Nan ya rike hannunta Suka fita gidan shiru sai securities ke kaiwa da komowa sunata kallon Mr president hannunsa tsarke ckn na matarsa suna taku a hnkli farinwata da hasken fitillun gidan sun haska koina , haka Suka cigaba da tafiya har xuwa bangaren shuairat aka bude musu kofa a tuaninta nan zai dakata da rakiyar se kuma taga ya biyota har dakin bacci ya bude kofar ga mamakinsa sultan ya gani kwance yana sharar baccinsa ya juya Suka hada ido tayi murmushi nan ya sake mata hannu ya koma kusa da sultan ya shafa kansa tare da tofa masa aduoi daga nan ya tashi yace
"Nagode sosai gud nite"
"Nite" ta fada a hnkli daga nan ya sa kai ya tafi tare da rufe musu kofar yana tafiya yana murmushi shi kadai yasan abunda yake ji.
0 comments:
Post a Comment