Wata duniya daban Suka fada..dakyar shuairat ta xame jikinta ta koma gefe ta kwanta idanunta a rufe mr president kam ko kwakwaran motsi ya kasa yi sun share 10mins a haka sannan ya jawota jikinsa a hnkli ya rada mata
" let's sleep"
Haka ya rungumeta gam a jikinsa akan rug carpet din Suka kwanta ranan har bacci yayi gaba dasu.
Da safe bayan sungama brkfst mr president ya tafi office tana xaune a falo wayarta ya fara ringing anti mairo ce , ta daga ta kara a kunne
"My only anty"
"Ke ki kira wadannan securities naku su bani ixinin shigowa tun daxu muna bakin gate kamar masu shigan aljannah se wulakanta mu ake"
Dariyane ya kubce mata sannan tace
"Sorry anty gani nan fitowa"
Daga nan ta xaro mayafi tayi waje ana gaisheta tana amsawa direct wajen adana motocin da take fita dasu ta wuce nan kuwa aka bude mata ta shiga ta shaida musu inda xasu je wato babban gate na shiga gidan.
Anty mairo tare da shukrah ta hangosu suna tsaye ta fito da faraa ta karasa ta rungumesu sannan Suka dugunzuma xuwa mota basu tsaya ko ina ba sai can bangaren ta har ckn bedroom Suka shige , shuairat tana rike da waleed dan shukrah tana masa wasa.masu aiki Suka jera musu abinci da fruits da drinks kala2* bayan sun gaisa anty mairo tace
"Baby naga gidan da mr president ya ginawa iyayenki gskiya gidan ya hadu Allah ya kara budi ya Baku xaman lfy, gdkiya mijinki mutumin kirki ne ki kara godewa ubangiji da ya hadaku"
Murmushi take tana jin dadin kalaman anti mairo, shukrah ta harareta tace
"Munafuka da kince baki son tsoho fah, gashi ynxu kin fada tarkon sonsa"
"Kai shukrah ..ni nace miki ina sonsa ne?
"Ahaf..ga xahiri ! Daga yabonsa kawai kin hau murmushi babu gaira ba dalili..yarinya kibar munafurci idanunki ma sun bayyana karara kin dulmiya ckn kogin sonsa"
Gaba daya Suka fashe ta dariya anti mairo tace
"Yawwa..nikam ba wannan bah, wai ina lbrin haihuwa ne har ynxu shiru"
Shuairat ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da hannun waleed
"Ah toh..gara dai kimata magana anti don gskiya ina xargin cewa dakyar in akwai abunda ya shiga tsakaninsu"
Shukrah ta fada tana hararar shuairat aikuwa anti mairo kamar jira take ta hau masifa
"Anya lfynki kuwa bby? Kinsan nauyin dake kanki kuwa? Ko angaya miki aure wasa ne...toh wllhi ki kiyayeni idan ba hakaba xan saba miki "
"Kiyi hkri anti Amma..
"Amma me? Rufemin baki wawiyar yarinya kawai, dame ya rage ki? Toh bari kiji wllhi samun nmji irinsu mr president sai antona a wannan xamanin namu.wani ma yana da kudin kina gani baxaki samu ba bare iyayenki, Amma bawan Allhn nan yanata hidima da danginki kaff babu Wanda ya bari, nidai ki farka daga baccin da kike kuma kiji tsoron Allah.
"Anti shima fa bai taba nemana bah" ta fada tana tura baki
Sallallami ne anti mairo ta fara yi sannan tace
"So kike yace miki ki zo mu sadu?
Shukrah da shuairat sun fashe da dariya sosai maganar ya basu dariya
"Aww..dariya na baki koh? Ki cigaba da rashin hnklin naki..wai ke ba na mace bane? Baki San yanda zaki ja raayin namji bah"
Haka dai anti mairo ta cire kunya ta wayar da kan shuairat sosai ta koya mata wasu abubuwa da dama , sun yini tare har yamma sannan Suka kira bash ya ajiyesu a gida.mr president bai shigo ba sai 11pm dakinsa ya wuce yayi wanka ya fito ya ci abinci har ya gama baiji motsinta bah dakinta ya shiga tare da sallama tana kwance a gado ckn wasu shu'uman kayan bacci , a hnkli ya karasa ya xauna kusa da ita ckn yanda da Jan hnkli tace
"Wlcm my man"
"Tnx my lady lfy yau baki xauna falo ba "
"Sorry kaji ni shiru koh..kaina kemin ciwo shine na dawo na kwanta"
Hannu yakai ya taba kan "eyya..sory gashi kai din baiyi wani zafi bah"
"Ehh..nasha magani ai"
"Ok..sorry"
"Tnx"
"Baraa tayani hira bane ko ciwon kan xe rabamu"
Tayi fari da ido tace
"Babu mai rabamu sai Allah"
"Hakane? "Ehh..ko kana shakka ne"
Murmushi ya sakar mata sannan ya gyara kwanciyarsa ya jawota a jiki ta kwantar da kanta a hnkli ta fara magana
"Mr president am so..sory nasan kana da juriya har ka xauna tsawon 1yr + baka taba Neman hakkinka ba duk da nasan cewa kana bukatar hakan, don Allah ka yafemin duk laifinda na aikata am sorry from....
"Shhhhh....Aysha ke nake so ba jikin ki bah, kuma na yafe miki. Idan har kina tare dani bana bukatar komai ok!
Ta daga kanta Suka hada ido yana murmushi yace
"Yes! Am ok..don't worry about me"
Wani tausayinsa ne ya kamata ta rungumeshi sosai tace
"I love u so much...Allah yabar min kai har abada , kuma daga yau ni taka ce sai yanda kayi dani am all urs"
Kankameta yayi a jikinsa yana jin wani irin shauki nan Suka fara kissing din juna daga nan kuma Suka fada wata duniyar..ya rabata da kayan jikinta sannan yasa hannu a switch ya kashe wuta, wani salon romance ne shuairat tayi amfani dashi ta birkita kwakwalwar mr president tmkar bai taba sanin wata mace a duniya bah gaba daya ya fita hayyacinsa sai sambatu yake ..........
Hmmm muje xuwa
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*61*
By *Reefat yahya*
Mr president ma ba tayan baya bane gun Iya sarrafa mace hmmm...wadan nan masoyan sun Lula sararin samaniya😜😜 sun Dade suna romancing juna kafin ya shigeta gaba daya basa ckn hayyacinsu, shuairat taji jiki kam ba laifi suna ta Abu daya har 3 kafin Suka sagaita nan kuwa ya kankameta a jikinsa sosai sai hawaye yakeyi duk da xafin da take ji bai hanata jin tausayin mijin nata bah a hnkli itama ta rungumesa bayan hnklinsa ya dawo jikinsa cak! Ya dagata xuwa toilet shi da kansa ya mata wanka sannan ya hada mata ruwan xafi yace ta xauna a ciki babu gardama ta xauna duk da radadin da takeji hakan nan ta hakura ta cigaba da xama a ckn shikuwa ya koma dakin ya cire bedsheet da Suka bata ya bude wardrobe ya fitar da wani ya shinfida sannan ya dawo ya sameta tana wankan tsarki daga nan ya dauketa ya shinfideta a gado ya rufa mata bargo sannan ya dawo yayi wanka . nafila yake yana kuka yana godewa ubangiji da irin ni'imomin da ya basa a rayuwa , shuairat kuwa tuni bacci yayi gaba da ita.
Da asuba ya tasheta ya taimaka mata tayi sallah sannan ta koma bacci.
11am ta bude ido ganin anti mairo tayi a gafen gado tana jera kwanukan abinci ckn mamaki ta tashi
"Anti ..
"Ah..Ya'r albrka har kin tashi ne, muje kiyi wanka kixo kici abinci koh"
Ba gardama ta tashi dakyar take Iya tfya anti mairo CE ta taimaka mata tayi wanka sannan ta hada mata ruwan xafi Wanda aka tafasa shi da magarya da bagaruwa tace ta xauna a cki, haka ta xauna kamar xatayi kuka bayan ta gama ta fito ta shirya ckn doguwar Riga lipgloss da powder kawai ta shafa sannan ta xauna cin abinci.farfesun kifi ne yasha hadi da kuma soyayyar dankalin Hausa sai kuma soyayyen kwai, tana ci mr president ya kira wayarta ta daga yana tmbayarta ya jiki.
Haka yinin ranar gaba daya anti mairo ce ke kula da ita, ko falo bata je bah mr president kuwa bayan kowane awa 1 sai ya kira yana aiki amma hnklinsa na gun shuairat. Kwana 2 anti mairo tayi tana jinyarta ta warke sumul kamar ba ita ba, daga nan ta shirya ta koma bayan tasha kyaututtuka gun mr president.
10:30pm tana kwance tana chatting a watsap ita da princess maimah tana korafin son ganin pix nata haka nan itama dukkansu basu taba saka pix nasu a dp ba sai na cartoons ko na couples shuairat tace nikam nafi son muhadu face-face ne"
"Allah koh..tohh ynxu haka ina Abj kefa?
"Uhmm...nima haka toh yaushe zaki zo gidan mu"
"A..ah ke zaki fara xuwa gidan mu"
"Naki wayon"
"Toh shikenan na yarda zanxo jibi, xan kiraki"
"Ok toh..ina jira"
"Let's sleep bacci nake ji"
"Ok nyt" daga nan shuairat ta kashe data dinta cos shukrah bata online. Wayarta ya fara ringing mr president ne bata daga bah ta tashi ta fada wanka bayan ta fito ta shirya ckn kayan baccinta masu daukan hnkli ta fesa turaruka da humra ta jefa chewing gum din orbit a bakinta sai qamshi yake sannan ta rike hijabinta ta nufi hnyar xuwa dakin oga..
Yana kwance ya kurawa ceiling ido baiji shigowarta ba ta jefar da hijabin a gefe ta fada a jikinsa wani dogon numfashi yaja sannan ya sauke idanunsa a kanta
"Ohh my lady kin tsoaratani"
"Haba..babba dakai"
"Ehh.mana banji shigowarki bah"
"Soryy..but tunanin me kake yi"
"Tunaninki nake" ya fada yana kallonta ta juya ido sannan ta xagaya hannayenta a bayN wuyansa tace
"Toh..ba gani bah"
"Yeah..am hpy to c u" ya hada lebensa da nata ya fara kissing a hnkli tun tana nokewa har ta fara maida martani haka Suka cigaba sai kuma ya fara shafa duk ilahirin jikinta a hnkli yake wasa da kirjinta nan ya turata ta fada kan gado ya susuce ganin yana Neman wuce gona da iri yasa shuairat ta fara kuka Amma ina..kamar kara tunxurasa take dakyar ta bude baki tace
"Plss...kasan ban gama warkewa ba fah..
A wahalce yace
"I knw baby ..don't wory a hnkli xanyi pls"
"No..."
Daga nan ta turashi gefe ta tashi ta xauna tana rawr jiki ya runtse ido ckn bacin rai ya juya yana kallonta kawar da kai gefe tayi ya tashi zai fita a hnkli tace
"Am sorry..
Tsaki yaja yayi ficewarsa xuwa falo ta rike kai innalillahi! Badai fushi yayi bah, Allah ka yafe ni"
Ckn axama tabi bayansa yana xaune da gorar ruwa a hnnunsa ya kurba sannan ya ajiye a hnkli ta karasa ta sunguna a gabansa
"Am sorry swt hrt ka yafemin pls"
"Tashi ki koma daki"
"Don Allah kayi hkri pls..
Kawar da fuskarsa gefe yayi nan ta tashi ta xauna a saman cinyoyinsa ta rungumesa tana kuka tana cewa
"Pls dad sultan ka yafemin kasan mala'iku xasu tsine min kuma ubangiji ma yana fushi dani pls am sorry"
Yana shafa kanta yace
"Baby baki jin magana ..toh na yafemiki shikenan?
"Da gaske?..tank u so..much😘
Ta manna masa peck a kumatu kai yarinyar nan xata haukatashi bakinta takai dai2* kunnensa tana yawo da harshenta ckn kunnen ..hmmm sauran kadan mr president ya suma baiyi wata2* ba ya dagata sai bedroom dinsa.acan Suka Lula duniyar masoya yaukam bata ji xafi sosai bah ita kanta tayi sambatun bare oga kam🤔hmmm..se a slow sau3 yayi sannan Suka kwanta manne da juna har bacci ya sace su.
10am mr president yana xaune a conference room suna meeting sai faman murmushi yake yana lumshe ido shi kadai yana tuna Daren jiya tabbas shuairat daban ce a ckn mata tana da abubuwa da dama Wanda ....
"Mr president sir!
Firgit ..ya juya yaga an xuba mishi ido wani senator ne yace
"Are u ok sir?
"Sure..am ok! Yeah...
Yana girgiza kai tmkar Mara gskiya sannan yayi gyaran murya yace
"So! Wat am I saying"
Gaba daya Suka juya suna kallon juna dakyar dayansu yace
"Sir! We are discussing about your trip to China"
"Waat? No..no.no pls...maybe mr Joshua will represent me"
"But sir! Its very important n u....
"I said am not going daz final" ya fada ckn daka tsawa daga nan ya tashi
Yana hushi sannan ya bar dakin taron kowa yana mamakin wannan al'amarin bash ne ya shigo a matsayin p.an sa ya basu hakuri kan cewa zai shawo kan al'amrin nan Suka sanar dashi lallai ya gaggauta yin hakan saboda muhimmancin tafiyar kuma gobe ne ya kamata su tafi don meeting na duniya gaba dayane zaayi a can kan tattalin arxiki don hada kasuwanci da kasar China.
Ku biyoni😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*62*
By *Reefat yahya*
Dakinsa ya wuce kai tsaye ya xauna kan rest chair ya cire hularsa ya ajiye a gefe ..sam bazai Iya yin nisa da shuairat ba koda na dare 1 tlkless of sati 1 no...yana runtse ido wani daci yake ji acan ckn makwakwaronsa .
Shuairat tana kwance a dakinta tana danna laptop wani file take saving na gidan marayu list din da aka turo mata jiya shine take shigarwa ..wayarta CE ta hau ruri yaya bash ne ta daga tare da sallama
"Baby ki fito falo ina jiranki"
Xumbur ta tashi ta saka hijabinta a hnkli take tfy har ta fito falon yana tsaye
"Zauna mana yaya"
"No..am ok! Dama magana nake so muyi"
"Ina jinka"
"Mr president ya shigo ne?
"Bangane bah...ba ya tafi office ba yacemin yana da meeting"
"Wato bby ina rokonki pls kisan hanyar da xaki bi ki tabbatar ya amince da wannan tafiyar"
"Wace tfy kuma?
"Ana nemansu a China ne n is very important shi kuma yace bazashi bah"
"Hmmm..mr president akwai rigima, don't wory I'll talk to him"
"Ynxu fah...pls ana meeting ne ya fita kuma dole suji daga garesa don asan shirin da xaayi na tafiyar"
"Ok..go n continue ynxu xaku ganshi insha Allah"
Murmushi yayi yace
"I trust mah sisy ..ina jiranki plss"
"Worry not my guy"
Daga nan ta wuce xuwa dakin mr president bash kuma ya juya ya tafi.ta shigo yana nan xaune shuairat Ya'r duniya tana ganinsa ta sakar masa Murmushi ta karasa ta xauna a kan cinyarsa tace
"Wane bako mukayi da tsakiyar rana haka, mr president yaukuma lfy dai ka shigo da wuri haka"
Harara ya jefa mata sannan yace
"Wato ma nikadai na damu dake koh...ina can na kasa tabka komai sai tunaninki nake amma ke kina nan hnkli kwance "
Ta langabe kai tace
"Eyya...Bahaka bane fah! Nima nayi missing dinka sosai" sai kuma ta hau kissing nasa saida ta tabbatar yazo hannu sannan ta sake shi tace
"Now..gayamin, me yasa ka dawo da wuri haka bayan kacemin kunada meeting?
Ya bata fuska sannan yace
"Wai tfy xamuyi xuwa China 4 1week"
"Allah sarki..Allah ya taimaka ya bada sa'ar abunda aka je nema"
"Haba..Aysha meyasa baki damu dani bane pls"
"My man..kaima kasan ina sonka kuma baxan so rabuwa da kai koda na min1 ne but ya xama dole ka kula da aikinka hkkin miliyoyin jamaa ne rataye a wuyarka kaga dole ka sauke hakkin ko?
Yayi shiru yana sauraron kalamanta tabbas abunda ta fada gskiyane muryarta ce ya katse masa tunani
"Ni taka CE har abada babu mai rabamu sai Allah, don haka ina son ka maida hnkli kan aikinka Allah ne ya baka shugabanci ba yinka bane so u have to tank him n handle everything ok"
Kai ya gyada mata nan ya rumgumeta sosai idanunsa a rufe yana rada mata a kunne
" tank u so much Ayshata Allah ya barmin ke tabbas ke macce ta kwarai nagode Allah ya miki albarka ya baki gidan aljannah nagode"
Murmushin jin dadi ne bayyane a fuskarta ta Dan sassauta rungumar tace
"Tashi kaje ana jiranka"
Yana murmushi ya tashi har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo ya manna mata peck a goshi yace
"Lov u"
"Lov u too" daga nan ya fita yana murmushi yana godewa Allah da ya hadashi da mace ta gari.
A can conference room sun fara surutun rashin ganin mr president kwatsam! Ya shigo fuskarsa dauke da murmushi sunata mamakin wannan al-amrin haka aka cigaba da meeting daga karshe aka zabi wadanda xasu raka mr president a yayinda mr Joshua kuwa xai xauna ya kula da harkokon kasar.
Ba karamin murna bash yayi ba da ganin mr president lallai kanwarsa tana ja😜😜.
Bayan sallar isha ta gama shirya kayan da mr president xeyi tfy dasu tana kwance a dakin ya fito daga wanka bayan ya gama shirinsa tsaf yana kallonta yana murmushi yace
"Baby I have somtin 4u"
"Aw..da gaske?
"Ehh.. Nan ya rike hannunta Suka fito falo wata Ya'r karamar kofa Suka bi ta bayan gidan Suka bullo suna tfy can sukaje garage inda yake ajiye motoci nan yaje kusa da wata katuwar mota an rufeshi da wani bakin kyalle a hnkli mr president yace ta rufe idonta bayan ya irga 3 ta bude guess wat😳😳h..........mmmmmmmmmmm....nikam saida na fadi a kasa shuairat ta bude ido a hnkli wata arniyar lemo CE fara Sol...yeah lemozin da kuke ji ko kuma kuna gani 😃😃 motar da take da komai a ciki ga kyau da tsada idan xaa kirga masu shi a duniya ma kalilan mutane ne basu da yawa☺☺.shuairat kam shiru tayi ta kasa cewa komai , daga nan ya sake nuna mata wata hadaddiyar Ferrari baka wuluk yana murmushi yace
"Dis my gift 4u na mallaka miki su duniya da lahiraa"
Hawayene Suka gangaro a kumatunta yayi saurin riketa yace
"No..pls bana son kuka"
Daga nan ya dagata cak! Suka koma ckn gida a dakinsa ya ajiyeta yace
"Cloz ur eyes again"
Ta rufe idonta alamar takardu taji a hannunta ta bude ido yana murmushi yace
"Ki duba ki gani"
Takardun filayene guda 5 😳😳 daya a mubi, yola, Lagos,2 a Abj .habawa ta rungumesa tana hawayen farin cki
"Tnk u soo..much Alllah ya biyaka nagode sosai"
Ita kam ta rasa wane irin godiya zatayi tace
"Bani da abunda xan biyaka dashi bansan da wane baki ko kalamai xan gode maka bah..nagode nagode I Lov u so much"
Ta kara shige jikinsa yana murmushi yace
"Bana bukatar komai ..fatana ki soni ki zauna dani ki haifamin yara masu kama dake"
Ckn jin kunya tace
"Ina sonka kuma har abada baxan barka komin tsanani komin wuya insha Allah, yara kuma Allah ya kawo masu albarka"
"Ameen"
Nima reefat nace
ameeeennnn.......
Ku biyoni😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*63*
By *Reefat yahya*
Sun dade suna rungume da juna sannan shuairat ta sakesa ta juya ta koma dakinta wani sabon wanka ta sake yi ta fito ta shafa mai ta gama shirinta ckn wata doguwar vest Iya cinya ko ina qamshin turare ne me tashi a jikinta ta dauko wayarta tana duba tym new mssg tagani tana budewa 😱😱😱 tsayuwa ya gagareta dakyar ta xauna ta kurawa wayar ido..alert ne daga bankin first bank kudi kimanin 500mil😜😜 tunda take a rayuwrta bata taba shiga irin yanayin da take cki bah gaba daya ta rikice nan kuwa ta tashi ta koma dakinsa yana kwance ya gama shirin bacci ta shigo ckn sanyin jiki hannu ya nuna mata alamar ta taho gunsa ta fada jknsa sai kuma ta fara kuka hnklinsa ya tashi ya fara rarrashinta dakyar ta daina kukan ta gaya masa batun alert da ta gani dariya sosai ya dinga yi yace
"Ki kwantar da hnklin ki dama akwai allowances na first lady shine na hada da kyautar da nayi niyya na bayar aka tura miki a account"
Godiya sosai tayi sannan Suka kwanta bacci a wannan Daren shuairat ta faranta masa sosai gaba daya tana Neman haukatashi da kalan soyayyarta ta kware sosai haka nan itama ta kasance ckn farin ciki.
Karfe 6:30am suna airport a ckn mota suke dakyar mr president ya banbareta a jikinsa shima yaji wani iri tmkar ya fasa tfyar ya cigaba da kwantar mata da hnkli sannan ya fita ya barta ckn motar taku 2 yayi ya sake dawowa ckn mota ya rungumeta gam a jiki yayi pecking nata a goshi yace
"I Lov u Aysha ki kular min da kanki da kuma ya'yana da dukiyata"
Daga nan ya juya ya tafi wani sabon kukane ya kubce mata driver ya shigo ya tada mota Suka dau hanyar gida.
A ckn jirgi sai faduwan gaba yakeyi idan ya tuna halinda ya bar shuairat a cki Allah sarki shuairat yarinya me hnkli haka dai mr president ya cigaba da tuna kyakkyawar fuskar matar tasa .
Shuairat kuwa yinin ranan sukuku tayi shi bata ckn walwala ko abinci ta kasa ci wayartace ta hau ruri princess maimah ce dakyar ta daga
"Kawata ya kke"
"Lfy princess ya gida"
"Lfy alhamdulillh dama ina son xuwa gidanku ne"
"Allah..gskiya naji dadi sosai "
"Kibani address dinki"
"Uhhmm..ynxu haka dai bana gidan mu naje villa ne"
😳"😃 really...kina ckn gidan ynxu haka?
"Ehh...
"Wane side?
"Ke dai idan kinxo bakin gate ki kirani"
"Ok toh"...
1hr leta..phn din shuairat ya fara ringing princess CE
"Kina ina"
"Na shigo ina ckn gidan"
"Ok kice a nuna miki bangaren mr president xan jiraki a bakin kofa"
Shuairat ta fito tana tsaye umaima taxo tayi shigewarta shuairat ta tabe baki tace kya jida shi"
Umaima CE ta sake fitowa wayarta ta xare tana danne2* can ta kara a kunne dai2* lokacin phn din shuairat ya fara ringing
"Hello princ...
Ckn mamaki da raxana Suka juya suna kallon juna
Wayar hannun umaima CE ta fadi a kasa ji kake kasssss.....
Screen yayi hali...
Hmmmmmm ...muje xuwa
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*64*
BY *Reefat yahya*
Sun dade suna kallon kallo sannan shuairat ta wuce ckn gida falo ta nufa ta xauna tana sauke numfashi har ynxu tana mamakn wannan al-amari wai umaima CE princess da suke chat a watsap...umaima ta shigo ckn mutuwr jiki ta xauna sunyi shiru can umaima ta daga kanta a hnkli tace
"Ynxu dama ke kanwar bash CE?
Murmushi shuairat tayi ta gyada kai alamar ehh..shiru Suka sake yi umaima kam mamakine karara a fuskarta sai kuma ta tuna irin abubuwan da takewa shuairat a matsayin matar mahaifinta nan taji wanni kunya ya kamata anya burinta na son auren bash xe cika? Ita kam bata San ta ina xata fara bah ta juya Suka hada ido shuairat kam se murmushi take umaima tana son bada hkri Amma girman kai ya hanata don haka ta tashi ta koma bangarenta.
Shukrah ce tazo mata ta Dan debe mata kewar rashin mjin nata a kusa haka Suka kasance tare da sultan shi kuma yaxo yana wasa da waleed don sultan akwai son yara shukrah ta kalli mutuniyar tata tayi Murmushi tace
"Ikon Allah ...an fada tarkon so hmmm!
"Nifa bana son gulma azo gidanka ana sa maka eyes"
Shuairat ta fada tana murguda baki
Shukrah ta kwashe da dariyan mugunta tana mai cewa
"Allah sarki wata tayi missing din mijinta...hmmm ko 1 day baiyi ba fah baby"
"Wai ke kwantar min da hnkli kika zo yi ko me?
"Oho..nidai ina son kiyi accepting cewa u r inlov daz ol"
"Ok fine shukrah.. Shuairat is inlov wit her gorgeous Darling husband, Alh Suleiman Mohammed shikenan!
Habawa me shukrah xatayi inba dry ba tayi mai isarta sannan Suka cigaba da yiwa juna shakiyanci.
Haka Suka kasance har dare suna xaune shukrah tana sanyawa waleed kaya saboda suna shirin komawa bash yana kan hanyar xuwa maidasu gida. Umaima ta shigo tare da sallama shuairat CE kawai ta amsa shukrah kam ko kallo bata isheta bah ..Sam! Ta tsani yarinyar umaima ta lura da rashin amsa sallamar da tayi ta tabe baki ta nemi kujera ta xauna can ta juya gun shuairat tace
"Amm...mom sultan nace bah..
Shuairat ta juya tana kallonta tana mmkin sabon sunan da ta kirata dashi *mom sultan* sabanin *ke* da ta saba
"Nace kunyi waya da dad ne layinsa baya shiga"
"Wllhi bamuyi bah..even me am worried Allah yasa dai lfy"
"Ameen...maybe yana busy ne"
Shuairat tace
"Ga matar bro dina Ku gaisa..
Shukrah ga umaima"
"Sannu koh..
"Yawwa ..kema sannunki"
Shukrah ta fada a takaice tana mai yatsina fuska umaima tabi ta da kallon mmki gaba daya shukrah ta canza don tana da pix din aurensu , tayi kiba ta kara hske tayi kyau sosai sai kace matar wani minister lallai bash ya Iya kiwo Amma ta rasa meyasa shukrah ke daure mata fuska haka ko meyasa oho! Ta tashi tayiwa shuairat saida safe abunda bata taba yi ba duk Iya tsawon xamansu a gidan a bakin kofa Suka cikaro da bash saura kadan su buge juna yayi saurin komawa da baya ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi
"Sorry...
Kamar hadin baki suka furta Kalmar tare murmushi Suka sakarwa juna dai2* nan shukrah ta hangosu wani kululun bkn ciki ne takeji tmkar ta shake wuyan umaima😳🙊shukrah akwai xafin kishi nan ta tashi ta karasa wajensu tace
"Bbn waleed tun dazu ina jiranka shine kazo ka tsaya bayan kasan munyi missing diinka sosai nida waleed"
Tana magana ckn wani salon makirci umaima kam xuba mata ido tayi tana kallon ikon Allah
"Ok sorry gani nan xuwa koh" ya fada kai tsaye shukrah ta juya tana hararin umaima ita kuma tayi wani guntun murmushi kamar cewa zanyi maganinki tayi saurin cewa
"Ohh..namanta zamuyi magana ynxu pls idan baxaka damu bah ka roki matarka ta bamu aron 10min pls"
"Sure..ba komai muje waje kiyi maganar"
Suka sakarwa juna harara shukrah ta koma ckn falo umaima kuwa tabi bayan bash Suka fita waje .
Shukrah ta koma kan sofa wani irin radadi take ji sai huci take kamar zakanya tace
"Hmmm...yarinyar nan xata ci ubanta wllhi xata San dani takeyi, hmmmmm..."
Abun yaso bawa shuairat dariya ta danne tace
"Wacce...
"Mtswww...wacece kuwa idan ba umaima ne ko me take da suna..
"Me tamiki best"
Da gangan shuairat tayi tmbayar shukrah sai karkada kafa take tace
"Dallah..karki rainan wayo, xaki CE baki lura da take taken bane..kina gani tana kashewa yayanku murya tana wani yanga...mtswww xata gane batada wayo..hmmm mijina take so koh? Tahmmm...xanyi maganinta"
"Chill..bestie kibi a hnkli kinga...
"Ke dakata malama! Nabi a hnkli? Lallai ma baby hmm...toh ba dai ni bah wllhi babu wata shegiyar da xata shiga tsakanina da mijina"
"Ah'ah shukrah abun bai kai hakaba Allah ya huci xuciyarki"
"Yakai harma ya wuce ..ahaf aikin banza Allah ya huci xuciyata? Daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa...mtsww"
😂😂😂😂
Shuairat kam taja bakinta tayi shiru daga nan ta dau sultan ta kaishi daki ta dawo remote ta dauka ta kunna TV tashar CCTV ta kama ta koma kan sofa ta gyara kwanciya shukrah kuwa tana cika tana batsewa.
Wani jirgi aka nuna ya fadi dayan bangaren jirgin duk ya kone ana fitoda gawarwaki shuairat ta gyara xama tana xare ido innalillahi take nanatawa sai kuma repotern ya fara magana ckn yaren China ana fassarawa da turanci
*yau da yamma ne akayi hadarin jirgin sama a kusa da garin Beijing ta kasar China an samu I'd card din matattun da kuma lambar jirgin Wanda ya nuna cewa jirgin ya fitone daga kasar Nigeria , bayan munyi bincike da hukumar kula da jiragen sama ta kasar Nigeria anshaida mana cewa jirgin yana dauke da jamaa da dama cki kuwa har da shugabankasa kasar.....* kunnuwanta basu karasa jin Kalmar karshe bah ta sake wata irin razananniyar kara ji kake timm! Ta fadi kasa bata ko motsi shukrah ta rude ta tashi tana taba jikinta Amma inaa...dai2* nan bash tare da umaima Suka shigo ckn tashin hnkli bash yana tmbayar lfy..shukrah se kuka take tana cewa
" mr president ne Allah yayi masa rasuwa ynxu muka...
Wani gigitaccen mari umaima ta ajiye mata idanunta sun rikide xuwa kalar ja tace
"Karya kike munafuka..karyane mahaifina bai mutu bah...
Tohfah...yau akeyinta 😱😱😱😭😭😭😭 masu karatu shin da gaske mr president ya rasu?
Ana surviving hatsarin jirgi kuwa?
Shin ya shuairat xata yi kodai itama mutuwar tayi?
Ya rayuwar umaima xata kasance?
Ku biyoni...mai fatan nishadantar daku
*Reefat CE* hop u enjoying d story....dis is just d beginning
4 comments o correction ~07030077024~
Bana editing so don't wory abt typing errors😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*65*
By *Reefat yahya*
A hnkli ta bude idonta tana bin dakin da kallo sai kuma ta tuna abunda ya faru hawaye ne ya fara gangarowa a gefen fuskar ta bash ne ya shigo tare da momsi suna mata sannu suna hada ido da momsi shuairat ta fashe da kuka nan Suka fara bata hakuri
"Momsi da gaske ne mr president ya rasu?
"Shhh...mr president yana nan ki kwantar da hnkli"
Ta xare ido ckn tsananin mamaki
"Hw comz"
"Ikon Allah kenan..ya'ta, Allah ya kaddara da sauran numfashinsa a doron kasa..ynxu haka mun sami lbrin cewa su 2 Suka rage a ckn jirgin suna can asibiti a Beijing"
"Alhamdulillh..
Ta furta a hnkli tare da ajiyar xuciya tana kokarin tashi xaune sai ynxu ma ta lura da drip da aka saka mata
"Ina sultan da umaima"
"Suna nan ki kwantar da hmklinki ga abinci nan ki ci"
Momsi ta deba mata abinci dan kadan taci tace ya isheta sai ynxu ta daga ido ta kalli agogon dake makale a dakin 8am lallai ta Dade a kwance nan ta koma tayi kwanciyar ta bada dadewa ba akayi sallama Muryar mamanta CE nan ta juya Suka hada ido mamace tare da shukrah Suka shigo tana ganin haka ta fara kuka dakyar aka rarrasheta daddy ne ya sake shigowa
"Ah..ta farka ne..alhamdulillh ya jikin de Aysha"
"Da sauki"
"Masha Allah..kici abinci ki kwantar da hnklinki mijinki yana nan a raye ynxu haka xamu tafi nida yayanki kinji koh"
Kai ta gyada masa daga nan sukayi sallama shi da bash akan xasu tafi China don ganin halin da mr president yake ciki.
Haka jamaa Suka dinga xuwa jaje gidan kullum cike yake makil da jama'a mr Joshua kuwa kullum sai ya shigo ya duba lfyar yaran tare da shuairat. Umaima ta rame kullum ckn tunani take tana yiwa mahaifinta adua haka nan shuairat ma ta warke se yawan tunani shiyasa momsi take matukar bata kulawa ta musamman.bash tare da daddy sun share 2 weeks kafin Suka dawo akan cewa yana samun sauki Amma shuairat kam Sam hnklinta bai kwanta bah don haka ta dage cewa xataje ta kula dashi babu yanda Suka Iya dole daddy ya amince aka mata visa ta faran shirin tafiya..bash yace tare zasu tafi firr taki yarda tace ya xauna ya kula da yara hakan kuwa akayi daddy da momsi sun shirya sun koma Lagos sultan kuwa gidan mama aka turashi can xai cigaba da xama umaima kuwa bash yace a gidansa xata xauna ba don tana so ba dole ta amince da haka.
Shuairat ta tattara motocinsu da nata da na mr president ta aika gidansu tare da duk wani Abu mai muhimmanci ta tura can daga nan taje sukayi sallama da iyayenta baba ya mata nasiha sosai daga nan ta koma gidan babu dadi sam .
Jirgin 7 Suka bi ita da bodyguard din da xai rakata bayan ta xauna ta fara jera aduoi kam😀😀 don ynxu ta tsani jirginma kwata2* .bayan sun sauka taxi Suka shiga xuwa doushin hospital ga yan China nan birjik kowa na shaanin gabansa babu mai kula harkar wani har dakin aka nuna musu Suka shiga yana kwance ckn coma ko motsi baya yi ga na'urori daban2* a manne ajikinsa shuairat tana ganin haka ta fara kuka bodyguard din yana bata hkri daga karshe ya mata sallama ya tafi ta kura masa ido yana kwance tmkar matacce haka ta cigaba da xubda hawaye babu mai bata hkri har ta gaji don kanta ta daina.toilet ta shiga tayi alwala ta fito da abun sallar ta nan ta biya duk sallolin dake kanta tana idarwa ta koma kusa dashi ta xauna tare da kura masa ido.gashi dai babu rauni sosai a jikin nasa Amma baya motsi lallai ikon Allah kenan, Allah mai yin yanda yaso da bayinsa.wata nurse CE ta shigo nan ta wuce ta dudduba na'uororin ba tare da tayuwa shuairat magana ba , allura ta saka ckn ledar drip din sannan ta juya ta fara yarensu murmushi shuairat tayi sannan ta nuna mata bata jin yaren yarinyar ta fita bayan mintuna kadan ta dawo tare da wani saurayi.
Murmushi yayi sannan ya fara magana da turanci
"Sunana baek San chu..ni ma'aikacin wannan asibiti ne, mr president yayi loosing memory dinsa..
😳😳innalillahi nan hawaye ya wanke mata fuska .
Yace
"Kiyi hkri ki kwantar da hnklinki xan warke very soon ana bashi kulawa ta musamman, kuma Chinese president ya aika a wuce dashi Hong Kong gobe..he is lucky to survive a plane crash"
Daga nan yacigaba da bata hkri da kalamai masu kwantar da hnkli Daga karshe Suka tafi Suka barta ita kadai.daddy ya kirata sun Dade suna hira nan ta sanar dashi komai ya bata momsi Suka gaisa tana gamawa wayar bash ya shigo nan ma sun Dade suna magana har umaima ma ta karba Suka gaisa tana tmbyn jikin mahaifin nata.
Haka shuairat ta kasnce ckn xaman kadaici ko yunwa bata ji dakyar bacci ya saceta.da safe tayi sallah ta watsa ruwa sai ynxu ta fara jin yunwa ba bata lokaci ta xari kudin ta fita wajen harabar asibitin , babbar asibiti ne na kudi ga kyau tana tafiya tana yan dube2* har bakin gate bata ga alaman shago bah , ta fita waje ne ta hango stores a tsallaken titi daga nan ta wuce ta shiga wani super market mai kyawun gaske drinks da snacks ta dauka sai kuma grapes n apple ta biya kudin ta koma ckn asibitin dakyar ta gane dakin.bayan ta gama ci tana xaune baek San ya shigo tare da wasu mutane ckn bakaken suit yana murmushi ya fara magana da turanci
" dafatan ki tashi lfy"
"Lfy kalau "
"Ga wadannan daga fadar shugabankasa aka turosu sunxo da private jet xaku tafi tare xuwa babban asibiti acan hong Kong "
Shuairat ta gyara akwatin ta daga nan aka kawo wani gadon tura marasa lfy nan aka dora mr president akai Suka wuce xuwa wata katuwar mota mai kyau sai Suka wuce filin da aka ajiye private jet din don xuwa hong Kong....
Muje xuwa Lov u all
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*66*
By *Reefat yahya*
A fadar shugaban kasar China akayi musu kyakkyawan tarba nan aka basu masauki mai kyau ckn kankanin lokaci aka shigar da mr president ckn wani daki dama can likitoci suna xaman jiransa nan take Suka fara aiwatar da aikinsu, shuairat kuwa an kaita wani bangare mai kyawun gaske babu bata lokaci ta fada wanka tana fitowa ta xauna gaban madubi tana kallon kanta ..tabbas ta rame sai Dan hasken da ta karayi tana nan xaune ta buga uban tagumi wayartace ta hau ruri tana dubawa taga layin umaima ta daga
"Hello princess ya kke"
"Lfy anti ya jikin dad"
"Alhamdulillh da sauki"
"Allah ya bashi lfy"
"Ameen..hop kina lfy koh"
"Uhmm lfy alhamdulillh"
Daga nan sukayi shiru hawaye ne ya cika idanun umaima tabbas tayi nadamar tsanar da ta nunawa shuairat a da can baya
"Hello princess yadai"
"Lfy ba komai"
"Ok toh..takkia koh ynxu muka sauka a hong Kong bari na huta xan kira anjima"
"Ok bye"
Daga nan Suka kashe wayar tare shuairat tana mmkin sauyin umaima ko don rashin lfyn dad dintane oho..nan ta shafa mai ta fesa turare, doguwar Riga ta saka mai kyau daga nan ta fita falo ta kunna TV tana kallo ammaa Sam hnklinta baya wajen ta kurawa TV ido amma tunaninta yana gun mr president.. Allah sarki kamar yasan abunda xe faru dashi yaki amincewa da tafiyar ita ta tilasta mishi , daren da zasu rabu ta fara tunawa..dare ne me kunce da so da kulawa Wanda baxata taba mantawa dashi ba har karshen rayuwarta..hawaye ne Suka diga a fuskarta ba tare da ta sani bah
"Excuse me!
Wata murya taji yasa ta waigo wata yar budurwa ta gani kyakkyawa bazata wuce 25yrs bah dakyar shuairat tace
"Yes! How may I help u"
Yarinyar ta mika mata hannu tana murmushi
"Gum jankim n u"
"Shuairat"
"Shu..??
"Shu..ai..rat"
"Wow nice name shu..-ai...-rat..."
Ta sake maimaita sunan nan ta xauna ta shaida mata cewa ita likita CE a america tayi karatu an daukota ne don kulawa da mr president a nan hong Kong take aiki a can babban asibitinsu.
Shuairat taji dadin xama da jankim sabida yarinyar akwai raha da fara'a tana da saurin sabo ckn kankanin lokaci shuairat ta sake da ita sosai suna hira ta Dan ji saukin damuwar da take ciki.
**********
Umaima tana xaune tayi jugum tana tuanin duniya da abunda ke cknta rayuwarta na baya ta fara tunawa har xuwa rasuwar mom da kuma auren dad da shuairat da irin cin mutuncin da ta dinga yiwa shuairat.. Allah sarki yarinyar akwai hkri ko kadan bata taba nuna damuwa ba duk irin rashin kunyar da take gwada mata, ga irin kulawa da take ba sultan ga sanin darajar Dan Adam ga fara'a ga yawan taimako ga kuma saukin kai..shuairat bata dau duniya a bakin komai bah ..Sam abun duniya baya rufe mata ido, hmm ita umaima ga girman kan tsiya ga kallon banza da kaskanci ynxu duk ina suke? Dad da take ji da kanta don ta kasance yarsa ma ina yake yau? Yana kwance rai a hannun Allah ko zai tashi ko baxai tashi ba wallahu Ahlam ..duniya kenan wata ran naka wata ran kuma na wasu shiyasa ake son mutum ya dinga hangen nesa ya tuna gobe.. Hawaye ne Suka wanke mata fuska tana mai jin haushin rayuwar da tayi a can baya.girman kai ya hanata samun kawaye haka nan ma samari , gani take tmkar tafi karfin kowa..Ashe ba haka abun yake bah, lallai ko ynxu ne ta karanci menene duniya tabbas duk...........garam!!!!! Banko kofar dakin da akayi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da take shukrah CE ta watsa mata kallon tsana ckn daga murya tace
"Munafuka! Kukan me kike yi? Kinzo kin share gindi kin xauna wato gaki ya'r gwal koh? Toh bazata sabu bah..maxa ki tashi kixo ki min wanke2* don ni ba ya'r aikin gidanku bane shegiya ba kina son mijina bah...hmmm mu xuba nida ke"
Umaima ta sunkuyar da kai kasa ta fara kuka Mara sauti..wannan wace irin rayuwace? Yau ita CE zatayi wanke2* ? Yau ita akewa gorin gida? Allah sarki duniya juyi..dad ta tuna nan ta kara fashewa da kuka Allah ya bashi lfy.shukrah ta fara tafa hannu
"Iyye..lallai ya'r gwal kenan.. Wanke2*n yake saki kukA? Ah..lallai kina da aiki babba don kuwa ynxu muka fara wllhi, ba kin bi mijina kika zo min gida kince zaki xauna bah? Toh sai ki koyi xama dani Dan wllhi sai na koya miki hnkli xaki gane borno gabas yake"
Daga nan shukrah ta juya tabar dakin , umaima ta tashi tabi bayanta kitchen Suka nufa..kwanukane tirim a ckn sink ga nan wasu ma a kasa daga nan ta fita tana dariyar mugunta umaima kuwa kuka takeyi tmkar ranta xe fita.
Bash ya shigo falon ba kowa amma ya ji motsi a kitchen kai tsaye yaa wuce tana xaune ta hada kai da guiwa tana kuka ckn hnzri ya karasa
😳😳" innalillahi! Umaima meya faru kike kuka"
Batayi magana ba ta cigaba da kukan taba daya hnklinsa ya tashi ya fara rarrashinta dakyar ta sagaita kukan ta daga jajayen idanunta
" don Allah yaya bash ka taimaka ka kaini gun anti shuairat ina son ganin dad pls"
"Is ok ..ki gayamin me ya faru? Wani Abu shukrah ta miki?
Shiru tayi bata CE komi ba ta sake fashewa da kuka tace
"Nikam don Allah ka kaini ko ina baxan xauna a wannan gidan ba"
"Ok kiyi hkri koh..muje xan kaiki gun mama na xaki xauna dasu ? Kinga sultan ma yana can nasan kinyi kewarsa daz y"
Kai ta gyada masa alamar ta amince nan ya rike hannunta Suka tashi tsaye a dai2* bakin kofa Suka ci karo da shukrah tana shiga..😳😳😱😱ta xare ido ckn takaici tace
"Me zan gani haka? Wanke wanken da na saki kenan? Shine zaki kira mijina a waya..sannan har da rike masa hannu?
Aikuwa shukrah ta daga hannu xata kaiwa umaima mari bash yayi saurin rike hannun ya fara magana
"Haba shukrah behave urslf mana.. Meyasa kike yin Abu as if u ar not matured"
"Which kind matured..wllhi bazan yarda ba ai wannan cin fuska ne"
"Naji..is ok toh kiyi hkri ni na rike mata hannu n am sorry ok! Batun wanke2* kuma kiyi hkri bata saba ba kinga amanarta aka bani n I have to takkia of her "
"Haba baban waleed ynxu aiki ma ban isa in sata tayi ba sabida an baka amanar ta? Allah is not fair"
Shukrah ta fara xubar da hawaye bash ya sake hannun umaima ya jawo shukrah a jiki yace
"Am sorry pls ki daina kukan nan kinsan bana so..n bawai na hanata bane wllhi am sure bata iya bah "
"Kai dai kace min sonta kake shiyasa dama ka kawo ta nan gida saboda Ku dinga ci min face toh wllhi baxan yarda bah"
Ya juya gun umaima yace
" kije dakin ki ina xuwa" daga nan ya ja shukrah Suka bar kitchen wani kishine ya turnuke umaima nan ta koma daki ta cigaba da kukanta tasan lallai ta rasa bash har abada idan ta tuna yanda yake lallaba shukrah sai ta ji wani tsananin kishinsa..hmmm anya burinta ze cika?
Muje xuwa😘😘
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*67*
By *Reefat yahya*
A daki bash yake bawa shukrah baki
"Haba my love ki Dan rage kishin nan mana ai zata raina ki..kuma ni ban ce miki ina sonta ba meyasa zaki damu kanki she is just lyk a 6ter to me pls kidaina wannan haukan"
"Ohh..hauka kace koh? Toh shikenan zaka ga haukan wllhi xanyi maganinta..zancen so kuma ai naga kwayar idonta sonka ne zalla a ciki, wllhi bazan barta bah"
Dariya sosai bash yayi sannan yace
"Hohh..shukrah! Dama haka kike da kishin tsiya?
Ta tura baki ckn shagwaba tace
"Dariya kake min koh..wllhi ni nasan tana sonka kuma kaima kana sonta kawai boyewa kake"
"Ok naji tana sona ..amma trust me ba komai tsakanimu kinji? Ki kwantar da hnklinki , aiki kuma idan kina janta a jiki ita da kanta xataji shaawar koya ba sai kin nuna mata karfi bah pls my love kiyi respecting din kanki ok"
Kai ta gyada masa haka nan ya lallaba abarsa sai gashi ta sakko abunka da mata da miji har ya mantar da ita xancen wata umaima ckn salon soyayyarsa nan Suka lula sararin samaniya duniyar masoya😜😜.
Umaima tun tana sa ran xuwansa har ta fidda rai tayi kuka mai isarta lallai namiji munafuki ne ynxu ya shanyata yana can tare da matarsa yana bata kulawa hmmm ke kuma a suwa? Hakane bata dawani matsayi a gunsa haka ta kwanta a gado ckn rashin kwarin guiwa.
Bayan 1hr ya shigo dakin tare da sallama ckn shigar kananan kaya yayi kyau sosai ga sajenasa kwance luf-luff se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi kyau sosai umaima ta kura mishi ido babu ko keftawa har ya karasa kan kujera ya xauna fuskarsa dauke da murmushi yace
"Em..sorry sis kinji ni shiru koh"
"Ah..ah ba komai "
Ta furta a hnkli se yaji tausayinta ya kamashi tabbas yasan kadaici na addabarta a rayuwa bata da abokin hira se TV ko waya don bai taba ganinta da kawaye bah toh saurayi fah?ya daga kansa Suka hada ido har ynxu kallonsa take ckn tsananin kunya ta dauke kanta
"Yadai ko nayi kama da wani ne?
"Wani? Kamar waye kenan?
"Oho..maybe mr right"
"Hmmm..kai kasan wannan"
" ohh..ke baki sani ba kenan, yawwa gskiya fa umaima baki taba hadani da bro-inlaw na bah ko rowarsa ake mana"
Haushin maganganun take ji wato shi bata taba burgeshi bah koh..Allah sarki baisan tana yi bah , nan kwalla ya cika mata ido
"Umaima lfy..ko tambayan da na miki ne? Am sorry pls"
"No..is ok ba komai"
"Akwai mana..gashi kina Neman xub da hawaye ko kun rabu ne shiyasa kika tunashi kina son yin kuka"
Ckn haushi tace
"Ya mutu"
😝😝😝😝bash yaso yin dariya amma ya gimtse don daga ganin yadda tayi maganr yasan karyace don haka yaja bakinsa yayi shiru.haka Suka xauna har tsawon minti10 babu Wanda ya sake cewa komai don haka bash ya tashi yabar mata dakin ta fada gado ta cigaba da kukan rashin masoyin nata.haka rayuwa ta kasance ba laifi ynxu shukrah na amsa gaisuwarta kuma ta daina takura mata , waleed ya fara sabawa da umaima haka nan sultan ma yana xuwa su yini idan babu makaranta.umaima kuwa tana xuwan tasu makarantar amma har yau bata da kawaye ko abokai, mr Joshua kuwa shi yake kula da al'amuran kasar..Rayuwa kenan.
****************
Shuairat ta share wata 2 da xuwa hong Kong ynxu wata3 kenan da kwanciyar mr president rashin lfy amma har yau bai farfado bah..wani lokaci shuairat gani take tmkar ya rasu kawai boye musu akeyi bayan likitoci kuwa sun bata tabbacin cewa zai warke don haka ta dage da adu'a ba dare ba rana tana yawan karanta masa Qur'an a saitin kunne haka nan tana tofa masa wasu ayoyin, nafilar dare kuma ba'a magana .daddy da momsi kafarsu2 suna xuwa haka nan bash ma yaje sau1 umaima kam duk nacinta daddy ya hana sabida cewa yayi idan taje hnklinta zai tashi.
Shuairat tana xaune apple ne a hannunta tana taunawa a hnkli mr president yana kwance a gadon marasa lfy na'urori ne iri2* makale a jikinsa ga kuma ledojin ruwa. Jankim CE ta shigo tana murmushi ta fara magana da turanci
"Maman bby gskiya babyn nan namu mayen apple ne..kusan kullum shine abincin ki fah"
"Jankim sarkin xolaya..wani bby kike nufi"
Ta karasa kusa da mr president ta fara dudduba na'urorin tana gyarawa tace
"Shu..ai..zaki cemin baki San cikine da ke bah"
"Watt??😳😳da gaske?
"Ehh..tun farkon haduwarmu na lura kina da ciki"
Mamakine ko murna ko bakin ciki wanne xatayi? Jankim ta bude Jakarta ta dauko kayan aikinta tace
"Muje na gwada ki"
Ba musu Suka wuce dakin da aka tanada don likitoci babu abunda babu a ciki nan da nan ta gama test din ya nuna musu result shuairat tana dauke da juna 2 na tsawon wata 3 ciff sai kuma ta kwanta akayi scanning sun duba komi.murna ne fal ckn ranta sai kuma hawayen tunawa da halin da uban yake ciki sai kuma ta tuna cewa rabonta da period tun a najeriya daga nan suka fita sun sayi magunguna da abubuwan kara lfy har nafila shuairat tayi ta godewa Allah sannan ta roki Allah ya bawa mr president lfy .
Haka ta cigaba da rainon ckn, jankim CE ke debe mata kewa first lady ma ta dawo daga tafiyar da tayi ta jajantawa shuairat haka nan manyan mutane na yawan xuwa duba mr president wasu abokanan aiki ne wasu kuma shuwagabannin kasace daban2* ga tarin duniya da suke xuwa dashi kudade kam ba'a magana shuairat tana turawa a account don bata bukatar komai Chinese president yana matukar kulawa dasu.
Ynxu ckn nata ya shiga wata4 ta kara cika tayi kyau sosai gwanin sha'awa tayi haske kamar me...ta shigo dakin tare da sallama kamar yanda ta saba duk tasan cewa babu me amsawa ta nemi kujera kusa dashi ta xauna ta kura masa ido
"Masoyin yaushe zaka tashi ne we rily missed u nida little... Pls get well soon Allah ya baka lfy"
Hawayen idonta take sharewa sai me??? Alamar ya motsa ta gani tayi waje da ido ta kara masawa
"My man...mafarki nake ne ko da gaske😳😳
Nan ma ya Dan motsa yatsa ckn hnzri ta gudu kiran jankim..tare Suka shigo nan ta kira likitoci ta sanar dasu ckn kankanin lkc Suka taru a dakin tabbas ya farka ynxu yana jin komai kuma memorynsa is ok a kowane lokaci zai tuna da rayuwarsa na baya don haka ake bukatan shuairat ta dinga zama kusa dashi don ya tuna komai, yana jin komai amma ba lallai bane ya fara magana ynxu .ranar shuairat ta kwana da farin ciki nafilfilu ta dinga yi bata samu bacci sai da safe sannan ta koma bacci.
Haka ta kasance ckn kula da mijin nata kullum tana bashi lbri kala2* na najeriya tare da nuna masa hotuna ..har ynxu motsi kawai yakeyi idanunsa ma a kafe suke sai daga baya ya fara ita kefta su.daddy ya xo ya dubashi yaji dadi sosai haka ya xubawa shuairat albarka nan ta nemi alfarma a gina musu gida a can najeriya kan su dawo, daddy ya shaida mata mr president yana da gidaje da dama sai dai a gyara hakan kuwa akayi yana komawa aka turawa bash kudi ya bada kwangilar sake gidan Nas dake garki babu bata lokaci aka fara aiki.
*****
Bayan wata2 Alhamdulillh mr president yaji sauki sosai har ya fara takawa tamkar karamin yaro haka ake koya masa tfy shuairat kuwa cknta ya Dan fito ta zama abunda shaawa duk Wanda ya kalleta dole ya maida ido ita take koya masa tfyar ya tuna komai na rayuwarsa na baya amma har ynxu baya son yin magana shiru kawai sai dai murmushi.
Yau suna xaune a masaukinsu ta ajiye masa magunguna a gaba ya hada fuska da alama baya son sha nan shuairat ta juya masa baya alamar tayi fushi ba shiri taji ya rungumeta ta baya
"Am sorry swt hrt"
Ya mata rada a kunne ckn mamaki ta juya suna fuskantar juna
"Mr..mr president dama kana magana? Na dauka ka samu problem fah"
Murmushi ya mata sannan ya jawota a jiki ya kankameta sosai har bata iya motsi mai kyau hawaye ne ya fara diga yana kuka ya fara magana a hnkli
"Nagode!! Nagode!! Nagode!! Nana Aysha ke ya'r aljannah CE insha Allah..Allah ya miki albarka ya baki duk abunda kike bukata duniya da lahira..ya baki ya'ya masu albarka bazan manta dake ba har karshen Rayuwata ..bazan tozartaki ba..ya Allah ka bani ikon rike wannan baiwa taka..ya Allah ka yafe mata dukkan zunubanta..ya Allah ka bata gida a aljannah ka biya mata bukatunta ameen...I love u Aysha"
Ya kara kankameta shuairat ma kukan farin ciki take ya Dan raba jikinsa da nata yana kallonta yace
"Swt hrt ke kuwa kukan me kike yi"
"My man..dole nayi kukan farin ciki saboda Abu 3"
"Menene wanna?
"Na farko ka warke Wanda har na cire tsammanin sake xama kusa da kai kamar ynxu na dauka na rasaka har abada kaga kuwa farin ciki ya zama dole"
"Hakane rahamar ubangiji kenan baya karewa ..uhmm na 2"
"Na 2 kuma adu'oin da ka jera tabbas duk macen da ta samu irin wannan aduar a bakin mijinta toh lallai tayi dace a duniya babu kamarta..kaga Allah yana amsa aduar miji ga matansa kaga dole nayi murnan samun wannan Alhamdulillh ko ynxu nabar duniya nayi dace"
"Uhmm...Ayshata kenan.. Allah ya miki albarka, idan har ta hanyar kyautatawa miji ake shiga aljannah toh na daga kafata..Allah ya baki jannatul firdaus..tabbas kin cika alkawarin da kika dauka na cewa komin tsanani komin wuya komin dadi kina tare dani bazaki barni ba har abada,
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*68*
By *Reefat yahya*
Mr president ya cigaba da cewa
"Tabbas da ace duk matan duniya halayensu irin naki ne da lallai zaman lfy xata dore a kowane gida ..Allah ya miki albarka Allah ya barmin ke har a gidan aljannah"
Ya kara kankameta yana me kuka shuairat ta kwantar da kanta a kirjinsa tana jin bugun xuciyarsa , a hnkli ta daga kai tace
"Mr president kawo kunnenka "
Ba musu ya kai kunnensa dai2* saitin bakinta a hnkli ta furta
"Am pregnant"
😳😳😳😭😭😭 ya xare ido sai kuma ya fara hawaye ya rungumeta gam a jiki yana kuka tamkar karamin yaro
"Haba my man..me abin kuka a ciki ? Kai da zakayi farin cki "
"Kuka ya xama dole Ayshata..bansan wane irin farin cki nake bah tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad manxonsa ne..Allahu Akbar! Allah mai ikon komai da kowa..yau ni Suleiman matata tana dauke da ciki? Allah nagode maka ..dama da rabon xan sake ganin jinina a doron kasa ..Allahu Akbar"
Haka mr president ya cigaba da sambatu Dakyar shuairat ta lallaba shi ya daina kuka har ya bata tausayi..eyya mr president😜.daga nan ya tashi ya wuce bayi ya daura alwala ya fito ya fara nafila yana godiyarsa ga ubangijin talikai, shuairat ta kwanta a gefe tana kallonsa tana jinjina masa sabida ya kasance daga ckn bayi masu nuna godiyarsu ga ubangijin da ya haliccesu..bacci ne yayi awon gaba da ita a yayinda mr president kuwa yacigaba da nuna godiyarsa ga ubangiji.
************
Shukrah tana xaune a falo sai hura hanci take tana cika tana batsewa bash ya fito daga dakin bacci ya kalleta sau1 ya kawar da kai gefe yana mmkin wasu halaye irin nata ..
"Wllhi ina kan bakata, idan har bazaayi tafiyan nan dani bah toh sai dai kaima ka hkura don bazan yarda da wannan salon yaudaran bah..uhmm inaji ina gani ka dauko wata can ka tafi da ita turai da sunan zakuje duba jikin mahaifinta salon kuje kuyi soyayya a can koh..toh ban amince bah'"
Sai ynxu ya juya ya kalleta sosai ya girgiza kai yace
"Wai dama haka halinki yake ne shukrah? Kodak kin fara bin xugin kawaye ne? 4Allah's sake shukrah ina matsayin mijinki mu haifi waleed amma ace har yau baki yarda dani bah? Yaushe zaki daina zargi na ne..bayan kinsan cewa aure da zargi babu kyau"
"Kaga malam..ni ba jahila bace da zaka min wa'azi ehen, bazaka fake kana min dadin baki bah kawai ka fito fili ka gayamin aurenta zakayi ba sai ka tsaya yin wani kame2* bah"
"Allah sarki..yau kuma ni nake kame2* shukrah! Lemmi ask u..idan ina son umaima wai tsoronki zanji? Ko kina tunanin cewa idan ina son aurenta wannan haukan taki xata hanani yin abunda nayi niyya?"
"Koma menene..tafiya ce baxa ayi bah "
Ran bash ya baci sosai gskiya shukrah ta canza amma dole ya ja mata birki ( mata a kiyaye..wannan kishin hauka ne kuma hakan yake kara tunxura miji har yayi aurenda be shirya yi bah Allah yasa mu dace ameen).
Ya tashi kai tsaye dakin umaima ya wuce fuu..shukrah tabi bayansa, umaima tana kwance bash ya shigo tare da sallama ta gyara zaman ta kenan shukrah ta shigo kamar wata zakanya😝😝😝(Wa ya gamin anti rabi ana kishi😜)
Bash yayi banza da ita yace
"Umaima hop kin gama shiryawa cos jirgin 8pm zamu bi"
"Na gama but yaya I tot tare zamu tafi dasu sultan da gran mah"
"No..I change my mind mu 2 kawai zamu tafi su kuma jirgin 7am na safe zasu bi , zamu jira su @ Beijing"
"Ok..Allah ya kaimu"
Basuyi aune ba sai ganin shukrah sukayi ta makure umaima a jikin gado tana huci ta fara magana
"Shegiya munafuka..wllhi mijina yafi karfinki kije can....
Bata karasa ba taji saukan mari Tass! A fuskarta ba shiri ta sake umaima ta juya tana kallonsa tmkar a mafarki wai yau bash ne ya daga hannunsa ya mareta? Hawaye ne Suka cika mata ido a hnkli Suka fara sauka
"Shine ka mareni? Ak..kan ..akan wannan yarinyar? Baban waleed?
Ya runtse ido ckn jin zafin abunda ya aikata.shukrah ta juya tabar dakin shi kuwa ya jingina da bango kansa na kallon kasa, umaima kam tayi Kim..tmkar gunki ta rasa me xatayi tabi bayan shukrah ko kuwa ta tsaya gun bash? Shiru ya ziyarci dakin a hnkli ta karasa kusa dashi
"Yaya bash kayi hkri laifina ne da nazo gidanka..na hanaku kwanciyar hnkli am sorry"
Hannu ya daga mata ya juya yace
"Ki shirya ynxu xamu bar gidan nan"
Daga nan dakinsa ya wuce ya shiga bayi ya watsa ruwa gaba daya ransa a bace yake , ckn kankanin lkci ya gama shirinsa ya dauko wani Dan karamin jaka dakin shukrah ya shiga tana kwance rub da ciki tana kuka Mara sauti waleed kuwa yana gefe sai sharar baccinsa yake ckn kwanciyar hnkli.
Ya karasa kusa da ita yace
"Am sorry..nayi kuskure ki yafe min ni zan tafi kiyi hkri"
Daga nan ya ajiye mata rafar yan 1k ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya tsaya cak! Yace
"Ki gyara kwanciyar ki Allah yana fushi da masu irin wannan kwanciyar"
Daga nan ya tura kofa yayi ficewarsa shukrah ta cigaba da kukan da take.umaima ta fito da jakar kayanta ta sanya a mota bash ya ja Suka wuce gidan iyayensa don yin sallama dasu.
**********
Shuairat ta caba ado tana xaune a gaban mirror mr president ya fito daga wanka bayan ta taimaka masa ya kimtsa Suka fito falo sai kallonta yake ya lura cewa tana ckn nishadi yau ya juya yace
"Nana Aysha !
"Sir! ta amsa tana murmushi, saida yayi dariya sannan yace
"Sir! Kuma? ..anyway na lura dake yau tun safe kike ckn nishadi ko meyasa?
"Hmmm..ba komai fah haka nan nake jin kaina ckn annashuwa "
"Kin tabbata?
Kai ta gyada tace
"Na tabbata sir!
"Hmm..ke din ne somtymz u r amazing, kuma am sure u ar hiding somtin baki son gaya min koma menene dai nasan gud news ne"
Murmushi kawai tayi bata CE masa komai ba tana duba agogon hannunta , bayan 30min aka kwankwasa kofa shuairat ta mike a hnxarce ta bude kofan tare Suka hada baki wurin cewa
*surprise*!!!
😳mr president ya tashi ckn tsananin mamaki yana binsu da ido..ko a mafarki bai taba tunanin ganinsu a wannan lokaci bah..
Bash, umaima, sultan, momsi, daddy da kuma baban shuairat.. Wow wani farin cki ne ya lullubesu wen last Suka hadu irin haka...
Muje xuwa😘😘😘
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*69*
By *Reefat yahya*
Gaba dayansu Suka dugunxuma ckn falon mr president kuwa murna ne har ya rasa ina zaisa kansa ya kankame daddy kamar xai shige jknsa momsi tana dariya, sultan kuwa da gudu ya fada jkn shuairat yana cewa
" I rily miss u mom Nah"
"Miss u mor my son"
Mr president ya raba jkinsa da na daddy ya jawo sultan ckn sauri yana cewa
"Boy kayi a hnkli kada ka ji wa kaninka ciwo"
"Wane kanin dad?
Ba sultan kadai bah ..duk wadanda suke ckn falon sun maida kallonsu ga mr president shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da cewa
"Sultan mom tana dauke da ckn kaninka very soon zata haifa mana baby koh"
"Wow...da gaske dad? Am so happy nima na huta da gorin frenz dina a skul "
Daga nan sultan ya koma gun shuairat ya sake kankameta ckn hanzari mr president ya sake rabasu shuairat kam kunya yasa ta bar falon ya shige bedroom.
Momsi da daddy kuwa wani farin cki ne ya lullubesu umaima ma haka , daga nan Suka zauna aka gaisa har ynxu shuairat bata fito bah momsi tana hararar mr president tace
"Kaga rashin kunyarka yasa ka korarar min ya' ko gaisawa bamuyi bah..anyway Allah ya raba lfy ya Baku zuri'a dayyibah"
"Ameen momsi nagode"
"Hooo..dad ko kunya babu"
Umaima CE ta fadi hakan gaba daya Suka sa dariya bash kam sai faman murmushi yake haka nan baba shikuwa yana son ganin ya'rtasa.momsi CE ta tashi ta nufi dakin a hnkli ta tura kofar shuairat tana xaune tayi jugum momsi ta rike mata hannu suna fuskantar juna tana murmushi tace
"Allah ya miki albarka ya'ta nagode sosai da irin kulawar da kike bawa dana Allah yasaka miki da gidan aljannah ya sauke ki lfy ya albarkaci abunda zaki Haifa"
Sunkuyar da kai tayi ckn tsananin jin nauyinta momsi ta cigaba da cewa
"Tabbas kin zame mana alheri a Rayuwa ..kin dawo da farin ckn mu , kin cancanci yabo a garemu mun gode Allah ya saka.tashi muje ki gaisa da mahaifinki nasan yana bukatar ganinki"
Ba musu ta tashi Suka fice xuwa falo.
Ckn jin kunya ta gaisa da baba da kuma daddy sai kuma bash , umaima kuwa Sam ta tashi ta koma kusa da shuairat. Haka Suka kasance daga nan Suka xauna akan dinning table lafiyayyen abinci masu aikin gidan Suka shirya musu, daga Chinese dishes da Nigerian duk babu abunda babu suna ci suna hira babu batun kunya abun dai gwanin burgewa.baban shuairat yake Dan jin kunya daddy ya lura da hakan yace
"Alhaji bello gara ma ka cire kunyan nan ka ajiyeta a gefe kaga surukin naka babu alamar kunya a tattare dashi"
Gaba daya Suka fashe da dariya mr president ya Dan Sosa kai..har ga Allah shi yamanta da cewa a gaban baba ya fadi xancen cikin. Bayan sun kammala cin abincin aka nuna musu masauki Chinese president yaxo Suka gaisa da iyayen nasu sannan ya tafi , mr president tare da iyayensa Suka ware suna hira haka nan shuairat ma dakin baban ta Suka xauna ita da bash da kuma sultan suna ta hiran yaushe gamo.
D next day Suka shirya gaba daya daddy momsi baba shuairat bash umaima sultan da gum jankim yawon bude ido Suka fita, sun zaga garin sosai gskiya hong Kong ya hadu har yamma Suka koma gida bayan sun tsaya sunci abinci a wani restaurant.
Washe gari Suka sake fita , haka dai Suka kasance har tsawon 5days kullum suna tare.shuairat sai nan2* ake da ita duk motsin da tayi mr president ko momsi ko daddy zasu tmbayeta wani Abu take ji ne? Itakam har kunya take ji irin yanda Suka dau son duniya Suka doramata ita da ckn nata gashi ynxu ckn ya bayyana cos yana 7mnth ne.bayan kwana 2 Suka fara shirye2* komawa 9ja duk nacin momsi na son tafiya da shuairat firr...mr president yaki yarda yace musu zasu ga likita kafin su koma Nigeria, babu yadda Suka Iya dole ta hakura nan Suka cigaba da shirinsu.
Misalin 8pm umaima tana kwance a dakin shuairat tana chat a waya shuairat ta shigo ta zauna a gefe tana fuskantar ta tace
"Baby ya maganan aure ne kinga ynxu kin girma fa ya kamata ace kin fito da Wanda kike so"
Shiru umaima tayi a yayinda xuciyarta ya fara bugawa can ta kirkiro murmushi tace
"Anti Nah dad ne yace ki min maganan aure?
"Ah'aa wllhi nice dai naga ya dace cos zaki shiga final year naki a uni daz y"
"Ok ki bari idan Allah yasa kin sauka lfy after den sai muyi maganar"
"Toh Allah ubangiji ya nuna mana.. Amma ni ban taba ji ko ganin wani saurayi yazo wajenki bah"
"Oh..antyyy...wllhi har kinsa naji kunya"
Daga nan ta tashi ta gudu tana murmushi ganin shuairat na Neman tona mata asiri. A bakin kofa ta tsaya tana maida numfashi, bash ne ya shigo Sam hnklinta baya ckn jikinta tunanin maganganun shuairat takeyi ynxu ya xata yi? Pamm! Bash ya tafa hannayensa a saitin fuskarta ckn tsoro ta bude baki xatayi ihu yasa hannu ya toshe bakin nata yana dariya sannan yace
"Matsoraciya kawai"
Daga nan ya cire hannun nasa ita kuwa taja dogon numfashi
"Haa..yaya kaban tsoro wllhi na razana ba kadan bah"
"Ajebo kawai..babu abunda kika iya sai shagwaba wllhi mijinki zai sha fama dake"
Umaima ta rage sautin muryarta tayi magana ciki2* tace
"Kaine zaka sha faman ai cos kaine mijina"
"Wat? Me kike cewa"
"UHmm
.ni nayi magana da kai ne?
Ta fada ckn tsigar shagwaba yana dariya yace
"Hmmm a cigaba da boye2* dai wata ran dole a amayar"
"Wat? Hw do u min?
Ta tambaya ckn tsarguwa
"Oho..nima nayi magana dake ne?
Harara ta watsa masa sannan ta wuce falo ta xauna yana dariya yabi bayanta shima xaman yayi kusa da ita.
"Yawwa..yaya bash nifa bazan koma gidanka bah"
"Ina zaki koma ?
"Gidan baba xan koma b4 su dad su koma"
"Matsoraciya shukrah ce ta hanaki koh"
"Hmm..wannan matar taka se a hnkli"
"Ba dole bah..ta gane kina son mijinta ai dole tayi kishi"
😳😳waat?..mijin wa? Ni din?
Ta jera masa tambayoyin ckn mamaki da firgita wani murmushi ya sakar mata sannan ya tashi Sam ya dawo kusa da ita har suna jin hucin juna ya kura mata ido yace
"C'mon baby sis..stop pretending ya isa haka ki daina wahalar da xuciyar taki kowa yasan cewa ni kike so stp hiding n b strait fowod"
Xuciyar umaima sai dukan 3-3 yake bash ya cigaba da cewa
"Umaima na Dade da sanin cewa kina sona kawai kunyace ya hana ki gayamin.tun bayan dawowata daga Adamawa kika kirani na sameki a gidanku kina kuka kina maijin haushin cewa nayi aure ban gaya miki bah, tun a wannan lokacin na fuskanci sona kike.duk rashin lafiyar da kikayi bayan aurena ina sane da hakan kuma dad ma ya gane lagonki shiyasa yake turani miki magana a duk lokacin da kikayi fushi dashi, n naga chat naki da shuairat a yayinda kike gaya mata cewa kina son wani amma kin kasa tunkararsa har yayi aure. Ranar da kuka samu misunderstanding da shukrah har na lallabata xuwa daki nace ki koma dakinki ki jirani bayan na dade kafin na je dakinki nan ma na hango kishina xalla a kwayar idanunki har na tambayeki hiran samarinki kika cemin saurayinki ya mutu kin tuna? kuma dazu maganan da kikayi cewa nine mijinki duk naji abunda kika fada , so umaima pls ki daina wahalar da xuciyarki ki fito ki bata abunda take nema"
Yana gama fadin haka ya tashi ya kashe mata ido daya sannan ya juya yayi tafiyarsa.mutuwar xaune umaima tayi tana mamakin faruwar al-amarin dakyar ta tashi ta koma dakinta ta hada kayanta don jirgin safe xasu bi.
*****da safe mr president da shuairat Suka rakasu xuwa airport har jirginsu ya daga sannan Suka juya don komawa gida.
A ckn jirgi kuwa umaima Sam taki hada ido da bash don wani Sabin kunyarsa take ji haka Suka kasance har lokaci da jirginsu ya sauka a Lagos.umaima tace xata kwana 2 kan ta koma Abj haka bash da sultan da kuma baba Suka wuce Abj gidan baba direct Suka sauka.bayan kwana2 umaima ta koma Abj a gidansu shuairat ta yada Zango ta sanarwa mama cewa tare zasu zauna ita kuwa taji dadi sosai dama zaman kadaici ya isheta don ma sultan yana nan kenan.
*********
Shuairat kuwa jankim CE ke kulawa da ita duk awon ciki da komai ita take mata tana shan magunguna masu inganci don karawa bbyn lfy.honey moon Suka shirya xuwa jankim tana xolayarsu wai honey moon da tsohon ciki, har airport ta rakasu jirginsu ya daga xuwa *Akita Japan* wani hadadden city ne a can Japan jankim CE ta xaba musu garin *akita* saboda tsarin yanayin garin akwai dadin xama don kuwa duk arean tsakanin Korea China da Japan babu garin da yakai akita kyawun weather.
Bayan sun sauka taxi ne ya kaisu can gefen gari a *akita snow fall* wow..kankara ne ke xuba kotaina wani hotel mai kyawun gaske Suka kama daga nan wanka Suka shiga tare ..tafasashen ruwan zafi Suka Tara a jacuzzi shuairat na ganin haka ta xare ido tace
"Haba😳 my man ynxu kana nufin ckn ruwan nan xamu shiga?
Ya jawota jikinsa yace
"Don't worry my lady ..kinga nan snow fall ne bqzaki ji xafin ruwan bah"
"Ah'ah nikam gskiya baxan shiga bah"
"Plsss..haba ke baki jin sanyi ne? Nida nake son ki haihu a nan kiyi wankan jego kinga bazaki ji radadin wanka da ruwan xafi bah"
"Mm..dama wa yace zanyi wanka da ruwan xafi"
Ckn dabara ya tura bakinsa ckn nata ya fara kissing dinta cak ya dagata sai ckn jacuzzi....
Ummmm a hnkli na ja kofar bayin nayi waje.
Ku biyoni😘😘😘😘
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*70*
By *Reefat yahya*
Wata sabuwar rayuwar soyayya da kulawa mr president da shuairat Suka shimfida a *akita* bata daga komai hatta wanka shi yake mata kullum suna fita trekking saboda yana da kyau mace mai ciki ta dinga motsa jikinta kwanciya ba naki bane..a wannan lokacin ne shuairat ta kara tabbatar da irin son da mr president ke mata shikuwa gani yake tmkar baxe Iya biyanta karamcin da ta nuna masa, kullum suna manne da juna basu rabuwa wata irin shakuwa da so mai karfi ya kullu tsakaninsu.cikin ya shiga wata 9 su momsi Suka damesu da kira kan cewa yaushe zasu dawo mr president yace suna nan tafe momsi ta umarcesa da ya dinga karanta yasin kafa1 ya tofa a ruwa ya bata tana sha kullum saboda Neman haihuwa ckn sauki da iznin Allah.hakan kuwa akayi kullum mr president sai ya tofe suratul yasin 1 ya bata tasha. *Doughbunji hospital akita Japan* can sukaje aka shaida musu cewa haihuwan na nan bada jimawa, habawa mr president ya fara shopping ne kamar ba gobe babu abunda be siyo bah.
10days leta... Gobene suke shirin komawa Nigeria by 11pm suna xaune a falo shuairat tayi filo da cinyar mr president suna kallon news ana election a can Nigeria shuairat ta daga kanta tana kallon mr president tace
"My man da ace kana nan akayi wannan zaben babu makawa na tabbata talakawa xasu xabeka"
Murmushi yayi yace
"Wllhi nikam dadi naji don dama ni ba son politics nake bah..wancan karon ma daddy ne da frenz dinsa Suka dage har na samu shiga but now I have u I have everything"
Ya manna mata peck a goshi tana murmushi ta gyara kwanciyarta batasan lokacin da bacci yayi awon gaba da ita bah.
1hr leta ...ckn bacci taji ciwon Mara a hnkli ta bude ido mr president yana bacci a xaune har ynxu tana kan jikinsa hannu tasa ta shafa sajen fuskarsa dake kwance luf-luf a hnkli shima ya bude idon
"My man dauko min magunguna na marata ke min ciwo"
😳ckn hanxari ya dagata yace
"Hospital xamu je am sure haihuwace my lady"
Ta tura baki tace
"Ah'ah nikam ba ynxu bah..kawai fah ciwon Mara CE da kuma ciwon baya"
Bai jira komai bah ya daga ta cak dama doguwar rigace a jikinta don haka yayi waje da ita tana tmbayar ina ze kaita bai kulata bah ckn sa'a kuwa a harabar asibitin ya hango wani mutum yayi parking motarsa yana fitowa wani Dan bature neh da harshen turanci Ya roki mutumin akan cewa ya taimaka ya kaisu asibiti matarsace take nakuda babu gardama mutumin ya bude musu gidan baya Suka shiga yana kallonsu ckn yanayin tausayi yana yiwa shuairat sannu.a wannan lokacin ne ciwo yace salamu alaikum Ashe da can wqsa ne aikuwa kuka ta fara masa ta kankameshi sosai gaba daya ya rikice haka nan baturen ma yana tuki yana juyawa yana mata sannu gudu yake da motar tamkar xasu tashi sama *doughbunji* hosptl Suka nufa ckn Sauri aka karbesu dakin haihuwa aka wuce da ita mr president ya nemi kujera ya xauna sai adua yake jerawa yana rokon Allah ya sauketa lfy.
45mins leta...wata nurse ta fito fuskarta dauke da murmushi ta hango mr president xaune ya buga uban tagumi tace
"Congratulations sir! Ur wife gave birth to a baby boy"
😳😀take fuskarka ya fadada da murmushi a hnkli ya furta
"Alhamdulillh.. Allah nagode maka da wannan kyauta"
Daga nan dakin Suka wuce an gyarasu ita da jaririn duka idanun mr president sun cika da kwallah ya wuce gun shuairat tana kallonsa sai murmushi take ya kankameta sosai a jikinsa yace
"Thank u so much my lady Allah yabar min ke "
Ya manna mata peck sannan ya wuce ya dauki yaron ya kura mishi ido suna kama sak babu abunda ya rabasu har hasken fata nan ya masa huduba sannan ya bude bakinsa ya tofa masa adu'oi da kuma sauran gabobin jikinsa haka nan ya dafe goshinsa ya karanta wata adu'a sai kuma ya shafa kansa yace
"Allah ya maka albarka yasa ka gama da duniya lfy Allah ya albarkaci rayuwarka ya tsareka da sharrin mutum da aljan ya doraka a tafarkin addinin Islam ameen "
Ya mikawa shuairat yana mata murmushi yace
" karbeshi ki masa adu'a Allah yana karban aduar iyaye ga ya'yansu ki sanya masa albarka"
Ckn jin kunya shuairat ta karbeshi tana kallonsa tana murmushi a ckn xuciya tayi tata adu'ar da ko ni *Reefat* bansamu naji me ta fada bah sai ta shafa kansa ta mikawa mr president yana dariya yace
"Aw..adu'ar sirri ne? Ba damuwa naga alama kunyarsa kike ji nidai kar kunya yasa a cutarmin da da' "
Murmushi kawai tayi ta kawar da fuska gefe hmmmm...real Fulani kenan *pulaku*☺☺☺☺👍🏼👍🏼 daga nan mr president yayi waya akan cewa a turo masa private jet dinsa sai kuma ya kwantar da yaron gefen mamansa yace
"Ki kula dashi ina xuwa baxan Dade bah..saura kunya yasa ki barshi ya fado kasa"
Dariya sosai sukayi gaba daya, mr president yasa kai ya fice a nan ne ta samu ta karewa yaron kallo
Sak!! Yana kama da uban kamar an tsaga kara. Wata nurse CE ta shigo rike da wani tray da wani Dan container tana mata sannu da harshen turanci ta samu kujera ta xauna nan ta mika mata wani babban mug cup shuairat ta karba tana binta da ido wani karamin flask ta daga ta siyaya mata wani hadadden tea mai kauri sai qamshi ke tashi ga kuma Tiririn da yake nan ta umarci shuairat ta shanye ckn zare ido take kallonta aikuwa matar ta hada rai nan da nan tasa a baki a hnkli ta fara sha sai kuma taji dadinsa don haka ta cigaba da kurba matar ta ajiye containern da tazo dashi ga mmkin shuairat abun gasa nama ne da jajayen gawayi a kasa nan matar ta fara gashin tanayi tana juyawa har yayi dai2* yanda take so ta xuba a plate ta turawa shuairat. Gaskiya naman ya gasu woww....kan ta Ankara ta cinye fiye da rabi tayi nak! Ta mikawa matar plate tana godiya daga nan ta bata wasu magunguna tasha sannan ta fara bata shawarwari dangane da ydda xata kula da kanta.
1hr leta shuairat ta fara bacci bayan tafiyar wannan nurse din..mr president ne ya shigo tare da sallama ya tsaya a kanta tana bacci ckn kwanciyar hnkli jankim CE ta shigo tana murmushi ta dauki yaron tana masa dry mr president baya son tashinta don haka y dagata kamar wata karamar yarinya jankim tabi bayansa da jaririn. Wani lungu sukabi Suka haura xuwa lift, last floor sukaje shuairat ta lafe a jikinsa ta cigaba da barcin.bayan sun iso last floor din can harabar wajen Suka nufa haba sai kawai na hango bash tare da wasu mutane 3 ckn bakaken suit ga private jet nan mai Karen kyau a gefensu suna xuwa kowa ya shiga ,har jankim tana yaba kyawun jirgin ya hadu sosai ga manya2* Leda seats masu kyau.tana rungume da jaririn bayan kowa ya shirya pilot ya tada jirgi Suka tashi don dawowa kasarmu mai albarka
*Nigeria*
🛩🛩🛩🛩🛩
Ni *Ree* nace musu safe trip perfect couples😘😘😘😘😘
Ku biyoni.........
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*71*
By *Reefat yahya*
Duk yanda Mr president yaso a wuce da Shuairat xuwa gidansa bai samu bh momsi taki amincewa tace lallai a wuce da ita gidan iyayenta babu yanda ya Iya dole ya hakura . gidan cike yake makil da jama'a cki kuwa har momsi da daddy, Shuairat kam dakin mama ta wuce bayan ta gaisa da surukan nata .momsi kuwa murna fal ckn ranta tana rike da jaririn anata musu barka.
Kwanciya tayi bayan kankanin lokaci anti mairo ta hada Mata ruwan wanka bayan ta gama ta sake zama ckn ruwan zafi Wanda aka tafasa da bagaruwa da magarya kamar zatayi kuka dole haka ta xauna acki .bayan ta fito aka kawo mata kunu da kuma tuwon semovita da miyar kuka ta xauna ta.cInyeshi Tass..sannan tabi lfyar gado bacci mai nauyi ya dauketa.
Da dare tana xaune bayan an wanke nonon ta fara bawa yaron yana tsotsa umaima ce ta shigo tare da sallama a gefenta ta xauna tana me sunkuyr da kai kasa ,Shuairat ta lura da ita tace
" umaima lfy akwai wata matsala ne?
"Umm..dama anti nazo ne domin na baki hkri kan abubuwanda suka faru a baya/, don Allah ki yafemin kiyi hkri"
"Dama don wannan ne? Ki kwantar da hnklinki ni ban taba rikeki a xuci bah"
"Nagode anti insha Allah daga yau ki daukeni a matsayin Ya'r da kika haifa ,ni kuma ina son ki xamo uwa a gareni"
"Nagode umaima insha Allah nayi alkawarin rikeku tskani da Allah ..Allah ya bani ikon cika alkawarin"
"Ameen"
Daga nan suka cigaba da hira sallama suka ji shukrah ce ta shigo sai wani yatsina take Shuairat dai tayi mamakin hakan Amma bata nuna bah..gaisuwa kawai sukyi bbu wata hirar arxiki tayi mata barka bayan yan mintuna tace xata tafi daga nan tasa kai tayi tafiyarta ko uffan bai hadata da umaima bah.
Bayan tafiyarta Shuairat tayi Jim..tana tunanin wannan sabon sauyin umaima ce tace mata
"Mom Shuairat kada kiyi mamakin ganinta ckn wannan yanyin ni nasan meyasa ta miki haka"
Daga nan ta labrta wa Shuairat irin xaman da tayi a gidan da kuma abubuwan da suka faru lokacin da take gidan bash.dariya sosai Shuairat tayi sannan tace
"In banda shukrah da kishin hauka ni me nawa a cki idan ma kuna soyayya da yaya?
" oho..maybe gani takeyi tamkar dake ake hada baki ana cutar da ita "
"Allah dai ya kyauta irin wannan ai ba kyau cos zatone n kuma zato kuma kowa yasan xunubine koda ya xamto gaskiya"
"Hakane..Allah de ya shirya"
"Ameen"
Jankim ce ta shigo a gajiye ta fda gado tana maida numfashi murmushi Shuairat ta fara mata magana da turanci
"Ina kika shiga tunda muka zo ban kara ganinki bah"
" bari kawai..nagaji sosai , muna tare da sultan "
"Lallai kinsha surutu kuwa"
"Ni ina son yaron sosai...Shuairat mutanen garinku suna da kirki "
"Da gaske?
" ehh...suna da karamci naji dadin xuwa kasarku"
"Nagode jankim"
Daga nan ta fito da magunguna ta bata tasha suka cigaba da hira karar wayar Shuairat ce ta katse su Mr president ne ya Kira.
Ckn natsuwa ta Daga
"Hi swt hrt"
"Don't swt hrt me...bayan kin manta dani "
Ya fda ckn tsigar wasa tana dariya tace
"Bahaka bane kayi hakuri wllhi baccin gajiya ne"
"Toh na yarda ya kike ya little dasu sultan"
"Lfyan mu kalau ya ka koma gida"
"Alhamdllh but nima ban Dade da shigowa gidan bah cos muna tare da jama'a a gidanku dasu daddy da baba"
"OK ya gidan toh"
"My lady u need to c d house.. Gaskiya gidan yayi tubarakallah..bash yayi kokari sosai Allah yasaka masa"
"Ameen..but kana ta yabashi gyara fa kawai yasa akayi"
"Yh I know..but samun Wanda xai kula maka lamura ma ai abun farin cki ne ,Amma gidan ba dadi "
"Haba meyasa?
" hmm..kinsani ai! Bcos baki kusa dani daz y, gaskiya na shaku dake sosai I'm realy missing u wllhi"
"Eyya my man sorrie...kayi hakuri ka daure just d matter of few days ne I miss u more"
Haka suka cigaba da soyewarsu ta waya jankim de ta xuba ido kawai tunda batajin me suke fada.
Umaima kuwa tana adu'a a ckn xuci itama Allah yasa bash ya sota.
Ku buyoni..Lov u all
*wannan page din naki ne kawaalliya romon jaba @ nanastically😘😘*
Lov u my fans n tanx 4yah support also my tanx goes to *nazeer Adam* of ~voice of ohr~
Tnx to all....
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*76*
BY *Reefat yahya*
1wik sukayi a garin mubi mr president yaji dadin zama a garin yanayin weather dinsu ya burge shi sosai don haka ya nemi siyan fili a garin daga nan Suka wuce yola Airport Suka wuce nan Suka hau flight xuwa birnin tarayya.
A gajiye shuairat ta fada gado saboda hanyar mubi xuwa yola da dan tazara tsakaninsu, bayan ta huta kadan ta fada wanka ta fito kenan mr president ya shigo rike da salman yana murmushi yace
"Ke kuwa haka akeyi...daga dawowa se ki gudu dakinki kin bar min daddy na da yunwa "
Dariya takeyi tace
"Wannan Dan lukutin daddyn naka ya gama tsoseni yana ramar dani"
Ckn wasa ya harareta yace
"Wato daddyn nawa ne Dan lukuti koh...shikenan bari na kira daddyn Lagos sai na sanar dashi abunda kika fada"
"Lahh..rufamin asiri nikam ba ruwana wllhi"
Daga nan ta karbe yaron ta xauna a gefen gadi dama towel ne a jikinta nan ta bude ckn style ta fara bashi nonon yana sha mr president ya xauna a gefe ya tallabo kumatu yana kallonsu yana murmushn jin dadi..shikam de yayi sa'a a duniya babu abunda ya rage bai mallaka bah daga ya'ya har dukiya ga kwanciyar hnkli da koshin lafiya ga kuma mace ta gari wacce ta wadata shi da komai a hnkli ya furta
"Alhamdulillh"
Shuairat ta juya Suka hada ido tace
"Lfy my man? ...naga kam zauna kayi shiru"
Ya taka ya dawo kusa da ita ya xauna yana murmushi yace
"Ina godewa ubangiji ne da ni'imomin da ya bani a rayuwa ..tabbas babu abunda narasa a nan duniya shiyasa nake godewa Allah da ya bani komai na rayuwa cki kuwa harda ke"
Ya karasa maganar yana shafa kumatunta wani dadi ne ya xiyarci xuciyar shuairat mr president ya lumshe ido sannan ya cigaba da cewa
"Ina alfahari dake akoda yaushe ..ina sonki har raina kuma baxan daina sonki ba har karshen rayuwata sabida ke kika dawo da farinciki a Rayuwa...da bansan me so bah, amma a kanki na fara soyayya nasan dadinta kuma a kanki na fara sanin menene shakuwa.shuairat ke abun alfahari na ne ..ina sonki sosai, kin soni kin zauna dani kin kular min da ya'ya na baki taba hantararsu bah kin jawosu a jiki kin maye gurmin mahaifiyarsu kin kula dani a lokacin da nake bukatar hakan baki gujeni bah kin xauna dani kin......
"Shhhhhh....haba ya isa haka pls"
Shuairat ta sanya Dan yatsa ta rufe masa baki
Wani guntun kwallah ne ya fito a idonsa yana murmushi yace
"Allow me ..kin cancanci yabo a gareni kinyi min halaccin da ba kowace mace bace xata iya yiwa mijinta"
"Nayi hakane saboda Allah da zuciya daya nayi ba don...
"I knw Ayshata..but u deserv it daz y...I rily Lov u Aysha"
"I lov u too"
Peck ya manna mata a goshi tana murmushi ta kwantar da salman a gado yana mata dariya tana kaunar yaron fiye da komai a duniya Amma kunyar mutane yasa take kawar da kai tana nuna masa halin ko in kula..hannu taji a saman kirjinta ckn tsananin kunya ta juya tace
"Haba swt hrt salman yana kallonka fah"
"Ah-ah yasha rabonsa saura ni "
Ba kunya kuwa ya fara tsotse na fulaninta shuairat kam kulle ido tayi wai tana kunyan salman🙄🙄🙄.yayi romancing dinta daga karshe ya dagata cak Suka fada bayi tare sukayi wankan sunayi suna wasanninsu irin ta masoya.
Bayan 5days ta gama ware gajiya ta shirya taje yini a gidansu ta kai musu tsarabar Adamawa da na Lagos sultan kuwa tamkar ya shige jikinta haka ma umaima yaran suna son shuairat ynxu jinta suke kamar ita ta haifesu.har yamma ta kira driver ya kaita gidan yayan ta, ta shigo da sallama a falon kida ke tashi kamar ana party a gidan carab! Suka hada ido da yarinyar shuairat ta nunata da yatsa
" kee...me kikeyi a nan gidan"
Yarinyar ta fara xaxxare ido...
🤔🤔🤔🤔 ina Suka taba haduwa???
Muje xuwa..Lov u all😘😘
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*77*
By *Reefat yahya*
Shuairat da fatee sun tsaya suna kallon -kallo shukrah ce ta sakko daga bene tana ganin shuairat ta hada face tace
"Lfy sahiba na ganku cirko-cirko"
"Uhm..emm..ba komai bakuwa kika yi daz ol"
"Dole ki ce bakuwa ai munafuka gara ma ki tattara kibar gidan nan cos yaya ba....
Shukrah ta dagawa shuairat hannu tace
"Um um...malama dakata! Nan ba gidan mr president bane bare azo ana bada order..nan gidana nane baxaki shigo har gida ki ci mutuncin bakuwata "
"Aw..haka kika CE? Shikenan a bar maganar Amma duk abunda ya biyo baya ki kuka da kanki"
Daga nan shuairat ta juya ckn bacin rai tabar gidan Allah yasa dama driver na jiranta a waje daga nan ya ja mota Suka koma gidan iyayenta, dakinta ta wuce ta fada gado ckn tsananin damuwa umaima ta shigo rike da salman ta zauna a gefe
"Lfy mom ya na ganki wani iri haka"
"Him..shukrah tana ckn hadari wllhi"
😳 me ya faru"
"Fatee lion na tarar a gidanta"
"Mom sultan wacece fatee lion kuma"
"Hmm..ynxu ne nagane meyasa shukrah ta canza min ta tsaneni ta daina kulani nasan duk hudubar fatee ce"
"Mom sultan kin ajiyeni a duhu"
"Umaima Allah ya rabamu da sharrin fatee cos yarinya ce mai hadarin gaske..ta kasance tana bin manyan mata masu kudi tana yin lesbianism dasu kuma tana asirce mazajensu ta rabasu sannan ta kwashe kudadensu tayi gaba, fatee bata taba yin aure bah kuma batada sha'awar hakan tafi son harka da mata a dalilinta mata dayawa Suka rabu da mazajensu she is a dangerous gal Allah"
Umaima ta nitsa tace
"Toh mom ina kika Santa kuma me takeyi a gidan yaya bash"
" a wani grp din watsap ne aka taba tura pix dinta dama tana grp din ta nemi wata daga ckn yan grp din da lalata yarinyar CE ta tona asirinta aka cireta daga grp tare da tura pix nata , kuma mun taba haduwa da ita a sahad stores ta cemin tana son yaya bash bata taba jin wani namiji ya burgeta ba sai shi..kuma tayi ikirarin aurensa kinga dole hankalina ya tashi "
Wani dogon numfashi umaima taja sannan tace
"Hw comz tazo gidan ?
"I rily donno...but ina zargin cewa a watsap Suka hadu da shukrah don shukrah ta fiya shiga grps sosai"
( mata a kiyaye masu shigan groups da basu sani bah muyi hnkli kada mu shiga inda yafi karfin mu ..ynxu watsap yayi kaurin suna ya zama hanyoyin yada jita-jita yada gulma da hotunan batsa , kungiyoyin cult , lesbians da sauransu don haka a kiyaye a kula asan grp din da zaayi joining Allah ya tsaremu baki daya ameen..wasu sun shiga watsap ne da wata manufar ta daban Allah ya tsaremu da sharrinsu)
Haka dai shuairat ta cigaba da bawa umaima labarin fatee har magriba tayi Suka gabatar da sallah tare da shirin komawa don umaima da sultan duk tare xasu tafi.
******shukrah kuwa ta juya gun fatee tace
"Dama kun taba haduwa ne?
Fari da ido tayi ckn kissa tace
"Laa..nifa yau na fara ganinta tamin kyau ne shiyasa na tsaya kallonta ita kuwa ko meyasa take son na bar gidan oho"
Guntun tsaki shukrah taja tace
"Rabu da munafuka haka take sai ta dinga commanding mutane tmkar ita ta haifesu wannan ma an sauke girman shugabancin da har ynxu mijintane shugabankasa kam bansan wane kallon banza zata yiwa mutane bah"
"Ohh...shuairat CE? Gaskiya tana da kyau akwai alamar Hutu a tattare da ita"
"Hmmm ba tana cin arxiki bah"
"Shiyasa nace miki ki daina sakewa mijin nan naki don zai rainaki wllhi matukar kina yawan bashi girma ze dinga nuna miki iko da gadara"
"Toh ni ya zanyi sahibah...
"Yawwa ki bude kunne da kyau ki saurareni...da farko duk wata tarba na Barka da dawowa ba naki bane, idan ya shigo ki daure fuska ki bari shi ya fara miki magana kuma ki daina yawan sake masa fuska don kar ya raunaki.matukar baki sake masa wllhi zeji tsoronki sosai, zancen girki kullum2* ba naki bane yana da kudi meyasa bazai kawo miki masu aiki bah? Ita kanwar tashi ba ke kanki cewa kikayi ko tsinke bata dagawa a gidan bah?"
Shukrah tayi shiru tana nazarin kalaman fatee🤔🤔🤔
"Kuma haka ne fah...wllhi duk abubuwan da kika fada gskiyane"
"Ahtoh...ki zauna kekam kina ta shan wahala kullum gaki nan a kitchen kamar wata mai aikin salary, wllhi kika sake kina aiki kullum ynxu zaki rame ki sabe kiyi losing shape ya auro sabuwar budurwa su zauna tare"
"Dankari...wllhi bai isa bah...cabdi ni da kishiya? Hmmmm...lallai zaa yita kuwa"
Dariyar mugunta fatee tayi tana xancen xuci tace
"Kidahuma bagidajiya kawai...xaki gane kurenki ai sai na auri mijin naki muga karshen tsiya"
A fili kuwa murmushi tayi tacewa shukrah
"Yawwa..ina fatan kinyi amfani da pils na hana daukan ciki da na kawo miki koh?
"Haba tun yaushe na shanye gaba daya mah"
Dariyar mugunta fatee tayi tace
"Ba sauki "
"Ah..kina ganin waleed kawai na Haifa Amma har na fara tsufa gashi nan da shegen jaraba "
Suka fashe da dariya har da tafawa ( hmm..Allah ya shirya).
Bayan sallar isha bash ya shigo tare da sallama suna xaune fatee ce ta amsa shukrah kam hankalinta na kan TV bash ya danyi Jim..sannan yace
"Shukrah tafiya ki sameni a daki"
"Me kake son gayamin ai wannan Ya'r uwata ce koma menene kam fada kawai"
Murmushi mai ciwo yayi sannan yace
"OK dama tafiyace ta kama ni
ynxu jirgin 10 xamu bi xuwa chicago"
"Aw..toh yayi kyau a dawo lfy"
Daga nan ta cigaba da kallonta ran bash ya baci sosai haka nan ya juya ya dauki jakarsa yabar gidan xuwa gidan iyayensa don waleed ma yana can..kuma duk shirin fatee CE ta CE shukrah ta mayar da waleed gun iyayen bash don ragewa kanta dawainiya.
Karfe 11 Suka kwanta bacci shukrah ta gama shirinta Sab...dama irin wannan Damar take jira ,ta tashi daga dakin da aka mata masauki ta xuba wasu kwayoyin magani a ckn exotic mai sanyi dakin shukrah ta wuce kai tsaye ta tura kofar shukrah tana danna wayarta da alama chat takeyi
"Sahiba bakiyi bacci bah"
"Mtsww wllhi na kasa baccin kuma wani tsoro ne ya shigeni "
"Haba dai..ko zaki zo mu kwana tare"
"Bazan takuraki bah"
"Aa ba komai wllhi"
"Toh nagode ..ga juice fah"
"No..kisha kayanki am ok"
"Kyamata kike yi? Ok sorry "
"Haba sahiba wace irin kyama kuwa"
Nan shukrah ta tashi ta karbi cup din fatee tana murmushn samun nasara aikuwa ta shanye gaba daya ta ajiye kofin...fatee ta kwanta a gefe dama wata Ya'r vest CE a jikinta.bayan 5mins shukrah taji gaba daya jikinta ya mutu ga kuma muguwar sha'awar da ta taso mata se maida numfashi take
"Lfy maman waleed"
"Uhmm..wllhi bana jin dadin jikna ne"
"Kodai kin fara missing din maigidan ne"
"Wllhi kuwa"
"Ok bari na taimaka miki"
"Taimako? Hw?
Bata Ankara ba taji bakin fatee ckn nata tana mata wani kalan kiss da koh bash bai taba mata irinsa bah..sai kuma ta fara shafa na fulaninta tana murzasu hankalin shukrah ya gushe nan itama ta fara maida martani haka dai Suka kasance har after 12 daga nan kuma fatee ta tura yatsanta a gaban shukrah ta fara wasa dashi har kururuwa shukrah take fatee shu'uma CE sosai...
(Hmm Allah ya tsaremu)
Muje xuwa
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*78*
By *Reefat yahya*
Da safe shukrah ce ta fara tashi ganin kanta babu kaya a jikinta yasa ta fara tuna abunda ya faru...nan kwakwalwarta ya tuna mata abubuwan da Suka faru a daren jiya, wani wawan mari ta sakarwa fatee ba shiri ta farka tare da tallabo kumatu wani Marin shukrah ta sake ajiye mata tare da cewa
"Azzaluma! Munafuka! Mayaudariya! Dama halinki kenan?...Allah ya isa tsakanina dake bazan yafe miki bah, kuma ynxu zaki tashi ki barmin gida macuciya...tirrr da hali irin naki"
Tana me xubda hawaye ta fada bayi wanka tayi tare da daura alwala sannan ta fito fatee bata dakin haka tayi sallah tana istigfari tana kuka tare da yin Allah wadai da hali irin na fatee.
Fatee kuwa dariyar mugunta tayi tare da cewa
"Yarinya ai kuka ynxu kika fara ...mu xuba nida ke kuma wannan marin se na dau fansa akai"
Daga nan taja akwatinta tabar gidan mai gadi yana mamakin fitan safiya irin haka.
Bayan kwana3 bash ya dawo daga tafiyarsa bai samu wani tarban kirki ba don kuwa har ynxu tana amfani da hudubar fatee ..sai wani hada rai take.
******shuairat CE zaune a falonta daga gefe kuma salman ne yana kwance ckn gadaje irin na kananan yara umaima ta shigo tare da sallama a gajiye ta fada kan kujera
"Yadai ..yan matan final year"
"Hmmm..mom wllhi na gaji sosai, exam din yau de se adua"
"Allah ya bada sa'a"
"Ameen...don Allah mom sultan ki tayani da adua"
"Don't worry u'll pass insha Allah ..ki kwantar da hankalinki baki da matsala"
"Nagode"
Waya ta kira masu aiki Suka shigo mata da abinci bayan ta gama ci shuairat tana murmushi tace
"Albishirinki"
"Goro"...
"Fari ko ja?
"Ummm...se wanda kika xaba amma xan baki fari Sol"
"Yawwa..gobe insha Allah dad xe bude textile industry a kano ki shirya flight din....
"Yeaaa...umaima bata bari ta karasa ma ta fada jikin shuairat ta rungumeta tana dariya"
"Nidai kada ki karyamin mata da shirmen nan naki"
Mr president ne yayi wannan furucin a yayinda yake shigowa nan kuwa yayi sallama ya koma kusa da shuairat ya xauna umaima ta xare jikinta tana murmushi tace
"Congrats dad"
"Tank u ya exam"
"Alhamdulillh"
"Allah ya taimaka ya bada sa'a kuma Allah yasa a gama lafiya"
"Ameen dad nagode"
"Ina fatan de baki da examz gobe "
"Ehh..har jibi ma bani dashi"
Dariya sukayi shuairat tace
"Ina ruwan umaima sarkin son yawo"
Umaima tana dariya tace
"Allah ina matukar son kano ne"
Dad ya juya yana murmushi yace
"Kodai a can surukin nawa yake"
Shuairat tayi saurin cewa
"Who knows ..nifa ban taba ganin wani yazo wajenta fah"
"Kyaleta..na bata nan da 1month ta fito da miji don tana gama final examz nata na next semester da 1week zan aurar da ita"
Umaima ta shagwabe fuska tace
"Haba dad..kamar ka gaji dani"
"Toh umaima zaman me zakimin? So kike na ajiyeki nayi ta kallo?..ynxu idan wani ya shigo ya ganki tare da Aysha ma ai se a rasa wacece matata a tsakaninku"
Shuairat me xatayi inba dariya bah..umaima kuwa tamkar xatayi kuka nan ta tashi tana tafiya dad yace mata
"Mark my words girl..am not joking"
Shuairat ta juya tana kallonsa tace
"Da gaske kake?
"Yeah...am serious wllhi, matukar lokacin da na bata ya wuce bata gabatar da kowa bah ni zan zaba mata duk wanda naga dama"
"Haba swt hrt ya xakayi haka"
"Don't worry..u will c Allah ya nuna mana lokacin"
"Ameen...
Nan ya jawota a jikinsa yana cewa
"Com here!..kin ajiyeni ko wlcm kiss baki min ba kun cikani da surutu"
Wani passionate kiss ya fara mata dakyar ta kwace kanta tana cewa
"Haba falo muke fah..baka tunanin wani ya shigo"
Murmushi yayi yace
"Babu mai shigowa don kuwa na basu rules na gidan babu wanda zai shiga last floor matukar ba ke kika nemesu bah"
Bai jira amsarta ba ya cigaba da kissing nata salman ne ya farka yana Neman abincinsa ba shiri Suka sake juna mr president ya shafa kai tare da cewa
"Gaskiya daddy na kana yawan shiga hakki na fah"
Dariya shuairat take masa sannan ta dauki salman tana basa nono mr president kuwa ya xauna a gefe yana masa wasa yaron se dariya yake
Shuairat tace
"Kana sa shi dariya idan ya kware ba ruwana"
"Da ruwanki"
Suna hira suna dariya.
A can ckn daki kuwa umaima ta kwanta tayi shiru tunanin kalaman mahaifin nata take ..tasan halinsa idan ya fadi magana baya canzawa , hankalinta ya tashi tabbas akwai matsala ita tasan duk duniya babu wanda take so sama da bash amma har yau bai furta yana sonta bah shin ya xatayi?
Zuwa xatayi ta zayyana masa halin da take ciki ko kuwa mahaifin nata xata fadawa? Haka ta kasance ckn rudani dakyar ta tashi ta shirya kayanta misalin 4pm jirginsu ya daga xuwa kano tana faman Neman bash a airport Amma Sam bata ganshi bah.
Bayan sallar isha suna zaune a falonsu dama mr president yana da gida a garin kano don haka can Suka sauka falo 2 ne a gidan da dakuna 6 se kitchen da dinning area daga waje kuma bangaren baki ne. Xaune suke a dayan falon shuairat tana kallon news umaima ta xauna shiru ta buga uban tagumi sultan kuwa yana wasa da salman , kamar daga sama Suka jiyo sallamar bash ya shigo tare da waleed nan kuwa sultan ya ruga a guje yayi hugging dinsa
"Oyoyo uncle Nah..
"My boy ya kke "
"Lfy uncle nayi kewarka sosai kuma nagode da ka kawomin kani Nah"
Nan sultan ya rike hannun waleed Suka koma gun salman Suka cigaba da masa wasa. Bash ya xauna Suka gaisa da shuairat tna kallonsa tace
"Ina maman waleed na dauka tare xaku zo"
"Nop...na barta a gida"
"Y?...haba my yaya "
"Bazaki gane bane baby..dama ina son muyi wata magana amma se mun koma ABJ"
"Hop de lafiya"
"Umm..kedai ki bari mu koma"
"Toh..Allah ya kaimu"
"Ameen "ya amsa a gajarce yana satan kallon umaima wacce tayi nisa ckn tunani yayi Dan kasa da Murya yace
"Ita waccan meyake damunta"
Murmushi shuairat tayi sannan tace
"Ita da dad ne as usual"
Daga nan bash ya tashi ba tare da ya kalli bangaren umaima ba ya sallami shuairat yayi ficewarsa.
Hmmm...wace irin magana bash xeyi da shuairat kodai batun umaima ne????🤔🤔🤔🤔
Muje xuwa.....
[2/21, 2:41 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*79*
BY *Reefat yahya*
10pm mr president ya shigo ya sanarda umaima ta hadawa bash tea ta kai masa yana dayan falon xuciyarta na harbawa dole ta tashi ta hada sai kuma ta xumbula dogon hijab ta nufi falon ta shigo tare da sallama firgigit ya amsa dama yayi nisa ckn tunani suna hada ido tayi saurin dauke kanta nan ta ajiye masa cup din ta juya xata tafi ya kira sunanta a hnkli
"Umaima!
Cak...ta tsaya ba tare da ta juya bah ya sake cewa
"Dawo ki xauna"
Ba musu ta dawo ta xauna a kujerar da yake kallon nasa
"Umaima meyake damunki"
"Kaima meyake damun ka?
Murmushi yayi wanda ya Kara fito da kyawunsa yace
"Ni nace miki wani Abu yana damuna ne?
"Toh.. Ni na gaya maka nawa ne?
"Umaima fuskarki ta nuna kina ckn matsala tell me"
"Kaima ai fuskar taka ce ta nuna hakan"
Shiru yayi daga bisani yace
"Bansan yaushe kika fara boyemin matsalolinki bah..da can baya har nemana kike idan kina ckn matsala Amma ynxu ki canzamin I donno y"
"Hmmm...naga babu amfanin hakan ne shiyasa"
"Haba umaima...don na kasa furta miki Kalmar so?
😳😳😳😳 ta daga kanta Suka hada ido tayi saurin sauke nata daga ta mike zumbur ta bar masa falon.tagumi bash yayi..shidai yasan yana matukar kaunar umaima tun ba yau bah Amma Sam ...ya kasa gaya mata hakan don gani yake tamkar tafi karfinsa bata dace dashi bah, mahaifinta babban mutum ne mai arziki shiyasa yake ganin kamar soyayyan nasu baxata yiwu bah..duk da cewa ya gane irin tsananin son da take masa Amma shi bazai iya tunkarar mr president da wannan zancen bah.
Umaima tana kwance bacci ya kaurace mata sai tunanin kyakkyawar fuskar bash take gani ..tana sonsa kamar ta hadiyeshi Amma tayi alkawarin danne wannan son matukar bai fito ya furta cewa yana sonta bah ta gwammace sonsa ya zamo ajalinta akan ta bude baki ta gaya masa duk da yagane halin da take ciki.
A bangaren bash ma hakan ta kasance sai faman sake2* yake ga uwa uba canjin da ya fuskanta a gun shukrah. ..kwata2* ta daina kulasa abinci ma sau1 take a rana ga kuma bukatarsa Sam ta daina amincewa dashi..abun duniya ya masa yawa dakyar bacci barawo ya saci wadannan masoyan biyu.
Taro yai taro jamaa ne makil duk inda ka duba ga kuma yan Chinese yawanci sune ma'aikatan katafaren kamfanin mai suna
*AS4 textile industry* bayan an kaddamar da bude sabon kamfanin aka raba abinci da sauran abubuwa daga karshe aka rufe taro da adua ga yan jarida nan birjik sai daukan rahoto suke..ckn kamfanin Suka shiga tare da iyalansa da sauran abokan arxiki daddy ma ya halarci taron yana rike da salman duk yawon da suke story building ne mai kyawun gaske ga ofishin maaikata nan birjik abun de ya hadu.
Har bayan azahar Suka dugunxuma xuwa gida dama da masu aiki Suka zo don haka bayan sunyi sallah Suka baje a dinning, daddy shuairat mr president umaima sultan bash waleed se kuma salman take hannun kakansa suna cin abinci suna barkwanci gwanin sha'awa daddy yayi gyaran murya ya fara magana
"Dama zancen umaima ne boy, akwai wani abokina yace yana nemawa dansa aurenta shine nace sai nazo zamuyi maganar"
😳😳😳😳 umaima ta zare ido tace
"Haba daddy...
"Ke rufemin baki shashasha kawai..kina ajin karshe a jami'a me ya rage miki?
Mr president ne yace
"Yi hakuri daddy daman nima na gaya mata idan ta gama da 1week zan aurar da ita kuma...
"Gafara can...dama ba kai kake biye mata bah, idan ba kam dage bama da zan bari tayi karatun jami'an ne?...toh nidai na gama magana aure de dole tayi ko taki ko taso"
"Sorry daddy Nah..ba ina goyon bayanta bane but na bata damane ta fito da wanda take so sai ayi auren"
"Bana son shiririta ita wannan ka taba ganin wani yazo wajenta ne? Ba ta dauki girman kan tsiya ta dorawa kanta bah..gani take tmkar tafi karfin kowa "
Sai ynxu shuairat tasa baki tace
"Allah ya huci xuciyarka daddy insha Allah xaayi auren nan ba da dadewa bah"
Sai ynxu yayi murmushi ckn jin dadi yace
"Yawwa Ya'r albarka ynxu naji magana..kinga mijin naki da ya'rtaki duk mashirmata ne rabu dasu "
Murmushi shuairat tayi ta kashewa mr president ido sannan tace
"Don't worry daddy kam kwantar da hankalinka "
"Tank u my Dota...am now counting on u"
"Trust me daddy"
Daga nan Suka fara hirarsu mr president kam yasha jinin jikinsa bash kuwa sai Satan kallon umaima take ita kuwa ta cika tayi famm..murmushi yayi ya mata gwalo batare da kowa ya gani bah yace
"Gaskiya gara a aurar da ita da wuri daddy..don kuwa ta fara tsufa"
"Yawwa ganemin hanya dai basheeru..mu a zamaninmu mace tana 13-14 zaa aurar da ita Amma ynxu yahudu ya bata muku rayuwa kuna nan kuna biyewa bokon banza"
Umaima dama kiris take jira nan ta fara kuka ta tashi tabar dinning daki ta wuce shuairat ta harari yayan nata tace
"Se kaje ka lallabata ai..kasan halinta sarai Amma kake tsokanarta"
Daddy yace
"Rabu da wannan shagwababbiyar "
Dama abunda bash yake so kenan..don haka ya tashi yabi bayanta mr president kuwa ya cigaba da cin abincinsa sultan kuwa sun koma falo da waleed. daddy ya juya yana kallon Dan nasa yace
"Boy wai fushi kayi "
Shiru bai amsa bah daddy ya shafa kansa yace
"C'mon..smile my boy, kam tsufa ai fushi ba naka bane "
Ya hada rai yace
"Toh..daddy ba Kaine kake min fada akan laifin da ba nawa ba"
😳😳😝😝😝shuairat bata San lokacin da dariya ya kubce mata bah tace
"Oh...dad sultan yaranka suyi shagwaba kaima kayi?
"Daddy ka jita koh..
"Yi hakuri boy din daddy duk laifina ne OK"
Haka daddy ya cigaba da lallaba mr president tamkar wani karamin yaro shuairat kuwa sai tsokanarsa take tana mamakin irin son da daddy yakewa dannasa Sam baya so yaga bacin ransa ko kadan.
Umaima kuwa ta fada gado tana rusa kuka ..ita ba kalaman bash ne damuwarta ba aa xancen hadata da wani da daddy yayi ne ya daga mata hankali ..shikenan ta rasa bash har abada! Ya shigo ya tsaya yana kallonta bata ji shigowarsa bah ya nemi kujera ya xauna a hnkli ya furta
"Tashi ki xauna magana xamuyi"
Ta juya jajayen idanunta tace
"Baka da abunda zaka gaya min kawai ka fita ka barmin daki "
"Look umaima am sorry bansan kalamai na zasu bata miki rai haka bah...am sorry pls"
..hmmm lallai ma wato ba zuwa yayi yace yana sonta ba kawai yaxo bata hakuri akan silly maganar da yayi dazu? Bash y? Meyasa yake wahalar da xuciyRta?...umaima CE ke wannan tunanin hawaye wani na bin wani ta nuna masa kofa ckn tsawa tace
"Out of my sight ..now!
"Sorry...
"I said...out...nowww!
Ta karasa ckn daga murya nan ya juya ya fita ckn bacin rai ita kuwa ta kara fashewa da wani sabon kuka
"Shikenan na rasashi har abada"
"Baki rasashi bah matukar ina Raye...babu abunda zaki nema a duniya ki rasashi umaima"
😳😳😳 ta juya don tabbatar da abunda kunnuwanta Suka jiye mata ...carab! Suka hada ido....
Muje xuwa..
0 comments:
Post a Comment