salam readers ina mai Baku hkri akan postinng din page 81 da wata tayi wacce bansan ko wacece bah( don't mind she is just trying 2b popular ne😜😜) but pls a kiyaye ban amince wata/wani ya canza min story bah duk wanda ya sake yi Allah ya isa kuma I'll take serious action about it..tnx fans.Lov u all😘😘*
8pm jirginsu na private ya sauka a babban kamfanin mr president daga nan driver ya saukesu gida bash kuwa gidan iyayensa ya wuce ...
Washegari sun hallara wajen cin abinci, umaima ta fito ta jawo kujera ta xauna tare da cewa
"Morning dad..morning mom"
Shuairat ce ta amsa
"Morning ya gajiya"
"Akwai fah...wannan ma flight kenan , Allah nayi bacci mai nauyin gaske"
"Yawon da kikayi a can ai is not easy"
Umaima ta marairaice tana kallon dad tace
"Dad shine ko hi babu"
Yana kurban tea ya kalleta yace
"How r u"
"Am fine dad how was nyt"
"Alhamdulillh"
Shuairat tana kallon sultan tace
"Boy ina alkawarin mu"
Murmushi sultan yake tare da cewa
"Mom ban manta bah..kin manta ke kika gaya min cewa idan babba yana magana kada na sa baki "
"Hakane my boy Ashe dai baka mantuwa"
"Morning anty umaima "
Ta shafa kansa tace
"Morning mom's boy"
Daga nan Suka cigaba da karyawa...wayar mr president ne ya hau ruri numban daddynsa ne nan ya daga tare da sallama
"Daddy Nah"
"Boy an tashi lfy"
"Lfy alhamdulillh ya momsi "
"Lfy kalau ya iyali"
"Duka suna nan lfy "
"Masha Allah..dama xancen yaran nan ne gode idan Allah ya yadda muna nan tafe "
"OK Allah ya kawoku lfy"
Daga nan Suka ajiye wayan tare, umaima wacce ta kura masa ido kirjinta na dukan 3-3 shuairat ma haka ..ya lura dasu Amma ya share ya cigaba da cin abincinsa daga bisani yace
"Gobe su daddy zasu zo tare da wannan mutumin "
😳😳😳
Umaima ta xare ido ckn firgita ta juya tana kallon shuairat. Shuairat tayi karfin hali tace
"Kana nufin....
Hannu ya daga mata yace
"Bana son jin komai..ba sharawa nake nema bah"
Daga nan ya tashi ya haura staircase xuwa floor dinsu, umaima kam hawaye sharr..wani na bin wani shuairat ta rasa ya xatayi tace
"Calm down princess evrtin will b fine"
Ckn Muryar kuka tace
"Wani irin fine mom..kina jin abinda dad ya fada, nidai shikenan an rabani da masoyina😫😫"
ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi shuairat ta hau lallashi daga bisani tace bari taje gun mijinta.
A can dakin mr president yana kwance yayi nisa ckn tunani ..har ga Allah shima yafi son ganin farin ckn umaima yafi son ta auri bash ko ba komai ya dade yana tare da basheer yasan halayensa mutumin kirkine ga rikon Amana ..amma wancan yana Lagos basu taba ganinsa bah basu San halayensa bah , kawai babu yanda ya iya adua shine mafita Allah ya xaba musu mafi alheri.shuairat CE ta shigo tare da sallama dakyar ya amsa domin shima yana ckn damuwa a hnkli ta karisa kusa dashi ta xauna yana kwance yana kallon ceiling daga ganinsa xaka San cewa yana ckn matsala tayi shiru ta rasa abun fadi , ta matso kusa dashi ta Dora kanta bisa kirjinsa tana jin karan bugun zuciyarsa.sun dau 5mins batare da wani yyi magana bah ..peck ta masa a kirji sannan ta daga kanta tana mai kallonsa ckn wata murya mai sace xuciya ta fara magana
"Swt hrt...duk da bansan meyake damunka bah..but ina son ka kwantar da hnklinka ka mika lamuranka ga ubangiji shi zai magance maka komai ckn sauki xai sama maka mafita, saboda haka bana son ganin kana daga hnklinka plss...
Yaji dadin kalamn nata ya juya idanunsa suna kallon kyakkyawar fuskarta yace
"Hakane my lady...Allah shike maganin komai, u knw wat? Ina son ganin farin ckn umaima but baxan iya rejecting offer din daddy na bah"
"Yeah..nasan kana son ta auri yaya but baka da ikon yin hakan, sabida daddy mahifinka ne baxe ji dadi bah idan ka nuna rashin amincewarka"
"Daz wat am thinking Aysha..Allah bana son auren nan da xaa hada"
Shuairat ta jawosa a jiki ya kankameta kamar xeyi kuka yace
"Ita marainiya ce nafison ta auri Wanda xe riketa har abada ..nasan halayen basheer na xauna dashi na tsawon lokaci bamu taba samun sabani dashi bah...
"Is ok swt hrt Allah xai kawo mana mafita don't worry ok! I promise xanyi magana da daddy insha Allah xamuyi nasara "
"Ok...Allah yasa"
"Ameen..Nagode Ayshata I Lov u so much "
"Lov u more swt hrt"
Daga nan ta tura bakinta ckn nasa sun fada duniyar masoya...
Umaima tayi kuka mai Ban tausayi sultan tun yana bata hkri har ya gaji ya daina.dakinta ta shige ta kulle kofa ta cigaba da kukan ganin bashi da amfani yasa ta Ciro wayarta ta kira bash bugu 2 yayi picking tare da cewa
"Baby Nah..I rily miss u"
Nan ta fashe masa da kuka ckn tsananin tashin hnkli yace
"Baby wats wrong.. Tell me don Allah wani Abu aka miki ne?
Kukan takeyi dakyar tace
"Ina son ganin ka"
Murmushi yyi yace
"Oh bby shagwaba..I tot is somtin serious fah, kawai kice kin fara missing dina "
Bata ce komai bah ta cigaba da kukan da take ya sake cewa
"C'mon is ok mana! Kukan ya isa haka pls..ok toh gani nan xuwa ynxu shikenan koh"
Kai ta gyada tamkar yana ganinta daga nan ta kashe wayar..
-40minz later-
Bash ya kirata akan cewa yana garden din gidansu yana jiranta , hijabi kawai ta Dora akan doguwar rigar dake jikinta ckn sanyin jiki ta karasa babban garden din gidan nasu Wanda yake dauke da manyan bishiyoyi da flowers masu kyau ga kuma swimming pool a gefe...yana xaune akan wasu fararen kujerun da aka tanada a lambun yana ckn suit ash color da red shirt a cki ya mata kyau sosai ta kura masa ido tana kallonsa har ta karasa tare da sallama shima kallonta yake ya tashi ya tsaya ita kuwa ta sunkuyar da kai tana mai kallon kasa ckn tsananin mmki yace
"Subhannallhi..bby kukan ne yasa idanunki Suka kumbura haka? Y...??
Shiru tayi ya cigaba da kallonta ya sake cewa
"Tlk to me pls"
Wani sabon kuka ta fara yi nan take bash ya rude hnklinsa ya tashi ya fara tambayarta me yake sata kuka..ta sagaita kukan tare da cewa
"Gobe zasu zoh.."
"Su waye"
"Daddy da wannan mutumin "
"Wani mutum?
"Wanda xai aureni ...xasu..
Bata karasa vah bash ya jawota ta fada jkinsa ya rungumeta sosai tamkar ya maidata cknsa hawayene Suka fara bin kumatunsa jikinsa har rawa yake ita ma kukan takeyi da karfi bash yace
"No...!!! Bazai yiwu bah...babu wanda xai rabani dake ..no!! It can't hpn I will Neva allow dat to hpn , u r my wife insha Allah"
😳😳😳🤔🤔🤔tohfah....Allah yasa...
Wayyo xaa raba laylah n majnoon😫😫😫😫😫😰😰
Fans kun amince da hakan????
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*88*
By *Reefat yahya*
Mr president ne yayi gyaran murya tare da cewa
"Ina son ganinku"
ckn tsananin jin kunya bash ya raba jikinsa da na umaima nan Suka bi bayan mr president.. Falon kasa Suka xaune Kansu na kallon kasa daga nan ya fara magana
"Bash na zauna tare da kai na lokaci mai tsawo bana taba bata min rai ko cin amanata bah, kai mutum ne nagartacce naso ace ka auri umaima don nasan ko bayan raina xaka rike iyalina bare kuma ynxu an xama daya..but unfortunately daddy yaxo min da wata magana mai girma Wanda ni kaina banso ace hakan ta kasance bah, amma da na duba cewa shi mahaifina ne bani da xabin da ya wuce na amince da hukuncinsa domin ko ni kaina idan ya umarceni da yin wani abu baxan tsallake bah talkless of ya'r da na Haifa..so am very sorry kuyi hakuri Allah ya zaba muku mafi alhri..umaima tashi ki koma ckn gida"
Ya mike ya haura sama ba tare da kara fadan wani Abu bah...ckn raxana bash ya daga kansa sun kurawa juna ido , umaima wacce idanunta sun cika da kwalla tunda dad ya fara magana hawayen suna gangarowa daga nan ta tashi ta fice tana kuka.
Bash ya share minti 30 a falon ya rasa me Ke masa dadi a nan duniya..baisan yyi nisa ckn son umaima se ynxu da xe rasata, dakyar ya tashi jiki ba karfi ya kama hnya tfy yake tamkar xai fadi jiri yake ji , hka ya cigaba da takawa a hnkli har ya kai inda yyi parking motarsa ya budeta a hnkli ya shiga cki ya hada kansa da siteri hawayene Ke fita a idanunsa ya dde ckn wannan yanayin daga karshe ya tada motar maigadi ya bude masa gate ya tafi, umaima wacce Ke kallonsa ta tagar dakinta nan ta fada gado ta cigaba da rusa kuka babu mai rarrashinta.a can bangaren mr president ma ya shiga dakinsa jiki a mace shuairat ce take kwantar masa da hnkli da kalamai masu sanyaya xuciya.
Bash bai tsaya ko ina bah sai gidan iyayensa dakin mama ya shige ya fada saman gado yana kuka wiwi kamar mace😆😆 mama ta fito daga dakin mijin nata taxo daukar abu a dakinta turus tana ta tsaya don ganin mutum akan gado ckn tsananin mamaki tace
"Lafiyanka kuwa"
Babu kunya bash ya tashi xaune yace
"Mama xasu rabani da umaima"
Mamakin nata ya wuce na farko domin kuwa bata taba Sabin cewa basheer yana kaunar umaima don ko alamar hakan bata taba gani bah duk tsawon xaman da sukayi da ita umaimar
"Wace umaima kake nufi?
"Umaim de wacce kika sani "
"Dama kuna soyayya ne da ita"
Ya tura baki ckn shagwaba yace
"Haba mama let's b serious.. Wani xaa aura mata bani ba fah, pls do somtin Allah ina sonta"
Hhhhh sabon salo wai namiji da suna hajara..bash da ya kasance yaro mai tsananin kunya yau shi yake fadawa mamansa wai yana son wata! Ikon Allah..wani Abu se soyayya so Baka San kunya bah..hmm
Mama tayi jugum ta rasa ta ina xata fara ita dai har ynxu mamaki take kan wannan lamarin dakin mijinta ta wuce nan ta sanar dashi halin da ake cki don shima ya sakko daga fushin da yake kan xancen Karin auren..tare Suka dawo dakin yana nan xaune ya buga uban tagumi take tausayinsa ya mamaye xukatansu baba ya rike hannunsa ya fara magana
"Haba babana...kayi hkri ka daure shi namiji da juriya aka sanshi , kuka baxai warware matsala bah pls stop crying"
Yasa hannu yana share masa hawayen ya cigaba da cewa
"Meyasa tun da dadewa baka sanar dani cewa kana sonta bah..but kaga ynxu is too late don...
"Pls baba is not too late..pls do somtin bana son rasa ta ka taimakamin"
Tausayi sosai ya basu..baba yace
" is ok toh..stop crying zanyi magana da shi daddy ok"
Kai ya gyada masa yana goge hawayen da Suka bata fuskarsa, haka Suka cigaba da lallaba shi dakyar yayi shiru ya daina kukan da yake, baba yace masa ya tashi ya koma gidansa firr yaki yace musu a nan xai huta xuwa yamma bayan kuwa tunda ya dawo ko gaisuwar arxiki bata hadashi da shukrah bah.
*washegari*masu aikin gidan mr president sun dafa abinci kala2* sun gyara ko ina a ckn gidan se qamshin tyraren wuta da airfreshners Ke tashi a can kitchen kuwa qamshin girkine..gidan yayi fes ya kara kyau shuairat tayi wanka ta shirya sultan da salman ckn kaya masu kyau se xuba qamshi suke , umaima tayi wanka tayi kwalliya ba laifi tana bin shawarar da shuairat ta bata.mr president kuwa fararen kaya ya saka har da babban Riga shuairat tana xolayarsa wai surukai xasu xo gaisuwa su mr president an tsufa..murmushi kawai yayi har ynxu de baya ckn walwala wannan ma don shuairat tana yawan jansa da magana ne tana son ganinsa ckn farin cki.
10am jirginsu ya sauka mr president tare da driver Suka je airport ckn jin dadin ganin Dan nasa ya karasa sukayi huggin din juna daga can gefe kuma wani dattijo ne tare da dansa ba sai ka tambaya bah mr president ya gane cewa surukin nasa ne, ckn girmamawa Suka gaisa daga nan Suka shige mota driver yaja Suka wuce gida.kyakkyawar sauka aka musu bayan sun ci abinci Suka koma falo daga nan shuairat ta shigo tare da salman da kuma sultan.. har kasa ta sunguna Suka gaisa da daddy da kuma mahaifin yaron shi kuma ya gaisheta ta amsa ckn sakin fuska ta tashi xata koma cki daddy yace
"Ah..ina zaki kuma, munxo Neman auren ya'rki ai kema magana ta shafe ki don haka yi xamanki "
Babu gardama ta xauna a can nesa daddy ya karbi salman yana masa wasa sultan kuwa yana manne da mahaifinsa.shuairat tana Satan kallon yaron yana da kyau ba laifi Amma be kai basheer Nash girma da kyau duka... Daddy ya kira umaima a waya babu bata lokaci ta fito ckn natsuwa ta gaisa dasu gaba daya daga nan ta koma kusa da shuairat ta xauna daddy yace
"Kuje Ku tattauna Ku daidaita kawananku..gashi Ann sunansa ismaeel "
Umaima tayi shiru bata ce komai bah, shuairat ta xunguri kafarta ba tare da wani ya lura da hakan bah nan umaima ta tashi tana wani nokewa wai a dole kunya take ji..falon baki Suka nufa tana gaba yana baya ta bude musu ta nemi kujera ta xauna suna mai fuskantar juna.
Yabi ta da ido tanada kyau sosai shikam ya amince da zabin iyayen nasa ita kuwa tana satar kallonsa ba laifi yana da Dan kyau Amma ko kadan baki burgeta bah hasalima haushinsa take ji don shine silar rabuwarta da Rabin rayuwarta wato basheer!
"Umaima.. Sunana ismaeel kamar yanda kika sani, nayi makaranta nayi degree ina aikine a *NPA* dake can Lagos"
"Aw..daz gud Allah ya taimaka"
ta kirkiro wani murmushn da bai kai har xuci bah..ba karamin daurewa take bah har take kulashi tana yin hakan ne don bin umarnin shuairat..
"Dafatan xaki bani hadin kai mu xauna lfy don faranta ran iyayenmu"
"Ohh..kana nufin tilasta maka ake son yi..kenan baka son auren?
"No..ba tilastani akayi bah, bin umarnin iyayena ne "
"Just tell me idan kana da wacce kake so kada ka boyemin"
"Ah.ah nidai na amince da auren ki domin kin kwantamin a rai..u have all d qualities dat I want"
Murmushn karfin hali take masa wani sa'in kuwa ta faki idonsa ta watsa masa harara karar bude Kofa da akayine ya jawao hankulansu umaima tana daga kanta sukayi ido 2 da bash 😳😳😳😳😳😳
Muje xuwa
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*89*
By *Reefat yahya*
*pals need ur pryrs pls...Allah ya biya min bukatata idan alheri ne ....Lov u all*
Fuskar basheer babu annuri ko kadan ya hada girar sama da ta kasa yana kallon umaima ismeel ya juya don ganin me umaima take kallo bash kam ko kallo bai isheshi bah gun umaima ya dosa ckn wani irin murya yace
"Ina son ganin ki ynxu"
Ya juya xai tafi tayi karfin halin cewa
"Uncle bash ga ismaeel nan , ismaeel dis my uncle basheer"
Kafin bash yayi magana ismaeel ya tashi ckn girmamawa ya mika masa hannu babu yanda ya iya dole ya mika nasa nan Suka gaisa daga nan bash yayi gaba abinsa umaima ta tashi tamkar wata munafuka ta kirkiro murmushn dole tace
"Amm..yi hkri pls 10 mins ina xuwa"
"Olryt no p"
Daga nan ta fice yana nan tsaye a bakin kofa daga waje sai cika yake yana batsewa tana fitowa bata kula dashi bah kawai jin an fisgo hannunta yasa ta firgita ta juya Suka hada ido dashi idanun nan nasa sunyi ka kamar jini ze fita da karfi yake Jan hannunta bai tsaya da ita bah se ckn dakin baki ya wurgata saman gado ita kam tsoro ya cika xuciyarta don bata taba ganinsa ckn wannan yanayin bah nan kuwa hawaye ya fara fitowa a idanunta ta fara kuka Mara sauti ..wani wawan tsawa ya daka mata seda na fadi a kasa😜😜 ckn daga murya ya fara magana
"Shiru! Shiru nace.. Just keep quite my fren, ina can ina rashin lfy xan rasaki Ke kuma kina nan hnkli kwance kuna soyayya koh"
"BB am...
Hannu ya daga bai bari ta karasa maganar bah ya cigaba da cewa
"U have notin to say umaima.. Kin nuna min halinku na mata halin yaudara da cin amana n ...
"Dakata ..kaima ka nuna min halinku na maza halin rashin hakuri da kuma mugun zargi, did u even kia to ask me ya akayi na xauna ina magana dashi...da xan so wani baxan xauna na bata shekaru da dama ina xaman jiranka bah ..dama Ku maza haka halinku yake, excuse me pls"
ta tashi xata bar dakin bash yayi Saurin rike mata hannu ta kwace sannan ta gyara tsayuwa fuskarta na kallon gefe jikinsa ya mutu da jin kalamnta shikam kishi ya rufe masa ido har ya fara ganin tmkar soyayya suke da ismaeel musamman idan ya tuna murmushin fuskarta a wannan lokacin da ya shiga ya samesu..Muryar umaima ce ta katse tunanin da yake
"Idan baka da abun fadi ni xan tafi cos na bar bako shi kadai"
Yayo kanta kamar xai cinyeta yace
"Baki da hnkli ne..wai meyake damunki ne har kina xancen wani bako a gaban idona"
Ta marairaice fuska
"Bb is risky fah..idan daddy yaje nemana bai sameni ba fah ?
" sai yazo nan ya sameki ..kinga daga nan xai San lallai baki son auren n am sure baxai miki auren dole bah"
Haka dai bash da umaima Suka kasance daga karshe ma xama sukayi suna ta hirarsu irin ta masoya sun manta da wani ismaeel a can.
Ismaeel yana xaune yana danne2* a wayarsa bayan yan mintuna ya duba agogan dake daure a hannunsa ta share 30 mins bayan kuma tace 10 mins anyways.. Ya gyara kwanciyarsa a kujera ya cigaba da danna wayarsa.a can falo kuwa suna hira ckn faraa , wayar baban ismaeel ne yayi ruri daga nan ya daga ya fita waje shuairat ta gyara xama tace
"Daddy wata alfarma nake nema"
"Fadi bukatarki ya'ta"
"Daddy xancen auren nan da xaayi ina ganin gara a hakura "
"Sabida me?
"Umm..umaima bata son auren tana da wani Wanda take so"
Dariya yayi sannan ya juya yana kallon mr president Wanda tun da Suka fara maganar bai sanya bakinsa a cki bah..daddy yayi murmushi yace
"Wato mijin naki ne ya turaki koh"
Shuairat tayi saurin girgiza kai tace
"Bahaka bane daddy, kawai gani nayi umaima...
"Aysha!
"Naam daddy"
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*90*
By *Reefat yahya*
Daddy ya cigaba da maganarsa
"Aysha kada ki biye ma mijinki , shi boko yasa a gaba idan na biye masa cewa xaiyi sai ta gama masters b4 ya aurar da ita"
"Daddy bahaka bane..dama
Hannu ya daga mata nan tayi shiru da bakinta..yace
"Zancen aure babu fashi , kuma na fasa jiran ta gama makarantar ma..bari Alhajin ya shigo"
Shuairat xata CE wani Abu baban ismaeel ya shigo tare da sallama daddy yace a kira ismaeel a waya su taho da umaima.
Yana can xaune a falon har ynxu babu umaima babu labarinta wayarsa ta hau ruri mahaifinsa ne ya daga yace
"Ku samesu a falo"
Daga nan ya kashe wayar ta tashi ya wuce falon da suke.ya karasa cki tare da sallama bayan ya xauna daddy yace
"Ina umaima?
"Uhm..tun dazu ta tafi, wani uncle waye..uhmm
Shuairat tayi carab tace
"Lahh..har ynxu basu dawo bah..dama ni nace suje ta xabi kalan furniture's da take so ita da uncle bash"
Idanunta Suka fada ckn na mr president ya harareta tayi Sauri ta tashi tsaye tace
"Bari na kirasu daddy ina zuwa"
Daga nan ta fice bata jira jin amsar su bah.
Bangaren baki ta fara xuwa tana nemansu taji murya kasa2* a dayan dakin nan ta tura kofar fuska a murtuke ta samesu suna xaune suna hira ckn kwanciyar hankali harara ta watsa musu tare da cewa
"Sai ku nuna ma duniya akanku aka fara soyayya"
Umaima ta tashi ta karasa kusa da ita
"Lfy mom sultan"kwafa tayi tare da cewa
" zaku gane ai ..kixo ana Neman ki"
Jikinsu yyi sanyi bash yace
"Sisy any progress?
"Wane irin progress..Abu yana Neman tabar barewa"
"Wat hpn"
"Muje dai kuji da kunnenku"
Daga nan ta juya tayi tafiyar ta umaima da bash kuwa sunyi jugum kowannensu yana tunani daga bisani Suka wuce falon.
Bayan kowa ya xauna daddy ya fara magana
"Ismaeel ina fatan babu matsala"
"Ba komai Abba mun daidaita mun amince da juna"
Ckn Sauri umaima ta daga kanta sukayi ido 2 dashi ta sake sunkuyar da kan, daddy ya cigaba
"Masha Allah..dama haka muke son ji Allah ya muku albarka"
"Ameen" kowa ya amsa banda bash da umaima
"Ynxu tunda sun fahimci juna ni na saka rana nan da wata 1 "
Tare Suka hada daga kai suna kallon juna babu Wanda ya lura dasu sai mr president ya kawar da fuskarsa tamkar baisan meke faruwa bah..hawayene Suka fara gangarowa a fuskar umaima ba shiri ta tashi tabar falon baban ismaeel yace
"Meyake damunta Alhaji naga kamar kuka take yi"
Murmushi daddy yake w
Sannan yace
"Babu komai nasan ta tuna da mahaifiyarta ce"
"Ka tabbata..? Kodai bata son auren ne"
"Ko kadan ..nasan tunowa tayi da marigayiya zainab Allah yajikan ta yasa ta huta"
"Ameen"
Haka Suka cigaba da hira bash ma barin falon yayi ya koma bangaren baki ya xauna ya buga uban tagumi yana Neman mafita.
Jirgin yamma su daddy Suka bi Suka koma Lagos mr president ma hankalinsa yaki kwanciya sai ynxu ya fara jin tausayin Ya'r tasa shi da kansa yaje har daki ya sameta yana bata hakuri dakyar ta daina kukan da take.
****bayan kwana 2 bash ya kwanta zazzabi ya rufeshi ya tare a gidansu yaki komawa gidansa , kullum shukrah tana xuwa dubansa ko kallo bata ishe sa bah.gashi umaima ta kashe wayoyinta gaba daya hnklinsa a tashe yake mama tana masa nasiha akan ya rungumi kaddaara Amma Sam baya sauraronta ya xama kamar wani xautacce daga karshe ya tashi ya shirya ckn kananan kaya yayi kyau sosai duk da ramar d yayi ya fada sosai , mama ta shigo dakin rike da magungunasa ckn mmki ganin yana fesa turare da alama fita xaiyi tace
"Babana ina kuma xaka je ..kaida baka da lfy"
"Na warke mama.."
"Toh ina xa ka?
"Zanje ganin umaima domin wayoyinta a kashe suke, xan duba ko lfy"
"Lfy kalau suke dazu munyi waya da Ya'r uwarka da akwai wani Abu ai kasan xata gaya min"
"Naji...Amma nikam sai naje"
Daga nan ya xare makullin mota yyi ficewarsa.
Umaima tana xaune a dai2* windon dakinta taga shigowar motar bash nan kuwa da gudu ta fito har tana tuntube masu aiki sai kallonta suke bata kulasu bah tayi hanyar last floor na kasa a bakin kofa Suka ci karo turus yaja ya tsaya...sun Dade sun kurawa juna ido daga bisani yayi karfin hali yace
"Meyasa zaki kashe min waya?
"Uhmm...dama
dama me? Just tell me dat baki damu da halin da muke cki bah, kina nan ckn kwanciyar hnkli ni ko ina fama da jinya"
Wato Kalmar da tafi tsana kenan a ce duk son da take masa Amma se ya goranta akan shiyafi damuwa da ita....
Idanunsa sun kada sunyi ja yace
"Umaima nasan kina sona Amma tsoronki ya hana ki fito fili ki nuna musu cewa baki son auren ni kike so ki aura y??
Kuka ta fara Mara sauti ya harde hannunsa a kirji ya tsaya yana kallonta daga bisani yace
"Mafita xaki kawo ba kuka bah pls"
ta cigaba da kukan
"Haba mana bby u knw I hate doz tears ki bari pls bana son ganin ki ckn wannan hali"
Ckn Muryar kuka tace
"Toh Bb ya xanyi..wane mafita xan kawo ? Ni gaba daya kwakwalwata ta toshe na rasa samun mafita kuma next week ance xaa kawo lefe"
"Wat???😳😳 next week? U know wat umaima kawai ki kira yaron ki CE masa baki sonsa kina da wani daban , daz d only solution"
"Bb ar u sure it'll work?
"Am very sure baby Nah try it"
"Ok muje na dauki phn dina yana can daki"
"Ok lets go"
Daga nan ta shiga gaba yana biye da ita a baya Suka haura xuwa sama don daukar wayarta.
Shin xata kira ismaeel kuwa??
Zai amince da bukatar tata??
Hmmm...muje xuwa
Lov u all😘😘
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞 NI DA SHUGABAN KASA💞
*91*
By *Reefat yahya*
A hanyarsu ta xuwa daukar waya Suka ci karo da shuairat tabi su da wani irin kallo sannan tace
" dad naki yana son ganinki ynxu"
Gaisawa sukayi da yayan nata sannan tayi wucewarta sum sum umaima ta tafi falon baban nata yana xaune da jarida a hannusa ta shigo tare da sallama ta nemi waje ta xauna
"Gani nan dad"
"Ki shirya gobe zaku wuce Dubai shopping Ke da Aysha"
A hnkli ta daga kanta tana kallonsa sannan tace
"Dad...
"Bana bukatar jin komai daga gareki tashi ki tafi Allah ya Baku xaman lfy"
Kuka ne ya kubce mata da gudu tabar falon a hanya ta hadu da bash yana tsaye ya jingina da bango da alama ita yake jira..
"Lfy my bby "
bata iya furta masa komai bah ta wuce bangarensu a kujera ta fada tana kuka mai ban tausayi bash ya shigo ckn tashin hnkli ya xauna kusa da ita ya fara magana ckn kwantar da murya
"Bby kullum ina gaya miki bana son wannan kukan naki amma baki ji pls stop it"
Haka ya cigaba da bata baki dakyar ta sagaita kukan ta sanar masa abunda yake faruwa shiru basheer yayi yana jin wani radadi a ckn xuciyarsa ya rasa ma wani mataki xe dauka daga nan ya tashi ya fita ba tare da ya furta ko kalma daya bah.
Umaima ta cigaba da kukan da take bash kuwa bai tsaya ko ina bah sai gun mahaifinsa wani sabon hauka ya tada musu mama kam se kuka take tana tausayawa dan nata , suna lallabashi tamkar kara tunxura shi suke baba ya rasa ya zayyi kawai ya fice ya koma dakinsa ya xauna. Mama ce ta cigaba da rarrashinsa dakyar ya tashi ya ci abinci.
***washe garin...mr president ya raka shuairat da umaima airport jirginsu ya daga xuwa Dubai ya rage dashi da sultan kadai a gida. Umaima se kuka take shuairat tana rarrashinta a haka Suka kasance a ckn jirgin ma babu abunda take sai kuka.
Bash yana xaune a ofishinsa yayi jugum..tunanin duniya ya addabesa ynxu shikenan an rabashi da umaima ?? Yau saura 3weeks auren ta da wani bashi bah ..kwankwasa kofa akayi sectry dinsa ne ya shigo ya shaida masa yayi bakuwa ba tare da wani dogon tunani bah yace a shigo da ita.yana xaune ta shigo qamshin turarenta ya gauraye ofishin gaba daya ba shiri basheer ya daga kansa fara ce Sol daga ganin hasken nata na mai ne tana tauna cingam ji kake kas! Kas!! Wata shaidaniyar doguwar Riga ce a jikinta Wanda ya matseta gam Rabin kirjinta duka a bayyane fatee kenan...hannu ta daga masa ckn salon Jan hankali tare da cewa
"Hi basheer am fateemah "
"Aw daz gud..fateema me Ke tafe dake ?
"Well..actually ba wani Abu bah illa so da kauna"
Ckn Sauri ya daga idonsa ya jefa mata wani mugun kallo bata ji ko darr ba ta cigaba da cewa
"Na Dade ina kaunar ka baaheer, a rayuwata ban taba son wani namiji bah sai kai..pls ka amince muyi aure"
Wani murmushi yayi sannan yace
"Wai ba kece Ya'r uwar shukrah da ta kawo mata ziyara kwanakin baya bah"
"Yeah...u r right anyi haka Ashe dai baka manta dani bah"
Ya juya idanunsa tamkar mai shirin yin bacci ya nuna kofa tare da cewa
"U can leave pls..
"C'mon basheer kasan nafi matar ka da komai kuma ynxu ita bata da wani amfani tunda ba haihuwa xatayi bah"
Ya bude ido sosai yana mamakin kalamanta ya akayi tasan shukrah baxata kara haihuwa bah??...wato shi ya rike maganar as sirri bai sanarwa kowa bah amma ita tana can tana yada kanta tana tona masa asiri..tirr da halaye irin nata.
"Kayi shiru my love, ko kana bukatan lokacin tunani?
Ya watsa mata wani mugun kallo tare da cewa
"Tunani? Koda a ce matan duniya sun kare kece autar mata , wllhi na hakura gara na mutu banyi aure bah akan na aure ki fateema"
Daga nan ya tashi ya bude kofa yace
"Out..now"
Ta gyara xama tana wani juya idanu taji saukan mari tass! Sai da taga taurari..ya nuna ta da dan yatsa yace
"Ki lura da inda zakiyi iskancinki ni ba sa'ar yin ki bane , ki kula..kada na kara ganinki fita ki ban waje "
Ya karasa maganar ckn tsawa nan take ta fisge Jakarta tayi waje hawaye na bin kuncinta Marin ya shiga sosai😆😆😆 tunda take a rayuwar ta babu Wanda ya taba cin xarafinta irin na yau, taxi ta tare ta gaya masa inda xata je ta biya kudin Suka dau hanya.
Shukrah tana xaune tayi nisa ckn tunani hawayene Ke sauka daga idanunta taji kamar motsi nan ta tashi Suka yi ido 4 da fatee ta rike kugu tana murmusawa ckn xafin nama shukrah ta cafke wuyar rigar ta
"Azzaluma me kike nema a gidana"
Wani irin dariya fatee take sannan tace
"Haba sahibar ki ce fah"
"Zan kasheki fatee kowa ya huta"
"Allah sarki yarinya har kisa kika koya..abun yayi sosai idan kin kasheni se ki karasa rayuwarki a gidan kurkuku umaima kuwa ta aure mijinki suyi rayuwarsu ckn so da kauna"
Shukrah ta sassauta rikon tana kallonta murmushi fatee tayi a karo na 2 daga bisani ta cigaba da cewa
"Oh...Ashe dai kinyi tunani mai kyau, ina son kisan cewa ba wai naxo Neman gafara kan abubuwan da na saki aikatawa bah ah 'ah..nazo ne don sanar dake cewa burina na son auren mijinki bai cika bah, kuma mijinki yana yan yana shirin kara aure nan da sati 3 xai auri umaima Ya'r gidan shugabankasa na da.ynxu haka suna kasar waje tare da aminiyarki suna siyayyan aure kuma.....
Shukrah bata bari ta karasa maganar ba shaketa sosai tamkar xata kai fatee lahira ckn daga murya tace
"Karya kike bakar munafuka me bakar aniya..
"Wllhi da gaske nake , idan baki yarda bah ki kira aminiyar taki ki tambayeta suna ina xata gaya miki"
Shukrah ta xame ta xauna a kasa ta tallabo kanta dake faman tsarawa a hnkli ta CE
"Fatee da gaske baban waleed zai auri umaima ? Kuma har ansa rana shine baxai sanar dani bah"
"Ehh..dama ina da masu bani labarin duk wani movement din mijinki su Suka gaya min abunda yake shirin faruwa"
Shukrah ta fashe da kuka mai ban tausayi fatee kam ta warce Jakarta tace
"Toh shukrah sahiba! A rungumi kaddara a kiyaye gaba kinga tafiyata sai wata rana tunda ma Allah yaso ki mijin naki yaki amincewa da aurena da kukan zaifi na ynxu don haka ki godewa Allah umaima xaa kawo miki ba niba"
Daga na tasa kai tayi ficewarta tana faman gyara gaban rigarta tana kunkuni tana cewa
"Boka kuwa xeci uwarsa ba ni xai yiwa karya bah...hmm gashi bukata bata biya bah wllhi xai gwammace kida da kara2"
🙄🙄🙄
Muje xuwa
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*92*
By *Reefat yahya*
*sorry fans bana yawan posting dese days pls bear wit me kunsan duniya up n down 😁😁 just busy hre n dre ne kawai..Lov u all, godiya gareku masoyana masu turamin mssgs ta private da masu kirana a waya tnx a lot Lov u all*
Fatee tana son raba tsakanin shuairat da shukrah shiyasa ta sanar da ita cewa basheer zai auri umaima..tana barin gidan ta xarce filin jirgin kasa don komawa kd.
Shukrah kuwa babu abinda take sai aikin kuka tana jin xuciyarta tamkar xata fito fili wani haushin shuairat take ji tasan tabbas aikinta ne hada auren bash da umaima lallai sai ta dauki mataki akansu duka xata nuna musu kuskuren da Suka tafka..umaima kuwa xatayi regret.
A can UAE wato birnin Dubai shuairat ce take shiga da fita xuwa kasuwanni daban2* umaima dai se kallo don bata xabi ko cokali bah haka nan shuairat ta fita sabgarta kullum a kasuwa suke yini idan sun koma masaukinsu kuma shuairat xata kira masu gyaran jiki a gyarata duk da bata so.
Haka Suka kasance har tsawon sati 2 sannan sukayi haramar dawowa 9ja.
Bayan dawowarsu da 2days aka kawo lefe akwati set3 da tulin kaya masu kyau da sada, daga nan aka soma shirye2*n biki yau saura 1 week ciff.duk yadda bash yaso ganin umaima abun ya faskara saboda shuairat ta gindaya mata sharuda sosai bata xuwan ko ina kullum tana ckn dakin baccinta gashi an kwace wayarta bata aiki se kuka, ga yan uwa sun fara xuwa shuairat se shiga da fita take Sam bata da lokacin xama ita ta kira tela yaxo har gida ya karbi dinkunan da xaa yi, mr president ya bude bakin aljihu ya xuba kudi sosai duk abunda ake bukata sun rigada sun siya ..
Shuairat ce kwance a dakinta salman yana gefe yaron ya girma yayi wayo sosai gashi da girman jiki tamkar ya'yan turawa ga fara'a ga kyau tubarakallah..mr president ya shigo yana waya bayan ya gama ya juya gun matarsa suna fuskantar juna
" sorry my Lady gskiya kina kokari Allah ya miki albarka"
"Ameen my man"
tana murmushi ta koma kusa dashi ta xauna tare da cewa
"Nasan ka gaji kwanta na maka tausa"
Babu gardama ya mike akan gado kwanciya yayi rub da cki nan ta fara masa tausa har wani lumshe ido yake tamkar mai shirin bacci shuairat tace
"Dad umaima"
"Uhmm..
"Pls gida nake son xuwa "
"Yaushe?
"Ko xuwa anjima "
"Ba damuwa ki shirya driver ya kai ki"
"Tnx swt hrt"
Ta manna masa peck a kumatu murmushi yake haka ta cigaba da masa tausa har bacci yayi awon gaba dashi.
Ta gama shirinta tsab ta shirya salman sun yi kyau sosai ta sanar da masu aiki kan cewa su kula da umaima xata je gidansu baxata Dade bah, daga nan ta wuce gun mota driver ya ja Suka dau hanyar xuwan gidan su.
Falon babanta ta fara xuwa yana xaune da carbi a hannu dayake baa dde da yin sallar axahar bah..yana ganinta fuskarsa ya fadada da murmushi yace
"Ya'r baba..Barka da xuwa"
"Yawwa..
Waje ta nema kusa dashi ta xauna yasa hannu ya karbi salman yana cewa
"Waii...haka kike fama da wannan lukutin Alhajin yana wahalar min dake"
Dariya kawai take musu gskiya salman akwai nauyi kamar my boy *haneef*😊😊.
Mama ta shigo tare da sallama ta tabe baki da ganin shuairat tace
"Oh..ni Fatima wato kedai kin nuna kinfi son mahaifin naki a kaina ..ah yayi kyau"
"Fateema wai kishi kike dani"
Baba ya fada yana dariya shuairat ta tashi ta fada jikin mama
"Mamana I miss u"
"Ba wani nan kin nuna kinfi damuwa akan mahaifinki"
"A'a mama kema kinsan ina sonku gaba daya"
Suna dariya mama ta dauki salman tana cewa
"Maigida nasan kai kam kafi sona koh"
Salman se wage baki yake kamar yana jin abunda take cewa baba ya karbe maganar yana cewa
"Wannan Dan lukutin maigidan naki yana ramar min da ya' "
"Alhaji kodai kishine"
"Haba..kishi da wannan maigidan ba chefene"
Suna ta raha daga karshe Suka gaisa mama ta kawo mata ruwa tasha Suka baje suna hira shuairat tace
"Ina majnoon neh kwana 2 bana ganinsa "
"Waye kuma majnoon"
Mama ta tambaya tana mai kallon shuairat
"Hhhhh.. Yaya bash mana"
Duka mama ta kai mata nan ta goce tana dariya tace
"Ehh..mana ai sunan ya dace dashi majnoon baban soyayya ko romeo ne"
"Bayan kun hanashi Ya'r taku me kuma xaki fada"
"Eyya mama rabone babu"
"Kiji dashi...Allah xai bashi wata"
Baba de se dariya yake musu haka shuairat ta yini har bayan sallan laasar ta tashi da cewa xataje gun shukrah kafin ta koma gida daga nan sukayi sallama tana rokon mama akan cewa don Allah taxo bikin , har mota Suka rabu nan driver ya ja Suka wuce gidan bash.
Shukrah tana xaune ta buga uban tagumi tunani fal a ckn xuciyar ta kamar a mafarki taji sallamar shuairat bata amsa bah shuairat tasa kai ta shigo falon tana faman sauke salman tare da cewa
"Kai mata kina nan shine baki amsa sallama ta bah, tunanin me kike haka"
Wata muguwar harara shukrah ta jefa mata tare da Jan dogon tsaki tace
"Allah wadaran naka ya lalace..mutum yayi asara tunda munafurci da hassada yasa a gaba"
Ckn rashin fahimta shuairat tace
"Ke kuwa waya tabo ki da yamma haka"
Dama jira take nan shukrah ta tashi tsaye tace
"Ke shuairat kada ki mayardani shashasha..kina jina, bayan kin gama hada munafurcin ki xaki xo kina raina min wayo..
"Haba shukrah meyayi xafi haka?
"Ehh..lallai kin nunamin halin yan duniya.ni kike tambaya? Hmm..shuairat kenan tsabar rashin kunya da bushewar ido har xaki iya fuskantata ki...
"Dakata madam! Bana son kwana2* ki fito fili ki gayamin meke faruwa"
"Danakari! Lallai yarinya kina da mugun rainin hnkli..bayan kin gama munafurcinki xaki dawo ki fake ki nuna Ke baki San komai bah??
Shuairat tayi jugum..wai meke faruwa ne?
Me shukrah take nufi??
Ni Reefat nace🤔🤔 kodai xancen auren ya tabbata ne??
Toh...muje xuwa dai
*Dr Reefat*😘😘😘
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*93*
By *Reefat yahya*
Shuairat taja wani gauron numfashi tace
"Look bestie..let's sit down n..
"Bestie! ..hmmm tsohon suna "
Shukrah ta tare numfashnta sannan ta cigaba da cewa
"Shuairat a da can baya idan wani ya gayamin cewa xaki iya aikata abunda kika min a ynxu wllhi baxan taba yarda bah amma ba abun mmki bane dama haka amintaka ta gada...cin amana da yaudara da munafurci"
"Haba shukrah wat r u talking about.. Nifa kin sani ckn duhu"
"Kinga malama ki tattara ki barmin gida Nah ..ko sai nan ma xaki nunamin gidan Dan uwanki ne?
"Pls shukrah let's talk abit "
"I don't want to...just get out now"
Shukrah ta fada tana nuna hanyar fita nan shuairat ta sabi salman tasa shi a kafada ta kama hanyar fita idanunta sun cika da kwalla tana mamakin sauyin halin shukrah kuma ta rasa gane dalilin.driver yana ganinta yayi saurin bude mata gidan baya ta xauna ya tada mota Suka koma gida.
Tana isowa ta share hawayen da ya bata mata fuska sannan ta karasa ckn gida baki ne a cike da falon suna ganinta Suka fara mata sannu da dawowa itama tana musu barka da xuwa se rawar jiki sukeyi a kanta wata ta karbe salman tana cewa
"Fine boy ya kke"
Dangin mahaifiyar umaima ne da kuwa wasu daga ckn yan uwan mr president sauran kuma washe garin xasu taho , shuairat ta shiga musu hidima se yabonta ake bayan ta tanada musu komai duk cewa masu aiki sun Riga sun kawo musu abinci har magrib ta samu ta koma dakinta tayi sallah bayan ta idar ta samu ta watsa ruwa har ynxu salman yana gun yan uwansa don haka ta shirya a nitse ta saka wata simple doguwar riga Mara nauyi ta fesa jikinta da turare nan ta kwanta a gado kalaman shukrah ne Ke yawo a kwa2lwarta ta rasa gane inda maganganun Suka dosa, mr president ya shigo har ya karasa kusa da ita ba tare da ta sani bah hannu taji ana shafa fuskarta yasa tayi saurin dagowa ya jawota a jiknsa ya rungumeta tamkar jira take nan ta fashe masa da kuka dakyar ya rarrasheta ta daina kukan wani light kiss ya mata na 2 mins sannan ya kwantar da kanta a saman kirjinsa tayi luff ta kwanta sosai ckn Muryar rada yace
"Tell me...
Babu gardama ta xayyana masa komai bata hakuri yake bata yana nuna mata cewa ta kwantar da hankalinta wataran xasu shirya daga nan ya fara mata wasu abubuwan da yasa ta manta da damuwar da take cki.
Washegari ...daddy da momsi Suka zo ga gida de a cike makil babu masaka tsinke a ckn dangin nata ne shuairat ta xabi kawaye 4 ta basu anko din ta shirya dinner hadadde bayan an daura aurene xaa yi , umaima kam tace ba ruwanta a cki ko walimah baxata yi bah..dakin umaima ta shiga ta xauna a gefen gado umaima ta tashi xaune tace
"Don Allah mom sultan ki taimaka ki barni naga uncle bash..wllhi ba dadewa zanyi bah kawai sallama zamuyi"
"Bbu inda zaki..so kike ki jawo min magana gun daddy koh, toh wllhi babu ruwana a cki"
" haba mana...eyya mom plsss"
ta marairaice shuairat tace
"xan kirashi yaxo nan gidan ya sameki"
" ehh..na amince don Allah ki taimaka"
Ta bata tausayi ba kadan bah..nan ta cire wayarta yayi ringing har ya katse baa daga bah, ta sake kira har sau3 daga bisani ya daga a wahalce yake magana
"Salamu alaikum"
Gaban shuairat ya fadi badai rashin umaima ne ya kwantar dashi haka bah ya salam! Muryarsa ne ya katse tunanin da take
"Baki jina ne"
"Yaya ina ji meyake damunka naji voice naka somhw"
tsaki yaja yace
"Wani Dan xaxxabine yake damuna amma naji sauki"
"Ahm..dama umaima ce take son ganin ka "
"Da gaske? tana ina?
"Yaya..tek it easy pls, kaxo gida ynxu amma kada ka bari mr president yasan da xuwan naka ok"
"Ok gani nan xuwa"
Nan ya kashe wayar tausayinsu ne ya kama shuairat jikinta ya mutu ta juya ga mmkinta hawayene a idon umaima tace
"Mom sultan kin gani koh...wllhi yana sona nasan yana ckn tashin hnkli ynxu"
"Umaima kiyi hakuri babu ynda muka iya umarnin iyaye ne Allah yasa hakan shine mafi alheri "
"No...ba alheri bane ni nasan aurena da uncle bash shine mafi alkairi "
Nan ta fashe da kuka shuairat tana bata hakuri dakyar ta sagaita kukan daga nan ta tashi tayi wanka ta xauna xaman jiran masoyin nata.
Har yamma babu labarin bash ga layinsa bayya shiga umaima ta birkita shuairat gaba daya ta xama tamkar wata mahaukaciya tun suna boyewa har jamaa Suka gane sun fara tambayar shuairat ko lfy shuairat de ce musu take kan umaima ta tuna da mahifiyarta shiyake sanyata yawan kuka.
Da dare suna xaune sunyi jugum shuairat ma ta shiga damuwa don rashin samun layin Dan uwan nata gashi tana kiran layin iyayen nata basa dagawa babu halin ta fita kuma don mr president baya gida.haka ta hakura momsi ta shigo dakin suna Dan taba hira sama2* dakyar Suka lallaba umaima ta yarda taci abinci, kadan ta ci ta kwanta.
11pm mr president ya shigo a wannan lokacin shuairat ta gama shirin bacci ta kwanta amma baccin yaki xuwa , ya shigo tare da sallama ta tarbesa tare da kawo masa abinci bayan ya gama wanka ya fito ya ci abincin sarai ya lura da halin da take cki amma ya share nan ya hau gado ya kwanta ckn sanyin murya ta kirasa
"Swt hrt!
"My lady yaya?
"Uhm..dama numban yaya bash ne baya shiga"
"Meya faru kuma meyasa kike nemansa"
"Uhm..dama ..daman "
Sai kuma tayi shiru ta rasa karyar da xata shirya ya kura mata ido yace
"Ina sauraronki"
"Uhm..numban mama ne idan na kira bata dagawa shine nake son ji ko lfy"
Murmushi yayi ya jawota yace
"Don't worry lfy suke babu abunda ya faru ok"
ta tura baki tare da marairaicewa
"How sure are u ko suna lfy"
"C'mon trust me..lfy lau don dazu na raka daddy yaje gun baba "
"Lfy dai koh?
"Uhm..kawai gaisuwa ce cos idan ya shiga hidimar bki baxai samu damar xuwa bah, kuma yayi inviting dinsa xuwa daurin aure "
"Ok yayi kyau"
Daga nan shiru sukayi kowa da tunanin da yake ya rungumeta sosai sannan ya kashe bedside lamp sukayi baccinsu.
*asuba ta gari masoya👌🏼*
~Gobene fah..👯👯👯rengem rengemgem gobe ne daurin auren umaima fah...rengem..rengem..gem..💃🏼💃🏼💃🏼dafatan xaku xo fah...rengem👯👯👯👯~ *dis1 naa gobe.. Oyakaka..original gobe..* 😁😁😁lolx don't mind me
U r all invited 2d wedding hop xaku xo fans..tohm duk mai xuwa ya daga hannu👆🏼👆🏼
😜😜😜sai naji daga gareku..Lov u all *Reefat CE*
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*94*
By *Reefat yahya*
*yesss oooh...2day na 2day...auren umaima n basheer😜😜*
12pm bash yana kwance a falon mahaifinsa baba ya fito ckn shirin jumaa yasha manyan kaya farare sol dasu se xuba uban qamshi yake..ya harari dan nasa tare da cewa
"Kwanciyan me kake min a falo baxaka je masallaci bane"
Ya marairaice kamar zaiyi kuka yace
"Allah baba bani da lfy I dnt tink xan iya xuwa "
"Bana son shashanci ka tashi maza ka shirya ynxun nan mu tafi don a can xaa daura auren umaima nasan take-taken naka salon kar kaje daurin auren ne kuma dole se kaje wllhi"
"Baba pls...
"Bana son maganar banxa ka tashi maxa ina nan ina jiranka"
Sum sum ya tashi ya koma dakin da yake zama ckn kankanin lokaci yayi wanka ya fito blue shadda yasa kayan sun masa kyau ba kadan bah ga qamshin turare kala2* ya ajiye hula sannan ya fito baba ya bisa da harara daga nan Suka wuce central mosque a can xaayi daurin auren.
Umaima tana kwance ta duba agogon dake makale a bangon dakin Karfe 1:10 shikenan saura kiris ta xama matar ismaeel , shuairat ce ta shigo tare da sallama abinci ta kawo mata farfesun kaxa ne yasha hadi sosai ta tura plate din agaban umaima ckn tamke fuska tace
"Maxa ki cinye ki bani plate ynxu"
"Mom sultan wai fushi kke dani"
"Mtsww..toh me! Ke kin damu kanki akan mutumin da bai damu dake bah, da a CE yana sonki ai da yaxo tuntuni amma saboda bai damu ba kinga ya nemeki ne? Kina nan kina Neman halaka kanki "
"Haba kinfi kowa sanin irin son da uncle bash yake min..ni nasan ba lfy bah...
"Dallah malama..ki ci abinci ki tashi ki shirya"
Tana kumbure2* haka tasha farfesun don bata ga alamar wasa a fuskar shuairat.
Bayan ta gama ta shiga bayi ta Dade kwance ckn jacuzzi tana lumshe idanunta hoton fuskan bash kawai take gani nan hawaye ya cika mata ido ta dauki tsawon minti 40 tana kwance , shuairat ce ta kira sunanta daga waje nan ta fara wanka daga bisani ta fito.
3:10pm an shiryata tayi kyau sosai ckn wasu dankareren leshi mai kyawun gaske umaima tayi kyau kamar a saceta a gudu a harabar gidan aka fito da ita masu daukar hotuna ne birjik ga nan yan uwa da abokan arxiki ma ga yan gayyan sodi irinsu Reefat😆😆 ga masu watsa labarai daga gidan telebijin da yan jarida , gidan de a cike makil da jamaa umaima de daurewa take tana kokarin boye halin da take cki shuairat ansha kyau ta xama tauraruwa sha kallo ga salman da sultan ma haka, abun de gwanin burgewa.
Momsi ta fito Suka fara daukar hotuna sunyi family pix kala2* dakyar na samu na dau kala 3nida shuairat da amarya se kuma Wanda mukayi tare da salman da sultan😜😜😜.
Horn muka ji a bakin gate take maigadi ya wangale kofar motoci ne birjik har na kasa tantance ko guda nawa ne, securities na fara gani ckn bakaken suits nace ah abun na manya ne☹☹..Nigerian president ne a gefen mr president (dad) ga Chinese President daga barin hagu se kuma new faces da bansan ko su wanene bah daga gani dai kasan shuwagabannin kasacen duniya ne don daga irin shigar kayansu da masu tsaron dake xagaye dasu xaka gane hakan.ga can daddy a baya tare da abokanansa manyan mutane se kuma ismaeel na hNgo fuskarsa dauke da murmushi sai kuma bash daga can gefe yana ta gaisawa da mutane yNa dariya fuskarsa kamar gonar audugA..haaa..am confused🙄🙄 ya naga bash haka?? ..uhmmm.
Dakyar mr president tare da tawagarsa Suka samu hanyar shiga ckn gidan saboda jamaa sunyi yawa babu masaka tsinke. A can babban falon gidan Suka xauna daddy kuma yana dayan falon tare da tawagarsa , abinci da na sha aka ajiye musu suna ci suna taba hira ana dariya daga bisani yan jarida Suka fara daukan hotuna don yadawa a gidan labarai, shuairat da umaima sun shigo falon anyi hotunan tare dasu ana tayasu murna.har 5pm ana abu guda dakyar shuairat ta jawo umaima Suka koma bangarensu a daki Suka xauna shuairat tace
"Ki shirya anjima xaa ne dinner"
Idanunta sun cika da kwalla tace
"Allah na gaji baxan iya xuwa bah"
"Shikenan bari naje na sanar da dad "
Ckn Sauri tace
"Ah'ah pls kiyi hkri xan shirya ynxu"
Murmushi shuairat tayi sannan tace
"Kije falona babu kowa a can angon yana son ganin ki"
"Eyya mom..Allah na gaji sosai"
"Ok bari na kirashi yaxo ya sameki "
Bata jira amsa bah tayi waje dama su 2 ne kawai a ckn dakin sauran jama'an suna can kasa suna faman daukan hotuna. Umaima ta hada kanta da guiwa ta fara rusa kuka..shikenan yau ta xama matar wani !
Kofar dakin aka bude ta cigaba da kukan da take ba tare da ta daga kai bah..a hnkli ya xauna kusa da ita ya jawota a jikinsa , qamshin turaren da har abada baxata manta dashi bah ckn Sauri ta daga ido tare da cewa
"Uncle bash😳😳
Murmushi ya sakar mata mai sanyaya xuciya , nan kuwa ta turesa gefe tana hawaye tace
"Kasan de ynxu na xama matar wani"
"Har abada Ke matata CE mutuwa CE xata rabamu"
Wani murmushi mai ciwo tayi tana girgixa kai tare da cewa
"Kana magana tmkar baka San yau an daura aurena bah"
"Yes ofcoz an daura auren ki but da masoyinki aka daura auren"
Ya karasa magana tare da lakuce masa hanci ckn rashin fahimta tace
"Bangane bah"
"Yes umaima Allah ya cika mana burin mu an daura mana aure n...
Bai samu damar karasa maganar ba ta fada jikinsa ta rungumesa gam hawaye wani na bin wani..murmushi bash yayi tare da daura hannayensa shima ya rungumeta 😍😍😍
Sun kasance ckn wannan hali har na lokaci mai tsaho sannan umaima ta xame jikinta sai kuma kunya ya kamata tasa tafin hannu ta rufe fuska wai ita kunya🙄🙄🙄 daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa...😬😬😜.
Toh ya akayi abun ya juya aka daura da basheer???
🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Fans ..just ignore d typing errors cos bana editin
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*95*
By *Reefat yahya*
Fuskokin nasu dauke da Murmushi suna kallon juna ..a hnkli bash ya jawota ya rike mata hannu tare da kura mata ido yace
"Baby no more kunya pls..kin xama matata u r mine n am urs murna xakiyi ki godewa Allah da ya cika mana burin mu"
ta daga kai tace
" but Bb ya akayi hakan ta faru har daddy ya amince aka daura mana aure"
"Ni zan baki amsa"
Shuairat ce ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da cewa
"Yau da safe na samu labarin but naki na gaya miki cos I want 2 surprise u"
Nan kuwa umaima ta ruga a guje ta rungumi shuairat tana dariya tace
"Tnk u so much mom..nasan da taimakon ki akayi wannan auren Nagode sosai Allah ne kadai zai biyaki tnx a lot"
"Mention not dia "
"Toh mom ki ban labarin ya akayi ..am waiting"
"Umaima hoo..irin xumudi haka"
Kunyace ya rufe ta nan ta koma gefen gado ta xauna bash kam se kallonta yake kamar wani tsohon maye ta birkita masa kwakwalwa ta kara kyau ba kadan bah..shuairat CE ta fara magana
"Jiya daddy yaje gun baba tare da dad naki sun dade suna hira har daddy xai dawo sai yake tambayan ina yaya don tunda yaxo be ganshi bah, aka ce masa yaya bashi da lfy yana bacci daga nan Suka dawo gida.yau da safe naje gun daddy bayan mun gaisa yake tmbyta ya me jiki ckn rashin fahimta nace masa waye ba lfy? Ckn mmki shima yace baki san yynki bashi da lfy bah? Nan hawaye ya cika idanu na hnklin daddy ya tashi ya fara bani hkri yace da yasan baa gayamin da baxai tmbyeni ba gashi ya dga min hnkli, nace masa ba batun rashin lfyn ne Ke sani kuka bah illa tausayin halin da yaya xai shiga nan gaba..daga nan na xayyana masa komai.fada yake ta inda yake shiga ba ta nan yake fita bah wai akan wane dalili xaa boye masa wannan lamarin, nace tun farko naso sanar da kai but baka saurareni bah daga nan ya kira baba nan ma fada yake akan cewa meyasa baba be sanar dashi bah.a takaice de haka ya kira ismaeel da babansa ya basu hakuri ya nuna musu yarinya bata so , haka Suka hakura har xuwa lokaci daurin auren ko shi yaya bai San cewa dashi xaa daura auren bah.toh kinji de yanda abun ya faru"
Wani dogon numfashi umaima ta sauke tare da cewa
"Ikon Allah kenan..tabbas wani baya auren matan wani, matar mutum kabarinsa hakika rabo in ya rantse babu mai hanawa don nikam tuni na fidda ran sake haduwa da Bb..Allah Nagode maka da ka cika min burina , mom Nagode miki da kokarin da kikayi kuma daddy ma dole na gode masa"
"Kai umaima ko Ya'r kunyan nan babu"
ta rufe fuska tana dariya shuairat ta tashi tsaye tare da cewa
"Ki shirya ynxu masu makeup suna nan tafe kinsan akwai dinner nima na tafi idan nayi sallah xan fara shiri na"
Basheer yayi murmushi yace
"Wait..sisy kina nufin kema xaki he?bayan kece mmn amarya"
Harara ta watsa masa tace
"Toh bari kaji har mijina ma sai yaje don abun tuwo na maina ne ...kuma a ckn gidan nan xaayi"
ta juya gun umaima tace
"Ke kuma ki xauna ki biye masa har lokaci ya kure Ku gaku nan romeo n Juliet , an de daura auren xamu gani ko xaku hadiye junanku"
Dariya sosai suke shuairat ta yi hanyar kofa bash yayi saurin cewa
"Kixo gidan mu ki ga yanda xaa hadiye juna ...ki xo na koya miki Lov yarinya"
"Ahaaff...wllhi karyan mutum yace xai koya min soyayya , duk kalan Lov da xakuyi de wasu sun Riga sun gama ..toh wai ma wane darene jemage bai gani bah"
"Daren goma sha hudu"
Ya fada yana dariya tsaki shuairat ta ja ta bar dakin umaima ta hararesa ckn salon so tace
"Mom ce fah..she is ur in law u have 2 learn hw to respect her"
"Lol..babu mai shiga tsakanina da baby so ki xuba mana ido kawai"
"Ni baby ! Ita baby! So which 1...gskiya ka xabi daya"
😳😳😳😳☹☹uhmm ni Reefat nace toh fah...umaima tun ynxu🙄🙄🙄🙄Dakyar bash ya fita ya barta ba don yana so bah nan ta fada wanka.
8:30pm garden din gidan mr president ya cika makil da jamaa an kawata wajen da kujeru da furanni masu kyau ga nan decoration de gwanin burgewa ga wutar lantarki ya haska wajen..yan mata da samari wasu suna xaune a bakin swimming pool suna ta hira manyan mata kuma suna can xaune daga masu cin abinci se masu shan drinks idan ka duba wani fannin kuma mr president ne tare da manyan mutane irin su US president Chinese president Nigerian president da dai sauran kasace daban2* daddy ma yana can tare da manyan abokanansa yan siyasa da yan kasuwa da ma talakawan gaba daya.amarya da ango sunyi ado sun sha kyau sai daukansu hotuna ake ana yadawa a social ntwrks suna can tare da frenz dinsu suna hira tare da xagayawa suna gaisawa da jama'a, shuairat tana xaune tare da manyan matan ministoci da shuwagabanni suna ta hira ckn nishadi.matured dinner irin Wanda baa taba yin irinsa ba a duk fadin kasar bcos babu irin kade-kade ko rawa da sauransu cool music kawai Ke tashi kowa na shaanin gabansa kyaututtuka kuwa wrapping ake sai a mikawa amarya da ango sannan security ya karba ya ajiye a wajen da aka tanada domin ajiye kyautar.gwanin shaawa jamaa da dama sun halarci taron Wanda baxan iya lissafa su bah.
Washe gari aka dauki amarya aka wuce da ita gidan mijinta dake can central area bayan shuairat da sauran yan uwan mamanta sun mata nasiha sosai..mr president kam yaki haduwa da ita don ya tuna da mahaifiyarta yinin ranar gaba daya a ckn daki ya kasance , shuairat ce take lallabashi.da yamma akayi fansa a can gidan iyayen shuairat shukrah ma ta daure taje fansar.
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*96*
Bayan an gama biki lfy jama'a sun watse amarya ta tare a dankareren gidan ta Wanda an narka uban dukiya a cki.da safe ta tashi ta gyara gidan ta kunna turaren wuta tare da fesa room freshener gidan ya dau qamshi ta fada wanka ta shirya ckn atamfa tayi kyau sosai ta ajiye daurin nan a gaban goshi se xuba qamshi take ta gaji sosai don bata saba da aiki bah gskiya dole a kawo mata masu aiki tana nan tsaye a gaban dressing mirror bash ya tura kofa ya shigo tare da sallama ta amsa ba tare da ta juya bah rungumota yayi ta baya ya kwantar da kansa a kafadarta suna kallon juna ta ckn mirror fuskokinsu dauke da murmushi tace
"Morning BB"
"Morning dia hw was ur nyt"
"Alhamdulillh...
"Kinyi kyau baby Nah"
"Kaima kayi kyau my BB"
"Nifa bana son wannan sunan "
"Bb ne baka so y?
"Ehh..nidai ki canza min bana so"
"Toh wanne kake so"
"Oho..
"Uhmm..na tuna *HP*
"Hp?...meaning?
"Honey pie"
Dariya sosai yake sannan yace
"Toh BB fah? Me ma'anarsa"
"Basheer Bello"
"Lah..sai na gayawa baba kina kiran sunansa direct"
"Eyya fah..yi hakuri toh, ba na daina bah..daga yau sunan ka HP"
"Ok tnx my baby"
Nan ya manna mata peck a kumatu ta bata fuska tace
"Toh nima bana son baby"
"Meyasa?
"Cos haka kake kiran mom sultan kuma ni baxanyi sharing bah"
"Lallai yarinya..kishi kike da mom naki, ai zan gaya mata"
Ta fashe da dariya tace
"Rufamin asiri pls..Bahaka nake nufi bah"
Wayarta ya hau ruri shi ya juya ya dauko yana dubawa yace
"Kinga Ya'r halak koh..wllhi baby ce"
Ya kara a kunne tare da cewa
"A ina kika taba ganin ana kiran amarya da sassafe haka?
Daga bangaren shuairat tace
"Toh Mara kunya ga nan surukinka yana jin duk abunda kake fada"
😳 ba shiri yayi saurin mikawa umaima wayar ta karba
"Hello mom ina kwana"
Dariya sosai shuairat take daga bisani ta amsa
"Lfy ya kuka tashi"
"Alhamdulillh ..ina sweetie salman n sultan da kuma dad"
"Lfynsu kalau..dama brkfast na ba driver ya kawo muku"
"Ok Nagode mom..dama mom nace gidan yayi kato dayawa pls a turomin masu aiki"
"Kai umaima..
"Allah mom gidan shegen girma ne dashi"
"Toh da kin dauka xaman auren wasa neh"
"Haba mom..pls ki taimaka kinsan xanje skul "
"Ok naji...but Ke xakiyi girki da kanki"
"Insha Allah babu matsala xanyi"
"Ok toh..ki kula da kanki idan akwai abunda kike bukata ki sanar dani "
"Ok Nagode..ki shafamin kan sweetie Nah"
"Ok bye.."
Daga nan Suka katse wayar ta juya tana kallon bash tace
"Muje muyi brkfast "
Ya hada rai yace
"Waye sweetie kuma"
Dariya ta basa tace
"C'mon salman ne fah"
"Oh ho! I tot wani ne ai"
"Ba kowa..kai kafi kowa sani duk duniya babu Wanda nake so fiye da kai so meyasa zaka damu"
Murmushi yayi sannan ya dagata cak! Kamar karamar yarinya Suka fito falo.
Bayan 5days da gama bikin umaima akayi resuming skul nasu 2weeks ta kara akai sannan ta fara xuwa.da yamma misalin 5pm ta dawo gidan a gajiye ta fada a saman kujerar falon matar da take mata aiki shigo tare da sallama
"Sannu anty kina kokari wllhi"
"Uhmm..ya xamu yi se hkri "
"Allah ya taimaka"
"Ameen Nagode.. Maigidan be dawo bane"
"Ya shigo de dazu tare da wani yaro mai kama dashi"
Murmushi umaima tayi tace
"Waleed dansa ne fah"
Ckn mmki matar tace
"Au dama yana da wata mata bayan Ke"
"Ehh..gidanta daban shiyasa baki taba ganinta bah"
Daga nan umaima ta tashi ta koma dakinta ta watsa ruwa ta fito ckn kankanin lokaci ta hada musu abincin dare couscous ne da miyar hanta se kuma lemun kankana da ayaba da kuma fruit salad, bayan ta gama tayi sallar magrib tayi assignment dinta ta gama sannan tayi isha har ynxu bash bai dawo bah ko me ya rikeshi oho! Kwalliya tayi ckn wata Ya'r karamar Riga iya guiwa tayi kyau sosai lipgloss kawai ta shafa se farar hoda da turare shikenan... Amma tayi kyau kamar a saceta a gudu har 9pm bash ya shigo tana nan xaune a falo yayi sallama cki2* ta amsa murmushi yayi don yasan laifinsa na rashin dawowa da wuri.
Ya karasa kusa ya xuba guiwowinsa a kasa tare da kama kunne yace
"Am sorry anty maimah"
Yadda ya furta sunan dole ya ba mutum dariya nan kuwa ta fashe da dariya hannu tasa ta jawo kunnensa har ya sake wata Ya'r kara yayi narai2* da ido yace
"Ahh..akwai xafi fah"
ta tura goshinsa tace
"Zaka sake"
"No...am sorry wllhi ina gun baba ne muna wata er magana ne dashi"
"Toh tashi..last warning"
"Ok mah!
Daga nan ya tashi tsaye batayi aune ba ya dagata sama yana dariya yace
"Sai na rama abunda aka min amma ni nawa se yafi wannan"
ta shagwabe fuska
"Haba HP..ni wani Abu na maka ne"
"Zaki gane yarinya hmmm..
Daga nan Suka wuce wajen cin abinci a kan cinyarsa ta xauna tana bashi a baki shima haka, bayan kowane loma daya sai anyi kiss daya😱😱 ...hmmm wannan wane irin Lov ne chabb🙊🙊Bayan sun gama bash ya shiga wanka yana fitowa sukayi shirin bacci ya kankameta a jikinsa yace
"Let's sleep nagaji sosai wllhi"
"Da magana xamuyi but tunda ka gaji is ok sai gobe we'll talk abt it"
"No...just say it now ina jin ki"
"Ok tnx...dama nace gashi munyi 3weeks tare kuma har yau baka koma gun Mmn waleed bah, nidai nasan 1week ya kamata muyi tare but har mun kara 2weeks akai gani nai....
Hannu ya daga mata yace
"Wannan ba maganar ki bah..kwanta kiyi baccin ki let's nt talk abt dis"
"No HP pls..b serious kaga ynxu laifina xaa gani wasu xasu ce daga xuwana na rabaka da matar kah n ...
" I said is non of ur business"
Umaima ta ja bakinta tayi shiru sai kuma ta juya masa baya ya runtse ido ya jawota a jiknsa ta fara kukan shagwabah
"Am sorry dear..I din min 2hurt u pls kiyi hkri"
Nan ya cigaba da bata hkri daga karshe ta bada kai bori ya hau ance idan kida ta canza dole rawa ma canza😜😜 wata duniya daban Suka fada...
Nasan wasu an baxa👂🏼 ana jiran 1st nyt koh..tohmm ya wuce Ku domin umaima ta kirani a phn tamin gargadi😉😜
👍🏼👍🏼lov u all
[2/21, 2:43 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*97*
By *Reefat yahya*
Yau umaima ta cika 1mont a gidan basheer ta shirya xai ajiyeta a gidansu se murna take ta gama shirinta tsab ta fito ya tsaya ya kura mata ido bbu ko kiftawa ta karasa kusa dashi tace
"Kai HP wane irin kallo ne haka"
"Alhamdulillh Allah Nagode maka da ka mallaka min umaima a matsayin matata"
Murmushi tayi tare da cewa
"Let's go honie kaga lokaci na tafiya"
"Oh haka ma xaki fada koh..naga alama Ke baki dami dani bah se murnar xuwa gida kawai kike ni kuma tun ynxu na fara missing naki"
"Hp rigima koh..yini fa xanje ba kwana bah kake wani xancen missing dina"
"Toh an fasa tafiyar ma ki bari se next week"
Ta shagawabe fuska tace
"Don Allah ka bari bana so"
"Haba baby girl Nah ...smile toh"
Dariya suke ya rike hannunta Suka wuce mota shi ya bude mata ta shiga ya rufe kofar sannan ya koma bangaren driver ya xauna daga nan Suka wuce gidan mr president.
Murna sosai suke sultan ya makale Ya'r uwar tasa nan Suka xauna ana ta hira daga bisani bash yyi sallama ya tafi.bayan axahar shuairat suna xaune a daki tare da umaima tace
"Yawwa mom ki ma bb Nah magana tun bayan auren mu har yau bai koma gidan Mmn waleed bah"
😳😳 shuairat ta xare ido ckn tsananin mmki tace
"Waat? Wata daya?.. Anya lfynsa kuwa...hmm bari yaxo ya sameni gskiya somtin is wrong"
"Allah babu yanda banyi dashi bah yaki komawa ..idan na kawo maganar ma se munyi fada wllhi"
"Barni dashi xai shigo ya sameni Allah se na hadashi da baba"
Haka Suka cigaba da yan hirarrakin su har xuwa dare bash yaxo daukar ta nan shuairat ta nemi yin magana dashi umaima ta tafi gun dad ta basu waje.
Shuairat ta hada fuska tace
"Yaya wat is wrong wit u..da hnklinka da tunaninka xaka share 1month kana danne hakkin matarka?..haba yaya ina amfanin ilimin da kke dashi..
"Baby ki bar maganar nan "
"No yaya let's talk abt it pls.."
"Ok fine..since kowa yana bani laifi let me explain, da banyi niyyar gayawa kowa wannan magana bah cos is my secret but now I have to" nan y xayyana mata komai duk irin xaman da suke da shukrah har xuwa lokacin da yaji batun family planning da komai..hawaye ne ya cika idanun shuairat tace
"Allah sarki bestie... Wllhi nasan zugin bad frenz ne if not da ba haka take bah..ni nasan ba laifinta bane yaya kayi hakuri ka yafe mata pls"
"Hmm..baby kenan"
"Allah yaya trust me nasan akwai wata a kasa ba haka kurum bah..duk da haka de ka daure ka yafe mata n pls ka raba musu kwana kana shiga hakkinta Allah"
"Naji..xanyi naxari akai"
Daga nan shuairat ta fara masa nasiha mai kashe jiki yayi shiru yana sauraronta
"My yaya kasan shi xaman aure sai da hkri duk irin kaunar da kuke nunawa juna wata ran dole Ku samu sabani amma hakuri shine maganin komai..kuma hakkin aure ba abun wasa bah musamman adalci tsakanin matayen ka, shiyasa Allah yace Ku auri mata 2 ko 3 ko 4 idan xaku iya yin adalci a tsakaninsu idan baxaku iya bah Ku auri 1 Ku bata dukkan hakkin ta na ci da sha sutura da sauran hakkin aure. Shin kana son ranar gobe kiyama ka tashi ckn mazajen da basu nuna adalci tskanin matayen su? Haba yaya ina amfanin karatun da kayi idan har baxaka yi aiki dashi bah"
Haka de shuairat ta cigaba da masa nasiha tare da kawo masa hadisai da ayoyin Qur'an jikinsa yyi sanyi sosai umaima tare da mr president da suke tsaye a bakin kofa sunyi shiru suna sauraronta wani shaukin sonta ne mr president ya tsinci kansa a cki ..tabbas shikam yyi dace a duniya Allah ya hadashi da mace ta gari hawayen farin cki ne ya cika idanunsa ya tsaya kim ya kura mata ido ya daina sauraron me take fada sai bakinta kawai yake kallo ya shagala da kallon taji a jikinta kamar wani na kallonta nan ta juya idanunta Suka fada ckn nasa murmushi ta sakar masa ta sunkuyar da kai daga naN Suka karasa shi da umaima xama sukayi nan mr president ma ya dora nasa nasihar yana musu fatan xaman lfy daga nan sukayi sallama bash ya dauki matarsa Suka koma gidansu.
Mr president ya kasa hakura suna fita ya jawo matar tasa a jiki ya rungumeta gam tamkar xai maidata ckinsa tayi lamo a jikinsa tana jin bugun xuciyarsa a hnkli ya rada mata a kunne
"I Lov u so much Ayshata Allah ya barmin Ke har gidan aljannah"
"Lov u more swt hrt"
Ya sassauta rungumar yana kallon kyakkyawar fuskar ta yace
"Ina da albishir da xan miki but se kin bani goro Nah"
"Aw rily..muje toh ynxu xan baka kuwa"
Daki Suka wuce ni kuma na tsaya a falo nace abun yafi karfina dole na hakura har xuwa lokacin fitowar su.
Bash da umaima ma hakan ta kasance soyewarsu kawai suke ni Reefat nace oh..duk inda naje ana ta xuba Lov kawai toh ina zan samu labarin ne☹☹
Da safe around 10 bash yayi parking a ckn gidan shukrah ya fito se xuba qamshi yake ya bude kofar falon tare da sallama tana xaune ta buga uban tagumi ckn sanyin murya ta amsa sallamar ya nemi kujera ya xauna dakyar ta bude bakinta ta gaida shi y amsa ba yabo ba fallasa yana satar kallonta ta rame kuma tayi sanyi dayawa ba haka yasan ta bah, ita ma satar kallon nasa take yayi kyau sosai hnklinsa kwance wato shi bai damu da ita bah ..wani guntun kwalla ne ya xuba a fuskanta tayi saurin goge wa yayi kamar bai ganta bah..ya katse shirun da cewa
"Kina bukatar wani Abu ne?
Ckn rawar murya tace
"Dama..ina son xuwa ganin waleed "
"Yaushe kika fara damuwa da dan naki"
Kukan da take boyewa ne ya kubce mata ckn Muryar kuka tace
"Don Allah kayi hakuri ynxu ganinsa ne kadai xai ragemin radadin da nake ji pls ka taimaka min"
Ya tabe baki tabbas yaji tausayinta amma dole ya hora ta ya tashi tsaye yace
"Maybe anjima xan kawo shi"
"Nagode "
Bai ce komai ba yasa kai ya fice.ta koma ta xauna ta cigaba da kukan da take lallai rayuwa kenan..ta fara tuna rayuwar da sukayi a baya har xuwa lokacin haduwarta da fatee a watsap da kuma irin gurbatattun shawarwarin da tayi amfani dasu gashi yau an rabata da mahaifarta an kuma rabata da masoyinta na gaskiyA..tana ji tana gani ya auri wata babu yanda ta iya sallama taji ta daga kanta Suka hada ido carab da shuairat😱😱 ..
....
[2/21, 2:43 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*98*
By *Reefat yahya*
Dakyar shukrah ta amsa sallamar ckn jin kunya idan ta tuna abubuwan da mata a baya batayi tsammanin xata sake xuwa gidan bah..Allah sarki shuairat bata chanja hali bah har ynxu tana nan yadda tasan ta.shuairat ta xauna fuskarta dauke da murmushi tace
"Shegiya anji jiki koh..naga kin rame nasan kinyi regretin "
Murmushin karfin hali shukrah tayi tana mamakin hali irin na shuairat Sam bata fushi bata dauki duniya a bakin komai bah bata...
"Bestie tunanin me kike haka..kinga yanda kika xama kuwa"
Hawaye ne ya fara saukowa nan ta fashe da kuka shuairat ta kwantar da salman ta dawo kusa da ita tace
"Pls..am here now kuka ya kare ki share hawayenki ki gayamin meke faruwa"
Haka kuwa shukrah tabi umarninta ta share hawayen tare da kwashe labarin komai ta xayyana mata shuairat tayi tsaki tare da cewa
"Daman nasani ai...tun ranar da na sameta a gidan nan nasan lallai kina ckn hadari amma baki saurareni bah, haba shukrah ya xaki yarda da wacce baki taba gani bah baki San daga ina ta fito bah daga haduwa a watsap shikenan? Haba kinsan koda a ce mutanen duniya xasu taru gaba daya su cutar dake kinsan baxan taba kasancewa daya daga cknsu bah , shukrah na xauna dake tun muna yara na dauke ki ne a matsayin Ya'r uwata ta jini bawai aminiya kawai bah..shukrah ba gori xan miki bah amma ina son ki sani cewa nice silar auren ki da yaya"
Shukrah ta xare ido ckn tsananin mamaki shuairat ta cigaba da cewa
"Yes...hakane shukrah ina son ki sani cewa xan iya mallaka miki duk abunda nake dashi a duniya bcos na dauke ki ne as my blood sister but meyasa xaki amince har mutane su shiga tsakaninmu? Y shukrah? U knw I Lov u"
Nan shukrah ta rungume shuairat suna ta kuka mai ban tausayi dakyar Suka sagaita kukan shuairat tace
"Ynxu duk ba wannan bah..ina son ki daura damarar gyara rayuwar aurenki ba don ance miki baxaki kara haihuwa Ke shikenan kin gama rayuwar aure bah no! Shukrah ki daidaita da mijinki Ku xauna lfy ki nemi lahirarki ki ajiye komai a gefe pls..
Shukrah tana kuka tana Neman gafara tana cewa
"Nasan duk duniya bayN iyayena bani da sama dake shuairat ki yafe min don Allah ba laifina bane sharrin shaidan ne"
Harararta tayi ckn wasa tace
"Ba wani sharrin shaidan dolancin ki ne ya jawo hakan"
"Ehh..koma menene de na amince ki kirani dashi nasan na cancanci hakan "
"C'mon ni baki min laifin komai bah..kedai ki bawa yayana hakuri Ku xauna lfy , shukrah kinsan Ke aminiyata CE kuma yar uwata umaima kuma ya'ta ce don haka ina Neman alfarma a wajenki pls ki danne xuciyarki ki daure Ku xauna lfy kishin hauka ba naki bane, babu ruwanki da ita ki kame girmanki kiyi sabgar ki pls"
"Insha Allah bani da matsala da wannan"
"Yawwa ..haka nake so kawata"
Shukrah ta sake rungumarta har ynxu bata
Daina kuka bah shuairat tace
"Haba kukan ya isa pls hajiya" murmushi tayi sannan ta juya gun salman tace
"Kinga har na manta da dana , rabona dashi tun kuna wankan jego"
Shuairat tayi dariya tace "baxai kira ki mom bah yana fushi dake"
"Ah ah yayi hakuri don Allah" daga nan ta dauki yaron katoto dashi tana cewa tubarakallah.shuairat ta tashi ta fara gyara gidan shukrah de se kallonta take tana jinjina mata a ckn xuciyarta shuairat tace
"Malama ba kallo xakiyi bah ki sauke wannan lukutin kixo mu kama aiki bamu da lokacin xama se mun gama gyara gidan nan"
Shukrah na murmushi ta nemi xani ta goya shi wannan suka cigaba da aiki, bayan sun gama gyara koina yayi fes Suka kunna turaren wuta se qamshi Ke tashi daga nan Suka fada kitchen lafiyayen girki sukayi abinci kala 3 Suka dafa.shukrah ta fada wanka tayi ado Wanda rabonta da kwalliya tun ranar fansan auren umaima , tayi kyau sosai ta fito fes shuairat ma ta watsa ruwa sannan tayi ma salman wanka ta chanja masa kaya daga nan Suka ci abinci bayan sun gama Suka cigaba da hirarsu, shuairat ta kawo mata tsaraba tun xuwansu China Hutu ..English wears ne masu kyau da kuma Chinese gowns da turaruka masu tsadan gaske shukrah kam se hawaye take shuairat na mata dariya tace
"Ke..namanta ma ban gaya miki bah, an sama min admission a new Delhi maybe next week xamu tafi"
"Da gaske wow na miki murna bestie Allah ya bada sa'a
"Ameen sahibata "
Daga jin wannan sunan shukrah ta hada rai shuairat tace
"Yaya de? "Mtsw..sahiba da kika kirani dashi ne ya tunamin tsinanniyar yarinyar can"
Dariya sosai take mata haka Suka cigaba da hira har bayan azahar shuairat ta kira driver nan sukayi sallama bayan ta tabbatar ta bawa aminiyar tata shawarwarin yanda xata shawo kan mijinta da kuma wasu bayanan sirri😜😜Daga nan sukayi sallama har bakin mota Suka rabu ckn kewar juna.
Karfe 8pm ya shigo har ta fidda ran ganinsa ya shigo tare da waleed wani farin cki ne ya lullubeta take ta rungumi Dan nata se kuma hawaye ya cika idanunta bash yayi saurin kawar da kai gefe dakinsa ya wuce dakin an gyara shi tsab se qamshi Ke tashi nan ya fada wanka.shukrah kuwa se nan nan take da waleed kamar xata hadiyeshi tana kaunar yaron nata haka ta xuba masa abinci ita take basa a baki har ya koshi ta dauko masa chocolate yNa xaune a samN cinyRta yana xuba suru2 dai2* nan bash ya fito ckn jallabiya qamshin turarensa ya mamaye falon shukrah tana satar kallonsa yayi kyau sosai waya yake daga ji tasan umaima ce yana lallabata akan ta kwanta tayi bacci wani kishine ya turnuketa dakyar take karanta innalillh nan ta Dan samu sauki ta daure dakyar tace masa
" a xuba maka abinci ne" yana faman danna waya ya amsa da
"Barshi kawai bana jin yunwa" waleed yace
"Abba ba dazu a mota kace yunwa kke ji bah"
"Na koshi my dear muje kayi wanka ka kwanta koh"
"Abba ba xamu koma gidan mama ba"
"Sorry nan xamu kwana se gobe mu koma koh"
"Toh"daga nan ya ja hannun yaron Suka wuce dakinsa shukrah tayi niyyar share sa amma ta tuna shawarwarin shuairat dole ta kwantar da kai.. Haka ta tashi tabi bayansu tace xata ma waleed wanka babu gardama ya amince ta masa wanka tare da shafa masa mai uban ya fito da kayan barcinsa aka sanya masa nan ya kwantar dashi tare da tofa masa adu'oi ya kwanta a gefensa ya cigaba da danna waya.
Shukrah ta gaji da tsayawa ta koma dakinta ta sake wanka tare da saka er rigar baccinta mai daukar hnkli ta fesa turaruka daban2* sannan ta koma dakin nasa. waleed yayi bacci shi kuma yNa nan yana danne2* a wayarsa da alama chat yake da matarsa ta xauna a gefen gadon ckn sanyin murya tace
"Bbn waleed ka yafemin nasan nayi kuskure kuma..
"Na yafe miki shukrah don't worry jeki ki kwanta "
Hawaye ne ya cika idonta a hnkli Suka fara sakkowa bash ya cigaba da abinda yake , sheshekar kukan nata ne ya janyo hankalinsa ckn Sauri ya daga kansa dama tunda ta shigo bai kalleta bah se ynxu...wow tayi kyau sosai shi kansa yasan tafi umaima diri cos tana da Dan jiki kadan take ta burkita masa lissafi ckn kasala yace
"Me na kuka kuma bayan nace na yafe miki ..haba shukrah ki daina kukan pls"
Bata sauraresa ba ta cigaba da kuka a hnkli ya sakko daga gadon ya dawo bangaren da take cak ya dagata sai dakinta ya dira ta kan gado yace
"Kiyi hakuri ki daina kuka na hakura ok..am sorry too nasan na miki laifi also ki yafemin" ckn dabara ta rungumesa yana jin dumin jikinta de labari ya chanza 🙈🙈 bakinsa ya tura ckn nata nan Suka fara kissin juna passionately tabbas yasan yayi missin nata ko kuma in ce sunyi missing din juna about 3months ko fiye da hakan..hmm a wannan daren shukrah taji jiki 😜😜 bash kuma se sambatu yake.
*ina theme shukrah Ku fito mu taka👯👯*
*theme umaima nko??*😏😏
Lols...
[2/21, 2:43 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*99*
By *Reefat yahya*
Albishirn da mr president yayi wa shuairat dama na samun admission ne , ya sama mata makaranta a new Delhi can kasar India. Bayan kwana2 shuairat tayi sallama da en uwa da abokan arxiki jirginsu ya daga xuwa delhi tare Suka tafi da mr president sultan kuma ya koma gidan umaima a can xai cigaba da xama.
Sun sauka lfy mr president dama ya kama musu gida.bayan sati 1 shuairat ta fara xuwan skul salman kuma an kaishi day care mr president yana gudanar da harkokinsa ckn kwanciyar hnkli, haka rayuwarsu ta kasance ckn so da kulawa kullum suna waya da en gida salman ya kara haske ya girma yyi kyau sosai, sunyi shekara 1 a can da yake shuairat suna Hutu a makarantar tasu donhaka Suka shirya kawo xiyara a Nigeria.
Bash tare da umaima da sultan su sukaje tarbansu a airport umaima ta kankame shuairat tana dariya tace
"Wow..mom kin kara kyau gskiya xaman Delhi ya karbeki "
"Rily...
"Yeah...Allah kinyi kyau sosai"
Suna dariya ta juya gun dad yana dauke da salman tace
"Oh..sweetie an kara girma irin wannan jiki haka"
Tasa hannu ta karbesa sultan ya karasa kusa da shuairat yNa cewa
"Mom I rily miss u"
"Miss u more my boy.. Daz y nace tare da kai xamu koma"
"Allah mom...gskiya naji dadi"
Bash ya gaisa da surukin nasa ckn jin kunya umaima ma haka tana wani sunne kai sabida katon cki ne da ita yakai 9months haihuwa ko yau ko gobe. Shuairat ta CE
"Umaima da karanbani ..ina Ke ina daga salman a ckn wannan condition din da kke cki"
tasa hannu xata karbeshi ta cigaba da cewa
"Duk laifin dad ne yaro ya iya tafiya da kafafunsa amma kullum yana hannu tamkar wani jariri"
Mr president yayi carab yace
"Aa aa hajiya kada ki wahalar min da yaro bani shi a nan"
Yasa hannu ya karbe salman yaron se dariya yake daga nan Suka shiga mota se gida.
An share gidan ko ina fes fes ga abinci an jera musu a falo Suka xauna gaba daya ana ta hira masu aiki na shigowa suna musu Barka da xuwa mr president ya shige cki ya barsu shuairat tana murmushi ta kalli umaima tace
"Mom 2b"
Kunya ne ya kamata ta rufe fuska tana dariya tace
"Mom ki tayani da adua Allah a tsorace nake kullum ckn fargaba nake kwana"
"Dong worry insha Allah zaki sauka lfy babu wata matsala..ba kina tofa yasin da na gaya miki ki yawaita yi bah"
"Ehh ..ina yinsa ever month"
"Masha Allah...Allah ya raba lfy"
"Ameen mom Nagode"
Salman ne ya shigo tare da sultan yana tafiya irin tasu ta yara a hnkli yake takawa sultan na masa wasa se dariya yake gashi yana koyon magana umaima tabi yaron da ido daga bisani ta juya gun shuairat tace
"Allah mom kin iya haihuwa..bana gajiya da kallon sweetie "
Dariya sosai shuairat tare da cewa
"Kedai kina son sweetien nan naki..Allah yasa ki haifi mai kama dashi"
"Ameen wllhi da naji dadi kuwa..nayi nayi muje scanning HP Nah yaki amincewa wai mu jira lokaci"
"Hmm ai halin yaya se a slow..anyway kwana nawa ma ya rage, Allah de ya saukeki lfy"
"Ameen"sallama Suka ji daga bakin kofa shukrah ce ta shigo tare da waleed se kuma bash yana biye dasu a baya
"Oyoyo anty shuairat"
"Wani irin anty ..bayan kin ki xuwa daukata a airport ai takardar saki xan baki"
"Wayyo...mijin a min afuwa"
Dariya suke shukrah ta karasa ta xauna kusa da shuairat umaima ta mata Barka da xuwa ta amsa ba tare da ta kalleta bah , bash ne ya jawo hnklinsu yana yi wa umaima magana da cewa
"Baby akwai abinda kke bukata ne"
"Aa ba komai"
"Babu inda yake miki ciwo"
"Babu"
"Ok ki kular min da kanki da kuma baby Nah xan fita se dare xan dawo mu koma gida koh"
ta shagwabe fuska tace
"Haba HP ba anan xan kwana bah"ganin abun nasu ba karewa xaiyi ba
Shuairat ta wayance tace
"Kwana kuma? I tot da dawo wankan jego ne "
Bash ya harareta da cewa
"Wankan bom ne...babu inda xata dawo a gidan mijinta xata haihu a can xatayi wanka"
"Oh..yaya ko kunya babu Allah ya bada saa ka tafi nikam ka katse mana hirar mu"
Yana dariya ya juya yace
"Mmn waleed na tafi"
"A dawo lfy" ta amsa a gajarce daga gani kasan ranta a bace.bash ya juya yayi tafiyarsa umaima tayi saurin bin bayansa ko me xata gaya masa oho!
Idanun shukrah ya cika da kwalla shuairat tayi saurin cewa
"Haba bestie karki ban kunya mana..ynxu dan wannan abun ne xaisa ki kuka? Idan ta haihu kuma sumewa xakiyi kenan.. Pls act maturely ki danne xuciyarki nasan cin fuska ne amma kiyi hkri kiyi behavin kanki kada raini ya shiga tsakaninku"
Shukrah ta share hawaye tana mai cewa
"Ba haushinsu nake ji bah...haushin kaina naji ni na cuci kaina "
"No...kaddara ce babu Wanda ya isa ya hanata afkuwa so just take hrt ki yarda da kaddarar ki kuma ki godewa tunda kin samu kina da daya , wani har ya koma ga mahallicinsa ma baxai samu ikon ganin jininsa don haka yana da kyau bawa ya kasance mai yawan godiya a duk halin da ya tsinci kansa a cki"
"Maganar ki gskiya ce Nagode Allah bar xumunci"
Shuairat ta cigaba da kwantar wa shukrah hankli umaima ta shigo kallo daya ta musu ta dauke kai tayi wucewarta.haka Suka cigaba da hira har lokaci sallah yyi Suka gabatar da sallah tare da cin abinci, umaima bata fito bah don haka shuairat ta ynke shawarar duba ta.
Tana kwance a dakinta ido 2 shuairat ta shigo tare da sallama cki cki ta amsa tamkar bata so shuairat tace
"Ki fito ki ci abinci" "na koshi"
"Lfynki kuwa..so kike ki kashe abunda Ke cikin ki da yunwa , tashi maxa ynxun nan"
"Allah ni nace miki bana jin yunwa"
Shuairat ta tabe baki tayi ficewarta shukrah kuwa tana ganinta ta hada rai shuairat ta koma ta xauna ta fara magana ta ga shukrah na amsawa kamar bata so , umaima ce ta fito fuska a hade ta bude fridge ta debo ruwan sha shuairat tace
"Haba umaima...ya xaki sha ruwan sanyi a ckn halin da kke cki "
"Haka nake so"
Tayi shiru tana mamakin wannan sauyin ckn kankanin lokaci ta juya gun shukrah itama ta hada rai nan shuairat ta gane matsalar ta tashi tsaye ckn masifa tace
"Nifa baxaku maida ni er iska bah...kowacce ta hada rai toh wllhi ni ba munafuka bace ga fili na bar muku kuyi abunda kuka ga dama"daga nan ta haura xuwa dakinta mr president yana kwance ta shigo ckn bacin rai yana kallonta yace
"Wa ya tabo min my lady"
"Mtsww...aikin banxa, nema suke su mayar dani munafuka wllhi karyansu"
"Su waye? "Umaim da shukrah man"
"Aw...kice min aminiyarki da ya'r ki matan yayanki"
Wani kallo ta jefa masa tare da cewa "meaning" "meaning notin ..kedai ki bi a hnkli" haushi taji nan ta fada toilet se cika take tana batsewa mr president kam dariya ta basa ya girgixa kai yace "oh Aysha ba dai rigima bah"
Har dare basu sanyata a ido bah har xuwa lokacin da bash yaxo daukarsu shukrah ta shiga gidan gaba ta xauna umaima tare da waleed Suka xauna a baya, ta cika tayi fam a haka Suka karisa gida.
Bayan kwna 3 da xuwan su shuairat momsi da daddy Suka kawo musu xiyara a wannan Daren umaima ta haifi kyakkyawar erta mace murna a gun bash baa magana shukrah kam kuka ta kwana yi a wannan Daren. Haka en uwa Suka yi ta xuwan Barka.
😍😍
[2/21, 2:43 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*100*
By *Reefat yahya*
*last page*
Ranar suna yarinya taci sunan maman umaima wato zainab anyi shagali sosai mai jego sun sha hotuna tare da en uwa da abokan arxiki a gidan mijinta ta xauna aka hadata da wata tsohuwa ta xauna da ita , bayan 2weeks shuairat taje gidan iyayenta da gidan shukrah da kuma umaima sukayi sallama wannan karon tare da sultan xasu koma hakan kuwa akayi jirgin yamma Suka bi sai Delhi.
1yr leta ...shuairat ta kammala degree nata dama kos din shekara 2 ne tayi ynxu ta fara masters sultan yana js2 salman kuwa yana da shekara 2 da rabi ya gara girma yayi wayo sosai sai shegen surutu muryarsa radau babu maganar da be iya bah .mr president ya bude wani kamfani a nan Delhi na sarrafa gwalagwalai😜 a China kuma yana da kamfanin sarrafa motoci , idan aka zo gida Nigeria kuma abun baa cewa komai don babu inda zaka shiga ka kira sunansa a ce da kai baa San shi ba..yayi kaurin suna yana da kamfanoni da dama ga gidajen mai da sauransu.bash Ke kula masa da harkokinsa na Nigeria se bayan wata 1 yake xuwa , umaima ta sake haihuwa namiji ta Haifa aka rada masa Suleiman suna kiransa Abbas zainab kuma Ummi ake kiranta.rayuwarsu ta kasance ckn so da kulawa umaima ta gama tana kula da daya daga ckn kamfonin mahaifin nata dake Abuja arxiki ya bunkasa babu harkan talauci shukrah ma mijin nasu ya gina mata katafaren boutique tana harkar kasuwanci ckn kwanciyar hnkli a jarida ta samu labarin an damka fatee tana gidan yari a can Kaduna.
Shuairat na kwance a kasan kafet ga katoton cki Wanda xai kai wata 6 idanunta a lumshe suke da alama bacci take ji mr president ya shigo ya xauna kusa da ita
"Pls my lady ki tashi bana son kina kwanciya a kasa ko so kke ki cutar min da ya'
Harararsa tayi tace "wato ni idan naga dama na mutu koh..dama ai Ku maxa haka kuke kunfi son ya'yan Ku fiye da komai mu mata...
"Pls not again Aysha ba haka nake nufi bah ki tashi don Allah"
"Ni ka rabu dani don Allah" ta sake gyara kwanciya ya rike kai haka yake fama da wannan ckin se masifa da shagwaba haka laulayin yaxo mata Abu kadan ta fara fada ko kuma ta fashe da kuka ..ya ja dogon numfashi ya marairaice "haba mom sultan kinsan ba kyau mace ta dinga kwanciya sanyi na shigarta is not gud pls"
"Ni a nan xan kwanta" yasa hannu ya dagata duk da nauyin da ta kara haka ya dagata xuwa daki ya shimfidata a gado nan kuwa ta fara kuka ya xauna a gefe yana lallabata dakyar bacci yayi gaba da ita. Bayan magrib ta farka ta gabatar da sallah sannan tayi wanka , wata doguwar farar Riga ta sa mai dogon hannu a hnkli take tafiya ta fito falo suna xaune sultan yana koya wa salman ABCD mr president yana kallon news ta shigo babu ko sallama fuska a hade salman ya daga kai Suka hada ido yayi dariya yace "lah...mother conpesho(confessor) bhai!( sunan da yake kiran sultan dashi wato yaya da harshen Hindu) bhai ka tuna film da muka kalla na mother conpesho..irin rigarta ne mummy ta shaka" yana magana da harshen yara masu koyan magana wata uwar cafka shuairat ta kai masa ta matse bakin tana huci tace "nice mother confessor? Uban wa yace ka kalli film har xaka rike sunayensu..ban hanaku kallon film bah" ta juya gun sultan cikinsa ya duri ruwa ya sunkuyar da kai yace
"Mom kiyi hkri wllhi...
"Rufemin baki daga yau nayi seizing laptop dinka " salman yana kuka ta turashi gefe nan mr president ya jawosa yana lallabashi yaron se kuka yake ita kuma ta xauna tana karkada kafa ta cika tayi fam ..sultan kuma jin an ambaci xaa rabashi da laptop nan ya fara kuka ya tashi xai koma dakinsa shuairat ta daka masa tsawa tare da cewa "dallah dawo nan ka xauna ina kake tunanin xaka je , ni Saar ka ce don na maka fada xaka tashi ka tafi..ynxu Ku rufemin baki Ku tashi Ku cigaba da karatu ko na tattaka yaro a nan wajen" sum-sum ya dawo ya xauna salman ma ya hadiye kukan da yake don yana tsoron maman nasu bata daukan wargi , mr president de sai kallo kawai yake musu bai tanka bah bayan ta gama yace "my lady can we talk" bata ce komai ba ta tashi ta koma daki yabi bayanta da ido daga bisani ya tashi ya wuce dakin tana kwance a bisa gado tayi matashi da filo se karkada kafa take ya xauna dab da ita tare da rike mata hannu "my lady pls ki rage yawan fadan da kike wa yaran nan xasu fara jin tsoron xama inda kike" "naji xan rage amma kasan yara idan an sake musu kadan shikenan se kaga tarbiyarsu na Neman lalacewa kuma gskiya kana sake musu too much" murmushi yayi yace "oh wannan babyn rigimammiya ce gata da yawan fada ga kuma shagwaba" ta gyara kwanciyarta ya jawota a jikinsa yace "baki ci abinci bah Ayshata y? "Ni bana jin yunwa" "pls ki daure ki ci koda dan kadan ne nikuma I promise u xan kawo miki icecrm" bitt ta tashi xaune ckn jin dadi tace "da gaske ..wllhi kuwa xan ci muje mu fara siyan icecrm b4..
"Haba my lady bani nace xan siya miki bah..trust me" ta tura baki tace "toh ba Kaine ka daina siyamin bah kana biyewa munafukar jankim wai ka hanani yawan shan sanyi da zaki" "yau kuma gum Jan takin ce ta xama munafuka..lallai babyn nan se a hnkli" ta tura baki wai fushi take bata Ankara ba taji bakinsa ckn nata nan ya rikita mata kwakwalwa tuni ya mantar da ita xancen wani icecrm😍😜.
Da safe tana xauna a falo da kofin tea a hannunta salman da sultan Suka shigo bayan sun gaisheta ta amsa ba laifi mr president ya shigo ya xauna tare da manna mata peck a kumatu murmushi tayi ta cigaba da kurban tea nata salman yana xaune yayi shiru mr president yace "fine boy meke damunka" ya bata fuska yace "ba mom ce ta daina kirana da sweetie bah" me zasuyi idan ba dariya bah mr president yace "ah toh..lyk mother lyk son shagwabar de gado ce" murmushi shuairat tayi tace "com here " ba gardama ya karasa kusa da ita ta ajiye cup din hannunta ta daga shi tana nishi "uhm..my sweetie ina sonka kaji..but ka daina kallon film kayi karatu ka xama likita kamar anti jankim.. Ba kacemin kana son saka fararen kaya irin nata bah" "ehh..Jan yiwa bhai allula koh" "ehh..har dad ma zaka masa" murmushn jin dadi yayi shuairat ta kalli sultan tace "zo nan engineer sultan Suleiman.. Ko injiniya ss ne" sultan yana dariya ya dawo kusa da ita ta hadasu ta rungumesu tare da cewa "I Lov u koh..mom tana sonku Allah ya rayamin Ku ya muku albarka" "ameen"Suka amsa har da mr president daga nan tace su koma daki suyi karatu tunda weekend ne babu makaranta da yamma kuma kullum ita take koya musu karatun Qur'an. Mr president ya rungumeta yace "I Lov u Ayshata kina burgeni kin bani komai na rayuwa Allah ya sakar miki da gidan aljannah" "ameen my man Lov u more" wow...Lov birds😍😍😍..
*3montz leta* shuairat ta sauka lfy ta haifi ya' mace kyakkyawa aka rada mata fateema( sunan mama) suna kiranta umaisa, daddy momsi baba mama umaima bash shukrah tare da ya'yansu Suka shiga jirgi xuwa Delhi bayan suna sun kara 2weeks sannan Suka dawo Nigeria. Umaisa Nada shekara daya da watanni 10 shuairat ta sake haihuwa wannan karon namiji ta Haifa aka rada masa bello suna kiransa saleem, a wannan lokacin ta kammala masters dinta tace karatun ya isheta haka Suka dugunxuma xuwa Nigeria tare kyawawan ya'yansu.
Yaran mr president 5 umaima sultan salman umaisa saleem.yana ji dasu tamkar ya hadiyesu amma yafi ji da salman da umaisa musamman ma umaisa yarinyar ta hadu sosai kamar ya'yan larabawa , umaima kuma ya'yanta 6 maza 3 mata 3 ..Ummi Abbas Ahmad feena Azeez shukrah. Suna xaune lfy kalau gwanin shaawa, shuairat ta kara kyau tayi maintaing na jikinta batayi kiba har can bah amma ta cika tayi kyau sosai an xama manyan mata naira ta xauna musu masha Allah.
Suna xaune a makeken falonsu ga yan jaridar tambari magazine sun xagayesu ana musu interview tare da daukansu hotuna saboda mr president ya tsaya Dan takarar shugabankasa kuma ana sa ran xaiyi nasara ga nan yaransu a gefe suma ana daukarsu hotuna wani Dan jarida ne ya matso kusa yace wane heading xaa saka a fuskar magazine din tarihin rayuwarku" shuairat tayi carab! Tace *ni da shugabankasa* murmushi mr president yayi nan ya fara tuna ranar da Suka fara haduwa..ikon Allah kenan.
*ALHAMDULILLH....*
anan xan dakata da wannan littafin nawa as usual bana wuce 100pages a novels dina😜😜 saura kuce am laxy ehen....
Nagode wa Allah subhanahu wataala da ya bani ikon kammala wannan littafin ckn rai da lfy...godiya gareku masoyana da kuke bani karfin guiwa da kuma shawarwari Nagode da kulawarku Lov u all...masu turamin sako da masu kirana ina godiya gareku Allah yabar mu tare..
*gaisuwa gareku*
Anty baby ( ummu Suleiman shuaib yan awaki)
Hadiza Salish Sharif
Abdulazeez sani
Shehu usman Mohd
Maryam k/mashi
Adda benah
Kheeleesat haiydar
Ummi Aisha
Batul Mamman
Maman shakur
Da sauran writers...
*blood is thicker dan water*...sis Reedat (Mmn haisam)
Sis teemah (Mmn afra)
N mie...(Mmn haneef)
*jinjina* gareku (grps)
Matan gidan gyara
Nisa'ul jannah
Professional writers
Duniyar novels
Manshat novels
FGGC yola class of 2012...
N to all fans of *nida shugabankasa* Lov u all
*maryam jika my PA😀👍🏼 jinjina gareki tare da kaneem dost* na gode da taimakon da kuke min😍
*nanasticaly Nah ban manta dake bah..tare da xeetah n teemah lov*...
Allah yasa mu dace.
0 comments:
Post a Comment