Hajiya tace haba lami ,tace wallahi hajiya kuma in zai fita har gurin muta take rakushi suyi ta iskan cin su ay shikam umar saidai ki sallama shi tunda ya auri yar boko,hajiya tace chabbb ay baa haifi ya macen da zan barmata dana ,,,
.umar da husna sinyi wanka sun shirya tsaf dasu kwanin shaawa ,,suka fito daga sashen su rike da hannu suna hira har bakin muta yashiga har ya zauna husna ta rankwafu ta window tace adawu lfy sweety na hannu yasa yashafa mamanta ya mannah mata kiss a goshi,,abin dabasu saniba hajiya na bayansu tana kallon su,,sai ji sukayi ance a lalle abu ya tabbata ka auro jarabbabiya baya wanda kukayi adaki kuma a filin gidah a bainar jamaa sai kunyi ,,yayimaka kyeu umar da tafiya za kai bazamin sallamaba ko ,,,kiyi hakuri hajiya mantuwace ,,,eh dole ka manta ka auro me soyeyyen ido ay,,shidai umar kunya ta rufeshi hakuri kawai yake bayarwa,,,husna kasa magana tayi ,,,hakadai umar ya samu ya tafi,,,
Yana tafiya ta juye kan husna jarababbiya kinbi ki kanainayemin da to ahir dinki, sumsum husna tayi daki tana shuga tasa kuka wannan wani irin Abu ne ni husna dama haka akeyi ne ko nice banyi saa ba,hakadai tagaji,tayi shuru ,,
Tana zaune shuru sai matar ishak tashogo mata suka gaisa suna dan taba hira ,,,husna tace anty kinga na rasa me nayiwa hajiya kamar bata sona,, zara tace hamm halin hajiya me kika gani ne ma ay bakiga kumaiba ,saidai kawai ki tanadi babban hakuri indai kinason zama da umar,,,husna tace nagode hakada,, Zara taita bata shawara ,har ta tafi,,,
Yau watan husna daya agidan ,,,umar ya shirya zai fita ayki yana fesa turare ,,,kawai husna tafara amai umar yakamata ina amai sai karuwa yake kanshi turaren kesata amai saida umar ya chanza kaya tukun yadauketa cidak yasa amuta yashiga yacewa hajiya zaigai husna asbity batada lfy,,ayya Allah yabata lfy ,,maza kuje sai kun dawu ,,har ransa yaji dadi,,,,suna inasa Asibity kwajin farko Akace tana dauke da ciki har na tsawun sati uku ,,,sosai umar da husna sukayi murna akabata makunkuna sukayu gidah,,,
Suna isowa ya kai husna daki sai gurin hajiya yanata washe baki ,,tace auta irin wannan farin cikin ko tasamu ne ya jikin husnar ,,,ay jiki da sauki hajiya Ashema yafara sosa keya ,,,Asheme auta yace ay cikine da ita ,,,ta dada washe baki kai masha Allah Allah yaraba lfy ,,,Amin yace ,,,,muje maza in dubata,,,tare sukashiga husna na kwance kan kujera ,,,ta sako suka gaisa da hajiya ,,,tamata ya jiki tafito,,,,
Bayan kwana biyu umar ne yake aykin gida sbd amai na wahalar da husna ,,,lami tashiga gaida hajiya bayan sun gaisa tace hajiya kina sane da umar kuwa shi yake aykin gidansa gabada sarauniyar na kwace wai ita mai ciki akanta aka suna ne ,,,tace haba banga tazamaba ay ina nan da yazama solobiyu ,,,baram tashiga sashen umar ,,,tasameshi yana wanke2 kuma ya jika inner ways naishi dana husna zai wanke ,,,aykuwa tafara jaraba ,,sbd ka auro jarababbiya shine zaka zama boyi ,,,hajiya kiyi hakuri batada lfy ne shiyasa ,,,rufemin baki akanta aka fara ciki ne ko sauron ba mata bane ,,,ke husna fito ki karbi aykin na ,,shegiya duka dauka kwata kwata kwanki nawa a gidan nan wai harkinada ciki gadon jaraba,,,da kyer ishaq yazu wucewa yajita ya shiga yafito da ita ,,,,
Kuka husna tasa tace umar kaiwa mahaifiyarka mgn mana wannan ay ba daidai bane tarinka min masifa ko yaushe haba,,,,kafin ta karasa yafara masifa haba husna ya kikiso nayi uwatace fa ita kikeso in hanata abin da takeyi ,,to bari kiji dolene in mata biyayya kekuma kimin ,,,dole kiyi hakuri da halinta sbd uwatace ita takawuni duniya kinason inyi yayane,,,,
ran husna fa yabaci tace amma ay ba daidai takeba nikadai ta stana kullu masifa kadau mataki ni bazan iyaba gaskiya,,,ba matakin da zan dauka husna uwatace dole kiyi hakuri da halinta har Allah yakawu mana mafuta in bazaki iyaba hanya abude take baxan bijirewa uwata ba,,,,kuka sosai husna keyi tace
Inna lillahi wannan fitina tayi yawa,,,
Taku ummu farhana
Yawan comments yawan posting π
*BRILLIANT WRITERS ASS*
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*YA,YA, MATAH*
(Abin Alfaharine)
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*BY UMMU FARHANA*
*INAI MUKU FATAN ALHERI DAN ALLAH MASOYA KUI HAKURI*π₯πΊπΈπΌ
*MAI DUBUN MASOYA DUNIYA SHIKE DA MAGANIN DACI*π·πΊπΈπΌ
*DEDICATE TO MY FANS*
*HAKURI DA MASOYI FANS*
*LEEMA FANS*
*SURAYYAH FANS*
*ASMENAT FANS*
*ALFAH FANS*
*SMASHER AND HUBBY FANS*
*BRILLIANT 1&2FAN*
*MARYAM FANS*
*INA MATUKAR GODIYA DA ADDU,UINKU GARENI NA GODE SOSAI*
*BRILLANT INA ALFAHARI DA KU A DUK INDA KUKE ALLAH YABAR ZUMUNCI*
*MY UMMA HARNIY GAISUWARKI DABANCE ILOVE U SOSAI*
*INA CIGIYARKI MOMYN MUSSADIK INA KIKA SHIGA NE FATAN LFY CE TA BOYEKI*
PAGE 5
Kuka sosai husna take sai da tayi mai isarda sannan tayi shuru ,,bayan ta nutsu ta dauki waya takira yayarta surayya ,,,
Surayya na daukan waya husna ta fashe da kuka ,,,lfy husna daga daga wayata sai kuka meyafaru ,,,,nan dai tagayamata duk yadda suke ciki da hajiya da kuma umar,,,,to ay wannan ba maganar waya bace kibari gobe week eid zan shigo maidugurin da wuri ,,,sukayi sallama ,,
Umar ma bayan yafita abin ya dameshi bai ma jira an tashiba ya bar offers yatsaya a wani wurin cin abinci yasiyawa husna ,,,sbd ko ta girka bata iya ci ,,,
Sallamarsa ke da wuya hajiya ta leko ta window tace auta har an taso daga aykin ne yau ,,,,shuru yayi zai wuce tace zonan umar ,,ba yadda ya iya haka ya zagaya yashiga tace bani laidar in gani mika mata yayi ta bude semo ne da miya da ferfeso ,,,tace eyyye wato ita kasiyuwa Dan daurewa karya gindi ko ,,mu ta dafa mana mara dadi ita asyu mata mai dadi ko?
Aa bahaka bane hajiya in tadafa ne bata iyaci ,,,to sabun salo kenan nikam ban taba jiba ace mace waidan tanada ciki bazataci abin da ta dafaba,,,to nima zaci tana ,,yace to barin in siyumiki naki ,,,,aaa duo ya ishemu bani kwano in diba ,,,haka dai badan ranshi yana soba yakawu da diba tabashi sauran,,,
Yana shiga bangarensu husna yasamu tanata amai kamar ranta zai fitah ,,,dagudu ya karasa yanamata sannu haka dai ya wankemata jiki ya dagata cidak sai falo,, kicin ya wuce yadakku plant yazubamata guntun abinci yamikamata ,,,,baiwar Allah tsabar yinwa ita batama kula da hajiya ta diba bah,,,,
Bayan taci tadawu hankalinta ta kalli umar ta harareshi shi umar ma abin dariya yabashi ,,,,yace my husy ya ya shuru tayi bata kulashiba ,,,tasowa yayi yazu inda take yadau kafarta yasa akan cinyarsa yafara mata susan kaya daga kafa ba saurarawa ba har kirjinta yanayi yana shafata daidai kirjinta yace my husy nida beby zamuyi kukawa akan nonon nanfa nima bazan barmishi ba ,,,,idai husna sai lumshe ido take ,,,ciro nonon yayi a riga yakai masa cafka tsutsa yake kamar yasamu lolypop kifin kace me su husna an mantama da fishi an shiga duniyar maaurata ,,,sosai suka farantawa juna rai ,,umar bai sake fitaba yana ciki yana taya matarshi aiki amma saida suka rufe har kufar palo tukun ,,,,,
Washe gari ma dai basu ko bude kufaba kasancewar ranar hutu haka suka gama gyeran gida suka bike da loveπ
Buga kufa sukaji da sauri husna ta zumbula katun hijabi tafito ,,,tana budewa daga yayar ta ihun murna tasa ta rungumeta suka shiga ciki,,,,,
Bayan sun gaisa tasha ruwa umar ma ya gansheta ,,,tace. Umar gunka nazu jiya husna takirani tagayamin halin da take ciki da hajiya shine Nazu inji hakane inko hakane yakamata kadau mataki ,,,shuru ne ya ratsa gurin chan dai umar yace hakane Anty to in hakane wani mataki ka dauka akai ,,,,
Murmushi yayi yace anty,ana daukan mataki akan iyayene ,,,to ko ana dauka nidai ban daukaba ,,,hajiya ita ta haifeni kuma duk da rashin kyawun halinta ina sonta ,,abinda takewa husna ba karamin damuna yakeba amma bayadda naiya inason husna sosai,,,ina jin baci rai sosai in a taba dawani ne yake taba husna zan iya kisama amma hajiya uwatace uwa kuma tafi karfin wasa ,,,,
Nasan husna tana sona to in son da gaskene to ta tayani yiwa mahaifiyata biyayya ,,,in kuma bazata iyaba bazan dau hakkin taba
Jikin surayyya yayi sanyi tace to umar amma dai kayi wani Abu tunda kana da hali kakuma wani wajen man ,,,yace said na Naimi izininta tukun ,,,,tashi yayi yafita
Hakada surayya tayi tabawa husna shawara kuma tace lalle umar yafiki gaskiya kiyi adua Allah yakawu rabuwarku haka dai husna ta hakura badan rants yasoba
*bayan wata takwas*
Hakadai rayuwar take tafiyawa husna da dadi ba dadi ,,,suna kwance da umar bayan sun gama harka ,,,daji ciwon Mara hakadai har takasa bacci ,,,wani fitsari yadameta tana shiga bayan gida ,,tana fitsari sai taji wani ciwo Mara misali salati ta zabga kafin kace me sai ga ya tafado ta rangada kuka ,,,,wani duruwa umar yayi yayi inda yakejin kuka aykuwa yana shiga ya tozali da jinjira sa wutsul wustul take ,,,haka dai suka yanke cibiya sukai kumai dama ita husna ta iya kumai dumin yayarta maikaciyar asivtyce,,,,
Sun gyra Ku ina hatta wankan jinjira sunyi ,,,bayan sungama tace baban amera sunan da take gayamasa tunda tasamu ciki, yace naam tace kaje kagawa hajiya mana,,,, aa kwanta ki huta dasafe sa ji ,,,,
Da Asuba bayan yadawu daga masallaci yashiga yagayawa hajiya ba laifi tayi murna kuma tazo kallon jinjira har tazaba mata suna halimatu sadiya sunan yayarta ,,,
Su lami iyayen gulma har dacewa Ashe da su husna ba a jaraba aka tsayaba har ahaihuwa ma keda mijin kukeyi,husna dai murmushi tayi ,,,,
Anyi suna sosai yan damaturu ma duk sunxo ya taci suna halima yayar hajiya ,,suna cemata leema,,,
Ba laifi hajiya nason lema ita ma husna abubuwa sun mata sauki yanzu ,,,,
Wata lema hudu sai ga wani ciki hakadai shima ansha rigima har ta haifi ,,jamila melat ,,melat nada wata hudu sai ciki rabiaa wato umma harniy,
To An an ne dai hajiya tafasa kuka tace said,umar yakara sure matarsa ka kwanika ga haihuwar yaya mata ,,,gayyar tsiya zasu talauta mata da
Taku ummu farhana
Yawan comments yawan postingπ
*BRILLIANT WRITERS ASS*
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*YA,YA, MATAH*
(Abin Alfarine)
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*BY UMMU FARHANA*
*DEDICATE ASMA,U ZAYYANU MARUBUCIYAR KUYAGAR KUNCI,,KIDIN DABANCE HALINKI MA DAMAN NE INA JI DAKE KUMA INA SON HALAYENKI ,,,KINA YAWAN BANI KWARIN GUIWA ALHERIN ALLAH YA KAIMIKI HAR GADON BACCINKI*❤❤❤
*INA MIKI BARKA DA DAWOWA NAYI MURNA SOSAI SBD MUNYI MISSING NAKI ,MUMYN MUSSADIK*ππ
*BRLLIANT INA SONKO INA JI DAKU INA ALFAHARI DAKU IRIN SOSAI DIN NAN LOVE U ALL*
PAGE 6
sosai hajiya take kuka tana rashin mutumci ,,,daker aka lallaba haji akan tayi hakuri,,
To ita husna abin ma mamaki yake bata a ganita ay ya,ya, matah ma arziki ne,,, hakadai take fama ita da yaran ta basuda sakat a gidan,,,,
Cikin wannan hali umar yasiya wani fili kusa da gidan nasu ya fara gini nan hajiya tace husna bazata kuma gidan ba sai ta haifi namiji ,,,,
Umma harniy ma dai watan ta hudu husna tasamu ciki ,,,sbd balain hajiya cikin ma buyeshi take ,,dan kullum cemata takiyi sbd jaraba ta tsuse mata da da rana yaje Aiki dare ma ba hutu ,,,,π
A haka ta haifi surraya dan dai husna baza ta iya boye yar bane Amma kam da zata boye,da umar yaje ya fadawa hajiya mamakk tayi Dan batama San da ciki ba ,,ko barka taki zuwa tace yaya mata ne barkan mai zataje tayi kiwon banza yasameka umar ka kiwata wa wasu su aura ,,,,yo ya mace inba karuwaci zatayiba ina zata samu kudi ta taimake ka,,,abin dai ba tsari ,,,ko tarun suna hanawa tayi wai zaa talauta mata da,,,,
To shima da umar abin ya fara isarsa shi gabada hahuwar ma yanzu bayaso ,,shekarasa biyar da aure ya ,ya hudu ya yanke shawara bawa husna shawara su huta,,,
Sbd yanzu Sam baya samun kulawa a gurin husna kuma shi mutum ne ma bukaci ,,,
Da kyer yasamu ta yadda akan su huta din ,,,
Husna har ta Dan dawo hayyacinta ,,sbd sury nada shekara daya ,,,suna gwangwaje love dinsu,,,,
Lema da melat ansasu mkrt pree nur ,,umma hary da sury ne a gida ,,,rannan an musu wanka an kaisu gun hajiya duk da dai bawani kulasu takeba
Sukuma iyayen suna falo suna hira suna manne da juna sai ,,,sai ga hajiya tashigo da sury a hannunta ,,wai tana kuka,,tace karbi yarki karbi tsiyarki jara babbiya ga son miji ga son yaya ,,,kin mayarni mai rainu ko in kula da ya,ya, kekoma kina shafe miji,, jibi shigar da kikayi keda karuwa ba banbaci ,,,,
Ran husna ya baci tace niba karuwa bace hajiya mijina nayi ba a titi nayiba,,kuma yaya mata ba tsiya bane rahama ne in sha Allahu sai kinci moreyarsu,,,kuka hajiya tasa tace umar kana jinta ko kanaji tanamin rashin kunya ko ,,,
Hajiya kiyi hakuri wanan ba girmanki bane kinshugo daki babu sallama,,,wanan zubar da mutumcine ay,, oho kabi bayan matarka ko na gode nikuma yau sai zaba koni ko husna ,,,
Kuka take tana sai yazaba ita ko husna,,
Kunjifa fitinaπ
Washi kaina,,,,,
Taku ummu farhana,
*BRILLIANT WRITERS ASS*
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*YA,YA, MATAH*
(Abin Alfahari ne)
π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀π±πΌ♀
*BY UMMU FARHANA*
*DEDICATE TO ASMENAT ZAYYAN ,MARUBUCIYAR BAKIN GANGA,HAR CIKIN RAINA INA JIN DADIN MUAMALA DAKE ,BA ABINDA ZANCEMINKI ,SAI SAKALLAHU KHAIRAN,ALHERIN ALLAH YA KAIMIKI HAR BIRNI SHEHU*
*BRLLIANT NAGODE DA KULAWARKU ALLAH YABAR ZIMUNCI MUYISHI HAR A ALJANNAH*
PAGE 7
Kuka sosai hajiya takeyi wai umar yazaba ko ita ko husna ,,,har kasa umar ya durkusa yana bata hakuri akan tayi hakuri ,,
Au kafito filli kacemin husna kazaba ,takuma fashewa da kuka shima umar sai yasa kuka chak hajiya ta tsaya tace nashiga uku ni rabi umar akan mace kake kuka haka lalle nayi sake ,kawai tajuya ta fita,,,
Sosai husna take kuka tace umar zan fita a rayuwarka kazauna da mahaifiyarka ,kazabeta ka barni ,,,umar yace haba husna kibarni da hajiya nasan yadda zanyi da ita kawai yabi bayanta,,,,
Daker da sidin goshi hajiya ta yarda da sharadi zaiyi aure,,yace Ya amence amma sai ya gama gini,,,
Husna dai haka ta hakura dan ita arayuwa ba abinda tafiso kamar yaranta kuma rabuwa da umar,kamar rabuwa da yaranta ne da tasa ko sun rabu ina zata da yara har hudu,,,malat ce tace momy kiyi hakuri kinji ,,murmushi tayi tace ya wuce kumuje kicin ,duk da yaran kanane tana shiga kicin dasu sbd a gidan badu isa su sakeba ,,,,
Da safe duk yaran gidan sun shirya skull ,,kafin sutafi sai sunbi sun gaida hajiya,,,sunje sun sameta tana raba sweet ,yaran hamza da ishak mazan duk anbasu bibiyu akwa khairat yar ishak itama biyu,akazo kan leema akabata day,,melat ma daya sai cewa tayi haji ya daya naga su affan biyu akabasu,,hajiya tace eh ,melat tace to mukuma day day akabamu,,,
Ran hajiya yabaci tace kunjini da yarinya zaki hada kanki dasu affan ay su mazane ,,,melat tace to khairat ma biyu kika bata,,, ce anbata ,kaji fitinanniyar yarinya nace anbata taci albarkacin yara mazan gidansu kekuwa gayamin akwai namiji a gidanku ne ,ay yara maza albarkace dasu maza bani guri, da gudu ta isa guri momynta tace momy meyasa baki hafi namiji ba hajiya kaka tace wai ,kafin ta karasa husna tace yi shuru melat karki damu da wasa hajiya take miki ,,maza je mkrt ki yi karatu kizama dr ki kaini makka,,,da gudu ta fita,,,
Dafe kai husna tayi tace wannan masifa tayi yawa wai shin me laifin ya,,ya,,mata ne
Haka dai ake tfy yau fari gobe baki,,,
Husna da umar ne suna hirarsu tace my kwana biyufa ina jin mutsi a cikina kuma naga yadan kumbura ,,,yace haba mugani ,,,daga rigar tayi ya dade yana kallon cikin,,chan yace husna anya baciki garekiba ,,,tashi tayi zaune tace haba dai,,,
Yace inaga yaushe kikayi alada tace ay tonda nafara planing banayi ,shuru yayi ,yace Allah ya kyeuta gobe maje asiviy,haka dai suka bige ta harka,
Dasafe sun shiraya tare da yara ,,don zuwa asivity ,,gabadaya suka shiga gaida hajiya,,da ker ta amsa ma husna ,takuma ce ina zaki kin wani jero yaya mata kamar samera ,,,husna murmushi tayi tace zanje asivity bana jin dadine ,,,dariya hajiya tayi tace ankuma kenan,,
A asivity anyi scan an tabbatar cikine ,,,da farko husna ranta ya baci amma kuma ana cewa namiji ne ,farin ciki ya bayyana a fiskarta ,suka rungumi juna da umar suna godewa Allah,,,
Haka suka nufi gida ciki farin ciki ,,suna tafy husna tace my yanxu kam an fasa mun kishiya nasan yau daga hajiya taji zata soni zata bari mukuma sabon gidah,,,dariya umar yayi yace my husna bazamu gayawa hajiya kina da ciki ba sai mun tabbatar,take husna ta hada rai tace ay yanxoma mun tabbatar tonda Dr ya fada ,,yace hakane duk da haka dai muyi shuru tace to ,,,
Haka husna take ta rainun cikinta bana bata boyeshiba ,,kuwa ya ganshi,,, siyayyar kayan yaro kuwa abin baa magana ,,,
Haka har Allah yakawu ranar haihuwa ikon Allah kuma aka haifi mace,,,,
*cigaban labarin*
0 comments:
Post a Comment