Bissmillahir rahmanin rahim
Ya murd'a k'ofar falo,yana cewa
"Ina y'an gidannan suke,kufito ga matata na kawo muku"
Yafad'a cikin d'aga murya yana k'arasa shiga cikin falon
Wata kyakkyawar budurwa ta taso daga cikin falon dasauri tana fad'in
"Dagaske?tare kuke?
Bata hanya yayi yanacewa
"Gatanan kuwa kina gani"
Budurwar da bazata wuce sa'ar Raudan ba ta k'an-k'anme Raudan cikin farinciki da jin dad'in ganinta
"Oyoyo sister"
Harararta Aasim yayi
"Kinga nazma,saketa daga zuwanta ko hutawa batayi ba zaki wani ruk'ur-k'usheta salan ki gajiyar min da ita"
Nazma ta zame daga jikin Raudan tana dariya
"Afuwan d'an uwa, sister mu shiga kizauna"
Tak'arasa fad'a tana jan hannun Raudan zuwa cikin falon
Itadai Rauda butun butumi tazama,dan takasa cewa komai kallonsu kawai takeyi,ga kuma tambayar dake zuciyarta
Jin Aasim yakirata da matarshi,shida ko maganar soyayya bata tab'a shiga tsakanin su ba,miye na kiranta da matarshi?
Nazma ta zaunar da ita akan kujera tana cewa
"Mekikeson infara kawo Miki?gasashhiyar kaza,ko gasasshen rago? Talo-talo ko kayan ciki?
Aasim yadafa kansa cikin damuwa da surutun nazma
"Kinga fad'ama ammi tafito su gaisa sannan kizo kiyi shirmen naki"
Dariya nazman tayi tana wucewa
Rauda da batace komai ba har lokacin,ganin nazman ta wuce yasa takalli Aasim da sauri tace
"Ina Nan?
Gyara zama yayi yana bata amsa
"Gidan mu Mana"
Tasauke numfashi dansai lokacin hankalinta ya kwanta
"Shine baka fad'amin ba tuntuni?
Yad'aga gira
"To ba gashi yanzu nafad'a Miki ba"
Harararsa tayi tana kallon kayan jikinta
"Ai sai ka fad'amin tun a makaranta nan zamuzo inje incanza Kaya Amma......
Shigowar wata farar mata ya sa tayi shuru
Da ka kalli fuskarta ka kalli ta Aasim zaka gane itace mahaifiyar shi
Matar tazauna akan kujera idanuwanta akan Rauda
Rauda tazame k'asa tana gaisheta
Matar ta amsa fuskarta a sake tana cewa
"Koma kizauna y'ata"
Takoma ta zauna tana duban Aasim daya tashi daga kujerar ya koma wacce mahaifiyar sa take yazauna yana kama hannunta
"Ammi,nayi missing d'inki sosai"
Ammi tayi murmushi tana shafa kansa
"Nima haka,kana lafiya dai ko?
Ya girgiza kai
"Aa ammi"
Nan da nan ko yana yinta yasauya zuwa damuwa tafara tattab'a jikinsa alamun tana so ta ji zafin jikinsa
"Me ke damunka,ina kema ka ciwo"
Yayi dariya yana kama hannunta yana matsawa
"Kwantar da hankalinki ammi,lafiya ta k'alau"
Ta sauke ajiyar zuciya
"Harkasa hankalina ya tashi,katabbata babu abunda ke damunka?
Ya gyad'a kai yana murmushi
Rauda ko Sha'awa suka bata,dan dukkanin alamu akwai soyayya da shak'uwa me k'arfi a tsakaninsu
Dede lokacin nazma tadawo falon d'auke da wani fankacecen tire
Wanda yike shak'e da takarcen kayan ciye-ciye dana lashe-lashe
Aasim yarik'e baki ganin yadda tad'auko tiren da k'yar
"Nazma duk wad'annan kayan ina zaki kaisu?
"Na antyna ne,ita na kawo mawa"
Dariya sukayi gabad'aya,ammi tace
"To kai mata sashensa,dannasan nan bazata iya sakewa ta ci ba"
Nazma tace to tana juyawa
Ammi tace tana kallon Aasim
"Yaro tashi kakaita sashenka"
Wata yarinya da bazata wuce shekaru biyu da rabi ba,ta tashigo falon rik'e da k'atuwar y'ar baby
Tafad'a jikin Aasim cike da jin dad'in ganinsa
Shima cikin farinciki yad'agata yana juyi da ita
Suna ta dariya,sannan ya rungume ta yanacewa
"Ina kika je banganki ba tunda nazo sai yanzu"
"Nade tallon wuwa"
Tafad'a da maganarta ta yara da bata gama iyawa ba
Ya dire ta a k'asa yana yimata nuni da Rauda dabata lura da ita ba
Aiko tana ganinta ta ruga aguje tayi wajenta
Rauda tad'auketa tana kallon yarinyar,farace k'ar kamar lantarki, kyakkyawa,ga gashi da aka kama mata da rimbom wanda yasauka har gadon bayanta
Lokaci d'aya taji yarinyar ta shiga ranta,
"Miye sunanki?
Rauda ta tambayeta tana kallonta
Cikin gwalantonta yarinyar tace
"Tatida"
"Tatida? Rauda ta nanata
Ammi tayi dariya tare da cewa
"Shahida ta ke so tace"
Rauda ta gyad'a kai tana murmushi
"Shahida,shekaraki nawa?
Hannu shahida ta d'aga tana nuni da yatsunta guda uku
"Shekararki uku?
Rauda ta tambaya tana mamakin wayon yarinyarShahida ta d'aga Kai
Alamar eh
Ammi tace
"Kinga y'ata karki biye ma shirmen shahida,tashi kuje kisa wani abu acikinki"
Rauda tayi dariya,tana mik'ewa rik'e da shahidan a hannunta
Aasim yayi gaba tana binsa a baya,wani madai-dai cin falo suka shiga
Komai na falon kalar golden ne,kama daga kan kujeru,kafet,labulaye kai komai na d'akin kalar golden akayi ado dashi
Yayi Mata nuni da kujera
"Bissmillah,zauna"
Ta zauna hankalinta na kan shahida gabad'aya k'aunar yarinyar ya shiga zuciyarta
Ta rasa dalilin hakan
Ko dan tanason fararen yarane oho
Aasim ya matso da zagayayyen tebur d'in da nazma ta d'aura tiren akansa gabanta yana cewa
"Madam ajeta fa zakiyi kici abinci"
Tad'an kallesa gami da cewa
"Nifa banajin yunwa"
Komawa yayi kan kujera ya zauna yana dubanta
"Kedai kice ganin shahida ya k'osar dake,da alamu tashiga ranki ko?
Rauda ta jinjina kai tana murmushi
"Kabari kawai,dan Allah ina mamanta take?
In tambayeta ta bani ita"
Ya rausayar dakai yace yana mik'ewa yad'auki shahida
"Bari inkaita gurin ammi,dan ba barinki zatayi kici abincin ba"
"Please Aasim kabarta,zanci Allah"
Be saurareta ba ya sab'a shahida a kafad'a ya yi hanyar fita
Shihada na d'aga mata hannu alamar bye bye
Ajiyar zuciya Rauda tasauke,azuciyarta tana addu'ar allah yabata irin shahida
Bayan yafice tamaida kallonta ga tiren dake gabanta,babu abunda babu akai,nama,nono,abinci ma kala-kala gashinan tarkace wasu ma bata tab'a ganin kalar su ba
Takuma sauke ajiyar zuciya tana tambayar zuciyarta,haryaushe daga zuwanta aka shirya mata wad'annan abubuwan?
Tunda a fahimtar da tayi basuma san da zatazo ba
Shigowar sa ne ya katse mata tunanin data fara,
"Wai haryanzu baki fara cin komai ba?
Ya tambaya yana zama a gefenta dayike kujerar da take kai three seeter ce
Bata ce mai komai ba,ya d'auko wani juice ya tsiyaya mata kofi yana mik'a Mata
Numfashi ta sauke tana kiran sunansa
"Aasim!
Yad'ago suka had'a ido
Tayi k'ok'orin cigaba da kallon cikin idonsa
"Meyasa kace y'an gidan ku ga matarka ka kawo?idan suka d'auka dagaske muna soyayya fa?
Hmmmmm ya sauke guntun numfashi
"Meyasa kika tambayeni?ko laifine dan nafad'i hakan?
Ta d'aga kai alamar eh tana kurb'ar juice d'in da ya mik'omata
Sannan tace
"Kadube kanka da kyau,kaduba irin baiwar kyau da allah yayi maka,sannan ka kalli gidan ku
Tafad'a tana zagaye falon da idanuwanta sannan tacigaba da cewa
"Kai ba k'aramin mutum bane,tayaya zaka dangantani da matar ka,kadubeni da kyau,ni ba kyakkyawa bace kuma ni ba y'ar babban gida bace,shin baka tunanin zasuji badad'i ayayinda kafad'i hakan?
Tak'ara sa maganar tana kallonsa
"Ina sonki"
Taji yafad'a,tayi y'ar dariya
"Ni maganar gaskiya Nike maka, please ka aje maganar wasa"
"Ina sonki"
Ya kuma fad'a
Ta ajiye kofin tana tambayar sa
"Wai kasan mekake cewa kuwa?
Akaro na uku ya kuma mai-maita wa
"Ina sonki"
Ta kallesa sosai tana nanata abunda yace
"Kana Sona?
Zamewa yayi daga kan kujeran yana kama hannunta
"Ina sonki Rauda,ina k'aunarki kece farin cikina"
Sororo tayi tana kallonsa tana kuma mamakin sa
Ya cigaba da cewa
"Meyasa baki fahimci cewa ina sonki ba tuntuni?
Ya kamata ace kin fahimci inasonki ko ta irin kallon da nike miki"
Ta zame hannunta daga rik'on da yayi mata tace
"Dan allah kabar maganar Nan, kaima kasan ba abu me yuwuwa bane"
"Miyene baze yuwu ba Rauda?
Ya tambaya da alamar damuwa a fuskarsa
Tasauke ajiyar zuciya tare da cewa
"Wai tayaya ma soyayya zata yuwu a tsakanina da Kai?
Nida kai sam ba mu dace da juna ba"
Mik'ewa yayi yana kama hannunta
"Tashi muje,infad'a agaban ammi,kisan cewa da gaske nikeyi"
Fizge hannunta tayi da sauri
"K'afad'a agaban ammi?dan allah karufamin asiri,ni muje ma ka maidani makaranta"
Tafad'a cikin zaro ido
Ya koma ya zauna yana sauke numfashi
"Shikenan,amma ki yarda ina sonki dagaske,dan Allah"
Dawowar nazma falon yasa suka bar zancen
"Haba antyna, kamar baki ci komai bafa nike gani"
Nazma tafad'a yayinda tak'ara sa shigowa falon
Rauda ta yi murmushi tace
"A k'oshe nike shiyasa"
Nazma ta gyad'a kai cikin nuna rashin jindad'i
"Shikenan Amma zan tattara miki su kitafi dasu,kuma dan Allah karkice aa"
Rauda ta gyad'a kai har lokacin da ragowar murmushi a fuskarta
"To shikenan nagode"
Ta k'arasa fad'a tana mik'ewa
"Muje kamaidani banaso dare yamin awaje"
Tafad'a tana kallon Aasim
Bece k'ala ba ya mik'e yana d'aukar wayoyinsa ya zuba su a aljihu
Yayi gaba,yayinda suka jera ita da nazma
Babban falo suka dawo,inda ammi take
"Badai har zaki tafi ba?
Ammi ta tambaya yayinda taga fitowarsu
Rauda ta durk'usa cikin girmamawa tace
"Eh zantafi,banaso nayi dare ne"
Ammi ta jinjina Kai
"Eh kinada gaskiya,jirani to inazuwa"
Tafad'a tana mik'ewa
Batafi minti biyar ba tadawo rik'e da k'atuwar leda
Tamik'a ma Aasim tace
"Gashi kasa mata amota,y'ata sai yaushe zamu sake ganinki?
"Insha'allah idan na samu lokaci"
"To shikenan nagode kinji"
Sukai sallama,Rauda na dube-duben inda zata hango shahida
Sai da suka fito zasu shiga mota,sannan ta hangota
"Shahida"
Ta kira sunanta,aiko tana jiyo kiran ta rugo a guje
Rauda tad'auketa tana cewa
"Ina ta nemanki muyi sallama ashe kina waje"
"Tafiya da tiyi?
Shahida ta tambaya tana kallonta
Rauda tad'aga kai alamar eh
Aiko Sai tayi narai-narai da ido zatayi kuka
Cikin d'an mamaki Rauda tace
"Shahida,baki so intafi ne?
Tad'aga kai alamar eh batason tatafi
Rauda tayi murmushi soyayyar yarinyar nak'ara shiga zuciyarta
"Karki damu zandawo nan bada jimawa ba"
Shahida ta girgiza Kai alamar bata yadda ba
"Nide kan titafi"
Rauda tayi shuru tana kallon ta sosai hakanan take jin zuciyarta wani iri,dan ita kanta bata son rabuwa da yarinyar
Aasim dake tsaye yana kallonsu ya mik'oma shahida hannu alamar tazo
"Shahida zo inkai ki gurin ammi kinji,nan da kwana biyu zanzo inkaiki gurinta kinji?
Ta mik'a mai nata hannun yad'auketa
Yace
"Yauwa Small habibty"
Wata kyakkyawar mata da bazata wuce shekara talatin ba tak'araso wurin
Suka gaisa da Rauda sannan ta amshi shahida a hannun Aasim ta juya
Basu dena kallon juna ba ita da shahida har saida matar ta sha kwanar falon
Rauda ta sauke ajiyar zuciya me nawi tana maida kallonta ga Aasim
"Wannan itace mamar shahida?
Aasim ya girgiza kai yace
"Aa me kula da itace"
"To ina mamarta take"
Be bata amsa ba ya zagaya ya bud'e motar ya shiga
Itama shiga tayi tana nanata tambayar ta
"Nace ina mamar shahidar fa?
Yatada motar yana cewa
"Meyasa kike tambaya akanta?
"Saboda kawai inaso inganta,dan ta iya haihuwa data haifo kyakkyawar yarinya irin haka,allah zuciyata ta kamu da son yarinyar"
Ya jinjina kai
"To nikuma fa?
Takallesa tace
"Kai kuma me?
"Zuciyarki bata kamu da sona ba?
Ta jingina da kujerar motar tana bashi amsa
"Dan Allah ka ajiye maganar wasa"
Ya jinjina kai yace.
"To shikenan tunda soyayya kin mai data wasa bari inyi miki ta gaske
Zaki aure ni?
"Miye?
Tatambaya tana d'an zaro ido
Yace
"To kince maganar soyayya wasace,aure kuma ai shi gaske ne ko?shine nace zaki aureni?
"Dan Allah ka rufamin asiri"
Tafad'a
Ya k'ara gudun motar yana cewa.
'kamarya in rufa miki asiri?
Ta gyara zama tana dubansa
"In aureka?cap ai tsoratani zaka rink'ayi idan dare yayi"
Yayi dariya har fararen hak'oransa suka bayyana
"Nidai nace ina sonki,kisoni ko karki soni wannan matsalar ki,danni soyayya dake ba gudu ba ja da baya"
Dariya ta kuma yi
"Allah Aasim bazan iya soyayya dakai ba,kafi k'arfina Allah"
Ya tab'e baki
"Nagaya miki wannan matsalar kice,amma ni inkinga na ja da baya to nadena numfashi ne Allah"
Dariya tayi tana girgiza kai batare da tak'ara cemai komai ba
Ana kiraye-kirayen sallar magriba suka koma makarantar
Bayan tafito, yafito mata da k'atuwar ledar da ammi tabata ya mik'ama ta
"Masoyiya gashi"
Harararsa tayi
"Wacece masoyiyar taka?
"Ke Mana,kodayike matata yakamata ince tunda baki san kalmar wasa"
Yafad'a cikin tsokana yana gimtse dariya
Itama dariyar tayi ta amshi ledar tana juyawa
"Nagode saida safe"
Murmushi kawai yayi,saida tad'an yi nisa sannan yace da k'arfi
"I love you habibty"
Wai gowa tayi dasauri tana kallon mutanen dake kai da komowa
Ze kuma magana tayi mai nuni da yayi hak'uri dan tasan ba k'aramin aikin d'alubai bane su taru suna kallonsu
Murmushi yayi yana kuma fad'a k'asa-k'asa yadda motsin bakinsa kawai ta hango
Ta maida mai martanin murmushin tana juyawa da sauri
Tana shiga d'akinsu ta tadda salma na ta patrol a d'akin da alamu hankalinta atashe yike
Rauda na ganin haka ta rungume ta tabaya tana fad'in
"K'awalliya romon jab'a,nasan duk rashin ganina ne yasa aketa patrol,to gani na dawo"
Salma ta galla mata harara tana k'wace jikinta
"Sakeni ni,kinsa hankalina yatashi yadda y'an kidnapping d'innan sukayi yawa gabana nata fad'uwa,ina fargaban ko su sukayi awon gaba dake.....
Dariya Rauda tayi sosai,ta zauna gefen gado tana kallon salmar
"To da ba sai ki saido gonar ki kibiya a sakoni ba"
Salma takuma galla mata harara tace
"Wace gona?ai nairata baza tayi ciwon kai ba"
Dariya Rauda takuma yi
"Amma ai idonki ze yi ko,dannasan idan kika dunga rusa kuka sai hawayenki sun k'are"
Tsaki salma taja, tabud'e tukunyar girkin da take yi batare da ta sake kula ta ba
Rauda ta taso daga gefen gadon ta dawo kusa da ita ta zauna
"Kinga k'awata,kiyi hak'uri,wallahi ina fitowa daga lectures Aasim yajani wai muje yawo"
Salma tad'ago tana kallonta
"Yawo Kuma?kuma kika bishi,allah Rauda kiyi hankali da Aasim d'innan,dan wallahi y'ay'an masu kud'i ba kirki garesu ba"
Rauda ta girgiza kai had'i da cewa
"Aa shi ba haka yike ba,ba yadda kike tunani bane,gidan su yakaini,gidan iyayenshi kinga ma abunda mahaifiyar sa tabani"
Tak'arasa fad'a tana janyo ledar,tafito da kayan dake ciki
Atamfofi ne masu tsada guda uku,sai less da doguwar jallabiya,sannan turarruka da kayan kwalliya
Salma ta saki baki tana d'aga kayan
"Daga zuwa gaisheta shine ta baki wannan uban kayan"
Rauda ta jinjina kai tare da cewa
"Wallahi k'awa bakiga kirkin mutanen ba,yadda suke da kud'i da kyau,saiki rantse zasuyi wulak'anci
Amma sam abunda suke dashi be rufe musu ido ba,baki ga yadda suka tarbeni ba,kuma ma kinsan me?
Salma ta girgiza kai
"Inafa na sani ai sai kin fad'a"
"Wai cewa yayi yana Sona"
Rauda tafad'a
Salma ta zaro ido tace
"Wa? Aasim d'in?
Rauda tad'aga mata kai alamar eh
"Babbar magana,to ke mekika ce Masa?
Rauda ta mik'e tace
"Me ko zance masa,ce masa nayi ni bazan iya soyayya dashi ba dan sam bamu dace da juna ba"
Salma ta jinjina kai gami dacewa
"Gaskiya Kam,amma kuma da baki cemai haka ba k'ila rabon jindad'i ne ke kiranmu"
Girgiza Kai Rauda tayi tana dariya tashige toilet dan d'auro alwala
Da daddare,tana kwance bacci yakasa d'aukar ta,hakanan take jin zuciyarta cikin farinciki mussaman idan ta tuno maganganun sa
Ta duba agogo k'arfe d'aya saura
Gyara kwanciyar ta tayi tana rufe ido da niyyar bacci
Saidai a memakon baccin yad'auketa, zuciyarta ce ta hasko mata kyakkyawar fuskarsa alokacin da yike dariya
Ta matse filon dake hannunta a k'irjinta, ahankali bakinta ya furta
"Please zuciya ta kada kifara son Aasim, Aasim yafi k'arfinki ta ko ina ba sa'an ki bane please"
Wayarta ce tayi k'ara alamar shigowar message
Tajanyo wayar ta bud'e
Ganin numban Aasim yasa tayi saurin bud'e wa k'irjinta na d'an bugawa
"Amincin Allah ya tabbata ga tauraruwa ma'abociyar haske da k'yal-k'yali, hak'ik'a a yau dana bayyana miki sirrin dana dad'e ina b'oyewa acikin zuciyata,
Naji kaman na sauke wani nawi da ya rataya a kaina,bazan iya kwatanta miki irin k'aunar da nikeyi miki ba
Ina sonki habibty!
Murmushi tayi tana jin wani farinciki na ratsa zuciyarta ajiye wayar tayi tana lumshe idanuwanta
Wani bacci medad'i yad'auketa
Washegari bata da lectures,hakan yasa suka kwashi kayan su dayayi datti suka fara wanki
Suna cikin wankin kira yashigo wayarta,salma dake kusa da wayar tad'auka zata mik'o mata
"Aje ta mugama kawai"
Salma takalleta tace
"Aasim ne fa"
Rauda ta jinjina kai
"Nasani ai"
Salma ta ce
"Ya akayi kikasani bayan baki duba wayar ba?
Murmushi tayi tana bata amsa
"Saboda gabana yafad'i lokacin da kiran yashigo"
Salma ta rik'e baki
"Kai Rauda badai har kinfara sonshi ba?
Rauda ta girgiza kai
"Allah bawai yau kad'ai ba,tun farkon had'uwarmu,indai kiransa zeshigo wayata to sai naji gabana yafad'i
Haka ma ko ganinsa nayi"
Salma ta matse kayan dake hannunta tana cewa
"Kedai kice kinfara sonsa kawai"
Ganin bata yadda da abunda tace ba yasa tabar zancen
Bayan wata d'aya
Soyayya me k'arfi tashiga tsakaninta da Aasim tayadda inbata ji muryarsa ko ta gansa ba, bata jin dad'i sai taji gabad'aya ta rasa sukuni
Duk yadda tayi da karta sa soyayyar sa aranta kasawa tayi dan shi d'in na dabanne
Arana sai yakirata fin sau goma,kuma duk sanda yakira da irin zafafan kalaman da yike fad'a Mata masu matuk'ar rikita mata zuciya
Kamar kullum tana mak'ale da waya a kunnenta suna fira
Tace
"Ni fa yunwa nike ji kuma yau batajin cin abinci wallahi"
Daga can b'angaren yace
"To mekike son ci habibty, fad'a min ko menene shi zan nemomiki shi"
Ta girgiza kai kamar yana ganinta
"Dambu nike son ci kuma babu inda zaka samo dambu"
"Ina zuwa"
Kawai yace ya kashe wayar
Bayan minti talatin sai gashi yakuma kira tana d'auka
Yace
"Kifito ina wajen hostel"
Tace to,tana ajiye wayar
Kasancewar ana sanyi a lokacin rigar sanyi kawai tad'aura akan doguwar rigar dake jikinta
Tafito,yana tsaye ya jingina da wata bishiya
Tayi mai sallama ya amsa yana sakar mata murmushi me cike da so da k'auna
Ya mik'o mata ledar dake hannunsa yana cewa.
"Amsa maza kije kici,banason kirink'a zama da yunwa"
Amsa tayi tana tambayar sa
"Menene aciki?
"Ba dambu kikace kinason ci ba? shine aciki"
Kallonsa tayi da d'an mamaki
"Habadai?
Ya jinjina kai
"To kiduba kigani Mana"
Tako bud'e ledar ta duba take away d'in da yike ciki
Dambunne kuwa yaji zogale,sai zuba k'amshin man k'uli yikeyi
Mamakine ya kamata
"A ina kasamo dambu a darennan?
Yayi murmushi
"Kedai ba cine naki ba?dan haka kije kici"
Ta girgiza kai tace
"Aa saikafad'amin inda kasamo shi,dan a iya sanina ba inda ake saida dambu anan kusa-kusa kai ko da ranane
Ballantana da daddare, please kafad'a min"
Hak'ik'a naji dad'in comments d'inku,ina kuma k'ara godiya a gareku yawan comments d'in ku shike k'ara k'arfafamin gwiwa Page 12 yana zuwa insha Allah,taku akullum
Yarfillo.
[20/10, 8:39 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🅿AGE📕 1⃣2⃣
Wannan Page d'in nakine mamana,allah ya k'ara miki lafiya yasa kaffarane, ina k'aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
NA KASA MANTAWA DAKE😭
Dede da rana d'aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak'ik'a nayi babban rashi da na rasaki,y'ar uwata hajara aliyu allah Nike rok'o ya jik'anki da rahama,ya gafarta Miki,yasa aljannah ce makomarki Amin😭😭😭
8:57🕐am. SUN,APR 21✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahimYa sauke numfashi idanuwansa na kanta,yace
"Akwai wani sabon restaurant da aka bud'e babu kalar abincin gargajiyan da basa saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo"
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
"Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek'a ko wajen makaranta ba"
Tayi dariya tana gyad'a Kai
"Hakane,to nagode allah ya k'ara bud'i "
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike rawa kad'an saboda sanyin dake kad'ata
"Wai shin kai baka jin sanyi ne?
Ya bata amsa
"Me kikagani?
Rauda tace
"Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi"
Aasim yayi murmushi
"Kafinnazo nan inajin sanyi sosai,amma ina had'a ido dake,sai naji wani d'umi na ratsani, gabad'aya sai naji sanyin ya tafi"
Tayi dariya tana girgiza Kai
"Kai ko?
Shima dariyar yayi yana kwai-kwayar yadda take magana
"Ni me nayi?
Dariya takuma yi sosai tace
"Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d'inka,da dariyar da kake sani,tunda nahad'u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin ciki ina godiya sosai"
Murmushi yayi me cike da abubuwa da yawa
"Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki"
Itama murmushin takeyi
"Dagaske?zaka iya yin komai akaina?
Ya jinjina kai
"Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki"
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin zuciyarta
Ta d'aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad'a ganyayyakinta,suna kad'awa ahankali
"Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba"
Yad'an matso gab da ita suna kallon juna
Yace
"Nima kaina bansan meyasa ba,abu d'aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne ya jarabceni da k'aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi tunanin nafad'a mikine dan kawai soyayya
Wallahi dagaske nikeyi,ina k'aunar ki"
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y'an sakwanni sannan tace
"Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai"
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad'a tayi masa dad'i sosai
"Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki"
Ta gyad'a kai tace
"Shikenan nagode, Saida safe"
"To sai da safe"
Tafad'a tana juyawa,harta d'an yi nisa tajuyo
Yana tsaye inda tabarsa yana kallonta
Tace
"Yadai da magana ne indawo?
Ya girgiza kai yace
"Aa,kawai inaso inga shigarki ne tukunna sai inwuce"
Ta gyad'a Kai tana murmushi
Sannan taci gaba da tafiya
"Rauda!
Ya Kira sunanta,ta waigo tana kallonsa batare da ta amsa ba
"Ina sonki"
Yafad'a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
Koda ta koma d'aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Ta ciro wayarta ta latsa numbansa taji a kashe
Ta maida wayar jaka taciga ba da tafiya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Tashiga damuwa sosai,dan bata tab'a kiran wayarsa taji a kashe ba
Har ta koma hostel, tana k'ara trying d'in kiran
Amma still a kashe
Ta yada jakar ta a k'asa tana zubewa a kan katifa
Salma dake zaune ta kalleta tana cewa
"Yadai?duk gajiyar ce?
Ta d'aga kai alamar eh tare da cewa
"Da gajiyar da kuma damuwa"
Salma tace
"Damuwa Kuma? Tamece?
Ta sauke numfashi tana tashi tazauna
"Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi wallahi,dan bantab'a kiransa naji irin haka ba"
Salma ta jinjina kai
"Gaskiya dole kishiga damuwa,to ko wayar tasa ta fad'i ne?
"Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad'uwa wayar tayi,da yazo yafad'a min kuma da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba"
Salma ta jinjina kai
"Gaskiya, to amma kik'ara gwadawa anjima insha'allah zata shiga,k'ila abubuwane suka mai yawa ya kashe"
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau d'ari amma abu d'aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab'a sanin tana k'aunar sa ba sai a lokacin
Ahaka aka kwashe kwana uku, lokacin tagama jigata da rashin sa
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d'insu ta tambaya
Suka ci karo da salma ita ma tafito daga nata lectures d'in
"Yadai Rauda ina zakije?
Salma ta tambaya,
"Zan lek'a b'angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani Hali yike ciki"
Salma ta jinjina Kai
"To muje inrakaki nima abun nadamuna wallahi"
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d'alubai na zaune suyi group-group sunata fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
Wani matashi suka gani a zaune shikad'ai da handout a hannunsa
Suka k'arasa gurin suka mai sallama
Ya amsa fuskarsa a sake suka gaisa,sannan Rauda tace
"Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
"Aasim?
Matashin ya tambaya, Rauda ta d'aga kai tana fad'in
"Eh "
Yace
"Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen gabad'aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da yawa"
Yak'arasa fad'a yanayimata nuni da wani
Rauda ta jinjina kai
"Hakane,nagode sai anjima"
Tafad'a sannan suka k'arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
Sannan suka tambayeshi
Shima mai-maita sunan yayi
"Aasim, Aasim,anya anan department d'in kuwa?Ta d'aga kai
"Eh"
Yad'an yi shuru yana nazari sannan yace
"Gaskiya bangane shi ba,abokina ko kasan me suna irin haka haka?
Yak'arasa fad'a yana kallon wanda yike kusa da shi
Shima girgiza kai yayi alamar be sani ba
Wanda suka fara tambayar yace
"To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d'inmu yike ba"
Rauda ta girgiza kai tace
"Anan fa yace yike,yananan zaka ganshi wani fari dogo haka"
Ya ajiye numfashi yace
"Nafad'a miki bansanshi ba gaskiya"
Ta gyad'a kai cike da damuwa a cikin zuciyata
"Shikenan nagode,mutafi Salma"
Suka juyo jiki babu k'wari
Salma tace
"To ya akayi haka Rauda?ni al'amarinnan yafara d'aure min kai fa,ace a department d'insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad'aya jikinta yayi sanyi
Wata mota ce tasha gabansu,cikin b'acin rai salma Tafara fad'a
"Wannan wani irin wulak'anci ne zaka wani.......
Kasa k'arsawa tayi yayinda ya sauke Glass d'in motar
Rauda ko kanta na k'asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema takeyi tafi k'arfinta
"Habibty...
Taji anfad'a, dasauri tad'ago kanta,suka had'a ido
Ya sakar mata lallausan murmushi
"Habibty,bazaki amsa kiran nawa bane,duk fushi dani d'inne ya jawo haka?
A memakon tabashi amsa,sai kawai idanunta suka cicciko da k'walla
Nan da nan hawaye yafara wanke mata fuska
Dasauri ya bud'e marfin motar,yafito yana fad'in
"Subhanallah,kuka habibty,me yake faruwa?
Ya tambaya hankalinsa a tashe
Ji tayi k'afafunta suna neman kasa d'aukarta,hakan yasa ta durk'usa tana cigaba da yin kukan
"Habibty please kiyi hak'uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo kanki"
Kasa mik'ewa tayi saida Salma ta kamata tukunna,sannan tashiga motar
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin kukan da ta rasa ko na menene
Ya sauke numfashi yana cewa
"Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin zuciya yike yi"
D'agowa tayi tana kallonsa da jik'akk'un idanunta
"Inyi shuru fa kace?kasa nashiga tashin hankali da tsananin damuwa,ina fargaban ko ba lafiya kake ba,inata fargaban ko wani abune ya sameka,ashe lafiyar ka k'alau.....
"Please kiyi hak'uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya ce takamani kuma cikin gaggawa......
"Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
Ta katseshi,ya girgiza kai yace
"Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman kiranki ba"
"To dakaje fa,meyasa baka kirani ba?
Ta kuma tambaya still idanuwanta na kansa
Ya bata amsa da yanayin damuwa a fuskarsa
"Habibty inda naje waya bata shiga shiyasa"
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k'ara cewa komai baYa matso kusa da ita yana cigaba da cewa
"Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok'eki habibty, ki tsayar da hawayennan haka"
Banza tayi dashi,ya gyad'a kai yana cewa
"To shikenan cikin biyu yanzu dole za ayi d'aya
Ko ki tsayar da hawayennan,ko kuma ki juyo da fuskar yana zubowa ina lashewa"
Harara ta galla Masa,yayi dariya yana kama kunnuwansa
"Please habibty I'm sorry"
Yadda ya lank'wasa muryar tasa taso tasata dariya
Ta share hawayen tana fuskantarsa,
"Dan Allah karka k'ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad'ai nasan tashin hankalin dana shiga"
Tafad'a cikin marai-raice fuska
Ya jinjina kai
"Shikenan, insha'allah bazan sake ba,kin hak'ura yanzu?
Ta d'aga kai alamar eh
Yayi murmushi
"Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad'amin ina kikeso muje,gurin shan ice cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Dariya tayi had'i da fad'in
"Sai dai gurin saida fate"
Shima dariyar yayi yana tada motar
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
"Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab'a tunanin zata k'ara sa wani d'a namiji a cikin zuciyarta ba
Dan gabad'aya a rayuwarta ta tsani soyayya,takuma yi alk'awarin bazata sake yinta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k'ara komawa soyayya
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi
Aasim ya juyo yad'an kalleta sannan yamaida kallonsa ga titi yace
"Yadai habibty,wannan ajiyar zuciya haka?
Ta kuma sauke wata a karo nabiyu sannan tace
"Aasim kasa na karya alk'awarin dana d'aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to gabad'aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya a baya banaso nasake mai-maita wa"
Ta k'arasa maganar idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Da alamu jikinsa yayi sanyi da jin magan-ganunta
"Insha'allah habibty,bazan zama mesaki damuwa ba,abu d'aya nike so agareki...
Yad'an dakata, Rauda ko kallonsa takeyi
Yavcigaba da cewa
"Inaso kiyimin alk'awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a tare Dani,to kiyi min alk'awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba, sannan kuma zaki gafarceni abisa b'oye mikin da nayi"
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad'aya bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba
"Bangane ba,dama kana b'oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
Yayi murmushin da ya tsaya masa iya labb'a kawai
"Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d'auka a lokacin ba"
Ta sauke guntun numfashi tace.
"To wai miye kake b'oyemin ne?
Sai kuma ta dakata alamar ta tuna wani abu, tacigaba da cewa
"Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b'oye kak'i fad'amin ko?
Ya murmushi yana girgiza kai
"Aa,wallahi bayan ke bani da wata Mata"
Tabud'e idanunta tana masa wani kallo
"Eyen,ni d'in ko?to yaushe na zama matarka?
Yad'an yi jim kaman ya naso ya tuna
"Eh to,kaman shekaru hud'u da suka wuce"
"Kai lokacin ma ko sanina kayi,duka-duka ko rabin shekara ma munyi da had'uwa ne?
Tafad'a tana k'walalomai ido
Yayi dariya yace
"Agurinki kenan amma ni agurina had'uwarmu tun bayan shekara ashirin ne?
Ta kuma bud'e idanuwanta sosai
"Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina jaririya ko?
Ta tambayesa cikin yi galala da baki
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
"Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad'a min muna da meeting"
Tace to,harzata bud'e motar kuma sai takoma tazauna
"Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda nashigo motarnan banji ankirata ba?
Yayi k'ok'orin tsaida natsuwarsa guri d'aya yace
"D'azu nike son ince"
Gyad'a kai tayi tana tab'e baki
"Ook muje"
Basu wani b'ata lokaci ba,suna shiga tazab'i kalar ice cream d'in datake so suka fito
Bayan yatada motar sunfara tafiya tace
"Namanta ban tambayi shahida ba,tana lafiya? Ya ammi da nazma?
"Duk sunanan k'alau"
Yabata amsa a tak'aice
Gudu yayi sosai saboda meeting d'in da yace suna dashi
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama ringing be d'auka ba
Tana ajiye wayar message na shigowa ta bud'e
"Habibty bamu gama meeting d'inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki"
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k'irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa yad'auketa
Bayan sati d'aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad'a yin k'arfi
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje yad'aukota
Saboda yace yana da meeting a lokacin
Hakan yasa tafito bakin titi ta tari adai-daita sahu
Sun d'an yi nisa kad'an wata kyakkyawar budurwa ta tsaida a dai-daitan da Rauda ke ciki
Da sallama tashiga, Rauda ta amsa suka gaisa
Napep d'in tacigaba da tafiya
Budurwar da tashi ga napep d'in tace
"Rauda ko?
Da mamaki Rauda ta kalleta jin takira sunanta
"Eh itace"
Budurwar tayi murmushi
"Ni kuma saima"
Rauda tak'ara kallonta, bata tab'a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Saima ta katse mata tunanin da takeyi
"Kinyi mamakin kiran sunanki da nayi ko?
Rauda ta d'aga Kai
"Eh gaskiya danni bansanki ba,to ko makarantar mu kike?
Saima ta girgiza kai alamar aa
"Ba a makarantar ku nike ba malama Rauda"
Rauda ta jinjina Kai
"To ya akayi kikasan sunana?
Saima ta kuma yin murmushi,sunan ki ai sananne awurina,ke bama nikad'ai ba gabad'aya ahalina,babu wanda be sanki ba"
Mamaki yakuma kama Rauda
"Ahalinki? bangane ba"
Saima ta d'aga kai tace
"Eh,amma bawannan surutun ya kawoni ba,meyasa zuciyarki take saurin amincewa da mutane?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K'ara cewa komai
Dan ji tayi tsigar jikinta tafara tashi
Saima takuma yin murmushi,tana cigaba da cewa
"Ya kamata dai kirink'a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare dake akodayaushe
Nabarki lafiya"
Tana gama fad'ar haka ta dire ko cewa me napep d'in ya tsaya batayi ba
Rauda tsoro ne yakamata, jikinta yayi sanyi sosai
Dede lokacin me napep d'in yatsaya a k'ofar shagon saloon d'in
Taciro kud'insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
Me saloon d'in me suna Amira tace
"Yadai customer?lafiya naganki wani iri?
Rauda ta girgiza Kai
"Aa bakomai"
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al'ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta rink'a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
Domin yana tare da ita a kodayaushe?
Maganar Amira ce ta katse mata tunanin data tafi
"Me za'amiki, retouching ko steaming?
"Steaming"
Tabata amsa a tak'aice
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai takeyi
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab'a kawota
Amira ce ta amsa tana bashi izinin shiga
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak'i sid'ik yana ta shek'i
"Wow habibty kinga yadda gashin yayi kyau kuwa?
Amira tayi dariya tana fad'in
"Sai ka biyani da yawa"
Ya rausayar da Kai yace
"Baki da matsala, tunda kina gyara min matata"
Murmushi Rauda jeyi
"Ai nayi zaton bazaka zo ba"
Ya girgiza Kai yace
"Haba nina Isa?muna gama meeting d'in nan nayo direct"
Ta jinjina Kai tana janyo d'an kwalinta zata d'aura gaban makeken madubin da ke manne a bango
Gabanta ne yafad'i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi gaggawar kallonsa a fili
Yana tsaye yana bawa amira kud'i sanye da k'anan Kaya
Ta murza idanuwanta dasauri tana ganin kaman gizo idanun ke mata
Takuma kallon madubin, still da kayan sarautar ta k'ara ganinsa
Maganar saima ce tadawo Mata, gabanta yayi wani mugun fad'uwa
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Kallonta yayi yace
"Yadai naganki a daburce meyafaru?
Ta girgiza kai dasauri batare da tace komai ba
Amira tace
"Nima dai yau tunda tashigo haka naganta"
Yakuma kallonta sosai
"Habibty,lafiya?meke faruwa"
Kuma girgiza kai tayi alamar babu komai
Ya jinjina kai amma be yadda babu komai d'in ba
"Shikenan muje"
Yayi gaba yana yiwa amira sallama
Bin bayansa tayi da kallo gabanta na fad'uwa
Yad'an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
"Yadai,ko baki gama bane"
Ta girgiza kai tana d'aga k'afarta datayi mata nawi a tafito
Yabud'e mata motar tashiga,sannan ya shiga ya tada
Yana cewa
"Kifad'a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce ba"
Tayi k'arfin halin danne tarin fargaban da yike zuciyarta
"Aasim,intambaye ka zaka fad'amin gaskiya"
Ya kalleta
"Eh zanfad'a miki indai nasani"
Ta jinjina Kai tace
"Aasim kai mutum ne?
Ta jeho mai tambayar da be shirya jinta ba
"Eyeh,mene?mekika ce?
Yafad'a cikin sark'ewar murya
"Nace kai mutum ne?
Yayi shuru na y'an sakwanni sannan yace
"Me yasa kika yimin wannan tambayar?
Ta gyad'a kai fad'uwar gabanta na dad'a tsananta
"Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k'afad'a min gaskiya kai mutum ne?
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Eh ni mutum ne"
Girgiza kai tayi cikin rashin yadda
"Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin madubi?
Ya taka burki da sauri yana kallonta
"Suffata Kuma,ayaushe?saidai in gizo idanun ki suka Miki"
Ta gyad'a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud'e tare da sawa akan yatsanta ta danna
Sai ga jini b'ul-b'ul,
"Miye haka habibty,yanka kanki kikayi fa?
Yafad'a dasauri,ta jinjina
" kai nasani ai,kai ma inaso ka yanki yatsanka,saboda in tabbatar da abunda nike zargi"
Girgiza kai yayi
"Habibty baki yadda dani bane?
"Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad'a min gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace"
Tafad'a cikin wani irin yanayi na tashin hankali
"Habibty..,.
Katseshi tayi ta hanyar kama hannunsa zata danna rezar
Yayi saurin rik'e hannunta da d'ayan hannunsa
Sai dai ina,kafin yayi wani yunk'uri ta yanke sa
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ja baya tayi dasauri, k'irjinta yayi wani mugun bugawa
Hannunta tasa akai,ta k'wala ihu
Yayi saurin matsowa yana fad'in
"Habibty narok'eki ki kwantar da hankalinki"
K'ok'arin bud'e motar tafarayi da sauri amma Gam,tak'i bud'ewa
Tafara jijjigata da k'arfi tana cigaba da yin ihu
Ya k'ara matsowa yana kiran sunanta
Ganin k'ofar bata da alamun bud'ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had'e hannun ta guri d'aya cikin kuka da tsananin firgici tace
"Narok'eka kada ka cutar Dani,kayi hak'uri idan laifi nemaka"
Hannunta yakama zeyi magana,ta fizge hannun da sauri
"Kada katab'ani kayiwa Allah kabud'emin infita"
Ajiyar zuciya yasauke tare dacewa
"Kiyi hak'uri ki fahimceni,ki natsu dan Allah"
"Nidai kabud'emin infita,karabu dani kayi hak'uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi ma komai ba......
Tsawa ya daka mata
"Nace ki natsu ko!!!!!!
Shurun ko tayi dan tsawar ta k'ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro ta da ga cikin k'an-k'ara
Aasim ya cigaba da cewa
"Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al'amarin cutarwa a tare Dani?
Yafad'a cikin yanayin damuwa
Sannan ya sassauta murya
"Kiyi hak'uri na d'aga miki murya,amma dan allah ki kwantar da hankalinki,
Tunda Kingane gaskiya ai dole zanyi miki bayani"
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar da ita d'in zeyi ba
Ya numfasa sannan yace
"Ayanzu babu abunda zan b'oye Miki,
Zanyi miki bayanin komai,kuma inaso ki saurareni da kunnen basira
Ki kuma fahimci bayanin da zanyi miki kinji?
Tad'aga kai alamar taji
Yacigaba da cewa
"Ni ba mutum bane,kuma ni ba aljani bane amma ni rauhani ne,
Kamar yadda kikasani sunana Aasim, Aasim bin ramzad,
Mahaifina shine sarki ramzad dake mulkar masarautar rauhanai
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud'u da suka wuce,sannan har da y'a a tsakanina dake"
Zaro ido tayi tana kallonsa
"Aure,harda y'a?kuma Dani?
Tafad'a cikin rawar murya da kuma mamaki
Ya jinjina Kai
"Eh Rauda,shahida da kika gani y'arki ce kece mahaifiyar ta"
Ta kuma zaro ido tana kallonsa
Yacigaba dacewa
"Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare da kinsani ba"
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad'u a Page 13
Yarfillo.🌹 JINNUL

[20/10, 8:39 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
🅿AGE📕 1⃣3⃣
Wannan Page d'innaki ne besty hajiyayye, Allah ya kaimu December musha biki,mu rak'ashe mu kwaso shoki😁😁
Fatan alkhairi ga golden pen writters gabad'aya,ina jinjina muku da kuma fatan Allah yak'ara mana basira.
3:28🕒pm.
WED,APR 24✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim👏🏻
Ya gyara zamansa sosai yana sauke nannauyar ajiyar zuciya
"Duk da banso ace zansanar dake a wannan lokacin ba,amma ya zamar min dole,
Amma ina rok'onki da kisa ma zuciyarki natsuwa, kicire duk wani tsoro dake cikinta
Nasan tsoro wajibine amma kisani bazan tab'a cutar dake ba
Rauda ina k'aunar ki kuma inaso kituna da alk'awarin dakika min rannan,akan ko kingane wani abu da baki sani ba atare Dani,
Zaki cigaba da Sona,bakuma zaki rabu dani ba
wallahi ina yimiki so me tsanani bazan iya rayuwa idan babu ke ba,dan allah ki fahimceni ki kuma amshi uzurina"
Yafad'a cikin wani irin yanayi wanda yak'ara sa jikinta yayi sanyi
Ganin abun takeyi kamar a mafarki,ga jikinta yayi wani mugun mutuwa
Daky'ar take iya motsa jikinta, hak'ik'a zuciyarta na cike da tarin tsoro amma maganganun sa sun d'an rage tsoron
Kallonsa kawai takeyi takasa gasgata al'amarin,wai Aasim ba mutum bane,kenan shine JINNUL AASHIQUE d'in da malamai ke fad'a Mata,yana hana ta aure.
"Rauda!
Aasim ya kira sunanta,ta kallesa kawai amma takasa amsawa
"Kinyi alk'awari zaki fahimceni?
Tad'aga kai alamar eh
Yasauke ajiyar zuciya yana cewa
"Nagode"
Yad'an yi shuru sannan ya cigaba da cewa
"Sunana Aasim,d'a agurin sarki Ramzad, mahaifina shike mulkar masarautar rauhanai.
Yana da mata biyu,da yara biyu
Ni ne nafarko kuma nikad'ai ne agurin mahaifiyata,sai k'anina yarima samran wanda yakasance d'a agurin kishiyar mahaifiyata.
Mahaifina na sona sosai dan yana fifitani a kan yarima sarman agaban kowa, Wanda hakan ke bak'anta ran sarauniya jalila(kishiyar mahaifiyarsa)
Masarautar mu babban masarauta ce dake can wata duniya,muna rayuwa kamar yadda ku mutane kukeyi
Kuma muna saukowa zuwa wannan duniyar duk k'arshen sati sau d'aya domin muga abunda yike tafiya
Mukuma shak'ata,mahifina yana da zafi sosai dan idan yayi magana d'aya to baya canza ta
Amma kuma duk yadda yakai ga zafi,idan narok'e sa akan abu yana yi yakuma hak'ura
Hakan yasa ko samran da mahaifiyar sa idan suna so suyi wani abun sai sunbiyo ta hanyata.
Muntaso cikin rayuwar jindad'i bamu tab'a neman wani abu mun rasa baMuna da k'arfin iko da kuma k'arfin mulki,tayadda ake tsoron mu a ko'ina,duk wani aljani fargaban ya had'u damu yikeyi
Akwai wata rana munsauko wannan duniyar,nida fada wa na,muna tafiya cikin nishad'i da kwanciyar hankali
Kwatsam sai muka fara jin k'amshin salbaan, salbaan wani abune da ake haihuwar rauhanai dashi kuma kowani rauhani da kalar nasa salvaan d'in
Amma abun mamaki sai naji k'amshin shi a duniyar mutane,na lula cikin tunanin ya akayi haka?meke faruwa?
Maganar d'aya daga cikin fadawa nane ya katsemin tunanin dana tafi inda yace
"Ranka shidad'e kajiyo k'amshin salvaan da muke ji kuwa?
Na d'aga kai alamar eh ina cewa
"Naji,amma ya akayi haka?tunda muke zuwa wannan duniyar bantab'a jin irin haka ba sai yau"
Ba faden me suna iliyas,wanda shine babba kuma shugaba agaba d'aya fada wana yace
"Ranka shidad'e idan kabani dama zanje naduba inda k'amshin ke futowa"
Nad'aga mai kai kawai,alamar nabashi
Cikin mintoci k'alilan sai gashi yadawo,yace
"Ranka shidad'e haihuwa ce akayi,kuma k'amshin daga jikin jaririyar yike fitowa,ina ganin kaman a jikinta salbaan d'in yake"
"Jaririya?kuma bil'adama ce?
Natambayesa da mamaki
Ya jinjina kai
"Eh ranka shidad'e"
Gyad'a kaina nayi ina cewa
"Muje inda jaririyar take"
Ko da naje naganki,natabbatar dake mutum ce kuma dakwai salbaan a jikinki,nayi mamaki sosai dan bantab'a ganin irin haka ba
Nayi miki addu'o i nakuma sa wata rauhaniya da tadinga kula dake da kuma al'amuranki"
Daganan naciga ba da harkokina batare da wani tunani akanki ba
Daganan kuma nayi tafiya nisa wacce bandawo ba sai da nayi shekaru goma Sha biyar
Bayan dawowa na,nazo wannan duniyar domin naga abubuwan da suka canza bayan tafiya ta
Munzo wucewa ta wuraren gidanku sai k'amshin salbaa nanki ya bugi hancina
Alokacin ne na tuna dake,dan gabad'aya na manta,natura ma rauniyar danasa ta rink'a kula dake sak'on ina son ganinta
Sai gata ta bayyana,ananne take bani labari akanki,da yadda kikai rayuwa tsawon shekaru goma sha biyar.
Sannan tak'ara da cewa,ayanzu baki da lafiya
Hakan yasa nace mata ina son inganki
Tayi min inso harzuwa d'akin dakike kwance
Koda naganki sai naji gabana na fad'uwa
Nayimata umarnin data fita,sannan nazauna gefen gadon ina k'are miki kallo
Hak'ik'a kin kasance kyakkyawa,na kama hannunki nayi miki addu'a
Sannan natafi,sai dai ko da natafi, zuciyata bata dena tunanin ki ba
Wanda narasa dalilin hakan,wani dare ina kwance d'akina naji babu abunda nike so illa naganki
Hakan yasa naciro wani madubi narik'e a hannuna tare da ambaton sunanki
Bayyanar da kikayi acikin madubin itace mafarin komai,domin babu kaya ajikinki da alamu wanka kikeyi
Nayi saurin kauda madubin domin a k'a'idar mu bama kallon mutane a wannan yanayin
Sai dai zuciya ta ta d'arsu da k'aunarki,
Nakuma sa tsoro me tsanani akanki,tayadda ko aljanun bayi bazasu iya kallonki a wancan yanayin ba
Alokacin dakika cika shekaru sha shida, alokacin nagama afkawa cikin kogin k'aunarki
Ban b'oye wa ammi komai ba,nasanar da ita dakuma auranki da nikeso inyi
Ammi tayi k'ok'orin fahimtar dani akan yaza'ayi ina jinsin rauhan in auri bil'adama?
Na nuna mata cewa nidai ina k'aunar ki kuma inason in aureki idan har tanason farincikina to ta amince min
Tace min to yazanyi da gimbiya saima y'ar k'anin mahaifina wacce tun muna yara take Sona?
Na sanar da ita cewa,ban tab'a son saima ba,ni ke nikeso kuma dake kad'ai zan iya zaman aure
Tunda taga na nace,ta tabbatar da ina yimiki so me tsanani,amma mahaifina fa?tasan inya sani bazetab'a yarda ba
Hakan yasa tace in aureki a sirrance,ta yadda masarauta bazasu sani ba
Na ko yi hakan,dan inbaki manta ba akwai wata rana dakikayi mafarkin wasu fararen mutane sunzo d'aura auranki
To alokacinne aka d'aura aure na dake,na kuma dunga rayuwar aure dake batare da kinsani ba
Wanda zuciya ta ta K'ara zafafa a k'aunar ki,tayadda bana iyayin kwana biyu banzo naganki ba.
Amma babu wanda yasani a masarautar illa fadawana
Alokacin manema suka fara b'ullo Miki,naso nad'auki mataki domin ina tsananin kishinki sai ammi ta hanani tanuna min ba dai-dai bane
Nadaure muka cigaba da rayuwa ahakan,
Alokacin da kikai sha bakwai,alokacinne me martaba yagano auren dake tsakanina dake
Wanda yashiga b'acin ran da duk wani wanda yike cikin masarautar sai da hankalinsa ya tashi
Ya umarci da a hukuntani ni da ke
Nadurk'usa ina kuka ina rok'onsa
Dana ga yak'i,sai na sanar dashi abunda yasa jikinsa yayi sanyi
"Abi,nasan nayi kuskure Amma kagafarceni,idan zakayi hukunci ka hukuntani nikad'ai domin,ita bata san ma ina tare da ita ba,sannan ayanzu tana d'auke da cikina"
Be k'ara cemin komai ba,yasa aka hukuntani abisa laifin b'oye masa danayi
Amma kuma be zartar da hukunci atsakanina dake ba wanda bansan abunda yasa sa yin hakan ba.
Haka lokaci ya cigaba da tafiya,har zuwa lokacin da kika haifi shahida
Duk da me martaba baya son auren,kuma be amince da shi ba,yayi matuk'ar farin ciki domin wannan karonne karo nafarko da aka sami jika a masarautar
Nayi farin ciki sosai haka ma ammi,ke gabad'aya masarautar sunyi farin ciki da haihuwar shahida
Hakan yasa taga gata,da riritawa,kuma tana tare da me martaba a kodayaushe domin yana sonta sosai
Maganar hana auranki kuma,ina kishinki bazan tab'a barin wani d'a namiji ya rab'e ki ba,duk ko ranar da hakan ta kasance to sai dai ranar da numfashina ze tsaya
Rauda wannan shine ainihin gaskiyar dake tsakanina dake,
Dan allah ki amince mucigaba da rayuwa ahakan,babu abunda bazan iyayimiki ba indai zesaki farinci kuma inaso yazama sirri atsakaninmu..........
Ahankali tabud'e idanuwanta da sukayi mata nawi,dan tunda yayi nisa a labarinsa taji kanta kaman and'aura mata dutse
Sai dai a memakon ta ganta acikin motarsa kuma kusa dashi
Sai taganta kwance kan gadonta,ga salma gefenta tana ta sharar bacci
Mamakine ya kamata,ita da take cikin motarsa ya akayi taganta a d'akinsu?
Ta tashi dak'yar ta jingina da jikin gadon,to kodai mafarki tayi?
Ta tambayi kanta tana k'ara yin mamaki,agogo ta kalla k'arfe Sha d'aya nadare
Tabbas mafarki tayi dan alokacin dasuna magana dashi ko magriba ba tayi ba yanzu kuma shad'aya na dare
Ajiyar zuciya tasauke me nawi tana godiya ga allah da ya sa mafarkine ba zahiri ba
Ta janyo wayarta dake gefe ta danna numbansa bugu d'aya yad'auka yana ambaton sunanta
"Habibty.....
Bata amsa ba illa "allah nagode maka"
Datace,daga can b'angaren yace
"Meya faru ake godiya ga allah"
Takuma sauke ajiyar zuciya tare da cewa
"Wani mugun mafarki nayi Wai...........
"Wai ni ba mutum bane ko?kuma inada aure dake harda y'a ko?
Ya katseta
Sororo tayi da wayar a kunnenta, yacigaba dacewa
"Ba mafarki kikayi ba habibty zahirine,ganin halin dakika shigane yasa na maidaki d'aki"
Muryarta na rawa ta kira sunansa
"Aasim! Dan Allah kacemin mafarki nikeyi,taya zaka kasance ba jinsin mutum ba,wallahi ina sonka,idan wasa kakeyi kadena..........
"Hmmmmmmmm habibty,dan Allah kikwantar da hankalinki,ayanzu babu wani abun da ya rage baki sani ba.......
Yafad'a,cikin tashin hankali ta katseshi
"Kak'yaleni haka,kada ka haukatani.....
Ze kuma magana ta maka wayar a k'asa tana fad'in
"Kak'yaleni nace!!!!
Sai kuma ta fashe da Kuka,tana sa hannunta akai
"Wayyoh allah na na shiga uku!!!!!
Kukan da takeyi ne ya tada Salma,
Tafarka a gigice tana tambayar waye ya mutu?
K'an-k'ameta Rauda tayi tana cigaba da yin kukan
Hankalin salma ya tashi
"Me yafaru Rauda?fad'amin me yafaru?
Waye ya mutu?
"Salma,inaso inje gida,inason inga mamana,bazan iya cigaba da zama a makarantar nan ba"
Rauda tafad'a cikin kuka
Salma tace
"Wani abune yasamu maman?
Rauda ta girgiza Kai
"Nidai inason inganta,muje kisani a motar kaduna dan Allah"
Salma tace
"Kinsan k'arfe nawane yanzu da zaki doshi kaduna??
Sannan keda zaki fara jarabawa jibi mezasa kitafi?
Kuma fashewa tayi da wani sabon kukan
"Wayyoh allah na, Salma k'wa-k'walwata zata juye,nashiga uku"
Salma hankalinta yak'ara tashi dan bata tab'a ganinta cikin wannan yanayin ba
"Nace kifad'a min meyafaru,meya sameki?
D'agowa Rauda tayi tana kalle-kalle a tsorace
"Ba mutum bane,ze iya zuwa Nan,kar ya cutar Dani,salma ki taimakeni,wallahi tsoro nikeji"
Tak'arasa fad'a tana k'ara shigewa jikin Salman
Maganganun da tafad'a yasa salma tunanin kotayi gamo da aljanune?
Hakan yasa tafara tottofa mata addu'o i,tanayi mata fifita
Aiko bata dad'e ba bacci me nawi yad'auketa
Salma tayi jugum tana kallon ta,da kuma tunanin abunda yasameta.
Washegari,bata farka ba sai wajen k'arfe tara na safe
Salma tadad'e da gama abun Kari,tana zaune gefenta tana jiran farka warta
Ganin tabud'e ido yasa tace
"Sannu Rauda kintashi?
Tad'aga mata Kai tana tashi ta zauna
"Yajikinnaki?
Salma ta kuma tambayar ta,
"Dasauk'i"
Rauda tabata amsa,salma tamik'e tana cewa
"Bari nakai miki ruwan wanka,inkinyi sai ki karya"
Bata ce mata komai ba tabi bayanta da kallo,sannan ta mai da idanuwanta kan wayar ta da salma ta had'a mata wacce ta ragar-gaje sakamakon bugata datayi a k'asa jiya
Bayan tayi wankan Salma tahad'a mata tea sannan tace
"Ki kwanta ki huta,zanje cikin makaranta indawo"
Gyad'a mata kai kawai Rauda tayi,tana bin bayanta da kallo harta fice
Sannan tasauke numfashi,tana tunanin abunda yafaru jiya
Takasa gasgata al'amarin,ta lumshe idanuwanta zuciyarta cike da tarin damuwa
"Habibty"
Taji muryarsa a cikin kunnuwanta
Tabud'e idanuwanta da sauri,agefenta ta gansa zaune
Ta danne tarin tsoron da ya taso mata tana kallonsa
Zeyi magana ta katse shi
"Dakata banason jin komai daga bakinka,mekayi kenan?kana ganin kayi dai-dai?kasan bak'in cikin da zuciya ta shiga alokacin da aka fasa aurena har sau biyu?
Naji alokacin kamar bak'in ciki ze kasheni,haka b'angaren samarina da mutum yafara zuwa sai ya dena ashe kaine kake hanasu, kenan ahaka kakeso ink'ara ci rayuwa ta batare da nayi aure ba ko?
Ya girgiza kai
"Ina tare dake,duk abunda d'an adam zeyi miki zan iya yimiki ninkin baninkin shi,amma tabbas maganar aure ki cireta a zuciyarki"
Ta gyad'a kai tana nuna masa hanyar fita
"Ka k'yaleni dan Allah,katashi katafi"
Yayi guntun murmushi
"Zan k'yaleki ayanzu har zuwa lokacin da zaki huce,amma ina tare dake har zuwa k'arshen rayuwata"
Yana gama fad'ar haka ya b'ace
Dafa kanta tayi dayike Sara mata tana ambaton sunan allah
Bayan sati biyu,bata k'ara ganinsa ba,bata kuma k'ara jin d'uriyarsa ba
Har suka kammala jaraba wa, suka fara Shirin tafiya gida
Tana cikin had'a kayanta taga wata farar takadda
Wani rubutu tagani me kyau kamar anyi shi da ruwan zinari
Tafara karantawa
"Amincin Allah yatabbata agareki,yake abar alfaharina,nasan nayi kuskure Amma kisani k'aunar ki ce tasani yin hakan kigafarceni dan Allah"
Tasan takaddar Aasim ce,ta ninketa tana sauke ajiyar zuciya sannan tacigaba da had'a kayan
Tare suka fito da Salma,dan yayan salman dake gombe yazo zed'auketa
Kowacce janye da akwatinta,
Suka gaisa da shi, sannan sukayi sallama,ita kuma Rauda tafito bakin titi tana jiran adai-deta sahu wacce zata Kai ta Tasha
Wata rantsattsiyar mota ce ta faka agabanta,tad'ago ta kalli wanda ke cikin motar
Aasim ne,yasha wasu maroon d'in jeans da T-shirt
Ya Salam, tafad'a afili dan yayi kyau nafitar hankali, azuciyarta tace dama ashe wannan kyan da walaki,dan yayi yawa
"Habibty Bismillah"
Girgiza kai tayi dasauri azuciyarta tana fad'in ba zan shiga ba
Sai dai kafin ta k'yafta ido,tuni taganta zaune acikin motar
Kallonsa tayi ad'an tsorace
Yayi dariya yana fad'in
"Wai ni naga ikon Allah,mata tana gudun mijinta"
Ta murd'a k'ofar zata fita,taji Gam
Ya kuma yin dariya
"Dama kin zauna dan ba bud'uwa zatayi ba"
Ajiyar zuciya tasauke tana jingina da kujerar motar,ko minti biyu cikakku ba ayi ba taga motar ta tsaya acikin wani gida me shegen kyau
Kallonsa tayi da mamaki sosai a fuskarta
"Inane nan kuma kakawoni?
"Gidanki Mana"
Yabata amsa a tak'aice
"Nida zantafi gida ya za'ayi kakawoni Nan?
Ya rausayar dakai yana cewa
"Nasani ai,awa uku kawai zamuyi"
Ta girgiza Kai
"Nariga nakira mama nafad'a mata nataho,idan taga nadad'e fa?nide kabarni intafi"
Yasauke guntun numfashi had'i da cewa
"Kinsan nisan dake tsakanin nan da katsina?
Ta girgiza kai,
Yacigaba da cewa
"Idan a mota zakije tafiyar awa arba'in da hud'uce,dan haka ki kwantar da hankalinki acikin minti d'aya zan iya kaiki har cikin gidanku"
Shuru tayi tana mamakinsa, yabud'e motar yafito,ya bud'e Mata
"Muje madam"
Kamar bazata fito ba,sai kuma tafito tana k'are ma gidan kallo,wanda yasha ado da furanni masu shegen kyau
Yayi gaba tana binsa abaya
Wani falo suka shiga,shima fad'an kyawunsa b'ata lokaci ne
Yayi mata nuni da kujera
"Zauna"
A d'erere ta zauna ta kallon kayan alatun da aka zuba ma falon
Maganar shi ce ta katseta
"Me zan kawo Miki?dannasan bawani karin kirki kikayi ba"
Girgiza mai kai tayi alamar babu komai
Shima ya girgiza nasa kan
"Nan fa d'aya,bazeyuwu kizauna da yunwa ba"
Yak'arasa fad'a yana janyo wani k'aramin tebur ya ajiye aganta tare da ambaton,tea,aarish
Sai gasu sun bayyana akan tebur d'in
"Oya Bismillah"
Mamakine ya k'ara kamata, kallon teburin kawai takeyi
Ya tashi daga kujerar da ya zauna,yadawo kusa da ita yana cewa
"Please mamakin ya isa haka,kici ko kuma yanzunnan kijisu a cikinki"
Kallonsa tayi amma ta kasa cewa komai
Yagyad'a kai gami da cewa
"Shikenan"
Abun al'ajabi gani tayi wayam,babu komai akan tiren sannan taji cikinta yayi dam
K'ara kallonsa tayi a hanzarce
Ya d'aga mata gira
"Na hutar dakene habibty"
Tasauke dogon numfashi tana fatan in mafarki takeyi ta farka hakanan
Durk'usa wa yayi agabanta yana ambaton sunanta
"Rauda!!!
Kallonsa kawai takeyi amma takasa amsawa
"Dan allah ki yafemin,nasan nayi kuskure kuma ban kyauta miki ba,amma ki gafarceni wallahi ina k'aunar ki,son da nikeyi miki ne yasa na aikata duk abunda nayi
Bakisan yadda naji ba,dakike jin wani iri akaina,zan iya yimiki komai dan insaki farinciki, nayi miki alk'awari amma inaso ki yafemin, bazan iya zama cikin kwanciyar hankali ba muddin kina fushi Dani"
Maganganun sa sun sa jikinta yayi sanyi,cikin sanyin jiki tace
"Na yafema,amma kaima kayi min alk'awarin bazaka cutar dani ba"
Yayi murmushin Jin dad'i yana kama hannunta
"Nayi miki alk'awari habibty,babu cutarwa a tsakanina dake,amma kicire tsoron da kike ji akaina wallahi da zan cutar dake da tuni nayi hakan kisani ke b'arin jikina ce, idan har zan iya cutar dake to zan iya cutar da kaina"
Hmmmmmmmm tasauke doguwar ajiyar zuciya
"Shikenan"
Mik'ewa yayi,yana dubanta
"Mik'e habibty"
Ta mik'e kamar yadda ya umarceta
Rungume ta yayi sosai ajikinsa yana maida numfashi
"Nasan dama zaki fahimceni,abu d'aya nikeso kiyimin,shine kiyarda ina k'aunarki"
Ji tayi gabad'aya tsoronsa da takeji ya yaye,ta Lumshe idanuwanta tana jin wani abu na ratsa zuciyarta
"Aasim!
Ta kira sunansa da murya k'asa-k'asa
Ya amsa
"Na'am habibty"
Sai kuma tayi shuru
Yad'ago ta ahankali yana kallon kyakkyawar fuskarta
Itama shid'in take kallo
"Habibty, kifad'a min duk abunda kikeso zanyi miki shi da izinin Allah"
Tayi murmushi tare da cewa
"Shikenan nagode"
Ya gyad'a kai yace
"Babu y'ar godiya,muje kizagaya gidan kigani komai natsara shine dan idan kika gani ya burgeki"
Tagyad'a kai tare da cewa
"To muje"
Kama hannunta yayi suka fara zagaye gidan,sannan suka dawo bedroom
Shima antsara shi komai na d'akin kalar pink,sannan ya bud'e mata toilet d'in dake ciki
Shima bayin abun burgewa
"Komai yayi Miki?
Ya tambaya yana kallonta
Jinjina kai tayi tare da cewa
"Yayi,amma nida ba zama zanyi aciki ba,meyasa......
Ya tsunsa biyu ya d'aura a lips d'inta
"Wayace Miki,aduk sanda kikaga dama zakizo,kuma nima aduk sanda naga dama zankawoki"
Tayi ajiyar zuciya kawai batare da ta k'ara cewa komai ba
Hannunsa yasa yana shafa dokin wuyanta ahankali yakai kan zip d'in doguwar rigar dake jikinta
Ta kallesa tace
"Yadai?
Guntun murmushi yayi tare da fad'in
"Dede, yakamata kiyi wanka ai ko?
Ta girgiza kai aa
Shima ya girgiza Kan
"Nikuma nace eh"
Kafin ta k'ara magana sai ganinta tayi cikin kwamin wanka shak'e da ruwa yasha wasu k'ana-nun fulawowi jajaye wanda suka lullub'e saman ruwan
Ta shafa jikinta dasauri taji wayam babu kaya
Kallonsa tayi har lokacin yana tsaye bakin bayin
Yad'aga mata rigar ta dake hannunsa
Yana cewa
"Gatanan kwantar da hankalinki"
Saurin kare jikinta tayi da hannayenta tana dun'k'ule wa guri d'aya
"Dan Allah kabani kayana"
Girgiza kai yayi gami da cewa
"Sai fa kinyi wanka,zanbaki"
"Please kabani"
Yakuma girgiza kai
"Allah bazan baki ba sai kinyi wankan,idan kuma bazakiyi ba to taso ki amsa"
Yafad'a yana mik'o mata kayan
Girgiza kai tayi
"Naji zanyi,amma ka ajiye min kayan kuma kafita ka kulle k'ofar"
Ya jinjina kai yana cewa
"Shikenan,kuma wankan tsakani da allah zakiyi ba kwara ruwa ba"
Ta jinjina kai
"Naji"
Ajiye kayan yayi akan abun wanke hannu,yafita ya kullo mata k'ofar
Numfashi tasauke, tana kallon cikin ruwan,sannan tayi wankan a gurguje
Tafito daga cikin kwamin zata d'auki,samtsin tiles ya kwasheta zata fad'i
Ji tayi an ruk'ota,a tsorace ta juya dan tasan yafita abayin
Sai dai me shid'in tagani yana mata murmushi
"Baka fita ba?
Ta tambayesa da mamaki
Ya jinjina kai
"Eh dawowa nayi"
"To ya akayi banga dawowar ka ba"
Dariya yayi tare da cewa
"Mutum ne inze shiga wuri sai ansani amma mu sai munga dama za'asani"
"Kenan agabanka nayi wankan?
Ta K'ara tambayar sa cikin yin sororo da baki
Dariya ya kuma yi yana fad'in
"Wad'ancan kayan a canzasu ne?
Baya tayi dasauri dan tama manta bata maida kayan jikinta ba
Dariya yakuma yi sosai,yana bud'e k'ofar bayin ya fice
Tazura kayan tare da fitowa tana cewa
"Allah munyi fad'a,ni muje ka kaini gida"
Ya janyo ta tafad'a jikinsa
Suka kalli juna sosai
"Habibty I'm sorry bazan sake ba,amma miye laifina danna kalli matata??
Sauke numfashi tayi
"Nidai muje kakaini"
Yasauke ajiyar zuciya
"Kingaji daganina ko?
Ta girgiza kai tace
"Bahaka bane"
"Aa kifad'a min gaskiya,yanzu danni ba mutum bane kin rage son dakikeyi min ko?
Ta kuma girgiza kai
"Inaso inje gida ne,amma bawai da wani abu araina"
Gyad'a kai kawai yayi amma yanayin fuskarsa yanuna Babu dad'i
"Amma yanzu innakai ki,za'a ga kin kai dawuri, kibari nan da minti arba'in sai inkai ki"
Tasauke numfashi tace
"Shikenan"
Sis nabila ina missing d'inki Allah ubangiji yabaki lafiya yasa kaffarene
Y'arfillo.
0 comments:
Post a Comment