Gefen had'add'en gadon ya zauna,yana kallon kafet d'in dake malale gaban gadon.
Ita ko tana tsaye,tana kallonsa,sai kuma taji babu dad'i ganin yadda yana yinsa ya sauya zuwa damuwa
K'arasawa tayi gabansa,tadurk'usa har lokacin idanuwanta na kansa
"Aasim"
Ta kira sunansa cikin sassanyar murya
Yad'ago suka had'a ido
"Nayi wani abunda ya b'ata maka Raine?
Ya girgiza kai yana k'ak'aro murmushi
"Aa,ko d'aya mekika gani?
Ta kauda idanuwanta da ga ga kansa jin tsigar jikinta nayi mata wani yarrr
"To meyasa yanayinka ya canza?
Ya juyo sosai yana fuskantarta
"Habibty bakiyi min komai ba,kawai dai inajin zuciyata babu dad'i ne,nasan bazaki tab'a min kwatan son danike yimiki ba
Koda na kasance a jinsin d'an adam,bare kuma jinsin rauhan,shiyasa nike jin babu dad'i danna tabbata da ace nakasance a cikin jinsin ki,da zanji dad'i domin ko bakomai zuciyarki zata natsu dani koda baki soni kamar yadda Nike son kiba
Amma yanzu zuciyarki ba a natse take dani ba,ina tsoron wata rana ragowar sona daya rage a zuciyarki shima yatafi kamar yadda natsuwar tatafi"
Yak'arasa maganar idanuwansa na rinewa
Tausayinsa taji ya mamaye zuciyarta,shin wani irin so yike mata ne har haka?
Ta tambayi zuciyarta
Murmushin damuwa yayi yana K'ara kallonta
"Wani irin so nikeyi miki kike tunani ko?
Ta kallesa sosai tace
"Ya akayi kasan abunda ke zuciyata?
Ya kuma yin murmushi yana kauda kallonsa akanta
"Ya akayi fa kikace?hmmmmm,
Yad'an numfasa sannan yacigaba dacewa
"Nima kaina bansan dalilin dayasa nike miki irin wannan son me tsanani ba,
Wani zubin har mamakin kaina nikeyi,amma abu d'aya nasani nakuma yarda dashi Allah ne ya jarabceni da k'aunarki,
Rauda dan Allah kitaimakeni koda kwatan son da nike yimiki ne kiyimin,wallahi ina sonki bansan tayaya zan fahimtar dake irin son da nikeyi miki ba"
Yak'arasa maganar yana kama hannunta
Zuciyar tace ta k'ara yin rauni, cikin kwantar mai da hankali tace
"Aasim,ba kace min in kwantar da hankalina ba?kai ma ka kwantar da naka dan Allah,tabbas ayanzu bana cikin natsuwata
Saboda bantab'a tunin al'amarin ka haka yike ba,amma nasan nan da wani d'an lokaci,komai zeyi dede insha'allahu"
Ya sauke gauron numfashi yana kad'a kai
"Shikenan,me kike da buk'ata yanzu?
"Buk'ata??? Kamarya"
Tatambaya cikin rashin fahimta
"Mekike buk'ata,miye kikeso, kifad'a min"
Shuru tayi tana kallonsa dan bata gane me yike nufi ba
Ya mik'e ya bud'e wata durowa yad'auko kwalin waya,sannan yadawo yazauna yana mik'amata
"Nasan kina buk'atar waya,tundaKinfasa taki,ga wannan kiduba idan tayi miki to,idan kuma batayi ba sai a canzo ta yanzu"
Amsar kwalin wayar tayi tana juyawa,wayace iPhone me tsadar gaske
Ta girgiza kai tana mik'amai
"Batayi miki ba?to wace kala kikeso?
Ta kuma girgiza kai a karo na biyu
"Bawai batamin bane,tayi danyi saidai idan aka ganni da ita a gida fa,wa zance yabani?
Yad'an yi shuru sannan yace
"Sai kice saurayin ki ne ya Baki"
"Hmmmmmmmm,wayar dubu d'ari biyun?wani saurayine ze bani kyautarta?ai Sai su tuhumeni,dan kasan yanzu awannan zamanin samari ba sa yin kyauta dan allah"
Ya jinjina kai yace
"Hakane,to fad'i wacce kike ganin babu matsala idan anganki da ita"
Tad'an yi shuru tana nazari daga bisani tace
"Infinix note"
Ya gyad'a kai
"Ook,bayan waya fa sai me kikeso?
"Babu komai"
Tace,ya jinjina kai
"Shikenan,ina ganin muje inkaiki yanzu,naga sak'on ammi tana son ganina"
Rauda ta mik'e tana cewa
"To"
Shima mik'ewar yayi yana kallonta
"To haka zaki tafi,babu abunda zaki bani?
Ta kallesa tace
"Babu abunda zanbaka?to mekakeso"
Matsowa yayi gab da ita,yana kallon cikin idonta
"Duk abunda kikaga yadace Dani"
Tayi k'asa da kanta dan bata iya jure kallon cikin idanunsa
"To ni bansan me ya dace dakai ba"
Hmmmmmm yasauke ajiyar zuciya yana d'ago hab'arta
"To shikenan,kibani wad'annan labb'an kawai,masu kama da jar tufa,na minti uku kawai"
"Labb'a?kayi me dasu??
Ta tambaya,be bata amsa ba illa sunkuyo da fuskarsa da yayi dede tata
Ta gane abunda yike Shirin yi, dasauri tak'ara sun kuyar da kanta tana k'ok'orin ja baya
Rik'ota yayi dasauri
"Please habibty,wannan k'aramin abunne bazaki iya min ba"
Ta marai-raice fuska tace
"Nidai ban iya ba,kabari please"
Yayi guntun murmushi
"To ai banace kin iya bane dama,kuma bance kiyi min ba,nida kaina zanyi"
"Nidai...nidai........
Bata k'arasa ba,taji bakinta cikin nasa
Wani irin yarrrrr taji jikinta nayi,ta lumshe idanuwanta a hankali tanajin gab'ob'inta nafara sarewa
"Habibty!"
Ya kirata,da sassanyar muryarsa data fara taushi
Tabud'e idanuwanta ahankali ta zubasu akansa,amma takasa amsawa
Dan ji tayi illahirin jikinta yayi mata wani iri
Ya kuma yin murmushi
"Ina sonki habibty"
Yafad'a yana rungume ta
K'ara lumshe idanuwanta tayi, tanajin zuciyarta na harbawa da sauri
"Ki kula min da kanki,anjima zamuyi magana"
Tabud'e idanunta zatayi magana,saidai wayam babu shi,takalli inda take
Zauren gidansu ne,gefenta kuma akwatinta ne
Tasauke ajiyar zuciya me nawi,tana jingina da jikin katangar zauren dan har lokacin bata koma dede ba
Maganar wani k'aramin yarone yasa tad'ago daga jinginar da tayi
"Laaa anty Rauda, oyoyo"
Ta yi murmushi tana d'aga shi sama
"Oyoyo my hanif,yaushe kukazo"
Hanif yace
"D'azu nida mummyna"
Ta dire shi k'asa tana jan akwatinta,d'ayan hannunta kuma takama hannunsa suka nufi cikin gida
"Dagaske?ina hanifa?
"Tana d'akin mama tana bacci"
"Eyyeh,tadaina rigima ko haryanzu tanayi?
Dede lokacin suka shiga cikin gidan,da umma tafara cin karo,tana zaune kan tabarma tana gyara wake
"Ina wuni umma?mun same ku lafiya?
Umma tad'ago tana yimata wani kallo,sannan ta amsa a dak'ile
"Lafiya"
Bata damu ba dan dama tasaba,tayi gaba
Har zata shiga d'akinsu ta hango inna a kicin, gudun kartayi laifi yasa takoma baya ta tsaya daga bakin k'ofar tana gaisheta
"Ita d'inma a dak'ilen ta amsa,juyawa Rauda tayi ta shiga d'akinsu tana sallama
Mama da anty ummi suka amsa cike da jindad'in ganinta
"Oyoyo auta,oyoyo autana"
Mama tafad'a fuskarta cike da annashuwa
Kusa da maman ta zauna tana kwantar da kanta a kan kafad'ar maman
"Mama wallahi nayi missing d'inki sosai"
Anty ummi ta galla mata harara,cikin wasa
"Dallah jibeki k'atuwa dake kin wani shige jikinta ko kunya bakyaji"
Rauda tayi dariya
"Kedai kice kawai kinji haushi ne,baki zo a auta ba,kuma mama tafi sona a kanki"
Anty ummi takuma harararta
"Ohon miki dai"
Mama dai dariya kawai takeyi
"Kinga ummi zubo mata abinci,kibar min auta ta huta daga isowarta har kinfara damunta?
Anty ummi tayi galala da baki
"Lallaima wannan yarinyar zanzuboma abinci,allah mama ke kike k'ara shawab'ata"
Rauda ta girgiza kai tana dariya
"K'yaleta mama bama najin yunwa,idan naji zan zuba"
Haka suka dinga barkwanci a tsakaninsu
Wacece Rauda?
Cikakken sunanta shine Rauda isma'il
Mahaifinta malan isma'il cikakken ba fulatani ne,yana kasuwancin saida hatsi,
Yana da mata uku,jummai(umma)
Itace uwargida,sai salamatu(inna)
Sannan Maryam (mama),allah ya azurtashi da yara dan umma yaranta takwas uku maza biyar Mata
Inna kuma tana da bakwai,ita kuma duka nata matane
Sai mama,wacce take da uku,dan tayi haihuwa takwas amma uku ne kawai suka tsaya
Kabir, Fatima (ummi) sai Rauda wacce takasance auta
Umma da inna kansu ahad'e yike dan komai tare sukeyi sun had'e ma mama kai babu abunda ke shiga tsakaninsu face kyara da hantara
Mussaman da suka ga tana da hak'uri dan duk abunda zasuyi mata bata tab'a d'aga ido ta kallesu bare tamaida musu martani
Haka suma y'ay'an sun tsani yaran d'akin mama,domin sun fisu kyau nesa ba kusa ba
Hakan yasa sauran y'ammatan suke tsananin jin haushin ummi da rauda dan duk inda suka shiga sai an kallesu
Haka aka dinga aurar dasu duk wad'anda aka ga girmansu yazo d'aya kuma sunsami masu neman auransu
Sai ahad'a su a aurar dasu,sau biyu ana fasa auran Rauda,kuma duka biyun sai ranar d'aurin ake fasawa
Hakan yasa yazama abun Gori,dansu gabad'aya babu wata y'a data rage a gabansu,kullum cikin yada habaici sukeyi
Rauda ganin yadda al'amarin aure yike kasancewa agareta yasa taciresa aranta, ta k'udiri niyyar yin karatu
Mahafinta be hanata ba yabata goyon baya d'ari bisa d'ari dan yana matuk'ar ji da ita acikin y'ay'ansa
Hakanko ba k'aramin k'ara basu haushi yayi ba dan su yaransu babu wanda yawuce secondary.
Cigaban labari
Sai yamma anty ummi tafara Shirin tafiya,suna zaune a falon rauda tashiga da akwatinta d'aki dan ta canza kayan jikinta da hanifa tab'ata da tumbud'i
Ta ajiye akwatin tana zaunawa a k'asa ta zage,bandir d'in kud'i tagani rafa na y'an dubu-dubu
Gabanta ne yafad'i,tad'auki kud'in tana juyawa da kuma mamakinsu dan tasan bata ajiye ko biyar acikin akwatin ba
Lokaci d'aya Zuciyarta ta tuno mata da Aasim,takuma fara jin maganar sa acikin zuciyarta
"Habibty,nasan kina buk'atar kud'i shiyasa na ajiye Miki,idan basu isheki ba kisanar Dani,sannan kisanya layinki awayar tana cikin k'aramar jakarki"
Jin motsin za'a shigo yasa tayi saurin rufe akwatin
Anty ummi ce da kwalin wayar a hannunta
"Rauda waya baki sabuwar waya me kyau haka?
Tad'an daburce,dan ganin kud'in ya rud'ata
"Am,am waya...
Anty ummi takalleta sosai tace
"Ke,miye na daburcewa daga tambayarki?
Rauda tayi k'ok'orin dai-daita natsuwarta tace
"Wani sabon saurayi nane"
Anty ummi ya k'walalo ido
"Dagaske?yaushe kuka had'u?
"Watanni takwas kenan"
Wani tsallen murna anty ummi tayi tare da k'arasawa kusa da Rauda ta tsugunna
"Kuma yana zuwa be dena zuwa ba?
(Dayike tun bayan fasa auranta,duk saurayin dayazo baya yin sati biyu yike tafiya,daganan bazata sake ganinsa bama bare wata maganar aure tashiga tsakaninsu)
Rauda ta d'aga kai alamar eh
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar anty ummi
"Kai alhamdulillah kenan,wannan shegen jinnul aashiquen beyi nasara akansa ba,allah yasa shine mijin"
Rauda tasauke ajiyar zuciya tana jin tausayin y'ar uwar tata ganin yadda lokaci d'aya tashiga farin ciki dagajin tasamu saurayin da ya dad'e,bata san cewa shine jinnul aashiquen ba
Maganar anty ummin ce ta katse mata tunanin data tafi
"Miye sunansa?ya kamanninsa suke?kyakkyawane?
Danna sanki da son kyakkyawan mutum
Lokaci d'aya ta yi mata tambayoyin ajere
Shuru Rauda tayi zuciyarta nayi mata wani iri
"Miye sunansa kifad'a min Mana"
Anty ummi ta kuma fad'a cikin zak'uwa
Rauda ta kuma sauke numfashi tana bata amsa cikin sanyin jiki
"Aasim"
Anty ummi tad'ago ido tana kallonta
"Mene?
"Aasim,sunan sa Aasim"
"Aasim?
Anty ummi ta mai-maita sunan fuskarta da d'an alamar mamaki
"Wani kalan sunane wannan?
Rauda ta gyad'a kai alamar bata sani ba
Anty ummi ta ce
"Koma dai miye sunansa nidai nayi farin ciki,yaushe zezo?
Kuma acan katsinan yike?
Cikin k'osawa da tambayoyin Rauda tace
"Anty ummi please yanzu kaina ciwo yikeyi,zanzo har gida inbaki labari"
Anty ummi ta mik'e tana tab'e baki
"Ke kenan ai dama,yau ciwon kaza gobe ciwon kaza"
Banza Rauda tayi da ita,ta zura hijabi tana dubanta
"Ni in yanzu zaki tafi muje inrakaki"
Goya hanifa anty ummi tayi tana ma mama sallama
Suka fito,a k'ofar gida suka ci karo da baba yadawoDaga kasuwa,suka rusuna suna gaisheshi
Cikin farin ciki ya amsa yana duban Rauda
"Y'ar albarka,isowar yaushe?
"D'azu baba"
Tabashi amsa cikin ladabi
"Masha Allah,ya karatun? anayi dai sosai ko?
Ta d'aga kai
"Eh baba"
Baba yace
"To Masha'allahu,tashi kirakata,kar duhu yayi,hanif kagaida gida ko"
Suka mik'e anty ummi na mai sallama
Bayan ta dawo daga rakata,tasanya layi a wayar ta kunna
Sak'onninsa ne suka fara shigowa,masu d'auke da kalaman soyayya
Ta na gama karantawa ta ajiye wayar taje takwanta, zuciyarta cike da sak'e-sak'e
Washegari tana gyara falo,mama na zaune tana karatu,ta kwashi kayan da ta wanke tashiga d'aki dan sawa a drower
Tana shiga taji anjanyo ta,kallon sa tayi da sauri
Yana tsaye hannunsa sak'ale da k'ugunta
Zaro ido tayi tana kallon k'ofar d'akin
"Miye haka,idan mama tashigo fa?
Tafad'a cikin murya k'asa-k'asa
Murmushi yayi yana girgiza kai
"Babu wanda ze shigo ayanzu,kuma koma tashigo bazata ganni ba"
"To amma meyasa baka fad'amin zakazo ba?
Ta fad'a
Yasauke guntun numfashi tare da cewa
"Saboda a buk'ace nike da inganki"
Ta sauke numfashi tace
"To nidai kadena zuwa please,banaso a fahimci wani Abu,kabari har inkoma makaranta sai mucigaba da had'uwa"
Zaro ido yayi tare da cewa
"Mene?kema kinsan bazan iya ba,bazan iya ko kwana d'aya batare dake ba"
"Hmmmmm bazaka gane ba,idan kai ba'a ganinka,aini wani zubin za'aga ina magana nikad'ai idan inayi dakai,basai ayi tunanin k'wa-k'walwata tafara samun matsala ba?
Ya jinjina kai
"Hakane,amma kema kinsan baze yuwu indena zuwa gurinki ba,sai dai inkin yadda murink'a had'uwa a gida"
"Gida?
Ta tambaya cikin rashin fahimta
"Eh,inda mukaje jiya"
"Shima kasan baze yuwu ba"
Ya kuma matso da ita jikinsa yana cewa
"Ze yuwu Mana,banace da rana ba ai,da daddare babu wanda ze fahimta"
Ajiyar zuciya tasauke
"Naji shikenan,sai anjima"
Tafad'a a gaggauce dan taji motsin mama alamar tana tahowa
Ya gyad'a kai tare da b'acewa
"Ke kuma ke da wa kike magana,nike jiyo magana k'asa-k'asa"
Mama tafad'a yayinda tashiga d'akin
Wuri-wuri da idanu tayi tana neman abunda zatace
"Am,en,waya nayi da y'ar makarantar mu"
Tafad'a tana mata nuni da wayar
Mama bata k'ara cewa komai ba ta koma falo
Dafe k'irjinta tayi dayike dukan uku-uku tana sauke ajiyar zuciya
Da daddare tagama Shirin kwanciya dan mama tuni tayi bacci
Fulo ta janyo ta d'aura kanta tana rufe ido,jitayi iska na kad'a ta ahankali
Ta bud'e ido sai dai a me makon taganta a gadon mama,awannan k'aya taccen gadon taganta
Tashi tayi dasauri tazauna,dede lokacin Aasim yafito daga bayin yana goge ruwan jikinsa daga shi sai k'aramin towel
K'irjinta ne ya buga dam, Dan karo nafarko kenan da tab'a ganin na miji ahaka,gashi babu inda babu gashi ajikinsa yana kwance kan farar fatar dake jikinsa
Murmushi yayi mata yana k'arasowa ya zauna bakin gadon
"Habibty"
"Idan mama tafarka bata ganni bafa"
Abunda tafara cewa kenan
Ya kuma yin murmushi
"Mama bazata farka ba sai asuba,ki kwantar da hankalinki"
"Nidai gaskiya tsoro Nike ji kamaidani dan Allah,sai muyi maganar da zamuyi acan tunda tayi bacci"
"Habibty nace miki bazata ta tashi ba.......
"Nidai kamaidani"
Ta katseshi, kallonta yayi da idanuwansa da cikinsu yafara canzawa
"Banason musu,bazan mai d'aki ba sai asuba"
Shuru tayi tana yin k'asa da kanta
Ya mik'e ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta
Jitayi tafara shiga wani yanayi,kamar na bacci kamar na suma,daga nan bata k'ara sanin inda kanta yike ba sai wajen k'arfe uku nadare tafarka
Akwance kusa da ita taganshi,ya zuba mata manyan idanuwansa
Tayi saurin rufe idanuwanta jin jikinta na amsawa
"Rauda!"
Ya kira sunanta,ta bud'e idon ahankali amma bata bari tak'ara kallon cikin idonsa ba
"Rauda ina sonki,rauda ina k'aunar ki,zan iya yin komai akanki"
Tasauke ajiyar zuciya tana mamakin yadda baya gajiya wajen fad'an wad'annan kalmomin
Sai lokacin ta lura da kayan ta dake gefe, tad'an zaro ido gabanta na fad'uwa tace
"Aasim,me kayimin?meyasa kicire min Kaya?
"Me na Miki?abunda nasaba yi dake"
Yabata amsa a tak'aice
Runtse idanuwanta tayi,cikin tsananin damuwa
"Amma meyasa?kenan da inason Abu da banaso zaka rink'a yimin?
Tafad'a cikin dashewar murya
Yasauke gauron numfashi yace
"Rauda baki yadda dani bane?
Tabud'e idanuwanta tana k'ok'orin d'aura su akan fuskarsa
"Amma badai-dai bane hakan,nidakai ba jinsi d'aya bane,kuma allah be halatta aure a tsakaninmu ba.......
Katseta yayi ta hanyar rufe mata baki
"Shhhhhh, bantab'a kusantar ki ba,saida aka d'aura aurena dake"
"Amma wayace maka auran ya d'auru?
Juya mata baya yi,dan baya buk'atar jin wad'annan kalaman nata,sosa masa zuciya suke yi
Ita d'inma juya mai bayan tayi,tana mamakin irin wannan al'amari
Saida suka kwashe minti goma ahaka,sannan ya juyo ya na kiran sunanta
Saukowa yayi yadawo gabanta ya durk'usa, idanuwansa sun rine sosai
"Rauda kitaimaki rayuwata kidaina fad'a min irin wad'annan maganganun,nidai ina sonki koma me zakice bazan iya rabuwa dake ba"
Kallonsa kawai takeyi, idanuwanta sun cicciko da hawaye
Wata k'aramar fulawa ce tasauka a hannunsa
Yayi saurin damk'eta yana rufe idanuwansa
"Ya Salam"
Yafad'a cikin tashin hankali
Ita dai kallon sa kawai takeyi,
Yabud'e idanuwan a wahalce yana zuba su akanta
"Sak'one daga sarki,yace yana son ganinmu ni dake gobe"
Mik'ewa tayi da sauri tace
"Mene?Ni,wallahi ba inda zani,nan ma a tsorace nake bare zuwa wata duniya, narok'eka ka taimakeni bakomai k'wa-k'walwata zata iya d'auka ba,kada inga wani abunda ze haukatar Dani"
Tafad'a cikin gigita
Zaunawa yayi yana kama hannunta
"Zuwa ya zama dole Rauda,dan ko ki yarda,ko kar ki yarda ya zamar miki dole kije,babu abunda ze sameki ina tare dake"
Girgiza kai tayi cikin tashin hankali da tsananin tsorata
"Nidai aa, duniyar aljanu fa? kataimakeni indai kana sona kada ka kaini dan Allah"
Ajiyar zuciya yasauke yana k'ara kama wata fulawar da ta sauko daga saman d'akin yakuma runtsewa a hannunsa
Kallonsa takeyi tana jiran jin abunda ze kuma cewa
"Sak'on ammi ne,tace inje yanzu tana son ganina"
Kama hannunsa tayi tana d'an jijjigawa
"Nidai bazan je ba,ka fad'a mishi bazan je ba"
Jitayi ana jijjigata
Dasauri ta bud'e ido,mama tagani zaune ta zuba mata ido
"Ina ne bazaki ba?
Mama ta jeho mata tambayar
Tashi tayi dasauri tafad'a jikinta tana fashewa da kuka
Mama tasauke numfashi tana tofa mata addu'o i
Maman isqah ina godiya,harda k'arfafa gwiwarki yike sawa nike daurewa Allah,amma typing akwai wuya😒
Y'arfillo
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 1⃣5⃣
Wannan page d'in nakune y'an golden forum,na sadaukar dashi gareku kuyi yadda kukeso da shi🧡🧡
8:00🕒 Am
FRI,MAY 3
Bissmillahir rahmanin rahim👏🏻👏🏻👏🏻
Mama bata k'ara tambayar ta ba,dan tafi kowa sanin matsalar y'arta
Addu'a taci gaba da tofa Mata,bata bari ba harsai da tadawo cikin natsuwata
Lokacin ana kiraye-kirayen sallar asuba
"Kina yin wasa da azkar ko Rauda?
Mama tafad'a tana kallonta
Rauda ta girgiza kai alamar aa
Mama ta cigaba da cewa
"Aa kina wasa dashi banace miki duk sanda zakiyi bacci kiyi alwala ba, sannan kitofa ma jikinki addu'o i?yaushe rabon da kiyi hakan?
Rauda ta yi shuru tana tunani,dan ita rabonta da tayi alwala ko azkar d'in bacci har ta manta
Mama ta girgiza kai cikin damuwa
"Karatun al'qur ani ma kin rabu da yi ko?
Shuru Rauda tayi nanma mik'ewa mama tayi tafice daga d'akin dan d'auro alwala
Rauda ta jingina da jikin gado kanta nawani irin sarawa, gabad'aya yanzu tunanin ta nema yikeyi ya tsaya jitayi kamar ba ita ba
B'angaren Aasim,atsaye ya tadda ammi jikin wata k'atuwar bishiyar da ke cikin sahara
Wacce take gefen shiga masarautar
Kallo d'aya yamata yagano tashin hankali da tsananin damuwa a tare da ita
Kama hannunsa tayi suka zauna suna kallon juna
"Ammi,wai meke faruwa ne naga sak'on me martaba"
Ammi ta sauke numfashi tana bashi amsa
"Akan tarayyarka da Rauda ne,kasan tun bayan haihuwar shahida be kuma cewa komai ba,to jiya abu saima yaje fada
Yike cewa abunda kakeyi sam be dace ba,saboda da wanine yike aikata hakan da tuni an d'auki mataki akansa
Amma saboda kai d'an sarki ne,sai azuba maka ido ak'i cemaka uffan
Shine sarki yaturama sak'on Kira,kafin na turama nawa sak'on sai da naje na sami me martaban akan wani mataki yike shirin d'auka
Shine yace bega laifin abu saima ba,dan tabbas ba adalci bane,kana d'an da ya haifa kana aikata laifuka wanda kaine jigon masarautar,kuma ya zamar maka dole ka rabu da ita,domin auran jinsin d'an adam baya daga cikin tsarin masarauta"
Numfashi Aasim ya sauke,ya na kad'a kai
"Inbanda munafurci meya ruwan abu saima da rayuwata,nafahimcesa tunda nak'i auran y'arsa na nuna banason ta yashiga bak'in ciki Dani"
Ammi tadafasa cikin damuwa tare da cewa
"Nidai duk wannan bashi bane,abunda nikeso da Kai dan Allah ka amince ka rabu da ita, banaso ka bijirewa umarnin da mahaifinka ze baka,nayi maka alk'awarin tara maka kyawawan mata a jinsinka kazab'i wacce tafi maka........
Katseta yayi ta hanyar girgiza kai
"Bazan iya ba ammi,wallahi bazan iya ba,bazan iya rabuwa da ita ba"
Ammi tayi shuru tana kallonsa,durk'usawa yayi agabanta yana kama hannayenta
"Ammi kitaimaki rayuwata dan Allah,ammi bazan iya rayuwa inba tare da ita ba,idan da abunda zaki iya yi kiyi dan Allah"
Yafad'a cikin tsananin damuwa
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonsa
"Aasim babu abunda zan iyayi,kasani kai kad'ai gareni bayan kai banida wani d'a aduniya, narok'eka kada ka fusata mahaifinka dan nasan ze iya d'aukar ko wani hukunci akanka,bar ganin yana sonka amma yafi son kimarsa da darajarsa fiye dakai kuma zeyi komai ne abisa adalci"
Aasim ze kuma magana ta had'e mai hannunta guri d'aya
"Kaga dai nice na haifeka amma narok'eka daka bi umarnin da ze baka,banaso wani abu ya sameka kai kad'ai nike dashi aduniya"
Ta k'arasa fad'a hawayen daya cika idanuwanta na gangarowa
Runtse idanuwansa yayi yana cize leb'ansa
Ammi ta mik'e tana kallonsa tare da cewa
"Zan wuce,gobe katabbata dakazo a lokacin da ya baka"
Jingina yayi da jikin bishiyar wasu zafafan hawaye na gangaro Masa
Ya bud'e idanuwansa yana kallon sararin samaniya
"Bazan iya rabuwa da ita ba,ya allah kataimakeni"
Yafad'a cikin damuwa da rashin sanin abunyi
Ita ko Rauda kasa komawa ta kwanta tayi,tunda tayi sallar asuba tana kan darduman
Gabad'aya jinta takeyi cikin damuwa,da kuma tsananin fargaba
Har mama ta kammala abun kari ta dawo d'akin bata tashi daga kan darduman ba
"Wai ke lafiyan ki k'alau kuwa? kintashi bazaki je kigaida baban ku ba"
Mik'ewa tayi jikinta babu k'wari,ta ninke dar duman tana yin hanyar waje
Mama ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta
"Rauda"
Rauda ta juyo tana amsawa
"Na'am"
"Meke damunki?
Mama ta tambaya tana tsare ta ido
Girgiza mata kai Rauda tayi
"Babu komai,banjin dad'ine kawai kai na ke ciwo"
Mama ta gyad'a kai had'i da cewa
"Shikenan jeki gaishe sa kidawo kisha magani"
Jinjina kai tayi tare da ficewa
Da sallama ta shiga d'akin Abba
Ya amsa,ta tsugunna tana gaishesa
Amsawa yayi yana kallon ta a tsanake
"Raudatu baki da lafiya ne?
Ta k'ak'aro murmushi tana cewa
"Aa baba,kaina ne ked'an min ciwo,shima kuma ba sosai ba"
Ya kad'a kai yace
"To tashi kije ki karya kisha magani,idan bedena ba anjima idan nadawo kasuwa sai inkaiki chemist"
"To"
Tace tare da mik'ewa tafito daga d'akin
Kan gadon mama tadawo takwanta
Tana jin maganar sa a cikin zuciyarta
"Habibty,anjima da daddare zamu tafi"
Shuru tayi tana lumshe idanuwanta,mama tadawo d'akin hannunta rik'e da kofin tea da paracetamol
Ta amsa tasha,tasha maganin sannan ta koma ta kwanta
Ranar mama ce da girkiDan haka bata zauna ba,tana ta ayyuka, Rauda tayi k'ok'orin fitowa ta tayata amma tace aa taje takwanta tunda bata jin dad'i
Wunin ranar haka Rauda tayi shi sukuku
Da yamma, tana bayi zatayi wanka ta tasa ruwan agaba tana kallo
Wani haske tagani ya b'ullo cikin bayin,sai ga Aasim ya bayyanaKallo d'aya suka ma juna suka gano damuwar da kowanensu yike ciki
Kauda kanta tayi daga kansa, gabanta na fad'uwa
Shiko wani kalar abune ya k'ara sukar sa,Wanda yasan tsan-tsar k'aunar tane
Tayaya ze iya rabuwa da wannan kyakkyawar halittan?
Yasan akwai kyawawan mata a duniya amma bega tamkar ta ba, tabbas baze iya rabuwa da ita ba
Gab da ita ya tsaya,dan tana jingine ne da bangon bayin
"Rauda"
Ya kira sunanta,ta juyo da kanta tana kallonsa ba tare da ta amsa ba
Shima shuru yayi suka kalli juna na y'an wasu sakwanni sannan yace
"Meyasa kika tada hankalinki?ba wani abun tsoro zaki gani ba idan munje,zaki ga kowane a suffar mutane kamar yadda kike ganina,kuma sannan ina tare dake,babu wani abun da zesa meki"
Juyawa tayi da niyyar fita daga bayin
Yasa hannu ya dafe bangon ya tare mata hanyar
"Rauda ki yarda dani, wallahi bazan cutar da ke ba"
Kallonsa tayi da idanuwanta da suka fara cikowa da hawaye
"Aasim,dan allah ka rabu Dani, kabarni inji da abunda yike damuna please"
Tak'ara sa fad'a tana tana juyawa da sauri ta d'ayan gefen
Jitayi ya rungumo ta tabaya,tayi saurin runtse idonta danji tayi illahirin jikinta ya amsa
Nannauyan numfashi yasauke yana sak'alo kansa ta gefen wuyanta
"Rauda,ina sonki,nasan kema kina sona dan allah kada kik'ara ambaton in rabu da ke"
Juyowa tayi dasauri,still Tana rungume a jikinsa,suna fuskantar juna
"To in ina sonka fa?yazanyi, zanciga ba da rayuwa dakai ne ahaka?
Meyasa kakasance a wani jinsi meyasa?
Tak'arasa fad'a tana fashewa da kuka
"Aasim ina sonka,dan girman allah idan mafarki nikeyi cewa kai ba mutum bane ka tasheni,nayi alk'awarin bazan sake yin baccin ba bare inkuma yin makamancin irinsa"
Tausayinta had'i da k'aunarta suka sake mamaye mai zuciya
K'ara rungumeta yayi yana runtse idanuwansa,cikin tsananin damuwa
Sai da suka kwashi minti biyar ahaka,sannan ya d'agota yana kallon kyakkyawar fuskarta data jik'e sharkaf da hawaye
"Rauda,nayi alk'awarin zan rayu dake ako wani irin yanayi, zanyi miki komai kamar yadda jinsin ki zeyi Miki,dan allah ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallonsa kawai batare da ta ka'ra cewa wani abu ba
Hannunsa yasa yana share mata hawayen
"Kinsan abunda natsana shine ganin hawayenki,shine abunda ke tada min da hankali,kibar yimin asarar su please"
Ya d'an numfasa sannan yacigaba da cewa
"Kinsan ya fuskarki take komawa idan kina kuka?
Ta tsaresa da kyawawan idanuwanta tana kallon yadda yike ya mutsa fuskarsa alamar haka tata fuskar take komawa idan tana kuka
Murmushi tayi,duk da batayi niyyar yi ba
Ya dafa kafad'unta yace
"Yauwa kokefa, Baki ga kinfi kyau ba"
Ya k'arasa fad'a yana sauke ajiyar zuciya
"Bari inbarki kiyi wankan,anjima dai kar ki manta"
Gyad'a masa kai kawai tayi,yayi murmushi tare da manna mata kiss a goshi
Ta sauke doguwar ajiyar zuciya bayan b'ace warsa sannan tayi wankan a sanyaye
Da daddare,misalin k'arfe goma,mama tagama Shirin ta tana mik'ewa
"Kisamin sakata a k'ofa,kada kibar min k'ofa ta kwana a bud'e sannan kiyi addu'a kafin ki kwanta"
"To"
Rauda tace,mama ta fice daga d'akin tana janyo mata k'ofa
Rauda tamik'e ta sa sakata a k'ofar falon sannan ta dawo ta zauna tana d'aukar wayarta dake k'ara
Numban Salma tagani,ta d'auka tana sallama
Daga can b'angaren salma tace
"Mara kirki,tunda baki kira kinji ya na sauka ba nina kiraki"
Rauda ta yi murmushi
"K'awa kina Raina,ya kike"
"Habibty"
Taji an fad'a abayan ta,ta waiga Aasim tagani
Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa salma
"Bari zankira ki ina zuwa"
Ta katse wayar tana kallon sa
"Muna iya tafiya?
Yatambaya,ta jinjina masa Kai alamar eh
A cikin y'an sakwanni taganta acikin sahara,babu gida gaba babu gida baya
Kallonsa tayi k'irjinta na dukan uku-uku
Amma takasa yin magana
"Abun hawa na hanyar zuwa yad'auke mu"
Begama rufe baki ba saiga wasu dokuna guda biyu,d'aure da wata kujera ta zaman mutum biyu da rumfa a samanta
Saurin rik'esa tayi,dan girman dokunan ya wuce misali,wani irin tsoro yafara d'arsuwa acikin zuciyarta
Aasim ya lura da hakan,ya yi mata murmushi cikin k'arfafa mata gwiwa
"Habibty kada kiji tsoro kinji?muje"
Yak'arasa fad'a yana kama hannunta,babu yadda ta iya suka shiga suka zauna,dokunan suka juya inda suka fito a guje
Rauda ko mamakine da aljabi ya dabai-bayeta
Gabad'aya gurin Sahara ne,amma kuma ga wasu bishiyoyi masu shegen kyau dasukayi ma wurin ado
Daga nesa ta hango wani katafaren gari wanda katanga ta za gayesa
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrr
Ta yi saurin runtse ido tana ambaton sunan allah
Kallonta Aasim yayi ganin yanayin data fara shiga
Yasa ya kama hannunta ya damk'e cikin nasa
Ahankali taji tsigar jikin ta dena tashi,suka kalli juna yayi mata murmushin k'arfin Hali dan gabad'aya hankalinsa a tashe yike
A k'ofar garin dokunan suka tsaya,wacce take a kulle
K'ofar tana da fad'in gaske,tsayawar dokunan keda wuya k'ofar tabud'e
Wasu zabga-zabgan mutane Rauda tagani masu matuk'ar girma sanye da bak'ak'en kaya da wasu manyan takobi ahannayensu
Idanuwannasu jawur kamar gauta,tayi saurin rufe idanuwanta k'irjinta nawani mugun bugawa
Maganar su ce tasa tabud'e idon dasauri jin muryoyinsu a kausheshe
Gabad'ayan su zubewa sukayi a k'asa suna fad'in
"Barka da isowa,yarima,allah shi baka nasara"
Ya d'aga masu hannu yanayi musu magana da wani yare
Nan da nan suka basu hanya,dokunan suka cigaba da tafiya
Rauda sakin baki tayi tana kallon cikin masarautar,da tsayawa fasalta ta b'ata lokacine
Ga mutane kala-kala iri-iri kuma duk inda suka gifta sai sun zube suna kwasar gaisuwa
Kallonsa tayi taga kayan jikinsa sun sauya zuwa kayan sarauta,idanuwansa ma k'wayar ciki sun tashi daga bak'in dasuke sun koma wani kala
Shima d'in tsoro yabata,ta k'an-k'anme jikinta tana ambaton sunan allah
Cikin sauri yace
"Rauda,yazamarmin dole inkoma yadda nikene,ki kwantar da hankalinki dan allah,"
Bata sauraresa ba tacigaba da karantasu addu'o i, jikinta na kakkarwa
Bata yadda tak'ara bud'e idanuwanta ba harsaida taji dokunan sun tsaya
Tabud'e idanuwanta a tsorace tana kallon inda suke
Wani k'ayataccen wurine me shegen kyau daga can gabansa kuma wata k'atuwar fada ce
Inda take hango wasu sanye da fararen kaya zazzaune
Ta kuma runtse idanuwanta tana fad'in
"Aasim,kataimakeni kamayar dani"
Hannunta yakama yana karanto wasu abubuwa da batasan ko menene ba
Take taji tsoron da takeji yatafi,sai abunda ba a za rasa ba
Takuma bud'e idanuwan ahankali tana watsasu akansa
"Habibty babu abunda zesameki,mutafi fada,kuma idan munje duk abunda kiga nayi kiyi irinsa kinji?
Gyad'a masa kai tayi tana bin bayansa
Har k'ofar fada, gabad'aya wad'anda ke zazzaune rusuna masa sukayi suna kwasar gaisuwa
Banda wani me kama da larabawa da ya hakimce a kan wata kujerar zinari
Aasim ya rusuna agabansa,itama Raudan ta rusuna kamar yadda taga yayi
Aasim yace
"Allah ya taimaki me martaba"
Sarki Ramzad ya kad'a kai batare da ya amsa ba
Mik'ewa Aasim yayi suka d'anyo baya sannan ya zauna,itama ta zauna kamar yadda yayi
"Yarinya!
Sarki Ramzad yafad'a yana kallon Rauda
Ta kallesa batare da ta amsa ba, gabanta na fad'uwa
"Shin kinsan waye Aasim?
Ya tambaya still idanuwansa na kanta
Nan ma shuru tayi,dan bata da bakin magana
Sarki Ramzad ya cigaba da cewa
"Aasim d'ane,kuma magaji a wannan masarauta,sannan kuma rauhani"
Ya d'an numfasa kad'an,sannan ya cigaba da cewa
"Amma duk da sanin hakan,kika amince zaki cigaba da rayuwa da shi?
Nayi miki uzuri,awancan lokacin domin ko kina cikin rashin sani,amma ayanzu zan yanke hukunci a bisa saninki"
Ya maida kallonsa kan Aasim yana ambaton sunan sa,
Aasim yad'ago da kansa k'irjinsa na bugawa
"Ina buk'atar ka furta kalmar saki,ayanzunnan sannan kayi alk'awarin rabuwa da ita,taje ta auri jinsinta"
Cikin kad'uwa da jin kalaman mahaifinsa ya zube,cikin tashin hankali yace
"Kayi min afuwa,abi bazan iya furta kalmar saki a gareta ba"
Sarki Ramzad ya had'e fuska ya kuma mai-maita abunda yace
Nan d'inma kuma zubewar yayi
"Abi kataimaki rayuwata, wallahi ita kad'ai nikeso bazan iya rayuwa idan babu ita ba"
Sarki Ramzad ya kad'a kai yace
"Amma kasan a dokar masarautar mu babu auran jinsin bil'adama ko?
Aasim ya jinjina kai
"Nasani abi,amma kayimin rai kabarni naciga ba da rayuwa tare da ita"
Sarki Ramzad ya girgiza kai
"Abune da baze tab'a yuwuwa ba kana d'an dana haifa inbarka ka sab'awa shari'ar masarauta,dan haka ka furta saki agareta"
Ammi dake gefe ta taso cikin tashin hankali ta wanka masa mari
"Baka da hankali ne Aasim?da mahaifinka kake jayayya?
Sarki Ramzad ya d'aga mata hannu
"Ya Isa,ki k'yaleshi zanga iya kafiyarsa dakuma taurin kansa"
Komawa tayi inda take,tanayi ma Aasim wani kallo me cike da bada umarnin ya aikata abunda akace Masa
"Na baka minti biyar,ka aiwatar da abunda nace"
Sarki Ramzad yafad'a cike da k'asaita
Aasim ji yayi kamar kansa ze juye saboda tsananin tashin hankali
Gabad'aya fadar tayi tsit,kowa maganar Aasim yike jira
Ahaka har minti biyar d'in tayi
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare da cewa
"Bazaka bi umarnina ba kenan?
Aasim jan gwiwowinsa yayi zuwa gabansa ya fashe da kuka
"Abi, kagafarceni bazan iya rabuwa da ita ba"
Runtse ido sarki Ramzad yayi,cike da tsananin takaici
Yabud'e su ya watsa su akansa
"Aasim akan bil'adama kake jayayya Dani?
Aasim ya kuma fashewa da kuka
"Ni me biyayya ne agareka abi,amma ina rok'onka da ka yimin agaji"
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon me fad'an hukunci
"Miye hukuncin duk wanda ya karya dokar masarauta?kuma akace ya bari ya yak'i bari"
Me fad'an hukunci yayi shuru,yana tunanin abunda zece ganin d'an sarki ne dakansa
Sarki Ramzad ya katse mai tunani ta hanyar cewa
"Kada kayi la'akari da wai d'anane,kafad'i hukuncin da ya rataya akanshi"
Me fad'an hukunci yasauke numfashi tare da cewa
"Za'a koresa daga masarautar gabad'aya"
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon Aasim yace
"Kaji hukuncin da ya rataya akan duk wanda ya aikata laifi irinnaka,dan haka sai ka zab'a cikin biyu,
Ko kasaketa karabu da ita,ko kuma ka bar masarautar gabad'aya"
"Abi ni d'anka ne,kaji tausayina........
Sarki Ramzad ya katsesa
"Tunda ni amatsayina na mahaifinka ban isa inbaka umarni kabi ba,yazamar min dole ind'auki hukunci akanka,dan haka fad'i ina jiranka,wane kazab'a"
Yak'arasa fad'a cikin d'aga murya
"abi,kayi hak'uri ka gafarceni........
"Nace kazab'a d'aya ko?
Sarki Ramzad ya katsesa a fusace
Kallon Rauda yayi wacce gabad'aya itama hankalinta ya gama ta shi
Ya maida kallonsa ga me martaba da yike cewa
"Zan irga uku,idan har na irga uku baka saketa ka rabu da ita ba,to tabbas zaka bar min masarauta"
"D'aya.....
Biyu........
Cikin tashin hankali Aasim yace
"Abi dan girman allah.........
Sarki Ramzad ya d'an dakata yana jiran jin abunda zece
Amma kuma sai yayi shuru,yana cize leb'ansa da k'arfi tare da runtse idanuwansa
"Uku"
Me martaba yafad'a,ammi ta taso da sauri tana jijjiga Aasim
"Aasim,kadawo hayyacinka,takan mace,macen ma bil'adama zaka zab'i rabuwa da ahalin ka,maza ka rok'i gafarar mahaifinka ka aiwatar da abunda yace"
Tafad'a a zafafe cikin kid'ima
Bud'e idanuwan sa Aasim yayi yana zuba su akanta
"Ammi kigafarceni,bazan iya rabuwa da ita ba..."
Yafad'a cikin zafin zuciya
Ammi baya tafara ja tana girgiza kai
"Aa,aa, Aasim kada kayi min haka"
Abu saima ne ya mik'e shima cikin tashin hankali dan betab'a zaton Aasim ze zab'i barin masarautar akan Rauda ba,ga saima can tana kukan inda babu shi bazata iya rayuwa ba,kuma shi yayi hakanne dan sama ma y'arshi farin ciki dan yasan idan Aasim yarabu da Rauda dole ze auri saima
"Yarima kasan hukuncin duk wanda ya zab'i barin masarauta kuwa? Dole fa sai ka bi ta tauran
(Tauran wani wurine zagayayye,da yike da k'unci da zafi, Wanda duk bayan minti biyu yike fitar da wani k'ara me kama da sautin tsawa,wanda duk wanda yike ciki sai hucin k'arannan ya tsattsaga jikinsa)
Abu saima ya cigaba da cewa
"Wanda sanin kankane sai rauhan yatsaya acikin tauran har sai ya tsallake k'arar tauran guda arba'in da tara,shin kamanta da azabar dake cikin tauran ne?
Aasim yayi masa wani kallo me cike da tsana dan inba da din munafuncinsa ba da yanzu wannan abubuwan basu faru ba
"Nasani,kuma na amince ko da hakan zeyi sanadiyyar rasa rayuwata ne"
Gabad'aya fadar zaro ido sukayi cike da al'ajabi
Rauda da jikinta ya gama mutuwa hawaye suka gama wanke mata fuska saboda tsananin tausayin Aasim,shin wani irin so yike mata da ze zab'i rabuwa da ahalinsa saboda ita?
Cikin kuka ta matsa kusa dashi tana fad'in
"Aa Aasim,kada ka bijirewa umarnin iyayenka akaina"
Girgiza kai yayi yana kallonta da idanuwansa da suka rine
"Rauda ina k'aunar ki,zan iya hak'ura da komai inhar zan rayu dake"
Sarki Ramzad da jikinsa yagama yin sanyi duk da b'acin ran dayike ciki kukan d'annasa na tab'a masa zuciya
"Na baka daganan zuwa gobe,kaje kanatsu kayanke wa kanka abunda yafi maka,wannan ne adalci na k'arshe da zan maka
Idan har ka amince da rabuwa da ita,to kazab'i ko y'ar sarkin wace k'asa ce zan aura ma ita
Idan kuma har kakai goben kana kan bakanka na k'in rabuwa da ita to tabbas zaka bar min masarauta
Sannan kuma zaka tsallake tauran ninki biyu, d'aya na barin masarauta d'aya kuma na jayayya dani"
Bubbuga k'ofar da akayine ya sa Rauda ta tashi,akan gadon mama ta ganta
Tana jiyo muryar maman tana cewa
"Kitashi kiyi sallah"
Dafa kanta tayi da yike sarawa kamar ze rabe biyu tana girgiza shi
"Aasim,kada kayi haka dan Allah"
Y'arfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE*🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_🧕🏻
_Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 1⃣6⃣
Ina yima ɗaukancin masoyana barka da sallah, dafatan anyi sallah lafiya, wannan Page na baku shi amatsayin barka da sallah, sannan ina me baku haƙuri akan jina shuru da kuka yi bani da lafiya ne ina buƙatar addu'arku
_7:32_🕒 PM
FRI, JUN 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_
"Aasim kada kayi haka,kada kayi haka dan Allah"
Tafad'a cikin tsananin damuwa
Bubbuga k'ofar mama ta kuma yi akaro na biyu
Cikin rashin k'warin jiki ta mik'e jiri na d'ibarta,ga kanta da yayi mata mugun nawi tana jin kamar an d'aura mata gingimemen dutse
Ta zare sakatar falon tana jingina da bango da sauri,dan ji tayi tana neman fad'uwa
Mama ta kalleta sosai tace
"Haryanzu kan bedena ciwon bane?
D'aga mata kai kawai tayi batare da tayi magana ba
Mama tasauke numfashi cikin damuwa tace
"Sannu,ina ganin idan gari yayi haske kawai zamu je k'aramin asibiti adubaki, k'ilan harda typhoid,kidaure kiyi sallan"
To Rauda tace tafito ta d'au buta tayi alwala,tana rawar sanyi
Lokaci d'aya zazzab'i me zafi ya rufeta,
A gaggauce tayi sallar saboda sanyin datake ji sosai,tana idar da sallar ta koma kan gado ta lullub'e
B'angaren Aasim kuwa,tunda taron fada ya tashi,yashige d'akinsa tare da kullewa dan gabad'aya baya son a damesa
Yana jiyo muryar ammi daga bakin k'ofar tana fad'in ya bud'e
Amma yak'i saboda baya son yaga tashin hankalin dake tare da ita,harta gaji ta wuce
Ya na zaune a k'asa kawai, cikin tsananin tashin hankali
K'wan-k'wasa k'ofar aka kuma yi,yaja gajeren tsaki tare da kifa kansa
Daga can k'ofar d'akin muryar mus'ab yaji Wanda ya kasance babban amininsa
Hannunsa ya d'aga yayi nuni da k'ofar, tabud'e
Mus'ab ya shiga d'akin Yana fad'in
"Wai meke damunka ne Aasim? Ace tun daren jiya ka kulle kanka a d'aki kakuma sawa d'akin takunkumi tayadda bawanda ze iya shigowa"
Aasim numfashi ya sauke yana d'auke kansa da ga kan mus'ab
"Kawai banaso a dameni ne,ina buk'atar natsuwa ne"
Mus'ab ya jinjina kai yace
"Hakan yayi kyau,inafatan a natsuwar da kasamu ka canza abunda ke zuciyarka,
Dan nasan jiya kana cikin rud'ani ne,shiyasa kak'i yin abunda me martaba ya umarce ka"
Aasim Ya sauke gauron numfashi tare da lumshe idanuwansa wad'anda suka kad'a sukayi ja
Mus'ab ya gyara tsugunnuwar da yayi yana k'ara fuskantar Aasim d'in
"Kayi shuru,ba kace komai ba,ko haryanzu kana kan bakannaka?
Ya bud'e idanuwansa yana d'aura su akan mus'ab
"Mus'ab,bazan iya rabuwa da ita ba,bazan iya ba"
Yafad'a cikin wani irin yanayi
Zaro ido mus'ab yayi yana kallonsa cike da mamaki
"Mekake nufi Aasim?kana nufin kazab'i rabuwa da ahalinka,takan bil'adama?
Yad'an numfasa sannan ya cigaba da cewa
"Ni wallahi banga abunda kagani agurin waccan bil'adamar ba,da yasa gabad'aya ka rikita tunaninka,
Dan allah kadawo cikin hankalinka,akwai kyawawan mata aduniya,ga kuma saima..........
Katsesa yayi ta hanyar d'aga masa hannu
"Dan allah kada ka k'ara b'ata min Rai,ni ita nike so kuma ita na zab'a zanyi rayuwa da ita,abunda nagani da ya rikita min tunani akanta kuma
Wannan ba damuwar ka bane,idan zaka bani shawara a matsayinka na aboki na kabani,idan kuma maganganun banza kazo kafad'a min ga hanya"
Ya k'arasa fad'a yana nuna mai hanyar fita
Mus'ab ya sauke ajiyar zuciya cike da juyayin al'amarin abokinnasa
"Aasim nikake fad'a ma haka?
Aasim ya d'aga kai yace
"To mekake so ince maka? A matsayinka na aminina kamata yayi kabani shawarar yadda zanyi insamu mafita amma kazo kana fad'a min abunda kasan ze k'ara min b'acin ran danike ciki"
Mus'ab yakuma sauke numfashi yana kad'a kai
"Shikenan,allah ya baka hak'uri"
Yafad'a yana mik'e wa ze fita
Sannan yace
"Bazan takuraka ba,akan fasa abunda kayi niyya,amma ina me baka shawara da kada ka bijirewa umarnin mahaifinka,katuna da haihuwar ka da yayi,da kuma rainonka har izuwa girmanka ko ba komai yaci wannan arzik'in "
Yana gama fad'ar haka ya fice
Doguwar ajiyar zuciya Aasim ya sauke tare da jinginar da kanshi
Tabbas yasan abunda yike shirin yi ba dai-dai bane,to amma ya zeyi? Ya zeyi da muradin zuciyarshi?
Ya runtse idanuwansa yana hango kyakkyawar fuskarta
"Bazan iya rayuwa babu keba *Rauda*"
Yafad'a tare da furzar da wata iska me zafi
Mik'ewa yayi yana fad'in
"Nasan zaka fahimceni abi,idan nak'ara yimaka bayanin yadda nike jinta a cikin zuciyata"
B'acewa yayi,be bayyana a ko ina ba sai abakin falon sarki inda yike hutawa
Kallo d'aya yayima kuyangin dake tsattsaye bakin k'ofar ya kauda kai tare da cewa
"Ku isar da zuwa na"
D'aya da ga cikinsu wacce take daf da k'ofar tace
"Yarima Aasim na buk'atar iso ranka shi dad'e"
Tafad'a cikin d'aga murya
Daga ciki aka basu izinin su bud'e k'ofar
Suka bud'e suna rusunawa
Gabanshi na fad'uwa ya shiga k'asaitaccen falon da akayi masa ado da zinarai kala-kala
Sarki Ramzad na zaune kan wata kujera me d'an fad'i ya jingina idanuwansa a lumshe
Shigowar Aasim d'inne yasa ya bud'e idanuwansa yana zubasu akansa
Cikin ladabi Aasim ya rusuna yana fad'in
"Barka me martaba,ina fatan kana cikin k'oshin lafiya"
Sarki Ramzad ya ce
"Lafiya,Ina fatan kaima haka?
Aasim yace
"Nima ina lafiya"
Sarki Ramzad ya gyad'a kai yana kauda kansa daga kallonsa
"Me ke tafe dakai?
Aasim ya d'an yi shuru sannan yace
"Inason magana dakai ne"
Jinjina kai sarki Ramzad yayi yana yima wazirin sa nuni da hannu alamar yafita ya basu guri
Cikin girmamawa wazirin ya rusuna tare da b'acewa
Sarki Ramzad ya maida hankalinsa kan Aasim yana cewa
"To ina jinka,fad'amin abunda kayanke ko sai munje fada tukunna?
Aasim ya sauke numfashi yana mik'e wa ya k'arasa gaban sa
Ya durk'usa tare da d'aura kansa a kan k'afafuwan mahaifinsa
Wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa daga idanuwansa
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare dasa hannunsa yadafa bayan sa
Tabbas babu abunda yi keso sama da Aasim, yana matuƙar jinsa acikin zuciyarsa
Kuma babu abunda yafiso irin yaga Aasim cikin farin ciki
Amma dole ne ya dakatar dashi
Cikin kwantar da hankali yace
"Aasim, ka sani bawai na hanaka abunda kake so bane, dan jin daɗina
A'a, saboda adalci ne, domin babu wani rauhani daya isa yayi haka a ƙyalesa, Kaga ko bekamata na ƙyaleka ba dan kana ɗan dana haifa
Kasani da zarar akace babu ni, to kaine mai mulkin wannan masarautar
Ya kamata ka fahimce ni, nayi maka alƙawarin ko ƴar gidan wacece idan Kaga tayi maka zan auramaka in har a jinsin ka ce
Amma baze yuwu in barka ka cigaba da rayuwa da bil adama ba bazeyu ba"
Aasim ya ɗago kansa cikin muryarsa da ta dishe yace
"Abi,dan Allah kabarni nayi rayuwa tare da ita,ita kaɗai nike so banajin zan iya rayuwa da wata mace a duniya in ba ita ba........
" dakata!
Sarki ramzad ya katse sa, sannan ya cigaba da cewa
"nabika ta faɗa bakaji ba, na bika ta lallami nanma bakaji ba
To kasani bazan takura ka ba, tunda har ban isa dakai ba, nan da awa ɗaya zamu je fada, duk abunda kayanke kafaɗa acan"
Aasim ze kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu
"bana son na kuma jin komai daga gareka, tashi ka bani wuri"
"Abi.....
Be ƙarasa ba, sarki ramzad yasa hannu ya ɓatar dashi
Ƙarfe takwas suka isa ƙaramin asibitin gwamnatin, sun tadda mutane da yawa akan Layin ganin likita
Hakan yasa suka zauna suna jiran layi yazo kansu
Kallo ɗaya zakama Rauda, kagano ramar da tayi acikin kwana ɗaya kacal
Kallon jama'ar dake wurin kawai take yi amma zahiri hankalinta baya gurin
Damuwarta ta kuma ƙaruwa yayin da taga har zuwa lokacin bata ji wani alamun Aasim ba,
Me ya faru dashi, bayan dawowarta? Shin ya amince ya rabu da itanne ko yaya?
Tambayar da tayi ma kanta kenan wacce bata da amsar ta
Maganar sa ce ta dawo mata
_"Rauda ina ƙaunarki, zan iya haƙura da komai inhar zan rayu dake"_
"baze amince ya rabu dani ba nasani"
Tafaɗa a fili batare da tasan maganar ta fito filin ba
Mama dake zaune kusa da ita ta kalleta cikin rashin fahimta tace
"mene?
Kallon maman tayi itama cikin rashin fahimtar
" waye baze amince ya rabu dake ba?
Mama ta jefo mata Tambayar tana kafeta da ido
Daburcewa Rauda tayi, dan ita bata san maganar da tayi a zuciya ta fito fili ba, ta rasa me zata ce
Numfashi mama ta sauke tana kaɗa kai, lokacin layi yazo kansu tamiƙe tayi gaba batare da ta kuma cewa komai ba
Rauda tabi bayan ta, gwajin farko da likita yayi ya gano BP ɗinta yayi ƙasa sosai
Kallon ta yayi yana cewa
"meke damunki? Da BP ɗinki yayi ƙasa haka?
Shuru Rauda tayi, likitan ya cigaba da cewa
" BP ɗinki yayi ƙasa sosai, shi yasa kike jin ciwon kai da kuma jiri, zan rubuta miki magunguna Asiya kisha, sannan kidena barin kina shiga cikin tunani Allah ya ƙara lafiya"
Mama ta amshi takaddar maganin suka, fito kowanne zuciyarsa babu daɗi
Napep suka hau ta kawo su gida suna gab da tsayawa taji maganar Aasim
_"kisameni a bayi yanzu"_
ko tsayawa bata bari mai nepep ɗin ya gama yi ba ta diro
Cikin faɗa mama tace
"wani irin ganganci ne wannan? miye kikema sauri da ba zaki tsaya yagama tsayawa ba?
Cikin sauri Rauda tace
" bayi nikeso na shiga"
guntun tsaki mama ta ja,tana zage Jakarta zata ba mai Napep ɗin kuɗi
itako Rauda ta ƙagara tagansa,juyawa tayi da sauri ta shige cikin gidan
Ko buta bata tsaya ɗauka ba ta shiga bayin
A tsaye tagansa,rufe ƙofar bayin tayi da sauri tare da ƙarasawa inda yike
"Aasim, kana lafiya? Me ya faru na jika shuru? Ince dai ba wani abu a kayi maka ba?
Ta jero mai tambayoyin cikin zaƙuwa da son jin abunda ta tambaye sa
Be bata amsa ba, illa rungumeta da yayi,yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya
Ita ɗinma ajiyar zuciyar ta sauke, tana jin sonsa na bin duk wani sassa na jikin ta
"kabani amsa mana Aasim"
Ɗagota yayi ya zuba ma fuskar ta ido amma kuma har lokacin beyi magana ba
Kawai yana hango yadda za ace yayi rayuwa babu ita ne
Girgiza kai yayi yana ƙara rungumeta sosai
"baze yuwu ba, baze yuwu ba"
Yafaɗa cikin tsananin damuwa
"miye baze yuwu ba, kayi min magana yadda zan fahimta dan Allah"
Kuma Ɗagota yayi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace
"Rauda inaso kiyimin alƙawarin cewa ba zaki taɓa rabuwa dani ba,har ƙarshen rayuwarki"
Kallon sa ta keyi sosai,
"Aasim kasani ai, bazan iya rabuwa dakai ba"
Girgiza kai yayi, yace
"nasani a yanzu, amma bansan meze iya faruwa nan gaba ba, shi yasa nikeso kiɗaukar min alƙawari da kanki da kuma bakinki"
Kaɗa kai tayi tare da cewa
"shi kenan nayi alƙawari bazan taɓa rabuwa da kai ba"
Gauron numfashi ya sauke yana gyaɗa kai
"nagode, wannan alƙawarin da kika ɗauka a yanzu ya kuma ƙarfafamin gwiwa,zanje in sanar dasu abunda na yanke"
"amma Aasim, bekamata.......
Katseta yayi
" kinga Rauda kada kice komai,na san watarana zamu dai-daita dasu, amma ke bazan iya jurar rashinki dai-dai da rana ɗaya ba"
Be jira jin mezata ce ya ɓace
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi, tare da fitowa daga bayin, ɗaki ta shiga ta zauna akan gado
Maganar daya faɗa ce kawai take yi mata yawo a kunne
_"kinga Rauda kada kice komai nasan wata rana zamu dai-daita dasu amma ke bazan iya jurar rashinki dai dai da rana ɗaya ba"_
Sauke ajiyar zuciya tayi, ta janyo filo ta ɗaura kanta
Meyasa ze zaɓi rabuwa da ahalinsa saboda ita? Me yasa?
Tayi wa kanta tambayar
Lumshe idanuwan ta tayi, tana fatan ace har yanzu Mafarki take yi
Dan har lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa
Ɓangaren Aasim kuwa, lokacin da ya koma masarauta saura ƴan mintoci a tafi fada
Yana zaune a ɗakinsa ya zuba tagumi, fulawar saƙo ta shigo ɗakin
Hannu yasa ya damƙe, saƙon ammi ne tana son ganin sa
Kamar baze je ba, sai kuma yaga rashin dacewar Hakan
Miƙewa yayi ya bayyana a ƙofar sashenta
"ku isar da zuwa na"
Yace ma kuyangin dake bakin ƙofar
Tun kan su kai gayin magana aka basu izinin buɗewa
Shiga yayi da sallama yana rusunawa
Ammi tayi ma jakadiyarta nuni data fita sannan ta dawo da kallon ta kansa
"Aasim ni kake wulaƙantawa ko? Ace tun jiya nikeson yin magana da kai amma ka sawa Ɓangaren ka takun kumi ko?
Ƙasa yayi da kansa
" kiyi haƙuri ammi, ba nayi Hakan danna ɓata miki bane, nayi ne dan nasamu natsuwa"
Ta jinjina kai tace
"yayi kyau, saura minti biyar taron fada, me ka yanke a zaɓin da aka baka?
Shuru yayi yana nazarin abunda zece
" tambayar ka nikeyi kayi min shuru"
Cikin fargaba yace
"ammi ki gafarceni, amma banajin zan iya haƙura da duka zaɓi biyu"
Kaɗa kai tayi cike da ɓacin rai da kuma tashin hankali
"kadai ce kawai ka zaɓe ta a kanmu, ka fifita bil adama akan iyayenka
Wai shin Aasim lafiyar ka ƙalau kuwa? Ko ko taɓin hankali ne yasa meka?
Taɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa
" shin kana tunanin bil adama zata sama ma dauwamamman farin ciki ne?
Kayi babban kuskure Aasim, ko da yike laifi na ne da na goyama baya tun farko
Amma ina so ka sani nadama da danasani zasu biyo bayan ka inhar kazaɓi rayuwa da ita sannan........
Ƙarar sanar wa data Kaɗa ita ta dakatar da ita
Numfashi ta sauke tana ɗauke idanuwan ta a kansa
"lokaci yayi, zaɓi ya rage gareka, abu na ƙarshe da nike so kasani shine. Idan har kazaɓi rayuwa da ita to kada ka ƙara zuwa inda nike,kaje inayi maka fatan alheri"
Tana gama faɗar haka ta ɓace daga gurin
Aasim numfashi ya sauke Yana Miƙewa cike da tsananin ruɗani tabbas ya san ze aikata babban kuskure amma yana da yaƙinin iyayen sa ba zasu iya jurar rashin sa ba, nan da wani ɗan lokaci zasu nemesa kuma ma ya san da wuya Abi ya zartar da hukuncin kora a kansa ƙilan yafaɗi Hakan ne dan ya tsorata sa ya rabu da rauda
Ɓacewa yayi ya bayyana a fada, kamar kullum fadar cike take da manyan rauhanai
Suna zazzaune, Aasim na bayyana suka rusuna suna gaishe sa
Saida Aasim ɗin ya zauna a kujerar sa sannan suka ɗago
Shuru ya biyo baya na wasu mintoci, sannan sarki ramzad yayi gyaran murya
Hakan yasa fadar yin tsit
"Aasim, kafaɗa ma fada abunda ka yanke, shin ka haƙura zaka rabu da itanne? Ko ko kana kan bakanka na rayuwa da ita?
Aasim yayi shuru cike da tsananin fargaba
Sarki ramzad ya kuma mai-maita tambayar sa sannan ya ƙara da cewa
" bana buƙatar jin shurun ka, rayuwa da mu kazaɓa ko rayuwa da ita?
Aasim saukowa yayi daga kan kujerar ya durƙursa
" Abi ka gafarceni, har yanzu nakasa yanke komai, bana jin zan iya Haƙura da duka zaɓi ɓiyun da ka bani"
Sarki ramzad ya jinjina kai yace
"kenan har yanzu kana kan bakanka na ƙin rabuwa da ita?
Aasim ya ƙara dur ƙurshewa
" Abi dan Allah, kayi haƙuri kabarni na cigaba da rayuwa da ita, nayi maka alƙawari bazan sake aikata kuskure ba.......
Ɗaga mai hannu sarki ramzad yayi cike da ƙunar zuciya
" ya isa, ka riga da ka bani amsar tambaya ta, dan haka kada ka ƙara cewa komai"
Aasim ya runtse idanuwan sa yana ambaton sunan Allah
Sarki ramzad ya maida kallon sa ga rauhanan da suka yi jugum jugum saboda mamakin kafiyar da Aasim yayi
Yace
"tunda abunda ya zaɓa kenan, to bazan fasa hukuncin dana yanke ba, dan haka aje a shirya tauran zuwa jibi za a zartar da hukuncin"
Ɗaya daga cikin manyan fadawanne ya durƙusa cike da tashin hankali yace
"mai martaba, Aasim ɗan kane, be kamata ayi masa hukuncin kora ba, a sassauta masa ranka shidaɗe"
Shima wani ba faden zubewar yayi yana faɗin
"a sassauta masa ranka shidaɗe, a canza masa wannan hukuncin"
Sarki ramzad ya girgiza kai
"babu ruwan ku da matsayinsa, na riga da na yanke hukunci kuma wannan hukuncin shine adalci dan haka bana so na ƙara jin wani daga cikin ku ya furta komai, aje a shirya tauran kamar yadda na bada umarni"
Gabaɗaya jikin Aasim ya gama mutuwa, amma ya kasa ƙara furta komai
Hawaye kawai yikeyi, a haka aka watse daga fadar cike da juyayin al'amarin
Tunda Aasim ya koma Ɓangaren sa ya kwanta, yana ta tunanin bijire ma mahaifinsa da yayi
Tabbas yayi kuskure kuma be kyauta ma kansa ba
Buɗe ƙofar ɗakin aka yi aka shigo
Ya ɗago yana duban me shigowan, shaida ce
Ya tashi ya zauna yana kamo hannunta
"shahida, lafiya na ganki wani iri? Baki da lafiya ne?
Cikin gwaran cinta tace
" ba kai bane,kake ta yin kuka ɗazu"
ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ 🧕🏻
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE 📕 1⃣7⃣
Wannan Page nakane......... Ina alfahari da kai a ko da yaushe
_9:15_🕒 PM
SAT, JUN 8
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_
Murmushin ƙarfin hali yayi yana ɗaukan ta ya ɗaura ta ajikinsa
"dan kinga ina kuka, shi ya sa kika yi wani iri? Ba kyaso kiga ina kuka ne?
Shahida ta ɗaga kai alamar eh
Murmushi ya kuma yi yana tallabo kyakkyawar fuskarta
"shi kenan farin ciki na, daga yau bazan sake yin kuka ba, kinsan Abi ɗinki na sonki da yawa baya so ya ganki cikin damuwa"
Shahida tayi murmushi tana kwanta wa a jikin sa
"abbi,ina ammi na?
Aasim yayi shuru, yana kallon ta
Shahida ta ɗago kanta tana kallon sa tare da nanata tambayar da tayi
Yayi ƙoƙorin kauda damuwar dake fuskar sa yace
" kinaso kiganta ne?
Shahida ta ɗaga kai da sauri
Ya rungume ta ajikinsa yana sauke numfashi
" shi kenan, ki ƙara haƙuri kinji? Zaki ganta har sai kin gaji, yanzu faɗamin me kikaci yau?
Haka ya dinga lallaɓata har tayi barci, sannan ya kwantar da ita
Ya tsura mata ido yana jin tausayinta, kullum bata da maganar da ta wuce ina amminta?
Gashi da wuya ta rayu da ita yadda take so numfashi ya sauke tare da nuni da hannun sa
Wani ƙaton madubi ya bayyana, ya sake yin nuni da hannun sa
Sai ga Rauda ta bayyana a ciki, har lokacin tana kwance akan gado tana rawar sanyi
Ta duƙunƙune da bargo
"Rauda!
Ya kira sunan ta, ta buɗe idanuwan ta a hankali tana duba inda ta jiyo muryarsa amma bata ga kowa ba
Ya sauke ajiyar zuciya yana jin ƙaunarta na ƙara ratsasa
Hannu yasa ta cikin madubin ya ɗaura a wuyan ta yaji zafi rau
Ita ko zabura tayi dan bata ga kowa ba ta kuma ji antaɓata
Guntun murmushi yayi tare da faɗin
"matsoraci ya, nine"
Ta ƙara duba kan gadon bata ganshi ba, a hankali tace
"to kana ina? Ya aka yi bana ganin ka?
" ina masarauta, nima banajin daɗine bazan iya zuwa ba, kinsan duk abunda kikeji ajikinki inaji ajikina,ga kuma damuwar da nike ci"
Ta maida idanuwan ta ta Lumshe tare da cewa
"da gaske kana jin yadda nikeji a yanzu?
Ya ɗaga kai kamar tana ganin sa
" sosai habibty,zafin jikin ki yayi yawa,kinsha magani?
Ta ɗaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
"sannu Allah ya baki lafiya,nan da ƙan-ƙanin lokaci zakiji sauƙi in sha Allahu"
"yanzu me kake yi? Ina so in ganka"
Ya gyara zamansa yana dai-dai ta saitin madubin
"to shi kenan rufe idanuwan ki ki natsu sosai"
Ta rufe kamar yadda yace, amma ba ta ganshi ba har zata buɗe, sai taga duhun dake cikin idanuwan ta ya fara yayewa
Ahankali Ahankali har duhun ya yaye gaba ɗaya ya bayyana
Guntun numfashi ta sauke tana cewa a zuciyar ta
"wannan kyawun naka dama ai sai jinsin aljanu"
"habibty"
Ya kira ta,ta amsa na'am
"kinyi mafarki ɗazu ko?
Ta ɗaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
" to ba mafarki bane, abunda ya faru a fada ne kika gani"
Jikinta yayi sanyi
"amma Aasim Meyasa zaka yi haka, Hakan ba dede bane, Meyasa bazaka bi umarnin su ka rabu dani ba?
Ya sauke nannauyan numfashi, tare da dafa ƙirjinsa
" ba zaki gane yadda nike jinki a nan ɗina ba, wallahi Rauda bansan dalilin da yasa nike miki irin wannan son me zafi ba, jini keyi kamar idan na rasa ki zan iya rasa rayuwa ta, nima ba da son raina na bijire wa umarnin su ba, amma nasan ba zamu jima ba zamu dai-daita dasu"
Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina girman ƙaunar da yike mata
"amma ya maganar tsallake tauran da Naji anyi magana?
Ya sauke gauron numfashi yace
"zan tsallake jibi"
Jikinta ya ƙara yin sanyi
"Aasim dan Allah inda hanyar da zaka bi kabi, bana so kasha wahala"
Yayi murmushi yana sa hannu ta cikin madubin ya kama hannun ta tare da matsewa cikin nasa
"kar ki damu habibty, tabbas nasan tsallake tauran akwai wahala kuma nima hankalina na tashi idan na tuna azabar dake ciki
Amma kuma hankalina ya kan kwanta idan na tuna cewa zan samu ƴancin yin rayuwa dake bayan wannan wahalar, fatana dai kiriƙe min alƙawarin da kika ɗaukar min"
Haƙiƙa ta ƙara jin ya shiga zuciyar ta to me ma zesa ta karya alƙawarin data ɗaukar mai?
Ta tambayi zuciyar ta tana ganin babu, Guntun murmushi yayi tare da katse mata gajeren tunanin da ta tafi
"ki tuna ke mutum ce, kuma halin mutanen yanzu sai Allah, zasu ɗaukar ma alƙawari amma daga baya su nuna su basu ma san da maganar wani alƙawari ba, amma dai ke na yarda dake na kuma san ba zaki taɓa juyamin baya ba"
Hmmmm Ta sauke ajiyar zuciya kawai batare da ce komai ba
Murmushi ya kuma yi yanayi mata nuni da gefen sa
"baki ga wacce take kusa dani bane?
Sai lokacin ta lura da Shahida dake kwance gefen sa
Ta ƙura ma yarinyar ido tana jin ƙaunar ta acikin zuciyarta
" na tashe tane? Dan ɗazu ta gama tambaya ta ina amminta"
Girgiza kai Rauda tayi alamar a'a tana cigaba da kallon ta
"Meyasa?
Ya tambaya
"saboda kanta ze iya yin ciwo idan ka tashe ta"
Dariya yayi yana duban Shahida dake ta baccinta
"wa yace miki muma rauhanai irin ku ne mutane ragwaye,babu abunda kanta zeyi"
Ta gyaɗa kai tace
"shi kenan tashe ta"
Ya durƙuso sai tin fuskarta yana shafa fuskarta da ambaton sunan ta
Sai ko tabuɗe idon
"Shahida tashi ga amminki"
Tashi zaune Shahida tayi da sauri tana rarraba idanu
Yayi murmushi tare da nuna mata madubin
Haka suka cigaba da fira har saida barci ya fara ɗaukar Rauda sannan ya kaudar da madubin
Yana jin kamar bashi da wata damuwa, dan firar da yayi da ita yasa hankalinsa ya ɗan kwanta
Miƙewa yayi ya isa sashen ammi, sai dai kuyangin ƙin buɗe masa ƙofa suka yi dan sunce tace bata buƙatar ganawa da kowa
*Ranar tsallake tauran*
Duk wani masoyin Aasim da ke cikin masarauta hankalinsa a tashe yike, musamman ammi da gaba ɗaya ta fita hayyacinta
Haka Shima sarki ramzad dauriya kawai yikeyi yana nuna kamar abun Be dame shi ba, amma zahiri ƙasan zuciyarsa cike take da tashin hankali
Ammi kasa haƙuri tayi saura minti goma sha biyar ta shiga Ɓangaren sarki ramzad
Umarni ta bawa waziri da ya fita sannan ta ƙarasa gaban sa ta durƙusa
Cikin tashin hankali da tsananin damuwa ta fara magana
"na roƙeka ka janye wannan hukuncin akan ɗana, shi kaɗai gareni"
Sarki ramzad yayi mata wani kallo yace
"in janye hukunci fa kika ce? Kema kinsan abunda baze taɓa yuwu wa ba kenan,akwai sauran minti sha biyar, kina iya zuwa kisa ɗanki ya bi abunda nace mai, dan shine kika isa dashi.
Amma ni baki isa kisani in canza abunda na yanke ba
Yadda bawa zeyi laifi in hukunta sa, haka zan hukunta abunda na haifa dan haka babu maganar janyewa"
Kuka ta fashe dashi
"amma kasan bayan Aasim bani da wani ɗa a duniya ko?
Gyara zama yayi cike da ƙaguwa da kukannata dan tashin hankalin da yike ciki kaɗai ya ishesa
"kinga Samira,bana buƙatar jin wannan kukan naki, ki tashi ki ɓace min da gani"
Miƙewa tayi cike da ɓacin rai
"na fahimci ni kaɗai nike son Aasim, kai wahalar da ze shiga ko ajikinka, to shi kenan zan tafi amma ka sani duk abunda ya sami ɗana da kai zanyi kuka"
Shima miƙewar yayi a fusace
"ki dakata min da waɗannan kalaman naki, duk ba laifinki bane da Ace tun farko baki basa goyon baya ba da munkawo wannan matakin?
Juya wa ammi tayi ta fice tana kuka bata zame a ko ina ba sai Ɓangaren Aasim
Yana tsaye jikin bango, ya Lumshe idanuwan sa da suka kaɗa sosai
Jin kukan ta yasa ya buɗe su da sauri
Ganin halin da ta shiga ya ƙara ɗaga mai hankali
Durƙushewa tayi a wurin tana cigaba dayin kukan
Ya ƙarasa gaban ta da sauri ze ɗaga ta
Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu
Ya durƙusa yana tambayar ta
"ammi me yafaru?
" idan kai baka son rayuwar ka ni ina so, ka duba wahalar da za kasha idan ka shiga tauran"
Ammi tafaɗa
Aasim ya sauke numfashi yana kama hannun ta
"ammi indai tsallake tauran ne,ki kwantar da hankalinki zan tsallake lafiya insha Allahu Babu abunda ze same ni"
Ta kallesa da jiƙaƙƙun idanunta
"Aasim......
Katseta yayi ta hanyar cewa
" ammi dan Allah kada ki ƙara cewa komai, ammi Rauda itace farin ciki na na kuma son kina son duk wani abu da ze faranta min
Kinsan kema bazan taɓa yin nisa dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki dan Allah, kada ki karya min gwiwa"
Miƙewa tayi tana jinjina kai
"shi kenan, tunda abunda ka zaɓa kenan, Allah ya baka sa'a"
Tana gama faɗar haka ta ɓace
Ajiyar zuciya Aasim ya sauke cike da tausayin mahaifiyar tasa
Sai dai baya jin ze fasa abunda yayi niyya
*filin tauran*
Wurin ya cika sosai da rauhanai, Aasim na tsaye daga gefe inda babban ba fade yike
"Yarima Aasim, shin da gaske ka amince da barin masarauta ta hanyar tsalle ke tauran??
Me faɗar hukunci ya tambaya
Aasim ya ɗaga kai
" na amince "
" ka tabbata?
Me faɗan hukunci ya kuma tambaya
Aasim ya jinjina kai
"na tabbata"
Sarki ramzad ya runtse idanuwan sa cike da tsananin takaici
Babban ba fade yayi nuni da tauran take ƙofarta ta buɗe
Kai tsaye Aasim ya dumfareta
Yana kallon yadda haya ƙin hucinta ke fita
Runtse idanuwan sa yayi yayin da ya isa ƙofar, ya ɗan tsaya ya karanto wasu abubuwa sannan ya kutsa kai
Yana shiga ƙofar ta rufe
Nan da nan garin yayi duhu, iska ta fara kaɗawa da ƙarfi
Wani baƙin hayaƙi ne ya dunƙule yayi tsawo baka iya ganin ƙarshensa a saman tauran ɗin
Wasu kibiyoyi masu haske suna shiga cikin hayaƙin
Zuwa can hayaƙin ya fitar da wata ƙara me razanar wa wanda ta sauka a jikin Aasim
Faɗuwa yayi a ƙasa saboda tsananin azaba,gashi ba a so a kwanta dan danne mutum take yi
Yun ƙurawa yayi ya tashi da ƙyar yana duban jikinsa daya fara huhhujewa
Haka ƙarar ta dinga sauka a jikinsa har sau arba'in da tara
Iya jigatuwa Aasim ya jigatu
Gaba ɗaya jikinsa ya huhhuje,lokacin da ƙofar ta buɗe faɗowa yayi
Mus'ab ne ya ruga da gudu ya taro sa yana Kiran sunansa cikin kaɗuwa da halin da ya shiga
Aasim be kuma sanin inda kansa yike ba, har saida yayi kwana biyu
Sannan ya farfaɗo, lokacin da ya farfaɗo mus'ab ya gani a kusa dashi
Mus'ab na ganin ya buɗe ido ya matso kusa dashi sosai yana faɗin
"sannu Aasim ka tashi? Yaya jikinnaka?
Aasim ya kaɗa mai kai kawai ba tare da yace komai ba
"sannu, ga magani ammi ta aiko maka, tace da ka farka kasha ze taimaka gurin komawar jikin ka dai-dai"
"Allah sarki ammi"
Aasim ya faɗa a cikin zuciyar sa, yunƙurawa yayi ze tashi
Mus'ab ya dakatar dashi
"kada ka tashi, baka ga halin da kake ciki bane?
Aasim ya girgiza kai
" mus'ab barni na tashi, taimaka min dai in jingina"
Mus'ab ya jinjina kai tare da tallafa masa ya jinginan
"amma ya kake ji yanzu? Da kwai wani guri da yike ma ciwo?
Mus'ab ya kuma tambayansa
Aasim yayi murmushin ƙarfin hali yana sake girgiza mai kai
" a'a abokina, ka kwantar da hankalinka babu inda ke min ciwo"
Ya faɗa da muryarsa da ta dashe sosai
Mus'ab ya jinjina kai,yana miƙa mai maganin da ke cikin wani kofin silver
"gashi kasha, me kake buƙatar kaci?
Jar abarba ko koriyarta?
Aasim ya girgiza kai yana kai kofin bakin sa
Sai da ya sha rabin maganin sannan ya ajiye yana kallon yana yin garin
" yau kwana nawa anan?
"kwanan ka biyu da yini"
Mus'ab ya bashi amsa
Ya ɗan zaro ido
"kwana biyu??
" eh kwana biyu me ya faru?
Mus'ab ya tambaya yana kafesa da ido
Cikin ƴar damuwa Aasim yace
"Rauda mana, Nasan tana cikin damuwa da jina shuru da tayi"
Mus'ab ya kauda kansa da ga kan Aasim yana mamakin irin ƙaunar da yike wa wannan bil'adamar
"to Meyasa zata damu, bayan ta juya ma tunani, ta san yanzu ka zama nata ita kaɗai"
Yana yin fuskar sa ya sauya
"Kaga mus'ab bana so kana faɗan magan ganu marasa daɗi a kanta"
Mus'ab yace
"to maida wuƙar angon bil'adama"
Guntun tsaki Aasim ya ja tare da yin nuni da hannun sa madubi ya bayyana
Ya kuma nuna sa da hannu, sai ga Rauda zaune ta zuba uban tagumi
Kallon mus'ab yayi yace
"ka nemomin ko ma miye ina jin yunwa"
Mus'ab yayi murmushi tare da faɗin
"kadai ce kana son ganawa da tauraruwar mata"
Ya faɗa yana Miƙewa
Aasim banza yayi dashi, sai da ya fice sannan yaja gajeren tsaki
Tare da fuskantar madubin sosai
" *habibty!*
Ya kira ta, ta ɗago kai da sauri tana kalle-kalle
" Aasim kana inane, me ya faru da kai najika shuru?
Ta tambaya a ƙagare
"ina nan lafiya habibty, ki kwantar da hankalinki"
Hmmmm ta sauke nannauyar ajiyar zuciya
"inaso inganka yanzu please"
Ya kalli jikinsa yadda ya huhhuje tare da sauke numfashi
"habibty kiyi haƙuri baza ki iya ganina ba"
"amma Meyasa? Ka san damuwar da na shiga kuwa? A sanadin na Dena jinka, na Dena ganin ka"
Ya kuma sauke numfashi yace
"da gaske habibty?
Ɗaga kai tayi da sauri
" da gaske Mana, nidai Ina son inganka yanzu dan allah"
"habibty bana so kiganni a yana yin da nike ciki ne, kiyi haƙuri a kwana biyu tukunna"
Ya faɗa
Ta jingina da kujerar da take kai tana sauke ajiyar zuciya
"ni ko a yaya kake Ina son ganin ka ahaka"
Yayi Guntun murmushi tare da cewa
"to bazan iya zuwa ba, sai dai in janyo ki ta cikin inda nike kallon ki, amma kafinnan ina mama?
" Mama bata nan"
Ya jinjina kai
"shi kenan"
Cikin minti biyu ta ganta a ɗakinsa
Sai dai yana yin data gansa ya yi mugun ɗaga mata hankali ta tsorata sosai
Gaba ɗaya tsigar jikin ta tashi take yi
Cikin kiɗima ta ja da baya tana kallon sa
A tsorace
"A...a..sim"
Ta Kira sunansa cikin rawar murya
Miƙewa yayi daƙyar ya ƙara sa inda take, dan har lokacin yana jin jiki
"kingani ba, shiyasa banso kika ganni ba"
Ya faɗa yayin da ya isa gabanta
Kallon sa kawai take yi cike da al'ajabi
"me yasa Meka haka? Ya aka yi kakoma haka?
Yayi murmushin ƙarfin hali yace
" tauran, ko kin manta?
Idanuwan ta ne suka cicciko da hawaye
"Aasim, saboda ni ka koma haka?
Ta faɗa hawayen da suka ciko idanuwan ta suna gangarowa
Murmushi ya kuma yi
"dan Allah kada kiyi kukannan, kinsan dai abunda bana so na gani a fuskar ki kenan ko?
Ji tayi zuciyar ta ta karye, Bata damu da yanayin data gansa ba ta rungume sa
Cikin shesshekar kuka tace
" duk a sanadina Aasim? Yanzu ahaka zaka cigaba da zama kenan?
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi yana jin guguwar ƙaunarta na daɗa lulluɓesa
Ɗago ta yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta
"a'a habibty, nan da wani ɗan lokaci zan koma yadda nike, ki kwantar da hankalinki kinji?
Mai da kanta tayi kan ƙirjinsa tana cigaba da yin kukan
Ya Lumshe idanuwan sa yana jin kukan ta har cikin ransa
"ki yi shuru hakanan dan Allah, ko kinaso Nima in fara ne?
Girgiza kai tayi tana share fuskarta
Ƴarfillo.
0 comments:
Post a Comment