_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Ya kuma yin murmushi ya na kama hannun ta zuwa bakin gadon suka zauna suna fuskantar juna
"to shi kenan ya isa haka,Nasha faɗa miki cewa idan kina kuka bakya yin kyau amma kinƙi yarda"
Ƙarasa goge ragowan hawayen tayi tana zuba masa fararen idanuwan ta
"ni dama bani da kyau, ko banyi kuka ba"
Ya ɗan fito da idanuwan sa waje tare da faɗin
"inji wa ya faɗa miki? Ai ke idan akwai abunda ya wuce kyakkyawa dashi ya kamata a kira ki, domin kyawun ki na daban ne"
Murmushi tayi tana girgiza kai
"zan iya yadda da Hakan amma a gurinka, dan nasan son da kake min ze iya sawa Kaga kyau na fiye da kima, amma ni nasan ni ba kyakkyawa bace"
Ya kama hannun ta yana matsewa cikin nasa
"da gaske habibty kina da kyau, bawai idona rufe wa yayi ba"
Ta kaɗa kai tace
"to shi kenan Naji, amma ya kake ji ajikinka nasan ko ina yima ciwo yike yi ko?
Ta Ƙarasa faɗa idanuwan ta na kuma yin rau-rau da ƙwalla
" ya ilah, habibty baki ji abunda nace miki ba ko? Kina so raina ya ɓaci ko?
Girgiza kai
Yace
"oook idan bakya so raina ya ɓaci ki maida hawayen nan kada ki bari su zubo"
Tayi ƙoƙorin maida hawayen amma ina kafin tayi wani yunƙuri su biyo kumatun ta
Hannayen sa yasa ya tare hawayen suka ɗiga akai
"bazan taɓa bari hawayenki su zuba a ƙasa ba, indai ina tare da ke Rauda, dan Allah ki bari"
Kwantawa tayi a jikinsa tana haɗiye wani ƙullutun damuwa da ya dunƙule mata maƙogoro
"ka barni inyi kukan dan Allah,in banyi ba ina jinsa yana dunƙule min a ƙirji"
Hmmmm ya sauke numfashi tare da cewa
"to wai kukan me kike yi ne? Faɗa min,indai kukan halin da nike ciki ne kibari, nan da wasu kwanaki zaki ga na koma dai-dai"
Dai de lokacin mus'ab ya shigo ɗakin ɗauke da tiren abinci
Ganin su a tare ya sa ya shigo da sallama
Aasim ne ya amsa yana tambayar har ya dawo?
Be bashi amsa ba illa ajiye tiren da yayi ya fice
Cike da takaicin ganin ta da yayi, dan shi gaba ɗaya haushinta yike ji
Dama ya san ze ganta Aida da ainihin suffarsa ze shiga ɗakin dan ya razana ta
Ƙwafa yayi tare da ɓacewa
Ita ko Rauda bayan fitar mus'ab ɗago wa tayi tana duban Aasim dan a kallon da mus'ab ya yi mata ta hango tsanarta ƙarara a tare dashi
"wanene wannan da ya shigo?
"abokina ne"
Ya bata amsa
Ta ɗanyi shuru sannan tace
"amma nayi masa wani laifi ne?
Girgiza kai yayi yana murmushi
" kinga ƙyalesa akwai abunda ya ɓata masa rai ne kawai"
Jinjina kai tayi tana duban tiren da ya ajiye
Wasu kalar abinci ta gani da bata san dasu ba a duniya
Abu ɗaya ta fahimta a tiren itace arbaba, kuma abarbar ma ja
Mamaki ne ya kamata dan ita a sanin ta abarba ba ja bace
Ganin yadda take kallon tiren yasa yace
"yadai, me kike mamaki ne?
"dama akwai abarba Jane?
" eh akwai amma anan duniyar mu"
Ta jinjina kai tana duban madubin
Mama ta gani ta dawo
Zaro ido tayi cikin fargaba
"mama ta dawo"
Ya kalli madubin yace
"to yanzu yaza ayi? Ta ina kike so in maida ki?
A gaggauce tace
" bayi, sai in yi kamar daga bayi nike"
Duba bayin yayi yaga akwai mutum a ciki
"da akwai mutum a bayin"
Dafa kai tayi cikin damuwa
"maidani uwar ɗaka kawai tunda tana falo"
Jinjina kai yayi ya maida ta yana cigaba da kallon madubin
Ita ko tana ganin ta a ɗaki ta miƙe ta yo falo
Ganin ta ba ƙaramin faɗar mama da gaba yayi ba
"ke ta ina kika ɓullo?
Rauda tayi saurin ɓoye fargaban da take ciki tace
" daga uwar ɗaka mana mama"
Mama mamakine ya bayyana a fuskarta
"bangane daga uwar ɗaka ba, ba yanzu na shiga na ajiye hijabi ba, ya aka yi ban ganki ba?
Tayi mata tambayar tana kafeta da idanu
Gaban Rauda ya cigaba da faɗuwa
"baki dai lura bane, ina kan gado,"
Ta faɗa cikin dake wa
Mama ta jinjina kai tace
"to gaskiya zanje adubamin hawan jinana ƙila ya hau da yawa da ni banga kowa ba a ɗaki wallahi"
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ganin mama ta yarda
Ƙarasowa kan kujera tayi ta zauna kusa da maman tana dariya
"mama Bawani hawan jini fa, tsufa ne kawai da kika fara"
Mama tace
"gidan ku, dudu nawa nike? Bari kiga kiyi aure kibani wuri yadda zan koma yarinya shataf, dan gayu zan dinga ci"
Dariya Rauda tayi sosai
"Haba ainasan babu wani gayu da zaki rinƙayi, ni da baba ze ji shawara ta ma da ya ƙaro muku ƴar budurwa"
Mama kai mata duka tayi
Ta goce tana cigaba da yin dariyar
Bayan sati biyu,hankalin Rauda ya kwanta sosai bata da wata damuwa musamman data ga Aasim ya warware ya koma yadda yike
Uwa uba ga soyayyar da suke yi me zafi, wacce tasa ko da yaushe bata rabo da tunanin sa
Kamar ko wani dare bayan mama tayi bacci
Rauda na zaune a falo tana guga
Maganar sa taji
"habibty ina son ganin ki"
Ɗan ɗagowa tayi tace
"kabari in gama guga please....
Kafin ta Ƙarasa maganar taji wata iska me daɗi ta lulluɓeta tana janta
Lumshe ido tayi tana faɗin
"oh Aasim kasan fa Bama samun wuta sosai yanzu waze Ƙarasa min gugar"
Jin iskar ta lafa yasa ta buɗe idon, a kwance tagansa gefen gado
Kanne mata ido ɗaya yayi yana faɗin
"ba dai guga bace? To juya kigani"
Juyawan ko tayi tana duban madubin
Abun mamaki ion ɗin da kansa taga yana yin gugan
Ta zaro ido cike da mamaki
Dariya yayi yana janyo ta ta faɗa jikin sa
"miye na wani zare idanu, abunda yafi haka ma zaki gani, zaki wani ce in bari ki gama guga, kinsan yadda na matsu in ganki kuwa?
Ta marai-raice fuska tace
" to ni yanzu me zan maka?
Murgina wa yayi da ita, ya zama itace a kwancen
"me ma zaki min kike tambaya na?
" to ni bacci nike son nayi"
Ta faɗa a shagwaɓe
Yadda tayi maganar ya ƙara rikita sa
Ya tsa yasa yana zagaye gefen fuskarta
"bacci? To kiyi mana aiban hanaki ba"
Ji tayi wani abu ya fara taso mata ta Lumshe idanuwan ta daga kallon sa da take yi
Shiko sun kuyowa yayi daf da fuskarta yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta
Yatsan sa ya dawo dashi yana zagaye tausasan lips ɗinta wanda Hakan ke ƙara sa tana shiga wani yanayi
Kissing ɗinta ya fara Ahankali yana bin duk wani sassan jikin ta
Gaba ɗaya jin ta take yi a wata duniya da bazata iya fasalta irin ta ba
Haka ya cigaba da sarrafa ta bata masan sanda ta shiga duniyar bacci ba
Shi ko Hakan ya bashi damar aiwata muradin zuciyar sa
Sai wuraren ƙarfe uku ta farka, yana kwance kusa da ita ya zuba mata ido
"habibty!
Ya faɗa cikin shauƙin ƙaunarta
Ɗago da kanta tayi tana kallon sa ba tare da ta amsa ba
"habibty ina sonki ina ƙaunar ki"
Murmushi tayi idanuwan su na cigaba da sarƙewa da juna
"Nima Ina son ka Aasim"
Ya rungume ta tsam a jikinsa
"ki faɗi,duk abunda kike so, nayi miki alƙawarin zanyi miki shi a take batare da ɓata loka ci ba"
Murmushi ta kuma yi
"babu"
Ya ɗago ta yana kuma kallon fuskarta
"mu cigaba da rayuwa a haka dan Allah habibty"
Gyaɗa mai kai tayi
"shi kenan"
Washegari
Bayan ta fito daga wanka tana zaune tana shafa
Bayan tagama ta ɗauko doguwar riga ta saka tana zage zip ɗin
Ji tayi zip ɗin ya kuma zagewa, ta kuma zagewa still ya kuma
Juya wa tayi dan tasan shine
Aiko shi ɗin ta gani ya harɗe hannayesa yana murmushi
Ta maida mai martanin murmushin tana cewa
"nifa bana son tsokana"
Ya matso gab da ita yana mai-maita abunda tafaɗa
"nifa bana son tsokana"
Dariya tayi dan yadda yayi maganar shi a dole ya kwai-kwaye ta
"ka ganka ko? To me ya faru na ganka da rana haka"
Wani zobe yaciro yana nuna mata
"wallahi kin gansa nan, nazo wucewa ta wata kasuwa nagansa naga ze yi miki kyau a hannun ki shine na siyo miki"
Murmushi tayi tana duba siririn zoben zinarin
"wow gaskiya yayi kyau kamar kasan kuwa ina son siririn zobe"
Ya kama yatsanta yana zura mata zoben
"yaza'ai bazan san abunda matata take so ba?
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar ta
"na gode, abban Shahida"
"shhhhh"
Yayi yana ɗaura Yatsan sa akan bakin ta
"kar in ƙara jin kalmar godiya abakinki, dan babu ita a tsakanin mu"
Sallamar da aka yi a falon ce tasa ya sumbace ta a goshi
"kije kunyi baƙuwa,sai mun haɗu anjima"
Gyaɗa kai tayi tana murmushi
Ya ɓace ƙara zage zip ɗin tayi ta fito falon
Anty ummi ce
"zama tayi kan kujera cike da nisha ɗi tana duban Anty ummin
"kune da rana haka?
Anty ummi kallon ta tayi tace
" eh me ya faru a gidan ne?
Cikin rashin fahimta Rauda tace
"bangane ba"
"gani nayi kina ta farin ciki"
Anty ummi ta faɗa
Dariya Rauda tayi tana girgiza kai
"to babu abunda ya faru kinsan wata ran zakiji ki cikin annashuwa"
Anty ummi ta jinjina kai tana kallon zoben hannun ta
"wannan zoben fa, kamar zinari, ina kika samoshi?
Rauda ta girgiza kai tace
" a'a ba zinari bane, ɓarawon zinari ne, a makarantar mu wata take saida wa dubu ɗaya to tunda na siya ma ban taɓa sawa ba sai yau"
Anty ummi ta jinjina kai
"aiko kamar zinari wallahi,zan baki kuɗi idan kun koma
Kisiyomin, ina mama?
" ta shiga gidan maman murja anyi haihuwa"
Anty ummi ta miƙe
"dama hanif zanɗauko a makaranta nace bari in biyo, kince zakizo har yanzu baki zo ba"
Rauda ta miƙe itama tana yafa ɗan kwalin ta dan ta rakata
"kinsan banji daɗi ba kwana biyu amma zan zo jibi in Allah ya kai mu"
Anty ummi tace
"shi kenan in maman ta dawo ki gaishe ta"
Washe gari suna zaune a tsakar gida gabaɗayan su suna gyara masarar da baba ya kawo
Suna cikin gyaran aisha ta shigo yarinyar umma da ƙaramin akwati a hannun ta idanuwan nan nata sun yi jawur da alamu kuka taci
Tana shigowa umma tace
"me zan gani Aisha, yau ma ya jin kikayo"
Aisha ta tsugunna tana fashewa da kuka
"umma ni wallahi na gaji,Ace kullum nasiru sai yayi waya da ƴammata"
Umma maka ta kai mata cike da harzuƙa
"ubanki kenan, nace ubanki kenan Aisha, dan yayi waya da ƴammata shine abun yaji?
Mazan yanzu ba haƙuri ake yi da su ba, ina farin ciki hankalina ya kwanta na gama aurar da ku shine kike kike so ki tattago naki auran?
Ga wasu nan auran ma ya gagare su suna neman mazan ruwa a jallo basu samu ba"
Inna ta jinjina kai tace
"ƙwarai kuwa jummai, a zamaninnan in ka samu ka aurar da ƴaƴanka ai ka gama hajji da ummara"
Umma tace
"faɗa mata dai, wata ma sau biyu ana fasa auran ta kuma babu wanda ya ƙara shinshinar ta, sai ke da Allah ya tarfa ma garin ki nono ya rufa miki asiri kikayi auran zaki rinƙayin yaji
Maza tashi ki ɓace min da gani in ba kinaso in rufe ki da duka ba, sakarya kawai"
Mama Miƙewa tayi ta shige ɗaki dan tasan da ita suke yada haibaicin
Rauda ma Miƙewa tayi tabi bayan maman
A zaune tasa meta ta zuba uban ta gumi
Ta zauna gefen ta tace
"mama dan Allah kada abunda suka faɗa ya ɓata miki rai"
Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jingina da kujerar
"dole ya dameni Rauda, kullum fatana Allah ya kawo miki miji kiyi aure amma har yanzu shuru, yanzu ankai matakin da babu me sallama wa yace yana kiranki
Addu'a nike, maganin nike nemar miki amma shuru"
Ta Ƙarasa maganar cike da tsananin damuwa
Jikin Rauda yayi sanyi sosai, tausayin mama take ji, anya wannan rayuwar da tekeyi a ɓoye da Aasim tayi wa kanta da mama adalci kuwa?
Ya zamar mata dole ta yi masa magana dan ta samu mafita
Dan tasan yana da hannu wajen ɗaukewar mane manta
Guntun numfashi ta sauke
Tace
"komai lokaci ne mama, kuma komai yayi farko yana da ƙarshe ki kwantar da hankalinki ai da banyi auran ba ba a zaune nike ba, karatu nikeyi"
Mama ta girgiza kai
"aure ai mutuncin ƴa mace ne, hankali na zefi kwanciya idan Naga kinyi auran kina cigaba da karatun"
Rauda tayi shuru kawai tana ƙara yin nazari
Allah Allah take yi dare yayi
A gaggauce tagama ayyukan da zata taya mama dan ranar itace da girki
Ƙarfe goma mama tayi mata sallama taja mata ƙofar da yike hadari ya taso sosai
Tana fita Aasim na bayyana a ɗakin
Cikin sauri Rauda tace
"yauwa dama yanzu nike shirin kiranka"
Kama hannun ta yayi yana ƙoƙarin janyo ta jikinsa
Ta dakatar dashi
"a'a Aasim, magana nike so muyi dan Allah"
Ganin yana yin fuskarta yasa ya gane da gaske take yi
Hakan yasa ya zauna a kan kujera itama ta zauna
"maganar me kike so muyi habibty?
Ta gyara zaman ta tana fuskantar sa
" ina so muyi wata muhimmi yar magana, kuma dan Allah inaso ka fahimce ni, ka kuma yarda da abunda zan faɗa ma"
Ya kaɗa kai
"to insha Allah ina jinki"
Ta sauke numfashi sannan ta fara cewa
"a gaskiya babu abunda nike so sama da kwanciyar hankalin mama, kuma hankalin ta baze kwanta ba har sai taga nayi aure sannan...........
Katseta yayi
" sannan me? Faɗamin kawai me kike so kice"
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu
"ina so kadena korar min mane mana kabar su su cigaba da zuwa....
" sannan me?
Ya tambaya cikin tsare gida da ɗaure fuska
"sannan kabarni inyi aure........
" dakata dakata Rauda, kin san me kike cewa kuwa?
Ya faɗa cikin ɓacin rai
Jinjina kai tayi tace
"na sani Aasim, kuma kai ma ka san baze yuwu In cigaba da zama a haka ba, idan ni nasan ina tare da kai ai mutane basu sani ba.......
"kinga kima dakatar da waɗannan shirmamman maganganun naki"
Yafa ɗa yana kauda kansa
"magan ganun nawa ne shirme?
Ya jinjina kai yace
"eh shirmammu ne mana, ina so ki sani bazan taɓa barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba, dan haka ki ma cire maganar aure a rayuwarki duk wani abun da ɗan adam zeyi miki nayi alƙawarin zanyi miki ninkin shi"
Kallon sa kawai take yi yadda ya tamke fuska kamar be taɓa dariya ba
Durƙusawa tayi a gaban sa idanuwan ta suka cicciko
"Aasim dan Allah na roƙeka,Hakan shine kwanciyar hankalin mama, ka riga da ka san a yanzu babu wanda nike so sama da kai, kuma bawai ina nufin kabar ni in yi aure dan inyi nisa da kai bane, a'a...
"kinga Rauda idan kinji abunda nafaɗamiki to, idan kuma baki ji ba bari in sake nanata miki
Bazan taɓa barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba"
Runtse idanuwan ta tayi wasu siraran hawaye na gangarowa
"kenan haka kake so incigaba da rayuwa?
Ɓacewa yayi ransa a ɓace batare da ya ƙara ce mata komai ba
Ita ko Rauda fashewa tayi da kuka cike da tsananin damuwa
Haka ta kwana bata runtsa ba
Sai da suka yi kwana biyu be kuma zuwa inda take ba,bata damu ba dan haushin sa take ji sosai dan ta fahimci ba zasu daidaita dashi ba dan baze yuwu ta cigaba da rayuwa mutane suna yada Mata habai ci ba
Rana na ukun tana tsaye a ɗaki tana ninke kayan da ta kwaso akan igiya
Ɗagowar da zata yi suka haɗa ido
Maida kanta tayi kamar Bata gansa ba cigaba dayin abunda take yi
Hakan ya sosa masa rai amma sai ya danne ya ƙara so tare da rungume ta ta baya
"habibty fushi kike yi dani?
Janye jikin ta tayi tana kallon sa
" dan Allah ka rabu dani,ka ƙyaleni"
Ta faɗa cikin dakiya
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa gab da ita
"shi kenan Naji nayi miki laifi, amma kiyi haƙuri"
"nayi"
Tafaɗa tana cigaba da ninke kayan
Cikin damuwa yace
"miye haka Rauda,? Nine fa?
Ta ɗaga ta watsa mai fararen idanuwan ta
"to inkaine sai mene Aasim? Me kake so ince maka? Tunda ka kasa fahimtata"
Ya girgiza kai yace
"ba haka bane, dan Allah ki saurareni, ranar ma raina ne ya ɓaci, kinsan ina ƙaunar ki, kishin ki da sonki ne suka hanani fahimtar ki a ranar"
Ta ajiye kayan tana faɗin
"shi kenan ina sauraron ka"
"amma ai ba atsaye zamuyi maganar ba ko?
Ta zauna bakin gado batare da ta sake magana ba
Ajiyar zuciya ya sauke yana zauna wa a kusa da ita
"to dan Allah ki saki ranki kinji? Ba na son ganin ki a yana yin ɓacin rai"
Ta sassauta ɗaurin da tayi ma fuskarta tana duban sa kawai
Gauron numfashi ya sauke yana kama hannun ta
"kinsan irin son da nike miki ba zaki taɓa neman wani abu agurina ban miki ba, amma gaskiya kamar yadda na faɗa miki bazan iya barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba sai dai ina da wata mafita guda ɗaya"
Ta kallesa sosai
"mafita? To wace kalar mafita? Faɗi inji"
Ya gyara zama yana kuma fuskantar ta
"kinga ƙarfin da nike dashi idan na bayyana ga mutane da yawa ba zasu iya ganina ba
Ƙarfin da nike dashi mutum biyar ne zasu iya ganina,
To akwai wani kogo da ake zuwa a ƙasar Iraq inda wani tsohon rauhani yike
Idan rauhan yayi training awurinsa na tsawon watanni ƙarfin sa ze ƙaru ta yadda ze iya bayyana a bainar mutane da yawa
Kinga idan nayi sai inbayyana a gidan ku a matsayin mutum in kuma auranki kinga shi kenan baki da wata damuwa"
Kallon sa tayi da mamaki
"da gaske ana yin Hakan?
Ya jin jina kai
" da gaske, dan haka ina ganin jibi zantafi"
Jinjina kai tayi da sauri dan dama burinta be wuce ta rayu dashi ba, kuma tunda ga hanyar da babu wanda ze gane ai shi kenan
"dama ka san da wannan hanyar shine bakayi ba tun tuni?
" yanzu ai zanyi dole na"
Ya faɗa
Kama ɗayan hannun sa tayi cike farin ciki
"dan Allah ka tafi yanzu, wallahi ina son ka da kai kaɗai nike so nayi rayuwa a yanzu"
Murmushi yayi
"kwantar da hankalinki, jibi in Allah ya kai mu zan tafi,sai dai innata fi babu wata hanya da zata sa damu har sai na gama watannin da zanyi"
Kaɗa kai tayi tace
"to miye abun damuwa? In ka dawo ba shi kenan ba"
Ya jinjina kai
"shi kenan, yanzu hankalinki ya kwanta ko?
Ta ɗaga kai tana murmushi
Bayan kwana biyu suna tsaye suna sallama dan ranar ze tafi
" habibty dan Allah ki kula da kanki,na ajiye miki kuɗi a cikin akwatinki duk abunda zaki buƙata kiyi dasu,inda zan shiga bani da damar koda ganin ki ta madubi dan haka ki kula min da kanki"
Jinjina kai tayi tana ɗan murmushi
"baka da matsala, zan kiyaye insha Allah, kaima ka kula da kanka sosai"
Ya sumbace ta a goshi
"shi kenan ni zan wuce"
"Allah ya kiyaye hanya ta faɗa"
Ya ɓace, zama tayi zuciyar ta cike da kewarsa da ƙaunar ta
Bayan sati ɗaya lokacin komawarta makaranta yayi
Dan haka ta gama shirin ta tsaf, motar rana zata bi
Mama nasiha ta mata sosai akan ta cigaba da tsare mutuncin ta
Baba da kanshi ya kai ta tasha
Sai da yaga motar su ta tashi sannan ya tafi
Ita ko Rauda kallon gefen hanya take tayi zuciyar ta cike da tunanin Aasim
Ƙarfe biyar ta sauka a bakin makaranta
Inda Salma ke tsaye tana jiran ta dan ta riga ta dawowa
Tana ganin ta suka rungume juna cike da kewar juna, salmar ce ta ɗauki akwatinta tana tambayar ya hanya
"lafiya lau"
Ta bata amsa suna tsallakawa
Wata rantsattsiyar mota ce ta shanyo kwana a guje
Salma ta Ƙarasa tsallakawa da gudu yayin da takalmin Rauda ya turguɗe
Kafin tayi wani yunƙuri tuni motar ta bugeta
Faɗuwa tayi tana ambaton sunan Allah tare da tashi da sauri tana kallon motar
Ganin motar ta tsaya yasa ta duba ƙafarta inda take jin zafi da alamu anan ne taji ciwon
Wanda yike tuƙa motar ya fito hankalinsa a tashe
Fari ne tas, dogo kyakkyawan gaske
Da hanzari ya isa gabanta
Ganin ta durƙusa tana duba ƙafarta yasa shima ya durƙusa yana faɗin
"sannu baiwar Allah, kinji ciwo haka? Tashi mu tafi asibiti wallahi bada niyya ta na buge ki ba, saurin da nike yi ne"
Ƙirjinta ne ya fara bugawa yayin da taji tausassar muryarsa
"dan Allah tashi inkaiki asibiti, kinga jini na zuba a ƙafarki"
Gabanta ne ya sake faɗuwa,ƙarfin hali ɗagowa tayi ta kallesa suka haɗa ido
Atare gabansu yayi mummunan faɗuwa
Kallon-kallo kawai suke yi
Shine ya katse ɗauke wutar da suka yi ta hanyar kiran sunan ta
*"Rauda"*
Ƙirjinta ne yaci gaba da bugawa, zuciyar ta ta fara harbawa da sauri
Ganin wanda bata taɓa sa ran zata gansa a duniya ba
Har zata amsa sai magan-ganunsa na baya suka dawo mata
_"kada ki ƙara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taɓa sanina ba a duniya, ki gogeni daga rayuwarki"_
Nan da nan ɓacin ran shekarun da suka wuce ya dawo mata sabo fil
Miƙewa tayi tana jin raɗaɗin dake ƙafarta ya tafi sakamakon tuno wa da maganar sa da tayi
shi ko jikinsa na rawa ya kuma kiran sunan ta
"Rauda ba zaki amsa min ba?
Wani kallo tamasa tare da haɗe fuskarta
"ba sunana Rauda ba"
Tana gama faɗar haka tayi gaba
Yayi saurin shan gabanta
"Haba Rauda, nasan kece ki tsaya inkai ki asibiti"
Ranta ya soma ɓaci
"nace maka ni ba sunana Rauda ba, ka tafi ka ƙyaleni"
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ 🧕🏻
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 1⃣9⃣
_Wannan Page nakune masoya ƴarfillo, haƙiƙa ina jin daɗin yadda kuke yaba labarina a koda yaushe, nayi kuma matuƙar mamakin yadda labarina ya samu karɓuwa a gurinku, babu abunda zance muku face godiya Allah ya bar zumunci_
*_Aishatu babayo_*
_ina jinjina miki a koda yaushe,ina kuma godiya da kulawar ki gareni_
*_fatan alkhairi_*
_ga babbar aminiyata da babu kamar ta, *Aisha a Ibrahim* marubuci yar hilwana_
_11:34_🕒AM
TUE,JUN 11
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Ze kuma yin magana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu
"malan ka bani hanya in wuce? Taimakon kai ni asibiti ne bana so ko ana yima mutum dole ne?
Mama kine ya kama sa sosai kallon ta kawai yike yi
" wai shin Rauda ko baki gane ni bane? Umar ne fa"
"Umar?
Ta mai-maita sunan tana kaɗa kai
"Kaga Malan ni bansan ka ba"
Kafin ya kuma wata magana tuni ta ratse ta gefen sa ta wuce
Binta yayi da kallo yana tambayar kansa to wai ko ba ita bace ne? Ko gizo idanuwan sa suke masa
Binta Salma tayi da sauri tana kiran sunan ta
"Rauda kinfaji ciwo sosai, ya kamata ki tsaya muje asibiti a dubaki"
Rauda ko waigo wa bata yi ba taci gaba da tafiya
Kira ta da Rauda da Salma tayi ya tabbatar mishi da itace
Har ze bisu cikin makaranta
Wayar sa ta fara ƙara
Ya zaro ta daga aljihu, ganin me kiran yasa yayi saurin ɗagawa tare da karawa a kunnen sa
"doctor Umar mutanen nanfa suna cikin wani hali suna gab da rasa rayukansu dan Allah ka hanzarta"
Be ce komai ba ya kashe wayar yana ƙara kallon get ɗin makarantar ganin sun shige yasa ya koma motar sa
Tare da tada wa ya jata a guje
Amma gaba ɗaya hankalinsa ya rabu biyu
Ita ko Rauda ba ta tsaya ba har sai da ta isa ɗakin su tana shiga ta wurgar da ƙaramar jakar dake hannun ta tare da zubewa a ƙasa tana mai da numfashi sama-sama
Gaba ɗaya ganin sa ya hautsina mata hankali gami da daburta zuciyar ta
Salma ce ta shigo ɗakin ganin halin da take ciki yasa tace
"Rauda kita shi mutafi asibiti"
Rauda ta girgiza kai alamar a'a
Salma ta durƙusa tana duba ƙafar Raudan da har lokacin take zubar da jini
"bangane a'a ba, kina ganin yadda jini ke zuba, ga kuma numfashin da kike yi sama-sama"
Rauda ta kuma girgiza kai a karo na biyu
"nace miki baza ni ba, ki ƙyaleni dan Allah"
Salma ta kaɗa kai tana miƙewa
"aiko bazan ƙyale ki ba, tunda ba zaki tashi mutafi asibitin ba bari na kira sadiya ƴar medicine tazo ta dubaki"
Rauda jingina tayi da bango tana ƙara sauke numfashi
Ƙarfe shida da kwata ya isa Abuja
A harabar tamfatsetsen asibitin yayi parking
A gaggauce ya shiga office ɗinsa ya sanya kayan aiki
Tare da fitowa inda sauran likitocin suke
Basu ɓata lokaci ba suka emergency room inda Majin yatan suke
Basu suka fito ba sai. Sai Ƙarfe tara
Office ɗinsa ya koma ya yi wanka sannan ya zauna akan kujera tare da miƙar da ƙafafunsa ya jingina su da zagayayyen tebur ɗin dake gabansa
Jingina yayi da kujerar zuciyarsa na hango masa fuskarta
Maganar ta ce kawai take yi masa yawo a kunne
_"Kaga Malan ni ban san ka ba"_
Ya Lumshe idanuwan sa yana tambayar zuciyar sa
"anya kuwa Raudar da ya sani ce kuwa?
Dan ya tabbata inda itace bazata yi masa haka ba
Zuciyar sa ta kuma hasko Masa ita a lokacin da ta ɗago fareren idanuwan ta ta kallesa
Mamaki haɗe da fargaba da kuma tashin hankali ya gani a cikin idanuwan ta
To idan ba ita bace me yasa zata yi masa wannan kallon?
Ya kuma tambayar kansa
Numfashi ya sauke yana Miƙewa tare da ɗaukar makullin motar sa
"ko ma dai yaya ne gobe zankoma katsinan in tabbatar"
Ya faɗa yana ficewa daga cikin office ɗin
Washegari
Rauda na zaune riƙe da plate ɗin abinci tana jujjuya cokalin dake hannun ta
Dan gaba ɗaya ba ta jin cin abincin hakanan take tsintar kanta da faɗuwar gaba a duk sanda ta tuna sa
_"kada ki ƙara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taɓa sanina ba a duniya, ki goge ni daga rayuwarki"_
Maganar sa ta kuma yi mata yawo a kunne
Aje plate ɗin tayi tana jijjiga kanta
"meyasa Nike yin tunaninsa? Meyasa?
Ta faɗa cikin yana yin damuwa
Salma kallon ta tayi sosai tace
"Rauda, wai me ke damunki ne wai?
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu tana kallon salma da idanuwan ta da suka canza launi
"babu komai"
Salma ta girgiza kai tace
"a'a da akwai komi fa, tun jiya yana yinki ya canza, wai shin ma waye ne wannan na jiyan da ya bugeki"
ta zame daga gefen gadon tana Lumshe ido
"waye kuwa Salma, a gabanki fa na fara ganin sa"
"to amma Meyasa tunda kika gansa yana yin ki ya canza?
Ada nayi tunanin ciwon da kika jini, sai da Naga ana wanke miki ciwon naga ko a jikin ki hankalinki da tunanin ki ma basa gurin gabaɗaya
Hakan ya tabbatar min da ba ciwon da kika ji bane"
Ta buɗe idanuwan ta da suka kaɗa suka yi ja saboda ɓacin ran da ta shiga sakamakon zafafan magan ganunsa da suka kasa dena yi mata yawo a kunne
"Salma dan Allah bana son Magana a halin yanzu"
Salma ta tana kaɗa tace
"shikenan"
Wunin ranar haka Rauda tayi shi cikin rashin wal-wala
Shi ma Umar haka ta kasance gareshi ko abincin kirki ya kasa ci Allah Allah yike gari ya waye ya tafi Katsina
Washegari da wuri ya tashi ya shirya ya ɗauki jakar sa wacce ya sa kaya kala biyu a ciki ya fito falo
A kan dining ya tadda Anty kaltum tana haɗa abun kari
Ya gaishe ta ta amsa tana kallon jakar hannun sa
"yadai na ganka da jaka"
Ya gyara ratayar da yayi wa jakar yana cewa
"tafiya zanyi zuwa Katsina"
"Katsina kuma? Ince shekaran jiya ka dawo daga katsinar? Me zaka je kayi kuma?
Ta tambaya tana kallon sa
" wani abu ne ze kaini, amma bazan wuce kwana biyu ba zan dawo insha allah"
Sanin sa baya son yawan tambaya yasa ta jinjina kai
"shikenan Allah ya tsare"
"amin"
Ya faɗa tare da juyawa ya nufi hanyar fita
Har ya kusa kaiwa ƙofa ta dakatar dashi ta hanyar cewa
"to bazaka tsaya ka karya ba?
Ya girgiza kai yana cigaba da tafiya
" no Anty bana jin yunwa"
Bata ƙara cemai komai ba ta bisa da kallo
A harabar gidan ya buɗe haɗaɗɗiyar motar sa ya shiga ya tada
Me gadi ya buɗe masa get yana gaishe sa
Ɗaga masa hannu kawai yayi ya figi motar a guje
Ɓangaren Rauda kuwa ta samu ɗan sassauci dan har ta shirya dan zuwa duba sakamakon jarabawar su da ya fito a ranar
Tare da Salma suka fito suna tafiya suna fira jefi-jefi har suka isa wurin
Kamar yadda wurin ya saba da cika maƙil da ɗalubai a duk sanda sakamakon ya fito
Haka yauma, dan ko wani ɗalubi burinsa yaga abunda yaci
Rauda tsayawa tayi daga baya kaɗan tana na zartar yana yin wurin yayin da Salma ta kutsa cikin ɗaluban
Rauda na tsaye har Salma ta dubo nata ta fito tana mai da numfashi
Ganin Raudar a tsaye a inda ta barta yasa tace
"ha'a baki duba ba?
Rauda ta ɗaga kai
" kema kinsan bazan iya shiga cikin dandazo nan ba, ya kiga na ki?
Salma tace
"ba laifi, bari na dubo miki"
Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin dandazon
Daga ƙasa ta fara duba na Rauda kamar ko da yaushe
Sai dai ba ta gani ba, Hakan yasa taɗaga kai sama tana dubawa
Numban jarabawar Rauda ta fara gani a farko ta ɗan ware idanu tana sake dubawa
Numban raudan ce kuwa, wani irin farin ciki ne ya lulluɓeta ta daka tsalle tana ihun murna
Tare da fitowa daga cikin dandazon
Tana ƙan-ƙame Rauda cikin tsananin farin ciki
Rauda riƙe ta tayi da sauri jin tana niyyar faɗuwa
"miye haka, Salma kada ki kadani mana"
Rauda ta ɗago tace.
"ƙawa result ɗinki first class, da first class Kika fito"
Rauda zaro ido tayi cikin mamaki
"first class? Bana son zolaya Salma please faɗamin me ki kagani"
Salma tace
"wallahi Rauda first class"
Rauda ta girgiza kai tana faɗin
"banyadda ba, bari in duba da kaina"
Ta Ƙarasa faɗa tana kutsawa
Tayi matuƙar mamaki ganin first class ɗin kuwa
Wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya
Fitowa tayi fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki, dan har wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta
Salma ta riƙe mata hannu tana dariyar jin daɗi
"yanzu kin yarda ƙawa?
Rauda ta jinjina kai kawai dan ta ma kasa magana
Salma ta cigaba da cewa
" kinga zauna a wurin bishiyar can ki jirani inje in haɗo mana drinks dan munana farin cikin mu"
Tana gama faɗa ta juya a guje ta nufi wurin da ake sai da drinks
Rauda ta Ƙarasa gurin bishiyar ta zauna Aasim ne ya faɗo mata
Tare da maganar da ya faɗa mata a rana ta farko da ya fara koya mata karatu
_"Rauda ina tabbatar miki da cewa zaki iya, kuma jarabawa me zuwa da first class Zaki fito Abu ɗaya nike so dake ki mai da hankali akan abunda zan rinƙa koya miki"_
Guntun murmushi tayi tana furta sunan sa a hankali
"Aasim nayi rashin ka sosai,zan so ace kana tare dani ayau nasan sai ka fini farin ciki"
Dai-dai lokacin Umar ya shigo cikin makarantar wuri ya samu yayi parking yana kallon ɗaluban da ke kai da komowa
"ta ina zan fara neman ta?
Ya tambayi kansa yana sauke ajiyar zuciya
wayar sa ya ɗauka tare da buɗe marfin motar
Tunda ya zuro da ƙafafunsa ƴammatan dake zaune suna tattauna wa akan saka makon jarabawar su suke kallon sa
Sai da yaɗan ɗauki wasu sakwanni yana nazarin wurin dan ta cikin glass ɗin motar yana hango yadda ƴammatan suka zuba masa ido suna jiran suga fitowarsa
Guntun tsaki ya ja dan shi a rayuwar sa ya tsani kallo
Ya Ƙarasa fitowa da jikinsa tare da dafa marfin motar
"wow"
Wasu daga cikin ƴammatan suka faɗa ya yinda wasu daga cikin su suka saki baki suna kallon sa
Haɗe fuskar sa yayi sosai yayi kamar be san da wasu a wurin ba
Hange-hangen inda ze hango ta kawai yike yi amma bega ko alamar ta ba
Ya ja Guntun tsaki
"to wai ta ina zan fara ne manta ne?
Ya faɗa a fili yana ci gaba da hange hangen
Wata daga cikin ƴammatan ta taso ta ƙaraso inda yike tana yauƙi wai dan ko zata ja hankalin sa
Ko kallon ta beyi ba, bare yasan ma wace kala ce
"yallaɓai akwai wanda kake ne mana?
Ta faɗa cikin karya murya
Kallon ta yayi a fusace yace
" idan da akwai wanda nike nema miye ya shafe ki? Miye ya ruwan ki? Ko akwai abunda ya dameki dani ne"
Ya faɗa cikin ɓacin rai
Tsaye kawai budurwar tayi dan gaba ɗaya kunya ta gama lulluɓeta ganin yadda ya yarfa ta cikin jama'a
Zuciyarsa ce ta ɗan lallashe
"fushi ba naka bane, kai da kake so ka nemo ta, kuma ai dole sai da tambaya zaka gano inda take"
Numfashi ya sauke ya juya sosai yana fuskantar budurwar tare da zare glass ɗin idanun sa
"I'm sorry, I'm sorry na ɗaga miki murya"
Ya ɗan numfasa yana ci gaba da cewa
"ina neman wata ne me suna Rauda"
Ƙarfin hali budurwar tayi dan ganin kyawawan idanuwan sa sun ƙara rikita ta
A ɗan daburce tace
"a wani department take?
Girgiza kai yayi yace
"no bansan department ɗinta ba"
Budurwar tace
"masu suna Rauda suna da yawa a makarantar nan, gano ta batare da sanin department ɗinta ba, zeyi wuya gaskiya amma miye sunan mahaifin ta?
Kuma ya kamannin ta suke? Dan akwai wata dana sani a department ɗin mu"
Gyara tsayuwar sa yayi yana so ya tuna sunan mahaifin ta
_"Cikakken suna na shine Rauda isma'il"_
Ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa maganar ta
"yauwa sunan ta Rauda isma'il,bata da jiki,kyakkyawa ce me fararen idanu"
Ya faɗa cikin sauri
Girgiza kai budurwar tayi
"gaskiya ba ita bace dan wannan sunan ta Rauda mannir kuma ita tana da jiki"
"ook bayan ita fa? Baki san wata ba?
Ya tambaya a ƙagarance
ɗaga kai tayi alamar eh
Ajiyar zuciya ya sauke yana kaɗa kai
" shikenan nagode "
Juya wa budurwar tayi da sauri tabar wurin
Shiko jingina da motar yayi cikin da muwa
Haka yayi ta tambayar mutane amma duk wanda ya tambaya sai yace be san ta ba
Rauda na zaune taji gaban ta na faɗuwa
Kamar ance ta waiga ta hango sa yana tambayar wasu
Gabanta ne yayi wani mugun faɗuwa
Tayi saurin ɗauke kanta tana dafa ƙirjinta dake bugawa da sauri
Shi ko Umar juyawa yayi da niyyar komawa mota dan ya fara gajiya
Karaf suka ci karo da Salma
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓesa
Cikin jin daɗin ganin ta yace
"yauwa alhamdulillah Allah na gode maka"
Rauda tayi saurin Miƙewa tana girgiza ma salma kai
Dayike ita take fuskantar inda take yayin da Umar ya juya mata baya
Salma ta kalli Rauda ta dan bata gane abunda take nufi ba amma sai ta mai da kallon ta ga Umar tana cewa
"bawan Allah lafiya?
" dan Allah ki nuna min inda Rauda take, ina son in yi magana da ita ne please "
Ƙara kallon Rauda tayi har lokacin girgiza mata kai take yi
"OK ɗan jirani bari in kai saƙon nan indawo"
Gyaɗa kai yayi yana bin bayan ta da kallo
Karaf suka haɗa ido da Rauda da ke shirin barin wurin
Cikin sauri ya Ƙarasa gurin bishiyar yana yi mata sallama dan kafin Salma ta Ƙarasa tuni ya riga ta Ƙarasa wa
Tattaro dauriyar ta tayi duk da faɗuwar da gaban ta keyi ta dake
Tare da yin banza da shi
"Rauda ko ba komai kya amsa min sallama aiko?
Ɗagowa tayi ta watsa masa wani kallo me cike da ma'anoni da yawa
"ok wa alaikumussalam"
Ya yi murmushi yana cewa
"nafi awa ɗaya ina neman ki, duk wanda na tambaya sai su ce basu sanki ba....
"nemana kuma? Akan me kake nema na? Lafiya?
Ta tambaya tana kafe sa da ido
Ya sauke numfashi yana gyara tsayuwar sa
" kinga Rauda dan Allah kiyi haƙuri, ki tsaya ki saurare ni ki sauko daga fushinnan please"
Itama ta gyara tsayuwar tata tana fuskantar sa sosai
"nifa bawan Allah bangane abunda kake nufi ba wani fushi?
Duka-duka inace yau ne haɗuwar mu ta biyu
Ta ɗan daka ta sannan ta kaɗa kai tana ci gaba da cewa
" ohh na tuna wai na bugeni da kayi? Ai babu komai nasan tsau tsayi ne, sai anjima"
Ta Ƙarasa faɗa tana niyyar wuce sa
Tare ta yayi da sauri ta hanyar shan Gabanta
"wai me kike yi ne haka ne? Me yasa kike nuna kamar baki sanni ba?
Ta harɗe hannayen ta a ƙirjinta tana ƙara kallon sa
"da alamu dai kayi ma kuwa ne, dan ni Banta taɓa ganin ka ba face ranar da ka bugeni"
Mamaki ne ya ƙara ka masa
Ya zuba mata ido kawai
zuciyarsa na cigaba da harbawa, wata kalar sabuwar ƙaunar tace ta fara bi masa jinin jikinsa
"Rauda nasan nayi kuskure a baya amma dan Allah kada kiyi min irin wannan hukuncin na nuna baki sanni ba..........
" daka ta bawan Allah, na gaya maka bansan ka, ban san ka ba, kaje Kane mi Raudar da ka sani dan Allah ka ƙyaleni"
Tana gama faɗar haka tabar wurin dan ji tayi zuciyar ta ta fara karye wa
Jingina da bishiyar yayi yana bin ta da kallo kawai
Numban zayyad ya kira babban amininsa bugu ɗaya ya ɗauka
"zayyad kana ina ne?
Daga can Ɓangaren zayyad yace
" gani zanje Katsina, mama ta aikeni kai kana ina ne?
Ya sauke ajiyar zuciya yace
"Nima Ina katsinan"
"kana Katsina? Yaushe kaje baka faɗa min ba"
Numfashi ya kuma sauke wa yace
"zayyad ina cikin damuwa ka hanzarta kazo dan Allah"
Zayyad yace
"ook ok ganinan zuwa, amma ka kwantar da hankalinka dan Allah, a Ina zan same ka?
Sunan hotel ɗin da ya sauka ya faɗa mishi, sannan ya kashe wayar ya koma motar sa
Tunda ta koma ɗaki take kuka wanda bata san taka mai-mai na menene ba, tana yi ne kawai dan ta samu sassauci a cikin zuciyar ta wacce take yi mata suya
Salma kallon ta kawai take yi tana mamakin irin wannan al'amari
Ƙarfe biyar zayyad ya isa hotel ɗin Numban ɗakin ya tambaya a ka nuna masa
Ya ƙwan-ƙwansa ƙofar
Umar na kwance kan gado ya Lumshe idanuwan sa jin ana ƙwan-ƙwansa ƙofar yasa ya miƙe
Ji yayi kansa ya sara, ya dafa kan yana cigaba da tafiya ya buɗe ƙofar
Zayyad kallon sa yayi sosai ganin yana yin sa ya tabbatar mai da yana cikin damuwan
Zama suka yi kan kujerar dake ɗakin zayyad na tambayar sa
"wai me yake faruwa ne umar? Me ke damunka?
Kwashe komai umar yayi ya faɗa masa
Zayyad yayi murmushi yana cewa
"to miye na damuwa anan? ince Rauda ce yarinyar da baka so Meyasa zaka dami kanka dan kawai tace bata sanka ba?
Umar ya sauke doguwar ajiyar zuciya yace
" zayyad bazaka gane ba, wallahi a yanzu zuciya ta ta kamu da tsananin ƙaunar ta, tun ranar dana haɗu da ita Naji naka sa sukuni"
Zayyad ya kuma yin murmushi
"aini wallahi Rauda tayi min dai-dai da ta nuna bata ma taɓa sanin ka ba
Yarin yar nan tasha wulaƙanci a wurin ka, dan kawai Kaga Tana mutuwar sonka kai ta wulaƙantata ni kaina ta sha kirana tana kuka akan abubuwan da kake mata
Har ta gaji, sai yanzu ne zaka zo kace wai kana son ta?
Ni wallahi dama nasan wannan ce damuwar taka dan ban tada hankali na nayi ta gudu akan hanya ba"
Hannun sa umar ya kama ya na marai-raice fuska
"zayyad tabbas nasan nayi kuskure a baya amma yanzu wallahi ina son ta, ka taimake ni muje tare da kai ka bata ha ƙuri nasan tana ganin girman ka"
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 2⃣0⃣
_Wannan Page na sa daukar da shi ga kan kaina,nawa ne ni kaɗai🤥_
*_fatan alkhairi_*
_Gareka yayana Abdullahi ɗan Fulani nagode da kulawar ka gareni da Allah ya ƙara dan ƙon zumunci a tsakanin mu_
*_Gaisuwa da fatan alkhairi_*
_Ga ansholly group ina muku fatan alkhairi musamman *meenah wayer* ina ganin yadda kike tambayar littafina a koda yaushe ina godiya sosai, *Hadiza tunau* ina jinjina miki Allah ya ƙara basira a cigaba da suburbuɗo mana me cetona😍_
_Ban manta da ku ba *matan ƙwarai* group kuma Allah ya bar zumunci_
_12:00_🕒AM
Wed, JUN 19
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Zayyad ya zame hannun sa yana faɗin
"wa? rufamin asiri inje inbata haƙuri ta saurare ka ka kuma wulaƙan tata? Ai wallahi babu ruwana"
Umar ya kuma marai-raice fuska
"Zayyad wallahi ina son ta,ka taimaka muje dan Allah wallahi tun safe ba abunda nasa ma cikina.....
Kallon sa Zayyad yike yi galala
"wai duk saboda Raudar ka kasa cin abinci?
Umar ya Gyaɗa kai
Murmushi Zayyad ya kuma yi yace
"to Naji zan yi tunani kafin goben, dan nasan ka nasan wannan shegen miskilancin halin naka"
Umar be ƙara cewa komai ba, har Zayyad ya tashi ya je ya siyo abinci ya ajiye ledar a gaban sa
"ka tashi muci abinci"
Umar girgiza kai yayi
"kaci kawai ni bana jin yunwa"
Dariya Zayyad yayi sosai
"ka san Allah Umar bana wani jin tausayin ka, wallahi dariya ma kake bani,dubi yadda ka wani marai-raice akan yarinyar da ka furta da bakinka baka son ta, baka ra'ayinta"
Dariya ya cigaba da yi ya zauna kan kujerar yana cigaba da cewa
"wallahi Rauda kinyi dai-dai Allah ya sa ma gobe ko mun je ta kuma nuna bata san ka ba"
Umar ta gumi ya zuba yana kallon Zayyad
"yanzu Zayyad dan kaganni cikin damuwa shine kake wannan dariyar har kana faɗin baka jin tausayi na?
Anya kai aminin kirki ne kuwa?
Zayyad ya kuma darawa
"to me kake so ince?
OK yi haƙuri, gaskiya kabani tausayi sosai jima nike yi kamar inyi ma kuka"
Ya faɗa cikin tsokana
Umar Miƙewa yayi yana jan tsaki ya bar mai ɗakin
Wurin da aka tana da dan shaƙatawa a hotel ɗin can ya nufa
Ya zauna ya tsurawa swimming pool ɗin dake wurin ido
Gaba ɗaya zuciyar sa ta cun kushe da tunanin ta
Salma ga jiya da jin kukan tayi tace
"wai ni Rauda na kasa gane miki wallahi, kin zauna kina ta kuka daga ganin mutumi,
Na tambaye ki waye shi kince baki san shi ba yakike so inyi da raina ne? Wallahi kukan nan naki ɗaga min hankali yike yi"
Rauda tayi ƙoƙorin tsai da kukan ta amma ta kasa dan da ta tuno sa sai taji wani dunƙulen abu ya to kare mata ƙirji
Kukanne kaɗai yike sa ta samu sassauci
"Salma kiyi haƙuri, baki san abunda nike ji bane, nayi alƙawarin zan faɗa miki amma ba a yanzu ba, dan yanzu ina buƙatar natsuwa ne"
Salma ta sauke ajiyar zuciya tace
"shikenan ubangiji ya yaye miki, amma ki rage sa kanki cikin wannan muguwar damuwar"
Kaɗa Mata kai kawai tayi alamar taji, amma Saman zuciyar ta ji take yi kamar an ɗaura mata wani abu me nawi
Tambayar kanta kawai take yi wacce ta rasa bawa kanta amsa
"me yasa dan nagansa hankalina ze tashi haka? Shin ko har yanzu ƙaunar sa bata fita acikin zuciya ta bane?
Girgiza kai tayi da sauri tana sa hannu ta bubbuga kanta
Dan gani take yi kamar ƙwa-ƙwalwarta na so ta bijiro mata da abunda ya wuce
"Rauda ki natsu, kin riga da kin cire sa aranki,tsayin lokaci,ki cigaba da man tawa da shi kamar yadda ya umarce ki a baya
Kada ki manta da alƙawarin da kika ɗaukar ma kanki na ko zaki mutu baza ki ƙara ne mansa ba"
Ta faɗa a fili, sannan ta share fuskar ta Tana ƙoƙarin sai-sai ta natsuwar ta
Tausayin ta Salma taji sosai, dan sai lokacin ta gane abunda take nufi
*Kogon iraq*
(bari mu wai-wayi Aasim)
Zaune yike cikin ƙan-ƙara tsananin sanyi na shiga jikinsa
Wani hayaƙin sanyi ne ke fita a duk yayin da ya buɗe bakin sa
Sunfi su arba'in a wurin
Kallo ɗaya zaka ma sauran rauhanan ka gano tsantsar gajiya da damuwa a tare da su
Domin suna matuƙar shan wuya a training ɗin
Banda Aasim da shi sam babu wannan alamar gajiyar a tare da shi
Abul simnan shine shugaban wurin
Tsohone tukuf fari sol me dogon gemu, dan gemun sa har jan ƙasa yike yi
Yana zaune kan kujerar sa ya na karantar yana yin rauhanan
Turawa yayi aka kira masa Aasim
Aasim ya durƙusa yana gaishe sa
Amsawa Abul simnan yayi yana ƙara karantar yana yin sa
"yaro wani abu ne ya tsaya min a rai ya sa na kira ka, gani nayi gaba ɗaya rauhanan da suke training sun nuna gajiya warsu da ƙosawar su
Amma kai Kwata-kwata banga Hakan a tare da kai ba, dan wani zubin ma hango ka nike yi kana murmushi"
Murmushi Aasim yayi yana cewa
"tabbas abunda kafaɗa gaskiya ne, Sam ajikina bana jin gajiya wa,ƙosawa ta ɗaya ce ingama inje inyi abunda nazo domin sa"
Jinjina kai Abul simnan yayi
"tabbas ba ƙaramar ƙauna kake yi wa bil'adamar can ba, tunda har ka iya rabuwa da ahalinka da matsayin ka na ɗan babban sarki, ka kuma zo kana shan wahala dan kawai ka cigaba da rayuwa da ita
Amma kana ganin ba kayi kuskure ba kuwa? Da ka bata yarda ɗari bisa ɗari?
Murmushi Aasim ya kuma yi yana girgiza kai
"ko kaɗan banjin nayi kuskure, domin yadda nike son ta, haka ita ma take sona"
Abu simnan yayi ɗan murmushi
"to shikenan Allah yasa Hakan, amma nasan halin mutane lokaci ɗaya zasu nuna son abu lokaci ɗaya kuma zasu nuna ba sa so, ina yi maka fatan nasara a rayuwar ka"
Miƙewa yayi ya koma cikin ƙan-ƙarar yana jujjuya maganar abu simnan
Maganar tace ta faɗo masa
_"Aasim ina son ka dan Allah mu cigaba da rayuwa a haka"_
Murmushi yayi yana faɗin
"nasan ba zaki taɓa juya min baya ba Rauda, ina tsananin rashin ki Allah yasa kina kula min da kanki"
Ya faɗa cikin tsananin begen ta
*** *** ***
Da sassafe Umar ya tashi ya shirya cikin manyan kaya, wani ya din malesia ne me silɓi kalar navy blue
Yayi kyau sosai ya taje sumar sa tare da fesa turare
Ya ɗauko hula ya saka yana maƙala tsadaddan agogo a hannunsa
_"Jaana idan kasa manyan kaya kana yin kyau, ganin ka nike yi kamar ango"_
Maganar ta tabaya ta dawo masa
Murmushi yayi yana kallon kansa a madubi
Inda ya bayyana na ainihinsa na halfcas
"na sane dan na burge ki Rauda Allah yasa ki saurare ni yau"
Ya faɗa yana komawa bakin gadon yana tashin Zayyad dake ta sharar baccin sa
Zayyad buɗe ido yayi yana miƙa
"wai miye ne ka takuramin ka hanani inyi bacci ne?
Umar yace
" ka ta shi mana mu tafi makarantar su Rauda"
Kallon agogo Zayyad yayi ƙarfe bakwai saura
"me zamuje muyi da sassafe haka? Kabari gari ya waye sosai mana"
Umar ya ce
"ai dama ba yanzu zamu tafi ba, kata shi dai ka shirya dan nasan wannan daɗewar da kake yi a wanka kamar me canza fata"
Zayyad Miƙewa yayi yana faɗin
"Allah ka cika ta kura umar, sai kaje ka haɗo mana abin kari ai kafin in fito"
Umar zama yayi yana duba agogon hannun sa
_Umar dan Kaga ina son ka shiya sa kake wulaƙan Tani ko? Ka sani cewa bani na ɗaura wa kaina ba, Allah ne ya ɗaura min"_
Maganar ta tabaya ta kuma yi masa yawo a kunne
Dafa kansa yayi cikin damuwa yana jin haushin kansa
"Meyasa nayi mata haka ne? Me yasa?
Ya faɗa cikin jin ta kai cin abunda yayi mata
Dogon tsaki yaja
Cike da Nadama
Ƙarfe goma da rabi ta fito daga lecture
Dai dai lokacin Umar suka yi parking
Suka fito suka tsaya jikin motar
Tun daga nesa suka hango juna wanda sai da ƙirjinsu ya amsa su duka biyun
Kamar ta juya ta koma sai kuma wata zuciyar tace ta cigaba da tafiya kawai
Tunda ga nesa yike kallon ta,tafiya take yi a natse kamar tana jin tsoron taka ƙasa
Komai nata daban ne, wani numfashi ya sauke tare da ajiyar zuciya
Domin be taɓa sanin haka Allah yayi mata kyau ba
Zayyad ko burgesa tayi ganin yadda ta ɗauke kanta kamar Bata gansu ba
Ta kuma haɗe fuskarta, har ta iso inda suke tana niyyar wucewa
Zayyad ne ya tare ta yana yi mata sallama
Ta amsa, tana neman ya bata hanya
"Rauda dan Allah ki tsaya ki saurare mu, mun san munyi kuskure amma kiyi wa girman Allah da soyayyar da kike yi wa annabi Muhammadu(s.a.w)"
"sallallahu alaihi was salam"
Ta faɗa tare da tsayawa
"to bawan Allah ina jin ka na tsaya ne ba dan niyya ba sai dan kira fiyayyen halitta da kayi"
Zayyad ya jinjina kai yace
"nagode sosai, amma me ze hana muɗan sami wuri mu zauna, saboda mu tattauna abunda ya kawo mu a tsana ke?
Girgiza kai tayi tace
" a'a nan ma ya isa,ina jinka"
Zayyad yace
"ok to shikenan,dama akan maganar Umar ne, ya ce min kin ƙi kula sa kina ce mai baki san shi ba, Rauda nasan Umar me laifi ne a wurin ki amma dan Allah kiyi haƙuri....
Dafa kanta tayi cikin damuwa tana kallon Umar da ya zuba mata ido
" oh Allah na,bawan Allah wai ba kaji abunda nafaɗa ma jiya bane? Nace ma ban san ka ba"
Ta mai da kallon ta ga Zayyad tana cewa
"bawan Allah idan baya jin hausa sosai ne kafaɗa masa yadda ze Fahimta bansan sa ba"
Zayyad yayi murmushi
"Rauda nasan zafin zuciya ne yasa kike faɗan haka, yanzu Nima zaki ce baki sanni ba?
Ta ɗaga kai
" eh kaima ban san ka ba, ina ga dai me kama da ni kuka sani amma bani bace gaskiya"
Ta juya gurin Umar tana ci gaba da cewa
"amma ita wacce kuka sanin miye cikakken sunan ta?
Gaba ɗaya kan shi ya ɗaure ganin irin kallon da take masa
" Rauda isma'il"
Ya faɗa cikin rashin sanin abun yi
"gashi sunan mu yazo ɗaya, amma shin ka taɓa haɗuwa da ita ne a baya?
Ya girgiza kai alamar a'a
Ta gyara tsayuwarta tana cigaba da kallon sa
" to a ina ka Santa kenan? Tunda baka taɓa haɗuwa da ita ba?
Cikin damuwa yace
"Rauda sau nawa zan baki haƙuri ne? Idan ma haƙurin da na baki beyi miki bari indurƙusa in baki amma kidena nuna min bake bace please"
Ya Ƙarasa faɗa yana niyyar durƙusawar
Dakatar dashi tayi da sauri
"ni bance ka dur ƙusa min ba, kadai bani amsar abunda na tambaye ka"
Gauron numfashi ya sauke yana kaɗa kai
"shikenan a waya na Santa"
"Ashe?
Ta tambaya tana buɗe idanuwan ta sosai
" kenan hotuna ta tura maka, ta kuma faɗa maka sunan ta Rauda isma'il
Shin baka tunanin tayi amfani da hotunan da ba nata ba, ta kuma yi maka ƙaryar suna?
Cikin tsananin damuwa da ƙosawa da yadda take masa yace
" idan tayi min ƙaryar suna da kuma hotuna ai bazata aro fuskar ki tasa ba, kinga Rauda kidena wani kwana-kwana ke ce domin har video call mun sha yi dake"
Taɓe baki tayi tace
"to ni dai ban san ka ba, nafaɗa kuma zan sake faɗa, dan Allah kada ka sake biyo ni inda nike, kaje ka nemi wacce ka sani amma bani Raudan ba Dan ni ko me kama da kai ban sani ba bare kuma kai"
Haƙiƙa maganganun ta sunyi masa ciwo amma sai ya danne
Zayyad yace
"Rauda ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana bare tsakanin mu ƴan adam........
Bata jira jin me ze gama cewa ba tayi gaba
Umar ze bita zayyad ya dakatar dashi
"Umar shiga mota mu tafi ko kabita bazata saurare ka ba, kuma Kaga hankalin mutane ya fara dawowa kanmu"
Be ce komai ba ya buɗe motar ya shiga, zayyad ya mara masa baya yana tada motar
Lumshe idanuwan sa yayi kawai yana jin kansa na sa rawa
"zayyad kafaɗamin yadda zanyi in shawo kanta, wallahi ina jin zuciya ta tana min nawi, ina sonta zayyad"
Zayyad ya ɗan kallesa sannan ya maida kallon sa ga titi
Tabbas a yanzu ya yadda Umar da gaske yi ke yi yana sonta, ganin duk irin zafin sa amma yana niyyar durƙusa mata
Amma Sam shi bega laifin ta ba, dan Umar ya cancan ci hukuncin da ya wuce haka ma a wurin ta
Guntun numfashi ya sauke yace
"kai ma Umar ka san ba ka kyauta mata ba,abunda da yawa maza ba su gane ba shine
A memakon su nuna kulawar su ga matan da suka nuna suna sonsu
Sai su yi amfani da wannan damar su dinga wulaƙanta mace, bayan sun mance cewa ita mace kunya gareta
Amma ta danne wannan kunyar ta nuna tana sonsu,
Wace magana ce ban gaya maka ba a wancan lokacin Umar?
Har roƙonka nayi akan ka sassauta jan ajin da kake mata
A gabana sai ta yi maka kira fin ashirin
Amma ka ɗauka ne kake ganin asara, kuma idan ka ɗaukan ma a daƙile kake yi mata magana
Idan taji baka da lafiya nikaina sai tamin kira fin goma tana tambayar ya jikin ka
Amma kai sau nawa tana faɗa ma tana gadon asibiti amma ka iya kira ko sau ɗaya ne kace mata ya jiki ba kayi
Umar maganar gaskiya ka wulaƙanta tata, dole ma tayi ma haka wallahi"
Umar ya runtse idon sa zuciyar sa cike da takaicin kansa
"zayyad dan Allah ka dena tuna min abunda ya wuce nasan ni me kuskure ne ka faɗa min yadda zanyi kawai"
Zayyad ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"ka cigaba da zuwa kana bata haƙuri insha Allah zata sauko"
Rauda na shiga ɗaki tafaɗa kan katifa tana maida numfashi dan zahiri ba ƙaramar dauriya tayi ba
Gaba ɗaya hankalin ta ya tashi,haƙiƙa ƙaunar sa ne ma take yi ta dawo mata
Ta rasa irin sa,ba ƙaramar wahala tasha ba wajen ya kice sa a zuciyar ta
Amma gashi yazo yana so ya burki ta mata lissafi
Tabbas ta san yadda taso Umar, babu wani mahaluki a duniya da za taso kamar yadda ta sosa
Tasha yin kuka,kasa barci akan ƙaunar sa kai har rashin lafiya
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta yayin da ta tuno wahalar da tasha a kan ƙaunar sa
"me yasa Umar? Me yasa kamin haka? Me yasa baka zo a sanda nike buƙatar ka ba sai bayan na cire ka a zuciyata?
Ta faɗa a fili tana share hawayen dake biyo kwarmin idanun ta
Dafa ƙirjinta tayi tana jingina da filo
"dan Allah zuciya ta kada ki dawo min da ƙaunar shi,ki ci gaba da manta wa da shi"
Ta faɗa cikin karyewar zuciya
Bayan sati ɗaya
Umar ya fita hayyacin sa sosai dan babu ranar da baze je makarantar su Rauda ba
Amma still nuna take yi bata Sansa ba, wani zubin ma ko saurarar sa bata tsaya wa yi
Ya Rame sosai, dan ko abincin kirki baya iya ci
Zayyad tun baya jin tausayin sa har ya fara bashi tausayi
Kamar kullum yana tsaye inda ya saba tsayawa
Ta fito zata je ɗaukar darasi
Daga nesa ta hango sa ya jingina da jikin mota
Gaban ta ne ya faɗi yayin da taga yadda ya Rame acikin ƴan kwana ki
Dauriya tayi ta cigaba da tafiya har tazo wuce wa ta inda yike
"Rauda!
Ya kira sunan ta cikin wani irin yana yi
Yadda ya kira sunan tan yasa taji jikin ta yayi sanyi
Ji tayi bazata iya wuce sa ba
Ta tsaya kawai batare da ta juya inda yike ba
Zagayo wa yayi Gabanta ya zuba mata kyawawan idanuwan sa
" Rauda ya kamata ki tausaya min, ki sassauta min haka, wallahi ko barci bana iya yi,Rauda ina ƙaunar ki a yanzu fiye da yadda kike tunani........
Ɗaga masa hannu tayi idanuwan ta na ciccikowa da hawaye
"na roƙeka ka fita da ga rayuwa ta kadena zuwa inda nike, dan Allah"
Umar ya kaɗa idanuwan sa da suka yi ja
Tare da cize lips ɗinsa
"ina sonki Rauda bazan iya rayuwa babu ke ba, dan girman Allah ki yafemin abunda nayi miki"
Ya Ƙarasa faɗa ya na durƙusawa bisa gwiwowin sa Be damu da jama'ar dake kallon sa ba
Ji tayi kuka na so ya ci ƙarfin ta,da sauri tabar wurin tana dafa ƙirjinta da yike yi mata suya
Can ƙarshen aji ta zauna ta kifa kanta tana kuka
Salma ta dafa ta dan a idon ta komai ya faru
"Rauda dan Allah ki sassauta masa haka, wallahi ya galabaita kuma kema fa har yanzu kina son sa"
Rauda ta ɗago jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon salma
"Salma ya zanyi da raina? Ki faɗamin ji nikeyi kamar zuciya ta zata fashe"
Salma sauke numfashi tace
"haƙuri zaki yi ki yafe masa, tunda ya amsa yayi kuskure"
_kada ki ƙara kirana ko nemana kisa aranki cewa baki taɓa sanina ba ki gogeni daga rayuwar ki_
Girgiza kai tayi da sauri yayin da zafafan kalaman sa suka sake yi mata yawo a kunne
"bazan iya ba Salma, bazan iya ba idan nayi haka ban kyauta wa kaina ba, shi da bakin sa yace in goge sa daga rayuwa ta, nayi kuma abunda yace Meyasa yanzu ze dawo gareni Meyasa?
Ta Ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka
Salma ta sauke numfashi tana cewa
" shikenan ya isa haka kukan, kinga lecturer ya shigo"
Share hawayen ta tayi tana kallon lecturen da ya fara darasi
Gaba ɗaya babu abunda take fahimta,dan kanta ya cushe
Tunda ya koma mota yike jin zuciyar sa na ƙuna tuƙi kawai yike yi batare da yana kallon hanya sosai ba
Gaba ɗaya ya rikice, jijiyoyin kansa sunyi burɗum-burɗum
Sakamakon tsananin ciwo da kansa keyi,
Ya zeyi mata ta fahimci ƙaunar da yike mata?
Ya zeyi ya goge laifin sa a gareta?
Tambayoyin da yayi ma kansa kenan wanda ya rasa amsar su
Runtse ido yayi cike da tsananin damuwa
Ƙarar horn yaji daf dashi
Ya buɗe idanuwan sa da sauri wata ƙatuwar mota ya gani gab da shi
Ya juya sitiyari da sauri dan ya kauce mata
Sai dai duk da haka Be tsira ba dan wata ƙatuwar bishiya ya daka
Ya yin da motar ta dawo baya ta daki jikin waccan motar
Ta kuma yo gaba ta tuntsura
*** *** ****
Tsattsaye suke sunyi layi gaban wani kogo
Wanda yike fitar da turi ri acikin sa
Abul simnan ne tsaye a gaban su inda yike yi musu jawabi
"kamar yadda muka gama da horon ƙan-ƙara yanzu zamu shiga kogon marzaj
Kogone dake ɗauke da tsumi wanda dashi ne zan haɗa muku bayyana acikin jama'a
Sai dai kusani kafin kuje inda tsumin yike akwai wasu baƙaƙen ifiritai wanda suke da sarauniyar su guda
Sanin kanku ne kamar yadda muke da ƙarfi haka suma ifiritai suke da shi
Dan haka sai kun dage dan idan ba kuyi da gaske ba, za ku iya rasa rayukan ku
Dan haka sai kun kula da kyau, kun kuma dage
Da zarar kun isa wurin wannan tsumin kuyi gaggawar ɗiba sannan kuyi gaggawar fitowa
Amsawa suka yi da to
Wasu daga ciki farga ba ne maƙil acikin ransu, yayin da shi Aasim Sam baya jin wata fargaba
Dan Abul simnan na shiga shi ya fara mara mai baya
Tafiya suka yi sosai har sai da suka kusa gab da wurin
Sannan Abul simnan ya tsaya yace
"anan zan dakata inbarku ina yi muku fatan nasara, sannan kusani shan wannan tsumi agareku bawai bayyana acikin jama'a kaɗai ze muku ba
Harda ƙarfi me tsanani da ze ƙara muku"
Jin Hakan yasa suka ƙara himma tare da yin gaba
Aasim ne a gaba, tafiya suka ƙara yi me nisa sannan suka isa ƙofar wurin
Sai da suka tsaya sukai nazarin wurin sannan suka doshi ƙofar
Wasu manyan ifiritai ne suka bayyana wanda girman su ya wuce na misali sanye da wasu baƙaƙen kaya da manyan wuƙaƙe
Suka zaga ye su
Nan da nan suka kaure da faɗa
Sunyi kusan awa ɗaya suna gabzawa yayin da su Aasim suka jigata sosai
Dan har sunfara sarewa
Tunawa da Rauda da yayi da irin ƙaunar da yike mata yasa yaji wani sabon ƙarfi yazo mishi
Nan da nan ya miƙe daga zubewar da yayi ya shiga tsakiyar su yana kai musu sara ta ko ina
*** **** ****
Suna tashi daga lecture Takoma ɗaki ta kwanta
Wani kalan zazzaɓi me zafi ne ya rufe ta
Ga kanta da yike sarawa kamar ze rabe biyu sakamakon kukan da taci
Wani bacci me cike da damuwa ne ya ɗauke ta
Bata farka ba sai bayan kiran sallar asuba
Har lokacin ciwon kan Be sauka ba
Ta ɗauro alwala ta gaba tar da sallah sannan ta ɗaga hannu tana kai kukan ta ga ubangiji
Ƙarfe bakwai takwas ta gama shiryawa
Tana ɗaukar jakarta
Salma tace
"ba zaki tsaya ki karya ba?
Girgiza kai tayi tace
"banajin cin komai"
Tana gama faɗa ta sa takalmi ta wuce
Tunda ga nesa take kallon inda yike tsayawa duk safiya amma bata ga motar sa ba
Wani iri taji a zuciyar ta
Kenan ya gaji ya haƙura?
Daga can gefe ta hango Zayyad
Yanayin data gansa ya sa ta faɗuwar gaba dan hankalinsa a tashe yike
Yana ganin ta ya ƙaraso yana cewa
"tun ɗazu nike jiran fitowar ki, har da zan juya"
Bata kula sa ba ta cigaba da tafiya
Zayyad ya bi bayan ta da kallo yana faɗin
"Rauda kitsa ya ki saurareni Umar ne ya yi accident jiya a hanyar sa ta koma wa daga wurin ki"
Ƙirjinta ne yayi wani mugun bugawa ta juyo a razane tana duban Zayyad
"ac.. cident!! "
Ta faɗa cikin rawar murya
Zayyad ya jinjina kai idanuwan sa na ci kowa da ƙwalla.
"Rauda Umar ya na cikin wani ma wuya cin hali bani da tabbacin ze rayu ko baze rayu ba"
Ji tayi ƙafafunta sunfara rawa sun gaza ɗaukar ta
Tayi saurin dafa ƙarfen dake wurin tana faɗin
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku!!!
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 2⃣1⃣
_Wannan Page naki ne *safnah* kiyi yadda kike so dashi_
~_Ina da wata buƙata kutayani da addu'a Allah ya biya min,ya cika min burina please_~
_8:50_🕒PM
THU, JUN 20
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"Zayyad me ya sami Umar? Ka faɗamin wani hali yake ciki?
Tayi mai tambayar cikin rawar murya da tsananin tashin hankali
Zayyad yace
"baki ji me nace bane? Accident yayi kuma duk kece sanadi, dan da kin saurare sa da Be shiga damuwar da ze fita hayya cin sa ba"
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, ka kai ni asibitin da yike ka kaini in gansa dan Allah"
Ta faɗa tana runtse idanuwan ta da suka cicciko da hawaye masu zafin gaske
Be ƙara cewa komai ba ya buɗe mota ya shiga
Binsa tayi ta shiga jikin ta na tsuma zuciyar ta cike da tarin fargaba
Ya tada motar ya fige ta aguje
Idanuwan sa sun kaɗa sunyi ja
"duk mutumin da yayi maka laifi ya dawo yace ka yafe masa ai Be kamata kaƙi kula sa ba
Sanin kanki ne Umar ɗin da kika sani da, ba shi bane yanzu
Wani irin roƙo ne be yi miki ba? Wani irin haƙuri ne be baki ba? Amma duk kika nuna baki san yanayi ba?
Dafa kanta kawai tayi da yike cigaba da sarawa batare da ta ƙara tanka masa ba
Suna isa asibitin suka fito yayi gaba tana Binsa
Ƙofar emergency room ya murɗa ze buɗe
Wata nurse ta ƙara so wurin da sauri tana faɗin
"baiwar Allah kijira a fito dashi daga emergency room tukunna"
Zayyad ya kalli nurse ɗin yace
"baki ga tare dani take bane?
Sun kuyar da kai nurse ɗin tayi
"sorry doctor Naga doka ce ba a shi.....
Be jira jin me zata Ƙarasa cewa ba ya buɗe Ƙofar ya shige
Gabanta na faɗuwa ta kutsa kanta ciki
Kwance ta hango Jikinsa duk bandeji, jikin ta na rawa ta Ƙarasa gaban gadon zuciyar ta na wani irin rawa
"Umar!
Ta Kira sunan sa,ko motsi Be yi ba ballantana ya amsa mata, idanuwan sa na rufe ruf
Zuba masa ido tayi, gani take yi kamar baya numfashi
Cikin tashin hankali da kiɗima ta fara jijjigasa tana faɗin
"Umar ka tashi, ka tashi dan Allah, Naji na haƙura"
Har lokacin ko motsi beyi ba
Kuka ta fashe da shi tana cigaba da jijjigasa
"na roƙeka katashi, kada ka tafi ka barni Umar"
Maganar ta ya fara ji tana ratsa kunnuwan sa
Ji yike yi kamar mafarki yike yi
"katashi Umar, dan Allah katashi wallahi na haƙura"
Ta kuma faɗa
Buɗe idanuwan sa yayi da suka yi masa nawi
Dishi-dishi ya fara ganin ta
Kafin ya ganta sosai,ita ko ganin ya buɗe idon yasa ta sauke wani nannauyan numfashi
"Rauda"
Ya kira sunan ahankali
Kasa amsawa tayi kallon sa kawai take yi
"Rauda ina son ki, dan Allah ki ce min kin haƙura da abunda nayi miki, ki amsa kin yafe mini"
Zuciyar ta tsinke,janyo kujera tayi ta zauna jin jiri-jiri ya fara ɗiban ta
Ze kuma magana ta katse shi
"Umar,na haƙura ya riga da ya wuce"
Ya Lumshe idanunsa yana faɗin
"nagode"
Hannu tasa ta share fuskar ta da tayi sharkaf da hawaye
Sannan ta ƙara matsawa kusa dashi
Tana kiran sunan sa
Kuma buɗe idanuwan sa yayi ya zuba su a kanta
"kayi haƙuri da jefa ka damuwa da nayi...
Girgiza kai yayi a hankali
"a'a Rauda, sam kada ki bani haƙuri na cancan ci fiye da abunda ma kikai min"
Ya faɗa da rauninniyar muryarsa
Kaɗa kai tayi tana kuma share fuskarta gaba ɗaya jikin ta ya mutu.
Miƙewa tayi tace
"zanta fi,anjima zan dawo"
Ta Ƙarasa faɗa tana niyyar juyawa
Ruƙo hannun ta yayi,ta juyo suka zuba ma juna ido
"kar ki tafi Rauda dan Allah,ina buƙatar ganinki a kusa dani"
Ta sauke ajiyar zuciya tace
"kayi haƙuri Nima bana jin daɗi ne, anjima zan dawo"
Ya girgiza kai
"a'a ki tsaya Zayyad ya duba ki, ki tsaya tare dani please"
Hannun ta ta zame tana girgiza kan itama
"a'a akwai wacce zata duba ni"
Bata jira jin me ze ƙara cewa ba tayi gaba,tana tafiya jiri na kwasar ta
Zayyad ya tashi da sauri ya tare ƙofar
"bafa ze yuwu ki tafi cikin wannan halin ba, tunda dai har kinzo asibiti muje induba ki"
Zatai magana Zayyad ya dakatar da ita
"kada ki ce zaki yi musu Rauda, dan Allah"
Numfashi ta sauke tana kaɗa kai dan ta ƙagara ta zauna ji take yi kamar zata faɗi
Zayyad ya dubi Umar ya ce
"bari muje na duba ta yanzu zan dawo"
Umar binsu da ido yayi kawai
Suka fita, wani office suka shiga ya nuna mata kujera ta zauna
"dame-dame kike ji yana damunki?
" ciwon kai, sai jiri da kuma ƙirji"
Ya jinjina kai, sannan yayi mata gwaje-gwaje
Nurses ya kira yace suzo su sa mata drip,da kuma allurai
Dole ta haƙura suka sa mata dan tana buƙata ita ma
Ta Kira Salma ta faɗa mata,ba'a fi minti ashirin ba Salma ta zo asibitin
Da daddare,tana zaune kan gadon asibitin ta tsura ma drip ɗin ido, gani take yi baya sauri dan kaɗan-kaɗan yike ɗiga, Allah Allah take yi ya ƙare su tafi
Zayyad ya shigo ɗakin yana yi mata ya jiki
Amsawa tayi da "dasauƙi"
Sannan ta ce
"kaɗan ƙara gudun ruwan bana so dare yayi sosai ba mu tafi ba"
Zayyad yace
"ai bayan wannan ma akwai wasu,dole tafiyar ki sai ta kai gobe da yamma saboda da alamu kinyi ta ciwon a tsattsaye"
Salma tace
"gaskiya gwara kitsaya ki samu sauƙi Ƙawa,kiyi haƙuri zuwa goben"
"Hakan ya kamata,Shima Umar yanzu muka dawo dashi ɗakin dake jikin wannan"
Bata ƙara cewa komai ba ta kwanta,
Bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta
Ƙarfe ɗaya na dare ta farka,a gigice
Sakamakon mafarkin da tayi wai Umar ya rasu
Lokacin Salma ta daɗe da yin bacci,zare abun ruwan tayi ta sauko ta fito
Babu kowa a harabar wurin ta windon ɗakin da yike ta hango sa
Murɗa ƙofar ɗakin tayi ta shiga ta Ƙarasa gaban gadon
Gabanta na faɗuwa ta dafa ƙirjinsa jin yana numfashi yasa ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare zauna wa a kujerar dake gaban gadon
Ta tsura mai ido,kyakkyawar fuskar nan nasa tayi fayau, sai dogon hanci
"Umar!
Ta Kira sunan,da alamu bacci yike yi dan be amsa ba
Ta cigaba da kallon sa zuciyar ta na saƙo mata abubuwa da yawa
Tabbas ta san har yanzu tana ƙaunar sa, dan sonsa da banne acikin zuciyarta
Shine wanda ta fara so, kuma shi kaɗai ne wanda tayi ma so me tsanani
Gashi lokacin ta daɗe tana fatan zuwan sa na ranar da Umar ze ƙauna ce ta yazo, amma sai dai kash
Aasim,ya riga da ya danne komai, dan Shima tana sonsa amma bazata taɓa haɗa son da take yima Umar da wanda take yi masa ba
Umar ƙaunar sa daga Allah ne, dan shine ya jarabce ta
Hawaye masu ɗumi suka shiga gangaro mata
"Meyasa sai yanzu Umar? Me yasa kabari lokacin Dana daɗe ina jira ya wuce?
Meyasa?
Ta jingina bayan ta da kujerar tana runtse idanunta wasu sababbin hawayen na gangarowa
"kai ne burina, kai ne zaɓi na, kai ne wanda nayi fatan rayuwa dashi a matsayin miji na har abada, amma kabari lokaci ya wuce dan bazan iya janye alƙawarin da nayi wa Aasim ba, bazan iya ba!
Kuka me ƙarfi ne yaci ƙarfin ta, ta kifa kanta jikin gadon tana kuka me tsuma zuciya
Umar duk abunda ta faɗa yana ji, da fari farin ciki ne da jin daɗi ya mamaye zuciyar sa amma Aasim da ta ambata yasa jikin sa yayi sanyi
Waye shi? Wani irin alƙawari ta ɗaukar masa da take faɗin bazata iya karyawa ba?
Yayi wa kansa tambayoyin,da bayi da amsar su
Ita ko Rauda Miƙewa tayi ta koma, ɗakin da take
Ta kwanta,har lokacin ƙaunar sa ce ke kuma bin jinin ta
Ta dafa sai tin zuciyar ta da take yi mata nawi tace
"dan Allah kada ki bari ƙaunar Umar ta kuma tasiri a zuciyar ki, Aasim shine wanda ya cancan ce ki, shi ne ya sadaukar da rayuwar sa da komai nasa akan ki, Umar ko shine ya wulaƙanta ki a lokacin da kike neman kulawar sa"
*** **** ****
Sunɗauki awanni suna gabzawa da manyan ifiritan, yayin da wasu daga cikin rauhanan sun ji ciwo sosai suka kuma sare
Aasim ne kaɗai har lokacin yike fafatawa dasu,duk da Shima ya galabaitan
Sarauniyar ifiritai tana zaune kan kujerar ta tana kallon abunda yike faruwa
Sai da tagama kallo tsaf, sannan ta cewa ifiritan su dakata
Dakatawar suka yi kuwa, yayin da Aasim da sauran suka tsaya suna mai da numfashi
Gurin yayi tsit,Sarauniyar da har lokacin idanuwan ta na kan Aasim tace
"nadaɗe banga jarumi irin ka ba,sannan kuma na daɗe banga sakarai irin ka ba wanda yike sadaukar da rayuwar shi dan kawai ya rayu da bil'adama wannan babban kuskure ne"
Aasim Shima da tun da ta fara maganar yike kallon ta yace
"a gareni Sam ba kuskure bane,kuma a shirye nike da inshiga kasadar da tafi wannan in har yin Hakan ze ƙara min kusanci da ita"
Murmushi Sarauniyar tayi yayin da tagama duba madubin tsafin ta
"tabbas kayi kuskure me girma da ka amince da bil'adama,sannan kuma zaka yi da na sani domin kuwa duk wannan wahalhalun da kake sha zasu tashi a banza"
Ta ɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa
"kun aikata laifi dan kawai ku sami bayyana acikin mutane kuka shigo mana kogo kuka karya mana doka,amma duk da Hakan jarumtar da ka nuna zata sa inyi abunda bantaɓa yi ba
Wato inbada gudunmuwa wajen karya dokar da kakannina suka kafa, tabbas wannan tsumi dokace bama bari a ɗiba amma kuje na baku dama ku ɗiba iya wanda ze muku"
Wazirin ta ne ya zube yace
"ranki shi daɗe maƙiyanmu ne fa ko kin manta gabar dake tsakanin mu dasu ne?
Ta girgiza kai tace
" ban manta ba zundaj,amma kada ku ƙara taɓa su ku bar su su ɗiba"
Aasim murmushin jin daɗi yayi tare da rusunawa
"godiya muke sarauniya, Allah ya ƙara girma, haƙiƙa kina da taushin zuciya me cike da tausayi ubangiji ya shiga cikin lamarinki"
Jinjina kai kawai tayi tana nuna musu hanya
Suka wuce zuwa inda tsumin yike, tun da suka isa wurin Aasim ke murmushi
Ya shafa hannun sa wani ƙoƙo me Marfi ya bayyana yasa ya ɗiba
"Rauda yanzu zamu rayu ni dake cikin kwanciyar hankali batare da wata damuwa aranki ba"
Ya faɗa yana rufe ƙoƙon
Sai da suka gama ɗiba sannan suka juyo suka yi ma sarauniyar godiya
Har sun juya zasu wuce ta dakatar da su ta hanyar kiran Aasim
Waigowa yayi yana kallon ta batare da ya amsa ba
"aduk lokacin da danasani ya riske ka,ka kuma yi niyyar ɗaukar fansa kada ka manta wajen neman agajina"
Yayi murmushi yana jinjina kai
"nagode sosai amma nasan babu danasani a rayuwa ta"
Murmushi kawai tayi ta ɓace
Shiko futowa suka yi zuciyar sa nayi masa wani iri
Meyasa ake yi masa zancen yayi kuskure, shi dai yasan Rauda bazata juya mai baya ba, to shi ko wani danasani zeyi?
*** *** ****
Washegari da sassafe Salma ta koma makaranta dan akwai test ɗin da zata yi
Rauda na kwance ita kaɗai, Umar kasa haƙuri yayi ya taso ya shigo ɗakin
Ta yunƙura tana kallon sa ganin yadda ya shigo yana bin bango
"lafiya ka fito kai da kake kwance?
Zaunawa yayi yana mai da numfashi
"nakasa haƙuri ne Rauda, inaso in ganki shiyasa"
Kallon sa tayi sosai, sannan tace
"amma ai da ka aiko an kirani"
"kema baki da lafiyar ai"
Ya faɗa, ta girgiza kai
"amma ai ban kai ka jin jiki ba ko?
Ya jinjina kai
"ya jikinna ki? Yanzu dame-dame kike ji yana damunki?
"naji sauƙi babu abunda ke damu na yanzu,ya naka jikin?
" Nima Naji sauƙi alhamdulillah, me kike so a kawo miki ki karya?
Ya tambaya
Dai-dai lokacin Zayyad ya shigo ɗakin ganin Umar yasa yayi sororo yace
"kai kuma fa? me ya fito da kai?
Umar yace
"bansani ba, me Kaga inayi?
Zayyad ya Ƙarasa shigowa yana faɗin
"kana fama da kanka shi ne kake ƙoƙarin yin jinya?
Ya Ƙarasa faɗa yana ajiye abun kari
Rauda tace
"dan Allah kabarni in tafi yanzu tunda Naji sauƙi abar ragowar alluran haka"
Ta faɗa tana duban Zayyad
Zayyad ɗan murmushi yayi yace
"ki kwantar da hankalinki anjima kaɗan zaki wuce"
Bata ƙara cewa komai ba,ta ɗauki wayar ta da ke ƙara
"hello Salma kintaho ne?
Daga can Ɓangaren Salma tace
" wallahi Rauda na taho babu hanya, baki ga yadda matasa suke ta zanga-zanga ba da Manyan makamai "
Rauda tace
" subhanallah zanga-zanga kuma? Na mene?
"Nima bansani ba amma nasan baze wuce na siyasa ba, bari in koma dan Naga faɗa yana so ya kaure a wurin"
Rauda ajiye wayar tayi cikin damuwa
Da yamma tana tsaye tana kallon tvn dake manne jikin bango
Yadda faɗan ya kaure ake nunawa, ga sojoji nan ta ko ina
Nurse ce ta shigo
Rauda tace
"wai yanzu ko kaɗan babu hanyar da mutum ze bi ya koma inda yike"
Nurse ɗin tace
"wallahi babu, dan muma tun rana aikin mu ya ƙare amma waɗanda zasu amshemu basu zoba ga kuma Waɗan da aka ji ma ciwo ana ta kawo su"
Babu yadda Rauda ta iya dole ta ƙara kwana a asibitin
Washegari hanya ta buɗe ta koma
Bayan sati ɗaya Umar yaji sauƙi sai ɗan abunda ba'a rasa ba, yayin da garin hankali ya kasa kwanciya
Dan kullum cikin ƙone-ƙone suke da hayaniya
Hakan yasa dole makaranta ta bada hutun gaggawa dan abun harya fara shafan ɗalubai
Ba yadda Umar beyi ba akan Tabari su taho tare amma taƙi
Dan bata son suna kasancewa tare a yanzu so take yi ta nisance sa ko dan ta hani zuciyar ta
Bayan kwana uku da dawowarta,suna zaune tsakar gida ita da mama suna girkin dare
Wayar ta ce ke ta ƙara kuma taƙi ɗagawa dan numban Umar ne
Wani kiran ne ya kuma shigowa mama ta kalli wayar tace
"wai waye ne yike ta kiran ki ba zaki ɗaga ba?
Ta ɗauki wayar ta kashe tana ba mama amsa
"kamfanin mtn ne"
Dai-dai lokacin baba ya shigo, suka mai sannu da zuwa
Ya amsa yana duban Rauda
"kije kina da baƙo a waje"
"baƙo?
Ta tambaya a zuciyar ta amma a fili shuru tayi tana mamakin wani baƙo ne zezo wurin ta
Katse mata tunani baba yayi
"ko baki ji ba, nace kina da baƙo a waje"
Amsawa tayi da to, yayin da baba ya wuce
Mama tace
"baƙo kuma? Wanene?
Rauda tace
" Nima bansani ba mama, dan bamuyi da wani zezo ba, amma bari naje nagani "
Ta Ƙarasa faɗa tana Miƙewa
Dogon hijabi ta zura ta fito ƙofar gida
Ko da mamakin ta, Umar ta gani tsaye ya sha wata maroon ɗin Shadda
Tsaye tayi jikin ƙofa tana kallon sa yayi kyau sosai
Ƙarasa fitowa tayi tana mamakin yadda akai ya san gidan su
Shiko murmushi ya saki yana amsa gaisuwar da ta masa
Ganin har lokacin da mamaki a fuskar sa yasa yace
"ki dena mamaki dan kinganni a ƙofar a gidan ku, nabi kwatancan da kikamin ne na shekarun da suka wuce"
Gyara tsayuwarta tayi tana yi masa wani irin Kanno masu fassarori da yawa
Ta danne zuciyar ta tare da ɗan ɗaure fuskarta
"to ka kyauta, amma me ya kawo ka gidan mu? Kuma Ƙarasa wanda zaka aika ya kirani sai mahaifi na?
Murmushi ya kuma yi yace
"adoka ta musulunci idan zaka nemi yarinya ai sai ka fara tambayar izinin iyayen ta, kuma na tambayi baba ya bani izini innemeki"
Gajeren murmushi tayi wanda ya tsaya mata iya baki kawai wanda ya rasa gane ma'anar sa
"izinin nemana fa kace Umar? To wai ma in tambaye ka, wani neman da ga ciki?
Cikin rashin fahimta yace
"wani nemane kuwa banda na aure?
Murmushin ta kuma yi tana ɗan kaɗa kai
" Umar ke nan, akan mene zaka nemi izinin aurena batare da ka nemi soyayya ta ba?
Yana yin fuskar sa ya sauya zuwa damuwa
"Rauda, ina ce waɗannan abubuwan sun wuce, nasan fa kina sona har yanzu Meyasa zaki ta maida hannun agogo baya....
Katsesa tayi
"har yanzu ina son ka? A yaushe na faɗa ma haka?
"ki faɗa sau biyu, da rana ta farko da kika je asibiti, da kuma rana ta biyu da kika shigo ɗakin da daddare
Duk abunda kika faɗa inaji"
"yayi kyau da kaji Hakan, amma ka sani faɗin ina son ka bashi zesa na saurare ka har na kuma yin wata soyayyar da kai ba, Umar dan Allah ka nisanci rayuwa ta ka gogeni daga rayuwar ka na roƙeka kamar yadda ka roƙeni a baya"
Ta faɗa cikin damuwa zuciyar ta na harbawa
Idanuwan sa suka kaɗa
"Rauda wallahi ina ƙaunar ki,idan kika amince min a gobe zan iya turo iyayena ayi maganar aure dan ki tabbatar da da gaske nike, wallahi a yanzu banajin zan iya rayuwa babu ke kuma nasan kema kanki a yanzu kin fahimci Hakan"
"babu abunda na fahimta, kaje kanemi wata, dan yanzu ina da wanda nike so dan Allah karka ƙara zuwa inda nike"
Ze kuma yin magana ta shigo gida da sauri
Ɗaki ta shiga ta zauna kan kujera tare da kifa kanta wasu hawaye masu ciwo suna biyo kuncin ta
Mama ta shigo ɗakin dan taga wucewar ta
Zama tayi tana tambayar lafiya?
Share hawayen tayi tana faɗin babu komai
Mama ta girgiza kai tace
"bangane ba komai ba, hakanan zaki shigo kina kuka dan jin daɗi?
Waye ne wanda ya zo?
Wasu hawayen ne suka kuma gangarowa
" Umar ne"
Mama ta ce
"wani Umar?
Umar da kika sani na da, wanda ba mu taɓa haɗuwa ba
Mama ta ɗan buɗe ido da mamaki tace
"wannan na wayar me kama da Larabawa? To ya aka yi kuka haɗu har yazo nan ba kundena waya ba tun tuni?
Kwashe komai tayi ta faɗa mata
Mama tayi murmushi
" to miye abun damuwa har da kuka? Ince Umar shine wanda kike so,ban manta ba fa duk mazajen da kika tsaida da Allah beyi auran ba kin tsaida su ne kawai dan baki samesa ba, Nasha ganin ki kina kuka kuma nasan duk a kansa ne, to tunda yanzu Allah ya kawo sa ba sai ki ma Allah godiya ƙila shine alkhairin kuma mijin shiyasa duk Waɗan can da akasa ranar da su aka fasa kuma yanzu kin tabbata da gaske yike yi?
Rauda ta numfasa tace
"cewa yayi wai a gobe ze iya turo iyayen sa dan intabbatar da gaske yike yi"
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyar mama
"to ba shikenan ba, ai kin rama abunda ya miki kuma ya gane kuskurensa kawai ki kula sa ki kuma amince dan nasan maƙiya sai sun kusan mutuwa saboda baƙin ciki"
Kallon mama kawai take yi yadda lokaci ɗaya ta shiga farin ciki tabbas mama tayi gaskiya ƙila shine alkhairin shiyasa aka fasa da waɗancan amma Aasim fa?
Gabanta ne ya faɗi yayin da ta tuno sa
~ƴarfillo~.
[20/10, 8:41 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
🅿AGE 📕 2⃣2⃣
_Wannan Page nakane *ASLAM* _haƙiƙa ka kasance ɗan albarka wanda aduk sanda na tuna nike jin sanyi ko da ko ina cikin damuwa ne, ina son ka sosai yarona Allah ya albarkaci rayuwar ka_
*(nasan bestie zata ce yaro ko zuwa duniya beyi ba kin damemu da aslam aslam, to ki kwantar da hankalin ki duk da ban riga na haife sa ba amma ƙaunar sa na zuciya ta)*
_Ako da yaushe bana gajiya da yi muku fatan alkhairi masoyana Allah ya bar zumunci_
*_Sannan ina me baku haƙuri sakamakon daɗewa da nike yi banyi typing ba saboda ƙarancin lokaci, na yanke shawarar ringa yi akai-akai amma sai dai zaku rinƙa gani ba yawa nagode_*
_8:32_🕒AM
WED,JUL 3
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Haka ya cigaba da kasancewa Umar kullum sai yazo gidan su Rauda, gaba ɗaya ya ajiye aikin sa dan ya tattaro ya dawo Kaduna kuma yayi ɗamarar baze koma Abuja ba har sai ya shawo kanta
Kamar kullum yana tsaye jikin motar sa yana jiran yaga wuce war yaro ya aika ya kira ta dan yayi ta kiran wayar a kashe
Be kai ga samun yaron ba sai gata ta fito zata amso candle
Sam bata lura da shi ba dan wurin yayi duhu babu haske
Cikin sauri take tafiya aiko tayi tintiɓe da wani dutse
Ƴar ƙara ta saki tana duƙawa da sauri
Shiko Umar ji yayi kamar shi yayi tuntuɓen ƙarasowa yayi da sauri
"subhanallah sannu, baki ji ciwo ba?
Yayi mata tambayar, ɗago wa tayi dan sai lokacin ta lura dashi
Duk da duhun dake wurin be hana ta ganin kyakkyawar fuskar sa ba ma'abociyar haske da kwarjini
Ya tsugunna yana haska fitilar wayar sa
Ganin jini a ɗan yatsan ta yasa yaji wani yarrr
Handkerchief ɗin sa ya zaro da sauri yana ƙoƙarin goge mata
Miƙewa tayi idanuwan ta a kansa
Amma takasa ce mai komai dan duk sanda ta gansa jikin ta mutuwa yike yi
Shima ya miƙe yana faɗin
"muje chemist a duba ki"
Girgiza kai tayi cikin muryanta da tayi ƙasa tace
"a'a ai ba wani ciwo bane babba da sai anje chemist"
Yayi shuru yana kallon ta yana jin ƙaunar ta na wani irin fizgar sa
Ganin yayi shuru yasa ta gyara takalmin ta tana ƙoƙarin wucewa
"Rauda!
Ya kira ta da wani irin salo wanda saida tsigar jikin ta tashi
Tsayawa tayi tare da zuba masa fararen idanunta masu ƙara masa ƙaunar ta
Guntun numfashi ya sauke yace
" Rauda Allah ma da halicce mu muna yi Masa laifi mun roƙesa gafara ya kuma yafe mana, ballan tana imu-imu ƴan Adam
Kisani ko Abaya wallahi ina sonki, amma bansan me ya hanani zuwa wurin ki ba, wani zubin sai na ɗauki waya zan kira ki sai inji nakasa, kuma ko wulaƙancin da nayi miki Abaya ba da son raina bane
Da kin kirani zanji babu wacce nike jin haushi a duniya sai ke shiyasa nike gaya miki magan ganu marasa daɗi
Amma wallahi da na kashe, zanji nayi nadama abun kuma ze yi ta damuna
Kiyi haƙuri ki amince dani dan Allah"
Ya Ƙarasa faɗa muryar sa na raunanewa
Maganar Aasim ce ta faɗo mata
_"Kisani ƙaunar da nike miki bazata taɓa bari inbar wani ya raɓeki ba,ke tawa ce ni kaɗai"_
To Kodai yana da hannu wajen hana Umar zuwa a wancan lokacin?
Tayi wa kanta tambayar
Ji tayi kanta yayi mata nawi, ta Lumshe idon ta tana ambaton sunan Allah
Tafi minti biyu a haka daga bisani ta buɗe su ta kuma ɗaura su a kanta
Ya Rame sosai,kallo ɗaya zaka masa ka gano baya cikin kwanciyar hankali
Tausayin sa gami da ƙaunar sa suka sake mamaye zuciyar ta
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"shikenan zanyi tunani,amma ka rage tada hankalin ka"
Murmushi yayi yana jin zuciyar sa cikin farin ciki
"hankalina baze taɓa kwantawa ba har sai kin amince dani,na kuma gode, sannan zuwa yaushe ne zaki gama tunanin?
"nan da sati ɗaya"
Ta faɗa
Ya jinjina kai
"Allah ya kai mu Allah kuma yasa kiyi tunanin da zanji alkhairi"
Bata ƙara cewa komai ba, ta juya zata koma gida dan bazata iya Ƙarasa wa shagon ba
"dan Allah zan kiraki anjima ki ɗauka"
Shige wa tayi tana tunanin yadda zata ɓullowa al'amarin
Dole tana buƙatar wanda ze bata shawara amma wa zata gaya mawa sirrinta?
Anty ummi zuciyar ta tabata amsa
Ita ce ƴar uwar ta, wacce zasu kashe su rufe batare da wani ya sani ba
Washegari da wuri ta shirya ta tafi gidan Anty ummi
Da sallama ta shiga gidan, mijin ta ne ya amsa yana yaye labulen falon dan ya gama shiri ze tafi kasuwa
Ganin ta yasa ya faɗaɗa fuskar sa
"auta kece da safiya haka?
Murmushi tayi tana faɗin
" ina kwana?
"Lafiya lau ya bata amsa yana bata hanya"
Shiga tayi ta zauna kan kujera tana kallon Anty ummi dake sanyawa hanif jakar makaranta
"yaro na yakake?
Ta faɗa yayin da take maida kallon ta ga hanif
"lafiya Anty kin kawo min sweet?
Tayi murmushi tana girgiza kai
" a'a my hanif ina sauri ne shiyasa amma zan kawo maka next time kaji?
Gyaɗa kai yayi yana bin baban sa
Anty ummi tace
"ya mama? Ince dai lafiya dannasan bakya fita da sassafe haka"
Rauda tace
"lafiya lau"
Anty ummi ta janyo flask tana niyyar zuba ruwan zafi
Dakatar da ita Rauda tayi
"kinga inni zaki zuba mawa karma ki zuba dan bana jin yunwa, magana nazo muyi"
Anty ummi ta kalle ta sosai
"magana kuma?
Rauda ta jinjina kai
" eh"
Anty ummi ta ajiye kofin tana cewa
"to inajinki nasan baze wuce kuɗi kike so ba"
Rauda ta sauke numfashi
"a'a Sam ba maganar kuɗi bace, ina cikin damuwa ne kawai na kuma rasa yadda zanyi"
Jin kalmar damuwa yasa Anty ummi ta gyara zama tare da tattara hankalin ta guri ɗaya
"damuwa kuma Rauda? Faɗa min me ke faruwa"
Ita ta gyara zaman ta tace
"zan faɗa miki amma inaso ki natsu sosai ki fahimce ni"
Anty ummi ta jinjina kai alamar taji
Rauda bata ɓoye mata komai ba tun daga ranar da ta fara ganin Aasim har zuwa tafiyar sa
Wani irin kallo Anty ummi take yi mata na wacce ta fara taɓuwa
Rauda ta numfasa tare da ƙarawa da cewa
"ki dena min kallon wacce ta fara taɓuwa Anty ummi, wallahi da gaske ne, kiyarda da abunda na faɗa miki"
Anty ummi ta sauke doguwar ajiyar zuciya
"bawai banyadda da abunda kika faɗa bane, a'a na yarda dan jinnul aashique mun san kina dashi amma tabbas baki da hankali
Dan Inba marar hankali ba babu wacce zata yi abunda kika yi, ace kiyar da kirinƙa rayuwa da jinnu har ki amsa mai zaki rayu dashi har abada kuma ki ɓoye mana"
Rauda gwauron numfashi ta sauke tace
"nidai Anty ummi kiga ya min yadda zanyi bagashi yanzu na faɗa miki ba, ki gaya min ya zanyi da Umar,ina tsananin ƙaunar sa har yanzu amma idan natuna wulaƙancin da Yamin Abaya sai inji duk ya fita a raina"
"ke yanzu har ma kya ga laifin Umar,ai wallahi kidena ganin laifin sa dan bayi da laifi kwata-kwata bayin kansa bane"
Anty ummi ta faɗa zuciyar ta cike da jimami
Rauda tace
"to yanzu yakike ganin zanyi?
Numfasawa Anty ummi tayi tare da nisawa tsayin mintoci
Daga bisani tace
"aganina tunda shi Aasim ɗin bada mugunta yazo miki ba ki kula Umar ɗin kucigaba da soyayya
Idan ya dawo sai ki basa haƙuri kice ya bar ki auri Umar, shi kuma ya cigaba da rayuwa dake a ɓoye, ina ganin Hakan itace hanya me sauƙi tunda Shima yana sonki"
Rauda ta Lumshe idanuwan ta da suka kaɗa saboda damuwa tace
"da wuya ya yadda, dan yana sona fiye da yadda kike tunani"
Numfashi Anty ummi ta kuma sauke wa
"dolen shi ma ya yarda dan babu inda aka ce aljan da mutum suyi rayuwa, kina ganin Gorin da ake yi miki akan rashin aurannan dan haka kada ki bari Umar ya kubce miki
Idan ma be yadda ta sauƙi ba ai sai aje gurin malamai ya rabu dake ta tsiya
Rauda ta girgiza kai
"Anty ummi ba zaki gane ba, Aasim ba kamar wanda kike tunani bane, kuma wallahi inajin tausayin sa a kaina fa......
Katseta Anty ummi tayi
" kinga Rauda kiyi abunda nace miki"
Ta kaɗa kai kawai amma ita ta san akwai babbar ƙura a gaba
Koda ta dawo gida haka ta wuni babu sukuni
Da daddare tana zaune abun duniya ya haɗu ya cunkushe mata kai
Tabbas dole tabi shawarar Anty ummi
Wayar ta ta ɗauko ta danna numban Umar
Kiran Nashiga ya katse, sai ga nashi ya shigo
0 comments:
Post a Comment