_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Tsura ma wayar ido tayi tana kallon numban sa ta fito ɓaro-ɓaro
Sai da ta kusan tsinkewa sannan ta ɗaga,tare da karawa a kunnen ta
Sassanyar Sallamar sa ce ta karaɗe kunnen ta
Ta Lumshe ido a zuciyar ta tana faɗin
"komai nasa na daban ne"
Sai da yayi sallama sau uku sannan ta amsa
"ya kike? Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?
Shuru tayi batare da ta bashi amsa ba
"chuchu!
Ya faɗa,jikin ta ne ya ƙara yin sanyi
Dan ko Abaya idan ya kira ta da chuchu wani iri take ji
"bakya jina ne chuchu?
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Umar ka tabbata da gaske kake yi yanzu kana sona,kuma zaka aurani?
Daga can Ɓangaren Umar tashi yayi daga kwancen da yike yana bata amsa
"na tabbata mana chuchu,wallahi a shirye nike da in aure ki koda kuwa anan da sati ɗaya ne"
Hmmmmmmm ta kuma sauke ajiyar zuciya
"shikenan idan da gaske kake yi inaso inga alama idan kuma bada gaske kake yi ba dan Allah kada ka kuma cutar da zuciya ta"
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar sa
"da gaske chuchu? Yanzu komai ya wuce a wurin ki?
Ɗan murmushi tayi tace
" ya wuce amma dan Allah Jaana......
Sai kuma ta kasa Ƙarasa wa dan bata san sanda sunan Jaana ya fito daga bakin ta ba
Shiko Umar wani farin cikine ya ƙara lulluɓesa
"dan Allah me Rauda? Ki faɗi kome kike so wallahi zanyi miki shi a yanzu Ba tare da na ɓata lokaci ba"
Yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata da ya shiga farin ciki
"dan Allah kada ka kuma cutar da zuciya ta, idan ka kuma yi min abunda kayi Abaya ina tabbatar maka da zan iya rasa raina......
Katseta yayi da sauri
"ba sai kin roƙe ni ba Rauda a yanzu bani da wacce nike so sama dake acikin zuciya ta,kuma ina me tabbatar miki da ba zaki sameni me kuma sanya ki damuwa ba, a yanzu buri na inga nasa ki farin ciki"
Wasu guntayen hawaye ne suka biyo kuncin ta wanda ta rasa na menene su
Na farin ciki ne? Ko kuma na tarin tunanin da ya cunkushe mata ƙwaƙwalwa
"Umar kasan Kaine wanda nike so kai ne zaɓin zuciya ta, me yasa kayi min abunda kayi Abaya me yasa?
Ta faɗa muryarta na raunanewa
Umar ya sauke dogon numfashi yace
"dan Allah ki dena tuna baya Rauda, na tabbata a yanzu son da nike miki ya ninka wanda kike min sau dubu"
Share hawayen tayi tace
"shikenan zan kwanta sai da safe"
"shikenan chuchu kiyi bacci me daɗi ina sonki"
Ya faɗa da murmushi a fuskar sa
Ajiye wayar tayi zuciyar ta na tambayar ta
"anya kin kyauta wa kanki kuwa Rauda? Ki tuna Aasim da ya bar ahalinsa matsayin sa da komai nasa akan ki, shin kina ganin kinyi masa dai-dai? Ya tafi yana fafutukar yadda ze rayu dake amma ke zaki ci amanar sa?
Ta karkaɗa kanta da sauri wasu sabbin hawayen na ciko idanuwan ta
"ban kyauta ba, ban kyautawa Aasim ba"
Ta faɗa cikin damuwa
"to idan baki amince kin auri jinsin ki ba, haka zaki ƙare rayuwar da jinsin da ba naki ba? Kuma Umar shine wanda kike so"
Wani sashe na zuciyar ta ya faɗa,
"idan Aasim ya samo abunda yaje nema fa, na bayyana acikin jama'a, baki da hujjar da zaki ce ya barki kiyi aure tunda dai Shima ze iya rayuwa dake a matsayin mutum batare da kowa ya sani ba"
Kanta ne ya Sara dan gaba ɗaya tunanin ta ya burki ce
Kwantawa tayi a kujerar da take zaune tana faɗin
"ya Allah ka taimake ni, bansan yadda zanyi Ba"
A haka bacci ɓarawo ya sace ta
Shiko Umar suna gama waya alwala ya ɗauro ya gabatar da nafiloli sannan ya ɗaga hannayen sa yana godiya ga ubangiji,yana kuma roƙon Allah da ya kaɗe duk wani sharri da ze sa ya ƙuntata mata
*** **** *****
Zaune suke cikin Sahara suna tattauna yadda suka yi gwaji akan bayyana cikin jama'a
Wani daga cikin rauhanan yace
"ni fa a suffar mace na bayyana, na yi shigar kaya masu kyau na bayyana a wata kasuwa
Idan Kaga yadda mazen bil'adama suke kallo na kai kace haɗiye ni zasu yi
Ina jin wani yana cewa
"wannan kyakkyawar budurwar sai kace ƴammatan aljanna"
Be san garjejen ƙaton rauhani bane"
Suka fashe da dariya wani yana cewa
"amma kai ko ka iya iskanci wallahi, ni a suffar almajiri na bayyana a wurin wani cin a binci kuma a suffar yaro
Wata mata da ta ganni sai da ta kusan yin kuka
Wai ji ɗan ƙaramin yaro amma yana neman abunda zeci bata san ƙila tun kan a haifi iyayen ta nike duniya ba"
Dariya suka kuma sawa cike da nishaɗi
Aasim ko na zaune ya jingina da dutse yana kallon su
Jefi-jefi ya kan yi murmushi idan suka faɗi abun dariya
"Aasim kai kowa yana bada labari amma ka zauna kayi shuru, lafiya dai ko?
Ɗaya daga cikin rauhanan ya tambaya
Suka maida hankalin su kansa suna jiran jin me zece
" babu komai"
Ya faɗa
Rauhanin dake fuskantar sa yace
"a'a akwai komai mana, nasan baze wuce tunanin bil'damar ka kake yi ba, to ka kwantar da hankalinka mana saura wata ɗaya fa mu koma, musha biki"
"aikuwa dan mune nan abokan ango"
Wani Rauhanin ya faɗa, wani kuma yace
"Nikuma nine zan zama waliyyi"
Dariya suka kuma sawa
Jazmi da tunda suka haɗu da Aasim suka zama abokai yace
"abokina a wace ƙasa zaka ci amarcinne? Dan nasan yadda ka zaƙu muna komawa zaka yi mata maganar aure"
Har lokacin dariya suke yi
Aasim Miƙewa yayi yana murmushi
"ni kunbi kun cika min kunne da surutu bari in baku wuri"
Jazmi dariya yayi yace
"afuwan fa mun manta da yarima ne a wurin, wanda baya son haya niya"
Be kuma saurarar su ba ya wuce can nesa dasu kaɗan ya zauna
Yana kallon yadda iska ke kaɗa saharan
Gaba ɗaya akwanakinnan tunanin ta ya hana sa sukuni, yayi tsananin rashin ta
Ya Lumshe ido yana hango kyakkyawar fuskar ta
"habibty ina tsananin rashin ki,nasan kema kina can kina tunani na, ke ce rayuwa ta habibty"
Ya faɗa cikin tsananin begenta
Motsi yaji a kusa dashi
Ya buɗe idonsa yana kallon inda yike jin motsin
Wata maciji ya ce,me kyau jikin ta fari sol
Hannu ya miƙa mata yace
"kyakkyawar maciji ya, zo inganki"
Macijiyar ta tsura mai ido amma ta kasa matsawa daga inda take
Ƙara kallon ta yayi, sai lokacin ya lura ciwon dake jikin ta
Cikin tausaya wa,ya ɗauko ta yana duba ciwon sosai taji
"ohhh sannu,ashe rauni kikaji, bari in sami ki magani kinji?
Abul simnan ya ƙara so wurin ya zauna
" Aasim ina ka samo maciji ya kuma?
Aasim yayi murmushi yana sama ta maganin
"anan na ganta,taji rauni"
Abul simnan ya jinjina kai yace
"ka kyauta da ka taimaka mata"
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar sa idanuwan sa kuma na kan Macijiyar
"na sa miki magani kinji, kiyi haƙuri zaki samu lafiya"
Ya Ƙarasa faɗa yana ajiye ta a ƙasa
Ta wuce
Ya maida kallon sa ga Abul simnan da yike kallon sa
"kana da kyakkyawar zuciya Aasim"
Aasim ya kuma murmushi
"kullum haka kake cewa Abul simnan"
Abul simnan ya jinjina kai
"da gaske nikeyi kana da kyakkyawar zuciya shiyasa nike tausaya maka"
Aasim ya maida kallon sa ga saharar dake kaɗawa
"kai ma kana da kyakkyawar zuciya,ina kuma godiya da yabo na da kake yi a koda yaushe"
**** ***** ******
Da safe, tana zaune tana tsakurar abun kari dan Sam bata jin cin komai
Wayar tace ta fara ƙara, ta ɗauka ta dubawa Umar ne
Ɗauka tayi tare da karawa a kunnen ta
Tana sallama
Daga can Ɓangaren Umar ya amsa yana faɗin
"barka da safiya chuchu,ina fatan kin tashi lafiya"
"lafiya lau"
Ta bashi amsa
Ya jinjina kai yace
"masha Allah Naji daɗi da Naji Hakan, tun ɗazu naso in kira ki sai nayi tunanin baki tashi ba"
Tayi ɗan murmushi dan jin muryar sa damuwar da ta cunkushe zuciyar ta ta rage
_~Ƴarfillo~_.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 2⃣4⃣
_Wannan Page nakine *maman isqah* kin kasance me dogon sharhi a duk lokacin da nayi posting ina matuƙar jin daɗin Hakan Allah ya bar zumunci_
*_Fatan alkhairi_*
_Ga *princess mazadu* ina miƙa gaisuwa_
_9:48_🕒 AM
MON, JUL 8
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"yau na tashi cikin farin ciki sakamakon wani kyakkyawan mafarki da nayi"
Umar ya faɗa
Rauda tace
"mafarki? Mafarkin me?
Daga can Ɓangaren Umar gyara zama yayi yana ɗan jingina da kujerar da yike zaune
"mafarki nayi munyi aure,kin haifa min kyawawan yara ƴan uku, masu kama da ke"
"ƴan uku fa? Amma a mafarkin naka na mutu ko?
Dariya Umar yayi yace
"dan kin haifi ƴan uku kuma sai ki mutu?
Ras na ganki kina ta yi musu wasa"
Wani murmushin ta kuma yi
"a'a nikam bazan iya haifar ƴan uku ba"
"zaki iya mana chuchu, ke fa jaruma ce"
Ta girgiza kai kamar yana ganin ta
"Allah bazan iya ba"
Jin tana amsa mai faran-faran yasa yaji ya ƙara shiga cikin nishaɗi
"inma ba zaki iya ba, ranar haihuwar sai mu raba in haifi biyu ki haifi ɗaya"
Dariya tayi tace
"to shikenan Allah ya nuna mana lokacin"
Amin ya faɗa haɗi da cewa
"wa yaga Umar na naƙuda, ai inaga duk faɗin garin Abuja sai sun taru"
Dariya ta kuma yi sosai, Shima ya taya ta
Yana cigaba da cewa
"Allah da gaske"
Rausayar da kanta tayi tace
"kawai dan kana rago"
"ke haihuwa fa, cap ai kudai mata sai dai mu muku fatan shiga aljannah amma zahiri kuna mugun ƙoƙari"
Ajiyar zuciya ta sauke, dan tunda ta fara jin muryar sa taji natsuwa na saukar mata
Tabbas ƙaunar sa daga allah ce
Katse mata gajeren tunanin da tafi yayi ta hanyar kiran sunan ta
"Rauda!
Ta kuma sauke ajiyar zuciya gami da amsawa
" na'am "
"kin karya?
Ya tambaya
" ina kan karyawan"
"ook to kigama sai in kuma kira, ko inzo yanzu ne?
Ta ajiye kofin tea ɗin da ya gama hucewa tace
" yanzu kuma? Safiya ce fa
Umar yace
"na sani kawai ina buƙatar inganki ne"
Murmushi tayi tace
"a'a kadai bari sai da yamma, ko da daddare"
Yace
"to shikenan Allah ya kai mu ki kula min da kanki"
"nagode"
Ta faɗa tana ajiye wayar
Ranar wuni tayi cikin farin ciki dan firar da suka yi ce kawai take mata yawo a kunne
Ya kira ta yafi sau biyar
Sai dai data tuna Aasim sai taji Gabanta ya faɗi
Tunda ga wannan ranar wata soyayya me ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin su
Koda yaushe suna manne a waya dan ya koma Abuja
Amma duk weekend sai yazo Kaduna ya ganta
Mama ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba
Ganin yadda su umma suke nuna hassadar su ƙarara
Dan duk wanda yaga Umar sai yayi mamaki ga kuɗi ka ga kyau ga kwarjini, duka Allah ya haɗa masa
Yau Asabar, tun ƙarfe huɗu Umar ya taso kuma tunda ya taso suke waya
Fira suke yi sosai me cike da annashuwa
Mama ta fito daga uwaɗɗaka tana faɗin
"wai ni Rauda yau wayar nan ba zata ƙare bane? Muna da aiki fa ga yamma nayi"
Murmushi Rauda tayi tana yin ƙasa da muryar ta tace
"mama na min magana, bari zan kira ka"
Tana gama faɗa ta kashe wayar tana duban mama dake ta zuba murmushin jin daɗi
"mama me za'a dafa ne?
Mama tace
"soyayya da mai da yaji"
Rauda tayi dariya tana faɗin
"kai mama"
Mama ma dariyar tayi tace
"eh mana, ace waya anfi ƙarfin awa ana yin ta"
Ƙasa Rauda tayi da kanta cike da jin kunya tana tura mai saƙo
_zamu ɗaura girki yanzu,Allah ya tsare hanya ya kawo ka lafiya_
Batafi minti biyu da turawa ba nashi saƙon ya shigo
_amin chuchu, ki kula min da kanki, ki kuma sa girkin dani zanci, ina sonki_
Murmushin jin daɗi tayi bayan ta gama karantawa a zuciyar ta tana faɗin
"na yarda da ake cewa addu'a bata faɗuwa ƙasa, kuma duk daren daɗewa Allah ze amsa ka"
Ta faɗa tana tuna lokacin da take tashi dare tayi ta addu'ar Allah ya ɗaura wa Umar son ta
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tana sake hamdala ga ubangiji
Miƙewa tayi ta fita tsakar gida suka fara aiki da mama
Da daddare, tun da ta idar da sallar issha take tsantsara kwalliya
Ta kwashi minti 30 tana shiryawa, sai da ta gama sannan ta ɗauko doguwar riga ta sanya
Tana kallon kanta a madubi
Dan tunda take bata taɓa kwalliya irin ta ranar ba
Kiran Umar ne ya shigo ta ɗaga
"madam ina waje"
Ya faɗa
To tace tare da ajiye wayar ta ɗauko gyale ta yafa tare da fesa turare emergency
Cikin natsuwa ta fito yana tsaye yana waya cikin ƙana nan kaya
Yayi kyau sosai, yana wayar yana murmushi yana kuma shafa kwataccen sajen sa wanda ya zagaye farar fuskar sa
Ƙarasa wa tayi tana zuba masa kyawawan idanuwan ta wanda suka narke da ƙaunar sa
Sai da ya gama wayar, sannan ya fuskance ta yana kallon fararen idanunta fuskar sa ɗauke da murmushi
"wow chuchu wannan irin kyau haka?
Ta maida mai da martanin murmushin
"kazo lafiya, ya hanya?
" lafiya lau,boo boo kinsan Allah kinyi kyau kamar wata balarabiya, ji nike yi kamar in sace ki"
Dariya tayi, tace
"to kasace mana, ai dama ta kace"
Ya jingina da jikin motar yana Lumshe shanyayyun idanun sa da suka jiƙe da tsananin ƙaunar ta
"chuchu Allah kintafi da tunanina ji nike fa kamar zan faɗi"
Ta kuma yin dariya tana janyo baccin dake kusa da ita
"zauna to dan in ka faɗi bazan iya ɗaga ka ba"
Yayi lallausan murmushi yace
"chuchu, gaskiya ki gaya ma baba zanturo magabatana ayi maganar aure"
Ta zauna gefen bencin tana kallon sa
"habadai Badai yanzu ba"
Ya ɗan ware idanun sa
"ba yanzu ba to sai yaushe? Kinsan Allah bazan iya ƙara wata uku ba tare da na mallake ki ba"
Itama ware nata idanun tayi tace
"wata uku fa? Karatu na fa?
" sai ayi transfer ki koma ta Abuja, amma Allah bazan iya ƙara wani lokaci me tsawo ba tare dake ba"
Farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta
"Jaana kadai bari,gaba tukunna"
Ya zauna gefen bencin idanuwan sa na kanta
"Allah bazan iya ba, ba zaki gane yadda nike jinki a raina bane, ki taimaka kiga ya ma baba kafin in koma na turo plz"
"shikenan kabari zanyi shawara da mama tukunna"
Ya jinjina kai
"shikenan"
Be bar gurin ta ba, sai tara da rabi kamar kar su rabu
Ko da ya koma gida sai da suka raba dare suna waya
*** **** ****
Tunda ya tashi yike jin kanshi cikin farin ciki da tsananin ɗoki dan gobe ne abul simnan ze sallami kowa
Gaba ɗaya ya ƙagara goben tayi jefi-jefi ya kan duba lokaci gani yike kamar lokacin baya gudu
Jazmi ya dafa sa ganin ya kasa zaune ya kasa tsaye yace
"abokina ka sa ranka a inuwa,nasan ka ƙagara ka ganta wallahi ni har mamaki nike yi"
Aasim yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya
"banga laifin ka ba, dan kayi mamaki ni kaina abun ɗaure min kai yike yi,dan bazan iya kwatanta adadin ƙaunar da nike mata ba"
Jazmi ya jinjina kai
"to Allah dai ya shige mana gaba"
Amin amsa ya faɗa
**** **** ****
Washe gari Rauda na zaune gaban Abba, dan tun a daren jiya ta gaya ma mama abunda Umar yace ita kuma mama ta faɗa masa
Sai da ya gama karyawa sannan ya maida hankalin sa akanta
"maman ki ta faɗa min abunda Yaron yace, gaskiya na yaba da hankalin sa da kuma tarbiyyar sa, kuma nasa ya yanki amadu dake Abuja yayi min bincike a kansa bayi da wata matsala
Dan haka kice masa ya turo su jibi
Amsawa tayi da to, sannan ta fito
Tana fitowa ta danna kiran sa
Bugu biyu ya ɗauka
Suka gaisa sannan ta faɗa masa abunda baba yace
Tsallen farin ciki yayi haɗi da sujada ga ubangiji
"ai ni dama gobe yace wallahi,amma Allah ya kai mu jibin ki tambaye sa da wani lokaci zasu zo?
" to zan faɗa ma mama, idan ta tambaye sa sai in faɗamaka"
"shikenan amarya"
Tayi dariya tace
"amarya kuma?
Umar yace
" eh mana, dan zan faɗa ma uncle ɗina yace nan da wata uku suke so"
Murmushi tayi tana jin zuciyar ta fes
**** **** *****
Tunda ya fara haɗa kayan sa ya lura da abul simnan na kallon sa
Sai da ya gama tsaf sannan ya zo gaban sa
Cikin ladabi ya ɗan risina yace
"to ni na gama shiryawa zan tafi"
Abul simnan ya sauke numfashi cike da tausayin sa
"to Aasim ina maka fatan alkhairi, amma kada ka manta da neman taimako na aduk sanda ka shiga tsaka me wuya"
Aasim da har lokacin da murmushi a fuskar sa yace
"ina godiya, kuma ai zan ringa ziyartar ka,insha Allahu"
Jinjina kai abul simnan yayi
"shikenan Allah ya tsare ya kaika lafiya"
Aasim ya fito daga kogon yana tunanin ta hanyar da zebi
Jazmi ya ƙara so wurin yana cewa
"badai har ka shirya ba?
" na shirya tafiya zanyi"
"Nima na gama shiryawa mu haɗa hanya, amma dan Allah ina neman wata alfarma a wurin ka"
Aasim ya kallesa yace
"alfarma kuma jazmi? Wace irin alfarma"
Jazmi yace
"inaso mu biya ta masarautar mu, nasan mahaifiyata zata ji daɗi idan ta ganka,saboda sunan ka ya karaɗe duniya na ɗan babban sarki, kuma masarautar mu zata ƙara matar ba da suna idan kaje"
Aasim yayi murmushi yana Gyaɗa kai
"shikenan muje, amma fa muna zuwa zan wuce dan bazan daɗe ba"
"nayar da mu tafi"
Ɓacewa suka yi atare suka nausa sararin samaniya
Tun kafin su isa, jazmi ya tura saƙo masarautar su na ga sunan zuwa
Jin harda Aasim yasa aka fara gagarumin shirye-shirye
Suna isowa gaba ɗaya ƴan masarautar suka zube
Suna kwasar gaisuwa
Amsawa Aasim ya dinga yi cikin sakin fuska
Har suka isa gaban mahafiyar jazmi
Tayi farin ciki sosai
Nan da nan aka cika gaban sa da kayan ciye-ciye dana lashe-lashe
Gefe kuma kyawawan kuyangi ne ke rawa cikin salon ƙwarewa da ɗaukar hankali
Kallon su kawai Aasim yike yi amma kwata-kwata hankalin sa baya kansu in banda ƙosawa babu abunda ya cika zuciyar sa
Allah-Allah yike yi yaje yaga abar ƙaunar sa
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE 📕 2⃣5⃣
_Wannan Page nakine *sister ummi*, ladar zuwa katsina_🥰
_11:59_🕒 PM
MON, JUL 8
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Duk ƙoƙarin da Aasim yayi ganin ya tafi a ranar gagara yayi
Domin magiyar duniya babu wacce jazmi da mahaifiyar sa basu masa ba akan ya kwana
Dole ya haƙura badan ransa ya so ba
washe gari
Ƙarfe bakwai tayi wa waliyyan Umar a gidan su Rauda, baba da ƙanin sa da kuma abokin sa malan shitu sun amshe su hannu bibbiyu
anan take suka bada kuɗin gaisuwa suna tambayar nawa aka yanke sadaki?
Dan su atake suke so agama yin komai
baba haƙuri ya basu akan ze neme su nan da wani ɗan lokaci amma dan ba Umar Rauda anbashi
Tun bayan tafiyar su Rauda da Umar suke maƙale a waya,wata kalar soyayya ce me zafi take ƙara shiga tsakanin su
kuma a ranar Umar ya koma Abuja
Ƙarfe biyar Aasim ya iso,kai tsaye gidan su Rauda ya isa
Yana bin ƙamshin jikin ta wanda yasa dashi da ita har uwaɗɗakan da take
Tana tsaye tana ninke kaya
Zubawa bayanna ta ido yayi yana jin kamar ya fizgota jikin sa
Ita ko tsayuwar mutum taji a bayan ta,kuma bata jiyo tafiya ba, Hakan ya sa gaban ta yaɗan fara faɗuwa
Juyo wa tayi a hankali,wani mummunan faɗuwa Gabanta yayi zuciyar ta na wani irin kaɗawa
Kallon-kallo suka shiga yi kamar lokacin suka fara ganin juna
Ya buɗe hannayen sa alamar ta shiga yana yi mata lallausan murmushi
Tsaye tayi tana kallon sa ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi,in banda fargaba da tunanin abunda ze faru babu abunda ya cika zuciyar ta
Shiko mamaki ne ka masa, ganin ita da zata yi farin ciki da murnar dawowar shi,shine zata tsaya tana kallon sa kamar ma bata so dawowar nasa ba
"habibty!
Ya kira ta, mamaki na fara bayyana a fuskar sa
"Rauda kidawo natsuwar ki kar ya fahimta tun yanzu"
Zuciyar ta ta sanar da ita
Ƙaƙaro murmushi tayi tare da Ƙarasa wa ta rungume sa
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"habibty duk ɗoki da murnan da nike yi akan naganki ashe ke bakyayin Hakan, nayi zaton zaki yi farin ciki da ganina amma sai Naga saɓanin Hakan, ki faɗa min me ke faruwa, ko kin canza min matsayi a zuciyar ki ne?
Ɗagowa tayi da sauri tana girgiza kai ganin yana so ya fahimta
"ko ɗaya kada kayi tunanin Hakan, matsayin ka yana nan babu abunda ya sauya, kawai dai gani nike kamar mafarki nike yi dan tun bayan tafiyar ka nike ta mafarkin gaka ka dawo sai na saki jiki ina jin daɗi kawai sai na farka, shi yasa Kaga Hakan"
Murmushi yayi tare da matse ta a jikin sa cikin tsananin ƙaunar ta yace
"to yanzu ba mafarki bane, zahiri ne nayi rashinki sosai habibty"
Ita ma murmushin tayi cikin fargaba tace
"ka dawo lafiya? Ina fatan kasamo abunda kaje nema?
Ta tambayesa tana fatan yace be samo ba dan ta samu hujjar kare kanta
"na samo habibty,yanzu baki da wata matsala ko nan da gobe kika ce na fito na bayyana a gidan ku zan bayyana"
Zahiri ba taso jin Hakan ba,amma sai tayi murmushi tace
"masha Allah alhamdulillah, Naji daɗi sosai, isowar ka kenan yanzu?
Ya jinjina kai alamar eh
" to shikenan yanzu kaje ka huta, anjima sai ka dawo dannasan mama tana gab da shigowa"
"a'a anjima kam sai dai Nazo mu tafi, dan wallahi ina buƙatar ki sosai"
Ya faɗa, Gyaɗa kai tayi tace
"Allah dai ya kai mu anjiman, ka huta lafiya"
Kiss ya manna mata a goshi sannan ya ɓace
Jaɓar, ta zauna tana faɗin
"na shiga uku, yanzu ni ya zanyi?
Tabbas nasan ze wargaza al'amarina da Umar,da zarar ya gane
Ta runtse idon ta cike da tashin hankali
" a'a bazan bari Hakan ta kasance ba,dole na nemi mafita nasan yadda zan ɓullo ma al'amarin tun kafin Aasim ya gane"
Miƙewa tayi ta zura hijabi kai tsaye gidan Anty ummi taje ta gaya mata
Itama hankalin ta ya tashi amma sai ta danne tace
"kisa Allah aranki babu abunda ze faru insha Allahu,ze ya fahimce ki da yardar Allah"
Girgiza kai Rauda tayi dan ta san Aasim baze taɓa yarda ba
"Anty ummi nasan baze yarda ba, damuwa ta mani kada yayi ma Umar wani abu, ina sonsa sosai bana so wani abu ya same sa"
Ta Ƙarasa faɗa muryar ta na raunanewa
Anty ummi ta sauke dogon numfashi
"insha Allahu ze yarda, yanzu dai ki masa maganar anjiman tun kafin ya fahimta da kansa,idan ya yadda to, idan kuma be yadda ba sai mu san yadda zamu ɓullowa al'amarin"
Miƙewa Rauda tayi tana kaɗa kai bata ƙara cewa komai ba tafi to tana tafiya tana harharɗewa
Wayar ta ta fara ƙara alamar kira na shigowa
Ko bata duba ba ta san Umar ne, dan taken kiransa daban tasa masa
Ta ɗauka ta kara a kunnen ta
Tattausar muryarsa ce ta karaɗe kunnuwanta
"chuchu, yau kin manta da mijin ki ko?
Nannauyan numfashi ta sauke tace
" a'a ba haka bane, na kira ka da rana wayar bata shiga ba, da yammannan kuma bana cikin natsuwa ne shiya sa"
"subhanallah me ya faru?
Ya tambaya da sauri
Ta kuma sauke numfashi tace
"Umar kasan dai ina son ka ko?
" na sani chuchu"
Ta kuma numfasawa sannan ta cigaba da cewa
"bazan iya rayuwa babu kai ba, ina fargaban ka kuma nisan tata"
Daga can Ɓangaren Umar gyara zama yayi a office ɗinsa
"chuchu taya za'ayi na nisance ki? Kema kinsan bazan iya ba, a yanzu babu wani abun da ze rabani dake sai dai mutuwa"
"akwai Umar, akwai, ni nasani"
Ta faɗa cikin tsananin damuwa
Ya zare farin glass ɗin dake manne I donsa yace
"Rauda, wai meke faruwa ne? Ki faɗamin dan Allah, dan wallahi hankalina ya fara tashi"
Ta share hawayen da suka fara biyo kuncin ta
"wannan ba maganar waya bace, kabari zan faɗa ma amma kafinnan inaso kamin wata alfarma guda ɗaya"
"alfarma? Wace kalar alfarma kinsan kin wuce da matsayin alfarma a gurina kifaɗamin kawai ko menene zan miki shi"
"zan kashe wayata na tsawon kwana uku,kuma bana so inkaji shuru kace zaka kira wayar mama ko wata wayar da zaka sameni, sannan kada kayi yunƙurin zuwa har sai na neme ka da kaina"
"what? Kinsan me kika ce kuwa Rauda? Inyi kwana uku batare da Naji muryar ki ba? Kema kinsan bazan iya ba"
Ya faɗa
Ta jingina da bangon waje dan ta iso gida
"kayi haƙuri, Nima ba da son raina bane,akwai matsalar da nike so inga yadda zata kasance ne tukunna"
Umar ya miƙe jin zufa ta fara karyo masa
"Rauda kifaɗamin abunda ke faruwa, kinsan ba ƙaramin aiki na bane nabaro Abuja yanzu ko?
"a'a, dan Allah kayi haƙuri,zan kashe wayar yanzu kuma dan Allah kayi abunda nace ma please Jaana"
Ze kuma yin magana ta katse kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya
Wani kalan nawi taji ƙirjinta ya mata ta shiga gida lokacin mama ta dawo
"ina kika je?
Mama ta tambaya
" gidan Anty ummi"
Rauda ta bata amsa tana zama kan kujera
Mama ta kalle ta tace
"lafiya na ganki wani iri?
Tayi ƙoƙarin danne damuwar ta tace
" babu komai, ƙirjina ne ke ɗan min ciwo"
Da daddare, saida mama ta ta tafi ɗakin baba sannan taji iska na ɗiban ta
Kafin ƙyaftawa da Bismillah ta ganta a ɗakin sa
Yana kwance Saman lallausan gadon sa
Kyakkyawan murmushi ya mata yana miƙa mata hannun sa
Kallon sa take yi kamar taga wani sabon halitta ta kasa Ƙarasa wa
Ya miƙe ya ƙara so inda take ya sa hannu ya shafa gefe n fuskar ta
"habibty miye ne haka, baki san yadda na ƙosa dake bane?
Ya Ƙarasa faɗa yana janta jikinsa
Har lokacin ta kasa cewa komai
Wata kalar runguma ya yi mata da tasa duk jikin ta ya amsa
" Aasim!
Ta Kira sunan sa, ya sassauta rungumar da yayi mata tare da ɗago kyakkyawar fuskarta ya zuba mata ido
Yanajin ƙaunar ta na ratsa duk kan gaɓɓan sa
cikin fargaba tace
" inaso muyi wata magana da kai kuma dan Allah ka Fahim ci abunda zan faɗa maka"
Girgiza kai yayi yace
"a'a yanzu ba lokacin da zamuyi magana bane, wata na nawa bana tare dake?
Shuru tayi tana kallon sa kawai, sun kuyo da fuskar sa yayi yana ƙoƙarin haɗa bakin sa da nata
Tayi saurin kauda kanta tana faɗin
"please ka tsaya"
Ya ƙura mata ido yana ganin yadda take maida numfashi
"habibty, wai bakya jin tausayi na ne?
Tayi shuru dan bata san me zata masa ba
Kuma matse ta yayi yana shasshafa ta gaba ɗaya ya rikice
Ya ɗauke ta cak, ya aje ta kan gadon
Zata miƙe yayi saurin danne hannayen ta dana sa, yana kissing ɗin wuyanta
Ƙoƙarin tashi take yi amma ta kasa, dan ji tayi kamar an ɗaɗɗaure ta
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 2⃣6⃣
_Wannan Page nakine *oum deedad*, nakine ke kaɗai kiyi yadda kikeso dashi_
_11:22_🕒 AM
TUE, JUL 9
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Kiciniya kawai take yi na ƙoƙarin ƙwace kanta
Hakan yasa ya dakata daga abunda yike yi ya tsura ma fuskar ta ido cike da mamakin sabon al'amarin da ta zo masa dashi
Dan yasan ada duk abunda ze mata bata yunƙurin hana sa
Yafi minti uku yana kallon ta da karantar yana yin ta, daga bisani ya ɗaga ta ya bar ɗakin
Tayi lamo akan gadon,zuciyar ta cike da tarin fargaba
"Rauda be kamata ki canza masa lokaci ɗaya ba, idan Hakan ya ɓata masa rai fa? Har ya gano kina ganin ze tsaya ya saurare ki?
Zuciyarta ta tunatar da ita
Tashi tayi da sauri ta dira daga kan gadon,ta fito falo
Kishingiɗe ta hango sa kan kujera ya Lumshe idanuwan sa
Ta riƙe ƙofar tana kallon sa kawai dan tama rasa yadda zata yi
Haƙuri zata je ta basa kome? Dan zahiri ba taso ya ƙara wata mu'amala da ita
Dan ta san aduk sanda wani abu ya shiga tsakanin su ƙara ƙaunar ta yike yi
Tana tsaye tana saƙe-saƙe taji ya kira sunan ta kuma har lokacin idanuwan sa na rufe
"Rauda! Zo nan"
Ta saki hannun ƙofar amma ta kasa Ƙarasa wa cikin falon
"nace kizo ko? Bawani abu zan yi miki ba ai tunda bakya so"
Ya faɗa still idanuwan sa na rufe
Jin ya haƙura da abunda yike niyyar yi yasa ta ƙara so gaban kujerar ta durƙusa
Tashi yayi daga kishingiɗar da yayi yana kama hannun ta na dama gami da shafa tafin hannun
Sai ga wani ganye ya fito, mamaki ne ya kamata ganin yadda ganye ya fito a hannun ta
Ta cigaba da kallon sa kawai cike da al'ajabi
Aasim ko zuba ma ganyen ido yayi wanda yasa mata a hannu tun ranar da ze tafi, wanda ze ɗaukar masa duk abunda ya faru bayan tafiyar sa ba tare da rauda ta sani ba
Shafa ganyen yayi sai ga tsakiyar ganyen ya zama kamar TV take ya fara nuna masa
Ita dai Rauda taga yana kallon ganyen amma bata san me yike gani ba dan yana zaune ne akan kujeran yayin da take tsugunne a gaban sa
Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ganin duk abunda ya faru
Hankalin sa ya tashi sosai take idanuwan sa suka sauya kala zuwa ja kamar garwashin wuta
Nan da nan jikinsa ya fara fitar da wani turiri wanda yasa taja baya da sauri cike da tsoro
Ɗago turararrun idanuwan sa yayi ya watsa su a kanta tare da Miƙewa cike da tsananin ɓacin rai da tashin hankalin abunda ya rikita ƙwaƙwalwarsa
"ni zaki ci amana Rauda ni!!
Ya faɗa yana nuna kansa
Ja da baya ta fara yi cike da tsananin razana dan ya zamar mata kamar wani namijin zaki
Shiko tana ja da baya yana cigaba da taka wa zuwa inda take
"nace ni zaki ci amana? Ina can ina shan baƙar wahala da saida rayuwa ta akanki, ashe ke kina nan kina cin amana ta?
Dede lokacin ta kai jikin bango babu kuma inda zata ƙara matsawa
Damƙo gashin kanta yayi wanda yasa ta saki wata ƙara saboda tsananin zafin da taji
Ya matso da fuskar ta dede tasa dan tana jin yadda yike fitar da wani huci me zafin gaske
"kiyi magana!!
Ya faɗa cikin tsawa wanda saida fitulun ɗakin wasu suka tarwatse
Babu inda baya kyarma a jikin ta cikin tashin hankali da tsananin tsorata tace
" ka.....yi...ha..ƙuri"
Cigaba da kallon ta yayi still hannun sa na damƙe da gashin ta amma ya kasa ƙara furta komai in banda suya babu abunda zuciyar sa ke masa
Jin yayi shuru yasa ta buɗe idanuwan ta Ahankali
Aiko suna haɗa ido ta maida su ta rufe gam
Dan yanzu ma babu ƙwayar idon kwata-kwata, ƙara rinewa kawai suke yi
"ashe shiyasa baki yi farin cikin dawowa na ba,ashe shiyasa kika ƙi amince wa da buƙata ta saboda kin canzani a zuciyar ki"
Aasim ya faɗa cike da tsananin takaici
Kaɗa kansa yayi yana cigaba da cewa
"bazan taɓa amince wa da wannan butulcin ba, bazan taɓa amincewa ba!!!!
Ya faɗa cikin ƙaraji tare da wurgar da ita gefe
"zanje inga uban da ya tsaya masa,zan ɗanɗana masa kuɗar da bake kaɗai ba duk wata mace idan tagansa bazata yi marmarin ƙara kallon sa ba"
Ya faɗa yana juyawa a fusace
Yunƙura wa tayi da sauri tariƙo ƙafafuwan sa ta baya
"naroƙeƙa kada ka cutar da shi,duk abunda kace inyi zanyi amma kada kataɓa lafiyar sa"
Fincike ƙafafuwan sa yayi da ƙarfin gaske ya kuma yin gaba
Ta sake kamo ƙafafun cikin tsananin tashin hankali
"wallahi zan rabu dashi amma kada ka cutar dashi dan Allah"
Juyowa yayi tare da sukuyowa yana yi mata wani kallo me cike da razanarwa
"na baki nan da kwana uku, ki yanke duk wata alaƙar dake tsakanin ki dashi idan kuma kika ƙi........
Ya dakata da maganar yana yi mata gargaɗi da ya tsansa wanda saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga yike rawa
"wallahi zaki yi mamakina, dan ke tawa ce ni kaɗai babu wani mahalukin da ya isa ya raɓeki, babu shi!!!!
Ya Ƙarasa faɗa yana ɓatar da ita
Bata ganta a ko ina ba sai, a uwaɗɗakan mama
Fashewa tayi da kuka me ciwo tana kifa kanta akan fulo
Kuka take yi sosai kamar ranta ze fita
Ji tayi an dafata, ta ɗago da sauri
Wata farar dattijuwa ta gani zaune kusa da ita
Rauda taja baya da sauri wani sabon tsoron na kuma kamata
"kada kiji tsorana Rauda, ni baiwar Allah ce me tsananin tsoron sa, bazan cutar dake ba"
Rauda ta takure da bangon gadon har lokacin illahirin jikin ta rawa yike yi
"wacece ke? Me ya kawo ki wurina?
Dattijuwar tayi murmushi tace
"sunana ummu Salma,kuma ni aljana ce, abunda ya kawoni gurin ki kuma nazo in taimake ki ne"
Rauda tayi shuru daga bisani tana ce
"taimako?
Ummu Salma ta jinjina kai
"na daɗe ina bibiyar rayuwarki, babu abunda bansani ba akan ki, tabbas rayuwar ki tana cike da sarƙaƙiya da ruɗani,shiyasa nazo na taimaka miki
Duk da ni aljana ce bani da ƙarfin da zan iya karawa da rauhani, rauhanin ma kuma Aasim bin ramzad wanda ya kasance ɗan sarkin rauhanai me ƙarfin gaske, nasan bani da ƙarfin da zan iya karawa dashi amma ina da ɗan taimakon da zan iya baki da kuma shawarwari waɗanda zasu amfane ki"
Cikin sauri Rauda ta girgiza mata kai
"a'a nagode da taimakon ki amma bana so wani abu ya same ki tunda kinyi niyyar taimakona, Aasim yana da wani madubi da yike ganina dashi yanzu nasan yana ganki ya na kuma jin duk abunda kike faɗa kiyi gaggawar barinnan dan Allah"
Ummu Salma tayi murmushi tana ciro wani ƙaramin turare
"kafinnazo nan saida nayi amfani da wannan turaren,a halin yanzu Aasim baya ganin mu
Kuma wannan turaren shi nazo na baki, saboda nasan a duk sanda yanzu Aasim ya ganki da Umar ze iyayi masa komai
Kuma ya kamata ki haɗu da Umar ki yi masa cikakken bayani, domin ya zauna da shiri da kuma addu'o i
Sannan kusan mafitar da zaku ne ma,a duk sanda zaki haɗu da Umar Kisha fa wannan turaren Aasim baze ganku ba, kuma inaso kuyi duk abunda zakuyi cikin gaggawa, sannan kijuye turaren a man shafawanki da zarar zaki haɗu da Umar ki shafa"
Ta Ƙarasa faɗa tana miƙa ma ta turaren
Amsa Rauda tayi tana kallon turaren
Yayin da ummu Salma ta cigaba da cewa
"ni zan tafi, kiyi ƙoƙari ki haɗu da Umar a gobe tunda kinga kwana uku kaɗai Aasim ya baki, sannan ki shafa idan zaki kira Umar ɗin, duk yadda kuka yi gobe zan dawo inji, na barki lafiya"
Rauda tayi shuru bayan ummu Salma ta ɓace tana juya turaren a hannun ta
**** **** ****
Tun bayan da suka yi waya yike kiran wayar ta yike jin a kashe
Ya shiga damuwa sosai,dan ko bacci ya kasa yi kuma har lokacin kuma trying ɗin wayar yike yi amma still ba ta shiga
Aje wayar yayi a gefe yana janyo fulo ya tada kansa
Maganar ta ce kawai ke yi masa yawo a kunne
_Bazan iya rayuwa babu kai ba, ina fargaban ka kuma nisan tata_
Ajiyar zuciya ya sauke, ya rasa ta yadda ze gane abunda take nufi, gashi tace kada yake sai ta ne mesa, to me ke faruwa??
Miƙewa yayi ya ɗauro alwala, ya dinga nafiloli dan bayajin ze iya yin barci
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:43 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
Dedicated to _little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 2⃣7⃣
_Wannan Page nakine *Aysha Abubakar* Allah ya bar zumunci_
*_Gaisuwa da jinjina ga umar ɗalha muna godiya da ƙoƙarin da kake yi a forum kai da sis nabila allah ya bar zumunci_*
_8:09_🕒 PM
WED, JUL 10
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Ya daɗe a tsaye yana za gaye ɗakin,jefi-jefi ya kan zauna ya zuba tagumi
Me yasa Rauda zata masa haka?
Meyasa take Umar wannan zazzafar ƙaunan?
Ya sani tun bayanzu ba tana tsananin ƙaunar Umar shiyasa ya sa ido sosai akan Umar
Me Umar yike dashi da yike ɗaukar hankalin ta? Ya zo mata asuffa me kyau dan yana tunanin kyan da Umar yike dashi shine yasa ta ke sonsa
Amma sai gashi duk ƙoƙarin da yayi ganin karsu haɗu bayan tafiyar sa sun haɗu, abunda dai yike gudu shiya faru
Furzar da wata iska yayi me zafi yana faɗin
"Rauda ke ta wace ni kaɗai, ba zaki yi rayuwa da wani ba"
Ya Ƙarasa faɗa yana jingina da kujerar
**** **** ****
Washe gari,Anty ummi tazo Rauda ta sanar da ita duk abunda ya faru
Ba ƙaramar kiɗima tayi ba tace
"yanzu maza ki shafa turaren ki kira sa, dan abun bana zama bane karya je ya cutar da ɗan mutane"
Rauda ta ɗauko turaren ta shafa sannan ta lalubo wayar ta, ta danna kiransa
Lokacin Umar yana zaune a office wata patient tana mai bayanin abunda ke damunta
Sam hankalin sa baya wurin, dan bejin abunda take cewa Sam
Zayyad da ke zaune ɗayan Ɓangaren Shima yana sauraren bayanin da patient ɗin dake zaune gaban sa take masa
Ya lura da yanayin Umar Sam hankalin sa baya wurin da alamama ya Lula cikin tunani ne
Ɗan buga tebur ɗin dake gaban sa yayi wanda ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi
"yadai doctor lafiya kuwa?
Umar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin
" babu komai"
Dede lokacin kiran Rauda ya shigo wayar sa
_chuchu_
Ya gani ɓaro-ɓaro a screen ɗin wayar
Ya miƙe da sauri yana ɗaukar wayar
"Zayyad ka duba wannan patient ɗin please ina zuwa"
Be jira jin me Zayyad zece ba, ya fice yana ɗaukar wayar
"Rauda yanzu fisabilillahi abunda kika yi kin kyau ta kenan? Kin sa hankalina ya tashi wallahi ko bacci ban iya yi ba"
Rauda ta sauke ajiyar zuciya
"kayi haƙuri,yanzu kana ina ne?
" ina asibiti"
Ya bata amsa
"ina son ganin ka ne da gaggawa ya za'ayi kenan?
" zan taho Kadunan, amma kafinnan faɗamin meke faruwa ne?
Ta gyara zamanta tana cewa
"kabari sai kazo, na gaya ma ba maganar waya bace"
Numfashi Umar ya sauke cike da damuwa
"shikenan zantaho yanzu, amma bazan iya driving ba zansa Zayyad ya kaini train station na biyo train kawai"
"to Allah ya kawo ka lafiya"
Ta faɗa tare da aje wayar
Anty ummi tace
"amma kina ganin idan kika faɗa masa yaji kina da aljani baze ce ya haƙura ba?
Rauda ta sauke numfashi tace
" to ya zanyi Anty ummi, ya zama dole infaɗa masa, idan yaji ze haƙura ba shikenan ba,haka Allah ya ƙaddaromin"
Ta ƙarasa faɗa idanuwan ta na cikowa da hawaye
Umar cikin sauri ya koma office, ko zama beyi ba ya fara tarkata takaddun dake gaban sa
"Zayyad tashi ka kaini train station please"
Cikin mamaki Zayyad yace
"train station kuma? Me zaka yi a can, kai da kake da patients ɗin da suke jiranka a waje?
Umar ya rataya jakar laptop ɗinsa yana duban Zayyad
" zanje Kaduna ne, kuma banajin zan iya driving shiyasa zanbi train"
"Kaduna?
Zayyad ya faɗa da mamaki sannan ya cigaba da cewa
" wai ba shekaran jiya ka dawo daga kadunan ba, me kuma zaka je kayi?
"bangane me kuma zanje inyi ba, kasan dai hakanan bazan tsiri tafiya ba, batare da dalili ba"
Zayyad ya ce
"Umar nifa kwata-kwata bangane maka ba, dan nasan ada sai kayi shekara ko watanni batare da kaje Kaduna ba
Amma tunda kafara son Rauda shikenan kamai da Kaduna kamar nan da wuse
Wai kana cikin hayyacin ka kuwa?
Umar ya Harare sa cike da ƙosawa
" to ba sai ka kaini asibitin mahaukata a duba ni ba, Kaga malan in zaka kaini ka kaini, in kuma bazaka kaini ba nafita na tari taxi drop"
Zayyad ya girgiza kai yace
"a'a muje inkai ka,ƙila takai sunan ka gurin malamai ne shiyasa duk kabi ka susuce"
Gaba yayi batare da ya ƙara kula Zayyad ba
Ƙarfe biyu ya iso Kaduna,da yike tsakanin tashar jirgin da gidan su Rauda Bawani nisa sosai yasa ya ɗauki keke napep ya kawo sa har ƙofar gidan
Ta zura hijabi, fuskar nan tata tayi fayau ga idanuwan ta da suka ƙanƙance saboda kukan da tasha
Tana fitowa suka haɗa ido, gaban sa ne yafaɗi dan yana kallon ta ya gano tsantsar damuwa atare da ita
Be amsa gaisuwar da take masa ba yace
"chuchu faɗamin abunda ke faruwa"
"ya kamata mu zauna tukunna, mu shiga ɗakin waje"
Be ƙara cewa komai ba suka shiga ɗakin da ba komai a ciki sai kujeru guda biyu da kafet
Ta Nuna masa kujera ya zauna sannan ta juya zata fita
"ina kuma zakiji je?
Ya tambaya
" zan kawo ma ruwa ne"
Ya girgiza kai
"a'a dan Allah ki zauna muyi magana, dan ganin ki a damuwa ya ƙara ɗaga min hankali"
Ta zauna a kujerar dake kallon tasa,yayin da shi ya zuba mata ido yana sauraran abunda zatace
Ta rasa ta inda zata fara faɗamai Gabanta ne kawai ke faɗuwa
"ke fa nike saurare Rauda"
Cikin damuwa tace
"bansan ta inda zanfara faɗama bane Umar, ina tsoron yadda zaka fahimci abun, da kuma hukuncin da zaka yanke idan na faɗama"
Ya gyara zaman sa sosai yana kallon ta
"ki faɗamin ko menene Rauda,zan fahimce ki insha Allahu"
Daurewa tayi ta faɗa mai labarin Aasim da kuma halin da take ciki a halin yanzu
Doguwar ajiyar zuciya Umar yayi yana zame hannayen sa daga kan haɓarsa
"wallahi na zata wani babban al'amari ne, da nasan wannan maganar ce ma da ban tada hankali na ba, duk ɗauka ta baba ne yace ya fasa bani ke"
Kallon sa tayi da mamaki a fuskarta tace
"yanzu wannan ba babban al'amari bane Umar?
Ya ɗaga gira sama yana faɗin
" yeah Rauda, ba tun yau ba na daɗe da fahimtar kina da jinnul aashique,kuma ni babu abunda zesa na janye daga neman aranki
Ki faɗa masa cewa neman ki yanzu nafara, alaƙa dake kuma yanzu nasa gaba"
Sororo tayi tana kallon sa
Ya taso daga inda yike ya tsugunna a gaban ta tare da kamo hannun ta
"kinga Rauda, ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru,ni da zaki min wata alfarma ma dakin amince munyi aurannan nan da wata ɗaya"
Zame hannun ta tayi tana jingina bayan ta da jikin kujerar dan ta san Be san waye Aasim bane shiyasa yike faɗar haka
"ba zaka gane ba Umar, ba zaka gane ba"
Ya gyara tsugunnuwar da yayi yace
"menene bazan gane ba Rauda?
Ta Lumshe idonta siriran hawaye na gangaro mata
" Aasim ba kamar aljanun da ka sani bane, yana da matuƙar ƙarfi,kuma ze iya yin komai akanmu"
"duk ƙarfin sa Allah ya fisa rauda, domin Allah shiya halicce mu ya kuma halicce shi, ubangiji shike da iko akan duk kanmu, dan haka babu abunda ya isa ya mana wanda Allah be yi mana ba, akwai wani babban malami da na sani zan faɗa masa nasan ze iya ɗaukar mataki a kansa
Amma kicire fargaban cewa ze raba mu, dan wallahi babu wanda isa ya raba ni dake sai Allah"
Kallon sa kawai take yi amma ta kasa ƙara furta komai
Yayi mata murmushin ƙarfafa gwiwa
"ki yarda dani babu abunda ze faru da izinin Allah, abu ɗaya nike so dake kidage da addu'a
Sannan ki kasance koda yaushe kina cikin alwala da kinji alamar sa kiyi addu'a
Kuma kada ki ƙara tanka masa, duk abunda ze ce miki kiyi banza dashi ya kasance bakin ki ba abunda yike faɗi face ambaton Allah"
Gyaɗa masa kai kawai tayi, yayin da ya miƙe yana faɗin
"yanzu zanje gida inyi wanka sai intafi zaria dan acan malamin yike,dama da mota nazo da daganan na wuce, amma kinga sai naje gida na ɗauki mota"
Ta sauke numfashi tana kallon sa ƙaunar sa na ƙara ƙaruwa acikin zuciyarta,tabbas shi na dabanne dan tabbata da wani ne yaji wannan labarin da yace ya haƙura amma shi ko ɗar beji ba
Katse mata Guntun tunanin da tafi yayi ta hanyar tafa hannun sa
"chuchu Banaso kina wannan tunanin, ki kwantar da hankalinki please"
Ta jinjina kai tare da cewa
"amma shekaran jiya ka koma, kuma yau na saka ka dawo, ka bar zuwa zarian sai gobe kada ka gaji da yawa"
Ya girgiza kai yace
"ai zama be ganni ba Rauda,anjimannan zan tafi"
"Allah ya kiyaye hanya, ya kaika lafiya"
Ta faɗa
Ya amsa da amin yana yin gaba
"Umar!
Ta Kira sunansa ya waigo yana zuba mata kyawawan idanuwan sa
"nagode da ƙaunar gareni"
Murmushi yayi tare da cewa
"kinga karki ƙaramin irin wannan godiyar muje ki rakani"
0 comments:
Post a Comment