_Bismillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
sai da ya watsa ruwa ya sauya kaya sannan ya fito hannun sa rik'e da makullin mota
hasina ce ta biyo sa dasauri tana fad'in
"ya umar inzo inrakaka?
girgiza kai yayi yana cigaba da tafiya
"na hutar dake,nasan rakiyar bata tsakani da allah bace dan asaimiki waya ne"
dariya hasina tayi tace
"kai ya umar amma dai kasan ina raka ka ai ko ba maganar waya ko?
ya jinjina kai
"nadai hutar dake kibari anjima in na dawo sai muje in sai miki"
"owo yaya nagane gurin anty rauda zakaje ko?
juyowa yayi yana kallonta dan tana so ta isheshi da surutu
"kinsan bana son yawan magana ko?allah idan kika ban haushi zan fasa siyan wayar"
dariya hasina tayi tana girgiza kai
"aa yi hak'uri yayana,d'an tsaya ma muyi selfie"
ta fad'a tana k'ok'arin kunna cameran wayanta
umar wucewa yayi ya shiga mota batare da ya k'ara saurararta ba
ana kiran sallar magriba ya isa zaria
ya faka motar a k'ofar gidan malan shitu
tare da fitowa lokacin har sun tada sallah shi da almajiran sa
gorar ruwa ya d'auko a motar ya yi alwala ya k'arasa inda suke sallar
sai da suka idar sannan malan shitu ya tashi dasauri yana d'aukar darduman da yike kai yace
"alhaji umar kaine da yamman nan tashi kan tabar man nan in shimfid'ama darduma"
umar yayi murmushi yace
"aa malan barni kan tabarman"
"aa dan allah tashi alhaji umar tabarma ba wurin zaman ka bane,bare wannan tabarman da ta yayyage"
umar ya kuma yin murmushi yace
"haba malan nida wataran cikin k'asa ma za a turbud'ani miye abun damuwa dan nazauna kan wannan tabarman?
malan shitu ya jinjina kai yace
"shiyasa a kullum kake burgeni alhaji umar sam baka da girman kai irinna masu kud'i ba ka nuna k'yamarka ga talakawa sam"
har lokacin da murmushi a fuskar umar
"bamu gaisa ba malan,ina wuni ya d'alubai"
malan ya amsa da lafiya lau
ya hanya,hala hanya ce ta biyo da kai?
umar ya girgiza kai yace
"aa malan wata y'ar matsala ce ta tasoni wallahi"
malan shitu yace
"subhanallah to allah ya warware mana,tashi mushiga d'aki to"
umar ya mik'e yabi bayan malan suka shiga madai-daicin d'akin
bayan sun zauna malan shitu yace
"ina jinka alhaji meke faruwa"
umar ya sauke numfashi yace
"wallahi malan akan yarinyar da nike nema ne"
ya koro masa bayani dallah-dallah
malan shitu ya sauke numfashi bayan ya gama sauraren bayanin umar
"gaskiya wannan al'amari akwai rikitarwa amma bari muyi isikhara mu gani"
umar ya gyad'a kai yana duban sa kawai
malan shitu ya d'auko carbi yafara ja zuwa can ya nisa yace
"gaskiya alhaji umar da zakaji shawarata da ka hak'ura da wannan yarinyar saboda akwai sark'ak'iya sosai acikin al'amarinnan"
umar ya sauke ajiyar zuciya
"malan bazan iya hak'ura da ita ba,dan ina sonta fiye da yadda kake tunani idan da mafita da kuma yadda za'ayi ayi kawai"
malan ya gyad'a kai yana kuma d'aukar carbin sannan yace
"dan mafita za asamu mafita da izinin allah amma fa za a sha gwagwarmaya sosai"
umar ya gyara zama yana k'ara fuskantar malan shitu
"malan ashirye nike da in fuskanci duk wata gwagwarmaya indai akanta ne,dan haka karkaji komai indai akaina ne,kai dai kayi duk abunda kaga ya dace dan allah ga wannan ayi duk sadakokin da za'ayi"
ya k'arasa fad'a zaro bandir d'in kud'i ya aje a gabansa
malan shitu ya jinjina kai yace
"insha allah zamuyi abunda zamu iya amma kaima fa sai kadage da addu'a sosai,musamman inzaka kwanta allah ya shige mana gaba"
"amin"
umar ya fad'a yana mik'ewa yace
"to ni zan wuce malan saboda kar dare yayi"
malan ma ya mik'e yace
"shikenan alhaji umar allah ya kiyaye hanya duk abunda ake ciki zankira ka in sanar dakai insha allah"
bayan kwana uku,bata k'ara jin d'uriyar Aasim ba hakan yasa taji tad'an rage fargaba dan umar be koma abuja ba kullum sai yazo ya kwantar mata da hankali
yauma suna tare ya d'auko wata leda ya bud'e wacce malan shitu ya aiko mai dashi
ya d'auko wasu turaruka da wani mai a wata kwalba ya mik'o mata yana fad'in
"d'azu malan shitu ya aiko dasu yace kifara amfani dasu a yau........
dagatawa yayi yana kallon yadda ta toshe hanci dan yana bud'e ledar taji wani mugun wari ya bugi hancin ta
"miye haka kuma?
ya tambaya idanuwansa akanta
"dan allah ka rufe ledar wallahi wari"
ya kalli ledar dan shi sam beji wani wari ba
"wari kuma?
ta d'aga kai tana k'ara toshe hancin dan ji take warin na kuma k'aruwa
"allah wari ka rufe kar inyi amai please"
ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idanuwan sa na kanta
"chuchu baki son hankalin mu ya kwanta ko?
cikin rashin fahimta tace
"kamarya jaana"
ya jinjina kai yace
"eh mana,kinsani muna cikin matsala amma kuma na kawo magani kina toshe hanci"
ta jingina da kujerar motar
bata re da ta k'ara cewa komai ba
"ki amsa maganin kisha fa sa yanzu a gabana"
d'an zaro ido tayi tana kallon sa
"inshafa fa kace"
ya d'aga kai
"eh ko bazaki shafa bane?
ta girgiza kai ahankali tare da cewa
"bawai bazan shafa bane,amma warin maganin yayi yawa"
ya gyara zamansa sosai yana fuskantar ta
"Rauda nasan bazaki ji dad'in amfani da magungunan nanba sam,amma ya zama dole ki daure ki duba damuwar da nike ciki dan allah "
ta sauke numfashi tare da zame hannayenta da toshe hancin dasu
ta amsa
murmushi umar yayi yace
"yauwa matar kirki nasan dama bazaki yimin musu ba"
dauriya kawai take yi dan warin maganin nema yike yi ya hautsina ta
"ya zanyi amfani da shi?
"kinga wannan idan zaki kwanta zaki shafa,wannan kuma da rana sai wannan hayak'i ne.........
ya d'an dakata ganin yadda take mashau-mashau da idanu
"lafiya chuchu?
ya tambaya,ta bud'e idanuwanta da suka fara yi mata nawi saboda sarawar da kanta ya fara yi mata
"kaina ke min ciwo"
cikin tausayawa yace
"sannu ze dena kinji,kiyi hak'uri dama malan yace dole zakiji haka"
kad'a kai kawai tayi tana bud'e turaren ta shafa a goshinta kamar yadda yace
wani kalan nawi taji goshin ya mata kamar an d'aura mata dutse
lumshe idanuwanta tayi tana ambaton sunan sa
"umar!
ta kira sunan cikin wani irin yanayi
gabad'aya tausayinta ya kamasa,
ya amsa yana jin kamar yadawo da ciwon da take ji jikin sa
"jikina na bani kamar wahalar da kanmu kawai zamuyi baza.......
katse ta yayi
"kada ki k'ara fad'in haka,insha allahu zamu yi nasara"
gyad'a kai kawai tayi amma ita zuciyar ta ta karaya
"please rauda kiyimin alk'awarin duk rashin dad'in maganinnan zaki daure kiyi"
ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali tana jinjina kai
"zanyi insha allah"
b'angaren Aasim kuwa yana zaune yana kallon su ta madubi
guntun murmushi yayi yana shafa sumar kansa had'i da kallon ummu salma wacce ya d'aure da wasu mugayen igiyoyi
"tabbas kin tafka kuskure da kikai tunanin wani k'aramin alhakin turaren ki zeyi tasiri akaina,kin manta waye Aasim ne amma zan tunatar dake yanzu"
cikin tashin hankali da rud'ani ummu salma tace
"ka gafarceni ranka shidad'e kayi min afuwa nasan nayi kuskure ka yafeni dan allah"
hannunsa ya sa yayi nuni da ita sai ga wani haske ya fito ya caki k'irjinta
tasaki wata razananniyar k'arar azaba
ya mik'e yana kallonta da razanannun idanunsa
"zaki kasance a haka har tsawon kwana bakwai,kinga gobe bazaki sake tunanin shiga gona ta ba"
yana gama fad'ar haka ya b'ace
gurin rauda ya nufa kai tsaye lokacin ta shiga gida dan umar aranar yike so ya koma abuja
tana zaune tana k'ok'orin shafa turarukan da maganin taji tsayuwar sa agabanta
d'ago kanta tayi da sauri suka had'a ido
gabanta ne yafara fad'uwa ganin kallon da yike mata
"habibty intayaki shafawa ne?
ya tambaya yana yimata wani shu'umin murmushi
runtse idanuwanta tayi dasauri tana karanto duk wasu addu'o i da suka zo bakinta
zaunawa yayi kusa da ita yana amsar turaren hannunta yana juyawa
"kinyi shuru ko baki so intayaki ne?ba rabuwa kikeso kiyi dani ba ince wannan.shine maganin da akace miki ze rabaki dani?
har lokacin addu a kawai take karantowa kamar yadda umar yace tarink'a yi aduk sanda yazo
murmushi ya kuma yi yana rausayar da kai
"ohh na tuna saurayinki yace kidena tankamin ko?
*~y'arfillo~*
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 2⃣9⃣
_2:28_🕒 PM
MON,JUL 22
_Bissmillahir rahmaninr rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"wato da nabaki lokaci ki yanke duk alak'ar dake tsakaninku shine kike neman ma rabuwa dani ko?
wallahi kinbani mamaki bantab'a tunanin haka daga gareki ba,na d'auki amana.da yardata na baki amma a k'arshe ni zaki watsa wa wa k'asa a ido"
hmmmm ya k'arasa fad'a yana sauke numfashi sannan ya cigaba da cewa
"Rauda kisani bazan tab'a rabuwa dake ba,kuma bazan tab'a bari wani namiji ya rab'eki ba,kada ma ki wahalar da kanki wajen yin maganin da ze wahalar dake domin banga maganin da zeyi shamaki atsakanina dake ba,
sannan kisani kina d'auke da cikina a tare dake dan haka kibi ahankali wajen yin amfani da wasu magungunan da zasu iya cutar min da yaro ina fatan kingane?
bud'e idanuwanta tayi sosai tana kallon sa
yayinda ya mik'e ya durk'uso saitinta gami da sa hannu akan cikinta ya shafa
"ki kulamin da yarona sosai"
be jira jin me zatace ba ya b'ace
"nashiga uku!
ta fad'a tana duban cikin,wasu hawayen tashin hankali suka fara biyo kuncinta
kwantawa tayi zuciyarta cike da tsananin damuwa
washegari umar na zaune a office bayan yagama duba iya adadin patient d'in da yace ze duba
kulle office d'in dan yana buk'atar ya huta sakamakon rashin baccin da bayayi kwana biyu dan duk dare tashi yike yi yay ta kai kukansa ga ubangiji akan wannan matsalar
wani sak'o ne ya shigo wayar sa ya bud'e yana dubawa
tsaki yaja ganin wasu kalar shirmen rubutu da besan ko na menene ba
d'agowa yayi ze aje wayar karaf idonshi yayi gamo da Aasim wanda ke zaune a kujerar dake gaban tasa
kallonsa umar yayi da mamaki dan shi sam beji shigowar mutum ba hasali ma k'ofar office d'in a rufe take to ta ina ya shigo?
yayi wa kansa tambayar
Aasim yayi murmushi tare da mik'amai hannu yana mai sallama
umar ya amsa kawai batare da ya mik'a masa nasa hannun ba
Aasim ya janye hannunsa yana cewa
"kayi hak'uri nashigo ma office batare da izinin ka ba"
umar ya gyad'a kai yace
"ok meke tafe dakai?
Aasim ya gyara zama
"kamata yayi kafara tambayar waye ni,kafin ka tambayi abunda nazo dashi"
umar ya jinjina kai
"to inajinka waye kai?
"sunana Aasim mijin wacce kake neman aure"
umar ya kallesa da sauri mamaki k'arara a fuskar sa,amma ko kad'an beji wani tsoro ba
hasalima d'an murmushi yayi
Aasim ya cigaba da cewa
"nazone inyi maka gargad'i cikin lalama,ka rabu da matata dan zan iyayin komai akanta"
umar ya sauke ajiyar zuciya yace
"naji dad'in zuwanka da kuma yadda kazomin cikin salama,hakan ya tabbatar min da kana da sauk'in kai
amma ina so kasani bazan iya rabuwa da rauda ba domin inason ta fiye da yadda kake tunani"
Aasim yayi murmushin takaici
"ba damuwa ta bane yawan son da kake mata,dannasan babu wanda zeso rauda fiye dani aduniya,inaso karabu da ita ayau ba sai gobe ba"
umar ya sauke numfashi yana girgiza kai
"bazan tab'a rabuwa da ita ba,domin itace zab'ina"
Aasim ya kad'a kai yace
"shikenan ni zan rabaka da ita dole,kashirya ma shiga tashin hankali kasa aranka cewa daga yau kun k'ulla abota da damuwa"
umar ya kad'a kai
"indai akanta ne,nashirya taryan komai"
Aasim ya mik'e yana jinjina
"shikenan mu zuba ni dakai"
numfashi me nawi umar ya sauke bayan b'acewar Aasim
yasa handkerchif ya share gumin da yafara tsattsafo masa tabbas wannan abun bana zama bane
zaro wayarsa yayi ya kira malan shitu ya sanar dashi
daga can b'angaren malan shitu yace
"gaskiya al'amarinnan me girma ne,amma ina ganin zanje gurin wani kakana gobe dan yana da lak'anin da yafi nawa inyaso sai muji abunda zece shi"
umar yace
"shikenan malan dan allah ka k'ok'arta"
sukayi sallama ya ajiye wayar
haka suka cigaba da gwagwarmaya,har na tsawon wata d'aya amma babu canji
inbanda wahala ma babu abunda rauda kesha,dan arana sai tayi suma fin biyar
babu wanda besan matsalar da ake ciki ba a gidan
rauda ta rame sosai,dan ita kad'ai tasan azabar da take sha dan Aasim yace muddin bata rabu da umar ba to bazata samu sassauci ba
b'angaren umar ma kullum cikin kawo masa farmaki akeyi,amma da yike jarumi ne shi kuma yana tsaye da addu'o i shiyasa shi nashi ya zo dasauk'i
duk inda sukaji wani malami sai sunje amma a banza,dan babu abunda yike canzawa
ga lokacin biki k'ara matsowa yike yi
gabad'aya sun fita hayyacinsu babu wanda be rame ba
wahalar da rauda ke sha tafi komai d'aga ma umar hankali
ranar wata alhamis umar yazo,kai tsaye yayi sallama yashigo falon mama dan yanzu ba maganar fita waje
da ta tashi zata fita zata zube,hakan yasa dole inyazo yike shigowa ciki
mama ta kawo mai ruwa sannan suka fara gaisawa
ya k'ara da tambayar me jiki
mama ta amsa da
"da dauk'i,d'azu dama nike niyyar nace a kira ka,wata k'anwar babansu tace akwai wani malami acan k'auyen yola kuma yanayin irin wannan aikin ana dacewa"
umar yace
"to mama ai babu matsala,yaushe kike ganin ya kamata atafi"
"zuwa lahadi"
umar ya sauke numfashi yace
"mama lahadi beyi nisa ba,me ze hana atafi asabar?
mama ta kallesa da tausayawa tace
"amma saidai kabari muje ko,kai ka huta dan.zirga-zirgan da kakeyi tayi yawa"
umar ya girgiza kai
"aa mama tare zamu tafi,babu damuwa ai"
mama ta sauke ajiyar zuciya tace
"shikenan,allah ya kaimu asabar d'in
bari na mata magana tafito"
ta k'arasa fad'a tana mik'ewa tashiga uwadd'aka
rauda na kwance kan gado ta dunk'un k'une da bargo
mama tace
"zaki iya fitowa falon?
Rauda ta girgiza kai
"bazan iya ba,gaba d'aya jikina nuk'urk'usa yike yi"
mama ta sauke numfashi,ta d'auko darduma ta shimfid'a mai a gefe sannan ta dawo falon tace
"shigo daga cikine,wai bazata iya fitowa ba"
amsawa yayi da to,ya mik'e cikin ladabi ya shiga uwadd'akan yana sallama
amsawa tayi da muryarta da tayi k'asa-k'asa
ya zauna yana kallonta
zuciyarsa cike da tsananin damuwar halin da take ciki
"sannu chuchu ya jikin?
"da sauk'i"
ta amsa tana duban yadda shima ya rame
ji tayi idanuwanta sun cicciko da hawaye tayi k'ok'arin shanye su amma takasa sai da zubo
shiko umar hankalinsa ne ya k'ara tashi
"chuchu me yafaru?ina ne ke miki ciwo kuma?
girgiza kai tayi ahankali tare da cewa
"ina tausayin ka ne umar,saboda ni ka rasa sukuni,karasa kwanciyar hankali"
umar ya sauke ajiyar zuciya yace
"ni banason ganin hawaye a fuskarki yana k'ara tada min da hankali,dan allah kibari"
hannu tasa ta share hawayen tanajin zuciyarta wani iri
mama ta shigo da kwanan abinci ta ajiye tana fad'in
"tun safe nike fama da ita tak'i cin komai,k'ila kai idan ka tursasata zata ci"
tana gama fad'a ta fice
"me yasa kika k'i cin abinci?
ya tambaya idanuwansa akanta
"banajin cin komai ne shiyasa"
ya bud'e kwanon yace
"to tashi kici yanzu bazeyuwu ki zauna da yunwa ba"
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣0⃣
_wannan page na kune *fans*,hak'ik'a sharhin ku na burgeni kuma yana k'ara k'arfafamin gwiwa,kuna burgeni irin sosai d'innan_
_5:13_🕒 PM
MON,JUL 22
_Bissmillahir rahamanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
daurewa tayi ta tashi ta zauna ya mik'a mata plate d'in abincin
dan bazata iya yi mai musu bane kawai yasa ta amsa tafara ci amma zahiri ji take kamar tana cin magani
kad'an taci ta ajiye plate d'in tare da komawa ta kwanta tana kuma jan bargon
ji yike yi kamar ya janyota jikinsa amma babu hali
hak'ik'a ayanzu k'aunar ta ta zame masa wani sashe na jikinsa
be bar gidan ba sai goma saura,
b'angaren Aasim ma gabad'aya baya cikin natsuwar sa,kullum fata yike rauda tace ta fasa auran umar dan shima bada son ransa yike mata abunda yike mata ba
yana yi ne kawai dan ta janye a kan k'udurinta amma gashi har lokacin bata da alamar janyewa
a gaban gadon da take kwance ya bayyana lokacin har tayi bacci
ya zaune gefen gadon tare da tsura ma kyakkyawar fuskarta ido
wani irin tausayinta ne ya k'ara dabai baye zuciyar sa
a hanakali ya furta
"me yasa Rauda? me yasa zaki zab'i kiyi ta wahala?
ina sonki,ina k'aunar ki bazan iya jurar ganin ki cikin wannan halin ba,ba zan iya ba habibty"
ya k'arasa fad'a cikin yana yin damuwa
kwantawa yayi kusa da ita ya rungumeta ta baya tare da sauke wani numfashi me nawi
tabbas rauda itace farin cikin rayuwar sa,taya ze bari wani ya rab'e ta
lumshe idanuwansa yayi wad'anda suka rine saboda tsananin damuwar da yike ciki
"please Rauda kada ki gujeni,bazan iya rayuwa idan babu ke ba,ki.kasance tare dani dan allah"
ya k'arasa fad'a yana k'ara matse ta a jikinsa
washegari umar ya shirya komai na tafiya yola driver ya samu wanda ze kaisu ya dawo dasu
ranar asabar dawuri suka tafi dan tara dai-dai suka fita
tafiyar awa hud'u sukayi suka isa yola,wani restaurant suka fara tsayawa
kafin su shiga k'auyen,mama da goggo hanne ne suka fara yin gaba
umar da rauda suna biye dasu
ahankali-ahankali take tafiya dan jikinta babu k'wari
umar kallonta kawai yike yi da tausayawa
mama can gefe suka zauna aka kawo musu abinci yayinda umar da rauda ma suka zauna daga can gefe
duka su biyun tsakurar abincin suke yi dan sam basa jin wata yunwa
ta ajiye cokalin tace
"jaana nifa na k'oshi"
shima aje nasa cokalin yayi yana fad'in
"wallahi nima haka,abincin ma babu dad'i ko na nemo mana abu me ruwa ne?
ta jinjina kai
"amma kafinnan inaso ind'an shiga bayi"
wata ma'ai kaciyar wurin ya kira yace ta nuna mata bayin shi kuma ya tafi inda ake saida drinks
Rauda ta tura k'ofar bayin ta shiga cikin y'an mintoci tagama abunda zatayi
alwala tayi ta maida hijabinta sannan ta murd'a k'ofar
saidai ta jita gam,ta kuma murd'awa amma taji k'ofar a gark'ame
jijjiga k'ofar tafarayi amma shuru
tsoro ne ya fara kamata yayinda taga bayin ya fara duhu
ta k'ara jijjiga k'ofar
tana fad'in
"azo a bud'e!
amma da alamun babu wani a kusa da bayin
motsi taji a bayanta ta waiga da sauri amma bata iya ganin komai dan bayin yayi duhu dund'um
baki ta bud'e zata kurma ihu
taji anrufe mata bakin
hankalinta ya k'ara tashi,k'ok'ari take ta b'anb'are hannun da ya toshe mata bakin amma takasa
wani irin juyewa kanta yafara yi,zubewa tayi awurin a sume
umar tunda ya dawo wurin yike duba agogon wayar sa,ganin anfara kiran sallar magriba gashi har lokacin bata fito ba
goggo hanne ce ta kalli mama tace
"k'auyen nan fa da nisa,ga duhu nayi "
mama tace
"bari naje bayin nace mata tayi sauri,nima bana son tafiyar dare wallahi"
mama ta mik'e tana tambayar wata ma'aikaciyar wurin
"dan allah ina bayin ku yike?"
nuni tayi mata da hanyar bayin,mama ta k'arasa wurin bayuka uku ne,biyu a bud'e alamar babu kowa aciki
sai d'ayan da yike a rufe,k'wank'wasa k'ofar mama tayi tana fad'in
"wai Rauda me kike yi a bayine haka tund'azu "
shuru taji,ta d'an saurara ko zata ji motsin ruwa amma bataji ba
hakan yasa ta murd'a k'ofar
babu kowa a cikin bayin,ta dawo baya kad'an tana nazarin ko akwai wani bayin awurin amma da alamu bayukan kenan
ta dawo wurin ma'aikatan wurin tana tambayar su
"dan allah kuna da wasu bayuka ne bayan wa'ancan?
d'aya daga cikin su ne ta girgiza mata kai
"aa wani abune"
mama tace
"yarinya ce tace zata zaga tund'azu to munji ta shuru shine nai tunanin ko banan ta shiga ba,dan na duba bayukan banganta aciki ba"
"to saidai in wani wurin tayi,danni dakaina na rakata har k'ofar bayin amma muje wurin bayin nagani"
d'ayar tafad'a,komawa ko sukayi sai dai babu alamunta,hankalin mama yafara tashi
da sassarfa ta dawo cikin wurin inda umar yike tace
"kaga fitowar rauda kuwa?
umar ya girgiza kai
"aa "
"to ina tashiga?na duba bayukan wurin gabad'aya bata ciki"
"bata ciki?to ko.sallah taje tayi?
umar ya tambaya da d'anmamaki
mama tace
"to ai da tanan dai zata wuce tunda naga wurin sallar nasu a waje yike"
umar ya sauke numfashi yace
"bari naduba waje to ku k'ara duba cikin ko da tafito bamu lura bane"
babu inda ba a duba ba awurin ba alamar Rauda ba hankalin su mama kad'ai ba har na ma'aikatan.wurin sai da ya tashi
lungu da sak'on wurin babu inda ba a duba ba
A hankali tafara bud'e idanuwanta,harta bud'esu gabad'aya slip d'akin tafara kallo daga bisani ta saukar dasu k'asa
kan wani k'asaitaccen gado ta ganta,mamakine ya kamata ita da take bayi ya akai taganta a kan gado
ahankali k'wak'walwarta ta tariyo mata abunda ya faru
tashi tayi da sauri tana kalle-kalle babu kowa acikin d'akin
wata k'ofa tagani,ta diro daga kan gadon dasauri ta nufi k'ofar
Aasim ta hango tsaye yana jera abinci kala-kala akan wani had'add'en dining table
"barka da tashi habibty"
ya fad'a da murmushi a fuskarsa
kallonsa kawai take yi amma takasa furta komai,ya k'arasa inda take ya tsaya gab da ita had'i da d'aura hannun sa akan wuyanta
"zazzab'in jikinki ya sauka ko? nasan kina jin yunwa me kikeso kifara ci"
ture hannun sa tayi tana kallonsa da idanuwanta da suka fara ciccikowa
"ina ne nan ka kawoni?
"ina ne?tambaya kike yi?to gidana ne gidanki kuma inda zakiyi rayuwa ta har abada"
hawayen da suka cika idonta suka fara gangarowa
"me kake nufi Aasim,me kake nufi da kawo ni nan?
"kinga muje kici abinci,sannan kimin tambayoyin"
yafad'a yana kama hannunta tare da yin gaba
fizge hannun tayi tana durk'ushewa k'asa tare da had'e hannayenta wuri d'aya
"narok'eka ka maidani inda ka d'auko ni,kabar ni nayi rayuwa da wanda nike so"
murmushin takaici yayi yana cigaba da tafiya ya zauna kan wata kujera yana kallonta kawai
ita ko kuka ta cigaba dayi tana cigaba da magiya
"umar shine zab'ina kataimakeni ka rabu dani,kaje kasamu jinsinka dan allah"
tasowa yayi ya dawo gabanta ya durk'usa yana kallonta da idanuwansa da suka fara rinewa
"Rauda!"
ya kira sunanta,kallonsa kawai takeyi amma ta kasa amsawa
"agabana kike fad'amin wani ne zab'inki ko?kuma inrabu dake ko?
ya kad'a kai yana cigaba da cewa
"to kisani wallahi tallahi babu abunda zesa inrabu dake,rayuwa dake yanzu nafara"
kuma fashewa tayi da kuka tana fad'in
"nidai kamaidani inda ka d'auko ni"
ya mik'e yana yi mata wani mugun kallo
tare da yimata nuni da k'ofar fita
"ga hanya nan ban hanaki tafiya ba ai"
yana gama fad'a ya juya ya bar wurin
kuka takeyi sosai dan tasan umar da mama suna can hankalinsu a tashe
mik'ewa tayi ta nufi k'ofar da ya nuna mata,ta murd'a dajine sosai me dogayen bishiyoyi
*~y'arfillo.~*
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣1⃣
_wannan page nakine *karima keffi*,ina godiya da k'aunarki gareni allah ya bar zumunci_💛💛
_3:07_🕒 PM
THU,AUG 1
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
dajine sosai me dogayen bishiyoyi inbanda kukan tsintsaye babu abunda take iya juyowa
zamewa tayi awurin wasu sababbin hawaye na kuma ambaliya a fuskarta
umar ko na can hankalinsa inyayi dubu ya tashi har jami'an tsaro aka kira aka had'u dasu aka cigaba da nemanta amma shuru
goggo hanne ta kira malamin da zasu je wajen sa ta sanar dashi
yace su ma dena bawa kansu wahala dan ba mutum ne ya d'auke ta ba suk'arasa k'auyen kawai
tafi k'arfin awa biyu durk'ushe awurin gabad'aya k'wa-k'walwarta nema takeyi ta dena aiki,ganinta takeyi wani iri takasa gasgata cewa rayuwar da take yi da gaskene
ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana kallon sararin samaniya da taurari sukamasa ado
a hankali ta furta
"ya allah ka taimakeni kafitar dani daga wannan rayuwar"
ta k'arasa fad'a wasu siraran.hawaye na biyo kwarmin idanuwan ta
Aasim yana tsaye yana kallonta gabad'aya jin zuciyar sa yike yi babu dad'i sam baya so ya ganta cikin damuwa
bayyana yayi a gabanta ya durk'usa tare da zuba mata kyawawan idanunsa
itama zuba masa nata idanun tayi da suka jik'e da hawaye
"Rauda wai shin bazaki fahimci k'aunar da nike miki bane?
ya fad'a da damuwa sosai a fuskar sa
"ina k'aunarki kece farin ciki na,dan allah ki rayu dani ni kad'ai nayi miki alk'awari zansaki farin cikin da babu wata mahalukiya da zata fiki jin dad'i a duniya"
ya d'an numfasa yana zaunawa dirshan a gabanta
"miye umar yike dashi wanda bana dashi?ki fad'amin kisani ayanzu babu siffar bazan iya yi ba,zan iya yin komai domin insaki farin ciki..........
katse shi tayi ta hanyar d'aga masa hannu
"idan har kana sona,kuma son da kakemini na gaskiya ne to ka ky'aleni in auri jinsina,naji na amince muciga ba da rayuwa a sirrance amma kabarni na auri umar "
"inbari inga kina rayuwa da wani a matsayin miji? bazan iya ba"
ya fad'a yana girgiza kai sannan ya cigaba da cewa
"kinsan zafin da nike ji a duk sanda naga umar tare dake? kisani zan iya mutuwa a duk ranar da wani mahakuli ya kusance ki,dan haka ki ajiye maganar aure arayuwar ki dan bazan tab'a amincewa ba"
jinjina kai tayi cikin tsananin damuwa,tasa hannu ta share fuskarta tana fad'in
"shikenan Aasim nasan bani da ikon saka ko hanaka,kayi duk abunda kayi niyya kada kabari wani ya rab'eni
amma kasani gangar jikina ce kad'ai zaka cigaba da rayuwa da ita dan zuciyata tana ga umar,ayanzu shine mallakinta.......
runtse idanuwansa yayi dasauri dan jin maganarta yayi kamar wani mashi ya cake sa
ya bud'e su a wahalce yana d'aurasu akan kyakkyawar fuskarta
hannunsa yasa ya janyo ta da k'arfi tare da matseta gam a jikinsa
"duk abunda zaki ce sai dai kice,amma bazan tab'a lamuncewa da wani ya rab'eki ba"
ta janye jikinta kad'a kai
"shikenan,kayi yadda kake so dani,nasan allah yana tare dani kuma nasan wata rana zeyi min maganin komai"
ze kuma janyo ta ta d'aga masa hannu
"kada ka k'ara tab'ani"
ajiyar zuciya ya sauke me nawi tare da mik'ewa ya bar wurin
*** * *** ***
bayan kwana biyu,addu a malan isa yasa almajiran sa suka duk'ufa yi,tare da saukar al qur ani
shima be zauna ba,ya duk'ufa sosai haka umar ma da ko abinci ba iya ci
cikin ikon allah aikin da malan isa ya farayi ya fara nasara
ranar ma suna zaune,gaban malan isa wani k'ok'o ne me ruwa aciki
addu'o yike karantowa sosai,cikin ikon allah saiga Rauda ta bayyana aciki lokacin tana zaune ta d'aura kanta bisa gwiwowinta
aka ci sa a ko,Aasim bayanan
kallonta kawai su mama sukeyi da mamaki k'arara a fuskarsu ganin irin had'add'en.wurin da take me kama da aljannar duniya
malan isa ya sauke numfashi yace
"tabbas inda take ba k'aramin wuri bane,kuma ba k'aramin nisa yike dashi ba,nasan ayanzu idan ni na kirata zataji tsoro saboda bata san muryata ba,dan.haka kai umar matso kusa da k'waryar ka kira sunanta da k'arfi"
umar ya matso jikinsa har rawa yike yi ya kwad'a mata kira
"Rauda!!
d'ago kanta tayi da sauri jin ankirata da kuma muryar umar,sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana maida kanta dan tasan ba dai-dai kunnenta yajiba
malan isa yace
"ka kuma kiranta kagayamata kaine"
umar ya kuma kiranta a karo na biyo
d'agowa ta kuma yi,da mamaki a fuskarta
"Rauda kina jina,nine umar"
mik'ewa tayi a zabure,tana kalle-kalle
"umar! kana ina ne?"
malan isa ya matso gab da k'waryar yace
"bazaki iya ganinsa ba amma mu muna ganinki,muna so muyi komai cikin gaggawa kafin Aasim ya dawo dan.haka ki natsu kiji abunda zan.fad'amiki"
jinjina kai tayi dasauri
"fad'i inaji"
malan isa ya sauke numfashi yace
"a yanzu rafanan da nike dasu bazasu iya shigowa inda kike ba,dan haka dole kifito daga cikin wannan gidan kiyi tafiya zuwa inda wata bishiya take"
kad'a kai tayi,tana yin hanyar waje kai tsaye
ta murd'a k'ofar ta bud'e,kallon dajin tayi gabanta na fad'uwa
malan isa yace
"dole ki hanzarta fa,dan ze iya dawowa a kowani irin lokaci"
ta gyad'a kai tana diro k'afarta d'aya k'asa
d'aga k'afar tayi dasauri jin ta taka wasu k'ayoyi masu zafin gaske tare da sakin wata y'ar k'ara
cikin tashin hankali umar yace
"me yafaru chuchu"
"bazan iya tafiya awurinnan ba,gaba d'aya wurin k'ayoyine"
malan isa yace
"ki daure dan wannan ita kad'aice damar da muke da ita,idan har ta kufce to ni gaskiya babu wani abun da zan iyayi kuma"
takawar tafara yi tana runtse idanuwanta saboda tsananin azabar datake ji a tafun k'afafun nata
ko rabin wurin bishiyar bata kaiba ta tsaya tana girgiza kai hawaye masu zafi na biyo kumatunta
"bazan iya cigaba da tafiya ba,bazan iya ba"
cikin tsananin tausayinta umar yace
"Rauda ki daure dan allah,kinji malan yace wannan ce kad'ai damar da muke da ita"
jinjina kai tayi wasu hawayen na ambaliya a fuskarta,ta cigaba da tafiyan
kafin takai gurin bishiyar ta galabaita dan tana kaiwa ta zube
malan isa yace
"yauwa alhamdulillah bari natura su yanzu"
wani turare ya d'auko ya d'iga acikin k'waryar
saiga wani hayak'i ya fara fita
umar ganin ya dena ganinta cikin k'waryar yasa hankalin sa ya k'ara tashi
"ya naga nadena ganintame ya faru kuma"
murmushi malan isa yayi yana masa nuni can bayansa
umar ya kalli wurin da sauri,Rauda ya hango kwance
tashi yayi ya k'arasa wurin sauri yana kiran sunanta
mamako hannu ta d'aga tana yima allah godiya
Rauda ta bud'e idanuwan ta da suka k'ank'ance saboda tsananin wahalar da ta sha ta d'aurasu akan umar
"sannu Rauda,ya kike jin jikinnaki....
malan isa ne ya katseshi
"malan umar bamu.da lokaci dan na tabbata Aasim na iya zuwa ayanzu,dan haka dole mu shirya cikin gaggawa"
umar ya jinjina kai
malan ya mik'a ma mama wani ruwan rubutu yace
"bata tasha yanzu"
mama ta tallabota ta bata tatasha,aiko tana sha taji cikinta yafara wani irin hautsinewa
Aasim yana tsaye cikin katafariyar kasuwar su,tunani yike me ze siya ya kaimata wanda ze sa ta farin ciki
wani rauhani ne ya k'arasa inda yike ya rusuna cikin girmamawa yace
"ranka shidad'e me kake da buk'ata"
Aasim ya sauke numfashi yace
"ina kan nazari ne tukunna"
ya k'arasa fad'a idanuwansa na sauka akan wasu sari had'e da wasu gwala gwalai masu masifar kyau
"yauwa ina buk'atar wa'ancan"
rauhanin ya mik'e ya d'auko ya mik'amai cikin girmamawa
b'acewa yayi,ya bayyana a falonsa inda ya barta
mamakine ya kamasa ganin be ganta a falon ba,ya lumshe idanuwansa
yana ganin abunda yafaru,bud'esu yayi dasauri
yana furzar da wata iska me zafi
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:45 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣2⃣
_wannan page nakine *fatima batula*,na sadaukar dashi gareki kiyi yadda kike so dashi_
_*gaisuwa da fatan alkhairi*_
_*ga duka marubutan mu na golden pen,hak'ik'a ina jinjina muku da kuma alfahari daku a koda yaushe*_
_12:04_🕒 PM
FRI,AUG 2
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
cikin tsananin b'acin rai da tashin hankali ya bayyana a gidan malan isa
kai tsaye ya danna kai ze shiga d'akin da suke amma wani turari me zafin gaske yasa yayo baya da sauri
kallon d'akin yafara yi da wani irin mugun wari ke fitowa daga cikinsa
ya kutsa kai cikin d'akin yana runtse idanunsa dan ji yayi wani zafi ya ratsasa kamar wuta
gabad'ayan su addu'a suke karantowa,banda Rauda da tayi lamo jikin mama tana jin k'wak'walwar ta kamar zata juye
akanta Aasim ya sauke idanun sa da suka kad'a sukayi ja
cikin zafin nama ya finciko ta yana kallon cikin idanunta
"meyasa zaki min haka,meyasa!
nafad'amiki cewa da akwai d'ana a jikin ki,meyasa zaki biye musu kisha wannan bak'in rubutun?
ya tambaya cikin fusata,ta kasa bashi amsa inbanda lumshewa babu abunda idanuwanta suke yi
maida idanunsa yayi kan malan isa da har lokacin yike ta kwararo addu'o
"narantse da allah idan har kayi sanadiyyar rasa d'ana sai ka d'an-d'ani kud'arka"
malan isa yayi ma Rauda nuni da hannu,alamar tayi abunda yasata
da k'yar ta iya bud'e bakinta ta feshe Aasim da turaren data guntsa
baya yayi dasauri yana sakin wata k'ara
ita ko inbanda rawa babu abunda jikinta yike yi
wasu kalar sark'ok'i ne suka bayyana suka d'add'auresa
wani kalar kallo yike mata me cike da mamaki
"Habibty,dake za a had'a baki amin haka?
zuciyar tace tafara karyewa ta durk'ushe awurin tana fashewa da kuka
malan isa ya sauke numfashi dan sai lokacin hankalinsa ya kwanta da yaga yayi nasarar kama sa
"duk zaune,ku kuma natsu,ina fatan yanzu zaka tsaya muyi magana ta fahimta"
ya k'arasa fad'a yana kallon Aasim
Aasim kallon Rauda kawai yike yi,yana jin zuciyarsa nayi masa wani irin rawa
"meyasa ka takura ma rayuwarta,me ta maka da ka addabi rayuwarta?
Aasim be bashi amsa ba,dan sam hankalinsa ma baya wurinsa
malan isa ya cigaba da cewa
"ina so ka rabu da ita,ka nisanci rayuwarta"
wani mugun kallo Aasim ya masa tare da cewa
"kada ma ka b'ata bakinka gurin fad'in inrabu da ita dan bazan tab'a rabuwa da ita ba har abada"
malan isa yace
"akan mene bazaka rabu da ita ba,bayan.kasan kasancewar ka tare da ita cutarwa ne a gareta?
"saboda itace farin cikina,matata kuma uwar y'ay'ana"
ya fad'a yana wurga masa wata muguwar harara
malan isa ya jinjina kai
"amma kasan aure be halatta a tsakaninku ba,akan mene bazakaje gurin jinsinka ba?
Aasim yace
"wannan ba damuwar ka bace,ita nagani na zab'a da kuma ita kad'ai zanyi rayuwa"
numfashi malan isa ya sauke yace
"to ina had'aka da allah,da ka furta ka rabu da ita ka kuma yi alk'awarin bazaka sake rab'arta ba"
Aasim ya girgiza kai yana ware idanunsa sosai
"kasani bazan tab'a rabuwa da ita ba"
malan isa ya kuma jinjina kai
"shikenan idan ba zaka rabu da ita dan allah ba,zamu rabaka da ita da ikonsa insha allahu"
ya k'arasa fad'a yana d'auko wata k'warya da ya cikata da rubutu da ruwan addu'a
ya d'iba ya watsa masa
wani irin k'ara Aasim yayi cikin gigita ya kallesa da mamakin wani irin abu ya sa acikin k'waryar da har yayi tasiri ajikinsa
malan isa ya kuma d'iban ruwan ya kuma watsa masa
wata k'ara ya k'ara saki yana runtse idanunsa cikin azaba
"yanzu zaka rabu da ita ko bazaka rabu da ita ba?
Aasim ya bud'e idanunsa da suka fara k'ank'ancewa yace
"kada kayi tunanin zaka tab'a jin kalamar rabuwa da ita a bakina,kasani duk abunda zakayi sai dai kayi"
malan isa ya jinjina kai yana kuma d'ina ya k'ara watsa masa,ze kuma watsa mai
Rauda tayi saurin dakatar dashi ta hanyar rik'e k'afafun sa
"dan allah kar ka kuma watsa masa,ka k'yalesa haka"
tafad'a cikin tsananin tashin hankali tausayin sa
Aasim yayi murmushin takaici
"kisani wannan zafin da nike ji be kai zafin da nike ji acikin zuciya ta ba,na cewa kinzab'i rabuwa dani,ki barshi ya cigaba da aikinsa"
kafin ta kuma magana,malan isa ya cigaba da watsa masa
kuka Rauda keyi sosai kamar ranta ze fita
yasha matuk'ar wahala gabad'aya jikinsa ya wani irin kwakkwailewa kamar an watsa masa ruwan zafi
saida ruwan addu'ar ya k'are gabad'aya sannan malan isa ya koma ya zauna yana mamakin kafiya irin na Aasim
"wannan wahalar bata isheka bane da kakasa amincewa da abunda nasaka?
Aasim ya d'ago kansa yace
"kasani da zan rasa raina ne,bazan tab'a rabuwa da Rauda ba"
tsananin tausayin sa ne ya k'ara dabai-baye zuciyar ta
a durk'ushe ta k'arasa gabansa idanuwan ta na tsiyayar da hawaye
ya kalleta yana murmushin takaici
"kinyi farin ciki ko habibty?haka dama kike so ko,da kinsan bazakiyi rayuwa dani ba da baki amince min ba tuntuni,ki kasa na k'ara shiga duniyar k'aunarki amma yanzu zaki juya min baya ko?
tabbas mahaifina yayi gaskiya da yace nayi babban kuskure da na baki yardata,amma ina so kisani bazan tab'a rabuwa dake ba duk da kin butulce min domin kece zab'in zuciyata"
zuciyar ta k'ara karyewa cikin raunanniyar murya tace
"kayi hak'uri Aasim,bada son raina bane amma umar shine farincikina kayi hak'uri kabarni na rayu dashi amatsayin mijina,ka amsa ka rabu dani bazan iya jurar ganin ka cikin wannan halin ba"
murmushin takaici yayi yana kad'a kai
"nasan bazaki tab'a ganewa ba,bazaki tab'a gane irin k'aunar da nike miki ba,dan da ace kinsan ko da rabin.k'aunar danike miki ne dake kanki baki zab'i ki rabu dani ba,amma babu komai"
kuma fashewa tayi da kuka,tana jin zuciyar ta na yima ta wani irin ciwo
malan isa ya taso hannunsa rik'e da wata kwalba yace
"idan har baka amince ka rabu da ita ba,zan saka.cikin kwalbar nan ka k'arake rayuwar ka acikin ta,dan haka gaggauta yin abun da nace"
Aasim ya kuma murmushi har lokacin idanuwan sa na kanta
"ta tafi da komai nawa,soyayyar ahalina,matsayina da kuma muk'ami na sannan kuma da soyayyata,bazan tab'a yin abunda kake so ba,amma idan har ita tana kan bakanta na son rabuwa dani to kayi duk abunda kayi niyya"
malan isa ya gyad'a kai yana k'ok'arin bud'e kwalbar
girgiza kai Rauda tafara yi
"Aasim aa,dan allah "
yayi mata kallon takaici yace
"bazan tab'a yarda ina gani.wani ya rab'eki ba,idan har hakan yana ganin shine dai-dai kuma maslaha yayi"
zata kuma magana malan isa ya kalli mama yace
"kufita da ita"
mama ta kama hannun ta,k'wace hannun tayi tana k'ara sawa gabansa
cikin kuka tace
"Aasim banace ka rabu dani bane gabad'aya kabarni kawai nai aure shine buk'atata narok'eka.......
malan isa ya katse ta yana cewa mama
"nace kufita da ita ko"
tana turjewa mama da goggo hanne suna janta ahaka suka fita da ita
k'ok'orin.komawa d'akin take yi amma sun hanata,gabad'aya k'wak'walwarta ta hautsine,ahankali tafara ganin duhu a idanunta
daga nan bata k'ara sanin inda kanta yike ba
sai dai farkawa tayi ta ganta a gadon Asibiti
ahankali tagama bud'e idanunta ta sauke su akan umar da ke zaune kan kujerar dake gaban gadon
cikin farin ciki ya mik'e yana fad'in
"chuchu kin farka sannu"
d'aga mai kai,ya tsiyayo ruwa a kofi yana mik'a mata
yunk'urawa tayi ta tashi,tana jin jikinta yayi mata sakayau kamar ancire.mata wani abu me nawi
"me ya kawoni asibiti kuma?
ta tambaya tana amsar kofin ruwan,umar yayi murmushi yana fad'in
"rashin lafiya mana,amma ya jikin naki me ke miki ciwo?
ta girgiza kai dan ji take kamar tafara wata sabuwar rayuwa,gaba d'aya jikinta babu inda ke mata ciwo
"ba ko ina,yaushe aka kawoni.asibiti"
"yau kwanan ki uku"
ta d'an ware ido da mamaki
"kwana uku?
umar ya d'aga kai
"eh kina ta bacci ba,ni da harkin fara bani tsoro ma"
d'an murmushi tayi
"habadai kayi zaton bazan farka bane.......
kasa k'arasawa tayi sakamakon tunawa da Aasim da tayi
kallon ta umar yayi sosai ganin yadda ta tsaya cak tana k'walalo idanu
"me ya faru?
ya tambaya yana kafeta da ido
"Aasim,ya aka.k'are dashi?
ta tambaya zuciyar ta narawa
umar ya sauke ajiyar zuciya yace
"wannan kima manta da zancen sa anriga da an rufe babinsa"
ji tayi zuciyarta tayi mata wani iri,gaba d'aya saitaji babu dad'i
ganin zata shiga wani tunani na daban yasa yace
"kinga chuchu me kike so kici,dannasan kintashi da yunwa"
hmmmmmm ina da exam,plz kutayani da addu'a allah ya bani sa'a
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:45 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣3⃣
_Ina bawa masoyana haƙuri abisa jina shuru da su kayi, na san wasu daga ciki sun fara manta labarin amma na san akwai waɗanda har yanzu suke zaman jirana kamar_
*_Karima, fati s noma, ummu kaltum, safnah, aisha babayo_*
_Ina matuƙar jin daɗin yadda kuka dinga kirana musamman *Karima* , da bata cikakken sati biyu sai ta kira tana faɗin a turo musu uncle *Aasim*_
_Dan haka wannan Page ɗin nakine *Karima* Allah yabar ƙauna_
_9:13_🕒PM
WED, SEP 25
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Jingina tayi da filo tana lumshe idanuwan ta A hankali batare da ta bashi amsa ba
Ya matso kusa da ita yace
"chuchu kifaɗamin me kike so kici? Zansa yanzu a kawo miki"
Ta buɗe idanuwan ta A hankali ta ɗaura su a kansa cikin wani irin yanayi na damuwa
"Sam ban kyauta masa ba, na zama me son kaina da kuma son zuciya ta, ya rabu da komai nasa, ya sha baƙar wahala duk a kaina amma be damu ba kullum burinsa ya zeyi ya rayu dani ya kuma sani farin ciki"
Ta ɗan dakata tana share hawayen da ya biyo daga kwarmin idanunta
Umar sauke ajiyar zuciya yayi cikin kwantar da hankali yace
"dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki manta da komai kisa wa ranki kamar rayuwar da kika yi da Aasim mafarki ce kinji farin cikina?
Ɗan murmushi tayi me ciwo zuciyar ta na hasko mata shi da maganganun sa
A lokacin suna tare
_habibty ina tsananin ƙaunar ki, dan Allah kada ki gujeni dan idan kika gujeni bansan ya zanyi da Raina ba, ki rayu dani dan kece farin cikina_
Rauda ta girgiza kai A hankali tace
"abune da baze yuwu ba Jaana bazan taɓa iya manta wa da Aasim ba, bawan Allah ne me haƙuri da tsananin ƙaunata"
Dai-dai lokacin mama ta turo ƙofa da sallama
Umar ne ya amsa
Bayan kwana biyu taji sauƙi sosai aka bata sallama suka dawo Kaduna
Ta zama shuru-shuru dan Sam bata son Magana dan koda suka koma gida ɗaki ta shiga ta kwanta
Gabaɗaya tunanin Aasim ya hana ta sukuni
Haka aka cigaba da gudanar da shirye-shiryen biki
Zuwan da Umar yike yi akai-akai shine yasa taɗan fara sake wa harta fara mantawa da Abunda ya faru
**** **** ****
*(Wannan shine ainihin labarin, da kuma dalilin da yasa Aasim yike wahalar dasu, yanzu zamu cigaba)*
_Idan masu karatu basu manta ba a baya mun tsaya ne a inda Rauda ta tafi dogon tunani tunda kan haɗuwar ta da Aasim da rayuwar da tayi dashi bayan irin wahalar da yike basu ita da Umar da kuma ruwan gubar da Aasim ya sa ma umar a asibiti a lokacin da ya bayyana da fuskar zayyad,kuma yace ma karin wannan gubar shine idan umar ya furta ya saki Rauda amma muddin yaƙi sakinta to duk kwanan duniya ruwan gubar na ƙara shiga cikin jikin sa_
Umar ya tashi da ƙyar daga kujerar da yike ya dawo kusa da ita ya zauna tare da kiran sunan ta
"Rauda"
Ta ɗago jiƙaƙƙun idanunta tana kallon sa batare da ta amsa ba
"kisani ina sonki kuma a shirye nike dan in fuskanci ko wace irin ƙalubale akanki, ki kwantar da hankalin ki kisawa ranki cewa duk runtsi duk wuya ina tare dake bazan taɓa guje miki ba"
Ta kwantar da kanta a kan cinyar sa wasu zafafan hawaye na biyo kuncin ta
"ina zamu samu mafita, a ina zamu samu ma karin wannan gubar dake jikin ka? Lafiyar ka tafi min komai Jaana bazan iya jurar ganin ka cikin wannan halin ba na san kanajin jiki daurewa kawai kake yi dan kar hankalina ya ƙara tashi"
Umar ya sauke gauron numfashi, yana runtse idanuwan sa dan ji yike yi kamar ana dafa naman jikin sa sabo da tsananin zafin da yike ji
Yafi minti biyu a haka yana ambaton sunan Allah a hankali
Sai da yaɗanji jikin ya lafa masa sannan ya fara magana da muryar sa da tayi sanyi ƙalau
"zamu samu makari chuchu, kisani babu abunda yafi ƙarfin Allah kuma yana sane damu mu cigaba da kai kukan mu garesa na tabbata ze yi mana maganin komai"
Da daddare suna kwance bacci ya ɗan ɗauki umar
Rauda ko ta kasa baccin kallon kyakkyawar fuskar sa kawai take yi da tayi mugun faɗawa kamar wanda yayi wata yana jinya
Tsananin tausayin sa da kuma ƙaunarsa ne suke ƙara ratsa zuciyar ta
A gigice umar ya farka yana ambaton sunan Allah
Tayi saurin tashi zaune tana tambayar sa lafiya
Ya kasa bata amsa in banda numfarfashi babu abunda yike yi
Ta matso ta kama hannun sa, saurin sakin hannun tayi dan ji tayi zafi rau
Hankalin ta ya tashi sosai dan tana jin hucin da yike fitowa daga jikin sa
"me ya faru? Me yasa Meka?
Ta tambaya cikin tashin hankali
Umar da ƙyar ya iya buɗe bakin sa yace
" ɗauko min ruwa me sanyi, ki haɗomin da ƙan-ƙara"
Ta miƙe jikin ta babu ƙwari dan ta fara karaya
A hankali ta murɗa ƙofar ɗakin ta fara saukowa a hankali
Ta ɗan da tsaya dan ji tayi kamar ana bin ta a baya
Waigawa tayi bata ga komai ba taci gaba da tafiya still tana jin sawun tafiyan a bayan ta
Kasa daurewa tayi ta kuma juyowa
Wani irin ihu ta ƙwala sakamakon ganin wani mutum zarƙameme me dogon ƙaho,baya ta fara yi da sauri yayin da ya cigaba da tahowa yana dariya da wata kalar murya me tsoratar wa
Ƙundun bala ta fara yi daga kan step ɗin har zuwa ƙasa
Goshinta ya bugu da bango, ta ƙara yin wata ƙara tare da dafa goshin wanda ya fara zubar da jini
Ta ɗago kai tana kallon step ɗin amma wurin wayam babu kowa
Ta miƙe jikin ta na rawa dan ta tsorata sosai
Ƙarasawa wurin fridge ɗin tayi tana waige-waigen inda zata sake ganin abunda ta gani
Ahaka ta buɗe fridge ɗin, tayi baya da sauri dan amemakon taga ruwa da drinks ɗin dake ciki wasu kalar macizai ta gani sun dunƙule wuri ɗaya
Babu inda baya rawa a jikin ta, ƙarar sawun tafiya taji daga wurin kicin tayi saurin juyawa
Wannan datagani ɗazu ne ya dumfarota gadan-gadan
Rufe idanuwan ta tayi gam tana karanto addu'a da ƙarfin gaske
Zuwa can taji shuru, bakinta be dena furta addu'an ba ta buɗe idanun tana wawware su
Amma babu kowa a wurin, ta kalli fridge ɗin Shima babu macizan
Da sauri ta ɗauki goron ruwa da ƙanƙara ta haye sama da sauri har tana cin tuntuɓe
Arazane ta koma ɗakin,umar ya kalle ta da idanuwansa da suka yi luhu-luhu sabo da Tsananin wahalar da yike sha
Basai ya tambaye ta abunda ya faru ba, dan ya san wani abu me tsoratar wa ta gani
Ya kamo hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana tsurawa kyakkyawar fuskar ta ido
Amsar ruwan yayi ya sha, sannan ya yunƙura da ƙyar ya ɗauko wani ƙaramin akwati wanda kayan taimakon gaggawa suke ciki
Ya dawo ya zauna ya fara goge mata jinin, ya gyara mata wurin sannan ya rufe akwatin ya aje a gefe
Ya janyo ta jikin sa tare da rungume ta sosai
Hawaye ne kawai ke bin fuskar ta,a hankali yike jin ɗigar hawayen a jikin sa
"da wanne kike so inji Rauda?
Ya faɗa idanuwansa na kanta
Numfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa
" kukan ki ƙara tada min hankali yike yi, kidena kinji"
Rauda ta ɗago kanta daga jikin sa tana kallon cikin idanun sa
"dan Allah Jaana kada kace zaka hanani kuka, wannan kukan shine yike rage min ciwon da nike ji acikin zuciya ta bazan iya dena yin shi ba"
Hmmmmm ya sauke doguwar ajiyar zuciya
"tashi muyo alwala"
Tashi tayi suka nufi ba yin, tsayawa tayi ya fara yi sannan itama tayi
Suka fara nafiloli suna kai kukan su ga ubangiji
Basu kwanta ba har saida akai sallar asuba
Washegari da safe ita ta fara tashi,ta sauko ta shiga kicin ruwan zafi kawai ta ɗaura, dan bata jin zata iya yin abun kari me wahala
Kakarinsa taji, tayi saurin komawa saman
Adurƙushe tagansa bakin gado yana ta kakari, jijiyoyin wuyan sa sun mummurɗe idanuwansa sun canza launi zuwa jawur
Zuba mai ido kawai tayi hawaye na bin fuskar ta
Yafi minti goma a haka, da ƙyar ya samu ya amayo wani dunƙulen jini
Ya kwanta a jikin gadon lamo yana maida numfashi
Gyara wurin tayi, ta taimaka masa yayi wanka sannan ya koma ya kwanta
Zata miƙe ya ruƙo hannun ta
"ina zakije?
" zan ɗauko ma abun kari ne"
Ta faɗa
Umar ya girgiza kai yace
"a'a banajin zan iya cin wani abu, ki zauna tare dani kawai"
Ta sa hannu tana share fuskar ta dan har lokacin ta kasa tsaida hawayen dake ta ambaliya a fuskar ta
"bazeyuwu ka zauna ba ka karya ba, kabari in kawo maka"
Ya kuma girgiza kai a karo na biyu
"banajin zan iya ci ne chuchu"
Ta sauke numfashi tana kaɗa kai, tare da fuskantar sa sosai tana matse hannun sa dake cikin nata
"Jaana idan na nemi wata alfarma a wurin ka zaka iya yimin?
Ya jinjina kai batare da yace komai ba
"kayi haƙuri da abunda zan faɗa Jaana, nasani bazaka ji daɗin sa ba Sam, amma inaso ka sani Nima ba dan inaso bane illah itace kaɗai mafitar mu a yanzu"
Taɗan numfasa sannan ta maida kallon ta gefe ta cigaba da cewa
"dan Allah inaso ka sake ni, bazan iya jurar ganin ka cikin wannan halin ba......
Katseta yayi ta hanyar ɗaga mata hannu
" dakata Rauda!
Tayi shuru tana kallon sa da yanayin sa da ya koma na damuwa
"yanzu kenan da Ace nine Nike da matsalar ki, rabuwa dani zaki yi kenan ko"?
Ta girgiza kai
Umar yace
"eh mana, kisani babu abunda zesa inrabu dake wallahi ko da zan mutu ne kuwa"
Ido kawai ta zuba masa, zata kuma magana ya dakatar da ita
"idan har akan wannan maganar ce, bana son in ƙara jin komai"
Jikinta a sanyaye ta baro ɗakin, kan kujera ta zauna tana jin zuciyar ta nayi mata nawi
Wayar ta ta ɗauko ta kira anty ummi tabata labarin komai sannan ta ƙara da cewa
"anty ummi ina cikin tashin hankali idan na rasa umar ban san ya rayuwa zata kasance ba, bansan ya zanyi ba"
Daga can ɓangaren anty ummi ta sauke gauron numfashi cike da al ajabi tace
"tabbas kina cikin tashin hankali Rauda, Allah ne kaɗai ze iya fitar daku, ina ganin ki nemi Aasim ɗin ki roƙesa tunda yana sonki ƙilan y tausaya ya cire mai gubar"
Kaɗa kai kawai tayi ta kashe wayar, ta san Aasim baze taɓa saurararta ba
Ɗakin ƙasa ta shiga babu komai a ciki sai katifa
Ta zauna gaban ta na ɗan faɗuwa
A zuciyar ta tayi masa sallama
Bata fi minti biyu da zama ba sai gashi ya bayyana, cikin shigar sa ta ƙasaita zaune kan kujera me kalar ruwan zinari
Nan da nan wani ƙamshi me daɗi ya gauraye ɗakin
Yayi kyau sosai, farin sa ya ƙara ƙaruwa dan har ɗaukar idanu yike
Da murmushi ya amsa sallamar yana shafa baƙin sajen da ya zagaye fuskar sa wanda ya kwanta luf
Dan jin zuciyar sa yike cikin farin ciki ganin ta fara neman saki a gurin umar
*yarfillo.*
[20/10, 8:46 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣4⃣
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
_5:36_🕒 PM
SUN, SEP 29
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Rauda ta zuba ma Aasim ido, yayin da shima ya zuba mata nasa yana cigaba da yin ƙasaitaccen murmushi
"Ashe so kan juye ya koma ƙiyayya Aasim? yanzu farin ciki kake yi da wahalar da nike sha ko?
Ta ɗan tsaya ta share hawayen da suka gangaro mata sannan ta ci gaba da cewa
"bantaɓa tunanin cewa zaka iya cutar dani ba, amma kaduba kagani...
Ta dafa goshinta inda taji ciwo
" sanadin tsoratarwar dakasa ake mini, ka hana zuciya ta sukuni ka hanamin kwanciyar hankali,shin kana ganin Hakan da kake yi dai-dai ne kenan?
Aasim yayi ɗan murmushi,a hankali ya taso daga kujerar da yike ya dawo gabanta ya durƙusa
"habibty banzo nan dan inji waɗannan bayanan daga wurin ki ba, koma menene ai ke kika jawo ma kanki, kifaɗamin abunda yasa kika kirani kai tsaye"
Jinjina kai tayi tace
"dan Allah ba dan ni ba, katausaya mana ka cire gubar da kasa ma mijina ina tsananin tausayin sa bazan iya jurar ganin sa cikin wannan halin ba"
Wani irin mugun kallo ya yi mata dan shi a duniya bashi da wanda ya tsana sama da umar, take murmushin dake fuskar sa ya ɗauke
Ganin irin kallon da yike mata yasa ta ƙara durƙushewa tana haɗe hannayen ta guri ɗaya
"dan Allah Aasim kaduba irin halin da yike ciki........
Katseta yayi ta hanyar ɗaga mata hannu
" kinga kada ma ki wahalar da kanki wurin roƙona dan bazan taɓa lamunce ma buƙatar ki ba, nafaɗamiki ma karin gubar ai kije ki tirsasa shi ya sake ki shi kenan ze warke ze samu lafiya"
Tayi shuru tana cigaba da kallon sa,wasu siraran hawaye na kuma biyo kuncin ta
Aasim ya sauke numfashi, dan yana tsananin jin zafi idan yaga tana zubar da hawaye
Ya rasa irin wannan ƙauna da yike mata, da ace ze iya da ya yi mata abunda take so, amma baze iya ba
Cikin damuwa yasa hannu ya share mata hawayen yana faɗin
"ya isa haka to, akwai wata mafita guda ɗaya, kuma ita kaɗai ce alfarmar da zan iya yi miki"
Kallon sa ta cigaba da yi, tana jiran jin abunda zece
Sai da ya kwashi minti uku yana nazari sannan yace
"na san ba lallai bane ki amince da wannan alfarmar da zan iya yi miki, duk da na san kina son lafiyar mijin ki amma na san da wuya ta yi miki"
Rauda ta girgiza kai a hankali tace
"zan amince in har ze sami lafiya, ka faɗamin"
Aasim yayi ɗan murmushi da ya tsaya masa iya laɓɓa kawai
"to shi kenan,mafitar ki guda ɗaya ce,kuma itace wannan....
Ya faɗa yana shafa gefen sa wata ƴar ƙaramar wuƙa ta bayyana, ya riƙe yana miƙa mata
"idan har kika caki saitin zuciyar sa da wannan wuƙar to ya riga da ya warke ya gama"
Wani irin kallo Rauda ke masa me cike da ma'anoni da yawa
"kana nufin inkashe sa kenan?to bazan iya ba, idan har Hakan shine burinka Kaga bayan sa a doron ƙasa to burinka baze taɓa cika ba Insha Allahu"
Aasim yayi guntun murmushi
"kinji nace miki ki kashe sa ne? Sam ni faɗa miki haka ba, wannan wuƙar ba abunda zata masa face fitar da gubar dake jikin sa kuma daga lokacin ze dawo lafiya kamar be taɓa yin wani ciwo ba a rayuwar sa, dan bana ce ki zurma mai wuƙar bane a'a ko yaya idan taɗan huda jikin sa jini ya fita shi kenan "
Shuru tayi tana cigaba da yi masa wani irin kallo me cike da rashin yadda
Ya kuma yin murmushi yace
" sanin kanki ne ban taɓa yi miki ƙarya ba, kuma ni rauhani ne ba mutum ba, bana saɓa alƙawari kamar yadda ku mutane ku keyi"
Tabbas ta san be taɓa mata ƙarya ba, amma ta san a yanzu ze iya yin komai, amma abunda take tantama a ranta Shine meyasa ze bata ma karin gubar cikin sauƙi anya ba wani abu ne yike shiryawa ba kuwa?
Ya ƙara matsowa kusa da ita yana shafa wuƙar a hannun ta sai ga wuƙar ta ɓace
"aduk sanda ki ka amince zaki yi amfani da ita ki shafa hannun ki kawai zata fito, sai dai wannan wuƙar tana da sharaɗi"
Ya ɗan tsaya yana kallon yana yin fuskar ta sannan ya cigaba da cewa
"a yayin da ta coki jikin sa zata fitar da duk wata cuta ta jikin sa a take, sai dai zata mantar dashi rayuwar da yayi na shekaru shida da suka wuce"
Cikin rashin fahimta Rauda tace
"zata mantar da shi rayuwar sa ta shekaru shida? ban gane abunda kake nufi ba"
"kije kiyi nazarin abunda na faɗa zaki gane abunda nike nufi, na barki lafiya"
Yana gama faɗar haka ya ɓace a wurin
Me yike nufi?
Ta tambayi kanta cike da tsananin damuwa
Kakarin da taji umar nayi ne, yasa dole ta miƙe batare da ta gane abunda Aasim yike nufi ba
Ɗakin ta shiga yana durƙushe kusa da bayi da alamu bayin yaso ya shiga ya kasa
Kakari yike yi kamar ransa ze fita,Idanuwansa sun yi jawur saboda tsananin wahala, hawaye kawai Rauda keyi
Yafi minti goma a haka, da ƙyar ya samu ya amayo wani dunƙulen jini
Jikinsa yayi mugun sanyi dan ya sha wahala sosai, ja baya yayi da ƙyar ya jingina da jikin gadon yana maida numfashi a wahalce
Tashi tayi ta gyara wurin har lokacin idanuwanta basu dena zubar da hawaye ba
Sai da tagama sannan ta dawo kusa dashi ta zauna ta zuba mai ido cike da tsananin tausayin sa
Kallon ta shima yike yi da idanuwan sa da suka yi luhu-luhu
Da ƙyar ya iya buɗe bakin sa da yayi masa nawi yace
"haɗamin ruwan wanka"
Ta haɗa masa, sannan ta kama sa zuwa ba yin
Sai da yayi wankan sannan ya ɗan ji dama-dama
"chuchu please ɗan dannamin ƙafafuna"
Ba tace komai ba ta fara mammatsa mai ƙafafun, zuwa can ta ɗago ta kalle sa tace
"Jaana yanzu a haka zamu cigaba da zama, kana cikin wannan halin?
"dan Allah ba Danni ba ka yi abunda yace, lafiyar ka tafi min komai, ko da bana tare da kai idan nasan kana cikin ƙoshin lafiya zanji daɗi amma bazan iya jurar ganin ka a wannan halin ba, bazan iya ba"
Ta ƙarasa tana fashewa da wani sabon kuka me tsuma zuciya
Umar ya sauke doguwar ajiyar zuciya tare da sa hannu ya janyo ta jikin sa ya matse ta tsam yana sauke numfashi
"Rauda ina miki so me tsanani wanda duk runtsi duk wuya bazan taɓa rabuwa dake ba,dan Allah kada ki ƙara ambaton rabuwa a tsakanin mu"
Kallon sa kawai take yi da jiƙaƙƙun idanunta
"tunda mukai aure baka samu farin ciki daga wurina ba, inbanda fargaba da tashin hankali umar dan Allah.......
Katseta yayi ta hanyar ɗaura yatsun sa biyu a bakin ta
"na faɗamiki duk runtsi ina tare da ke, wallahi koda mutuwa zanyi bazan taɓa cikama wancan azzalumin burin sa ba"
*~ƴarfillo.~*
[20/10, 8:47 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣5⃣
Wannan page nakine my aneesah kiyi yadda kike so dashi
_10:23_🕒 AM
MON, OCT 14
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Yana rungume da ita bacci ya ɗauke shi,tashi tayi ta janye jikin ta zauna
Tare da zabga tagumi tana kallon kyakkyawar fuskar sa da ta faɗa sosai
Maganar da suka yi da Aasim ce ta dawo mata, me yike nufi da idan wuƙar ta caki Jikinsa zata mantar dashi rayuwar da yayi na shekaru shida?
Ta ɗan yi shuru tana nazari, kenan yana nufin har da ita umar ze manta a rayuwar shi dan shekarunsu biyar da sanin juna
Ta ya ya Hakan ze yuwu?
Tashi tayi jikinta babu ƙwari ta sauko ƙasa dan dole ta sake neman Aasim
Sai da ta daɗe a zaune tana jiran zuwan sa, sannan ya bayyana
Kallon juna suka yi na ƴan sakwanni sannan ta ɗauke kanta ta maida kallon ta gefe
"inaso ka ƙara yimin bayani akan abunda kace ɗazu, dan ni ban gane ba"
Aasim shima ya kauda kallon sa da ga kanta yace
"miye baki gane ba?
Sai da ta sauke numfashi sannan tace
"kace ze warke amma ze manta da rayuwar da yayi abaya har ta tsawon shekaru shida, kenan kana nufin har dani ze manta?
Aasim ya jinjina kai yana murmushi
" eh har dake ze manta,dan idan har kika Coke sa da ita ze suma baze farfaɗo ba har sai yayi minti talatin, a lokacin da ze farka ze manta dake ze manta wacece ke da kuma matsayin da kike dashi a wurin sa, kinga shi kenan burina ya cika dole zaki nisance sa kikasan ce tare dani ni kaɗai"
Takasa ƙara furta komai kallon sa kawai take yi, ya matso kusa da ita yasa hannu yana shafa gefen wuyan ta
"dani kaɗai zaki rayu Rauda, har ƙarshen rayuwar ki kuma kisani da zarar yayi wannan Suman ya farfaɗo kada ki sake ki nuna masa ke matar sa ce ke duk wani abu ma da kika san idan ya gani ze tuna dole ki fara kauda sa tun yanzu"
"ya kake so inyi da iyayena ƴan uwa na da kuma ƴan uwan shi da basu san matsalar da muke ciki ba? Aasim wannan ba adalci bane kar kamanta fa nidashi ma'aurata ne ta yaya zaka sanya wannan shamakin a tsakanin mu?
Ta ƙarasa faɗa muryar ta na raunanewa
Guntun murmushi yayi yana taɓe baki cikin yana yin ko in kula
"wannan matsalar ki ce ba tawa ba, nadai gaya miki wannan ce kaɗai damar da kike da ita idan kinga dama kiyi amfani da ita idan kuma bakiga dama ba ki barta"
Zata kuma magana ya katse ta
"kinga ni daga yanzu ma ba zaki ƙara nemana kiganni ba, dan haka zaɓi ya rage gareki abu ɗaya dai nike so ki ƙara sani ke Rauda tawa ce ni kaɗai
Na barki lafiya"
Kanta ta kifa kan gwiwowin ta, wasu hawaye masu ciwo suna gangaro mata
Ya zata yi da ranta? Ina zata tsoma zuciyar ta tayi sanyi?
Bayan sati ɗaya, umar ya jigata iya jigatuwa dan ya fita daga hayyacin sa ma tuƙa
Duk wanda ya gan sa sai ya tausaya masa dan ya koma kamar bashi ba
Hankalin ƴan uwa ya tashi sosai, musamman anty kaltum da kullum a gidan take wuni
Rauda ko ta rame sosai dan rabon da ta sama cikin ta wani abu har ta manta
Ranar wata Asabar Jikinsa yayi tsanani sosai dan be taɓa shan wahalar da ya sha a ranar ba
Zayyad da anty kaltum suna ɗakin sun zuba uban tagumi
Zayyad ne ke ƙarfin halin yi masa sannu
Anty kaltum ta fito daga ɗakin tana share hawaye dan gani take tana gab da rasa ɗan uwan ta
Falon ta dawo ta zauna inda Rauda ke zaune
Cikin tausayawa ta dafa ta tace
"Rauda ba nace kidena zurfafa tunani bane? So kike yi kema wani abu ya same ki?
Rauda ta kalli anty kaltum sannan ta kauda kanta tace
" anty dan Allah inaso in roƙeƙi wani abu"
Anty kaltum tace
"faɗi inajin ki Rauda"
Rauda ta share hawayen da suka zubo mata tace
"inaso kisa umar ya sake ni"
Cikin mamaki anty kaltum tace
"ya sake ki? Kamar ya? Kina nufin Harkin fara gajiya da lalurar da Allah ya ɗaura masa?
Rauda tayi shuru, anty kaltum ta cigaba da cewa
" gaskiya kin bani mamaki bantaɓa tunanin jin haka daga gareki ba"
Rauda ta girgiza kai tace
"anty Sam ba wai dan lalurar da Allah ya ɗaura masa bane nace Hakan, a'a saboda nice sanadiyyar shigar sa cikin halin da yike ciki"
Cikin rashin fahimta anty kaltum tace
"bangane ba"
Kwashe komai Rauda tayi ta faɗa mata sannan ta fashe da kuka tana cigaba da cewa
"anty inason umar bazan iya jurar ganin sa cikin wannan halin ba, kisa baki dan Allah ya sake ni ko ya samu sassauci"
Anty kaltum zufa ce kawai ke karyo mata gabaɗaya tausayin Rauda ya kamata
Sai da ta kwashi minti biyar tana nazari sannan ta dafa ta tace
"kunsan kuna cikin wannan matsalar me yasa baku sanar mana ba tun tuni?
Ta numfasa tana cigaba da cewa
" dole zamu nemi mafita baze yuwu ayi masa yadda yike so ba, bari na kira hajiya (kakar su)
Na sanar da ita,nasan akwai malamai manya a Niger "
Ta ƙarasa faɗa tana lalubo wayar ta ta danna numban hajiya
Sai da ta kusan tsinkewa sannan ta ɗauka dan ta fara barci
"alo kaltume yau kuma tsiyar taki ta dare ce?
Anty kaltum tace
" hajiya yanzu ba lokacin wasa bane a kan maganar rashin lafiyar umar ne"
Daga can ɓangaren hajiya tace
"to inajin ki badai jikin ne ya ƙara tashi ba?
A gaggauce anty kaltum ta sanar da ita
Hajiya ta dinga zabga salati cike da jimami
Anty kaltum tace
" yanzu yaki ke ganin za ayi? Akwai wani malamin da kike ganin ze iya?
Hajiya tace
"akwai shi nan kusa damu ma kuwa"
*~ƴarfillo~*
[20/10, 8:47 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣6⃣
*_Wannan page naki ne mariam Nijer ina godiya da ƙaunarki ga wannan littafi Allah ya bar zumunci_*
_9:22_🕒 PM
SUN, OCT 20
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"shi kenan kije kisamesa yanzu gobe sai ku biyo jirgin yamma dan allah hajiya"
Anty kaltum ta faɗa, daga can ɓangaren hajiya tace
"Insha Allahu"
Sallama suka yi anty kaltum ta ajiye wayar tana duban Rauda wacce ta zabga tagumi
"ki kwantar da hankalin ki Rauda Insha Allah zamu sami mafita kinji"
Kai kawai Rauda ta gyaɗa mata
Washegari ana kiran sallar magariba hajiya t iso da malan Audu
Da ƙyar umar ya iya saukowa daga sama da taimakon zayyad da ya tallabosa
Rawar sanyi yike yi sosai dan haƙorarsa har wasu ƙarar karawa da juna suke yi
Ya rame ya ɗashe jikin sa kamar babu jini abunka ga farin mutum sai yayi kamar takadda
Jingina yayi da kujerar da zayyad ya zaunar da shi, ya buɗe manyan idanuwansa da suka lumshe yana ɗaura su akan Rauda
Tausayin ta da tsananin ƙaunar ta ne suka ƙara dabaibaye zuciyar sa
"ina tare dake masoyiyata duk runtsi duk wuya bazan taɓa guje miki ba"
Ya faɗa a cikin zuciyar sa yana maida idanuwansa ya rufe saboda azabar da yike ji na nuƙurƙusar cikin ƙasusuwan jikin sa
Hajiya kam kuka take yi sosai ganin yadda umar ya koma cikin ƙanƙanin lokaci
Malan Audu ya ɗauko wata ƙaramar jarka wacce take cike da ruwan rubutu
Ya miƙa ma umar yace ya sha
Umar ya amsa ya kafa kai sai dai yana sha yaji cikin sa yayi wani irin ƙullewa
Ya dafa cikin yana ambaton sunan Allah
Gaf-gaf-gaf jikin sa ya fara rawa kan kace kwabo kujerar da yike ta fara jijjiga da ƙarfin gaske
Wata kalar iska ce zagaye kujerar da yike kai ta fara ɗaga sa ta maka sa da bango
Sannan ta maida sa ɗaya bangon ta kuma makawa kafin wani ɗan lokaci tuni yayi jina-jina
Rauda kuka da ihu take yi sosai, hankalin su ya tashi matuƙa
Da taimakon addu'ar da malan Audu yayi tayi ne iskar ta lafa, lakwaf ya faɗo kan kujerar
Rauda ta durƙushe a gaban sa tana jijjigasa cikin kuka me tsanani
Da ƙyar ya iya buɗe idanuwansa ya ɗaura su a kanta duk da dishi-dishi yike ganin ta
Malan Audu ya girgiza kai cikin tausaya wa yace
"a gaskiya hajiya iyakar abunda zan iya kenan domin idan aka ce za a cigaba wahalar da tafi ta yanzu ze kuma sha saboda wannan gubar dake jikin sa"
Cikin kuka hajiya tace
"yanzu miye mafita malan?
Malan Audu ya sauke dogon numfashi yace
" aganina ya haƙura ya sauwaƙe mata kawai"
Hajiya ta jinjina kai tana duban umar tace
"to kadai ji tunda ba ƴar gwal bace ai sai ka sake ta ko?
Umar be bata amsa ba dan be ma san abunda take cewa ba har lokacin kallon Rauda kawai yike yi
Hajiya ta taso tana gallawa Rauda harara dan gabaɗaya haushin ta take ji saboda dalilin ta ji kanta ya shiga cikin wahala
Jijjigasa tayi tana faɗin
"magana nike yi ko baka Jina ne? Nace ka sake ta yanzu yanzunnan tunda ba ƴar gwal bace, kai ko ƴar gwal ɗince ma rabuwa zaka yi da ita dole!
A galabaice yike kallon hajiya cikin muryar sa da tayi sanyi sosai yace
"bazan iya sakin ta ba hajiya ina son matata"
"ya zamar maka dole umar, wallahi sai ka sake ta ba zamu zuba ma ido ka mutu akan mace ba, kayi abunda nace!
Hajiya ta faɗa cike da tsananin ɓacin rai
" bazan.... Bazan iya.. Ba"
Umar ya faɗa cikin sarƙewar murya da tari
Hajiya zata kuma magana Rauda ta dakatar da ita ta hanyar cewa
"umar baze taɓa iya Sakina ba hajiya, kiyi haƙuri nikaina bazan iya cigaba da ganin sa acikin wannan halin ba ina da wata mafita guda ɗaya"
Hajiya ta koma ta zauna cikin sababi take faɗin
"au dama kina da mafitar Shine kika barshi cikin wahala?
Rauda ta share hawayen da suka zubo mata tace
"ya bani zaɓi amma Hakan baze yuwu ba har sai kun bani goyon baya da haɗin kai"
Kallon ta kawai suke yi suna jiran jin abunda zata ce
Kwashe abunda Aasim ya faɗa mata tayi ta faɗa musu sannan ta ƙara da cewa
"yace dole ne inkauda duk abunda ze tuna ma umar dani matar sace dan duk ranar da ya tuna to ciwon da yafi nada ze dawo masa kuma bayi da makari, ina roƙon ku da ku taimake ni wajen cika sharuɗɗan wannan mafitar"
Ta ƙarasa faɗa tana fashe wa da wani sabon kuka me ciwo
Gabaɗaya jikin su yayi sanyi, harda hajiya
Umar kallon Rauda kawai yi keyi
"yanzu ashe zaki iya bin umarnin azzaluminnan wurin rabuwa dani? Kenan kin zaɓi rayuwa dashi dani kenan? Ashe ƙaunar da kike masa tafi wacce kike min?
Girgiza kai tayi cikin kuka tace
" ba haka bane umar kasani rayuwa ta ragaggiya ce idan har zanyi ta babu kai, amma kasani son da nike yi maka ne yasa na amince da buƙatar sa dan bazan iya ganin ka a wahala ba"
"ina baki umarni a matsayi na na mijin ki da kada ki sake ki aikata haka agareni, dan idan kika yi sanadiyyar da zan manta dake wallahi bazan taɓa yafe miki ba Rauda"
Tashi tayi dag wurin ta haye sama tana kuka kan gado ta faɗa tana jin numfashin ta nayi mata sama-sama to wai ita ya zata yi da rayuwar ta ne?
Anty kaltum ce ta tashi ta bita
Zama tayi gefen gadon tana kallon ta gabaɗaya ma ta rasa me zata ce mata
Rauda ta taɗago jiƙaƙƙun idanuwanta ta ɗaura su akan anty kaltum tace
"ya zanyi da raina, anty wallahi dama mutuwa nayi da ganin wannan rayuwar me cike da ruɗani"
Anty kaltum da sauke numfashi tana girgiza kai cikin damuwa tace
"kada ki ce haka Rauda ko wani ɗan adam yana tare da jarbawar sa kiyi haƙuri ki cinye nasan Allah yana tare dake"
Jinjina kai tayi tana share hawayen ta
"shi kenan anty, dan Allah ki taimakamin gurin aiwatar da wannan abun, acikin kwana biyu kaɗai"
Anty kaltum gabaɗaya tausayin ta ya dabai bayeta cikin sanyin jiki tace
"Insha Allahu zan taimaka miki Rauda kuma wannan soyayyar da kuke wa juna nasan Allah baze barku a haka ba duk daren daɗe wa ze yassare muku Insha Allahu
Da daddare kowa ya kwanta dan hajiya da anty kaltum ma a gidan zasu kwana zayyad ne kaɗai ya tafi
Rauda bayan ta idar da sallah ta shiga kicin ta haɗa mai lipton dan shi kaɗai yike iya sha
Ɗakin sa ta nufa ta tura ƙofar
Yana jingine da gado ya Lula cikin tunani murɗa ƙofar da tayi ne yasa ya dawo daga dogon tunanin da ya tafi
Hannu ya ɗaga mata tun kan ta ƙarasa shiga ɗakin
"kada ki sake ki shigo min ɗaki, ki koma bana buƙatar ganin ki"
Sororo ta tsaya tana kallon sa da kuma mamakin abunda yace
"kada inshigo ma ɗaki fa kace?
Ya jinjina kai
" eh haka nace"
Ajiyar zuciya ta sauke ta na ƙarasa shiga ɗakin
Zumbur ya miƙe yana ɗan ja da baya dan gani yike yi kamar zata caka mai wuƙar da Aasim yace, bawai tsoron wuƙar yike ji ba a'a yana tsoron ya manta da ita ne
"kada ki matso kusa dani ki fitar min a daƙi nace"
Mamaki ne ya ƙara kama Rauda cikin rashin Fahim ta tace
"bangane ba me kake nufi wai?
Jiri yaji yana neman ya kwashe sa yayi ƙoƙarin dafa bango amma kafin ya kai ga dafa bangon tuni ya zube a ƙasa
Ƙarasawa tayi da sauri tana ƙoƙarin ka masa
Yayi saurin ja baya ya na ɗaga mata hannu
"kada ki sake ki taɓani!
😂😂😂Tofa nikam sai mun haɗu a page na gaba
*~ƴarfillo~*.
0 comments:
Post a Comment