🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
_NA_
_HARIRA ALIYU_ ( *Yar Fillo*)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to aisha a ibrahim
*Bissmillahirrah manirrahim*
Fatan alkhairi ga kowa inafatan za ayimin hakuri abisa ga wasu kura kuran da kila zanyi
Gaisuwa da jinjina ga GOLDEN PEN WRITTERS
🅿AGE📕 1⃣
Gid'ane madai-daici dayike cike taf da jama'a idan kakalli kowa zaka fuskarsa dauke da farinciki da annashuwa banda wacce akayi taron da gayyar dominta
Datake makwabta tare da kawayenta anayimata lalle
Kallo daya zakamata kagano tashin hankali da tsananin fargaba atare da ita
Batawuce seconni batare data duba agogon wayarta ba faduwar gabanta na dada tsananta
Babbar aminiyarta ce tafahimci halin datake ciki ta matso gab da ita tafara magana ahankali
"Rauda please kikwantar da hankalinki banaso jama a sufahimci halin dakikeciki"
Kai kawai Rauda tagyada ma salma dantasan bazata fahimci tashin hankalin datakecikibane
Hakanma bakaramin dauriya takeyi ba
Tanaji kawayenta nayaba kyan lallen amma takasa tankamusu
Wata yar makarantarsuce tashigo tana sallama
Suka amsa salma nafadin"munyi fushi saiyanzu"
Tazauna kusa da rauda tana yar dariya"nabiya kasuwane salma yanzukuma danashigo layin dakyar na iya kutsowa
Jama a suncika layin tundaga farkonsa har karshensa"
Rauda tayi saurin tambayar jamila
"kinga umar?
Jamila ta girgiza kai"gaskiya ban lura ba kinsan mutanen dayawa"
Tajinjina kai tare da kara lalubar numbansa amma har lokacin akashe
Takara duba agogo karfe biyu saura hankalinta yakara tashi
Kallon me lallen tayi tace"dan allah kitakaita lallen haka"
"To"
Me lallen tace batafi minti biyar ba kuwa tace tagama
Mikewa tayi ganin mama tashigo suka shiga dakin matar gidan dasuke lallen
Mamar ma hankalinta atashe yike
Rauda da jikinta yagama yin sanyi ta dubi mama tanacewa
"mama wayar umar tundazu nike kira akashe kuma bana tunanin yazo gurin daurin aurannan gashi yanzu biyu dai dai"
Mama tasauke numfashi
Dan tama kasa cewa komai
Kasa rauda tayi dakanta hawaye na gangarowa
"mama idan aka fasa aurannan awannan karon bansan yaya zanyi da raina ba"
Mama takara sauke numfashi tare dacewa cikin kwantar da hankali
"insha allahu ba abunda zefaru"
Zaunawa kawai tayi amma ita ta riga da ta sadakar
Mama tafice zuciyarta cike da damuwa
Salma tashigo dakin tazauna kusa da ita tana karemata kallo
"haba Rauda meyasa bazaki kwantar da hankalinki bane bakisan wannan damuwar zata iya haifarmiki da wani ciwon na dabanba"
Wasu hawayenne suka kara gangarowa cikin shesshekar kuka tace
"Salma bansan yazanyi da rayuwata ba tundazu nike kiran wayar umar batashiga,gashi yanzu biyu harta gota amma banji alamun wani nasa yazoba bare maganar daurin aure ba
Salma inason umar bantaba son wani kamar yadda nike sonsa ba,idan narasasa bansan yazanyi da rayuwata ba......
Takarasa maganar cikin karyewar zuciya
Salma tasauke ajiyar zuciya hakika itama tagama karaya amma bataso ta nunama Raudan bataso hankalin raudan yakara tashi
Cikin karfafa gwiwa tajanyota jikinta tanadan bubbuga bayanta
"kawata kukannan ya isa haka dan allah insha allah ba abunda zefaru"
Kuka kawai takeyi me cin zuciya
Khadija ce tashigo dakin aguje fuskarta dauke da tsananin farinciki
Salma tace
"lafiya"
Cikin sauri khadija tace
"gasu umar can sunzo da tawagarsu"
Dasauri Rauda tamike
"dagaske khadija?
Khadija tadaga kai
"dagaske wallahi"
yaye labulen dakin tayi dasauri wanda ke fuskantar cikin layin tafara hange hangen inda zata hangosa
Daga can nesa tahangosa cikin abokanansa yasha wata purple din shadda abunka ga fari tas
Sai shaddar ta hausa kyawunsa yakara futowa
Kuramasa ido Rauda tayi da jikakkun idanunta
Tanajin wani sanyi da farinciki naratsa zuciyarta
Salma tadafa kafadunta tana dan murmushi
"kinga ni ba,bagashi yazo ba amma da duk kinbi kintada hankalinki nima kin tada nawa"
Kallon salma tayi tana yar dariya "karkiga laifina kawata kinsan yadda nike sonsa kuwa?
Dariya salma tayi itama sai lokacin hankalinnata yakwanta
"jibeki hawaye na zubowa kina kuma dariya, kuka da dariya alokaci daya"
Hannu tasa ta goge fuskarta dasauri tarasa
Ma mezatace saboda tsananin farinciki
"salma bazaki gane bane aure biyu anafasawa dole hankalina yatashi bare umar danike sonsa kamar raina"
Murmushi salma tayi tana girgiza kai
"allah dai yasa yadda kike son umar shima yana sonki haka"
Rauda ta jingina tana lumshe idanuwanta
"aganina salma ayanzu dai babu wanda yakai umar sona
Saboda kullum maganarsa batawuce idan babu ni baze iya rayuwa"
Dariya salma takuma yi
"lallaikam kunason junanku dayawa,amma dai kada wannan son yasa kibada kanki da ankaiki ehe
Kija aji kidan bashi wuya tukunna
Bude idanu rauda tayi tanayima salma wani irin kallo
"lallai salma bakida saiti,tunda nike aduniya bantaba yima umar musu ba
Ko bani da lafiya nakasa cin abinci idan yacemin inci sainaci kobadadi
Haka bacci ma kobanaji idan yace inyi dole nikeyi alokacin
Anguwa ma haka idan yace kar inje to ko inason zuwa fasawa nikeyi
Kekomai idan Umar yace inyi atake nikeyi bana bata lokaci
Bare kuma abunda ya dade yana muradi sai kawai in hanasa saboda wani ajin banza......
"Ya isa ya isa mamar soyayya"
Salma tafada tana mikewa
Sannan tacigaba dacewa
Yanzu nasan ko rijiya Umar yace kifada fadawa zakiyi wannan soyayyar taki tayi yawa wallahi
Dariya Rauda tayi
"najidai koma mezakice dan haka kigayawa wa'ancan
(sauran kawayen)
Dannaji suna zancen kwana babu wacce zata kwananmin agida"
Baki Rauda tarike
"eyyeh lallaima Rauda yazune bakinki yabude ko?
Amma dazu ko ihin kasa furtawa kikayi
To kwana ko zamuyi yazama dole"
Waro idanu Rauda tayi tanajin kamar mafarki takeyi
Yayinda taji ana sanarwa
"andaura auran umar da Rauda bisa ga sadaki naira dubu dari
Cinta,shanta,suturarta duk sunkoma kan umar
Jama a sunshaida
Fatiha
Runkunkume salma tayi tanfadin
"kinji abunda kunnuwa na sukaji salma"
Salma tadaga kai
"naji andaura auran Rauda da umar"
Durkushewa Rauda tayi,tayi sujada ga ubangiji
Tana fadin allah nagodemaka allah nagodemaka
Wayarta tafara kara tadago ahankali tana duban wayar
Salma tamikamata wayar tanufi hanyar fita tana cewa
"kinga bari naje muciga da shirye shirye tunda dai allah ya yadda"
Kallon wayar tayi ganin numban umar yasa tadauka
Cikin tattausar muryarsa mesata natsuwa aduk sanda tajita yace
"madam yadai"
Fashewa tayi da kuka wanda batasan ko namenene bane
"haba madam kukan kuma namene?
Yatambaya yana sassauta muryarsa
Cikin kukan tace
"yau tunda natashi nike kiranka amma wayarka akashe kasa hankalina yatashi...
Yakatseta"haba honey,kema kinsan hakanan dai bazan kashe wayata ba
Kinsan hidimar bikinnan jiya agajiye nakoma gida dasafe kuma mutanene suka addabeni da kira
Shiyasa nakashe"
Numfashi tasauke
"kasani cikin fargaba da tsoro bazan iya kwatantamaka tashin hankalin dashiga ba"
Murmushi yayi wanda tajiyo sautinsa
"kiyi hakuri bama jina kadai ba yanzu gabadayana nazama naki
Mallakinki ke kadai
Murmushi ya subucemata zuciyarta har harbawa takeyi saboda tsananin farinciki
"jaana"
(sunan datake kiransa kenan)
Takira sunan ahankali sannan tacigaba dacewa
"ina sonka bazan iya kwatanta kaunar danike maka ba.....
Ya katseta
"chuchu inasonki fiye da yadda kikesona,
Inasonki fiyeda yadda nikeson kaina
Zan iya yin komai akanki zan iya yin komai dan inga nakasance
Tare dake har abada
Kece farinciki
Lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen farinciki masu dumi suka gangaromata
Anty larai ce tashigo dakin tana salallami
"wai dama amaryan tananan ko wanka batayi ba bare tashirya?
Ga jama a saikara cika sukeyi?
Murmushi Rauda tayi,tayi kasa da muryarta tare da kara matse wayar akunnenta
"jaana bari naje nayi wanka "
Yace to afito lafiya
Yarfillo
[20/10, 8:34 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU( *Yar Fillo*)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to aisha a ibrahim
🅿AGE📕 2⃣
Cikin kankanin lokaci aka tsantsara mata kwalliya
Take kyawunta yakara fitowa
Farinciki agunta kuwa baya misaltuwa bakinta yakasa rufuwa
Haka mahaifiyarta ma itama farinciki gareta baya misaltuwa
Karfe hudu suka kammala shirin zuwa reception
Motocine manya masu tsadan gaske sukazo daukansu zuwa gurin reception din
ansha shagali sosai saikarfe bakwai akatashi Harsu salma sunshigo motar datake
Abokin umar yazo yace sukoma dayar motar
Wannan motar amarya da angone zasushiga
Basuyi musu ba suka koma dayar motar
Saida motocin suka gama tafiya sannan umar yashiga motar
Tanazaune tayi shuru tana tunani batasan yashiga motarba harsaida yashafamata wuya
Tadanyi firgigit tana kallonsa
Murmushi yayi yanafadin
"matsoraciya tunanin mekikeyi?
Girgiza kai tayi
"babu komai"
Ya gyada kai
"ook fadamin wani hotel kikeso muje mukwana"
Danzaro ido tayi tana kallonsa
"hotel kuma?
Yadaga gira
"yes hotel ko da aurena zan kwana nikadaine?
Ta rausayar da kai
"dan allah kabar wasa mutafi gida"
Ya gyara zamansa yana fuskantarta
"allah dagaske nikeyi da aurena bazan kwana nikadai ba idan bazaki zabi
Hotel din dakikeso ba nizanzaba"
Ganin dagaske yikeyi yasa ta marairaice fuska
"haba jaana kaima kasan abunda bazeyuwu bane.....
"mene bazeyuwuba?
Yakatseta ya na hade fuska
Tasauke numfashi
"tayaya bamu tare ba zamutafi hotel?
"keba matata bace?
Yawurgo mata tambayar
"matarka ce mana amma......
Yadaga mata hannu
"kinga dakata!
Banason wasu surutai marasa tushe ke matata ce ina da ikon dazanyi duk yadda naga dama dake
Zata kuma magana yakuma katseta
"nace taredake zan kwana idan kuma tunyanzu zakifara min gardamane sai inji"
Shuru tayi tana kallonsa tarasa tayadda zatamai magana yafahimta
Ganin zetada motar yasa tarike mai hannu tana langabar dakai
"jaana please kayi hakuri kasani bazantaba iya yima musu ba amma hakan badai dai bane
Duk da nasan ba haramun bane dan na kwana tare da kai
Amma surutun mutane nike gudu
Kaga za a daukeni marar kunya
Kayi hakuri gobe iyanzu inadakinka duk abinda kaga dama saikayi amma kayimin hakurin yau please"
Bekara cemata komai ba yatada motar ya nufi hanyar gida da ita
Kallonsa kawai takeyi tasan ransa yabaci itama saitaji zuciyarta babu dadi
kwata-kwata batason ganin bacin ransa
"jaana.....
Zatai magana yayi saurin dakatar da ita tahanyar daga mata hannu batare da ya ko dubeta ba
"inace gida kikace inkaiki?
Tadaga kai
Yacigaba da cewa"to yanzu hanyar gidan nikeyi ai dan haka banason surutu please"
Jikinta yayi sanyi takuma kai hannunta tarike nasa
"muje hotel din inhar zuwan zesaka farinciki"
Fakawa yayi agefen titi yazuba mata manyan idanuwansa masu juya mata lissafi
"bazantaba yimiki abunda bakyaso ba chuchu,danhaka kibari kawai ba fushi nayi ba kawai dai banji dadi bane"
"amma....
Shhhhhhh yadora yatsunsa biyu akan dan karamin bakinta
"nacemiki banyi fushi bakarki damu,dayau da goben ai duk na allah ne
Kuma goben kaman yaune"
Yakarasa maganar yana sakin fuskarsa
Sai lokacin taji hankalinta yakwanta bata kaunar bacin ransa kwata
"nagode mijina dakafahimceni"
Yasakarmata murmushi tare da shafa gefen fuskarta
"bar wani jindadi gobe zaki gane kurenki ne yarinya"
dariya tayi tana kauda kanta
Washegari karfe goma nasafe sukabar kaduna zuwa garin abuja
Iyayenta sunyimata fada da nasiha sosai
Taci kuka kamar ranta zefita dan tanada kawa zuci sosai ko tafiyar kwana biyu tayi allah allah takeyi takoma inko tayi sati to dama wajibine saitayi rashin lafiya
To bare wannan da tafiyar dun-dun-dunce saidai takaima gidansu ziyara
Saiwajen karfe shabiyu suka isa birnin tarayya
Cikin wata hadaddiyar unguwa suka shiga wani kayatacce fankacecen gida me kama da gidan sanator
ko nawani gomna gidan yatsaru sosai gaba d'aya wadanda suka rakota sakin baki sukayi suna kallon gidan
Wasu daga cikinsu suna fadin
"gaskiya Rauda ta dace"
Yan uwan Umar ne suka futo da ga ciki yayarsa me suna kaltum itace tazo tarungumota
Tana rangada buda
Nandanan sauran suka fara yan wake-wakensu na buzaye
Ahaka suka shiga kayataccen falon dayasha kayan alatu
Atsakiyar falon anty kaltum tazaunar da ita inda sauran suka zagayeta
Anty kaltum tayaye lullubin da ke kan rauda fuskarsa ta bayanna
"masha allah"
Sauran yan uwansa suka fara fada suna yaba kyanta
Kasa tayi dakanta dangani takeyi kaman zaginta sukeyi yadda sukeda tsananin kyau har zasu dubeta su kirata kyakkyawa
Ba abata lokaci ba aka cika gabansu da abinci kala kala
Saiwajen karfe biyar yan kaduna suka fara shirin komawa
Fada suka kara yimata sosai sannan suka juyo
Suma yan uwan umar din fashewa sukayi yan kaduna suka juyo yan niger suka nufi masaukinsu
Anty kaltum ce kawai tarage itama kuma tanajiran zuwan angwaye ne takama gabanta
Wanka tasa Rauda takumayi taciromata wani leshi rantsatsse tasa
Sannan tazauna tatsaramata kwalliya kasancewar ta kware afannin kwalliya
Saida akayi sallar issha sannan umar yashigo tare da babban abokinsa zayyad
Nan itama takarayimusu tata nasihar sannan tamusu sallama shima zayyad yayimusu nasa
Sannan yayimusu saida safe
Umar yarakasa yarufe kofofin
Tanazaune saman gado inda yabarta yashigo yana zuba kamshi
Yazauna kusa da ita yasa hannu ya tallabo fuskarta
Suka hada ido
Jitayi gabanta yafadi wanda batasan dalilin faduwar tasa ba
Yasakar mata murmushi
"yadai amarya kinwani yi shuru ko duk jimamin rabuwa da mamane?
Takakaro murmushi
"kaman kasani jinikeyi kaman intashi inkoma"
Yayi yar dariya har fararen hakoransa suka bayyana
"lallai yarinya bakiji dakyau ba keda zuwa kaduna saikin shekara kila ma da jariri zakijemusu"
Dariyar itama tayi
"ai inayin sati biyu zanje"
Ya jinjina kai
"lallai kam"
Tashi kidaukomana plate muci abinci dannasan yau bakici komai
Tamike tabude kofar dakin tafara saukowa daga step tana karema falon kallo
Azuciyarta tana yaba kyansa dakuma kokarin mijinnata
Ta murda kofar kicin din
Komai ashirye yike tsaf-tsaf
Tayi guntun murmushin jindadi
Lallai umar yanasonta dayawa dan ko tsinke kinyarda ayimata yayi shi yayi komai
Tazaro plate daya acikin kitchenwire
Tajuyo zata fita
"kwaram"
Taji karar wani plate din yafado
Tajuya tana cewa garin saurina banciro ahankali ba
Tagyara su tsaf sannan takuma juya
Hartakai bakin kofa takuma jin karar faduwar plates din
Dasauri tajuyo plates biyu tagani akasa
Gabanta yafadi take taji tsoro yafara kamata
Bata koma dauke plates dinba gaba kawai tayi tarufo kofar kicin din
Tafara tafiya dasauri tahau step.
Tahau daya biyu uku tatsaya cak.
Wani fargaba da tsoro yakuma kamata
Jitayi kaman ana bin sawunta
Tayi karfin halin juyawa amma bata ga kowa ba
Dasauri tacigaba da hawa harda tuntube gurin shiga dakin
Kallonta yayi yana fadin
"lafiya madam?
Zama tayi tana dan sauke numfashi
"jinayi kaman wani yanabina"
Dariya yayi
"oh my dear tsoronki yayi yawa wallahi waye zebiyoki?bayan kinsan gidannan dagani saike?
Hmmmmmmmm
Tasauke ajiyar zuciya
"nidai yanzu bazankara fita nikadai ba saidai muje tare"
Yagirgiza kai yana murmushi
"to madam ai duk yadda kikace haka za ayi"
Ya amshi plates din yajuye gasassun kaji biyu aciki
Sannan yafara bata abaki
Saida yaga takoshi dam sannan ya kyaleta
Yakwashe kayan yamaidasu gefe sannan yadauro alwala itama yace tadauro
Sallah raka a biyu sukayi yayimata tambayoyi game da addininta ta amsa mai
Sannan yadafa kanta ya dinga kwarara addu o i
Sunmike kenan yana ninke darduma wayarsa tafara kara
Ganin numban asibi ne yasa ya dauka
Magana uku yayi yace "ook kubashi taimakon gaggawa ganinan zuwa"
Ya ajiye wayar yana dubanta
"baby kirane daga asibiti wai ankawo wani emergency"
Kallonsa tayi sosai
"toyanzu mekake nufi?
"zuwa zanyimana chuchu ceton raine fa?
Waro idanuwanta tayi tana kallon agogo sannan tamaida idanuwanta kansa
"yanzufa karfe shabiyu"
Yadaga kai
"nasani ai amma ai komin dare dole infita tunda aikinane
"
Nan danan idanuwanta suka cicciko da kwalla
Matsowa yayi gab da ita yajanyota jikinsa
"please honey kiyi hakuri naje ance mutumin yana cikin wani hali please....
Dago kanta tayi daga jikinsa
Tazuba masa fararen idanuwanta
"amma kasan bazan iya kwana nikadai acikin gidan nan ba ko?saidai inmutafi tare"
Ya waro ido
"dawa?baze yuwu ba ba bu inda zakije acikin darannan
Nima dan yazamarmin dole ne
Danhaka kikwanta kiyi baccinki inagamawa zandawo
Zata kuma magana ya katseta
"chuchu bata lokacinnan danikeyi bawan allahn can ze iya rasa ransa da haka natafi
Yakarasa fada yana ficewa da sauri
Bin bayansa tayi da kallo cike da tsananin damuwa dan ita ko agida batasaba kwana itakadai
Bare awannan katoton gidan
Zama tayi turus gefen gado yayinda taji tashin motarsa
Tayi shuru tana tunanin yadda zatayi
Ga iskar hadari tanata kadawa
Mikewa tayi ta janyo windon dakin dayike abude iska nata kadashi
Rufe windon yayi dede da dauke wutar gidan
Kirjinta yabuga dam take matsanancin tsoro yakamata
Tayi karfin halin dawowa bakin gadon tasa hannu tana laluben wayarta
Jitayi antaba mata kafa dasauri tahaye gadon tana karanto duk addu o in da suka zo bakinta
Yarfillo.
[20/10, 8:35 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
🅿AGE📕 3⃣
Dakyar ta iya lalubo wayar gabadaya firgici da tsoro sungama kamata
Hannunta na rawa takunna fitilar wayar,tahaska tsakar dakin inda takejin kaman akwai wani atsaye
Saidai bataga kowaba,ajiyar zuciya tasauke me nawi
Tajingina da jikin gadon tana maida numfashi.
Amma idanuwanta sunkasa tsayawa wuri daya kalle-kallen dakin kawai takeyi
Azuciyarta kuma tana karanto addu'o in neman tsari.
Dai-dai lokacin akafara ruwan sama wanda yataho da karfi kaman da bakin kwarya
Hankalinta yakara tashi dantasan yadda ruwan yataho da karfi,to lallai sai anyi tsawa,itakuma allah ya jarabceta da jin tsoron tsawa
Takurewa tayi guri daya ko motsin kirki takasa yi
Ahankali taji karar bude kofar falon sannan taji anrufe
Daga bisani tajiyo karar tafiya kamar ana haurowa saman
Babu inda baya rawa ajikinta saboda tsabar tsorata,gabadaya ta daburce
Addu'o inma sunbace mata
Inbanda ayatul kursiyyu ba abunda bakinta ke iya furtawa,itama din bata kaiwa karshenta take dawowa farko.
Jin karar sawun tafiyan daf da kofar dakin datakeciki,yasa ta cusa kanta cikin gwiwo winta
Danbataso taga abunda ze shigo din tasan ba alheri bane
Murda kofar dakin akayi
Da karfi tafara karanta ayatul kursiyyu,amma har lokacin takasa dago kanta bare taga me shigowar,
Jitayi andafata,takwala ihu tana fadin
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un !
Muryar umar taji yana fadin
"lafiya madam meke faruwane haka?
Tabude idanuwanta da sauri,ganin shine yasa ta rungume sa dasauri gami da fashewa da kuka.
Zaunawa yayi tana rungume ajinkinsa
"meyake faruwane?fadamin mana"
Cikin kuka tafara magana tana girgiza kai
"bazan iya zama agidannan ba wallahi tsoro nikeji,bazan iyaba"
Yasauke numfashi yana dan bubbuga mata baya ahankali
Cikin sigar rarrashi yace
"ok..ok kiyi shuru hakanan banason kukannan please"
Saida tadan dauki lokaci sannan tadena kukan takomai sauke numfashi ahankali
Ya dagota daga jikinsa yazuba mata kyawawan idanuwansa
"chuchu,meyasa kikeda tsoro dayawane? Bakisan yawan tsoro babu kyau ba?
Ta ajiye numfashi tace
"to ba laifinka bane katafi kabarni a wannan daren,badole inji tsoro ba"
Shima numfashin yasauke
"toyanzu da bandawo ba fa?dole fa kikoyi rage tsoronnan saboda kinsan aikina,
Ana iya kirana ako wani lokaci"
Ta jinjina mai kawai sannan tace
"waima ya akayi kadawo?bakace zakaje kaduba mara lafiya bane,kuma ya akayi banji tsayuwar motarka ba?
Yayi dan murmushi
"wallahi inazuwa natadda doctor zubairu a asibitin,yanata yima nurse din data kirana fada
Wai akanme tasan yaune natare zata kirani,shine yacemin injuyo shi zeduba marar lafiyan
Karar mota kuma ya zayi kiji?bayan kin sama zuciyarki tsoro,sannan kuma kinmanta ruwa akeyi?
Tagyada kai
"hakane amma please jaana karka kara barina nikadai wallahi inajin tsoro sai intajin wasu abubuwan tsoro dayawa"
yayi murmushi dayakara bayyana kyan fuskarsa
"dama koda yaushe ni inatare dake,danhaka kirage tsoro kinji"
Ta gyada kai tana nata murmushin
"tom insha allahu zan rage"
Yakwanta gamida kwanto da ita jikinsa
"chuchu ina alkawarina na jiya?
Tadanzame
"tomiye nasauri jaana,nifa takace"
Dariya yayi ya kashe fitilar wayartata
Misalin karfe uku da rabi,suna rungume da juna yana shafa sumar kanta
"chuchu allah yayimiki albarka hakika ke tadabance kinsanyani farinciki mara misaltuwa"
Murmushi tayi tanajin wani sanyi acikin zuciyarta
"jaana inasonka,kayimin alkawarin bazaka taba rabuwa dani ba"
hannu yasa yadago fuskarta suna kallon juna
Tasauke ajiyar zuciya
"hmmmmmm hakika nayi dace da miji kyakkyawa wanda samun irinsa aduniya ze yi matukar wahala,amma ina fargaban kada watarana wata takwacemin kai"
ya girgiza kai
"bakisan irin son danakemiki ba chuchu,zan iyayin komai akanki kuma babu wacce ta isa takwace soyayyata agareki
Maganar yimiki alkawari kuwa,nayi ada kuma ayanzu ma zankuma yimiki
bazan taba rabuwa dake ba....."
Ta lumshe idanuwanta ahankali farinciki yakuma lullubeta
Gani takeyi kamar ayanzu bata da wata sauran matsala arayuwarta
Kara shigewa jikinsa tayi bacci medadi yadauketa.
Washegari sai wajen karfe bakwai tafarka
ganin haske yagauraye dakin yasa ta kalli agogo
Karfe bakwai harda mintoci.
Takalli gefenta inda yakwanta, baya wurin
Mikewa tayi tashiga toilet tayi wanka tadauro alwala
Ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar ta ninke dardumar tanufi wardrop tanajin jikinta nayimata tsami dan gabadaya ciwo yikeyi.
Riga doguwa tadauko tasa,sannan tasauko daga saman dantasan yana kasan
Saidai bataganshi a falon ba,taduba kicin nanma baya ciki
"ina yaje"
Tayi wa kanta tambayar
Zuciyarta ce tabata amsa
"kila yaje siyomuku abun kari ne"
Tagyada kai dantasan baze wuce hakan ba
Falon tadawo tazauna adaya daga cikin kujerun
Tadanna kiran numban mama
Ringing biyu tadauka suka fara gaisawa.
Kwan-kwasa kofar akafara yi
Tamike da wayar akunnenta tabude
Umar ne tsaye rike da rigarsa ta likitoci
Suka sakarma juna murmushi
Katse wayar tayi tanacewa
"ina kwana"
Ya janyo hannunta tafada kan faffadan kirjinsa
"wayace miki haka ake tarban miji?kintsaya daga nesa kina wani cewa ina kwana"
Tayi kasa dakanta cike da jin kunyarsa
Suka karasa cikin falon yana rike da ita
A three seater suka zauna,ya ajiye rigar ahannun kujera yanacewa
"wallahi nagaji kokadan jiya ban runtsa ba,amma nasan ke barcinki kikai harda munshari"
Megadi ne yayi sallama
Ya miko ya miko wani kwando cike da kayan karin kumallo yace anty kaltum ce ta aiko dashi
Umar yamike
"kinga jera abincinnan akan dining bari in watso ruwa"
Tadauki kwandon ta kai kan dining din ta jejjera komai,tazauna tana jiransa.
Befi minti goma da shiga ba yafito sanye da three-quater da T-shirt
Yazauna a kujerar dake fuskantarta suka fara karyawa yana janta da fira
"shine ko kitambayeni ya me jiki ko?
Yafada yana kai kofin tea bakinsa
"yihakuri yanzu nike shirin intambayeka"
Ya gyada kai
"ook ai bawan allahnnan ya jigata dayawa motarsa karkashin traler fa tashige da kyar muka iya ceto ransa danni banyi zaton ma zeyi rai ba"
Tadakata daga kurban tea din datakeyi tana kallonsa dan bata fahimci abunda yike nufi ba
Shima kalonnata yayi ganin takafashe da ido yasa yace
"yadai?naga kinayimin wani irin kallo,kamar bakigane abunda nike cewa ba"
Ta jinjina kai
"to gani nayi ba kai kayi aikinnan ba,doctor zubairu ne yayi amma kana cewa da kyar kuka ceto rayuwarsa
Kallon rashin fahimtar shima yafara yimata
"bangane ba,wani doctor zubairu kuma?
"doctor zubairu na asibitin ku mana"
Tabashi amsa atakaice
Yagyara zamansa yana maida hankalinsa akanta
"wai wani doctor zubairun kike magana akansa?
Doctor zubairun da watansa biyu kenan a kasar china"
Takauda idanuwanta akansa,tamaida kan wayar ta, tana duba sakon da aka turo mata
"to nidai bansani ba,kaida bakinka jiya kace doctor zubairu yace kadawo gida bekamata kafita aiki a daren jiya ba"
Har lokacin idanuwansa nakanta
"ayaushe nace miki hakan?
"a jiya da kadawo mana"
Tabashi amsa cikin kosawa da zancen dan dan tafahimci so yike yamaida abun wasa
"nifa bandawo gidannan jiya ba"
Yafada
Tadago kanta daga kan wayar suka hada idanu
"mekace?
Ta tambaya dan tabbatar da jin abunda yace
"nace bandawo jiya bani,tunda mukai natafi asibiti bandawo gidannan ba sai a safiyarnan"
Ganin fuskarsa ba bu alamar wasa yasa tace
"wai meyasa kaketa wasu maganganu da bangane bane,jiya bakadawo ba,misalin shabiyu da rabi?
Ta girgiza kai
"saidai in mafarki kikayi danni lokacin ma ina emergency room"
Ta gyada kai
"dan allah kabar wasannan haka"
Hannunta yakama
"kedai zancema wa kibar wasan haka,nida na kwana asibiti zaki wani ce wai nadawo gida...........
Takatse shi
"jaana please wasan ya isa haka"
Ya jingina bayansa da kujerar dining yana kallonta
"chuchu i'm serious saidai in mafarki kikayi amma ni wallahi bandawo gidannan ba"
Jin yayi rantsuwa yasa gabanta yafara faduwa
"jaana harda rantsuwa?
Ya jinjina kai
"to nafadamiki mafarki kikayi baki yarda ba.......
"to dawaye na kwana jiya?
Takatsesa da sauri
"kwana kuma?banganeba"
Ta jinjina kai yanayinta yafara komawa na firgici
"jaana wallahi jiya kadawo kacemin doctor zubairu ya amsheka,kuma tare dakai muka kwana."
Wani kallo yayimata gami da cewa
"kidawo hankalinki please,ban kwana agidannan ba..............
Yarfillo.
[20/10, 8:35 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
Wannan page din nakine anty nabila ina godiya da kokarinki gareni allah yabar zumunci
🅿AGE📕 4⃣
Dire kofin tayi,ranta yadan soma baci,akanmene yikeso yayi mata wasa da hankali?
"wai meke damunka ne? Indawo hankalina kamar yaya?tayaya munkwana dakai zaka cemin kai ba a gidannan kakwana ba........
Buga teburin yayi dan shima nashi ran yasoma bacin
"nace miki a asibiti nakwana!
Jikinta yasoma bari,zuciyarta tafara rawa
Zagayawa tayi inda yike ta durkusa tadafa gwiwowinsa
"jaana kasan bama irin wasannan ko?dan allah kafadamin dagaske ne baka kwana agidana?
Wani irin kallo yikemata nawacce tafara tabuwa
"chuchu wallahi a asibiti nakwana......
matsawa tayi arazane idanuwanta suka cicciko
Cikin rawar murya tace
"inna lillahi wa inna ilaihi ra'ji un.......
Kallonta kawai yikeyi
Maganar malan ce tadawo mata
"kirike wannan lemun tsamin kitabbatar dakin shiga dashi cikin gidanki
Aranar da kika kwana daya kibude kullin da lemun tsamin ke ciki
Idan kiga yananan akalarsa to tabbas munyi nasara a wannan aikin da mukayi na karshe
Idan kuma kiga yacanza kala zuwa ja,to tabbas akwai matsala
Wannan lemun tsamin yana dauke da magunguna masu karfin gaske kitabbata kinshiga dashi"
Mikewa tayi dasauri tafara hawa step dagudu
Tanajin umar yana kiranta bata tsaya ba,harsaida tashiga bedroom dinta
Handbag din ta tadauko ta zazzage kayan dake ciki
Hannunta na rawa tadauki kullin lemun tsamin tafara kwancewa
Gabanta nafaduwa
Saidai me,tana gama kwance kullin taga lemun tsamin yayi jawur
Ihu takwala ta wurgar dashi
Dai-dai lokacin umar yashigo dakin
"chuchu me kikeyi ne wai.......
Kankamesa tayi dasauri jikinta narawa
"Aasim!Aasim!"
Yadagota dasauri
"Aasim kuma?
Cikin kuka tafara cewa
"nashiga uku jaana Aasim yanatare dani haryanzu,wallahi jiya ba mafarki nayi ba shi yazomin a suffarka.........
Kamata yayi suka zauna akan gadon yakura mata ido yana karantar yanayinta
"Aasim chuchu?ba malan yace anriga da ankullesa a kwalba ba?
Ta jinjina kai dasauri
"haka yace amma lemun tsamin dayabani yacanza kala kuma.....kuma jiya inatajin anatsoratani sannan yazomin asuffarka"
Rungumeta yayi yana shafa bayanta
"okay,okay,kwantar da hankalinki please bari inkira wayar malan din"
Yazaro wayarsa daga aljihu yadanna numban malan saidai kira biyu yana masa bedauka ba
Yakuma danna kiran a karo na uku,saida takusan tsinkewa sannan aka daga
Yayi sallama yana fadin
"ina kwana malan,antashi lafiya?
Daga can bangaren wani ne ya amsa
"ba malan bane,malan allah yayi masa rasuwa jiya da daddare yanzu haka muna shirin kaisa makwancinsa"
"inna lillahi wa inna ilaihi ra'ji un,ya rasu?hatsari yayi kome?
daga can bangaren ya amsa
"wallahi lafiyarsa lau ya kwanta saidai dubawa akayi akaga yarasu"
Ajiye wayar yayi yana share gumin da ke keto masa a goshi
Itako kuka tafashe dashi tana fadin
"wayyoh allah na,nashiga uku!!
Be hanata kukantaba,zura mata ido kawai yayi zuciyarsa cike da damuwa
Da tarin fargaba,me yike shirin faruwa da sune?
Jiyayi kansa yayi wani dum
"la ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin"
Bakinsa ya furta ahankali
Sannan
Ya kira sunanta a sanyaye
"Rauda.....
Sanin kankine kukannan ba bu maganin da zemana face yajanyo miki ciwon kai,
Kiyi shuru kidaina kukan haka,munemi mafita......
Dagaowa tayi tana kallonsa da jikakkun idanunta
"mafita?a ina zamu samo mafitar jaana?gurin malan isah ne kadai muka sa ran zamu sami mafita,
Amma gashi,sanadiyyar taimakona har ya rasa ransa nasan.......
Ya girgiza kai
"malan kwanan sa ne yakare,kuma na tabbata zamu samu waraka awani gurin.
Abinda nikeso dake,ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta jinjina mai kai kawai amma ita kadai tasan tashin hankalin datake ciki.
Shima din dauriya yayi kawai amma zuciyar sa cike taf da da damuwa.
Yarasa wani irin al'amarine wannan me cike da rudani
Ya kalli fuskarta,tayi kuka harta gaji bacci yadauketa.
Kwantar da ita yayi
Ya mike,yana zagagaye acikin dakin yana tunanin ta inda ze bullo ma al'amarin
Itako Rauda mafarki takeyi cikin barcinta,malan isa tagani zaune yana lazumi
Saiga hayaki yafara shigowa dakin dayike,kan kace kwabo jijiyoyin wuyansa sun mummurde,idanuwansa sun kakkafe
Zuwa can taga yazame kasa,alamun numfashin sa yadauke
Dariya taji anfara yi me tsoratarwa daga bisani taga wani farin saurayi yabayanna
Dariyar ya cigaba dayi,lokaci daya kuma ya murtuke fuska kamar bashi yagama yin dariyar ba.
Yakalli malan isa yana nuna sa da da yatsa
"kallesa,wai shi ze ja dani,ni Aasim"
Ya girgiza kai yana cigaba dacewa
"bazaka iya ba! Bazaka iya ba!
Na gargadeka tun farko amma kayi taurin kai kana ganin kaman zaka iya ja dani......"
Yadan durkusa sai saitin malan isan
"tashi mana! Tashi kaciga ba da aikin da kakeyi.........bazaka iya ba,bazaka iya ba ko?
Ya mike tsaye yana cigaba da yin dariyar sannan ya dubeta da razanannun idanunsa
"kinsa nayi abunda ban taba yi ba,tunda nike aduniya bantaba kisa ba
Amma gashi sanadinki kinsa nafara,kinsa naka sheshi.......
Yakara sa fada idanuwansa na kuma runewa
"Kiyi babban kuskure a rayuwanki,da kika karya sharuddan dana gindaya akanki
Mafi girman kuskuren da kikayi kuwa,shine dakika bari na kusanceki azahiri..."
"kisani daga yanzu kinrabu da farin ciki,kwanciyar hankali sannan abunda zance miki na karshe shine
Idan har kinason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki dan duk ranar daya yi hakan to tabbas ze mutu kamar yadda wannan ya mutu!!!!!
Yakara sa fada yana nuna malan isa sannan yakuma fashewa da dariya
A razane tafarka jikinta nabari
Umar dake ta patrol acikin dakin yadawo bakin gadon dasauri
Rirrikesa tayi tana waige-waige
"shine yakashe shi,wayyoh allah na!!!
Bayi da bukatar tambayarta dan yasan mafarki tayi
Rungumeta yayi kawai,azuciyarsa yana jin tausayinta
"dan allah kada kabarni koda na minti dayane,cutar dani zeyi"
Tafada jikinta na kakkarwa
Ya jinjina kai
"zan kasance tare dake,akodayaushe,babu abunda zesameki da izinin allah"
Yarfillo.
[20/10, 8:36 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little Hajjo
*_A kullum forum dinmu Kara bunk'asa yakeyi,mutanen cikinsa Kara basira da fasaha sukeyi,ina jinjina ma golden writters Allah yabar zumunci a tsakaninmu_*
_GAISUWA Ga *MATAN K'WARAI* group *yar fillo* na godiya da addu'o inku gareta,ina Kuma Jin dadin yadda kuke yaba labarina,ina godiya sosai_
🅿AGE📕 5⃣
Hannunsa takama,Tana kallonsa da jik'akk'un idanuwanta da suka yi luhu-luhu
"Jaana,kayi min alkawarin duk rintsi bazaka taba rabuwa Dani ba,nasan matsala yanzu muka fara ganinta......
Ya sauke numfashi Yana kallon cikin idanuwanta
"Chuchu kina tunanin akwai abunda ze bani tsoro har yasa nai tunanin rabuwa dake?”
Ya girgiza Kai sannan yaciga ba da cewa
"Son Dana ke yimiki,ba k'aramin so bane,kuma bana tunanin akwai abunda ze razanani akanki,nasan yayi hakane Dan yasanya shakku da fitina atsakaninmu Amma ni ina k'aunarki Kuma ko me zeyi sai dai yayi Amma tarayya dake yanzu nafara Kuma ashirye Nike da indauki duk wani abun da zezo dashi"
Ta maida kanta kan k'irjinsa,tanajin zuciyarta babu dadi
"Nasan zaka iya jure komai,Amma ina Jin tsoro,nafi kowa sanin waye Aasim,abunda ze iya?da abunda baze iya ba.
Nasan ze iyayin komai domin yaga yarabani da kowa,baze cutar Dani ba,ina da tabbacin hakan Amma........
Tadan dakata Tana share hawayen dake ambaliya a fuskarta,sannan tacigaba
"Kai ze iya cutar da Kai,banason wani Abu yasameka abunda Nike tsoro kenan"
Murmushi yayi me dauke da damuwa
"Kinmanta da cewa Allah Yana tare damu?idan har muka rike addu'a,to tabbas muna tare da kariyar Allah a kodayaushe.
Dan Haka kikwantar da hankalinki,zankira zayyad akwai wani malami dayace yasani a k'auyensu,sai muji yadda za'ayi"
"A'a,banaso wani yak'ara rasa ransa a sanadina"
Tafara cikin karyewar zuciya
"Hmmmmmmmmm!!
Yakuma sauke numfashi
"To Rauda zamu zauna hakane?dole mukuma neman mafita,tun abun beyi k'arfi ba"
Shuru tayimai kawai,Amma ita ta Riga da ta Gama karaya
Wunin ranar be leka ko kofar gida ba,Dan yasan a tsorace take,hatta salloli agida yayi.
Abincin Rana Dana dare duk anty kaltum ce ta aikomusu,Dan Basu da nisa sosai
Bawani cin abincin sukayi dayawa ba,Dan hankalinsu ba a kwance yike ba.
Suna zaune a kan kujera,da daddare,bayan sun kammala cin abinci,yamike Yana maida sauran kula
"bari in d'an watsa ruwa,yanzu zandawo"
Ta gyad'a mai,batare da tace komai ba.
Sama ya haura yashiga bedroom dinsa,yarage saura ita kadai a falon
Tunanin Daren jiya kawai takeyi da abunda ya wakana atsakaninta da Wanda ba jinsinta ba,
Zuciyarta ce take ta haskomata lokacin, gani takeyi Kamar mafarki takeyi.
Karar da TV d'in falon yikeyi ne yafara damunta,ganin hankalinta bama akan TV d'in yike ba,yasa tadauki remote d'in dake dake gefen kujerar takashe
Ko second biyu batayi da kashewa ba ya kunnu
Ta Kuma d'aukar remote d'in takuma kashewa,still ya sake kunnuwa.
Gajeren tsaki taja tamik'e ta zare socket din,tajuyo zata dawo kan kujerar
Karar TV d'inne yasa ta tsaya cak,tare da juyawa ahankali
Still TVn yasake kunnuwa
Takalli socket d'in da ta zare Yana nan akasa Amma Kuma TV Yana aiki
Tsoro yafara kamata,zuciyarta tafara rawa
Ta kalli cikin TVn,wasu mutane tagani a zazzaune sanye da bak'ak'en Kaya sunyi kasa da kansu suna karatu da wani yare
Zuwa can suka d'ago suka kalleta da manyan idanuwansu da yike bak'kk'irin babu wani alamar fari acikinsa.
Tayi baya dasauri jikinta yafara rawa
Hannayensu suka d'ago sunayimata alamar Kira
"Ta'al huna Rauda!
Ta'al huna Rauda!"
Zuciyarta tafara bugawa da k'arfi kaman zata fito waje saboda tsananin razana
Matsowa sukeyi suna Kuma fadin
"Ta'al huna!
A razane tajuya da gudu,Tafara hayewa saman,maganganunsu kawai ke yimata yawo akunne tanajin sautin muryarsu yana dad'a k'aruwa
Ta banka k'ofar bedroom dinsa da k'arfi,tare da tura k'ofar bayin
Yana tsaye jikin shower,Yana sakar ma kansa ruwan sanyi
K'an-k'amesa tayi jikinta na kyar-kyarwa
“gasu can.......kirana sukeyi,d'aukata zasuyi,kataimakeni kafitar Dani daga cikin gidannan......
"Suwaye?”
Yatambayeta dasauri
Kasa bashi amsa tayi Dan ta rud'e sosai
K'aramin towel ya d'aura yakamo hannunta suka fito daga bayin
Addu'o I yadinga tofa Mata,zuwa can tadena sambatun datakeyi, Takoma sauke ajiyar zuciya
Ya dauko wani tawul din yafara gogemata gashin kanta daya jike yayinda tashiga bayin
"Aduk sanda kika ga wani Abu na tsoratarwa,ki rinka ambaton sunan Allah kikuma dungayin addu'a,
Tsoratar dakikeyi shizeba masu tsoratar dake damar cutar dake"
tadago kanta tana kallonsa har lokacin jikinta bedena rawa ba
"Bazan iya zama agidannan ba,bazan iya ba,ka maidani gida Dan Allah"
Hmmmmmmmmm yasauke numfashi
"Ko zaki iya gaya min yanayin da mama take ciki a halin yanzu?
Nasan tana cikin farin ciki,da jin dadin kinyi aure,abunda tadade tanason tagani,
Me kike tunanin zataji idan har ta fuskanci kina cikin matsala a halin yanzu?
Yad'an numfasa sannan yacigaba da cewa
"Nasan zata shiga damuwa,da tashin hankali,wanda ze iya tado mata da ciwonta,sam komawarki gida ba mafita bane
Ta yayama daga yin auranki kwananki daya da tarewa ace kinkoma gida,me kike tunanin mutane zasu ce?
Nasan mak'iya dariya zasuyi,Dan haka kicire wannan tunanin a zuciyarki
Badai sai bana tare dake a ke tsorataki ba?
To bazan kara zuwa ko nan da can batare dake ba,ba abunda ze koma tsorataki ina tare dake"
Yak'arasa fada yana share mata hawayen dake gangarowa daga idanuwanta
Tabbas abunda yafada gaskiyane,mama tanacikin farin ciki a halin yanzu
Dole ta hak'ura ta danne damuwarta
Mik'ewa yayi yazaro mata rigar bacci ya mik'a Mata
"Kayan jikinki sun jik'e,kisanya wannan"
Amsa tayi tana dubansa,shid'inma ita yike kallo ganin nawin cire kayan takeyi agabansa yasa yace
"Kinajin kunya ko?to bari infita kisa kayan"
Yak'arasa fada yana juyawa
Da hanzari ta rik'o hannunsa
"Baka ce bakace bazaka k'ara barina nikadai ba?
Ya jinjina Kai
"Eh,Amma ai naga nawin cire kayan kikeji agabana,shiyasa zanfita"
"To nidai karkafita,zan canza ai"
Tafad'a tanayin k'asa da kanta
Ya gyad'a kai yana kafeta da kyawawan idanuwansa
"To canza"
D'ago kanta takumayi suka had'a ido
Ta marai-raice fuska
"To ka dena kallona"
"Aa,bari ma infita kawai"
Yafada Yana niyyar zame hannusa dake rik'e cikin nata
Kara matse hannun nasa tayi tana cewa
"Kayi hakuri"
Ya gyara tsayuwarsa yana k'ara kafeta da ido
Cikin sanyin jiki ta war-ware k'aramin gyalen da ke kanta tadan daura a k'irjinta
Sannan tafara yaye doguwar rigar dake jikinta,cikin sauri tacire rigar tasa hannu zata d'auki rigar baccin
Dakatar da ita yayi tahanyar rik'emata hannu
Kallonsa tayi da rinannun idanunta
"Menene kuma?
Ya sauke gauron numfashi tare dacewa
"Kitsaya ahaka,ina buk'atar ganinki ahaka"
Zatai magana,yajanyota tafad'a jikinsa
Gabanta yafara fad'uwa
"Jaana,kamanta damuwar da muke cikine wai?
Ya girgiza Kai
"Ina sane banmanta ba"
"Amma......
Yakuma katseta
"Chuchu duk wad'annan abubuwan dakika ga anayi,anayine dan ahanamu samun cikar burinmu,shiyasa aka biyo ta wannan hanyar dan aga ankauda tunaninmu akan abunda mukadad'e muna muradi"
Ta girgiza kai
"Amma ai ba ayau ba,kabari sai mundawo cikin natsuwar mu tukunna.......
Yatsunsa biyu yad'aura akan labb'anta
"Kada kibawa azzalumai damar cin galaba akan rayuwar auranmu,nasan da zarar mun cika burinmu to tabbas wannan tsoratakin da akeyi za Adena,Dan dama anayine Dan aga ancanza mana tunani
Maganganun Aasim ne suka fara dawo mata da yi mata yawo akunne
"Idan har kanason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki Dan duk ranar da yayi hakan to tabbas ze mutu Kamar yadda wannan ya mutu"
Umar ya katsemata tunanin da takeyi
"Kada kibari maganganunsa suyi tasiri a zuciyarki,kibani dama zaki tabbatar da abunda Nike fadamiki.....
Yak'ara matseta a jikinsa
Hankalinta yak'ara tashi
"Aa kayi hak'uri Dan Allah,bazan iya ba!
Kallonta yayi sosai, daga bisani ya janye jikinsa ya kwanta agefen gadon yana juya mata baya
Hawaye ne yacigaba da gangaro mata,yaza tayi da rayuwarta ne?
Aduniya babu abunda ta tsana irin taga b'acin ran Umar,Amma yaza ayi ya fahimci irin abubuwan datake gani na razanarwa??
Durk'usawa tayi agaban gadon,cikin kuka tafara cewa
"Dan Allah kayi hak'uri.......
Juyowa yayi ahankali yana kallonta,ya sakar mata murmushin karfin Hali
"Kada kidamu kanki,ki hawo kikwanta,nima nasan ba dai-dai bane inbukaci hakan agareki awannan yanayin danike ciki
Amma idan muka ce zamu biyema wannan al'amarin haka zamuyita zama,kuma kimin uzuri kinfi kowa sanin hak'urin dana dad'e inayi"
Ta jinjina Kai
"Nasani,amma ka gafarceni tukunna Dan Allah"
Ya gyad'a kai yana kuma yimata murmushi tare da dagota
Suka kwanta suna fuskantar juna
"Karki damu,kiyi baccinki Amma kibari in rungumeki ki kwana ajikina,babu abunda zanmiki"
Ta jinjina mai Kai,ahaka suka kwana rungume da juna
Kowane da abunda yike sak'awa acikin zuciyarsa
Da Asuba,ita Tafara tashi,wani irin yunk'urin amai ne yatasheta
Bayi tashiga dasauri tanata kakarin amai
Sai dai babu amai babu labarinsa sai uban kakarin datakeyi
Tsayawa tayi tana maida numfashi
Ta kunna famfo Dan ta dauraye bakin da fuskarta
Sai dai me? A memakon taga ruwa saitaga jini nata bul-bulowa
Baya tayi dasauri tana murza idanuwanta Dan tabbatar da jinin datagani
Still jinin tagani harda guda-guda
Yarfillo.
[20/10, 8:36 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo
Gisuwa da fatan alkhairi ga babbar Yaya hafsat aliyu
🅿AGE📕 6⃣
Bissmillahir rahmanin rahim
Hannunta na rawa takulle kan famfon tafito daga bayin
Ta zauna bakin gadon tana kallon fuskar Umar
Bacci yikeyi sosai,tafashe da kuka tana dafa kanta datakeji yanayimata wani irin ciwo Kamar ze rabe biyu
*** *** ***
Washegari
Anty kaltum da yaranta anan suka wuni,hakan yasa tad'an saki sai yamma suka tafi
Bayan sun dawo daga yimusu rakiya,umar yakalleta yanacewa
"Kishirya mufita yawo"
Tayi murmushin Jin dad'i Dan dama zaman gidan ya isheta jitakeyi kaman akan k'aya take
"Yanzu,ko anjima?
"Yanzu mana,"
Ya bata amsa
Ta gyad'a kai
"To muje karakani d'akin"
Dariya yayi had'i da cewa
"Matsoraciya zanga yadda zakiyi innafara fita aiki"
Tafiya tafara yi Tana cewa
"Tare zamu rink'a zuwa ai Dan bazan taba zama nikadai ba Allah"
Bedroom d'inta suka shiga tasauya kayan dake jikinta zuwa ga bak'ar jallabiya
Tayana gyalen rigar tana d'aukar wayarta
"Muje nagama"
Kallonsa tayi jin yayi shuru
"Yadai nace nagama muje"
Janyota yayi gab dashi suna shak'ar numfashin juna
"Chuchu!
Yakirata da wata kalar kasalalliyar murya
Suka kalli juna,yasauke numfashi me nawi
Tare da kama hannunta yad'aura akan k'irjinsa
"Chuchu,zuciyata tana bugawa da k'aunarki ne,a duk sanda nakalleki inajin k'aunarki na k'ara bin jinina da dukkanin jijiyoyina......
Tayi guntun murmushi tare da kama nasa hannun tad'aura akan nata k'irjin tace
"Nima haka, kodayaushe zuciyata bata wani abun da take ambato face sunanka,ina sonka fiye da yadda Nike son kaina,fiye da yadda nike son rayuwata,bazan iya rayuwa idan babu Kai na"
Rungumeta yayi yana k'ara sauke sassanyar ajiyar zuciya
"Ina alfahari da samunki danayi amatsayin Mata,zankasance tare dake har k'arshen rayuwata"
Har lokacin murmushi be bar fuskarta ba
"Muje,kada dare yayi"
Yakama hannunta suka jero zuciyoyinsu cike da begen juna
Saida suka shiga motar me gadi yabud'e suka hau Kan titi sannan yace
"Ina kikeson mujene,inda zesakaki nishadi?
Tad'an rausayar da fararen idanuwanta
"Uhm muje.......
Ya ketseta
"Wajen shan ice cream ko?
Dariya tayi tana kallonsa
"Ya akayi kasan abunda zanfad'a?
Hankalinsa nakan tuk'in yabata amsa
"Saboda nasan kinasan Ice cream sosai"
Ta jinjina Kai
"Hakane,kumafa na kwana biyu bansha ba,tun zuwan dakayi kaduna wancan karen dakazo mindashi"
Ya gyad'a Kai
"To yau zaki sha ki k'oshi harkiyi odarsa zuwa gida"
Basu dad'e suna tafiya ba suka isa katafaren wurin
Wuri me kyau suka zauna aka kawo musu ice cream d'in,suna sha suna fira cikin nishad'i
Duk da k'asan zuciyarta akwai damuwa amma tayi k'ok'ori ta danne.
Basu suka bar wurin ba sai tara saura
Suna shiga falo ko zama basuyi ba,ya fizgota jikinsa yana shisshin shina wuyanta cikin wani irin yanayi
K'ok'orin janye jikinta tafara yi tanacewa
"Jaana please"
Kuma matseta yayi yana k'ok'orin had'a bakinsa da nata
Yayi nasan cafkar labb'anta masu ban Sha'awa aduk sanda take motsasu gurin yin magana
Kissing d'inta yafarayi azafafe,yana shasshafata
Maganganun Aasim ne suka fara yimata yawo a kunne
K'arfinta tasa gabad'aya,ta turesa tare da janye jikinta tana maida numfashi
Yakuma janyota yana kallonta da idanuwansa dasuka canza launi
Cikin wata kalar murya me cike da buk'ata yace
"Rauda please kada kihanani,ayanzu ke matata ce babu wani shamaki atsakaninmu"
Girgiza kai tayi idanuwanta suka fara cikowa da hawaye
"Jaana dan Allah kayi hak'uri bazan iya ba........
Ya k'ura mata ido zuciyarsa na bugawa dasauri
"Chuchu idan kika hanani yin abunda zuciyata take muradi ahalin yanzu,wallahi zanshiga wani Hali,kitausayamin please......
Zuciyarta tafara karyewa,hak'ik'a tana tsananin k'aunarsa tana son tafaranta Masa, Amma yazatayi?idan wani abu yasamesa fa?
Kuka tafarayi me cike da tsananin damuwa
Yasauke numfashi me nawi
Tare da jinjina kai
"Shikenan ya Isa,tunda bakyaso shikenan"
Yak'arasa fad'a Yana sakinta yakoma kan kujera yazauna,ya lumshe manyan idanuwansa shikad'ai yasan halin dayike ciki
Kuka takeyi sosai tarasa yadda zatayi da rayuwarta
Sun d'auki lokaci ahaka,daga bisani yataso yadawo inda take durk'ushe
Zatai magana ya katseta ta hanyar cewa
"Karkice komai,nafahimceki,bazan tab'a yimiki abunda bakyaso ba,akullum burina infarantamiki,danhaka kada kidami kanki zancigaba da hak'uri har zuwa sanda zakiyi niyya"
Takallesa da jik'akk'un idanunta da sukayi luhu-luhu tace
"Wallahi inason infaranta maka kaima kasani Amma...........
Yatsunsa biyu y d'aura akan lips d'inta
"Nace nafahimta,tashi muje kiwatsa
Ruwa kikwanta"
Tamik'e tanajin zuciyarta babu dad'i
Dakanshi yashiga yahad'amata ruwan wanka tashiga
Kafin tafito haryaciro mata kayan bacci,hakan yak'ara mata tausayinsa sosai
Bayan tasa kayan tazauna kusa da shi tare da kama hannunsa ta matse cikin nata
Cikin murya me taushi tafara magana
"Jaana kagafarceni,nasan hukuncin duk macen da tak'i zuwa shimfid'ar mijinta,nasan mala'iku ke tsinemata har gari yawaye
Amma.......
D'aga mata hannu yayi yace
"Nacemiki nafahimceki meyasa kikeson nanata abu d'ayane,alfarma d'aya kawai Nike so kimin"
Kallonsa tayi suka had'a ido
Yacigaba dacewa
"Inaso muraba d'aki wajen kwanciya,kikwana a naki in kwana anawa,saboda aduk sanda nike tare dake hankalina tashi yikeyi.........
Ta katseshi
"Jaana amma kasan bazan iya kwana a d'aki ni kad'ai ba ko?
Ya jinjina kai
"Nasani amma hak'uri zakiyi, Kamar yadda kika rok'i alfarmar in k'yaleki nakuma k'yaleki
Nima kimin wannan alfarmar dan Allah ta wannan hanyarce kad'ai zansamu sa'ida"
Kasa cewa komai tayi, kallonsa kawai takeyi
Yamik'e Yana tambayarta
"Akwai wani abun da kike buk'ata ne?
Ta girgiza kai alamar aa
Yace
"To shikenan zanje inkwanta,kiyi addu a kafin kiyi bacci kinji?
Gyad'a Masa kai kawai tayi zuciyarta cike da fargaba
Ya durk'uso yanayimata murmushin k'arfin Hali tare da manna mata kiss a goshinta
"Good night''
Yafad'a yana ficewa daga d'akin tare da rufomata k'ofa
Ajiyar zuciya tasauke gabanta nafad'uwa,
Shiko Umar bedroom d'insa yashiga,yashiga toilet tare da sakar ma kansa ruwan sanyi
Dafa bangon bayin yayi ruwan na sauka ajikinsa
Ya runtse idanuwansa yana tunanin yadda ze b'ullo ma al'amarin,shikad'ai yasan irin feeling d'in da yikeyi akanta
Zuciyarsa ta haskomata kyakkyawar k'irarta
Yakuma runtse idon yana dun'k'ule hannunsa yabuga a bango
"Why Rauda?meyasa bazaki fahimci yadda kike araina bane?
Yafurta ahankali
Janyo tawul yayi yad'aura ya janyo wani yana goge gashin kansa
A gaggauce yasanya kayan bacci yafad'a Kan gado
Yayi rub da ciki,tsananin sha'awarta na kuma taso Masa.
Itako tana zaune gefen gadon tana rarraba idanu,dan gani takeyi kamar zataga wani abun tsoro
Kallon agogo tayi k'arfe shad'aya da minti arba'in
Haka tacigaba da zama tana dube-dube ahaka bacci yafara d'aukarata
Sama-sama taji andafa mata kafad'a,tabud'e ido cikin yanayin bacci tana kallon kafad'ar,wasu dogayen yatsu tagani bak'ak'e sid'ik tare da zak'o-zak'on k'umbuna
Wartsakewa tayi dasauri tana k'ara kallon kafad'ar
Still hannun yana kafad'ar ta
Azabure tamik'e tana kallon kan gadon,babu kowa akai
Motsi tafara ji ak'asan gadon, hakan yatabbatar mata abunda yatab'atan yana k'ark'ashin gadon
Hanyar fita d'akin tayi,ta murd'a hannun k'ofar amma gam tak'i bud'ewa,
Tafara jijjiga k'ofar da ka k'arfi gabanta na wani mugun fad'uwa
Shafata wuya akayi tabaya
Ta k'wala ihu tare da juyawa a razane
Wayam babu kowa,bubbuga k'ofar tayi tana kiran sunan Umar,amma shuru
Tazame k'asa tana numfarfashi,
Wani kalan gurnani tafaraji me tsoratarwa yana fitowo daga cikin bayi
Bam!
Aka banko k'ofar bayin,runtse idanuwanta tayi dasauri tana ambaton sunan Allah Dan tasan shikad'ai ze kawomata agaji
"Habibty!
Taji anfad'a cikin wani irin salo
Tabud'e idanuwanta dasauri tana kallon inda tajiyo Kiran
Aasim tagani kwance kan gadon ya kishingid'a da fulo
Yanayimata wani irin kallo da idanuwansa masu d'auke da k'wayar ido kalar golden
Yacigaba da cewa
"Barka dai habibty,barka da dare"
Yarrr yarrr tsigar jikinta ta tashi,ba bu inda baya rawa ajikinta
Addu'a kawai takeyi
Dariya yafarayi yanacewa
"Nazo tayaki kwana ne bazaki yimin maraba ba?
"Dan.....Dan.....Allah...kayi.... hak'uri'
Tace cikin rawar murya da tsananin razana
Dariya yakuma yi akaro na biyu
"Gabad'aya ni natsani kalmar hak'uri,dan haka kada kik'ara ambaton hak'uri agabana,kitaso ki hawo kan gadon"
Girgiza kai tayi jikinta na kyar-kyarwa kamar wacce akaciro daga cikin k'ank'ara
Yagyad'a kai yana murmushin k'asaita
"Kinfi kowa sanin bana nanata magana sau biyu,idan bazaki taso ba to akwai wad'anda zasu taso dake
Yana gama fad'a kuwa taji anciccib'eta and'agata sama amma kuma bata ganin wad'anda suka d'agatan
Tana ihu kuma amma ihun baya fita
Kan gadon aka direta, gabad'aya jikinta ya mutu bata da kuzarin dazata iya guduwa
Duk surar datazo bakinta karantawa takeyi
Yayi murmushi tare da cewa
"Tun kan asan za a haifeki nike karanta al'qur ani,yanzuma zanso ace ni nike karantamiki tunda naga arud'e kike wasu ayoyinma ba dede kike karantasu ba"
Cikin tsananin tsorata tace.
"Menayi maka ne da kake bibiyar rayuwata,meyasa bazaka k'yaleni nayi rayuwa kamar yadda sauran al'umma sukeyi ba,meyasa!
Yayi guntun murmushi
"Sabida ba'ayiki dan kowa ba,anyiki ne danni kad'ai,kuma dani kad'ai zaki rayu,ina sonki habibty bazan tab'a iya rayuwa babu keba.........
Cikin kuka tace
"Wannan ba so bane,zalunci ne.........
Bata k'arasa ba ya damk'o gashin kanta yana kallon fuskarta
"Kada ki kuskura,ki zageni,kinsan halina sarai"
Ya matso yana gogga fuskarsa me zagaye saje a wuyanta
"Hak'ik'a kinacin albarkacin son dankeyi Miki,shiyasa nike k'yaleki,amma da tuni na b'atar dake a duniya,Dan babu mahaluk'in da ya isa yafad'amin maka manciyar abubuwan dakike fad'amin batare dana shafe labarinsa ba!
Runtse idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suna gangaro gefen kuncinta
"Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
Tabud'e ido tana kallon sa
"Kicire tunanin cewa zanrabu dake arayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa yarabani dake"
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
_Kuna a raina yan uwana yan *Golden Pen* hadin kanku na burgeni hakika kun cika Zinarai, kuma yan Amana, inama yan k'ungiyoyi zasuyi kuyi daku yan uwana, da tabbas zasu samu ci gaba, wlh *Golden Pen* kun hadu dari bisa milyoyi, bani da abunda zan baku shiyasa na baku wannan page kuyi yan da kukeso dashi na bakushi kyau ta,👌_
🅿AGE📕 7⃣
Bissmillahir rahmanin rahim
"Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
Tabud'e ido tana kallon sa
"Kicire tunanin cewa zanrabu dake a rayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa yarabani dake"
Tanaso tayi magana amma taji bakinta yayi mata nawi takasa motsashi,kamar yadda takasa motsa koda d'an ya tsanta
Yakuma yin murmushi yana shafa lip's d'inta da yatsansa
"Wani hukunci yakamata inyima wannan labb'an?dasuka bari wani ya tsotsesu"
Yad'an rausayar dakai cikin yanayin nishad'i
Bakisan cewa wa'annan kyawawan labb'an suna d'aya daga cikin manyan dalilan dana kasa rabuwa dake ba??
Hmmmmmm yasauke numfashi
Sannan yacigaba da cewa
"Kada ki sake,habibty kisani komai na jikinki mallakina ne nikad'ai"
Ya matso da fuskarta kusa da tasa,dan har lokacin gashin kanta na damk'e a hannunsa
Kallon lips d'inta yikeyi
"Hukunci d'aya zanyima labb'an Nan,zanta shansu har gari ya waye"
Tanaji yafara tsotsar lips d'in cikin wani salo na mugunta
Bata da ikon hanasa dan bata da yadda zatayi, in Banda rad'ad'i babu abunda lips d'in kemata
Wani kalan yanayi taji tafara shiga, ahankali tunaninta yafata tsayawa taji kanta yanayimata waiwayi take wani kalan bacci me cike da wahala ya d'auketa.
B'angaren Umar ko kai-kawo yike tayi acikin d'akin
Ahankali yaji mararsa tayi wani k'arfi tare da fara ciwo
Ya kwanta a k'asan kafet hannunsa dafe da mararsa
Da k'yar bacci ya d'aukesa
*** *** ***
Washegari,ana kiran assalatu tafarka, tabud'e idanuwanta dasukayi mata nawi tana kallon cikin d'akin
Babu kowa aciki,jitayi bakinta nayimata zugi ahankali k'wa-k'walwarta tafara tariyomata abunda yafaru
Ajiyar zuciya tasauke tatashi daga kwanciyar datake ta jingina da jikin gadon
Gani takeyi kamar mafarki take,amma kuma tasan ba mafarkin bane
Nannauyar ajiyar zuciya tasauke tana tunanin yadda zata cigaba da rayuwa da aljani amatsayin mijinta bayan kuma ga nata mijin yanaso yarabata dashi
Mik'ewa tayi tashiga bayi tad'auro alwala,tagabatar da sallar Asuba
Sannan tafito falon lokacin gari yafara haske, bedroom d'insa ta nufa dan bataji fitowarsa sallah ba
Ta tura k'ofar d'akin tana sallama
Yana kwance k'asan kafet yatakure guri d'aya
A sanyaye ta k'arasa inda yike ta durk'sa tana kallonsa cike da tausayinsa
"Na k'osa muyi aurannan chuchu,inhuta da kwanciya nikad'ai,yazamana kullum ina manne dake ina shak'ar daddad'an k'amshinki"
Maganar umar tadawo mata
Sassanyar ajiyar zuciya tasauke tasa hannu a gefen fuskarsa tana shafawa ahankali
Ya bud'e idanunsa ya watsasu akanta dama ba baccin yikeyi ba ya farka tuntuni
Kallon juna sukayi sosai
Daga bisani ya sakarmata guntun murmushi
"Madam har kintashi?
Ta d'aga masa kai alamar eh tare da cewa
"Kaima yakamata katashi kayi sallah"
Ya yunk'ura ya mik'e zetashi,mararsa tayi wani mugun k'ullewa
Dasauri yakoma yazauna yana d'an runtse idonsa alamar ciwon na damunsa
Rauda tace
"Lafiya jaana?
Guntun numfashi ya sauke yana bata amsa
"Cikinane ke ciwo"
Cikin tausayawa tace
"Sannu,tunyaushe yafara ma?
"Cikin dare amma nasha magani nasan zebari nan bada jimawa ba"
Ta gyad'a kai tare da mik'ewa
"Allah yak'ara sauki bari inhad'ama ruwan wankan"
Bayin tashiga tahad'a mai tafito tace ta had'a
Saida yashiga sannan tafito da ga d'akin tashiga kicin
A gurguje ta had'a abun kari,tana cikin jerawa,yasauko
Ya zauna yanayimata sannu
Itama tazauna suna fuskantar juna tafara tsiyaya ruwan zafi a Kofi
Kallonta yikeyi anatse ya lura da lips d'inta dasukayi ja
Yace
"Chuchu meyasami lips d'inki?
Kallonsa tayi tana ajiye kofin
"Babu komai"
Ze kuma magana mararsa takuma k'ullewa
Dasauri ya dafa cikinsa,tasowa tayi dasauri ta dawo inda yike tana tambayar
"Jaana cikinne?
Ya d'aga mata kai kawai
Hankalinta yatashi
"Fad'amin inda maganin yike in d'auko maka"
Ya girgiza Kai
"Aa,d'auko min wayata kawai inkira doctor zainab nasan yanzu bata wuce asibiti ba sai ta biyo takawomin allura"
Tad'auko mai wayar tamik'amai har lokacin yana dafe cikinsa
Ya lalubo numban doctor zainab yadanna
Ringing biyu tad'auka tana fad'in ango kasha k'amshi
"Kinwuce asibiti ne?
Tace aa
"Yace kibiyo please banad'an jin dad'i"
Daga can b'angaren doctor zainab tace
"Subhanallah meke damunka?
Yafad'a mata
Tace
"To shikenan ganinan zuwa yanzu insha Allah"
Ya ajiye wayar Yana mik'ewa da gyar
"Bari naje nakwanta kafin tazo,kibiyoni da Lipton d'aki"
Ta jinjina kai cikin damuwa tana bin bayansa da kallo haryashige
Sannan tasauke ajiyar zuciya,ta had'a Lipton d'in tabishi da shi
Ya amsa yana kurb'a kad'an-kad'an
Hannunta yakama ganin yadda duk tashi ga damuwa
"Chuchu bafa wani abu bane,inayin alluran zedena dama nasaba irin ciwon kada kid'aga hankalinki please"
Hmmmmmm tasauke doguwar ajiyar zuciya
Knocking d'in k'ofar falon akafarayi taje tabud'e
Doctor zainab ce,suka gaisa sannan tayimata jagora zuwa d'akinsa.
Sama-sama ya amsa gaisuwar doctor zainab dan ciwon ya matsamasa
Doctor zainab ta fahimci abunda yike damunsa tsaf hakan yasa data mai allura zata wuce tacema Rauda tana son magana da ita
A falo suka zauna,Rauda zata had'amata tee tacemata tabarshi ta k'oshi tazauna suyi maganar kawai
Bayan sun zauna doctor zainab takalleta sosai tace
"Kinayin al'ada ne?
Rauda takalleta tana mamakin tambayar
Doctor zainab tayi murmushi tare dacewa
"Kiyi hak'uri inason infahimci wani abune"
Girgiza mata kai Rauda tayi
"Aa banayi"
Doctor zainab ta jinjina Kai
"Amma meyasa kik'i yarda da mijinki?
Cikin rashin fahimta Rauda take kallonta
Doctor zainab tayi murmushi tana cigaba dacewa
"Nasani yawancin y'ammata idan akakawosu gidan auransu sukank'i yarda da angwayensu,badan komai ba sai dan tsoro
Kuma dama tsoro wajibine ga duk macen da takai budurcinta gidan mijinta
Amma yanzu kai ya waye andaina wannan k'in amincewar,kuma miyema abun gudu ga wanda yazama muharraminka?
Bakisan idan Sha'awa tayiwa namiji yawa tana iya halaka saba?
Wannan ciwon cikin dakikaga yanayi somin tab'i ne inhar bazaki yadda da mijinki ba
Tad'an dakata sannan tacigaba da cewa
"Dan allah ki ajiye wani tsoro da fargaba agefe ki bawa mijinki kulawa kinji?
Gyad'a mata kai kawai Rauda tayi tana nazarin maganganunta
Doctor zainab tamik'e tana d'aukar jakarta.
"Nizan wuce nasan yanzu yasamu bacci dan allurar tanasa bacci sai anjima"
Rauda tamik'e tayimata rakiya zuwa k'ofar falo sannan takoma d'akinsa
Ganin yasamu bacci yasa ta janyo mai k'ofar tadawo falo tana nazarin abunyi
Gabad'aya tarasa yadda zatayi,wayarta tad'auko tadanna numban aminiyarta Salma bugu d'aya salma ta d'auka tanacewa
"Amarya kinsha k'amshi,sai yau akatuna dani?anata ragargazar amarci?
Rauda tasauke ajiyar zuciya cikin damuwa tace
"Salma ina cikin matsala bansan ya zanyi ba"
Daga can b'angaren salma tace
"Subhanallah matsala kuma Rauda?
Rauda tafashe da kuka
"Salma bansan yazanyi da rayuwata ba,inaganin na tsallake rijiya da baya ashe bansani ba cikin rijiyar nafad'a"
Cikin tashin hankali Salma tace
"Nashiga uku ni Salma,me yafaru Kuma?
Rauda takwashe komai tafad'a mata
Hak'ik'a Salma ta kad'u da jin labarin
Tama rasa abunda zatace
Zuwa can tasauke numfashi tare da cewa
"Kenan Aasim kwantan b'auna yayi,yayi kaman yarabu dake ashe azzalumin yananan......
Rauda tayi saurin katseta
"Aa Salma karki zagesa wallahi ayanzu yawuce duk inda kike tunani"
Salma tasauke doguwar ajiyar zuciya
"Hmmmmmm yanzu miye abunyi Rauda?danni wallahi kaina ya kulle"
Itama Rauda ajiyar zuciyar tasauke
"Ni yanzu damuwata d'aya cewa dayayi Umar ze mutu idan har ya kusanceni,gashi umar yana matuk'ar buk'atata, kifad'a min yadda zanyi please Salma,ke kad'aice wacce nike iya gayama damuwata"
Salma tasauke numfashi
"Ina ganin kaman yafad'a miki hakane dan ya tsorataki, Amma baze iya kashesa ba, Dan ina tunanin umar yafi k'arfinsa tunda har yabari kika auresa"
Ta girgiza Kai
"Bana tunanin hakan"
Salma tace
"To yakamata munemi wani malamin Rauda,zan k'ara yin tunani anjima inga yadda za'ayi amma kafinnan kinsan y'ar dabaran dazakiyima umar d'in dan ki rage masa feeling d'in"
"Shikenan saina jiki anjiman"
Rauda tafad'a tare da aje wayar
Tanaciga da lulawa cikin tunani
Sai k'arfe biyun rana yatashi tana zaune agefen sa
Tasha fa gefen fuskarsa tana cewa da tausassar muryarta
"Jaana,yajikin?cikin yadena ciwo?
Yayi murmushi yana bata amsa
"Yadena chuchu,saidai kukan yunwa dayikeyi"
Tamaida mai martanin murmushin
"To alhamdulillah,kawatsa ruwa bari ind'auko ma ferfesun kifin danayima"
Yagyad'a kai yana mik'ewa
"To madam"
Fitowa daga d'akin tayi tashiga kicin tabud'e kular data zuba ferfesun kifin tare da d'auko plate zata zuba?
Saidai me a memakon taga kifin saitaga manyan b'eraye kwance acikin kular da alamu sun dahu sosai sai uban turiri sukeyi"
Mamakine ya kamata kodayike ba abun mamaki bane dantasan zata iya ganin abunda yafi hakama ayanzu
Rufe kular tayi tad'auka ta wurgata dustbin
Ruwan indomie ta maida tana tsaye har indomin ta nuna tajuye a plate
Tadawo d'akin lokacin yafito da wanka yana sallah
Tazauna tanajiran ya idar,yasallame sallar yana shafa addu'a
Sannan ya juyo yana dubanta
"Madam yadai?
"Dede"
Tafad'a tana ajiye plate d'in agabansa
Yayi murmushi tare da kamo hannunta yazaunar da ita a k'asa inda yike zaune
"Ai tare zamu ci,dannasan kema baki ci abincin rana ba"
Bata mai musu ba sukaci indomin tare
Bayan sunkammala yace
"D'azu bayan fitarki zayyad ya kirani akan maganar danamai na malaminnan,yace ze turomin numban malamin inyaso sai muyi masa bayani"
Tagyad'a kai
"To allah yasa mudace"
Ya amsa da amin
Daddare suna zaune a falo wuraren misalin shabiyu nadare
Yakalleta yana cewa
"Madam tashi inrakaki kije kikwanta"
Marai-raice fuska tayi tana kallon sa
"Allah yau bazan iya kwana nikad'ai ba,jiya nikad'ai nasan abunda nagani"
Hmmmmm yasauke numfashi
"To yanzu yakike so ayi?.
"Mukwana tare,wannan tsarin naraba d'aki a sokeshi please"
Yayi guntun murmushi
"To shikenan tashi muje,a wani bedroom d'in zamu kwana?naki ko nawa?
"Naka"
Tafad'a
Yace
"Ok tashi muje"
Yakashe kayan kallon
Bedroom d'inta yafara rakata dan tasa kayan bacci tabud'e wardrobe d'in kayan baccin tana tunanin wanda zata sa
Umar ya d'auko wata maroon d'in riga yamik'o Mata
"Naga sai ruwan ido kikeyi kisa wannan"
Murmushi tayi ta amsa
Yakauda kansa yayinda takesa rigar dan bayaso yaga abunda zetada mai hankali
Takammala sa rigan tace
"Muje"
Suka rufe bedroom d'inta suka shiga nasa
Zama tayi bakin gadon tana duba addu'o in da salma taturomata
Shiko canza kayan yikeyi yana kallonta,wani irin feeling d'inta na taso Masa
Tun yana kauda abun aransa haryaji baze iya ba
Jingina yayi da bangon d'akin yana maida numfashi ahankal
Tad'ago tana kallonsa
"Lafiya jaana?
Ya girgiza kai batare dayace mata komai ba
Ajiye wayar tayi tataso,tana k'ara tambayar sa
"Jaana cikinne?
Yabud'e idanuwansa ahankali yana kallonta
Rigar tabi jikinta sosai
Jiyayi wani abu na fizgarsa da k'arfi
Besan sanda ya janyota yamannata da jikinsa ba yafara kissing d'inta ta ko Ina
"Jaana!
Be saurareta ba ya sureta ya ajiyeta kan gadon yana cigaba da kissing d'inta
"Jaana please kabari sai munje gun malamin tukunna banaso wani abu yasameka.....
Rufe mata bakin yayi da nasa,takasa k'arasa abunda zatace
Shasshafata yashiga yi ta ko Ina yana sauke wani numfashi a wahalce
Bakinta dake cikin nasa yasaki yamaidasa kan wuyanta
Yanacigaba da kissing d'inta ta ko ina
Wata irin iskace da guguwa ta turniki'e d'akin
Lokaci d'aya, hankalinta yatashi jin batajin motsin Umar, tabud'e idanuwanta a firgice data rufe yayinda guguwar ta turnik'e d'akin
Aasim tagani tsaye idanuwansa sunyi jawur yana nuna wani abu da hannunsa
Dasauri takalli abunda yike nunawan, Umar ta hango can saman d'akin jijiyoyin wuyansa sun mummurd'e idanuwansa sun firfito waje
Ta zabura tamik'e jikinta yafara rawa
"Narok'eka kada ka kasheshi,dan girman allah"
Ko kallonta beyi ba,ta taso dasauri tana nufar inda yike
"Dan girman allah narok'eka........
Da razanannun idanunsa yayimata wani kallo
Wani irin haske yafito daga cikin idonsa
Wata iskace tad'auketa tahad'a da bango wanda kanta yayi mugun buguwa
Durk'ushe wa tayi tana kuka tana cigaba da rok'onsa
"Wallahi bazan k'ara sab'a ma umarninka ba,duk abunda kace inyi zanyi amma dan allah kada karabasa da rayuwarsa
Kuma kallonta yayi idanuwansa nakuma rinewa
Yafara magana muryarsa nafita bibbiyu
"Kina ganin kamar bazan iya abunda nace ba ne ko,to yau zanbaki mamaki!!!!
"Wallahi bazan k'ara sab'a ma ka ba nayi alk'awari,kada ka kashesa dan allah"
Hannunsa yaja baya, umar yafad'o daga saman yazube a k'asa yana maida numfashi sama-sama dan ya wahala matuk'a
Dagudu tatashi ta isa gun Umar tana jijjigasa tana kiran sunansa
"Kisani ayanzu dama biyu zanbaki,ko kisa yasakeki ko kuma ki rasasa gabad'aya"
Yana gama fad'ar haka ya b'ace
Hankalinta yayi matuk'ar tashi jijjigasa kawai takeyi
"Jaana katashi karkata fi kabarni......
Yabud'e idanuwansa a wahalce yana kallonta
Ahankali yamaida idanunsa yarufe
Kuka takeyi sosai tana jijjigasa
"Ayanzu dama biyu tarage miki, ko kisa shi yasakeki kokuma kirasasa gaba d'aya"
Maganar Aasim tadawo mata
Hannunta tasa a k'irjinsa da sauri,jin yana numfashi yasa ta mik'e tad'auki wayarsa jikinta na rawa ta lalubo numban zayyad tadanna Kira
Zayyad naganin kiran yasan ba lafiya ba,ya d'auka Jin muryar Rauda yasa yace
"Lafiya Rauda?a darennan ina umar d'in?
Muryarta narawa tace
"Zayyad kazo kataimakeni Umar ze mutu"
Mik'ewa zayyad ya yi daga kujerar da yike na office dan ranar Yana asibiti duty d'in dare yikeyi
"What?meyasamesa
"Kazo yanzu dan Allah"
Kawai tafad'a tana ajiye wayar tana cigaba da kuka
Shima aje tashi wayar yayi yafito dasauri yashiga motarsa
Gudu yike yi sosai har ya kawo gidan,saidayayita horn sannan me gadi yabud'e dan shi baccinsa yikeyi besanma wainar da ake toyawa ba
A tsakar gidan yayi parking yafito dasauri yana bubbuga k'ofar falon
Tana rungume dashi tana kuka taji ana bubbuga k'ofar
Tasan zayyad ne ta tashi har lokacin jikinta narawa taje tabud'e k'ofar
Ganin yanayin datake ciki yasa zayyad tambayar ta dasauri
"Ina Umar d'in?
D'akinsa ta nunamai da hannu kawai dan tama kasa magana
Yashiga d'akin,ganin halin da umar ke ciki yatada mai hankali sosai
Ciccib'osa yayi yafito dashi tana tsaye gabad'aya ta firgice
"Maza d'auko mayafinki muwuce asibiti"
Hijabin datake sallah dashi dake gefen kujera tad'auko tazura,yashimfid'eshi abayan motar
Yatada,zata shiga baya yace aa tashiga gaba dan ba inda zata zauna abayan
Yafigi motar aguje yana kuma tambayarta
"Kifad'a min meyasamesa?
Bakinta narawa tace
"Aasim...Aasim....
Yakalleta da sauri dayike yasan duk abunda kefaruwa
"Aasim?
Ta jinjina mai kai
Yasauke numfashi yana cewa
"Shikenan idan munje asibiti koda za atambayeki ace meyasamesa kice accident yayi kinji?
Ta gyad'a mai kai kawai tanajin kanta kamar ze juye
Suna isa asibitin akabashi taimakon gaggawa
Lokacin da doctor zayyad da nurses suka fito biyu saura
Ta taso daga durk'usan datayi tana kallon zayyad
Kafin ta tambayesa yace
"Kikwantar da hankalinki yadawo cikin hayyacinsa yanzu amma yasamu bacci kina iya shiga"
Tatura k'ofar d'akin tashiga
Zayyad yabita da kallon tausayawa
A kujerar da ke gaban gadon tazauna tana kallonsa
Lokaci d'aya harya fad'a,tana zaune tana kallonsa har asuba inbanda kuka ba abunda takeyi
Lokacin yafarka,ganinsa a asibiti yasa k'wa-k'walwarsa ta tariyo masa abunda yafaru
Cikin kuka taruko hannunsa tanacewa
”kayi hak'uri,duk sanadina kashiga wannan halin.....
Ya girgiza kai yana cewa
"Hak'urin mekike bani chuchu?
Kuka yacigaba dayi cikin tsananin damuwa
Ajiyar zuciya yasauke me nawi
Tare da sa hannu ya share mata hawayen da suke bin fuskarta
"Saiyanzu nafahimceki chuchu, saiyanzu na fahimci abundance yasa kika k'i yarda Dani, Amma inaso kisani babu abunda zesa inrabu dake
Inatare dake duk runtsi duk wuya"
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 *_JINNUL_*
*_AASHIQUE_*🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Little hajjo and my elder sister
🅿AGE📕 8⃣
_Wannan page d'in nakune masoya jinnul aashique,na sadaukar dashi gareku,saboda k'aunarku ga littafin,ina godiya ga yadda kuke son wannan labari allah yabar zumunci,sannan ina baku hak'uri akan dad'ewa danikeyi bana typing insha allahu zanyi k'ok'ori inga ina yin yadda yadace nagode._
*_GAISUWA ga Aishatu Babayo Jos,ina godiya da kulawarki gareni,ba irin su o'o ba @maman ummi,dan inbanda tsokana babu abunda ta iya ba😜 amma dai duk da haka kema ina gaisuwa_*
_ADDU'A Ga besty safiyya maina,allah yabaki lafiya yasa kaffarane_
Bissmillahir rahmanir rahim👏🏻
Ta girgiza Kai cikin kuka tace
"Yanzu inane keyimaka ciwo?
Ajiyar zuciya yasauke dan babu inda bayamasa ciwo ajikinsa amma dan kada yak'ara tada mata hankali yasa yace
"Chuchu nifa naji sauk'i yanzu,wuyanane kawai ked'an yimin zafi,kuma shima nasan zuwa anjima zedaina insha allahu"
Ta kwantar dakanta agaban gadon
"Jaana tunanina yafara raguwa,Ina tsoron watarana k'wak'walwata ta juye danjina nikeyi kamar na kusa haukacewa"
Numfashi yasauke me nawi zuciyarsa cike da tarin damuwa dan shima tunanin nasa ya tsaya yarasa ta inda ze b'ulloma al'amarin,ada yayi tunanin al'amarin mesauk'i ne amma daren jiya yatabbatar mai da al'amarin Aasim ba k'aramin babban al'amari bane
Idanuwansa ya runtse yana furta ya rabb!
Ahankali
K'arfe takwas doctor zayyad yashigo d'akin yana sallama
Umar ne ya amsa mai,dan ita Rauda baccine yad'auketa me tattare da ciwon kai me tsanani
Zayyad yajanyo wata kujera yazauna yana duban umar
"Yajikinnaka?
"Dasauk'i"
Ya amsa mai
Zayyad yace
"Jiya cikin dare Rauda takirani tace inje kana cikin wani Hali dana tambayeta meke faruwa sai tace min Aasim,wai meke faruwane Umar?
Umar yasauke numfashi yana cewa
"Zayyad yanzu ba lokacin dazanyima bayani bane amma aikasan bana b'oyemaka komai"
Zayyad ya jinjina Kai
"Hakane,to yanzu inane kedamunka ajikinka?
"Wuyana,yanamin zafi da ciwo sosai kad'auko alluran....... yafad'a mai sunan alluran sannan yacigaba da cewa
"Kayimin,koze d'an lafamin"
Zayyad yamik'e yafice daga office d'in batare da yakuma cewa komai ba amma zahiri yana cikin damuwa da ganin halin da abokinsa keciki
Allurar yad'auko yamasa bayan yagama yace
"Ni zanje gida na dawo"
Umar yace
"To amma da na tashi Rauda ka ajiyeta itama inzaka dawo sai kabiya kad'aukota"
Zayyad yagyad'a kai yatsaya yana dubansu.
Hannunsa yasa Yana d'an bubbuga bayanta yana kiran sunanta
A d'an razane tafarka dan gabad'aya atsorace take
"Chuchu calm down nine"
Umar yafad'a,tasauke numfashi tana kallonsa
"Jikinne?
Ya girgiza Kai
"Aa ni naji sauk'i kitashi zayyad ze wuce ya ajeki agida inze dawo sai ya biya yad'auko ki"
Girgiza kai tayi ahankali
"Ni ba inda zanje,bazan barka kai kad'ai ba"
Hmmmmm chuchu kinmanta da night gawn ne ajikinki kiyi hak'uri kije kicanza kaya ai ba dad'ewa zaki yi ba"
Umar yafad'a,shuru tayi Tana nazari dan gani takeyi kamar idan tatafi wani abunne zekuma samunsa
Gefen fuskarta yashafa
"Tashi kinji nima kitaho min da kaya kala d'aya tunda nasan zuwa dare ko gobe dasafe zamukoma gidan gabad'aya"
Mik'ewa tayi badan ranta yasoba tana tafiya tana waigensa
Harta fice daga d'akin
Tunda suka shiga motar babu wanda yayi magana harsuka iso gidan
Sannan zayyad yace
"Nan da awa nawa zaki kammala abunda zakiyi"
"Minti talatin ma yayi yawa"
Zayyad yayi murmushi
"Kidai shirya atsanake nan da awa d'aya zandawo"
Tagyad'a mai kai kawai tare da ficewa daga motar yaja yawuce.
Tunda ta doshi k'ofar falon ta tsinci kanta da fad'uwar gaba
Tatsaya a bakin k'ofar tanajin kamar kartashiga amma babu yadda ta iya yazamarmata dole
Murd'a k'ofar tayi ahankali gabanta na fad'uwa
Saida tatsaya tana k'arema falon kallo kamar yaune tafara ganinsa sannan tashiga tamaida k'ofar tarufe
Ahankali tafara takawa zuwa step tafara hawa step d'in ahankali
Jitayi k'arar sawun tafiyar bibbiyu
Tad'an dakata da tafiyar tana kallon gefenta
Babu kowa azahiri amma tasan a bad'ini akwai wani awurin
K'arfin halin cigaba da tafiya tayi tashiga d'akinta
Tana tunanin abunda zata farayi,tana tsoron yin wanka gashi Kuma yazama dole
Ahankali tacire hijabi da rigar dake jikinta tashiga bayin
Bata tsaya sa ruwan zafi ba,nasanyi ta tatara cikin k'an k'anin lokaci tayi wankan daba ta da tabbacin tafita.
Ko mai bata tsaya shafawa ba ta sanya atamfa riga da skirt d'akinsa ta nufa dan d'auko masa kayan
Ta bud'e wardrobe tana tunanin kayan dazata d'auka
Shesshekar kuka tafaraji sama-sama
Tad'an dakata da abunda takeyi tana k'ara kasa kunne dan tabbatar da abunda taji
Sautin shesshekar kukanne yacigaba da k'aruwa kuma da dukkanin alamu daga bayi shesshekar yike futowa
Gabanta yacigaba da fad'uwa
Kayan tad'auka da sauri tafita daga d'akin
Ajiyar zuciya tasauke mai nawi tana hamdala da bataga abunda ke kukanba dan tabbata ba alkhairi bane
Saidai me kukan tak'ara ji anayi a falon dake k'asa
Fargaba da tsoro suka k'ara kamata, ahankali tafara saukowa daga step k'irjinta na dukan uku-uku
Harta gama saukowa can gefe tahango wata tsohuwa kwance tana d'ago mata hannu tana cigaba da kukan
Wani irin lugude k'irjinta yacigaba dayi tana jin zuciyarta na rawa kamar zata fito waje saboda tsananin tsoro
Tama rasa inda zatayi dan dole saitabi gaban tsohuwar kafin tafita waje ita kuma ba abun takoma sama ba taga abinda yafi wanda takegani ayanzu
Sautin kukan tsohuwar nafita tsigar jikin Rauda na tashi
Jikinta na rawa tafara tafiya tana nufar hanyar fita
Idanun tsohuwar akanta tana cigaba da kukan
Tazo saitinta da addu a abakinta tana shirin rugawa
Tsohuwar tatashi tazauna gashin kanta ya barbazu a ajikinta
Dukda akwai tazara atsakaninsu sosai amma hannu kawai tsohuwar tasa tajanyo wuyanta
Tsananin tashin hankali da tsorata Rauda tashiga,hannunta tasa ta na k'ok'orin b'an-b'are na tsohuwar amma takasa
Dan gam ya manne da wuyanta
Cikin wata kalar murya me tsoratarwa tsohuwar tace
"Babu inda zakije ki gujemana,duk inda kikaje muna tare dake"
Runtse ido Rauda tayi dan kallon fuskar tsohuwar na k'ara razanata
Jin shuru yasa tabud'e idanuwan a tsorace saidai wayam bataga kowa ba babu tsohuwar
Abun mamaki kuma ganinta tayi a d'akin umar gaban wardrobe d'insa
Ita da har tad'auki kayan tafita falo ya akayi kuma taganta a d'aki
Jikinta narawa tabaro d'akin tana k'ara kallon inda taga tsohuwar
Amma babu kowa awurin
Ficewa tayi dasauri tamaida k'ofar tarufe sannan ta jingina da k'ofar tana maida numfashi
Ahaka zayyad yadawo yatadda ta
Tana ganinsa ta taso tashiga motar dan jinta takeyi kamar akan k'aya take
Kallon ta zayyad yayi sosai take yafahimci firgici atare da ita hakan yasa shi tambayarta yace
"Rauda lafiya naganki atsorace haka?
Ta jinjina mai kai
"Lafiya"
Yagyad'a nashi kan yana cigaba da tuk'in
Suna isa asibitin ko parking begama yiba tafito
Dan gani takeyi kaman wani abu ya samu umar.
Da hanzari ta ke tafiya har ta isa d'akin
Ganin sa jingine yasa tasauke ajiyar zuciya
Kallonta yayi ganin yadda tashigo a hargitse
"Lafiya madam?
K'arasawa tayi bakin gadon saikuma ta fashe da kuka
Hannunta yakama yazaunar da ita kusa dashi yace
"Mekuma yafaru chuchu?
Cikin kuka tace
"Bazan iya cigaba da zama agidannan ba,bazan iya ba......
Ya sauke numfashi me nawi,tare da fara rarrashinta
"To shikenan, kukan ya isa haka,ya isa"
Yafad'a yana d'an bubbuga bayanta
Saida tadena kukan,sannan ya k'ara tambayar ta
"Mekika gani yau Kuma?
Ta fad'a Masa,yayi ajiyar zuciya yana nazarin abunda tafad'a mai sannan yace
"Inaganin gobe idan allah yakaimu mutafi katsinan kawai gurin malamin da zayyad yace"
Ta jinjina Kai kawai batare data k'ara cewa komai ba
Daddare tana zaune kusa dashi yafarayin bacci, itama gyan-gyad'i ne yafara d'aukanta
Taji ana k'wan-k'wasa k'ofar
Ta mik'e taje tabud'e
Doctor zayyad tagani,yace
"Yihakuri kinfara bacci natasheki ko?
Tayi d'an murmushi tace
"Aa babu komai"
Yagyad'a kai
"Dama akwai allurar daban masa bane saiyanzu na tuna shine nazo inmasa"
Tad'an kallesa tanacewa
"Ba d'azu kayimasa ba?
Ya d'aga kai alamar eh sannan yace
"Wannan watace daban"
Shuru tad'an yi daga bisani tabashi hanya tanacewa
"Gashi kuma yayi bacci natashesa kenan?
Ya girgiza Kai
"Aa basai kintashesa ba,ai allurar bata baya bace ahannu za aimasa"
Tace to tare da zama tana kallon Umar d'in
Yakama hannun yana tsira mai allurar
Kallonsa tayi sosai ganin ko jijiya be nema ba amma yanayin allura
"Doctor dama ana allura ba a nemi jijiya ba?
Be bata amsa ba yacigaba da abunda yikeyi
Jin yayi mata shuru yasa takuma cewa
"Doctor magana nikeyi fa"
Still banza yayi da ita,cikin idanuwansa takalla taga k'wayar idonsa golden
Azabure tamik'e lokacin yagama allurar yazare yana wani mugun murmushi
Dede lokacin Umar yafarka
Jikin Rauda na rawa tace
"Allurar me kamasa zayyad...
Kasa k'arasawa tayi yayinda ya kauda fuskar zayyad dayayi amfani da ita fuskarsa ta bayyana
Subiyun duka suka zaro ido suna kallonsa
"A..asim"
Tafad'a cikin rawar murya
Yashafa gefensa da hannunsa saiga wata kujera tabayyana
Yazauna har lokacin da murmushin mugunta a fuskarsa
Zatai magana ya katseta tahanyar cewa
"Kafin kitambayeni bari ni na baki amsa,danna san tambayar ki bazata wuce"allurar mekamasa ba"
To allura ce wacce ruwan dake cikinta yike d'auke da abubuwa da dama,zanfad'a miki kad'an daga ciki
Dafarko dai tana d'auke da guba wacce bata kisa amma tana shiga cikin k'ashi da b'argo da kuma jijiyoyin mutum,ta rink'a rugurguza k'ashi tana tsittsinka jijiyoyi,abu nabiyu shine takan saka mutum ya cutar da kanshi yanaji yanagani batare da ya iya hana kansa ba,
Sannan tana d'auke da abubuwan dasuke canza halittar d'an adam"
Yad'an dakata sannan yacigaba dacewa
"Wannan kyauta ce daga gareni,kuma kinsan makarin wannan guba??
Magani ko wani abu baze tab'a karyata ba face saki
Yafad'a yana maida kallonsa ga Umar sannan yacigaba
"Kaga saika zab'a,ko lafiyarka kokuma zama da matarka"
Umar yatashi daga kwanciyar dayayi daky'ar yana dubansa cikin dakewar zuciya yace
"Duk wad'annan abubuwan kanayine dan karabani da matata,to kasani inason matata fiye da yadda nike son kaina,kuma babu wata barazanarka da zata sani naji Tsoro
Sannan inaso kasani kalmar saki bazata tab'a fitowa daga bakina ba
Dariya Aasim yayi sosai sannan yace
"Banga laifinka ba dan kafad'i haka ayanzu,saboda allurata batadad'e da shiga jikinka ba,nabaka sati biyu kacal dakanka,dabakinka zaka furta "
Yamaida kallonsa kan Rauda
Yana cigaba da dariyan ya b'ace
Zubewa Rauda tayi tana fashewa da kuka
Umar yasauko ahankali ya durk'usa agabanta yanajin kukanta harcikin zuciyarsa
"Rauda kisani inasonki babu abunda zesani fargaba akanki,ko kad'an kalamansa basu dameni ba Dan nasan be isa yamin abunda allah be minba,ki kwantar da hankalinki babu abunda zesameni kinji?
Ta jinjina Kai kawai tanacigaba dayin kukan tarasa wannan wace irin Jarabawa ce take bibiyarta takuma kasa rabuwa da ita
Ya d'aga ta suka kwanta akan gadon asibitin yana cigaba da kwantar mata da hankali
Washegari, yafarka jikinsa da sauk'i,hakan yasa yace sukoma gida
Zayyad yad'auko su, yadawo dasu,suna shigowa motar anty kaltum nashigowa
Suka fito atare
Suka gaisheta ta amsa had'i da cewa
"Kukan lafiya nike ta kiran wayoyinku basa shiga?
Umar ne yabata amsa
" Wayoyinne suka samu matsala amma lafiya Lau"
Kallonsa anty kaltum tayi ganin yadda yarame
"Meyasameka naga kafad'a?
Zayyad yace
"Habadai anty idonki ne amma babu ramar dayayi"
Jinjina kai tayi amma bata yarda ba dan tafi kowa sanin k'anin nata
Rauda ce takatsemata tunanin da datakeyi tahanyar cewa
"Anty kaltum mushiga daga ciki Mana"
Anty kaltum ta girgiza Kai
"Aa, office zani dama nabiyo ne inga lafiyarku tunda kuma kuna lafiya shikenan"
Tafad'a idanuwanta akan umar tana k'ara yin nazarinsa
Umar yace
"To sister gobe zamuzo amana girki medad'i"
Gyad'a mai kai kawai tayi tashiga motarta ta tada
Suka sauke numfashi lokaci d'aya
Zayyad yace
"Ni zan tafi daddare zanbiyo in k'ara duba jikinnaka mukuma k'ara tattaunawa akan zuwa katsinan"
Umar yagyad'a kai tare dacewa
"Shikenan sai anjiman"
Suka shiga falon bayan wucewar zayyad
Zama sukayi na y'an mintoci sannan Rauda tace
"Mezan had'a maka na karyawa"
"Kisa ruwan zafi kawai musha tea"
Tace to tare da shiga kicin
Shiko kwantawa yayi yanajin jikinsa nayimasa wani iri, ya lumshe idanunsa cike da damuwa da fargaba
Ahaka ta gama had'a abun karin tasamesa,tadad'e tsaye akansa tana magana amma bejiba dan yalula cikin tunani
Saida ta tatab'asa sannan tad'anyi firgigit yana kallonta
"Lafiya?ko jikinne?
Tatambayesa
Yakakaro murmushi yana tashi daga kwanciyar dayayi
"Aa lafiya lau harkin kammala"
Tad'aga masa Kai alamar eh
Sunfara karyawan yana shan tea hannunsa rik'e da Kofi
Jikinsa yafara rawa,yanajin cikin naman jikinsa kamar ana huramai wuta
Aje kofin hannunta tayi dasauri tana dubansa tare da amsar kofin hannunsa
"Jaana,meke faruwa?
Kasa bata amsa yayi dan zafin cikin jikinsa dad'a k'aruwa yikeyi
Daky'ar ya iya furta
"D'auko min ruwan sanyi kizubamin ajikina"
Dasauri tamik'e tabud'e fridge tad'auko goran ruwan tafara shafamai ajiki
Amma kamar k'aramai zafin takeyi
Yadakatar da ita tahanyar cewa
'barshi haka ya isa"
Aje goran tayi hankalinta atashe
Jiyayi hannunsa yafara wani irin ciwo yarike hannun dasauri yana ambaton sunan Allah
Saida yakusan awa d'aya ahaka sannan hannun yalafa,amma still zafin jikin yananan
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 9⃣
Ina bawa masoyana hak'uri abisa ga jimawa dani keyi ban yi posting ba,nima ba da son raina bane,bank'i ace kullum naturo muku ba amma uzururruka sunyi min yawa inafatan zaku amshi uzurina,kuma zanyi k'ok'ari insha allahu inga ina yin posting akan lokaci nagode da k'aunarku gareni da kuma jinnul aashique.
GAISUWA
Ga y'an uwana y'an Golden pen writters allah yak'ara mana dank'on zumunci
FATAN ALKHAIRI
Ga aminiyata AISHA A IBRAHIM allah yazab'a miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki Amin.
Wannan page d'in sadaukarwa ne gareka jarumi sadauki,AASIM na sadaukar dashi gareka ranka shi dad'e allah yak'ara girma👍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim
Duk iya k'ok'orin da umar yayi,wajen ganin ya b'oye yadda yikeji ajikinsa dan gudun kada hankalinta ya tashi,kasawa yayi saboda tunda yike a duniya betab'a jin irin yadda yike ji ahalin yanzu ba,iya kuma karatunsa na likita da yayi betab'a karo da wannan irin ciwon da yikeji ajikinsa ba bare yasan wani magani ko allura ze ma kansa yaji sassauci.
Yasa ta k'ure AC d'in falon,takuma kawo mai fankar k'asa,badda wacce take sama tanata nata aikin
Amma a banza,a memakon yaji sanyi-sanyi sai ma yikejin zafin nakuma k'aruwa.
"Chuchu"
Ya kira sunanta ahankali ganin yadda tashiga damuwa sosai
Ta zare hannunta daga tagumin da tayi tana amsawa
"Na'am"
"Please karki d'aga hankalinki,naji ma jikin yafara lafamin"
Yafad'a cikin son kwantar mata da hankali
Ta sauke ajiyar zuciya hmmmmm
"Taya hankalina baze tashi ba,bayan ina ganin ka cikin wannan halin?
Jaana ina jin tsoro,jikina na bani wani babban al'amari yana shirin faruwa damu,bana so wani abu yasameka"
Tak'ara sa fad'a idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Yayi murmushin k'arfin Hali Yana kama hannunta yace
"Banaso kina fad'in haka,babu abunda ze samemu da izinin Allah,kinji?
Ta d'aga mai kai kawai amma ita jikinta ya gama yin sanyi
"Yauwa chuchu na,mik'omin wayata inkira zayyad"
Yafad'a
Ta mik'amai wayar,yadanna numban zayyad bugu biyu ya d'auka
Yace mai yazo yaduba shi,ga abunda yikeji
Ba a jima ba kuwa zayyad yadawo gidan,gwaje-gwaje yayi masa amma bega komai ba
Cikin mamaki yadubi Umar
"A bayanin dakamin nayimaka gwaji akan abunda nike tunani yana damunka amma banga komai ba"
Hmmmmmm umar yasauke numfashi
"Dama banyi tunanin zaka komai d'in ba......
Sai kuma ya dakata yana duban Rauda dan ba ya so yayi maganar agabanta
"Madam had'a min ruwan wanka"
Ta mik'e ta hau sama,ya maida kallonsa kan zayyad Yana cigaba da cewa
"Zayyad,zafin dani keji a jikina yawuce yadda zan kwatanta maka,jini keyi kamar ana huramin wuta acikin jikina"
Zayyad yasauke numfashi yace
"Wai to meke faruwa haka?
Umar ya zayyana mishi abunda yafaru daren jiya a asibiti,da allurar da Aasim yayi masa
Zayyad zaro ido yayi zuciyarsa cike da tsoro
"Yayi shigata yayimaka allura?nashiga uku nikuma me yasakoni a al'amarinsa?
Umar shuru yayi yana kallon zayyad
Zayyad ya ciga ba da cewa
"Amma wannan al'mari akwai rud'ani da rikitar wa wallahi,kace ciwon maka ba na asibiti bane"
Umar ya yi ajiyar zuciya me nawi
"Hmmmmmm zayyad al'amarinnan yafara bani tsoro,duk inda kake tunanin Aasim wallahi ya wuce Nan,ina fargaban abun da ze iya faruwa gaba"
Zayyad ya jinjina kai cike da tsananin mamaki danshi tunda yike aduniya betab'a jin makamancin al'amari irin wannan ba Koda kuwa a littafi ballan tana a zahiri
"Gaskiya dole musan abunyi,inaga mushirya mutafi katsinan yanzu kawai"
Umar ya girgiza Kai yace
"Allah bazan iya tafiya me nisa ba,idan ka rok'esa baze yarda a turamai kud'i yazo ba?
Zayyad yad'an yi shuru yana tunani sannan yace
"Babban malami ne gaskiya,kuma koda yaushe gidan shi cike yike taf da jama'a bana tunanin ze iya barinsu yazo,amma bari na kirasa naji"
Yak'arasa fad'a yana zaro wayarsa a aljihu
Ya danna numban malamin bugu biyu ya d'auka suka gaisa,zayyad yasanar dashi buk'tarsu akan yazo tare da rok'onsa daya taimaka
Yace ba matsala gobe da safe ze taho
Zayyad yayi mai godiya sannan ya kashe wayar yana kallon Umar yace
"Bari yaturo account numban sai inmai transfer"
Acan bedroom kuwa Rauda,
Ta gama had'a ruwan,zata fito kenan taji wani k'ara
Ta waiga da sauri tana kallon cikin bayin,ruwan data had'a acikin kwamin wanka ne taga yana ta zakud'owa kamar dakwai wani abu aciki
Ta rufe idanuwanta da sauri jin tsigar jikinta na tashi bakinta na ambaton sunan Allah
"RAUDA!
Taji ankira sunanta da wata kalar murya me tsoratarwa
Tabud'e idanuwanta da sauri tana kallon cikin ruwan inda taji ankira sunannata
Wani mutumi tagani d'an k'arami shi ba wada ba shi ba yayan wada ba,d'an siriri,fatar jikinsa wata kala kamar gansa kuka,koriya shataf,idanuwansa wasu kala kamar na mage
Futowa yayi daga cikin ruwan yana tahowa inda take
Jikinta na rawa ta murd'a k'ofar bayin zata fita amma gam k'ofar ta rufe
Addu'o i tacigaba dayi dasauri tana jijjiga k'ofar
Ganin ya iso gab da ita yasa tayi sarranda
Ta runtse idanuwanta kawai,jitayi an damk'i hannunta ta ware idanun tana k'wala ihu
"Bazamu tab'a rabuwa dake ba"
Taji yafad'a
Tare da kecewa da wata kalar dariya
Takuma k'wala ihun tare da zubewa a sume,
Umar nafalo, yajuyo ihunta, zayyad ya dubesa yana fad'in
"Kamar ihun Rauda ko?
Umar ya d'aga kai yana mik'ewa
"Bari Naduba Ina zuwa"
Yafad'a yana hayewa sama da sauri
A dur k'ushe yasameta,ya d'agata dasauri yana kiran sunanta
"Rauda!Rauda!
Amma shuru,d'aukota yayi ya yo falo da ita, zayyad na hangosa ya mik'e yanacewa
"Subhanallah me yasameta?
"Wallahi bansani ba"
Umar yafad'a yana shimfid'ar da ita a kan doguwar kujera
Yazauna gefenta yana d'an girgiza ta,yana cigaba da kiran sunanta
Zayyad da ke tsaye yad'auko ruwa agora ya mik'ama umar yana cewa
"Ina ganin suma tayi,yayyafa mata mugani"
Ya amsa ruwan ya yayyaffa Mata,ko minti biyu beyi da yayyafa mata ruwan ba,tafarfad'o tana sauke ajiyar zuciya me nawi
Lokaci d'aya ta bud'e idanuwanta ahankali harta gama bud'e su akansa
Ahankali k'wa-k'walwarta ta tariyo mata abunda tagani a bayi
Tashi tayi a zabure ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka
"So sukeyi su kasheni,sunce bazasu tab'a rabuwa dani ba wayyoh allahna na shiga uku!
Umar yasauke numfashi zuciyarsa cike da tsananin damuwa,
Kasa cewa komai yayi,ya rungume ta kawai yana sauke numfashi ahankali
Zayyad yayi jugum Yana kallonsu gabad'aya tausayinsu yikeji,lokaci d'aya yanayinsu ya sauya daga farin ciki zuwa tashin hankali
Be bar gidan ba sai da aka kira sallar magriba
Suko suna falon har lokacin,ba maganar neman abinci dan babu me jin yunwa acikinsu
Zuwa can dai ya dubeta tana kwance akan k'afafunsa yayinda yike zaune kan doguwar kujera yace
"Mekike buk'atar kici insa me gadi ya siyo Miki?
Girgiza masa kai tayi tace
"Ni banajin yunwa"
"Nasan bakyaji ai,nima baji nike yi ba amma yazama dole munemi wani abu musa acikin mu dan zama da yunwar itama babbar matsalar ce"
Ta jinjina Kai
"Shikenan kasa yakawo koma miye"
Koda me gadin yasiyo kuwa,kad'an suka tsakura, suka gabatar da sallar magriba da issha,sannan suka kunna karatun qur'ani acikin a falon
A haka bacci ya d'auke Rauda,shiko umar ko kad'an be runtsa ba dan jikeyi kamar ana d'add'aure jijiyoyin jikinsa,ga zafin da yike ji Yana dad'a k'aruwa.
Sai wajen asuba Rauda ta farka,taga yadda ya had'a zufa
"Ba kayi bacci bane?
Ta tambayesa da damuwa a fuskarta
Ya girgiza Kai yana k'ok'orin b'oye yanayin da yikeji
"A a nayi Mana kiran sallar da akayi ne ya tasheni"
Hmmmmm tasauke numfashi
"To muje muyi alwala ko"
Suka mik'e atare,jiyayi k'afarsa ta rik'e tana mai zugi
Yad'an tsaya yana kallon k'afar,kallon Rauda tayi tace
"Lafiya?
Yad'an k'ak'aro murmushi
"K'afata ce ta rik'e ina ganin Dan na kwana a zaune ne shiyasa"
Cikin tausaya wa tace
"Meyasa baka tasheni ba to,dana kwanta akan k'afafunka?
Ya kuma yin murmushi
"Taya zan tasheki?zan iya kwana a tsaye ma inhar ke zakiyi baccin cikin kwan ciyar hankali"
Sonsa da k'aunarsa da kuma tausayinsa suka k'ara shiga cikin zuciyarta
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncinta
Cikin damuwa yace
"Miye kuma na kuka chuchu"
Hannu tasa tashare hawayen tana cewa
"Tabbas samunka matsayin miji agareni,wani babban rabo ne daga ubangiji,na tabbata da bakai na aura ba da yanzu wanda na aura ya maidani gidanmu danna tabbata babu me iya zama dani da wannan lalurar atare Dani"
Tak'arasa fad'a wasu sabbin hawayen na gangarowa daga idanunta
Ajiyar zuciya yasauke tare da kama hannayenta yana kallon cikin idonta
"Rauda,allah yayi nine mijinki shiyasa ma ya k'addaro miki wannan al'amarin,dan Allah ki kwantar da hankalinki banaso inga damuwa a fuskarki,wallahi nikad'ai nasan yadda Nike Jin zuciyata idan naganki acikin damuwa"
Tayi murmushi still hawaye nabin fuskarta
"Zan rink'a b'oye wa dan kawai hankalin naka ya kwanta amma kasan damuwata bazata tab'a ciruwa ba face na rabu da matsalar dake tattare Dani"
Har lokacin hannayenta na rik'e cikin nasa
"Jikina nabani kinkusa rabuwa da wannan matsalar,ko ince munkusa rabuwa da ita,insha allahu muna gab da fita daga cikinta"
Ta gyad'a kai kawai dan ita tasan yanzu ma suka fara shiga cikin matsala
"To allah yasa"
Tafad'a,suka shiga cikin bedroom suka d'auro alwala
Shiya jasu sallar, Allah-allah yikeyi ya idar sabida zugin da k'afarsa keyi masa
A daddafe ya sallame sallar,ya mik'ar da k'afar yana mamakin zugin da k'afar ke masa
Jikinta yayi sanyi dan ta fahimci ba kwanan dayayi azaune bane yasa k'afar tasa haka,k'ila abunda ke shiga cikin jikinsa ne
"Jaana haryanzu k'afar bata dena ba ko?
K'ak'aro murmushi yayi yace
"Aa ta Dena,kawai dai na mik'ar da ita ne"
Ajiyar zuciya tayi tana girgiza Kai,batasan me yasa yike son b'oye mata halin da yike ciki ba
"Jaana dan allah kadena min irin haka, at least in kanajin abu kafad'a min ko kana da wacce tafi nine?
Nida bani da wanda yafika ai komai naji saina sanar dakai amma Kai......
Ya katseta
"Chuchu kinsani babu abunda zan b'oye Miki,k'afar ta Dena tund'azu"
Ta kauda kanta gefe gudun kada yaga hawayen da ke Shirin zubo Mata
"Chuchu"
Yakira sunanta,saida tashare hawayen sannan ta juyo tana amsawa
"Na'am"
"Zonan"
Yafad'a,ta taso tak'arso gabansa ta durk'usa
Janyota yayi ya rungume ta yana sauke wani numfashi me nawi
"Kizauna ajikina,ko zanji sanyi acikin zuciyata"
Yafad'a yanajin yanayin sa na k'ara canzawa,k'afa da zafin jikin nakuma addabarsa
Runtse idanuwanta tayi wasu sababbin hawayen na ambaliya a fuskarta
Yakuma matseta ajikinsa bakinsa na ambaton
"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalumin"
Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallon yadda ya runtse idonsa alamar yana jin rad'ad'i
Addu'o i tafara tofa Masa, idanuwanta na fitar da hawayen tausayi da tsantsar damuwa
K'arfe tara tayima zayyad a Tasha,Dan malam aminu ya sanar dashi sunkusa isowa
Ko minti goma beyi da zuwa ba,motarsu ta tsaya
Yafito cikin manyan kayansa da nad'in rawani akansa
Dattijone kamilalle me cike da natsuwa,ya mik'ama zayyad hannu sukai musa baha suka gaisa,sannan suka shiga motar zayyad d'in
Bayan zayyad yatada motar yace
"Malan sannu da hanya,gaskiya kun iso da wuri motar tayi gudu"
Malan yace
"Ai da wuri nafito ina idar da sallah danma motar tad'an tsaya mana amma da mun iso tund'azu"
Zayyad ya jinjina kai yana cewa
"Allah sarki,kayi hak'uri fa malan,muntasoka mu yakamata ace munzo da kanmu amma halin da abokinnawa ke ciki yasa nace bari dai kazo d'in"
Malan yayi d'an murmushi
"Babu komai"
Tunda suka iso get d'in gidan malan aminu ya fahimci akwai gagarumar matsala acikin gidan
Hakan yasa ya umarci zayyad da ya dakata da shiga cikin gidan
Sai da yayi addu'o I sosai sannan yace zayyad ya shiga
Zayyad ya shiga yayi parking,sannan suka fito zayyad yafara knocking d'in falon
Har lokacin suna rungume da juna, bakinta kuma bedena karanto addu'o in ba
K'wan-k'wasa k'ofar da zayyad yayine yasa suka bud'e idanuwansu atare
Dede lokacin wayar Umar tafara k'ara ganin numban zayyad yasa yace
"Ina ganin zayyad ne,mukoma falon"
Suka mik'e sukayo falon yana d'an ciccije bakinsa dan ciwon dad'a k'aruwa yikeyi
Kan kujera ya zauna,Rauda ta bud'e k'ofar
Ta gaishe da su tana kallon malan aminu Wanda shima ita yazuba ma ido
Ta basu hanya suka shiga sannan ta maida k'ofar tarufe,takoma kusa da Umar tazauna
Yayinda suma suka zauna suna gaisawa da Umar d'in
Malan aminu yatashi ya dafa kan umar yana nazartar abunda ke damunsa
Ya girgiza kai fuskarsa d'auke da damuwa yana duban Rauda sannan itama ya dafa nata kan
Janye hannunsa yayi dasauri yana kallonta fuskarsa d'auke da tsantsar mamaki
A fili yace
"Aasim bin ramzad?
Yasauke numfashi Yana kuma girgiza kai cike da tarin fargaba
"La haula wala k'uwwata illah billah"
Malan aminu yafurta yana komawa kan kujerar ya zauna
Gabad'aya sun zuba mai ido suna jiran suji abunda zece
Ya sauke numfashi yana kallonsu
"Zahiri kuna cikin babbar matsala,domin kuna tare da rauhanin da ba kowani malami bane ze iya ja dashi"
Yad'an numfasa sannan yacigaba dacewa
"Amma nayi mamaki,Aasim bin ramzad rauhanine,kuma a iya sanina rauhanai basa cutarwa,wani laifi kuka masa haka da ya tunzurasa yike azabtar daku?
Ya k'arasa maganar Yana kallonsu sosai
Ganin basu bashi amsa ba yasa yacigaba da cewa
"Tabbas akwai laifin dakuka masa mai girma wanda ya tunzurasa ya canza daga ainihinsa,kuma ni tabbas bazan iya ja dashi ba amma zan iya nemansa inji dalili inkuma jaraba rok'onsa ko ze iya hak'ura"
Har lokacin babu wanda yayi magana kallonsa kawai sukeyi,umar ne yakatse shurun ta hanyar cewa
"Malan dan Allah kataimaka kayi iya abunda zaka iya, wallahi muna cikin damuwar da bazamu iya kwatanta maka ba"
Malan aminu yagyad'a kai yaciro wani turare a aljihunsa ya fesa sannan yafara karanto addu'o I da basajin me yake fad'a illa bakinsa da suke gani yana motsawa
Ahankali d'akin yafara duhu,saiga shi ya bayyana cikin ainihin suffarsa ta yarima
Malan aminu nagani,yazube a k'asa yana faman jera kirari
"Allah yataimaki yarima,me martaba d'an sarki,basarake me dubbannin dawakuna"
Fuskarnar tasa a tamke ya watsawa malan aminu razanannun idanunsa cikin b'acin rai yace
"Kai wanene,da har ka kai matsayin da zaka nemeni"
Bakin malan aminu na rawa yace
"Ka gafarceni ranka shidad'e,tuba nike allah ya huci zuciyarka"
Ya kad'a kai yana cewa
"Fad'i kiran me kakemini,meke tafe dakai,me Kuma yashigo dakai matsalar da babu ruwanka,shin kanaso rayuwarka ta salwanta ne?
Jikin malan aminu na kyar-kyarwa yace
"Tuba nike ranka shidad'e,amsa Kira na dakayi kad'ai ya isheni,bakuma nanemeka bane dan na Isa,illa Dan na rok'eka da ka sassauta ma wad'annan bayin allahn.....
Da wata kalar tsawa ya katsesa
"Kai!
Kashiga taitayinka,kakuma tuna da wanda kake magana,kai baka isa ka nemar musu afuwa ba,kuma hukuncine nariga da na yanke,mafita ta rage garesu"
Malan aminu bakinsa na rawa saboda kid'imar da yayi
Yace
"Kagafarceni tuba nike allah ya huci zuciyarka"
Aasim ya kalli Rauda da umar yana yimusu wani kallo da shi kad'ai yasan ma anarsa
"Nafad'a kuma zansake fad'a muku,ko ku rabu da juna kokuma daga yanzu kicigaba da fuskantar barazana,kuma gubata akullum k'ara ratsaka zatayi wallahi sai ka gwammace mutuwarka da halin da zaka shiga
Ke Kuma....yanuna Rauda sannan yacigaba da cewa
"Yanzu ne zaki fahimci ko ni waye dakuma matsayin da nike dashi"
Yana gama fad'ar haka yab'a ce
Nan danan haske ya gauraye falon ya dawo yadda yike
Gabad'aya malan aminu ya jik'e sharkaf da zufa,shiko zayyad harda fitsari ya saki saboda tsananin tsorata
Malan aminu yasauke doguwar ajiyar zuciya yace
"Agaskiya bazan iya ba,ku gafarceni amma ya wuce k'arfin da kuke tunani,bazan iya ba dan allah karku sake nemana dan rayuwata zata iya shiga cikin hatsari"
Yak'arasa fad'a yana mik'ewa ze fita
Zayyad na kiransa amma be tsaya sauraronsa ba ya k'arasa ficewa daga falon dan gabad'aya ya firgita
Rauda ta runtse idanuwanta cikin tashin hankali maganganun malan aminu nayimata yawo acikin kunnuwanta
"Aasim bin ramzad rauhanine kuma rauhanai basa cutarwa tabbas kunyi masa laifin dakuka tunzurasa wanda yasa ya canza daga ainihinsa"
Wasu hawaye ne masu zafi suka cigaba da gangaro mata
Ahankali ta furta
"Tabbas ban kyauta ba maka ba,amma ban cancanci wannan hukuncin daga gareka ba"
Wanene Aasim? Menene had'insa da Rauda? Me suka masa da ya canza sa daga ainihinsa?
Muhad'u a page 🔟 dan jin yadda zata cigaba da kasancewa taku a kullum
Y'arfillo.
[20/10, 8:38 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo) 🧕🏻
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
🅿AGE📕 🔟
_Wannan Page naki ne anty Nabeelt Allah nike rok'o ya baki lafiya, yasa kaffara ne ya kuma k'ara dank'on zumunci a tsakaninmu Amiiiin_
Maman ummi kema ina Allah yak'ara lafiya yasa kaffarane yakuma nuna mana auran ummi lafiya😅
Ban manta da ke ba safnah👩🏻🎤. Ina godiya da addu'o in ki gareni
_GAISUWA DA JINJINA_
*_Ga ya ommer allah yak'ara k'warin ido muna godiya da zak'ulo mana kura-kuran mu daka keyi, da kuma gyara dakake mana, bazamu iya biyanka ba ya Ommer wlh muna jin dad'in shugabancin ka sosai Allah ya bar mana kai da rai da lafiya mai anfani, ya kawo bata tagari kuje har katsina musha ringen-rigegen_*💃🏻💃🏻💃🏻
Bissmillahir rahmanin rahim✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
FARKON LABARI
Cikin katafariyar jami'ar dake cikin katsina
D'alubai ne sukayi dandazo a wani wuri da alama sakamon jarabawarsu da sukayi suke dubawa
Hayaniya da turereniya sunyi yawa a wurin,dan ko wani d'alubi burinsa yaga sakamakon sa
Tafiya Rauda Take yi cikin sauri har da gudu-gudu yayinda ta hango dandazon d'aluban
Gabanta na fad'uwa, k'irjinta na dukan uku-uku ta isa wurin
Ganin yadda maza da mata suka cakud'e yasa tasamu gefe ta tsaya,dan bazata iya shiga cikin maza ba
Saida taga d'aluban sun ragu,sannan ta k'arasa wurin gabanta na fad'uwa
Bata ma fara duba sunan ta daga sama ba,daga tsakiya tafara tanayin k'asa
K'irjinta yayi mugun bugawa yayinda taga abunda taci
Takasa d'auke hannun ta awurin sakamakon sanyin da jikinta yayi
Wasu y'ammata masu ji da kansu dake gefenta suka fashe da dariya
Cikin haibaci d'ayar me suna laurat wacce itace take fitowa da first class a department d'insu,takalli d'ayar me suna farida tace
"Farida waike wace irin k'wa-k'walwa kike da itane,ace kowani semester bakya iya fitowa da ko third class sai dai probation"
Farida taga ne nufin laurat sarai hakan yasa ta fashe da dariya tace
"Kannawa ne a toshe yike, kwata-kwata baya iya d'aukar komai,saboda dattin talauci da kuma miyar kuka sun toshesa"
Dariya suka sakeyi gabad'aya su biyun cikin nishad'i da annashuwa
Rauda tasan da ita suke,hakan yasa tabar gurin jikinta a sanyaye ba tare da ta tanka mu su ba
Can baya taje tazauna k'asan wata bishiya, gabad'aya tarasa me ke mata dad'i dan ta tabbata idan tacigaba da kasancewa tanafitowa da wannan sakamakon to tabbas watarana koranta za ayi
Wasu hawaye ne masu zafi sukafara biyo kuncinta yayinda ta tuno mahaifinta dakuma yadda yike so tayi karatu
Shin ya zatayi?
Wata tattausar murya taji tayi mata sallama,tad'ago da idanuwanta da sukayi sharkaf tana kallon me yin sallamar
Wani kyakkyawan saurayi ne tsaye cikin k'ananan kaya
Kyawunsa yawuce yadda za a fasalta
Duk da damuwar datake ciki behana zuciyarta yaba kyawunsa ba
Yakuma yin sallama a karo na biyu
Amma nanma kasa amsawa tayi dan ji tayi jikinta yayi mata wani iri tsigar jikinta tafara tashi
Murmushi saurayin yayi yana durk'usawa daga tsayen dayike,tazarar dake tsananin su bazata wuce kamu hud'u ba
Har lokacin da murmushi a fuskarsa
"Be kamata ace kink'i amsamin sallama ba,domin ko nasan ke musulma ce yakamata ace kin amsamin"
Cikin muryarta da ta fara dashewa tace
"Wa alaikumus Salam"
Murmushi ya kuma yi yana zaro farin handkerchief daga aljihunsa,ya mik'ama ta
"Kwata-kwata hawaye beyi kyau a wannan kyakkyawar fuskar ba,kamata yayi ace murmushi ne akanta ba hawaye ba"
Murmushin ko tayi dan taji dad'in abunda yafad'a
Amma still da hawayen a fuskarta
Yazauna dirshan a k'asan kamar yadda take a zaunen yana cewa
"Wa yacemiki ana had'a murmushi da kuka?ai sai kin share hawayen tukunna"
Mamakine ya kamata ganin yanayinsa da Kuma tsadaddun kayan dake jikinsa amma kuma ya zauna a k'asa
Handkerchief d'in ya sake mik'amata
"Amsa Mana na k'osa inga kingoge wannan hawayen"
Amsa tayi idanuwanta a kansa,tana tambayar zuciyarta, shi kuma wannan wanene?
"Baki sanni ba ko,nazo na cika ki da surutu,kiyi hak'uri nima surutu ba d'abi'ata bace kawai dai banaso naga mutum ya na cikin da muwa ne"
Tayi murmushin daya tsayamata iya baki tana share fuskarta
Bayan ta gama goge hawayen ta mik'a mai handkerchief d'in tana mamakin kafeta da idanu dayi
Be amsa ba kuma har lokacin bata ce mai komai ba
Ya rausayar da kai yana cewa
"Menene yasaki kuka haka,ko kin fad'i jarabawa ne?
Ajiyar zuciya ta sauke yanayin fuskarta ya k'ara nuna alamun damuwa
Amma kuma har lokacin batace uffan ba
Ya sauke numfashi Yana K'ara kallonta sannan yace
"Da dukkanin alamu bakyaso kifad'a min,to koma menene ba kuka yakamata kiyi ba,addu a yakamata kiyi,ki rok'i Allah da ya yayemiki
Abunda ke damunki kinji?
Dede lokacin k'awarta Salma ta iso wurin tana cewa
"Haba Rauda, tund'azu inata nemanki ashe kinanan.........
Takasa k'arasawa samakon lura da saurayin dake zaune dirshan gaban Raudan
Rauda tamik'e tace
"Inanan,kindubo result d'innaki?
Cikin daburcewa salma ta d'aga mata kai tana kallon saurayin wanda shima ya mik'e
Ganin yadda salmar ta saki baki tana kallon sa yasa Rauda ta galla mata harara tana matsowa kusa da ita
Cikin murya k'asa-k'asa tace
"Miye haka?
Salma tad'an dai-daita natsuwarta tana maida kallonta ga Rauda
"Am....nace...dama...
Harara Rauda takuma galla mata ganin yadda duk tawani daburce daga ganin mutum
"Kikace me? Ta tambaya tana kafeta da idanu
Salma zata kuma magana ta katseta
"Kinga malama muje ko?
Tak'arasa fad'a tana nuna mata hanya
"Amma dan Allah inaso ind'an yi magana dake,na y'an mintoci idan bazaki damu ba"
Saurayin yafad'a yana duban Rauda
Rauda ta girgiza Kai tace
"Kayi hak'uri bani da lokaci,inada abunda zanyi"
Bata jira jin me zece ba taja hannun salma suka wuce
Tunda suka bar wurin Rauda ke mita
"Wannan ai zubar da ajine,ki wani saki baki kina kallon mutum salon ya rainaki,inbanda shashanci miye zaki wani kafe mutum da ido kamar kinga wani sabon halitta "
Itadai salma bata tanka mata ba,harsaida suka koma d'akinsu
Rauda wurgar da k'aramar jakar dake hannunta tayi tafad'a kan k'aramin gadon k'asa tana lumshe idanuwanta dasuka k'an-k'ance saboda b'acin rai da kuma damuwar da take ciki
Salma ta zauna kan kujerar dake tsakar d'akin,
Tace
"K'awa waye wannan dana gani,a ina kika samosa?
Rauda ta tashi daga kwanciyar da tayi tana dafa kanta
"Wai meyasa kike tambaya akansa ne?miye damuwar ki da shine?
Kamata yayi kidamu da jarabawar Dana fad'i ba ki tsaya kina tambaya akan wani can da k'ila ma ba k'ara ganinsa zaki yi ba"
Salma ta sauke numfashi tana tasowa daga kan kujerar tada wo gefen raudar ta zauna
Dafa kafad'ar ta tayi tace cikin kwantar da murya
"K'awata kema kinsani nafi kowa damuwa da damuwarki,kawai dai na tambaya waye shine ganin bantab'a ganinki tare da shi ba,amma kiyi hak'uri"
Rauda ta tasauke doguwar ajiyar zuciya
"Bansan ya zanyi da raina ba,kiduba fa kiga tunda jarabawar nan ta matso na dena bacci,kwana nikeyi ina karatu,amma abun haushi sai naje rubuta jarabawar sai inji namanta komai,
Haka b'angaren lissafi kwata-kwata bana ganewa, nasan nan gaba korata za'ayi"
Tak'arasa fad'a idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Salma tasauke numfashi,tana girgiza mata Kai
"Dan Allah karkiyi kukannan,addu'a zamu cigaba da yi,sannan kuma kik'ara dagewa insha'allah za'a wuce wurin"
Gyad'a Kai kawai tayi takoma ta kwanta
Daddare tana zaune bacci yakasa d'aukar ta, tunanin sakamakon jarabawar ta kawai takeyi
Taja guntun tsaki tare da mik'ewa tasha ruwa sannan ta dawo zata kwanta
Handkerchief d'in da yabata d'azu ne tagani a k'asa,sai lokacin ta tuna be amsa ba
Ta durk'usa ta d'auka sannan takoma bakin gadonta,tana jin k'amshin dake fita ajikin handkerchief d'in sama-sama
Zaunawa tayi tana k'arema handkerchief d'in kallo,farine k'ar sai wani zanen fulawa golden a jiki,ta kara kusa da hancinta
Wani sassanyan k'amshi ne medad'i ya bugi hancinta
Ta lumshe ido zuciyarta na hasko mata kyakkyawar fuskarsa
"Waye shi?
Ta tambayi zuciyarta,Tana sake kallon handkerchief d'in
Ganin bata da amsa,yasa takwanta batajima da kwanciya ba bacci ya d'auketa
Washegari da sassafe ta shirya dan k'arfe tara take da lecture
Ko karyawa bata tsaya tayi ba,kasancewar tasan halin lecture ran bayi da kirki ko kad'an gashi yayi mugun samata ido
Gabad'aya ajin yayi tsit, yayinda yashigo ya gabatar da bayani me tsawo sannan sannan ya rubuta wani word ajikin allo
Ya juyo yana kallon d'aluban yana duba wanda ze zak'ulo ya maka mai tambaya
Ba abunda k'irjin Rauda keyi face dukan uku-uku
Dan tasan zeyi wuya be kira sunanta ba
"Rauda"
Taji yakira sunanta,k'irjinta yayi wani mugun bugawa
Yakuma Kiran sunan
"Rauda"
Yana nunata da hannu
Sannan yacigaba da cewa
"Tashi kifad'a min miye na rabuta"
Jikinta na rawa ta mik'e tana kallon allon,cikin rawar murya takaranta
"Radi..cals"
Lecturer mamman ya gyad'a kai
"Fad'amin miye ma'anar radicals?
Shuru tayi dan batasan miye ma'anarsa ba,bugun zuciyarta nadad'a k'aruwa
Tsawa ya daka Mata
"Ba tambayar ki nayi ba kikayimin shuru"
"Radicals is a........
Saikuma tayi shuru
Lecturer mamman ya dafa kansa na y'an mintuna sannan ya ware jajayen idanuwansa yana kallonta
"Yauma baki sani ba ko?duk wata tambayar da za'ayima d'an secondary idan akayimiki Baki sani ba,wai shin a wace makaranta kikayi karatu kafin kizo jami'a?
Shin lefin daga malamankine wad'anda suka koyar dake?kokuma daga k'wa-k'walwarki ne?
Yad'an numfasa tare da jan dogon tsaki sannan ya d'auke kallon sa daga kanta yamaida kan sauran d'aluban
"Waye ne ze fad'amana ma'anar radicals?
Cikin yauk'i da yanga laurat ta mik'e tafara bayani cikin wani salo na turanci me burgewa
Lecturer mamman ya jinjina kai cike da gamsuwa da bayanin da tayi
Yak'ara dacewa
"Haka akeson d'alubai masu hazak'a ba wanda kullum k'wa-k'walwarsu take a toshe ba"
Tunda Rauda tafito da ga ajin zuciyarta ke suya, gabad'aya taji rayuwar tafitan mata arai,
Gabad'aya d'aluban dake tsakar makarantar sauri sukeyi saboda hadarin da yayi bak'ink'irin yanata cida alamar yana gab da fara ruwa
Banda Rauda datake tafiya kamar wacce k'wai ya fashemawa aciki
Jitayi ta bangaji mutum,litattafan da ke hannunta suka zube a k'asa
Dasauri takallesa,saurayin jiya ne
Atare suka durk'usa dan kwashe litattafan
Cikin muryarsa me taushi yace
"Yauma allah ya k'ara had'amu"
Yafad'a yana tattara litattafan
"Kayi hak'uri bansan ya kayi na bangajeka ba"
Ya jinjina kai iska na kad'a kwantaccen gashin kansa
"Babu damuwa,ina zaki je haka?ga hadari ya taso?
"Hostel zankoma"
Ya d'an kalleta yace
"Amma tsakanin hostel da nan aida d'an nisa natabbata kafin kikai ruwannan ya sakko......
Be k'arasa ba ruwa yafara saukowa da k'arfi
Hannu tamik'a yabata litattafan,ya mik'o yana cewa
"Amma ki fake acan wurin........
Hannunta da nashine suka gogi juna,
Wani irin yarr taji ajikinta, dasauri takallesa suka had'a ido
Jitayi gabanta yafad'i ahankali taji kanta yad'an Sara
Ta d'auke idanuwanta akansa Tana mik'ewa da niyyar cigaba da tafiya zuwa hostel d'in
Jitayi ya ruk'o hannunta tajuyo da sauri tana kallonsa
"Tafiya cikin ruwannan ze iya haifar miki da zazzab'i ki fake ruwan ya tsaya dan Allah"
Yafad'a yana kallon cikin idanunta
Zame hannunta tayi ahankali idanuwansu na sark'e da juna,batamai musu ba suka k'arasa gurin barandar
Kan wani dankali ta zauna,shikuma ya tsaya Yana goge gashin kansa da ruwa yafara jik'awa
Kallonsa takeyi sosai takasa d'auke idanuwanta akansa
Ya maida handkerchief d'in aljihu yana kallon yadda ruwan ke sauka da k'arfi
Daga bisani ya juya yana dubanta
"Dama ance mata ba sa tsoron ruwa, amma kuma hakan kuskure ne,saboda ze iya shafar lafiyar mutum"
Ya k'araso wurin dakalin ya zauna a gefe
Yana kallonta atsanake, yacigaba da cewa
"Yau kuma meyafaru naga damuwa a fuskarki, ko tun da muwar jiya ce?
Itama kallonnasa takeyi gani takeyi kamar ta sanshi,kamar ta tab'a ganinshi,to amma a ina?
"Wanene Kai?
Tambayar tafito daga bakinta batare da ta shirya yinta ba
Yayi d'an murmushi
"Kinaso kisan ko ni waye? Yad'an dakata sannan yacigaba dacewa
"To ai ba damuwa bane,sunana Aasim ni sabon d'alubi ne"
"Aasim?
Ta mai-maita sunan tanaso ta tuna inda ta tab'a jinsa
Ya d'aga kai
"Eh Aasim,kinji sunan wani iri ko?
Ta gyad'a Kai tana k'ara nanata sunan a zahiri
"Aasim?narasa a inda na tab'a jin sunannan,amma kai ba d'an k'asar nan bane ko?
Be bata amsa ba ya wurgo mata nasa tambayar
"Me kika gani?ban yi kama da y'an nigeria bane?
Ta d'aga kai alamar eh tace
"Kaima kasani ai"
Dariya yayi,wacce tabayyana fararen hak'oransa
"To inni ba d'an Nigeria bane ya akayi nike jin hausa?
Tayi dan murmushi tana bashi amsa
"May be zama yakawoka, Nigerian ka koya"
Dariya ya Kuma yi
"To ni d'an Nigeria ne"
Tak'ara kallonsa
"Amma iyayenka su ba y'an nigeria bane"
"Um to,yanzu dai abar maganar Nigeria ko wata k'asa,da y'an wata k'asa nayi miki Kama?
Tayi jim tana nazarin da wata k'asa zata dangan tashi
"Ummm to nina rasa ma da wata k'asa zan dan gantaka,saudiyya ne ko india?ko da yikema farinka ba irin na indian bane"
"Tofa? to ko da y'an china nike kama ne?
Yafad'a cikin zolaya
Tayi murmushi gami da cewa
" Ni gani nikeyi kamar muntab'a had'uwa kafin wannan lokacin"
"Nima haka nike gani,baki fad'amin naki sunan ba"
Yafad'a yana son kawda zacen da ta kawo
"Sunana Rauda"
"Suna medad'i, kamar yadda me sunan ta kasance"
Yafad'a fuskarsa na nuna tsantsar farinciki data rasa gan me ko farincikin menene
"Nagode"
Tafad'a tana maida kallonta ga ruwan da yafara rage k'arfi
Ya sauke numfashi,yace
"Zanso muk'ulla alak'a ta abota,ma'ana muzama kaman y'an uwa ni dake,tunda nafara ganinki naji na natsu dake,bansani ba ko zaki bani damar hakan"
Tayi guntun murmushi tana sauke numfashi
"Gaskiya aa,saboda nidakai bamu had'a hanya ba kwata-kwata"
Cikin rashin fahimta yace
"Bangane ba"
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu
"Ni ina alak'a ne da wad'anda suke Dede Dani,amma kai kafi k'arfina kayi hak'uri"
Ya jingina da bango har lokacin idanunsa na kanta
"Wannan ba magana bace,dani dake duk d'aya ne,kuma duk allah ne yayimu danhaka kada kisake fad'in haka"
Ta jinjina Kai
"Shikenan"
Tundaga wannan Rana alak'a me k'arfi tashiga tsakaninta dashi
Kodayaushe idan batada lecture suna tare Yana koya mata karatu wanda take fahimta sosai
Ahankali k'wa-k'walwarta tafara bud'ewa yazamana duk wata tambayar da za'ayima ta a aji tana amsawa
Wanda hakan yafara ba wa mutane mamaki,ita kanta tana mamakin kanta,da ta karanta abu sau d'aya sai taji ya zauna mata
Kamar kullum tagama d'aukar darasi,tafito daga lecture room fuskarta d'auke da nishad'i daga nesa ta hango motarsa,inda yayi mata horn
Tak'arasa suna ma juna murmushi,sallama ta mai ya amsa yana K'ara rage glass d'in motar
"Yau kindad'e"
Ta d'aga Kai tana murmushi
"Kasan jarabawa ta kusa,shiyasa"
Yace
"Hakane shigo to yau yawo zamuje"
Bata musa ba,ta zagaya ta bud'e marfin motar tashiga, Saida tazauna ya tada motar sannan tace
"Yawo Kuma? To ina zamuje?
Hankalinsa nakan tuk'in yabata amsa
"Yawo,kawai ko kuma akwai inda kikasani ki kaimu?
Ta girgiza Kai
"Aa ni bansan ko inafa,danni ko a kaduna ba yawo nike yi ba ballantana a garin da ba nawa ba"
Ya jinjina kai cikin gamsuwa
"Hakan yana da kyau ai,ba kimar mace bace ace tana yawo"
Gyara zamanta tayi tana kallonsa sosai
ya juyo suka had'a ido,tayi saurin lumshe nata tana cewa cikin wata kalar murya me sanyi
"Wai meyasa idan muka had'a ido sai inji tsigar jikina na tashi ne?
Tayi mai tambayar idanuwanta a lumshe
Guntun murmushi yayi,yana k'ara kallon ta
"Nima bansani ba, hala nawa idanun sunfi naki k'arfi ne shiyasa"
Ta bud'e idanun ta sauke su akansa,tana jin jikinta nayi mata wani iri
"Kace dai kai d'an baiwa ne kawai,dan komai naka ya bam-banta dana sauran mutane"
"To kodai ni ba mutum bane?
Ya jeho mata tambayar
Tayi dariya tace
"Haba dai to ko da aljani nike tarayya bansani ba?
Itama tayi mai tata tambayar tana dariya
Ya d'aga kai tare da cewa
"Ze iya kasancewa,kinsan aljanu duk inda kike tunaninsu sun wuce Nan"
Dariyar ta kuma yi
"Eh lallai Kam,ai duk k'arfin aljani baze iya yin siffar mutum kaman naka ba,sufa ance ko sunyi suffar mutum to basa iya yin k'afar mutum saidai kaga kofato"
Idanunsa na kan titi yace
"Ashe?tofa
Ta jinjina kai
"Eh Mana,ai ta k'afafunsu ake gane su,kuma ance muryarsu ma basa iya yin ta mutane"
"Hu'um ashe basa samun cigaba kenan?
Yafad'a
Rauda ta d'aga hai had'i da cewa
"Kaga,mu bar maganar aljanun nan kar su jimu,dan wallahi ni tsoronsu nike ji,wai shin ma ina zaka kaini ne,naga kana ta luluk'awa?
Dariya yayi sosai harda rik'e ciki
"Rashin sani yafi dare duhu"
Ta kallesa cikin rashin fahimta
"Bangane ba?
Ya tsayar da dariyar yana cewa
"Nufina inda zankai ki,da kinsan inda zan kaiki da baki ce inata luluk'awa ba"
Ta gyad'a Kai
"To ina zaka kaini?
"Gidan aljanu"
Yabata amsar a tak'aice yana guntse dariya
Galala,tayi mai wani kallo
"Sai dai ka kaini gidan sarkinsu"
"Nan ma idan kinaso zan kaiki ai kwantar da hankalinki"
Y'ar dariya tayi tana cewa
"Kasan duk ina tsoronsu ina kuma sonsu?
Ya kalleta na y'an sakwanni sannan yamaida kallonsa kan titi
"Bangane ba aljanun kikeso?
Ta d'aga Kai
"Eh bari kaji inbaka wani labari,akwai wata rana ina kwance bayan sallar magriba,d'akin babu haske sosai najuya zan gyara kwanciya sai naga jariri akwance kusa Dani,amma banga fuskarsa ba,mace ne ko na miji bansani ba,nak'ara kallo a karo na biyu still nagani,amma kafin in k'yafta idona sai naga babu komai,
Washegari nike ba y'an gidanmu labari har Nike ce musu,da ace zankuma ganin jaririn dana d'auka shine suka dinga min dariya wai inje ind'auka ma aljanu d'ansu zan gane kurena"
Aasim ya jinjina kai fuskarsa na nuna alamun mamaki da jin labarin
"Cap kuma da kikagani baki ji tsoro ba?ai ni innine bazan iya bacci ba?
"Lallai baccina nayi harda munshari"
Dede lokacin suka isa bakin wani gida,yayi horn
Masu gadi suka bud'e get
Wani madai-dai cin gidane me kyan gaske wanda tsayawa fasalta shima b'ata lokacine
Gabad'aya jikinta yayi sanyi kallon gidan kawai takeyi gabanta na fad'uwa
Ya faka motar,agefe yana cewa
"Muje ko?
Kallonsa tayi
"Ina ka kawoni?
"Idan muka shiga zaki gani"
Ta girgiza Kai
"Aa bazan shigaba kafad'a min inane Nan?
Yasauke ajiyar zuciya hmmmmmm
"kinsan dai bazan kawoki inda zan cutar dake ba ko?
Shuru tayi tana k'ara kallon gidan jinsa da tayi tsit da alamun babu kowa aciki
"To inane Nan?me yakawo ta yamata?
Ya katse mata tunanin
"Please muje kinga yamma nayi "
Ajiyar zuciya tasauke me nawi,yafito yabud'e mata k'ofar
Tafito,yayi gaba tana binsa abaya
0 comments:
Post a Comment