```Wannan littafin daga farkon shi har zuwa karshe sadaukarwa ne ga mahaifina ina rokan Allah ya jikansa tare da salihan bayi```
*Kamar yadda na fara lafiya Allah ya bani ikon gamawa lafiya tare da isar da sakon dana ke son isarwa cikin aminci*
Page 1~2
___________📲"Abba ba lalle bane sai na bi zaɓinka, domin Allah ma ya faɗa laɗa'atun bi mahlukin fi ma'asiyatul khalik. Ma'ana babu biyayya ga abokin halitta matuƙar sabon Allah ne dan haka ka janye kudirinka a kaina"
Wasu zafafan mari Ummi ta ƙwaɗa mata cikin tsananin bacin rai ta ce "Azeezat kinsan dawa kike magana kuwa? Mahaifinnaki? Lalle wuyarki tayi kauri har ke kina da bakin ja wa mutum aya ne mara tarbiyya."
Zabura Azeezat tayi tabi ta ƙafar Abi ta wuce fuu, biyota Ummi tayi da gudu kafin ta iso ta Abi ya dakatar da ita."Dakata! Habiba kyaleta duniya ce zata isar mata."
Tsayawa tayi tana haki ta ce"Haba Abi ya za'ayi abar yarinya kamar Azeezat tana yin abinda take so,ko da yaushe fa ce wa kake duniya ta isar mata baka tinanin hakan zai iya janyo lalacewar ƙarshenta."
Ƙwafa Abi yayi wannan lokacin ranshi ya gama ɓaci gaba ɗaya a ranshi yana ce wa ina ma ba shi ne ma'ahaifin Azeezat ba. Lura da yanayin sa tayi alamun cutar shi na neman tashi da sauri tayi kansa ta riko sa, bedroom ta kaisa tare da kwantar da shi a kan bed.
Cikin sanda Azeezat ta leka parlor ba komai ne ya sata lekewa ba sai jin muryar su Ummi ya lafa. Ganin ba ko wa ya sa tayi ƙwafa gami da ce wa
"Yan iska kawai haka kawai zaku hanani yin abinda nake so dan kuna iyayena to wallahi baku isa ba."
Bata yi wata² ta saka Ƙafa ta fice ba tare da ta bi ta kan su Ummi ba.
Daidai bishiyar mongue ta tsaya tana ta leke² can taga wani yaro ta kwalla masa kira.
"Dan albarka a unguwar nan kake?"
"Eh anan nake ga gidan mu ma can"
"Yawwa shiga gidannan ka kira min Abdulmalik".
Minti uku yayi ya fito ya ce mata yana zuwa. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi.
"Haba Azeezat me haka kuma ba na hanaki zuwa inda nake ba" rai a ɓace ya faɗa bayan ya fito
"Abdul malik ka taba ganin inda kifi ya rayu ba tare da ruwa ba? Mutum zai iya rayuwa ba tare da jini a jikinsa ko ya shaki numfashi ba? "
"A'a meyasa kike ce haka"
"Indai haka ne to ba yanda zaiyu na rayu a doran kasa ba tare da kai ba, Abdul ka ki yadda da ce wa kaine jigon rayuwata inajin wutar kaunar ka na daɗa ruruwa a cikin zuciyata ka taimaka ka bani dama na shiga cikin zuciyarka na tabbata sannu a hankali zaka faɗa cikin shauƙin kaunata."
Tabe baki Abdul malik yayi yana wani cin magani kamar yana ciwon baki ya ce
"A hakan? Idan fa ana maganar so Azeezat kiyi gefe domin babu shakka nasan babu soyayya ta daidai da kwayar zarra a cikin zuciyarki so karki fara."
Durkusawa Azeezat tayi a gaban Abdul malik, hawayenta na zuba tamkar yayyafa ake, zuciyarta na bugu gami da jin ciwon kin yadda da Abdul yake nuna mata.
"Abdul me zanyi ya tabbatar maka ina kaunar ka?"
Harara ya watsa mata tare da bace mata a wurin, a zabure ta bi bayansa kafin ta ankare ya shige gidansa. Harta sa kai zata shiga komai ta tuna sai ta koma jikin bishiyar taci gaba da kuka. Bayan shigan shi yana ta jira ta karaso dan yaga time din da ta biyoshi amma shiru. Rintse ido yayi ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa ba tare daya ce komai ba. Baccin wahala ce tayi gaba dashi sai daf magrib ya farka da addu'ar a bakin shi. Toilet ya nufa babu bata lokaci yayi wanka ya dauro alwala, darduma mai laushi ya shimfida, magrib ya fara gabatarwa sakamakon ya fara jiyo kiraye²n sallah daga bisani yayi azahar da la'asar. Ga mamakinsa yana fita ya ga Azeezat har yanzu na dunkule a karkashin bishiyar fuskar ta ta kumbura suntum idan ta yayi jajur.Dauke kansa yayi, ganin shi ya sata ta tashi a guje tayi inda yake ta zube masa a kasa tana kuka. Dake Unguwar ba jama'a sosai kuma anshiga sallah hakan ya bashi damar durkusawa a gabanta, kokarin kama hanunta yake gami da rungumeta a kidime ta janye. ɗan karamin tsaki yayi ya tashi wai idan an tambayesa yayi fushi. motarshi ya shiga duk da binshi da take bai hanashi tafiya ya barta ba."Azeezat indai bazaki amince da kudirina ba babu ni ba ke." ya faɗa bayan ya tada motarshi.
"Oh ya Rabbi wannan wacce iriyar *MAKAUNIYA SO CE* ni *AZEEZAT*.
Jiki ba ƙwari ta kama hanyar gida ƙwaƙwalwarta na zayyanu mata tinani iri² wanda ita kanta bazata iya tantance me take tunawa ba.da kyar ta samu a daidaita dan hadari ne sosai har an fara ruwa kaɗan². Daidai kofar gidansu ya sauke ta,zuru² tayi da ido dan ba kudi ne da ita ba, kuma daga inda ya daukota zuwa unguwarsu dari biyar ne. Hannu tasa a aljihu tana lalubawa.
"Ke malama na fa san irinku ba yau aka saba mana ba wallahi bazan lamunta ba ki cire min kuɗina ko na miki tsinannen duka"
Fari tayi da ido tafara magana cikin salo na kissa
"Honey napep yanzu ni zaka yiwa haka ai ko kyauta zaka iya kawun..." Bata karasa shegantakar ba taji saukar bell a jiki.
"Ni zaki rainawa wa wayo ciro min kuɗi ko jikinki yayi tsami"
"Laaa! Ni zaka daka yau zaka gamu da sharri na. Juyawa tayi sai taga wani dattijo na zuwa nan fa Azeezat ta fara ihun neman taimako.
"Baba ka taimaka min zai min fyaɗe a kan titi na shiga uku".
Bude baki mai napep yayi ya kasa cewa komai tabbas wannan makira ce, ganin zata tara masa jama'a ya saita hanya da kyar ya sha.
Abi ne yaji hayaniyar jama'a ya fito dama yasan bai wuce Azeezat ba. Kaɗa kai yayi ya ce
"To sai ki wuce ko gantalalliya wacce bata san kanta ba"
"Nidai ba gantalalliya bace kuma ai ko baka ce na shiga ciki ba tunda gidan ubana ne dole ne na shiga,haka kawai sai anga jama'a a fara zagin mutum wallahi ni bazan lamunta ba."
Abi da kunya ta gama rufe sa ko daga kai ya kalli jama'ar da suka taru ya kasa. Cikin sanyin jiki ya shige gidan sa ya rufe ƙofarsa."Allah ya wadaran hali irinna Azeezat,kai wannan asarar haihuwa ce".Abinda jama'ar wurin ke faɗa kenan.
Tsaye take a harabar gidan hanunta rike da tsaleliyar bulala gefe guda Kudrat ce ke ta famar kuka tana bata hakuri.Abi na sa kai Ummi ta jefo masa tambaya."ina Azeezat din."kafin ta gama rufe baki Azeezat ta ce "to uwar mita kinfi mayya takura gani nan me zaki min ni dan Allah karku cinye ni wannan wanne irin iyayene subhanallah.uhmmm lallai ma Ummi da kika rike wannan dogowar bulalar duka na zakiyi?"
Hannu Ummi tasa ta goge hawayen fuskarta rai na ƙona ta ce "Azeeza tambaya ta kike?idan dukar zan miki ramawa zakiyi?"
Tafe hannu Azeeza tayi kana ta ce "jar uban can,wai da kina tunanin tsayawa zanyi ki dake ni ina kallo?hmm lalle matar nan kada kiga ina kiranki da Ummi wallahi kika taɓani sai naga wacce tayi nakuda ta haifu ki,yasin cin mutuncinki zanyi idan baki sani ba."
"Ya ilahi!Azeezat ni kike faɗawa mugayen kalamai irin wannan?" tayi maganar zuciya a karye."o!ko konkonto kike ko dan ban ce Habiba ba"
Kudrat cin mutuncinne ya isheta ta tashi tayo kan Azeezat ta kama ta da faɗa.Ummi ce ta ce "Ƙyaleta Kudrat bana son raini yayarki ce kinsani saboda haka ki bata matsayinta."
Zatayi magana Ummi ta tsayar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.da gudu Kudrat ta yi ɗaki tana mai tsananin jin kiyayyar Yayarta.Ummi bata kara tankawa Azeezat ba tayi shigewarta itama.Ajiyar zuciya Azeezat ta sauke ta ce "bara na ɗauro alwala ko azahar banyi ba."
Bayan ta idda alwala ta isa Palour ganinsu tayi sunyi jugum.murguɗa baki tayi kana ta ce "munafuki dai Allah ya kashe shi,ko da safe ko da rana ko da maraice." Kudrat zatayi magana Abi ya ce "Kudrat bana son kice wani abu anan."shiru tayi kamar yadda mahaifinta ya umarce ta amma jin zuciyarta take kamar zata tsage tsabar baƙin ciƙi.Azeezat kuwa cigaba da wake wakenta tayi.ganin ba wanda ya kulata sai ta shiga ɗakinta tana nazarin mai zatayiwa su Abi su kwana cikin bakin ciki.wata dabara ce ta faɗo mata cikin farin ciki ta fita Parlour tana dariya ta ce "Abi tsuhu mai ran ƙarfe,dan Allah meyasa ka haifu ni?ni wallahi ka cuce ni da ƴar masu kuɗi nayi kama amma haka kawai ka...ni anya ma ba sato ni kayi ba?"
Ido kawai suka zuba mata bayan ta gama rashin kunyarta ta shiga kitchen ta debo tuwo miyar yakuwa da semo tana tafe tana ci haɗi da korafi ce wa abincin talakawa ne.
"Abi dan Allah ka bar Azeezat ta auri wanda take so,cin mutuncin ya isa haka a ganina tunda ba mu zamu zauna mata a gidan ba kawai mu ƙyaleta ko ma waye ta aura." "idan nayi hakan ya tabbata ita ta haifi kanta kenan,ta gama rashin kunyarta miji de na riga na zaɓa mata in shaa Allah gobe Yaya zaizu a tsaida rana dan haka bana so ki saka baki a cikin zancennan."
Kaɗa kai Ummi tayi tana jimamin abinda zai faru nan gaba dan Azeezat ta wuce tinanin mutum.
*Comment After read coz the COMMENTS are like oxygen for a writer dont forget to SHARE*
Cute HapCyyy
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *AZEEZAT.......*
*MAKAUNIYAR SO CE*
written by
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
```Dedicated to my lyf Abbanah Allah ya kai haske kabarinka. Ameen```
Page 3~4
___________📲Washe gari da misalin ƙarfe takwas na safe Baba na Yobe suka karasa garin maiduguri da zummar sanya wa Azeezat da Kareeem rana.bayan sun huta an gama cin abinci aka zauna domin tattaunawa Babana Yobe ne ya ce "Lawan bazaiyu a aurawa yara juna ba matukar basa so zaifi kyau a kira Azeezat tunda ga Kareem a ji ta bakin su."
"yanzu Yaya mu haifi ƴaƴa a cikinmu shine har sai mun tambayesu kafin zamu aiwatar da wani abu a kansu?"
"Ba haka nake nufi ba Lawan,ina gudun abinda zaije ya dawo ne kar muzu muji kunya daga baya"
"Shinenan Kudrat jeki kira Azeezat ɗin."
Babu musu Kudrat ta shiga dakin Azeezat, a jikin mirror ta hangota tana shafa lips tick. Sanye take da wando iya gwaiwa red color sai kuma farin shirt da bai karasa cibinta ba sai siririyar gyale fari ta naɗe wuyarta dashi.
"Lafiya kuwa kika shigo min daki?"
"Kiji daɗi ma Allah yasa na shigo daki mai najasa dole ce ta sa ni idan ba haka ba kinyi karya kike ki ka kafa ta kusa da ke, kizo Abi na kiranki."bata jira amsar ta ba tayi tafiyarta."kanki akeji" Azeezat ta faɗa tana hararan bayan Kudrat.cikin kwanciyar hankali ta gama shirinta, fitowa Azeezat tayi cikin wannan dan iskar shigar ba tare da damuwa da abinda zasu ce ba.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Lawan me nake gani haka, Azeezat dama ɗabi'un naki sunyi muni kamar haka ne"
"Dakata Baba kana ta faman ihu sai kace kaga aljana yanzu dan Allah idan ba neman magaba mai aibun shigarnan da har zaka fara ihu,ni wallahi ka tsinka min zuciya.ba wannan ba ma,minti daya na baka ka fadi dalilinka na kirana sauri nake". Sake baki sukayi suna aikin kallan Azeezat da ke taunar chewing gum tana fari da ido. Ummi ce ta tashi jiki na ɓari ta saka hannu ta wanke Azeezat da zafafan mari. Dafe kuncinta tayi ta ce "ni kika mara?" Cikin kuka Ummi ta ce "An mareki me zaki iya yi." Hannu Azeezat ta daga zata kai kan fuskar Ummi KAREEM ya rike hanun a hatsile. "Ke wato rashin tarbiyyar taki ta wuce yadda ake zato har zaki daga hannu ki mari mahaifiyarki a gaban idan mu." "Kai wawa sake min hannu sai na nuna mata ni yar zamani ce." Kara damke hanunta yayi sai da tayi kara, durkushewa tayi ta rafka ihu "wayyo hanuna ya karye, hanuna ya karye" ko kallanta ba wanda yayi bare ta saka ran samun sannu.sai da tayi mai isarta ba wanda ya kulata.tashi tayi ta ɗau hanyar gidan Abdulmalik.
Waya ta samu yanayi bayan ta isa, ganinta yasa ya kashe wayar tasa haɗi da kura mata ido, shigar da tayi ya matukar tafiya da imaninsa bai taba zaton Azeezat zata iya yin abinda ya sa ta ba.da murmushi a fuskarsa ya isa inda take hannu yasa ya tallabo fuskarta yana smilling ya ce
"Zezaty ke nake gani ko ido na ne ke min gizo" fari tayi da ido tasa hannu ta ja karan hancinsa sannan ta ce "Kana mamakin ganina a haka ne Abudul,indai a kanka ne ba abinda bazan iya ba"
"niko na tabbatar da hakan Zeezaty daga yau ko inace yanzu,soyayyata har sai ta ishe ki zan nuna miki tawa ba wasa bace"
"da gaske Abdul kana so na" tayi maganar tana kallan cikin idan sa.haryanzu bai saki fuskarta ba ya ce "kina so na tabbatar miki da hakan ne." sunkuyar da kai tayi tana jin daɗin kasancewa da shi a irin wannan yanayin,musamman ma yanda yake suburbuɗu mata kalaman soyayya.
"Me na rufe fuskar kuma matata." jin ya ambace ta da suna matarshi sai taji wani abu ya ziyarce ta tun daga tafin kafarta har sakiyar ƙwaƙwalwarta.cije libs Abdul yayi ko ba komai hakan ya tabbatar masa da ya fara rikita mata ƙwaƙwalwa.ɗagota yayi cak bai direta a ko ina ba sai toilet.daddaɗan ƙamshi ne ya dakan mata hanci,ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke take taji wani yanayi na zuwar mata wanda bata san da shi ba.shower ya sakar masu sai da jikinsu ya jike sharkaf kafin ya fara ƙoƙarin rabata da kayan dake jikinta.hankalinta ne ya fara neman gushewa dan bata saba jinta a irin wannan yanayin ba,koƙarin hanasa ta fara tuni idanunta sun fara neman zubar da ƙwalla.
"dan Allah Abdul ka ƙyaleni bana so" cikin muryarsa da bata fita ya ce "haba Zeezaty karkimin haka na kai matakin da bazan iya jurewa ba" abinne ya soma fin ƙarfina nan take na rufe musu ƙofar da ƙarfi.for about 30mins kafin ya fito da ita ɗauke a hanunsa tamkar jaririya. Gaban mirror ya ajiyeta ya ɗauko lotion mai ƙamshi ya shafeta sai narke masa take dan yau taji abinda bata taba ji ba kuma ya mata daɗi sosai.ganin shafe-shafen ba karewa zaiyi ba tayi ƙarfin halin ce wa "Abdul zan tafi gida" "Zeezaty yanzu ko ni nace ki tafi zaki iya tafiya ki barni cikin wannan yanayi" "ba wai haka bane..." kafin ta karasa ya haɗe bakinsu wuri ɗaya yanawa lips nata mugun tsotsa.zaman kan kujera bazatayu ba ya cinciɓuta sai kan bed.
Sun ɓata loƙaci sosai suna abu ɗaya gabannin magrib kafin suka fito rike da hanun juna.
"Zeezaty yanzu tafiya zakiyi ki barni" "nima fa bada so na bane Abdul anfi ƙarfi na ne" "hmm bawani anfi ƙarfi amma ba komai jeki,amma fa karki manta gobe kiyi sammako kinji" manna mata kiss yayi a goshi,murmushi tayi ta saka kai ta fita tana ɗaga masa hannu shima haka har suka daina kallan juna.
Tsaye take bakin ƙwalta tana jiran adaidaita sai ga jeep ƙirar zamani tayi parking gabanta,sauke glass yayi anan ne ta samu damar ganin mai motar,dattijo ne mai kimanin shekaru akalla 55 ya ce "ƴan mata ko zaki shigo na rage miki hanya ne" "wow!dole ma na shiga ai irin wannan mota haka da gani zan kwashi ƙuɗi" tayi maganar a rai.sai da ya kara mai-maitawa sannan ta shiga har bakin ƙofar gidan su a ajeta tare da bata card nashi sukayi sallama ta shige.
A zaure ta tarar da Kareem da alama masjid zai wuce.zuciyarta ce tayi harbin tara wani tsoron shi ne ya ziyarci ilahirin jikinta ta kama karkarwa.hakan sai ya bashi dariya amma sai ya dake ya ce "hmm Azeezat kenan ahaka kika fita kina ƴar musulmai hakan ya da ce kenan." idan akwai abinda Azeezat ta tsana bai wuce faɗa ko wa'azi ba.duk da tsoron da take ciki bai hanata mayar masa da martani ba "Dan Allah Kareem karka fara bana so ka ƙyale ni" ɗage kafaɗa yayi tare da ce wa "its on ur own cup of tea." Matsawa kaɗan yayi ta shige tana mursike fuska.ajiyar zuciya ya sauke yana mai ƙara jin tsanar Azeezat "hmmm bana kaunarki amma ko dan na gana miki azaba zan amince da aurannan."
Wucewa ciki tayi da tunanin sai ta yiwa Kareem tabon da bazai taɓa mantawa ba indai ya kuskura ya aure ta.
Washe gari su Abi suka yanke ranar Azeezat da Kareem.wata biyu kacal suka saka,Abi ne ya tarasu gaba ɗaya dan ya shaida masu.
"Alhamdulillah,Allah ya nuna mana lokacin da muka daɗe muna jiran zuwanta,Kareem Azeezat a matsayin mu na iyayenku mun zaɓa muku juna a matsayin abokan rayuwa fatan zakuyi biyayya garemu" Baba ne yayi maganar ɗauke da murmushi a fuskarsa.
"Yaya kenan,biyayya ya zama wajibi nasan Kareem ɗana ba zai taɓa bamu kunya ba,amma wannan" ya nuna Azeezat da yatsa ya kuma ce wa "wannan fitsararriyar yarinyar bata gaji arziki ba" inji Abi.
Taɓe baki Azeezat tayi kamar bazata ce komai ba can ta ce "Abi dan Allah meyasa kai da Ummi kuke son neman magana ne,ni yanzu na tanka maka ne amma kana zagina yanzu idan mutum ya rama sai a ga laifinsa nidai nayi maka last warni....." tas taji saukar mari har biyu,sanin kanta ne idan ba Kareem ba ba mai mata hakan kukuni ta soma ya daka mata tsawa ai ko tsab ta nutsu.
"Alhamdulillah Kareem shine dai-dai ke zai gyara miki zama aure kuwa babu fashi" Ummi tayi maganar yayinda take ƙokarin tashi.
Tashi Azeezat tayi ta kama hanyar ɗaki Kareem zai dakatar da ita Baba ya masa alamar daya barta,daf bakin kofar ɗakinta ta tsaya ta ce "Baba!Abi!Kareem! Ku zuba ido ku gani indai anyi aurannan to Lawan da Habiba shigiya suka haife ni." shigewa tayi da sauri.
"Ya ilahi! Wani laifi nayi ka jarrabe ni da irin wannan yarinya,Allah na tuba ka yafe min" share hawayensa yayi banda ciwo ba abinda yake ji a rai. Baba kam kasa ce wa komai yayi sai Kareem da yayi karfin halin ce wa "Abi dan Allah ka kwantar da hankalinka in shaa Allah zan gyarawa Azeezat zama komai zai wuce ka daina damuwa"
Ajiyar zuciya mai nauyi Abi ya sauke gami da ce wa "ina fatan hakan."
Hira suka ɗauko dan kore masa damuwa har aka kira sallan azahar.
*Comments is na Oxygen for a writer try it pls dont forget to Share*
Cute HapCyy ce😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗi da nadamar rayuwa_
Story /Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
[Karamci tushen mu'amula ta gari]
```Dedicated to you my lyf Abbanah Allah ya jikanka ya kai haske kabarinka yasa canne mafi hutu a gareka. Ameen😭```
*To be a successful person you most face some interruptions, consequences or painful stories , a successful person is the one who always accepts his mistakes and try to cover it. Proudly wit mah self I took it as a gift and I really appreciate ur corrections*
*Bisa duba da wasu dalilai sunar littafin AZEEZAT! MAKAUNIYAR SO CE ya dawo MAKAUNIYAR SOYAYYA fatan zamu cigaba da tafiya tare masoyana*
Page 5~6
_____________📲Zama tayi bakin gado tare da zabga uban tagumi. ba komai ne ke ɓata mata rai ba sai yanda taga su Abi suka dage akan zancen auranta da Kareem."dole na dakatar da aukuwar auran nan tun wuri,yanda naga Kareem na dagewa akai wallahi cutar dani zai yi kuma wallahi ni Azeezat sai nayi masa tabon da bazai taɓa mantawa ba muddin ya kuskura ya aure ni." ganin tinanin na so ma yimata yawa ta ɗau ɗan ƙaramin gyale zata je gidan su Kareema. fitowarta yayi dai-dai da fitowar Kareem tofar da miyau tayi ta ce "shi dai mutum idan bai gaji arziki ba koda yaushe naima yake ya saka kanshi cikin matsala,ni kuma Azeezat bana taɓa bari akawu min tsalle duk wata ɓuli da zata janyomin zubar ruwa a randa toshe ta nake." sarai Kareem ya san da shi take amma sai ya ƙyaleta ko kallanta baiyi ba. Haka ta wuce tana ta fama habaice-habaicen ta. daga nesa ta tsaya ta samu dutse tana wurgawa ta window na Kareema dama haka suke dan Abban Kareema ya hanata zuwa gidan sa a faɗanshi zata lalata masa Ƴa. Babu jimawa Kareema ta fito sukayi bayan gida.
"lafiya kuwa Azeezat na ganki da yammacinnan haka"
"ina fa lafiya Kareema, Kareem de da kika sani ɗan gidan Baba na Yobe tsabar sun raina ni wai shine mijina an yanke rana wata biyu"
"kutmeleci wata biyu?to ina Abdul din ko bakya son shi ne wannan Kareem ɗin ɗan shegen girman kai ai ko da kinyi asara"
"haba Kareema ke ma fa kinsan yanda nake kaunar Abdul,kawai kinsan su ƴan boko ne gidan su wai ba a aure da wuri,yanzu idan ya gama service ma zai cigaba kafin yayi aure ban san ya zanyi ba,bana jin zan iya yadda da auran Kareem dan Allah wani taimako zaki iya bani"
"hmm tab to wai taya zaki yadda da zaɓin tsufi irinsu Abi,wallahi Azeezat indai kika yadda tabbas kin cucu,abinda nake so da ke shi ne ki cigaba da zabga masu rashin kunya har su gaji suce jeki zaki gani"
Murmushi Azeezat tayi sannan ta ce "shiyasa nake ƙara kaunarki ƙawata hakan zanyi"
Tashi Kareema tayi cikin gaggawa ta ce "ba komai ai matsalarki tawa ce,zan tafi gida kar Abba yazo ya sameni a waje wanki nakewa Mama na"
"jeki ƴar wahala kullum cikin yiwa Mama wanki kike"
Tafiyarta Kareema tayi tare da furta "wawiya kawai" a hankali.
Komawarta gida bayan sallar isha Kareem yasa aka kirawota da kamar bazata je ba sai kuma tayi yanke shawarar zuwa taji ko da mai ya zo.
"taƙamar me kake har zaka fara kirana fira da dare,angayamaka ka samu ƙarɓowa ne a zuciyata,indai haka ne ka makara"
Ƙara bajewa yayi akan kujerarsa yana latsa wayar shi game ɗin temple run yake ko kallan inda take baiyi ba ya ce "Khadija kenan! Yanzu har daƙiƙancin naki ya fara saki tunanin son ki ne yasa na kirawo ki? Indai haka ne kina ruwa"
"naji sai ka faɗa abinda yasa ka kirana sauri nake"
Tashi yayi daga kwancen da yake kana ya ce zauna zamu fuskanci juna.zama tayi kamar yadda ya faɗa.
"Khadija..." bai ƙarasa ba ta ce "wai Kareem me ke damunaka ne? Ko Abi baya kirana da suna Khadija amma kawani dage sai kirana kake dashi,look bana so ka daina" murtuke fuska yayi ganin yadda ta hayayyaɓo masa indai bai taka mata biriki ba zata ci tuwo a kansa.kamar bazai ɗau mataki ba ya tashi a hankali ya rufe ƙofar ɗakinsa. Duk inda ya gifta tana kallonsa zuciyarta ta fara harbawa gami da nadamar yi masa ihu. Bell mai kauri ya samo ya fara zuba mata ta ko ina. Azeezat tun tana daurewa har ta fara ihun neman agaji da ke ƙaramin gida ne ihunta ya kauraye ko ina. Su Abi na ji basu kula ba sai ma Allah ya ƙara da suke mata. Sai da yagama jibgarta iya son ransa kuma ya sata yin shiru kafin ya so ma faɗan dalilinsa na kiranta.
"wato Khadija ganin inawa iyayena biyayya bisa zaɓa min ke a matsayin mata shi ne kike tunanin sonki nake ko,to bara na faɗa miki wallahi ko za a haɗa min dukiyar duniya gaba ɗaya ace na aureki da so na bazanyi ba, dana aureki gwara corona virus ta kama ni na tsane ki" turu baki Azeezat tayi ta ce "ina ruwana ai nima ba sonka nake ba ni dan Allah ka faɗi abinda ya sa ka kirani" o! Azeezat bakinta baya mutuwa, ya faɗa a rai. A zahiri kuwa ce wa yayi " Azeezat so nake muyi yarjejeniya"
" Akan me fa"
"Akan auran mu, duk da kince bazaki bari ayi auran ba amma zan baki shawara akan ki amince muyi auran shekara ɗaya,inya so na miki alkawarin zan sake ki atleast iyayenki bazasu ce kin bijirewa maganar su ba"
Shiru tayi na ɗan wasu mintuna can ta ce " amma taya zaka sake ni bayan kasan ko mai za a yi a family sai an nemi izinin Iyaye?"
"yawwa tambaya mai kyau,a ranar da aka ɗaura mana aure ana kaiki gidana zaki fara aljanun ƙarya,ki dunga ikirarin zaki kashe ni ki kashe kanki idan bamu rabu ba kinga daga nan ai shikenan"
Shirun ta kuma yi tana nazarin maganarsa kamar de ta amince da hakan.
"ke nake jira Azeezat,ko fa baki yadda da hakan ba inada hanyar da zan iya bi na rabu da ke ba tare da iyayenmu sunga baki na ba,kawai bana so nayi hakan ne ba tare da na sanar da ke ba amma kiyi tunani akai"
"hmm wani tinani kuma,da ina sonka ne zaka faɗi hakan amma nima ba kaunarka nake ba saboda haka na amince ayi hakan,amma fa nima da sharaɗina babu zancen ce wa ni matarka ce kayi tinanin alaƙar aure zata shiga tsakanin mu" Dariya yayi sosai sannan ya ce " ni namiji ne mai matuƙar kishi,bazan taba kusantar macen da ta zama tamkar ledar pure water ba kinji indai wannan ne karki damu"
"naji ledar pure water amma hakan bai hanani samun masoyi na hakiƙa ba" tana idda zancenta tayi gama abunta dan idan tacigaba da zama Kareem zai kasheta da baƙin ciki. Zubewa tayi akan bed fuskarta ba fara'a ko ƙaɗan "bazaka taɓa burgeni ba Kareem kuma ba zan fasa niyyar da na ɗauka akan ka ba wannan alkawari ne." ta faɗa cikin ɓacin rai.
Harara Kareem ya bita dashi gami da ce wa " zan ɗanɗana miki kuɗarki Azeezat,cikin shekara ɗaya zakiyi danamar tusawa iyayenki bakin ciki"
********
Washe gari Baba na Yobe ya koma sai de Kareem haryanzu yana nan a ce warsa bazai tafi ba zaiyi kiwon matarsa dan baya son wani ya raɓeta wanda yayi kokarin hakan kuma kashe shi zaiyi. Ummi ce tayi murmushi irinna su na manƴa ta ce
"to! Suruki na haka abin yake,lalle wannan matar taka ƴar gata ce"
"hmm Ummi kenan kinsan yanda nake ji da ita kuwa, ban taba zaton mafarki na zai zama gaskiya ba"
"kaji shi nan ku kunyata baka ji,oh ni Habiba"
Tayi maganar cikin wasa. Satan kallan Azeezat yayi da ta gama cika saura kiris ta fashe bakinta kuwa cike yake da abun ce wa,dama kuma so yake tayi rashin kunya ya ci kaniyarta da duka.
"da alama korata kuke to bara na bar muku wurin ko sha fira ke da mijinki ko Ƴata." inji Ummi.
Buɗan bakin Azeezat ta ce " ya Rabbi,kujimin mata yanzu Ummi tun kafin ayi auran har kina kiransa da mijina sai kace faɗin Allah yanzu idan na ce kinyi ƙarya sai ace banida kunya nidai bana so ki daina" inda sabo Ummi ta saba jin irin waɗannan kalamai wurin Azeezat kaɗa kai tayi ta wuce kitchen ba tare da ta tanka ba duk jikita yayi sanyi.Kareem ko daɗin hakan ya ji ya ce " Azeezat ki zo ki min shara a ɗaki"
"kut angayamaka niɗin wawiyace in kai kaina ka jibgeni to bazani ba" a rai ta faɗa zahiri kuwa ce wa tayi "to."
Hanya ta nema sai gidan Abdul.ta shi yayi ya mannata da jikinshi ya jima a haka kafin ya sake ta ya na ce wa "Zeezaty kinsan yadda nayi kewarki kuwa,inata jiran zuwanki shiru ko dai laifi nayi"
"ba haka bane Abdul,wata gagarumar matsala ce"
"matsala kuma kamar ta mai" yayi maganar yana kara shegewa jikinta.
"Abdul an saka min ranar aure nida ɗan uwa na" ta faɗa kamar zatayi kuka.ta ɗauka zai razana ga mamaki sai ya ce "yanzu wannan ne matsala"
"eh mana nifa nafiso ace kaine zaka fara sani na ƴa mace ba wani kato ba"
"Zezaty ai tun ba yau ba naso ke ce de ba kya so,amma gaskiya yanzu kam bazan taɓa bari wani ya same ki ba,idan bazaki iya bani ba karki kara zuwa wurina."
Marairaice wa tayi ta ce "to yanzu ya kake so nayi"
"ko yaya ne kada ki taɓa bari ayi auran nan"
"Abdul anriga fa an gama magana amma ya ce min zaman shekara ɗaya zamuyi"
"inji Kareem?ƙarya yake miki babu wani sakinki da zaiyi,rashin kuɗi ne ba dan haka ba mai zai hanani auranki Azeezat"
"na yarda da kai Abdul amma ga wata shawara,jiya ne na haɗu da wani dattijo mai kuɗi ko dai haɗa baki zamuyi ina ƙarɓo kudi a wurinsa"
"tab to me kike jira maza ga waya kirasa"
Amsar wayar tayi ta ko ci sa'a ta rike numban,bugu biyu ya ɗauka ta masa bayanin wacece ita. Nan yake cewa gobe da misalin karfe 9 na dare su haɗu a hotel.
"wow! Amma fa naji daɗin labarin nan kinga shikenan mun huta da rashin kuɗi zan ɗauke ki muyita yawon shakatawa"
"Amma de aure zamu fara ko"
"matsalata da ke kenan aure meyasa jarabarki tayi yawa ne"
Ɗan ɓata rai tayi ta ce "naji yanzu de ka kaini gida ban fito da kuɗi ba"
"tab wallahi Azeezat petrol kaɗanne kuma zan shiga school gobe dashi kiyi hakuri ki taka"
"To" ta faɗa tare da mikewa,tayi-tayi ya rakata amma yakiya haka ta kama hanya da kyar da karasa gida duk ta galabaita. Washe gari kamar yadda Alhaji Mamu ya faɗa karfe tara suka haɗu a cities star hotel. Duk yadda Azeezat ta kai ga kuɓuta a hanunsa ta kasa sai da ta kwana tare da shi, su Abi na can hankalinsu duk a tashe Kareem ya kasa zama ya kasa tsaye wannan daren ko rintsawa basuyi ba. Hakura sukayi suka fawwala Allah lamarin ba Azeezat ce ta dawo gida ba sai washe gari da yamma duk kuɗin da Alhaji Mamu ya bata haka ta ɗauka ta kaiwa Abdul sai sanya mata albarka yake yana ce wa i love you tana washe masa hakura bata damu da halin da iyayenta zasu shiga ba.
Cikin kuka Ummi ta fara mata faɗa bayan ta zo "Azeezat me kike so ki zama ne,so kike ki zama silar mutuwarmu ne wannan rashin kunyar duk akan an zaɓa miki miji? Azeezat zan ɓata miki rai wallahi tun jiya ina kika tafi ɗan uwanki ba inda bai nemeki ba ya rasa ki"
Sosa keya Azeezat tayi ta ce "me kika ce banji ba sake faɗa" ran Ummi ne ya tafaso ta zabura ta hau kan Azeezat da duka tana sai ta kashe ta. Iya ƙarfinta Azeezat tasa ta ture Ummi har sai da ta buge kanta jikin bango dafe wurin Ummi tayi dan taji zafi sosai kamar ma da ɗan jini ta ce "Khadija faɗa zakiyi dani"
"kina tunanin kinfi ƙarfi ne,haka kawai zaki hayayyaɓo min sai ka ce wanda na kwana da mijinki Allah Ummi idan baki daina shiga harkata ba zan miki rashin kunya"
"rashin kunya kuwa na nawa Khadija amma ba komai duniya ce zaki gani"
"ai wannan ba rashin kunya bane ina miki kara ne matsayinki na uwata kuma ba abunda zan gani sai alheri,baki ba nama yake samu ba kimin fata ya bini"
"Khadija Allah ya....." Abi ne ya ce "kyaleta Habiba karki ƙarasa ga Kareem nan ya ishe ta" ya faɗa yayinda suke ƙoƙarin shigowa. Fashewa da matsanaciyar kukaUmmi tayi ta wuce ɗaki, Azeezat na ganin Kareem babu ɓata lokaci ta shiga a guje ta saka key a ɗakinta tana haki.
Zaki sani ne yau Khadija, Kareem ne ya faɗa ranshi a matukar ɓace.
*I repeat COMMENTS are OXYGEN for a writer nd dont forget to SHARE PLS*
Cute HapCyyy😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗi da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
```Dedicated to my life Abbanah Allah ya jikanka ya kai haske kabarinka. Ameen```
Special greetings for those who keep praying for me from the beginning of my new novel. Hrt u all🌹
A gift for commenters u guyz are a real fans❤️
Page 7~8
__________📲Baiyi ƙasa a guiwa ba wurin biyota sosai yake buga ƙofar tana ji taki buɗewa daga ƙarshe ma kunna mp tayi ta ƙure vulume tana tiƙar rawa. Abi ne yazu ranshi ya matukar ɓace ya ce
"Azeezat wato ana miki magana shine kika maida mu ƴan iska ko,zaki buɗe ƙofar ne ko sai an ɓalle shi"
"to me maraban dambe da faɗa idan nace muku ƴan iskan ma ai ba laifi nayi ba,dan Allah ni ku ƙyaleni na samu hutu na gaji" kallan Kareem Abi yayi zuciya a karye ya ce
"Kareem ƙyaleta mu wuce in shaa Allah zata gani ba de duniya bace, ta ishe ta tuwo da miya." ba musu ya bishi amma ba dan ya so ba.
Kudrat yasa aka kirawo masa dan ya mata wasu tambayoyi,cikin ladabi ta ce
"Yaya Kareem gani." gyaran murya yayi sannan ya ce "yawwa Kudrat,wasu ƴan tambayoyi nake so na miki amma dan Allah inaso ki faɗamin gaskiyar abinda kika sani." kanta a sunkuye ta ce "in shaa Allahu Yaya bazan taɓa maka ƙarya ba." "yawwa ƴar ƙanwata,kina ji na shin tun da Azeezat haka takewa su Ummi ko sai bayan anyi zancen auranmu." kuka ne ya kufce mata sai da tayi mai isarta kafin ta ce "Yaya tun dana taso haka na kalli Azeezat nayiwa su Ummi,abin na ɗaure min kai tamƙar batada hankali,anya Yaya Azeezat ba aljanu ne da ita ba."
"ki daina kuka Kudrat,nima abinda na fara tinani kenan,yanzu de abinda nake so da ke shine ki daina gudun ta, kina yawan zuwa tayata hira daga nan ki ɗan yi mata wa'azi cikin wasa inaga zamu gano wani abu tattare da ita abin ya fara tsoratani matuka"
"Yaya duk duniya ba wanda nake jin tsanar shi a rai na kamar Azeezat bazan iya zu...." bata karasa ba ya ce " hakuri zakiyi Kudrat,ki danne zuciya idan ba hakan ba bazamu taɓa gyarata ba,shi hanunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar."
"shikenan Yaya zanyi iya ƙokari na amma fa bisa umarninka ba so na ba."
"yawwa ƴar ƙanwa tashi kije" tashi tayi ta wuce tana mai bakin cikin kasancewa a duniya.
A zaune ta tarar da Azeezat tana ƙare ma sabon wayarta iphone kallo fuskarta ɗauke da farin ciki,ganin Kudrat sai ta ɗan ɓata rai gami da ce wa "mai ya shigo da ke ɗakina" danne zuciya Kudrat tayi ta ce "mai da wukar fira nazo tayaki" zata ƙara magana sukajiyo Ummi na ƙiran Kudrat sai ta tashi ta fita a bakin ƙofa ta ce "zan ƙara zuwa akwai abinda nake so na faɗa miki ne" turu baki Azeezat tayi gami da ce wa "makir cinki akan ki zai ƙare mayya"
Bayan wasu ƴan kwanaki
Azeezat da Alhji Mamu soyayyarsu na daɗa ƙaruwa ta bangaren Abdul kuwa yanzu ya fara jin ɗaɗin kasancewa da Azeezat,apart of biya masa buƙata ta kasance tamkar atm na shi ko da yaushe ita ke basa kuɗi.ranar Azeezat ta zo a gajiye kafin ta saka kai a parlour taji muryar su Abi ƙasa-ƙasa,nutsuwa tayi dan jin mai suke cewa
"kinga de wannan kuɗin bashi na ɗauko,dashi nake so nayi muku kayan ɗaki yadda dake ne yasa zan baki ki ajiye min kinji ƴata ƴar albarka" "in shaa Allahu Abi zan adana su a wurin daya dace har sai ranar da kace na ɗauƙo na baka,amma Abi dama auran harda ni ne ba Azeezat kaɗai ba" " oh kinga na manta ne ban faɗa miki ba,ke da Bello ɗan gidan Abokina na haɗaku Abbansa da kanshi yazo ya same ni da wannan batun kuma kinga bai kamata da watsa masa kasa a ido ba" har cikin zuciyarta bata so wannan zaɓin ba domin Bello ba mutumin kirki bane banda shan taba bashida abinyi ganin bata tanka ba kuma farin cikinta ya gushe Abi ya ƙara ce wa "Kudrat ko dai haɗin bai miki bane" murmushi ta ƙirkiro sannan ta ce "ko ƙaɗan Abi ai nasan bazaku min zaɓin da zai cutar dani ba" "Allah ya miki albarka ƴata" da Amin ta amsa ta bar wurin dan zuwa ɓoye kuɗin.ƙwafa Azeezat tayi tana mai ce wa "zaku sani ne ai bazan taɓa bari kuyi farin ciki ba,ke ma Kudrat zaki gamu da sharrina Bello de kwalelenki duk da ba mutumin kirki bane bazan so haka ba ni dai burina ki mutu ba tare da aure ba kuma indai ina raye bazan bari kiji daɗin rayuwarki ba."
Watsa wa Abi harara tayi tare da jan dogon tsaki kana ta ce "Allah ya tsinewa uban daya ke neman ƴarsa,ai wasu ƴaƴan ba banza suke raina iyeyensu ba idan aka ga hakan tabbas akwai makarkashiya,nidai bazance Allah ya shirya ba sai de nace Allah ya tsine,kuma idan ƙarya ne ayi musu na ji,tsohun banza kuma sai na tuna maka asiri,gani ake banida hankali duniya na tsine min ba tare da sanin mai ke faruwa a ƙasa ba saura kiris na tona wa ɗan iska asiri yasin." Tanayi tana satan kallan Abi da hawaye caɓa-caɓa a fuskarsa .
Tashi Abi yayi zai shiga ɗaki ya kasa ƙwaƙwarar motsi,nema yake ya faɗi Ummi da Kudrat suka tare sa,,daren basuyi bacci ba gashi Kareem baya nan da kyar suka samu cutarshi ta lafa.
Ganinta tayi cikin wani rami macizai sun lullubeta baƙar fuskarta kawai ake gani ga wutar da take ci ta ƙasanta, ga Abdul can a gefe sai dariyar mugunta yake mata.a firgice ta tashi tana haki mai ke shirin faruwa dani ta faɗa a razane, a daren ta ɗau waya ta gayawa Abdul ko daya budi baki ce wa yayi "wannan mafarkin batada ma'ana kada ki damu kanki gobe inaso ki kawo min dubu ɗari bana so kice babu"
"Abdul Alhaji fa baya gari"
"nidai na faɗa miki dubu ɗari nake so kuma kiyi sammako ina buƙatar jin ɗumin jikinki" kafin ta ce wani abu ya katse waya. Dafe kan dake mugun sara mata tayi tana tuna mafarkin da tayi da ƙyar bacci ɓarawo yayi gaba da ita.washe gari da safe ta sanya hijab har kasa ta durkusa a gaban su Abi tana me naimar afuwansu dan mafarkin ya firgita ta,aure kuwa saura sati uku. Sosai su Abi sukayi mamaki amma sunji daɗi matuka yadda Azeezat ta nuna tsantsar nadama babu ɓata lokaci suka yafe mata dama abinda suke jira kenan.
"nagode sosai Abi da Ummi kuma in shaa Allahu bazaku ƙara samun matsala daga ni ba,idan da hali inaso na shiga ɗakin Kudrat itama na bata hakuri."
"haba ba komai ƴata ai ƙanwarkice dama hayaniya ce ya sa na miki iyaka da ita tunda kin gane kuskurenki zaki iya zuwa Allah yayi albarka." "Ameen Abina"
Da sallamarta ta shiga yanayin shigarta ne ya bawa Kudrat mamaki,ba tare da ta ce komai ba ta fara mata kuka sai da tayi mai isarta kamin ta naimi yafiyarta itama Kudrat ɗin sosai taji daɗi nan take ta yafe mata,kasancewar Kudrat na zuwa islamiya da time yayi sai ta tafi Ummi ma ta wuce kasuwa nan aka bar Azeezat,ganin ba kowa ta soma bincika inda Kudrat ta ajiye kuɗin da Abi ya bata,da ƙyar ta samu a wani lungu an lullube da ƙeda."shegiya ta iya ɓoye abu ko ba komai na sha wahalar nema." inji Azeezat yayin da take fita. Abi ta samu a ɗaki ganin yana bacci sai tayi tafiyarta,bata tsaya a ko ina ba sai gidan Abdul. Sosai ya ɓata rai ko kallan inda take baiyi ba,matsowa tayi ta dafe kafaɗarshi ta ce "Abdul ina fushi kake dani,wallahi ba yin kaina bane hakan ma da kyar na samu na sato kuɗin da Abi ya bawa Kudrat,da kasan ɓadda kamar da nayi kafin na samu kuɗinnan bazaka taɓa min fushi ba" ajiye masa kuɗin tayi a cinya sai yanzu ya sake fuskar ya fara kokarin rungumarta. Murmushi ta sake masa tare da masa alamar ya cigaba nan suka faɗa wata duniyar.
"Zeezaty yau de dan Allah ki bani abunda nake bukata kinga yau auranku sati uku ne incase ko anyi bazan yi baƙin ciki ba tunda ni na fara shan romon matata" salon da yake mata magana ne ya kara firgitata ba abinda ta iya cewa sai faman narke masa a jiki, alamar tana so ya gani babu ɓata loƙaci ya cigaba da aika mata sakonni ta ko ina.rufa masu kofar nayi a hankali ina masu fatan shiriya cikin zuciyata mugun haushin Azeezat nake sakamakon zubda budurcin ta da tayi.
Bayan sun gama ta koma gida Ummi ce ta lura Azeezat ba dai-dai take tafiya ba tambayarta tayi sai ta ce ai period take dama kuma yana wahalar da ita.
"yawwa Kudrat ɗauko min kudin dana baki ajiya" Abi ya faɗa lokacin suna injoying na dinner tare. Murmushi Azeezat tayi kasa-kasa ta ce lokacin yayi.a gigice ta fito ta ce
"Abi shin ka ɗau ƙuɗinne na duba inda na ajiye ban gani ba"
"kamarya Kudrat idan wasa kike dan Allah ki bari sanin kanki ne fa ƙuɗin nan bashi naci"
"Nikam Kudrat karde kuɗin da kika bawa saurayinkin can" Azeezat tayi maganar tana taunar abinci.
Cikin rashin fahimta suke kallanta musamman Kudrat data rasa inda Azeezat ta dosa.
"saurayi kuma" inji Ummi.
"ƙwarai Ummi,duk da nasan ba lalle ku yadda da abinda nake faɗa ba amma inada tabbacin saurayi ta kaiwa kuɗin sai da ta nemi shawarata ma nace kartayi amma ta nuna bazata iya ganinshi cikin wani hali ba tare da ta taimaka masa ba.
"Kudrat ni zaki munafurta"Abi ya faɗa cikin raunin murya.
Kudrat bata iya magana sai kukar da ta ke ba tsayawa.
"wallahi Abi Kudrat na abinda idan na faɗa maka zaka ce gwara ni,inaso ka bani dama na faɗa muku hujjuji na" Azeezat ce ta ɓata rai tana maganar kai ka ce gaskiya ce.
"Abi wallahi...." "dakata Kudrat bana son jin komai daga gareki,Azeezat na baki dama faɗa mana duk abinda kika sani. Rai a matukar ɓace Abi yake maganar,Ummi kam banda taya Kudrat kuka ta kasa ce wa ƙomai wani irin Ƴaƴa Allah ya jarrbeta dashi abinda nake sakawa a rai kenan.
Tattaro nutsuwarta Azeezat tayi tare da ƙirkiro kukan karya ta fara ce wa ".........
Muje zuwa ƙaɗan daga cikin maƙircin Azeezat rigimar na nan zuwa a gaba ku dai ku cigaba da bibiyar cute HapCyyy.
*DON'T FORGET COMMENTS ARE AN OXYGEN FOR A WRITERS! ND SHARE PLS*
HapCy😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗi da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
```Dedicated to my lyf Abbanah ina rokon Allah ya jikanka tare da maka rahama yasa canne gidan hutu a gareka tare da bamu hakuri da juriyar rashinka. Hakika abin na da zafi bazamu taɓa iya cirewa a rai ba fatana shine Allah ya haɗa mu a Jannatul Firdaus. Ameeen```
Ina matukar godiya bisa nunamin kauna da kuke ta hanyar sambaɗomin comments masoyana😍 Gaisuwar ban girma gareku.
Page 9~10
___________📲Tattaru nutsuwarta Azeezat tayo tare da ƙirkiro kukan munafurci ta fara ce wa "Abi wallahi gaskiya nake faɗa maka Kudrat ce ta ɗau ƙuɗinnan da saninta ta baiwa saurayinta,saboda bata son Bello a cewarta idan ta rabaka da ƙuɗin babu yadda za'ayi ayi auran,gashi ni yanzu ta janyo min za a ɗage aurena da Kareem"
"Ya Rabbi,Azeezat meyasa kike son shiga tsakanina da iyayena,mai nai maki kike son ɓata min farin ciki na" cikin tsananin kuka da firgici Kudrat ke magana.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah kaine Allah ya Allah ka cireni a cikin wannan musiba dana faɗa,idan kuma wani laifin na aikata Allah ka yafemin. Sai da yayi shiru yana nazari tukunna ya ƙara ce wa,
"Azeezat idan har da gaske kike ki kawo shaida,ke ma haka Kudrat anan ne zamu tantace mai gaskiya" tashi Ummi tayi zata shiga ɗaki dan bazata iya juran bakin ciki irin wannan ba. "ina zaki kuma Habiba,dawo ki zauna dake za a gama komai" dawowa tayi ta zauna tana shakar kuka.
"indai shaida ne Abi inada shi" waya Azeezat ta ɗauka direct record list ta shiga,babu tantama muryar Kudrat ce tana ce wa " indai a kanka ne ba abinda bazan iya ba,yanzu haka kuɗin na wurina dan Allah kada kayi fushi dani idan ba so kake a daren nan na fito ba, gobe idan zanje islamiya zan kawo maka kaji,I luv you" inda hiran ya tsaya kenan. Kudrat ta gama ji ta ƙwalla ihu tana "na shiga uku Abi wallahi ita..." cikin matuƙar ɓacin rai Abi ya ce " yi min shiru Kudrat,ashe munafurtata kike a bayan ido" ƙasa cigaba da maganar yayi Ummi ma banda kuka ba abinda take yi shi ma Abi ta maza yayi.
Fashe wa Azeezat tayi da sabon kuka ta kara ce wa "Wallahi Abi da kunnuwa na naji tana ce wa zasu gudu tare ɓacin ranku kawai nake gudu shiyasa ban faɗa maku ba"
"ya isa Azeezat a yanzu na fahimci Kudrat,babu shaidar da ta wuce jiyo muryarta da saurayinta kan batun kuɗi dama ana yawan faɗa ka ji tsoron mutumin da ke nunawa shi na Allah ne a fili,kin matukar bani kunya Kudrat" fuskantarta yayi banda kaɗa kai bata ce wa komai yayinda fuskarta ke cike da hawaye ya ce
"Kudrat ki shirya zaki koma gidan Alhaji kiyi aiki ki biyasa kuɗinsa dan banida halinda zan iya biya"
Karfin hali tayi ta ce "Ummi dan Allah kitayani bawa Abi hakuri walla..." " Ki bari Kudrat ba abinda ya wuce abinda kunnuwan mu suka jiyo mana dan haka kibi umarnin Abi,sanin kanki ne Alhaji baya taɓa ɗaukan asara sabida haka aikin shekara ɗaya ya kamaki"
Zata ƙara magana Kareem yayi sallama ganinsu cikin firgici duk ya tsorata a gigice yake tambayar su "lafiya?" Abi ne ya masa bayanin yadda abin ya kasance tare da kunna masa recording ɗin,tabbas muryar Kudrat ce amma zuciyarsa bata gaskata hakan ba,kallanta yayi cike da kulawa ya ce
"ƴar kanwata nasan ba kya faɗan ƙarya yau ma inaso ki faɗa gaskiyar kamar yadda kika saba,shin da gaske kin bawa wani kuɗin da Abi ya baki ajiya?"
Kanta a sunkuye sai shan majina take bata ce komai ba. Mai-maita mata tambayar yayi nan ne ta ce
"eh Yaya Kareem" ta kuma fashewa da sabowar kuka,a hatsile Abi ya shiga ɗakin Kudrat ya fito mata da kayanta ya watsar a filin gida bakin shi sai kumfa yake fitarwa hanyar waje kawai yake nuna mata.
"Yaya Kareem dan Allah ka tayani bawa Abi hakuri" tashi Kareem yayi ya bar parlo jiki a sanyaye ba abinda ya iya ce wa. Dawowa ga Ummi tayi ta ce "Ummi dan...."
"bana son jin komai daga gareki Kudrat ko wani mataki Abi ya ɗauka babu abinda zan iya ce wa akai,Kudrat kinmin taɓon da bazan taɓa mantawa ba duk da Azeezat tayi makamacin hakan amma alamu sun nuna ta shiryu shine ke yanzu zaki bijiru mana da taki halayyar wannan shine green snake in a green grass Allah yana gani iyayena basu taɓa kukawa akaina ba Allah ne kaɗai zai sa ka min"tana idda maganar ta wuce ɗakinta,cikin tsananin ɓacin rai a yayinda zuciyarta ke harbawa gami da ciwo,idanunta kuwa sun kasa daina zubda kwalla.
Azeezat ma tata ɗakin ta nufa zuciyarta cike da farin ciki fal.
Kudrat ce kaɗai a parlo sai rafka kuka ta ke kwa'kwalwarta ba abunda suke mai-maita mata fa ce " Allah yana gani iyayena basu taɓa kuka akaina ba Allah ne kaɗai zai saka min" Mai Ummi ke nufi karde ace baki ta min. Kudrat ke maganar zuci
"meyasa na mata haka ne,ko da yake ita ta janyo" ta faɗa yayinda take ƙokarin janyo pilor zata kwanta.Duk da haka de zuciyarta wani iri.
Abi kuwa kiran Alhaji yayi ya shaida masa ɓatan kuɗin, Alhaji kuwa bai ya son asara ko da kuwa na sisi ne,yace asan yadda za'ayi a biya masa kuɗinsa Abi ya ce ya yadda Kudrat zataje ta yiwa matarsa da ƴaƴansa aiki na tsawon shekara ɗaya domin biyan kuɗin.
"Alhaji Mamu dan Allah kayi hakuri bada so na bane amma na yarda zataje ta maka aikin shekara ɗaya" bansan me ya faɗa ta ɗayan bangaren ba babu jimawa driver ya zo ya ɗauki Kudrat tana mai ɓakin cikin abinda yayarta ta mata.
Ta window Azeezat ta ji Abi na ce wa Alhaji Mamu nan ta shiga tinanin anya ba Alhji Mamun daya ke kashe mata kuɗi bane? Rashin mai bata amsa ne yasa ta kawar da tinanin zuwa wani daban.
************
Kwana a tashi babu wuya aure saura sati ɗaya,Azeezat kuwa rashin lafiya ta ke sosai haka de ta daddafa taje gidan Abdul.
"Abdul,auran fa saura sati ɗaya banga kana shirya mana komai ba,kuma Abdul bana tantama inada ciki haka mai chemist din unguwarmu ya ce"
Laptop yake dannawa ko yasan da mutum a gefensa. "Abdul magana fa nake maka"
"oh ashe fa,to me kike so na ce miki,so kike nace ki bijirewa maganar iyayenki?Ko so kike nace ki zubar da cikin shegen da kika kwaso? Kuma da kike ce wa kinada ciki ina ruwana Allah ne yasan adadin mazan da kike tarayya dasu dan haka kada ki yadda ki laƙaba min"
Zaro ido tayi tana mamakin furucinsa "Abdul kana cikin hayyacinka kuwa"
"ashe fa bana cikin hayyacina ai na manta sai da kika sanar min"
Saukowa tayi ta dafa kafarshi tana kuka sosai har a zuciya tana jin zafin yadda ya ɗauki issue ta da rashin muhimmaci. "Abdul dan Allah kada ka bari soyayyar da nake maka ta salwanta,ka sani zafin soyayya tamkar zafin kukan jariri ne,ranka na matukar kona yayin da kake ji amma bazaka iya bayyana damuwarka akai ba"
"Allah malamar soyayya,ai ban sani ba"
Cigaba da kuka tayi haryanzu tana dafe da ƙafarsa. Kallanta yayi na kusan minti goma can yayi murmushi ya taso ta yana shafar bayanta,sosai ya lallasheta sai da tayi shiru kafin ya ce "sorry Zeezaty ɓacin rai ne kuma kema bakiyi tunanin mai ya ɓata min ba,yanzu yaushe rabon da alkhairi na kuɗi ya shiga tsakaninmu,ni dai bansani ba ko rowa kika fara"
Cikin kuka ta ce "ba rowa ban...." kafin ta karasa ya sa mata yatsa a baki ya ce "shiii abu ɗaya nake so da ke,a kunne ya raɗa mata,har sai da ta firgita yayin da taji.
"Abdul anya kuwa,to na waye zance kafasan ba wanda ya taɓa ..."
"aa to indai ba haka ba babu ruwana da ke" ya katse ta.
"shikenan hakan zanyi"
Yawwa lovely Zeezaty! Ya manna mata kiss a goshi.
Sai dare ta koma gida duk bata cikin hayyacinta. "taya zance mahaifina ne ya min ciki?tabbas ina yiwa Abdul *MAKAUNIYAR SO* amma bana tinanin hakan abu ne mai kyau" haka de ta cigaba da sambatu ta rasa ma tsaya.
Da ciwon ciki ciwon kai, hajijiya kasaya da sauran su de Azeezat ta kai, aure saura kwana biyu mahaifanta basu damu da rashin lafiyarta ba ɗaukawa sukayi normal rashin lafiya ne da wasu amare keyi gabannin aurensu. Kwance take a kan sallaya cikinta na murɗawa kamar zata mutu,fuskarta kuwa hawaye ne caɓa-caɓa ita kaɗai tasan yadda take ji,karar wayarta taji alamar ana kira sautin kiran Abdul ne amma azabar da take ji ya hanata ɗauƙa ta kai awa biyu kafin taji sauki kaɗan nemansa tayi a waya bugu ɗaya ya daga rai a ɓace ya fara kwararo mata masifa akan kin ɗaga wayarsa.
"kayi hakuri Abdul da kyar na dawo hayyacina wallahi na ɗauka ma mutuwa zanyi"
Ta faɗa cikin muryar marasa lafiya.
Kwafa yayi sannan ya ce
"hmm ina ruwana kwaɗayinki ne ya janyo miki,wai yanzu ya ake ciki ne"
"Abdul an..." bata idda magana a ya ce
"look Azeezat bana so kice a'a muddin kika kasa to da kyar zamu mallaki juna yadda muka shirya"
"Amma Abdul taya zanje mahaifina ne ya min ciki wannan ba abu ne mai sauki ba"
"okay haka ma zakice ko,fine kiyi abinda kike so amma make sure kin cireni a cikin zuciyarki"
Hanging na call ɗin yayi ya cillar da wayar.
Hankalinta ne ya tashi sosai cikin gaggawa ta fito direct ɗakin Kareem ta nufa yana kwance kan kujera mai mazaunin mutum uku yayi zurfi cikin tunani ko shigowarta baiji ba,kare masa kallo tayi sai yau ta lura da shi ma ashe kyakyawa ne black skin nasa ya dace da yanayinsa. Kawar da tunanin kyawunsa tayi ta kurma ihu a zabure Kareem ya taso dan baiyi tsammanin haka ba,durkushewa Azeezat tayi kan floor tana rafka ihu hankalin kowa yayi kanta anyi-anyi ta faɗi dalili ta ki, da kyar Baba na yobe ya lallasheta ya ce ta faɗamasa sai ta ce bara ta idar ta sallar isha amma su tabbatar family ne kaɗai a wurin. Ummi da hankalinta ba a kwance yake ba sai addu'ar Allah yasa lafiya ta ke. Dariya Azeezat tayi sosai bayan ta shigo ɗakinta kana ta ce "Kareem kenan manufarka ka saita ni cikin shekara ɗaya ko,yau zaka san Azeeza ba sa'ar kowani ɗan jagaliya bane zan ɗanɗan maka azaba cikin second ɗaya"
Faɗawa kan gado tayi ta lula duniyar tinani ta jima a hakan kamin ta gyara fuska ta fita a zaune ta hangosu ko wanne da abunda yake sakawa a ransa.
"muna jinki Khadija faɗa mana abunda ke damunki kike kuka"
Ɗagowa tayi ta duba Kareem daya kura mata ido haka kawai yaji ya rasa nutsuwarsa. Da sauri ta sauke ta ce
"Baba ina da ciki"
Ta fashe da sabowar kuka.
Zaro ido sukayi jin maganar tata suke a baibai, "ciki!" Ummi ta mai-maita. Su ko kasa tankawa sukayi. "Azeezat ciki kuma na waye" Baba na yobe yayi karfin halin tambaya
"Na Abi ne"
"Lailahaillallah muhammadurrasulullah sallallahu alaihi wa sallam" gaba ɗaya suka faɗa Abi da Ummi ko tuntuni sun suma tsabar tashin hankali,shi kanshi Baba dauriya ya ke bai yi kasa a guiwa ba ya ƙara tambayarta wani Abi dan kunnuwansa basu gaskata abunda yaji ba.
"Khadija wani Abi kike nufi"
"Baba Kareem nake nufi ai takwaran Abi ne ,Kareem ne ya mun ciki na rantse da Allah"
Ɗago rinannun idan sa Kareem yayi yana kallanta ya kasa magana. Ya rasa wani yanayi yake ciki.
Baba ne ya taso rai a ɓace ya rufe Kareem da duka yana kuka,ƙwaƙwarar motsi Kareem ya kasa bare ya faɗi kalmar da zata kare sa,Baba n acikin dukan Kareem ya faɗi ƙasa shima sumamme.
Hummmmmmm! Muje zuwa cute taku ce.
*Idan har kuna jin ɗaɗin littafin nan to lalle inaso comments naku su iso ni,hakan ne kaɗai zai bani damar cigaba da baje fasahata domin faɗakar daku gami da nishaɗantarwa. Comment na Ho² for us try nd Share pls*
0 comments:
Post a Comment