___________📲Rai a ɓace Kareem ya tako inda Azeezat ke zaune,ba tai kokarin motsi ba sam al'amarin bai ɗaga mata hankali ba.
"Me kika aikata Azeezat, wani suna yakamata na kiraki?, makira?,muguwa?, mara hankali, ko mara imani da tinani? Mai ribarki yanzu, kalli iyayanmu a kwance,cikin yan daƙiƙu kin batawa kowa farin ciki,faɗa min hakan daɗi ya miki shin nayi laifi ne da nake kokarin gyara miki rayuwa dan ki samu albarkar iyaye? Shine zaki saka min da wannan makircin? rayuwar da kika zaɓa wa kanki kenan,ko babu komai kin cutar dani saboda kin sawa iyayena shakku akaina amma ki sani lokacin nadama da kunci na zuwa"
Furzar da iska mai zafi yayi ba tare daya cigaba da magana ba dan bayajin zai iya.
"ka faÉ—i kuma mai nene ba damuwa ta bace amma fa ka sani na riga nayi nasara akanka"
Kallo kawai ya bita dashi, tare da kaÉ—a kai ya yace "zaki gani" ya wuce kan su Abi.
Hospital ya nufa dasu da kyar aka samu aka shawo kansu suka farfado Abi kuwa har yanzu yana jin jiki. Baba ne ya ke jingine kan gado ya nemi kallan Kareem ckin sanyin jiki Kareem ya zo.
"Baba gani, ya karin saukin jiki"
"Ba ruwanka da jikina, Ina umartanka daka barmin gida bana so na kara ganin ka"
Dago fararen idan sa yayi ya daura akan fuskar Baba da babu alamun wasa. Zai ce wani abu Ummansa ta masa alamar da yayi shiru. Tashi yayi ya wuce bai tsaya a ko ina ba sai Mustafa Umar Elkanemi Arabic Collage Maiduguri domin ga na wa da abokinsa a É—aki ya samesa kwance tamkar mara lafiya alamu sun nuna akwai abinda yake damunsa. Cikin sanyin murya ya masa sallama a hankali ya amsa tamkar mai ciwon baki dafa sa Kareem yayi ya sakar masa murmushi wanda da ka gani kasan kirkiro sa yayi ya ce
"Abdulmalik lafiya kuwa?"
Tashi yayi zaune ya lumshe idansa ba tare daya ce komai ba. Tausayinsa ne ya kama Kareem tabbas Abdul na cikin gagarumar matsala kuma ba komai ne ke saka sa damuwa ba sai Abbansa.
"Look Abdulmalik har tsawon wani lokaci zaka dauka kana tinanin abinda baka da halin gyarawa? Ko wanne hali yake baka da hurumin da zaka gyara shi uba yake a wurin ka kuma dole ka masa biyayya fatana shine kacigaba da masa addu...... "
"Ya isa Abdulkareem shekara nawa nayi ina sauraron wannan zancen amma babu sauyi, abubuwa duk sun lalace Abbana nada dukiyar da ya ci ace ina rayuwa tamkar tsuntsu a sararin samaniya babu damuwa barai takura amma tsabar rashin hankali irin nasa banda bin kananan mata da kashe musu kuÉ—i bashida aiki,ka duba yadda nake shan wahala anan a hakanne zan kirasa Uba? Hmm never."
Mtsw yaja É—an karamin tsaki tare da dafe kansa da ke mugun sara masa.
"Hmm matsalar da kake ciki kadanne Abdulmalik, ni da nake da iyayen tsautsayi ta saka na rasa su yayin da suke raye fa mai zanyi kashe kaina?"
"Mai kake nufi Abdulkareem"
Guntun hawayen da ke shirin zubu masa ya goge tukunna ya ce
"Kwarai, Baba ya ce baya bukatar gani na, bazan boye maka ba kanwata Khadija da ake shirin haÉ—a mu aure da ita tamin sharrin ce wa na mata ciki"
"Khadija!" Ya mai-maita a rai cike da tsoro. Numfashi ya sauke bai ce uffan ba.
"Kayi shiru Abdul,yanzu mainene abinyi"
"to! A gaskiya ina tausaya maka Kareem rashin yaddar iyaye abu ne mai mugun ciwo amma idan ba damuwa ka bani dama naje na bawa Abi hakuri"
"a'a Abdul,barshi kawai fatana shine Allah ya tashi kafaÉ—ar Abi tabbas zai fahimce ni fiye da ko wa"
Shiru ne ya biyo baya daga bisani Kareem ya ce "AZEEZAT!" tare da fito da iska.
Mamaki Abdul ya kama Azeezat kuma karde itace Khadija? Kasa hakura yayi ya ce
"wacece Azeezat?"
"hmm itace silar rushewar farin ciki na,itace ta fara buÉ—e min file É—in bakin ciki a rayuwata"
"kana nufin itace Khadija?"
alamar ae ya masa da kai,luuu Abdul ya soma jin hajijiya na É—aukansa.
"lafiya kuwa abokina?"
Cike da rashin gamsuwa da yanayinsa ya tambaya.
"lafiya kalau karka damu kawai ina mamaki ne ace cousin taka ta maka irin wannan sharrin.
"Hmm" abinda ya faÉ—a kawai. Sosa keya Abdul yayi ya ce "Abokina bara na shiga toilet na watsa ruwa ko zanji daÉ—in jikana. Okay Kareem ya ce shi kuma ya wuce.
"Tabbas alamun nasara sun fara tunkaro ni,hhhhm naji ɗaɗin wannan labarin Kareem, Azeezat kin matukar burgeni. Kareem! Yanzu ka fara fuskantar ƙalubale a rayuwarka indai kana tare da ni"
Sauri Abdul yayi ya fito daga toilet É—in É—aure da towel, cikin kwanciyar hankali yayi shirinsa lokaci É—aya farin ciki ya wanzu a fuskarsa har sai da Kareem yayi mamaki.
"Abdul ya naga ka canza ko dai kayi gamu ne a toilet"
"ko kusa Kareem kawai ina kokarin maida damuwata ba komai bane gudun ciwon zuciya,kai ma dan Allah kamin hakan"
A hankali ya tako ya kama hanun Kareem ya marai-raice face ya ce
"Kareem matsala ta da taka abokan tarayya ne,inaso mu rungume juna domin samawa kanmu mafita hakan ne kaÉ—ai ya dace a garemu"
Nannauyar numfashi Kareem ya sauki gami da ce wa
"nagode kuma naji daÉ—in sauyin tinaninka abokina Allah ya shige mana gaba"
"Am..." ringing na wayar Kareem ce ta katse su,cikin sauri ya amsa ganin kiran Abi ne. Magana sukayi na second goma.Ficewa yayi bayan ya ma Abdul sallama alamu sun nuna ana nemansa a gida cikin gaggawa.
Baiyi mamakin ganinsu tare a parlo ba wannan wajibi ne cikin ladabi ya gaishe su kallan kirki bai samu ba dama bai sa ran haka ba,zama yayi tare da sunkuyar da kai wurin tsit tamkar ba kowa ko wanne daga cikinsu da abinda yake sakawa a rai hawayen dake gangarowa kan kuncinsu da yanayin fuskarsu kaÉ—ai ya isa ya isar maka da sakonnin zuciyoyinsu.
"Ya Allah! Ka bani ikon cinye jarrabawar da kamin,tabbas laifina ya girmama,hummm Æ´ata ta cikina tace ni na mata ciki innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Tinanin da Abi yake a rai.
"Duk tarbiyyan dana baka sai da ka nuna na gaza,wanne irin rashin hakuri ne zaisa ka ƙasa jiran ɗaurin auren ku,ƴar uwarka ta jini ka mata ciki?mai yarinyar zatace idan ta taso taji labarinnan"
Baba ma da tasa tunanin.
"Allah ka bani ikon tserewa daga tarkon Azeezat"
Kareem ma da tasa. Su Ummi kam banda aikin kuka basuda ta ce wa. Domin kawo karshen shirun Baba ya fara magana.
"Hakika wannan al'amarin ya sanya mu cikin gagarumin firgici haÉ—i da tashin hankali mara musaltuwa. Kamar yadda kunnuwanku suka jiyo maku zancen Khadija daren jiya zanso ku fuskanci lamarin da kyau domin kawo sauki cikin zuciyarku, Lawan da Habiba har yanzu tinaninku na kan Azeezat ce wa tayi kai ka mata ciki wanda ko kaÉ—an ba haka take nufi ba,Kareem ne ya mata a faÉ—anta tayi amfani da kalmar Abi ne sabida takwaran shi ne"
"wannan kuma wata sabuwa ce? Haba Yaya ya zaka yadda da zancen wannan mara hankalin,au dama kan Kareem ta dawo to baki isa ba wannan daga ji karya ne ɗana Kareem bazai taɓa aikata sharrin da kike nufinsa da shi ba"
"kwarai kuwa wannan shirmen banza ne,zaki faÉ—a mana wanda ya miki ciki ko sai kin sha É—an karan duka"
Ummi ma ta ƙara nata.
"ku dakata,ba hayaniya ce ta tara mu ba ba kwa tinanin ihun da kuke mata zai kara harzukata? A hankali ya kamata ku bi idan kukayi la'akari da komai ya faru mukaddari ne"
"amma Yaya ya za'ayi a....."
"a'a Lawan ba yanzu ba ka bari mu dai-daita matsalar a hankali. Khadija faÉ—a min wa ya maki ciki?"
Ido duk a kanta yake ana sauraron amsarta Kareem ji yayi bugun zuciyarsa ya tsananta addua ya so ma karantowa dan kawar da shaidan tare da kudurtawa ba abinda zai samesa sai alkhairi.
"Ina jinki Azeezat faÉ—a min"
"Baba wai ni cikinnan naga a jikina yake to kuma mai damuwarku"
Bata ankara ba taji saukar duka,ganin Ummi ce ta fara kokarin ramawa Kareem ne ya mata wani kallo tuni taji Æ´aÆ´an cikinta na kaÉ—awa.
"Habiba jeki samu wuri ku bar komai a hanuna. Azeezat zaki faÉ—a ko sai na saka anyi maki shegiyar duka"
"mtsw Baba nace maku na Kareem ne kunki yadda to ya kuke so nayi"
"Indai hakane Abi aje asibiti a gwada mu ko kuma a kira malam Liman ya rantsar damu da kur'ani indai nina mata ciki la'antar Allah ta tabbata a kaina idan kuma nema na take da sharri Allah ya bi min hakkina"
"Hakan yayi dai-dai"
Inji Abi
Zaro ido Azeezat ta fara duk shashancinta ta san girman kur'ani. Kowa ya lura da rashin gaskiya tattare da ita.
"Ni fa bazaku É—aura min masifa ba, ba Kareem ne yamin ciki ba masoyina abun alfaharina ne ya mun kuma ko bayan raina zan yi alfahari domin shi na fara mallakawa jiki da zuciyata"
"Alhamdulillah Yaya ka gani ko,Khadija ki fitar min a gida bana so na kara ganin koda inuwarki ce kusa dani,ko mutuwa nayi ban yadda kizo kan gawata ba"
Cikin muryar kuka Abi ya faÉ—a. Rabon da suka Abi cikin wannan yanayi anjima shiyasa ba wanda yayi kokarin dakatar dashi.
"Allah na gode maka da ka cireni cikin wannan zargi"
Inji Kareem yana share hawayensa zuciyarsa cike da tausayin su Abi.
"sai mai? Yanzu ne nake tashe na bazai taɓa yuwa ka gurɓata min rayuwa ba kasani a person who's his age is above eighteen has a right to do what ever he want a, saboda haka babu abinda ya dameni idan ka mutu ina maka fatan alkhairi umma ta gaida aisha gidan ka kuma ko baka ce na bari ba zan bari. Kai kuma Kareem kake ko wa ba wai ka tsallake wannan tarkon ba na gaba na zuwa rijiya ce mai zurfi wanda na tabbata idan ka faɗa bazaka taɓa iya fitowa ba nikadai ke da damar cireka idan naga dama"
Ta karashe da Æ´ar dariya.
"Me zaki iya masa? Tir da irin wannnan rayuwa taki baki ne kaɗai bazan miki ba amma ki sani bazaki taɓa jin daɗin rayuwarki ba"
Sosai Ummi ke kuka yayinda take magana cike da É“acin rai.
"idan ke ce mai bada jin daÉ—in rayuwar ki hanani,nace ki hanani"
Inji Azeezat
Kokarin tashi Kareem ya so ma dan É—aukan mataki lura da hakanne yasa ta fice a guje haryanzu bata bar rashin kunyar ba.
Mai zai faru yayin da Abdul yaji labarin Azeezat da mahaifin shi take tarayya?
Ouh Mai Abdul yake shiryawa Kareem bayan idansa?
Ya Kudrat zaka kasance a gidan Alhaji Mamu?
Amsoshin na gaba ku dai kawai muje zuwa............
*COMMENT AND SHARE PLS*
Cute HapCyy ce😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike kunci haÉ—e da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
```Dedicated to my lyf Allah ya jikanka ya sa mutuwa ta zame maka hutu Abbanah```
Inawa Æ´an uwa musulmai barka da sallah tare da fatan Allah ya maimaita mana, Ameen.
*Gaisuwa ta ban girma ga ilahirin Æ´an KARAMCI WRITERS ASSOCIATION Allah ya daÉ—a haÉ—a kanmu baki É—aya kamar yadda muke tafiya cikin tsari da kaunar juna fatana shine mukasance a hakan har illa masha Allah,zanyi amfani da wannan page É—in na sadaukar muku shi as ur Happy SallahðŸ¤*
_Writers,readers,da masu tayani postings na novel nawa wanda na sani da akasin haka musammam ma MK ina godiya gareku fatan an gudanar da bikin sallah lafiya_
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ce wa "Duk wanda yamin salati É—aya Allah zai masa goma,wanda ya min goma Allah zai masa É—ari,wanda ya min É—ari Allah zai masa dubu,wanda ya min dubu kafaÉ—ata da tasa tare zamu zamu shiga aljanna. Allahumma salli wa sallim ala khatimul ambiya'i wa imamul mursalin sallallahu alaihi wa sallam. Ameeen
Page 13~14
____________📲Stations ta nufa Direct cikin rashin sa'a ta tarar da DPO baya nan.bata kulasu ba ta kusa hanyar da take tinanin zai sa da ta da office na DPO. Shawo gabanta yayi cikin hanzari yana tambayar
" lafiya zaki shiga ciki kai tsaye ba tare da an baki izini ba. ÆŠan karamin tsaki ta ja gami da ce wa
"ogan ka nake nema ba kai ba"
"oga kuma,kina nufin DPO?"
"Amm baiwar Allah wanne irin ƙara ne da lallai sai DPO zaki faɗawa"
ÆŠayan police É—in ya kuma jefo mata tambaya.
"nidai shi nake nema kuma zan iya jiransa ko zuwa gobe ne"
"Okay amma fa ki sani wallahi da kanki zakiyi nadamar jiran DPO gwara ma ki faɗa mana bazamu taɓa rasa hanyar taimako ba"
"tunda ka matsa bara na faɗa maka,ƙara na kawo inaso na shigar da wasu kotu ya zanyi"
"mtsw dan Allah Audu kaji kan É—an karamin case shine sai ta jira DPO kawo wani abu kafin mu cigaba da magana"
"ban fito da kuɗi ba yallaɓai amma na maka alkawarin indai nayi nasara zan baka kuɗinka"
"kinyi alkawari?"
"kwarai kuwa"
Ta amsa da sauri.
Bayanin yadda case É—in nata ta masa ya rubuta tare da cewa ta tafi kawai zai sanar da ita ranar shiga kotu. Cikin kwana biyu komai ya kankama. Abi da Ummi na kwanace basu jin daÉ—i haryanzu suka jiyo sallamar bako Kareem ne ya fito domin duba wanda ke sallama hannu ya fara mika masu sukayi sallama,wata Æ´ar takarda suka mika masa bai buÉ—e ba sai da ya shiga cikin gida.
"Kareem baki akayi ne"
"ae Abi amma sun tafi"
"Allah sa dai alkhairi ne,kai suke nema ko wa?"
Shiru Kareem yayi idansa na kan takardar tunaninsa bai wuce taya zai fara wa Abi bayanin sammaci ne daga kotu ba.
"É—ana kada ka É“oye mana abinda ke shirin faruwa,Allah ke tsara komai duk abinda ya faru da bawa idan yayi hakuri Allah zai musanya masa da alkhairinsa tare da basa ladan hakuri da juriya da yayi"
"Hakane Ummi,ba wai faÉ—a muku ne ban so ba sai dai gudun yadda zaku É—au al'amarin,dan Allah kada ku É—aga hankalinku indai kuna tare dani komai zai zo da sauki"
"in shaa Allah zamu kasance masu hakuri da duk abinda kunnuwanmu zasu jiyo mana"
Suka faÉ—a tare.
Numfashi ya sauke a hankali ya furta,
"sammaci ne daga koto"
Kallan juna Abi da Ummi sukayi cikin mamaki suka haÉ—e baki wurin ce wa
"SAMMACI!?"
Da karfi.
"Kwarai Abi amma in shaa Allah komai zaizo da sauki saboda wacce tayi ƙaran ba cikakken hankali ne da ita ba"
Yana faÉ—an hakan suka tabbatar da Azeezat ce, shiru sukayi ya cigaba da kwantar masu da hankali gudun kar rashin lafiyar su ta tashi.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Ta bangaren Kudrat kuwa cikin ƙunci da tashin hankali tsantsa take batada aikin yi banda kuka gami da bakin cikin sharrin da Azeezat ta mata,ta wani ɓangaren kuwa harda haushin kanta na amincewa da laifin da ba nata ba da tayi. Jugum tayi a kan stool dake ɗakinta tinanin duniya duk ya isheta ringing na wayarta ne ya dawo da ita cikin hayyacinta da gaggawa ta ɗauka sanin mai kiran baya mata da wasa.
"Coffe"
Ya faÉ—a tare da hanging na calling É—in,fushin da take bai hanata yiwa wayar gwalo tare da murguda masa baki ba kamar yana kallanta.
Kamar kullum a tsakiyar gado yake yana aiki da system nasa ita kuma ta rungumesa ta baya sai narke masa take a jiki, kallo É—aya na masa tare da É—auke kaina zuciyata na tsananta bugu, bance komai ba na ajiye cup É—in a site drower na juya zan tafi muryarshi ce ta katse min hanzari na tsaya domin sauraran cewarsa.
"bakiga mu biyu bane zaki wani kawo guda É—aya"
Zanyi magana naji tana ce wa
"a'a ni bazansha abin hannun kazamar nan ba kaima da kake sha ina tausaya maka ranar da ciwon ciki zai sarke ka"
Ban kara tankawa ba na juya zan wuce zuciyata na kara jin tsanar Billy fiye da yadda take ƙyamatata.
"owk,jeki wanke min toilet as usual"
Ya kuma faÉ—a a gadarance.
Hawaye na bin kuncina na wuce ban É“ata lokaci ba na fito.
"har kin gama?wannan wani irin wanki kikayi"
Shiru nayi kamar yadda na saba na rasa dalilin da yasa Ammar ke takura min musamman idan yana tare da Billy.
"mtsw malama wuce dan Allah bana kaunar haÉ—a inuwa da ke idan ba son kai kai inda mutum bai kai ba ina ke ina Ammar?yarinya naga take-taken ki gwara ma kicire rai dan Ammar ba sa'an auran irin ki bane"
Inji Billy
Nida duk hankalina a tashe yake burina bai wuce na fice a É—akin ba,ban damu da zancen Billy ba inda sabo na saba saka kai nayi na fice da sauri inajin shi ya furzar da iska a bakinsa gami na dukan katifar tashi.
Akan gado na faɗa ina sauke numfashi sama-sama a hankali har nutsuwata ta gama dawowa jikina ji nayi bacci na naiman ɗaukana ban bari ba na tashi cikin gaggawa na buga kararrawar aiki take sauran ma'aikatan suka fito muka wuce kitchen haɗa abincin rana cikin mintuna kalilan muka gama na ɗauki na Alhaji domin kai masa duk da zuciyata bata kaunar shiga ɗakin Alhaji amma babu yadda na iya,ɓata rai nayi ba tare dana buɗe baki sosai ba nayi sallama dai-dai fitowarshi a toilet ɗaure da towel a kugunsa sai karamin wanda yayi ɗan kwali dashi,da sauri na ɗauke kai har ina tuntuɓe na ajiye zan koma.
"Kudrat!"
Naji ya ambaci sunana da karfi. Ba tare dana juya ba na tsaya lokacin hankalina ya matukar tashi zuciyata kuwa bugun tara-tara take.
"Haba Kudrat ke daga kin shigo É—akina sam ba kya son zama sai kace cizonki nake"
Banyi magana ba sai ma tsanar shi dana ke ji na karuwa a zuciyata.
Murmushi yayi ya ce
"yanzu dai ba wannan ba tahu ki shafa min magani a baya na,kijini nan Kudrat ba wasa nake ba idan kika sake yau kika gudu wallahi sai na saka an kashe iyayenki kuma an kashe banza dan haka tun muna mu biyu kizo kiyi abunda na sa ki"
Kuka ne ya kufce min na rasa mai zanyi gashi bana tinanin zan iya juyuwa na kalli Alhaji a yanayin da yake ciki bare har ta kaiga shafa masa abu a baya.
"babu abinda kuka zai miki sai ma É“ata miki lokaci zan kirga uku idan har baki juyo ba taki ta kare. ÆŠaya,biyu,uk..."
Kofar É—akin aka buÉ—e hakan ne yasa bai karasa kirgawa ba cikin e'ena ya ce
"waye wannan zai shigo..."
"haba Abba,yanzo ya dace ka tsaya a gaban yarinya da É—an karamin towel? Ya Rabbi! Kudrat jeki É—akinki maza"
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke da gudu nayi ɗakina ina kara godewa Allah da kuma Mahfuz,da wannan sau biyu yake kuɓutar dani a hanun Abbansa. Da tinanin yadda zan karashe shekara ɗaya cikin kalubalen gidan Alhaji Mamu bacci yayi gaba dani.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Kotu cike yake da mutane makil kowa na tufe Azeezat da kalmar Allah ya tsine,yayinda ita kuma fuskarta ko kaÉ—an bata nuna alamun nadama ko bakin ciki ba. Shigowar alkali ta sanya kowa kame bakinsa,bayan an gabatar da addu'a kamar yadda aka saba registre ya mike ya fara karanta case É—in kamar haka
"yau talata 4/8/2020,zamu saurari ƙarar Azeezat inda ta ke ce wa iyayenta sun koreta a gida ba tare da ta musu komai ba tana bukatar kotu ta bi mata hakkinta. Mikawa alkali takardar yayi ya ko ma ya zauna. Suruce-suruce jama'a suka fara alkali yayi umarni da ayi shiru.
kallon paper yake ba tare da ya ce komai ba. Bayannan ya É—anyi rubuce-rubuce kana ya ce
"ina lawyer mai ƙara?".
James ya mike tsaye ya ce "ya mai girma mai shari'a sunana James David nine lauyan mai ƙara.
Alkali ya ƙara ce wa,"shin wanda ake kara yanada lawyer?"
Abi da Ummi kansu a sunkuye kunya da bakin ciki sun gama lulluɓesu. Kareem ne ya ce,
"Bamu da shi kuma bama bukata ya mai girma mai shari'a"
"Shin kunji abinda ake karar ku akai?"
Kareem ne ya mike ya ce "ya mai girma mai shari'a dattijan nan basu da cikakken lafiyar da zasu iya kare kansu akan ƙarar da wannan shashashar ƴar tasu take dan haka nake so kotu ta bani dama na tsaya a maimakon su.
Jinjina kai alkali yayi shi kanshi yana mamakin wacce iriyar Æ´a ce da zata shigar da iyayenta kotu. "kotu ta baka dama"
Bayan ya tsaya a inda aka tanadar wa mai kara da wanda yake ƙara alkali ya kuma tambayarsa
"mai zaka iya ce wa gami da ƙarar da ake tuhumar iyayenka?"
Ido ya tsurawa Azeezat yana mai bakin ciki da nadamar haÉ—a jini da ita ya ce
"ya mai girma mai shari'a wannan karar bata da asali bare tushe tabbas iyayen Azeezat sun koreta a gida amma bisa hujjuji ƙwarara,Azeezat bata da wani buri wanda ya wuce ta sanya iyayenta cikin kunci da bakin ciki,rashin kunya da fitsara babu wanda bata yi har ta kai ga tayi cikin shege kawai dan ta bakantawa iyayenta bata tsaya anan ba tace mahaifinta ne ya mata cikin wannan shine silar kamuwa da hawan jinin iyayenta har yanzu suna karɓar magani,duk wani bayani da zan maka bazai taɓa zayyanu maka munin hallayar Azeezat ba,ta wuce yadda ake zato idan shaida kake nema ga ƴan unguwa sun isa su kara gamsar da kai,ya mai girma mai shari'a inaso wannan kotu mai adalci ta kwantanta adalcinta tayi watsi da wannan ƙarar domin bata da amfani"
"Ayi shiru! Alkali ya faÉ—a surutan sun fara yawa bayan an nutsu ya ce
"shin lauyan mai ƙara yanada ja akan abinda wanda ake ƙara ya faɗa?"
Mikewa tsaye James David yayi ya ce
"ya mai girma mai shari'a banida ja akan abunda ya ce domin a iya binciken da nayi na gano ce wa Azeezat ba mutuniyar kirki ba ce dan haka nima ina mai goyon bayan ayi watsi da wannan ƙarar tare da mata hukunci mai tsanani dan ya zama izina ga ƴan baya"
Ajiyar zuciya Kareem ya sauke ya ji daɗin zancen James David. Zare-zaren ido Azeezat ta so ma gami da nadamar shigar da ƙarannan. Lura tayi hankalin jama'a ba a kanta yake ba ko wa na jajantawa su Abi,hanya ta saita ta fice a guje kafin ayi auni ta yi nisa,biyota polices sukayi kafin su cin mata ta haye adai-daita basu karaya ba suka ko ma ɗauko mota sai dai kash bazasu iya tantance kalar Napep ɗin ba. Hakuri Abi ya basu ya ce a barta duniya ƙaɗai ta isa ta isar mata.
Bayan ta isa gidan Abdul ta basa labarin abinda ya faru. Ya ce "wannan labarin bata min daÉ—i ba amma abinda nake so da ke yanzu shine mu bar batun su Abi, da Kareem zamu fara"
"Kareem kuma dama kunsan juna ne? Amma meke tsakaninku haka? Ina nufin mai ya maka kake son ganin bayansa?"
Cikin rashin fahimta ta tambaya.
"wannan labari ne mai tsawo zan baki bayan kin cika min aiki na,kuma ki sani rashin cika aikinnan dai-dai yake da fasa auranki"
"shikenan Abdul,indai Kareem ne kamar an shafe labarinsa akan ka ba abinda bazan iya ba"
Smilling yayi ya janyota jikinsa yana shafan bayanta a hankali yana raÉ—a mata yadda zasu É“ullowa Kareem.
Tafiyar zata fi daɗi idan kuka cigaba da COMMENTS domin shike karan ƙarfin gwiwa.muje zuwa guyz
*Comment*
*Vote*
*Share*
Cute HapCyyy ce😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haÉ—e da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*Infuse your life with action. Don't wait for it to happen. Make it happen. Make your own future. Make your own hope. Make your own love. And whatever your beliefs, honor your creator, not by passively waiting for grace to come down from upon high, but by doing what you can to make grace happen... yourself, right now, right down here on Earth.*
Page 15~16
__________📲 Bugun kofar yake sosai bubu kakkautawa,bai yi gaggawar buɗewa ba dan sanin Kareem ne sai da Azeezat ta ɓoye kafin ya buɗe masa. Zubewa yayi kan kujera tare da dafe kansa da hannu bibbiyu bayan ya shigo.
Kallansa yayi cike da tsana a cikin zuciya yayinda yake nuna tsantsar kauna a fuska, murmushi yayi kasa-kasa wanda ba kowa ne zai lura da murmushin ba ya ce
"ba haka na saba ganin fuskarka ba abokina"
"hummm bazaka taɓa ganewa ba abdul dole ce ta sanya na saɓa fuskar da ba tawa ba"
"meyasa bazan gane ba indai kayi min yadda zan fahimta,ka manta yanzu fa matsalarka ta wa ce ko dan kaga taka matsalar ta gushe"
"ko kusa,kawai ina jimami game da rayuwar Azeezat ne,na rasa meke damunta ina kokonto anya lafiyarta kuwa?"
"ikon Allah! Me kuma ta sake yi kai wannan yarinya ba Æ´ar arziki bace sai kace É—iyar Allah ba mu"
"hmm kai ma dai ka faÉ—a,wanne irin tsantsar jahilci ne zai sanya yaro ya shigar iyayensa kotu, Kai subhanallah"
"innalillahi! Har rashin É—a'ar tata ta kai ta kai iyayenta kotu? Tir da irin wannan haihuwar Allah ya shireyeta"
"Amin indai mai shiryuwa ce ba,yanzu dai ba wannan ba Alhaji DAGASH ya nemi na kawo masa takarduna"
Ya faÉ—a yana murmushi.
"na shiga uku,Alhaji Dagash É—in dana ke ji ana maganarsa a gari? A rai ya faÉ—a a zahiri kuma ya ce
"You mean DAGASH INDUSTRIES LIMITED wow i'm morethan happy abokina"
"Nagode! Sai dai wani hanzari ba gudu ba Alhaji Dagash baya É—aukar ma'aikata indai ba É—an local government nasa ba, shin ya kake ganin ya kamata ayi tunda karamar hukumar mu ta banbanta"
"Idan baka faÉ—a masa ba taya zai sani"
"Sha'anin amana Abdul,ya yadda dani sosai bai kamata na ki faÉ—a masa ba a tunani na gwara na faÉ—a idan zai iya É—auka na a haka fine"
"Kul Kareem, shekara nawa muna zaune babu aiki dare É—aya Allah ya kawo shine kake so ka mana bakin ciki"
"ba haka bane Abdul ina....."
"Look abokina wannan fa damace da samemu ba kai kaÉ—ai ba har ni,bai kamata muyi wasa da ita ba, Alhaji ya amince da kai sosai wanda na tabbata bazai wani bincike ba, ka manta sadaukar da rai da kayi a baya sabida shi? Ai wannan ma kaÉ—ai ya isa"
"Hakane kuma ta wani bangaren"
"Gaskiya time É—in Kareem nayi matukar mamakinka abun kuma ya....."
"please Abdul bana so ka daina tuna min wannan muyi focusing kan presents ba past tense ba"
"As you said,but karka soma tinanin faÉ—awa Alhaji ainihin local goverment naka"
Jim yayi yana nazarin zancen Abdul daga bisani ya yanke shawarar kai takardun ba tare daya faÉ—a ma Alhaji Dagash ba. Ajiyar zuciya ya sauke tare da É—aura hanunsa a kafaÉ—ar Abdul ya É—an murzawa sannan ya ce
"zanyi yadda kace abokina,Allah ya bar kauna nagode da kulawarka"
Murmushin shima ya mayar masa ba tare daya tanka ba, haramar tafiya Kareem yayi har bakin kofa ya rakasa sai da ya tabbatar ya ɓace masa da gani kafin ya sanya kwaɗo ya kulle gidan. Zubewa yayi akan kujera kanshi ya ɗau zafi zuciyarshi na ƙona tsabar baƙin ciki,a wannan lokacin yadda yake ji da za'a bashi damar ɗaukan rai mutum tabbas na Kareem zai bayar saboda duk duniya babu wanda yafi tsana kamar Kareem yana zama dashi ne dan ribar kansa sai kuma plan ɗin da yake shirya masa.
"ina raye! Da rai da lafiya a tare da ni! Bazan taɓa bari Kareem yayi rayuwar farin ciki ba.... Ina ma ace kaii! Ya Allah meyasa ka zaɓe shi a kaina,ya Allah meyasa ka daga martabansa fiye da ni alhaline ni na cancanci hakan, ya Allah..."
Kasa cigaba da sambatun yayi saboda kukar dayaci karfinsa,zuciyarsa bugu take tamkar ana daka. Kamar daga nesa take jiyo kuka a firgice ta fito tana tambayarsa
"Abdul meyafaru? Dan Allah faÉ—amin meyasa kake kuka kodai Kareem ne ya É“ata maka rai"
Tana maganar tana share masa hawaye batayi auni ba taji ya tureta da iya karfinsa. Sosai ta buge kafarta bata damu da ciwon da taji ba ta kara isa inda yake. Wani kallo ya mata wanda yasa Æ´aÆ´an cikinta kaÉ—awa hanyar É—aki ya nuna mata babu musu ta wuce tana shekar kuka.
Da kyar bacci É“arawo ya saci Abdul da sake-sake a ransa itama haka.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Skiy blue shadda ce dakakkiya yasha aiki irinta manya jikinsa,kalar ta fito da cikakkiyar kamalarsa ya kuma ƙara haske chocolate colour ɗin fatarsa,farin cikin daya bayyana a fuskarsa ba zai hana gane ɗan karamin damuwa da ke makale a fuskarsa ba. Jingina kai yayi jikin kofa yana mai kallan Ummi dake cin abinci hankali kwance yayinda Abi ke kwance kan cinyarta jifa-jifa tana saka masa a baki hakanne ya tabbatar masa da sun fara manta damuwarsu. Ɗago kai tayi ta gansa tsaye,sakar masa murushi tayi ya mayar mata ba tare da sun ce komai ba.
"a'a É—ana yaushe ka fito"
"yanzun nan fitowata Abi"
"to yanzu kuma sai ina"
Ummi ta É—aura.
"amm a takaice dai zan iya ce wa na samu aiki a wani kamfani dama so nake sai komai ya kankama kafin na faÉ—a muku,to alhamdulillah komai ya shiga hanya sai dai ku tayamu da addu'a"
Ya karashe maganar tare da sosa keya.
"masha Allah, wannan abu ne mai kyau Allah ya dafa maka É—ana"
"Amin Abi"
"Sai kuma ayi riko da amana da gaskiya kaji duk dana tabbata baza ka taɓa bamu kunya ba"
"in shaa Allah zan kasance É—an da zakuyi alfahari da shi Abi"
"Yawwa É—an albarka,mijina na kaina babu zancen kishiya Æ´ar sa ido bare nayi arba da tashin hankali"
"af kika san ma ko wurin surukar zashi ya ci ado haka,ke dai kawai kiyi hakuri kin tsufa"
Dariya sukayi gaba ɗaya banda Ummi da ke cin magani sai zumɓora baki take abin dariya ga wanda ya gani.
"Haba Amaryata ke kaÉ—ai ce dani tsaleliyar budurwa babu wacce zatayi takara dake"
Ya faÉ—a yana kokarin barin gidan sanin idan ta cafkusa kayansa ya tashi a aiki.
Cuo ta wurga masa sai dai bai samesa ba,dariya Abi yake mata sosai. Gefe tayi tana bubbuga kafarta tamkar jaririya,janyota jikinsa yayi yana rarrashinta sai ruwan shagwaɓa take zuba masa.
Lolz niko nace tsufi yau an tuno da tsuhuwar kauna.
Bai bata lokaci ba ya isa industry kasancewar an san da zuwansa bai sha wahalar ganin MD ba, walima ta musamman akayi tare da shaidawa ko wa sabon accaunter wato Kareem. Ba a misalta farin ciki wurinsa ya manta da duk wata damuwa. Haka ya cigaba da aikinsa cikin jin daÉ—i da kwanciyar hankali.
Ta ɓangaren Abdul kuwa tun dayaji labarin upper ɗin Kareem yake kulle da baƙin ciki,yaci alwashin zubarda martaban Kareem ta har abada.
*SOME DAYS LATER*
Kallo É—aya zaka masa ka gane aiki mai muhimmanci yake domin duk wata nutsuwarsa na kan system É—in,É—ago kai da zaiyi yaga mutum tsaye a kansa har sai daya tsorata. Numfashi yaja lokacin dayaga Abdul ne.
"ka bani tsoro fa abokina,zauna mana"
Ya nuna masa kujerar dake opposite da tasa yana mai murmushi.
"Tsoro kuma,da sauri haka"
Fuskarsa babu yabo ba fallasa yayi maganar.
"banji shigowarka ba ai,yanzu dai ya kake akwai wata matsala ce"
"to! Sai akwai matsala zanzo wurinka? Abokina aikinnan yana so ya canza ka fa"
"Ba wai haka bane kasan sha'ani....."
Bai karasa ba wayarsa ta fara neman agaji,É—aukar kiran yayi cikin hanzari.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna daga nan ya ce
"Ae ga kundin nan yana tare dani,sai dai akwai wanda za'a karɓo a bank yanzu ma kokarin tashi nake naje na ɗauko"
Abinda aka faÉ—a ta É—ayan É“angarenne ya daÉ—aÉ—a masa,murmushi yayi ya furta
"Amin nagode yallaɓai"
Abdul daya kura mishi ido ko kiftawa bayayi har sai da Kareem ya É—age masa gira. Baiyi magana ba ya kauda dubansa wani gefe.
"kasan me ne abokina,wasu kundi zanje ɗauƙowa a Bank ko zamu tafi tare ne"
Janyo file din Abdul yayi ya ce
"Wannan fa?"
"tab wannan idan basu babu ni,tare da su zamu tafi"
Tare suka wuce Bank É—in ya jirasa har sai da ya gama uzurinsa daga nan ya ce shima ya rakasa wani wuri,bai masa musu ba cikin mintuna kalilan suka isa.
"Abdul me zakayi anan kuma"
Ya tambaya a razane ganin inda Abdul ya nufo dasu dama shi ke driving.
"Dan Allah,dan kaunarka ga fiyayyen halitta,da darajar iyayenka karka hanani"
Abdul da idan sa ya gama rinewa ya faÉ—a.
"Shikenan naji,amma karka sha dayawa dan Allah"
"Nagode"
Ya faÉ—a tare da ficewa a motar. Jingina kai yayi jikin sitiyarin motar yana nazari tare da bakin cikin halinda abokinsa ya sinci kansa,yana matukar tausaya masa har cikin rai. Ganin wata yarinya wanda shekarunta bazasu É—ara goma ba yayi tana gudu ga kartin samari na binta,da gudu shima yayi kansu sunyi nisa sosai kafin ya cin musu,ganin Kareem yasa su nemar hanya bai damu da su ba burinshi ya tseratar da ita ba. Tambayarta ya so ma ta faÉ—a masa inda take,sai da ya fara shiga gidan da Kareem ya shiga ya É—auko sa lokacin hankalinsa ma baya jikinsa,fara sauketa yayi kafin ya kai Abdul ma ya bugu da giya ko sanin inda yake baiyi ba.
Shida da rabi na dare Alhaji Dagash ya kira Kareem kan ya kawo takardun koda ya duba babu su babu alamarsu. Iya tashin hankali ya shiga baya tinanin Abdul ne saboda lokacin a buge yake.
"Amma aina na zubar da muhimman takardunnan? Abdul....? Kai bashi bane bayida masaniya kan É“atan su, kodai aljanu ne suka É—auke? Daga ni babu kowa a motar. Wancan yarinyar ce...? Ina gani ta sauka hanunta babu komai."
Shiru yayi ya ma rasa abin faÉ—a,addu'ar Allah ya bayyana masa kawai yayi ya barwa Allah komai.
Waya ya ciro ganin misscals na bakon number yayi,bai damu daya kira ba dan ba cikin hayyacinsa yake ba sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya da numbar. Yana cikin kallon screen É—in wayar kira ta sake shigowa,É—auka yayi bai ce komai ba ya tsaya sauraron wanda zai fara magana.
"MuhaÉ—u a GSM Qurters da misalin karfe tara"
DaddaÉ—an muryarta ta matukar sanyaya masa zuciya. Ganin bashida ta ce wa ta katse wayarta. Bai tsaya jiran tara ba ya É—auki hanyar GCM,tara dai-dai ya hango fitowarta daga gate É—in Qurters É—in nasu,sanye take da dogowar hijabi har kasa sai nikab daya rufe fuskarta. Mika masa tayi bayan ta isa ta ce
"Gashi,ina tunanin naka ne a kasa na tsinta"
Kamar bashida jini jiki a sanyaye ya karba tare da furta "nagode"
"Mu shiga ka sha ruwa daga nan ku gaisa da Mama"
Tsintar kansa yayi da son kasancewa da ita ko dan ya dinga jin muryarta mai daÉ—in gaske,bashida wani buri wanda ya wuce mararin ganin fuskarta. Yana biye da ita har suka kai parlon gidan sai dai baiga alamun akwai mutum a gidan ba. Bottle water ta kawo masa yasha bayan É—an mintuna ya ce
"Ina mamar take"
Sunkuyar da kai tayi,ta marairice murya kafin ta ce
"Mama basa nan,indai ba hakan na faɗa maka ba nasan bazaka biyoni ba,kayi hakuri na maka ƙarya"
"Amma ina suka tafi babban gida haka ke kaÉ—ai ke rayuwa a ciki ba kya tsoro?"
Kuka ne ya kufce mata,ya fuskanci tambayar bai mata daÉ—i ba duk yadda akayi akwai abinda ya faru da mahaifanta. Ajiye cup É—in ruwan yayi dai-dai bakin kofa ya tsaya ya ce
"nagode da wannan taimakon bazan taɓa mantawa da ke ba,kiyi hakuri bansan tambayar zai ɓata miki rai har haka ba sunana Kareem idan kina son ganina ga address ɗina"
Ya mika mata card É—in.
"nayi farin cikin haɗuwa da kai, sai dai bana zuwa wurin namiji ko na karɓi card naka bazai amfaneni ba, ina maka fatan alkhairi sunana Kareema"
Juyowa yayi da sauri yayindayaji ta amɓaci sunanta,hakika Allah shi ke haɗa komai a duk lokacin daya so ya faɗa a rai.
Yaye nikab É—in tayi suka fuskanci juna,kallanta yake cike da so da kauna lokaci É—aya yaji ta kwanta masa a rai. Gefe yayi da kai ya ce
"na barki lafiya malama Kareema"
Tsalle ta daga gami da ce wa
"oh yes!!!"
Da alama tarkona ya naÉ—esa.
Ganin lokacin zuwar mijinta yayi ta tattaro nutsuwa tare da É—an gyare gidan,tana cikin yi taji ana fi to akanta wannan jarabar ta zame masa jiki baya sallama sai dai fi to. Zubewa tayi kasa cikin tsoro ta ce
"Sannu da zuwa ƴallaɓai"
"Mtsww haka ake gaida miji a gidanku? Wai yaushe zaki waye ne koda yake laifin iyayenki ne maza karɓi jakarnan ki kai ɗaki"
Jikinta na ɓari ta mike ta karɓa ya bi bayanta da harara.
"Kareema! Kareema! Kareema!..."
Share hawayenta tayi ta fito da sauri.
"yi hakuri ƴallaɓai, na fito maka da kayan sawa ne"
"da kika fito da kayan sawan ba wanka haka zan saɓa ne?"
"ƴallaɓai nariga na haɗa maka ruwan wankan ma"
A tsorace take maganar.
"jeki sai na neme ki karki kuskura ki fito"
Kamar jira take ya ce ta wuce da sauri tayi É—akinta tana goge hawayen dake gangarowa kan fuskarta. Akan gado ta baje kolin tinanin Kareem tanayi tana share hawaye,
"ban taɓa tinanin shiga irin wannan hali ba,hakika Kareem ka tafi ka barni cikin yanayi mara misaltuwa....oh! Allah na mai nake yi ne,Kareem ba komai bane a wurina banda....,hummm amma fa zuciyata ka kamu da kaunars...Ya Allah Kareema mai kike yi haka ki dawo hayyacinki.
Ta fada tana dukan kanta.
*~~~~~~~~~~~~*
Sai da ya fara biyawa ta gidan Abdul a tsatsaye suka gaisa Kareem ya ciro dubu goma ya basa ya ɗanyi kwana biyu kasancewar ba aiki yake ba,sosai ya masa godiya ya sanya masa albarka. Tafiya yake amma hankalinsa na kan Kareema rana ɗaya amma tinaninta ya dabaibaya jinin jikinsa ba iya ƙwaƙwalwa ba, a backyard ya tarar da su Abi hankalinsu a tashe ganin kusan sha ɗaya bai zo ba kiran waya yafi a kirga bai amsa ba.
"haba Kareem ina ka tsaya haka,duk hankulanmu ya tashi gashi baka amsar kira"
Zubewa yayi akan tabarma ya zare gilas din idansa ya ce
"wash Allah na gaji sosai Ummi, ko zauna mana ba wata matsala aiki ne ya min waya"
"wanne irin aiki kuma aina?"
"a office mana Abi"
"shine kuma DAGASH ya zo naimanka har gida? Kuma ya ce baka office É—in kiran duniya ya maka baka amsa ba?"
"Dagash kuma Abi? Wai gidannan ya zo?, ina zuwa Ummi"
Ya shiga É—akinsa da sauri,wayar sa ya ciro a cikin aljihu ya kunna misscal ya gani dayawa na Alhaji Dagash. Cikin sauri ya danna kira bugu É—aya ya É—auka hakanne ya tabbatar masa da Alhaji na nemansa ugently.
"haba Kareem haka amana ta ce sanin kanka ne ana bukatar kundinnan yau da karfe tara,tun yaushe nake kiranka amma no response meyasa ka min haka? Buɗe kunnuwanka kaji bazan taɓa lamuntan irin wannan shashancin ba bazaka ɓata min aikin da na daɗe ina ci dashi ba"
Cikin tsananin É“acin rai Alhaji ke magana.
"ba haka bane....."
"Dakata! Ina jiranka kayi maza ka kawo min yanzu sannan ka biya ta atm zan tura maka amount É—in da zaka cire via message"
"amma Alhaji ɗauƙo kuɗi a wannan lokaci nada matukar haɗari"
"kai ka santa,uban wa ya saka ka É“ata lokaci,da kasan asarar daka janyo min baza ka soma faÉ—an haka ba"
"Amma Alhaji...."
Kit,ya datse kiran,dafe kai Kareem yayi yana tinanin abinda ya dace yayi.
Wani É—an matashi ne kusa da Alhaji Dagash lokacin da yake waya,jin Kareem zai fito da wannan kundin take yayi gefe ya danna kira a hankali ya ce
"Kareem zai fito da file ɗin yanzu,kuma zai biya ta bank ya ciro kuɗi make sure a shirye kuke kada ku taɓa lafiyarsa amma ku tabbatar kun raba sa da file ɗin da kuma kuɗin.
Hanging yayi da sauri jin ana kiransa.
"ina zuwa kuma cikin darennan? Kareem ka barmu cikin duhu fa maike faruwa ne?"
Murmushi ya kirkiro ya ce
"b...ba..ba komai Abi,É“arayi ne suka yiwa Alhaji sata so ana bukata ta a office yanzu"
"yanzu!"
Suka faÉ—a a tare.
"Kwarai Ummi, karku damu in shaa Allah zan dawo nan bada jimawa ba"
Ficewa yayi cikin gaggawa kawo yanzu zuciyarsa babu tsoro ko fargaba Allah kaÉ—ai ya sanya a rai.
Dai-dai fidelity bank dake hanyar living things ya hango wasu karti hanunsu É—auke da manyan makamai, sai hura ta ba suke,parking yayi wurin parking space ya kashe mutar,rintse ido yayi ya karanto addu'oi ya shafa tare da fara kokarin buÉ—e kofar motar.
Comments after read pls coz comments are HO²
0 comments:
Post a Comment