"Kawo kuɗinnan ko ka rasa ranka."
Tsayawa yayi cak ba tare daya tanka ba.
"baka ji mai nake ce wa bane,tun kan jikinka ya gaya maka kayi abinda nace."
"ku kuma ta inda kuke cin abinci kenan? Allah ne kaɗai ya san adadin mutanen da kuka salwantar da rayuwarsu akan hakan kafinni bana nufin tsayar da ku sai dai ga wata tsaraba Allah yana ce wa....,
_"man katala nafsan bi gairi nafsin fa ka'anna ma katalan nasa jami'a_
Ba kwa tinanin Allah zai kamaku ranar da bakuda karfi ko damar kuɓuta daga azaba,ina mai wa'azantarku da tun wuri ku tuba kafin lokaci ya kure muku."
"Har kai zaka faɗa mana abinda ya dace damu ko rayuwarmu?."
"kwarai ya dace na faɗa muku a matsayina na musulmi ɗan uwanku mai son ku da alkhairi,ko da ban sani ba oganku ne ya saka ku biyoni yayinda yanzu haka yana can kwance cikin ɗakinsa yana sharar bacci,ku kuma ga ku ido biyu kuna masa farauta,abinda zaku samu ku kai masa na tabbata kason da zai baku bazai taka kara ya karya ba ko wannan kaɗai bai ishe ku tinani ba? Bana tsoro ko fargaban mutuwa saboda rai na a hanun Allah yake idan har kunga na mutu a hanunku bakune kuka kashe ni ba Allah ne yayi sanadina tana gareku."
Jikinsu ne yayi sanyi cikin su babu mai iya ƙwa'kwaran motsi,babban cikinsu ne yayi karfin halin ce wa
"Nayi mamaki kwarai da zantukanka suka taɓa min zuciya,ban taɓa niyyar cin ma aiki na fasa ba sai a kanka kuma nayi alkawarin daina ta'addanci na har abada,sai dai ina maka tuni da ce wa ka kula da waɗanda suke tare da kai musamman abokanka domin sune makasudin zuwanmu nan sannan kada kaga ka tsallake wannan tarkon kayi tunanin ka tsira,gabanka babban rami ne dayake kunshe da abubuwan tsoro da firgitarwa. Mu wuce gayu"
Ya faɗa tare da tsallake kwalta.
Kallansa yayi cike da mamakin maganganunsa ganin lokaci na kure masa ya kauda tinanin ya shege motarsa.
Bai ɓata lokaci ba ya kai masa sai dai Alhaji Dagash bai wani nuna jin daɗi ko farin ciki game da hakan ba,rai a ɓace ya ce
"Jeka kada kazo wurin aiki sai na nemeka"
Dago kai yayi cike da mamakin furucinsa.
"Amma Alhaji..."
Dakatar dashi yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. Bai kuma ce wa komai ba hawaye na bin fuskarsa ya basa waje.
Da safe ya faɗawa su Ummi abinda ya faru,hakuri suka basa gami da karfafa masa guiwar ce wa da yardar Allah zai samu aikin dayafi wannan, jarrabta ce ta Ubangiji.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Fuskarsa ɗauke da farin ciki fal ya fito daga cikin ɗaki hanunsa ɗauke da tea cup,kiss ya manna mata a goshi.
"I love you Zezaty,duk da aikin bai tafi yadda muka tsara ba,hakan ma yayi an sallame sa a aiki"
"Wow! Amma fa naji daɗin wannan labarin Abdul,to yanzu sai yaushe za a ɗaura mana auran?"
Ɗan ɓata rai yayi
"matsala ta da ke kenan zancen aure da baya karewa,aina aka taɓayin aure bayan mace nada juna?"
Kallan cikin ta daya ɗan taso tayi ta kara maida ɗubanta ga Abdul,
"Mtsw,dan Allah Abdul muje a zubda cikinnan nifa na kagu muyu aure "
"Kai Azeeza wai gaggawar me kike? Wani abu ne wanda miji ke wa mata kika gaza samu a wurina? Jarabar ki ta fara isa na gaskiya bana tinanin akwai...."
"stop that Abdul kullum fa zancen dake fitowa a bakinka kenan,amma ai kasan duk abinda muke aikatawa Allah baya..."
"o, ke yanzu kinada bakin faɗawa mutum abunda Allah ke so da saɓanin hakan, ke da iyayenki ke kukawa da ke?"
"au gori zakamin? Idan ma hakanne ai dan kai nake."
"nidai yanzu bari tashi muje ɗaki ina bukatarki"
Kafin tace komai ya ɗaga ta, a toilet ya direta sun ɓata mintuna masu yawa kafin ya fito da ita ɗauke a hanunsa ya kwantar da ita kan bed tare da rufe ta da blanket.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
"Abi,nifa hankalina bai gama kwanciya da zuwan Kudrat aiki ba,anya ma Azeezat ba sharri tayi mata ba duba da abubuwan da suka faru bayan lokacin?"
"Gaskiya kam,nima nayi tinanin hakan"
Ummi ta ɗaura.
Numfashi Abi ya sauke kafin ya ce
"ko ma dai menene,nariga na yanke hukunci idan ta gama biya na yarje mata ta dawo ta cigaba da zama a gida."
"Allah ya kaimu lokacin"
Ya faɗa amma kawo yanzu yanada tabbacin sharrin Azeezat ce,Sai dai mahaifan nata haryanzu zuciyarsu bata huce ba.
Suna taɓa hira suka jiyo sallamar Abdul,da saurin shi ya fito tare da masa iso zuwa cikin gida.
"a'a Abdulkareemu sai kace bako zaka tsaya a bakin kofa"
Kai a sunkuye ya ce
"Kuna lafiya Abi?"
"Lafiya kalau ɗana kaki mu ko kazo sai dai muji labari"
Bai yi magana ba sai gyara zama da yayi.
"ai ku dai nima fushi nake dashi,sai wani sunkuyar da kai kake ka saki jiki nan ma gidanku ne."
"Ummi ayi hakuri abubune suka ɗanyi zafi "
"Allah ya dai-daita,ya wurin shi Baban naka?."
"haba Abi,kafi ko wa sanin halinsa idan ba wani ikon Allah ba bazai canzu ba Allah dai ya kyauta."
Abdul da hawaye har sun fara bin kuncinsa ya furta
"Amin",a hankali.
"Abokina kana min kokari nasani har kunyar tambayarka nake amma kuma ba yadda na iya ya zama dole"
Abdul ya faɗa bayan sun keɓence.
"karka ji komai ka tambaya indai baifi karfina ba bazan gaza ba."
"dan Allah so nake ka ranta min dubu hamsin idan na samu zan mayar maka."
Murmushi Kareem yayi,ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauko credit card nasa suka wuce bank,dubu ɗari. Ya ciro "Kyauta na baka Abdul,banida ɗan uwa daya wuce kai idan baka ci nawa ba wa zai ci?."
"Allah ya bani abinda zan saka mak Kareem duk da bazan iya ba."
Tissue yasa ya goge masa guntun hawayen ba tare da ya ce wani abu ba.
Kiran wayar Kareema ce ta shigi dama kuwa yana matukar bukatarta,bai ɗaga ba bayan ya yanke sai ya kirata.
Sautin kukanta kawai ya jiyo a firgice yake tambayarta lafiya amma taki magana sai ma kara volume da take,Kareem tsintar kansa yayi cikin firgici da tashin hankali babu abinda yake so wanda ya wuce ganinsa kusa da ita.
"lafiya kuwa abokina?lokaci ɗaya ka firgice?."
Bai basa amsa ba sai tare masu abin hawa da yayi cikin mintuna kalilan suka isa gidan Kareema,kofar a buɗe hakan ya basu damar shiga kai tsaye,waige-waige suke ba tare da sun hangota ba sai dai muryarta da ta dashe dan kuka da suke ji. Kai Kareem ya saka zai shiga ɗakin dayake tsammanin acan take,
"Kareem me kake yi wannan?"
Abdul ya tambaya cike da mamaki ganin yanda abokin nasa ke rawan jiki.
"Abdul bazan iya juran ganin wani abu ya same Kareema ba,idan ban shiga ɗakin ba taya zan san halin da take cike bare na taimaka mata kamar yadda ta bukata?"
Kafe shi yayi da ido ganin baida niyyar ce wa komai yayi wuce warsa.
"baka san wacece Kareema ba shiyasa kake rawar ƙafa a kanta,amma time will show"
Har ya shiga ya dawo ya ce
"magana kake ne?"
Da kai ya basa amsa,bai damu da lallai sai yaji ba shima saboda ya san bashi da niyyar sharri kan Kareema.
A hankali ya karasa gami da durkusawa kusa da ita
"Kareema! Kareema!"
Ya kira sunanta a hankali.
Bata ɗago ba sai kara dunkulewa gu ɗaya tana shakar kuka. Yana matukar jin zafin kukan nata sosai ya kara magana in a cool nd sweet voice nasa
"Kareema crying? Kina so nima nayi?"
Kaɗa kai tayi
"a'a"
"to indai hakane i wan't you to tell me what makes you cry."
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke cikin muryarta dake rawa ta ce
"ɓarawo"
Ta ja karshen kana ta ɓuɗe sabuwar shafin kuka. Har a rai yaji tsoro sai dai baya so ya firgita ta hakan yasa ya maida abin wasa
"kai dai Kareema! Gizo ne kawai amma babu wani ɓarawo,kinji kwantar da hankalinki babu abunda zai sameki kinga nan kusa police collage ne kuma akwai camp na sojoji zan sanar dasu kinji daina kuka haba Kareema karki saka nima na fara."
Kara kukan take da karfi kamar zugata yake,rasa yadda zaiyi ya rarrasheta yayi gashi kukan na ƙona masa rai,tashi tayi da niyyar barin ɗakin jiri ya ɗebeta,da sauri ya tarota ta faɗa kirjinsa,luf ta kwanta kamar bata motsi bai kawo komai a ransa ba ya cigaba da bubbuga bayanta a hankali yana bata hakuri sannu a hankali take sauke numfashi har ya dainaji ɗago kanta da zaiyi yaga ashe bacci tayi,kwantar ta yayi kan gado haryanzu tana maƙele da wuyarsa gam motsi kaɗan take yin kamar zata farka shikuma tsoron hakan yake dan yana matukar tausaya mata,tare suka kwanta duk da yana jin babu dadi sakamakon manni masa a jiki da tayi tana shiga jikinsa. Duk abinda ke faruwa Abdul na gani ya rakuɓe a ɗan longo bayan ya saita wayarsa a auto video tana ɗaukar masa duk wani motsi tasu,nannauyar bacci ne shima yayi gaba dashi daga nan bai kuma sanin abinda ya faru dashi ba hakan ya bawa Abdul damar ɗaukarsu san ransa.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Cikin farin ciki ya koma gida tarar da Azeezat yayi kwance babu lafiya,bai kulata ba ya wuce ya rage kaya bayan yayi wanka,ɗan gajeran boxers da T-shirt blue colour ya amshi jikinsa sosai satar kallanta yayi yaga duk ta galabaita ba dan ya tausaya mata ba ya durkusa gabanta,
"menene Azeezat,lafiya kike kuwa?"
Takaicin tambayar tasa taji sosai ya za'ayi ka ganni kwance kuma ka tambayeni lafiya,ta faɗa a rai. Shirin magana take amai ya zo duk ya ɓata masa kaya.
"subhanallah ke wacce iriyar mata ce kazama sha-sha-sha duba yadda kika ɓata min kaya mtsww ban san ma wanne zagi zan miki na huce ba mara hankali wanda bata gaji arziki ba wawiya kawai"
Rai a ɓace yayi toilet yana faman mita.
Kukar ma kasawa tayi ido kawai ta zuba masa.
"yawwa ki buɗe kunnuwa ki jini,mun bawa Kareema aikin ɗauko files wurin Kareem ta ɗauka amma ta mayar masa sa'ar ki ɗaya anyi dismissing nashi wurin aiki badan haka ba da ta miki asara,na kula take takensu sun faɗa soyayya ya rage naku idan zaki iya zuwa ki bayyana mata asalin Kareem fine,in kuma a'a nan ma sani gareku sai dai abu ɗaya! Azeezat idan kika sake kika faɗawa wani shirina,hmmm"
"Soyayya kuma? Kareema da take da aure? Karde zata ce bata san Kareem namu bane?"
Niyyar tashi tayi cikinta ya murɗa komawa tayi ta saki ƙara tana rike da cikin ɗan cije lips tayi "Ash" ta faɗa. ko yasan tanayi cikin wannan azababben yanayin barcin wahala ya ɗauke ta.
********
Ba Kareem ne ya farka ba sai wajajen isha,yanayin daya ke ciki ne yayi mugun ɓata masa rai take ya fara nadamar sanin Kareema,a gigice ya nemi kayansa ya gyara jikinsa sosai yake jin kunyar kansa gami da nadamar amsa kiran Kareema. Kamar wacce akace ta buɗe ido ta hango shi yana fice wa da sauri.
"Ƴallaɓai! Watakila daga yau bazaka kara ganina da kima ko mutunci ba,nayi nadamar abinda ya faru duk da bada so na bane amma dan Allah kayi hakuri a yanzu kai kaɗai ne gareni indai kaima ka juya min baya hakika rayuwata zata shiga garari"
Ta karashe da kuka.
Shiru Kareem yayi yana mai jin kunyar juyowa ya haɗa ido da ita,a iya hasashen shi babu alamun abinda ya shiga tsakanin su banda kwanciya da sukayi tare,ajiyar zuciya ya sauke wata zuciyar na raya masa hakan ba komai bane tunda ba da niyyar shi bane ita ma haka.
"kina tunanin na miki wani abu ne?"
Da sauri ta ɗago ta ce
"a'a"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin
"karki damu babu abinda zai rabani da ke,sai dai zanyi kokari naga irin haka bata kara furuwa ba."
"Godiya nake"
Fuskarta ɗauke da murmushi.
*VOTE ND SHARE PLS*
Cute HapCyy ce😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/Dze968iAT8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*Be miserable. Or motivate yourself. Whatever has to be done, it's always your choice.*
Page 19~20
____________📲Washe gari ta tashi da ɗan karfin jiki sassafe tayi gidan Kareema har ta karasa bataji shigowarta ba sakamakon zurfi da tayi cikin tinani,kare mata kallo tayi duk da Kareema ba mai ƙiba bace amma ramar ta ta, ta fito fili sosai tayi baki idon ya fito waje tamkar na mujiya.Jikinta ne ya bata ana kallanta tinanin hakan yasa ta kai dubanta ga ƙofa. Murmushin ƙarfin hali tayi lokacin da suka haɗa ido da sauri ta yo inda Azeezat ke tsaye.
"ƙawata kece a gidana yau,sannu da zuwa kinci sa'a jarabebben baya nan"
Ƙallo kawai Azeezat ke binta dashi har suka isa bedroom.
"Kareema meke damunki ne wai? Mekika rasa a rayuwarki Allah ya baki miji me dukiya ki dubi inda kike rayuwa fa"
Cike da rashin fahimta ta ce
"Me kike so ki ce Azeezat?"
"hmm har sai na fito fili? Okay faɗamin dalilin ramarƙi ko a gidan ko da bai kai nan ba kinfi haka kauri"
"mtsw dan Allah share,yanzu dai dame kika zo nasan ba kya zuwa sai da sabowa"
"wannan labarin ta sha banban da saura,ba dogon bayani nazo miki ba Kareema kina gab da sanya rayuwarki cikin matsala"
"Matsala kuma?"
"Yes matsala,kin fini sanin hakan kina neman namiji bayan da auranki,kuma wannan Kareem ɗin shine nake baki labarin an bani shi a gida,Kareema karde ki ce baki san da hakan ba"
"Ya Rabbi! Wai mai kike faɗa ne Azeezat kina so kice Kareem shine Cousin naki?"
"Kwarai da gaske wannan dalili ne yasa nayi gaggawar zuwa na faɗa miki kafin kuyi nisa ki canza ra'ayinki akan shi, tarayyarku ba karamin kalubale bane a gareni"
"hmmmm amma Azeezat kin cuci kanki da kanki,kamilin mutum kamar Kareem wanda yasan darajar mace abaki shi kiyi watsi?"
"Bana son shi! Bana son shi! Na gaya miki Kareema karki sake min makamancin wannan zancen abinda nake so da ke shine kiyi gaggawar rabuwa da shi"
Bakin window ta tsaya ta ɗan murmusa.
"kin makara Azeezat,a yanzu babu abinda zuciyata tafi bukatar fiye da kasance wa da Kareem,ina muradin mallakar shi matsayin mijina uban ƴaƴana bazan taɓa iya ciresa a zuciyata ba kamar yadda kike wa abdul *MAKAUNIYAR SOYAYYA* haka nima nake masa ina tayaki jimamin rasa jarumi mai riko da amana Azeezat kin tafka babban kuskure sai dai ba laifi hakan ya min daɗi tunda zan samu damar mallakar sa"
"Kareema anya kina da hankali,ina zaki kai auran naki har kike ikrarin Kareem ya zamo mijinki,bari kiji wallahi bazan taɓa bari hakan ta faru ba"
Idan ta har sun ciko ruwa ta ɗago ta kalli Azeezat,a hankali ta durkusa tare da dafa kafafunta cikin raunin murya ta ce
"Azeezat duk abinda kika ce zaki aikata nasan zaki iya,dan Allah kada ki rabani da Kareem na roke ki zan iya yi miki koma menene amma dan Allah ki bar ni dashi"
She really sympathyze for her coz ta san feeling na rashin samun abinda zuciya ke so.
"Kareema na amince bazan miki komai ba,sai dai ina so ki min alkawari Kareem bazai taɓa gane Abdul ne ya sa ki ɗauko files ɗin can ba"
"na miki alkawari ba zai taɓa sanin ni ce na ɗauko ba ma bare yayi tinanin wa ya saka ni ,kamar dai yadda nace masa tsinta nayi a hakan zamu tafi in shaa Allah"
"shikenan Allah yasa,sannan pls baki sanni ba nima haka okay?"
Kaɗa kai Kareema tayi tare da jan numfashi ta ce
"Azeezat kiyafe min da shawarwarin dana baki kan ki bijerewa iyyayenki"
Murmushi tayi ta ce
"na yafe miki amma Kareema meyasa kike son kashe auranki ki auri wani,ba kya tinanin Kareem zai iya gano ke matar mutane ce? Idan kuma ya gano wani mataki kike tunanin zai ɗauka me kika rasa a giɗanki Kareema da har kike son fita?"
"Azeezat kenan,muna haɗuwa a bayan gidan mu ne amma baki san tarihin rayuwar da nake a cikin gidan ba,da kuma yadda na auri wannan mijin da gwara babu dashi ko me na aikata duk muninsa ba laifi na bane idan lokaci yayi zan baki labari"
"Okay ina jira"
Bata kara sauraranta ba tayi gaba. Tagumi ta rafka abubuwa dayawa suna zuwar mata kai wanda ita kaɗai ce tasan yadda suke mata raɗaɗi.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
kwance yake luf rashin lafiyar ta sa ta tsanan ta ko magana baya iyawa da kyau. Cikin karfin hali yace
"Abdulkareem"
"na'am Abi"
"ina son baka wata shawara,tunda Alhaji Dagash haryanzu bai nemeka ba me zai hana ka fara kasuwanci da ɗan kuɗin da ka tara shekaru fa ja suke gashi ko auran fari bakayi ba."
"baka ce komai ba ko hakan bata maka ba"
Ummi ta faɗa tana kokarin ɓarewa Abi magani.
"ba wai naki bane Abi,rashin lafiyarka yana bukatar afitar da kai kasar waje neman magani wannan shine dalilin da yasaka har yanzu ban fara sana'a ba"
"kada kayi tinanin fitar dani wata kasa ɗana,nariga nasan tawa ta ƙare banida sauran rayuwa a nan gaba dan haka kayi amfani da dukiyarka"
"a'a Abi zuwa jibi zan maka passport inyaso mu tafi bazan taɓa bari ranka ya salwanta ba alhalin inada yadda zanyi"
"Allah ya maka albarka ɗana,nagode da ɗawainiyar da kake damu ba wai naki bane ina jin alamun lokaci na yayi ne"
"haba Abi ai cuta ba mutuwa bace zaka warke da yardar Allah"
"Habiba hakika duk tsawon rayuwata da ke baki taɓa ɓatamin rai ba,ke ce kika fi ko wa fahimtata Allah ya albarkaci rayuwarki kinji,kuyi hakuri da rashina da zakuyi ina kyautata zaton can sai yafi min daɗi akan rayuwar da nake yi a yanzu,kuyafemin mutuwa zanyi idan Kudrat tazo kuce na yafe mata duniya da lahira Allah ya mata albarka"
"Abi Azeezat fa? Ka daure ka yafe mata"
Kareem ya faɗa yana kuka.
"bazan taɓa yafe wa yarinyar data jefa rayuwata cikin bakin ciki ba"
"Ummi dan Allah ki saka baki ya yafe mata"
Bata tanka ba sai kuka take itama. Jiki a sanyaye ya shiga ɗaki dan samun hutu kasancewar jikin Abi ya matsa ido biyu suka kwana daren jiya. Misalin azahar kamar a mafarki yake jin sautin kuka a firgice ya yo tsakar gida,jikinsa ya ɗau zafi sosai numfashin sa na fita sama-sama cikin gaggawa Kareem ya kirawo doctor,drip ya fara saka masa bayan ya gwada jininsa.
"yallaɓai jininsa ne ya hau?"
Hankali tashe suke tambaya.
"well! Jininsa bata hau ba sai ma ƙasa da tayi,ga wannan drugs ɗin ko siya amma fa kuyi gaggawar kaishi hospital dan jikinnasa yayi tsanani"
Firts aid box nasa ya ɗauka ya barsu tsaye,zama suka yi kusa dashi ko wanne cikinsu fuskarsu hawaye kaca-kaca. Drip ya daɗe da karewa sai dai Abi bai farfaɗo ba,tun suna tsammnin bacci yayi har abin ya fara basu tsoro,likitan suka kuma kirawo wa gwajen farko ya shaida masu Abi baya raye.
"baya raye? Kana nufin ya mutu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Habiba....."ta fashe da kuka.
Kasa furta komai Kareem yayi sai ambaton Allah dayake a zuciya mutuwar Abi ta matukar girgiza sa. Abban sa ya fara kira ya shaida masa makota duk sunzo a daren aka masa sitira,jana'izar kuwa sai gobe da misalin karfe goma.
"ya salam! Duniya ba matabbata ba,bawan Allah ya tafi Allah ya jikansa,sai dai kamar banga Baban Kareema ba anya ya shigo kuwa?"
"ai Baban Kareema yana kullace da Abi shiyasa bazai shigo ba kana ji rahin lafiyar ma shine ya faɗa masa ɗacin magana zuciyarshi ta buga"
"innalillahi! Kai gaskiya Baban Kareema ba karamin azzalumi bane,duk da haka tunda mutum ya bar duniyar ai...."
"kaga sallau tafiya zanyi dare yayi Allah ya bamu alkhairi"
Asubar fari Kareem ya fita neman Azeezat ko gawar shi tazo ta kalla,ya kira numbarta babu adadi taki amsawa.
"abokina aina zan samu Azeezat ne,akwai bukatar tazo ta kalli ko da gawar sa ce"
"duk inda Azeezat take ba ƴar arziki ba ce,bani numbar na kira ta"
Bugu ɗaya ta ɗaga kafin ta ce wani abu ya ce
"Kareem,anan ta fuskanci tare suke dashi.
"shashasha zaka ce ba Kareem ba,faɗi dalilin kirana sauri nake zan ajiye wayar"
Ƙarɓar phone ɗin yayi cikin kuka ya ce
"Azeezat Ab...abi ya rasu dan Allah ki daure ki dawo gida"
"ya rasu? Allah ya jikanshi amma ni bazan iya zuwa ba ka basu hakuri"
"dan Allah Khadija,ki daure kizo k...."
Kit yaji ta kashe wayar,dubawa yayi yaga Azeezat KM ajikin numban,yayi mamaki matuka ya akayi numbar harda suna.
"ya naga ka kurewa screen ɗin kallo"
Nuna masa yayi sai yanzu ya ankara.
"au wai sunar jiki,yanzu nayi serving abokina mu tafi kaga an kusa a kaishi ka share Azeezat Allah zai ganar da ita"
A zabure ya kara ce wa,
"Kudrat! Ya kamata ta sani muje gida yanzu na ɗau numbar da zan same ta"
Kiranta yayi ya shaida mata,Kudrat bata taɓa jin labari mara daɗi kamar wannan ba,duk da ce wa yayi Abi baiji daɗi ba ta taho gida.
"Abi bai ji daɗi ba? Wayyo Allah na ya Allah ka taimakeni"
Ban tsaya wani shiri ba na kama hanya cikin sauri ina tafe ina share hawayena, ji nake tamkar na fire, gidan Alhaji dana matukar tsayi kafin na fita daga harabar gidan naji muryar da ko a mafarki bana muradin ji ya ce
"saurin zuwa ina haka"
Da rinannun idanuna na nayi passing nashi baki na har rawa ya ke kalmomi na rige-rigen fita
"dan Allah kayi hakuri ka barni na fita,Babana bashi da lafiya ka barni naje naga halin da iyayena ke ciki dan Allah"
Na kuma fashewa da rikitacciyar kuka.
"babu ina zakije,wuce ki gyara min ɗaki"
"dan Allah yallaɓai kayi hak...."
"kina so na barki kije?"
Da sauri na ce
"ae"
"okay muje ɗaki kimin wasu ayyuka kafin kije"
Ina biye dashi har muka isa ɗakinsa,ina ta addu'ar Allah yasa Billy bata nan kusa kaina nayi banga kowa ba ina shirin tambayar wani aiki zan masa naga ya kulleni ta waje babu roko da magiyar da ban masa ba amma yaki saurarata haka na hakura na zauna cikin tashin hankali na rashin jin halin da iyayena ke ciki,hakuri nayi na fawwala wa Allah lamarin,abinda yafi bakanta min shine ina ji Kareem ya sake bugu wayar buɗan bakinsa ya ce Kudrat ta ce bazata samu damar zuwa ba abashi hakuri,wannan lokacin ji nayi tamkar na kashe kaina na huta sai can dare Mahfuz ya zo daukar kayansa a ɗakin ya buɗe ni ban ɓoye masa komai ba ya matukar jajantamin gami da bani hakuri. Wanke jikina nayi dan ya ce zai kaini gida naga iyayena take farin ciki ya lulluɓeni na ɗan samu saukin damuwar dake addabar zuciyata,a main parlour muka haɗu da Alhaji Mamu yayin fitowa cikin tsawa ya ce
"me nake gani,Mahfuz ina zakuje?"
"am..e..umm Alhaji Babana ne bashida lafiya zanje na dubasa"
"eh Alhaji mahaifinta ne..."
"quit! Bana son jin komai daga gareku maza ku ɓace min da gani mashirmata kawai"
Jiki a sanyaye Mahfuz yayi tasa ɗakin sanin halin Alhaji ba mai wasa da su bane, ni kuma nabi bayan Alhaji kamar yadda ya umarce ni. babu abunda ya canza idan ban bashi kaina ba bazan je gida ba,jiki babu kwari ina me mugun jin haushin kaina nayi ɗakina baccin da banyi ba kenan a wannan daren.
Bayan Ummi ta gama takaba Abban Kareem ya ɗauketa suka koma Yobe da zama shima Kareem ɗin dan yaki amince wa ya komane Abban sa ya hakura.
Yau ma zaune take ta mikar da kafarta shi kuma yayi matashi da cinyarta minti-minti take masa magana amma baya kulata ransa a haɗe.
"Abdul meyafaru ne naga kamar ranka a ɓace dan Allah idan wata matsalar ce ka faɗamin"
Furzar da isa mai zafi yayi ya ce
"Azeezat alamu suna nuna wahalar banza nake,nayi sanadin barin Kareem aiki gashi zai so ma sana'a da kuɗin daya tara"
"mai kake so ayi akai?"
"so nake waɗannan kuɗin su dawo hanuna kinga dai kin kusa haihuwa,gashi an kore ni a gidannan dole muna bukatar kuɗi"
Tallafu fuskarshi tayi da hannu ɗaya,ta sa karamin yatsanta a bakinsa tana juyawa ta ce
"yau ba sai gobe ba kuɗinnan zasu dawo hanunka,Kareem zai zama tamkar almajiri"
Dariya ya fara sosai tare da rungumeta yana shafar bayanta.
"sake ni naje na shirya ko?"
"a'a ni zan shirya ki dai muje"
Rike a hannu ya shiga da ita ɗakin,babu ɓata lokaci ta fito cikin shirin fita sanye take da nikab ko ina na jikinta a rufe. Buɗe kofar da zatayi yayi dai-dai da na Kareem kafe juna da ido sukayi na tsawon mintuna.
"Anya ba Khadija bace?"
Ya tambaye kansa a rai. Babu wanda ya tankawa juna a zahiri matsa mata yayi ta wuce har tayi nisa kafin ya shige yana mamakin yanayinta da tayi kala ɗaya da Azeezat. Kallan tuhuma yayiwa Abdul ya ce
"Abdul wacece ta fita a gidanka sanye da nikab? Karde kace mata ka fara ajiyewa a gida?"
Acting yake tamkar bai gane meya ke nufi ba ya ce
"kamar ya ajiye mata ban fahimceka ba"
"okay,bara na maka yadda zaka fahimta naga Azeezat ta fito daga gidanka yanzu me alakar ka da ita"
Sosai ya tsorata ya ce
"karde Azeeza ta cire nikab ɗinnan? A zahiri kuwa kauda tsoron yayi ya dake ya ce
"ni ban san wata Azeezat ba,wannan da kaga ta fita itake kawo min abinci ƴar makotanmu ce"
"Abdul amma fa....."
"zargina kake Kareem? Dama babu yadda tsakaninmu? Kana tinanin munafurtarka nake? Nagode da wannan shaidar"
Ya faɗa yayinda yake shiga ɗaki rai a ɓace. Shawo gabansa yayi da sauri ya ce
"look Abdul ba haka nake nufi ba Allah ya huci zuciyarka forget about this issue nazo maka da albishir wanda nasan kai ne mutum na farko da zaka tayani farin ciki"
Murmushi yayi a fuska,cikin ransa kuwa zallar duhu ne zuciyarsa na tsananta bugu ya daure ya ce
"ina tayaka murna abokina faɗamin albishir ɗin i'm wit all my ears"
"have a place and cool down ur mind"
A tare suka zauna kan kujera mai ɗaukar mutum biyu.
"Alhaji Dagash ya kirani zan fara aiki gobe idan Allah ya kaimu"
Tamkar an soka masa mashi a rai haka yaji,kansa ne ya fara juyawa bai san sanda ya fara salati ba,sosai Kareem yayi mamakinsa sai kace wanda yaji labarin mutuwa,duk da haka Kareem bai fahimci komai ba ɗaukawa yayi duk cikin taya murna ne.
"hhhh salatin ai ya isa haka abokina"
"wow! I'm so happy wallahi Allah ya dafa maka abokina ya kauda idan makiya,yakamata muje mu kara jaddada godiyarmu garesa ko"
"gaskiya kam,zuwa karfe uku na yamma sai muje"
Tsayawa saurarar hirar su Kareem ce ta sanya na makara wajen biyo Azeezat, abinda ya fara faɗawa kunne na shine
"idan bazaki iya ba,shiknan babu lallai ba dole amma fa ki sani duk wasu shirinki sun lalace"
"Azeezat dan Allah ki tausayawa rayuwata kada ki jefani cikin halin dana baro a baya"
"banida lokacin sauraran banzayen kalamanki,idan komai ya ɓaci kada ki kuskura ki nemeni dan babu abinda zan iya miki"
Ta tashi zata tafi taji muryarta da cike yake da tashin hankali ta ce
"na amince"
Murmushi Azeezat ta sakar mata ta ce
"better! Yanzu zan turo a ɗauke ki tun yanzu ki faɗawa Kareem ɗin kina kauyen malari"
Ido kawai take binta dashi tamkar bata da niyyar aikata komai.
"o! Bazaki kira ba,shikenan"
"a'a bance ba amma dan Allah kija masu kunne kada su cutar da shi"
Amsa mata tayi ta hanyar ɗage mata gira,sauri tayi ta danna numban Kareem kamar yadda ya saba bai ɗaga ba sai daga baya ya kira,kwace wayar Azeezat tayi ta mika wa Tony lokacin sun iso gidan cikin kaushin murya ya ce
"Kareema tana hanunmu million goma ne zai iya fansarta idan kana bukatarta kazo da kuɗin kafin faɗiwar rana kada ka sake ka faɗawa jami'ai yin hakan ba karamin kuskure bane"
Kunnen ta yaja da karfi take ta kurma ihu dan taji zafi ba karami ba muryarta a dashe ta ce
"KAREEEM kazo kashe ni zasuyi"
Ta fashe da matsanaciyar kuka.
Kareem duk ya daburce ya rasa me zaice,shiru yayi kawai yana sauraran sautin kukanta. Abdul ne ya amshi wayar ya ce
"ina za a kawo maku kuɗin"
Shiru yayi yana jin abinda Tony ke faɗa kafin ya ce
"kada ku taɓa lafiyarta,yanzu zamu kawo muku kuɗin"
"Abdul banida million goma,shida ne kawai da ni"
"tab aiko ko sisi bazasu rage ba suka ce amma mai zai hana kaje wurin Dagash ka karɓa"
"me zance masa?"
"ce wa zakayi an sace kanwarka kana bukatar kuɗi"
Bai gamsu da hakan ba sakamakon tilasta masa da Abdul yayi sai ya amince,tare sukaje suka karɓo cikon kuɗin sunsha wahala sosai kafin Tony ya basu Kareema ita kanta Kareema ba karamin wahala tasha a hanun Tony ba. Daf magrib suka shigo gari duk sun galabaita hutawar awa ɗaya sukayi ya ce zai ko ma gida. Kuka ta fara masa tana magiyar ya kwana tare da ita tsoro take ji.
"hakane Abokina,bai kamata ka bar Kareema ita kaɗai a gidannan ba duba da a tsorace ta ke"
"dan Allah Kareem,ka dawo gidana da zama idan kuma ka ce a'a wallahi kashe kaina zanyi tunda ko wa ya kini"
A razane suke binta da kallo,tausayinta ne duk ya cika shi banda Abdul daya kewa Kareem kallan sha-sha-sha.
"kana tinanin karya nake ko wasa ko?"
"sorry Kareema kwanta ki huta zan je gidan ogana na miki alkawarin zan zo kinji? Kafinnan ki kwanta ki huta okay?"
"kamin alkawari?"
"ae da yardar Allah"
Shikenan ta furta a hankali su kuma suka fice daga gidan.
"Kareem yi hakuri bazan samu zuwa gidan Dagash ba kawai sai mun haɗu"
"haba Abdul indai hakane nima fasawa zanyi idan ya so goben maje tare"
"a'a bai dace ba Kareem ya baka aran 4million,gobe zaka fara zuwa aiki ai yakamata kafin ku haɗu a Industry ka fara masa godiya a gida"
Numfashi ya sauke ya ce
"okay bara nayi dropping naka"
Sai da ya fara siya mashi take away saboda yasan gajiya ba lallai ta barshi yayi girki ba,godiya ya masa sosai yana fatan Allah yasa abotansu ta ɗaure na har abada. Abdul kuwa smilling kawai yake mai tarin ma'anoni.
Unguwace zam wanda aka ƙawata ta sosai tsayawa a kwantanta tsari da ƙyan wurin ma abin ɓata lokaci ne sai dai duba da nasabar ALHAJI DAGGASH ƙaɗai ya isa ya kwatanta maka kyawun Estate nasa,kafin ka karaso gidan jami'an tsaro ne dayawa ke zirga-zirga suna checking na masu kai kawo ga mamakin Kareem dukkanin jami'an basa nan ɗai-ɗaiku kuma bacci suke.
"ikon Allah kodai meeting suke"
Ya faɗa yana dube-dube ,hango wani dattijo yayi kai tsaye ya riskesa ya ce
"Mai gidan baya nan ne?"
"yana nan ka shiga ciki"
"okay"
Ya faɗa.
Tafiya yake cike da tsoro,jikinsa duk yayi sanyi ji yake tamkar wani abu zai faru dashi. Kamar kazar da kwai ta fashe mata a ciki ya isa bakin main parlour dayake kyautata zaton na Alhaji ne. Sai daya karanta ayatul kursiyyu kafin ya shiga.
"Subnahallah!"
Kawai ya iya faɗa yayinda yaga gwalagwalan da suke ƙyalli a parlour. Kamar wanda akace ya kalli gefe hango su yayi rai huɗu kwance cikin jini.
Drmmmdmmmmm! Zuciyarsa ta saki razananniyar ƙara,da sauri yaje yana jijigasu jinin duk ya fantsamu a jikinsa.
"hahahahhah"
Yaji an fashe da muguwar dariya,ganin sa yayi hanunsa rike da bindiga,kansa yayi ya cukume wuyar rigarsa ya na ce wa
"kai ne ka kashe su,kaine kaine"
Yana jijigashi a ruɗe.
"eh nine,ga bindigar sai ka ɗau fansa"
Ya wurga masa bindigar,ba tare da dogon tinani ba Kareem ya ɗau ka yana mai masa nuni dashi. Dai-dai wannan gaɓar mutumin ya kaɗa kararrawa parlour ya cika da jami'ai.
Kuka ya saka ya ce
"shi....shi,shine ya kashe su"
Kallan pistol ɗin dake hanunsa Kareem yayi ya kasa ce wa komai tsabar rikicewa duban jikinsa yayi jini tamkar yayi wanka dashi,kokarin buɗe baki yake ya ji ɗaya daga cikin commenders ɗin ya ce
"you are under arrest"
Ya saka masa ankwa a hannu.
*COMMENTS* naku ya iso ni masoya littafin MAKAUNIYAR SOYAYYA coz comments is na HO²
*VOTE ND SHARE PLS*
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*Be Impeccable With Your Word. Speak with integrity. Say only what you mean. Avoid using the word to speak against yourself or to gossip about others. Use the power of your word in the direction of truth and love.*
Page 21~22
____________📲Ɗaure yake akan kujera, kallo daya zaka masa ka dauke kai tsabar raunin dake jikin sa ya tsananta. Kara jona masa shocking ɗin yayi
"bazaka faɗa mana gaskiya ba sai ka kusa matuwa ko"
Kareem ko sanin inda yake baiyi ba sai juyi yake cikin azababben yanayi,hawaye na bin fuskarsa.
"Sir al'amarin nan na ƙara ɗaure min kai,yaron nan mun daɗe mana gana masa azaba a ganina indai shine ai zai faɗa mana kawo yanzu."
Mugun kallo ya bi shi dashi hakan yasa ya kama bakinsa.
"Ku cigaba da azabtar dashi har sai ya faɗi gaskiya."
Hakanan suka cigaba da gana masa azaba babu kakkautawa amma hakan bai sa Kareem daina faɗan,
"Bani na kashe su ba."
Sai dai kuma hakan bai amfanar dashi da komai ba domin bashida wata shaidar da zai kare kansa,kasancewar Dagash na ɗaya daga cikin manyan mutane masu faɗa a ji,lawyers nasa sun bada damar a kulle Kareem a gidan kurkuku tare da basa aiki mai tsananin wuya na shekara biyar kafin Dagash ya warke ya faɗi irin hukuncin da yake so ya masa.
Ta ɓagaren Abdul kuwa duniyarshi ce ta fara haskawa a yanzu bashida matsala tinanin sa ɗaya shine ya zaiyi ya rabu da Azeezat.
"Bana tinanin wannan zai zame min matsala,rabuwa da Azeezat abu mai sauki ne."
Ya faɗa ɗauke da murmushi a fuskar sa.
Yana cikin wannan tinanin yaji ta manna fuskarta a bayansa.
"My Abdul! Meya sanya ka farin ciki haka"
"hhm gaskiya ina matukar farin ciki Azeezat,matsala ta ta kau tunda Kareem bazai taɓa fita daga kurkuku ba"
"Kurkuku kuma? Meyayi haka"
"hhhhm yaje gidan Alhaji Dagash ya kashe ƴaƴansa da matarsa"
A razane ta ce
"Kisa kuma! Kareem ɗin?"
"kwarai dama irinsu haka suke musulmai a fuska arna a zuci"
"Yanzu kana nufin Kareem ne ya kashe su?"
"Of coure yes"
"Allah sarki Kareem shikenan rayuwarshi zata ƙare a kurkuku."
Ƙamar zatayi kuka ta ƙarashe maganar.
Rai a ɓace yake kallanta
"O Tausayi ma yake baki,ki dubi ran daya yi sanadi su ba abin tausayawa bane? Maganar da nake miki Dagash na kwance a gadon asibi ko sanin inda yake bai yi ba."
Kallan sa Azeezat take cike da mamakin yadda yake kumfam baki.
"Allah ya baka hakuri"
Ta tashi zata shiga ɗaki. Yanjota yayi da karfi,
"keeee mara tarbiyya ni zaki yiwa tsaki"
A fusace ya hau kanta da duka bai damu da cikin da take ɗauke dashi ba. Iya azaba tana sha tun muryarta na fita harta daina,sai da ya yi iya san ransa kafin ya kyaleta.
Haka Abdul ya cigaba da gana wa Azeezat azaba ba dare ba rana ba akan komai yake hakan ba sai dan ta gaji ta rabo dashi,amma taki. Ɗaukarta yayi suka nufi asibiti bata san me za suyi ba kuma ba halin tambayarsa yanzu ya haura kanta da duka.
"Likita matata ce wannan so nake a zubar da cikin dake jikinta"
Zare eye glass ɗin idonsa yayi before ya ce
"Meyasa kake so ayi mata abortion,cikin ba naka bane?"
"Haba Abdul,taya za'a zubar da cikin da haihuwarsa yau ko gobe yanzu idan na mutu fa"
"Idan baza a zubda wannan cikin ba kada ki kuskura ki biyoni gidana"
Ya tashi a zuciye zai bar office ɗin,likitanne ya tsaidashi ya so ma masa nasiha har ya hakura da zancen Abortion ɗin.
Kwanaki na tafiya komai na masa yadda yake so sai dai ya rasa yadda zaiyi da ita ko wacce matsala ta kau itace kawai ta rage,yanke shawarar ƙaura zuwa hotel yayi a faɗarsa acan komai zai tafi normal,bayan ɗan wani lokaci Azeezat ta haifi ƴa mace a cikin hotel ɗin akayi suna lokacin Abdul ya ɗan fara sake mata ƙwasam wata rana yace,
"Azeezat tafiya ce ta gaggawa ta kama ni ina tsammanin gobe da safe zan fita"
Ƙasa ce wa komai tayi a ranta sam bataji daɗin labarin ba.
"Kar ki ɗaga hankali babyta,bazan jima ba kinji"
Ya janyota jikinsa.
Washe gari ya ɗau hanyar Yobe sai daya fara zuwa gidan su Kareem,dandazon jama'a ya gani zaune a bakin ƙofa kowanne da carbi a hanunsa,can gefe ya hango Abban Kareem ya nufi inda yake yana mai ƙaguwa da son ji zaman me ake. Cikin girmamawa ya gaishe su,shiru ne ya biyo baya daga bisani ya ce,
"Abba meyafaru ne"
Share hawayen daya ɓata masa fuska yayi ba tare da yayi magana ba.
Numfashi Abdul yaja
"Abba dama nayi tafiya ne,jiya zuwa na nakejin labarin tsausayin daya riski Kareem amma na maka alƙawari zanyi iya kokarina naga an fidda shi domin na tabbata Kareem sawon ɓarawo ya taka"
Kaɗa kai Abba yayi,yana kuka a hankali. Ɗaya daga cikin manƴan dake kusa dashi ne yace
"Kareem kam lokaci yayi sai da mu bishi da addu'a."
"What!"
Abinda ya iya faɗa kawai ya faɗi sumamme.
Agajin gaggawa aka kawo masa bai jima ba ya farka ɗauke da salati a bakinsa yana kuka sosai yana kuma faɗan alkhairun da Kareem ya masa,tun suna bashi hakuri har suka fara tayasa. Labarin mutuwar Kareem ta kasance tamkar sabowa a gare su.
Kwanansa uku a gidan ranar da zai tafi yake tambayar Abba
"Abba amma dai kunga gawar Kareem dai ko"
"Da mun sanya gawarsa a ido bazamu damu ba,labari kawai muka ji"
"Anya Kareem ya mutu kuwa"
Ya tambayi kansa a rai.
"Babu shakka ya mutu domin an tabbatar mana da hakan"
Inji Umma ta kuma fashewa da matsanaciyar kuka.
Amsar data bashi ne ya tabbar masa da ce wa maganar tasa ta fito fili.
"Allah ya jikansa. Zan wuce Abba."
Ya faɗa yana haramar tashi, addu'a suka masa tare da fatan alheri.
Bayan tafiyansa Azeezat na ta zuba ido yaushe zaizo amma shiru numbobinsa gaba ɗaya basa shiga abun da yafi ɗaga mata hankali ma shine tunda ya barta ko flashing nashi bata taɓa gani ba,banda rayuwar wahala babu abunda take har takai ta fara fita bara domin samon abinci,kuɗin hotel nasu ne ya kare har da ɗaurin bashi akai ganin batada niyyar biya masu hotel suka koreta.
Tattaren kaya take cikin tsuhuwar jakarta taga wata paper da rubutu kamar haka a jiki
_"Azeezat kin tafka babban kuskure wanda bazaki taɓa iya gyarawa ba,idonki ya rufe akan son wanda baya kaunarki ni Abdul na gama da breadi na yaga laida babu ni babu ke kuma ƴar da ke hanunki kada ki sake ki laƙaba min kije can ki nema mata uba karuwa kawai"_
Tana gama karantawa ta sulale kasa.
Manage wit za short page🙏
Comment
Vote
Share
Pls
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*The level of our success is limited only by our imagination and no act of kindness, however small, is ever wasted.*
Page 23~24
_________📲Wani razanannen ƙara ta saka tana kiran sunan Abdul cikin fitar hayyaci.
"Abdul meyasa zakayimin haka,Haba Abdul ina zan saka rai na,wa zan gani naji daɗi? Nashiga uku ni Azeezat! Abdul kaine jigona bazan iya rayuwa idan ba tare da kai ba meyasa ka kasa fahimtar kaunar da nake maka? Meyasa...."
Ta kwanta tacigaba kuka tana sambatu. Tana cikin wannan zullumi ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin yazo da sharɓeɓiyar bulala,ganin shi yasa ta kankame ƴarta da take ƙira Yasmin tana shaƙar kuka, warce Yasmin yayi ya jefar da ita gefe ya so ma zubawa Azeezat bulala babu kakkautawa.
"ƴar iska dama karuwa ce ke bamu sani ba,muna tausaya maki ashe ke ƴar tasha ce kin biye wa namiji gashi ya gudu ya barki wawiya kawai,ni na rasa kalmar da ta dace da ke, sha-sha-sha kuma bari kiji wallahi kuɗaɗe na ban yafe ba biyana zakiyi."
Sautin kukan ta ne ya karaɗe wurin cikin sauri suka yo kansu.
"Haba ƴallaɓai macece fa komai tayi bata cancanci irin wannan cin mutunci ba dubi fa yadda ƴarta ke kuka ko dan ita ya kamata a sarara mata."
"Hmm dan baka san yarinyar nan bane shiyasa kake neman kareta."
Yayi maganar yana kokarin zuba mata bulalar a jiki,take suka rike sa.
"kunga ku kyaleni na mata dukan tsiya,idan kuma ba haka ba ku biyani kuɗina."
Ƙaɗa kai wani gayen dake wurin yayi ya ce
"Nawane kuɗin naka."
"Au,goya mata baya zakayi? Okay kai ka sani kuɗina dubu hamsin ne."
Account numbarsa ya amsa a wurin ya masa transfer,tukun ya bar Azeezat ta tafi. Rasa ina zata nufa tayi duniya ta mata zafi ba tada wata mafaka. A bakin kwalta ta hango sa jingine jikin mota babu ɓata lokaci tayi inda yake.
"Ƴallaɓai nagode sosai ba dan kai ba da bansan halin da zan shiga ba."
"Kada ki damu ki godewa Allah ba ni ba."
Sunkuyar da kai tayi ta goge hawayen da suke shirin zubuwa.
"Ko zan iya sanin sunanka?."
"Sunana Aliyu."
"Nikuma....."
Kafin ta karasa ya ce
"Azeezat ta Abdul."
Ya yi smilling.
Sosai tayi mamaki,ya akayi ya santa? Sanin hakan ma ba wata amfani zata min ba.
Tayi maganar a rai,zahiri kuwa ce wa tayi,
"Sai anjima."
Kamar daga sama taji ya ce
"Azeezat idan bazaki damu ba ɗan bani minti kaɗan muyi magana."
Bayan sun shiga mota ya fara magana cikin nutsuwa da tausasawa.
"Azeezat ba wata dogowar zance bane ta sa na tsaida ke,na tabbata kina bukatar taimako hakanne yasa nake bibiyar rayuwarki ina kuma fatan Allah ya kawo ranar da zan bayyana maki abinda na daɗe ina ɓoyewa."
Cikin rashin inda ya dosa take sauraran shi.
"Ke macece mai karancin shekaru,bayan wannan soyayya ta rufe miki ido har ta kai kin kasa fahimtar abinda ake kira so bare wanda yake sonki dan Allah."
"Ban fahimceka ba,dama cin fuskata kake so kayi shiyasa ka tsayar dani?"
"Ko kusa."
"Indai dan Allah ka taimaka min ina rokonka ka barni na tafi."
"Zan barki ki tafi bayan na faɗa miki sakon zuciyata izuwa taki."
Ido kawai ta zuba masa ji take tamkar ta matse bakinsa ya faɗa mata abinda ke ransa.
Numfashi ya sauke wanda yayi silar janyo hankalinta garesa.
"Azeezat ina kaunarki kuma a shirye nake dana aureki idan kin amince."
Kafe sa tayi da ido tana mai jin tsanar shi na ziyartanta. Cikin fushi ta fara kokarin buɗe kofar motar taji a kulle.
"Bana kaunarka bana sonka da nasan da wannan zancen zaka zo bazan taɓa sauraranka ba,zuciyata mallakin Abdul ne na ɗau alkawari bazan taɓa son wani halitta bayan shi ba."
Binta yake da kallo yana son gano wani abu tattare da ita amma ya kasa.
"Anya yarinyar nan tana cikin hayyacinta kuwa? Duk wulakancin da Abdul ya mata amma ta makale masa bayan kuma tasan gudu yayi ya barta."
Kauda wannan tinanin yayi ya ɓata rai.
"Kina nufin bakya so na Abdul...."
Bai karasa ba ta katse sa ta hanyar furta
"Ae Abdul zan jira na tabbata akwai dalilin dayasa ya bar ni kuma bana tinanin hakan zai shafe soyayyar da muke wa juna."
"Kwarai dalilin shine baya kaunarki kin gane?"
"Ka buɗe min kofa na fita bana son jin komai daga gareka."
A tsawace take maganar.
"Ba sai kin ɗaga min murya ba,zan barki ki tafi amma ki sani ba kowanne namiji bane zai aureki bayan yasan tarihinki ko wannan ya isa ya ganar da mai hankali ni masoyinki ne na hakika,batun Abdul kuma bazai taɓa zuwa gareki ba zakice na faɗa miki."
"Naji"
Ta faɗa bayan ta fice.
Tafe take tana aikin kuka
"Ya Allah! Ya zanyi" to kije gidan Kareema mana? Amma anya Kareema zata karɓeki? To mai zai hana ki cewa Aliyu kin amince ko dan ki samu nagartacciyar rayuwa? Kai na tsanesa baka kaunar haɗa inuwa dashi. Cigaba da hasashe tayi ba tare da samun mafita ba. Daga karshe ta yanke shawarar zuwa gidan Kareema. Kamar ɓarauniya ta shigo cikin sanɗa cin karo tayi da ita kwance a bakin pampo ruwa na dukanta.
"Kareema"
Ta furta a hankali.
Da gudu tazo ta shake ta tana
"Kin kashe min shi Azeezat kun kashe shi kun huta wani irin son duniya ne wannan. Meya maku kukayi silar barin shi duniya Allah ya isa Azeezat kin gama da rayuwata....."
Kuka ne yasa ta kasa aikata mata komai sai ma sake ta da tayi ta cigaba da kuka.
"Dan Allah Kareema ki saurareni wallahi bani na kashe shi ba."
"Faɗa min me kika sani game da mutuwar Kareem?"
Mushiga daga ciki tukunna. Bayan sun dai-daita zama ta fara ce wa
"Kareema kamar yadda na faɗa maki ne,babu hanuna a cikin mutuwar Kareem haka shima Abdul bai san komai ba game da hakan ki yadda dani."
"Azeezat kin yadda Kareem ne ya kashe ƴaƴan Alhaji Daggash?"
Numfashi kawai ta sauke ba tare data tanka ba,sai da ta kuma tambayarta kafin ta ce.
"Ban yadda ba gaskiya wannan shiri ne akayi dama dan a laƙaba masa amma inada tabbacin Kareem bazai taɓa kashe ko da kiyashi ba bare ɗan Adam."
"Wayyo Allah na me ake nufi dani yanzu? Shikenan duk wata soyayyar da nake masa ta tashi a banza...."
Fashewa tayi da sabuwar kuka mai cin rai. Babu mai rarrashin juna cikinsu sai da sukayi mai isarsu sannan Azeezat ta ce
"Kareema,meyasa kike son Kareem bayan kinsan da auran wani a kanki."
"Saboda inada tabbacin shi zai cireni cikin matsalar da nake ciki."
"Matsala kuma wacce iri? Aurannaki ne matsala ko me."
"Azeezat kenan bana tinanin zaman aure nake a gidannan,kin taɓa sa mijina a ido tunda kike zuwa gidannan?"
"a'a"
"Dama nace zan baki labarin rayuwata,ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau....."
Gyara zama tayi kafin tacigaba.
"Azeezat!"
"Na'am Kareema."
"Hakika babu abinda yafi samun iyaye na gari daɗi a duniya sai dai nawa iyayen Allah bai kaddara zan gana dasu ba,Babana attajiri ne sosai mata ɗaya gare sa Amina sun kwashi tsawan shekaru basu haifu ba, kowa burinshi yaga bayansa ba dan komai ba sai dan su gaji dukiyar kasancewar Allah bai basa haihuwa ba, a na cikin wannan yanayin ya auro Mamata bata daɗe ba ta samu juna ahalin sunyi farin ciki sosai babu kamar Amina matar Babana har sai da tayi azumi goma dan murna,cikin watan da za a haifeni ɓarayi suka shigo gidan mu suka kashe Babana take nakudar dole ta taso wa mahaifiyata tasha wahala sosai kafin ta haifeni,kafin ayi suna itama tabi bayansa sakamakon ciwon ciki da yayi tsanani, na tashi a hanun Amina babu gata da bata nuna min ba a rayuwa ina cikin shekara ta biyar bazan iya tuna meyafaru ba kwasam na ganni a gidan Abba Mahadi, ya kuma ce min Ummana Amina ta mutu kuma na tabbata karya ne yayi hakanne dan yaci dukiyata daga wannan lokacin ne na fuskanci canji a rayuwa na rasa gata na zamto tamkar ƴar bola dukkan aikin gida nina keyi wannan dalili ne yasa zuciyata ta bushe har nake ingizaki ki bijirewa iyayenki kawai dan su tsaneki kamar yadda ake min...."
Cigaba da kuka tayi zuciyarta na ƙona. Batayi yunkurin hanata ba sai tayata da ta ke.
"Watarana Abba ya zo da yammaci yake shaida min an ɗaura aurena da abokinsa,na shiga tashin hankali sosai haka nayi biyayya har aka kawo ni,sai daga baya na fuskanci ba aure bane siyar dani sukayi kuma inada tabbacin harda haɗin bakinsu wajen kashe min iyaye babu wanda zai iya share min hawaye sai Kareem."
"Ya salam! To amma ina ita Amina,zai iya zama dukiyarki na wurinta."
"Banida masaniyar halinda take ciki,kuma ni kaɗai ba zan iya binciken lamarinnan ba tun dana haɗu da Kareem nake farin ciki domin nasan zai iya cire ni cikin wannan zullumi kafin azzalumannan su kashe ni nima sai dai kash."
"Kiyi hakuri Kareema komai mai wuce wa ne,amma me zai hana mu gudu tare da ke ko bazaki iya bina ba."
"Kin kawo shawara mai kyau,amma ina ganin zaifi kyau ko zamu gudu muje gidan su Kareem a Yobe."
Taɓe baki tayi
"Ke nifa idan kika kara kira min sunan ɗaya daga cikin su nida ke"
"Haba Azeezat duk da Abdul ya gudu ya barki bazaki koma gida ba."
"Nidai bazan koma ba kuma Abdul ba guduwa yayi ya barni ba,indai na rasa Abdul to yawon duniya zan shiga na rantse."
"Ya ilahi! Allah ya shiryaki Azeezat."
"Amin,ɗan bani waya na ƙira Alhaji Mamu dan Allah."
Amsar wayar tayi ta ƙira bayan sun gaisa yake ce mata zai tura mata sadaki suyi aure kawai. Sosai taji daɗi hakan tuni ta amince cikin farin ciki sukayi sallama.
"Azeezat meyasa ba kya tuna karshenki ne? Yanzu aure zakiyi ba tare da yardar iyayenki ba,ba wannan ba ina zaki kai Yasmin."
Murmushi tayi sannan tace
"Allah ne ya kawo min sauki,zan aureshi kafin Abdul ya dawo wannan auran wasa ne karki damu batun Yasmin kuma batada wani muhimmanci ko rasa ta nayi bazanji haushi ba ni dama mutuwa tayi."
Ta karashe maganar da ƴar dariya.
Ido kawai Kareema ta zuba mata lalle Azeezat sheɗancinki nada girma.
*Comment* na Oxygen o so try pls
0 comments:
Post a Comment