*ABUJA*
______________📲 Parlour ne babba wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa,golden colors furnitures ne masu tsada sai sheki suke abin sha'awa.
Gefe guda throw pillows ne masu yawa a gere acan na hango Alhaji Mamu hanunshi rike da kwalbar giya ƴaƴan shi sun kafe sa da ido fuskokinsu babu walwala ko ƙaɗan hasali ma da ka gansu zaka fuskanci bakin ciki tattare da su.
Ma'aikatan gidan suma sunyi jugum a cikinsu na hango Kudrat da ta kafe wuri ɗaya da ido ko giftawa babu tayi zurfi cikin tinani, ajiye kwalbar yayi ya so ma magana.
"Wato ba komai bane yasa na taraku anan face ina so na sanar daku ce wa zan ƙara aure."
Kallon kallo suka fara tsakaninsu kowa na mamaki aure kuma a wannan shekarunnasa? Tukunna ma wace tsuhuwar ce zata aure sa.
Ko wanne da tinanin nan a ransa, domin kawo karshen shirun Hajiya Amina ta kirkiro murmushi,
"Allah ya sanya alkhairi Alhaji."
Cikin ƴaƴansa babu wanda ya tanka. A zuciye Yaya Ammar ya bar wurin,gaba ɗaya suka bishi da ido,Billy na ganin haka itama tabi bayansa.
Alhaji Mamu ko a jikinsa,ƙara bajewa akan pillow yayi tare da buɗe kwalbar giya ya fara kwankwaɗa.
Aliyu ranshi tamƙar zai fice daga kirjinsa haka yake ji da kyar ya iya ce wa
"Zaku iya tashi kutafi."
Jiki a sanyaye kowa ya ɓace.
Tun da ya shiga ɗakinsa ya rasa meke masa daɗi tinaninsa yaushe Alhaji zai daina aure-aure,a iya saninsa matansa sun kai tara wanda yake aura yana saka banda ƴammatan sa na waje abin bakin cikin ma bai damu da ya san halin da suke ciki ba.
Ɗaukar waya yayi ya kira Yaya Ammar da Mahfuz domin su tattauna duk yadda za'ayi kada amaryar ta tare a gidan. Babu jimawa sai gasu sun shigo jiki a sanyaye suka nemi wurin zama.
"Yaya Ammar yaushe Alhaji zai shiryu nifa na gaji yanzu idan akaji zai ƙara aure wallahi ragowar mutuncin mu ta zube."
Cewar Aliyu.
"To ya zamuyi,abu yaki ci yaki cinyewa."
"Babu wani kin cinyewa Yaya Ammar kawai a san yadda za'ay, Mahfuz magana fa muke kayi shiru."
Aliyu ya ƙara faɗa cikin ɓacin rai.
"To me zance ne Yaya Aliyu, ko Hajiya Amina za'ayiwa magana tasan yadda zatayi ta dakatar dashi tunda kamar yana sauraranta."
"Ita kanta Hajiya ba yadda da ita nayi ba,ido kawai na zuba mata kaf nasan shirinta kuma da sannu zan tona mata asiri."
"Ya Allah! To Yaya Ammar menene abin yi."
Kafin ya basa amsa sukaji ana nocking na door,Mahfuz ne ya buɗe kofar yayi matukar mamaki lokacin da sukayi ido huɗu da ɗan uwansa,rungume juna sukayi tuni su Ammar ma sukayo kansu jin ya ƙira sunan Abdulmalik. Sai da sukayi kuka mai isarsu kafin suka shaidawa Abdul labarin ƙarin auran Babansu da duk wani abu da ya faru bayan tafiyansa.
Yayi bakin ciki matuka tsawon lokacin daya ɗauƙa baya tare da Alhaji amma haryanzu bai daina mummunar halinsa ba.
"Dan Allah ku ƙyalesa addu'a ce kawai zata gyarasa,yanzu dai nazo da kuɗaɗe dayawa wanda ko aure ne zamu iya yi mu duka huɗun kunga sai mubar masa gidan."
"Yaya Abdul makaranta kaje ko sana'a."
Murmushi Abdul yayi
"Mahfuz kenan dan naje makaranta sai kuma na zauna kara zube?."
"Hakane Allah yayi albarka."
"Yaro yaro ne,ƙarshen ka ce tazo Abdul dan kana ɗan uwana ba zan taɓa rufa maka asiri ba tunda baka san halacci ba."
A rai Aliyu yayi maganar zahiri kuwa haɗe baki sukayi wajen faɗin.
"Amin."
Ba ayi sati ba Azeezat ta tare a gidan Alhaji Mamu,part na musamman aka samar mata mai kyau sosai bayan kwana biyu ta nemi a ɗauƙo mata mai aiki Alhaji yace zai sa akawo mata ƴar aiki daga kauye nan tace bata so akwai wata mata da ta santa zata ɗauko bayan kwana biyu sai ga Kareema ta zo a matsayin ƴar aiki tare da Yasmin.
Kamar koda yaushe tana zaune ƙarkashin bishiyar mongue tinaninta bai wuce yadda zata ƙare karshen shekara tare da jarabebben Alhaji ba duk da kwana biyu ya sarara mata,gefe guda kuma jimamin mutuwar mahaifinta ne ke azabtar da ida.
Hangoshi tayi yana ƙarasowa inda take tuni ta goge guntun hawayen dayake ƙokarin silalowa dan karya fahimci kuka take.
Ɗan ƙaramin duka ya kai mata a wasa ya ce
"Kin bani wahala sai nemanki nake ashe anan kika ɓoye."
"Ba ɓoya nayi ba hutu nazo."
"Ko?."
"Ae meyakawo ka wurina ba nace karka sake zuwa inda nake ba."
"hhhm kema kinsan hakan ba abu ne mai sauki ba,yanzu dai tashi Alhaji zai gabatar mana da amaryarsa,kuma nima ina miki albishir da ce wa zanyi aure."
"Wa zaka aura?"
Ta yi maganar cikin yanayi na rashin jin daɗin jin labarin.
Cikin wasa Mahfuz ya ce
"Ya naga kin haɗe rai ko ba kya son auranne.?"
Taɓe baki tayi ba tare data ce komai ba tayi hanyar da zai sa da ta da cikin gida,biyota shima yayi fuskarshi ɗauke da walwala yana mai kudurtawa a ransa haka zai tayi har sai ya tabbatar da abinda yake tinani gaskiya ce.
Suna shiga suka tarar da ko wa ya zo su kaɗai ake jira,cikin ladabi Kudrat ta samu gefe guda ta zauna tare da sunkuyar da kai,zama shima yayi setin ta cike da jin daɗi ko wanne motsi tana idonsa a kanta.
Tun shigowarta Aliyu ya zuba mata manƴan idanunsa babu ko giftawa kasa hakuri yayi saida ya tambayi Ammar wacece ita.
"Ƴar aiki ce itama."
Ya basa amsa a taƙaice.
"Wow ina kamu."
Cewar Aliyu cikin farin ciki.
"Me...mekake nufi."
"I mean i'm in love with her and i'm ready to marry her."
Wani mugun ƙulli ne ya sarke zuciyar Ammar,kansa ya ɗau zafi amma sai ya nuna hali na jarumta.
"Okay Allah ya baka ita."
Aliyu zai ƙara magana yayi gaggawar faɗin
"We will talk letter."
Daga nan babu wanda ya ƙara kula wani cikinsu. Sai Ammar dayake satan kallan Kudrat jifa-jifa.
Alhaji Mamu ne yayi gyaran murya duka suka maida hankalinsu garesa.
"Da farko dai ina godiya da Allah yasa ɗana Abdulmalik ya dawo gida bayan tsawan lokaci daya ɗauka baya tare damu,kamar kullum ban cika yin dogon zance ba yau ma hakan ce zata kasance a takaice yau zakuga tsaleliyar amaryata domin ku san juna."
Kurbar giya yayi tukun ya ƙara faɗin
"Amarya ba kya laifi,buɗe kuma ki ɗago su kalle ki."
A hankali ta fara yaye mayafin tana mai murmushi yayinda su kuma sun kafe ta ido ko wa burinshi yaga fuskarta.
Cikin yanayi na firgici Abdul ya tashi a gigice yana nuna ta da yatsa bayan ta yaye mayafin ya ce,
"Azeezat!"
"Azeezat!"
Cewar Kundrat.
"Azeezat."
Aliyu ma ya ɗaura cikin yanayi na tashin hankali.
"D..dama kunsan juna ne.?"
Cikin rashin fahimta Alhaji yake tambayansu.
Rasa ƙiran wa zata fara amsawa tayi tsoro-tsoro da ido ,Ammar ne ya masu alamar su zauna kuma kada su bari Alhaji ya fahimci komai.
"Aa Alhaji dama munyi makaranta ɗaya ne shine abin ya bamu mamaki."
Yaya Ammar ya faɗa cikin inda-inda.
Numfashi ya sauke yace
"Okay, Hajiya Amina baki ce komai ba."
Da sauri Kareema ta ɗago dan ta gane wa idanta wacce Aminar. Ganinta yasata fashe da kuka tana nunata ta kasa magana.
Kallanta suke cike da rashin fahimta lokacin da Hajiya Amina ta saka ta a ido sai da ƴaƴan cikinta suka kaɗa.
Dama yarinyar nan tana raye? Bana saka a kashe ta ba?."
Bata san zancen ya fito fili ba sai ji tayi ana salati.
Alhaji Mamu zaiyi magana giya ta fara aiki a wurin bacci ya ɗauke sa sannan suka samu damar baje kolin zanjen dan su warware abinda ke ɓoye.
Ammar ne ya fara magana kasancewar shine babba.
"Kudrat dake zamu fara a ina kika san Azeezat da ganinta ya firgita ki"
Cikin kuka tace
"Yayata ce uwa ɗaya uba ɗaya."
Abdul tun kan azo kansa ya soma rawar ɗari,duk sanyin ac sai da jikinshi ya jike da gumi sharkaf.
"Aliyu ina jinka wacece Azeezat a ina ka santa."
"Na san Azeezat dalili kuwa shine na nemi soyayyarta amma taki amince wa bayannan kuma akwai wata sirri tsakaninsu da ɗaya dake cikinmu."
"Abdul saura kai."
Kansa a ƙasa hawayen baƙin ciki na ƙeto masa,lallai Azeezat wato dan na guje mata shine zata auri mahaifinsa amma ta gama dashi a rayuwa.
Cewar Abdul cikin rai.
"Kai muke sauraro fa sauri muke ga case ɗin Kareema da Hajiya dama na faɗa maku ce wa ban yadda da ita ba."
Zuru-zuwa Hajiya Amina tayi batada ta ce wa ta riga ta tonawa kanta asiri.
"Yaya Ammar Abdulmalik ba zai iya ce wa komai ba,domin bashi da hujja da zai ƙare kansa kan laifukan daya aikata,Azeezat budurwarsa ce hakan ma bashi ne abin haushi ba ya maida ta tamkar remote ɗin wasan yara juyata yake son ransa. Azeezat sun jima suna soyayya da Abdul a kansa ba taji bata gani hatta iyayenta basuda ƙima a idonta Abdul yayi amfani da ƙarfin so da take masa ya cutar da ita ya mata ciki daga karshe ya gudu ya barta bayan ya sa ta ƙarɓo kuɗin ɗan uwanta ta basa,wannan ƴar dake hanun Kareema ƴar Abdul ce wanda suka haifa da Azeezat idan nacigaba da faɗa maku mugayen hallayar Abdul ranku ne kawai zai cigaba da ɓaci."
Firgici da tashin hankali ta hanasu faɗar komai hakan yabawa Aliyu damar amayar da dukkanin abinda ke ɓoye.
"Baton Hajiya Amina kuwa tsuhuwar matar baban Kareema ce wanda suka haɗa baki da Alhaji suka kashe shi,bayannan suka kashe mamarta tare da kwashe dukiyarta."
Wurin duk ya kauraye da ihun kukan su kowa da yadda yake jin zafi a rai.
Comment
Vote
Share nd like pls
Cute hapCy ce 😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
Page 27~28
___________📲 Yaya Ammar ne ke ƙokarin dakatar da su amma babu wanda ya kulasa cikinsu.
Cikin sheƙar kuka Abdul ya ce,
"Dan Allah kuyafe min wallahi sharrin shiɗanne ku rufamin asiri banida inda zanje bayan cikin ku."
"Babu wani sharrin shaiɗan ka biyewa son zuciyarka dai,yanzu idan ƴarinyar ta taso wani irin labari zata tadda? Idan kuma akayi rashin sa'a Azeezat nada cikin Alhaji fa? How can you imagine...."
"Yaya Ammar wallahi....."
"Ya isa Abdulmalik,ka riga ya ƙeta iyakarka kayi wasa da damarka duk da nasan lalacewarka nada nasaba da rashin kulawar Alhaji amma wannan abinda ka aikata son rai ne."
"Ba iya son rai ba Yaya Ammar,harda tsantsar butulci,yaudara,cin amana bayan aminci uwa uba ga rashin tsoron Allah da jahilci."
"Dan Allah kuyi ha....."
Ya kuma fashewa da kuka mai cin rai.
Babu wanda ya kulasa Aliyu ya juyo ya fuskanci Hajiya Amina da duk tsoro ya lulluɓeta.
"Ke kuma ki tattaro dukiyar Kareema kafin nan da rabin sa'a ko na mika ki court maciya Amana kawai."
Bakinta na rawa ta ce
"A...a yanzu nan zaku gani."
Da sauri tabar wurin dan zuwa ɗauko kuɗaɗen.
Mahfuz na kusa da Kudrat sai rarrashinta yake,Kareema ma na dunkule sai yanzu take kukan bakin cikin rashin iyayenta.
Ƙaɗa kai Aliyu yayi yana jimami gami da bakin ciki ya ce,
"Kuyi hakuri Kareema da Kudrat,nasan ba abune mai sauki ba amma ku daure in shaa Allah ƙarshen bakin ciki ta zo, Kai kuma, "
Ya dawo ga Abdul dake durkushe ransa na sosa,
" Ka ɓace daga mu tun kan na ƙira maka jami'ai,babu mu babu kai."
"Yaya wallahi na tuba kuyafemin sharrin shaiɗan ne."
Wuƙa Ammar ya ɗauko yayi kansa da gudu,a guje Abdul ya bar gidan ko takalmi babu sai kuka yake.
Bayan sun huta kowa ya nutsu Yaya Ammar ya danƙawa Kareema dukiyarta,batayi wani farin ciki ba gani take tamkar jinin iyayenta ne hakan yasa ta yanke shawarar komawa gidan su Kudrat ta kuma bawa Abba kuɗin.
Sun yaba da hukuncin data yanke dan su ma babu inda zasuje fiye da gidan Abba tunda dama abokin Alhaji Mamu ne.
Kowa yayi na'am da shawarar Yaya Ammar yake tambayar Azeezat,
"Azeezat idan kin shirya komawa gida tare damu,muna maki maraba kuma in shaa Allahu zamuyi iya ƙokarin mu wajen ganin su Ummi sun yafe maki,domin kada ki ƙara fadawa halin nadama."
"Gaskiya bayyane take sai dai idan zaki ki bi,Abdul gudu yayi ya barki yakamata ki fahimci hakan kuma bazai ƙara zuwa gareki ba kina da damar da zaki koma gida Azeezat kada kiyi wasa dashi."
Yaya Aliyu ma ya ɗaura.
Shiru tayi na ƴan mintuna daga bisani ta ce,
"Abinda kuke faɗa ba haka bane,Abdul yana ƙaunata haryanzu kuyi tafiyarku ni bazan koma gida ba."
Cikin halin ku in kula ta faɗa.
Kallanta suke cike da mamaki,anya akwai zuciya a ƙirjin Azeezat kuwa?
Tambayar da kowannensu yake saƙawa a rai.
Ya buɗe baki da niyyar ƙara magana tayi saurin ɗaga masa hannu,
"Idan kana tinanin gaskiya kake faɗamin to ka rike abarka,watakila ya maka amfani a wani wuri amma ba ga Azeezat ba kaji Ammar."
Ɗage kafaɗa yayi alamar ko ajikina,ya fuskanto su Kudrat ya ce,
"Ku tashi ku fara shiryawa jirgin yamma zamu bi zuwa Yobe."
Cikin zumuɗi Kudrat tayi ɗaki da gudu,fuskanta kaɗai ya isa ya faɗa maka tana cikin farin ciki.
Mikewa tayi zata wuce ta ta ɗakin taji Azeezat na faɗin,
"Ina zaki tafi min da ƴa? Bani ita idan kina so kiyi zuciya ki haifi taki."
"Ba sai kinyi min gori ba ga ƴarki."
Ta mika mata ta wuce.
Daga Azeezat sai Alhaji Mamu da haryanzu bai farka ba cikin gidan,sai dai kafin su tafi sun siyarda duk wasu kayan amfanin gidan kama daga kayan abinci da sauransu.
Ƙarfe shida da wani abu suka isa ƙofar gidansu Abba,tun daga waje Kudrat ke kiran sunan Ummi tana kuka.
Tana alwala ta jiyo muryarta tuni hawaye suka so ma zuba ji tayi an faɗa jikinta ana shekar kuka babu kakkautawa.
Sosai sukayi mai isarsu kafin suka dai-daita nutsuwa duk da haka Kudrat bata bari ba,Yaya Aliyu ne ya bawa su Abba labarin abinda ya faru harda yadda sukayi da Azeezat,fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce,
"Ku daina sa Azeezat a sahun masu hankali don bata dashi fatanmu dai Allah ya shirya ta,sannan inaso ku ɗauke ni tamkar mahaifinku ku manta da dukkanin kuncin da Mahaifinku ya saka ku da abinda ɗan uwanku Abdul ya aikata in shaa Allahu komai ya wuce muna masu fatan shiriya."
Godiya sukai masa sosai,a ka buɗe masu part na Kareem su zauna nan take Kareema tace wa Yaya Ammar ya siya masu babban gida da kuɗinta wanda zai ishe su baki ɗaya,sauran kuɗin kuma yasan yadda zaiyi ya fito da Kareem.
"Allah ya maki albarka ƴata,sai dai Kareem ya rigamu gidan gaskiya."
Abba ya faɗa ƙamar mai shirin yin kuka.
"A'a Abba wallahi Kareem bai mutu ba a jikina nake ji."
Cewar Kareema muryarta na rawa.
"Inada labarin Kareem Abba,a halin yanzu ina bincike Allah ya haɗani da wani Barrister kuma yayi min alƙawarin fito dashi."
Numfashi mai nauyi Kareema ta sauke,"Allah yasa kana raye Kareem."
Tayi maganar a rai.
"Aliyu an riga an faɗa mana Kareem baya raye,kuɗinka kawai zaici."
"Bamu tabbatar da hakan ba Abba sai dai akoda yaushe mu kasance masu kyautata zato."
"Allah yasa a dace."
"Amin thumma Amin Abba."
Dukkansu suka amsa.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Washe gari ya shirya zai fita ta ce sam sai dai su tafi tare,Ummi da Umma sunyi-sunyi ta zauna amma fur taki babu yadda ya iya hakanan suka kama hanya tare.
Mintuna kalilan ne suka ɗaukeso zuwa Office na Barrister Haladu jega,zaman rabin awa sukayi kafin ya basu damar shigowa daga ciki.
Cikin girmamawa Aliyu ya gaishe sa tare da masa tunin abinda ya kawo su ga mamakinsa sai Barrister ya nuna tamkar bai taɓa sa Aliyu ya ido ba,babu bayanin da Aliyu bai masa ba amma yaki, daga ƙarshe ya ce su bada 15million kafin ya san yadda za a yi ya buɗe case ɗin idan yaso sai suji labarin yana raye ko a'a.
Aliyu ranshi tamkar zai fice daga ƙirjinsa a zuciye ya bar office ɗin,ido kawai ta bisa dashi harya fice daga nan ta dawo da hankalinta ga Barrister tana kuka ta ce,
"Dan Allah Barrister ka taimaka min zan iya rasa raina matukar ba a fito min da Kareem dina ba."
Ajiye takardar hanunsa yayi tare da zare glass ɗin idonsa.
"Wow! Mijinki ne da idan babu shi zaki rasa ranki?."
Kafe sa da ido tayi bata ce komai ba.
"Tsawan lokacin da ya ɗauka ba tare da ke ba meyasa baki rasa rannaki ba,fice min daga office da Allah."
"Dan Allah,dan Annabi dan matsayin iyayenka Barrister ka taimaka min."
"Babu wanda za a haɗasa da Allah da manzonsa kuma ya kauda kai sai kafiri,dan haka na amince zanyi iya koƙari na wajen samo maku ainihin labarin inda Kareem yake amma fa bisa wata yarjejeniya."
"Nagode Barrister a shirye nake da amincewa da duk wata yarjejeniya indai za a fitar dashi."
Mika mata card yayi,sunan Hotel ne da numban ɗaki ya ce,
"Gobe nake son ganinki."
"Amma ƴallaɓ...."
"Stop! Idan bazaki iya ba have a way ba dole bane."
"Shikenan na amince yanzu ka ƙira Aliyu kace masa ka yadda zaka taimaka mana ba tare da ko sisi ba dan bana so ko wa yaji,ya zama sirri tsakaninmu dan Allah."
Cikin kuka sosai Kareema ke magana.
Ƙiran Aliyu yayi yace ya amince zuwa jibi zasuji abu ɗaya ya kuma basa hakuri, cike da murna suka koma gida banda Kareema da take cikin yanayi na firgici da tashin hankali.
Comment
Vote
Like nd
Share pls
Cute_HapCy 😉
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dedicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
*Whatever you want in life, other people are going to want it too. Believe in yourself enough to accept the idea that you have an equal right to it.*
Page 29~30
__________📲Misalin karfe shida na safe ta shirya tsaf cikin doguwar hijabi fuskar ta rufe da nikab, fitowarta tayi dai-dai da fitowar Umma daga kitchen cikin ladabi Kareema ta ce"Ina kwana Umma." "Lafiya ƙalau ƴata,ina zuwa haka da sanyin safiyar nan." ta amsa tare da jefo mata tambaya,dukar da kai Kareema tayi ta shanye kukan dake shirin zuwar mata ta ce "Umma saloon za ni." "Haba Kareema ai kya bari gari tayi haske idan ya so Yayanku ya kai ki ko?." "A'a Umma bana so layi yayi yawa ne kuma akwai inda zanje bayan nan." numfashi Umma ta sauke bata yadda da yanayin Kareema ba sai dai takura mata da tambaya ne bata so hakan yasa ta ce "Adawo lafiya ki kula sosai." Amin ta amsa ta fice daga gidan.
Kukan zuci take harta isa Hotel ɗin, tsayawa tayi bakin ƙofar ɗakin daya umarce ta ta sauke nannauyar numfashi ta ce "La haula wala kuwwata illa billah" ta goge siraran hawayen daya sauka kan fuskar ta, knocking tayi babu jimawa ya buɗe,rintse ido tayi yayin da ta ga yanayin shigarsa "Allah wadaran naka ya lalace." ta faɗa a rai tana mai bakin ciki mara misaltuwa tare da mugun jin haushin sa.
"Ƴammata barkan ki dai mai kike son sha ko ci a kawo maki.?" yayi maganar yana ƙokarin cire ɗan ƙaramin boxers ɗin dake jikinsa,lura da abinda yake ƙokarin yi ne yasa Kareema shiga tsananin tashin hankali,manne wa tayi jikin bango tana kuka mai tsoma rai "Dan Allah Barrister ka taimaka min kada isar ka tasa ka aikata hakan na roke ka." tamkar ba da shi take ba ya fara matsowa inda ta rakuɓe zata gudu ya damko ta,ɗaga ta yayi tana kokarin zille masa amma ta kasa kuɓucewa daga garesa,cilla ta kan lallausar katifar yayi ya hau yana murmushin mugunta.
Lulluɓe jikinta da blanket tayi "Dan Allah Barrister na rokeka ka da...." bata ƙarasa ba sai ji tayi ya manne ta a jikinsa,kokawa suka fara tanayi yanayi abinka da ƙato sai da tayi laushi ligis kafin ya fara aika mata sakonnin haram, Kareema kwak'ƙwaran motsi ta kasa tana ji tana gani ya cinma mummunar kudirinsa a kanta.
Raina ne ya soma sosa nayi kuka sosai ganin bazan iya jure wa ba nayi gaggawar ficewa daga ɗakin zuwa gidan su Umma.
Cikin farin ciki na tadda su zaune kan dining,wayar Yaya Aliyu ce tayi ƙara duka suka nutsu,bakowar number ce hakan yasa yaki ɗauka dan bai fiye ɗaukar new number ba.
Ganin ana ƙira yana rejecting,cikin kulawa Ummi ta ce "Ka ɗauki wayar mana Aliyu." "Ummi bansan numbar ba shiyasa." murmushi tayi ta ce "Idan ka ɗauka ai zakaji ko..." bata gama faɗa ba ƙiran ya sake shigowa har ya kusa tsinkewa kafin ya ƙara a kunne "Ina magana da Aliyu Haidar?" "Ae shi ne,lafiya?" "Good,kana magana da Barrister Ishaku ni nake handling na case ɗin Abdulkareem kuma abokinsa ne ni,da yardar Allah mun gano waɗanda sukayi kisan yanzu haka an sake Kareem sai dai akwai wasu abubuwa da bamu kammala ba ina bukatar ganinka yanzu." Aliyu zuciyarsa tamkar an zuba kankara wani sanyi ne ya ratsa dukkanin sassan jikinsa, ya kasa ce wa komai sai washe hakura,dukansu shi suke kallo cikin matsowa da son jin labari Yaya Ammar ya ce "Aliyu wani labari ne ya faranta maka haka." bai tanka ba cikin zumuɗi ya ɗauki car keys ɗinsa ya fice da ido suka raka sa suna murmushin suma.
"Hmm babu mamaki itace ta ƙirasa shiyasa kuka ga yana ta zumuɗi." cewar Mahfuz cikin wasa.
"Ai hakan ma abin jin daɗi ne dama na gaji da ganinku babu aure." Umma ta ɗaura.
"Ke ma dai kya faɗa katin-katin daku babu aure wannan ai abin kunya ne" inji Ummi ma.
"Faɗa masu dai Yaya Ammar da Yaya Aliyu nikam ga matata nan juyi kaɗan nayi ina hangota fara ƙyaƙyawa ƙirar.....hhhm bara dai nayi shiru kar wata ta fara kishi." idonsa akan Kudrat yake maganar,cikin ɓacin rai ta tashi su Ummi sai dariya suke irin nasu na manƴa "Yakamata ko wanne cikin ku ya fidda mata zuwa ƙarshen watannan." karo na farko da Abba yayi magana kenan.
Sunkuyar da kai Yaya Ammar yayi ya ɗan sosa keya "In shaa Allahu Abba bada jimawa ba." "Allah ya sa." ya faɗa tare da shigewa ɗakinsa, su Ummi ma sukayi tasu ɗakin.
"Kaga tafiyata nima zanje ganawa da masoyiya ta." "Kai Mahfuz wai maganar wacce yarinya kake, wacece masoyiyar ta ka." "Kada ka damu babban Yaya very soon zakaji ko wacece keep waiting." bai jira cewarsa ba ya bar wurin cike da farin ciki.
Ganinta yayi zaune ƙarkashin bishiyar mango dake garden na su rike da takarda tana zane nutsuwarta gaba ɗaya na kan aikin da take har ya iso bataji ba "Me kike zanawa?" taji tsoro sosai har kamar zata gudu dan batayi tsammanin mutum lokacin ba "Haba Mahfuz me haka duk ka tsorata ni." cikin tsawa take masa magana "To! Maida wukar ba yaƙi nazo ba." "Wato ma matsifaffiya ka ɗauke ni da har kake ce wa maida wukar." "Ya salam me yayi zafi ne Kudrat ban sanki da faɗa ba da alama wani ne ya ɓata maki rai faɗa min wanene shi na ɗauki mummunar mataki a kansa." tushe kunnenta duka tayi dan ƙar taji abinda yake faɗa.
"Kudrat toshe min kunne kike? Shikenan dama waya na siyo mana nida ke,gashi." ya ajiye wayar akan table ɗin da take zaune,cikin sanyin jiki ya ƙara faɗin "Na barki lafiya,idan kuma na ɓata maki rai ki gafarce ni." idonsa cike da hawaye ya barta,kallo ƙawai ta bisa dashi tana jin haushin kanta "Mtw meyasa..." ƙamar zatayi kuka ta faɗa,kawar da tinanin tayi ta cigaba da za na suffan da take.
Kudrat! Kudrat! Taji Ummi na ƙwala mata ƙira, ɗaki ta fara zuwa bataga kowa ba,har ban ɗaki ta leƙa wayam.
Tana cikin dube-dube taji kamar hayaniya na tashi a parlour da sauri ta fice,Kareem ne durkushe Ummi da Umma sun rungumesa,su Yaya Ammar da Aliyu na gefe suna tayasu kuka,tsintar kanta tayi cikin wani irin yanayi da gudu ta faɗa jikinsu tana sheƙar kuka.
"Yaya ashe zamuga juna? Yaya dama baka mutu ba? Yaya suwa suka maka haka? Yaya.... " kuka ya ci karfinta ta kasa cigaba, Abba kam sai hamdala da godiya ga Allah yake bai taba tsammanin Kareem na raye ba, bayan sun gama jimamin rashin sa ya huta Aliyu ya ce "Alhamdulillah mahakurci mawadaci, ciki da gaskiya wuka baya hudashi ka gode wa Allah daya farfado da Dagash har ya wanke ka." Numfashi Kareem ya sauke haryanzu ya kasa gaskata yanayin daya ke ciki "Ya Allah nagode maka daka sanya min juriya da yarda da kaddara, Allah ka bani ladar hakurin danayi, kayimin sakkaya tsakanina da duk wanda ya min wannan sharrin." "Amin ya Allah, Kareem makiyinka na tare da kai sai dai kayi koƙarin nesantar da kanka da shi." "A iya sanina banida abokin faɗa,ban taɓa neman mutum da sharri ba,ban san me suke nema a wurina ba Aliyu." "Ranka suke nema Kareem kuma ba kowa bane fa ce Abdulmalik." "What! Abdulmalik kuma? Kai ina ko duniya zata taru tana faɗa min wannan kalmar bazan taɓa yadda ba,Abdul yafi kowa so na ni shaida ne." kallon Ammar da Mahfuz yayi cikin tashin hankali ya ce "Ammar,Mahfuz shin kun yadda da abinda Aliyu yake faɗa?" "Ƙwarai da gaske,duk abubuwan da suke faruwa da kai kama daga ɓatan files na Alhaji Dagash har zuwa kashe iyalansa duk dasa hanun Abdul,hatta sa ce Kareema." Rasa abin faɗa yayi tsabar tashin hankali "Yanzu ina yake,ina Kareema kuma?." cewar Kareem cikin sanyin murya.
Aliyu ne yayi gyaran murya ya fara basa labarin yadda abubuwa suka gudana a bayansa,Kareem yayi jimami sosai jin Abdul ne saurayin Azeezat har ta haifa masa ƴa,ji yake idan har zai yi do huɗu da Abdul babu abinda zai hana ya so ka masa wuka a ciki.
Ba itace ta zo gida ba sai gabannin Magrib,idonta yaki daina zubda ƙwalla zuciyarta tamkar ana babbaka shi haka take ji.
"Kareema! Kareema! Labari mai daɗi Kareem ya fito yana ɗaki." jefar da jakar hanunta tayi ta ce "Da gaske? Bana son wasa Kudrat." Cewar Kareema cikin muryar irinta masu kuka, "Idan ƙarya nake kar rabbi ya min gafa..." bata tsaya jiran ƙarshen zancen ba dan ta tabbata gaskiya ce,ihu take tana kiran sunansa duk gidan ya ɗau muryarta,tsaye ta ganshi ya naɗe hanunsa a kirjinsa fuskarsa shimfiɗe da murmushi, "Kareeeem!" ta faɗa da gudu ta je ta rungumesa tana kuka sosai.
Comment
Vote
Like nd share pls
Cute_hapCy ce☺️
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: https://chat.whatsapp.com/Be0bxCflxHwLRQTyYRI5La
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
_Gaisuwa ta musamman ga👇_
*AISHA A*
*MMN BILAL*
*SAFOURA*
*FENAH*
*MRS ZAHRADDEN*
*NAPEESAT*
*NAMECY NA*
*KULIYATA🤭*
*TEMZY*
*ANTY ZEE*
_Cute na gaishe ku kyauta_
Page 31~32
_____________📲Rasa yadda zaiyi ya rarrasheta yayi gashi kukan nata a rai yake ji, ganin taki dainawa ya shiga bubbuga bayanta yana mata magana a kunne cikin sanyin murya,sake shi tayi ta wuce ɗaki a guje cikin yanayi na tashin hankali ta faɗa kan gado ta cigaba kuka mai cin rai wanda baya fita. "Ina ma ban amince da zancen Barrister ba,na zubda mutuncina gashi an saki Kareem ba tare da sa hanun sa ba,ya Allah na tuba ka yafe min,Allah kada ka sa idan Kareem ya ga no yaƙi amincewa dani, Barrister ka cuce ni Allah ya isa tsakanina da kai, kasa na rasa abinda nake taka ma dashi saboda son zuciya irin ta ka, bazaka taɓa gamawa da duniya lafiya ba azzalumi kawai..." ji tayi ana ƙokarin buɗe ƙofar ɗakin da sauri ta shanye kukan ta dai-daita nutsuwarta.
Ƙare mata kallo tayi cikin yanayi na tausayawa ta ce,
"Kareema kukan nan ya isa haka, ba gashi Allah ya dawo dashi lafiya ba,kamata yayi kifi kowa farin ciki amma sai nake ganin tamkar zuwanshi damuwa ta ƙara maki."
Numfashi ta sauke bata ce komai ba sai ƙara dunkulewa waje ɗaya da ta yi.
"Je kiyi wanka zamu fita shan ice cream." cewar Kudrat tana koƙarin tashi. daurewa tayi ta ce "Bazanje ba Kudrat na gaji bacci zanyi." cike da tausayinta ta ce "To shikenan wani lokaci ma je tare."
A hanya ta ci karo da Mahfuz hanunsa rike da waya,sakar mata murmushi yayi yayin da suka fuskanci juna ya ce
"Zumuɗi ta sa kin mance wayar a garden shi ne na ɗauko maki." tsaye take kanta a ƙasa kamar ba da ita ya ke ba,ɗan murmushi ya sake ya ƙara faɗin "ƙarɓi wayar ko." "Ka fara nunawa su Abba tukunna." ta faɗa tamkar mai shirin yin kuka. "Kuka baya maki wuya Kudrat,ai sai da na fara nuna masu tukunna,maza amshi bana son jayayya." ya faɗa cikin dagiya. A hankali ta mika hannu ta ƙarɓa tare da ce wa "Nagode." Haryanzu da murmushi a faskarsa bai ƙara faɗin wani abu ba sai hanya daya bata ta wuce.
Cikin murna ta faɗa kan gado tana ƙarewa wayar kallo,yau ce karo na farko da ta taɓa mallakar wayar kanta abin ya mata daɗi sosai,sai da ta fara nunawa Ummi da Umma ta kuma wucewa gun Abba ma ta shaida masa duk suka sa mata albarka. Dawowa ɗaki tayi ta cigaba ta kallon abarta ba tare data kunna ba,a hankali taji an turo kofar ɗakin ta ta ɗago da sauri ganin Ummi ce sai ta sauke numfashi gami ta ce wa "Ummi ke ce,meyasa baki aika an ƙirani ba zaki taho da kanki bana so ki dinga wahalar min da lafiyarki fa" Murmushi Ummi tayi tana ƙara jin son ƴar tata cikin rai,"Abincin Yayunki zaki kai ko kin manta ne." "laa wallahi na sha'afa ne bara nazo na kai." fita Ummi tayi Kudrat tabi bayanta.
Bakin ta ɗauke da sallama bata karasa shiga ba sai da suka amsa mata ganin hanunta rike da katowar try yayi saurin tarota.
"Kai ya zaki ɗauki abu mai nauyi haka gaskiya bana so ki daina." cewar Mahfuz yana koƙarin karɓe tryn daga hanunta,bata ce komai ba ta mika masa ta fice. Ammar da Aliyu da reactions na Mahfuz kan Kudrat na ɗaga masu hankali tuni sun haɗe rai. Bayan sun gama cin abinci Ammar yake ce wa Mahfuz "Wai wani irin alaka ce ke tsakaninka da Kudrat?" "Yaya! Na faɗa maka idan lokaci yayi zaka ji."
"Yaushe na fara wasa da kai zaka faɗan ko kuwa?" Cike da ɓacin rai Yaya Ammar ya faɗa,sosai Mahfuz yayi mamaki ganin Yayanna sa bai zo da wasa ba ya ce "She is my friend shikenan." yana faɗa yayi saurin barin ɗakin yana dariya.
"Yakamata na faɗi abinda ke raina tun kan na makara." Aliyu yayi maganar cikin ransa. "Me zai faru idan soyayya ce tsakanin Kudrat da Mahfuz? Dole na sami Abba gobe na faɗa masa bukatata ayi a gama." Yaya Ammar ma da tasa tunanin." "Guyz ni zan kwanta sai da safe." Maganar Kareem ce ta dawo da su cikin hayyacin su Aliyu yayi ƙarfin halin ce wa "Owk." "Bacci kuma?" Inji Ammar. "Ae na gaji sosai."Inji Kareem
"Shikenan sai da safe." Ammar ya sake fada, ya amsa da "Allah ya tashe mu lafiya." ya kwanta.
Mahfuz ko yana shiga dakinsa cikin rawar jiki ya dannawa Kudrat ƙira har wayar ya gama ringing bata dauka ba, kira yake akai-akai har sai da ya kira sau goma kafin ta ɗauka.
Yes ya fada da karfi bayan ya ƙara a kunne.
Shiru ne ya biyo baya can ya ce "Kudratuna ya kike so nayi ne ehm? Kinsan abinda ke tafe dani amma sai ki dinga nunawa kamar bakisan komai ba why?" Ko alamun motsin rai babu kamar da gunki yake waya, music ya shiga ya kunna wakar hamisu breaker, na SO NE tana ji ta ce "Yaya saboda me zaka kirani ka kunna min waka so kake ka toshe min kunne ,ka kashe nidai" "Yawwa dama dan kiyi magana na kunna kuma naji muryarki, yeeee na miki wayo."
Dariya ne ya zo mata ta sa hannu ta toshe dan kar ya ji,kasa-kasa yaji tamkar kuka take,hankalinsa ne yayi mummunar tashi kamar zaiyi kuka ya ce "Na ɓata miki rai ko? Kiyi hakuri bansan zai saki jin haushi ba,farin cikin ki shine nawa idan na zamo silar ɓata maki walwala cikin darennan bazan taɓa jin dadi ba."
Shiru yayi still yana jiran cewar ta but taki ce wa komai. Numfashi ya sauke zuciyarsa na jin wani iri "Kudrat tun ranar dana fara ganinki kibiyar sonki ta yi min mummunar suka,bana iya aiwatar da komai ba tare da tinaninki cikin ƙwaƙwalwata ba,kin zamto tamkar haske dake haskaka duniya ta ki yadda dani domin zan baki kulawa ta musamman,zan maidake tamkar sarauniyarda tayi fice,dan Allah Kudrat ki amince dani na miki alkawari bazaki taɓa yin kuka dani ba." Numfashi mai nauyi ta sauke"Hmmmm Mahfuz gaskiya bazan iya......" "Kada kiji tsoro ku kunyar faɗa min,indai ba kya so na bazan tilasta miki ba,na miki alkawarin zan rabo dake bawai na daina sonki ba a'a, sai dai soyayyar da nake maki ta kai na iya sadaukar maki da farin cikina baki ɗaya,babu ɓoye-ɓoye dan Allah ki faɗamin matsayin da kika bani ko zanji saukin raɗaɗin da nake ji." "Yaya Mahfuz...." Sai kuma ta kara shiru.
"Inajinki ƙanwata bakya so na ko." da sauri ta kaɗa kai tamkar yana kallanta. "Kinyi shiru haka ne ko?" "A'a." "To menene?" "Amma kasan ba a kin mutum ko,musamman ma kai da kake ɗan uwana a musulunci kuma wanda ya taimaka min a lokacin da nake tsaka da neman taimako." "Ba irin wannan son nake nufi ba." "Wanne irin so kenan?" Rintse ido yayi ya furzar da iska mai zafi,tana jin sa sai dariya take kasa-kasa. Muryarsa da bata fita sosai ne ta dai-dai ta mata tinanin ta ta hanyar faɗin "Kudrat zaki aure ni?" taɓe baki tayi ta ce "Wannan wanne irin tambaya ne amsa kake son ji ko? to bazan aure ka ba ka ƙyaleni nayi bacci sai anjima." jin kansa yayi cikin yanayi mara misaltuwa,baƙin cikinsa ya yawaita salon yadda tayi maganar babu wasa ko kaɗan sai ma tsantsar ɓacin rai,bai ƙara tanka wa ba ya so ma rera kuka mai cin rai ba tare da ya kashe wayar ba. Sautin kukan sa taji yana fita a hankali ta ce "Yaya Mahfuz kuka kuma? Dan Allah ka daina wallahi ina so....." da sauri ya shanye kukan sa ya ce "Kina me Kudrat? Karasar min ko zan ji sauki." "Inaso nayi bacci Yaya." "Abinda kike son faɗa kenan?" "Eh" ta faɗa a takaice. "Shikenan ki ƙwanta abinki sai da safe,karki manta kiyi addu'a before going to bed kinji." da kai ta amsa tare da ajiye wayar.
Gallery ya shiga ya na kallan pictures ɗin da sukayi tare time ɗin bata fara guje masa ba. Duk wayar da suke a kunnen Aliyu ya zo ɗaukar System ɗinsa a ɗakin Mahfuz, "Bani na cancanci mallakar Kudrat ba Mahfuz ne dan haka na bar maka ita kanina Allah ya sanya alkhairi ya kuma baka nasarar shawo kanta."
komawa yayi ba tare daya ƙarasa ɗakin ba. Sai gabannin asuba bacci ta ɗauke su daga Mahfuz har Kudrat.
Washe gari duka suna tare Yaya Ammar ya faɗawa Abba zancen auran Kudrat kamar yadda ya kudurta a rai zaiyi.
Sosai Abba yayi farin cikin jin haka daga garesa,ya ce "Idan ni na haifi Kudrat to na baka ita duniya da lahira ya rage gareka kaje ka nemi soyayyarta." Kallan Abba Mahfuz yake cike da tashin hankali,haka Kudrat ma take hawaye ya fara biyo fuskata gashi batada ikon jayayya da zabin Abba.
Comment
Like
Vote nd share pls
Cute_HapCy ce💃🏼
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
Page 33~34
____________📲Duƙar da kai Yaya Ammar yayi fuskarsa shimfiɗe da wadatacciyar murmushi ya ce "Abba nagode sosai Allah ya ƙara lafiya da tsawan kwana." "Amin." duk wurin suka amsa. Haɗiye kukansa Mahfuz yayi ya ƙirƙiro murmushi ya ce "Kai gaskiya ina tayaka murna babban Yaya,kayi dacen mata domin nasan ƙawata ba daga nan ba Allah dai ya nuna min wannan ranar sai nafi kowa cin abinci." ya ƙarashe da ƴar dariya suma suka tayasa.
Kudrat kanta gaba ɗaya ya kulle "ya za'ayi hakan ta kasance? Kai ina bazan bari ya faru ba,amma meyasa yafi kowa nuna farin ciki? Ko dai dama ba so na yake ba?." Ita kaɗai ke hasashen hakan a rai,gefe guda mugun haushin Ammar take.
Hira suka cigaba da yi duk da yanayin da suke ciki na tashin hankali,sai dai Mahfuz ya yi iya kokarin kawar da damuwarsa ta hanyar hira da wasa da dariya.Ganin bazata iya juran cigaba da zama a wurin ba, kamar wanda ke tausayin ƙasa a hankali ta wuce ɗaki, duk abinda take Ummi na kallanta cikin zuciyarta tana raya abubuwa daban-daban. Babu jimawa ta biyota can kuryar ɗaki ta shiga tana kuka mara sauti. Dafa ta Ummi tayi, tayi saurin ɗagowa ta zuba mata jikakkun idanunta. Numfashi Ummi ta sauke tare da neman wurin zama "Kudrat menene?" "Ummi......" sai kuma ta fashe da kuka.jawota jikinta tayi tana jinjina yanayin da ƴar tata ke ciki,ajiyar zuciya take saukewa a hankali har nutsuwarta ta dai-daita, bayan Ummi ta tabbatar da hakan ta ƙara ɗagota,ta kafe ta da ido tana son gano wani abu tattare da ita.mai-maita mata tambayar tayi "Kudrat ni mahaifiyarki ce ni ce nafi ko wa cancanta ki faɗamin matsalar ki,meyake damunki yanayinki duk ya sauya ba kya son auranne? Idan ba kya son shi ki faɗa na tabbata Abbanku bazai maki dole ba." cikin yanayi mara misaltuwa Kudrat ta ce "Ummi indai bazan yi jayayya da zaɓin Abi ba,bai kamata nayiwa Abba ba,idan nayi hakan duniya zata zageni sannan ni kaina bazan taɓa yafewa kaina ba." murmushi Ummi tayi ta ce "Allah na gode maka daka bani ƴa mai biyayya,in shaa Allahu zakiga ribar hakan." "Nagode Ummina." ta faɗa a kasa-kasa. Barin ɗakin Ummi tayi zuciyarta cike da tausayin ƴarta,sabon shafin kuka Kudrat ta buɗe tana mai jin ƙona cikin ranta musamman ma idan ta tuno da yanda Mahfuz ɗin da ke ikirarin yana sonta ya taƙarkare yana nuna farin cikinsa game da zaɓin da aka mata bayan yasan tana ƙaunarsa. "Amma ai baki faɗa masa kina son sa ba." wata zuciyar ta bata amsa. Pillow ta ɗauka ta danne kanta tana kuka mai tsanani.
Yaya Aliyu tunda aka fara zancen bai ce komai ba kuma baiyi murna da hakan ba domin yana kyautata zaton Mahfuz na son Kudrat ita ma haka,ƙiran ƴan uwannasa yayi ɗaki ya fara magana cikin nutsuwa. "Yaya Ammar a gaskiya baka mana adalci ba a matsayinka na babban Yaya a garemu,kafin ka aiwatar da wani abu,ya dace ka naimi shawararmu." cikin rashin fahimta Ammar ya ce "Sai ka faɗamin wani abu ne nayi ba tare da neman shawararku ba ya zama illa ko abin rashin dacewa." "Abinda kayi ɗazu sam bai dace ba,baka nemi shawarar yarinya ba,baka san ko tana da wanda take so ba,haka kawai zaka zo wa mahaifinta da zancen auranta bayan kasan bazai taɓa iya hanaka ba koda kuwa bata sonka." taɓe baki Ammar yayi ya ce "Dama wannan zancenne? To menene matsalar ka? In faɗa maka a takaice nayi hakan ne domin ta zama mallakina koda kuwa bata so na." "Idan ko hakane baka cika mai imani da tausayin ƴa mace ba kuma kai ba masoyin daya dace a so bane....." "Ya isa Aliyu." ya dakatar dashi cikin tsawa yana huci. "Amma Yaya Aliyu menene aibu dan ya nemi auranta,ni aganina Yaya Ammar na ƙaunar Kudrat kuma na tabbata zata so shi itama." Mahfuz ya faɗa cikin dauriya domin zuciyarsa tuni ta karye. "Ƙarya kake Mahfuz,wannan ƙarya ne,ka daina ɓoye damuwarka,fuskarka ta nuna tsantsar tashin hankali kana wayencewa ne amma ni na daɗe da sanin kana son Kudrat itama kuma kai take so." Duka suka sauke idonuwansu kansa,da sauri Mahfuz ya fara girgiza kai ya ce "A'a Yaya ba haka bane,Kudrat ƙawata ce amma ba soyayya muke ba,maganar gaskiya bana sonta da aure dan inada wacce nake so." Yana ɗago kai ya ganta tsaye a bakin ƙofa,gaba ɗaya kalamansa sun daburta mata hankali,ƙwaƙwalwarta na mai-maita mata maganganunsa "Dama ba so na yake ba? Dama ni ce kaɗai nake shirmen tinani na?" Tana ire-iren wannan tinanin taji Aliyu ya ce "Kudrat ƙaraso kamar kinsan ina bukatar ganinki." shanye kukan dake shirin zuwar mata tayi,ta tako a hankali,ta samu gefe guda ta zauna tare da sunkuyar da kai. "Kudrat ƙarya bata kamaceki ba kuma nasan baki sa ba ba,Mahfuz ya taɓa faɗa maki yana sonki ko a'a?" a hankali ta tago kai duk ita suke kallo,tuni zuciyarta ta fara harbawa wani ɓangare na raya mata ce wa ta faɗi gaskiya ko dan ta cika masu burinsu,wata zuciyar kuwa ce mata tayi _"Wani irin sakarci ne zaisa kice kina sonsa bayan da kunnuwanki kikaji ya ce ba ke yake so ba"_ Dake wa tayi, "A....a'a Yaya." ta faɗa a takaice. "Kin tabbata ku...." "Haba Aliyu,ya yarinya ta faɗa maka gaskiya kuma kana ƙara na-nata mata ko sai ka tilastata ta faɗi ƙarya." inji Ammar. Numfashi Aliyu ya sauke yana jinjina taurin zuciya irin ta Mahfuz da Kudrat,ya ce "Zaku iya tafiya." kamar jira take a bata izinin tashi ta wuce cikin sauri dama neman Kareem ta zo,tana fita ta tadda shi zai shiga ɗakin,bata bari ya gane tana kuka ba tayi saurin saukar da kai ta ce "Yaya Kareem,Kareema na nemanka tace a faɗa maka tana jiranka a garden." Yana gama sauraran ce warta yayi hanyar garden,ƙarƙashin bishiyar Guava ya ganta,duk ta rame tayi baƙi damuwa ce ɓarau-ɓarau a dukkanin sassan jikinta. Ba yabo ba fallasa ya ce "Assalamu alaikum." amsa masa tayi kasa-kasa,ɓata rai yayi ya ce "Idan ma bazaki kulani ba ai amsa sallamar wajibi ne ko?Kuma ai ke kika bukaci ganina ba ni ba,ba re kija min aji." cike da mamaki take kallonsa ya haɗe duka gira yana cin magani. "Amin wa'alaikassalam,na amsa maka Yaya Kareem mura nake shiyasa muryata bata fita." "Uhm,kince kina son ganina wani abu ne.?" sake baki Kareema tayi "Anya ba a canza min Kareem ɗina a gidan yari ba.?" ta faɗa a rai yayinda a zahiri tayi gaggawar ce wa "Yaya Kareem tunda kazo baka neme ni ba,bansan ko laifin me na maka ba,na shiga damuwa sosai lokacin dana ji labarin anka...." "Indai wannan ne zaki faɗamin to banida lokacin saurara sai anjima." shawo gabansa tayi,gwiwowinta a ƙasa ta ce "Ba wannan ba Kareem,inaso na faɗa maka kalmar da ban taɓa faɗawa wani mahaluƙi ba a doran ƙasa,inaso na sauke nauyin da na daɗe ina fama dashi a zuciyata ,Kareem ina ƙaunarka dan Allah ka amince ka aureni hakan shi zai samar min da farin ciki." "Mtswweww" ya ja dogon tsaki yana mata kallan tara saura kwata ba tare daya ce wani abu ba. "I'm saying it deep in my heart, I love you Kareem." "Nikuma nace bana sonki,bana ƙaunar haɗa inuwa da ke,fasika macuciya annamimiya tir da irin hali naki,alfarma ɗaya zan miki shine zan rufa miki asiri ko zaki samu wanda zai aure ki." yana kai wa nan yayi shigewarsa cikin gida ya barta durkushe tana kuka mai so sa zuciya.
Comment
Like
Vote nd share pls
0 comments:
Post a Comment