____________📲Kuka take sosai tana kurma ihu, tunowa tayi za a iya jiyota da sauri ta toshe bakinta,sai da tayi mai isarta before ta shiga ciki,cikin mutuwar jiki ta nufo ɗakinsa a hankali ta tura ƙofar a buɗe take hakan ya bata damar shigewa daga ciki,dube-dube ta tsaya yi ɗakin ya tsaro ga ƙamshi mai daɗi dayake tashi,ko ina ta duba ba ya nan,ƙarar saukar ruwa take ji da alama wanka yake.
Zama tayi kan site drawer ta zuba uban tagumi tana sake-sake a ranta.
"Yau ce ranar data dace na faɗa masa abinda bai sani ba game da ni." tana cikin wannan tinanin a rai taji ƙaƙƙausar muryarsa ya dakan mata kunne har sai da ta zabura.
"Ke me yakawo ki ɗakina? Wato rashin kunyar taki ta wuce yanda aka zato ko? Zaki nuna min ke cikakkiyar ƴar bariki ce,to maza ki fitar min a ɗaki tun kan na saɓa miki kammani."
Zubewa tayi ta dafa kafarsa tana kuka ta ce "Kareem dan Allah ka saurari abinda zan faɗa maka na tabbata zaka fahimce ni,banida niyyar cutar da ka..." "Cuta na nawa kuma? Nace cutarwa na nawa kuma? Sai dai a karo na uku,zaki wuce ki fita ko kuwa?." Yayi maganar da ƙarfi,bakinsa har wani kumfa yake fitarwa idonsa yayi jajur. A gigice ta bar masa ɗakin ganin yadda yake huci tamkar mayunwacin zaki.
Toilet ta faɗa ta sakarwa kanta shower still idonta bai daina zubda ƙwalla ba duba da yadda Kareem yayi ignoring nata duk da sacrifices ɗin da tayi a rayuwa domin sa. Awa uku ta ɗauka cikin toilet ƙiran sallar azahar ne ya fidda ita ba dan ta so ba.
Nafila ta fara gabatarwa raka'a biyu kafin ta yi azahar bayannan ta sake jero raka'a biyu. Addu'o'i ta karanto sosai tana mai neman yafiyar Ubangiji,nan take taji nutsuwa na ziyartar ta, bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita ba tare da auni ba.
Tana cikin baccin Kareem ya faɗo mata tayi firgit ta farka gami da zabga uban tagumi, "Amma meyasa Kareem ke faɗar mugayen kalamai a kaina? Dan na bada kai na saboda shi.....? Numfashi ta sauke tare da yin shirun ƴan mintuna ta na nazari.
"Duk da nasan na aikata kuskure babba da na amincewa Barrister,amma ai akansa nayi hakan shin na cancanci ya watsar dani? Haba Kareem think please,i did'nt deserve all this thing. Hmmm ina bukatar naje na fahimtar da shi amma yaki saurarata ya zanyi,ina zan sa raina farin ciki ƙwaya ɗaya tal da nake tutiya dashi yana nema ya zama ƙwalelena." cikin she-sheƙar kuka take magana.
Sambato tayi tayi har bacci ɓarawo ya sake sacanta.
Haka Kareema tacigaba da bin Kareem amma yaki kulata ko kallo bata ishe sa ba,ranar ta kudurci niyyar ko ta halin ƙaka sai ya bata aran lokaci sunyi magana dan haka ta sako Ummi a gaba ta rakata ɗakinsa,faɗa sosai Ummi ta yi akan kin kulata da yake kuma ta basa umarnin ya saurareta ko tayi fushi da shi. Badan ya so ba ya amince gudun ɓacin ran Ummi.
"Me kike buƙatar kiji daga gareni ki tambaya da sauri domin baki da isasshen lokaci." ɗan murmushi mai cike da takaici tayi ta ce "Kareem ina so ka fahimci ce wa ba wai da son rai na na biyewa Barrister ba,nayi hakanne dan na ceto rayuwarka,shine ya ce sai na bashi...." Bata ƙarasa ba ta fara kuka. Ko kaɗan bai san inda ta dosa ba ya ce "Wani zance kike ne Kareema? Wanne Barrister kuma a ina yake,kiyi min yanda zan gane." cike da ƙwaɗayin jin kanun zance yayi maganar. "Ha'a! Indai bai san da zancen na bawa Barrister kaina ba to akan me yake mugun fushi dani?" ta tambayi kanta. "Kareema! Me kike tinawa?." cikin e'ena ta ce "Amm babu komai." "Ya zakice min babu komai,yanzu fa kika fara zancen Barrister ya ce ki bashi kaza,ki faɗamin ko naje nayi bincike,idan ko na gano gaskiya da kaina zaki fuskanci ɓacin rai kuma sai kinyi nadamar sanina." "Kayi hakuri Kareem bazan iya faɗa maka gaskiya ba saboda nasan bazaka auri macen da ta zubar da mutuncinta a titi ba,kuma ni nayi alƙawarin kaine mijina ina son kasancewa da kai a rayuwa.....,ta faɗa rai a zahiri kuwa ce wa tayi "Tare da Yaya aliyu mukaje wurin wani Barrister mun nemi taimako dan Allah amma sai ya nuna yana neman kuɗi a hanunmu,Aliyu yaki amince wa da hakan,nikuma ina bukatarka shine na bada kuɗin a ɓoye ba tare da sanin kowa ba,shin wannan abun ya kai ka nesantar da kanka daga ni har haka?." Kallonta yake sosai yana son ya haɗa ido da ita ko zai gano wani abu,sai dai taki yadda ta ɗago kai.
"Well,ni bansan wannan zancen ba ko da nasani ma akanshi bazan yi fushi da ke ba,Kareema kece silar shiga duk wata damuwata a rayuwa." da sauri da ɗago ta zuba masa ido cike da mamaki. "Yes,ke ce kika fara satar files ɗina na wurin aiki,daga karshe kika ce a ƙasa kika tsinta,laifi har biyu,na ɗaya sata,ga ƙarya. Bayannan kika ce iyayenki ba masu zama bane ashe ƙarya kike gidan mijinki ne,kika zo kika ce anyi garkuwa da ke nan ma ashe haɗa baki kukayi da Abdul dan ku rabani da kuɗina, kafinnan ma ranar da kika bani files kin tura ɓarayi subiyoni Bank sai dai kuma shi Allah ba azzalumin sarki bane ya kare ni daga sharrin ki,ina da yaƙini kinsan wani abu akan sharrin da aka min na kashe iyalan Alhaji Dagash.waɗannan hujuji sun kai na nesanta kai na dake na har abada,bana zama da makaryaci." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,wallahi Kareem cikin abubuwan daka lissafa ɗaya ne kawai nasan na aikata shine ɗauke files kuma shima daga baya nayi nadama shiyasa na maida maka,batun iyaye kuma na faɗa ne saboda ka saurareni amma wallahi ban da su,ba gidan mijina bane banida aure idan na baka labarin zaka yadda da abin da nake faɗa." "Lala bana bukata,tun farko ban taɓa furta maki kalmar so ba bare kice na yaudareki,ki ƙara gaba."
Zuciyarta na raɗaɗi tana nadamar kasancewa a raye,ganin babu alamar zai yarda da ita ta mike a sanyaye ta bar ɗakin,tana rayawa a rai hakan ma bai san ba ta tare da budurcinta ba,idan yaji kam korarta za a yi a gidan.
Bayan sati ɗaya Abba ya tarasu baki ɗaya,su mazan ya kara jaddada masu su cire mata,ya kuma yanke ranar auran Ammar da Kudrat nan da wata biyu masu zuwa,so yake ya haɗasu baki ɗaya,Kareema na jin haka zuciyarta ta fara harbawa tana tsoron kada Kareem yaki tsayar da ita a matsayin matar da zai aura.
"Kareem naji abu mai kama da labari kun dai-daita da Kareema ko?" Inji Abba. Sosa keya yayi ya ce "Amm a'a Abba,wata ce dai idan komai ya kankama zakuji." Sauke kai tayi hawayen takaici na zuba kan fuskarta "Shikenan na rasa zaɓi na." ta faɗa a hankali. Ko shi Abba bai so hakan ba sai dai yayi shiru ne. "To Kareema sai ke ma kiyi kokari ko?" "In shaa Allah Abba." "Hmm wato ma kinada wani bayanni." Inji Kareem a rai a ƙufule. Niko nace me naka a ciki.
Aliyu da Mahfuz ma irin tambayar daya masu kenan duk suka amsa da In shaa Allah.
Abba ne yacewa su Kudrat su wuce ɗaki ba musu suka haye upstairs,kamar wanda aka basu labarin ranar mutuwar su suna shiga suka rungume juna suna kuka mai tsuma rai."Kareema na rasa Mahfuz,shikenan na rasa sa." "Kudrat gwara ke,matsalar da nake ciki tafi ƙarfin gashin kaina,Kudrat Kareem ya juyamin baya." Dukkansu cikin kuka suke zancen babu mai rarrashin juna. Ƙarar wayar Kudrat ce ya tsayar dasu,tana dubawa taga misscals uku da text ɗin Mahfuz ya na ce wa _"Ki sameni a garden."_ da gudu taje ta sameshi tsaye ya juyawa baya hakan yasa bata ga fuskarsa ba. "Baka da zuciya Mahfuz tunda har zaka iya bari wani ya mallakeni,meyasa ka tusa min sonka kuma ka gujemin meyasa,idan har kana so na kaje kacewa Abba kai ka dace dani ba Yaya Ammar ba,idan ko ka sake ka bar aurena da Ammar ya faru a daren bikin zan kashe kaina sai ko wa ya huta." Ambatan kisa da tayi ne yasa shi gaggawar juyowa,sake baki tayi lokacin da ta ga Ammar ne ba Mahfuz ba,sai yanzu ta lura da yanayin ma sam ba ta Mahfuz bane domin Mahfuz yafi Ammar tsawo da jiki. "Kin daɗe baki kashe kanki ba,ashe ba son gaskiya kike masa ba tunda bazaki iya gane bayan sa ba ko mutuwa zakiyi ni zaki aura ki sa hakan a rai." Ya bar mata wurin yana dariya.
A wannan lokacin kukan ma yaki zuwa sai zafi da zuciyarta ke mata tana mai ƙara jin mugun tsanar Ammar,ruwa ya mika mata a glass cup,bigewa tayi ya faɗi ya fashe. "Bana son ganinka ka,na tsani ganinka." cewar Kudrat cikin ɓacin rai. "Kudrat ya kamata ki gane ba laifina bane,nayi iya ƙokari na wajen bayyana maki soyayyata amma kika nuna bakya so na." "To amme meyasa baka faɗawa Abba tun wuri ba." "Bana so na faɗawa iyayeni ne kuma ya zo bani kike so ba." "Hmm ga abinda hakan ya janyo ai." "Kudrat idan kika duba babu laifina a ciki." "Naji laifin ni kake son ɗaurawa ko?" "Ba haka nake nufi ba." "Shikenan idan har kana so na mu gudu mu bar gida,bama gidan kawai ba ƙasar baki ɗaya." Sake baki yayi yana kallanta,ya rasa ta ce wa. "Ina cikin hayyacina Mahfuz kadaina min kallon mara hankali,as i said mu bar gidannan yanzu-yanzu,bana so mu ƙara kwana ɗaya anan ai bazamu rasa masu ɗaura mana auran ba."
Comment
Like
Vote and share pls
Cute_hapCy ce🎀
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Abbana Allah ya maka rahama,Ubangiji ya kai haske kabarin ka,i have miss alots sai dai Allah ya fini bukatarka.May jannatul firdaus be ur final place amin```
_*There are no plans that always work in life. the secret to happiness is being positive and looking at the brighter side of my life.*_
Page 37~38
____________📲Murmushi yayi wanda shi kaɗai yasan ma'anarta, kulle ƙofar da zata sada su da cikin gida yayi,dawowa yayi ya bata kujera. "Zauna Kudrat." Zama tayi tare da kafe sa da ido. Cikin kulawa da tausasa murya ya ce "Maganar barin gida duk bata taso ba Kudrat,nasan ke yarinya ce wanda bazata taɓa yin abinda zai baƙanta ma iyayanta ko ya sasu kunci ba amma a hankali irin taki kina ganin guduwarmu shine mafita.?" shiru tayi daga bisani ta ce "Eh." "Kada ki manta faɗin Allah a cikin alkur'ani da hadisan ma'aiki kan biyayya ga iyaye da kuma ribar da hakan zai haifar." "Nasani amma ai ƴaƴa ma suna da hakki kan iyayensu, meyasa ni nawa zasu tauye min." ta faɗa cikin kuka. "Ƙwarai amma ai....." "Dan Allah Mahfuz ka daina kawo hujuji marasa karfi,ka daina karya min gwiwa,Ammar baya so na tayaya zan amince na auri wanda yafi tsanata, wanne irin zama zamuyi haba Mahfuz kayi tinani dan Allah." "Ke ya kamata kiyi tinani Kudrat,amma tunda kinki ji shikenan na amince mu bar gida amma da sharaɗi,je kiyi nazari ina Azeezat? Sannan kuma me Abi ya faɗa kafin ya bar duniya a ƙanta? Wani dalili ne yasa ta bar gida? Bayan ki amsa min da waɗannan tambayoyi sai ki bani labarin ribar da Azeezat ta samu bayan barinta gida,daga ƙarshe ina maki tuni da ce wa duk abinda hakuri bai bayar ba,rashin hakuri bazai taɓa bayarwa ba,tun ran gini tun ran zane Allah ya kan jarrabcemu ga rasa abunda muke so domin ya gwada imanin mu,idan mukayi hakuri sai hakan ya zame mana alkhairi,sai naji daga gareki." shigewa ciki yayi ya barta tana faman kuka,ganin ba shi ne mafita ba ta tattara ta shiga itama,ɗakinta ta wuce maganganun Mahfuz na mata yawo a ƙwalƙwalwa sun sanyar mata jiki. Mikewa tayi kan doguwar kujera hawayen taƙaici na bin fuskarta. "Tabbas,tabbas na furta kalmar da a yanzu nake nadamar faɗinsa,sai dai ina roƙon Allah ya yafe min,Ummi kiyi hakuri bazan iya tafiya na barki ba soyayyarki ta musamman ce a zuciyata,na amince na auri Ammar ba dan ina so ba,sai dai dan na kasance ƴa mai biyayya wanda zakuyi alfahari da ita koda bayan mutuwarku." tana murmushi ta faɗa ga kuma hawayen baƙin ciki ya ɓata mata fuska.
Mahfuz ma tunda ya shiga ya haɗa kayansa tsab ya shirya barin gidan a faɗarsa hakanne kwanciyar hankalinsa. Kudrat idan bata kallesa ba wataƙila zata ɗan samu sauƙi shiyasa ya yanke hakan,daddaɗan muryarta ce ta dakan masa kunne,amsawa yayi tare da ɗagowa,kallonta yake cike da tausayawa yana mautuƙar jin yanayin da take ciki,share tasa hawayen yayi cikin ƙarfin hali ya ce "Ƙanwata ina fata kinyi ƙyaƙyawar nazari." tana tsaye ta ki ce wa komai sai kuka da take kasa-kasa. Naɗe hannayensa yayi a ƙirji ya kuma ɓata rai gami da ce wa "Kudrat kina son ganin ɓacin rai na?" da sauri ta kaɗa kai. "To indai hakane zauna ki min magana kuma ki tabbatar kin daina wannan kukar." share hawayen daya mata caɓa-caɓa a fuska tayi ta zauna bakin gado. "D...dama nazo ne na baka hakuri kan abinda na faɗa dazu,bansan me yazu kaina ba amma bazan taɓa iya barin Ummi ba,zanyi biyayya na auri Ammar ko dan farin cikin iyayenmu." da sauri ta fice a ɗakin.
. Zubewa yayi bakin gado tinani iri-iri na zuwar masa,ganin hakan ba zata amfanar dashi da komai ba ja trolley yayi ɗakin Abba.
Akan darduma ya sameshi cikin ladabi ya gaishe sa. Amsawa Abba yayi cike da kulawa. "Ina zakaje haka ɗana?" sosa keya yayi "Amm Abba ina so naje ƙauyen su Momy ne tun bayan rasuwarta ban samu zuwa ba." "Ƙwarai hakan yana da kyau daga nan sai ka faɗa masu bikin Ammar,ko kuma zansa shi yaje da kansa." "To Abba ni na tafi." "Allah ya kiyaye ɗana a gaishe su da kyau." "In shaa Allahu, Abba a faɗawa su Umma ma." "A'a jeka da kanka ka faɗa masu idan ya so sai ka wuce." amsawa yayi da to ya wuce,kamar kullum Ummi da Umma na tare suna hira cikin nishaɗi,shaida masu tafiyar yayi,addu'a suka masa ya fice cikin fara'a.
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
*BIKI SAURA SATI BIYU*
Shirye-shirye ake babu kama ƙafar yaro,an ɗauko mai gyaran jiki ta musamman tana gyara Kudrat,tun bata so har ta hakura ta fara nata shirin.
Kareema ko na nan damuwa ta mata ɗaurin goro,ganin bata da wata mafita ga biki saura kiris,taje ta sami su Umma ta faɗa masu duk abinda yasa Kareem ke fushi da ita,wurin Abba suka kai zancen,nan take yasa aka ƙira masa Kareem. "Duk abinda Kareema tayi saboda kai ne idan kayi nazari ta amince da mugayen nufin su Azeezat ne gudun karta rasa ka,idan ka mata haka ka mata adalci kuwa? Meyasa bazaka zamo mai tausasa zuciyar ƴa mace ba? Suna da rauni kasan da hakan." cigaba da masa nasiha sukayi jikinsa yayi weak,yana nadamar abinda ya mata. Itama Kareema faɗa aka mata sosai a wurin aka dai-daita su dama kuma Kareem ɗin ya sake zurfafa bincike ya gano duk abinda Kareema ta aikata a baya sharrin Azeezat da Abdul ne,kuma ya ga tsantsar nadama a ƙwayar idonta.Hakan yasa ya sauke duk wata gaba dake tsakanin su.
Sosai tayi farin ciki take taji duk wata damuwar ta gushe,sai dai tsoronta ɗaya idan Kareem ya gane tayi gangancin salwantar da budurcinta fa? Wanne irin mataki kuma zai ɗauka? Koma menene Allah ya kamin sauki cikin al'amurana. Ta faɗa tanawa kanta ƙyaƙyawar zato.
A facebook Billy taga Ammar yayi postings na date ɗin auransa,ta shiga tashin hankali matuƙa,tattaki tayi ta zo Yobe,da kyar ta samu location ɗinsu,ƙyaƙyawar tarba aka mata,tun kan ta huta gajiya ta buɗe wa Ammar shafin kuka bayan sun keɓence."Haba Yaya Ammar,dama zaka iya zaman aure,kayi tarayya da wata macen bayanni?." "Look Billy ba wai zan..." knocking na door akayi hakan yasa ya dakata da magana. Sakewa akayi tukun ya ce" Shigo." sallama tayi ciki-ciki wanda ita kaɗai zata iya jiyowa. Rai a ɓace ya ce "Wani irin rashin hankali ne zaki shigo min ɗaki babu sallama." bata ce komai ba ta juya zata koma taji ya ce "Ina maki magana shine zaki juya kai ko? Wato ke kin girma." a rai take jin maganganun daya ke mata gaban Billy da babu abinda take sai dariya,ganin girmansa ne kawai yasa bata mayar masa martani ba ta dawo ta tsugunna gabansa. Shareta yayi suka cigaba da hira da Billy,sosai ya sake mata tanayi kamar zata shige jikinsa shi kuma yana biye mata. "O! Allah wadaran naka ya lalace." Kudrat ta faɗa rai a ɓace. "Amm ke yarinyar nan,tukunna dai bani Coffe." mika masa tayi tana hararansa kasa-kasa,ƙurɓa ɗaya ya kai baki cikin izza ya ce "Har sai yaushe zaki koyi yadda ake haɗa coffe,anyway tunda ga Billy zata koya miki." "Dan Allah Yaya ka bani izinin fita daga ɗakinnan." "Zan baki idan na gama abinda nake,wato Kudrat ina so na faɗa miki ko ince na gabatar miki da Billy wacce zata kasance abokiyar zamanki." cikin rashin fahimta ta ɗago ta ce "Ban gane manufarka ba." murmushi yayi "Ba komai nake nufi ba illa,zan haɗa da ke da Billy a ɗaura mana aure rana ɗaya,haka nayi planing tun ba yau ba." "What!" da ƙarfi ta faɗa. "Yes i mean i will marry her too,kuma dole ki mata biyayya,saboda itace zaɓina." shagwaɓe fuska Billy tayi ta ce "Uhm Super Darling zaka haɗani da kucakar kishiya ni banga abin so a jikin wannan ba." "Kiyi hakuri Billyta sadaka aka bani ba dan ina so ba,ke ma kinsan inada ke babu macen da zata rufe min ido yanzu ma bata wuce ƴar aikin ki ba." bata damu da abinda suke faɗa mata ba,idonta cike da ƙwalla ta ce "Babu komai Allah ya bamu zaman lafiya." "Sakariya wacce bata kishi." inji Billy. Murmushi Kudrat tayi ta ce "Ke kuma haka Allah ya yiki? Menene abin kishi akan namijin duniya? Sha kuruminki na yafe miki kwanan ɗakina na har abada." da sauri ta fice dan kar ma taji maganar da zai ɓata mata rai,ƙwafa yayi "Wato ma ko kishi dani ba tayi,zanyi maganinta ne very soon kuma aurena da Billy kamar anyi." inji Ammar a rai.
Tunda ta shiga ɗaki take kuka wulakanci tun kan taje gidansa."Ammar baka da imani azzalumi ne kai. Tunda ku kuka zaɓar min shi na amince bakin ciki ya kashe ni amma bazan taɓa kawo ƙorafi akan sa ba." Kudrat ta faɗa tana jin jiki.
A daren Ammar ya sanar wa Abba bukatar yana so a haɗa masa auran Billy da Kudrat,ya ƙara da ce wa tun ba yau ba sunyi alkawarin aure da ita ba zai so a samu nakaso wajen cika alƙawarin ta bangarensa ba. Abba na da saukin kai sosai haka su Ummi ma basuyi wani jayayya ba duk sun amince a haɗa a faɗar Abba ai namiji mijin mace huɗu ne. Ita dai Kudrat abin yanzu mamaki ya so ma bata,ta fuskanci Ammar baƙanta mata kawai ya shirya ba tare da sanin laifin da ta masa ba,amma ta shirya ɗaukar duk wata ɓacin rai indai zai farantawa mahaifanta.
Comment
Like
Vote nd share pls
Cutie ce💃🏼💃🏼
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
_*Each minute is a little thing, and yet, with respect to our personal productivity, to manage the minute is the secret of success.*_
Page 39~40
_____________📲A kwana a tashi babu wuya shiye-shiryen bikin sun kanka ma,babu wanda ya kai Kareema nuna farin ciki domin ta samu cikar burinta,shi kanshi Kareem ɗin Allah-Allah yake gobe tayi ya mallaki abarsa,Billy da Ammar ma hakance ta ɓangarensu,Kudrat ce kawai ke fama da sake-saken yanda zata fara zama da waɗanda basa ƙaunarta musamman ma shi Ammar da zai kasance miji kuma maƙiyinta. Washe gari aure anyita gwada layin Mahfuz sam yaƙi shiga da alama babu shi za a yi auran.Abba ya damu a samesa a waya zuwansa na da matuƙar muhimmanci. "Ammar duk yadda za a yi ku samo layin Mahfuz,bazaiyu a ɗaura masa aure baya nan ba." "Abba wallahi babu ƙokarin da banyi ba,ni inaga kawai ayi tunda nasan bazaiki ba." "Gaskiya ne Abba,a ɗaura kawai."inji Aliyu ma." Bazaiyu ba sai dai a ɗaga auran zuwa sati mai zuwa." inji Abba. Zaro ido Kareem yayi ya ce "Abba a ɗaga aure kuma haba dan Allah." sai daya faɗa kuma yaji kunya ta lulluɓesa,simi-simi ya haye upstairs,dariya kawai suke masa shi ma yi yake ciki-ciki. "Ai inaga idan na ɗage aurannan ciwon zuciya ne zai buge ku." Abba ya faɗa cikin wasa,kasa sukayi da kai kowanne da murmushi a fuskarsa.
Da safe ƙofar gida ya cika makel da jama'a,angwaye na hango sunci ado cikin farar gezna wanda ya sha aikin nevy blue,hula takalmi,agogo duk kala ɗaya masu tsada,hatta Aliyu da ba ango ba yaci ado cikin favorite colour ɗinsa skie blue ya sha ƙyau.
Komai ya kankama limami na isa babu ɓata lokaci aka fara shirin ɗaura aure.
Bakin masallacin nake ƙokarin zuwa naji an ce
"HapCy dan Allah ki shige wurin mata nan duk maza ne." "Haba Ammar baƙin halin naka harni sai daya shafa? Ka barni na ji dawa za a ɗaurawa Mahfuz aure mana nasan warhaka su Aisha A,Nafisat,Safoura,Mmn bilal,Teemah da sauransu na can suna zumuɗi..." Katse ne yayi ban gama faɗin abin da zan ce ba "Baki abin magana,kice masu Ammar ya hana dama zagina suke kuma in shaa Allah zasuyi nadamar kirana da suna mugu." Zan ƙara magana ya murtuke fuska har sai da hanjin cikina ya kaɗa,simi-simi na wuce can nesa da masallacin na tsaya.
Duk yadda na kai ka kasa kunne na nakasa jiyo abubuwan da suka gudana amma sai dai fuskar Yaya Aliyu ya tabbatar min da akwai gagarumar al'amari daya faru na farin ciki.
Cikin gidan na shiga,a haraba mata nata girke-girke ƙamshi na tashi ta ko ina,ɗakin Abba na wuce ganin Ummi da Umma da nayi ta windo shi ya jawo hankalina. Ko da na isa naji Abba na ce wa "Bana so yariyar nan taji har sai shi ya zo." "In shaa Allah bazata ji ba,kai Alhamdulillah,Allah ya dubi al'amarin." "Ni zan fita duk abinda kuke bukata ku sami Aliyu." to sukace tare da barin ɗakin suma.
An gudanar da shagalin biki lafiya,kasancewar abun na gida ne Abba ya ce bazasu tare ba sai Mahfuz ya zo,Kudrat hakan ya mata daɗi sosai domin hankalinta a tashi yake idan ta tuna anjima za a kaita,Kareema da Billy kam sun kasa ɓoye bakin cikin su babu kamar Ammar ma,Aliyu banda dariya babu abinda yake masu yana ce wa Allah yasa Mahfuz ya kai sati.
Karfe buyun dare amma ta gagara bacci,juyi Kudrat tayi ta ganta jugum tayi tagumi. "Lafiya kuwa Kareema haryanzu bakiyi bacci ba.?" "Gajiya ne Kuɗrat." "ai gajiya shi ke sa bacci ba wai ya hana ba." bata ƙara magana ba ta wuce toilet ta ɗauro alwala da niyyar sallah kawai ta tsinci kanta cikin yanayi wanda bazaiyu ta gudanar da ibada ba. Sosai tayi farin ciki dama tun wancan watan take tsammanin zuwarsa bata gani ba hankalinta ya tashi tinaninta ciki ne da ita. "Alhamdulillah banida komai,saura ƙalubale na biyu kuma." da sauri ta gyara jikinta ta fito ta kwanta.
Washe gari akayi wani bikin yini,da azahar baƙi suka watse haryanzu dai Mahfuz bai zo ba lamarin ya fara bawa Abba tsoro,yanke shawarar Kareem da Ammar suje su dubu shi yayi suna cikin wannan yanayi Aliyu ya gwada layinsa ta shiga. "Assalamu laikum." Mahfuz yayi sallama. Ko amsawa baiyi ba ya fara zazzagu masa masifa. "Yaya ba wai naki zuwa bane auran Indo ƴar ƙanwar Mommy ake shiyasa na tsaya." "To maza Abba na neman ka nan ma ai auran Yayyenka ake." "Anjima dama zamu taho." da haka suke tsinke wayar.
Gabannin Magrib Mahfuz ya dawo tare da wata ƴar ƙauye,sosai ya taya ƴan uwannasa murna,bayan isha Abba ya haɗasu gaba ɗaya a babban parlo banda Kudrat da Kareema.
"Tsakanin mu babu wata kunya saboda haka ku saki jiki." Inji Abba yana mai murmushi.Suma murmushin suka maida masa. Daga nan ya so ma masu nasiha kan su rike juna da amana,hakuri,juriya da kuma biyayya ga juna. Daga ƙarshe yake ce wa "Mahfuz da Kudrat ko gobe ban yarda ku ƙara yin abinda kukayi a baya ba,ina nufin ɓoye mana son junanku da kukayi alhalin kun san munfi kowa ƙaunar farin cikin ku,nasan kuna rike da Ammar,gani kuke ya zalunceku ya raba ku,musamman ma Kudrat." Shiru yayi yana murmushi tukan ya ce "To Ammar baiyi haka ba sai dan ya gwada ku zaku faɗi abinda yake tsakaninku ne ko zaku bijire mana kamar yadda *AZEEZAT* tayi,Alhamdulillah kun kasance ƴaƴa masu biyayya kun wanke min zuciyata da hakurin da juriya tare da sadaukarwa da kukayi,wannan dalili ne yasa aka haɗa auran Kudrat da Mahfuz." Da sauri suka ɗago suna kallon sa cike da mamaki. Tamkar a mafarki sukaji an faɗi hakan. "Ba mafarki bane Kudrat matarka ce Mahfuz duniya da lahira ka gode wa Yayanka shine ya jajirce akan hakan idan ta nine sai a barku da zurfin cikinku." kasa jurewa Mahfuz yayi sai dayaje ya rungume Abba yana kuka yana masa godiya,sai dayabi mazan ɗaya bayan ɗaya yayi hugging nasu,da kyar aka basa hakuri ya dai-daita nutsuwarshi ya ce "Hakika kunyi min komai,babu abinda za saka maku dashi illa addu'a sai dai wani hanzari ba gudu ba,ya zanyi da auran Indo da nayi." Haɗe baki wurin faɗin "Aure kuma? Kana nufin matarka ce.?" Sukayi. "Eh lokacin da naje kauye na tarar Mami larai ta daɗe da rasuwa,tsawon wannan lokacin an kasa samun wanda zai ɗau responsibilities ɗin Indo,shine na nemi a aura min ita domin na inganta rayuwarta,bansan cewa Kudrat matata ba ce da bazan auri wat..." "a'a karka ɓata ladanka,wannan ba matsala bace Kudrat zata fahimceka yadda ya kamata,kuma naji daɗin abinda kayi." Nasiha Abba ya ƙara masu daga bisani yace kowa yaje ya kwanta.
Abba ne yasa Umma suje su faɗawa Kudrat Mahfuz yayi aure su kuma nuna mata ce wa kishiya abokiyar zama ce amma kar a faɗa mata Mahfuz ne mijinta,hakan akayi ta amsa masu da "In shaa Allah zan kasance ƴa mai biyayya Yaya na ɗau Billy ba kishiya ba." a azatonta kan Billy ake mata nasihar.
Washe gari da dare aka kai ko wacce amarya gidanta. Mahfuz suka fara rakowa,ɗakin Indo ya fara shiga kasancewar auranta aka fara ɗaurawa tukun suka wuce ɗakin Kudrat,can ƙarshen gado take kanta a lullube da gani kuka take. Gabatar mata da angonta akayi tsalle ne kawai batayi ba,ji take tafi kowa farin ciki a faɗin duniya. Kamar yanda abokan ango suke ɗan yiwa Amarya da Ango tunatarwa haka Yayun nasa suka masu sunja kunnensa sosai kan yayi adalci.
Gidan Ammar suka wuce,daga ƙarshe Yaya Aliyu ya raka Kareem. Cikin sanyin jiki ya koma gida yana yiwa ƴan uwansa fatan alkhairi a zamantakewarsu.
"Mahfuz da gaske kaine mijina! Dan Allah idan mafarki nake kar a tashe ni,a barni na dawwama cikin wannan yanayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Allah nagode maka." Ta faɗa tana hawaye, tallafo fuskarta yayi "Kudrat ba mafarki kike ba,da gaske ne Mahfuz ya zama mallakinki,duk da haryanzu banji kin faɗa min kalmar ba." "Mahfuz ko ban faɗa maka ka sani I love you to the extend." wani sanyi ne ya ratsa dukkan sassan jikinsa,hugging tana yayi sosai kamar zai shigarta jikinsa su zama ɗaya. Indo ce ta faɗo masa a rai jikin sanyin jiki ya sake ta,kallonta yake yana zubar da hawaye,tsintar kanta tayi da tayasa cikin tashin hankali ta so ma tambayarsa da ƙyar ya buɗa baki ya ce "Bansan ko zaki fahimce ni ba,amma hakika nayi na...." yatsa ta sa masa a baki domin ta gane inda ya dosa. "Wannan ba abin damuwa bace Indo ƴar uwata ce ba kishiya ba,tana ina yanzu." sauke numfashi mai nauyi yayi "Tana ɗakinta." murmushi tayi ta ce "Taso muje ko?" bata jirasa ba ta zauka har ta fara tafiya taji ya dago ta,nishi ya so ma cikin wasa ya ce "Kai Kudrat ba dai nauyi ba." murmushi tayi ta rufe fuska,da ƙyar ya sauketa a bakin kofar ɗakin Indo da ce wa yayi har ciki zai shiga da ita.
"Indo wannan itace Matata Kudrat,fatan zakuyi zaman lumana,banda yanke-yanke banda cizo da yaguni,ko jin zugin kawaye,zanyi adalci iya iyawata in shaa Allah amma idan kukayi tawaye zanyi bulala." ya ƙarashe da ƴar dariya. "In shaa Allah mai gida zamuyi zaman lahiya." Inji Indo. Yanayin maganar tata abin dariya da kyar Kudrat da daure shima kanshi Mahfuz mazgewa yayi. "Mai gida kuyi tahiyarku ni ban bukatarka na ban mata kwanar kunji jeku amma kafinnan ka kunna min kallo." "Haba Anty Indo a ɗakin ki ya dace ya kwana." "Laa ya naji kina haɗe min suna da wata aba,karde zagina kike." "Haba Indo ina nufin Yaya." "Ayyo yanzu naji bayani,mai gida kunna min ku fice kallo zanyi." abin neman ya samu da sauri Mahfuz ya kunna mata tv ya ja Kudrat suka fita bayan sunyi addu'a. Zan biyo su ɗaki ya ce "Yanzu kam idan kika biyomu zaki haɗu da....." kafin ma ya ƙarshe na canza hanya gaba ɗaya na fice a gidan.
Gidan Kareem na wuce na tarar ta gama faɗa masa abinda ya shiga tsakaninsu da Barrister. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Dama bakida hankali,ke wacce iri ce? Meyasa kika yaudareni wannan karan ma? Zama da ke bazai taɓa yiwuwa ba dole ki bar min gida bakida wurin kwana a nan." shiru yayi yana huci. Kuka ta saka ta na "Dama na sani,nasan babu wanda zaiji haka ya kuma amince ya zauna dani amma Allah ya gani banyi dan jin daɗi ba sai dan na kubutar da kai dan Allah Kareem ka tai....." jikinsa ya janyuta,cikin sanyin murya ya ce "Yi shiru ƴar lele hakan bazaisa na guje ki ba sai dai ma na ƙara sonki,ke ɗin karan kanki nake so ba wani ɓari na jikinki ba,amma kin tafka kuskure da kika saɓawa mai Halitta saboda abin Halitta,Allahu gafururahim zan tayaki da addu'ar Allah ya yafe miki karki sake yin irin wannan ganganci." batayi zaton abin zai zo da sauki ba,hamdala tayiwa Ubangiji bisa ni'imar daya mata.
Bayan sati ɗaya Ammar da Billy suka zo bawa Kudrat hakurin abubuwan da suka faru,duk da yayi hakanne dan ya gwada su,sai dai shi kanshi yanajin babu daɗi idan ya tuna abubuwan daya ma Kudrat ɗin. Dama Mahfuz ya bata labari bata bari an kawo zancen ba tace ba komai ta yafe.
_*NOTE*_
_At the end kunga yanda biyayya tasa Kudrat ta samu abinda take so cikin sauki,duk da wannan is finctional,amma nasan baza a rasa cases irin wannan ba,a duk lokacin da iyayenmu suka nuna kin amincewa da zaɓin da muka fidda ƴan uwana matasa mata muyi ƙokarin yin biyayya garesu,abinda ciwo amma mahakurci mawadaci,akwai ayar kur'ani da ya ke ce wa "Sau da dama zamu so abu amma kuma ba alkhairi bane garemu,wani abun muna matukar ƙinsa amma shine mafi alkhairi garemu. Idan muka kasance ƴaƴa masu biyayya na tabbata zamuci ribar hakan duniya da lahira._😊
_*FEW MONTHS*_
_*GARIN MAIDUGURI*_
Hanyar post Office wuri ne mai cike da cin kosun ƴan kasuwa,ababen hawa da masu wuce wa ƙya'kyawar budurwa sai dai tayi kaca-kaca da datti,ɗauke da farantin talla akanta,daga gefe ga yarinya ƙarama da alama ƴartace rike da monguro a hannu kuda na binta datti ya mata yawa sosai kamar uwarta. Hold-on ɗin titin ne ya basu damar tsallake kwaltar ba tare da wata matsala ba. Tafiya mai nisa sukayi duk sun galabaita. Wani ɗan ƙaramin gida suka shige suna jan kafa daga ita har ƴarta,direct wurin randa ta nufa cikin gaggawa ta ɗauki cup tana Allah-Allah ta kai baki dan kore ƙishir ruwar da take addabarta, warce ruwan akayi,sauri tayi ta juyo ganin shi ne yasa ta marairaice fuska "Dan Allah Abdul ka bani na sha ƙishirruwa zai kashe ni ga Yasmin ma tanaji." kamar zatayi kuka ta karashe. "Ace duk yawon da kikayi baki siyar da goronnan baki ɗaya ba kinzo kina wani narke min dan naji tausayinki,kin isa kimim wayo ne Azeezat." Ya faɗa cikim masifa.
_~Kucigaba da bibiyar *MAKAUNIYAR SOYAYYA* tare da A,k,a Cute HapCy💃🏼~_
Comment
Like
Share
Vote Pls
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dadicated to my life Allah ya maka rahama tare da salihan bayi Abbanah```
_*If you believe in yourself and have dedication and pride - and never quit, you'll be a winner. The price of victory is high but so are the rewards.*_
Page 41~42
_____________📲Kallon shi kawai da tsaya idonta cike da hawaye,azabben ƙishir ruwa ne ke damunta gashi ya hana ta. "Me kika ƙura min ido zaki ɓace dagani ko sai kinji na jaki." cikin masifa yake magana,marairaicewa tayi ta durkusa ƙasan kafafunsa ta ce "Dan Allah Abdu...." kafin ta ƙarasa taji sauƙar mari har biyu fuskarta,hakan ba abin mamaki bane a wurinta don ta saba shan dukar sa. "Ban hanaki ƙirana da sunana ba?" "Ka hanani." cewer Azeezat tana hawaye. "Okay kin dai na tsorona ko,na zama tsararki, yanzu jikinki zai gayamiki." magiya ta shiga masa tana mai kuka amma ko sanin tanayi baiyi ba,ciki ya shiga ya samo cable ya fito yana zuba mata a jiki babu sassauci,ihu Azeezat ke kurmawa tana neman agaji itada ƴarta. Da gudu Sarah makuciyarsu ta shigo tana "Haba,haba Abdul kai ba ka gajiya da duka ne wani irin miji ne kai wanda baka tausayawa matarka.?" turesa tayi ta taso da Azeezat da duk ta galabaita motsin ƙirki bata iyawa. "Kyaleta Sarah kina kallonta sam bata da tarbiyya ƴar iska kawai." ya faɗa yana huci. Kaɗa kai Sarah tayi domin idan ta tsaya exchanging na words dashi abinda ya saba faɗa mata ne zata ji dan haka ta taimakawa Azeezat ta tashi ta janyo hanun Yasmin suka fita,tanaji ya ce "Wannan da kike kallonta mayya ce ko kin tafi da ita zata dawo,ni ban taɓa ganin mara zuciya kamar ki ba karuwa kawai wacce bata ɗauki iyayenta bakin komai ba." duk taji amma babu damar maida masa gudun rasa sa, domin batada kowa sai shi.
Ruwan wanka ta fara kai mata toilet mai ɗumi,kafin ta fito tayiwa Yasmin ma,abinci da ruwa duk tayi arranging babu jimawa ta fito ɗaure da zanin wanka,cikin kayanta Sarah ta ɗauka mai kyau ta bata ta saka,tayi kyau amma duk a rame take.
Sakar mata murmushi tayi "Kinga yadda kika haɗu kuwa? Da Abdul zai ganki cikin wannan shigar na tabbata duk wata fushi da yake zai daina." taɓe baki tayi,ita kaɗai tasan yadda take jin zafi a ranta komai na duniya ya isheta,zama tayi gefen Sarah ta zabga uban tagumi hawaye na sauka fuskarta. Cike da tausayi ta dube ta ta ce "Azeezat kukannan ya isa ki ci abinci yau ina so ki bani labarin rayuwarki ko da kaɗanne domin tunda nake ban taɓa ganin ma'aurata kamarku ba anya ba dole akawa Abdul ya aure ki ba?" ɗaura kanta kan cinyar Sarah tayi tana rera kuka mai sosa rai,rarrashinta tayi ta mika mata kwanon abincin,ci suke ita da Yasmin tamkar bata taɓa sa abinci a bakinta ba,bayan sun kammala Sarah ta ce "To yanzu ina jinki." gyaran murya tayi ranta na ƙona ta ce "Sarah kada kiyi mamaki idan nace Abdul ba mijina bane." "What! Ban fahimceki ba." "Nasan zakiji abun wani iri,dole ne ya baki mamaki amma kuma ba abun mamaki bane dan mahaukaci ya fita sirara." "Azeezat kin san ni ba wani hausa nakeji sosai ba yimin yanda zan gane." murmushi tayi mai cike da takaici "Kalmar dai shi zan ƙara nanata maki,Abdul ba mijina bane Allah ne ya jarbaceni da ƙaunarsa,na makance bana ganin kowa sai shi,kunnuwata basa jin ko wani ƙira sai nashi bakina kullum cikin ambatansa yake." "Oh my Lord! Whats wrong with you sister? Are you in sence?" Kuka ta so ma tana "Nima bansani ba Sarah,bansan ko inada hankali ba,amma na tabbata mutum mai aiki da ƙwaƙwalwa ba zai aikata ɓarnar da nayi ba." "Idan na fahimceki da kyau gudu kikayi daga gida,gaskiya kin tafka kuskure mai girma,ke kanki ki zauna kiyi nazari,misali ace Yasmin ƴarki ta bi saurayi ya zakiji.?" "A wannan lokacin fahimtata ta gushe,bana gane fari bare baƙi,kaito na." "My goodness! Me wannan Abdul ɗin ya miki haka,a ina kuka haɗu.?" numfashi ta sauke ta ce "A duk sa'in da na tuna wannan lokacin ina baƙin ciki matuka domin ranar ne rayuwata ta fara sauyawa,na fifita zaɓin wani fiye dana iyayena,na fita daga Khadijan da aka sani mai biyayya na dawo sha-sha-sha,mahaukaciya wacce bata iya banbance mai kyau da akasin haka....." fashewa tayi da kuka mai tsanani,yi tayi mai isarta kafin tacigaba da faɗin
"Tafiya nake cikin sauri ina dube-duben ko Allah zai sa naga kuɗin aiken dana jefar,na karaɗe unguwar kaf ban samu ba gashi ina tsoron komawa gida gudun kar Ummi ko Abi su dake ni,zama nayi kan wani dakali ina kuka ɗagowa da zanyi na ganshi tsaye a kaina hanunsa cikin aljihu,lokacin da idonuwarmu suka sarƙe da na juna naji wani irin abu da ban taɓa ji ba,hakan yasa nayi saurin kaudawa. Zan tashi na bar wurin naji ya ce "Ɗan tsaya mana." tsintar kaina nayi da kasa yi masa gardama,dawowa nayi na zauna cikin kulawa ya tambayeni meyafaru,na faɗa masa ce wa an aikeni ne kuma kuɗin ya faɗi,dariya yayi ya ciro 5k da ƙyar na ƙarɓa kasancewar Ummi ta hanamu ƙarɓan kuɗin saurayi,tun daga wannan ranar Abdul ya kasance wani ɓangare na rayuwata,na kamu da ƙaunarsa kullum cikin tinaninsa nake gashi bai furta min ba,ganin bazan iya jurewa ba rana ɗaya na faɗa masa ina son sa,da farko bai amince ba har ya kasance yayi blocking ɗina bana samun shi for good 2months daga baya bansan me ya sauya masa tinani ba ya zo ya ce ya amince amma da sharaɗin zamuyi mu'amula irinta ma'aurata,naƙi amincewa da hakan daga bisani komai ya sauya,domin ya ƙara juyamin baya kuma gashi raɗaɗin rashinsa na azabtar da ni,babu yadda na iya kawai na amince a haka muka samu ƴarmu Yasmin." Baje kunnuwarta tayi tana saurarar labarin mai cike da al'ajabi.
"Bayan na bar gida, abubuwa dayawa sun faru daga ciki harda mutuwar Abbana amma ban koma ba ana haka Abdul ya gudu ya barni still ban farga ba zuciyata na raya min ba gudu yayi ba, na yanke shawarar yin aure kafin ya zo,na auri wani mutum dattijo wanda yake kashe min kudi a baya ashe Babansa ne bansani ba,sai bayan an kaini gidan muka haɗu dashi a lokacin anyimin tayin na koma gida amma da ke zuciyata bata mutane bane na ki amincewa haka na ƙara bin Abdul." "Gaskiya Azeeezat kinyi wauta,a bar ma zancen sauran,da auran wani a kanki kuma kike tare da wani,wanin ma ɗansa haba dan Allah keda kanki ma kinsan wannan ba dai-dai bane,nidai shawarata gareki shine kiyi gaggawar komawa gida tun kafin lokaci ya ƙure miki." "Sarah bana tinanin inada sauran lokaci,rayuwata ta gama lalacewa tun ina ƴar ƙaramata,duk abinda suke faruwa da ni na ƙunci sakayyar iyayena ne kuma nasan a hakan ma banga komai ba." "Karki ce haka Azeezat,komawarki gida shine zai sassauta miki duk wata tsanani." "Na baki labarin ne a taƙaice,da kinji wasu abubuwan ke kanki zaki tsinemin kuma bazaki ƙara ƙaunar sa ni a ido ba saboda munin abinda na aikata." "Su iyaye daban suke Azeezat,sunada tausayin ƴaƴansu,wannan lokacinne ya dace ki koma gida ko dan ki inganta rayuwar Yasmin da taki." haka Sarah taciga da ƙara mata ƙwarin guiwa harta amince zata koma gida,hiran nishaɗi suka ɗauko sai ga Williams ya faɗo gida,Azeezat na ganinshi tasan bazata ƙare da kyau ba domin tasan sarai ya tsaneta. "Sarah ban hana yarinyarnan shigowa gidana ba.?" bata basa amsa ba sai sunkuyar da kai da tayi,tattarawa tayi cikin mutuwar jiki ta koma gidan Abdul duk da tana cikin tsoro "Ya zanyi kowa ya tsaneni,Sarah ce kaɗai ke tausaya min." a hankali ta furta hakan. Bayan ta shiga sai daya ɗaureta kafin ya ƙara mata shegen duka ya mata jina-jina still bai kunce ta ba a faɗarsa a hakan zata kwana. Cikin dare Polices suke haura gidan aka kame Abdul sakamakon kama ogansu mai yi masu dillan kwaya,cocaine da akayi,ita kanta Azeezat ɗin ganinta ɗaure da akayi ne yasa sukayi tinanin sato ta yayi,a taƙaice ana tuhumarsa da laifin tsaida kwaya ga satar mutum. Babu wani dogon bincike direct gidan yari aka kaishi inda aka yanke masa hukuncin life in prison tare da aiki mai tsanani.
Daga ƙarshe Abubuwan da Abdul ya aikata wa Kareem ne ke faɗo masa ɗaya bayan ɗaya,yau shima ya shiga ina Kareem ya shiga ya fito,sai dai nasa na har abada ne,neman ƴan uwansa da Kareem yake ido rufe domin ya nemi yafiyarsu amma babu hali,ga shiga cikin kunci da nadamar kasancewa mutum banza da yayi.
_Ita rayuwa juyi-juyi ce,ka aikata mai kyau zaka ga mai kyau da yardar Allah,idan kuma kayi akasin haka kafin mutuwarka zaka girba,kada kaci amanar iyaye,amini ko masoyi yin hakan babban kuskure ne._
*BAYAN ƊAN WANI LOKACI*
Tafiya take tana jan ƙafa kallo ɗaya zaka mata ya tabbatar maka da hankalinta sam baya jikinta,sauke niƙab ɗin kanta tayi domin ta isa Unguwarsu bata so a ganeta,tsayawa tayi tana ƙarewa gidansu da yake akulle da ƙaton kwaɗo kallo,Nuhu ne yazo wucewa ta canza murya ta tambayesa ina suke,ya bata amsa da tun malam Abdulkareem,wanda wasu daga cikin ƴan uwansa ke kiransa da suna Lawan Allah ya masa rasuwa suka koma Yobe da zama. "Allah sarki Abi,ka yafemin nayi nadama." cewar Azeezat cikin sanyin murya,tinanin a ina zata samu kuɗin motar tafiya take,ji tayi an ƙira sunanta da sauri ta juya,ganin Linda ce ta sauke ajiyar zuciya. "Azeezat ƴar bariki daga ina?" "Hmm Linda kenan,wannan sunar ada ne amma a yanzu zamu ɓata da duk wanda ya kirani da hakan daga ciki harda ke." "Hhhhm duk wanda ya tuba dan wuya ba lada,wato kinga an kame Abdul shine kika tuba ko? Cewa nake kinsha faɗin idan babu shi bazaki iya rayuwa ba,yanzun da aka ƙargamesa a gidan yari why not bazaki bishi ba." "Mtsww wannan zancen iska ne wanda bashida asali,ni da wannan surutun dama wayarki kika aramin nayi kira." "Babu kuɗin ƙira sai dai text." "Shikenan bani." karɓa tayi ta rubuta kamar haka _"Kudrat Azeezat ce,nasan zakiyi mamaki idan nace nayi nadamar abubuwan danayiwa su Ummi,ni kaina idan na tuna kunya da haushin kaina ne ke mamayeni dan Allah ki bawa su Ummi hakuri a madadina,ina bukatar yafiyarsu hakan ne kaɗai kwanciyar hankalina a wannan lokacin,sai naji daga gareki."_ ta turawa Kudrat,babu jimawa ta mata reply,tsoro ne ya hanata karantawa da kanta ta mikawa Linda. _"Farin cikina bazai misaltu ba,Allah ya amshi addu'armu,tunda kin gane kuskurenki babu abinda ya rage wanda ya wuci ki dawo gida yanzu dai ki faɗamin inda kike nazo na ɗaukeki..._ Sosai Linda tayi bakincikin karɓan Azeezat da akayi a gida hakan yasa ta ce "Cewa tayi Ummi ta tsine miki albarka,kowa na family yayi Allah wadai da ke ba a bukatarki domin tuban muzuru kikayi,jeki cigaba da girban abinda kika shuka." "Dan Allah Linda da gaske haka ta turo?" "Idan baki yadda ba gashi ki karanta." "Ba sai na karanta ba,dama na sani,da wannan rayuwa gwara min mutuwa." hawaye ta soma tana jan Yasmin da gudu tamkar mahaukaciya. "Ƴar iska,jeki cigaba da rayuwa irinta almajirai,taya ma zan bari ki koma gida cikin sauki haka alhalin ni ina nan cikin ƙunci." cewar Linda.
Cikin wannan kudunnata bata ankara ba ta shige gaban wata babbar mota,sai da tayi sama da ita kafin ta sauko da ita ƙasa. Jama'a ne suka taro a kanta kowa na ambaton Allah,raunin da taji ya ruɗar da su,kasa fitowa a motar yayi a ranshi yana saƙawa tun kan ya gama da wancan matsalar wata ta ƙara afka masa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ya faɗa cikin tashin hankali tare da fitowa a motar,hanunsa ya ɗaura a hancinta babu wani alamun fitar numfashi,cikin hanzari koma muta kamar zai ɗauko wani abu,cikin dabara ya juya ba a ankara ba sai ganinshi akayi a figi motar a guje ya bar wurin,ƴan wurin gaba ɗaya an rasa mai taimaka mata da ɗaɗɗaya suka watse.
Comment
Like
Share nd
Vote if you are a real fans💃🏼💃🏼
Cutie ce🥰
~Commenters kuna matukar burgeni💃🏼A,k,a Cute HapCy na gaisheku kyauta a duk inda kuke~
Always
Comment
Like
Share nd
✅ote
[9/21, 4:35 PM] Kawallie Hafsah💖💋🌹: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*
_Labarin *AZEEZAT* mai cike da kunci haɗe da nadamar rayuwa_
Story/Written
By
Hafsat Ibrahim Khalil
Cute HapCyyy
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to Like our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatspp
Wattpad
https://my.w.tt/zKU4d0JvE8
Youtube
https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
```Dedicated to my life Allah ya jikanka da rahamarsa Abbanah```
_*Infuse your life with action. Don't wait for it to happen. Make it happen. Make your own future. Make your own hope. Make your own love. And whatever your beliefs, honor your creator, not by passively waiting for grace to come down from upon high, but by doing what you can to make grace happen... yourself, right now, right down here on Earth.*_
Page 43~44
_____________📲Da ɗaɗɗaya jama'ar wurin suka watse babu wanda yaji tausayin ta ko ƴarta,kasancewar arean duk sun san labarin abinda tayi,tana shanye kan rana babu alamun rai a jikinta,kusan Magrib Napep yayi parking nesa da inda take kwance,Samari guda biyu ne suka fito fuskarsu babu annuri,juyawa ɗayan yayi ya kalli ɗan uwansa ya ce "Nuhu Napep fa bazai ɗauke su ba,shima Isma'il ina hankalinsa yake ya yi wannan aika-aikar." wanɗa aka ƙira da suna Nuhu yayi kwafa tare da amsawa da ce wa "Ok tare mana motar ɗaukar icce."
Haka akayi kuwa,da motar itace aka ɗauke su zuwa asibiti,an ɗauki tsawon watanni kafin Azeezat da dawo hayyacinta sai dai tayi ɓarin ɗan ƙaramin cikin da take ɗauke dashi.
A hankali take buɗe idonta,ƙarewa wurin kallo tayi yayin da ta gama buɗewa ta soma juye-juye.
Tayi-tayi ta tuno abinda ya faru da ita amma ta kasa kawai ta fashe da kuka,Isma'il dake gefe ne ya matso kusa da ita fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce "Kiyi hakuri baiwar Allah,tsautsayi ne ya afka min na bugeki dan Allah kiyi hakuri yanzu ki faɗamin address naki na kaiki warhaka nasan mijinki na cikin damuwa na rashin sanin inda kike." "Meyasa baka min bugin da bazan ƙara rayuwa a duran ƙasa ba,meyasa baka sa anyimin allurar mutuwa ba,meyasa ka barni na rayu,rayuwata batada amfani dan Allah ka sa a kashe ni na huta da takaicin duniya." tana kuka kamar zata kashe kanta,cikin rasa gane inda ta dosa ya ce "Baiwar Allah kinsan abinda kike faɗa kuwa." batayi magana ba sai ma kauda kai da tayi. "Ko zan iya sanin wani abu dangane da rayuwarki." "Faɗa maka bazai amfanar dani komai ba fa ce jawo wa kaina la'anta,tafiya zanyi ina ƴata?." "Zan baki ƴarki amma sai nasan wani abu game da ke." "Bawan Allah kada kaja wa kanka masifa,ka bani ƴata kawai." "Baiwar Allah nidai bansanki ba amma a shirye nake da na taimaka miki koda kuwa baki cancanci hakan ba." Numfashi ta sauke tayi shiru tana nazari,wata zuciyar na raya mata ce wa kada ta kuskura ta faɗi gaskiya don yin hakan zai iya sa wa ya fasa taimaka mata,idan yaji ɓarnar da tayi,amanna tayi da hukuncin da zuciyarta ta yanke ba tare da dogon nazari ba,ta ce "Sunana Khadija,iyayena ƴan ƙasar Libiya ne sakamakon yake-yake da ake a garinmu na rasa iyayena da mijina banida kowa sai ƴa ta Yasmin ina yawo ne kawai ba tare da sanin makomata ba." sosai isma'il ya tausaya mata cikin tattausar murya ya ce "Ki daina kuka,in shaa Allah zan kasance miki ginshikin rayuwa daga yau ƙunci ta kare cikin rayuwarku." godiya tayi sosai tana sa masa albarka.
Sunkuyar da kai yayi cikin shakka ya ce "Amm sai dai ina ƙara neman gafararki,cikin dake jikinki ya zube." damm zuciyarta ta bada razananniyar ƙara,sai yanzu ta tuno da batun cikin da ke jikinta,hamdala tayi a rai tana mai farin ciki, a zahiri kuwa nunawa tayi ta ɗan damu. "Khadija wallahi bani....." "Ka bar wannan ba yanzu ba,babu wanda ya isa ya canza kaddarar Allah,du abinda Ubangiji yayi shine dai-dai." "Nagode da kika fahimceni,tashi muje."
Yana gaba tana biye dashi har suka je parking lot ya ɗau motarsa suka wuce gidansa,duk da kai ta gidansa babban tashin hankaline haka ya daure yana mai kyautata zaton bazai samu matsala ba.
Madai-daicin gida ne mai ɗauke da ƙaramin backyard,shigarsu ciki ne ya bani damar tsarin gidan daga cikin yadda ya kamata,parlo ne ɗaya sai ɗaki biyu a jere,wata ƴar siririyar mata tamƙar a hureta ta faɗi na hango zaune kan kujera hanunta rike da phone tayi zurfi cikin chatting,murmushi bayyane a fuskarta,daga bakin kofar ya tsaya gami da naɗe hannu a kirji yana kallonta cikin zuciyarsa banda sake-sake ba abinda yake. Jikinta ne ya bata ana kallonta ta maida dubanta ga kofa tuni ta ajiye wayar ta nufu sa da gudu. "Yaya Ma'il,i miss you." ta faɗa tana ƙokarin hugging nasa cikin farin ciki. Hannunsa yasa ya dafa kafarɗarta,"Bana so bazakiyi hugging ɗina ba babu wani missing." kamar zatayi kuka ta ce "Haba Yayana ni ce fa." "Nima ai nine." cikin salon yanda tayi maganar cikin shagwaɓa shima yayi. "Uhmmm uhmm Mama....." "Yi shiru ƴar kanwata,amma ai kinsan na hanaki chattin kuma kikeyi,meyasa rai na bazai ɓaci ba." "Yaya ba fa wani abu mara kyau nake ba hira da kawaye ne." "Um hakane daga nan su fara zugaki ki fara raina mijinki ko." "A'a Yaya to niɗin banida hankali ne da zan yarda da zugin ƙawa." "Nidai na gaya miki ki rage chatting." "Owk dear,to yanzu sai a barni nayi hugging na....." kafin ma ta ƙarasa ya haɗe jikinsa da nata,duk abinda suke Azeezat na kallonsu sun matuƙar burgeta,"Inama ban gujewa zaɓin iyayena ba." cewar Azeezat tana mai ƙara yin nadama. Bata ankara ba sai gani tayi ya ɗauketa cak sunyi ɗaki ba tare da bin takanta ba,toshe bakinta tayi tana kuka sosai.
Sun jima sosai a ɗakin kafin suka fito maƙale da juna,ganinta zaune bayan kujera ne yasa ya tuno da ita. "Subhanallah dan Allah Khadija kiyi hakuri." da sauri matarsa ta juya ta kalli inda yake kallo,ganin Azeezat ya matuƙar tayar mata da hankali. "Yaya me nake gani?" cikin ɓacin rai ta tambaya. "Zaifi dacewa mu samu zama kafin na fara baki labarin wacece ita." "Wato rashin mutuncin ma ya wuce ayi da su a waje har sai an kawo min ita gida? Wannan shine sakayyar da zan samu daga gareka? Lallai na yarda maza basu da tabbas,bazan zauna da karuwa ba idan har inada ƙima a wurinka,kuma kana bukatata kaje ka kare kanka gaban iyayenmu." hijabinta dake kan kujera ta zara dai-dai innda Azeezat ke zaune tayi tsuru-tsuru ta tsaya,tinaninta bai wuce kar a ce Fatima ta santa ba. "Sai kinyi nadamar sanin mijina banza ƴar iska kawai." tana gama faɗar abinda zata faɗa ta wuce,Isma'il yayi ta ƙiranta amma ko juyawa takiyi.
"Bazan so na zama silar rugujewar farin cikinku ba,nagode da niyyar taimakamin da kayi Allah ya biya." inji Azeezat tana hawaye. "Kina nufin tafiya zakiyi? To kije ina wa kike dashi?" "Bansan kowa ba." "Fatima nada zafin kishi ne amma nasan zata sauko,ko su iyayenmu idan sukaji niyyar alkhairin da zanyi nasan zasu fahimtar da ita kar hakan da tada miki hankali."
"Eh dole karya tada mata hankali ko,sannu sadauki to yau idan hankalinta yayi dubu sai ya tashi tunda take shirin shiga rayuwar ƴata." Shigowar Mama kenan ita da Fatima take zabga uban bala'i. Kanta yayi da sauri ya ce "Anyini lafiya Mama." "Kaci gidanku,nace kaci gidanku,da ban wuni ba ka ganni,ka ɗebo karuwa ka kawo gida har kana da bakin tambayar lafiya ta." "Mama abinda fatima ta faɗa miki akan yarinyar nan fa ba haka bane." "O,hakkun tun yanzu har ka fara ƙaryata matarka akan karuwa ko." "Ba wai haka bane amma ai yakamata kujita bakina." "To Baba nayi laifi a hukunta ni." "Mama nifa ba nufi na kenan ba." " Isma'il ka saurareni,wannan umarni ne ba shawara ba,kayi maza ka ɗauke ƴar iskar matar nan da shegiyar ƴarta ƙafin nan da awa ɗaya,idan kuma ba haka ba sai na tsine maka albarka kuma ba ni ba kai, sai ka dawwama da ita karuwar." Rinannun idonsa ya saukar fuskar Mama, hankalin sa ne yayi mummunar tashi lokacin daya fuskanci bacin ran mahaifiyar tasa "Khadija ta so muje." Babu musu ta tashi, tana hawaye sosai don su Mama haryanzu dacin magana suke fada mata har suka fice daga gidan. Direct gidansu ya wuce da ita yayi sa'a Baba na nan, fada masa komai yayi dan haka ya ce suje gidan nasa, Fatima na kwance kan cinyar Mama tana mata tsifa sukayi sallama Mama na ganin Azeezat tayi ihu ta ce "Wato kai isma'il ka daina jin magana ko uban wa ya sa ka dawo da ita." "Uban shi ne ya ce ya dawo da ita." Baba ya bata amsa. Sunkuyar da kai tayi duk masifar ta tana shakkar Baba. Bayan sun samu wurin zama Baba ya ce "Isma'il ga ni ga Mahaifiyar ka da matarka ka fada mana wacece wannan matar da yarta."
"Baba wata daya da ya wuce lokacin da aka sace Fatima ina cikin tafiya kai na ya dau zafi sosai, banyi auni ba sai gani nayi na bege ta, bayan na kaita asibiti wata daya kafin ta warke domin taji rauni sosai, sa'a ta daya bata mutu ba tashin ta ta ke fada min ce wa marainiya ce bata da kowa shine nace tunda Allah ya hure min Baba a taimaka kamar yadda Allah taimaka mana." Babu wani alamun tausaya mata da su Mama sukayi sai Baba ne dai ya jin jina wa lamarin can ya ce "To shi taimako dai abu ne mai kyau, idan ka rufa ma wani asiri Allah sai ya rufa maka, amma abin tsoro ne ka dauko mutumin da baka san asalinsa ba da sunan taimako." Sunkuyar da kai yayi cikin rai yana kyautata zaton Baba zai shige masa gaba. "Baba wannan matar ba kamar yadda kake zato bace, na tabbata baza samu matsala ba." "Baba, Mama zama ta da isma'il ta kare indai ba zai kai ta inda ya dauko ta ba."Inji Fatima.
Kwanciya tayi kan cinyar Mama tana rera kuka, shi kansa Isma'il hakan ba dadi yake masa ba domin yana matukar kaunar matarsa ko dan halaccin data masa.
"Fatima dan Allah kiyi hakuri ki fahimce ni, banida wani niyya illa taimaka mata." Harara Mama ta watsa masa tuni yayi shiru, rarrashin ta Mama ta shiga yi tana ce wa "Indai nina haifi Isma'il bai isa ya ajiye wata bayan ke ba." Duk abinda ake Azeezat na ji, ta shiga rudun duniya sosai cin fuskar da ake mata ke mata daci. "Na bijerewa maganar iyayena banga dai-dai ba, Abdul ka cuce ni ka gama da rayuwata, ka jefa ni cikin kangin rayuwa ina ma Allah zai dauke raina a dai-dai wannan lokacin da nafi kowa farin ciki." Goge hawayen dake bin fuskar ta tayi ta ce "Mam.... " "Ke kar ki sake ki kirani da Mama ni ba Mamarki bace." Inji Mama. "Tunda abin ya zama haka, me zai hana ta zauna matsayin ƴar aiki ma Fatima."Inji Baba
"Baba indai ba umarnin hakan kake bani ba, ni bana bukata yanda duniyar nan ta zama abin tsoro ba zan taɓa lamuncewa da labarin ƙaryarta na zauna tare da ita ba aje watarana baya nan ta kashe ni." "Isma'il dole ne ka maida yarinyar nan inda ta fito, don farin cikin Fatima shine namu ka tuna ce wa amana take a hanunmu." "Baba kaima ka goyi bayan na hakura da aikin alherin danayi niyya?" "Kwarai, umarni nake baka, zaka iya mata alkhairi,misali ka bata kuɗi wannan ban hana ka ba amma zama cikin gidanka ne bai ta so ba."
Rintse ido yayi yana matukar bakin cikin abinda su Mama suke fada. Babu yadda ya iya hakanan ya tashi jiki a sanyaye. "Sai a tashi a bishi ko karuwa." Inji Fatima. Simi-simi ta ja yarta tana hawaye har suka fice a harabar gidan.
Comment
Like
Share nd vote
0 comments:
Post a Comment