65-66
⚖ππππππππππππππ⚖Maidubu ta tashi ta janyo akwatinta sae lokacin ta tuna da inda Ahmad ya nunawa yan fashinnan inda ya aje jakar taje ta dauko ta tasaka ta a dayan akwatinta, ta fito tana kuka ta shiga napeep sae kofar gidansu, ta shiga gidan ta samu mama na kitchen baba bayanan, ta wuce dakinta ta aje kayanta ta cigaba da neman wayar da bindigar, amma bata gansu ba tana cikin neman ne taji motsi a waje tana fitowa suka hado ido ita da mama ae ko mama ta karaso da gudu ta rungume yar'ta Mai-dubu kuka mama kuka.
Baba ne ya shigo gidan, jiki a sanyaye yana ganin Mai-dubu bacin ranshi ya qaru, baba ya hade fuska sosae kamar bai taba dariya ba.
Ya fara da "fadin ke wa yayi miki ixini xuwa nan gidan? Mi kikaxo yi? ko muma din xuwa kikayi ki kashemu ?tau bara kiji wallahi! Kiyi maxa kibar gidan nan, Maidubu ta kalli Babanta tana share kwalla "tace baba nan ne gidanmu, kuma kaine mahaifina idan nabar nan gidan ina zanje?
Sae da Baba ya cije bakinshi ya kwadawa Mai-dubu shoe din shi a kai inda akayi mata dinki ya sake faccewa sae jini yake fiddawa Kasancewar shurun da yayi mata daxun sae da akayi mata dinki .
"Baba yaci gaba da fadin ni ba ubanki bane, Allah ya tsaran in haifi dan da ke neman ganin bayan raina, kije dae can ki nemi ubanki, da kika tanbeni inda zakije ki bi duniya mana, na fiki sanin inda ake xuwa ne dom sayarda mutunci, ga gidan karuwwai nan daban dabam kisamu Wanda kikayi joining mana, kuma ki fita idona wallahi Kiyi maxa kibar gidan nan kafin in kasheki, dom rayuwarki batada wani anfani a garemu Mai-dubu sae aikin kuka takeyi.
Baba shiga daki da alama abun bugu zai daukko mama ta kalli maidubu "tace Maidubu ban yafe maki ba kibi duniya kamar yarda babanki ya furta, inason Kiyi hakuri ki jure wuya da duk tashin hankali da kika sami kanki, kije gidansu Balkisu ki xauna har babanki ya gama fushinshi, nasan da kanshi zai nemeki maidubu ta dauko hijjab dinta ta kulle dakinta ta rike key a hannunta.
Baba ya fito rike da bulala yana fadin tau tunda makyajin magana ki jirani inxo, yana sako shoe din shi Mai-dubu ta kalli mama "tace yake mahaifiyata nasan idan kowa yakasa fahinta ta nasan ke kin fahinceni, kuma kin yarda da tarbiyyata wallahi mama ban aikata ba, kuma banada sa hannu a kisan Ahmad ta fashe da kuka .
Mama "tace nafi kowa sanin baki aikata ba, ya'ta, Mai-dubu "tace mama zan tafi kuma nayi maki alkhawarin kare mutunci na aduk inda na sami kaina Mai-dubu ta riqe mama itama ta riqeta duk suka sa kuka.
Baba ya iso wajen yana shirin dukan Mai-dubu, mama ta riqe shi tana "fadin dakata baban yara ko baka qaunar maidubu ni ina qaunar ta! kuma Wallahi sae haqqin wannan yarinyar ya bika, baba "yace kice in mutu yau din nan sannan insan naci amanar maidubu kuma ki saki bulalar nan ko in dakeki wallahi .
Maidubu ta russuna har qasa ta kalli babanta "tace kayi hakuri yakai babana bantaba ganin sabaninku ba, Dom Allh kuyi hakuri karku fara akaina. baba "yace idan ma bamu taba yi ba, ae munyi a zamanin ki tsinanniya kawae,
Maidubu "tace baba zan tafi kamar yarda kayimin umurni, kuma insha Allh baxan qara dawuwa nan gidan ba, har abada. baba "yace da kin kyautawa kanki.
Maidubu taci gaba da "fadin baba inason kasa a Ranka har yau banada sa hannu a kisan Ahmad, kayi hakuri baba banyi rashin kunya ba idan nace lokacin da zakayi da kasani wulaqanta yar'ka da kanka! yana nan xuwa, sae dae zuwa lokacin nadamar ka bata da anfani .
Baba ya fashe da kuka yana "fadin tsinuwar da nayi miki akaina ta fara aiki kenan maidubu, keda idan ina magana bakya tada kai sae na qare yau ni kike gayawa sae nayi nadama, lallai ni Alhaji Muhammad nayi baqar haihuwar.
Tau wallahi kibar gidan nan tun ban kiramaki police ba .
Mai-dubu "tace yi hakuri baba idan na batama sannan ta maido kallon ta ga mama ta bata key din dakinta "tace mama Dom Allh kayimin alkhawarin duk wuya duk rintsi baxaki bar kowa ya shiga dakina ba da hakan zan tabbatar da har yanxu kina qaunata. ta fashe da kuka ta fita.
Mama ta rushe da kuka itama "tana fadin zama da kai ko hasara wallahi ayau din nan nayi danasanin auren ka kuma ba dom mahafiyata "tace idan na kuskura na bar gidanka ba tare da kai ka koreni ba ko tana lafiya bata yafemin ba shine maganarta ta qarshe dani Allah ya dauki ranta. da yau din nan nabar gidanka baba dae bai tanka ta ba yashige dakin shi .
Maidubu na fita tayi gidansu qawarta balkisu, tana shiga inna ta qaraso wajen ta da sauri, "tana fadin Mai-dubu lafiya? Miyasameki haka? Inna ta cire Dan kwallin Mai-dubu ta daure mata inda jini ke fita, Maidubu ta fashe da kuka ta rungumi inna, sannan ta kwashe duk labarin abunda ya faru ta gayama inna, inna ta dau taslima hawaye nabin idonta duk Wanda yasan maidubu ya ganta yanxu da qar ya ganeta Dom tayi baqi tayi rama amma har yanxu kyanta yana nan. inna ta xaunar da ita "tace zasu xauna da ita har babanta yadaina fushin da ita, ko idan gaskiya ta bayyana Mai-dubu "tace inna ko angane gaskiya baxan koma gidanmu ba, dom baba baya qaunata nima bana qaunar..... Inna tayi saurin dakatar da ita da "fadin 'kul maidubu kar ki bari kiyi qusquren furta mummunan kalami akan mahaifinki.
"Jita jitar da mutane keyi akan Ridwan da momyn shi, wae sunada sa hannu akan mutuwar Ahmad yakai ga yan sanda kuma qanin Ahmad yayi alkhawarin ko duk dukiyar da Ahmad ya bari zata qare sae sun nemo mai haqqinshi, na kisan da akayiwa yayanshi. sae ankama wadanda suka aikata wannan kisan ko su waye, yakai report ga police Dom yaji labarin Ridwan har dukan da momy tasa anyiwa yayanshi Ahmad, sae dae police na hangen matsala daya xuwa gidan JUSTICE ALIYU DA JUSTICE HUWAILA.
Wani daga cikin police din ya dauki report din qannan Ahmad yakaiwa Commissioner of police, tare da neman ixinin xuwa kamun Ridwan Dan gidan JUSTICES ALIYU DA HUWAILA sae da Commissioner ya tashi tsaye da sauri ya doki tebur yana fadin nop!!! kar Wanda yayi kuskuren xuwa gidan JUSTICE ALIYU Dom kamun dansu shida JUSTICE HUWAILA tau bara kaji in gayama JUSTICE HUWAILA kadai ta isa tasa duk kanninmu a sallamemu akan wannan kujerar dom haka kujira sae na kira JUSTICE ALIYU dom neman ixinin shiga gidan shi, dom kamo dansu RIDWAN.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖πππππππππππππ⚖
[11:16, 1/8/2018] Barista: ⚖πππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Sadaukarwa ga Zahra Muhammad Muhmad Surbajo π€π
Mijin barrister
67-68
⚖ππππππππππππππ⚖Commissioner ya daga waya ya kira "JUSTICE ALIYU" suka gaisa cikin ladabi da girmamawa. Commissioner yayi shuru dom yama rasa ta inda xai fara yiwa Justice bayani, Justice "yace uhim ina jinka commissioner! ya kayi shuru.
Sannan Commissioner "yace sir, "sir Ridwan" ne ake xargi da kisan wani Ahmad Wanda sukayi neman yarinya daya. Justice na kwance yana hutawa jin abunda commissioner ke gayamai yasashi tashi tsaye da sauri yana fadin qarya ne! wallahi qaryane! Ridwan ko tsuntsu baya kashi balle mutum, wannan kawae bita da kulline kuma ni ake yiwa Dom na gagara ne aka juya ga dan da nafiso dan da nakeso fiye da rayuwata amma ba komi.
JUSTICE "yace commissioner mi kuke buqata ne yanxu? commissioner "yace "am sorry sir, permission dinka muke nema Dom xuwa kamun RIDWAN, sae da JUSTICE ya runtse idonshi Dom jin maganar zaaje kamun RIDWAN sae da idanunshi suka cika da kwalla.
JUSTICE "yace Commissioner U re permitted amma inason kasani wallahi! koda alama kar wani yayi qusquren dukan RIDWAN ko yimai mummunan kallo duk Wanda ya taba lafiyar Ridwan! yasani ya taba kujerar sa. Commissioner "yace ok sir, thank you sir, JUSTICE ya kashe wayar shi ya kira wani bodyguard din shi "yace ya hada musu kayan su kuma kowa ya hada nashi kayan zasu koma gida Nigeria yau din nan.
Bodyguard din "yace ranka ya Dade Nigeria fa? JUSTICE "yace eh ko mu barka nan ne? Bodyguard din "yace No sir, Sorry Sir .
"Yafita yasami sauran yayi musu bayani duk suka shirya" jet "dinsu kawae suke jira yasha mai su diru Nigeria.
Motocine na police har guda 3 ko wacce cike take da police, suka wuce gidan JUSTICE. suna isa suka fara firfitowa ko wannen su da bindiga a hannun shi, suka zagaye gidan wasu suka shiga gate din farko, suna shiga gate na biyu Wanda ke sadaka da cikin gidan,
bodyguards suka taresu police suka fiddo bindigoginsu suma bodyguards suka fiddo nasu dom sun aje ne da subasu damar shiga cikin gidan gara kawae suyi farin wuta kowa ma zai mutu ya Dade bai mutu ba.
Daya daga cikin police din ne yayi wa police, umurni da kowa ya sauke bindigar sa. DA alama shine babbansu. Ya maido kallon shi ga bodyguards din momy "yace salamu Alaikum. suka ansamai da Amin waalaikassalam. Dom Allh ku yi hakuri nasan kuna Bakin aikin ku ne nan muka sameku amma yanxu mun gane kuskuren mu naqin neman ixinin ku. kuyi hakuri kuyi mana sallama da yaron gidan nan Ridwan. Bodyguards suka ce, Ridwan bayada lafiya.
"Police din "yace OK momyn shi fa? Daya daga cikin bodyguards dinne ya kira wayar momy ya sanar da ita xuwan police din. Momy ta fito tagansu ba Kadan ba, haka kuma taga bodyguards dinta suma duk sun halarci Copound din gidan Dom jin meke tafe da police a gidan.
Dayan police dinne yayiwa "momy bayanin abunda yakawo su, momy ta fiddo ido waje "tana fadin qarya, Ridwan ko tsuntsu baya kashe balle mutum, Dom haka kuyi gaggawar barin gidan nan tun Muna gane juna.
Police din ya koma gefe ya kira Commissioner ya gayamai abunda momy "tace. Commissioner "yace kar wani yayi qusquren jayayya da ita, mubani 2 minute inyi waya da mijinta. Police din "yace OK sir.
Commissioner ya kira "JUSTICE ALIYU" ya gayamai. Justice Aliyu ya kira Matar shi, justice HUWAILA "yace da ixinin shi akaxo kamun RIDWAN momy "tace da ixinin ka fa kace? "yace ki basu shi kawae.
" momy tace haba husby, ya axayi inbari a fita da RIDWAN gidan nan bayan nasan bayada laifin, justice "yace "wify idan har na isa dake ki basu dama su fita da RIDWAN,
Kuma karki damu ina hanyar Nigeria. momy "tace baka ce sae kayi 3 month acan ba justice "yace dolene in dawo yanxu karki manta Ridwan bayada kowa sae Allah sae mu. Momy "tace wishes u safe trip husby" Justice ya ansa da "thank you wify".
Momy "tace ina shaidar ku ta Kama my son suka bata warrant of arrest ta ansa ta karanta sannan tace su shiga dom RIDWAN bayada lafiya har baisan ko waye a kanshi ba. Ta shiga gaba tana fadin follow me, suka bi bayanta suka shiga room din momy dom ta maidashi dakinta tunda bayada lafiya.
Ridwan ne kwance baya ko motsi kuma ba suma bane yayi ba. dom wani lokacin yakan bude ido yabi momy da kallo idan "tace yadae my son sae ya lunshe ido batare da yayi magana ba.
Suka ganshi kwance suka kira waya a headquarter dinsu cikin minute kalilan aka kawo musu gado mai taya na daukar maras lafiya suka axa RIDWAN bisa suka fito dashi waje, momy ta fashe da kuka "Jet ne ke qoqarin sauka a Compound din gidan bayan Jet din an rubuta ("JUSTICE ALIYU".).
"Jet din yagama sauka Justice ya fito shida bodyguards din shi, suka iso wajen RIDWAN Justice ya rike hannun shi yana "fadin wify miya sami my son? Momy ta rungume justice tana fadin husby Ridwan ya fada tarkon soyayya ne, Justice "yace wace ce wannan yarinyar? Wify ko bana gari ai kin isa ki zamewa "our son" garkuwa momy "tace naje koda naje "babanta har ya daura mata aure.
JUSTICE ya rungumi RIDWAN yasaka mai kiss a goshi, "yace kayi hakuri my son insha Allh baxaka sha gwagwar mayar rayuwa ba, Mutukar muna raye . duk abunda suke yi RIDWAN yana kwance baisan sunayi ba. Justice ya dagawa police din hannu alamar su wuce. shiko ya rike hannun momy sukayi cikin gidan, momy na kuka tana waiwayar su har suka fito, shma JUSTICE juriya kawae yake dom da Kadan yayi kukan, suko suka shiga gidan.
Da "qar justice ya samu momy ta dan nutsu yatashi ya fito yabi bayansu Ridwan suna isa police station aka wuce da RIDWAN hospital tare da jami'an su, su suke kula da Ridwan daga su sae doctors bayansu ba mai shiga room din.
JUSTICE ya nemi da atura case dinsu Ridwan court. Aka tura su court amma sauraren kara sae accused person yaji sauqi.....
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[08:03, 1/9/2018] Barista: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyama Nura. Daughter's lyk no othersππ
Mijin barrister
69-70
⚖ππππππππππππππ⚖Sae da RIDWAN ya kwashe 3days a hospital aka sallameshi anbashi sallamar da Safe aka shiga court da qarfe 12:00 na rana, aka fara sauraren qara RIDWAN baima damu da qanshi ba. Maidubu yake tausayi dom baisan halin da take ciki ba yanxu.
Aka saurari qara, iyayen Ridwan duk sun halarci Court alkhali "yace a wuce da Ridwan prison sae xama na gaba.
Maidubu batasan halinda Ridwan yake ciki ba. Amma tana yawan jin damuwa gameda Ridwan ta rasa miye dalili. "xarah ce ta shigo gidan su maidubu da sallamar ta suka gaisa da mama! ta tanbayi ko Mai-dubu na nan?. Mama ta kwatanta mata gidan su balkisu taje tashiga da sallama inna na xaune waje Mai-dubu da balkisu na daki suka gaisa da inna, ta shiga suka rungumi juna ita da Mai-dubu, Maidubu "tace xarah kinji abunda a kayimin tana "fadin maganar hawaye nabin fuskar ta zarah ta share mata kwallar tana "fadin daina kuka qawata, duk Wanda yasanki yasan baxaki iya aikata Kisa ba, suka xauna xarah ta kwashe duk labarin abunda ke faruwa da Ridwan ta gayama Mai-dubu, "tace yanxu haka Ridwan yana Prison, ranar Monday ne xama na gaba Mai-dubu tayi kuka kamar ranta zai fita tana "fadin sunci amanarshi wallahi ba Ridwan bane tayi kuka harta gode Allah.
Maidubu ce kwance tana tunanin Ridwan kwalla nabin fuskar ta tana fadin kayi hakuri Ridwan duk abunda yafaru dakai nice silar, pls RIDWAN, "forgive me RIDWAN" tana fadin maganar tana kuka Balkisu tashigo tana rarrashinta har Mai-dubu tadanyi shuru, sae lokacin ta tuna gobe Monday kuma gobene xasu fara rubuta exam a skul dinsu, gashi gobe ne xama na gaba da xaayi a court dole ne inyi duk abunda xan iya don ganin kafita wannan qangin rayuwar Ridwan.
"Maidubu ta tashi tayi shiri ta fito taje gidan wani Dan uwan mama ta gayamai matsalar ta sannan "tace tanason yanemo mata masu sayen motar ta yau din nan, haka kuwa akayi, ya nemo mai sayen motar aka sayarda motar million 2 da dubu dari biyar, Mai-dubu taba Dan Uwan mama din da ya kawo mata mai sayen motar dubu dari biyar, ta riqe sauran ta nemo Wata ta rubuta mata exam sae ta biyata Dom tasan idan ta xauna da kanta sae Allah taci exam din, Dom yanxu batada aiki sae tunanin Ridwan da kuma kukan da har yabi jikinta.
"Maidubu ta samu wani kwararren Barrister Wanda kowa ke fadin baitaba samun matsala akan sharia ba. Baya failure. Duk Wanda ya tsayawa Shike nasara ta bashi dubu dari biyar dom "yace 1million xata bashi idan yayi nasara a case din.
"Yau takama "Monday" tunda safe Mai-dubu ta tashi tayi shiri dom yau qarfe 10: 00 na safe xaa fara shariar Ridwan taje court ta cika maqil Dom ganin shariar Dan gidan JUSTICES aka shigo da Ridwan court kallo daya Mai-dubu tayiwa Ridwan ta fashe da kuka sae da kowa ya kalleta shima RIDWAN kasa jurewa yayi sae da yayi kuka marar sauti kwalla nabin fuskar sa.
Registerer "ya doki kofa sau 3 alamar Alkhali xai shigo court kenan. kowa ya tashi tsaye sae da alkhali yashigo ya xauna, sannan kowa ya xauna aka fara karanta kara Barristers sun tashi sun gabatar da Kansu da sunayensu ga court.
"Barrister" da Mai-dubu ta kawo duk da babu Wata takamammiyar hujjar da xata fitar da Ridwan a wannan halin duk shaidar da Barrister din ke qoqarin gabatar wa ga court idan yafada sae kawae Alkhali yayi watsi da ita, haka aka tashi zaman ranar.
"Alkhali yayi gyaran murya sannan yafara da "fadin The case is adjoin to 5 january 2018 ya buga hama duk jama'ar court din suka dau ka da "fadin coooooourt!!! Sae da Alkhali yafita sannan kowa ya fito.
Hankalin "Mai-dubu ya kara tashi sosae ta nemu wani Barrister shima kwarrare ne sosae amma yakasa yin nasara, haka Mai-dubu tayita wahala har duk kuddin hannunta suka qare .
"A bangaren iyayen Ridwan kuwa, tunda akace Justice Usman ne xaiyi shariar Ridwan, JUSTICE ALIYU yasan akwae matsala dom matsayin kujerar su daya kuma basa ko ga maciji, kasancewar Justice Usman mutum ne mai ansar cin hanci shiko JUSTICE ALIYU baya ansar cin hanci, Justice Usman yataba bawa Justice Aliyu bribery lokacin da Danshi yayi raping ga Wata yarinya.
Diyar talakkawa Justice Aliyu yaji tausayinta hakan yasa ya daukarwa kanshi alkhawarin hukunta wanda yayi mata wannan aika aikar ko dan gidan waye yace ko Dan shine sae ya fuskanci hukunci. Ashe dan gidan Justice Usman ne. Justice Usman Yayi yayi ya kashe maganar amma Justice Aliyu yaki yarda "yace baya ansar cin hanci. kama dolene yabiwa yarinya haqqinta. hakan yayi sanadin da Justice Aliyu yayi Sentencing Dan Justice Usman 25years in prison for d offence of raping.
Justice Aliyu "yace nasan ya riqeni da wannan abun shine yake son ya dauki fansa akan dana .Momy ta buga ko ina ba mafita. yanxu batada aiki sae kuka kawae.
Su maidubu an qare exam tabiya wace ta hau mata exam din kuddi yanxu exam din kawae suke jira ta fito.
Yau takama 5th ga January kuma yau ne akayi xama na qarshe a court inda Alkhali yayi watsi da duk Wata shaidar dake bawa Ridwan kariya. Yace Ridwan ya tabbatar mai laifi. Alkhali yayi gyaran murya sannan yace "I JUSTICE USMAN SAHABI " I REALIZED DAT THE ACUSSED PERSON IS FOUNDED QUILTY FOR THE OFFENCE OF MURDER I SENTENCE RIDWAN ALKHALI ALIYU TO LIFE IN PRISON WITH HARD LABOUR ND WITHOUT OPTION OF FINE.
"Allah Sarki RIDWAN police suka saka shi mota aka wuce dashi prison, duk da juriya irinta JUSTICE ALIYU amma da yaji ankai Dan shi prison sae da ya xubar da kwalla, Kasancewar shi mutum mai power a fannin sharia hakan yasa yayi umurni da achanxawa Ridwan prison akaishi na manyan attajirrai. Wanda ke dauke da gado, Fridge, air conditioner, da kayan kallo, kuma yace kar asashi ko wanne irin aiki haka kuwa akayi.kuma sae abunda yaga dama yakeci duk wani jin dadin rayuwa akwaishi cin wannan prison din Baban cin wannan prison din da house kawae ambata record din mutum antaba kaishi prison shine kawae banban cin. Kuma baa fita xuwa ko ina kamar yarda kake yi a gida shine kawai babancin wannan prison din da house.
Tunda aka zartarwa da Ridwan hukunci Mai-dubu tayi kamar tayi hauka kuka kan baa magana. sae da aka fito da ita a court din. Maidubu tayi alkhawarin ko xata rasa ranta baxata bar Ridwan ya qare rayuwar shi a prison ba. ta koma gida ta daina cin abunci tayi baqi ta qara rama bayan kwana biyu results dinsu na shaidar kammala secondary skul dinsu ta fito, kuma duk Mai-dubu ta samu nasara ta kira yayanta Bello "tace Dom Allh ya nema mata Admission a India tanason tayi karatun (Law), yaya ya jinjina maganar Mai-dubu "yace Mai-dubu ( Law) fa kika ce, kinsan yarda karatun (Law) yake kuwa? Mai-dubu tace aikin sharia wasa da rayuwa ne fa kuma mi xakiyi ne da karatun Law keda ko maganar Kiyi karatun Law akayi maki sae kin ce God Forbid. Maidubu tace Yaya dole ne xata sakani karatun sharia ko yanxu.
⚖πππππππππππππ⚖Maidubu "tace yaya duk wahalar dake gareshi zan jure, kuma insha Allh xan fito da kyakkyawan results, yaya "yace Mai-dubu duk abunda kikaga iyayen Ridwan sun kasa yimai bana tunanin ke xaki iya yimai shi, iyayenshi Nada power ko wanne gefe idan kuddi ne suna da power, haka fanin sharia
Shima, kinsan ko, kosu waye iyayen Ridwan, Maidubu tace bansan su ba, kuma ban damu da matsayin su ba. Ina magana akaina ba akan iyayenshi ba. Tau bara Kiji RIDWAN dane ga JUSTICE ALIYU da JUSTICE HUWAILA su masu taimakon wasu ne, amma kikaga sun kasa taimakon dan'su. yi hakuri kawae Mai-dubu idan kin sami wani mijin Kiyi aure ki manta da wani Ridwan,
Maidubu "tace Nop! Nop !! yaya ta Fadi maganar da tsawa tsawa, sae kuma ta rushe da kuka tana fadin yaya idan baxan sami taimakonka ba, kawae ka gayamin wallahi yaya! wallahi yaya!! ko xan rasa raina nayi alkhawarin sae nayi saving life din Ridwan, ina so kasani "yaya idan xan mutu banyi aure ba, wallahi baxan aure kowa ba sae Ridwan tasake rushewa da kuka mai ban tausayi tana fadin..
"Yaya inason kasani wata sadaukarwa sae a masoya, na yarda na bada rayuwar fansar Ridwan, yaya Ridwan bayada laifi bayada sa hannu a kisan Ahmad, "yaya kasa a ranka ni Mai-dubu na dau damarar fiddo Ridwan prison koda ko yana fito ina rasa raina ne.
"Yaya Bello yaji tausayin qanwar shi sosae Kasancewar dama yana ji da Mai-dubu sosae ko a cikin qannensa, dom ko lokacin da Baba ya tarasu ya gayamasu ya kori maidubu, kuma ya fidda ta cikin xuriar sa, "yace ko mutuwa yayi bai yafe abawa maidubu gadonshi ba, tun lokacin yaya yasu ya maida maidubu gidan shi, amma mama "tace yabarta gidansu Balkisu kawae .
"Yaya "yace Maidubu kin tabbatar xaki iya wannan karatun? Ta ansa dafadin eh! "yace Kiyi hakuri qanwata xan kaiki amma "under 1 condition" maidubu "tace inajinka yayana yaya "yace idan kinje baxaki dawo gida Nigeria ba har sae kin kammala karatun ki, maidubu "tace na yarda yaya "yace nasan baxaki taba yin nasara ba a wannan sharia maidubu "tace kayimin fatar alkhairi yayana yaya "yace maidubu Allah yabaki nasara aduk abunda kika saka gaba na alkhairi kuma karki gayama kowa xakije ko ina.
Mai-dubu "tace yaya har mama "yace har kowa ma. kuma xanyi duk abunda yadace. xaki wuce a satin nan insha Allh. Mai-dubu taji dadi "tace nagode yaya sukayi sae anjuma.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖πππππππππππππ⚖
[14:02, 1/10/2018] Barista: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat Nasir Gwandu Nd Seeyamah Nura. Daughter's lyk no other'sπ
Reader's ina godiya da qaunar ku da kulawar da kuke nunawa novel din nan MIJIN BARRISTERπ ina qaunar ku reader's aduk inda kukeπ love u die π
Mijin barrister
71-72
⚖ππππππππππππππ⚖Mai-dubu tayi shirin zuwa "prison Dom ziyarar Ridwan, taje anbata damar ganinshi na 10 minute aka fiddo shi Maidubu ta rugo da gudu ta rungume shi tana fadin, "I miss u Ridwan," Shima "yace "miss u too Babatah" Ridwan ya daga fuskar maidubu yaga tana hawaye shima kwallar ya share, sannan ya saka harshin shi ya lashe hawayen ta tas yana fadin daina kuka kinji babytah.
"Maidubu "tace dole ne inyi kuka Ridwan! "nice silar shigar ka wannan halin, Maidubu ta sake fashewa da kuka Ridwan ya rungumeta yana bata haquri ya zaunar da ita yana ta aikin rarrashi, Ridwan "yace banason ki xargi kanki, baby duk abunda ya faru dani muqaddari ne daga Allh, ki daina damuwa kinji. Maidubu ta daga kai alamar eh! "yace sannan dom Allah baby kiyi qoqarin mantaniπ idan kin sami miji Kiyi aure kinji baby, tunda Allah ya hukunta ni tawa rayuwar a "prison zata qare,
"Maidubu ta rufe mai baki tana kuka tana "fadin Nop! Ridwan wallahi ko xan mutu banyi aure ba, baxan iya rayuwa da wani bakai ba, dakai na tsara rayuwa ta, kuma dakai xanyi rayuwar aure insha Allh,. Ridwan kuka Maidubu kuka ba mai rarrashin wani. "prison officer" ne ya leqo yana fadin Ranka ya dade lokacin da aka baku yayi Ridwan "yace OK duk suka tashi tsaye shida Maidubu suna kallon juna kwalla nabin fuskarsu suka sake rungumar juna da qar suka rabu.
"Maidubu ta dawo gida "qawarta Balkisu "tace mata yaya Bello ya kira waya "yace agayamaki, tayi parking kayanki, yana nan xuwa anjuma Maidubu "tace OK .Maidubu "tace xan fiddo wayata in fara anfani da ita dom nasayo line .
Balkisu "tace hop! dae lafiya, kuma ina xaki koma ne, kodae munyi miki wani laifine? Maidubu "tayi murmushi "tace wallahi! qawata bayan alkhairi ba abunda kukayimin, Balkisu "tace tau miyasa yaya "yace Kiyi parking kayan ki? Maidubu "tace bari har yaxo sae muji .
Maidubu taje tayiwa qawarta zarah sallama tagayama inda xataji amma tace dom Allah ko Nura batason yasan inda taje.
"Ana gama sallar magarib "yaya yayi parking a kofar gidansu Balkisu, inna "tace yashigo ya shiga har dakin inna, sukayi magana da inna ta fahinta, yagayamata xai dauki Maidubu da Balkisu. Dom yanema masu admissions xasu cigaba da karatunsu ita Maidubu India xaikaita. "yace itama Balkisu yanema mata admission a London bayasan ya hadesu ne dom kar suqe yin karatun idan suna ganin junan su, tunda har yanxa ba wace ta mallaki hankalinta cikinsu Dom yanxu ne suke 17years. Inna taji dadi sosae kuma tayi farinciki ba Kadan ba.
"Yaya ya sako qeyarsu gaba, suka shiga mota ko wace su kuka takeyi "inna tayo musu rakiya har wajen mota tana "fadin tau yan mata na, Allah ya karemin ku aduk inda kuka sami kanku kuma Dom Allh a mayarda hankali sosae ga karatu.
"Yaya yakaisu gidanshi suka kwana, da asuba ya wuce dasu "airport" baikoma gida ba, sae da yaga tashin jiragensu.
⚖ππππππππππππ⚖
INDIA
Jirginsu Maidubu na sauka a INDIA. suka shiga mota sae cikin gari daga nan aka dauki maidubu da motar haya sae gate din UNIVERSITY OF LAW INDIA. Makarata ce wace take koyarda harkar sharia kawae makaranta ce mai koyarda duk wani Law na duniya tare da koyon duka da qa ida."
"Maidubu sae raba ido takeyi wayarta ce ta hau ruri, koda ta duba taga nom din yaya ta dauka suka gaisa, ta shaidamai isowarta kenan gate din University din, "yaya yayi mata fatar nasara sukayi mai anjuma .
Maidubu ta shiga skul din taga wasu clases maqil da "students suna lecture, ta nemi waje ta xauna ba jimawa suka fito. Wasu kyawawan yan mata wa danda ko baa gayama ba Kasan suna ji da Kansu. Su na hango suna dosowa wajen Maidubu suka iso suka ce da ita" Hello Maidubu ta kallesu "tace "Hy dayar ta bata hannu itama Maidubu ta bata, suka gaisa tana "fadin Sunana Sa'adatu Alkhali, Kuma ni yar Nigeria ce, ina karatun Law a University dinnan.
" Itama dayar tabata hannu suka gaisa. "tace Sunana, Maryam Aliyu, nima yar Nigeria ce, karatu ya kawo ni nan India, ina degree ne a Law Maidubu tayi murmushi "tace Allah Sarki.
"Dayar tabata hannu itama suka gaisa "tace Sunana, Nana Aisha Bala, nima yar Nigeria ce, ina karatun law ne a nan da fatar xamu xama friends, Maidubu tayi murmushi tace why not dear.
Sunana, Maidubu Muhammad, nima yar Nigeria ce, kuma yau ne "first day" dina a university din nan, nima xanyi degree ne a Law insha Allh, naji dadin haduwa da ku, ku duka kuma daga yau munxan frnds .
Tun daga ranar suka xan qawayen juna sosae. duk inda kaga dayansu dolene kaga sauran. tare suke daukar lecture! kuma tare suke xuwa karatun dare! Maidubu ta maido hankalinta sosae. hakan yasa take fahintar lectures dinta, har lecturers suna maganar irin basirar da Allah yayiwa Maidubu, dom ko su ya'yan indiyawa Maidubu tafisu fahintar lectures. akwana atashi na Allah ne, yau ne su Maidubu suka xana jarabawarsu ta shiga aji 4 a university, Maidubu batayi kwana ba karatu kawae takeyi ita da kwayenta, har gari ya waje suka shiga hell din exam da qarfe 8 :00 na safe Kasancewar "course dinda sukayi exam dinshi yau yana da wuya dom "LEGAL SYSTEM" ce suka rubuta yau. Hakan yasa suka dauki 3hours amma Maidubu 1 hour kawae tayi tafito Dom ta kare.
Maidubu na hango kwance tana kuka, marar sauti idan da sabo qawayen maidubu sun saba ganin ta tana kuka, idan suka tanbeta dalili sae "tace bakomi ko "tace musu tayi "Missing parent dinta ne. Har suka hakura suka daina tanbayarta, sae dae idan tafara kuka su riqa rarrashinta.
Lokacin sallah yayi sukaje sukayi sallah. Maidubu ta dade tana yiwa Ridwan addua kuma tana yiwa kanta fatar samun nasara akan abunda ta saka a gaba
Wayar maidubu tayi kara tana dagowa taga number qawarta, Balkisu ce ta dauka tana murmushi suka gaisa suka danyi fira sannan sukayi sae anjuma Tun bata kashe wayar ba, "waiting call" yashigo taga qawarta Zarah ce ke kiranta ta dauka tana yiwa zarah tsiya, tana fadin tsohuwa! tsohuwa!! zarah tayi dariya itama maidubu dariyar tayi.
"Tana fadin Kiyi da kyau naki lokacin yana xuwa. kuma sae na rama duk sukasa dariya. "Maidubu tace ya Babynki Nura, Niko ya tawa babyn, Zarah tayi dariya tana "fadin duk lafiyarsu qalau ., babynki ta wahar dani sosae, jira kawae nake taxo duniya in rama. Maidubu tayi dariya tana "fadin kina ma farashi, ae ko bana kusa nasan Nura baxai bari ki dake babynmu ba, duk suka sa dariya.
"Maidubu "tace kina jimin labarin Ridwan, zarah "tace Maidubu Ridwan ya wahala akan rashinki, duk ya rame yayi baqi miyasa kika ce kar a gayamai inda kike, Maidubu ta share kwalla sannan "tace Allah Sarki Ridwan. Zarah taci gaba da fadin lokacin da yaga kin daina xuwa xiyarar sa. momynshi taje dubashi "yace Dom Allah ta bincikeki ko lafiya kike ya daina ganin ki, koda momy taje gidanku !
Baba ya tareta da fada yana fadin basu San inda kike ba, Dom ya koreki har bodyguards dinta suka tashi dukanshi, ita ta hanasu "tace ko ba komi yaci albarkacin yar"shi Maidubu tace... Allah Sarki zarah "tace idan kikaga Ridwan yanxu sae kinji tausayinshi. har cewa yayi shidae akashe shi kawae ya futa, sae da Nura yayimai magana ya bashi hakuri, Dom Nura duk Friday yana xuwa wajenshi Maidubu ta share kwalla tana fadin injin dae ko Nura baisan inda nake ba? zarah "tace ah ah baisani ba suka sha firarsu sukayi sae anjuma.
Barrister for life π
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin Barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[14:04, 1/10/2018] Barista: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamahπ
πAm sick reader's ur prayers is needed plsπ
Mijin barrister
73-74
⚖πππππππππππππππ⚖Maidubu na qare waya da qawarta zarah ta fada gado tana kuka sosae, tana mai jin tausayin rayuwar Ridwan halinda ya tsinci kanshi ciki duk a dalilinta.
"Qawayenta ne suka shigo room din da sallamarsu sukaga maidubu kwantace idanunta na kallon sama fuskarta duk ta jiqe da kwalla, sukayita sallama amma Maidubu ko motsi bata yi ba, hakan yasa suka gane tayi nisa a duniyar tunani, Nana ce ta iso dab da ita tana "fadin Barrister Maidubu lafiyarki qalau kuwa? Mi kike tunani haka ne ? Munata sallama bakiko sani ba? Sae da Nana ta dafa kafadar barrister Maidubu tana "fadin Barrister! Barrister!! Sannan Maidubu ta tashi xaune da sauri kamar wace taji tsoro. Tana "fadin kayi hakuri Ridwan, naso ace munyi aurenmu cikin kwancin hankali, amma babana yaqi yarda da hakan ya dauramin aure da Ahmad sae ta dago kai sukayi 4 eyes ita da Nana.
Maidubu "tace ina Ridwan din yashiga ne? Nana "tace waye Ridwan?Maidubu ta fashe da kuka tana "fadin ashe ba kaiba ne a xahiri?" Ashe gixo kakemin? yaushe xan ganka ne Ridwan? yaushe xan hado ido da muradin xuciyata ne? sae ta fashe da kuka Sa'a ce ta shigo itada Maryam suna "fadin "Barrister" lafiya kike kuka? Maidubu ta kasa magana sae Nana "ce tayi musu bayanin abunda taji "Barrister Maidubu na "fada. Maganar ta daurewa ko wace su kai, sae tunani suke yi daban daban suka rarrashi Maidubu har tayi shuru .
"Ko wace su, ta nemi wuri ta xauna, suna kallon Maidubu, Maryam ce ta fara magana.Barrister Maidubu! Munason yau ki gayamana abunda kike boye mana har na tsawon shekara 3! ko fiye. Maidubu "tace kuyi hakuri frnds ba abunda nake boye muku. duk suka ce qarya ne, "at dsame time" Maidubu tayi tagwomi hawaye nabin fuskarta suka tutse ta har sae da tagayamasu labarinta .
"Sunji tausayinta sosae. sannan sun jinjina irin namijin qoqarin da tayi. kuma take kam yi har yanxu sun jinjinawa soyayyar da maidubu da Ridwan suke yiwa junan su. more especially Maidubu dom inda Wata ce da yanxu tayi aurenta, ta manta tarihin wani Ridwan .
Suka bata shawarwari sannan suka yi alkhawarin tayata da addua. Maidubu tadanji sanyi a Santa tayimusu godiya suka tashi xuwa karatu dare.
"Da safe suka shiga "exam hell" suka xana jarabawar "PUBLIC INTERNATIONAL LAW. Maidubu ta rigasu fitowa tasami wasu "resting chairs" ta xauna akan dayar qawayenta suka fito suka sameta xaune wajen, suma suka xauna suna fira Maidubu tayi nisa a duniyar tunani" tana tuna ko wanne irin hali mamanta take ciki, yanxu na rashinta a kusa da ita.?, ta share kwalla tana "fadin Allah Sarki mamana, Allah Sarki Ridwan! Allah yasa inada rabon sake ganawa daku.
"Qawayenta suka bata hakuri! suka tashi xuwa hostel! suna yiwa maidubu tsiya wae aunty ce! tunda ta taba aure tasan abunda basu sani ba, duk da halinda maidubu take ciki amma sae da tayi murmushin maganar su. Maidubu bata faye dariya ba sae dae tayi murmushi mai daukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji, hakan yasa maxa dayawa kan nemi kulla alaqa da ita, amma San maidubu taqi bawa kowa damar xama ko friend dinta, idan dae namiji ne balle soyayya! Maidubu Nada kamun kai fiye da tunanin duk wani mai karatu wani lokacin tana yiwa kanta kallon Matar Ridwan ta aure Dom Ridwan kawae take tunawa tayi murmushi .
"Akwana atashi na Allah ne, su Maidubu an kammala "degree " har sunje "BAR SCHOOL" sukayi shekara daya a "BAR SCHOOL." suka kammala ranar da suka fito "BAR SCHOOL" ba karamin murna sukayi ba, sukayi photona da rigar lauyoyi, suka kare . yanxu SERVICE xasu wuce.
Su Maidubu ankwashe shekara (6 )saura shekara (1) tadawo gida Nigeria tare da shaidar kammala karatunta na xama cikakkiyar Barrister kasancewar karatun law shekara(7) ne. Tayi murna ba Kadan ba, dom gani take lokacin da xata tsayawa Ridwan yayi, lokacin da xata fiddo Ridwan a prison yayi.
⚖ππππππππππππππ⚖
NIGERIA
"Mama ce kwance tana cikin halin rashin lafiya mai tsanani sosae. batada aiki sae kuka da kiran sunan Maidubu tana "fadin ya Allah! karka kasheni sae na sako fuskar ya'ta maidubu a ido! tana maganar tana kuka sosae. Tun lokacin da mama tagane maidubu tabar gidansu Balkisu. rashin lafiya ya kamata don innar Balkisu "tace mata sun kwanta ne kafin safiya maidubu tabar gidan.
"Babane xaune a gefen mama yana fadin sannu maman yara ! ya jikinki! Mama tayimai banxa ta kwaleshi, tun lokacin da Baba ya kori Maidubu a gida Mama ta juyamai baya duk farincikin gidan ya rushe .
Baba ya tashi yayi knelling gaban Mama ya fashe da kuka. yana "fadin dom maman yara Kiyi hakuri ki yafemin wallahi! harga Allah nayi nadamar abunda nayiwa ya'ta Maidubu yasake fashewa da kuka yana "fadin duk abunda kikaga nayi dom Maidubu ta xauna gidan Ahmad wallahi nayi hakan ne dom naga Ahmad yaron kirkine, kuma naga bata mallaki hankalinta ba, na dauka auren xai xama gata ne a rayuwar maidubu yasake share kwalla.
"Yana fadin ya Allah! Kaine shaidata Ya Allh nayi nadamar abunda nayiwa ya'ta. Ya Allh ka mayar mana da Maidubu tun Muna raye in nemi gafarar ta, nasan idan na mutu maidubu bata gafarceni ba wallahi haqqinta baxai bari inyi kwanciyar kabari ba, ya fadi maganar yana kuka sosae.
"Mama ta tashi xaune tana "fadin Baban yara wai yanxu Dan kwanciyar nan da nayi ne nake mafarkin wae kana neman gafarar maidubu! kagane quskurenka kagane batada hannu a kisan Ahmah har kana roqon Allah yadawo da ita kanemi gafarar ta .
Mama na dago kai ta kalli baba ai ko taga yana hawaye yana fadin ba mafarki ki kayi ba maman yara, tabbas na cutar da yarmu mama tace yarmu fa kace? Ya'ta sae ! Baba "yace Kiyi hakuri maman yara wallahi ina qaunar maidubu. Maidubu ya'ce wace take binmu sau da kafa amma idona ya rufe nakasa gane hakan, nayi mata auren dole ta hakura, na hana ayimata hidimomin bikin da akeyiwa kowa ta hakura, ankashe mijin ta, na xargeta da wannan kisan, tana kan gadon hospital tana jinya nayi mata wani rauni, ta dawo gida na tsinemata, wayyo ni Allh! wayyo ni Muhammad! idan Maidubu bata dawo na nemi gafararta ba Maman yara nasan haqqin Maidubu kawae xai iya sadani da jahhannama, Ya Allah ka mayar mana da Maidubu gida lafiya, ya fashe da kuka mai sauti har makobta sun fara shigowa gidan suna tanbayar ko lafiya Bana ne da kanshi yake yimisu bayannin irin cin xarafin da yayiwa Maidubu wasu har kuka suke yi akan tausayin maidubun da sukaji.
"Baba "yace tabbas Maidubu kinyi gaskiya da kika ce akwai ranar da xan yi nadamar da batada anfani Dom gata inayi ayau. Baba kuka Mama kuka sae makobtansu ne ke basu hakuri.
JUSTICE USMAN SAHABI. Yayi korafin ga shugaban kasa. ya aikamai latoti bila adadin yana neman shugaban kasa ya sako hannu akan takardar, dom yanason duk wanda aka xartarwa da hukunci xama prison har iyakar ranshi wato (life in prison) shugaban kasa yabada dama kawae ayi "Executing" dinsu Dom rayuwarsu batada wani anfani bayan karawa "gonnati nauyin ciyardasu kawae.
JUSTICE USMAN "yace amma idan aka kashesu kuddin nan na ciyarwarsu xaa iya yiwa" qasa" wani abun anfani dasu Shugaban kasa yaji dadin shawarar da JUSTICE USMAN yabashi. hakan yasa ya sakawa takardun hannu duk abunda JUSTICE USMAN yakeyi yana yinshi ne, Dom ya cusawa JUSTICE ALIYU DA MATASHI JUSTICE HUWAILA bakinciki .
JUSTICE ALIYU yana gida suna kallon "New shida matarshi sukaga an nuno JUSTICE Usman yana "fadin duk "prisoner "dinda aka kai gidan yari har iyakar ranshi xa'ayi "Executing" dinsu dom nemawa "gonnati " sauqin ciyarwa kuma duk Wanda yake ganin "shariar" da akayiwa dan'shi ko Dan uwan'shi ba'a kyauta musu ba, yanada damar sake suka kara, idan yayi nasarar fidar da prisoner dinshi shikenan, idan ko baiyi nasara ba sae ayi "Executing prisoner "din ambawa kowa dama daga yanxu har tsawon shekara daya. Wannan umurni ne daga PRESIDENT.
"JUSTICES" duk suka tashi tsaye JUSTICE ALIYU taslima kawae yake xabgawa ya maido kallon shi ta JUSTICE HUWAILA yana fadin tabbas Justice Usman kasheni yakeson yi amma Wallahi! Wallahi!!Wallahi!!! Ni JUSTICE ALIYU nayi alkhawarin sae na nunawa mai na karanci (LAW)"" Baxan yimai qarya ba. Kuma baxan yimai qaxafi ba. Amma nayi Alkhawarin ! bankado duk wani assiri naka! justice Usman !!! sae nasa ka banban ce! tsakuwa da aya. "maganin biri , Karen maguxawa," ya "fadi maganar da fada da tsawa! tsawa! yatashi xai fita kenan jiri ya debi JUSTICE HUWAILA ta fadi kasa! JUSTICE yayi maxa ya dawo ya rungumeta, ya kira family doctor dinsu yaxo ya shiga bawa JUSTICE HUWAILA taimakon gaggawa daqer aka samo ranta ya dawo amma bata farka ba.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[07:42, 1/11/2018] Barista: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamahπ
Ban manta dake ba sister Samira Malami (Mrs Mukhtar) Ina rokon Allah yabarku tare yasa ke matarshi ce har a jannatul fiddausππ
Mijin barrister
75-76
⚖ππππππππππππππ⚖Tun lokacin momy bata sake lafiya ba. "Prisoners" sunyi kuka dasukaji xaa kashesu, wasu sunji dadin hakan, acewar su mutuwar tafi musu sauqi akan rayuwa, lokacin da labarin ya risqi Ridwan ba qaramin tashin hankali ya shiga ba. Shi ba ta rayuwarshi yake ba yana tuna halinda iyayensa xasu tsinci Kansu ne a bayan ranshi.
"Yayi kuka sosae yana buga kanshi ga gina yana kiran sunan maidubu, yana "fadin ina kikaje baby ta ?Baby ina kikaje? Baby nasan ina Ranki a duk inda kike. Baby bansan halinda xaki tsinci kanki ba a lokacin da labarin mutuwa na ya risqiki.
Yasake fashewa da kuka yana buga kanshi ta gina sae da prison officers suka shigo da gudu suka riqeshi sunga alamar idan suka barshi shi kadae xai iya kashe kanshi, hakan yasa suka saka prison officer daya xama a dakin Dom ya kula dashi.
"RIDWAN ya sami bacci can cikin baccin ya hango Maidubu tana yimai murmushi mai tada hankali. shima yana mayar mata da martani tana "fadin kayi hakuri yakai masoyina nasan kana cikin halin damuwa amma Allah xai fiddaka insha Allah.
"Ridwan ya tashi da sauri yana fadin ina take ne? Prison officer din ya riqeshi yana fadin Ranka ya dade lafiya kuwa? Ridwan "yace Ashe mafarki nake! Ridwan "yace Kiyi hakuri Baby! ta! nasan da xaki iya taimakona da kinyi hakan, tunda dadewa, sae ya fashe da kuka, prison officer ya riqa rarrashinsa.
" Yaya Bello yaje ya sayowa su maidubu motoci guda biyu ita da Balkisu. ( Judgement day)Ash color. Inna sae shirye shiryen dawowarsu maidubu takeyi Dom yau Saura Wata daya su dawo.
"Balkisu ce xaune itada saurayin da tayi a London shima Dan Nigeria ne, kuma dan jahar kebbi ne, garinsu daya sun shiryarda kansu da maganar aure Balkisu tabawa Maidubu labarin saurayin da tayi Umar farouk maidubu taji dadi sosae tayiwa qawarta fatar alkhairi.
INDIA
"Yau ne su Maidubu suka kammala karatunsu duka sun anso certificate dinsu ta tabbacin xamansu kwararren lawyer's Maidubu ta fito da "Distinction" su Maidubu baki baya rufewa.
"Jitake kamar tayo firi tadawo Nigeria yanxu dom ta fiddo Ridwan yau, amma ba damar yin hakan dole ne su jira har anjuma, Dom sae sunyi attending Wata dinner wace ake hadawa sababbin Barristers .
"Wani gaye na hango yana tahowa wajensu maidubu yana murmushi har ya iso wajensu da ganinshi ko ba'a gayama ba Kasan ba indiyene ya iso suka gaisa cikin harshen indiyawa Kasancewar Maidubu najin indiyanci sosae, idan ma ta juya bakinta xuwa harshen indiyawa xaka iya rantsiwa bata taba jin Hausa ba, gayen yayi wa su maidubu fatar alkhairi, ita da friends dinta "yace sae sun hadu anjuma dinner shima Barrister ne.
Anyi dinner anbasu uniform wato rigar lauyoyi da hula kuma a yanxu sunada damar shiga duk court duniya dom neman inci ko tsayawa wani.
Anyi komi suka kwanta, Maidubu kasa bacci tayi yanda taga dare hakan taga Safiya ta matsu taga kanta a NIGERIA" asuba kawae sukayi itada friends dinta Nana Aisha Bala, Sa'a Alkhali, Maryam Aliyu, suka shiga mota tare sae airport daga airport suka shigo jirgi sae NIGERIA .
"Tare jiragensu suka diro NIGERIA, jirginsu maidubu na isowa nasu balkisu na isowa suka fito ko wace su waige waige kawae take, ko xata hango yar uwarta ae ko suna hango juna suka rugo da gudu suka rungumi juna suna murna, iyayen kowa sunxo daukarsu nan fa akayi kukan rabuwa da juna kuma sunyiwa maidubu alkhawarin dukkaninsu xasu halarci court, dom ganinan irin jajircewar da Barr Maidubu xatayi a court Dom ceton masoyinta, Maidubu tayi murmushi, Baban Maryam ya dauketa da mota, haka Baban Nana ya dauketa da mota, itama Saa babanta ya dauketa da mota, Yaya ya iso ya dauki Barrister Maidubu da Doctor Balkisu a motarshi, suka wuce ya mayardasu gidan inna. Gidansu Balkisu kenan inna ba karamin murna dawowar yaranta tayi ba.
Inna "tace kunganku kuwa kunga yarda kuka kara girma? duk da maidubu batada hankali kwance, amma tayi jiki ba sosae ba, hips dinta sun kara budewa, na fulaninta sun ciko sunyi dara dara dasu, tadan yi haske ba sosae ba hancin ta ya kara tsawo kamar fensil .
"Yaya nafita yadawo da motoci akayi parking dinsu a kofar gidansu Balkisu. "yace duk su fito har inna. Duk suka fito sukaga motoci ash color, irin daya komi nasu irin daya, "yaya ya mikawa Barrister key daya, ya mikawa Doctor key! yace wadannan motocin naku ne.
Barr Maidubu ta daka tsalle ta rungumi yayanta. Inna ko har kuka tayi na murna yaya "yace ta daina kuka ae tunda kika riqe Maidubu tsakani da Allah ba abunda baxan iya yimiki ba. Inna tayita godiya Balkisu sae da takai har kasa tana yiwa yaya godiya yaya "yace ta tashi ae itama qanwarshi ce.
"Maidubu kasa hakuri tayi tana fargabar xuwa wajen mamanta kar baba ya korota kuma tanajin bazata iya jure "missing" dinda tayiwa mamanta ba.
"Tayi shiri ta hau motarta taje gidan qawarta Zarah suka rungumi juna, tana fadin ina baby ta? zarah "tace tana daki da gudu Barr Maidubu ta shiga dakin, ta rungumo baby tafito tana "fadin masha Allah" Kasancewar xatah ta haifi yarta lokacin su Maidubu na BAR SKUL, ranar suna yarinyar taci sunan ta. Fatima(Seeyamah) Maidubu ta bawa baby Seeyamah tsarabar da takawo mata.
"Zarah ta shigo tana "fadin Barrister ya hanya? Maidubu "tace hanya alhamdulillah, Maidubu "tace "Mrs Nura " muje kiga motata tana gate din gidan nan. Ba karamin murna zarah ta taya qawarta ba.
Maidubu "tace zarah xanje "prison" yanxu Dom inason ganawa da Ridwan ranar Monday nakeso na sake maido maganarshi court. Zarah ta kalli maidubu idonunta na fiddo kwalla "tace.......
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[21:22, 1/11/2018] Barista: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamahπ
Mijin barrister
77-78
⚖ππππππππππππππππ⚖Maidubu ta kalli zarah tana "fadin ya kinyi shuru kina kuka zarah ina Ridwan? Gayamin ina yake? Dom nasan yana cikin qoshin lafiya.
"Zarah "tace Kiyi hakuri qawata! Barr Maidubu ta dakawa zarah tsawa! tana fadin he!!! My friend! karkiyi qauskuren gayamin wani abun ya faru da Ridwan. Dom wallahi ba Wanda ya aikata mai ba har ke da kika bani Labari sae kin fuskanci hukuncina, sae kuma ta riqe zarah ta fashe da kuka tana fadin kigayamin ina Ridwan.
Zarah "tace Barrister Kiyi hakuri kin dawo a qurarren lokaci, dom inaga idan dae ba'ayi "executing" din Ridwan yau ba, gobe xaayi , da laifin me? Me Ridwan yayi musu ne? Maidubu bata jira ansar da zarah xata fada ba ta shiga mota da gudu taja mota driving take bana hankali ba Dom ta riqe motarta har (200) tana kai gate din prison Wata motar na isowa itama da irin gudunda Barrister Maidubu keyi, Saura kiris suyi kaura kuma da sunyi wannan kaurar baa saran ko mutum daya yafito motoci da rayuwa.
Haka suka shiga cikin "compound" din "prison din a gigice, Maidubu ta bude motar ta, ta fito da gudu batako kulle kofar motarta ba, tana isowa taga antara prisoners ansaka su a layi, ana rubuta sunayen wadanda xaayi Executing dinsu gobe da asuba.
Barr. Maidubu na isowa wajen ana tanbayar Ridwan sunan sa kuma idan har sunan mutum yashiga wannan book din sae ankasheshi gobe ba makawa.
Ridwan ya fada mutumin ya fara rubutawa Ridwan Justice Ali..... Maidubu ta iso da gudu ta fixge book din a hannun mutumin ta tauneshi da bakinta, ta hade kowa ya maido kallon shi ga Maidubu suna yimata kallon mamaki, mai rubuta sunan "yace wannan fa ko batada hankali ne?. ya kalli shigarta yaga babu alamun hauka a tare da ita.
Barr. Maidubu "tace tabbas banada hankali indae akan Ridwan ne! kuma ba book ba, wallahi ko kai xan iya taunewa idan kayi qusquren taba Ridwan, sae lokacin Ridwan ya dago kanshi Dom tunda yafadi sunan sa ya rufe idonshi kwalla na kwaranya. yana bude idonshi sukayi 4 'eyes da Maidubu ya rugo da gudu Dom rungumarta, amma ina badama, "prison officers" suka hanashi isa wajenta.
Barrister maidubu da kanta ta karaso wajen Ridwan, "tace kayi hakuri Ridwan ko sun hanaka isa wajena karka damu kaji, insha Allah akwae ranar da xamu kwana a daki daya sae inga uban da xai fiddaka a dakinka na aure.
Maidubu ta maido kallon ta ga mai rubuta sunayen "tace kai "case" din Ridwan xai koma court yau kasani! Dom haka karkayi gangancin sako sunan Ridwan cikin book nan. Ta juya xata wuce mutumin ya kalli wani police "yace kai ku kama min wannan karamar yar iskar ayimata "discipline" police din na isowa Maidubu ta fiddo I.D card dinta ta nunamai, batare da kowa yasan mi ta nunamai ba. Police din Yayi saurin tsayawa chak. ta watsa mai harara ta wuce tashiga mota tajata da irin gudun da tashigo sae da ta barmusu kura a wajen tafito
Motar da suka shiga tare da ta Maidubu Ashe JUSTICE ALIYU ne yashigo yana isowa ana rubuta sunan Ridwan JUSTICE yaja ya tsaya yana hawaye. Tunda maidubu ta isowa wajen Justice Aliyu yabita da ido yana kwalla. Har ta taune book din sae da JUSTICE yayi murmushin jindadi dom yasan matsalar ta ragu Dom yanada damar sake saka kara ko a yanxu duk da bayada tabbacin nasara Dom wannan shine karo na 4 da yake sake mayarda case din Ridwan court amma sae justice tayi watsi da qarar. Maidubu tace yanxu babu xancen Executing din Ridwan gobe tayi maganar da ixxa. JUSTICE sae binta kawae yake da ido yana yimata kallon mamaki Dom shi yama kasa magana.
Tana fito yaje ta mayarda maganar Ridwan court kuma ranar Monday xaa fara shariar sa kasancewar yau Friday ne.
Maidubu ta fito daga court ta dau hanyarta ta xuwa gidansu Balkisu, tana tafiya Wata motar na binta a baya har ta iso tana fitowa mota mutum ya fito a tashi motar yana "fadin Maidubu! Maidubu!! Maidubu!!!. Barrister tayi banxa dashi xata shige gidansu Balkisu kenan mutumin "yace Maidubu nine fa ubanki! ae da sauri Maidubu ta tsaye chak! ta juyo tana kallon shi sae da ta karemai kallon mamaki sannan "tace Baba! Baba ya fashe da kuka yana "fadin maidubu ina kikaje? Maidubu munyi neman ki har mun gaji. Maidubu Dom Allh ki yafemin kuma ina kika sami mota? Allah yasa ba duniya kikabi ba Maidubu.
Maidubu ta kalleshi "tace Ubana fa kace? Ae banada uba inadai da uwa! kuma miye na kuka? idan ma nabi duniya ae addua kayimin, dom haka bakomi bata kara kallon shi ba, ta shige warta gidan .
Baba yayi kukan dayasani sosae yana "fadin Maidubu kece yau da Bakin ki kike gayamin magana a yau. keda ko kallona bakyayi a lokacin da nake magana, tabbas duk abunda ya faru ni najawa kaina nayi nadamar abunda nayiwa ya'ta.
Maidubu na shiga gidan tagayama su inna abunda ya faru da taje prison sannan ta gayamata yarda sukayi da baba a kofar gida, inna taji dadin jin baba ya gane qusqurenshi da kuma nadamar sa.
"Baba yaja motarshi . ya shiga da sauri yayi gida yana shiga ya fashe da kuka ya gayama mama yaga Maidubu har yayimata magana tayi kamar bata gane shi ba.
"Mama dake kwance tana jinya! ta tashi da sauri tana fadin da gaske baban yara kaga Maidubu? Baba "yace yanxu haka tana gidansu Balkisu mama ta tashi da sauri ta dauko gyalenta suka fito xuwa gidansu Balkisu. mama na fadin Alhmdllh, Allah Sarki Ashe inada rabon sake ganawa dake Maidubu! suna shigowa sukaji tattaunawar da inna keyi itada Maidubu.
"Inna "tace Alhamdulillah, tunda Babanki ya gane qurenshi Maidubu sae ki shirya in maidaki gida kinji. Barr Maidubu "tace inna baxan koma gidanmu ba, banason xama achan, Baba ne yashigo yana fadin ae dole ki koma tunda mune iyayenki .
"Inna ta tashi tsaye tana "fadin ba dole ba kam, idan dae taga dama idan ko tace baxata koma ba, ba ko inda xataje, Baba "yace Ashe ko xan kaiki court wallahi kinyi Kadan ki mallakemin yarinya.
Maidubu da tun shigowar su ta rungumi mamanta suna murnar ganin juna, mama "tace Maidubu ina kikaje yau tsawon shekara 7 ? maidubu dae tayi murmushi lokaci daya kuma ta share kwalla, jin baba na maganar kai inna court ne yadawo da ita garesu ta saki mama tace me kace baba? Baba "yace idan taki bamu yar mu "nace sae inkaita court.
" Barr Maidubu "tace wallahi Baba idan kayi qarar inna da kaina xan tsaya mata a court. Baba yace Eyyeh to wallahi ko xaki mutum sae kin dawo garemu Dom munfi kowa qaunar ki a duniya.
Duk basu gane inda maganar maidubu ta dosa ba, Dom sun dauka tana nufin xata biya kuddi ne a tsayawa inna Kasancewar daga mama har baba duk basusan shekarrun da tayi bata gari tana wajen karatu ba .
"Mama "tace kul, Maidubu uba ubane duk yarda ya xama Kiyi hakuri da naki uban kinji! nan fa aka sasanta amma Maidubu taqi yarda ta koma gida tayi xamanta a gidansu Balkisu.
Magarib nayi balkisu ta fara shirin xuwan farouq, yaxo ya ga guardians din Balkisu an tsayarda ranar baki nan da Wata daya mai xuwa .
"Yau takama "Monday" ranar xa'a fara sauraren shariar Ridwan.
Maidubu tayi complete dress na lawyoyi tasako "black Gownπ¨π»π da fatar shirt a ciki da hular layoyi Golding color ,ta sako farin glass dom baa saka ko wace kalar glass a court idan ba fari ba, tafito da cover shoe dinta plate. Dom baa sako hellshoe a court doka ce⚖
"Kyawon da Barr. Maidubu tayi bansan ta inda xan fara misaltashi shi ba, tayi kyawo masha Allah. Ta fito a "Barrister dinta sak. Innah tayimata fatar nasara sannan tafito,
Taja motarta bata tsaya ko ina ba sae gate din court.
" Kuma Justice Usman ne xai sake xaman shariar ko yanxu. Dom anso ayi Appeal din shariar amma San maidubu taqi yarda "tace shidin nan takeson tayi hakuri yasake shariar Ridwan ko yanxu.
Hakan yasa JUSTICE USMAN yake yiwa Ridwan kallon gawa, Dom yanada tabbaci shine da nasara akan Ridwan.
"Court ta cika da mutane masu xuwa kallon sharia, Barrister maidubu na shigowa, JUSTICE "yace Alhmdllh Barrister da ake jira ta karaso, barrister wace take kare wanda ake kara RIDWAN! ya dago kai da sauri Dom ganin wace xata bashi kariy, ae ko sukayi ido 4 da Maidubu .
"Ridwan ya fiddo ido waje yana fadin baby miya kawoki nan? Barrister Maidubu ta daga mai hannu tayi shhhhhhhhhhhhhh fuskarta ba alamar wasa ko dariya.
"Tana fadin "don't call me ur baby, I am not ! my name is Barrister Maidubu Muhammad I stand here becouse of u, nd I will Fight for ur right, ta juya ga JUSTICE tace.........
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππππππππ⚖
[16:03, 1/12/2018] Barista: ⚖πππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamahπ
Kina raina babbar qawata soyayya ta dake bata qarewa baayi kamar ki ba kuma baxaayi kamar ki ba a birnin xuciyar Barrister kin nunamin qaunar a gabana kuma kinyi hakan a bayana Zarah Abdullahi Sokoto( Mrs Nura) gaisuwar Barrister gareki lodi lodiππ
Mijin barrister
79-80
⚖ππππππππππππππ⚖Barrister Maidubu ta maido kallon ta ga Justice Usman tace My lord Sunana Barrister Maidubu Muhammad lawyer dake kare Wanda ake kara wato accused person.
Ta fadi maganar tana nuna Ridwan da yatsar hannunta
RIDWAN sae bin Barr. Maidubu kawae yakeyi da ido yana kallon yarda take moving before d judge har yanxu Ridwan bai yarda da Maidubu tayi karatun law ba. shi kallon ma tausayi yake yimata kar justice yagane ba Barrister din gaskiya bace ya kaita prison dom shi ya dauka tayi acting din Barristers ne kawae Dom ta fiddashi.
Sae kuma yayi mamakin irin kalaman da take furtawa yarda take fadar chapters na CONSTITUTION daki daki Ridwan dae yabita da ido kamar wani soko .
Friends din Barrister Maidubu sunyi mamakin irin qoqarin da Maidubu keyi a court duk da wannan shine karo na farkon da ta tsaye gaban Real Judge Dom bawa wani kariya.
Barr. Maidubu ta gayama court Ridwan bayada sa hannu a kisa Ahmad tace Ahmad ya Kasance Dan fashi. wato (Armed robber)
Lawyer din Gonnati ya tashi tsaye yana fadin" Objection my lord "baikamata abokiyar aikina "Barrister Maidubu ta rika fadar munanan kalamai ba ga late Ahmad, dom tana alakantashi da laifin Fashi kai tsaye bayan batada shaidar hakan wannan yana nufin bata mai suna ga late Ahmad.
Bayan kowa yasan Alhaji Ahmad mutumin kirki mai kamun kai kuma hanshaqin Dan kasuwa Wanda kowa yasan sanaar sa .
Justice yace Barrister ki saisaita kalamanki Barr. Maidubu ta sunkuyar da kai tace Thank u my lord.
Maidubu ta maido kallon ta ga lawyer din Gonnati tana murmushi tace Barrister ko xaka iya gayawa wannan court din ko miye sanaar late Ahmad.
Lawyer din yayi shuru sannan yace ba dolene sae court tasan sanaarsa ba don ba abunda muka xo yi ba kenan anan.
Barr. Maidubu tayi murmushi tace Point of correction Barrister. Court ko keson sannan ko miye sanaar late Ahmad. Idan har ko baka San sanarsa ya tabbata Dan fashi kenan.
Lawyer din Gonnati yace My lord late Ahmad yana kasuwanci ne a Dubai Barr Maidubu tace ko xaka iya fadar irin kasuwancin da late Ahmad keyi a dubai?
Lawyer din ya juyo ga maidubu yace late Ahmad yana dai kasuwanci a dubai Barr. Maidubu tace ko xaka iya fadar sunan company ko Wata masana-antar da yake aiki dasu ko? Kodaya mallaka amatsayinshi na hanshaqin dan kasuwa kamar yanda kace ?
Lawyer din Gonnati yace Banada Masanniya akan wannan. Amma yana aikine da companyn Sutura wato wa danda ke kirar clothes sunan companyn ne bansani ba.
Barrister Maidubu tayi murmushi tace ae ko akwae bukatar musan wannan.
Barrister Maidubu ta kalli Justice tace ya mai girma mai sharia ina neman wannan court mai alfarma mai adalci data daga wannan shariar nadan wani lokacin Dom gabatar da kwararrun shaidar da xata gansar da wannan court.
Sannan ina neman wannan court mai adalci dataai da Maaikatanta muje Dubai tare Dom gane gaskiyar waye late Ahmad
Sae da Justice yayi murmushin qeta ya karewa Barr. Maidubu kallo sannan yace Barrister anbaki damar yin bincikenki na kwana ukku kacal Kuma wannan adjoint din da xan yi shine na qarshe a shariar RIDWAN.
Maidubu ta sunkuyarda kanta tana fadin nagode ya mai girma mai sharia.
Justice yace the case is adjoint to 11 January 2018.
Mutane sun fito shiko Ridwan ansaka shi a mota ankoma dashi prison. Ridwan duk kanshi ya daure da wannan sabon alamari da yagani.
Barr. Maidubu ta rungumi qawayenta suna murnar ganin juna sun jinjina ma qoqarin Maidubu ba Kadan ba sannan suka ce Barrister wannan kyakkyawan gaye haka ai dole ki rude. Ita dai Barrister maidubu sae murmushi take.
Justice Aliyu ne ya fito a court din ya sami su maidubu tsaye shima ya tsaya yace Barrister duk suka juyo Kasancewar dukkanin su barrister's ne.
Yace Barrister Maidubu sannan ta Dan matso kusa dashi Dom ita bata ma San koshi waye ba .
Justice Aliyu yace nine Mahaifin RIDWAN Wanda kike bawa kariya, Maidubu ta fadi qasa tayi knelling agaban justice ta gaidashi ya ansa yace mata tashi tsaye, ta tashi ta sunkuyar da kanta.
Justice yace Dom Allah waye ke? Barrister ta sunkuyar da kanta. Justice yace kuma waya turuki ki tsayawa Ridwan a sharia? Justice yace Kiyi haquri kinji Barrister wahalar banxa kawae xakiyi Dom wannan shine karo na 5 danake saka kara amma JUSTICE USMAN yayi watsi da ita. bakiji ko yanxu yace xamanda xaayi ranar 11January shine na qarshe ba ko yanxu nasan duk hujjar da xaki bayar a court JUSTICE USMAN watse xaiyi da ita.
⚖ππππππππππππππ⚖Sae da Barr. Maidubu ta sako idonta cikin na JUSTICE tace wallahi! Wallahi! Wannan karon bayada nasara akan Ridwan kuma shine xaiyi wannan shariar baxanyi appeal dinta xuwa ko ina ba.
Sae da JUSTICE ya karewa Barrister kallo sannan yace idan kika fiddo Ridwan kin gama min komi a duniya kuma ba abunda baxan iya baki ba daga naira daya har Billion dubu. Barr. Maidubu tayi murmushi tace bana bukatar komi a wajenka kayimin fatar nasara kawae.
JUSTICE ya fiddo ido waje yana fadin bakyason komi? Tace eh!. JUSTICE yace Dom Allah waye ke? kuma miye tsakaninki da Dana RIDWAN? Barr tayi murmushi tace lokacin da Ridwan xai fito prison xaka San koni waye I promise u. Abun ya daurewa Justice kai yace tau waye kuma wannan? A ranshi yake rayawa kodai yarinyar nan ce da tayi so wato Matar late Ahmad ta turu wannan barrister din sae kuma ya tuna momy tace babanta ya koreta. JUSTICE yace ina yi miki fatar nasara.
Duk abunda akeyi momyn Ridwan bata sani ba Dom Justice bai gayama ta ba Dom yasan ko yanxu basu nasara Dom Justice watsi kawae xaiyi da shariar.
Barr. Maidubu taja motarta ta koma gidan inna ta gayama inna maganar tafiyarta inna tayimata fatar nasara a ranar bata kwana NIGERIA ba ta shiga jirgi sae Dubai itada maaikatan court guda 2 itace ta 3.
Barr Maidubu tayi anfani da ragowar kuddin da yaya Bello ke tura mata lokacin tana INDIA
Sun je a company dinda aka ce yana aiki dasu suka tanbesu amma mutanen suka ce su basu ma sanshi ba sunyita bincike babu wani company da late Ahmad yake aiki dashi a Dubai kuma company daya ne babba nayin clothes a can. Kwanan su 2 acan. Suka dawo gida NIGERIA kuma gobe ne xama na gaba a court kuma na qarshe.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[19:03, 1/18/2018] +234 704 645 3026: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamah
Kina raina sister Zarah amaryar February amarya kuma uwargida a gidan Nura makers Allah ya nuna mana February musha bikinku(Mrs Nura makers)π idan yayi laifi ki riqa hakuri karki kulle mai daki kuma karki dauko wuka Dom wallahi sae yayi hijira yabar gidan baki dayaπ€£ππ
Mijin barrister
81-82
⚖ππππππππππππππ⚖Maidubu na kwance da dare ta kasa bacci tana tunani ko ya shariar gobe xata kaya.
Da misalin qarfe 12:00 na dare ne wayar Barr. Maidubu tahau ruri tayi saurin dauko ta tasaka silent sannan tayi picking call din, da mamakinta na ko waye yake kiranta da wannan daren?
Barr. Maidubu na dauka taji muryar namiji yana fadin Assalamu alaikum! Da fadar ina magana da Barrister Maidubu. tace eh! yace yawwa kina waya ne da Justice Usman Sahabi.
Barrister Maidubu tayi saurin danna wayarta (recording) tace banji ba waye kai yace kina magana da Justice Usman sahabi Barrister tayi murmushi tace Ranka ya Dade ya gida? suka gaisa da girmamawa.
Justice Usman yace nasan bakisan dalilin da yasa na kiraki ba kuma bakisan inda nasamu nonbar wayar ki ba kuma kin matsu kisan duk wannan ko?
Barrister tace sosae kuwa. Justice yayi murmushi mai sauti yace maison Dan tsuntsu Shike biyarsa da jifa.
Justice yace inason Kiyi Stepping back ga wannan shariar ta RIDWAN Dom bakyada nasara.
Bara kiji na riga nayi niyyar kashe Ridwan sae da Barrister ta runtse idonta lokacin da taji an kirawa Ridwan mutuwa Barrister tace me Ridwan yayima ne ? da har kake yimai fatar mutuwa.
Justice yace justice Aliyu mahaifin Ridwan yakai dana prison na tsawon 25years yasamin bakin ciki na dan lokaci. Niko ina shirin samai na har abada xan sashi kukan da bayada magana a ranar da nayi Executing danshi niko xan kwana ina murna a wannan ranar.
Barrister Maidubu tace baxan taba yin stepping back ga wannan shariar ba kuma kasani wallahi Ridwan yafi qarfinka.
Justice yace barrister karkiyimin taurin kai idan kuddi ne matsalar ki ni xan iya wadataki da kuddi daga naira dubu har billion 3.
Maidubu tayi murmushi tace kuddi ba matsala ta bace kuma bana bukatar kuddin ka.
Justice yace tunda nabi dake ta lalama kinqi tau bara kiji wallahi xan iyasa akawar dake daga doron qasa akan wannan maganar kuma nasan kina son Ranki.
Kuma wallahi nadau alwashin kashe duk Wanda yakeson kawo min matsala akan wannan case din ki sani.
Barrister tayi murmushi tace ae tunda nayi karatun law yakama ta kagane rayuwata ba komi bace, kuma ko baka fada ba nasan rayuwa ta tana cikin hadari I want u to bear dis in ur mind. Wannan shariar yanxu na fara ta kuma baxan daina ba har sae ranar da nayi nasara akanka.
Justice yayi murmushi yace tunda kinyimin gardama wallahi nayimiki alkhawarin duk ki kayi qusquren fita gobe Dom xuwa bawa Ridwan kariya a court.
wallahi! wallahi!! Wallahi!!! sae dae akai gawarki a court badae kije a raye ba.
Barrister Maidubu tayi murmushi tace idan har kayi nasara akan Ridwan sae bayan raina insha Allh idan dae bana raye na yarda xaka iya kasheshi niko idan har ina nunfashi na dau damarar yakarka.
Justice yayi dariya sosae sannan yace ki fara yiwa kanki kallo gawa daga yanxu xuwa gobe da safen da xakije court.
Barr. Maidubu ta kashe wayarta ta tashi tsaye tana safa da marwa a dakin hankalin Barrister yatashi ba Kadan ba dajin kalaman Justice Barrister bata yi bacci ba har gari ya waye
A bangaren Justice Usman kuwa Barrister na kashe wayarta yayi mamakin irin taurin kanya yana yimata baraxana da mutuwa amma batako damu ba .
Yayi murmushi yace Barrister ki kira kanki da mai kararren kwana.
Ya daga waya ya kira wani sukayi Wata maganar da bansan me suke cewa ba ya kare ya kashe wayar yana Wata irin dariya qeta.
Barrister Maidubu batayi bacci ba har asuba tayi sallah taci gaba da addua har gari yayi haske.
Ta tashi ta taya Balkisu aikin gida tana yi tana tunanin kalaman Justice sae ta koma daki tana fadin wannan ranar ita ce ranata ta qarshe da xan iya nunawa Ridwan irin qaunar da nake yimai.
Ta fashe da kuka tana fadin rashin nasara ta a yau yana nufin qarshen rayuwata Dom wallahi ana kashe Ridwan ina kashe kaina.
Balkisu ce tashigo dakin tana fadin subhanallah Barr. Why are u cry? Barr. Maidubu tace Doctor rayuwata tana cikin hadari jiya bayan kinyi bacci wani ya kirani yana yimin bara xana da mutuwa.
Ba wannan ne yafi damuna ba abunda yafi damuna shine bansan yarda wannan shariar xata kaya ba.
Balkisu tace Barr. Kodae xaki hakura ne da wannan shariar banason wani abunda yasameki Barr. Maidubu ta juyo ga Balkisu har suna shaqar nunfashin junansu tace wallahi doctor idan aka aje mutuwa agefe daya aka aje shariar RIDWAN aka aje rayuwa a gefe daya aka ce in xabe daya.
Wallahi Wallahi xan dau shariar Ridwan ne bayan na kare a kasheni saboda qaunar da nakeyimai.
Qawata kiyimin fatar alkhairi kawai Barr. Maidubu ta daga waya ta kira wani mutum amma bansan maganar da sukayi ba ta kashe waya.
Barr. Maidubu taje tayi wanka tayi shiri cikin kayan ta na lauyoyi ta fito a barrister dinta sak ta sako farin glass itama Balkisu tayi shiri tace sae dae suje tare idan antashi kashe Barrister akashesu tare.
Barrister tayi tayi Balkisu tayi xamanta amma taqi tace sae dae akashesu tare suka shirya suka fito Barrister tace wa Balkisu tabari taje su gana itada mamanta kafin su wuce Barr. Maidubu taja motarta sae kofar gidansu.
Tana shiga taga duk ilahirin yayyun ta suna gidan Dom duk mama ta gayamasu dawowar Maidubu suka rungumi juna ita da yayyunta sunyi mamakin ganinta da kayan Barristers sae tanbayarta suke yi ina tasamu wannan kayan? Barr. Dae sae murmushi take yi Baba yashigo yace waye wannan da kayan lauyoyi? mama tace kwalla da kyau yace kamar Maidubu mama da baba duk kallon mamaki sukeyiwa Maidubu.
Barr. Ta kalli Mama tace mama ina key din dakina? mama taje ta dauko mata key din ta bata Maidubu ta amsa tayi godiya taje taga duk dakin yayi kura ta bude ta shiga sae da takarewa dakin kallo sannan ta fara neman bindigar nan da waya dom tana bukatar su yanxu a tare da ita.
Maidubu ta bata fiye da 2hours tana nemasu sae da ta fiddo duk kayan dakin sannan tagan su ba karamin murna tayi da ganinsu ba.
Amma kuma tayi delay sosae da xuwa court tayi sauri ta bude akwatinta da ta dauko gidan Ahmad ranar da yarasu ta bude akwatin ta dauko Wata bakar jeka ta dauko empty din akwati ta sako jekar a ciki ta sako bindigar da waya ta kulle akwatin.
Tasake sako uniform dinta na lauyoyi tayi shiri da sauri sauri ta fito ta janyo akwatinta mama ce tace maidubu ina xakije kuma Harda akwati.
Maidubu ta russuna har qasa tace pls forgive me mama dadewar da nayi bana gida ba duniya nabi ba naje INDIA ne nayi karatun law na tsawon 7years kuma nayi wannan karatun ne badon kowa ba sae Dom in fidda Ridwan a prison
Mama ta fiddo ido waje tana fadin me wanne Ridwan barkiyi wahalar banxa kinji yata tunda kikaga ko iyayenshi sun haqura.
Barrister tayi knelling gaban mamanta tace Don't mind them mama ur prayer is needed.
Mama tace what d u want my daughter? Barrister tace ur gud wishes mama.
Mama tace I wish u all d best in dis trial. Thanks u mamanta Baba ne yashigo gidan yana fadin maidubu nima ina yi miki fatar nasara a wannan shariar Maidubu tace Nagode Babana.
Sae da idanunta suka ciko da kwalla bata tashi daga knelling dinda tayi ba tace yaku iyayena Dom Allah ku samin albarka Mama ta dafe kanta shima baba ya dafe kanta suka saka mata albarka.
Barrister na kuka tace kuma Dom Allah ku yafeni yayarta ce Hauwa ta iso wajen ta riqe Barrister tana fadin maidubu lafiyarki qalau kuwa kike roqon gafara.
Barrister tace kudai ku yafemin duk suka ce sun yafeta dukkaninsu sae da suka share kwalla Dom sunyi tausayinta Barrister ta janyo wannan akwatin ta fito duk suka bita da ido .
Baba ya fito yace duk kowa ya shirya dom xasuje kallon shariar Maidubu.
Su baba na shiga court Justice na cewa xamu karawa Barrister Wanda ake kara 10 minuth ne kachal idan har sukayi bata iso ba xaa koma da Ridwan prison gobe a xartar mai da hukunci Kisa ta hanyar rataya. Kuma har ansara reading time.
Baba ne da kanshi yayi maxa ya kira maidubu a waya yagayamata abunda Justice yace.
Tau fa ko ya wannan shariar xata kaya kuwa?
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barrister⚖ππππππππππππππ⚖
[19:04, 1/18/2018] +234 704 645 3026: ⚖ππππππππππππππ⚖
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamahπ
I really love dis my stupid friend Asmau Umar Ibrahim ban manta dake ba qawata adduar ki tana tasiri agareni ina qaunar ki sis love u dieπ
Mijin barrister
83-84
⚖ππππππππππππππ⚖Barrister najin abunda baba ya fada lokacin tayi kusan kai gidansu Balkisu Barrister ta ruga da gudun da ita kanta batasan yarda takeyinshi ba.Tana kai kofar gidan ta shiga motarta ta jefa akwatin a site din gefenta tayiwa motarta key ta sakawa Balkisu wani irin hone Wanda koni sae da kunnena ya rude.
Balkisu na leqowa barrister tayi mata alamar da ta shiga motarta su wuce kafin Balkisu ta shiga motarta har Barrister taja motarta da gudun tashin hankali tabar wajen.
Balkisu tashiga motarta Dan tsayawar da tayi yiwa motarta key ae koda ta duba ko kurar barrister bata gani ba hakan yasa tabi Wata hanyar da take tunanin nan ne maidubu tabi amma bata ganta ba.
Barrister gudu take da motarta bana wasa ba tana wannan gudun ta hango an gifta xare hanyar da xatabi kuma batada wata hanyar sae wannan hanyar Barrister ta sadakar da rayuwarta kawae dom ba fasa tafiyar xatayi ba sae dae su kashe ta ko sun kasheta batayi hasara ba Dom ta mutu ne a hanyar ta ta taimakon masoyi.
Barr. Maidubu ta kalli agogon hannunta taga Saura 4minute ga lokacin da justice a fada tayi kuka tasaka hannunta ta daki stiry din motarta taja motarta kawae ta sauka akan road. Gudu takeyi sosae can taji Harbin bindiga abayanta.
Barr. Maidubu ta riqe motarta 200 gudu take har motarta nadan rabuwa da qasa mutanen nan sun biyo motar Maidubu sunata harbinta itake ta riqe motar sae gudu takeyi.
Barrister gudu take suna harbinta har suka harbemata tayar mota Barrister ta cigaba da gudu da geren tayar mota duk sun harbe motar duk da haka bata tsaya ba.
Sae da tashiga gate din Court suka daina binta Barr. Maidubu na isa wajen tayi saurin janyo akwatin ta fito dom motar tayi xafi sosae tana fitowa motarta na kamawa da wuta .
Idan ta tsaya neman akashe wutar lokacin zai cika Dom Saura minti daya Barr.Maidubu ta kalli motarta ta saki kuka sae kuma ta ruga da gudu tashiga court.
Justice na ganin Barr. Maidubu sae da ya tashi taye akan rudewa yace Barrister are u still alive? Ya Fadi maganar yana fiddo ido waje.
Kallon kallo suka rika yiwa juna itada Justice sae da Barr.maidubu ta share kwalla tayi murmushi sannan tace Yes Sir I m still alive sir.
Justice yayi shuru Barr.Maidubu ta juyo ta kalli court din taga mutane cike da court din ta kalli iyayenta ta maido kallon ta ga Ridwan shima kallon ta yakeyi babu alamar wasa a fuskar ko wannensu.
Barr. Maidubu ta juyo ga Justice ta fara da fadin Ya mai girma mai sharia ayimin afuwa akan delay dinda nayi.
Sannan tace kuma ina roqon wannan court din da idan Labbo da Ibrahim suna nan su gabatar da Kansu ga wannan court din.
Registerer. ya tashi tsaye yace idan labbo da Ibrahim suna nan court na nemasu suka fito suka shiga bayan kanta.
Court Clark ne ya tashi ya rantsar dasu tare da daukar alkhawarin fadar gaskiyar abunda suka sani.
Barr. Maidubu tace labbo ko xaka gayama court sunnan ka ya fada sannan Barr. Maidubu ta fara tanbayarta kamar haka .
Malam labbo shin ko kaga wani company ko Wata masana-antar da late Ahmad ke aiki xasu a Dubai ?
Labbo yace ah ah!.
Barr. Tace shin ko kaje babban company nayin sutura a can?
Yace eh naje tace tau ya akayi a can? Labbo yace munyita tanbaya amma sun ce basuma sanshi ba.
Barr. Tace OK.
Amma da ka fito daga wannan company bakaje wani company nayi sutura ba ? Labbo yace ae company daya ne garesu na sutura. Barr. Maidubu tace OK.
Dsame questions tayima Ibrahim da Wanda tayiwa labbo kuma ansar su iri daya ce. kuma da labbo xai fara bada tashi shaidar waje aka fidda Ibrahim har sae da labbo ya kare.
Barr. Maidubu ta maido kallon ta ga Justice tace ya mai girma mai sharia da wannan shariar da aka bayar nikeson court ta qaryata xancen late Ahmad yana aiki a Dubai Dom ba gasjiya bane.
Barrister maidubu tace ya mai girma mai sharia ina neman court da ta gabatar da maigadin gidan late Ahmad.
Registerer yace Court na neman malam sani maigadi
Malam sani ya fito ya shiga bayan kanta aka rantsar dashi sannan Barrister ta fara yimai questions.
Malam sani a ranar Wata Friday ta shekara ta dubu biyu da sha daya Wato ranar 10/11/2011 da misalin qarfe 1 na dare kana ina? Yace ina dakina a gidan late Ahmad.
Barr. Tace shin ko kaji wani motsi ko wata alamar shigowar mutane a gidan?
Malam sani yace nadae ga fitarsu ina leqowa sukayi harbi lokacin kuma fitane xasuyi Dom gaskiya banji shigowar su ba.
Kasancewar anyi baki mutane da dama yan rikan ango sun shigo gidan. Dom amarya baban ta kawae ta kawota Barrister maidubu tayi murmushi Dom sae da ta tuna wannan mummunar ranar a rayuwar ta.
Barrister Maidubu tace....
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππ
0 comments:
Post a Comment