Yamma nayi tabar saloon din ta wuce gida
ba tare da izini Haseena ba, tana isa ta
tadda Mom agidan, suka gaisa, Inna na
daga gefe tana waya da Baffa, tasamu gu
ta xaune, Mom tace “yanxu Inna ke
gayamin ashe aiki keki zuwa, ni duk tunani
na scul keki xuwa” shuru tayi,anya xata
gayamata aikin goge goge take, idan Inna
taji xata hanata xuwa, ta nisa tace “eh wlh
aiki nake as a receptionist awani saloon”
Mom ta girgiza kai, ita dai bata ga abun
sha’awa a aikin saloon ba, ga ita Haseena
tadau son duniya ta daurawa shegen saloon
da baxai fisheta ba,tace “amma dai kikai
aure zaki bar aikin ?’
” aikam da gudu xan bari, dan nasan
da wuya yabarni nayi aiki” Mom ta kalleta
ataikaice “kina da boifrnd be ?’ murmushi
tayi tace ” eh, amma yayi tafiya”
Duk sai taji ba dadi jin tace tana da Bf
“Allah ya dawo dashi lapia musha buki” ba
kunya Ayna tayi dariya tace “Amin”
faketa da ido Mom tayi ganin yadda
take xabga uban murmushi.
Inna ta gama waya ta kalleta tace ” nan da
sati biu zamu je zaria na gaji da korafin
shehu (baffah)” uhmm Ayna tayi, rai bace
ta Mike ta shiga daki. banxa Inna tayi da
ita, suka cigaba da hiransu da Mom.
Kwas!! Kwas!! take takunta mai daukan
hankali har ta karaso wajen Helen “am
leaving” ta mika mata daya daga cikin
keycard na saloon din “make such u lock d
entrance door” tace yes ma….sannan ta
fice.
Koda ta isa gida harya dawo, ta duba
bedroom dinsa bay ciki, ta leka ko ina bata
gansa ba, nan take hankali ta ya tashi,
Allah sa ba fushi yay ya tafiya ya yabarta
ba. Da sauri ta duba tennis court, baya ciki,
tana shiga basketball field ta ganshi sanye
cikin white jersey rike da ball ahannu.
kirjinta ta tab’a tare da sauke duguwar
ajiyar zuciya, “Kamil” ta kira sunansa daidai
lokacin da yayi niyyan jefa ball cikin hoop.
Ko juyowa bayi ba yaja guntun tsaki tare da
ajiye ball din akasa, “shida yake kokarin
avoiding dinta, Miya kawo ta nan” ya fada
aransa, da gudu taxo tayi hugging dinshi, ta
dago araunane tace “hankali na ya tashi
ban ganka ba, kasan dai I can’t live witawt
yhu” kallonta kawai yayi bai rike taba bece
uffan ba, ta kara hugging dinsa gam “I love
u with all mah heart & soul, I’ll die if u
ever leave me” shuru yayi still baice uffan
ba, “Plz say sumtn, your silence is killing
me” dariya ma taba bashi, wato ta manta
lokacin daxaiyi 2hrs yana mata magana tayi
banxa, Murmushi yayi yace “calm down,
yanxu ai kin gani” ta girgiza kai alama eh,
“okay toh go & rest ganin nan xuwa” tace
“owkay, come soon” ta kaima kiss a lip
sannan ta wuce. Yayi k’wafa tare da
daukan ball din ya cigaba. Koda Mom ta
dawo, basa palo, ta shige daki abunta.
Agurguje filis
****kwanaki na tafiya, Kullum Mom agidan
Inna take wuni, sun saba sosai kaman
yan’uwan juna, Ayna na nan amatsayin ta
cleaner, cin mutunci da wulakanci iri iri
Haseena ke mata, amma still tak’i quitting
job din cox tana sa ran wataran M.k xaixo.
Zaman Kamil da Haseena ba yabo ba
fallasa, dou sumtymz en wulakanci yatashi
bata ko kallonsa, dukda shima yan kokarin
maintainin distance, burinsa mai wuce
wataran Allah ya sada shi da pretty ba.
Bayan sati biu
Tun safe take duba wayanta ko xataji bank
alert, amma shiru…..ta.ajiye mopstick dake
hannuta tana tunani yadda xata tunkari
Haseena, kusan kwana hudu da suka wuce
akayi albashi bata samu nata ba. Ta daure
taje wajan secretary naima izinin shiga
office dinta, sec ta shiga ta fito “kina iya
shiga nan da 1hr” tace “toh” ta tsaya jira
har lokacin yayi sannan tayi knocking ta
shiga.
Yau dai she is bizy, gabadaya hankalin ta
nakan laptop dake gabanta, “morning” Ayna
ta fada, bata amsa ba tace “Do you need
sumtn” uhmm ta sosa keya sannan tace
“dama salary dina ne naji shuru, shine naxo
tambaya” murmushi mugunta Haseena tayi,
“lokacin amsan salary ya wuce, kina iya
jiran na next month” kallan rashin fahimta
tay mata “I don’t understand” sai sannan
Haseena ta dago tayi mata wani malalacin
kallo “Daz ur punishment 4 not been
punctual at work”.
” Don Allah kiyi hakuri, I really need d
money” banxa da ita Haseena tayi, ta
cigaba da aikin gabanta.
Shuru har kusan 40mins bata ce uffan
ba kuma bata dago ba. Rai bace ta hukara
ta fice daga office din, aikin ma bari tayi ta
wuce gida abunta.
Inna ce tare da Mom suna tankade garin
masara a tsakar gida, ta shigo jiki sanyaye,
ta gaida su sanna ta xauna, Inna
tace”barka kin dawo da wuri, kinsan dai
tafiyar mu Zaria gobe ce, ki shiga daki ki
hada mana kayan mu” nan take annurin
fuskan Ayna ya dauke “inna nifah bazan
biki Zaria ba, yaushe ma muka dawo da
zamu koma” ta kai Mata dundu abayana
“shegia, sai kinje dan bazan barki ke daya
agidan nan ba” Mom tace ” haba Inna karki
dake ta” ta kalli Ayna datai rau rau da ido
“miyasa bakya son xuwa Zaria ?’
” Mom idan naje Adda Jamie ke xagi na
kullum ta dinga tsine min, kwanaki har kona
min fuska ta kusayi akan yan unguwa
sunce nafi ya’yanta kyau” Mom ta
numfasa, “wace ce Jamie ?’ Caraf Inna
tace “Matar baffan suce, itama ya’yanta
gabadaya mata ne, shiyasa Sam basa
jituwa da Ayna” Mom tace “ohh itace
Matar shehu da kike ban labari” Inna ta
gyara sannan tace “itace, sam bata da
kirki”
Ajiyar zuciya Mom ta sauke, tace “Inna
tunda batason xuwa maxai hada taxo
wajena ta xauna kafin ki dawo” caraf Ayna
tace “eh Inna idan kin dawo sai nadawo”
harara ta watsa mata, ta kalli Mom “a’a
karmu takuraki, ki barta kawai mu tafi”
Dariya Mom tayi tana fadin “tsakani na
daku ai mun xama yan’uwa, ba wata takura
wlh, kinga na huta da zaman kad’aci na
kwana biu”
“toh shikenan, gobe kyaxo ki dauke ta
Ku tafi, tunda tafiyar tawa ta yamma ce”
murna sosai Ayna tayi tama manta da
wani batun albashi, dadin ta daya bazata
hadu da Adda ba. Suka cigaba da hirar su
daga bisani Mom ta tashi tayi gida.
*****Washe gari, Har karfe goma na safe
Ayna na daki bata fitoba, Inna ta shigo ta
sameta “yau bazaa saloon ba ?’ Ta bata rai
jin an ambaci Saloon, dama tun jiya ta
yanke shawara bazata kara xuwa ba. ” eh
Inna hutu nake bazani ba”
Inna tace “ah lailai kam, kin siyo mon
maganin hawan jinin nawa ?’ dumm
gabanta ya fadi, tun jiya yakamata ta siyo
maganin bata siyo ba, gashi bata da ko sisi
sai yar dubu uku dake jankanta, ” na manta
wlh, bari naje nasiyo yanxu” ta mike da
sauri tare da daukan purse da black veil na
gown dinta tayi rolling tayi waje.
Sanye yake cikin blue jean da red T-shirts,
ya fito ya leka dakin Haseena, tana
bathroom tana wanka, yayi dariya, yau
Madam stylish baa fita da wuri ba. Ya
sauko ya leka Mom, tana zauna kan sallaya
tana karatun Qur’an, ya xauna harta idar
sannan suka gaisa, yace”Mom ni xan wuce
office saina dawo” tace “yauwa dama xan
gayama, baby gal dita xataxo min hutun
kwana biu”
“Wace kuma baby gal”
Harara takaima “kamanta little sister dinka”
yayi shuru dan yama manta da xancen, sai
yanxu dai ya gasgasta xancen Haseena,
Mom tafiya kwashe kwashe, ko miye
nakawo yarinyan mutane gidan nan “okay
Mom, saita xo, we have alot of empty
rooms” tace “kafin kaje office, ka biya
pharmacy ka siyomin maganin ciwon bayan
nan nawa” yace toh sannan ya tashi ya
fice.
Pharmacy kusan biyar taje bata samu ba,
tahau motar haya yakaita wani babban
pharmacy dake hanya Ahmadu Bello Way.
Tana shiga ciki, ya danno kan motar sa ya
shiga haraban gun yayi parking ya fito.
“do u have joltan Valsartan 160mg”
pharmacist din yace akwai, tace “hw much
ist?’
” 5k” yace mata, tace “I only have 2500,
plz take it, by tomorrow I’ll bring d
balance” ya kalleta awulakance” we don’t
do dat here, if u don’t have cash u can pay
wit ur credit card” tayi shuru bata ce uffan
ba, tama rasa ya xatai.
Yana daga dayan gefe, wani pharmacist na
attending to him, kuma da alama yaji
abunda wacan pharmacist din ke gayawa
yarinyar daya gani ta baya sanye da gown,
ya siya maganin sannan yace “hw much is
d balance 2geda wit wat dat lady bought ?’
Ya nunata da yatsa ” u mean d lady wit
blue dress” yace “yap”
Still tana tsaye bata motsa ba, yaxo
ya tambaya shi amount din abunda ta siya,
ya fada mai 5k ne, ya koma ya gayamai
sannan yabiya ya juya ya fice.
“Take” ya mika mata maganin aleda, tayi
murmushi ta amsa hada da mai godiyan ya
yadda ya bata, yace” dont thank me, d man
dat paid just left, if u really want to thank
him hurry up & go outside b4 leaves” da
sauri tace okay” ta fito haraban gun, ba
kowa, ta duba parking lot taga wani na
shirin shiga mota, da sauri ta ruga tana
fadin “excuse me plz” harya shiga motan
yaji familiar Voice, ya fito adaidai lokacin
data karaso tana haki.
Suka xubawa juna ido.
*Need ur prayerz idona na ciwo*o
*cute xarah*
[27/10 11:58 AM] ҳąřąɧ bųҠąř : [27/10
9:14 AM] cųtҽ ҳaɾaɧ :
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Aɭɧamɖųɭɩɭaɧ ŋaﻯ amų ﻯ aųkɩŋ ɩɖɷŋa
ma ﻯų kɩɾa ta waʏa ɖa m ﻯɠʑ ŋaɠɷɖҽ
ﻯɷ ﻯ aɩ, Aɭɭaɧ ʏabaɾ kaųŋa, ɭɷѵҽ ųɾ aɭɭ
*
*Page*
Kusan 5mins sukayi suna xubawa juna ido,
dakyar ta saita kanta tace “thanks”
Ya murmusa “for what?’
tayi murmushi hade da dago mai ledar
maganin, ya share yace ” you left without
saying goodbye”
“ųɧmm ina ŋaŋ, maybe I wasn’t on duty
lokaci da kaxo”
“Oh! dat means d old lady delude me”
dariya tayi danta gane Helen yake nufi da
old lady, ta duba time a agogonta sannan
ta dago suka kara hada ido, ta kalli
hadaddiyar motarsa kirar 2016 Buick
cascade “nice car, ist 4 delivery ?” ya
murmushi wato har yanxu kallon
deliveryman take mai, “naga kaman kina
sauri, lemme drop u off” ta kuma tsakar
mai murmushi “dun worry my house is near
by, I can trek” yace “owkay” ta juya ta tafi
hade da jin haushi bai roketa ta shiga ba,
dama dan Jan aji tayi.
Yana tsaye yana kallon tafiyar ta mai
daukan hankali, ya numfasa sannan ya
shiga mota yaja ya karaso inda take hade
da jan barki, cak ta tsaya jin abunda xaice,
taga ya fito ya bude dayan side din “get in”
yace mata, ta dauke kai kama bata ji saba,
ya karaso dab da ita “if yhu don’t I’ll starve
mʏ ﻯ ҽɭʆ to death” ta harare shi cikin salon
kauna tace “i’ll never 4give maself if u try
dat”
Ta shiga yasa mata seatbelt, ya
tambaye ta Addy ta fadamai sannan ya
shiga yaja. Shuru babu mai cewa uffan,
kowa da abunda yake sak’awa axuciya.
Sun iso inda akwai traffic beam ya
tsaye, ya kalleta, gabadaya hankalinta na
waje, da alama akwai abunda take kallo,
shima ya kalli wajan, Haseena ce xauna
cikin motar ta tasha uban black shades a
ido, Sam bata lura da motar saba, jira
kawai take traffic light ya nuna green ta
wuce abunta.
“Kin santa ne” sai sannan ta dawo
hankalin ta “yea, she is my boss” yace
“nasanta ai” ta kalle shi araunane “yes i
knw, Am so sorry da yadda tay treating
dinka, Helen ta gayamin komai” ya sauke
ajiyar zuciya “karki damu, do u hate her ?’
” Nope, I don’t have any reason to hate
her, dukda ma she is alwyz rude to me, but
tnkxx to her naga sakon daka kawo min” ta
bude purse dinta ta fiddo karamin red rose
flower “I so much love it” yayi murmushi
yana mamakin ya akai Haseena ta bata gift
warp din, “hw cms ta baki, I tot ko jefarwa
tayi”
Ta nisa sannan ta fada mai duk yadda
akayi amma bata nuna mai ita cleaner ce
ba.
Ran shi ya baci matuk’a, kawai ya
boyene karta gane, ya kara kallon Haseena
adaidai lokacin da light ya nuna green,
afusace taja motar tayi gaba. K’wafa yayi
yaja mota, yabi roundabout ya shiga layin
gidan data nuna mai.
Suka iso gida, “tnx 4 d ride” tace mai hade
da bude motan ta fito ta shige gida da
gudu, ko kallan Inna batay ba ta shige daki
tana hak’i rik’e da rose din.
ya kalli seat, yaga ta manta purse da
ledar maganin, yasa hannu ya dauka, ko
saurin mi take ?’ ya fito xuwa kai mata.
“Ban san haukar banxa, fito kiban
maganin” Ayna bata amsa ba, ta mike xata
shiga dakin taji ana kwankwasa kofar gidan,
taje ta bude, “ina kwana goggo” yace mata,
“lapia lau, ya hajiya ?’ Ya kalleta da
mamaki, ganin tsohuwa ce yasa yayi dariya
yace ” tana nan kalau” xata kara magana
Ayna ta fito da sauri jin muryarsa “Inna
wace hajiya kuma, shine ne fah….” tayi
shuru, Inna ta kalleta a takaice “shine wa?”
xatayi magana wayar hannu Inna tafara
ringing, “Alo” ta Kara akunne tayi ciki. Suka
kalli juna yay murmushi hade da mika mata
kayanta, taxo amsa ya hada da hannuta y
rike yace “baki karasa ba, shine wa ?” tayi
gutun smiling daya Kara fito da actual
beauty dinta, ta sunne kai akunyace, tace
“D light in me” ya lumshe ido ya matso dab
da ita har suna jin numfashi juna, ya tallafo
fuskan ta suka kalli juna sannan ya riko
dayan hannu ta yamata slight peck, da
sauri ta runtse ido.
Inna dake daki ta kwalla mata kira
“Ayna zoki amshi waya” ya saketa, ta
amshi purse da ledar ta juya.
“Ayn” ya kirata da wata kasalalliyar
voice, ta tsaya chak jin yadda ya Kira
sunan ya burgeta, ta juyo, yace “nyc
name”
“Tnx” ta fada, ta shige daki da sauri jin
Inna ta kirata. lumshe ido yayi sannan ya
koma mota, yadau wayarsa ya duba yaga
missed calls, yaja guntun tsaki, danya
manta suna da meeting, ya kuma jan tsaki
akaro na biyu, ya manta bai amshi contact
dinta ba amma tunda yagane gidan zai
dawo.
Tana shiga dakin,Inna ta mika mata wayan,
Auta ce (zainabu ce autar Adda), “Hello
Auta, yammatan kauye ya kike” Auta tayi
hhhh, tace “sumul nike, tunda baxa kixo ba
kibawa Inna yan tsofin kayanki ta kawo
min” tayi dariya “toh aikuwa xan bata, ina
Abdallah masoyi” taja tsaki “tun yaushe
nasashi ashara, yanxu jamilu ne alayi har
an kawo Kudin sa rana” Ayna tace “lailai
kice akwai bidiri” ,suka cigaba da hirarsu
daga bisani kati yakare, Inna tace ” yanxu
ke bakiji kunya ba, saida aka haifeki da
wata shida sannan aka haifi Auta, gashi
xatai aure ta barki”
“Kaji Inna da xance, Aure fah lokaci ne,
itama lokacinta ne yayi, dan Allah ki
shafamin lafiya” Inna tace “na shafa, duk
shawara da baffa ya yanke ba ruwana”.
Haushi da takaici ya hanata magana, ta
hau hada kayanta cikin jaka.
Agurguje ya isa gida, ya bawa Mom
maganin ya wuce office, itama ta shirya ta
wuce gidan Inna.
Tana zaune office ta kira Helen ta waya, ta
shigo da saurinta, “Weldon ma”, Haseena ta
gyara xama “have a sit” ta xauna.
“Am travelling tomorrow, make sure u
take good care of my saloon and plz don’t
talk to client anyhow” tace “ah no problem
madam, safe journey”
“Yhu can go” tace mata, harta mike
xata fita ta kirata tace “wia is Ayna, I dint
c her ?’
“She didn’t come today”
“Okay”, Helen ta fice.
Ta buga uban tsaki, wato yarinyan nan
tafara growing wings, ko aikin ma ta daina
xuwa, tayi k’wafa.
Tunda Mom taje suke ta xuba hira, yamma
nayi Inna ta fiddo yar Jakarta, Mom ta ijiye
ta tasha ta fada motan Zaria, Ayna sai
kukan rabuwan su take, dakyar Mom ta
lallashe ta sannan suka wuce gida.
Ta kara karewa gidan kallo, sai yanxu
ta lura da motocin sun karu sunkai kusan
200, suka shigo ciki, Mom ta kaita wani
hadaddan daki mai girman gaske kusa da
nata, tace ” Mom dakin nan yamin girma”
tayi dariya “shine smallest bedroom agidan
nan, saidai ko dakina xa muna sharing”.
” haba dai, xan zauna anan din, Allah
sa dai masu gidan karsu raina ni”
“Masu gidan babu ruwansu da kowa,
maybe ma harki tafi bazasu ganni ba,
yanxu kiyi wanka ki huta, idan kika Sallah
sai kixo dakina musha hira” tace “toh” ta
shige ciki.
Itama ta shige daki tayi Sallah ta dawo
entrance Palo ta xauna, Haseena ta shigo
“ina wuni Mom in-law”
“lapia daughter in-law” ta fada
ayatsine, tsum tsum Haseena ta wuce
sama, tasan bata da gaskia, 1week kenan
basu hadu ba.
Mom tace “Allah ya saukewa, wato d’an
dabaka haifa ba yana k’ashin k’iranka da
uwa.
Agajiye ya shigo gidan, ganin Mom zaune
tana kallon islam channel shima ya zaune
hade da gaida ta, ta amsa da fara’arta
sukayi dan hira daga bisani ya haura sama,
itama ta mike ta shige daki.
Dakin Haseena ya shiga, tana tsaye tana
xuba kaya ciki akwati, ya bata rai dama
haushi ta yakeji, ta kalle shi ta dauke kai
“ka dawo ashe, am traveling 2moa” ya
kalleta a takaice ” ina xaki, kuma da izinin
wa ?’
Afusace ta kalle shi “am not a slave
daxan tsaya naimi izini, like it or not am
traveln to New Zealand to change my
wardrobe and cosmetics”
Ya K’ara tamke fuska, “just 3month ago
kika je Barcelona yanxu kam babu inda
xakiji” harara ta balla mai sannan tace “my
life, my rules, no one can stop me not even
your Mom….” tass ya wanke ta da
kakkaywan mari saida ta fada gado, tayi
k’ara hade da rik’e kuncinta “I hate you” ya
kalleta awulakance “you are insane” ya
juya yabar dakin.
Agigice ta mike taje gaban mirror, ta
kalli inda yayi Marin yayi ja sosai, ta buga
uban ihu “wayyo my beautiful skin,
shikenan face dina xaiyi swelling” afusace
tahau wurgi da duk abun fashewa dake
dakin, tana fadin “I hate you”.
Ayna dake wanka ta fito daga
bathroom daure da towel atsorace, ta shige
dakin Mom da gudu, Mom ta mike da sauri
tare da rikota ” miya faru, miya sameki ?” ta
tambaye ta akidime.
Jiki na rawa tace “Mom sumtn is
wrong, naji kaman ana ihu” ta sauke ajiyan
zuciya, danta gane abunda take nufi, indai
gidan nan ne tasaba ji, ta zaunar da ita kan
gado tace “calm down, notin is wrong,
k’aran TV kikeji” jikin sanyaye tace toh”
daidai lokacin Haseena tadau bedside lamp
tayi wurgi dashi jikin bango.
Atsorace ta xabura hade da toshe
kunnuwanta, Mom dake kallonta saida ta
tsorata, aranta tace “na shiga uku xasu
firgigita min yarinya”
*cųtҽ ҳaɾaɧ*
12:50 PM] cųtҽ ҳaɾaɧ :
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Page*
Dakyar Mom tasamu ta lallaba har tayi
bacci.
Washe gari 6am dot Haseena ta sauko
rike da suitcase dinta, bata bi takan kowa
ba ta wuce waje, ta shige mota daya daga
cikin officers ya jata xuwa Airport. 7am
nacika jirgi ya daga xuwa southwestern
Pacific ocean (New Zealand ).
Tun bayan sallah asubah Ayna tabar dakin
Mom ta koma dakinta ta kwanta jiki
sanyaye, gari na wayewa tadau wayanta ta
kira Inna suka gaisa hade da tambayan
kota isa lapia, suka dan taba hira daga
bisani sukay sallama.
Ya fito cikin shirin sa tsaf na kanana kaya,
har xai sauko yayi tunani lekata, ya tura
kofan ahankali ya shiga, dakin kaca-kaca,
glass ta ko ina afashe, yayi K’wafa, Ya
fiddo waya yayi calling head Quarter na
clean House suxo nan da 3hrs su gyara
dakin.
“Haseena” ya Kira sunanta.
Shuru ba amsa ya duba bathroom bata
ciki, dressing closest bata ciki, ajiyar zuciya
ya sauke “kodai ta tafi ne ?’ da sauri ya
fiddo waya yay dialing no dinta.
Yaji ringing din wayar kan gado, ta
daura paper akai, ya dauka ya karanta.
“c ya after a month” ta rubuta da
manyan harofa, yayi yak’e hade da
squeezing paper ya jefar, araunane yace “I
cnt believe yhu broke my heart” ya juya ya
fice.
Mom na zaune kan gado ya shigo ya
gaida ta sannan ya fada mata Haseena taje
trip na kwana biu, ta girgiza kai dan tasan
akwai wani lamari akasa, “Son gayamin
gaskia, am sure sumtn is fishy, ga fuskan
ka yanuna you’re sad” ya kirkiro murmushi
dole “Don’t worry, ur son is alwayz happy”
xata kara magana ya katse “am late saina
dawo” ya fice da sauri.
Ta numfasa game dayin tagumi, burinta
bai wuce taga farin cikin 1&only son dinta
ba, ta dago asanyaye sukayi ido hudu da
Ayna tsaye tana kallonta.
Da sauri ta karaso ta xauna kusa da ita
“Mom tunanin mi kike haka ?’ Yak’e tayi
tace ” ba komai, bana jin dade” ajiyar
zuciya Ayna tayi tana fadin “ni kaina am
not at ease, ina ji ajikina sum1 very close
to my heart is hurt amma nakasa figuring
out” sai sannan Mom tayi dariya “kodai
siriki nane da kika cemin yayi tafiya” ta
sunne, akunyace tace “I don’t tink so cox
he is too good to b harm” Ido kawai Mom
ta bita dashi batace uffan ba.
Itama shiru tayi tana tunani, sai yanxu
ta tuno basu da contact din juna, ko yaje
gida ba kowa, “ya kenan” ta fada aranta,
shawara daya itace ta cigaba da aikin
saloon, koda yaxo ya ganta.
ta mike da sauri tana fadin Mom barin je
n hada mana breakfast, ta shige kitchen ta
hado masu sandwich tare da tea takai
dining, taje ta kirata suka xauna kari. Ko
minti biu batai da xama ba, ta mike ta
shiga daki ta sauyo kawa tafito, “Mom
natafi bazan dade ba” tayi hanyar kofa da
sauri, Mom tace “baby gal dawo” ta dawo
da sauri, Mom ta kalleta daga sama har
kasa sannan tace “I tot turquoise blue &
white outfit kike sawa idan zaki aikin” tace
“eh” Mom ta numfasa “yanaga yau kinsa
gray & white ?” nan take tasha jinin jikinta,
saboda outfit na cleaners ne, tace “uhmm
mun canxa ne”
“oh, I c….idan kinje waje akwai driver
dana ba in charge ya kaiki kullum yadawo
dake”
tace “toh Mom nagode” tayi gaba,
“banda kawo samari kofar gida fah” acewar
Mom tana dariya
Murmushi kawai Ayna tayi tace toh,
aranta tace tab dama yaushe xan nunawa
MK gidan nan, haka kurum masu gidan
sumai wulakanci.
0 comments:
Post a Comment