yabi aguje tare da k’wala mata k’ira, yasa
hannu zai bude kofan ya jita gam rufe, ta
sa lock ta waje data fita.
Hankali tashe yahau jijjiga kofan,
Haseena ta fito rike da k’ank’ara a leda
tana fadin “ina yar iska yarinyar take ?”
Akufule ya kalleta yadau Jakarta dake
wajan ya zazzage yadauki keycard, ciki da
karaji ta karaso ta rik’e shi “ba inda zaka
saika gayamin yaushe ka fara cin amanata”
banxa yayi da ita. “sau nawa ka kwanta da
ita….” bata ida maganar ba ya tsakar mata
k’akk’aywan mari a kunci “karki kuskura ki
danganta ni da aikawa zina” kuka ta fashe
dashi, zata kara magana ya tureta ya fice.
Ta zauna dirshan akasa tana tsula kuka
tana fadin wayyo na shiga uku Ayna kin
cuce ni, na tsane ki.
Da gudu ya fito haraban saloon din bai
ganta ba, ya karasa bakin titi babu alaman
ta, da sauri ya shige mota yaja zuwa gidan
data nuna mai, ya isa ya k’wankwasa gate,
mai gadi ya fito suka gaisa, yacemai wajen
Ayna yaxo, girgiza kai maigad yayi yace “ai
babu kowa gidan nan, asalin masu gidan
kasar waje suke xama” sai yanxu yagane
wato karya take shiyasa ta hanasa shiga,
sallama yamai ya tafi, hankali tashe yaje
gidan Inna shima arufe.
Cikin shessakar kuka Mom taji anyi
sallama, ta juyo afirgice, ganin Ayna ce
yasa ta mike tsaye “daga ina kike haka,
gabadaya kayanki ruwa, miyasa meki ?”
Kasa magana tayi saboda kukan dayaci
karfinta, da gudu ta shiga daki ta fada
bandaki ta rufe kanta. Mom ta karaso ta
murda ta jita gam, tace “baby kukan mi
kike ?’ shuru Ayna batayi magana ba saima
sautin kuka data k’ara.
Palo ta dawo hankali tashe, Allah yasa
ba wani mugun abu akamata ba. Haseena
ta shigo fuska murtake, tasha kuka harta
gaji, tana ganin Mom ta karasa gabanta
“Mom ina wuni, ya gida ?” Cike da mamaki
ta kalleta, basaban ba yau Haseena ta
gaida ta aladabce. “Lafiya, mik’e
damunki ?”
Ta fashe da kuka ta gayamata komai,
k’wafa Mom tayi tace “karki damu ni kaina
bason yarinyar nake ba, bari yaxo xai hadu
dani” nan take Haseena ta murmusa, koba
komai Mom na bayanta. Ya shigo rai
ajagule tana ganin sa ta haura sama da
gudu. Ya gaida Mom xai wuce, tace “tsaya
zanyi magana dakai” ya zauna “son na
gayama ka rabu da yarinyan nan, kaki koh,
toh kasani ko bayan raina ka aureta ban
yafe ba” agigice ya dago idonsa da ya
sauya launi “Mom kiyi hakuri, karki min
haka, ina sonta” hannu ta dagamai “na
gama magana” ta juya ta koma dakinta
asanyaye, tausayin su ukun takeji, ta
tabbata soyayya ke wahalar da Ayna.
*****washe gari
Gidan tsit kaman anyi mutuwa, kowanan su
da abun dake addabar zuciyar sa. Tun
bayan sallah asubah ta zauna gado tana
shawarar kwalla, Mom ta turo kofan
ahankali ta shigo, suka hada ido, dumm
gabanta ya fadi ganin idon Ayna ya canxa
launi xuwa ja, gashi yau Inna xata zo
daukarta.
Da sauri ta mik’e hade da k’irkiro
murmushi dole “mom ina kwana, dama
kaina ke ciwo amma nasha magani” kallon
karya kike tay mata, ta zaunar da ita tace
“ni uwar kice, karki boye min komai,
gayamin mike damunki” ta nisa sannan ta
fayyace mata komai tana kuka. “Kiyi mai
uxuri mana, kika sani ko yana da reason
dayasa yay miki karyan” tayi shuru batace
komai ba, “kin daina sonshi kenan ?” ta
dago da sauri tana fadin “a’a, bazan iya
daina sonshi ba kawai dai raina ya baci”
Ikon Allah Mom ta fada aranta, wato
bazata daina sonsa ba dukda kukan daya
sata.
Wayarta yahau ruri, ta duba taga shine
taki dauka, Mom tadau wayar ta rike “tunda
kina sonshi ki dauka mana” tana shiri mik’a
mata call din ya tsinke, ta kalli wayan taga
pic dinsu tare a screen din wayar, ta kalla
dakyau anya ba kamil bane. Nuna mata tayi
tace “waye wannan ?” Ta duba ta k’ara
fashewa da kuka hade da fadawa jikin
Mom tana fadin “shi ne” nan take Mom
tasha jikin jikinta, dama sunsa juna ? ta
tambayi kanta, sai yanxu tagane abunda ke
faruwa.
Rikota tayi “tashi muje Palo kiyi
breakfast kisha magani” ba musu tabita
sukaje, ta zauna k’asa hade da daura kai
kan kujera, Mom taje kitchen ta dauko
sandwich tare da juice tafito ta haura
sama. Zata k’wankwasa kofan ya fito cikin
shirin sa, ya gaidata ta amsa da fara’arta.
Ta mik’a mai abinci, bai karba ba yace
“Mom sauri nake akwai inda zani” ta bata
rai “ba inda zaka, sai kayi feeding little sis
dinka”
“Dan Allah taci da kanta, sauri nake”
“Bata da lafiya shiyasa nakeso ka
taimaketa, tana palo” ba yadda ya iya dole
ya amsa ya sauko, itama ta sauko ta labe
daga gefe dan sauraron abunda zasu ce.
K’amshin turaran sa taji ahancinta, ta
share bata dago ba, ya zauna kusa da ita,
yama rasa ya zaiyi dakyar ya daure yace
“sister ga abinci” arazane ta dago jin
sanyayyiyar murya sa, ta mike da sauri ciki
da mamaki, shima ya girgiza ainuhi, ya
nunata da yatsa dama kece little sis ?” Ta
fashe da kuka tace “mayaudari kaci
amanata, miya kawoka ka gidan nan ?”
Mom dake sauraron su ta runtse ido da
sauri jin kalaman Ayna marasa dadi. Yace
“calm down, nan gidana ne” Harara ta
watsa mai “makarya ci…..”
“Ayna” Mom ta kira sunanta rai bace
“d’ana kike zagi agabana” cikin tashin
hankali Ayna ta mata kallon rashin fahimta.
Haseena dake sauko wa fuska kumbure
tana Sosa ido tace “Ayna agidana ?” Duk
suka juya suna kallanta.
*cute xarah*
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Page*
Rai b’ace ta karaso k’asa tana fadin “miya
kawo ki nan?”
“ya’ta ce kuma ta dade agidan nan,
baki damu da kowa ba taya zaki san tana
nan” Mom tafada tana kare mata kallo. Ita
kanta Ayna ta shiga rud’ani, duhu kawai
take gani, kaman zata shid’e tsananin
sarawar da kanta yake.
Cikin tashin hankali Haseena ta karasa
gaban sa “bazan yadda da rainin hankali
ba, sai dai ka zab’a ko ni ko ita ?” Ya ware
ido yana kallanta baice uffan ba, tayi
k’wafa sannan tace “shurun ka ya nuna ita
ka zab’a kenan ?” Amsa zai bata suka ga
Ayna ta yanki jiki ta fadi k’asa wanwas, da
sauri suka karasa wajan ta hade da k’ira
sunanta, rik’eta Mom tayi tare da jijjiga ta,
shuru babu alamun rai tattare da ita.
Ta dago ta kalle shi akid’ime tana
fadin “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, ta
cika.” Afirgice yace “Mom mu kaita asibiti
a duba ta” ta mik’e da sauri ta shiga daki
ta dauka hijab ta fito, Haseena dake kallon
yadda suka gigice yasa takaici ya cikata ta
kumbura kamar ta fashe, tace “Allah yasa
ta mutu kuma nima bazan zauna agidan
nan ba” ko kallan ta basuyi ba suka fice
zuwa asibiti.
Dak’yar ta lallashi kanta, ta haura sama
hade k’unk’uni bazan ta zauna ba, Katsina
zata tafi gidan iyayenta.
Suna zuwa Crystal Hospital aka bata gado
ba tare da b’ata lokaci ba, da yake asibitin
zuwan su kenan. Bayan mintuna talatin Dr.
Faiza ta fito daga dakin, suka tare ta da
sauri hade da tambayan ko tana da rai, ta
numfasa sannan tace “da ranta, sai dai
bata farfado ba, her condition is critical.”
Hankali tashe kamil yace “mike damun ta?”
tace ” ciwon kai kuma gwaje gwaje mu ya
nuna kanta ya bugu, ta samu accident ne
kafin ku kawota ?” Kallon juna sukayi da
mamaki, Mom tace “a’a, lafiya kalau take.”
Tace “toh yanxu dai mun mata allurai,
xuwa anjima kuna iya shiga ku ganta.” jiki
sanyaye suka zauna, wayantar tayi ruri ta
duba taga Inna ce, dum gabanta ya fadi,
tace “son Innarta ce ke kira, bansan mai
zancen ba” kafin yayi magana wayar ta
kara ruri, yamata nuni da hannu ta dauka.
Dakyar ta dauka, suka gaisa, Inna tace
“gamu nan zuwa, Ayna ta dawo gida ” Mom
ta nisa sannan tace “Inna muna asibiti,
Ayna ba lafiya.”
“Allah ya bata lafiya, kuna wana
asibiti ?” ta fada masu hade da kwatance
yadda zasu gane, sukayi sallama.
****Haseena
Gudu take shararawa a titi na fitar hankali
harta iso Katsina, tana zuwa unguwar
dakyar ta gane gidan, ta iso bakin gate ta
tsayar da motan tana tunani, shekara biyar
kenan tunda ta auri kamil tabar gidan bata
k’ara zuwa ba, sam ta manta karshe data
k’ira Mami da Abbanta amma ba komai
tunda Kamil na zuwa gaida su kuma yana
Isar mata da sakon gaisuwar ta garesu.
Horn tayi maigadi yafito, ganin kamarsu
da Alhaji yasa ya bude mata, ta shiga tayi
parking.
Alhaji munir babban dan siyasa ne mai
kudin gaske, matar shi daya Hajiya Karima,
ya’yan su biyu kacal aduniya, Haseena da
karamar kanwarta Hanifa mai shekara
goma ayanxu.
Hajiya karima mace ce mai zafi da
bata daukan raini, shiyasa koda Haseena
tana yarinyar basa jituwa, abu kadan tayi
sai tahau ta da fada.
Dalilin dayasa Abba ya kaita Amsterdam
karatu.
Ta fito daga motan tana karewa gidan
kallo, sukayi kicibis da Hanifa sanye da
hijab zata islamiya, tace “autar mu haka
kika girma ?” Kallon wace ce ke Hanifa tayi
mata bata ce uffan ba, “bakya magana ne,
Mami na nan ?” Da gudu Hanifa ta juya ta
shiga gida, Abba da Mami na zaune Palo ta
shigo tana hak’i, harara Mami ta wurga
mata “baki da hankali ne.” Ba shiri takama
kanta tace “Mami wata aunty yar gayu ce
tazo naiman ki.” Magana zatayi suka ga
Haseena ta shigo Palo, atsorace suka mik’e
tsaye suna kallonta, tace “Abba, Mami ina
wuni ?”
“lafiya lau” Abba yace cike da mamaki.
k’are mata kallo Mami tayi ganinta sanye
da wando jean da top tayi rolling kanta da
dankwali, tayi K’wafa, aranta tace “yarinyan
nan tana nan da halinta.”
Awulakance ta shiga jero mata
tambayoyi “wace ce ke, daga ina kike,
wajan wa kika zo ?” Nan take Haseena
tasha jinin jikinta.
Dakyar su Inna suka gane asibitin, Kamil
yaje ya shigo dasu, tana zaune tayi tagumi
suka karaso, ta mike da sauri hade da
gaida su, Baffah yace make faruwa, daga
zuwa daukan ya’ta ance tana asibiti” Inna
tace “shehu miye haka, ka bari tayi mana
bayani atsana ke.” Doguwar ajiyar zuciya
Mom ta sauke sannan ta gayama su
komai.
Lokaci daya annurin fuskan Baffah ya
dauke, rai bace yace “zancen banza kenan,
ni zaa maida karamin mutum.” Hankali
tashe su duka suka kalle shi, ya kalli kamil
sannan yace “ba wanda ya isa…….”
*cute xarah*
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Page*
K’are mai kallo yayi sannan yace “ba
Wanda ya isa ya canza min kudiri na, ko ita
tayi kad’an tace zatayi fushi dan kawai ka
boye mata kana da mata” duk suka bisa da
kallo hade da sauke ajiyar zuciya, a tunanin
su sab’anin hakan zai furta, ya girgiza kai
yana fadin “kwarai kuwa, burina bai wuce
naga na aurar da ita dan fita hakkin
amanar da ubanta yabar min, dan haka
aure dakai zan aura mata sai dai ta mutu”
Mom tace ” karmu so kanmu dayawa, mu
bari harta farfado idan ta yadda sai ayi
auran”.
“aiko bata yadda ba dama niyyata
acikin satin nan zan daura mata aure game
rabo, idan kun shirya ku turo anyi magana”.
Kamil da Mom suka kalli suna murmushi,
tace ” gobe Insha Allah magabata zasu zo
ayi magana” yace “Allah kaimu, ni zan
koma Zaria, idan ta farfado Inna sai ta
kawota afara shiri” sallama yay masu,
Kamil ya kai shi tasha.
****Katsina
Cikin karaji da zare ido ta karaso gabata
tana fadin “magana nake kinyi shuru ?”
atsorace tace “nice Haseena, wajanku
nazo” akufule tace “fice min daga gida”
zata k’ara magana Mami ta daka mata
tsawa, ta fice da sauri har tana naiman
faduwa.
Abba yace “tunda yau ta tuno damu,
kibarta ta zauna” uhm tayi batace uffan ba,
yadau mukulli motan sa yaja hannu Hanifa
suka fice. Tana tsaye haraban gidan bata
da niyyan tafiya, ganin Abba yasa ta
k’irk’iro kukan dole, ko kallon ta bai yiba ya
shige mota yaja.
Tayi rau da ido tasamu inuwa ta zauna
hade dayin tagumi, mijinta kawai take
tunani tasan ba k’aramin sonta yake ba,
shiyasa tayi alkawarin ba inda zata har sai
yazo da kansa daukarta, wayarta ta fiddo
ta kira PA dinta, ta gayamata arufe saloon
till further notice.
Mami na tsaye bakin window tana kallon ta,
tausayin ta taji ba kadan ba, ba yadda ta
iya dole ta koyawa Haseena hankali, ta
tabbata gagarimin laifi tayi kamil ya korota.
Jamila (yar aiki) ta aika taje ta shigo da
ita, jiki sanyaye ta shigo ta zaune, Mami
tace “laifin mai kikayi ya koroki ?”
“ba korata yayi ba, kishiya zai min
shiyasa na dawo dan banzan iya zama da
ita ba” harara Mami ta wurga mata “dayake
baki da hankali shine kika zo nan, toh
kisani zama da kishiya sai ya fiye miki
zama dani” ciki da tsoro tace “Mami kiyi
hakuri ki tayani rokansa karya aureta.”
“akan mi zan rokeshi alhalin nasa baki
da hali, zan k’ira shi awaya namai godiya
da Allah sanya alheri, tunda adalilin zai
k’ara aure kika tuna damu”
Shuru tayi bata ce uffan ba, ta fashe da
kuka. “bana son hauka tashi ki shiga daki”
ta mik’e sum sum ta wuce, Jamila ta shigo
mata da kayanta. Ita kanta Mami bata ji
dadin zaa mata kishiya ba, tayi k’wafa,
koma miya ita ta d’ibo ruwan dafa kanta.
Kusan Magrib Ayna ta farka, Mom da Inna
suka shigo suna mata sannu, dakyar ta
mik’e zaune tana fadin “ina nake ?” Mom ta
rikota “asibiti kike, ya ciwon kai ?” sai
sannan ta tuno da abunda ya faru da safe,
ta fashe da kuka. Inna tace “ke bansan
iyayin banza, daga tambaya ya jiki sai
kuka” dariya Mom tayi bata ce komai ba,
ya shigo ya tsaya daga gefe yace “kin
tashi ?” Banza tayi dashi kaman bata ji ba,
Inna tace “ya Kamata ku koma gida, zan
zauna da ita” Mom tace “toh zata aiko
masu da duk abunda zasu buk’ata.” Duk
yadda yaso su hada ido ki tayi, har suka
fita.
[04/11 9:20 pm] Cute xarah : Suna zuwa
gida ya duba ko’ina bai ganta ba, ya k’ira
layin ta kashe, yayi shuru yana tunani ina
taje, yasan bata da friends, “ko gidan su
taje” ya girgiza kai “anya kuwa” ya fiddo
wayansa, bari ya k’ira Mami ya gaishe ta.
Buga daya ta dauka suka gaisa da
fara’arta, yayi shuru ya kasa cewa komai,
tace “Haseena tazo dazu” yace “eh, layin
ta kashe Allah yasa lafiya”.
” lafiya wlh, kasan halin Haseena sai
hakuri, ta gayamin komai kuma na tabbata
laifin tane” yace “Mami kiyi hakuri, gobe
zanzo na dauke ta”.
” a’a Kamil karka zo, ta dade batazo
gida ba, kadan barta tayi kwana biu” cike
da farin ciki yace toh, sukayi sallama.
Washe gari dangin babansa kusan biyar
daga Kebbi suka zo Zaria naiman auran,
hannu bibbiyu Baffah ya tarbe su, akayi
magana aka tsayar da rana sati kacal,
sukayi godiya sosai daga bisani suka
wuce.
Asibiti Mom ke wuni sai dare ta dawo,
tsakanin Ayna da kamil sai kallo, ko
magana yay mata bata cewa uffan sai dai
ta fake da bacci take ji.
*****Bayan kwana biyu
jikinta yayi sauki sosai, Dr. Faiza ta sallame
su, kamil ne yazo ya dauke su.
cika take tana batsewa akan Inna tace
mata Zaria zasu wuce, ba yadda bai yiba ta
zauna gaba tak’i, baya ta zauna da Inna
har suka isa.
Ta fito da sauri ta shige gida, murmushi
yayi ya fito ya taimakawa Inna ta fito
sannan suka gaisa da Baffah daga bisani
ya masu sallama ya koma Kaduna.
***Katsina
Mami ce tare da Jamila suna aiki a kitchen,
ta fito Palo ta zauna, jamila ta fito rik’e da
apple drink zata wuce, Mami tace “ina zaki
kai ?”
“aunty tace na kawo mata”
“Okay” koma kitchen bani nakai mata, ta
mik’a mata.
Tana zauna kan gado taci uban kwaliya,
tana danna waya, Mami ta shigo rai bace
“ga drink din” tace mata tare da kare mata
kallo, ta amsa tare da murmushi, baki takai
zata sha…taji tas din kakkaywan mari
akuncinta, nan take ta saki drink din akasa,
Mami tace “waye bawan ki agidan nan,
wato kina daga kwance kina bada order
koh ?” tayi shuru tana sharar kwalla.
Kayanta da cosmetics Mami ta kwashe
tsaf sanna ta kwallawa Jamila kira, tazo da
saurinta.
“na baki hutu, ki koma gidanku
bayan wata shida ki dawo” ta amsa toh da
murnan ta sannan ta fice, ta kalli Haseena
tace “daga yanxu aikin gidan nan naki ne”
ta fice afusace sannan ta dawo ta wurgo
mata dogayan riguna guda shida, tace “ki
cire na cikin ki kisa daya daga ciki” ko
amsar ta bata jira ba, ta fice.
Fashewa da kuka Haseena tayi, ta
zauna kasa tana dana sanin zuwa, cikin
tashin hankali ta mik’e naiman wayanta,
wayan babu komai, Mami ta dauke, ihu ta
saki tana k’iran sunan Kamil yazo ya
ceceta…….
*cute xarah*
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Page*
***Bayan sati daya
Ran asabar, ranar daurin aure kenan, tun
safe ake hidima da Kai da kawowa agidan,
Adda taci kwalliya sai hidimar tarb’ar bak’i
dake, Ayna da Auta suna mak’ota ana
shirya su. Bangaren Mom suna ta shiyin su,
yan’uwa da abokan arziki duk sun zo daga
kebbi dukda ta gayamasu ba wani
gagarumin buki za tayi ba.
Tun karfe biyu manyan bak’i suka fara
hallara, biyu da rabi na cika aka daura
auren su a babban masallacin juma’a na
Zaria, wanda limamin masallacin ya daura
akan sadaki dubu ashirin nako wacce.
Acan gida kuwa, yar karamar liyafar walima
Adda ta hada, ta gayyato shahararriyar
malamar nan mai k’arin haske akan yadda
ake zaman aure, da hanyoyin da mace za
ta bi na halak don ganin ta kame mijinta
ahannu, wato Malama Hudda A Yusuf.
Bayan sallama da godiya ga rabbi
subhanahu wata’ala, da gaishe gaishe,
Malama Hudda tafara wa’azi mai dauke da
hikima da salon fadakarwa da tunatarwa, da
yadda rayuwar aure zata kasance tare da
hannunka mai sanda ga tab’arb’arewar
tarbiyan yaran zamani.
Da dare ko wace aka mik’a ta gidan mijinta
bayan Baffah ya masu fadan da duk uban
k’warai yake ma ya’yanshi idan zaa kasu
dakin aure, Ayna tasha kukan rabuwa da
Inna dakyar Adda ta samu ta b’anb’areta
daga jikinta, aka sakata mota tana
shessaka. Gidan tsit yake, yawanci bak’in
sun koma sai kadan da zasu tafi gobe,
sunyi farin cikin ganin Amarya mai hankali,
kowa nasiha da fatan zaman lafiya ya mata
daga bisani aka rakata dakinta.
K’arewa dakin kallo tayi, kayan gado da
Baffah yasa mata dan ma daidaici a
talauce, ga lefen nan ajiye agefe, tayi farin
ciki sosai da gadon dan batayi tsammanin
zai mata komai ba. shuru tayi tana ganin
kaman amafarki yau ta aure rabin ranta
daga bisani bacci ya kwashe ta. Koda ya
shigo ba kowa Palo, bai ratsa ko ina ba ya
wuce dakinsa.
Washe gari, ta shirya ciki blue less mai
kyau ta fito ta shiga dakin Mom bata nan,
tana zuwa Palo ta ganta tare da bak’i suna
sallama zasu koma kebbi, ta karaso hade
da gaida su aladabce, suka amsa da
fara’arsu, suka k’ara mata nasiha sannan
suka tafi. Kallan ta Mom tayi tana
murmushi, duk sai taji kunya tayi saurin
sunkuyar dakai, “muje dakina ki tayani hada
kaya” tace “toh” akunyace ta bita.
Akwati Mom ta fiddo tace mata ta
kwashe kayan wardrobe tasa su ciki, tayi
tsuru da ido “Mom karki tafi ki barni” dariya
tayi tace “buk’ata ta tabiya zaman mi
zanyi, kinzo gidanki nima tattara wa zanyi
na koma nawa gidan” magana za tayi taji
muryan sa yana k’iran Mom, da sauri ta
shige toilet ta boye, ya shigo yana fadin
“Mom ki bari gobe na kaiki da kaina.”
“a’a nikam yau zan wuce, already driver
dina yazo” ba yadda ya iya yace toh, ya
fice a sanyaye, Ta fito tana sosa k’eya, ko
kallanta Mom ba tayiba ta cigaba harkar
gabanta, aranta tace kudai kuka kasani,
idan nabar maku gidan kwa k’arata.
Tana gama hada kayanta ta fito waje
Ayna na biye da ita tana jan akwatin, yana
tsaye bakin mota ya karaso ya amshi
kayan, suka hada ido tayi saurin k’awar da
fuska, nasiha sosai Mom ta masu sannan
driver yajata suka tafi, da gudu ta koma
cikin gida tana kukan rabuwa da ita, ya bita
yana k’iranta tayi banza, zama yayi Palo
yana murmushi.
****Bayan kwana biyu
Zaune take a palo tana kallon Tv, ba taji
motsin shigowar sa ba, taji an zare mata
dankwalin kanta, a razane ta mik’e zatayi
ihu ya rikota hade da rufe mata baki da
hannu, ware ido tayi tana kallan sa, yace
“na kama ki, yau ba hide & seek tsakani na
dake” ta girgiza kai alamun “a’a” hannun
sa yacire daga bakinta yana fadin “miyasa
kike gudu na ?” tayi shuru, ya kai bakinsa
zai mata kiss tayi saurin runtse ido,
murmushi yayi ya sunkuceta zuwa dakin sa
Kan gado ya dire ta, taji hadaddan kamshi
ya bugi hancinta, ta bude ido ahankali tana
k’arewa dakin kallo, suka hada ido ta sakar
mai lausassar murmushi, ya mik’e tsaye
hade da mika mata hannu “tashi muyi
sallah” akunyace ta mik’a mai hannu,
sukayi alwala suka gabatar da sallar godiya
ga Allah da neman zaman lafiya da zuri’a
mai albarka, yayi mata tambayoyi game
da addini, ta amshe su.
Wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi sannan
ya tsare ta idanuwa sa, ta k’awar da fuska
cike da fargaba, ya matso da ita jikin sa
har tana jiyo numfashinsa, gaba d’aya ta
kid’ime bugun zuciyar ta ya sauya, tsoro ya
shige ta ganin yadda yanayinsa ya canza.
Hada bakinsa yayi da nasa yafara kai
mata hot kisses tare da shafa jikinta ta ko
ina, ya dauketa ya dire ta kan gado ya
cigaba da sarrafa ta, duk ta gigice tarasa
yanayin da take ciki, ya fara kokarin rabata
da kayan cikinta, ta kwalla ihu hade da
kiciniyar kwace kanta ganin yana shirin
wuce gona da iri, cikin wahalallar murya
yakai bakinsa kunanta yace “help me,
nasan you’re strong.” kasan cewa komai
tayi, gabadaya tsikar jikinta ya tashi wani
irin yanayi marar fassara take ji ajikinta. ya
cigaba da aika mata sakonnin ta ko ina
daga bisani ya fara karanto addu’a saduwa
da iyali. Nayi murmushi hade da mik’ewa
tsaye na fita nabasu wuri.
Shi ya fara tashi ya shiga wanka, ya dawo
ya dauke ta cak ya kaita bathroom domin
yana ganin kamar yaji mata ciwo, sai dai ya
kula ba ciwo yaji mata ba, bayan sun gama
ya bata pain relief tasha, yaje kitchen ya
hado mata hot tea ya kawo yana bata, tana
sha tana zuba mai shagwaba kaman za tayi
kuka.
Tun daga wannan ranar wata irin Soyayya
suke ma juna mai cike da kauna da
mutunta juna, kullum suna mak’ale da juna
sun mata da wata Haseena a duniya.
*cute xarah*
~* Mijin Mai Saloon*~
_*Story & written*_
_*by*_
_*xarah bukær*_
*Page*
*Bayan wata uku*
Tun safe take tik’ar wanki bayan ta gama
shara da goge goge, da girkin abincin
gidan, gaba daya jikinta ciwon yake adalilin
rashin hutu da kwanciyar hankali, Hanifa
tazo da wasu tilin kaya ta ijiye, tace “Aunty
sannu da aiki, Mami na k’iran ki” tayi
murmushi tana fadin “jeki, gani nan zuwa.”
Barin wankin tayi ta dauraye hannuta ta
tsaye fargaban abunda Mami za tace, a
sanyaye tadau hijabi tasa sanna ta wuce
ciki.
Abba da Mami na zaune kan dining
suna k’arin kumallo, ta shigo a d’an tsorace
“Mami gani” guntun tsaki Mami taja “bana
hanaki cika mata gishiri a abinci ba” tayi
tsuro da ido “Mami kiyi hakuri, tunda nabar
gidan nan banyi girki ba shiyasa ake dan
samun kuskure” harara ta balla mata, tace
“wawiya ko kunya bakya ji, da auranki
bakya wa miji girki” tsawa tayi mata tace
tabasu guri, ta fice sanyaye.
Abba ya numfasa “haba Karima, takurar
tayi yawa, sai kace ba y’arki ba, kin
tsangwama yarinya duk tabi ta fige ta
lalace, palo ma kin hanata zama, kullum
tana kitchen zunbule da hijabi azaune sai
kace marar gata.”
“gatan kenan ai, kasan tandar waina
sai da horo.”
“Koma miye ya isheki haka, yarinya ta
tattara ta koma gidan mijinta” mik’ewa yayi
ya koma daki afusace. Ajiyar zuciya ta
sauke, ita kanta tasan yanxu Haseena ta
shiga taitayin ta.
Da yamma tana zaune daki, taci kuka harta
gaji, babban tashi hankalinta shine yadda
Kamil ya manta da ita, gashi ko waya bata
dashi, can dabarar k’ira Mom tazo mata,
amma ya za tayi bata da waya. Ta mik’e
ahankali ta leka dakin Mami batanan tana
dakin Abba, ta shiga da sauri tayi sa’ar
ganin wayar Mami kan gado, ta dauka ta
binciko nambar Mom tayi dialing, bugu daya
Mom ta dauka, cikin muryar kuka ta gaida
ta, Mom tace hajiya karima lafiya kuwa ?”
“Mom ba ita bace, Haseena ce” ta
k’ara fashewa da kuka, hakuri taba Mom
hade da rokonta gafara, kuma dan Allah
tama kamil magana yazo ya dauke ta. ba
k’aramin tausayinta ta jiba, tace “ki daina
kuka, duk abunda keki min ban taba
damuwa ba saboda kowa yayi na gari
kansa, duk abunda ka shuga shi zaka girbe,
nagode wa Allah tunda kin gane kuranki,
karki damu gobe zaizo ya dauke ki” nasiha
sosai mai ratsa jiki Mom tayi mata daga
bisani sukayi sallama.
Ta ajiye wayan zata fita sukayi kicibis da
Mami bakin kofar, jiki na rawa ta fara
magana “dama dakin na shigo gyarawa”
murmushi ta sakar mata hade da jan
hannuta suka zauna kan gado,” Mami kiyi
hakuri ki yafemin” ta fada cikin shessakar
kuka.
Rik’o hannuta tayi tace “duk abunda namiki
cikin so ne, Haseena ya kamata a shekarun
ki kisan darajan mutane balle ma iyayenki
da suka kawoki duniya, kedai kawai rayuwar
karya da al’adar daba taki ba kika daukan
wa kanki alhalin bazai fishe ki da komai ba
sai fushin ubangiji, Allah ya baki miji na
gari baki dauke shi abakin komai ba, toh
kisani duk ranar daya sakoki ki tabbata
babu wanda zai kwashe ki.” Fada sosai
Mami tayi mata, tayi ta kuka cike da
danama.
***Kaduna
Tana mak’ale jikin sa wayarsa yayi ringing
ya duba yace Mom ce, ta mik’e zauna, ya
dauka suka gaisa da fara’arsa, ta tambayi
Ayna ya mika mata suka gaisa sannan ta
bashi wayan, tace mai ya kamata gobe yaje
Katsina ya dauko Haseena tunda dai akwai
aure tsakanin su, yace toh Insha Allah zai
je, suka dan tab’a hira daga bisani sukayi
sallama.
Ta kalle shi a shagwab’e “ina zakaje ka
bari ?” ya fada mata, nan take annurin
fuskan ta ya dauke, za tayi magana taji
amai yazo mata, ta tashi ta shiga toilet da
gudu tana kwarara amai, cike da tashin
hankali ya bita ya taimaka mata harta
gama, “sannu, mai ke damunki ?” dakyar
tace “nima bansani ba, kwana biyu bana jin
dadin jikina na” gado ya kawota ya kwantar
da ita sanna ya k’ira Dr Faiza, cikin minti
ashiri tazo ta dubata ta sanar mai tana
dauke da ciki na wata biyu.
Farin ciki sosai yayi, sabon tattali ya fara
mata aranar har washe gari dazai tafi
katsina, dakyar ta barshi ya tafi tana ta
kuka.
**Katsina
Tun safe ta shirya tazo Palo zaman jiran
sa, kayanta kaf Mami ta bata. Sai bayan
sallah azahar ya iso gidan, suka hadu da
Abba a haraban gidan suka gaisa sannan
suka shiga ciki, tana zaune tare da Mom
suka shigo, dif jinin jikinta ya dauke ganin
yadda ya kara kyau da kwarjini, ya gaisa da
Mami tana mai tsiyan ango kasha kamshi,
kunya yaji ya zauna, ya kalle ta asace duk
ta rame sai fari kawai. Harara Mami ta
balla mata, ta mike da sauri ta gaida shi
sannan taje kitchen ta kawo mai abinci da
kayan sha, dariya yayi aranshi ganin sauyin
halinta, yau itace harda gaida shi.
Nasiha sosai Abba da Mami sukayi masu
hade da kara ja mata kunne zaman aure
ibadace, duk wani mugun halinta dason
kanta bazai k’wato mata mutunci ba balle
yanxu da take da abokiyar zama, iya kaci
miji yayi watsi da ita. Fada sosai sukai
mata, sukayi sallama suka tafi, zaa turo
driver yazo yadau motar ta.
Har suka iso Kaduna ba wanda yace
uffan, suna isowa gida, Ayna ta fito ta
tarb’e su da murnan ta “Aunty sannu da
zuwa.”
“yauwa” a atakaice ta amsa ta haura
sama, bata damu ba ta karasa wajen sa
tayi hugging dinsa tanamai welcome back,
suka zauna Palo takawo ruwa mai sanyin
taba shi yasha. Haseena dake makale kan
stairs tana kallon su kaman ta kurma ihu
dan haushi da takaici, ta shiga dakinta,
komai an canza sabo, ga akwati sabi agefe,
ko kallansu batay ba dan tasan na fadar
kishiya ne, fadawa bandaki tayi tayo wanka
tayi sallah magrib ta kwanta. K’wankwasa
kofa taji, ta mik’e ta bude, Ayna ce, tace
“baby yace kizo muji abinci” bata amsa
taba saima rufe kofan da tayi, ta fada gado
tana rusa kuka, duk ita ta jama kanta yau
gashi wata na k’iran shi da baby.
Yana zaune kan dining tazo ta zauna hade
da sakar mai murmushi, yace “ina take ?”
Tana zuwa tace mai. Dakyar ta lallami
kanta ta fito ta iske su, tayi yak’en dole ta
zauna hade da bude kulolin, fried rice ce da
pepper meat, tace “sweety gaskia masu
dafa mata abinci sunyi improving sosai”
caraf Ayna tace “aina sallame masu aikin
gidan, nice na dafa da kaina.”
“lailai ma, ke wace dazaki canza min
rules din gidana” ta fada rai bace tana
kallon sa, yace “hakan ne daidai, daga yau
kowa ranar girkinta zatayi abinci” akufule
ta mik’e tsaya tana fadin “bazan ci ba” zata
wuce yace “dawo ki zauna kici” ba yadda
ta iya ta dawo ta zauna, Ayna ta zuba
masu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, basa
shiga harka juna, ko gaida ta Ayna tayi
bata amsawa, ranar girkinta abincin ta
kadai take dafawa taci, amma idan Ayna
tayi ba kunya zata zauna taci tayi nak,
tunda ta lura Ayna nada ciki ta koma
zaman daki bata kula kowa sai kuka,
babban tashin hankalin ta shine baya kulata
ko magana tamai dakyar yake amsawa
tarasa dalili, ta mik’e ta kalli kanta
amadubi, ta hadu iya haduwa amma mi ya
rage, can tayi tunani taje ta bude akwati
tadau atamfa tasa, ta kalli kanta tayi
murmushi, yau zai kulata tunda tasa kayan
da Ayna take sawa, taci uban dauri ta
dawo Palo kasa ta zauna jiran shi, daga
kitchen taji k’akarin mai, ta mik’e a tsorace
ta karasa wajan ta leka taga Ayna na amai
duk ta fita hayyacinta, da sauri ta shiga ta
riko ta tanai mata sannu, suka dawo Palo,
ta dauko ruwa ta bata, “nagode” Ayna ta
fada, tayi murmushi tace “ki huta, bara naje
na karasa girkin” ta mik’e ta koma kitchen.
Ta fito rike da Tea a hannu, tace “Ayna
tashi kisha ko zaki samu karfi” ta yunkuro
dakyar ta amsa, ya shigo tare da sallama,
Haseena ta amsa da fara’arta, kallon
mamaki yayi masu ganinsu tare, ta karaso
tana mai sannu da zuwa, ciki ciki ya
amsata ya rab’a gefenta ya wuce wajan
Ayna, jiki sanyaye tabi sa da ido, “ya jikin”
ya fada yana tab’a zafin wuyanta, “da
sauki, Aunty taban magani nasha” ya dago
ya kalleta hade da mata murmushi, taji dadi
sosai, ta dawo ta zauna tare da murmusa.
Tun daga wannan ranar suka shirya, zaman
su zama na mutuncin da mutunta juna
gwanin sha’awa, Haseena akwai tausayi ko
ciwon kai taji Ayna nayi saita naimo
magani ta bata, ta bangaran kamil yana
kokarin adalci a tsakanin su dan dukan su
yana sonsu, har katsina Haseena taje gaida
iyayenta, baa kwana biyu bata kira Mami
ba.
Ayna ta haihu ta haife santalelan yaro sak
ubansa, murna sosai Haseena tayi dan
tasan ita da haihuwa sai ikon Allah saboda
allurai iri iri datayi ma kanta dan karta
haihu, gashi yanxu naima take ruwa a jallo.
Ran suna yan’uwa da abokan arziki duk sun
hallara, su Inna, Adda da auta duk sun zo,
yaro yaji suna Usman ana kiransa da
sudais. Mom tayi farin ciki sosai ganin
yadda kansu ke hada, Haseena sai kula
take da ita.
Rik’e take da sudais ta shigo daki ta dauki
kudi, har zata fita ta dawo ta karewa daya
daga cikin handbags dinta kallo, tayi
murmushi kasan cewar ta tuno handbag din
ne sanadin haduwar Kamil da Ayna, gashi
harda rabo atsakani, “kaico” ta fada aranta,
inda ana canza past data koma ta gyara
mistakes dinta.
Dakin Ayna ta shigo, tana zaune tana ninke
kaya, ta zauna hade da mik’a mata kudin,
ta amsa tace “Aunty kudin miye ?”
“kudin ki ne” kallan rashin fahimta tayi
mata tace “kudi na ?”
“eh, sha’anin rai karna mutu da hakkinki
akaina shiyasa na baki albashin ki dana
hanaki da dadewa.” Dariya Ayna tayi tace
“haba Aunty, plz ki barshi.”
“a’a, tunda na baki bazan karba ba”
kin karba tayi shiyasa ta kyaleta, tace
“Aunty naga kin daina zuwa saloon” dariya
tayi tace “tun yaushe nasa saloon akasuwa,
yanxu haka nasamu masu siya.” Ido Ayna
ta ware tana fadin “wayyo Aunty aida kin
cigaba da zuwa.” k’ara darawa Haseena
tayi tace “sannu mai wayo, so kike inje
saloon ke kina gida da miji koh ?” Duk suka
kwashe da dariya, yana tsaye bakin kofa
yana jinsu yana dariya, ya shigo yace
“nasamu karin matsayi” duk suka kallo shi,
atare sukace nami ?” Zama yayi tsakiyan su
yace ” babban matsayi kuwa, daga Mijin
Mai Saloon na koma Mijin Haseena da
Ayna” duk suka kwashe da dariya.
*Alhamdulilah*
Anan na kawo masu k’arshen wannan
gajeran littafi nawa mai suna *Mijin Mai
Saloon* na godewa Allah daya baki ikon
kammala wa.
Jinjinar ban girma tare da godiya ga
k’ungiya mai albarka *NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION*, Allah ya k’ara had’in kai
atsakanin mu, mak’iyan mu da mahassada
Allah ya mayar masu da abunsu. (Amin)
Gaisuwa gareku gaba daya yan;
*Excellent writers*
*Online Hausa writers*
*Extreme writers*
*Wisdom writers*
Dama sauran da ban ambata ba duk na
gaishe Ku, kuma ina godiya.
Godiya ga dukkan masoyana, Allah yabar
kauna
Members na group dina *Xarah’s Novel*
na gaishe Ku kyauta;)
By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
07039625239
0 comments:
Post a Comment