BABI NA ASHIRIN DA DAYA.
Tun ranar da Dr.Aqeel ya dauki kafarsa ya bar kasa najeriya shikenan natsuwar zuciya da ruhi suka gagari duniyar Mariya sosai ta shiga tashin hankali mara musaltuwa bata taba zaton zata yi k'ewarsa har haka ba bata zaton zuciyarta da gangar jikinta za su kasa sukuni har haka ba tayi kuka, kukan wanda take zaton zai rage mata raɗaɗi zuciya amma hakan bai yuwuwa ba sosai ta raya darurruka masu yawa cikin yanayi na damuwa da takomshin saƙar zuciya.
Sosai takoma shiru-shiru magana ta za me mata wani aiki kato a duniyarta ba ta san ya kayi ta batawa ran mutumin da ya jikanta a rayuwa ba ba ta san mai yasa tayi gangancin haka ba bata san mai yasa a ranar da za su rabu ta barshi sa tukwuicin bacin rai ta sani da fushin ta ya bar kasan nan ta sani dole ya shiga cikin yanayi na bacin rai duk a dalilin ta ina zata gan shi ta bashi hakuri a ina zata ganshi ko ba a zahiri ta wanke laifin da ta yi masa ta sani sosai yayi mata nisa nisan da ba ta da damar da zata je in da yake har karshen rayuwarta in bashi ne ya dawo ba ya tadda ita tunanin ya ta'allaka ne a yarda za t rayu dashi a zuciyarta wanda ba ta san adadin lokacin da zai dauka kafun ya dawo ba sosai take hango gangancin da tayi na bata damar da ta samu.
Haka ta cigaba da rayuwa cikin wannan yanayi da tunanin Dr.Karami lokaci mai tsayi cikin duniyarta haka ta cigaba da zuwa makaranta tana karatu da tunanin Dr.Karami a ranta da ruhi dama duniyarta baki daya.
Mutum daya ce take samun damar da take zama tana zantawa da ita har ta rage mata damuwar dake addabar zuciyarta sosai Baseera ta taka muhimmiyar rawa a duniyar Mariya sosai take nuna mata rashin dacewa ga halin da ta je fa kanta duk yarda zatayi don ganin ta rage mata tunanin abin dake dawainiya da Mariya tana yi sosai take hanata zaman shiru kulli-yau min in dai basu da lesson to tabbas zaka same su zaune waje guda suna bitar karatun su domin Baseera ta hakikance haka ne kawai zai rage abubuwa da yawa a duniyar Mariya da suka addabe ta.
A bangare guda kuma Dr.Aqeel da Huzaif suma sosai suke saka ta cikin halin rashin kwanciyar hankali domin ta hakikance a ta dalilinsu komai ya faru da ita tsakaninta da Dr.Karami sosai take jin tashin hankali a duk lokacin da suka kwaso jiki suka zo gareta bata san abin da suke nufi da ita ba sosai take ganin suna takura mata domin kuwa laifin komai da komai da ya faru akan su ta daura su ne silar faruwar komai.
Ko dai dai in tayi duba ta wani fannin duk wanda ya zo a tsakaninsu tana kula su hakan kuma na kara tuna mata da Dr.Karami tana ba su lokaci sosai da sosai domin Dr.Aqeel ba abin yadawa bane shima ya taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarta sosai da sosai ba za ta yi masa halin dan'adam ba mai mai da alheri zuwa akasin sa.
Haka shima Huzaif duk da tabon da yayi mata a zuciya hakan bai sa ta watsar dashi tun da ya nuna nadamarsa akan abin da yayi amma kuma ba hakan bane ya sanya ta tsayawa dashi har ta bashi lokacin ta illa soyayya da yake nunawa kaninta Mu'azzam soyayya ce mai girma a tsakaninsu gami da shakuwa sosai da sosai yake bashi kulawa yake tattalin sa kamar dan'uwansa na jini hakan ba karamar rawa ya taka ba har Huzaif ya samu matsayi a filin zuciyarta.
ba ta san wata irin ƙaddara bace take yawo da ita a duniyarta a duk lokacin da ta tuno abubuwa da suke ta faruwa da ita a filin rayuwarta sosai take hango tashin hankali mai girma nan gaba duk ranar da Dr.Karami ya duro kasar nan.
*****
"Nikam ina ganin Bariki 'ya duk idanuwanta sun gama buɗewa tana kallon mutane ɗai-ɗai kamar tsararrakin ta ni ban san wani tsohon makiri bane da wannan danyen aiki in ban da son sani da kalan-dangi da neman mai da yariya karamar yar duniya me nene haka kullum yarinya kenan da tsukanken wando da guntun hijabi tana zarya a hanya kowa ni kare da doki suna kare mata kallo".
Goggo Marka ce take fadin haka tana tafa hannu a daidai lokacin da Mariya ta dawo daga makaranta jikinta sanye da Uniform riga da wando sai hijabi wanda iyakarsa kirjinta.
Tun da Mariya tafara daukar kafarta zuwa makaranta tun daga wannan rana Goggo Marka take debe mata albarka akan cewa iskanci kawai da duniyanci ya sanya aka saka ta makarantar yahudawa yarinya sai kara girma take yi tana buɗewa kowa ni namiji sai kallon ta yake yana haɗiyar yawu.
Ba karamin tashin hankali Mariya tashiga ba a ranar da taji mugun nufin da Goggo Marka ke jfanta dashi tayi kuka kuka mai amsa sunansa kuka Umma ita kanta tayi bakin ciki mai girma sosai zuciyarta tashiga tashin hankali jin mugun nufin da ake jefar 'yarta da shi a ranar ta so ta hana Mariya zuwa makarantar amma zuciyarta ta hanata tana mai gargaɗin ta akan sabawa alkawari da kuma rashin baiwa Dr.karami muhimmancin abin da yayi musu na alheri sosai tayi duba akan ilmi tasan ilmi na da matukar muhimmanci a duniyar rayuwar 'yarta sosai karatun da tayi zai taimaka mata a fannoni masu yawa a wannan zamanin da ake ba wai ita kadai Mariya ba har da su iyayenta da al'umma a duk ranar da ta zama wani abu a filin duniyar nan a dalilin karatu tasan za suyi alfahari da ita sosai da sosai.
Ta sani dole ne ta jajirce sannan ta kau da kunnuwanta ga sauraron duk wani mugun furuci da za a fada mata ita da 'yarta dole ta rarrashi zuciyarta dole ne ta cigaba da yi ma 'yarta addu'a sannan ta kara mata karfin gwuiwa ta nuna mata amfanin karatu a duniyarta da su iyayenta dama Al'umma gabadaya ita dai fatanta a kullum Mariya ta tsare rayuwarta da martaba gami da darajarta ta dage wajan karatu sosai da sosai duk wuyarsa da wahalarsa zata ga amfaninsa nan gaba sosai da sosai domin a yarda suke yanzu karatunta zai matukar taimaka masu nan gaba sannan ta kara tunatar da ita cewa ta dube su da rayuwar da suke yi ta tabbata in da sunyi karatu a zamaninsu ba a za su fuskanci kalubalin rayuwa har haka ba ko ma za su fuska to ba zai yi tsauri haka sosai da sosai ba.
Huɗubar Umma sosai ya samu waje a filin zuciyar Mariya ta ajje waje na musamman.
Sosai take jin tausayin iyayenta na kara samun fili mai girma a zuciyarta da ruhinta sosai take hango irin rayuwar da suke gudanarwa tana hasashe kafun zuwanta duniyar nan ta sani sun fuskanci KALUBALE sosai da sosai in tayi duba da yarda auren iyayen nata ya kasance a yarda take samun labari sosai suka shiga tashin hankali kafun tabbatar auren iko na Allah ne kawai yayi aiki a tsakanin iyayensu har suka bar su suka auri junansu.
Domin sosai ake fuskarta matsala tsakanin Fulani iyayen Habeeba da manoma iyayen Bello sosai rashin jituwa ke tsakaninsu amma sai Allah ya kulla soyayya mai girma tsakanin 'ya'yansu wanda haka sam bai yi musu dadi ba su iyayen musamman ta bangaren iyayen Habeeba domin AKAN SO da take yi wa Bello ta zabi kin bin iyayenta domin da rigima tayi rigima abu yaki ci yaki cinyewa sosai suka fara kokarin haɗe kayan su domin canza mazauni nan Habeeba tayi tsalle ta dire ta nuna ita ina ba za ta bi su ba komai za suyi mata kuwa tana tare da Bello gani take in aka raba ta dashi to tabbas zata iya rasa rayuwarta sosai iyayenta sukayi fushi da ita har ya kai ba sa yi mata magana ganin da sukayi da gaske take sannan da ban baki da mutane suke ba su hakan ya sanya su barwa Habeeba auranta akan kuma komai yasa me ta kar ta sake ta tako kafa in da suke domin kuwa duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka a ranar da aka daura auren Habeeba da Bello a ranar iyayenta suka bar garin Gwada gabadaya zuciyoyin su cike da abubuwa marasa dadi su yi KUDIRI a ran su ba za su sake takowa zuwa wannan garin ba har gaban abada.
A lokacin da akayi auren Bello mahaifiyarsa bata raye mahaifinsa ne kawai yake duniya sai matarsa Marka wanda tun lokacin ita ce take rura wutar komai domin sam bata kaunar auren ta tsani Bello da uwarsa domin a tunaninta shi ne ɗa namiji a gidan kuma shi ne magaji ita kuwa 'yarta daya Zainabu wanda suke kira da Abulle Abulle macece mai hakuri bata biyo halin mahaifiyarta ba domin sosai take bakin cikin duk abin da taga mahaifiyar ta ta nayi wa su Bello Abulle ta riga Bello Aure domin tun tana shekaru sha biyar aka auren da ita tun da tayi auren bata taba haihuwa ba har akayi bikin Bello lokacin da Bello shima ya tare a nan gidan su sun jima kafun ita ma Habeeba ta samu ciki wannan rashin samun ciki sai ya buɗe wa Goggo Marka katon filin tsula rashin mutunci ga Habeeba tana mai aibata ta wai juya ce bata haihuwa kila ta gama yawon bin mazan ta acan rugarsu ta gama zubda kwayayen haihuwarta a layi wajan tallar su ta gado shine aka likawa Bello sosai take jin bakin ciki da takaici sosai ta so yin dana sanin auren Bello amma in ta tuna irin HALACCI da yayi mata ya nuna mata so da kauna ya tattale ta ya za me mata MIJIN MARAINIYA sai taji a ranta za ta iya zama dashi da ko wani irin hali ne ko da kuwa Goggo Marka za ta dinga yankar naman jikinta ta miya dashi.
Ba karamin tashin hankali Habeeba ta fuskanta ba a tsayin shekaru biyu da tayi a gidan auranta sosai duk hakurin ta da kai zuciya nesa hakan bai hana ta shiga matsananciyar damawu ba duk da bata gayawa Bello abin da ke faruwa tun ba ya ganewa har ya zo ya na fuskanta ya yi bakinciki ya nuna bacin ransa amma mahaifinsa ya dinga ba shi hakuri akan kar ya damu wata rana sai labari.
A na cikin wannn tataburzar ciki ya bayyana jikin Abulle Innalillahi wa inna ilaihir raji'una.
Ina wuta Goggo Marka ta saka Habeeba nan fa ta sake bude sabon shafin gori da aibatawa bakaken maganun kuwa ba a magana a lokacin Habeeba ta ga tashin hankalin da bata yi tsammani ba domin kuwa Goggo Marka zuwa tayi da kanta tun cikin na wata bakwai ta danko Abulle ta kawo gida bayan an sha dirama in da Abulle tace ba in da zata je a bar ta gidan mijinta ita kuwa ta dire tace bata san zance ba haihuwar farko ce dole sai taje gida GOYON CIKI ban dan ta so ba haka ta kwaso jiki ta zo gida bayan mijinta ya amince mata ganin da yayi Goggo Marka na shirin birkita musu rayuwar auren su.
Tun da Abulle ta dawo gida fa nan Aiki ya cewa Habeeba Salamu alaikum domin komai na Abulle ita ke yin sa ba abin da aka dauke mata hakan bai dame ta ba domin Bello ya bata baki akan cewa tayi kwana nawa ne Abulle zata koma gidan mijinta a haka har ta haihuwa inda ta samu ɗa namiji nan wata sabuwar duniyar habaici da cin mutunci ta buɗe akan Habeeba haka zata shiga daki tayi kukanta ta godewa Allah duk abin da ke faruwa Abulle na sa ne wani lokacin haka za ta faki idon Goggo Marka ta fada dakin Habeeba tai ta bata hakuri akan abin da ke faruwa domin har ga Allah tana jin bakin ciki da takaicin abin da ake yiwa Habeeba sai dai bata da damar hanawa in tayi magana haka Goggo Marka zata ta surfa mata zagi wai bata kishin kanta sannan ai Habeeba bata da amfanin komai a gidan tun da ba haihuwa take ba sai dai taci ta kwanta tayi kashi.
Sai da Abulle tayi wata biyu cur! san nan ta koma gidan mijin ta a dan tsakanin Habeeba ta samu sa'idar aiki.
Shekarun Abulle ashirin da Haihuwa ta sake samun ciki a lokacin ita ma Habeeba Allah ya taimake ta ya amsa du'a'in ta ya bata na ta rabon.
Yaa Allah!.
Ku zo ku ga murna wajan Habeeba da Bello da Mahaifin Bello wanda a lokacin girma ya kama shi sosai da sosai.
Ita kuwa Goggo Marka ji tayi kamar ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki da takaici haka tana kallo Habeeba tayi rainon cikin ta da taimakon mijinta har ta sauka lafiya ta samu 'ya mace hakan yayi wa Goggo Marka dadi sosai domin haihuwar mace da akayi ta san ko ba komai dai ai an rage mugun abu in da namiji aka haifa ai da ta shiga uku.
Satin su daya ita ma Abulle ta haihu ita ma dai 'ya mace ce.
Ranar su aka sanyawa yarinya Mariya ita kuma Abulle aka saka ma 'yar ta ta Hafsatu.
Tun daga wannan lokacin zama dai ya ki dadi a tsakin Goggo Marka da Habeeba har zuwa lokacin da su Mariya suka isa Yaye a lokacin Goggo Marka ta dauko Hafsatu da sunan yaye ta tun daga lokacin ta zama 'yar gidan ta sosai ta sargarta ta da sunan wai gata ba ta jin kunyar uban kowa tun tana karamar ta ta iya zagi da dukan mutane ba yarda Abulle bata yi ba domin ansar 'yarta ganin irin tarbiyar da ake yi mata Goggo Marka ta hau ta dire akan ba wanda ya isa ya rabata da Hafsatu wannan shi ne silar sangartar Hafsatu sai ta ga dama take zuwa wajan iyayenta ko taje to da rigima suke rabuwa da uwarta ta dawo tana kuka haka Goggo Marka zata zari mayafi ta je har gidan Abulle tayi mata rashin mutunci ta dawo gida.
Shekarun Mariya Hudu Allah yayiwa kakanta Mahaifin Bello rasuwa sakamakon gobara da ta kama gidan duk kan su ba sa nan shi kuma jikinsa yayi nauyi sosai da sosai ko tashi bai ya iyayi haka yana kallo wuta ta kama shi ba shi da halin taimakon kan sa.
A ranar sun ga tashin hankali a gidan domin komai ya kone ba abin mamora gabadaya wannan shine silar fadawarsu kangin rayuwa su ka fuskanci kunci sosai ya kasance abin da za su samu su ci ma sai Bello ya fita yayi buga-buga domin dama sana'ar tambobi yake yi to duk gobara ta lamushe jarin d kuma sauran dambobin da yake kiwo cikin gida.
Wannan kenan.
********
Sanye take da bakar jallabiya mai dogon hannu wanda ta dan kamata jikinta kadan sai hijabi mai kalar pink sai fulawowi masu kaloli da suka karawa hijabin kyau sosai tayi wa kayan kyau ba wai su sukayi mata kyau ba ba wata kwalliya tayi ba a fuska ba domin Mariya sam ba irin matan nan ba ne masu son kwalliya in kuwa ka ganta da kwalliya to tabbata Baseera ta zo gidan ko kuma ita taje gidan su.
Bayan ta gama shirin ta dubi Umma dake sauyawa Mu'azzam wando.
"Umma ni na tafi sai na dawo".
Ta fadi tana mai daukar jakar Islamiyyarta dake rataye.
"Allah ya kiyaye hanya a kula sosai Mariya Allah ya bada ilmi mai amfani a dahe da karatu kin ji karatu yana bukatar jajircewa da mai da hankali akan abin da ake koya wa".
Murmushi Mariya tayi tana mai gyaɗa kai a kullu-yau min in zata tafi makaranta maganar Umma kenan na nuna son ta kula da kanta kuma ta mai da hankali akan abin da taje koya har ta hadda ce maganar ta ta wanda ta samu fili a zuciyarta ta ajje ta kuma tayi Alkawari in Allah ya yarda za ta yi abin da Umma ke so ta ga ta yi.
Da wannan tunanin ta fice daga dakin bayan ta jawa Mu'azzam hanci da yake ta faman kallon ta dariya ya saki ita ma mai da masa tayi sannan ta fito daga cikin dakin.
Ta na cikin saka takalmin ta ta tsinkayi muryar Goggo Marka.
"ina ganin lalata nikam wai sai a zage ai ta nuna wa mutane Allah a baki zuciya kuwa ta fir'auna ce yanzu in ban da kuturun kinibibi Hafsi ji be ta don Allah ta zabga doguwar riga har da zabgegen hijabi an rakito jaka wai za a karatun addini bayan an gama tambaɗewa a waccan boko jahanna ma din wai mu za ayi wa BIRI BOKO".
Tsaki Hafsi tayi daga in da take zaune ta mimmike kaf kamar sabuwar 'yar kaciya sai faman kai noma bakin ta take yi.
"Uhmm yo Goggo wani dare jemage bai gani ba ai sai na mutuwarsa ai mu tuni muka gane barno ba gabas take ba balle a juyar mana da alkibla kawai kallon mutum muke".
Ta karashe tana sake yanko katuwar lomar taliya da taji yaji da mai har canza kala take yi kallo daya zakayi wa taliyar kasan an kashe mata kuzarin ta da barkono.
In da sabo Mariya ta saba da irin wadannan habaice-habaicen don haka ko ta kan su ba ta bi ba ta na saka takalminta ta kama hanyar ficewa daga cikin gidan.
"Hehehehe wai mu za a nuna wa bariki".
Fadin Hafsi tana daukar kofin ruwa tana kai wa bakin ta gabadaya ta gama hada gumi kamar mai jego a lokacin zafi ta sha kunun kanwa.
Zuciyarta sosai ta kuntata jin abin da Hafsi ta fadi akan ta a duniyar nan ba abin da ta tsana irin ace da ita 'YAR DUNIYA ko 'YAR BARIKI sosai take jin zuciyarta na kuna da zafi...
"Mariya!".
Kamar daga sama taji amon muryar ko ba a fadi mata ba ta gane ko waye in hadda ma ake akan muryar mutum ita kam! ta hadda ce.
Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba tana jin takusan har ya iso in da take tsaye ya zo ta gabanta ya tsaya hannayensa harɗe a kirjinsa sosai yake kallon ta da duk idanuwansa sosai ya karanci akwai abin da yake faruwa da ita mara dadi daga cikin gidan kafun fitowarta ga idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir numfashi ya ja mai girma kafun ya kau da idanunsa yana jin wani iri game da ita a zuciyarsa wanda har zuwa wannan lokacin ya kasa yarda da hakan sai fafatawa da zuciyar tasa yake yi akan kalubalantar ta akan abin da take sanar dashi.
"Me ya same ki Mariya?".
Ya fadi idanuwansa sosai a fuskarta da kallon tuhuma.
Kasa ta karayi da kai tana mai girgizawa alamun babu komai a zuciyarta kuwa ba abin da ke kona mata ita sai kalaman Hafsi sosai ta tsani taji an jona mata rayuwar duniyarta da bariki ta tsani haka amma ita kuwa Hafsi ta mai da mata rayuwa kamar wacce take zaman kanta ko wacce aka ce je ki kya gani in dai duniya ce.
"haba mana Mariya dake fa nake".
Ba ta son tsayawa bata son bata lokacin ta tana bukatar ta isa makaranta da wuri.
"Ba komai kawai dai yau na tashi ne bana jin dadin jiki na".
Ware idanu yayi yana dubanta cikin yanayi na tausayawa kafun ya ja numfashi.
"Amma kuma a haka zaki tafi makaranta kin san bakya jin dadi ya kamata ace kin sha magani kin kwanta".
maganar ta fara gundurarta don haka ta dago idanuwanta ta dube shi sosai kafun ta kau da idanunta ba ta so suna hada idanu da Huzaif sosai take jin wani iri a zuciyarta da duk kan gangar jikinta sosai take hango wasu abubuwa masu girma cikin ƙwayar idanuwansa wanda ta rasa da me zata danganta su.
"ba wai bani da lafiya bane, kawai dai yanayin garin ne yau gabadaya naji shi ba dadi".
Ta karashe tana mai daga kafafuwan tana wuce wa.
"Sai anjima".
Ta sake fadi bayan ta gota shi tana cikin tafiyar cikin yanayi na rashin armashi ta tsinkayo muryar Hafsi na daka mata kira kiran da taji shi har tsakar kanta gabanta taji yayi wani irin bugawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito.
Da sassarafa ta iso gareta fuskarta ba yabo ba fallasa ta mika mata hannu.
"Bani abin da kika dauka inji Umma".
Duban rashin fahimta Mariya ta shiga yi mata mamaki ya cika mata zuciya akan abin da taji tace da ita to mai ta dauka mai Umma zata aiko Hafsi ta amsa a wajanta mai yasa tun kafun ta fito ba tayi mata magana ba sai bayan ta fito ta ya ya tasan tana tsaye kofar gida bata wuce ba har zuwa wannan lokacin?.
Ware idanunta tayi sosai akan Hafsi da ta mata kerere akai sai faman yatsine baki take yi kamar ta ga wani abin kyankyami a hankali ta shiga motsa bakin ta cikin rashin abin cewa.
"Ban gane ba".
Ta fadi bakin ta na rawa sannan tana juyar da kallonta zuwa Huzaif da ya harɗe hannunsa yana kallon su gabanta taji ya sake faduwa domin ta gama yanke hukuncin akwai kullin da Hafsi ke kokarin yi mata domin tsinka ta a gaban Huzaif ba yau bane ranar farko da ta fara zuwa in da take tare da Huzaif in ya zo wajanta tana neman shafa mata bakin fatti ta tabbata yau nasara take hangowa a idanun Hafsi...
"Kudin da kika dauka ta ce ki bani".
'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
Yaa hayyu ya kayyum'.
Ware idanu tayi sosai tana duban Hafsi da take jin kalaman ta kamar saukar aradu akan ta sosai ta hango tsabar kullin zarge a idanunwanta yarda take yawo da idanuwanta da motsa baki sai ka rantse da Allah gaskiya ne ga hannu data turo mata alamun ta ba ta kudin ji tayi kamar kasa ta tsage ta fada ciki don takaici da bakin ciki sosai taji a jikinta Huzaif na kallonta kallon da ba ta san wani yanayi ya ajje shi ba ta sani kallon wata iri yake yi mata ta sani yanzu haka a zuciyarsa ya yarda da maganar Hafsi da ta zo dashi kuma ta sani yanzu haka kallon tuhuma yake yi mata kuma wacce bata da GASKIYAR RAYUWA cikin duniyarta.
"Hafsi kudi fa ki kace ita Umma din ta ce ki biyo ni ki amshi kudi?".
Mariya ta fadi muryarta na karyewa da wani irin yanayi mai girma da tashi a hankali acikinsa wata irin sarawa taji kanta nayi kamar zai rabe gida biyu a hankali ta kai hannunta ta dafe kan.
'Yaa Allah'.
"Malama ni fa 'yar aike ce ba wai ni nayi gaban kaina ba don haka ko ki bani ko kuma ki fada min abin da zan fada mata don cewa tayi in amso mata kudin ta in ba haka ba kar in sake in dawo domin sai ta bata min rai".
'A'uzubillahi minal shaiɗanin rajim'.
Mariya ta fadi can kasar zuciyarta da ruhi wata irin juw ta ji ta na daukarta tana kokarin dire ta da kasa da sauri ta dubi Hafsi izuwa lokacin idanunta sun tara kwalla sosai take kallon ta da yanayi na baki yi min adalci ba ba ki kyauta min ba.
Amma ita sai faman kau da fuska take yi tana kara tafke ta alamun ba wasa.
"Wai shin me ke faruwa ne?".
Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Huzaif ya na fadin haka 'Yaa Allah' Mariya ta sake fadi ita kadai take jin abin da take ji a zuciyarta sosai take cikin tashin hankali wanda bata taba zaton ƙaddara za ta dauko mata ta kawo mata ba kuma da ta tashi dauko mata sai ta jeho mata Hafsi dauke da makirci ta zo ta dire mata a gaban Huzaif da yake mata kallon mutunci da mutuntawa.
"Kudi ta dauka shi ne aka ce in biyo ta in ansa shi ne fa ta tsaya tana min yawo da hankali bayan kuma ta san ita ce ta dauki kudin".
Muryar Hafsi ta karaɗe kwanyar Mariya da kunnuwanta da karin bayanin da take yi wa Huzaif wanda ta tabbata hakan zai kara mata wani bakin fatti a zuciyarsa.
"Hafsi!!".
Mariya ta fadi da sauti kafun ta dago jajjayan idanuwanta tana mata wani irin kallo na ban kiyi mani adalci ba.
"Mariya".
Taji Muryar Huzaif wani irin yankewa taji gabanta yayi a hankali ta juyo da kallonta zuwa gareshi sosai ta hango kallo wanda ba tayi tsammanin shi za ta gani ba kallo ne na rauni da tausayawa ta hango cikin idanuwamsa sai faman gyaɗa kai yake yi alamun tausayawa.
"wuce ki tafi makarantar ki karki bata lokacin ki".
Abin da taji ya fadi kenan da sauri ta ja jiki ta tafi zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi sosai taji abin da Hafsi tayi mata ya taba mata zuciya ba kadan ba amma abu daya ya sanyata tafiya shine ganin irin kallon da Huzaif yayi mata wanda ba tuhuma ko zarge a cikinsa amma duk da hakan zuciyarta ta yi matukar kaɗuwa da faruwar wannan lamarin a gaban sa da wannan tunanin ta bar layin nasu.
Huzaif da yake kallonta ganin ta kule ya juyo ya dubi Hafsi da tayi masa ƙyar da idanu tana kallonsa kamar wanda ta ga sabuwar halinta a duniyarta.
"anshi ki kai wa Umma din sannan ki ce mata ba Mariya ba ce ta dauki kudin domin an duba ba a gani ba a dai sake duba cikin gidan a in da aka ajje su".
gudar duba ce ya zaro ya mikawa Hafsi a dan kuntace ta ansa ba haka ta so ba ta so ace Huzaif ya ci mutuncin Mariya sosai a gabanta hakan zai fi mata komai farin ciki kwaɓa tayi tana mai juya duba dayar a zuciyar ta ce "raba mugu da makami ibada ne".
Wani kallo ta jefawa Huzaif da wani irin yanayi kafun ta ja kafafuwanta ta koma cikin gida ranta fes ta sani dole zargi ya dalsu ko ya ya ne a zuciyarsa musamman irin kallon da ta ga yana yiwa Mariya da kuma irin muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata magana.
A hankali ya isa motarsa ya buɗe ya shiga yana jin wani irin sarawa da kan sa ke yi kamar zai rabe guda biyu don tsananin kaɗuwa da yayi da abin da ya faru yanzu duk da dai zuciyarsa ba wai ta amshi lamarin bane da gaskiya amma ya ji rashin jin dadi a zuciyarsa.
Da wannan tunanin ya ja motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fal da tunanin Mariya gami da damuwa da yanayin da ya ga ta shiga lokaci guda...
*KAMALA MINNA*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA BIYU.
Sosai da sosai zuciyar Mariya ta taɓu akan abin da Hafsi tayi mata na kulla sharri ba abin da ke kara sanya ta cikin bakin ciki in ta tuna kamar yarda ta tsinka ta a gaban Huzaif wanda sam ba ta so haka ba inda ta san abin da Hafsi za tayi mata kenan da bata tsaya ta saurare ta ba balle ta saka mata CIWON RAI.
Haka ta je makaranta har ta gama zaman ta ba tare da ta fahimci abin da aka koyar da su ba da wannan yanayi aka ta so su ta yo gida gabanta na tsananta bugu ba ta san ya Umma zata karbe ta ba, ba ta san da wata irin fuska zata kalle ta ba in abin da Hafsi tayi mata ya tabbata tabbas zata shiga yanayi mai taba zuciya sosai da sosai tana tsoron fushin Umma gareta sosai take tsoron abin da zai je ya dawo ta sani wannan halin da Hafsi ta jona mata yana cikin abubuwan da Umma ta tsana tsana kuwa mai tsanani domin a kullu yau min in tana yi mata magana akan abin da ta tsana dauke-dauke na sahun farko musamman akan abin da ba naka ba kuma ba tare da sanin mai shi ka dauka ba.
Sosai zuciyarta tayi rauni wasu hawaye masu zafi da taba zuciya da ruhi ta ji suna sauka saman fuskarta sosai take jin zafin su a fatar fuskarta tana jin wani raɗaɗi mai ciwo na bin ko wani sashi na jikinta.
Hannayenta ta saka duk biyun ta na shafe fuskarta ba abin da take ai yana wa a zuciyarta sai.
'Yaa Hayyu Yaa kayyum'.
Fatan ta Allah yasa kar wannan lamarin ya zama gaske domin ita kadai ta san tsananin da za ta shiga ta sani Umma Za tayi fushi da ita fushi mai tsanani ita kuwa ba abin da ta tsana a duniyar rayuwarta kamar Umma tayi fushi da ita sosai hakan ke jefa cikin tashin hankali da rashin natsuwa sosai take jin zuciyar da ruhinta na shiga yanayi na matukar ciwo da zafi gami da raɗadi.
Nisawa tayi akaro na ba adadi kafun ta sanya haɓar hijabin ta ta goge fuskarta sai da ta natsu sosai da sosai bayan ta kirayi sunayen Allah a zuciyar hakan ya rage mata faduwar gaba.
Da Sallama dauke a bakin ta ta shiga cikin gidan wani wawan faduwar gaba taji ya ziyarce ta zaune ta hango su sun kafa da'ira kamar ko yaushe yarda kasan ƙawaye haka suke daukar junansu sam! Goggo Marka bata rike girman ta ba ta tauna lafazi kafun ta furta a gaban Hafsi bata kunyar ta saki baki tayi ta ratata zance ko wani iri ne ya dace ko bai dace ba ita ba ruwanta.
Kasa tayi da kanta tana mai jan numfashi gabanta na cigaba da bugawa fata take yi Allah yasa har ta shige daki ba tare da sun tsinka mata ba domin ta sani in har su kayi magana to ba mai dauke da alheri bane mugun abu za su fadi akan ta ita kuwa ciwon da zuciyarta take yi a yanzu ya isheta ba sai sun dauko wani sun kara mata ba.
"Hehehehe an dai ji kunya wallahi an fita da sunan zuwa makaranta ashe halin bera akayi shiyasa ake ta ɓarin jiki a je a turmushe kudin sai gashi da yake Allah ba azzalumin bayin sa ba ne a gaban saurayi ko nace abokin sheke aya asiri ya tonu".
Sautin muryar Goggo Marka ta doki kunnuwar Mariya da mugayen kalaman da take furtawa wata irin juwa taji ana yi da ita a filin duniyar rayuwarta ji tayi komai na kwance mata komai take ji ya na fadowa kanta da kayan tashin hankali wani bugu taji zuciyarta tayi kamar zata faso kirji ta fito wani makaƙi mai ɗaci gami da ɓauri taji suna yawatawa cikin makoshinta zuwa saman harshenta.
Cak! ta tsaya waje guda tana faman jan numfashi don ji take numfashin na kokarin ficewa gabadaya daga gangar jikinta yake yi a hankali ta fara taka kafafuwanta da take ji suna lauyewa kamar roba suna kokarin watsar da ita.
"wai mu za a nuna wa son addini da tsoron Allah bayan ko an fita ba can wajan neman ilmin ake yi ba sa dai yawon ta zubar".
muryar Goggo Marka ta sake fadin haka kafun Hafsi ita ma ta caɓe.
"rungume da juna fa na tadda su cikin mota yana faman laguda ta ita kuwa sai faman yashe mssa baki take yi".
'A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim'
Zuciyar Mariya ta shiga ambata tashin hankalin da take ciki ta ji yana daɗuwa komai taji yana juya mata kanta da gangar jikin ta sai majajjawa suke yi da ita cikin wannan yanayi ta ja jiki kanta rike a hannayenta wanda take jin sa kamar zai tarwatse saboda tsabar daukar zafi da taji yayi.
Shigar ta dakin ke da wuya ta zube tsakar dakin wani kuka ne mai ɗaci a zuciya taji ya kufce mata sai dai ba hawaye kukan zuciya ne kawai wanda ke kokarin yayyaga mata ko wani fili da zuciyarta da kirjinta HAWAYEN ZUCIYA da take jin suna zuba kamar za su kashe mata zuciya da ruhi.
Girgiza kai kawai take faman yi jin lamarin take kamar ba gaske ba jin komai take kamar a duniyar mafarkinta jin komai take yi kamar duk kuncin duniya akanta a sauke mata a duk sassan jikinta wani fili taji a zuciyarta yana kamawa da wuta ya na babbakewa lokaci guda.
Lokaci mai girma ta shafe cikin wannan yanayin kafun zuciyarta ta sarara mata dalilin ambaton sunan Allah da take faman yi cikin wani irin yanayi mai girma da tashin hankali a cikin sa sosai idanuwanta suka sauya kala kamar wacce akayi wa hayaki da barkono mai tsananin zafi.
A hankali ta dago kanta tana yawatawa da idanuwanta cikin dakin gabanta na tsananta faduwa sake ware idanu tayi ganin ba Umma a cikin dakin da sauri ta zabura ta mike tana kara buɗe idanuwanta sosai kafun ta furta
'Yaa Rabbi'.
Laɓɓanta na rawa cikin yanayi na firgata ganin Umma bata cikin dakin hakan ba karamin fadar mata da gaba yayi ba da sauri ta yo waje tana yawatawa da idanuwanta tsakar gidan ba ta ga kowa ba da sauri tayi hanyar bandakin su mai dauke da langa-langa ta shiga kwalawa Umma kira amma ina babu ita babu dalilinta hakan ya sanyata sauri karawasa cikin bandakin ba kowa a ciki da sauri ta yo waje tana duban su Hafsi so take yi ta tambaye su amma tana tsoro ta san dole sun fadi kalma mara dadi ko da kuwa za su bata amsar in da Ummanta tayi ita dai ta san Ummanta ba ma'abociya fita ba ce domin za ta iya tunawa tun da suƙa dawo daga asibiti tsayin wannan lokaci Umma ko kofar gida ba ta leka ba dole hankalin ta ya tashi tana tsoron Abin da zai je ya dawo.
Zuciyarta taji tana sanar da ita kawai ta tambayesu kar ta tsorata da abin da za su ce da ita wanda zai bata mata rai domin ko mai su kayi mata baya yake da ace bata ga Umma ba da wannan shawarar tayi amfani ta dago rinannun idanuwanta ta na saukewa akan su kafun ta shiga motsa laɓɓanta gabanta na wani iri bugu mai girma gareta.
"Uhmm...Goggo don Allah Umma ta ina ta je...?".
Muryarta da rawa a ciki duk kalmar da za ta fadi a dandatse take ajje ta.
Duban shekeke sukayi mata su duka kafun Hafsi ta saki shewa suna tafawa tare da Goggo Marka.
"mu kika ba ajjiyar ta da za ki zo kina tambayar mu ki fita mana ai gari da yawa maye baya cin kan sa itama ta fice yawon ta kamar yarda ke ma ki fic...".
"Hafsi!!!".
Mariya ta buɗe muryarta sosai ta ambaci sunan da wani irin bacin rai mai girma dubanta take cikin yanayi na gargaɗi da karki sake tafka irin wannan kuskuren sosai bacin rai ya wadatu a cikin muryarta hannu ta daga tana nuna Hafsi wacce muryar Mariya ita ce ta sanya ta tsaida da maganar take yi domin sosai taji faduwar gaba ganin yanayin da Mariya ta nuna.
"Hafsi ya kamata ki san irin maganganun da za ki dinga fadi a kan Umma ta komai za kiyi ko wani irin cin kashi zaki yi ya kamata ki sauke a kaina ba wai sai kin sako Umma ta ba".
Ta karashe da gargaɗi mai girma muryarta.
Tana gama fadin haka tayi hanyar waje cikin yanayi da zafin zuciya da raɗaɗi a kasan ruhi.
Duk kan su sakin baki sukayi suna duban juna kafun Goggo tayi kwaɓa tana girgiza kai gami da cizon yatsa.
"ji tsinanniya mai kalar muciya da zani aiko zata ci dangin uwarta bari ta dawo ita da uwar ta ta mai shegen kalan dangin tsiya da shisshigi gami da kwala kai a faranti in ban da haka uban meye hadinta da gidan kultum daga 'yarta ta haihuwa shine ta kwashi jiki zuwa barka za su zo su tadda ni sai sun ga ne shayi ruwa ne ba komai ba ".
*******
"Alkawari nayi maka Alhaji Abdulwahaab don haka ka saka zuciyarka cikin ruwan sanyi kamar kayi amarya ta mutu A DAREN FARKO".
Areefa ta karashe tana mai kai glass cup da ke zaune a tsakar hannunta mai dauke da tataccen lemon kankana da ya sha kayan hadi sai tashin kamshi yake yi da rangwamin sanyi idanuwanta take juyawa akan Alhaji Abdulwahaab dake zaune yana dubanta da wani irin yanayi mai girma kafun ya saki wani shu'umin murmushi yana gyaɗa kai bayan ya kurbi lemon da ke hannunsa.
"Ba ki da dama Areefa. Na sani za ki iya yin koma me nene don ganin cin ma burin ki dama nawa amma kuma ya kamata ki sani Dr.Erena ba saukin kamuwa yake a hannu ba ya kama ta ki san wannan karki yi saurin sakin jiki dashi domin ba karamin NAMIJIN DUNIYA bane da kike ganin sa nan ba ko wacce mace ba ne take samun abin da take so game dashi ya san hannunsa sosai da sosai don haka sai kin yi shiri sosai kafun ki aikata komai karki ga lokaci guda yana rawar jiki akan ki kiyi zaton tarkon ki ya kama miki giwa to wallahi a,a ni nasan halin sa ni zan fada miki waye Dr.Erena ni zan fada miki irin shu'umancin sa".
Murmushi a fuskarta take kallon sa dashi sosai take raina maganar ta sa a ranta har yanzu ta lura bai san wacece Areefa ba bai san salon hannnun na taba zata ba shi mamaki za ta nuna masa sabon jini da tsohon jini akwai bambanci a tsakanin su ba kadan ba za ta nuna masa zamanin Dr.Erena gaf! yake da shuɗewa ko ma tace ya shuɗe yanzu kuwa zamanin ta ne ita ce dashi dole kuma tayi amfani da damar ta sannan kuma ta nuna wa Dr.Erena har da shi Alhaji Abdulwahaab din wacece mace za ta nuna masa zamanin da Dr.Erena yayi rayuwarsa bai samu mata irinta ba a duniyar rayuwar tasa dole duk su biyun ta ba su mamaki za su san wacece Areefa.
"Ban san da me zan sanar da kai wacece ni ba amma dai zan barka da lokaci shine zai mana Alkalanci a tsakanin ni da kai kawai kai dai ka zuba ido kayi kallon wannan GAME din da za a buga".
Ta karashe tana kara sakin wani shu'umin murmushi wanda daka kalle shi zaka san akwai tarko mai girma da aka ɗana cikin sa kafun a sake shi.
Gyaɗa kai yake yi yana yawatawa idanuwansa a nata ba tare da fargaban komai ba sosai da sosai ya hango tsantsar rashin tsoro ko SHAKKA cikin idanuwanta sosai da sosai ya hango gaskiyar kalaman da suke fitowa daga bakinta amma duk da hakan bai gasgata ba domin shi ya san Dr.Erena kuma ya san wanene shi a cikin wannan harkar dole Areefa tayi taka tsantsan domin wannan wasan da take ganin shan ruwa ya fishi wahala to tabbas zai iya juyewa a ko wacce dakika ba tare da ta fargaba ya zame mata katon aiki mafi girma da wahala a filin rayuwarta.
"Ba wai ina raina yanayin ki ba ne a,a ko daya ina dai so na sanar dake wanene Dr.Erena...".
"Ya isa haka!".
Areefa tayi saurin tare shi cikin kakkausar muryar kafun ta mike kan kafafunta ta fara taku a hankali tana mai gyaɗa kan ta juyowa tayi a hankali ta dube shi bayan ta tsaya cak! da takun da take yi.
"Me yasa zakayi mani haka mai yasa ba zaka barni na karanci wanene Dr.Erena AKARAN KAINA ba mai yasa kake son ka cusawa zuciyata shakka ko wani fargaba akan sa bana zaton wannan zuzutawa da kambawa da kake yi masa zai samu muhalli a zuciya ta ba na tunanin yarda zuciyarka ke shakka a kan sa nima ta wa za tayi haka zuciya ta da taka suna da bambanci sosai da sosai don haka ka kula".
Ajje Cup din da ke hannun ta tayi kan table din dake gaban su ta sanya hannu ta dauki jakar ta da mukullin motarta bayan ta watsa masa wani kallo na gargaɗi ta fara taka kafafuwanta domin fita daga cikin Office din ranta a jagule domin kuwa sosai taji raini a maganar Alhaji Abdulwahaab sosai ta hango ya raina ta ya raina yanayin ta amma ba komi zata ba shi mamaki wanda zai jima yana taba masa zuciya da ruhi.
"Areefa!".
Ya fadi yana mikewa kan kafafuwansa a hankali ya fara takawa domin isa wajanta tsaye take rike da Handle din kofar tana faman jujjuyashi.
"Ban san mai yasa kika fiye daukar zafi akan abin da bai taka kara ya karya ba, Ban san wacce irin zuciya gareshi ki wacce take saurin daukar abu da girma ko da kuwa bai kai a dauke shi din ba".
A hankali ta juyo tana sauke idanuwanta cikin nashi kafun taja numfashi tana gyara zaman glass din da ta daura a fuskarta a wannan lokaci mai taken 'No respect' wanda yayi matukar karawa fuskar ta ta kwarjini da kyau sosai.
"A rayuwa na tsani a raina kwazo na ko ya ya ne shiyasa nake so mutum ya rike duk wasu kalaman sa akai na har ya ga in da zan tsaya da kwazon nawa sai ya bashi Mark daidai dashi".
Yanayin da take ajje kalamanta da dakewa a ciki ya sanya shi kara gasgata ta akan kwazon nata da take kambawa amma kuma ba wai fadi a baki ba a,a gani a aika ce shine sahihin aiki inji kare yace 'mu gani a kasa' ana biki a gidan su.
Shirun da taji yayi ne ba tare da ya ce komai ba ya sanya ta nisawa domin har yanzu ta lura akwai kokwanto a zuciyarsa murmushi tayi kafun ta juya tana murɗa Handle din tana fadin.
"Uhmmm...kar fa ka saka zuciyarka cikin tunanin lamari na kawai ajje shi gefe ka yi kallo kawai kamar yarda na fadi maka a baya".
Tana gama fadin haka ta sake sakar masa murmushi tana ficewa daga Office din da hanzari.
Sosai yake murmushi shima yana kallon yanayin Areefa da yanayin da take kokarin ya yarda da maganarta zai iya yarda sai sai wani sashi na zuciyarsa yana tuno masa da Dr.Erena yana hango wanene shi a duniyar filin rayuwarsa da irin gamzuwa da yake yi da mutane yana zubda su sosai yake samun nasara kafun a samu kan sa wanda ya tabbatar wannan a jinin sa yake.
Juyawa yayi ya koma tsakar Office din yana safah da marwa hannayensa harɗe a bayan sa.
*****
April 2000.
Sosai garin ya haɗe da wani irin haɗari mai matukar razanar wa wanda a ko wani lokaci zai iya zubda ruwa mai karfi gaske gami da iska.
Dr.Erena tsaye bakin kofar dakin wani hotel dake tsakanin Abuja da Suleja kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da akwai abin da ke damun sa a ransa sosai da sosai bi sa yanayin da fuskarsa ta nuna na tsananin bacin rai.
"Mr. Ekele na lura har yanzu ba ka san wanene ni ba a fadin duniyar nan har kake tunanin yaudarata ka hada baki da wasu wajan cuta ta".
Wani murmushi ya ajje a fuskarsa yana kai hannunsa zuwa haɓarsa dake cike da suma kamar wanda yayi shekara ashirin bai bi ta kan ta ba.
Mr.Ekele da ke tsaye sai faman rarraba idanuwansa yake yi a tsakanin na Dr.Erena ya shiga sharce gumin da ke tsatsafo masa a ko ina na kofar gashin dake jikin sa na fuskarsa yake saukewa duk da iskar ake yi a wannan lokacin bakin sa na rawa cikin gurbatacciyar hausar sa ya shiga magana.
"aleji ke yi hakuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba na rantse miki".
Wani wawan kallo Dr.Erena ya watsa masa kafun ya dungule hannu kamar zai sakar masa naushi a fuska hakan da Mr.Ekele ya gani ya sanya shi ja da baya yana kiran.
'Jesus'.
Bakin sa na ɓari jikin sa sai karkarwa yake yi kamar wanda aka jonawa wayar wuta.
"Get out now!".
Muryar Dr.Erena ta karaɗe wajan da amo mai zurfi da bacin rai a cikinsa.
wata irin zabura yayi har yana kokarin haduwa da bango da sauri ya juya duk da hakan bai hanashi haɗe hannayensa waje daya yana bashi hakuri ba cikin tsananin tashin hankali.
Fitar Mr. Ekele ke da wuya Dr.Erena ya juya cikin dakin sa da sauri fuskarsa kunshe da bakin ciki da bacin rai mai tsanani ga kuma wani murmushi da ya dauko yake ajje a fuskar tashi gefen gadon ya zauna yana mai janyo na'urar sadarwa ta waccan zamanin talfon a hankali ya ja abin sanya wa a kunne ya na mai kai dayan hannun nasa zuwa madannan jikin talfon din dakikun kadan a ka daga cikin yanayi na umarni da nuna isa akan wanda ake waya dashi ya fara magana.
"Yanzu nan nake so ku isa titin da zai shigar da ku Abuja Mr.Ekele nan akan hanya ina so cikin mintina goma ya bar filin duniyar nan bana so ko gawarsa a gani balle a shaida shi da cewa ya bar duniyar nan".
Yana gama fadin haka kamar da minti daya ya sauke wayar yana faman sakin wani murmushi mai razanar da wanda ya gani kafun ya saki wata mahaukaciyar dariya yana mai bajewa gabadaya kan gadon.
Gudu yake yi cikin motarsa zuciyarsa sai faman tsalle-tsalle take da tashin hankali mai girma a wannan lokacin kuma a ka saki wani ruwa mai karfi da iska ga tsawa da ake ta kwaɗawa gabadaya Mr.Ekele ya gama tafiya cikin duniyar tashin hankali jikin sa faman karkawa yake yi ga wani gumi dake karyo masa duk da feshin ruwan da dake shigowa ta cikin glass din motar da bai rufe duka ba.
Zuciyarta ba abin da take zaryar dauko masa sai a rangamar su da Dr.Erena ya sani sosai zai shiga cikin matsala tun da har ya san da hannunsa cikin wannan yaudarar da aka shirya yi masa duk da dai shi akaran kan sa ba a son ran sa wannan lamarin ya afku ba takura masa akayi ba yarda ya iya ga shi yanzu ya shiga hali wanda Allah kadai ne zai iya fiddo shi daga hannun wannan mutumin mara imani da tausayin a zuciyarsa ya sani sai wani ikon Allah zai bar shi ya cigaba da rayuwa a duniyar nan ya sani koma ya cigaba da rayuwa to lokaci kalilan ne zai yi ko da kuwa be bar duniyar ba to tabbas zai shiga halin ƙaƙani kayi...
Wani iri bugu yaji an yiwa bayan motarsa wanda sanadiyyar haka sai da ta tuntsiya ta shiga katantanwa a tsakiyar titi ga ruwa da ake ta mamakawa dakiku masu yawa ta dauka tana katantanwa kafun ta tsaya waje guda bayan ta dawo daidai gabadaya glass din jikin motar su yi kwatsa-kwatsa ita kanta motar duk ta gama molewa Mr.Ekele da ya gama rikicewa gabadaya kansa da fuskarsa jini ne sosai gabansa sai bugawa yake yi da sauri sauri a hankali ya fara kokarin tayar da motar don ya gama tabbatar wa kansa ba wanda zai yi masa wannan aikin sai Dr.Erena tuni ya tabbatar wa kan sa ba zai bar shi da numfashi a doron duniyar nan ba key ya shiga juya a mazauninsa cikin iko na Allah motar ta dau wuta ganin ta tashi yayi mata birki gami da fizgarta kamar daga sama yana yin gaba yaji ya doku da katon abu wanda ya sanya motar sake wuntsulawa baya can bayar ma karo ya sake yi da wani abu mai girman gaske kafun motar tayi sama ta dawo kasa lokaci guda.
Izuwa wannan lokaci ya gama fita daga hayyacin sa ba abin da yake ambata sai 'jesus' ya ce ce shi daga wannan halin da yake ciki na tashin hankali.
A hankali yaji a na bugun motar tasa kamar daga sama lokaci guda ya ji an balle murfin wani irin haske ya ga an dalle masa idanuwa dashi wanda hakan ya karasa rufe masa ganin nasa da jini ya wanzu a fuskar sa gabansa ne ya cigaba da faduwa yana ji ya na gani aka fizgo shi waje aka watsar tsakiyar titi kamar wani kayan wanki sosai ya bugu a bayansa wanda hakan ya sanya shi sakin kara mai sauti bai kai ga dire karar ta sa ba yaji an kwaɗa masa wani abu mai girma a tsakar kai wanda hakan ya kara sanya shi bajewa a tsakiyar titi yana mai sakin numfashi wahalalle wata tsawa kayi mai dan karan haske hakan ya baiwa Mr.Ekele damar ganin mutanan dake tsaye akansa gabza gabza har su biyar ko wanne rike da mugun makami a hannunsa hakan ya kara tsinkar masa da gaba ya sadakar shi tashi ta kare a filin duniyar nan a hankali ya mai da kansa ya langwaɓar jira kawai yake yi yaji saukar wani makamin wanda zai tafi masa da rai daga gangar jikinsa.
"Kai dan uban baban ka shine don ka raina wa oga sense shine zakayi masa eya ne ko to yau zaka bar duniyar nan dan kundun uba jikan oduduwa mai katon ciki".
muryar dake wannan zantukar kadai in ka saurara zaka gane tsantsar rashin imani da tausayi daga ji kuma zaka gane ma'aboci zuke-zuke ne zauna gari banza da ake amfani da su wajan cutar da jama'a da ba su ji ba su gani ba.
"Bobby kawai yi masa eya ne kamar yarda ya yi wa Oga shi ya yaji inda dadi".
Wata muryar ce ta daban ta sake fadin haka.
A wahale Mr.Ekele ya motsa yana mai sakin numfashi mai tsananin ciwo.
"ki taimake ni kin ji karki kashe ni zan baki duk abin da kike so Allah...".
Wani bugun bazata yaji ya saukar masa a baki wanda ya sanya shi zubewa a kasa yana kiran jesus ya cece shi za su kashe shi.
Wata irin shaka ya ji anyi wa wuyansa kafun lokaci guda a durkusar dashi a dage masa kai yana ji yana gani aka daura masa wata irin sharɓebiyar wuka wanda walwalin ta ke haske duhun daren da suke ciki kafun yayi wani yinkuri tuni an sauke kan sa a kasa yabi titi yana ta tintsirawa yana tsartuwar jini gangar jikin kuwa nan suka yi cilli da ita kafun daga bisa suka dauke ta sukayi cikin motar shi da ita suka banka masa wuta lokaci daya kamar an kunna wutar auduga haka ta kama ranga ranga.
A hankali suka shiga motocin su fuskar su na bayyanar da tsantsar murna da farincikin samun damar cika wannan aikin domin sun tabbata da ba su samu wannar sa'ar ba Allah kadai ya san abin da Dr.Erena zai musu domin sun lura sosai Mr.Ekele ya bata masa rai wanda ya kasa boyewa har sai da ya fiddo a muryarsa suka fahimta kuma yayi musu gargaɗin kar su sake a samu akasi akan aikin nan sannan ga kudin da ya saka musu masu auki wanda tun da suke yi masa aiki bai taba basu kudi haka ba.
*****
"Yaa Allah! Dr.Erena kasan me ke faruwa kuwa yanzun nan muna kan hanyarmu ta dawo wa daga Abuja mu kayi kaci ɓus da wani abun tashin hankali Mutumin ka Mr.Ekele an kashe shi an kona gawarsa har da motarsa sai dai kuma kansa da aka yanke kafun a ko ne shi shine yasa muka gane shi ne".
Numfashi mai karfi yaja kafun ya saki Murmushi mai cike da mugunta har sai da Alhaji Abdulwahaab yaji sautin.
"Ni na sanya aka kashe shi?".
"What! kai fa kace akan mi?".
"wannan ba damuwar ka bace abin da kake bukata na fadi maka don haka ka rabu dani kawai a wuce wajan domin ni har na manta da wani mai irin wannan sunan a filin duniyar nan".
"Yaa Salam! Me ya sa kayi haka Dr.Karami haka sam bai dace ba Mr.Ekele komai yayi maka bai dace ace ka sanya anyi masa wannan mugun aikin b...".
"Ya kamata ka kiyaye lafazun ka Alhaji Abdulwahaab na rantse da Allah ko kai ne kayi mani abin da Waccen mataccen yayi mani sai na sanya a kau da min da kai a filin duniyar nan wallahi don haka ka kiyaye lafazinka".
"Dr.Erena ni ka ke wa ikirari haka Allah ya baka hakuri ban san lamarin zai taba maka zuciya har haka ba".
"Da dai yafi haka wallahi don haka mu yi wani batun na daban in kana dashi in kuma babu mu sauke wayar".
Murmushi Alhaji Abdulwahaab ya saki mai zafin gaske kafun ya nisa.
"Ni ba ni da wani abin cewa dama akan waccan maganar ce kuma kace ba ka so komai ya wuce".
Bai jira cewarsa ba ya sauke wayar yana mai mamakin Dr.Erena da irin rayuwar da yake yi wa kansa tanaji ko da yake bai kamata ya zauna tunanin sa har haka ba tun da shi ma akwai tasu a tsakaninsu....
Nisawa Alhaji Abdulwahaab ya yi sosai lokaci guda gumi ya karyo masa duk da sanyin A-c dake busawa cikin Office din tausayin Areefa yake yi akan yarda lokaci guda ta daukar wa kanta wannan aikin mai cike da hatsari da tarin kalubale shi kansa tsoron Dr.Erena yake yi kuma yana tsoron ranar da zai san yana bibiyarsa ya san tabbas shima wani abu zai faru dashi sai dai zai wa kansa Alkawarin ajje duk wani fargaba da tsoro akan Dr.Erena ya fuskance shi ya marawa Areefa baya domin ganin sun cin ma abin da suke bukata akan sa sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa duk lokacin da ya tuno da kunci da bakin cikin da Dr.Erena ya cusa masa a zuciya dama filin duniyar rayuwarsa gabadaya.
*KAMALA MINNA*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA UKU.
Sosai take jin maganganun Alhaji Abdulwahaab na mata kuwwa a kunne ta rasa mai yasa haka, ta rasa mai yasa zuciyarta take koƙarin dauko mata abin da bata shirya tarbarsa ba, kokari take ta kau da komai a zuciyarta wanda sam bata muradin ace sun shigo har suna ƙoƙarin sanyata wani hali Dr.Erena mutum ne da ya kama ace ta ajje komai nata ta fuskance shi sosai da sosai sannan duk wata fargaba ko SHAKKA gami da tsoro ya dace ma ace babu su a filin rayuwarta.
Nisawa tayi tana mai jan numfashi mai zafi tana fesawar wasu lamura ne masu matukar tasiri a rayuwarta taji suna dawo mata kamar yanzu ne suke fado duniyarta ji take yi kamar yanzu ƙaddara ta hadata da Dr.Erena komai taji ya sanko mata lokaci guda a zuciyart da sauri ta ja burki a gefen titi tana mai hada kanta da sitiyari zuciyarta taji tana wani lugudan bugu wasu hawaye masu tsananin zafi da kokarin yayyaga zuciya suka shiga zubo mata...
*******
*JANUARY 2004.*
*KADUNA GIDAN MARAYU.*
"Alhaji Mati ba wai ban yarda da kai ba ne, kawai dai ka san sha'ani na rayuwar a wannan zamanin sosai yara irin wadannan suke shiga kuncin rayuwa a hannun wanda suke daukar su anyi ba sau daya ba, ba sau biyu ba a nan gidan shiyasa kaga gabadaya yanzu ba ma yarda da mutane sam! da suke zuwa daukar marayu da sunan rike su wasun su da yawa ba saboda Allah suke daukar su ba su da tasu manufar akan marayun da suka dauka...".
Nisawa yayi yana kara gyara glass din fuskarsa kafun ya dubi Alhaji Mati da yayi masa kuri da idanu yana dubansa kamar zai cinye shi danye sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa sosai da sosai yake jin zuciyarsa na wani irin zugi ji yake yi kamar ya tashi ya makure wannan mutumin da yake kokarin yi masa sakiyar da ba ruwa ba zai yarda ba da wannan gangancin ba ba zai lamunci wannan haukar da wannan mutumin ke kokarin yi masa ba.
Nisawa yayi yana kokarin boye bacin ran dake kokarin bayyana kansa a fuskarsa wani shu'umin murmushi ya kalato ya sauke kafun ya kau da kai yana hirji kasa-kasa.
"a zamanin nan da muke ciki da yawa marayun da ake dauka suke shiga gararin rayuwa suke shiga tashin hankali sai mutane su zo da sunan ba su da 'ya'ya Allah bai basu haihuwa ba a taimaka a ba su za su rike tamkar 'ya'yan cikin su amma daga baya bayan sun samu cikar burin su sai su canza alkibla akan 'ya'yan da aka ba su da KUDIRI da sukayi niyya a zuciyarsu ba zan boye maka ba Alhaji Mati ka ganni nan nayi kuka da idona da girmana da kake gani a haka akan tashi hankalin da marayu suke shiga a hannun masu daukar su da sunan riko ban san adadin yawan marayun da suka bata ba ban san adadin marayun da aka bata wa rayuwa ba ban san adadin marayun da aka ciwa zarafi ba ban san adadin marayu mata da aka KETA HADDI a garesu ba haka ma mazan su ma ba a bar su ba...".
Shiru yayi yana jan numfashi zuciyar na wani irin bugawa ransa na kara ɓaci a hankali ya ja glass din idanunsa ya dauke wasu kwalla da suka tarun masa kafun ya sake nisawa yana duban Alhaji Mati da izuwa wannan lokaci ya kosa da dogon sharrin da yake yi masa wanda shi dai a karan kansa ba abin da suke yi masa domin bi sukeyi ta bayan kunnan sa suna wuce wa ba abin da ya kawo shi kenan a zaunar dashi ana karanta masa halin marayu ba shi zuwa yayi a bashi abin da yake bukata ko nawa ne zai biya a zuciyarsa ba wai marayu ya zo dauka ba siyar maraya ya zo yi da kudin sa domin bukatarsa ce ta taso a filin duniyar rayuwarsa.
"MARAYU MA 'YA'YA kamar ko wani ɗa a filin duniyar nan suna da gata da galihu gami da 'yanci a rayuwarsu kawai dai har yanzu ba a san wanene maraya ba duk marayu da ka ga ana ajje su a wannan gidan to in ka bincika ba su da laifin ko miskala zarratin a filin duniyar su da yawan su haihuwar su ake ana yasar da su a titi ba tare da sun sani ba da yawan su iyayen su da suka haife su ba wai ta hanyar sunna bace ake samun su ya kamata a daina ganin laifin marayu ba su suka halicci kan su ba haka ƙaddarar su ce ta zo a hakan in da suna da iko wallahi ba yarda za ayi su bar iyayensu su haife su ta wannan gurbatacciyar hanyar...abin takaici yawan mutanan mu ba sa duba ga hakan kawai yankewa maraya hukunci suke yi da bahagon tunani ya kamata ace an daina ganin laifin maraya maraya rauni gareshi maraya mai bukata ne a filin duniyarsa maraya shima ɗa ne kamar ko wani ɗa a filin duniyar nan...".
Nisawa yayi muryarsa a lokacin ta kara rauni.
"...don Allah Alhaji Mati ka dubi girman Allah da Annabi kayi mani alkawari ba zaka zamo daya daga cikin mutane da masu cin zarafin marayu ba...".
"Ba sai ka roke ni ba Uban Marayu".
Alhaji Mati ya fadi da murmushi kwance a fuskarsa kafun ya cigaba da cewa.
"Bana cikin irin wadannan mutanan masu tauye hakki har haka ka yarda dani Alkawari nayi maka ba zaka samu matsala dani ba domin nasan darajar maraya domin nima na ɗanɗani irin rayuwar tasa kuma ban ji dadi ba ka ga kuwa ba yarda za ayi ace na so wani dan uwa nawa ya shiga irin wannan halin".
Ya karashe da yanayin rauni a fuskarsa.
"Naji dadin haka sosai da sosai Allah yayi mana jagora".
Bai amsa ba illa yatsine fuska da yayi cikin yanayi kamar akwai abin da ke damun sa yana mai duban yarinyar dake zaune can gefe da su ta takure waje daya a shekarun ta ba za su hau goma zuwa sha daya ba fara ce tas! kamar shuwa bata da jiki sosai kallo daya zakayi mata ka gane irin matan nan ne ma su tsayi da kirar jiki.
Duban ta sosai Alhaji Mati yayi zuciyarsa na wani irin zullon farin ciki KUDIRI da burinsa gaf! suke da cika komai na duniyarsa ya kusan zamar masa sabo filin a leda.
Takardun da yaji Uban Marayu ya turo masa gabansa ne ya tsinke masa tunanin da yake yi cikin yanayi na son abin da aka turo masa ya dauki takardun yana yawatawa da idanuwansa kan su yana mai sakin wani Shu'umin murmushi.
Takardu ne na yarjejiniyar da sukayi a tsakaninsu zuwan sa na farko da suka je kotu komai da komai gashi nan a rubuce har da sanya hannun lauya da shi uban marayun.
Duban sa yayi kafun ya numfasa.
"Uban marayu na ga komai kuma hakan yayi daidai sosai da sosai"
ya fadi yana mai dauko Biro yana sanya hannu a wajan da Uban Marayun ya nuna masa da hannunsa.
"Godiya muke sosai Uban Marayu".
Alhaji Mati ya sake fadi yaka mai mika masa hannu suna gaisawa duk kan su da murmushi a saman fuskarsu.
Matar da take gefen sa zaune ya duba yana murmushi.
"Hajiya kiyi masa godiya ta tabbata yau dai mun samu 'ya".
Tsukankiyar matar mai kama da muciya da zani fuskar nan ta ta tasha mai sai kyalli take da wani kala-kala kallo daya zakayi mata ka kau da kan ka.
Yak'e ta saki tana mai washe hakoranta da suka gama dafewa da dattin hayakin sigari godiya tayi kamar bata so ba kafun ta mike tana sabar jakarta.
Dama tuntuni sunyi komai da komai jira kawai suke su samu damar tafiya daga wajan Uban Marayu.
"Khairiyya shikenan kuma kin bar mu kin ga yanzu ga iyayenki nan da za ki koma wajan su da zama ina yi miki fatan alheri a rayuwa".
Khairiyya dake kwakumi da jikinta da sauri ta dago idanunta da suka ci taf! da hawaye tana dubansa sosai yaji ta bashi tausayi a ransa kau da kai yayi don ya san tabbas in ya cigaba da kallon ta shima hawaye zai yi gaban sa yake ji yana bugawa amma bai kawo komai a kai ba kawai tunanin sa kamar yarda ya saba rabuwa da marayu cikin damuwa yau ma haka ne yake ji dalilin rabuwa da Khairiyya.
Kuka sosai take yi har suka fito daga cikin gidan bayan sun yi BANKWANA da yan uwanta sai kuka suke yi suma tana ji tana ga aka sakata cikin motar Alhaji Mati cikin yan mintina kalilan suka bar harabar gidan kallon gidan take yi tana ji a ranta ba za ta sake dawowa ba kallon gidan take yi kallo na karshe a filin rayuwarta tana ji a ranta bazata sake zuwa cikin gidan nan ba in ba wani iko na Allah ba sosai take ji gabanta na faduwa duk lokacin da ta kalli Alhaji Mati ko kuma taji amon muryarsa mai razana ta.
Tafiya mai nisa sukayi tun tana hango gidaje har suka fara shiga dazuka masu bishiyoyi kala daban-daban izuwa nan lokaci ta tsaigaita da kukan da take sai jan numfashi take tana ajiyar zuciya.
Awanni Hudu sukayi a hanya kafun su iso cikin Garin Sulaje suna kokarin shiga cikin gari Alhaji Mati yayi parking gefen titi yana duban matar dake gefensa zaune murmushi yake saki mai dauke da mugunta a ciki.
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki".
Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba.
"Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan".
Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa.
Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati.
"batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata".
Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su.
"Hajiya Layla"
Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora.
"...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe".
yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta.
Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.
tafiya yayi mai dan tsayi mai makon ya shiga gari kawai sai ya ratse ya yanki daji hakan da Khairiyya ta gani ya dan tsoro ta ta ware idanu tayi tana duban hanyar da suke shiga daji sosai da sosai tun suna hango gidaje har suka daina sai bishiyoyi kala kala can nesa kadan ta hango wani gida shi kadai kwallin kwal! a tsakar daji ba ka jin kukan komai sai na tsintsaye da sauran halittun daji gida dan madaidaici ne anyi masa farin fenti gabadayansa haka kwanon rufin ma fari ne aka saka. A hankali Alhaji Mati ya isa kofar gidan yayi Parking ita dai Khairiyya gabanta sai faduwa yake yi ta saki baki tana kallon gidan tana jin sa lokacin da ya buɗe kofar ya fita kafun taji amon muryarsa akanta a dan razane ta dube shi kafun tayi kasa da kai gabanta na tsanan ta faduwa a hankali ta fara kokarin fito bayan ya bude mata kofa ya turke a gefe gyara zaman babbar rigarsa yake yi kamar wani sabon ango gefen sa ta ratsa ta tsaya hannunta harɗe waje guda a kirjinta.
"Muje ko".
Ya fadi yana kamo hannunta wani irin razana tayi idanuwanta sukayo waje gabadaya jikinta ya shiga rawa kamar wacce wayar wuta ta kama.
Bai damu da yanayin da ya ga ta shiga ba haka ya ja ta har zuwa kofar gidan ba tare da wani shamaki ba ya turo kofar ya shiga ba kowa a tsakar gidan sai fili kawai da aka malale da sumunti kallo daya zakayi wa gidan ka gane ya na samun gyara sosai da sosai duk girma gidan da fadinsa daki daya ne jal! sai can gefe kuma wani dan karamin daki ne wanda kallo daya zakayi masa ka gane makewayi ne.
"Dr.Erena da kan sa".
Kamar daga sama suka ji muryar ta amsa amo a filin gidan baki daya da sauri Khairiyya ta shiga dube dube don ganin daga in da muryar take amma bata ga kowa ba tana cikin wannan halin taji Alhaji Mati ya ja hannunta sun nufi dakin nan guda daya ta so ta tirje amma sai ya sa mata karfi ya shigar da ita dakin zaune su ka tadda shi babban mutum ne wanda a kalla zai baiwa shekaru hamsin baya sanye yake da riga da malum-malum farare tas sai rawa ni shima na farin kyalle ne duk dakin haka aka kawata shi da farin abubuwa dangin su kwarya da su casbaha da sauran su gabansa kuma in da yake zaune wani faskeken faranti ne shima fari ne an cika shi da yashi mai laushi sosai gefe da gefen faranti din goran duba ne cike da wani farin ruwa mai daukar ido sosai da sosai.
"Ita ce wannan?".
Mutumin ya fadi yana mai kallon Khairiyya da wata irin siga kafun ya sake duban Alhaji Mati da shima yake ta faman yashe baki burin sa ya kusan cika wannan karon Malamin sa ko mu ce boka bai katse masa hanzari ba.
"Irin wadannan ake so masu kyau da tsari sosai wanda kai a karan kanka sai kaji komai daidai amma da kaje kana kwaso yaku bayi ina aiki zai yiwu kasan komai yan son MAI ƘYAU domin har kace za ayi ta arziki da kyau kuma".
Shi dai Alhaji Mati sai zabga murmushi yake yi kamar ango a daren farko hankalin sa gabadaya ya koma kan Khairiyya da jikin ta ya fara rawa jin kalaman da suke fadi akan ta ko ba a fadi mata ba tabbas akwai abin da ake kokarin yi akanta.
Wani Alkalami ya dauko wanda aka shafe jikinsa gabadaya da farin wani abu amma daga kansa in da aka yi don dangwalo tawada bakinkirin ne sosai.
Nuna Khairiyya ya shiga yi da shi kafun ya dubi Alhaji Mati yana mai saka laɓɓansa duka cikin bakinsa yana tsotsawa kamar wanda ya samu alawa.
"Zan yi mata wani aiki yanzu ina bukatar kadaicewa ni da ita".
Ya fadi da wani murmushi a fuskarsa sosai Alhaji Mati ya shiga gyaɗa kai yana faman sakin yak'e haka da Malamin ya gani ya sanya shi mikewa da wani zabgegen carbi a hannunsa yana mai yawatawa akan Khairiyya kafun lokaci guda ya watsa shi gaban Alhaji Mati.
"Zabi guda daya".
Ba musu ya kai hannunsa ya sauke kan 'ya'yan carbin ya zabi daya gami da mikawa Malamin ya ansa kafun yayi jim na dan lokaci bakinsa na motsawa sannan ya tofe a jikin zabin Alhaji Mati yan sakanni ya dauka kafun ya dubi Alhaji Mati.
"Tun yanzu duniyar nasarorinka sun fara shan sharafin su don haka ka fara lissafin kan ka a cikin manya-manyan ATTAJIRAN DUNIYA".
Wani irin murmushi ya kufce masa kafun ya dubi Khairiyya yana jin wani irin nishaɗi da farinciki na ƙaruwa a ko wani fili na zuciyarsa dama duniyarsa baki daya.
"Dakyau Malam Dan-Tani".
Gyaɗa masa kai yayi yana masa nuni da ido da yayi wa Khairiyya magana ta biyo shi ba musu Alhaji Mati ya dubi Khairiyya da ta gama hargitsewa gabadaya.
"Tashi ki bi Malam yayi maganin ganin iyayenki".
Wani irin ware idanu tayi tana dubansa kamar ta ga bakuwar fuska a filin duniyarta cikin hanzari ta mike har tana kokarin faduwa hanyar da taga Malam ya nufa nan tabi labulan da ke jikin bango taga ya yaye sai ga wata kofa ta bayyana ba tsoro komi ta bishi bayansa ta shiga.
Daki ne dan madaidai ci ba komai a cikin sai buzu babban dake shimfiɗe a tsakar dakin sai wata babbar kwarya wacce aka zane da rubutun sunayen Allah da farin abu shi ba fetti ba sannan shi ba tawada ba.
"Cire kayan jikin ki duka".
Kamar daga sama taji ya fadi haka a dan razane ta dawo daga tunanin da ta fada ta shiga dubansa da idanuwanta da sukayo warwaje kamar mai son fashe da kuka.
"Ki cire kayan ki nace".
Ya sake fadi a wannan karo wata murya ce mai sauti yayi maganar da ita hakan ya tsora ta ta sosai da sauri tayi baya tana kokarin ficewa daga dakin kafun ta yi taku biyu ya fizgo ta wata kara ta saki hakan da ya gani da sauri ya janyo wani dan karamin buzu ya yafa mata a fuska gabadaya jikin ta ya saki lokaci guda ta zube kasa kamar matacciya.
Cikin hanzari ya dauko wani katon Alkalami ya tsoma cikin katuwar kwaryar nan dake girke tsakar dakin bayan ya fito dashi ya shiga yan tofe-tofe din sa fuskar Khairiyya ya dosa yana wani irin rubutu a jiki shi ba chainanci ba shi ba indiyanci ba sannan shi dai gashi gashi nan za dai a iya dangantashi da na Arabic bisa wasu harufa da suke yawo cikin rubutun da yake mata a fuska.
Sai da ya zane ko ina ns fuskarts kafun ya zare dan kwalin dake kanta sosai gashin kanta ya bazu wanda ya kasance mai yawa gashi baki sidik!
Sannan ya zare rigar jikinta nan ma zane mata jiki yayi da rubutun kafun ya zare mata dogon wandon dake jikinta da dan kanfai dinta nan ma zane ta yashiga yi ta ko ina har da farjinta..
(Wa'iyazubilla!)
sai da ya tabbatar ko ina na jikinta ya samu rubutun da yake yi kafun ya dawon kan gashin ta ya shiga ya mutsawa da ruwan da yayi rubutun sannan ya mai da mata da kayan jikinta sakanni kadan da kammalawar ya dauko buzun nan ya shafa a fuskarta lokaci guda ta dawo hayyacinta da sauri ta mike tana kokarin zurawa da gudu ya sanya hannu ya kamota ya zaunar da ita.
"Ba abin da zan miki zauna ki huta yanzu za ku tafi ki ga iyayenki".
Ba musu ta koma ta zauna shi kuma ya tashi ya fice wajan Alhaji Mati ya koma kafun ya zauna yana mai jan carbin da ya samu zube.
"An kammala komai yanzu aiki ya rage gareka".
Gyaɗa kai yayi yana faman murmushi kafun Malamin ya cigaba da cewa.
"Aikin da yake gaban ka yanzu shi tun daga daren yau za ka fara amfani da ita wato saduwa har na tsawon kwana uku a ko wani kwana daya kuma sau uku zaka sadu da ita a dare ka ga ya kama sau tara kenan zaka sadu da ita a dare uku daga ranar da ka cika kwana ukun to a ranar zata bar gidan ka karka sake ko minti tara ta kara domin za a iya samun matsala mai girma wanda za ta iya ruguzo aikin mu da muka ɗade muna kokarin cimma sa".
Wani irin dokawa gaban Alhaji Mati yayi amma bai bari Malamin ya gane ba ya shiga yaƙe yana sharce gumin da yake ta faman tsantsafo masa duban Malam yayi.
"Amma Malam kai fa kace ba zan taba kusantar mace ba Amma kima yanzu...".
"Nasan da haka shiyasa nace daga dare na uku karka sake kulata kar ma ka sake ta kwana gidan ka".
Hadiye miyau yayi mai tauri jin samun mafita da yayi amma da duk ya gama ruɗewa jin bayanin da Malam din yayi masa.
"za ku iya tafiya".
Ya fadi ya na kau da kai daga kallon sa.
Tashi Alhaji Mati yayi jiki a sanyaye ya kira yi Khiariyya da sauri ta fito tana duban su daya bayan daya.
"Zaka ji sako na Malam Dan-Tani nan zuwa gobe".
Bai ansa masa ba illa gyaɗa kai da yayi.
Hannunta ya ja suka fice bayan yayi masa Sallama.
Suna shiga mota ya dau hanya izuwa lokacin dare ya fara shigowa sosai don har an idar da Sallar issha'i.
Cikin mintinan da ba su haura talatin ba suka isa wani tankameman gida mai rai da lafiya wanda kallo daya zakayi masa sai kayi zaton ba a filin kasar najeriya yake ba saboda yanayin tsarin gininsa da kayan alatun da aka zuba.
Bayan yayi Parking wajan sauran motocin gidan suka fito yana rike da hannun Khairiyya har suka isa kofar da zata sada su da baban falon gidan key ya saka ya buɗe suka shiga.
Yaa Allah!
Zo ku ga Aljanar duniya tsayawa tsara suffar falon ma katon aiki ne a gare ni ku dai ku baiwa kan ku amsa da kan ku makaranta.
Zaunar da iya yayi akan duma duman kujerun Falon kafun ya zare babbar rigarsa ya yasar a nan ya sake cire yar ciki ya sake ajjewa ya shiga kokarin kwance wandon sa da sauri Khairiyya tayi kasa da kai tana dukunkunewa waje daya numfashinta taji yana sama da kasa kamar zai dauke sosai da sosai ta firgita zuciyar tashiga bugu ba ƙaƙƙautawa.
Ba ta san lokacin da ya iso gareta har ya zauna ba kawai jin hannun mutum tayi a jikinta da sauri ta kara takurewa kafun ta dago idanuwanta da suka rine lokaci guda.
'Innalillahi wa inna ilair raji'un'.
Abin da ta fadi kenan a zuciyarta ganinsa tumbur haihuwar uwarsa komai na halittarsa a bayyane yake ba ta san lokacin da ta saki wata wawuyar kara ba gami da kokarin mikewa amma ina ta kasa domin lokaci guda taji ya daukota gabadayanta ya ajje kan cinyarsa ya shiga yage duk wata suntura dake jikinta fuskarsa dauke da murmushin mugunta wani irin yanayi yake ji a jikinta dama zuciyarsa baki daya ya shiga lumshe idanuwansa bayan ya kammala zare mata komai na jikin ta ta koma haihuwar uwarta ita ma kuka take yi wanda bata san lokacin da ya kufce mata ba sai faman tirje tirje take amma ina hakan bai hanashi haike mata ba cikin yanayi na karfi yake sarrafata kamar zai karyata ita kuwa ihu take yi amma ina ba alamun wani mai cetonta tun tana ihun har muryar ta ta dashe lokacin da ya shigeta tun da ta saki wata kara bata sake sanin in da kanta yake ba har yayi kidin sa yayi rawarsa ya ta shi ya barta nan yashe cikin yanayi na tashin hankali da taba zuciya komai nata in ka kalla sai ka kau da kai domin kace kace yayi mata kamar ba mutum mai rai a jiki ba kujerar da take kai kuwa kamar an yanka kaza a wajan tayi FESHIN JINI haka ya koma.
Ba ita ta farka ba sai cikin dare sosai da wata irin kara ta saki ta tashi jikinta na kyarma kuka take yi kuka mai taba zuciya kuka ne take yi wanda ba ta san iya lokacin da zata daina shi ba ko ina na jikinta ciwo yake yi mata ga wani zafi da raɗaɗi da take jin sa ya na amsa wa har cikin kanta tun daga mararta har zuwa kafafuwanta ji take yi kamar ana saka guduma ana kwankwatsa su.
Cikin wannan yanayin garin Allah ya waye haka ya fito ya tadda ita ko kallon arzuki bai yi mata ba ya sa kai ya fice bai sake dawowa ba sai dare a wannan daren ma haka ce ta kasance don Khairiyya ji tayi kamar a daren ranar da ya kawota gidan ba komai yayi mata ba don sai da ta gwanma ce da ma ta mutu suma dai bata san iya adadin da tayi ba.
A dare na uku kuwa har yayi ya gama bata ta sani ba don gabadaya ba numfashi a jikinta shi kansa sai da yayi tunanin mutuwa tayi yana kammala abin da yake yi ya mai da kayansa ya dauke ta a cikin wannan mugun halin ya saka ta a motarshi yaja ya fice daga cikin layin sosai yayi nisa da unguwarsu kafin ya sami gefen titi ya fito a hankali kamar wanda fitsari ya matsawa zai yi haka ya ja motar sosai gefe yayi Parking ya fito ya buɗe ya zaro ta har zuwa lokacin ba numfashi a jikinta ya yasar da ita sai da ya dubi gabas da yamma kudu da arewa ya ga ba wanda ya gan shi domin lokacin dare yayi sosai da sosai ya ja motarsa yayi gaba zuciyarsa fes! KUDIRI da burinsa sun cika zai zama daya daga cikin ATTAJIRAN DUNIYA.
Gudu yake yi sosai fuskarsa na bayyanar da jin dadi har ya koma gida yayi wanka ya shige dakin sa ya baje saman kafcecen gadonsa yana faman sakin numfashi na farinciki da jindadi har barci barawo yayi awan gaba dashi.
*****
sosai take jin gabanta na faduwa tun daga nesa idanuwanta take kara warewa sosai daga cikin motarta har ta iso wajan tayi parking gabanta na tsananta faduwa.
'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un'.
Ta fadi tana mai daura hannu akai tana mai rushe da wani irin kuka.
"Khairiyya".
Ta kira sunanta da wata irin muryar mai cike da tashin hankali da tsananin kaɗuwa isa tayi gareta tana janyota daga cikin ciyayin da take rintse idanuwanta tayi lokacin da ta ga mugun halin da take ciki.
"Na shiga uku ni Layla wani irin mugun abu nake shirin gani a filin duniyar rayuwa ta ne".
A daidai lokacin hannun Khairiyya yayi motsi ganin haka ya sanya ta jijjigata amma ina ba alamun zata iya ko da sake motsi a halin da take sai dai numfashin da ke fita daga hancin ta cikin yanayi na tsananin wahala da yanke rayuwar duniyar nan.
Kuka sosai Hajiya Layla ke yi tana faman kiran sunan Khairiyya amma ina ba alamun motsawa da sauri ta sungume tayi motar ta da ita cikin tsananin tashin hankali har zuwa lokacin hawaye ba su daina zuba a idanuwanta ba zuciyarta na faman karyewa da wani irin yanayi mai girma na tashin hankali.
"Alhaji Mati-Dr.Erena".
Ta fadi cikin yanayi na takaicin zuciya da ruhi sosai ta zauna kan set din motar tana hada kanta da Sitiyari wani numfashi take saki a wahale mai tsananin zafi da ku na.
"Ban san rashin imanin naka ya kai haka ba, ban san baka da tausayi har haka ba, ban san abin da yasa na yarda har na san ka a rayuwata ba, ban san mai yasa na anshi bukatarka ba, in da nasan kudirin da ke ranka kenan ba zan taba yarda har hakan ta faru ba".
Numfashi taja kafun ta cigaba cikin muryar kuka.
"na tsani kaina na tsani rayuwarta da nayi da kai a duniyata Alhaji Mati ban san har lamarin naka ya kai haka ba ban san da wani ido zan kalli yarinyar da na saka hannu wajen KETA HADDI a gareta ba ban san wata irin tsana za tayi mani ba in har tana da sauran rayuwa a duniyar nan kaico na kaicon wannan rayuwa kaicon haduwa da irin ku Alhaji Mati a wannan duniyar na tsane ka na tsane duk mai hali irin naka na tsani sake ko da ganin fuskar ka ce a wannan rayuwa".
Hannu ta sa ta dauke zafafan hawayen da take jin su kamar za su dauke mata fatar fuska kafun fuskarta ts kara tamkewa kamar Alhaji Mati na gabanta.
"ka tsuwa maye ni Alhaji Mati na rantse maka da Allah sai ka ga ne kurin ka sai na mai da Khairiyya mace sai na mai da ita mai 'yanci sannan kuma da hannunta za ta dauki fansa ka jira lokacin ka Alhaji Mati yana nan tafe".
Ta karashe idanuwanta na zubda hawaye kafun ta saki wani murmushi mai ciwo a zuciya da ruhi.
Juyawa tayi ta dubi Khairiyya wani kuka ne ya zo mata da sauri ta dake kafun ta fizgi motar ta cilla saman titi gudu take yi kamar zata tashi sama...
*******
A hankali ta dago fuskarta tana kallon Get din da zai kaita cikin ABDURRAZAQ FASHION CLUB COMPANY.
ba za ta iya shiga ba da yanayin da take ciki a fuskarta ba zata iya zuwa ta kalle shi ba ba ta san mai za tayi masa ba a daidai wannan lokacin in har suka hadu a waje daya.
Da sauri tayi wa Motar Key cikin wani irin yanayi na tashin hankali amma fuskarta wani murmushi yake bayyana a kanta juyar da akalar motar tayi ta cilla saman titi kamar zata tashi sama haka take zabga gudu.
*KAMALA MINNA*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA HUDU.
"Ban san ya zanyi ba Baseera, Ban san mai ke damun zuciyata ba, sosai da sosai nake jin zuciyata wani iri, komai nake ji yana sauya mani a filin duniyata kamar bani ce ba".
Ajje numfashi take tana faman tura laɓɓanta duka cikin bakinta tana cizawa fuskarta na kara ya mutsewa kamar mai shirin fashewa da kuka a hankali ta goge gumin da ya taru a goshin ta bayan ta ja gwauron numfashi.
"Shekara daya fa...haba mana Baseera ya dace ace ko wani irin laifi akayi wa mutum yayi afuwa".
Ta sake fadi tana jin zuciyarta na wani irin duka kadan-kadan.
"Ban san laifina har ya kai haka ba...ba ma wannan ba, wallahi ban san mai ma nayi masa ba har ya yi fushi da ni har haka..anya kuwa Baseera Dr.Karami bai manta dani a filin duniyar rayuwarsa ba akan abin da yake ganin babban laifi ne nayi a garesa har ya yanke mani wannan hukuncin wanda yake kokarin tarwatsa komai nawa haba!...".
sosai take jin kanta ya shiga sarawa duniyar ta ji tana juya mata komai taji yana kwance mata kamar ba nata ba a hankali ta dago fararen idanuwanta da suka fara kaɗawa zuwa ja laɓɓanta sai faman ƙarkawa suke kadan-kadan yanayin ta ya nuna gaf! take da rushewa da kuka hakan ya sanyata tsagaitawa da maganar da take yi.
"Tun tafiyarsa Baseera...tun dan ya bar kasar nan nakasa kwanciyar hankali a filin duniya ta ban son ace ya tafi da bacin rai na a duniyar rayuwarsa ba, ban so ace tun waccan lokacin na fara bata masa rai ba, ban so ace alherin sa garemu na mai da masa da bacin rai ba".
Baseera da tun dazu ta zabga tagumi tana duban Mariya da take ta zaro zance cikin rashin hayyaci kallo daya zaka yi mata ka karanci yanayin damuwar da take ciki itama sosai da sosai jikinta da komai nata yayi sanyi.
A hankali ta shiga gyara hijabinta cikin yanayi na sanyin jiki kafun ta kau da kanta daga barin kallon Mariya domin ji take kamar ta rushe da kuka ganin yanayin da ƙawar ta ta take ciki ta sani Mariya ta jima cikin yanayin damuwa ta shafe lokaci mai tsayi lamarin na sukar mata zuciya ba tare da ta bayyana hakan ba sai dai in abun ya matsa mata take shiga damuwa sosai har fuskarta ta sauya a nan zaka gane tana cikin wani hali Mariya akwaita da ZURFIN CIKI ba komai nata take fadi ba ba komai dake zuciyarta ake saurin ganowa ba tana da daukon abu a zuciya irin mutanan nan ne masu boye duk yanayin da suke ciki suna da kokarin boye SIRRI komin girmansa.
"Na sani Mariya kina cikin yanayi amma hakan bai dace ace kin saka rayuwarki cikin damuwa har haka ba as your age ya kamata ace kin mai da hankali sosai akan wannan karatun da kike yi bai dace ace Tension ya fara samun masauki a filin zuciyarki ba a yarda kike kwakwalwarki ya kamata ace saukaken lamari take dauka ba wanda zai hargitsa komai na ta ba".
Nisawa Mariya tayi tana mai sauke wani murmushi mai zafi a zuciya.
"duk abin da kika gani a filin duniyar nan tawa na karuwa har izuwa matakin da nake yanzu SHINE SILA Baseera ya kamata ki san da hakan".
"Na sani Mariya ba sai kin yi mani tuni ba amma hakan ba wai yana nufin don yana fushi dake ba kuma ki lalata komai abin da baki sani ba shine ya kamata ace kin mai da hankali akan komai musamman karatun nan ina mai tabbatar miki duk ranar da ya sako kafarsa kasar nan to abin da zai bukata shine ya kika kasance bayan tafiyarsa shin kin dauki abubuwan da duk yake miki da muhimmanci ko kuma dama can ba wani martabarsa kike gani ba to hanya daya ce shine ki mai da hankali kan komai da komai da kika san na karuwa ne kuma shine sila kamar yarda kika fadi to ki mai da hankali akan su na tabbata in ya dawo duk wani laifi naki zai kau in har kika cika masa alkawarin da kika daukar masa".
Shiru tayi tana dubanta tun da ta fara magana take kallon bakinta ta sani maganar Baseera akan hanya take sai dai kuma bata tunanin maganganun za suyi tasiri azuciyarta domin tashin hankalin da take ciki a filin duniyarta ba ta tunanin zancen wani ba na Dr.Karami ba za su sanya ta cikin natsuwa.
Gyaɗa kai ta shiga yi kamar wata ƙadangaruwa sai faman jan numfashi take.
"Tashi mu tafi Mariya zaman nan a nan ba zai yi mana ba ki dubi fa kowa ya gama tafiya mu ne kadai mu ka rage".
yawatawa da idanuwanta ta cigaba da yi a filin makarantar kafun ta dubi Baseera da ta mike take saɓa jakar ta gami da daukar sauran littatafan ta a hannu ita ma mikewa tayi ta sungumi littatafan ta suka doshi get.
"ni ban san ma abin da ya motsa miki tunanin Dr.Karami ba kwana biyu na lura kin rage amma tun da muka fara Exam din nan shikenan komai ya zama sabo fil! kuma hakan ba karamin nakasu zai kawo miki ba ba fata ake ba amma yakamata ace kin mai da hankali wajan Exam din da muke ba wai tunanin wani lamari ba wanda ba ki san ranar karewarsa ba".
Gyaɗa kai kawai take yi tana jin zancen Baseera wanda ba ta tunanin zai iya yi mata komai a halin da take ciki.
"Shikenan".
Ta furta murya can kasar makoshi.
*******
Da Sallama a bakin ta ta shiga cikin gidan.
Kamar ko yaushe yau ma dai Da'irar aka kafa sai baza idanu ake yi ana kallon mai shigowa da ficewa.
Kofar dakin su ta kai wa kallo ganin Umma bata nan zaune hakan ya tabbatar mata tana cikin dakin domin ita dama Al'adar tace haka in dai su Goggo Marka na tsakar gidan nan to bata da filin shan iska a cikin sa in kuwa ta zauna ta san sauran.
"nikam cikin kwanakin nan gabadaya Mariya ta canza anya kuwa?".
Hafsi ce ta fadi can kasar makoshi tana duban Goggo Marka da ta kafe Mariya da kallo tana binta gaɓa gaɓa kamar wacce take neman wani boyayyan abu.
"Allah yasa ba mugun abu ta kunso ba".
Hafsi ta sake fadi tana kallon Goggo Marka cikin yanayi na son tace wani abu da zai karawa gulmar ta ta matsayi har ta kara rurata.
"Ke nima fa na so ganin haka 'yar Albarka duk naga ta ɗashe tayi fari ga shi ta rage walwala kai jama'a Allah yasa ba mugun abu ta kunso ba mu ga karshen BIRI BOKO da ake yi mana da fankama wai karatu ake yi ita ga mista ƙyanƙyan 'yar gidan mangwafan".
Muryar Abulle ne da ta fito daga makewayi ya sanya su yin mukus.
Fuskart da fara'a take duban Mariya.
"Ahh Yar gidan Umma har an ta so kenan".
Mariya da hankalin ta gabadaya bai wajan su jin muryar Abulle ta yi saurin tsayawa tana sakin yaƙe.
"Inna ina wuni".
Ta fadi tana durkusawa gabanta cikin yanayi na girmama.
"Lafiya lau Mariya ya karatun dafatan dai ana mai da hankali?".
Gyaɗa kai tayi ba tare da ta ansa ba.
"To maza aje a cire kayan a huta Ummanku ta ce mani Jarabawa ku ke ko? to Allah ya taimaka ya ba da sa'a gami da nasara".
"Ameen".
Mariya ta ansa ta na mikewa ta karasa shiga cikin dakin da Sallama a bakin ta.
Abulle dake ta faman sakin murmushi jindadi ganin yarda Mariya take duk sai taji ta burgeta sosai a hankali ta gyaɗa kai tana duban Hafsi wanda suke bin ta da kallo Uku ahu da sauri suka kau da kai.
"Ke yanzu ba ki ji kunya ba don Allah ki dubi Mariya ke ba abin kiyi sha'awar ta bane yarda take a natse komai tana yin sa cikin hankali".
ta fadi cikin yanayi na bacin rai sosai a fuskarta wani takaicin Hafsi take jin yana tokare mata zuciya ji take yi kamar ta rufe ta da duka.
"To sababba nuna min Mariya tafi Hafsi a wajan ki da kike cewa ita abin sha'awa ne da burgewa a hakan ki ka san mugun abin da take aikatawa kawai ta mai dake sauna da sunan tana zuwa makaranta ke kuma ki yarda nan kuwa tsiyarta take kitsawa".
Dama ta san za ayi haka shiyasa tun farko bata so cewa komai ba abin ne yake ci mata zuciya amma duk da hakan ba za ta fasa fada masu gaskiya ba don haka ta dubi Goggo Marka murya a tausashe.
"Haba Goggo ZATO ZUNUBI fa ko da ya kasance gaskiya ne ke kin san Mariya ba zata yi wannan wautar ba yarinya ce mai hankali ni zan iya shedarta wallahi akan kula da kai".
"To naji ita kuma 'yar taki ballagaza ko".
Goggo Marka ta tare ta a zafafe har tana kumfar baki.
"Nace ita Hafsi ai bata da natsuwa Zainabu ki kiyaye ni bar ganin kin tara su Hafsi hakan ba zai hana ni kwaɗa miki mari ba wallahi don na lura mugun halin naki na nan irin na su baki son laifin su kamar su ne suka sunkuto ki duniyar nan".
Sosai Abulle taji zafin maganar don haka ta dubi Hafsi dake ta faman turo baki gama ita ala dole anyi mata ba daidai.
"ke dai kin ji kunya wallahi ba fata zan miki ba amma wallahi sai kin yi takaici duk ranar da kika ga Mariya ta zama wani abu a filin duniyar nan da karatun nan nata da kuke ma kallon hadarin kaji...".
"Tsine mata nace in baki tsine mata ba ba ki cika ke ce ba yar bakin fata kawai ki san Allah Abulle ki kiyaye ne akan takurawa Hafsi da kikeyi acan gidan naki in taje ba ki kyale ta ba haka in kika zo nan gidan ki sakata gaba da hayyata haba! sai kace ba kya ki ka haife ta ba wannan kiyayyar har ina".
"Haba mana Goggo daga fadin gaskiya ni fa tsakani da Allah bana jin dadin yanayin da kike nuna min akan Hafsi ita kenan ba a isa a fada mata gaskiya akan abin da take yi na ba daidai ba kullum ita kenan cikin SANGARTA ni dai ba zan dauki haka ba ya kamata ace ta tsaya ta kula da kanta ita 'ya mace ce...".
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un".
Goggo Marka ta fadi kafun ta dora.
"Zainabu me kike yi haka ba dai mugun abu kike kokarin daukowa 'yar taki ba nikam Marka ina ganin lalata yau ina ganin mugun abu".
Hannu ta daura akai ta rushe da kuka kamar wanda ka zagarwa uwa nan da nan Hankalin Abulle ya tashi takaici da bakin ciki suka turnuke ta shiyasa sam! bata son zuwa gidan nan domin in dai ta zo ba sa rabuwa ta dadi kuma duk akan Hafsi ne.
"kiyi hakuri Goggo ni fa ba abin da nake nufi kenan ba ta ya ya zan yi wa 'yar da na haifa mugun fata Allah ya tsareni ya tsari baki na da furta kalmar batacin gareta".
"Ke dalla can rufe mani baki ai dama tuntuni na lura kin fi kaunar makiran can akan mu ni da 'yarki ke kenan kullum baki yi mata abun kirki sai dai fada da kushe a haka ki ke so ta dinga zuwa wajan ki a haka kike so ta dinga miki kallon uwarta bayan bakya kaunarta".
Sababi na kin kari ta cigaba da yi tun Abulle na danne zuciyarta har idanuwanta suka kawo ruwa da sauri ta zari mahaifinta tana bata hakuri ta bar gidan zuciyarta cike da bakin ciki da takaicin abin da MAHAIFIYARTA take yi mata akan 'yarta.
Umma da Mariya da tun da suka ji hayaniyar suka leko ganin abin da ke faruwa ya sanya su tsayawa daga bakin kofa domin sun san in har suka takka kan su komai zai koma a shiga kwashe musu Albarka.
Sosai Umma taji rashin jin dadi a zuciyar ta ganin halin da Abulle ta bar gidan da hawaye wanda ta tabbata na bakin ciki ne da takaici ba komai ba.
Ba ta san mai yasa Goggo Marka ke haka ba sam haka bai dace ba ya kamata ace tana baiwa Abulle matsayin ta na Uwa ga Hafsi domin nuna mata hanyoyin da suka dace ba wai ita Goggon Marka ta dinga nunawa Abulle bata isa da Hafsi ba hakan ba karamin ganganci ba ne domin ta tabbata Hafsi ba zata taba ganin Mutuncin uwarta ba sai tafi ganin Goggo Marka da mutunci akan uwarta hakan sam bai da ce ba AKWAI ILLA! sosai da sosai a ciki.
"Umma mana".
Mariya ta fadi da sauti tana mai jinjiga Umma ganin tayi nisa a tunanin.
Dubanta tayi tana ajje numfashi mai karfi ta shiga gyaɗa kai kafun ta juya ta koma cikin dakin fuskarta na kara bayyanar da damuwa sosai da sosai.
"Ban san wacce irin rayuwa bace wannan ake yi, Ban san mai zan kira wannan rayuwar ba, mai dauke da son zuciya da son kai, sosai ake shiga hakkin zainabu wanda sam hakan bai dace ba ita uwa ce fa ya kamata, ace ana bata hakkinta da damarta akan Hafsi domin 'yarta ce dole ta kula da rayuwarta komai ya same ta ita zata fi kowa kuka akan abin da ya faru da 'yarta haka in abin farinciki ne ya same ta zata fi kowa son haka maganar gaskiya ya kamata Goggo Marka ta daina irin haka SANGARTA da take sanya Hafsi nayi ba zai haifa musu ɗa mai idanu ba".
Numfashi Mariya taja tana komawa gefe tana zaunawa hannayenta duk biyu a haɓarta ta zabga tagumi tana duban Umma cikin yanayi na rashin abin cewa ta tabbata da Goggo Marka zata ji wannan maganar kila cewa zatayi Umma ta kafurta ta a filin duniyar rayuwar musulunci gyaɗa kai tayi kafun ta sake duban Umma.
"Allah ya kyauta".
Da sauri Umma ta dube ta jin abin da ta ce cikin yanayi na son karin bayani.
"Umma mu bar maganar nan don Allah a nan in ma son yin ta kike yi gwanda ki je gidan Inna Abulle kuyi domin na tabbata in kika ce wani abu kwaɓarki ce za tayi ruwa wallahi".
"Amma Mariya Anya rayuwar zata kasance a haka 'Ya mace ce fa ita Hafsi din nan gaba so take yi a kira ta Uwa anya kuwa hakan za ta kasance haba mana ake duba da idon basira ana daura abin da ya dace a MIZANIN HANKALI...".
Cikin yanayi na gundura da batun Mariya ta haɗe hannayenta waje guda alamun roko tana kara marere ce fuska kamar za tayi kuka ba abinda take tsoro illa Goggo Marka ta sani ba za a kwashe ta dadi da ita ba in har ta ji wannan batun...
"To Almunafunfun masu lissafa zunubai da ladan bawa tare da yanke masa hukunci shiga aljanna ko wuta ina shiryayyin 'yar taki".
Kamar daga sama suka tsunkayo murya Goggo Marka a kofar dakin su tana kokarin shigowa wata irin zabura Mariya tayi tana komawa can gefen katifar daki inda Mu'azzam ke kwance yana barci tana duban Umma da taja wani Numfashi mai girman gaske tana sauke idanuwanta a kofar dakin.
A daidai lokacin da Goggo Marka ta bankaɗo labulan kamar zata tsinke ta ajje shi gefe ta karasa shigowa wani kallo ta watsa musu su duka.
"Ai duk ɗan da bai san darajar tirelan itace ba to uwarsa bata dumame da wankan jego kuma sanin darajar 'Ya yake sanya iyaye rikon ta ko da ta aikata ba daida ba".
'Yaa hayyu Yaa kayyum'.
Umma ta fadi tana mai dafe kanta da take ji yana juya mata yana wata irin sarawa kamar zai rabe gida biyu idanuwanta lokaci guda suka kada sukayi jajir sosai da sosai taji zuciyarta da kasan ruhinta na wani irin tururin zafi kamar an rura wutar makera.
A hankali take jan numfashi da take ji kamar zai samu a rauni a tattare da ita sosai take jin wani irin tashin hankali na ziyartata komai na duniyar rayuwarta taji yana canzawa maganganun Goggo Marka ba karamin tayar mata da hankali sukayi ba sosai ta lura shaguɓe da haibaici ta watsa mata wanda hakan ba karamin sanyata cikin ɗacin rai yayi ba gyaɗa kai ta shiga yi cikin rashin abin yi.
"wai har mu za nuna wa bariki a filin duniyar nan ni ban san lokacin da dan yawo da shanu jeji jeji ba har ya san bariki...ko da yake ba abin mamaki bane tunda kullum ana zarya da gantali a ko wani titi da layi na cikin gari ana koyon kissa da yarda barbaɗaɗɗun mutane ke yi ba shagon gardawa ba a gidan caca".
Hawaye suka zubowa Umma lokaci guda ba tare da ta ba su dama ba, tashin hankalin da take jin kanta aciki a wannan lokacin yafi gaban kwatance sosai take jin wani iri a zuciyarta sosai take jin wani abu mai girma ya tsaya mata a kirji sosai take jin wani irin yanayi mai tattare da kayan takaici da bakin ciki tun daga kasan ruhinta har zuciyarta.
Ba za ta iya cigaba da sauraron wadannan bakaƙen kalaman ba. Zuciyarta..Zuciyarta da kwanyarta sosai take ji ba za su iya daukar tashin hankalin dake cikin kalaman Goggo Marka ba ba ta san lamarin tsana da ƙyarar da take yi akanta har ya kai haka ba, ko da yake ba abin mamaki ba ne in dai Goggo Marka ne za ta iya fiye da haka.
"Nace wani Kullin ku ka jefi 'yata dashi ta sanyawa 'yarta karan tsana a filin duniyar nan, gabadaya na lura natsuwa da hankalin Zainabu ya na kan ku ko ku ne kuka yi nakudarta sai haka".
Ba ta san mai zata ce ma taba a wannan lokacin, ba ta mai ya dace ma tace da ita ba domin komai ya gama kwance mata ta gama tsinkewa da lamarin Goggo Marka.
Hawaye ne suka shiga zubo mata ba ƙanƙautawa kanta a kasa lamarin yana kara sanyata tashin hankali dukan ya yi yawa ta lura Goggo Marka so take yi ta kashe ta da ranta ta kunsa mata bakin cikin da zai sanya zuciyarta bugawa.
"Da ke fa nake kikayi banza dani Habeeba kisan Allah zan baki mamaki sai na shayar dake ruwan tashin hankali ba dai ki dauki damarar tsayawa a rayuwata ba da ta 'yata mu zuba shege ka fasa a tsakanina dake".
Ta na gama fadin haka ta juya tana huci kamar kububuwa ta bar dakin.
Mariya da tun dazu jikinta ke ƙarƙarwa hawaye na zuba ganin irin cin mutuncin da ake wa Umma gabadaya ta shiga tashin hankali mai tsananin gaske zuciyarta na faman yi mata zafi da raɗaɗi kamar zata faso kirji ta yo waje.
Kuka ta rushe dashi mai tsananin zafi da sanya zuciya tashin hankali , kuka take yi da dukkanin yanayin da ta samu kanta a ciki, kuka take yi da duk wani tashin hankalin da zuciyarta ke dauke dashi.
"wannan wani irin BALA'I ne, wannan wani irin tashin hankali ne, Yaa Allah...".
Da sauri ta tsaigaita jin wani sabon kuka ya zo mata dunkulewa tayi waje guda tana haɗe jikinta hannunta guda ta tura cikin baki tana cizawa ji take yi komai kamar ba a gaske ba jin komai take yi kamar A MAFARKINTA ba a zahiri ba.
"Ya isa haka Mariya".
Umma ta fadi da wata irin murya mai dauke da tsananin rauni da damuwa.
"Haba mana Umma wai don Girma Allah haka za mu ci gaba da zama ana gaya miki irin wadannan bakaken kalaman ba tare da laifi ba tsakani har ga Allah Goggo Marka ba ta k...".
"Nace kiyi shiru ko Mariya".
Yanayin zafi mai zurfi da ya fito a muryarta ya sanya Mariya sakin sabon kuka mai cike da haushi.
"Ban san mai yasa har yanzu baki san rayuwa ba, Ban san mai yasa har yanzu baki san abin da duniya ta kunsa ba na lura har yanzu baki san kaifaffan ALKALAMIN ƘADDARA ba a duniyar rayuwar dangin rai".
numfashi taja tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa waje gudu da tashin hankali mai girma.
Sakanni ta kwashe kafun ta sake numfasawa.
"ƘADDARARMU CE haka Mariya ya kamata ki san wannan duniya tamkar makaranta take rayuwar da muke yi jarabawa ce mai matukar muhimmanci bai kamata tun yanzu ki karaya da wannan rayuwar ba bai kamata ace tun yanzu ki nuna kosawarki akan ALKALAMIN ƘADDARAnki ba ki sani duk wani rai da yayi saura a filin duniyar nan yana DA SAURAN KALLO ita fa rayuwar nan dama uku ce farko tsakiya karshe misali farko shine haihuwa ki san wannan tsakiya kuma baki san abin da ALKALAMIN ƘADDARA zai dauko miki ba karshe kuma mutuwa ce wanda take tamkar riga a jikin ko wani bawa kullum tana makale dashi har ranar da zata dauke shi".
Sosai Mariya kukan ta ya ragu tana duban Umma da jin irin kalamin da take sanar da ita cikin murya mai laushi da kokarin kwantar da hankali gareta sosai take jin zuciyarta na sassautawa komai na raguwa HAWAYEN ZUCIYA da take jin suna kona mata ko ina na kirjin ta suna raguwa.
"Mariya ki koyi rayuwar zaman duniya DUNIYA MAKARANTA CE mai girma wacce tafi ko wacce makaranta dake cikinta ba abin da ba a koya a cikinta na dadi da akasinsa sannan a makarantar duniya akwai fannoni masu zafi kuma akwai masu sauki kamar yarda kike ganin salo a makarantun da kike zuwa kamar jarabawa ce in kayi karatu ka jajirce sai ka samu nasara amma in ka saka wasa a lamarin sai ka rasa gane kan komai".
Gyara zama tayi sosai tana duban Umma bayan ta tankwashe kafafuwanta kamar mai shirin cin abinci hannayenta a haɓarta ta zuba mata ido.
Murmushi Umma tayi kafun ta sake motsa laɓɓanta da salo na rarrashi.
"Na shiga cikin yanayi na cuta bayan na warke na rasa miji na kafun nan kuma ga halin da nake ciki tare da Goggo Marka kin ga duk wannan ALKALAMIN ƘADDARA ta tuni ya rubuta su da izinin Rabbil izzati za su faru dani tun kafun na zo duniya".
"UKU BALA'I kenan".
Mariya ta fadi can kasar zuciyarta da wani irin yanayi mai zafin gaske domin ita dai ba abin da za ta kira wannan lamarin sai haka ba ta hango alheri a cikin su ba sam! balle ta ce musu UKU ALHERI.
"Karki dauki wannan a matsayin bala'o'i ki dauke su a matsayin jarabawa da kuma abin da ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuta miki TUN FIL'AZAL da sahalewar ubangijin".
Da sauri Mariya ta dubi Umma tana ware ido gani take yi kamar ta jiyo abin da ta ke zantawa da zuciyarta.
"Sannan ki sani ba ko wacce Ƙaddara ba ce take samun bawa hka kawai sai da sanadi ko sila sannan kuma akwai abubuwa da yawa da suke faruwa a filin DUNIYARMU wanda da yarda mu da sanadinmu komai ke faruwa damu sosai muke daukan wasu abubuwa da suke faru damu mu jinginawa ƙaddara bayan da saka hannunmu komai ke faruwa shiyasa ake so komai DAN'ADAM zai yi a filin rayuwar duniyarsa ya dinga dubawa yana daurawa a MIZANIN HANKALI kafun ya aikata shi, saboda gujewa kuskure domin KUSKURE DAYA TAK! yake saka mutum a da na sani".
Sosai jikin Mariya yayi sanyi hawaye kadan-kadan suka shiga zubo mata ji take yi kamar JIRWAYE Umma ke yi mata da zantukanta ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Dr.Karami da fushin da yayi da ita ta tabbata ita ce sila ita ce sanadin faruwar komai amma kuma ai ba ta san sanadi ba ba ta san abin da ya sa yayi fashi da ita ba har haka.
"Kan Uban can ke! Habeeba".
Kamar daga sama sukaji Goggo Marka ta lailayo ashar ta kudunma ta daura da fadin haka sosai gabansu su duka ya fadi.
"Yaa Rabbi?".
Umma ta fadi tana mai sakin wani murmushi mai ciwo a zuciya.
"Ni za ku mai da 'yar iska ko".
Ta sake fadi tana fadowa cikin dakin hannun ta rike da zanin atamfa da ya sha jiki kallo daya zaka yi masa ka gane mugunta da aka yi masa reza ce aka saka aka kekketa shi ketawa wanda baza ta bari a sake morarsa ba.
"Uban waye yayi mani wannan mugun abun?".
Ta fadi tana mai duban Umma kafun ta sake idanu akan Mariya da tayi mata kuri da idanu tana jiran Sharrin da zai biyo baya don ta lura TUTAR MAKIRCI ce ta motsa.
"Da ku fa nake yi ku ka yi mani carko carko da ido kamar kwarto ya fada dakin suruka ya rasa dan kamfansa".
Ajiyar zuciya suka saki su duka zuciyarsu da wani irin yanayi mai sanya ɗaci a kasan zuciya da ruhi.
"in ban da bakar mugun ta da bakin sharri yanzu Mariya saboda an koya miki bakin hali irin na dangin uwarki shine zanin nawo kika kama ki ka kekketa sabo mugun abu".
'Yaa Salam!'.
Umma da Mariya suka fadi a zuciyoyin su
Ba su an karaba sai kawai saukan mari Mariya taji a kuncin ta ji kake kau!.
"Dan uban uwarki Lamiɗo ne ya saka ki yi mani mugun halin nan ko billahillazi sai kin biyani in ba haka ba na dake ki dukan shan gishiri".
Tana gama fadin haka ta jefa mata zanin a fuska ta juya tana watsa wa Umma wani makirin kallo da tukuicin tsaki sannan ta fice daga dakin.
Hawaye suka ciccko a idanun Mariya ta shiga gyaɗa kai ganin irin kallon da Umma take yi mata mai kama da TUHUMA.
"BA NI BA CE".
"Na sani".
Umma ta fadi tana mai sakar mata murmushi kafun ta kau da kai tana dauke Kwallar da suka kawo idanunta farmaki...
*KAMALA MINNA*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.
💕 *_Ki Karba. ki Koya, Idan Kalma So Ta Amsu Yarda Ke Tabbatar Da Kauna._* 💕
-Usaini Danko.
A hankali take sauke jakar dake rataye a kafaɗarta cikin yanayi na sanyi jiki idanuwanta na kan kayan da ta gani zube tsakar dakin tana yawatawa idanuwanta akan su cikin yanayi na son sanin daga in da suka fito domin wani irin bugu taji gabanta yayi lokacin da idanuwanta suka sauka kan kayan.
Motsa laɓɓanta tayi da take jin suna cijewa kamar ba sa son ta motsa su.
"Umma wadannan kayan daga ina kuma?".
Ta fadi har zuwa lokacin idanuwanta na kan kayan ta dubi Mu'azzam da ya koma gefe ya tasa choculat gaba yana faman gabza.
"Uhmm!".
Ta sake fadi tana mai duban Umma da tayi tagumi fuskarta da yanayin damuwa dago idanu tayi ta dubi Mariya da gabanta ke ci gaba da bugawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito.
"Uhmm baki hadu da Yayan naki bane?".
Cikin yanayi na rashin fahimta take duban Umma da son nuna bata sani ba gyaɗa kai tayi a hankali tana mai samun waje tana zama don ji take yi kamar kafafuwanta ba za su iya daukarta ba sosai yanayin ta ya canza lokaci guda ta shiga tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa gabanta take ji yana kara tsinkewa gaɓadaya tun da ta tashi yau take jin wani iri a jikinta kasala da rashin son magana duk su ne suka zama abokan hirarta ko da taje makaranta yau haka ta wuni sukuku Baseera ba yarda ba tayi ba akan ta fadi mata abin da ke damunta amma fir! ta nuna ita ba abin da ke damun ta kawai ba ta jindadin garin ne yau.
Lamarin yayi tsamari yanzu don sosai da sosai take jin faduwar gabanta na daɗuwa.
Wani numfashi Umma ta ja tana fesarwa kafun ta dubi Mariya da tayi sakato da baki tana dubanta alamun son karin bayani.
"Ban san mai kike nufi ba Umma. Wani Yayan nawa ne ya zo?".
Murmushi Umma ta saki mai dan zurfi don ta lura Mariya a dan ruɗe take kamar wani abu na damunta.
"Hashim mana".
'Yaa Allah'.
Mariya ta fadi tana mai kai hannayenta duk biyu tana dafe kanta idanuwanta lokaci guda suka dan kaɗa domin yanayin da take ciki ta kosa ta ji inda Umma ta dosa da zancen domin har yanzu a duhu kanta yake ta rasa gane in da lamarin ya dosa.
Duban kayan ta sake yi tana mai yarfe hannunta da ta cire daga baki kamar wacce ta taɓa wuta.
"Ban gane ba Umma waye haka?".
Wani irin kallon Mamaki Umma take bin ta dashi cikin yanayi na rashin zaton maganar Mariya din sosai take dubanta da yanayi na bata so abin da Mariyar tace ba numfashi ta ja kafun ta motsa laɓɓanta a raunane.
"Yaa Allah mai kike nufi Mariya ba dai har kin manta alheri ba ba dai zaki ce dani kin manta dashi a filin duniyar rayuwarki ba haba! mana yaushe har yaushe hakan zai faru ina! fada min shekaru nawa kuka dauka da rabuwarku dama akwai wannan rana Yaa Salma Haba mana Mariya karki saka zuciyata ta buga mana karki canza mana daga yarda na sanki".
Sosai rauni ya bayyana a muryar Umma bakin ta na rawa har ta dire furucin ta tana duban Mariya da wani irin yanayi mai dauke da daci sosai a zuciya fuskarta lokaci guda ta shiga sauyawa tana rinewa da wani irin abu mai girman gaske.
Tsoro ne sosai ya bayyana a idanun Mariya lokaci guda idanuwanta su kayo waje sosai tana duban Umma da su yanayin da ta ganta a ciki da bacin rai yayi matukar daga mata hankali ba kadan ba da sauri ta mike kanta na wani irin dokawa kamar zai rabe biyu gaban Umma ta karasa ta durkusa kwalla suka cika mata idanu lokaci guda laɓɓanta suka shiga ƙarƙarwa kamar wacce ruwan sama yayi wa dan banzan duka.
"Don Allah Umma...".
"Ya isa haka mana Mariya".
Umma ta tare ta a zafafe tana mai daga mata hannu da wan irin yanayi mai bayyanar da bacin rai kafun ta ja numfashi mai zafi ta dubi Mariya wacce a lokacin hawayen su fara digo mata.
"Ban san haka ki ka koma ba, Ban san yaushe ki ka fara canza halayenki ba, Ban san mai yasa kike kokarin daukar hali na manta Alheri ba, sosai nayi mamaki sosai naji wani iri a raina ban yi tsammanin hakan ba ko A MAFARKINA".
Shiru tayi tana maida numfashi kafun ta dora da cewa,
"Nayi tunanin dama akwai abin da kikayi masa a lokacin baya kafun ya tafi na daɗe ina zargi haka banyi zaton samun haka ba a gareki Mariya Yaa Allah".
Rikicewa Mariya tayi lokaci guda kamar wata zautacciya tana duban Umma cikin yanayi na bayyanuwar tsoro a idanuwanta.
"Wallahi ban san wanene ba, ban san akan wa ki ke magana ba don Allah Umma kiyi hakuri ina nan a yarda kika san ni ban sauya halayena ba komai na nan a yarda kika sani na daga halayena na san ALHERI ban mantawa da wanda yayi mani shi".
"Bana tunanin haka, ba yarda za ayi ki ce mani baki manta da shi ba na yarda domin ga shi nan kin nuna na gani don haka...".
"Umma Please mana".
"Kin manta Dr.Karami ko Mariya kin manta mutumin da ya yi...".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Astagfurullah wa'atubu'ilai".
Abin da tayi saurin ambata kenan tana mikewa tsaye hannunta a goshin ta wani irin hajijiya take ji anayi da ita komai taji yana kwance mata a lokacin runtse idanu tayi komai taji ya na dawo mata a shekara daya da rabi da suka gaba komai take ji kamar yanzu yake wakana fatanta Allah yasa ba fushin nasa bane har yanzu ba ta san ya za tayi ba in bai yafe mata ba bata san wani hali zata shiga ba in bai yi mata afuwa ba.
'Yah Dr.Karami ya zo'.
Ta ambata da wani irin yanayi a zuciyarta wani irin bugu taji zuciyarta tayi a hankali ta sauke hannayenta tana dafe kirjinta da su Umma take duba kafun ta dubi kayan da suke jibge tsakar dakin Mu'azzam da ya gama shan sharafin sa da chocolut duk ya bata jikin sa ya tashi yana takawa a hankali kamar mai tsoron ya fadi saboda rashin kwarin tafiyar tasa.
"Da gaske Umma? Yaa Allah! Yana ina Umma don Allah yana ina fada min".
Yanayin da take magana da rawar jiki wani murmushi mai kauri yana samun mazauni a fuskarta zai tabbatar maka kamar ba a hayyacin ta take ba jin komai tayi a hargitse a daidai wannan lokacin.
Sosai Umma ta dube ta tana shirin gasgata yanayin da Mariya take nunawa na rashin sanin Dr.Karami ya zo da farko ta dauka rashin hankali zata nuna mata kamar ta mance dashi shiyasa gabadaya taji wani iri a ranta matuƙa domin kuwa a duniyar nan bai kamata ace Mariya ta mance Dr.Karami ba ko da kuwa shekara nawa zai yi ya dawo.
"Ya koma".
Ware ido tayi tana duban Umma.
"Yaa Hayyu Yaa Kayyum! me yasa yayi mani haka Umma mai yasa ya tafi ba tare da ya tsaya mun ga juna ba shin ya mace shekara da muka dauka har da rabi ba tare da mun sanya juna a idanu ba bai kamata yayi min haka ba haba! Umma mai yasa ba ki ce yaje makaranta ba ko kuma ya jirani na dawo".
Muryarta tayi rauni kamar mai son fashewa da kuka a hankali ta fara kokarin zubewa kasa domin jin komai take yi yana sauyawa komai take jin ya narkewa na jikin ta kafafuwanta take jin su kamar ba za su iya daukar gangar jikinta ba.
'Ban san laifi na ya kai har haka ba, ban san abin da na aikata yayi tsamari haka ba, ya kamata ace ka tausaya min kayi mani uzuri akan abin da ban san na aikata ba haba mana! haba mana!'.
Zuciyarta ta shiga fadin kalamai kamar mai shirin zaucewa sosai take jin wani irin zafi na tururi suna wanzuwa a zuciyarta da kasan ruhinta.
Ba ta san ya zata fassara yarda take jin wannan lamarin ba bata san ya zata fassara yarda take jin akan yanayin da Dr.karami ke nuna mata ba sosai zuciyarta da dukkan jikinta ke shiga tashin hankali mara yankewa.
Cikin yanayi na rashin fahimta Umma ke dubanta fuska na bayyanar da tausayin da take ji akan 'yarta ta ta sani dole ta ji ba dadi ta jima da lura da yanayin Mariya akan Dr.Karami shakuwa ce mai girman gaske Allah ya halitta a tsakaninsu wacce rabuwarta take da matuƙar hatsari a junansu musamman Mariya da ta zurfafa lamarin ta bashi matsayi mai girman gaske a filin zuciyarta.
"Assalamu alaikum! Wai ana sallama da Mariya".
Kamar daga sama suka jiyo amon muryar yaro daga tsakar gida.
Umma ta dubi Mariya ita ma ita take kallo.
"Waye?".
Umma ta fadi da sanyin murya har lokacin idanuwanta na kan Mariya da tayi fakare tana zazzare ido fata take yi Allah yasa Dr.Karami ne.
"Wani ne a cikin mota".
Zabura Mariya tayi ba tare da wani jinkiri ba ta sa kai za tayi waje.
"Mariya!".
Umma ta fadi da sauti tana mai tsayar da ita Cak! ta tsaya jikin ta sai faman rawa yake yi kamar wacce aka kaɗawa gangi.
"Ban so abin da kikeyi haba mana Mariya sai kace wata karamar yarinya ko wacce bata da kamun kai meye haka yanzu ke da wannnan yanayin zaki fita shin kin san ko waye yake kiran ki kin san yarda zaki taddashi ba kya tsoron kallon da zai miki na rashin kamun kai ban yarda ba don haka dawo".
Ji tayi kamar ta daura hannu aka ta rusa ihu don takaici da haushi hana ta fita da akayi domin zuciyarta sai tsalle take yi tana sanar da ita ta fita shine ya zo nemanta.
Jiki a sanyaye hawaye na kokarin zuba mata ta samu gefe ta zauna tana wasa da hannayenta.
"Ke haka zaki girma ko da rawar kai ana yabon ki sallah alwala zata gagari ki wannan wacce irin wauta ce sai kace ba 'ya mace ba ki ke irin wannan haukar to ba zan lamunta ba kin ji ko tun wuri ki daina hakan tun kafun ya zame miki jiki ai kewar mutum ba hauka bane...ba ma wannan ba yanzu dake ki barin jiki zuwa ganinsa ki na da tabbacin shine".
Kasa takara yi da kai tana girgizawa zuciyarta na kara matsewa a filin kirjinta so take yi kawai ta ganta a wajan nan.
"Maza tashi ki wanke wannan fuskar taki".
Ba musu ta mike tayi waje ji take yi kamar ta zura da gudu amma tana tsoron bacin ran Ummanta don haka tana wanke fuskar ta dawo ta zauna tana ajje numfashi kadan-kadan.
"ki goge fuskarki ki tashi ki tafi".
Umma ta fadi da Umarni a zuciyarta cikin yanayi na daure fuska sosai. Ba musu mafiya tasa ta goge fuskarta har tana muttsuƙa ɗan basilin kafun ta mike bayan ta zare kayan makarantar dake jikinta ta saka doguwar jallabiya da hijab sannan ta sa kai ta fice.
A hankali take taku tana jin gabanta na dokawa duk takun daya sai taji ya karu sosai a haka har ta isa soro nan ta ja burki ta tsaya tana mai da numfashi a hankali ta shiga kokarin daidaita kanta.
Motarsa dake girke gefe guda take sauke idanuwanta akanta sabuwa ce fil! sai daukar idanu take yi kamar yanzu aka gama ƙerata bakin glass din ta mai duhu wanda ya boye sirrin komai na cikin motar sosai taji gaban ya doka lokacin da ta fara takawa cikin sanyi jiki zuwa wajan motar ba abin da take ambata a zuciyar sai sunayen Allah.
"Yaa Rabb!".
Ta furta lokacin da wani kamshi mai karfi ya daki hancinta har sai da ta kusan dauke numfashi gabanta yayi wani irin bugu ta shiga ware idanu cikin yanayi na tsoro a fuskarta hannayenta biyu ta saka ta dafe goshinta da take ji kamar zai fice gefe daya wani irin abu ne taji zuciyarta ta buge ta dashi da bata yi tsammani ba dago idanunta tayi ta na saukewa akan motar a daidai lokacin shi kuma ya buɗe murfin yana zuru kafafuwansa masu dauke da wani haɗaɗɗen takalmi sau ciki mai kalar baki sai daukar idanu yake yi.
Gabanta ya cigaba da dokawa tana kara ware idanu so take yi ta karyata zuciyar da idanuwanta da suke kokarin wanzar mata da abin da ba tayi zato ba ko kadan a daidai wannan lokacin ba ta fada abin dake shirin faruwa a yanzu ya faru ba haka take so ba bashi tayi KUDIRI ta gani ba a daidai wannan lokacin.
"Dr.Aqeel".
Ta fadi da wani irin yanayi mai zurfi a zuciyarta da gangar jikinta numfashi take kokawa dashi da yake kokarin yanke mata tashin hankalin ta take jin ya karu ba kadan ba ba ta shirya ba bata shirya karbar wani tashin hankalin ba bayan wanda take ciki mai yasa zai mata haka mai yasa zai katse mata hanzarin ta mai yasa ya zo a daidai irin wannan lokacin da bai dace sam dashi ba mai yasa?.
A hankali ya gama fitowa yana mikewa kan kafafuwansa idanuwansa na kan Mariya dake tsaye kamar wacce aka dasa kwankwarar motsi ba tayi illa numfashinta da yake fita da sauri-sauri fuskarta a haɗe kamar hadarin dake shirin zubda ruwa a hakan kuma take yaƙe wanda yafi kuka ciwo.
Murmushi a fuskarsa mai girma duk da glass din da ya mannawa idanuwansa hakan bai hana ta hango tsakar idanun nasa ba kau da kai tayi da sauri tana jin yarda zuciyarta ke bugawa cikin wani irin yanayi mai girma in ba ta manta ba rabon ta dashi yau kusan wata shidda kenan tun wani zuwa da yayi da wani lamari mai girma da ta kasa fahimtarsa tun daga lokacin ya dauke kafarsa da zuwa gidan su da sunan ya bata lokaci tayi tunani akan lamarin da ya zo mata dashi Alal-hakika ta mance da wanzuwansa duk da dai tana jin sa a ranta amma abin da ya zo mata dashi tuni ta ajje shi gefe domin ita a tunanin haukar ta ba zai dawo ba tsokanar ta yake yi a sigar wasa amma ganinsa a yanzu ya dawo mata da komai tsoronta daya ya tuhumeta bata san mai zata ce dashi ba bata san ma ya za tayi da maganar ba domin ko a MIZANIN HANKALIn ta da ta daura bata ga komai ba.
"Mariya".
Ya fadi yana kara ƙawata fuskarsa da murmushi sanye yake da Suit light Blue wanda tayi matukar amsar jikinsa sosai hannu rike da hula mai kama da malfa baka haka takalmin kafarsa baki ne sai kyallin sabuntaka yake yi.
Tun daga kafafuwansa ta fara kallonsa har izuwa kirjinsa sosai shigar tasa ta burgeta ba kadan ba sai dai turaren da ya fesa ne yake hawa mata kai sosai ji takeyi kamar zata yi amai.
"Dama kai ne?".
Ta fadi tana mai tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta cikin wani irin yanayi na karfin hali.
Dubanta yayi cikin mamaki da kuma tuhuma yana sauke glass din idonsa sosai yake kallonta yana karantar yanayin da yake ganin ta a ciki sosai ya fuskanta kamar da matsala a tattare da ita lakari da yanayin da yarda ta nuna na rashin hayyaci a tattare da ita kuma ga idanunta da fuskarta a haɗe kamar hadari.
"Ba kiyi tsammani ba ko?".
Ya fadi yana daga mata gira da murmushi a fuskarsa kafun ya sake cewa,
"Akwai wanda kikayi tsammanin gani kenan ba ni ba?".
Ya sake jeho mata tambayar da ta sanya cikinta kaɗawa domin gabadaya a tsora ce take.
"Uhmm!?".
Ya sake fadi yana mai jingina da jikin motarsa bayan ya rufe.
Shiru ya gifta a tsakaninsu ba wanda ya sake cewa komai Dr.Aqeel dubanta yake yana jiran cewarta yana harɗe hannayensa a kirjinsa
Ita kuwa gabadaya ba ma ta san ya take ba komai nata a kwance yake laɓɓanta sai motsawa suke yi alamun ta na son cewa wani abu amma ta gagara idanunwanta har zuwa lokacin a kasa suke.
"Dr.Karami ya zo ko?".
Da sauri ta dago kai tana dubansa jin abin da yace idanunwanta take yawatawa a nasa wani abubuwa ne masu matukar girma take gani suna fitowa suna doso ta daga idanuwansa da sauri ta janye idanunta tana faman kokawa da numfashin ta da ke kokarin kufce mata.
"Uhmm nima yanzu na dawo makaranta Umma ke fada min amma ba mu hadu dashi ba".
Ta karashe tana yarfe hannaye kamar wacce ta taba wuta.
Sosai ya fuskanci ruɗanin da take ciki sosai ya gane in da yanayin da tashi ya dosa wato Dr.Karami tayi tunanin ya kira ta shi yasa ta fito cikin yanayi na hanzari amma ganin sa da tayi ya sanya komai nata kwancewa.
"Shi kika son gani ko Mariya, Dr.Karami kika so ki gani bani ba, na sani domin na gane hakan a tattare dake".
Sosai yaji wani irin abu mai girma ya tokare masa zuciya. Ya fuskanci Mariya hankalinta da natsuwarta suna tare da Dr.Karami tun da yake zuwa bai ta ganin rawar jiki ko wani ɗoki ba a game da ita amma yanzu ya gane in da tafi wayo sai dai kuma ba zai yarda da hakan ba.
"Mariya!".
Ya fadi da wata irin murya mai girma da zurfi da abubuwa masu yawa a ciki.
Ita kanta wani yanayi taji da salon da ya kira sunan nata komai taji ya zama kamar ruwa na jikinta yana narkewa zuciyarta ta yi wani irin zillo da wani abu mai girman gaske wanda ta jima tana a jiyarsa a zuciyarta a tsakaninta da Dr.Aqeel wanda har izuwa wannan lokaci bata san menene ba.
Sosai ya gyara tsayuwarsa don ji yake yi kamar zai tiku da kasa kansa yake ji yana sara masa da wani irin yanayi mai zafi bai san haka zata faru ba da bai bata lokacin sa ba da ya san haka zata kasance da ya mika bukatarsa tun wuri sosai da sosai zuciyarsa ta jima tana gargaɗin sa akan yayi abin da ya dace amma yayi ragwanci shi a tunanin sa ya raina yanayin Mariya bai san ba a nan lamarin yake ba yana cikin filin zuciya domin ita zuciya ba ruwanta da kankanta ko girma in ta nuna so da kulawa a abu to tabbas hakan ne.
Nisawa ya yi kafun ya furzar da wani huci mai zafi.
"Mariya wai shin mai ke damun ki ne ko dai ni din ne ba kya bukatar gani a filin rayuwarki?".
Ya fadi da wani irin yanayi mai zafi da nuna bacin rai hakan ya sanya Mariya saurin dagowa tana dubansa lokaci guda wani haske mai kama da kibiya ya fito daga idanuwansa ya sauka a nata.
'Yaa Rabb!'.
Ta furta jin yarda zuciyarta ke amsawa da wani irin yanayi mai girman gaske.
Girgiza kai ta shiga yi alamun ba haka bane.
"haka ne ma na gashi nan kin nuna min tun da na zo gabadaya na ga sauyawarki komai naki ya canza kamar bakya maraba dani ko na lura bani kika yi tsammanin gani ba nayi miki shigar sauri ".
"Kayi Hakuri Dr.Aqeel".
Ta fadi da rauni a muryarta kamar zata saki kuka laɓɓanta take motsawa alamun ta na so ta sake cewa wani abu amma zuciyarta taki bata dama.
"Ba maganar bada hakuri bane Mariya so nake yi ki buɗe baki sannan ki dube ni muyi magana so nake yi komai ya kasance a wannan lokaci so nake yi duk wani SIRRIN DAKE RAINA ki ji shi a yau so nake yi komai da yake cikin zuciya ki ji shi da kunnuwanki so nake yi ki bani dama na shigo rayuwarki mu kasance a INUWA DAYA".
A razane ta dago kai tana dubansa gabanta na daɗa faduwa ji take yi komai na duniyarta a lokacin yana wurgi da ita ta ko wani fanni ba ta san mai Dr.Aqeel yake kokarin dauko mata ya jeho mata a filin duniyar rayuwarta ba bata san wani irin tashin hankali bane yake kokarin jeho mata.
Tsoron ta ya karu sosai ta shiga gyaɗa kai wasu kwalla ne taji su na taruwa a idanuwanta wanda bata san dalilin su ba sosai zuciyarta take matsewa da zancen Dr.Aqeel wanda ba ta san yarda zata fassara yarda suke kasancewa a zuciyarta ba.
"Mai zai hana ki karba Mariya sannan ki koya kuma tun da nasan baki iya ba baki taba yi ba wannan shi First time dinki a cikin wannan lamarin ya kamata ki bani dama da yarda na tabbatar miki na san zaki karba kuma ki koya a lokacin da kika bani hadin kan ki na bayyana miki SIRRIN DAKE RAINA".
Zuciyarta taji ta yi wani irin harbawa gabadaya ta dago mata kirji sama hannu tasa ta dafe kirjin nata ji take yi kamar ta kurma ihu ko ta samu sa'ida amma ina ba za ta iya yin haka ba bata san mai ALKALAMIN ƘADDARARTA ke kokarin dauko mata ba da ya jona ta da Dr.Aqeel da wannan lamarin mai girman gaske.
"Ban san me kake nufi ba, ban san ina zancen ka ya saka gaba ba don Allah Dr.Aqeel...".
"Haba mana Mariya me yasa zaki fadi haka mai yasa kike kokarin dauko abin da kika san ba zan taba yarda dashi ba na sani kin ji ni sa rai kuma kin fahimta kawai karba ne ba zaki yi ba saboda baki yarda dani ba".
"Yaa Allah! haba mana Dr.Aqeel mai yasa kake fadin haka mai yasa kake kokarin kasa fahimta ta da ganga bayan kuma kasan ba haka lamarin yake ba".
Sosai yaji jikinsa yayi sanyi da maganganun Mariya dubanta yake yi da wani irin yanayi mai girma a zuciyarsa kafun ya nisa.
"Mariya mai zai hana mu fahimci junamu mu bai wa zuciyoyinmu damar fahimtar tsakanin su hakan ne kadai zai sanya lamarin da muke fuskanta ya zo mana da sauki a filin duniyar nan ta mu".
"Ta ya ya kake zaton haka zai kasance bayan kasan ni ba kowan kowa bace a duniyar nan".
"Ba abin da nake so naji daga gareki ba kenan Mariya ki daina kauce hanya yakamata ki tsaya a mataki daya wanda zai kawo mana mafita a tsakaninmu".
Shiru tayi tana tunanin abin da za ta ce dashi zuciyarta ta rabu gida biyu hankalinta ya karkata izuwa wajan Dr.Karami shi take bukatar gani shi take bukatar sanyawa a idanunta a wannan lokaci tafi bukatar dashi da kowa so take yi su gamu da juna ba ta san wani matsayi ya ajje ta ba bata san ko har yanzu ya na fushi da ita ba zuciyarta ta na sanar da ita har yanzu yana nan kan bakarsa tun da har ya iya zuwa bai neme ta ba kuma ya san inda zai same ta amma yayi birisda ita dan hakan tana cikin TSAKA MAI WUYA domin ta lura da Umma ita kanta ta nuna bacin ranta nunawa da tayi bata gane Dr.Karami ba to ina ga kuma ta san halin da suke ciki a tsakaninsu na bacin rai da ta sanya shi.
So take yi ta gujewa tashin hankalin da Dr.Aqeel ke kokarin turata a ciki domin kuwa zuciyarta gabadaya ta hargitse kwanyarta sai tururi take yi.
"Ki bani lokaci mana a lokacin da ke cikin rayuwarki na sani zaki fahimce ni nan gaba kadan".
Gƴaɗa kai take yi cikin rashin abin cewa bata san abin da zata ce dashi ba ta sani Dr.Aqeel yayi mata HALACCI bai kamata ta watsa masa kasa a ido ba bai kamata ta mance ALHERI da yayi mata ba a filin duniyar rayuwarta ba ma ita kadai ba har da iyayenta sai dai zuciyarta ba ta san matsayar da zata ajje shi ba bata san a wani matsayi yake ba a cikinta.
"Shikenan".
Ta fadi da wani irin nauyi mai girma a zuciyarta domin ita dai ba ta san mai zata ce dashi ba bata so ta fadi abin da zai sanya shi bacin rai ko ya tafi da fushin ta a zuciyarsa bata so ayi na biyu kamar Dr.Karami.
Gyaɗa kai kawai yayi yana mai sakin yaƙe sosai ya fuskanta Mariya na bukatar lokaci sosai take matakin koyon komai da yake nuna mata zai yi kokarin don ganar da ita komai yarda ya kamata ba ya so yayi sake a cikin wannan lamarin.
"Sai anjima ki gaida su Umma".
Ya fadi da murya mai sauti wanda tayi matukar tasiri a zuciyar Mariya ta saukar mata da kasala.
Tana kallon shi ya shiga motarsa ya bar layin tana bin sa da kallo har ya bacewa ganin ta kafun ta ja raunannan jikin ta ta koma cikin gida zuciya cike da rikici mai yawan gaske...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.
Ta jima sosai cikin soron gidan nasu tana jan numfashi, yanayin da take jin kanta a ciki a wannan lokacin ba zata iya cewa ga yarda yake ba ta san dai tana cikin wani irin yanayi na rashin natsuwa gami da ciwon rai.
Bata san ya zata yi da Dr.Aqeel ba bata san mai ya kamata tayi masa ba zuciyarta take jin tana shiga wani irin mataki mai raunin gaske yana haifar mata da yanayi na shiga ruɗani sosai take jin wani fili a zuciyarta ya na baiwa Dr.Aqeel matsayi da kalamansa wanda take jin su sun fi komai daga mata hankalin a wannan rana.
Hannunta daya ta saka cikin baki tana cizawa kafun ta fiddo shi tana yarfewa fuskarta na ya mutsewa da wani irin yanayi mai girman gaske a gareta. Ta jima kafun ta fara jan kafafuwanta da take jin su kamar ba nata ba kamar ba jikinta suke ba sosai take jin gajiya a cikin su ji take yi kamar za su watsar da ita kasa a hankali ta kai hannunta ta dafa bango tana tafiya a hankali har ta karasa shigewa cikin gidan.
"Na ce karuwanci kike koyawa 'yarki tana bin gardawa kamar wata karya kin ce ba haka ba yanzu me ne ne wannan Iyee nace yanzu menene wannan ai duk wanda ya ga wadannan kayan ya san da walakin goro a miya ba yarda za ayi a dauki wannan uba uban kayan a baku su haka zikau ba tare da kuma an ci ribar ku ba".
Maganganun da suka shiga dukan kunnuwan Mariya kenan a daidai lokacin da ta iso tsakar gidan ta tsinkayo muryar Goggo Marka cikin dakin su wani tashin hankali ne taji zuciyarta da kwanyarta sun dauka lokaci guda sun tsaya cak! da aikin da sukeyi lokaci guda duk wani magudanan jinin ta suka tsaya komai nata take jin sa ya sauya ji take yi kamar ba a duniyar nan take ba ji take yi kamar ba RAI DA RUHI a gangar jikinta juwa taji ta fara daukarta lokaci guda ta durkushe a wajan cikin wani yanayi tana mai jan numfashi da k'yar yana fizgar kansa shi kuka take so tayi amma zuciyarta da idanuwanta sun ki bata damar haka sai zafi da raɗaɗi da take jin sunayi kamar zasu tayar da kan su daga gareta.
Hannayenta ta saka a saman kirjinta tana shafawa domin ji take kamar ya tarwatse gabadaya idanuwanta a runtse a hankali ta fara kokarin tashi tana jin yarda kirjin nata yayi mata wani irin nauyi da abu mai girman gaske wanda take jin yana rinjayarta.
"Kin ce 'yar ki makaranta take yi ita ga wacce ta fi kowa son ilmi ko yanzu tsakanin ki da Allah Habeeba wannan shine makarantar da take zuwa don na tabbata a hanyar fitar da take yi ne ta hadu da wanda yayi mata wannan hidimar kuma na tabbata ba haka kawai bane sai da ta biyasa kafun ya bayar".
'Yaa zuljalalu wal'Ikram Ya Hayyu Yaa Kayyum'.
Abin da take jin wani sashi na zuciyarta na fadi kenan har ta iso bakin kofar ta tokare hannayenta a saman goshinta ji take yi kanta kamar zai tarwatse idanuwanta a runtse ta shiga ajje numfashi mai girma gaske wani abu taji ya zo mata makoshi ya tsaya tana jin yarda yake kartar mata ko ina na kirjinta har zuwa makoshi.
"Haba mana Goggo Marka ta ya kike tunanin zan jefa 'yar da na haifa a cikina cikin wannan mugun yanayi ribar mai zan samu a ciki".
Muryar Umma ta tsinkayo ta fadin haka muryarta cikin yanayi mai kama da kuka da sauri ta dago kanta ta ware idanunta kafun ta dage labulan dakin tsaye ta hango Goggo Marka sai faman tsaki take ja tana jifan Umma da mugun kallo jin motsi ne ya sanyata juyowa ganin Mariya ya sanya ta sakin wani murmushi na mugun kafun ta shiga tafa hannayenta.
"Uhmm a hakan kamar gaske musa a baki fir'auna a zuci".
Ta fadi tana yatsine fuska kafun ta dan rangwafa inda kayan suke tana bincike kafun ta shiga ware wasu a gefe guda sai da ta ware masu isarta sannan ta sunguma tana duban su Umma.
"To mu ma dai bari mu ci albarkar kacin bariki ko kin san ko ina kayan alheri suke dadi gare su Allah ya karo mana irin su masu kyautatawa".
Ta na gama fadin haka tayi hanyar yo wa waje Mariya da tayi sumar tsaye bangazar da taji anyi mata ya dawo da ita hayyacinta a rikice ta dubi Goggo Marka sannan ta dubi Umma wacce ta zabga tagumi hawaye sai shatata suke yi a fuskarta bakin ciki da takaicin duniya duk sun cike mata zuciya gabadaya ta hargitse sosai fuskarta ta ke nuni da tsananin tashin hankalin da take ciki ganin Mariya na dubanta ya sanyata saurin dauke hawayen da suke zubo mata tana sakin wani yake wanda yafi kuka ciwo.
Wani irin kuka ne Mariya taji yana zo mata a daidai wannan lokacin hannu ta saka ta toshe bakinta tana karasawa cikin dakin durkushewa tayi gaban Umma da wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske laɓɓanta na rawa ta shiga motsa su.
"Na Shiga Uku wanna wacce irin rayuwa ce take kokarin tunkaromu a daidai wannan lokacin wannan wani irin yanayi ne mai sanya ciwon rai ya sanyo mu gaba".
Hannu Umma ta daga mata alamun tayi shiru kafun ta fara magana cikin yanayi na rauni.
"Ni ban ga abin shiga uku ba don haka ki daina ambatar mana Uku a nan kin ji ko kina dai bata hawayenki ki share su domin in har kika ce zaki cigaba da zubda su to na tabbata zaki shekara dubu a haka in dai kina cikin wannan rayuwar duniyar nan".
Fakare tayi da kunnuwa ta zubawa Umma idanu kamar wacce taga bakuwar fuska kafun ta shiga jan hanci kamar zata fizgeshi daga fuskanta.
"Haka nake nufi domin kuwa in har kace ba zaka dauki abin da ALKALAMIN ƘADDARA ya kawo maka rayuwa ba to kana tare da tashin hankali mai girman gaske".
Hawaye suka sake balle mata domin ji tayi komai ya kwance mata zuciyarta na wani irin zugi da raɗaɗi.
"Amma Umma..".
"Haba mana Mariya".
Tayi sauri katseta kafun ta ja numfashi da take jin sa da wani irin yanayi mai zafi gaske.
"Ina kika baro shi".
Runtse idanu tayi jin zuciya ta bugu kafun ta ciza laɓɓanta tana jin wani abu mai nauyin gaske na danne mata kirji da zuciya.
"Ba shi bane".
Ta fadi a raunane kamar zata fashe da wani sabon kukan wanda ya fi wanda ta gama ciwo.
Ware idanu Umma tayi cike da mamaki jin abin da Mariya tace.
"Kamar ya bashi bane to waye?".
Kamar ba zata ansa ta ba sai kuma tana ja numfashi ta fesar.
"Dr.Aqeel ne".
Duban sosai Umma ta shiga yi mata kamar mai son karin bayani akan abin da ta fadi yanayin da ta nuna ya tabbatar mata akwai abin da yake faruwa ganin sai yatsi ne fuska take yi tana cizon laɓɓa.
"Me ke faruwa na ga sai dakune fuska ki ke yi?".
"Bakomai yace yana gaishe ki".
"Mariya!".
Umma tafadi cikin wata irin murya mai zurfi har sai da gaban Mariya ya yanke ya fadi dago idanuwanta tayi da suke kasa ta dubi Umma da tayi mata kuri da Idanu da tuhuma cikinsu.
"Akwai abinda ke damun ki bayan Dr.Karami ki fada min ina bukatar sanin ko mene ne na gaji da wannan halin da kika aro ki ka saka a filin rayuwarki wanda sam! ban ga amfaninsa ba".
Gyaɗa kai ta shiga yi kamar zata rushe da kuka zuciyarta da kwakwalwarta take jin su kamar za su kama da wuta saboda wani irin tashin hankali mai dauke da turiri take ji yana wanzuwa acikinsu.
"da ke nake magana Mariya na gaji fa".
"Umma!".
Ta fadi cikin wani irin yanayi da rauri a muryarta kafun ta nisa ta na cizon laɓɓanta.
"ba abin da yake damu na...".
"ban yarda ba...shikenan ma komai ya shige ki bar komai a zuciyar ki hakan daidai ne".
Umma ta fadi tana mai kokarin mikewa kayan dake tsakar dakin ta shiga janyewa tana ajewa gefe guda ganin haka da Mariya tayi ta san Umma haushin taji shiyasa ta rabu da ita da sauri ta mike tana kokarin taya Umma kwashe kayan hannu ta daga mata ba tare da ta kalle ta ba.
"Bar shi kawai ki zauna ki yi tunanin abin da ya dace ki fidda kan ki daga damuwar da kike ciki tun da bakya bukatar abokin shawara a filin a rayuwarki".
Jikin ta lokaci guda yayi sanyi jin abin da Umma tace hannu ta sa tana goge kwallar da taji sun kawo mata ziyara idanuwa.
"Kiyi hakuri Umma..".
"ni ba kiyi mani komai ba Mariya ki je ki zauna ki huta ni na bukaci haka".
Ba yarda ta iya domin yarda ta ga Umma na maganar ta san har kasar zuciyarta don haka a hankali ta ja jiki ta zauna in da Mu'azzam ke kwance yana faman barci abun sa.
Bata san mai ya dace tayi ba, ba ta san mai ya kamata ace tayi a filin duniyar rayuwarta a yanzu ba komai take ji yana sauya wa komai take ji yana canzawa a filin rayuwarta ji take yi kamar ba ita ba jikinta take ji yana yi mata wani iri kamar wacce bata da lafiya zuciyarta take ji tana yi mata nauyi kamar wacce aka daura dutsen dala.
Ta jima cikin wannan yanayin kafun ta lura da har Umma ta gama kwashe kayan ta bar mata daki hannu bibbiyu ta daura a fuskarta ta zabga tagumi domin kuwa gabadaya take jin tunanin ta ya tsaya komai na ta ya tsaya cak! ba abin da take hangowa sai tashin hankalin dake gabanta yanzu bata san ina Dr.Karami yake ba a yanzu tsoron ta daya kar ya sake komawa ba tare da sun hadu da juna ba.
*******
"Umma Zan je gidan su Baseera".
Mariya ta fadi cikin yanayi na fargaban abin da Umma zata ce domin tun jiya da ta shareta har yau bata sake tsayawa sun yi wata magana mai tsayi ba bayan gaisuwa da tayi mata da safe.
"Allah ya kiyaye hanya ki gaida Hajiyar ta Baseera".
Abin da ta fadi kenan ba tare da ta dube ta ba hakan ya sanyayata jikin Mariya ta shiga gyaɗa kai da susar gefen fuskarta kafun ta shiga motsa baki.
"Umma don Allah kiyi hakuri...".
"Mariya haba mana nace miki bakomai ki tafi kawai".
Jin abin da tace ya sanya ta duban Mu'azzam dake hannun Umma hannunta kai ta shafi fuskarsa tana sakar masa murmushi kafun taja jiki ta fice daga cikin dakin.
A tsakar gida ta tsaya tana gyara hijabin dake jikinta domin ji take yi kamar bai zauna daidai ba a hankalinta juya ta dubi bangaren su Goggo Marka Hafsi ta hango tsaye daga ita sai daurin kirji kamar wata uwar mata ta kafe ta da idanu tana faman yatsine fuska kau da kai tayi kamar bata ganta ba da sauri ta zira takalmanta ta fice daga cikin gidan domin a yarda take jin kanta ba ta bukatar wata magana ta sake shiga tsakanin ta da wani har ta isa gidan su Baseera.
Tafiya take yi a hankali domin isa bakin layi ko za ta samu napep din da zai kai ta Unguwarsu Baseera taji take yi zuciyarta da kwanyarta sai faman dauko mata tunani suke yi wanda sam bata so ace sune a kanta ba yanzu.
Kamar daga sama taji ana yi mata Horn bata yi tunanin da ita ake ba hakan ya sanyata kara sauri tana komawa gefe duk a tunanin ta wani ne a bayan ta yake mata horn domin ta bashi hanya amma ina ta ji an ci gaba da yi ba kankautawa hakan ya sanyata tsaya wa cak! waje daya tana daga kanta don dubin ganin abin da ke faruwa motar Huzaif ta hango yayi parking yana kokarin fitowa wata irin faduwar gaba taji tana zo mata lokaci guda wanda ita a karan kanta ba zata ce ga dalili.
Dubansa ta shiga yi cikin wani irin yanayi wanda ba za ta ce gashi ba amma dai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa a dukkanin sakan idanuwanta take yawatawa a kasa tana tunano yaushe rabon ta dashi sun kwana biyu ba su hadu ba sosai ta lura da yanayinsa kamar mara lafiya domin tafiyar ma kamar mai koyanta haka yake yin ta har ya iso in da take tsaye tana faman jan numfashi.
Lokaci guda idanuwansu suka sarƙe da juna aka rasa mai dauke nasa tsayin lokaci suna a haka kafun Mariya ta ja dogon numfashi ta fesar fuskar ta cikin yanayi na karan kadahan.
"Uhmm Huzaif dama kana duniyar nan".
Hakan da ta fadi da yanayin da tayi maganar ba karamin sanya Huzaif cikin wani irin yanayi mai armashi a hankali ya shiga motsa laɓɓansa fuskarsa na wanzar da wani farinciki mai dauke da fara'a jan numfashi yake yi yana fesar wa idanunsa akan Mariya zuciyarsa yake ji tana daukar kanta tana kaiwa wani mataki mai girman gaske yanayin da yake kallon Mariya wani farin ciki da muradan jindadi yake jin sa a ciki.
Ya sani yayi kewar Mariya ba kadan ba zuciyarsa tayi jinyar rashin ta sosai ya shiga cikin wani hali na rashin jindadi sosai duniyar yake jin ta wani mataki a kwanakin baya da yake zaune yana jinyar kan sa dalilin rashin lafiyar da ta same shi.
" Baki damu dani ba Mariya shiyasa sam rashi na bai d'ad'a ki da kasa ba".
Ya fadi yana mai dan haɗe rai kanta ta dago ta dube shi tana mai yatsine fuska kafun ta ja numfashi.
"akan mi zaka ce haka wa na sani na ka da zan tambaya ina kake so naje ko so kake yi na bi layi ina cigiyar ka Huzaif bai dace ka yi mani wannan maganar ba sam".
Kuri yayi mata da idanu yana kallon yarda take motsa laɓɓanta kalamai na fitowa wani irin farin ciki yake ji yana sake zundumawa a ciki.
"Allah ya baki hakuri amma dai zaman tare ai bai ce haka ba ko?".
Ya fadi yana murmushi kau da kai tayi tana mai yatsine fuska sam bata bukatar magana ba ta so ace ta sake gamuwa da wani a daidai wannan lokacin ba tafi bukatar su hadu da Baseera domin ita kadai ne take so su zauna domin sanin abin da ya dace ita kadai take tunanin zata fada wa abin da yake kokarin faruwa da ita ko ma tace ya faru da ita...
"Ina su Umma da Mu'azzam?".
Maganar Huzaif ta katse mata tunanin da ta jefa kanta a ciki.
"Uhmm suna gida suna lafiya".
Ta fadi tana kokarin raɓashi ta wuce ganin haka ya sanya shi saurin dubanta.
"Meye haka kuma Mariya yake kike kokarin tafiya...wai ma ina zaki kike wannan saurin".
Yanayin da yayi maganar kamar da bacin rai a ciki ita hakan ita ma ya so bata mata rai jin irin tambayar da yake yi mata kamar shi ne ya ajje ta ba ta ansa shi ba illa duban sa da tayi ta kau da kanta.
"Ina Zaki je ne?".
Ya fadi ganin kamar ranta ya so baci yayi kasa da muryar.
"Unguwa zani shiyasa nake sauri bana so na bata lokaci a bakin titi".
Gyaɗa kai yayi yana dubanta kafun ya numfasa cikin d'ard'dar.
"muje mana in kai ki ko".
Wani duba tayi masa wanda sai da yaji yan cikin sa sun motsa dama ya san za ayi haka da sauri ya kau da kai don ba zai iya jure irin kallon da take masa ba zuciyarsa wani irin yanayi take fadawa mai girman gaske.
"Don Allah mana".
Ya sake fadi yana mai hada hannayensa waje daya alamun roko.
Girgiza kai tashiga yi tana mai taku a hankali za ta bar wajan gabanta yasha yana mai harɗe hannayensa a kirjinsa idanuwansa ana ta tana watsa masa kallon ban son haka.
"Mariya wai shin ko laifi na sake yi ne ake kokarin hukunta ni ta wannan hanyar?".
"ko daya kawai dai bana ra'ayin abin da ka zo mani dashi ne nagode kawai kayi tafiyarka".
Ware idanu yayi jin abin da tace sosai yake dubanta yana kallon yadda ta kara haɗe fuska kamar hadari amma hakan bai hana kyanta ƙara bayyana ba wani irin kwarjini yake ganin tana yi masa wanda ya shagalar dashi ga kallon ta har bai san lokacin da ta raɓashi ta wuce ba.
Firgigin yayi ya dawo hayyacin sa ganin bata wajan ya yi saurin juyawa can ya hange ta tayi nisa dashi kadan.'Yaa Rabbi'.
Ya ambata yana takunsa cikin hanzari ya isa in da motasa take ya shige tare da yi mata key bayan yayi ribas ya bi bayan ta da gudu cikin yan sakanni ya isa in da take tsaye tana kokarin tsaida wani mai Napep parking yayi ya fito ya iso in da take tsaye suna magana da mai Napep din ba tare da yace mata komai ba yace dubi mai Napep din.
"Yi hakuri don Allah yi tafiyarka".
Ya fadi yana mai hade fuska da sauri Mariya ta juyo ta dubeshi da wani irin kallo ganin yarda ya hade fuska ita ma sai ta hade.
"Ya haka ya za ayi in tsaida abun hawa ka ce ya tafi ina ruwan ka dashi?".
Bai tanka mata ba illa nuni da yayi mata da motarsa alamun ta je ta shiga.
"Ba zan shiga ba kaji ko Allah ba in da zani Huzaif bana bukatar takurawa bana son abin da zai bata mutuncin junanmu".
"kawai Malama ki je ki shiga mu tafi ya za ayi ace ina waje kuma ga abin hawa a tare dani amma ki tare wani mai Napep wannan ai ba mutuncin ki bake".
'Ikon Allah'.
Ta fadi a ranta ta na sakin guntun murmushi kafun ta dubi Huzaif da ya haɗe rai kamar wani hadarin dake shirin zubda ruwa.
"wai don Allah Huzaif me yasa kake son takura mani ne na ce maka nagode ba zan shiga motarka ba to ka hakura mana".
"Ban san wannan zancen ba kisan Allah in har baki shiga mun je ba sai dai mu kwana a nan in zaki tsaida Napep dari sai na kore su".
Ware idanu tayi cikin yanayi na mamaki na karfi halin Huzaif ita abin ma dariya ya so ya bata.
Bata ga dalilin da zai sanya shi takura mata ba akan sai tayi abin da yake so shi ba mijinta ba shi ba ubanta ba amma ya kafe da bata Umarni.
Duban sa tayi ganin ya harɗe hannayenda ya jingina da gaban motarsa sai faman kaɗa kafa yake yi fuska a tamke ba alamun wasa kuma ta lura da gaske yake yi din sai dai su kwana a nan.
Wani tunani ne ya fado mata da sauri ta dube shi cikin mika wuya domin ta tabbata maganarsa da ya fadi tsaf zai aikata ita kuwa ta tsani tsayawa bakin titi ba ma wannan ba lokaci tafiya yake yi kuma in har ta jima bata koma gida ba dole ta fuskanci fushi a wajan Umma da ma ya ya ta barota balle kuma yanzu ta kara wani laifin ai sai abin yayi yawa shege da hauka.
Tsuke fuska tayi kamar hadari ita ma sannan ta isa wajansa tana mai kau da kai tana turo baki gaba hakan ba karamar dariya ya baiwa Huzaif ba amma sai ya kanne domin ya san in har yayi dariya zainl iya bata shirin nasa a hankali ya dube ta cikin danne dariyar da take kawo masa hari.
"To ya yan mata muje ne ko kuma mu cigaba da zama a nan har mahadi ya bayyana?".
wata harara ta watsa masa bai san lokacin da ya saki dariya ba har da buga kafa ya isa ya bude mata gidan gama yayi mata alamun ta zo ta shiga.
Ware idanu tayi kafun ta kau da kai.
"nikam ba zan shiga gaba ba baya zan shiga".
Dubanta yayi ganin da gaske take ba za tashiga ba cikin yanayi na zolaya ya dube ta.
"Kuturu mana..."
"A'uzubillahi minal shaidanir rajim zagi Huzaif".
Ta fadi tana ware idanunwanta akansa shima zaro idanu yayi yana faman gyada kai.
"Uhm Uhm fa kar ki fassara ni Malama ni ba zagi zan yi ba".
Harara ta wurga masa kafun ta isa wajan motar ta buɗe gidan baya ta shige.
Dariya yake yi mata ganin yanayin da ta nuna kamar zai hana ta shiga.
Shiga yayi shima ya na fadin.
"wato kin mai dani direban ki ko?".
Ko kallon sa ba tayi ba kanta na bakin kofar tana kallon waje har yayi wa motar key kafun ya tambaya ne ta in da sukayi
"Pabeyi".
Yanayin da ta fadi sunan Unguwar tana turo baki gaba sai ya bashi dariya ita ala dole fushi take yi dashi da gasken gaske.
Tafiya sukayi ta tsayin mintuna biyu ba wanda ya yi magana a tsakanin su ba abin da ke tashi cikin motar sai wakar 'Because of You' ta Amanda Mena sosai wakar ta tafi da hankalin Mariya don sosai taji muryar mawakiyar da yarda take sarrafa kalaman ta sun burgeta lokaci guda taji kaunar mawakiyar ya dalsu a zuciyarta ji take yi kamar ta tambayi Huzaif wace ce ita amma ba za ta iya wannan ganganci ba yanzu ji take yi kamar tana zaune akan k'aya.
"Mariya"
Kamar daga sama taji muryar Huzaif ya furta hakan gabanta taji ya yanke ya fadi ta madubin gaban motar ta hango irin kallon da yake yi mata ba tare da sani ba ba ta ansa shi ba illa idanu da suka hada da sauri ta dauke kanta tana jin gabanta na cigaba da bugawa.
"me yasa wai har yanzu baki yarda dani bane na lura mafi akasari in muna tare bakya sakin jikin dani kamar zan cutar dake".
Gyada kai tayi ba tare da tayi masa magana ba lokaci guda ta shashantar da maganar ma ta na nuna masa hanyar da za ta kai su layin su Baseera.
"Ya kamata ki bani hankalin ki nan magana nake so muyi ta fahimtar juna a tsakanina da ke".
Da sauri ta dubeshi jin abin da yace gabanta lokaci guda ya yanke ya fadi ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Dr.Aqeel da yanayin da suka kasance a tsakanin ta dashi a jiya maganganun sa ne suka shiga dawo mata kamar yanzu suka yi su gabanta ya cigaba da tsanar ta faduwa zuciyarta na dauko mata wani lamari mai girman gaske wanda yake kara sanyaya mata jiki numfashi ta shiga ja a hankali kafun ta sake daga kai ta dubeshi har zuwa lokacin idanuwansa na kanta wani abu mai girman gaske take hangowa a idanuwansa wanda suke ruɗa mata nata idanun da sauri ta dauke kai jin da tayi numfashin ta na fizga kamar zai fice daga gangar jikin ta lokaci guda ta ji nadama ta saukar mata ba ta san abin da yasa ta tsaya da Huzaif ba ta san abin da ya kai ta shiga motarsa ba har yake kokarin firgita ta.
"ba zan boye miki ba Mariya ina cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa ban san ta ya ya zan fada miki halin da nake ciki ba zuciyata tana cikin wani hali mai girman gaske Mariya komai na faruwa ne a dalilinki".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Abin da taji bakin ta na fadi kenan daga nan bata san wata duniyar kuma ta fada ba sai da ta shafe sakanni kafun ta dawo hayyacin ta dauke da tashin hankali sosai taji ana hajijiya da ita ji take yi kamar tana saman gajimare ana yawo da ita kwanyarta taji ta tsaya cak! da aiki zuciyarta na wani irin bugu kamar zata faso kirji ta fito a hankali ta dago kanta tana duban kofar motar Huzaif ganin sun shiga layin su Baseera ta fara kokarin tsaida shi domin ya sauke ta a yanayin da take jin kanta ko sakan bata fata ta sake yi a cikin wannan motar domin kuwa ji take yi kamar an daura ta a kan KASKON WUTA.
Idanuwanta ne sauka sauka kan wata dalleliyar mota sabuwa fil sai kyalli take yi haska rana na kara haskata hannu ta sa ta rufe idanuwanta domin sosai motar ta haske mata fuska da kyallin haka kawai taji gabanta ya fadi sannan kuma tana son kallon motar ware idanu tayi har motar ta karasa fitowa daga get din gidan su Baseera tana kokarin barin layin sosai take kallon motar har ta iso daidai in da suke shi kansa Huzaif hankalinsa ya tafi wajan motar sosai.
"Yaa Allah".
Mariya ta furta da wani irin yanayi domin bugun da taji gabanta yayi sosai glass din motar a dage yake kuma gashi mai duhu ba ka gano wanda yake cikin motar hakan ya dan bata ran Mariya duk da tashin hankalin da take ciki ta so ace ta ga waye a cikin motar domin zuciyarta sosai ta kwadaitu da son ganin ko waye.
"ajje ni a nan".
Mariya ta fadi tana mai dafe kanta da sauri ya dawo da hankalinsa gareta ya dubanta ganin hankalinta bai gareshi hakan ya bashi damar sake kare mata kallo kafun yace.
"Ina son magana dake Mariya ki bani lokaci ko ya ya ne".
"Please don Allah Huzaif ka barni da naji da abin da yake damu na bani da lokacin da zan iya zama naji abin da zaka fadi don Allah ka kyale ni".
Ta karashe tana kokarin buɗe motar ta fice.
"Mariya!".
Cak! ta tsaya ba tare da ta karasa ficewa ba a hankali ta juya ta dubeshi ganin yanayin da yake ba karamin faduwa gaba taji ba da sauri ta fice daga cikin motar har tana kokarin faduwa ko tsayawa dubansa bata yi ba ta doshi gidan su Baseera cikin yanayi na rashin hayyaci sai faman hada hanya take yi kamar wacce ta sha kaya maye...
*_KAMALA MINNA_*😍😍😍
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.
Mariya ta jima tsaye bakin get domin daidai kanta, sosai ta shiga tashin hankali komai taji yana kwance mata. tsayuwar ta a nan shine kawai take ganin mafita domin in har ta cigaba da tafiya zubewa zatayi warwas a kasa, domin kuwa kafafuwanta take ji suna harɗewa kamar an narka roba.
Numfashi take ja ta na saukewa kafun ta sanya hannu tana kwankwasa Get din a yan sakanni mai gadi ya iso sai da ya leko ta 'yar karamar kofar dake jiki ya ga wacece sannan ya zo ya buɗe karamar kofar yana bin Mariya da kallo fuskarsa da fara'a da alamun ya santa dama.
Gaidashi tayi kafun ta juyo ta dubi in da Huzaif yake abin mamaki tsaye ta hango shi ya harɗe hannayensa idanuwansa na in da take tsaye saurin dauke kai tayi tana mai cusa kanta cikin gidan bayan ta gaida baba maigadi.
Huzaif ganin ta shige cikin gidan hakan ya sanya shi dukan jikin motarsa da wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske.
Zuciyarsa yake ji tana wani karta masa kamar an saka kaifaffiyar wuka ana yayyagawa idanuwansa sun kad'a sun yi jajir kamar wanda akayi wa surace da barkono hannayensa ya daura saman kansa yana dafewa ji yake yi kamar zai tarwatse komai yaji yana kwance masa duniyar yake ji ta ishe shi ba san mai ya dace yayi ba bai san abin da ya kamata ace yayi a daidai wannan lokacin ba akan Mariya.
Ya sani zuciyarsa ba karamar wauta da ganganci tayi masa ba wanda bai san ya zai yi ba in har Mariya ba ta dubeshi ta anshi abin da ya zo mata dashi ba dole filin duniyar rayuwarsa ya kasance cikin tashin hankali mai girma.
A hankali ya fara taka kafafuwansa kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yana jan numfashi da yake jinsa kamar zai gushe masa isa yayi ya bude motar ya shiga sai da ya shafe mintina kansa haɗe da sitiyari domin ji yake yi kamar ba zai iya tukin ba gabadaya a haka ya ja motar yana mai ficewa daga cikin unguwar domin dai ba zai iya tsayawa ba don ya tabbata Mariya ko ta fito ba hawa motar tashi za tayi ba a yanayin da ya ga ta nuna akwai alamun tashin hankali da bacin rai mai girma tare da ita yana zaton laifin sa ne kuma ba na kowa ba da wannan tunanin zucin ya bar unguwar gabadaya.
Da Sallama ta shiga cikin babban falon yanayin ta kawai zaka kalla kasan akwai abin da ke damun ta a zuciyarta.
Sakanni ta shafe kafun a ansata a bata izinin shiga
Tunda ta saka kafarta cikin falon ta lura akwai mutane da yawa a ciki ba kamar daba da take zuwa ta samu Mami kawai ko Baseera amma yau abun ya sauya da alamun anyi bak'i.
Ba ta san ta karasa cikin falon ba sai da taji muryar Mami nayi mata sannu da zuwa da sauri ta gayyato natsuwa ta azawa kanta sosai ta shiga cikin wani yanayi ganin duk mutanan dakin ita suke kallo a hankali ta fara takawa ta isa cikin falon sosai tana mai zubewa ta gaishe da Mami sanna ta gaida mace da namijin da taka gani wanda kallo daya tayi musu ta gane suna da alak'a da Mami domin ga kama nan da suke yi da Baseera musamman ma namijin.
"Mariya ke ce a gidan namu yau?".
Gyada kai tayi tana faman yake don ta san da biyu Mami tayi mata magana na kin son zuwan ta gidan nasu sai dai Baseera taje nasu Mami ta sha turawa Mariya ta zo amma sai taki zuwa amma kuma ba laifin ta bane Umma ce ta nuna rashin yardarta don bata son shige-shigen nan musamman gida irin na su Mami masu farcen susa sai ayi wani tunanin daban ko wani abu ke kawo ta.
"Uhmm Mami dafatan na same ku lafiya?".
"Lafiya lau Mariya ya su Umman da Mu'azzam".
"Duk suna lafiya Umma tace na gaishe ki sosai da sosai".
"Madalla ina ansawa".
Daga nan ba wanda ya sake yin magana Mariya na son tambayar Baseera don bata ganta a falon ba amma duk sai taji ta kasa nauyin mutanan dake zaune take ji.
"Yusra yau dai Allah ya hadaku da 'yar gidan mutuniyar taki ga Mariya nan da ake tayi miki kwakwazo akanta".
Wacce aka kira da Yusra din da sauri ta dago kanta daga kan waya fuskar da fara'a kallo daya za kayi mata ka gane JINI DAYA suke da Baseera matashiya ce wacce ba zata haura shekaru talatin a duniya ba da alamun ma tana da aure akan ta domin akwai jariri wanda bai haura wata shidda ba a gefenta yana barci.
"Masha Allah ashe dai Aku mai magana ba tayi karya ba Mariya Sannu ko ya su Umma?".
Mariya dake sunkuye da kai ta dago tana duban Yusra sosai tana mamakin yarda take yi mata magana cikin sakin jiki da fara'a da alamun dai wannan a jini su yake dukkan su ita ma Mami haka take haka ma Dady da wuya ka ga fushin sa gyada kai Mariya tayi tana ansa ta kafun ta sake gaishe ta fuska ita ma a sake.
"Mutuniyar taki tana sama dakinta tun dazu ta shiga ban san abin da take kintsawa ba".
Murmushi Mariya tayi kafun ta mike ta bi hanyar da za ta sada ta da dakin Baseera.
"Ba ki ji ba Mariya".
Mami ta fadi hakan ya sanya Mariya saurin tsayawa ta juyo ta na duban Mami.
"wadannan duk yayin Baseera ne wannan shine Babban su Babban d'ana kenan su nan sa Tareeq ita kuma wannan Yusra tana aure a Abuja shi kuma Tareeq yana karatu ne a kasar waje".
Gyada kai take yi tana faman sakin murmushi tunda Umma ta fara yi mata bayani mai da kanta tayi kan su tana kara dubansu.
Da sauri ta isa wajan Yusra kamar wacce aka tura ta isa wajan jaririyar dake kwance ta shafa mata kai kafun su hada ido da Yusra ta sakar mata murmushi.
"Dauke ta mana".
Kamar abin da take jira kenan ta sanya hannu ta dauka tana faman sakin yake ita ana ta ganin murnushi take yi kamar wanda aka matsawar baki.
"Yah Yusra yariyarki mai kyau kamar Mu'azzam din mu ya sunanta?".
Dariya Mami tayi kafun ta dubi Yusra da ta kafe Mariya da ido ganin yarda take barin jiki akan 'yar ta duk sai taji Mariya ta kwanta mata a zuciya sosai da sosai.
"Mariya wai dama kina magana haka".
Mami ta fadi cikin mamaki.
Da sauri tayi kasa da kai alamun jin kunya tana kokarin juyawa ta haye sama.
"Sunanta Nawwara".
Yusra ta fadi da tausassan murmushi a fuskarta.
A hankali Mariya ta juyo ta dube su kafun ta sauke ganin ta kan Tareeq wanda ko kallon ta bai yi ba tun da tashigo har ga Allah taji zafin yanayin da ya nuna mata bata son mutum irin haka mai shariya duk hakan ta dauke shi a matsayin wulakanci ne a filin rayuwarta.
Dago kai tayi da zumar barin wajan caraf! suka hada ido da Mami rausayar da kai tayi da alamun ita ma Mami ta lura da halin-ko-in-kula da Tareeq ya nuna don haka tayi mata alamu da ido tayi hakuri kar ta damu.
A hankali taja jiki ta bar falon tana jin Yusra na yabata a kan yanayin da ta nuna mata akan Nawwara da ita kanta.
A baje ta same ta tsakar gadonta duk ta warwatsa littattafai kamar wacce aka yi wa dole sai ta karance su a lokacin. Mariya bata san lokacin da ta saki dariya ba tana isa cikin dakin sosai.
Dariyar ce ta fargar da Baseera da sauri ta daga kai ganin Mariya ya sanya ta sakin wata kara tana dirow daga kan gadon gabadaya tayo kanta ganin haka ya sanya Mariya matsawa gefe don ta san karamin aikin ta ne tace zata rungume ta kuma ga jaririya a hannunta.
"Uhm Uhm yau anyi kyan kai kenan, Mariya yau kece a gidanmu?".
Ta fadi tana galla mata harara kamar idanunta za su fado kasa.
"Uhmm ni fa matsala ta dake wani lokacin hankali yawa yake yi miki yasin baki ganni da Yarinya bane zaki fado kai na".
Yatsine fuska tayi kafun ta dubi Nawwara.
"Hala Adda Yusra ce ta hadaki da wannan 'yar ta ta mai shegen kuka kamar gyare?".
Ware ido Mariya tayi.
"Nawwara din ce mai kuka".
"Yo eh mana ba ta gajiya da kuka yanzu ma don tana barci ne amma yasin ta tashi ko Hmm sai kin mai da ita wajan uwarta nima abin da ya koro ni daga falon kenan kukanta tun dazu take abu guda kamar cin kwan makauniya".
"ikon Allah gani da gajiyawa yo ke duk abin da kike yi ba a gaji dake ba sai kece zaki ce kin gaji irin wannan son kai haka har ina".
Dariya Baseera tayi tana mai jawo ta ta zaunar da ita bakin gadon kafun ta juya ta isa wajan da dan madaidaicin firij dake can gefe lemo ta dauko mata da gorar ruwa gami da Cake ta kawo mata da kanta tayi saving din ta amma sai bari Mariya tace ta bari zata dauko ta gode a hakan ma.
Sun jima cikin wannan yanayin Baseera sai fama ratata zance take yi kamar wata rediyo cikin maganganun nata ne wata magana ta so narkar da Mariya daga in da take zaune.
"wai shin da zaki shigo baki ga wata hadaddiyar mota ta fice daga layin nan ba?".
Baseera ta fadi tana mai daukar Nawwara daga jikin Mariya, kaɗa idanu tayi kamar mai tunani kafun ta gyada kai alamun eh ta gani domin ta lura da mota da Baseera ke magana akanta.
"Dr.Karami ne ya zo muka gaisa...".
Daga wannan batun Mariya ba ta sake sanin in da kanta yake ba gabadaya taji ana juyata kamar waina a tadda tashin hankalin da take ciki taji ya karu sosai sai yanzu ta gane faduwar gaban da tayi dazu da taga motar ashe Dr.Karami ne.
Sosai kan ta ya kulle komai taji na tunanin ta ya tsaya cak! Ba abin da ke dawainiya da ita sai mamaki da al'ajabi ta yarda Dr.Karami gabadaya ya sauya yake gujewa haduwarsu ba ta san ya ya za tayi ba ita kam! Ba ta san mai yake nufi da ita ba.
"Yace ma jiya a gidanku ya wuni tun muna makaranta yaje ashe".
Gyaɗa kai kawai Mariya take yi tana faman jan numfashi kirjinta take ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske numfashin ma da k'yar take iya jan sa.
Jin shirun yayi yawa ya sanya Baseera dubanta sosai da sauri ta ware ido ganin yanayin Mariya dafa ta tayi cikin yanayi na sanyin jiki.
"Me ke faruwa ne wai lafiya kike kuwa Mariya naga gabadaya lokaci guda kin sauya ne me ke damun ki".
Wani numfashi mai zafi ta ja ta fesar kafun ta dubi Baseera da idanunta masu kwalla cikin rauni ta fara magana tana cizon laɓɓanta.
"Kin san kuwa har yau ba mu hadu dashi ba".
Ta karashe kamar zata rushe da kuka jin zuciyar ta take tana zafi da raɗaɗi kanta na wani irin sarawa kamar zai rabe gida biyu.
Ware idanu Baseera tayi gami da dafe kirji.
"Na Shiga Aljanna".
Wani murmushi Mariya ta saki wanda ya fi kuka ciwo kafun ta ja numfashi wanda ya haifar mata da wani irin ciwo a zuciya dama duk gangar jikinta.
"Ni kuma na shiga Uku Bala'i Baseera".
Zabura Baseera tayi ta mike gabadaya kan kafafuwan ta jikinta lokaci guda ya shiga rawa kamar wacce aka jonawa wayar wuta Nawwar dake hannunta har kokarin faduwa take yi duban Mariya take yi cikin wani irin yanayi na ban san in da kika dosa ba dubanta take yi da wani irin yanayi mai dauke da rauni da tausayi dubanta da take yi da wani irin tashin hankali mai girma da ya ziyarci zuciyarta dama dukkannin jikinta.
A hankali ta shiga jan numfashi tana mai kokarin kwantar da Nawwara don ta tabbata in ta cigaba da riketa zata iya watsar da ita ba tare da ta sani ba ba abin da ya kara daga mata hankali sai hawayen da ta gani a idanun Mariya suna zuba.
"Yaa Rabbi!".
Ta fadi tana zubewa bakin gado kamar wata kayan wanki tagumi ta zabga tana ganin ikon Allah wai uwar miji da cin kazar amarci.
"Mariya wai shin me ke damun ki ne haka wallahi kin ta yar min da hankali ba kadan ba".
Nisawa tayi zuciyarta na wani irin harbawa kafun ta ciji laɓɓanta.
"Ban san mai Alkalamin ƙaddarata yake kokarin rubuta mani ba, ban san wani irin tashin hankali ne yake kokarin shigowa rayuwata ba a daidai wannan lokaci Baseera ina cikin matsala, matsala babban wacce ban san maganin taba zuciyata zafi take yi ruhina raɗaɗi yake yi kwanyata ta cushe da tashin hankali mai girma ji nake yi kamar bani ba a filin duniyar nan ji nake yi kamar komai ya sauya a jikina...".
"Ya isa haka".
Baseera ta fadi jin muryar Mariya ta fara rawa tana kokarin sakin kuka.
Ruwa ta tsiyaya cikin glass cup din dake ajje kan farantin da ta kawo mata lemo akai a hankali ta dauka ta mika mata ba musu ta ansa ta kwankwade kamar dama can kishin ruwan take ji wani numfashi taja wanda ya sanya Baseera dubanta da sauri tana mai ware idanunwanta akanta domin gabadaya ta tsorata da yanayin da ta ga Mariyar a ciki.
Sun shafe mintina a haka ba wanda ya sake magana a tsakaninsu sai ajiyar zuciyar Mariya kawai sautin ki tashi ita kuwa Baseera kafeta tayi da ido gami da zabga tagumi domin ta rasa ma mai ya dace domin sosai da sosai kanta ya dau caji ba kadan ba.
"wai shin har yanzu fushin da Dr.Karami yake yi dake ne duk ya sanya ki cikin wannan halin ko me ne ne?".
Baseera ta fadi da wani irin yanayi mai girman gaske a zuciyarta muryarta tayi laushi sosai.
Girgiza kai Mariya ta shiga yi cikin rashin fahimta Baseera tace.
"To me ke damun ki wai shin?".
Sai da taja numfashi mai ciwo kafun ta dubi Baseera.
"Sun sako ni gaba Baseera ban san ya zan yi ba ina cikin tashin hankali".
"Yaa Allah! sun sako ki a gaba fa kika ce su waye haka me kuma suke nema dake?".
"kina dai kallon yarda nake cikin tashin hankali akan Dr.Karami to ban gaba dawowa hayyacina ba shi kuma Dr.Aqeel ya sako ni gaba da wani lamari wanda ban san ya zan fassara miki shi ba bayan haka ga kuma Huzaif shima ya dauko mani wani tashin hankalin yana kokarin jonawa min a filin rayuwata".
"Uhmm ni fa ban gane ba ban san ina kika dosa ba?".
Girgiza kai tayi tana jin yarda zuciyarta ke wani irin harbawa da wani tashin hankali mai girman gaske.
"Dr.Karami fushi yake yi dani wanda ban san dalilin fushin ba".
"wai shin Mariya na tambaye ki mana ke tsakanin ki da Allah zaki ce baki san laifin da kikayi masa ba har yake gudun haduwarku anya kuwa Mariya ya kamata ace kin yi tunani ya kamata ace kin zauna kin yi nazari kin binciko abin da ya haifar da wannan lamarin a tsakaninku".
Shiru Mariya tayi kamar mai tunano wani abu na daban kafun ta nisa ta dubi Baseera.
"kisan Allah tun ranar da muka fara haduwa dake har period dina ya zo to tun ranar rabona da samun fuska daga Dr.Karami tun ranar muka rabu wanda har yau ban sake sakashi a idona ba".
Zaro idanu Baseera tayi tana dafe kirji.
"ke Mariya da gaske kike don Allah?".
Murmushi Mariya tayi mai ciwo kafun ta gyada kai alamun eh.
"Mun shiga Uku anya kuwa Mariya ba wani abu a kasa tsakaninki dashi kuwa?".
"Ke ma dai Baseera ta ya ya zan yi wa Dr.Karami wani abu don na bata masa rai ai Alheri bai ce haka ba amma dai ban sani ba ko a cikin RASHIN SANI wanda ake cewa YAFI DARE DUHU nayi masa amma kuma ai ya kamata ace ya nuna min eh ga abin da nayi masa sai in bashi hakuri ba wai ya zauna yana fushi dani ba kuma bai son ganina kin ga kenan abin da nayi masa ba sauki gareshi ba...".
"ki daina cewa baya son ganinki Dr.karami yafi kowa a filin duniyar nan son ganinki domin kuwa ni zan yi shaidar haka".
Cikin rashin fahimta Mariya take dubanta kafun lokaci guda taji wani lamari ya tunkaro zuciyarta har ya kai cikin kwanyarta da sauri ta mike ta shiga zarya cikin dakin kafun ta tsaya cak! tana tura dan yatsar ta cikin baki tana yawata idanuwanta a sassa na cikin dakin kamar mai son tuno wani abu na daban.
"Ya akayi Mariya ko kin tuno wani abu ne na daban".
Gyaɗa kai tayi kafun ta dubi Baseera.
"Ina zargin wani abu guda domin daga shine koma ya canza tsakanina da Dr.Karami".
Da sauri Baseera ta mike jin abin da Mariya take fadi.
"zo ki bani labari zo ki sanar dani komai na san za a samu hanyar mafita".
Hannunta ta janyo ta zaunar da ita bakin gado tana mai dubanta.
"Bani labari Mariya sanar dani komai".
Sai da taja numfashi sosai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa waje daya da wani irin yanayi na damuwa matsananciya.
"bana zargin komai sai su Dr.Aqeel da Huzaif domin ranar da muka baro gidanku mun tadda Huzaifa a kofar gidanmu yanayin da naga Dr.Karami ya nuna kamar bai so ba kuma daga lokacin ko kallona bai sake yi ba bayan haka na fito daga motarsa ina kokarin shiga gida sai ga Dr.Aqeel shima ya zo to a wannan lokacin zan iya cewa komai ya faru domin daga lokacin ko kalma daya ba ta sake shiga tsakanina da Dr.Karami ba sosai na tsoro ta da irin kallon da yake mani a lokacin ko dai dai ban san tsananin bacin rai ba amma lokacin na lura da yanayin da ya shiga na bacin rai sosai domin har sai da fuskarsa ta nuna".
Hawaye ne suka zubo mata da sauri ta sanya hannu ta na shafe su Baseera ce ta dafa mata kafada tana girgiza kai alamun ya isa haka ta daina zubda hawayen.
"Meye tsakaninki da Dr.Karami".
Kamar daga sam taji Baseera ta watso mata tambayar wanda hakan ya bata mamaki sosai nan tayi fakare da jajayen idanuwanta tana duban Baseera cikin yanayi na ban gane in da kika dosa ba.
"Bakomai".
Ta kokarta ta fadi amma tana jin yarda zuciyarta ke karya ta ta akan abin da tace ita a karan kanta ta sani akwai wani abu mai girma tsakanin ta da Dr.Karami amma har zuwa wannan lokacin ba ta san menene ba, ba ta san yarda zata fassara yarda take ji game dashi ba...
"Shi kuma Dr.Aqeel fa?".
Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Baseera ta sake fadi.
Sosai ta shiga dubanta a wannan karon tana kallon idanun Baseera da yanayin da fuskarta take nuna alamun maganar da take yi da gaske, ba alamun wani wasa a ciki kan ta shia gyaɗawa kafun ta ja numfashi.
"Ban san me zan ce miki ba akan sa, amma dai shima...".
"shima ba komai din ko?".
Baseera ta katse ta da sauri tana mikewa kan kafafuwanta girgiza kai tashiga yi tana faman sakin yake mai kama da ciwo sosai a zuciya da ruhi take ji, taku biyu zuwa uku tayi kafun ta tsaya waje guda ta juyo ta fuskani Mariya sosai hannayenta sarke a kirjinta kallon sosai tayi mata kafun ta fesar da wata iska mai zafi.
"Huzaif fa shi kuma a wani mataki yake a gareki?".
Runtse idanu tayi tana mai tallabe kanta da take jin yana dauko mata wani lamari a bangarori duk ukun ba tasan me yake kokarin tarwatsa mata kwanya ba sosai tajin komai na kwance mata tunani ne barkatai taji suna kawo mata farmaki.
"Yaa Allah! ban san abin da zana ce dake ba Baseera komai nawa ba ya kan mizanin natsuwa da zan iya warware miki".
"Eh dole kice haka mana kuma dole komai ya rikice miki ki kasa gane in da komai na filin duniyar ki ya dosa".
Duban ta take yi cikin rashin fahimta sosai ta kasa gane maganganun da Baseera ke yi a hankali taja numfashi kafun ta fesar da iska mai zafi.
"Da gaske nake sanar dake ban san komai ba".
A hankali Baseera ta tako ta iso gareta kafadarta ta kama ta girgiza sosai idanuwansu suka sarke a juna.
"kisan me yake faruwa dake?".
Girgiza kai tayi.
"Kin san abin da yasa kika shiga wannan matsalar ko ma nace matsaloli?".
Nan ma girgiza kai tayi izuwa lokacin jikin ta ya fara sanyi gabanta na tsananta bugawa tana jin yarda zuciyarta ke harbawa da sauri-sauri.
Murmushi Baseera ta saki tana mai gyada kai kallo daya zakayi mata ka gane kallon tausayi da rauni take jifan Mariya dashi sai da ta ja numfashi sosai ta fesar kafun ta dauki gorar ruwa ta bulbulawa cikinta zuciyarta taji ta dan sarara da tashin hankalin da take hangowa Mariya a rayuwa ba ta san ta ya zata fara sanar da ita halin da take ciki ba ba ta san ta ya ya zata fahimtar ita ba tare da ta shiga tashin hankali ba ba ma wannan ba sosai take ji a jikinta abin fa ba sauki mutuwar arne.
Tana numfasawa zuciyarta na kara mata kwarin gwuiwa akan kawai ta fahimtar da Mariya ita ce hanya daya da take gani komai zai gyaru har a samu mafita.
"Mariya ba zan boye miki ba a yarda na fahimci lamarin nan gabadayan wadannan mazajen da kike gani su uku kishi ne a tsakanin su".
Wani irin duba na razana Mariya tayi mata tana sauke hannun da Baseera ta daura mata a kafada ta shiga ja da baya a hankali tashiga motsa laɓɓanta.
"Ban gane kishi suke yi a tsakanin su ba a akan mi suke kishi".
"AKAN SONKI duk kan su son ki suke yi so kuwa mai tsanani ko wanne a tsakanin su akwai kalar so da yake yi miki tun kafun wanann lokacin...".
Sulalewar da Mariya tayi ne kasa tare zaman yan bori ya sanya Baseera dubanta tana tsaigaitawa da maganarta ta.
Hawaye ne shaɓe-shaɓe ta hanga idanuwan Mariya suna zuba ta hade hannayenta duk waje daya ta daura a kai lokaci guda ta hade jikin ta waje guda kamar mai jin sanyi ko wacce za a rabata da wani abu nata.
"Na Shiga uku".
Ta fadi tana mai bajewa kan Capet din dake malale tsakar dakin kamar wacce aka tsikara kuma ta mike zumbur tana duban. Baseera da wani irin yanayi.
"Ban yarda ba wallahi wannan ba gaskiya bane hauka suke yi wallahi hauka suke yi haba mana Baseera kamar ni za su ce suna so ki dube ni fa guda nawa nake a filin duniyar nan suke kokarin kashe ni da raina wannan wani irin Bala'i uku ne nake ciki ni Mariya".
Haka ta saki baki tana sambatu kamar wata zautacciya kafun ta durkushe ta saki wani irin kuka mai zafin gaske da jefa zuciya cikin wani irin raɗaɗi na tashin hankali wanda ba tsammanin yankewarsa.
Baseera dake tsaye bata san lokacin da idanunta ita ma suka shiga zubda kwalla ba wani kuka ta ji ya zo mata da sauri ta sanya hannu ta toshe bakin ta tana karasawa wajan Mariya ita ma ta zube nan suka rugumi juna suka shiga rera kuka aka rasa mai rarrashi wani daga cikin su....
*_KAMALA MINNA_*😍😍😍
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.
A hankali ta turo kofar dakin ta shigo tafiya take yi cikin natsuwa da kuma yanga da ta zame mata jiki da wuya kaga Areefa na tafiya da sauri-sauri a,a sai dai ka ga tafiyar ta kamar mai koyo duk hakan na cikin salo da take amfani dashi cikin filin duniyar rayuwarta sanye take da doguwar Riga Gown wanda tayi matukar amsar jikinta sosai da sosai ta fiddo mata da asalin kyanta da kuma fatarta mai haske wanda tayi Fresh sosai da sosai hutu da jindadi sun taimaka kwarai wajan bayyana a jikin ta kanta ba kallabi sai dai ta tufke gashinta ta sanya rinbos mai kalar pink ta saki jelar gashin na reto a bayan ta fuskar nan fayau ba alamun ko digon tabo na kuraje.
Ba ta shafa komai ba natural fatarta kawai ce ke kyalli manyan idanuwanta masu haske sun kara taimakawa waja fiddo da kyan fuskarta hancinta dan madaidaici shi dai ba za a kira shi dogo ba sannan ba za ace dashi gajera ba yana tsaka tsakiya haka bakinta mai dauke da manyan laɓɓa masu kalar ja kadan ba sosai ba suma sun taimaka wajan kara bayyanar da kyan fuskar ta na halinta da Allah yayi mata.
A yanayin da ta shigo dakin in ka kalle ta zaka gane akwai abun dake damun ta a filin duniyar rayuwarta bisa yanayin da take yatsine fuska kamar wacce aka sanya dole shan magani sai faman kaɗa idanuwa take yi tana bin dakin da kallo.
Hajiya Layla dake zaune can gefe guda tana faman goge jikinta da shawul da alamun wanka ta fito take tsane jikinta.
Fuskarta take kallo cikin wani irin yanayi tana yatsine fuska tana duban MADUBI dake tsaye a bangon dakin.
Shigowar Areefa ya sanyata tsayawa da abin da take yi ta juyo ta dube ta kafun ta mai da kanta wajan fuskartar madubin.
A hankali ta karasa takowa ta iso gareta idanu suka hada ta madubi duk fuskokin su cike da damuwa sosai.
"Maama Lafiya kuwa na ga fuskar ki wani iri daban kamar akwai abin dake damun ki ko?".
Areefa ta fadi tana mai yawatawa idanuwanta cikin na Hajiya Layla.
Numfashi ta ajje mai tauri kafun ta juyo ta dubi Areefa sosai da sosai kafun ta ajje shawul din tana mai riko hannun Areefa tana damkewa cikin nata kamar zata muntsuke sosai Areefa ta ji rikon har sai da ta rintse idanunta tana furta.
"Ouchhh!!".
Dubanta tayi tana jin zuciyarta na wani irin shiga yanayi sosai take jin rashin dadi a jikinta gabadaya a hankali ta fara motsa laɓɓanta tana son yin magana amma kafun ta kai ga furta kalma daya tari mai karfi ya turnuketa ta shiga yin sa ba k'ank'autawa da sauri Areefa ta ware idanu tana dubanta cikin yanayi na tsoro ta rikota sosai ita ma ta isa da ita daidai karamar kujerar dake gaban Madubin ta zaunar da ita har zuwa lokacin tarin bai lafa ba kwace hannunta tayi daga rikon da tayi mata ta fice daga cikin dakin cikin minti daya ta dawo hannunta rike da glass cup mai dauke da ruwa da sauri ta kai bakin Hajiya Layla wanda a lokacin tari ya tsaigaita sai dai wani lamari da Areefa ta gani ya so tayar mata da hankali domin kuwa wani bakin abu taga yana fita daga bakin Hajiya Layla.
"Yaa Rabb!".
Ta furta tana mai janyo shawul din tana goge mata baki sannan ta sake mika mata ruwan zuwa bakinta kadan ta sha ta kau da kanta.
"Maama meke damunki haka baki da lafiya ne tashi mu tafi asibiti a duba ki mana don Allah kin ji".
Yanayin da Areefa take maganar duk a rikice hakan ya sanya Hajiya Layla kakalo murmushi ta ajje a fuskarta duk da raɗaɗin da take jin zuciyarta nayi da wani abu mai girman gaske da ya tokare mata kirji sosai take jin tashin hankali komai take ji na duniyar ya sauya mata ba tun yau ba kusan shekara uku kenan take jin canji a jikinta tayi zayar zuwa asibiti wanda ita a karan kanta ba za ta ce a ga dadi ba sosai ta fara nadamar rayuwar da tayi a shekarun baya sosai take jin daci a zuciyarta dama ruhinta gabadaya nisawa tayi tana mai sake kakalo murmushi tana daurawa a fuskarta domin ta lura Areefa ta shiga tashin hankali matuka ganin yanayin da take ciki wanda ta hakikan ce ba laifin kowa bane sai nata ita ce silar komai da komai a rayuwarta.
"Uhmm Ya isa haka Areefa ba komai fa kawai dai tari ne ya tsarke ni magani na sha shine fa tun dazu nake wannan tarin amma yanzu naji komai ya yi sauki ki kwantar da hankalin ki".
Rausayar da kai tayi cikin yanayi na sanyin jiki idanuwanta na duban Hajiya Layla da alamun bata gasgata abin da tace ba amma ba zata iya yi mata korafi ba a yarda take kallon ta a matsayin uwa mai kaunar 'yar ta a filin duniyar nan ba za ta mance halaccin Hajiya Layla ba a duniyar ta ba zata taba manta taba domin tayi mata komai na rayuwa ita ce ta sauya mata komai na filin duniyarta a lokcin da ta rasa gata ta rasa wanda zai kula da rayuwarta ya taimaka mata ya ji k'anta a lokacin da ta rasa 'yancita da komai nata a lokacin da take bukatar taimako ta rasa a lokacin Hajiya Layla ta fado rayuwarta tayi mata suttura da taimakon Allah ita ta taimaka mata ta dawo cikakkiyar mace mai 'yanci wacce ba wulakanta ba duk da KETA HADDI da akayi mata aka ci zarafin ta a matsayinta na mace mai rauni a filin a rayuwarta.
Bata san hawaye na zuba a fuskarta ba sai da taji hannun Hajiya Layla na dauke mata su da sauri tayi firgigin ta dawo hayyacin ta suka kurawa juna ido kafun Hajiya Layla ta shiga girgiza kai.
"Haba mana Areefa har sai yaushe ne idanuwanki za su dai na wahalar da kan su ne har sai yaushe zaki daina zubda hawaye akan abin da ya riga ya wuce bana so ki daina kawai kin ji ko".
Gyada kai ta shiga yi kamar wata kankanuwar yarinya kafun ta sanya hannu ta na kara goge fuskarta tana k'akalo yaken dole tana ajjewa a saman fuskarta.
Kuri Areefa tayi wa Fuskar Hajiya Layla tana yawatawa da idanuwanta kafun ta nisa.
"Maama me ya samu fuskarki haka duk tayi wani iri kamar wacce ta kone da wuta sosai naga ta canza tana tattarewa?".
Murmushi tayi wanda ya sanya zuciyarta da ruhinta ciwo sosai wasu HAWAYEN ZUCIYA taji suna ta kwaranyo mata sosai ta san za a yi haka ta san komai daren dadewa sai yanayin nan ya faru da ita wanda ita a karan kan ta ta san ita ce silar faruwar komai a gareta numfashi ta fesar mai zafi kafun ta motsa laɓɓanta.
"Ban san ta ya ya zan sanar dake halin da nake ciki ba, ban san ta ya ya zan sanar dake lamarin da na daura wa kai na ba gashi yanzu yana kokarin illa tani ban san mai ya kai ni haka ba ban san mai yasa na kasa godewa Allah da baiwar da yayi mani ba na butulce masa da sani na".
Shiru tayi tana jin yarda zuciyarta ke zafi da radadi rufe idanuwanta tayi ta buɗe su akan Areefa da tayi fakare tana kallon ta sosai taji tausayin ta sosai jikinta yayi sanyi da kalaman Hajiya Layla ko da bata ji abin da ya sanya ta shiga damuwa haka ba ta tabbata abin ba mai dadin bane a filin rayuwarta da alamu kuskure tayi ba tare da ta san kuskure bne a rayuwarta.
"Areefa kin ga yarda fuskata take a haka cikin rashin kyan gani to haka duk wani sassan jiki na yake".
Tana maganar tana janye shawul din dake daure daga kugunta zuwa kasa cinyoyinta ta bude sosai Areefa ta tsorata tana mai runtse idanuwanta kafun ta buɗe su a hankali zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri kafar Hajiya Layla take kallo har zuwa cinyarta gabadaya sun sauya kala kamar wanda tayi muguwar k'una ta bada tangarɗa wajan warkewa duk tayi wani bakinkirin ga wasu dikon dikon kuraje marasa kyan gani dago idanunta tayi ta dubi Hajiy Layla dake faman sakin murmushi wanda yafi kuka ciwo.
"Maama me ya same ki haka a jiki nace baki da lafiya kin ce a,a ba haka ba ga kuma jikin ki ya nuna alamun baki da lafiya".
Areefa ta fadi tana kai hannunta saman fuskar Hajiya Layla tana tabawa cikin yanayi na tsoro a fuskarta runtse idanu tayi jin yarda fatar tayi wani irin tauri da wani giris-giris kamar an shafa mata dakanken gawayi.
"Wai meye haka a jikin ki Maama sosai fa jikin ki ya baci fa dubi kafarki ji fuskarki Maam muje asibiti a duba fatarki anya ba cutar fata ba ce ta kama ki?".
Girgiza kai kawai take yi cikin matsananciyar nadama da dana sani kafin ta ciji laɓɓanta.
"Ba cutar fata bace Areefa ni na sanya wa kai na ba laifin kowa ni na ja wa kaina".
Cikin rashin fahimta Areefa ke dubanta tana kara buɗe idanuwanta sosai cikin yanayi na firgici da abin da take ji Hajiya Layla na fadin.
"A can baya ni BAKAR MACE ce mutane da yawa suna yabawa na kalar fata ta duk da bakar ce amma ana cewa ina da kalar fata me kyau ba kowa bane ake samu da irin ta Natural skin ce mai wuyar samu domin da wuya ki ga fatar jiki na ta tattare ko ta yi kuraje ni kaina nasan ina da kyan fa sai dai abin takaici abin haushi a lokacin ni kuma ba abin da nake kauna kamar farar fata da yawan kawayena in suka ji ina cewa ina kaunar farar fata sai su ce bani da hankali ban san abu mai kyau ba har cewa suke yi da ana masayar fata dani za suyi ni kuwa a ganina hauka ce kawai suke yi me ake yi da bakar fata ga 'ya mace budurwa mai aji ai bakar fata sai namiji wanda ya gaji wuya da shiga rana ba 'ya mace ba da aka sani 'yar hutu da da zaman jindadi.
Duk kururuwar da zuzutawa da akeyi mani ina da kyan fata hakan bai hanani burin canza kalar fata ta ba a lokacin na shiga bincike har sai da na gano irin maya-mayen da ake shafawa ake canza fata zuwa fara a lokacin ba karamin dadi naji a rayuwa ta ba nayi farin ciki mara musaltuwa tun daga wannan lokacin na canza mayuka na da nake amfani da su haka sabulai na duk sai da na canza ban yi sati guda ina amfani da su ba na fara canzawa fuskata ta fara haske a lokacin mutane da yawa sun so nusar dani amma ina na yi kunnan uwar shegu da su na cigaba da harkar ta in takaice miki cikin kankanin lokaci na sauya gabadaya nayi fara tas na koma kamar in kika latsani jini ne zai fito daga jikina sosai na sauya komai nawa ya canza mutane da yawa sun nuna rashin kyautawa akan abin da nayi domin cewa ma suke yi na koma sam bani da kyan gani fatata tada ta fi dacewa dani ni kuwa ko a jikina Areefa na fi shekara goma sha biyar ina wannan abun tun ina kuruciya ta har zuwa tsufana ban daina ba domin ban gano illar haka ba sam sai da shekaruna suka ja fatar jikina ta fara gajiya domin ta rigaya ta gama rauni sosai komai nata ya gama komawa nakashasshe".
Shiru tayi tana shafar kafafuwan ta da suka koma kamar mai ciwon kuturta.
"Bani da yarda zan yi yanzu domin ni na jawa kaina duk abin da ya faru dani ni ce sila".
Ta karasha cikin raunin muryar kafun ta miki ta isa gaban madubi ta janyo robar mai basilin tashiga muttsukawa jikin ta a hankali idanuwanta na kan fatarta tana kallon yarda ta sauya gabadaya kamar wata mai cutar kuturta nisawa tayi ta dubi Areefa da tayi fakare tana bin ta da kallon ko motsi ta kasa yi.
"Yau ba zaki aiki bane hala lokaci fa na tafiya".
Sai lokacin Areefa ta kaɗa idanuwanta tana mai jan numfashi ta bude idanunta sosai ga Hajiya Layla wani irin tausayinta take ji yana samun masauki a zuciyarta da ko ina na gangar jikinta girgiza kai ta shiga yi alamun ba za ta je ba domin yanayin da take jin jikin ta duk yayi sanyi kalaman Hajiya Layla ba karamin sanya zuciyarta rauni sukayi ba.
Ware idanu Hajiya Layla tayi ganin abin da Areefa tayi kallonta tayi tana ma tsuke fuska.
"Maza wuce ki shirya ki tafi aiki kin ji ko akan me zaki ce ba zaki ba ke da ba wani abu ke damun ki ba".
kau da kai tayi tana kokarin yin magana Hajiya Layla ta daga mata hannu.
"Bana bukatar naji komai kawai ki tafi nace ki shirya ki wuce Office".
Ba ta sake yin magana ba gani ba wasa a fuskar Hajiya Layla din cikin sanyi jiki ta ja jiki ta fice daga daga dakin.
Kamar jira take yi Areefa ta fice ta zube kan gado gami da zabga uban tagumi tana mai runtse idanuwanta sosai taji kanta na sara mata zuciyarta na zafi da wani irin yanayi mai girman gaske nadama sosai take yi tana jin kunyar kanta fita ma waje kunya take ji ba ta so su hadu da muta ne gani take yi kamar kallon banza da kallon kyama suke yi mata.
*******
A hankali ta karasa shigowa cikin harabar Company din can gefe inda aka tanada Parking Space ta isa ta ajje motarta sai da ta shafe mintina kafun ta fito daga cikin motar hannun ta rike da Key sai jaka kunnanta kuwa iyafis ta mak'ala fuskar ta kawai zaka kalla ka gane akwai damuwa tattare da ita.
A hankali ta fara taku lokaci-lokaci tana lumshe idanuwanta har ta isa babbar kofar da za ta shigar da ita cikin wajan aikin nata Securty suna yi mata sannu da zuwa amma ina hankalin ta yayi dogon zango.
Ko da ta isa ciki ba wanda ta tsaya kallo har ta isa wajan gefen ta ta buɗe yar karamar kofar da kayi domin kare wajan zaman nata ta buɗe ta shiga ta zauna tana sakin numfashi kadan-kadan table din dake dauke da computer da file ta duba kafun ta janye files din da taga an anje mata gefe kanta ta daura akai tana tallabewa da hannayen ta zuciyarta take ji tana tayi mata wani irin sosai take jin rashin dadi a jikin sosai komai taki ji nata ya sauya yau daya wani irin kunci da zafin zuciya take ji sam bata so wani ya zo ya takura mata shiyasa bata so fitowa aiki ba amma ba yarda za tayi ne shiyasa...
Kwakwasa mata kofa da akayi ne ya sanya ta dago kai tana mai sakin guntun tsaki Sakatariyar Dr.Erena ce tsaye sai faman wani shan kamshi take yi tana harare harare kamar wacce ke kokarin kai duka.
"Sir ya ce sai ki zo".
Ta fadi tana wani basarwa kamar ba da Areefa take yi ba.
Sosai Areefa ta ware ido tana kallon ikon Allah wai suruka ta mari uwar miji ita abin ma dariya ya so ya bata wai batar basira rokon Allah da goge sai da ta gama kalle ta kafun ta ja wani dogon tsaki tana mai da kan ta kasa ta na kwanciya.
kwankwasawa taji an sake yi da sauri ta dago cikin bacin rai ta mike kan kafafuwan ta tana dubanta.
"Ke! ina wasa dake ne ko ni tsaran ki ce ba sako aka baki ba kin fadi ba sai ki tafi ba ko da sauran wani abu ne?".
Areefa ta fadi cikin daga muryar har sai da sauran ma'aikatar hankalin su ya yo kan Areefa da sauri ta fizgi wayar ta ta fito ta tsaya gabanta tana watsa mata wani irin kallo kafun ta ja wani tsaki ta wuce abin ta. ta bar ta shanye da baki cikin yanayi na tsoro don bata taba tunanin Areefa haka take ba tun da ta fara aiki a Company din ba tayi zaton tana da fada haka ba ashe kallon kitse take yi wa rogo kwaɓe baki tayi kafun ta ja jiki ta bar wajan tana duban Sauran ma'aikatan da suka kureta da ido kamar za su lashe duk sai taji kunya ta kamata.
Ko da Areefa ta isa Office din Dr.Erena banka kofar tayi ta shiga cike da bacin rai tsaye ta hangeshi sai faman safa da marwa yake yi jin banko kofar da akayi ne yayi sauri tsaya cak! Yana duban kofar ganin Areefa ya sanya shi ware idanu musamman ganin yarda ta shigo kamar wacce zata rufe shi da duka.
"Dr.Erena ya kamata ka san wani abu ba wai don ina karkashin ka bane ina aiki zai baiwa sakatariyarka dama wani duk da yake cikin ma'aikatar nan raina ni ba fa maula na zo yi ba aiki na zo yi kamar kowa da yake tutiyar aiki ya zo yi don haka ba wanda ya isa ya taka ni na kyale shi".
Ta karashe tana fesar da iska mai zafi shi kan sa sai da ya razana da yanayin ta da sauri ya iso gareta jikin sa har rawa yakeyi.
"Lafiya me aka yi miki wani dan iskar ne ya bata miki rai a cikin Company nan nawa?".
Yanayin da yake maganar cikin yanayi na harzuka ya sanya Areefa duban sa cike da mamaki kafun ta kau da fuska.
"kar ka sake tura mani sakatariyarka in kana nema na ai akwai waya ko ka kira ni mana".
Tun kafun ta dire maganar ta taga ya figi jikin sa yayi kofar fita kofar ya banka cikin sauri ya fara kiran sunan sakatariyarsa wacce a daidai lokacin ta iso tana kokarin zama amma jin kiran da Ogan nata yake yi mata ya sanyata sauri mikewa tana rarraba ido kamar wacce ta san bata da gaskiya.
Yana isa gareta ya nuna ta da hannu kafun ya kwasheta da mari ji kake tas! wata kara ta saki gami da kiran 'jesus'.
saura kadan ta hantsila bayan kujera nan ta shiga ja da baya idanuwanta a warwaje ganin yanayin da yake nunata da yatsa cikin matsanancin bacin rai.
"Sorry Sir...".
Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata kafun ya fara magana cikin masifa.
"Baki da hankali uban me tayi miki zaki nemi raina mata wayo dana aike ki cewa nayi ki yi mata rashin mutunci ba cewa nayi kawai ki duba in ta zo ki ce ina kiranta ba da yake ke dakikiya ce shine kika je kina yi mata hauka ko".
ware idanu tayi tana duban hanyar Office din sa da wani irin yanayi na dacin rai a ranta tana sa ba wanda zai mata haka sai Areefa tun da suke da Dr.Erena bai taba ko zaginta ba amma yau ta dalilin ta ya mare ta dubansa tayi cike da takaici kafun ta kau da fuskarta zuciyarta na yi mata zafi ba abin da take yi a zuciyarta sai 'Allah ya isa ba ta yafe ba'
Wani mugun kallo tabi shi dashi lokacin da ta ga ya ja tsaki ya koma office din itama dogon tsaki ta ja zuciyarta kamar ta fashe janyo kujera tayi cikin takaici ta zauna tana dukan saman table din dake gabanta.
Shikuwa Dr.Erena yana shiga Office dinsa zaune ya tadda Areefa sai faman girgiza kafa takeyi fuskar nan ta ta kamar hadari ba karamar razana yayi ba da sauri ya isa wajan yana mai bata hakuri yana kokarin zama kusa da ita tayi saurin jan jikin ta tana wurga masa wani wulakataccen kallon.
"Don Allah Areefa kiyi hakuri waccen tsinaniyar yarinyar ba hankali gareta ba shiyasa don Allah karki bata ran ki akan ta na hukunta ta".
Kallo shekeke tayi masa gami da na raina maka wayo kafun ta ja guntun tsaki tana kokarin tsahi ta fice da sauri ya sha gabanta yana kallon idanuwanta da wani irin yanayi na tsananin so da yake yi mata.
"Haba mana magana fa zamuyi shiyasa nace a kira mani ke don Allah koma ki zauna maganar ba za ta yuwuwa ba a tsaye".
"ka ga don Allah Dr.Erena ka rabu dani bana bukatar yawan magana a daidai wannan lokaci ina bukatar zaman kadaici ni kadai please".
"Areefa don Allah ko mintin biyu ki bani wallahi maganar mai muhimmanci ce".
Duban sa tayi ba tare da ta ce dashi komai ba ta koma ta zauna hakan da ya gani shima yayi saurin jan kujera ya zauna yana fuskartanta sai faman ajiya numfashi yake yi kafun ya kokarta duban idanunta sosai da sosai.
"Areefa ba zan boye miki ba a gaskiya nagaji da yanayin da kike yi mani na shariya da halin-ko-in- kula ya kamata in san matsayina domin ni dai da gaske son ki nake yi kuma ko auren ki zan iya yi...".
wata irin zabura tayi ta mike kan kafafuwan ta kafun ta lailayo wasu tawagar ashariya ta sauke ta dora da fadin.
"Kan Uban can! So Aure fa ka ce Dr.Erena wa zaka aura".
Ta fadi tana mai sakin wani murmushi mai kokarin tarwatsa mata zuciya da ruhi wani daci ne gami da raɗaɗi taji sun saukar mata a zuciya kirjinta yana wani irin bugawa kamar zai tarwatse lokaci guda taji kwanyarta tayi wani irin hautsinewa kamar zata tarwatse itama duban sa take yi da wani irin yanayi na tsana mai girman gaske idanuwanta lokaci guda suka sauya fuskarta tashiga wani kunci runtse idanuwan ta tayi kafun ta sake dubansa ta girgiza kai da sauri ta ja kafarta tayi hanyar ficewa daga cikin office din cike da tashin hankali da a zuciya kiranta ya shiga yi amma ina ko ta kan sa ba tabi ba illa banka kofar da tayi har sai da office din gabadaya ya amsa da sauti mai girman gaske.
Da gudu ta isa kasa ba ta tsaya wata wata ba ta fizgo jakarta ta fice daga cikin wajan da yawan ma'aikata kallo suka bita dashi har fa fice wajan motarta ta isa ta buɗe ta shige tana mai da numfashi kai ta hada da sitiyarin motar gabanta na wani irin dokawa tsanar Dr.Erena take ji tana kara samun filin zama a zuciyarta ko son ganin sa ba ta so ta sake yi ta lura da gaske yake yi kokari yake yi ya gama da ita tun kafun ta cika burin ta akan sa wanda ba zata so hakan ba sam!.
Ya zame mata dole ta canza taku dole na biyo masa ta hanya wacce zata yi saurin cimma kudirin ta domin a gaskiya ta gaji da zuwa wajan gani take yi kamar komai zai lalace yar da ta fuskanci al'amarin Dr.Erena so yake yi yayi mata yawo da hankali wanda ba za ta yarda haka ta kasance ba dole ta sake sabon lale tun wuri....
*_KAMALA MINNA_*😍😍😍
UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA TARA.
Cikin wani irin yanayi ta kai wayar kunnan ta sai faman jan numfashi take yi daƙyar idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar an watsa mata barkono zuciyarta take ji tana mikata cikin wani irin waje mai dauke da tashin hankali mai girman gaske komai take ji ya tsaya mata cak! ji take yi kamar motar ta ta tuntsiran da ita ta mace ko ta huta da wannan tashin hankalin da kunar da zuciyarta ke yi tana babbaka duk wani sashi na kirjin ta ruhinta take ji yana wani irin fizga mai haifar mata da wani matsanan cin ciwo a dukkan sassan jikinta.
Girgiza kai take yi tana jin yarda yake wani irin sarawa da duk tashin hankalin da take ciki komai take ji a wannan lokacin yana barazana da duk ragowar farincikin da yayi sauya a gareta na filin duniyarta.
Ba ta san abin da ya sa ta fito yau ba bata san mai alkalamin ƙaddararta yake kokarin rubuto mata ba sosai take jin zuciyarta na haifar da wani kunci mai radadin gaske sosai take jin duk wani sashi na jikinta yake narkewa kamar ba na ta ba kafafuwan da suke kan giyoyin motar take jin su kamar ba a jikin ta suke ba ta tabbata da a tsaye take ba za su iya daukar gangar jikinta ba.
Nisawa tayi a daidai lokacin da taji iska mai nuna alamun an daga wayarta ta buso cikin kunnuwan ta runtse idanu tayi gami da tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta tana cizawa kamar zata fizgesu daga mazauninsu.
A hankali ta fara gangarawa gefen titin domin ba zata iya furta ko da kalma daya a yarda take jin zuciyarta ba, ba za iya motsa wani sashi na laɓɓanta a cikin halin tuki ba ji take yi kamar in ta motsa su komai zai tarwatse a gareta.
Sai da ta shafe mintina biyu kafun ta ja wani dogon numfashi ta fesar mai matukar ciwo.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ta fadi can kasar makoshin ta kamar wacce akayi wa dole sai ta ambaci sunan.
"Na'am Areefa".
Ya ansa da yanayi na farinciki a muryarsa.
Runtse idanu tayi kafun ta sake jan numfashi.
"Kana ina Please I need your help right now?".
Yanayin da take furta kalmar cikin sauti mai rauni ya sanya Alhaji Abdulwahaab yin sanyi sosai.
"What is wrong with you Areefa me ke faruwa dake ne naji muryar ki So Sad?".
"Kana ina right now Alhaji Abdulwahaab don Allah ina son ganin ka ko a ina kake ka fada min gani nan zuwa".
Sosai muryarta tayi rauni kamar zata fashe da kuka a hankali ta kai hannunta baki tana toshewa.
"Ok...Cool down Please yanzu haka ina Muhabbir Coffee daidai Alo-Vera Hotel ki zo nan ki same ni".
Ba ta ji ra abin da zai ce ba da sauri ta sauke wayar tana cilli da ita kan kujerar dake gefen ta wani wawan ribas tayi tare da juya akalar motar ta koma kan titin sosai ta hau hanya.
Zabga gudu take yi kamar wacce zata tashi sama ita akaran kanta ba ta san ta nayin sa ba zuciya ce kawai ke aikinta domin ba ta cikin hayyacita motoci da yawa sai dai su kauce mata domin sun lura ba ta cikin hayyacin ta cikin mintina kalilan ta hau titin da zai kai ta alo-vera Hotel kwanar da zata sha saitin W. I .WUSHISHI ESTATE. Sukayi a rangama da wata motar saura kadan su haye juna Allah ya tsagaita amma duk da hakan ta bugar wa mai motar fitilu har sun dan tsage hannu kawai ta daga masa alamun bashi hakuri ta shiga layin girgiza kai yayi mai motar don ya lura bata cikin hayyacin ta.
Tun kafun ta isa Muhabbir Coffee din tayo parking din motarta gefe guda ta fito cikin hanzari murfin motar ma da kafarta ta tura ta shiga sauri kamar zata kifa har tana turgudewa Allah ya taimaka bata je kasa ba.
Ta shiga Get din wajan ta shiga rarraba idanu can gefe guda ta hango shi yana dago mata hannu kamar wacce aka ingiza haka ta tafi tana isa ta tsaya kinkam! A tsaye tana mai da numfashi ta shiga nuna kanta da hannu kirjinta sai faman dagawa yake yi idanuwanta na juyawa kamar mai shirin zubewa a kasa da sauri Alhaji Abdulwahaab ya mike don ya lura bata cikin hayyacinta jakarta ya riko ya ajje kan Table din dake wajan kafun ya riko hannunta ya zauna da ita sosai gorar ruwan dake ajje a wajan ya murɗewa kai ya tsiyaya cikin Glass Cup ya mika mata kau da kai tayi cikin wani irin yanayi.
"Haba mana anshi ki sha ko kya samu sa'ida a zuciyarki".
"Bana tunanin ruwa zan yi mani wani amfani a halin da nake ciki a yanzu".
Ta fadi cikin wani irin yanayi tana daura hannayenta saman goshinta da take ji kamar zai dare gida biyƴ.
"Ki ansa ki sha Areefa ruwa zai miki abin da baki taba zato ba".
Ba ta bukatar surutu da yawa don haka ta anshi ruwan ta kai bakinta aiko sai gashi ta take ruwan gabadaya ta dire kofin da karfi har sai da ya tsage don wahala runtse idanuwanta tayi tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali gumi ya karyo mata saman goshi idanuwanta a lumshe sosai taji wani sashi na zuciyarta da ruhinta sun yi sanyi kadan da ta sha ruwan.
Lokaci guda ta ware idanuwanta kan na Alhaji Abdulwahaab da yayi kuri yana dubanta nisawa tayi cikin fesar da wani zazzafan huci.
"Wai ni Dr.Erena yake so har yana ikirarin zai aure ni".
Ta fadi tana runtse idanuwanta zuciyarta take ji tana kartawa da wani irin tashin hankali mai girma wata irin tsana mai tsanani da take ji akan Dr.Erena take samun fili a zuciyarta tana kara hauhawa sosai take jin kalamansa na ansa kuwwa a kwanyarta da zuciyarta.
Da na sani take yi na zuwan Company yau da na sani take yi da har ta je Office din sa ta saurare shi dana sani take yi da har ta bari kunnuwanta su ka jiyo mata kalaman da suke kokarin tarwatsa mata zuciya.
Wasu hawaye ne masu tsananin dumi taji suna biyo fuskarta da sauri ta ware ido tana kai hannayenta tana taba su murmushi take saki mai tsananin ciwo kafun ta dubi Alhaji Abdulwahaab mamaki fal a zuciyarta da fuskarta murmushi taga yanayi har hakoransa na bayyana kafun ya mike kan kafafuwansa yana taku a hankali hannayensa goye a bayan sa.
Juyowa yayi ya dubi Areefa har lokacin murmushin bai kau ba sai ma kara fadada da ya yi dawo wa yayi ya zauna sosai yana daura kafa daya kan daya ya jawo Mug din Coffee yana kaiwa bakin sa da wani irin yanayi na nishadi sai da ya kurba sosai sannan ya dire ya daura hannunsa kan Table din yana dan kwankwasawa har zuwa lokacin idanuwansa na kan Areefa da tayi fakare tana dubansa a wani irin yanayi mai cike da mamaki da AL'AJABI mai girma gaske wanda ya kusan sanya zuciyarta tsalle sama.
"wondefull Story".
Ya fadi yana mai girgiza kai cike da farin ciki kafun ya dora da fadin.
"Sosai da sosai naji dadin wannan ranar a daidai wannan lokacin da na samu daddadar lamari irin wannan How Comes na ce miki yau ce ranar farko da nake hango cinmma nasarata akan Dr.Erena".
Mikewa ya kuma yi kan kafafuwansa hannunsa rike da Mug din Coffee.
"Areefa ya kamata ace wannan lamarin ya samu nishadi a filin duniyar rayuwarki a yanzu...".
"Alhaji Abdulwahaabbb!!".
Areefa ta fadi cikin wani irin sauti mai haifar da ɗaci a saman zuciya tana mikewa kam kafafuwanta idanuwanta a warwaje tana dubansa ciki da kunci zuciyarta na wani irin zafi.
"Ban san mai yasa kake farin ciki da haka ba, Ban san mai yasa kake so nayi farin ciki da wannan lamarin ba, shin ka mance abin da ke tsakanani da Dr.Erena, shin ka mance abin da yasa na ke zaune a INUWA DAYA tare dashi, shin ka mance bani da makiyi a filin duniyar nan sam dashi, shin ka manta ba wanda na tsana duniyar nan na ke son na ga bayansa sama da Dr.Erena".
Runtse idanu tayi tana jan numfshi kafun ta ciji laɓɓanta tana dakune fuska.
"Alhaji Abdulwahaab ta ya ya ke zaton zan yi farin ciki, ta ya ya kake zaton ko hakorana zan bayyana a fili a dalilin wannan maganar haba mana Alhaji Abdulwahaab kayi tunani mana".
Ta karashe tana komawa saman kujera ta zauna hannayenta dukka biyu ta dafe kanta dasu wani irin yanayi take jin zuciyarta na haifa mata wanda take jinsa kamar kirjinta zai kama da wuta ya babbake duk wata halitta dake da gurbi a filin kirjin nata ba ta san mai yasa ma ta zo wajan Alhaji Abdulwahaab ba tayi tunani zai ce da ita wani abu akan wannan lamarin ba amma sai taga sabanin haka wai farin ciki yake yi har ma da dariya.
"Yaa Salam".
Ta fadi tana saukar da hannunta daya tana dafe kirjinta dake ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske.
"AREEFA!".
Alhaji Abdulwahaab ya fadi da murya mai zurfi. Dago kai tayi ba tare da ta ansa shi ba illa ido da ta zuba masa.
"Wannan lamarin da ya faru nasara ce a tsakanin ni da ke".
Kau da fuskarta tayi jin zuciyarta na kara rura wutar zafin da take ji.
"Nasan zaki ji ba dadi amma wannan hanyar ita ce ta dace ki bi don cimma kudirin ki har ma da nawa".
Girgiza kai ta shiga yi tana yatsine fuska kafun ta mike kan kafafuwanta tana dubansa.
"Ina! wannan ba hanyar mafita bace Alhaji Abdulwahaab bana hango nasara ta a wannan hanyar".
"Don ya furta ya na son ki ko shine kike wa kallon rashin nasara?".
Ta gaji da sauraron kalaman sa domin ranta ya fara baci ba za ta iya cigaba da zama ta na sauraronsa ba.
Hannu ta saka ta janyo jakarta kafun ta dube shi.
"Tafiya zan yi nayi tunanin in na zo maka da maganar nan zan samu mafita a gareka domin cimma burinmu da KUDIRI ashe ba haka bane".
Ta karashe tana takawa kan kafafuwanta.
"Areefa".
Ya fadi yana mikewa da sauri ya isa gabanta yanayin sa ya sauya sosai yake jin tausayin Areefa sai dai wani abu guda yake hango wanda wannan hanyar ce kawai da suka samu ita ce dama da ya kamata ace sunyi amfani da ita kar su sake ta kubace musu.
"ki tuna Areefa kudina ya ansa da sunan muyi haɗaka wajan bude Company kudin da bana wa ba kudin Marayu wanda sam bani da hakki a cikin su kudin da suke zama masifa ga duk wanda ya cisu ya kamata ki tuna ba yarda za ayi na so bayar da gudun mawa ya cutar dake nima ina bukatar naga Dr. Erena ya shiga tashin hankali ina so naga Dr.Erena ya fada cikin halin masifa domin ba mutum bane mai tausayi ba mutum bane mai imani jahadi zakiyi sosai yaci zarafin mutane da ba su ji ba su gani ba sosai ya zalunci mutane wanda na tabbata har dake a ciki. AL'UMMA zaki taimakawa jama'a duniyar na zaki ceto daga fadawa komarsa damarki ce wannan lokacin ki ne wannan Areefa kiyi amfani da ita nasara na tare dake mutane da yawa za su shi miki albarka za suyi miki fata nagari za suyi miki addu'a ki gama da duniya lafiya na rokeki ke kadai ce zaki iya wannan aikin".
Komawa yayi ya zauna yana mai ajjiyar zuciya tausayin Areefa yake ji sosai a ransa ya sani dole taji ba dadi a ranta dole tashiga wani hali na tashin hankali
Amma kuma jahadi za tayi taimakon mutane za tayi ya sani Dr.Erena yana da hatsari Areefa kawai zata iya yin komai in tayi taka tsantsan ba tare da ya gano ta ba musamman yanzu da ya nuna yana sonta ya sani sosai hankalinsa zai karka akanta da komai na shi ya sani Dr.Erena bai iya son abu ba yana nuna maitarsa a fili kuma yana bi ko ta halin k'ak'a ne don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so.
Areefa da ta kasa tafiya tun lokacin da Alhaji Abdulwahaab ya fara bayaninsa gabadaya jikinta yayi sanyi sosai taji zuciyarta narkewa da wani irin rauni mai girma a hankali ta juyo ta dube shi kafun ta gyada masa kai shima kai ya gyada mata don bai gane in da ta dosa ba.
A hankali ta juya ta fara tafiya a jiki a sanyaye zuciyarta na shiga wani iri yanayi tana cakuda maganganun Alhaji Abdulwahaab a zuciyarta da kwakwalwarta har ta fice daga wajan ta isa inda ta ajje motarta tashiga sai da ta shafe mintina kanta akan sitiyari domin komai take ji ya tsaya mata cak! gabadaya taji duniyar tayi mata wani gin-girin-gim kafun ta yi wa Motar Key ta falle kan titi.
*******
A hankali ta turo kofar falon idanuwanta a rufe kadan saboda raɗaɗin da taji sunayi mata kamar jijiyoyin su zasu tsintsinke haka ta zuro kafa cikin falon tana mai ware idanuwanta baki daya tana kokarin gayyato natsuwa ko ya ya ne bata so Hajiya Layla ta san tashin hankalin da tashiga sosai da sosai bata so ta gane tayi kuka da idanuwanta bata so ta saka ita ma cikin tashin hankali don ta tabbata itama akwai abin da ke damun filin rayuwarta.
Nisawa take yi a hankali zuciyarta na kara matsewa wani irin yanayi mai girman gaske idanuwanta ta sauke a inda take tsammanin samunta kamar ko yaushe da ta maida wajan zaunin ta har in ita ba ta nan.
Hango tayi zaune ta zabga tagumi da hannu daya hannu guda m
Kuma rike yake da wani kwali wanda bata gama hakikance na mane ne ba amma zuciyarta ta buga lokacin da taga Hajiya Layla ta kura masa idanuwa ko kaftawa bata yi.
Kara ware idanuwa tayi tana fiddo su kamar wacce zata barsu su faɗo kasa nisawa take yi da wani irin yanayi ganin kwalin dake hannunta sosai ta tsorata tana sakin jakar dake hannunta tana faduwa kasa ba tare da ta sani ba kafafuwanta taji sun shiga rawa kamar za su kasa daukar gangar jikinta da sauri ta fara taku tana haɗe hanya har ta isa gareta ba tare da ta sani ba.
Hannu ta kai ta ansa kwalin cikin wani irin yanayi mai nuna alamun mamaki matuka gaya idanuwanta take yawatawa kan kwalin ba tare da tace kazil ba ta shiga bin Hajiya Layla da kallo wacce ita ma ansar kwalin da Areefa da tayi a hannunta shi ya dawo da ita hayyacinta ta shiga duban Areefa a daidai lokacin kwalla masu yawan gaske wanda suka jima tare a idanuwanta suka zubo ta shiga girgiza kai.
"Maama".
Areefa ta fadi da muryarta mai zurfi idanuwanta da tuhuma acikin su take dubanta tana mai gyada kai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa da mamakin da bata yi zaton taddashi a gidan ba.
"Dama Da...ma ba ki dai...na baaa!".
Ta sake fadi muryarta na rawa kalmomin da take fadi suna rarrabuwa da junansu.
Wani kuka ne ya kufcewa Hajiya Layla hannu ta saka ta toshe bakin ta kafun ta shiga girgiza kai.
"A,a Areefa wallahi na daina ban sha yanzu kwata-kwata ko kaunar ta bana yi kisan nayi miki alkawari har gaban abada ba zan sake ba".
Girgiza kai Areefa ta shiga yi tana mai zubewa a wajan numfashi take ja dakyar zuciyarta na wani irin zafi da radadi kafun ta fesar da wani zazzafan huci.
"Haba mana Maama sau nawa za muyi maganar nan dake na fada miki illar wannan abun likitoci ma sun fada miki wanda suke k'irk'irarta ma sunyi nuni da cewa tana da illa ga rayuwar duk mai ta'amali da ita ya kamata ki san wannan ya kamata ki duba halin da kike ciki ya kamata ace kin ceto sauran rayuwarki da tayi saura a filin duniyar nan kina ji likita ya fadi ta fara baki matsala sosai wanda yace in ba daina wa kikayi ba to tabbas nan da dan lokaci kadan zaki rasa rayuwarki gabadaya ni kuma ba zan so haka ba Maama AKWAI ILLA a rayuwar shan taba tana da matukar hatsari ga duk mai rayuwa da ita kin sani kuma kinji a jikinki lokacin da kika kwanta rashin lafiya kin ga yanayin da kika shiga na tashin hankali da kyar da taimakon Allah ki ka samu kan ki sosai likitoci suka nuna miki dokoki da zaki bi sannan kiyi kokarin fidda sha'awarta a rayuwarki ko ganinta ki nisanta daga rayuwarki haba mana Maama me yasa haka me ya kawo kwallin taba cikin nan gidan?".
Areefa ta karashe cikin muryar rawa da son fashewa da kuka tasowa tayi ta iso gareta ta kama hannayenta ta rike su gam!. Tana mai a jiyar zuciya laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa a hankali.
"Me ya kawo kwallin sigari nan gidan Maama?".
Ta sake fadi idanuwanta na kawo kwalla kafun ta rintse idanu.
"Nayi dana sani a rayuwa ta nayi tir da rayuwar da nayi a duniyata duk a dalilin rashin 'yanci yau na ga illar rashin iyaye yau na ga illar haihuwata da kayi a titi ban san me nayi wa iyayena ba suka yasar dani suka tafi suka bar ni a titin Allah ban san mai yasa sukayi mani haka ba yanzu ga shi nan na rayuwa cikin rashin amfani na tashi cikin rashin 'yanci na rasa mai kwaɓata na rasa mai kula min da rayuwa har ya nuna min kuskure na rayuwata gabadaya ba tayi amfani a duniyar nan ba ni ban yi aure ba balle na samu zuri'ar da za su ji k'ai na ni ban yi rayuwar yanci ba rayuwar titi nayi wacce ba zan ce miki ga yarda na kasance a rayuwata a shekarun yarinta ta ba".
Nisawa tayi wasu hawaye suka zubo mata kafun ta cigaba da fadin.
"kawai na yi rayuwa ce a yarda ta zo mani a yarda Alkalamin kaddara ya zana min wani fannin kuma da nawa kason na lalacewar rayuwata ban san dadin iyaye ba ban san su waye iyaye ba ban san ya yaro yake ji a wajan iyayen sa ba ban san wacce irin kauna ce da ake fadi ana ji a wajan UWA DA UBA ba iyayena sun kasance ne bakin titi da wajan masu abincin saidawa nan ne suka kasance jigon rayuwa ta su ne suka kasance iyaye a gareni har lokacin da na dauki kazamar rayuwa da nake zaton ita ce mafita a gareni na daura a duniya ta".
runtse idanu tayi tana jin yarda kirjinta ke harbawa da duk wani ɗaci gami da zafi a ranta.
"Areefa na daina shan sigari tun da nayi miki alkawari yau ma fita nayi aka zageni aka tsine mani har ake kokarin marina akan sigari wai don kawai nace na daina yaro karami wanda in a haife ne na haife shi in jika ne ma zan iyayi dashi amma akan abin banza abin Allah wadai ya zage ni yana jifana da kwalin sigari dake hannunsa Yaa Allah wannan wacce irin rayuwa ce Areefa nayi dana sanin rayuwa a duniyar nan".
Wata irin zabura tayi idanuwanta a warwaje hannayenta saman kirjinta.
"Maama zagi fa kika ce waye ya zage ki fada min waye shi na nuna masa ke ma kina da gata a rayuwarki rashin iyaye ba hauka bane zan nuna masa kina da gata kuma kina da 'ya a filin duniyar nan da ta san darajar ki da kimarki ki fada min shi please Maama".
Cikin sauti take maganar kamar wacce ta fice daga hayyacin ta da sauri Hajiya Layla ta mike ganin Areefa na kokarin ficewa daga gidan sosai ta rikota ta zauna da ita tana mai kwantar da ita a jikinta tashiga shafa mata baya a hankali har zuwa lokacin idanuwanta na zubda hawaye masu tsananin zafi da take ji kamar za su keta mata duk wani sashi na kirjinta.
"ki bar komai na yafe masa rayuwa ce ta zo da haka inda ban yi harkar shan sigari ba ba yarda za ayi ya tare ni a hanya har ya ci mani mutunci in ba don ya ga alamun nayi shaye shaye ba a zamani na ba yarda za ayi ya dube ni yace na bashi sigari komai ya faru ni ce sanadi ni ce sila Areefa ki bar komai na yafe masa".
Da sauri ta dago kanta tana duban Hajiya Layla da take shafe hawaye.
"Haba mana Maama hawaye fa ya sakaki zubdawa akan mi zaki ce a bar shi bayan ya ci miki mutunci".
"ki bar shi nace kawai ki bar shi komai ya wuce a wajena har a zuciyata na yafe masa fata na Allah ya shirye shi ya sa daga kaina ya daina abin da yake yi domin na lura illar shaye-shaye yawa gareta ba abin da ba zata iya sanya wa ka aikata ba wanda zai cutar da rayuwarka sosai AKWAI ILLA sosai da sosai".
Ta karashe tana mai kalato murmushi tana daurawa a fuskarta domin kwantarwa da Areefa hankali domin bata so ta sake sanya rayuwarta a damuwa nan ta shiga bubbuga bayanta domin kwantar mata da hankali.
Wani numfashi a Areefa taja mai tsayi kafin ta saki ajiyar zuciya.
"Maama ke dama baki da iyaye dama ke ma marainiya ce kamar ni".
"Ya isa haka Areefa mu bar wannan zance haka ba shi da amfani".
Ta katse ta da wani irin yanayi da ta ji zuciyarta na shiga da tashin hankali mai girma.
"Mai ya dawo dake wannan lokacin ba tare da lokacin tashi ya yi?".
Ta fadi domin kau da zancen da Areefa ta dauko.
Da sauri ta tashi zaune tana duban idanun Hajiya Layla kafun taji wata irin tsanar Dr.Erena ta sake samun fili mai girma a zuciyarta a hankali ta shiga cizon laɓɓanta tana runtse idanu.
"Dr.Erena Maama".
Ware idanu tayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo a tsakar falon lokaci guda ta tsaya cak! fuskarta ta kara cakuɗewa da bacin rai mai girman gaske.
"Ba dai kin yi sake ya gano ke wa ce ce ba in kuwa haka ne komai zai wargaje mana".
"A,a Maama wai cewa yayi yana sona har cewa yayi zai iya aure na in har na yarda dashi".
Zare idanu tayi waje bakin ta na buɗe ta iso ta zauna tana janyo Areefa jikinta gami da sarke hannayensu waje guda wani murmushi na takaici ta sako kafun ta dubi Areefa sosai da tayi fakare tana dubanta ganin abin da ke fuskarta.
"Lokaci ya zo Areefa lokacin da nake dako ne Allah ya kawo mana shi tabbas lokaci ne ya zo tsakanimu da Dr.Erena".
"Ban gane ba Maama?".
Areefa ta fadi a dan tsora ce tana kwace hannayenta daga cikin na Hajiya Layla.
"Karki damu kawai ke dai ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da zuwa aiki karki sake ko da wasa ki nuna masa baki amince ba sannan gobe karki sake ki ce ba zaki office ba ki shirya ki je ki bar komai a hannu na".
Cikin rashin fahimta da kara bayyanuwar mamaki ta shiga motsa laɓɓanta tana kokarin yin magana amma Hajiya Layla ta hana ta tana mai cewa.
"Maza ta shi ki je ki watsa ruwa ki ci abinci ki huta kafin lokacin Sallah yayi".
Ba musu ta mike zuciyarta da wani irin AL'AMARI wanda ta kasa gane kansa sosai kanta ya kulle sosai taji tunanin ta ya kasa buɗe mata wannan lamari wanda ya jefata a duhu sosai da sosai haka ta ja jiki tana duban Hajiya Layla har ta isa dakinta.
Mikewa Hajiya Layla tayi tana kai kawo cikin falon hannayenta take hadawa waje daya tana bugawa wani irin yanayi take ji a jikinta sosai taji dadin maganar nan da Areefa ta fadi mata komai take hangowa ya canza sosai take hango nasara a tsakanin ta da Dr.Erena za ta nuna masa ita wacece kuma za ta nuna masa mace ma daraja gareta a duniyar nan ba kamar yarda ya dauka ba...
*_KAMALA MINNA_*😍😍😍
UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN.
💕💕 *_Kibiyar Ajali Taken Sone, Ya Mamayen da Gangawa, Yai Min Barin Makauniya_* 💕💕
-- *Hamisu Breaker*
Tunda ta dago labulan dakin ta sanyo kai take dubanta da kallo kamar wacce taga bakuwar fuska, sosai ta lura da Mariya cikin yan kwanakin nan gabadaya ta sauya kamar ba ita ba sai sanyi jiki da rashin son magana ko aiki take yi haka take zama wata sukuku duk ta rame sai idanu da sukayi mata zuru-zuru ga tsayi da takuma yi sosai.
Gyaɗa kai Umma tayi kafun ta kau da kanta daga kallon da takeyi mata sosai ta fahimta sosai ta gane akwai abin da ke dawainiya da 'yarta wanda yake haifar mata da damuwa sosai a zuciya da ma jiki baki daya ba ta san mai Mariya take nufi da hakan ba ba ta san wacce irin rayuwa ta daukarwa kanta ba na zama cikin damuwa sosai ita kanta abin ke damunta a zuciyarta sai dai tana boyewa ne saboda ita Mariyar domin ba ta bukatar ta ganta itama cikin damuwa abubuwa da yawa suke nukurkusar zuciyarta musamman batun mahaifin Mariya ba shi babu dalilin sa anyi cigiyar amma ina ta sha fita ba tare da kowa ya sani ba ta nufi cikin gari amma ina haka take dawowa jiki a sage tasha zama tayi kukan dare domin rage radadin dake damunta in abun yayi mata yawa alwala take daurowa ta kaiwa Allah kukan ta akan ya bayyanar mata da mijinta in har yana raye a filin duniyar nan.
Wasu kwalle taji sun kawo mata ziyara cikin idanuwanta da sauri ta shafe su kafun Mariya ta gani. Dago kanta tayi tana duban Mariya dake tsaye tana zare hijabin makarantar da ta dawo kafun ta zube kan katifar tsakar dakin idanuwanta gabadaya ta daga sama tana kallon rufin dakin.
"Mariya!".
Umma ta fadi cikin wata irin murya mai zurfin gaske tana sauke idanuwanta akan Mariya da ta dago tana dubanta daga kwance.
"Tashi mana magana nake so muyi".
Wani irin yatsine fuska tayi kamar wacce zata fashe da kuka gabadaya bata so taji ana yi mata magana komai take ji ba dadi zuciyarta take ji wani iri tana yi mata ciwo mai girman gaske bata so a fiye tuhumanta akan abin da ke damun ta domin bata da abin da za ta iya cewa tasan Umma kuma tambayar ta za tayi gabadaya sai taji wani ba dadi a hankali ta shiga kokarin tashi tana cizon laɓɓanta kamar zata tsinke su zama tayi sosai kanta a kasa domin bata bukatar Umma ta gane yanayi da take ciki domin ta tabbata duk wanda ya kalli idanuwanta sai yayi zargin wani abu daban ita kanta ta san tana cikin tashin hankali sosai take jin canji yanayi a jikinta sosai ta lura da komai nata ya sauya ji take yi kamar ba ita ce ba zuciyarta take ji tana wani irin ciwo mai matukar raɗaɗi da zafi ga kasar ruhinta da yake furzar da wani zazzafan huci.
"Mariya akwai abin da kike boye wa a ranki, wanda kika kasa bayyanar dashi a filin rayuwarki na lura dake kusan wata guda kenan gabadaya kin sauya kamar wacce bata da lafiya Me yasa haka?".
Umma ta fadi cikin sanyin murya
Mariya kamar jira take yi Umma ta idar sai hawaye shar-shar sun fara zubo mata wani kuka take ji yana zuwa mata da sauri ta kai hannunta tana rufe bakin nata zuciyarta taji tana yi mata wani irin zafi da raɗaɗi kamar zata fasa kirjinta tayo waje kanta taji yana juya mata komai take kin na filin duniyar yana zama kunci a gareta ji take yi kamar ta mutu ta huta da wannan rayuwar ta duniyar nan ita kanta ta sani tana cikin tashin hankali zuciyarta ciwo take yi ciwo mai girman gaske wanda ko tantama ba tayi shine ajalinta.
Ware idanu Umma tayi sosai tana kallon ikon Allah wai na kwance ya fadi hawayen da take gani a fuskar 'yarta ya sanyata faduwar gaba.
"Yaa Salam! Mariya meye haka nake shirin gani hawaye a idanuwanki da girman ki me aka yi miki har haka ya sanya ki zubda hawaye".
Runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyarta ke zafi da wani irin huci kirjinta take ji yana kartawa da wani tashin hankali mai girman gaske.
Laɓɓanta ta shiga motsawa sosai muryarta tayi rauni jikinta har rawa yake yi.
"Inda mahaifina na filin duniyar nan ba yarda za ayi na kasance a haka, inda mahaifina na kusa dani ba yarda za ayi rayuwata ta kasance a haka, inda mahaifina na filin rayuwata ba wanda ya isa ya saka ni gaba ya dasa min ciwon rai. Ban san me ke kokarin shigowa rayuwa ta ba, Ban san me yake shirin faruwa dani ba, ban san wani irin BALA'I bane yake zawarcin rayuwa ta ba...".
A firgice Umma take dubanta kamar wacce ta ga sabuwar halitta wani irin bugu take jin zuciyarta nayi daga kirjinta sosai taji duniyar na juya mata tsoro take ji yana kara girma a gareta komai taji lokaci guda na duniyar na juya mata tsoronta daya ba damuwar batar Mijinta bane ya sanya 'yarta cikin tashin hankali har haka gabanta taji ya sauya bugu da sauri-sauri a hankali ta shiga nuna Mariya da hannu idanuwanta na kawo kwalla ita kuwa Mariya sai kaar sautin kukan ta take yi kamar wacce ake bugu.
"Mariya karki ce dani damuwar rashin mahaifinki ce ta kai ki har haka, karki ce dani jarabawar da Allah ya dorawa rayuwarki kike kokarin butulce masa karki ce mani kin kasa YARDA DA ƘADDARA ba fa ke kadai wannan abun ke damu ba ni fa Mijina ne shi kadai ne yayi mani saura a rayuwata bani da kowa sai shi akan sa na rasa iyaye na ga shi yanzu shima na rasa shi amma nayi TAWAKKALI na mikawa Allah kuka na domin shi kadai ne zai yi mani duk wata maganin matsalata Mariya ki sassautawa rayuwarki rayuwa bata son a dauke ta da zafi ke fa yarinya ce wacce take matakin kuruciyarta.
Bai kamata ace kin matsawa rayuwa ba karatu kike yi ya kamata ace kin ajje komai a gefe ki bar komai a zuciyarki sannan ki mikawa Allah lamarinki".
Sosai Muryar Umma tayi sanyi zuciyarta take ji tana zafi da wani irin raɗaɗi mai girman gaske mikewa tayi kan kafafuwanta tana jin yarda idanuwanta suke kawo ruwa ficewa tayi daga cikin dakin domin ba za ta iya zama ba ta tabbata in ta zauna dukkannin su sai an rasa mai rarrashin dan'uwansa a cikinsu.
Kwanciya Mariya ta koma tayi tana faman ajjiyar zuciya mai sanya kirjinta zafi sosai runtse idanuwa ta tayi ba abin da take hangowa sai tashin hankali mai girman gaske a bangarori UKU wanda suke shirin haifa mata da BALA'I UKU.
Ba ta san ya rayuwarta zata kasance ba cikin lokacin nan ba ta san ya za tayi ba sosai komai ya tsaya cak! a kwanyarta ina ma ta san a shafin rayuwarta akwai wannan masifar da ta roki Allah ya kasheta tun a cikin Ummanta ba ta san haka duniyar take ba da kwazazzaban tashin hankali da bata shigo ta ba amma ina ikon Allah sai kallo duk mai sauran rai a duniyar nan yana DA SAURAN KALLO.
Iskar da taji ta shigo cikin dakin ne ya sanyata sauri buɗe idanuwanta da suke rufe sun kaɗa sunyi jajir kofa ta kalla Hafsi ta gani tsaye tana watsa mata wani irin kallo tana faman yatsine fuska gami da tsaki sosai ta hango kiyayya tsantsa cikin idanuwan Hafsi tun da take da ita bata taba ganin tayi mata irin wannan kallon ba mai cike da tsana da sauri ta tashi zaune tana cizon laɓɓa.
"Yo me akai da maza, ai yanzu a ka fara zaman kishi da uwar miji, ki je waje ana kiran ki".
Tana fadin haka ta buga wani uban tsaki kamar zata tsinke harshen ta ta fice daga cikin dakin.
Fakare Mariya tayi tana kallon ikon Allah wai uwar miji da cin kazar amarci wasu hawaye taji sun zuba mata a zuciyarta ta na ayyanawa anya tana da sa'a a filin duniyar nan anya kuwa ba wani laifi tayi wa ubangiji ba yake hukuntata ta wannan hanyar.
"Astagafurullah wa'atubu ilai".
Ta shiga fadi kafun ta shiga kokarin komawa ta kwanta tayi luf! kamar wacce bata numfashi tunanuka ne taji sun addabi zuciyarta da kwanyarta da sauri ta mike tana goge fuskarta ta zura hijabin ta akan kayan makarantar da ba ta cire ba waje ta fito ta zira takalmin ta tana dube dube kafun ta jiyo karar saukar ruwa cikin bandakin su ajiyar zuciya ta sauke don ta tabbata Umma ce a hankali tayi hanyar waje Hafsi dake tokare bakin kofa tana kallonta wani mugun tsaki taja fuskarta a hargitse kamar zata fashe da kuka ta juya ta koma cikin dakin kamar wata sabon kamu bakin gadon karfe ta zauna ta na faman turo baki gaba tana wani kumbure-kumbure kamar zata fashe.
Dubanta Goggo Marka ta shiga yi da mamaki ganin yarda take hauhawa kamar fulawa taji yis.
"Ke kuma meye haka na ga sai faman hawa kike kamar fulawa?".
Sake turo baki tayi gaba tana buga kafa a kasa.
"Haba Goggo wai ni nafi kowa bakin jini ne a garin nan ace kullum nikenan ina zaune ko matayi babu".
Zaro ido Goggo Marka tayi tana ajje kaɗin da take yi kafun tashiga sallallami tana tafawa hannaye baki sake.
"Muhammadu dan abdullahi me nake shirin gani Hafsi".
Kau da kai tayi tana turo baki gaba.
"Ni gaskiya na ga ji kina kallon Mariya sai zarya samari masu zunduma-zudunman motoci suke mata jiniya a kofar gida nikuwa ko 'ya'yan gidan Malam Shehu bana gani".
"Iyee to ai shikenan bara na zo na sanya a rubuce miki suratul-Yusufa ki shanye tun da kin rasa mashinshi ne sai mu ga yarda Allah zai yi".
Goggo Marka ta fadi tana mai bankamata harara kamar idanuwanta za su zubo kasa.
"nifa gaskiya Goggo kisan yarda za kiyi dani ba yarda za ayi ace Mariya ta fini farin jini samari kanta kawai suke zarya nikuwa kamar na hadiyi jaɓa don bakin jini dame ta fini ki duba fa ki gani".
Ta fadi tana mai mikewa tana jujjuya jikinta.
Mamaki fal! zuciyar Goggo Marka gabadaya ta rasa ma abin da zata ce sai faman bin Hafsi take yi da ido ba tayi zaton Hafsi za tayi haka ba ba taba zaton irin wannan maganar zata fito daga bakinta ba ba kunya ba tsoron Allah.
Girgiza kai tayi tana mai sake duban Hafsi kwalla ta gani a idanunta tana yatsine fuska kamar zata rushe da kuka da sauri ta ware idanu ciki da tu'ajibi.
"Samarin Mariya Uku kuma duk masu Mota ni kuwa ko mai keke bani dashi ni gaskiya ba zan yarda ba ni dai kawai ki san yarda zakiyi dani na gaji nima saurayi nake so na ganni dashi in ba haka ba ai sai Mariya ta rainani sosai da sosai".
"Ya isa haka Hafsi yi shiru zauna muyi magana".
Turo baki tayi tana zauna sai faman kumburi take yi.
"Ke kina da wanda kike so?".
"Na fa ce miki ba wanda yace yana sona sai fa kwanaki Danliti mai gini yace wai ni yake so ni kuma ba abin da zan yi dashi katon hanci gareshi ga kunnuwa fala-fala".
Kuri Goggo Marka tayi mata dariya ta so kama ta amma sai ta kanne tana mai cewa.
"Naji to ke yanzu wa kike so?".
farrr! tayi da idanunta tana mai saka dan yatsa cikin baki kamar mai son tunano wani abu kafun ta dubi Goggo.
"ni so nake yi na samu mai mota irin na Mariya ko ma ta ban saurayin ta guda daya a ciki".
"Shikenan waye a cikin su kike so nayi miki Alkawari zaki same shi Hafsi farin cikinki shine nawa yo me akayi da waccan mai kalar zazzafin shawarar ki sha kurumin ki ko duka samarin kike so zaki mallake su....".
Wani ihu tayi tana mai kaiwa Goggo cafka tana rungume ta sai faman kyalkyalar dariya take yi.
"zo muje na zabi wanda ya zo yanzu gashi can a waje zo muje ki ganshi mai kyau ne motarsa luntsumemiya gashi dan gayu".
"Nifa tsiyata dake gajen hakuri wallahi Hafsi me zamu je yi kuma ke dai kwantar da hankalin ki kamar kin yi bako ya mutu ki bar komai a waje na shi da kansa zai zo yana rokonki ki so shi".
Wata irin dariya ta sake yi kafun ta mike tana tikar rawa.
Ita dai Goggo Marka baki ta saki tana kallon ikon Allah.
Tsagaitawa tayi da rawar da take yi ta shiga dube-dube kafun ta hango abin da take so kwanon soson wanka ta dauka tana duban Goggo Marka sannan ta fice.
Goggo Marka ta margaya kai tana mai fadin.
"ai sha kuruminki magana ai kuma ta kare mata tace da mijinta shege".
******
Tun da Mariya ta doshi soron gidan su take ji gabanta na tsananta faduwa sosai take jin wani iri kamar ta koma amma wani sashi na zuciyarta na ingizata da taje ta gano waye sai da ta tsaya ta numfasa gami da saita kanta sanan tayi shahadar kuɗa ta fice gabadaya fuskarta a kasa.
Tsaye yake jikin motarsa kansa na duban takalman dake kafarsa kallo daya zakayi masa ka gano irin ramar da yayi sosai da sosai ya kara haske duk da duhun fatar da yake da ita takun da yaji ne ya sanya shi dago kansa a daidai lokacin ita ma Mariya ta dago kanta gabadaya suka sarke juna da kallo zuciyoyinsu suka shiga bugu da sauri-sauri kowa ya kasa dauke ido daga kallon dan uwansa sai da suka shafe tsayin lokaci kafun Mariya taja wani dogon numfashi kafafuwanta taji sun shiga rawa sosai ji take yi kamar zata zube kasa.
"Yaa Rabbi!".
Ta furta cikin wani irin yanayi na rashin hayyaci a hankali tashiga juyawa domin komawa cikin gida gaban ta ji yana duka ba ta san abin da yasa ta fito ba, bata san ya akayi ba ta fito ba ba tare da ta san waye ba tajima da ajje Huzaif a gefe duk da kullum zuciyarta sai ta yi mata tunanin shi bata so ace sun sake haduwa ba domin bata bukatar sake ganinsa domin ganin sa ba karamin sanya ta yake yi cikin tashin hankali ba.
Ciwon zuciyarta daɗuwa yake yi tashin hankalin ta karuwa yake yi duniyarta sake rikicewa take yi a duk lokacin da tayi arba da Huzaif ba ma Huzaif ba duk wani wanda yake da takomashin sanya zuciyarta tashin hankali.
"karki yi mani haka Mariya zuciyata zata iya bugawa a ko wani lokaci in har kika ki tsayawa ki saurare ni ban san ya ba zuciya tana kuna ruhina na ciwo gangar jikina ya zama kamar ba nawa ba".
Numfasa yasake yi yana jin yarda kirjinsa ke harbawa da duk wani tashin hankali da yake ciki zuciyarsa ciwo take masa ciwo mai tsanani.
"Rayuwata na cikin hatsari komai nawa ya shiga ruɗani ban san ya zan kwatanta miki tashin hankalin da duniya ta take ciki ba na rokeki ki saurare ni Mariya".
A hankali ta fara tsaigatawa da tafiyar da take yi gabadaya taji duniyar na juya mata kafafuwan take ji kamar suna narkewa jikinta rawa yake yi zuciyarta lokaci guda ta sauya da bugu tana buɗe shafin da ta baiwa Huzaif ya zauna a ciki runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyar ta ta ke kartawa kamar ana soka mata KIBIYAR AJALINTA.
A hankali ya shiga takowa yana jin yarda bugun zuciyarsa ke canza bugu da wani irin yanayi game da Mariya numfashi yake ajjewa da duk kamshi da yake ji yana tasowa daga jikin Mariya yana haifar masa da wani irin yanayi na kasala a jikin sa da zuciyarsa gabanta ya karaso ya tsaya yana mai juya idanuwansa da suka kaɗa kadan fuskarsa cike da yanayi na rauni hannunsa ya kai saitin in da yake zaton zuciya na wajan ajje.
"Mariya kin ga nan dina ji nake yi kamar KIBIYAR AJALI ake sokamin ji nake yi kamar KASKON WUTA ake sauke mani a wajan Mariya sosai nake jin wani iri a game dake sosai nake jin zuciya tana kara buɗe fili mai girman gaske a game dake komai ma da komai na zuciyar ke ce a cikinsa...".
"Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka na gaji da jin wannan kalaman ka bar ni haka in har ba so kake yi kwanyarta ta tarwatse ba in har ba so kake yi zuciyata ta buga ba na mutu hankalin ka ya kwanta".
Numfashi ta shiga ja ta kai hannayenta duk biyu tana rufe bakinta jin kalaman nasa take yi kamar saukar narkakkiyar dalma a zuciyarta jin sa take yi kamar yana doka mata ganga mai matukar kara a cikin kunnuwanta sosai taji bugun zuciyarta ya sauya komai take ji na jikinta yana narkewa kamar ruwa.
'Yaa Allah'.
Ta furta a can kasar zuciyarta da take ji tana kecewa da tashin hankali mai girman gaske.
"Mariya...".
"Nace maka ya isa haka ka bar zuciyata ta huta mana Huzaif".
Ta sake katse shi tana toshe kunnuwanta da take ji kamar za su tsinke.
Runtse idanu Huzaif yayi yana jin sautin muryarta na amsa sauti mai girma a kunnuwansa da kwanyarsa sosai ya ji zuciyarsa na bugawa da yanayin da Mariya take nuna wa a gareshi numfashinsa yake ji ya canza yanayi yana sama da kasa kamar zai dauke cikin yanayi na ciwo yake cizon laɓɓansa.
"Baki so na ko Mariya baki kauna ta bakya son gani na a filin duniyarki ko kiyi hakuri zuciyata ce ta matsa min zuciya ta kasa hakuri gabadaya ta hauka ce a dalilin ki ba ta jin sautin komai sai naki Mariya ki taimaka Huzaif din ki ne fa".
Ya karashe muryarsa na karyewa da yanayi na son kuka a hankali yake hadiyar wani abu mai tauri da ya tsaya masa a kirji zafi yake ji zafi na sosai da sosai kansa yake ji yana kokarin darewa biyu nauyi yake ji yayi masa ji yake yi kamar bana sa ba.
A hankali ya fara juya yana kai kawo kamar wani sabon hauka.
"Ban sani ba ashe zuciya ta tayi ganganci, ban san zuciya ta hauka take yi ba, ban san wai dama hauka nake yi ba, ban san dama ban dace da wajan da zuciya ta kawo ni ba, ban dan dama ni kadai nake jin irin wannan yanayin ba a zuciya komai nawa ya sauya ya canza kamar bani ba, kamar ba Huzaif ba duniyar ta yi wani iri ba dadi komai ma ba dadi".
Sosai Mariya ta tsorata da yanayin da taji yana sambatu idanuwanta sosai suka fito waje kanta ta ji ya shiga juyawa kamar zata zube kasa runtse idanu tayi zuciyarta na wani irin bugu da sauri-sauri.
"Yaa hayyu Yaa Kayyum".
Kawai take fadi wasu zafafan HAWAYEN ZUCIYA ne taji suna saukar mata jin su take yi kamar tafasassu.
"Shikenan Mariya na tafi...na tafi tun da ba ki son ganina na takura miki ko yi hakuri shikenan na tafi".
Ya fadi yana mai daga mata hannu murmushi a fuskarsa mai sanya zuciya ciwo mai girma a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.
"Huzaif!".
Ta fadi da wani irin yanayi mai girman gaske cak! Ya tsaya yana mai juyowa gabadaya idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir.
"Kar ka tafi kayi hakuri karka ga laifi na nima ba yi na bane laifin zuciya tane ban san ya zan yi ba komai ya kulle a cikinta ta kasa daukar komai ma".
Duban ta yake yi da wani irin yanayi cikin idanuwanta yake hango wasu abubuwa masu girman gaske su na sanya jikinsa narkewa da wani irin yanayi.
Baki ya shiga motsawa yana nuna ta da hannu magana yake son yi amma ya kasa sai faman girgiza kai kawai yake yana sakin wani yaƙe mai girma a fuskarsa.
Wani dogon tsaki suka ji an saki duk kan su suka juya suna duban in da suka ji sautin na tashi.
Hafsi ce tsaye ta rike kugu sai faman kumburi take yi kamar zata tarwatse wani kallon tsana da ƙi ta sake jifan Mariya dashi tana faman huci kamar kububuwa kafin ta juyar da kallonta wajan Huzaif tana kare masa kallo zuciyarta take ji tana shiga yanayi game dashi girgiza kai tayi tana mai tsartar da yawu a hankali ta juya tana kallon Mariya ita ma ita take kallo cike da mamaki da tu'ajibi.
"Huzaif sai anjima"
Mariya ta fadi cike da wani yanyi mai ciwo yana kokarin yin magana amma ina har ta shige cikin soro duban Hafsi yayi cikin haushi da takaici ji yake yi kamar ya shake ta don bakin ciki dunkule hannu yayi yana bugun iska yana mai cizon laɓɓa da sauri ya juya jikin sa sai kyarma yake yi ya isa wajan motarsa a hanzarce yayi mata key ya fizge ta rai bace har yana baɗe Hafsi da kura ya bar unguwar.
Wata irin shewa tayi tana tafa hannunta sannan ta juya cikin sauri ta fada cikin gida ranta fes!!...
0 comments:
Post a Comment