Dedicated to all Victims of Rape, never give up, fight for your right, this is not something to be ashamed of your self. Make the guilty ones feel ashamed of themselves* ππΎππΎππΎππΎππΎ
"Garin Dukku jihar Gombe, gari ne wanda akasarin mutanen dake zaune wajen fulbe ne, ma'ana fulani ne. Ni Sameena tafe nake cikin garin ina bin tsarin garin da kallo yayinda zuciyata ta cika da nishad'i. Can na hangi wata matashiyar budurwa wacce ak'alla bazata gaza shekaru goma sha shida 16 a duniya ba. Daga yanayin halittarta zaka fahimci cewa bafulatana ce ta usul. Bata da matsanancin tsayi snn bata a layin gajeru, farinta irin mai d'auke idon nan ne don saida ta matso kusa sosai na fahimci hakan. Yanayin suturan dake jikinta zai tabbatar maka iyayenta talakawa ne sosai. Silipas din dake k'afufunta kuwa duk ya b'ule yaji jiki.
"Sauri take tamkar mai shirin tashi sama, yanayin tsoro da firgici da ya wanzu a fuskarta zai tabbatar maka cikin matsanancin tashin hankali take. Kaman ta zunduma a guje haka take tafiyar, Yar da d'an karan dake hannunta tayi ta soma sassarfa hadi da gudu gudu sakamakon jiyo muryar dake sata firgici koda a mafarkinta ne tana k'walla mata kira har waje ake jiyowa,. *ZUBAIDAH! ZUBAIDAH, ZUBAIDAH!!!
"Ni kuwa Queen Samy nace " Bari na bi wann yarinya na rubuto wa d'inbin masoyana labarinta mai cikeda tausayi, Al'ajabi da kuma ban mamaki had'i da darrusa masu girgiza zukata.
"Dan ubanki sai yanzu kika daman dawowa daga karuwancin naki? Macen dake tsaye tsakar gidan rik 'e da guga ta fad ' tana watsa wa Zubaida mugun kallo me nuni da cewa zaki yaba wa aya zak'inta.
"Bakinta na rawa take fad 'in Yaya Hadiza wllhi ban sami Yayan a kasuwa bane shine na k'arasa bakin tasha..... Ai bata gama cewa tasaha ba Yaya Hadiza ta jefa mata gugan dake hannunta ji kake tum ya fad 'I a tsakar kanta.
"Durk'usawa Zubaidah tayi tana rik'e da tsakar kanta hawaye na zuba bisa k'uncinta.
Hadiza ta k'araso gamida mak'urota tana fad'in" Dan ubanki ni na aikeki bakin tasha, wani munafurcin ne ya kaiki bakin tasha, auho kice mun karuwanci kika tafi, shegiya Me suffan mayu da aljanai. Rankwashin da ta sake mata a tsakar ka yasa Zubaidah sakin k'ara sabida azaban dataji.
"Hadiza ta shiga janta a k'asa tana fad'in" Au kuka ma zakiyi shegiya munafuka saikace wacce na bugeki toh bari kiga na tapkeki sosai sai kiyi mai dalili.
"Duk kukan da Zubaidah take tana rok 'on Hadiza tayi hak 'uri ko gizau bata fasa jibgangta ba kaman Allah ne ya aikota.
"Inna Furera mak'ociyarsu ce ta shigo a guje don ceton Zubaidah dama mak'ota sun saba shigowa kawo mata d'auki, tunda Hadiza ta tsefe ido taci mutuncinsu tsaf suka daina, saiko Inna Furera ce kawai bata fasa ba.
"Da sauri tayi tsalle ta kwace Itacen da Hadiza ke jibgan Zubaidah dashi, dama Jadiza irin ingarman matan nanne.
"Ta shige tsakani tana fad'in" Haba, haba Hadiza, anya kina kuwa tuna mutuwa, kullum sai ki kama wann 'yar marainiya kita jibga ke ko tsoron kamuwar Allah bakya yi. Cewar Inna Furera .
"Galala take Kallon Inna Fure kafin ta gyara tsayuwa ta soma fad'in" Fure! Fure!! Fure!!? Billahilazim hawainiyarki ta kiyayi ramata, banda munafunci irin taki ina ruwanki da ita, ci kike bata ko sha, cikin biyu babu d'aya. Toh wllhi wllhi ki fice a idanu na.
"Inna Fure tai murmushin takaici kafin tace " Lokaci ne, da zaran lokacin da Zubaidah zata sami kulawata yazo zata samu kuma ke baki isa kiyi komai ba.
"Shewa Hadiza ta kwashe dashi kafin tace " Ai dama nasan wajen munafukin wann d'an naki me matse yaran mutane a lungu take zuwa, bacin haka babu abinda zai kaita bakin tasha, Toh wllhi idan ni Hadiza ina numfashi Zubaidah bazata auri Ummaru dreban tanka ba. Ke na tak'sita maki zance Zubaidaha bazata tan's aure a rayuwarta ba, makarantar data samu na bari tayi ya isheta, amma aure kam saidai tayitaji k'annen bayanta suna tafiya d'akin miji amma banda ita, tunda dama sa 'anninta Sun k'are k'annenma sun kusa k'arewa. Ta juyo ta narkawa Zubaidah da har lokacin kukan zuci take hawaye na bin k'umcinta tace " Ke kuma bak'ar munafuka ki tashi ki min wanke wanke kafin ki d'aura sanwa don yau islamiyar ma ba zuwanta zakiyi ba. Daga haka ta wuce d'aki fuuu kamar me shirin tashi sama.
"Inna Fure ta girgiza kai ta k'arasa ga Zibaidah wacce ke faman mik'ewa da k'yar sabida raunin da Hadiza taji mata da itace, tsugunawa Inna Fure tayi tausayin yarinyar ya cika zuciyarta, a hankali tasa hannu ta goge k'wallan da ya zubo mata. Hannu tasa ta shiga sunce d'aurin da Hadiza tai ma Zubaidah da igiyan guga.
"Suna had'a ido Zubaida taji wani sabon kuka na shirin kufce mata, ........
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: πππZUBAIDAHπππ
02
*©Sameena Aleeyou... ✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum.... ππ_
*Dedicated to all victims of rape, never keep silence, keep fighting for your right, this is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves*ππΎππΎππΎππΎ
"Murya na rawa Zubaidah take fad 'in" Inna meyasa iyayenmu suka mutu suka barni dagani sai yaya na, meyasa Yaya na ya kasance haka, meyasa bai zama kaman ko wani d'an Adam ba...... " Tausayin kalamanta sun cika zuciyar Inna Fure, a hankali ta kwance bakin zaninta ta goge wa Zubaidah hawayen dake kwaranya a fuskarta. Hannayenta ta rik 'e suna fuskantar juna kafin ta soma fad 'in" Zubaidah kar ki bijire wa ubangijin ki, kar ki bari shedan ya rinjayi zuciyarki, har yake kawo maki ire iren wad'an nan tunani. Mutuwa dole ce kan ko wani mahaluk'i, snn kasancewar yayanki cikin mutane marrasa k'oshin lafiyan k'wak'walwa jarabawace daga Allah, wanda kema jarabawar ya shafeki. Shi kansa Habibu baijin dadin abinda Hadiza ke maki, amma babu yanda ya iya, bazai iya k'watan 'yancin kansa ba balle naki daga hannun Hadiza, hak'uri shine zakici gaba da yi.
"Goge hawayen tayi kafin ta furta a hankali " Kenan shikenan ni bazan tab'a jin dad'in rayuwa ba kenn, bazan rayu kaman yanda ko wani d'an adam yake rayuwa cikin 'yanci ba. ...."Kasa jure saurarenta Inna Fure tayi sabida tausayi, mik 'ewa tayi kafin tace "Tashi ki soma ayyukanki kafin ta fito ta sameki. Jiki a sanyaye Zubaidah ta mik 'e daidai lokacin " Kamalu d'an Yaya Hadiza ya fito cikin shirin tafiya islamiya fuskarsa da alamun bacci ya tashi, yaro d'an shekaru bakwai a duniya. Rungume Zubaidah ya k'araso yayi yana mata magiyan ta shirya su tafi islamiya, itama rungumesa tayi tana k'k'arin lalumo k'aryar da zata shata masa, don tasan yau kam babu ita babu islamiya. Inna Fure ta fice tana sak'sak'en lamarin Zubaidah a zuciyarta.
"Kamalu ya lura da hawayen dake bisa fuskan Zubaidah, Ya kalli gwiwar hannunta yaga jini, shiru yayi kaman bazaice komai ba kafin yace " Na sani yauma Umma tace ta dakeki ta hanaki zuwa makaranta ko Anty. Kame kame Zubaidah ta soma yi don yaron akwaishi da wayo da kaifin basira, daidai nan Yaya Habibu yayi sallama ya shigo cikin yanayin tafiyarsa na sokaye _Phsycos_ da maganansu.
Kamalu ne kawai ya tafi ya masa oyoyo Zubaidah kam wucewa tayi bakin rijiya don taran ruwan wanke wanke, tabbas tasan Yaya Habibu ya ganta a haka toh fah haka zai wuni yana kuka.
"Inna Fure tana shiga gida ta tarar da Umar dawowarsa kenan. Koda ya gaisheta sama sama ta amsa, Umar ya lura da yanayinta, don ko tambayarsa ko yaci abinci batayi ba, kaman yanda take a kullum. don haka zama yayi bisa gefen tabarman da take zaune " Sadda murya yayi kafin yace Innata meke faruwa ya tambaya yana kallon Inna Fure. Sauk 'e ajiyan zuciya tayi kafin ta soma fad'in" Umar shin da gaske kake son Zubaidah.
"Kallon mamaki yayiwa mahaifiyar tasa kafin yace "Haba Inna wann wace irin tambaya ne, Kowa ya sani duk fad 'in garin nan Zubaidah kadai nake so, nake burin mallaka, bansan meyasa Zubaidah tak'i barina na kai tambaya gidansu ba. Don wllhi Inna na k'agu na rabata da wann muguwar matan yayan nata.
"Inna ta sauk 'e ajiyan zuciya kafin tace " A gaskiya Hadiza bata da imani Ummaru....... "Ganin yanayinta yasa mik 'ewa zuciyarsa na bugawa yake fad'in" Inna ki fad 'a mun me tayi mata, ta kuma dukanta kaman yanda ta saba ko..
"Gjrgiza kai Inna ta soma tana fad'in a'a Umar don Allah ka zauna, zauna nace ba dukanta tayi ba, kawai dai so nake ayi maganar aurenku, da zaran malam ya dawo zan masa batun insha Allah, take farin ciki ya mamaye zuciyarsa nan ya shagala da zancen......Inna ta bisa da ido yanda yake murna kaman an masa alk'awarin hajji, gwara da ta kawo masa wnn zancen don tasan kalan zuciyar d'anta yanzu sai yaje yayi ma Hadiza kaca kaca.
**********************
*Abuja, Maitama*
"Wasu tagwayen gidaje na hango masu d'an karen kyau, exactly babu abinda ya raba da na gefe, komai iri guda. Wadan nan gidaje gidajen Yaya ne da kuma k'ani, Alhaji Kasim Dasuki shine Babba, yayinda Alhj Jamil Dasuki shine k'ani. Alhj Kasim da k'aninsa sunyi kaurin suna wajen hold'an kasuwanci ta yanda k'asashen duniya da dama suke hold'a dasu, tareda shahararriyar Company dinsu mai suna *Dasuki Holders*, Ko wannensu Allah Ya albarkacesa da yaro namiji k'wara dad'd'daya,.
SALIM KASIM DASUKI, da kuma LABIB KASIM DASUKI, tsakanin Salim da Labib shekara gudane cal, haka nan yaran suka taso cikin sangarci da rashin tarbiya, saboda so da iyayensu ke nuna masu, wanda a nasu tunanin gata ne. Babu mai taba masu 'Ya'ya Ya zauna lafiya sai sun ga k'arshensa, musamman Alhj Kasim shi yafi k'aninsa bak'in zuciya, wani sa'in Alhj Jamil dinne ke nusar dashi hanya. Haka zai balbalesa tsaf da masifa, uwa uba WA'azin da Alhj Jamil ke masa kan su guje dukiyar haramun cikin kasuwamcinsu, wann dalili Ya soma sakawa Alhj Kasim tsanar Dan'uwarsa har yake tunanin tabbas zasu iya samun sab'ani koma takaisu ga raba dukiyarasu.
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: πππ»ZUBAIDAHππ»π
03
*©Sameena Aleeyou...✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum..ππ_
*Dedicated to all victims of rape, never keep silence, fight for your right,... This is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves ππΎππΎππΎππΎ*
"Salim ne kwance saman coach a bakin pool dake a cikin gidansu, da gani daga ruwan ya fito don daga shi sai gajeren wando. Idonsa manne da bak'in sunshade ya k'ura wa rana ido, gefe dashi k'aramar table ne wanda wayoyinsa ne da kuma Chapman akai.
"A hankali ya kai hannunsa kan table din gamida daukar d'aya daga cikin wayoyin nasa nan ya shiga dialling lambar budurwarsa KAUSAR wacce ake batun saka masu rana. Sosai suke hiran soyayya daga ji kasan suna tsananin son junansu.
"Daga can bayansa yanda Labeeb ke tsaye ya k'urawa cousin d'in nasa ido, shakka babu su duka biyu sunyi tarayya wajen son mace guda, zuciyarsa yaci gaba da tafarfasa, da sauri ya juya ba tareda yayiwa d'an uwan nasa magana ba.
"KAUSAR TAHIR MARAFA, shine asalin sunanta, mahaifin Kausar abokin kasuwancin iyayen Labeeb da Salim ne, musamman Mahaifin Salim Alhj Kasim Dasuki, Shima Alhj Tahir Marafa dan asalin garin Dukku ne, Kausar basu jima da dawowa Nigeria ba daga k'asar Holland dalilin dawowarsu ma sabida neman muk'akin kujeran Shugaban k'asa da mahifinta zai fara ne, farkon dawowarsu sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Labeeb a lokacin Salim yana can Scotland yana k'arasa wani course dinsa shi, koda Salim ya dawo Labeeb shi yayi masa introducing Kausar, tunda Kausar da Salim suka k'yalla ido akan juna soyayya mai tsanani ta shige tsakaninsu, toh fah run daga wann lokaci Labeeb ya rasa sukuni, a ganinsa cin amana ce wnn k'wace Salim yayi masa.
"Iyayensu gaba d'aya sunyi farin cikin wann Al'amari tun basu hadasu ba gashi sun hada kansu, babu kaman Alhj Kasim Dasuki wanda dama shi Money hungry, baya rab'an mutum sai zai sami alkhairi. Dukda tarin dukiyar da yake dashi baya hanasa hangar na wani. Yasan muddin tilon d'ansa Salim ya auri tilon 'yar Alhj Marafa wataran zasu mallaki gaba d'aya dukiyar Alhj Marafa.
"JALAL! Na'am Anna ya amsa gamida ajiye takalmimsa da yake faman gogewa, fitowa yayi ya tarar da Annah zaune tana stincen wake
. Kallonsa tayi yanda ya shirya tsaf cikin kaya masu kyau da tsada kaman wani d'an hamshak'i.
"Jalal ina zaka, Jalal farin saurayi dogo mai cikar zati kyakkyawa ya murmusa kafin yace "Annah birthday d'in abokinmu TARIQ zamuje su Salim suna waje suna jira na.
"Fuskar Annah tamau dama tasan zancen bazai wuce haka ba, tasha raba Jalal dasu Salim amma baya ji, yak'i yarda ya tsaya a matsayinsa na talaka bashi da aiki kullum sai k'ok'arin had'a kansa da sangartattun yaran masu kud'i musamman su Labeeb.
"Gyaran murya Annah tayi kafin ta soma fad 'in" Jalal har yaushe zan maka magana kaji, ka sani kai maraya ne kuma talaka, idan baka tashi ka tsaya ma rayuwarka ba babu wanda zai maka, kai kullum bakada aiki se biyewa su Salim ko, toh ka sani su sunada masu masu, sunada gatansu kaifah, baka dashi , tunda ka gama jami 'a ka'ki neman aiki ka tsaya kana biye masu, yau kune wancan club din gobe wancan, kune bin 'yanmata kune shaye shaye...... "Jalal yayi saurin d'ago kai yana kallon Annah, haba Annah shaye shaye fah kikace nasan dai su Salim suna yi amma ni banayi, ina dai da 'yammata banyi musu ba amma wllhi bana shan komai tunda kika hanani....... "Rufe mun baki Annah, ta dakatar dashi kafin taci gaba da fad'in" Da da kakeyi na maka uzuri don na d'auka yarinta ne zaka daina amma yanzu na gane shashanci ne kawai ke damunka, shekaranka 25 ace bakasan abu me kyau ba toh wllhi ka kiyayeni..... "Sallaman Labeeb ya katsesu.
"Gaisar da Annah Labeeb yayi, ta amsa masa babu yabo babu fallasa, kafin ya d'an daki kafad 'un Jalal yace Guy let's get going.. Jalal ya mike yana satan kallon Annah kafin yace Annah sai mun dawo, kallo tabisu dashi har suka fice, girgiza kai tayi kafin tace bazan fasa maka addu'an shiriya ba.
Sameena ce ππΎ
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: πππ»ZUBAIDAHππ»π
04
*©Sameena Aleeyou..✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum... ππ_
*Dedicated to all Victims of rape, never keep silence. Fight for your right, this is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselvesππΎππΎππΎππΎ*
"JALAL, abokin su Saleem ne wanda tun tasowarsu tare suka taso, Jalal maraya ne wanda bashida kowa sai mahaifiyarsa Annah, Annah tayi komai a rayuwarta don ganin ta inganta rayuwar Jalal tun yana yaro, kama daga karatunsa har zuwa girmansa, haka nan ya tashi ba tareda yasan mahaifinsa ba, don Annah ta sanar dashi cewa mahaifinsa ya rasu tun yana k'arami. Annah ta jima tana yiwa matar Alhj Kasim aiki wato mahaifiyar Salim, tun wani lokaci da suka zauna a Gombe, tun yaran gaba d'aya suna k'anana, Annah ita ta rainesu gaba d'aya, Salim Labeeb da kuma Jalal d'inta, wann dalili yasa lokacin da zasu komo Abuja suka taho tareda ita don tun a lokacin bata da miji ya rasu. Ta zauna da d'anta a nan BQ din gidan Alhj Kasim.
"Tunda yaran suka taso iyayen ke k'ok'arin rabasu da Jalal, suna nuna masu cewa shi ba daidai dasu bane, babu yanda basuyi ba don ganin sun rabasu amma abu yaci tura dole suka hak 'ura suka k'yalesu, amma ko kid'an babu wani abu na arziki da suke masa.
"Shi kuwa Jalal babban abun da ke masa dad'i shine yanda emmata da samaruka yaran masu kud'u suke zaton shima DASUKI'S ne, ma'ana shima dan familyn Dasuki ne, ko ina tare dasu Salim suke zuwa party shisha spot da dai sauransu. Allah ya masa kyaun hallita gabba d'aya yafisu kyau 'yanmata suna rubibinsa shiko na ja masu class kaman wani d'an hamshak"i ko kad'an bakace Jalal ya had'a jini da talaka ba...wann kenan.
*Gombe, Dukku*
"Huci take kaman wata kububuwa tana watsawa malam Habu mahaifin Umar da abokinsa malam Tanko harara, Malam Habu suka saki baki suna kallon ikon Allah sanda Yaya Habibu ya mik'e ya rusuna gaban Hadiza yana tambayanga shin ta amince a karb 'I baikon Zubaidah, .... Mikewa Hadiza tayi kafin ta d'ibi 'yan goron da malam Habu suka shigo dashi ta shiga juye masu a tsakar kansu, tana balbala wutan bala 'i da masifa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba.
"Malam Tanko ya mik'e yana fad'in subuhanallah, Malam Habu ya baka fad 'a mun haka lamarin yake ba, Malam Habu da kunyar abokinsa mutum mai muhimmaci a gari irin Malam Tanko ya baibayesa, dama yasan haka ka iya faruwa, shiyasa tun farko bai so Ummaru ya nemi Zubaidah ba dukda ya aminta daehankali yarinyar kuma na tausayinta, amma ko kad'an bashi fatan abinda zai hadasa da dilalliya Hadiza,.....
"Zubaidah dake mak 'ale bayan k'yaure bata san sanda ta sulale gwiwoyinta a k'asa ba tana hawaye sanda ta jiyo irin fatattakan da Yaya Hadiza tayima iyayen Umar, shikenan itakam tasan bazata tab'a aure ba, bazata tab'a jin dad'in rayuwarta ba, mafarkin ta bazai tab'a tabbata ba, takaicin yayanta da tausayin kansu shida ita ya lullub'e zuciyarta. A hankali ta k'arasa kan tabarman da ya kasance makwancinta ta kwanta tana kuka mai tsuma zuciya.
"Malam Habu jiki a sanyaye ya shiga bawa Malam Tanko hak'uri, Malam Tanko yace a'a abokina baza 'a bar wann magana ba tunda yaran suna son junansu ni nasan yanda za'ayi, ka shige gida zan nemeka zuwa gobe, Malam Habu ya masa godiya sukayi sallama kafin malam Tanko ya hau babur dinsa ya wuce.
*******************
*Abuja*
"Suna isa wajen partyn pili ya dauki shewa da ihu, manyan yara wanda duk gabaki d'aya Abuja sunansu yayi k'auri Sun samu halarta, Tariq ya k'araso yana welcoming nasu sai wani tafe hannaye suke yanda niggas keyi. Tariq shine cikon na hud 'u a clik d'insu, shima mahaifinsa nada shears a companyn *Dasuki Holdings* kampanin mahaifan Salim da Labib, ..
*Zubaidah, Jalal, Umar, Salim, Labib da kuma Tariq*
*Ku biyo Sameena don jin labarin gumurzumon da wad'annan matasa suka fuskanta.......... ππΎ*
[1/23, 22:08] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
05
*©Sameena Aleeyou.....✍πΎ*
_Queen Same Novels Forum...ππ_
"Alhj Kasim Dasuki, Alhj Jamil Dasuki da kuma Alhj Yusuf Maina mahaifin Tariq sai Barrister Munir Malami lawyer na company Ιinsu *Dasuki Holdings* kuma yaya ga mahaifiyar Salim Haj Farha Dasuki.
"Zaune suke gaba Ιaya a babban parlorn taraban baΖin Alhj Tahir, magana suke na tsaida ranar auren Salim da Kausar, an tsayar sati mai zuwa za a yi bikin saka rana. Daga nan suka Ιuge da hiran kasuwanci da siyayasa. Tunda dama Alhj Tahir na neman tsayawa takaran shugaban Ζasa, nan Barr Munir ya bada shawarin a tafi chan Dukku ayi bikin saka rana hakan ba Ζaramin nasara zai kawo wa neman takaransa ba, gaba Ιaya sukayi na'am da batun Barr Munir snn Ζ΄an garinsu zasu tabbatar shi Ιin mai Ζaunar mahaifarsa ne..... Har farfajiyar gidan Alhj Tahir ya rakosu yanda bodyguards Ιinsu suke... Daga nan ya wuce Ιangaren matarsa uwar Ζ΄arsa Hajiya Raliya don sanar da ita yanda suka tsai da batun auren yaran.
"Kausar da Asmah ya samu a parlorn Ζasa suna playin PSP, gaba Ιaya suka soma gaidashi... Papa sannu da shigowa amsawa yayi da sakin fuska kafin yace ina momman taku, har suna haΙe baki wajen cewa she's upstirs, Ζarasawa yayi ya nufi stirs Ιin.
"Kausar da Asmah suka ci gaba da game Ιinsu. Asmah cousin Ιin Kausar ce wacce a shekare baifi ta girme wa Kausar da shekera guda ba, tun dawowarsu Nigeria Asmah take gidansu daga zuwa kwana biyu Kausar taΖi barinta ta koma dole Aunty Miemie mahaifiyar Asmah ta haΖura da zancen don tasan halin Kausar da kafiya.
"Momma na zaune gaban dressing mirror tana gyaran fuska as usual don itakam taΖi yarda ta tsufa at her late 40s bats sahun matan nan masu barin gyaran jiki da zaran sunga shekaru ya soma ja masu,... Murmushi Papa yayi gamida rungumota ta baya, murmushi itama ta sakar masa kafin tace" Papa how do i look like, Ιan jan hancinta yayi kafin yace as always my one you look so gorgeous manna mata peck yayi a goshi kafin suka zauna bakin gado ya soma faΙa mata yanda suka tsai da maganan bikin Kausar, nan da nan idon momma yayi raurau Kausar is her only daughter Ζaunar ranar rabuwarsu tazo dukda tasan dole wata rana hakan ta kasance.... Papa yasan kwanan zancen don haka rungumota cikin jikinsa yayi ya soma lallashinta da kalamai masu taushi, "Haba first lady you need to be very strong you know, sooner or later zaki zama mother of the country insha Allah, bama Kausar kawai ba, the whole country will be yours, and for now akwai Asmah though nasan itama tana samu miji zamu aurarta but atleast zata Ιauke mana kewar Kausar.... Jin yanda mijin nata keta faman riritata yana shagwaΙata yasata sakin murmishi gamida goge guntun hawayenta tace" Pappy you Ζnow what made me cry...." Ζan girgiza kai yayi har lokacin tana cikin jikinsa kafin taci gaba da faΙin" I dont know why, but har raina banjin son auren Kausar da Salim duk da Ιan aminiyata ne, quite alright nasan gidan girma arziki da mutunci zata but.... Kasan yaran zamani kar Salim ya hurting mana baby girl Ιinmu...."Papa yayi murmushi gamida shafa goshinta zuwa gashinta kafin yace" Raliya insha Allah we won't regret it, bazamuyi danasanin aurar da Kausar wa Salim ba, besides they both love each other wanda kinga hakan akeso ya kasance. Yanzu abunda nake so dake, you shud start preparing we leaving in a couple of days gwara mu mu fara isa tunda mune iyayen bride, I'll make sure the house is ready from now to tomrrw, ki kira su Kausar Ιin ki sanar dasu su fara shiri, barin Ζarasa parlor inada wasu baΖin.. Gyada kai kawai momma tayi da Ζyar kafin ya manna mata kiss a chick Ιinta ya fice.
"Wann shine rayuwar gidan Alhj Tahir, mutane ne masu Dattako da sanin ya kamata, ko kaΙan basuda Ζyamar talaka kaman Dasuki family, snn abin hannunsu sam bai rufe masu ido ba, da wann dalili yasa akasarin mutane suke mara masa baya a siyaysarsa, yayinda wasu ke ganin The Dasuki family ks iya ja masa cikas a siyasarsa sabida izzan su da Ζyamar talaka ds suke dashi.
"Kausar da Asmah sai murna suke zasu Dukku dukda kakanninsu gaba Ιaya sun rasu amma skwai sauran dangi, Momsy ya maganar kayan gaskiya ki sake masu waya we need them this week, they shud make it possible this week. Momsy ta Ιan sakar mata harara kafin tace" Kausar this is not Holland fah, na faΙa maki ki rage wann rawar kan taki, ba irin auren da kika saba gani bane na turawa, wann auren fulani ne wanda aka san sansu da kunya so be careful,... Momsy tana ficewa Asmah da Kausar suka kalli junah, suna daroya Ζasa Ζasa don suma har sun Ιagota bata son Kausar ta bar gidan ne Asmah ta Ιau waya tace bari kiga na kira *Mamza beauty* (makeup artist) na sanar mata, ke kuma pls ki kira Sarah fashion ( Fashion stylist ne a Dubai wanda zasu Ιinka kayyaykin Kausar da zatayi amfani dasu a events) Ιin ki sanar dasu.
"Rungume pillow tayi gamida lumewa cikin hashaΖin gadon tana tuno farin cikinta Salim, ya kusa zama *Mallakinta* Asmah na mata magana ko saurara batayi ba tayi nisa wata duniyar, girgiza kai kawai Asmah tayi ganida jifar ta da pillow kafin ta fice.
"Tafe suke suna tangaΙi da gani kasan sun bugu da giya, da Ζyar suka iya fitowa daga motan ,Alhj Kasim da har loΖacin idanunsa biyu baiyi barci ba ya dubi agogon bango dake maΖale a Ιakin ya nuna Ζarfe uku na talatainin dare, yasan ba kowa bane zai shigo gidan a yanzu sai Salim, kai tsaye down stirs ya sauΖo ya buΙe Ζofar parlor, chan ya hangesu suna tafe suna tangaΙi gaba Ιayansu, Jalal na riΖe dasu don dama duk randa suka je party suka shawu toh shi ke driving nasu da shike shi bai sha yanda za'a gane sama sama yake kora wine maras bugarwa sosai shide barshi da harΖan bin mata, shiΙinma da yawa Ζ΄an matan ke kawo kansu wasu na zaton shi Ιin Ιan Dasuki Family ne yayinda wasu ke sonsa sabida kyaun da Allah ya masa.
"Wani mugun kallo kawai Alhj Kasim ke binsu dashi musamman Jalal, shikan ya tsana ganin yaransu da sidecake Ιin,..... "
"Ζ΄an kame kame Jalal ya soma, tuni Alhk Kasim y dakatar dashi da faΙin" meyas baka kai shi gidansu ba ya Ζarashe maganar yana nuni da Labib, Jalal da tuni ya shaΖi kallon ΖasΖancin da Alhj Kasim ke masa, a daΖile yace " Gani nayi nan ma gidansu ne......"Jar ubancan haka Alhj Kasim yace a zuciyarsa lallai wnn talakan raini na neman shiga tsakaninsu, baiga laifinsa ba lafin su Salim ne,... Securities ne suka Ζaraso suka shiga taimaka wa Jalal, Ιaya security Ιin daga gidansu Labib yake yazo tafiya dashi don hankali mom Ιinsa ba Ζaramin tashi yake ba duk randa yayi dare a waje, duk da hakan ba sabo bane amma she couldnt get used to it har yanzu. Haka aka wuce da Salim da Labib kaman wasu mutattu don tuni bacci yayi awon gabadasu.
"Jalal ya Ιaga gira sama kafin ya dubi Alhj Kasim yace" Have a good evening Sir , daga nan yayi wucewarsa can sashensu. Kallo Alhj Kasim yabisa dashi kafin yayi Ζwafa ya shige cikin gida.
"Washe gari zaune suke gaba Ιaya a babban parlorn Alhj Kasim, Ya kuma duban Hajiya Farha dake zaune gefen Hajiya Nurah mahaifiyar Labib yace" Farha jeki taho min da yaran nan Labib da Salim suna sashen Salim, babu musu Hajiya Farha tabi umarnin mijinta ta fice kiransu.
"Sai ihu suke suna buga game na Ζwallo ko saurarenta basuyi ba, da takaici ya isheta batasan sanda ta fincike socket Ιinba....."Whatttt!!!!! Suka fadi a tare, Salim yayi jifa path Ιin hannunsa gamida faΙin " Shitttt, why mum haba haba mum.... Rufe mun baki marassa hankali kawai Mum ta Ζasesu, Labib ya Ιan langΙe kai kana yace" We are sorry favorite Aunty, Kunnens ta janyo kafin tace" Daga yau zaka tashi daga fav son idan baku zama good boys ba, Dad na kiranku bata jira cewarsu ba tayi ficewsrta. Labib yace nasan Uncle ne dama zai sa Fav Aunt ta mana haka he will never change. Salim ya watsa masa mugun kallo kafin ya fice ba tareda yace komai ba.
" Cikin tafiyarsu na samarin da tarbiya bai ishesu ba suka Ζaraso parlorn, gamida tsayuwa ma iyayayen tsegehe akai.
"Alhj Jamil, ya sauΖe ajiyan zuciya kafin yace" Seat down boys, zama suΖayi da Ζyar saman carpet Alhj Kasim kuwa banda hararsu babu abinda yake. Kaman jira yake nan ya soma surfa masu masifa " When are you boys going to start acting like real Dasuki's huh?Har yaushene zaku daina alaΖa da wann matsiyacin yaron, he's not one of you ba daidai ku bane get this to your heads..... " Alhj Jamil da mamaki yake kallon Ιan uwan nasa ko kaΙan baisan kan hulΙa da Jalal zai masu faΙa ba, a'a ya Ιauka kan Ιabi'u marassa kayu da suke zai masu faΙa, to his gretest surprised sai jin akasin haka yayi, lallai yayansa yayi nisa.
"Labib ne ya Ιago kai yanai ma uncle Ιin nasa mugun kallo Ζafin yace" Pls uncle will give us break, idan dai akan Jalal zaka mana faΙa you can keep on doing it but bazamu taΙa rabuwa dashi ba he's our childhood friend a brother from another mother....."Enough Labiiiib! DaddΖ΄nsa ya daka masa tsawa, kafin yaci gaba da faΙin " Ma ucle Ιin naka kake faΙun magana haka, be careful kana jina, Labib yana wani hure huren hanci yake watsa wa uncle Ιin nasa mugun kallo, Barr Munir ya sako baki da faΙin" Ni kawai a kori ysron da mahaifiyarsa kowa ya huta. Wata harara Labib ya watsa masa kafin yace" Malam ka mana shiru dalla this is family issue who invited you..." Salim ya caΖumo wuyar Labib yana huci yake faΙin " First kayi rashin kunya wa Dad Ιin second kanayi wa Uncle Ιina, Brothern mahaifiyata how dare you Labib.... Saida aka shiga tsakanin Labib da Salim don kaΙan ya rage basu kaure da faΙa ba.
" Alhj Kasim ya goge zufar data keto masa dukda ac dake busawa a parlorn, iyayensu matan su suka lallashesu kafin suk sanar Ιasu maΖasudin haΙuwarsu.
"Take annuri ya cika fuskat Salim tuni ya mance wani baΖin ciki ya soma farin ciki, Yayinda zuciyar Labib taci gaΙa da tafarfasa, a cikin ransa yake furta " _no way it can't be happening, Kausar is mine not yours Salim Dasuki_
"Ζarasawa yayi ya Ιan daki kafaΙan Salim yayi con granulating nasa kafin ya fice cikin sauri.zuciyarsa naci gaba da tafarfasa
*****************************
"Mai anguwa yaci gaba da faΙin' ni mai anguwa ni na karΙi baikon Zubaidah kina jina ya Ζarashe maganar yana duban Hadiza data sadda kai a gabansa ta cika tayi fam. Ζiris ya rage bata fashe ba.
"Hamma Habibu kuwa sai wsge baki yake kaman gonar audiga yanai wa mai anguwa godiya, banda hararsa babu abinda Hadiza keyi tanai masa kallon zaka shigi hannu ne. Mai anguwa yaci gaba da faΙin ya ysai da aure nan da wata mai kamawa kowa yaje yaci gaba da shirye shiryensa, kuma uffan Hadiza tayiwa Zubaidah za'a mata hukunci mai tsanani koma ya miΖa case Ιin gaban sarki, daga nan ya sallami Hadiza da Habibu suka wuce.
"Malam Tanko da mlam Habu sukayi godiya sukayiwa mai unguwa suka Ιan tattauna kafin ya sallalmesu.
"Tsakanin Ummaru da Inna an rasa wayafi farin ciki, tuni ya ficr ganin masoyiyarsa, mai shirin kasancewa amaryarsa......
Sameena ceππΎ
[1/23, 22:08] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
06
*©Sameena Aleeyou...✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
"Zubaidah zaune bakin murhu tana kan hura wutan girki, ko kaΙan yau bata jin zafin duk tulin aikin da zatayi, snn ko kusa masifan Yaya Hadiza bai Ιaga mata hankali ba, jinta take tamkar sallah, muddin zata bar wann kurkukun dole taji farin ciki a zuciyarta, uwa uba zata ci gaba da karatunta saidai zatayi kewan Kamalu da Hammanta.
"Wani yaro ne yayi sallama snn yace wai ana sallama da Zubaidah...... "Wulli wulli tai da idanu tana kallon yaya Hadiza dake zaune bakin Ζofar Ιaki ta cika tayi fam Ζiris ya rage ta fashe.
"Meye kike mun kallon Ζurilla mayya jarababbiya, ai shikenan hankalinki ya kwanta za'a maki auren abinda kike so, Ζaramar karuwa kodayake ba laifinki bane kin riga kin san namiji tun a gantalinki na karuwanci......."Ζwalla suks ciko idanunta kanta na sunkuye a Ζasa, wann mummunar kalma na karuwanci da Hadiza ke jifarta dashi sosai yake Ιaga mata hankali.... Bata gama tunanin da take ba sai ji tayi yaya Hadiza ta janyo wuyarta ta jefata bakin Ζyaure tana faΙin "Wuce kije shegiya mayya kafin ki cinyeni, maza kije yaci gaba da mammatse a lungu yanda ya saba...."
" Ko Ιan kwalliya da Ζ΄ammata keyi idan zasu wajen saurayi Hadiza bata bar Zubaidah tayi ba, haka nan yanda ta tashi daga bakin murhu da warin hayaΖin da komai ta turata waje....
"Daga can bakin bishiyar da yake tsaye ya hangeta tana goge hawayen da ya jiΖa mata fuska.. Cikin sauri Umar ya Ζaraso yanda take, tuni ta soma matsawa da baya don bata so yaji Ζaurin hayaΖin da take, gashi shi yayi tsaf ya sha gayu abinsa irin na samari daidai da ajinsa.
" HarΙe hannaye yayi a Ζirjinsa yana kallonta, tausayinta da Ζaunarta na daΙa ratsa Ιargo da tsokarsa,.. Saida ya bari ta gama Ζ΄an goge gogen hawayen kafin ya Ιanyi gyaran murya cikin tattausar murya ya soma faΙi" ZuΙaidah, shiru bata amsa ba har lokacin kanta na kallon Ζasa, kafe ta idanu yayi kafin ya kuma kiran sunan nata, sai snn ta Ιago koΙaΙΙun idanunta ta mar duba guda, Umar yanada Ζwarjini ta yanda duk budurwar da tayi ido huΙu dashi sai ta tsinci kanta da faΙuwar gaba, gashi a yau yafi kullum mata kyau, shi ba fari bane snn ba baΖi can bane, kallo guda zaka masa ka gane asalin bafulatani ne haΙi da kwantattun sumanss da sajensa da suks Ζara masa kyau da Ζwarjini...."Muryarsa ya katseta sanda yayi mata nuni da wani kututturen dabino yace" Mu karasa ki zauna, babu musu tabi umarninsa......" Har sun soma tafiya suka jiyo muryar Hadiza ashe tana laΙe jikin Ζyaure tana saurarensu nan ta soma faΙin "Ku Ζarasa ina, kai wani irin jarabebbe ne, baka jira akai maka ita ba sai kazo har Ζofar gidansu kana matseta, auho ashema kun saba kinji kunya Zubaidah tuna kika zaΙi zama karuwa, toh ni dai kar ki kawo min abin kunya kafin wata gudan da aka Ιiba maku ya cika taΖarashe maganar tana watsa masu mugun kallo.
"Umar yabits da kallon mamaki, Ζarasowa gabanta yayi yanda take tsaye kafin yace" Dillaliya kike ko wa? Galala take dubansa cike da mamaki kodashike tasan Ummaru da wann taurin ran nasa zaiyi fin haka, muryarsa ya katse mata tunaninta yanda yaci gaba da faΙin" Yau ta kasance rana ta Ζarshe da zaki saka masoyita kuka, don wllhi kinji na rantse kika kuma kiranta karuwa kotu zan maka ki sai munyi shari'a daga nan har birnin tarayya, kuma da kike cewa ni jarabebbe, naji na yarda idan dai akan Zubaidah ne sai nafi jaraba ma naci, don nasan bazan taΙa Ζosawa da ita ba, ki kalleta da kyau mana, ke ai kina ganinta kinga mace ba irinki ba, nasan hassada ce tsan tsa kike da ita ba wani abu, yayi wata murmushi mai cike da nishaΙi da gargaΙi kafin yace" This should be the last warning idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira, daga haka ya dubi Zubaidah da Ζiris ya rage bata saki fitsari a jikinta ba don tsoro kana yace" Amaryata lets go, dont mind this witch, don yasan Hadiza dai ba turanci take ji ba......"Kallon Yays Hadiza tayi alamun tana jiran umarninta" Haba tuni ta soma bambami tana kunfan baki, yo har ni za'a yi ma turanci, ke Zubaida har kinyi kaurin da zaki biyewa saurayi inji ni nayi Ιawainiyar karatun naki, har shine zaki zaΙi saurayi akaina ya zageni da kalman turanci kina tsaye kina biyesa yayi maki kyau, idan dai namiji ne kije gaki gashi ..... Daga haka tasa kai ta wuce cikin gida fuu zuciyarta naci gaba da tafarfasa....
"Juyowa tayi tana duban Umar, murmushi ya sakar mata kafin suka Ζarasa suka zauna.
"cikin tattausar muryarta ta gaidashi, ya amsa yana wani kasheta da mayen kallo, ita kiwa duk kunyarsa ya rufeta musamman cewa da yayi, idan dai akanta ne sai yafi jaraba naci, wann kalmomi sun matuΖar mata nauyi, kaman yasan hakan kuwa nan yasa hannu ya karΙi Ιan karan da take wasa dashi aiko nan ta Ιago ido suka kalli juna, tai saurin sadda nata idon,
"Zubaidah, ki sani ina sonki ina Ζaunarki sann zanyi komai a sabida ke, nasan kalan rayuwar da kike da wann matar, daga rana mai kaman ta yau ki sani bazan sake barinta taci zarafinki ba.
"Ζan murmusawa tayi kafin tace" Na gode, cikin muryarta mai daΙin saurare, kaman waccd aka zabura ta miΖe tsaye, Ιan dubanta yayi kafin yace" Yaya dai ko har mun gama hiran ne, Ιan girgiza kai tai kanta na Ζasa kafin tace" A'a gani nayi kaman Ζaurin dake jikina ya dameka.
"Tsuke fuska yayi ya kira sunanta da dakakkiyar murya, Ιago ki kalleni Zubaidah, ta Ιago tana dubansa, Umar yaci gaba da fadin" Nida ke mun zama Ιaya, bana jin Ζauri ajikinki, akasin haka nike ji, ma'ana Ζamshi nake ji, kasancewa taredake yafiye mun komai ina sonki a duk yanda kike. Murmushi tayi harda Ιan rufe fuska alamun taji kunya,.. Dariya ya Ιanyi mai bayyanar da hΖwara kafin yaxe" Oya faΙa mun kina sona... Ware idanu tayi alamun bazata iya ba, Umar yayi murmushi kafin yace" Surbajo na nasan kinayi koh... Kasa cewa komai tayi sai murmushi.... Hira sosai suka sha a wann rana kamsr karsu rabu da juna, basu taΙa hira irin haka ba, kullum saidai su haΙu a bakin rafi taje Ιibo ruws ko kuma ta kai saniyar yaya Hadiza kiwo.
*********************
" Salim ne tafe waya manne a kunnensa yayinda hannunsa Ιaya ke riΖe da coffee cup, "What com'on Tariq pls ka shirya yanzu yanzu, we will fetched you up sai mu wuce airport Ιin... Yeah right , see you soon. Yayi hanging up kafin ya tura Ζofar Ιakin da hannu guda.
"Cak ya tsaya yana kallon Labib dake baccinsa hankali kwance. Kan gadon ya Ζarasa ya Ιauki pillow ya shiga dukan Labib dashi yana faΙin" Will you get your lazy ass out of bed,...
"Labib, yayi miΖa gamida cusa kansa cikin bedcover yana faΙin" Shitt, pls mana Salim, kasan ba'a tashina a bacci i'll fall sick.
"Salim ya shiga yaye blancket Ιin yana faΙin whatever, You know we cant miss this flight, tun jiya Daddy ya mana bucking flight Ιin Gombe mukayi missing still yauma muyi missing what will u expect, they'll get mad ai.
"Gajeren tsaki Labib yayi kafin yace" Does it really has to be now, " Labib ya miΖe yana wangale labulayen tapΖa tapkan windunan Ιakin kafin yace" The flight is 10am and yet is almost 30mins pass 9.. Tsaki Labib ya kumayi babu salati yake hamma kafin yace" waima ina private jet Ιin Dasuki Holdings ne ba sai mu tafi dashi ba, Salim yace gaba Ιaya Jets ukun suna da prob, Daddy yace zaiyi firing masu maintenance Ιinsu, kaga idan mukayi missing wann flight Ιin tofa saidai mu tafi Gombe by road, kai ina I cnat afford to miss this flight ma, i'm dying ti see my Kausar,.. "Galala Labib ke kallonsa kafin yace" Waye ma kake tunanin zaiyi tafiya mai nisa haka by road, haba ba dai ni Labib Dasuki ba.
"Salim yayi dariya kafin yace" Freaking Dude sai ka tashi ka shirya ai na masu Tariq da Jalal magana suna shiryaw Ya Ζarashe maganar yana jifan Labib da towel.
Ba don yaso ba ya miΖe ya nufi bathroom..
"Gaba Ιaya Annah bataso tafiyar Jalal Dukku ba, don tun yana Ζarami data taho dashi Abuja basu kuma leΖawa ba, tana tunanin abinda ka iya zuwa yazo, kar wata rana daΙeΙΙiyar sirrinta data Ιoye masa ya bayyana. Haka tai kusan kwana zullimi......
*Gombe, Dukku*
_Toh fah readers gasu Jalal, Labib, Salim, da kuma Tariq a garin Dukku, shin me zai faru. Shin me Annah take Ιoyewa Jalal tsawon rayuwarsa. Ku biyo Sameena don jin yanda zata kasance_
Sameena ceππΎ
[1/23, 22:09] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
07
*©Sameena Aleeyou.... ✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
"Drivers Ιin da suka Ιibo su daga airport suka soma paka luxurious cars Ιin a farfajiyan tangamemen gidan wanda yasha tsari da kayan alatu, idan ka shiga gidan sai ka ranste ba'a Dukku kake ba.
"Kai ysaye cikin gidan suka nufa yayinda gurds suka shiga firfito da luggage Ιinsu.
"Iyayen nasu ne zaune a babban parlorn, ciki harda iyayen Tariq.
"Tun daga nesa Alhj Kasim ya haΙe giran sama da Ζasa sakamakon abinda ya gani, wayo wann tsinannen mayen yaron saida ya biyosu...... Ko saurarensu baiyi ba sanda iyayayen keta faman hugging yaran suna masu sannu da zuwa, rai Ιace ko kulasu baiyi ba yayi ficewarsa, Labib ya rakasa da harara har ya fice. Cikin sauri Barr.Munir ya miΖe yabi bayan uban gidan nasa.
"Da yamma lis hadari ne sosai a garin already dama an idda wani ruwan don haka garin yayi sanyi weather yayi dadΙi. Samarukan guda huΙu suka shirya cikin Ζanan kaya kafin suka shige motarsu mai buΙeΙΙen sama don zagaya gari.
"Mutumina na maka murna fah ka kusa zama ango, cewar Balele dake zaune saman mota a bakin tasha, Umar yayi wani murmushin jin daΙi kafin yace insha Allah abokina, Balele ya kashe masa ido guda kafin yace" Ina tausayin yarinyar nan duk randa aka kulleta a Ιaki daga kai sai ita mutumina nasanka fah babu Ιaga Ζafa ranar..."Wata dariya Umar yayi kafin ya dubi Balele ya soma faΙin" Naji tunda nayi haΖuri ban taΙa bin ko wata mace ba, ban taΙa danne Ζ΄ar kowa ba ko Ζanwar kowa, kaga dole duk randa na sami nawa nayi budurina, babban farin cikina shine zan kasance da macen da nake so....."Balele ya busa sigarinsa a daidai fuskan Umar yana murmushi gamida jinjina kai.... Wani mugun kallo Ummaru ya watsa masa kafin yace waikai baka gajjiya da kayan maye ne? Murmushi Balele yayi kafin yace tuΖa manyan motoci ai saida kayan maye, gaskiya Ummaru ina gani ΖoΖarinka da ko karar sigari baka sha, Umar ya girgiza kai ba tareda yace komai ba ya soma ΖoΖarin miΖewa.
"Ina kuma zaka Balele ya biΙa,
"Bakin Rafi zanje munyi da Zubaidah zamu haΙu can, Balele ya murmusa kafin yace" Zubaidah tsokale idon samarin Dukku, gaskiya kayi sa'a da har ake ΖoΖarin maganar aurenku su Gwatse basu taΙa kai mata hari ba.
"Umar yayu wata murmushi mai cike da ma'anoni kafin yace" Balele kasanni akan abinda nike so, wallhi duk garin nan babu wanda ya isa ya taΖura Zubaidah muddin ina numfashi matar yayanta ma data tashi gabanta ban ragar mata idan dai akan sanyin idaniyana Zubaidah ne balle wasu Ζananun tsageru su Gwaste, wani murmushin ya kuma kafin yace "Shege ka fasa gasu ga ita......"Balele ya bushe da dariya kafin yace" Kai mutumina daΙina da kai akwai zuciya.... "Ba tareda ya kallesa ba yace" Kaga ni zan wuce idan Oga Kabiru ya iso ka basa uzurina dan Allah.
"Aff ai yau bazamuga Oga KB ba cewar Balele.
"Umar ya jiyo gamida mada kallon meyasa.
"Bakada labarin zuwansu Alhj Dasuki da Ζaninsa da kuma Alhj Tahir Marafa na unguwar dutse, mai neman tsayawa takaran shugaban Ζasa..... "Ζaga kafaΙu Umar yayu kafin yace" Toh ni ina ruwana da zuwansu, Balele ya sake baki yana kallonsa kafin yace" Toh bikin saka ranar auren Ζ΄aΖ΄ansu za'ayi jibi jibin nan kuma Ζofa a buΙe take ga dukk mai niyan zuwa kasan dai yanda suke neman muΖamin nan dile suja talakawa jiki. Na tabbata Oga yana can ana yana neman ganin Su.
"Gajerwn tsaki Ummaru yayi kafin ya miΖe gamida Ιaukat hankacip Ιinsa da yake riΖe kan starry dashi idan zai tuΖi musamman mai nisa kafin ya wuce ya bar Balele a nan zaune yana shaΖan kayan mayensa, Balele na masa sallama ko kulasa baiyi ba don baiso ya bar masoyiyarsa tayita jira.
"Wow.... This is so woow I just cant believe it yau gani a mother land Ιina, infact motherland Ιinmu dukanmu cewar Salim dake kwance bayar convertible Ιin shida Tariq yayinda Jalal ke driving Labib ke zaune mazaunin me zamar banza.
"Salim yaci gaba da faΙin" Guys mu Ιan bi ta gefen can rafin I knw it will be awesome....."Gajeren tsaki Labib yayu sanda Jalal ya karyi kwanan rafin da gudun gaske..... Ihu Tariq da Salim sukayi suna shewa alamun suna cikin farin ciki yayinda Jalal ke tayasu....."Will shut up for heavens sake, haba... Cewar Labib da gaba Ιaya ransa a jagule yake sabida gani yake shikenan bazai samu Kausar ba ta kufce masa.
"Guy chill up muna celebrating ne, cewar Salim. Tsaki Labib ya kumayi kafin yace" What's even awesome in this place, this place is sucks dont you see it. Ever since I came to this town nake fama da rashes a jikina for heavens sake i dont even knw who the heck came with the idea a zo nan garin ayi engagement..... Ni idande a nan garin za'ayi Ιaurin aurenka believe me I wont attend your wedding don wllhi na gama zuwa garin nan.
"Tariq yace" Guy chill pills we wunt stay long here, besides nan shine mahaifarku...."Ζan tsaki Labib yayi kafin yace" Meyasa tuntuni basa zuwa garin sai yanzu sabida suna neman wani abi a wajen Ζ΄an garin sabida a nuna a Network labarun tara cewa Alhj Tahir Marafah yazo garinsu yayi engagement Ιin tilon Ζ΄arsa, people will be thinking sabida Allah yayi hakan amma mu munsan sabida buΖatarsa yayi don yaci takaran shugaban Ζasa....."Enougj of this Labib, Salim ya dakatar dashi kafin yaci gaba da faΙin" Inlawn nawa kake faΙin horrible things akansa you need to watch your mouth buddy.
"Murmushi Labib yagi a daΖile kafin yace" And who cared if he's your inlaw, gaskiya ne dole a faΙe ta, nasan Uncle shi ya ya basa wann shawaran don nasan Alhj Tahir is a responsible mutum bai iya Ζaryar Ζ΄an siyasa ba....." Kan yayi shiru saiji yayi Salim ya cakumu wuyarsa yana faΙin" How dare you say those things to my very own father,..... Kan kace me faΙa na ΖoΖarin kufcewa ysakanin Labib da Salim..... Sai sn Jalal da tun fara cecekucensu bai tofah uffan ba dama sun san miskilancinsa sun san bazai ce dasu komai ba don ya saba, burki yaja ya tsaya tsakiyan hanya Ζiiiiiiiiiiiiiiittttttttt" Gaba Ιaya saida suka jirkita. Juyows yayi yana watsa masu kallo kafin yace" Let me know if u done... Daga haka bai kuma cewa komai ba. Tariq ya fuzar da iska kafin yace" Guys pls lets not ruin our day, besides bai kamata kuna haka ba, this is childishness you're all matured enough, snn abinda gayika Labib shi yayi Salim, we are all here because of you guys, what will you expect us to feel idan kuna abu makamancin wann a gabanmu nida Jalal, ku tuna we arr all friends and we love each other like brothers, pls lets not ruin this special moment especially you Salim this part of your wedding the beginning of your happiness lts chirrr it pls.
"Murmushi Salim yayi kafin yace" Yeah Buddy you right i shoudnt hve done that, ya kalle Labib kafin yace I knw why my cousin is acting this way sabida nan babu Ζ΄an matansa i'm right.... "Sai snn sukayi murmushi su duka gaba Ιaya harda Labib Ιin ya Ιan daki kfaΙun Salim yace" Sorry Bro for been mean to you...." Its okay Buddy Salim ya faΙi da murmushi saman fuskarsa. Sai snn Jalal yaci gaba da Driving.
"Tsaye take bakin rafi saniyarta tana shan ruwa yayinda ita kuma Zubaidar keta faman tsane rigarta da ya jiΖe shaΖaf da ruwa sakamakon ruwan da aka tsulala, tafiya mai Ιan nisa ne daga wajen rafin zuwa cikin gari shiyasa har Ζ΄anzu Umar bai zo ba, so take ta tafi amma tana tunanin kar ta tafi yazo bai sameta ba ransa ya Ιaci, don ita kanta tsoron Ιacin ransa take sabida zuciya da yake dashi, don haka dole ba don taso ba taci gaba da tsane kayan duk ya kakkame jikinta shape Ιinta ya fito sosai.
"Gama parking Ιinsa keda wuya idanunsa suka sauΖa kanta, baiga fuskarta ba sai bayanta, shi tunda Allah ya haliccess zaice bai taΙa ganin mace mai kyawun sura irin ta wnn yarinya ba, haka kurum yaji ya Ζagu ta juyo yaga fuskarta, Su Labib daketa faman selfie basu ko lura dashi ba, Saida Salim ya taΙosa kafin suka hangi abinda ya hango, sai faman tsane rigarta take ko kaΙan batasan akwai wasu halittu a wajen ba bayan ita da saniyarta......" *God have Mercy* Cewar Labib cikin sandarewar murya yayinda su Salim da Tariq suka kasa furta koda kalma guda,.. Haka kurum Jalal yaji baison kallonta dasuke, dukda shi tantirin Ιan iska ne wajen hulΙa da mata amma ko kaΙan yau ji yayi bai son su kalle wann yarinya da har lokacin bai ga fuskarta ba......
Sameena ceππΎ
[1/23, 22:09] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
08
*©Sameena Aleeyou....✍πΎ
_Queen Samy Novels Forum.... ππ_
"Cikin sauri Jalal ya tada motan ganin abokan nasa basu da niyyan daina kallon budurwan nan, jin Ζaran mota yasata juyowa babu shiri cike da firgici da tsoro...."
"Gaba Ιaya suka bi kyakkyawan fuskarta da kallo, Zubaidah ta razana matuΖa da ganin irin waΙan nan samari, bata taΙa ganin mota irin tasu ba snn yanayinsu yasha banban da samarukan garinsu, sunfi kama da taurarin cikin shirin wasan kwaikwayo wato film.... Cike da tsoro da firgici ta shiga tare jikinta da hannayenta....." Kaman wanda aka tsinkara haka Jalal yaja motar da Ζarfin gaske suka bar wajen, gaba Ιaya sai chaaa suka masa meyasa zai masu haka, meyasa bai bari sunyiwa yarinyar chan magana ba.. Salim ya murmusa a fili yace *"Cow Girl"* She's very beautiful I've never seen a beautiful girl like her before my whole life, cewar Tariq... Labib kuwa cewa yayi " I already have that imagination me and her on my bed making love together...... " Bai gama rufe baki ba Jalal yaja wata shegiyar burki a tsakiyar titi, sa'an su Ιaya babu mota a bayansu dan kuwa shakka babu da sun bigi juna.
"Mugun kallo Jalal ke watsa masu yayinda suma suka bisa da kallon mamaki, yana huci yake faΙin"
" Dont mess with her, I perfectly well know you guys, dont you dare hurt her....."Dariya Labib ya kwashe dashi kafin yace" Man nasan fah duk cikinmu nan babu wanda ya kaika son morewa da mace so I believe kaima da zaka samu mace kamar wancan yarinyar ta ringa Ιebe maka kewa I'm sure da garin nan yafi maka daΙi.....Salim yayi saurin cewa " Wait why you do you even care? Naga baka taΙa yin irin haka ba koda Ζ΄ammatan ka muka nema.
"Jalal ya Ιago ido yana dibansu one by one kafin yaci gaba da faΙin" Salim you are getting married soon ya juyo ya dubi Labib da Tariq kafin yace ku kuma I'm quite sure babu me sonta tsakani da Allah cikinku....." Bai ida ba Labib ya tuntsure da wata dariya kafin yace" For Gods sake Jalal ya kake haΙamu da wann low class chick Ιin kiwo fa take could you even imaging. Com'on Dude a bar wann zancen dukanmu dai muna son jikinta Ζuma kaima nasan kana so...." Wani mugun kallo Jalal ya watsa masa kafin yace" Kaima kasan duk neman matana bana neman yara kaman wann yarinyar don bazan taΙa lalata rayuwar Ζ΄ar kowa ba, duk Ζ΄ammatan da nake hulΙa dasu kasan matured babes ne daga waΙan da suka girmeni ne sai sa'anni na I see no reason da zai sa na lalata rayuwar Ζaramar yarinya wanda kamata yayi ace tana school kaman wann yarinyar. Nidai na faΙa maku dont mess with that girl, daga haka ya fincike mota suka ci gaba da tafiya.
"Har lokacin jikinta rawa yake don tana tuno sautinsu sanda suke faΙin " Hi chick, you beaitiful kasancewar tayi karatu har zuwa aji uku na matakin sakandare yasa ta gane wasu dga cikin kalmomin da suke faΙi da harshen turanci, haka kurum taji ta tsnesu ko kaΙan bata taΙa ganin mutanen da ta tsana irinsu ba dukda kyawun hallita da suke dashi... Babu shiri ta kaΙa saniyarta ta soma tafiya don gani take kaman zasu dawo.
"A daidai bakin kwalta ta haΙu da Ummaru, ganin yanayinta yasa shi Ιan razana, don gaba Ιaya a figice take.
" Surbajo na yaya dai lafiya ya tambaya yana ΖoΖarin kota maya saniyar, Ιan langaΙe kai tayi cike da yarinta take faΙin" Ba kaine kaΖi zuwa ba gashi ruwa ya min duka.
"Ζan murmushi Ummaru yayi dama yasan hakan ka iya kasancewa. HaΖuri ya soma bata yana lallashinta har ta haΖura kafin ya sako zancen tafoyar da zaiyi nan da kwana biyu.
"Take idanun Zubaidah suka yi raurau, Ζwalla ya ciko idanunta, kaman me shirin kuka take faΙin" Yanzu shikenan tafiya zakayi ka barni...." Nan da nan yaji babu daΙi rausayinta ya cikasa, sandar hannunta ya karΙa kafin yace" Zubaidah Ιago ki kalleni, da Ζyar ta iya Ιagowa tana dubansa, Ummaru yaci gaba da faΙin" Ba jimawa zanyi ba sayi guda kacal zanyi, Shanu zamu kao chan jihar Lagos, na maki alΖawarin bazan wuce sati gudan nan ba. "Turi baki ta kumayi cikin harshenta na fullanci take faΙin" Nide da ka bar wann tofiya mu zauna kawai abinmu. "Umar yayi murmushi yana jin daΙin zance da ita yarintarta da Ζuriciyarta na birgesa, "
"Kinga kuΙin aurenmu zanje nemowa, ko bakiso ayi auren ne....."Tuni tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta dashi alamun kunya, mirmushi kawai yayi kana suka ci gaba da tafiyansu suna hiransu gwanin ban sha'awa..
***************************
"Hankalin Annah ya gaza kwanciya, haka kurum take jin mummunar faΙuwan gaba, tana jin gwara ta kasance da Jalal Ιinta don kuwa ziciyarta tana raya mata mummunan tunani sarara, tasan tabbas taje Dukku da yawa daga danginta zasu gujeta, don haka bazata je wajensu ba ko taje, toh wajen wa zataje ta tambayi kanta, take tunanin Ζawarta Inna Wuro ya faΙo mata hakan kuwa za'ayi don tabbas su Lado sukayi ido huΙu da Jalal zasu iya ganesa kuma zasu faΙa masa komai.. Babu shiri Annah ta hau shiri ta nufi Dukku.
"Yaya Hadiza ce zaune saman tabarma sai karyan loman tuwo take tana jefawa baki kaman bata taΙa cin abinci ba, dama wann Ιabi'arta ce idan tana cin abinci kai kace wani zai wabce ne, jin sallamar aminiyarta Iyalle yasata saurin wurga kwanon tuwon bayan Ζyaure, nan ta shiga shage miyar kukan jikin rigarga kafin ta amsa sallaman Iyalle, tsegege Iyalle ke kallonta kafin ta taΙe baki tace" Meye kike Ιoye mun.
"Hadiza ta haΙe gira tace ban gane ba, kaman yaya me zan Ιoge maki, abinci na ida ci yanzun nan.....
"TaΙe baki Iyalle tayi kafin tace" Umhm Ζawata kenan sekace bansanki ba, keni ba wann ba labari nazo maki dashi na arziki da Ιumi Ιuminta. Tuni Hadiza ta kaΙe bujenta ta gyara zama, ina saurarenki.
" Iyalle ta zauna da Ζyar kafin ta ciro gudan Ζ΄an dubu dubu cikin pose Ιinta ta goga su idanun Hadiza......
" Aiko baki sake Hadiza ke faΙin" Ζawata ina kikayi babban kamu haka, " Iyalle ta murmusa kafin tace" umhm toh ki zauna a nan ke anayi banda ke.
"Ban gane anayi vanda ni ba, cewar Hadiza,
" Iyalle ta gyara zama kafin tace" Albishirinki idan kinson waΙan nan bugun habujan kema kina iya samu.
"Hadiza anji zancen arziki tuni ta miΖe Ζafafu tana faΙin Ζawata ina daurafenki wazaiΖi masu gidan rana ai sede bai samu ba.
" Iyalle ta mutmusa kafin tace" Ai kindaiji labarin zuwan su Alhj Dasuki da Alhj Marafa me neman kujeran shugaban Ζasa,.... Hadiza ta gyaΙa kai da sauri kafin tace" Ai ancema layin anguwan ba'abi duk sojojine a wajen suke tsaro. Wai idan muyum yabi wajen ke ko Ζwaronr yabi wajen sai an harbe sa
" Iyalle tace" Toh barikiji na faΙa maki sojoji dai suna tsaron anguwar amma basu hana mutane zuwa ba, ke yau na taΖaice maki Ζofar gidan tamkar kasuwa , a nan aka raba mana dubu biyar biyar duk wanda yaje babu babba babu yaro, inaga dai da ingin buga kuΙi ma suka taho don kuΙin baya Ζarewa.
" Haba idanun Hadiza sukayi wulli wulli taji kuΙi tuni ta wawuro Ζafar silipers Ιinta tana faΙin " Ζawata tashi ki rakani, ... " Iyalle ta sheΖe da dariya kafin ta jawo Hadiza ta zaunar kana tace" Ζawata ai kin makara na yau kam an gama. Hadiza rai Ιace take faΙin amma Ζawata baki kyauta min ba, ai aminta batace haka ba, ni duk yanda naga kaya mai kyau kafin wata dilalliya a garin nan ta sani sai na sanar dake ...."
" Iyalle tayi dariya kafin tace" Nima yau na sani da Ζyar su Dije suka yarda suka tafi dani kinsan suke aiki a gidan, toh a daΖilin haka na samu, sann da naji sunce suna neman Ζarin ma'aikata sabida hidiman da zasuyi na bikin Ζ΄aΖ΄ansu nace bara na sanar dake kema ki samu, kinga sai ki tafi da wnn aljanar Ζanwar mijin taki tunda naga ta iya kala kalan abinci ko yaya kikace.
" Hadiza harza buga tsalle don murna kafin tace" Kai gaskiga Ζawata kin burge, kin kyauta min, aiko dolenta ma taje kinga nayi riba biyu ga kuΙinta ga nawa...... Dariya sukayi gamida tafe hannaye suka ci gaba da hiransu, kafin Iyalle ta tafi akan sai sun HaΙu.......
" Momyn Salim ce keta faman kaikomo yayinda ma'aikata suke take mata baya sai nuna yanda take so wajen da za'ayi event Ιin tsarin ya kasance, mussaman suka taho da masu tsara wajen daga Abuja, Annah ta dubi momy tace" Hajiya idan babu wani aikin zan wuce masauΖi. Momy ta murmusa kafin tace" Haba Annah ai gwara ki zauna a nan, ni banyi zaton jikin naki zai sakeki ki samu zuwa ba, snn wann biki fah na Salim ne kinga kuwa ai yakamata a soma komai dake.
" Annah ta murmusa kafin tace toh shikenan Hajiya yanda kikace.
"Isowan su Zubaidah kenan cikin kataparen gidan, daga ita har Yaya Hadiza kallo suka bi gidan dashi ko a mafarki basu taΙa shigowa gida irinsa ba, nan da nan Iyalle ta gabatar dasu ma Dije, Dije sai wani yauΖi take tana masu tambayoyin ΖaΖa uwaka ta haifeka irin ta smi matsayin nan, da Ζyar da roΖo dai ta yarda ta amince ta kaisu gaban momy a matsayin extra ma'aikata da aka Ιauka. Daga nan kitchen suka wuce suka soma aiki babu kama Ζafan yaro.
Sameena ceππΎ
[1/23, 22:09] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
09
*©Sameena Aleeyou....✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
"Balele nifa kaga irin abinda bana so muzo muna ΖoΖarin kutsawa da Ζyar Ιa don Zubaidah na wajen nan ba wlhi babu abinda zai kawo ni, Cewar Umar dake tsaye gefen Balele suna ΖoΖarin kutsawa cikin gidan da Ζyar.
"Ko saurarensa Balele beyi ba sai fizgo hannunsa da ya samu yayi suka shige daga kansu kuwa aka kulle gate.
"Can gefe suka samu suka zauna sai kalle kalle suke irin Ζyale kyalen dake a wann gida, darene amma tamkar rana sabida yanda wutan lantarki ya gewaye ko ina, mutane sai kai komo ake.
"Momy da Mamin Labib ne tafe suna haΖ΄ewa bene yanda baΖinsu suke yayinda Zubaidah ke take masu baya hannunta Ιauke da tray, sai kalle kalle take tana mamakin dama akwai gidaje masu kyau da tsari irin wann a garinsu, kai idan aka ce zata taΙa shiga gida irin haka a rayuwarta zata musa.
"Suna Mami ta mata umarni ta ajiye. Nan tabi umarnin Mami ta ajiye ta nufi Ζasa, nan ne fah ta Ιata a hanya, don kuwa wann girma gida dole ma mutum ya Ιata musamman irinta da bata taΙa shiga irin gidan ba.
"Hanyar da ta miΖe dama nan tabi, sai wage waige take, gashi abinda yafi bata mamaki shine wann hanyar yayi shiru da yawa, anya nan suka biyo dasu Hajiya kuwa, haka dai taci gaba da tafiya har ta hangi stirs da sauri tayi wajen ta soma sauΖowa.....
" Bata ankara ba saiji tayi ta bugi jikin mutum, kallon kallo suka shiga yima juna, haka kueum taji gabanta yayi mugun faduwa snn ta rasa a ina tasan wann fuska, shi kuwa Jalal kasa daina kallonta yayi, haka kurum yaji ya tsinci kansa cikin farin ciki,.... Murya na rawa ta soma basa haΖuri.
"Dan Allah kayi haΖuri wllhi bansan da mutum bane, kayi haΖuri kaji yallaΙai kar ka sa sojojinku su harbeni......" Jalal kam dariya taso basa ganin duk yanda ta daburce, is Okay is Okay... Ya faΙi fuskarsa Ιauke da murmushi kafin yace zo ki wuce, da sauri ta raΙa ta gefensa ta nufi downstirs,
"Har ta kusa sauΖa Jalal yace" Emm ina zakije.
" Cikin sauri tace dashi sashen ma'aikata. Ζan murmushi yayi mai bayyana dimpls Ιinsa kafin yace" I think Ζ³ou miss the way, kallonsa tayi ba tareda tace komai ba don kyaun halittarsa na firgita ta tamjar ba mutum ba haka take dubansa musamman da yayi murmishi.
"Ganin tayi sakare tana dubansa yasa yin wani murmushin kafin yace "muje na nuna maki, babu musu tabi bayansa, har Ζofan da zai fitar da kai BQ ya fito da ita,.... Da sauri ta nufi Ζofan ba tareda tace dashi komai ba, "Jiyo daddaΙan muryarsa tayi yana faΙin" Baki min godiya ba.
"Ζan juyowa tayi gamida masa godiya cikin harshen fillanci, Shima murmushin yayi ya amsa mata cikin harshen fillanci... Jin yayi mata fillanci yasata ficewa da sauri tana Ζunshe dariyan da yazo bakinta da hannunta don kuwa da kalman tsokana ta masa godiya shima kuma da hakan ya amsa. Itakam tafi bashi balarabe ko bature kwata kwata bata kawo bafilatani bane.... Har ta isa kitchen murmushi take....
" Wani uwar harara Hadiza ta watsa mata kafin tace" Ke murmushin me kike, snn meyasa kika jima daga kai abu kinsan aiki na jiranki. Kinje kin saki baki da hanci kina masu kallon Ζurillan da kika saba koh.
" A'a emm dama..... bata gama faΙin abinda zata faΙa ba Hadiza ta jawota da niyan jibganta.... Sauran ma'aikata sai Ζ΄an gulmammaki suke, Annah ce ta shigo dama itace incharge na ma'aikatan tunda ta taho, da sauri ta Ζwaci Zubaidah daga hannun Hadiza tace" Haba baiwar Allah, ko me ta maki ai bai kamata kina dukan budurwa kaman wann ba, Hadiza dai bata ce komai ba sai hararan Zubaidah da take.
"Annah ta kalli Zubaidah gamida sakar mata murmushi kafin tace " Ζauko karas Ιin chan kin fere min babu musu Zubaidah tayi yanda tace cike da girmamawa. Haka kurum Annah taji yarinyar ya burgeta ta shiga ranta lokaci guda...
" Tun shigowarsa Ιakin yake murmushi ya kasa ce masu komai sai murmushi. Salim dake tsaye cikin closet Ιinsa na shiryawa ango to be, ya kalli Jalal ta jikin mirror kaΙin yace" Whats up with you Buddy, you seems very happy, Murmushi Jalal ya kumayi gamida zama tsakanin Tariq da Labib da suke kan buga PS5..... Ζaura hannayensa yayi bisa kafaΙunsu yana duban Salim dake tsaye closet kafin yace" Guys I just saw her, I saw her......
" Da mamaki suke kallonsa har suna haΙa baki wajen cewa" sawWho"???
" Kaman wanda ya tuna abu, murmushi yayi ya miΖe ya nufi Ζaramin fridge Ιin dake Ιakin ya Ιauko kwalban wine ya tsiyaya a cup ya kurΙa, Labib ya dara kafin yace" Guy wacece ka gani.
" Jalal yayi murmushi ya kuma kurΙan wine Ιin kafin yace "Never mind its just my imagination... "Dariya kawai sukayi sanda Salim ya Ζarasa shirinsa suka fito gaba Ιayansu suka nufi filin event wanda aka tsara shi kai kace a turai ne, .....
"Isowar su Kausar kenan fili ya kacame, Salim ya shagala da kallonta don kuwa tayi kyau har ta gaji, wata arniyar silver gown ta saka kai komai nata silver ne sai ta fito tamkar wata me zuwa gasar sarauniyar kyau.
"Idon Labib ya sauΖa kan Asmah wacce itama tasha gayunta cikin red gown tayi Ιauri irin na yayi da royal blue vail a kanta tayi kyau matuΖa, duk haΙuwan da suke bata taΙa masa kyau irin ta yau ba.
"Taro yayi taro nan da nan aka soma gudanar da Event.
"Zubaidah sai leΖe take ta windon kitchen tanason fita taga amaryar don taji anyi annoucing isowarta. Ta Ιan saci kallon yaya Hadiza kana tace" Yaya don Allah naje na kalli amaryar.....Wani uwar harara Hadiza ta watsa mata kafin tace" Bazakije ba don uwarki, shegiya me shegen son kallon tsiya, wann abu duk a kunnen Annah ya faru. Ζan girgiza kai tayi dukda batasan alaΖan dake tsakanin Hadiza da Zubaidah ba ta tabbata Zubaidah tana shan wuya wajen Hadiza, Ζarasowa cikin tangamemen Kitchen Ιin Annah tayi ta dubi Zubaidah dake Ιaman leΖe ta window tace" Zubaidah kina son kallo ne.
" Da sauri Zubaidah ta juyo ta dubi Annah gamida kallon yaya Hadiza data sakar mata harara. Annah tayi murmushi don kuwa taga irin kallon da Hadiza tayima Zubaidah..... Baki na rawa Zubaidah tace " a'a Annah ban Ζarasa haΙa waΙan nan parantan ba.
"Annah ta murmusa kafin tace kar ki damu zo muje ki kalla, juyawa Annah tayi ta dubi Elizabeth Ιaya daga cikin ma'aikatan da suka taho dasu daga Abuja masu uniform kana tace" Elizabeth continue with the plates arrangement" Elizabeth ta amsa da Okay Ma.
"Duk sunsha mamakin jin Annah na turanci harta Zubaidah saida tayi mamakin jin Annah tana turanci... "Hannunta Annah ta riΖe suka nufi farfajiyan gidan yanda ake gudnar da shagalin.
"Tun fitowarsu idanun Jalal ya sauΖa kansu, yasha mamaki sosai ganin Annah tare da Zubaida riΖe da hanun juna har suna magana. Toh dama Annah tasanta ne, toh a ina tasan ta??? Kasa samo amsar tambayoyin nasa yayi.
"Salim dake rawa da bride to be Ιinsa idanunsa suka sauΖa kan Zubaidah, kallon ta yake da mamaki, a hankali ya furta *"Cow Girl"* me take yi a nan.???
" Ζan sunkuyowa yayi saitin kunnen Kausar kana yace" Sweetheart barin je wajen su Labib I'll back in some minutes.
" Kausar ta murmusa kafin tace" No prblm Dear take ur time. Satan idon mutane yayu gamida manna mata kiss a kumatu...."Zari ido waje Kausar tayi tana dubansa, harda wani kashe mata ido guda kafin ya wuce.
" Asmah ta taso da sauri tana dariya, a daidai saitin kunnen Kausar take faΙin " Girl I saw that, lallai wann angi naki za'a sha fama, nide kar aje ana kiran mumsy da Papy suzo su kawo.Ιauki, Hararan wasa Kausar ta watsa mata gamida riΖo hannayen Asmah suka soma yin rawan a tare.....
"Salim yana Ζarasowa table Ιinsu ya samu zancen cow girl suke dun babu wanda yasan sunanta cikn su, as usual Jalal yana warning nasu. Caraf idanun Jalal suka haΙu dana Annah, alama ta masa da hannu kan yazo.
"Su Salim suka dubesa suna murmushi Ζasa Ζasa suke faΙin yaje Ζila Annah tasnta ne. Zubaidah kuwa tana ganinsu a tare a haka, ta tunosu ta tuno yanda ta gansu bakin rafi, faΙuwar gaba ta tsinci kanta dashi..... Tana cikin tunanin ta jiyo nuryar Annah tana faΙin" Zubaidah barin yi magana da yarona, gyaΙa mata kai kawai Zubaidh tayi ba tare da tace komai ba, har lokacin Ζirjinta na bugawa musamman da Labib ya Ιago mata hannu tare da kashe mata ido guda.
"Ζan matsawa gefe Annah tayi itada Jalal tana masa magana amma idonsa da hankalinsa gaba Ιaya suna kan Zubaidah......
" Daga yanda suke zaune can baya shida Balele ya hangeta sai faman rarraba ido take, ya kuma duban Jalal daya kafe ta da idanu, yaga sanda suka sakar wa junansu murmushi..." Take gabansa yayi mugun faΙuwa Da sauri ya miΖe ya nufi yanda take.
" Saida ta razana da ganin Umar don batayi zaton zata gansa a nan ba.... Juyawa yayi sukayi ido huΙu da Jalal, Jalal yayi saurin kauda nasa kan gefe.
" Fuska a tamke tana gaishesa ko amsawa baiyi ba ya soma faΙin" Wanene wancan saurayin da kike masa murmushi.
"Ido ta zari tana dubansa kafin tayi magana a zuciye yake faΙin" Naga irin kallon da yake maki, ke bakisan yaran masu kuΙin nan ba koh, waima har yanzu aikin uwar me kike da bazaki tafi gida ba,..." Kasa cemasa komai tayi sai kallon data busa dashi, kishinsa yayi yawa bacin bata ga laifin datayi a nan ba ko Ζwara.... " Umar ya kuma hasaΖa ganin tai masa biris,...." Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryarsa naci gaba da faΙin" Wani gulmar ne ma ya fito dake nan keda kike aiki a kitchen, Okay dama kallon maza kikazo yi, fine kici gaba. Yayi maki kyau, ni zan wuce lagos gobe da asubahin fari. Idan kinga dama ki bar wajen nan as soon as u can. Daga haka bai kuma cewa komai ba ya wuce fuuuu, Ko sallama da Balele bai samu zarafin yi ba ya fice abinsa.
" Labib ya dubi Salim da Tariq kafin yace guys ku kwantar da hankalinku ni nasan maganin Jalal, kan wann Ζazamar talakan yarinyar zai nemi raina mana hankali, muna buΖatan jikinta kuma dole mu samu bamu taΙa neman abu mun rasa ba so bazamu fara yau ba.
"Jalal na isowa suka sakar ma juna murmushi, farin ciki yakeji na ganin wann yarinyar, baisan me yakr ji gameda ita ba amma tabbas yana jin wani abu.
"Labib ya sunkuya Ζasan table ya ciro waΙi Ζwaya a aljihinsa ya tsiyayi drink a cup ya jefa a ciki. Hankalin Jalal gaba Ιaya naga neman ta ina ,ubaidah ta koma don bai ganta ba kuma. Be kawo komai a ransa ba ya karΙi drink ΙΙin ya soma sha, nan ya soma jinsa a sama, nan suma suka biyesa kaman suma a bugen suke, Salim ya miΖe ya nufi yanda Kausar da Ζawayenta suke yace mata " bara suje su Ιanyi freshing up dasu Labib, Kausar bata kawo komai ba tace dashi sai sun dawo take care. Kiss ya hura mata kan tafin hannunsa kafin ya wuce" Ζ΄ammata Ζawayenta suka Ιauki shewa, cewa suke wow Kausy tayi sa'an miji mai sonta snn romantic guy. Kausar kuwa sai jin kanta take mai sa'a a cikin mata.
"Zubaidah kuwa sauri sauri ta nufi hanyar fita amma bata cimma Umar ba, ko kaΙan bata son fushinsa, gashi tafiya zaiyi gobe gobe kuma gari mai nisa, itakam bazata so suyi irin wann sallama ba, cikin sauri ta nufi titi tana nemansa, abinka da yarinta ko tunawa da darene batayi ba ga yanayin anguwar babu mutane sosai gini ma can ΙaiΙaiya kake hangowa.snn ko tunawa ta faΙawa Annah batayi ba. Haka Annah tayi neman duniya bata ganta wajen taron ba eata zuciya tace Ζila ta koma kitchen.
"Haka su Labib suka ja Jalal suka nufi cikin mota dashi, suka fice.... " Zubaidah sai faman shate hawayen fuskarta take tana bin salΙalelen titin nan Ζarshe har ta Ζarasa Ζarshen layin yanda babu kwalta, nan ta soma tunanin anya ma ba Ιata tayi ba, tsoro dafirgici suka shigeta, nan take ta soma Ζwalla kiran sunan Umar tana wani sabon kuka,... Daga yanda suke suka jiyo sautin ta, tuni Labib ya karya kan mota suka nufi wajen.... Zubaidah na hango fitilan mota ta nufota ta soma ja da baya, tuni Labib yayi parking suka fito gaba Ιayansu.... Kan kace me sun gewayeta, kallonsu take tana ΖoΖarin ja da baya amma sai taga wani a bayan nata, idan rayi nan gefen sai wani ma ya tarota.... Duk wani addu'an da ya,o bakinta yinsa take, cike da tsoro da firgici cikin murya irinta me kuka take faΙin" Don Allah kar ku cutar dani, su waye ku meyasa kuke bibiyata......" Bata gama yin shiru ba taji Jalal ya rungumota cikin muryar maye yake faΙin" here she is......" Wani irin ihu Zibaidah ta sake tana mai ΖanΖame jikints, Jalal kuwa da su Labib dariya suka fashe dashi, Jalal yana dariya yana tangaΙi ya Ιora Ιan yatsansa akan bakin Zubaidah yana faΙin" Shiiiiiii, har loΖacin tana rungume cikin hannayensa, Kuka take kaman ranta zai fita, Labib ya Ζaraso gamida fizgeta hannun Jalal.......
" Dukda ba a cikin hankalinsa take va da Ζyar Labib ya iya fincike Zubaidah daga hannunsa, cikin muryar maye yake faΙin" Don't Labib dont you date think of doing that,........" Yana faΙuwa yana tashiwa da Ζyar, su kuwa su Salim da Tariq me zasuyi banda dariya,.........
"Ihu Zubaidah tayi sanda su duka uku suka nufota, Saalim Labib da kuma Tariq, Labib ya basu umarni dasu banΖare masa ita, hakan kuwa akayi, Jalal babu yanda ya iya Ζwayan da Labib ya basa ya hanasa taΙuΖa komi k motsi me kyau ya kasa balle ya tashi,
"Allah sarki, haka tanaji tana gani tana roΖonsu tana kuka basu fasa Ζudirin da sukayi niyya akanta ba, Tariq da Salim suka banΖareta ta hanyar rirriΖe mata hannaye, Labib yasa hannu ya kama tun daga wuyar rigarta ya keta daga sama har Ζasa, gaba Ιaya ruΙewa suka yi sanda na shanunta suka bayyana wanda suke a cike manya manya a tsartsaye, tuni Labib yakai masu capka kaman tsohon haka ya ringa wasa da albarkatun Ζirjinta su Salim na tayasa Ζarshe chaa suka mata akai su duka uku kowa nason ya fara biyan buΖatansa, ta yunΖura zata tashi Labib ya kifa mata mari. Bige bige take kamar mahaukaciya ta kuma yunΖura Salim ya danneta, Labib ya jawo wani duysi ya buga mata a Ζafa, tuni ta saki Ζaran azaba, haka su Tariq da Salim suka banΖare Ζafafunta suka rabata da suturanta,.....Wani ihu mai Ζarfin gaske ta sake sanda Labib ya shigeta, gaba Ιaya ba zuwan wasa ya mata ba, tunda Zubaidh tayi wann Ζaran bata kuma sanin yanda kanta yake ba.
"Haka Labib yayita gurzanta babu tausayi balle imani, saida yayi mai isansa kafin ya miΖe Salim ya soma, shima saida yayi iyaka yinsa kafin Tariq ma Ιora da nasa, haka sukayi ma baiwar Allah nan kaca kaca babu imani babu tausayi valle tuna mahaliccinsu π......
Sameena.ceππΎ
[1/23, 22:10] +234 803 619 0581: ππππ *ZUBAIDAH*
10
*©Sameena Aleeyou...✍πΎ*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
" Komawa gefe sukayi suna maida numfashi, Tariq ya dubi Jalal dake kwance gefe alamun bacci yayi gaba dashi tuntuni, Dariya ya fashe dashi kafin yace" Guys lets get going kafin wani ya ganmu.
"Salim ya busar da iska kafin yace" Ban taΙa jin mace me daΙinta ba, shes so sweet I wish I could have her everyday...." Labib ya miΖe da Ζyar yana maida belt Ιin wandonsa kafin ya nufi mota ba tareda yace komai ba, jin har ya tada mota yasasu saurin Ιauko Jalal suka saka sa cikin motan, Tariq yakai dubaΙsa ga Zubaidah wscce ke kwsnce lifeless tamkar maras numfashi kafin ya dubi abokansa yace" What about her? Are we gonna leave her here???
"Tsaki Labib ya buga kafin yace" Dude idan zaka shiga mota mu tafi ka shiga what next, badai ka biya buΖanta ka ba me kuma yayi saura..." Tariq ya Ιanyi jimm kafin yace" Com'on guys we can leave her here lifeless she almost died...." Cike da Ζosawa Labib yace" If you cant leave fine, ka tsaya idan police suka kama ka da dead body sai ka masu bayani, kokuma Dad Ιinka ya ganka da ita kaga he'll definitely be proud of you huh??
" Salim ne ya riΖo Tsriq suka wuce mota yana faΙin" lets go Buddy I dont think that girl is still alive.
"Labib kuwa kaman jira yake suna shiga ya fincike motar......
" Har aka gama event babu Zubaidah babu dalilinta , Neman duniyar nan sunyi basuga Zubaidah ba, Ζarshe dai Hadiza ta wuce gida da tΖ΄nanin ko Zubaidah ta koma gida..
"Hadiza ta cika tayi fam sai banbamin masifa da bala'i take" wllhi yau Zubaiidah sai na kusan kasheki a gidan nn..." Hamma Habibu sai faman bata haΖuri yake yana faΙin" Kiyi haΖuri Hadiza zata dawo ne, Kamalu ya Ζaraso ya rungume babansa yana kuka yana faΙin shidai yana son ganin Didinsa.. Rungumesa Habibu yayi suka soma kuka a tare. Wani takaicin ya kuma tokaran Hadiza, ficewa tayi waje ta barsu sunata sharΙan kuka.
"Mami ta kuma kallon momy datayi jugum duk suna jiran dawowan Ζ΄aΖ΄ansu kafin tace" Anya Farha bazamu sa securities neman yaran nan ba, what if simething bad happens to them, nan Ζaramin gari ne ba kaman Abuja ba da suka saba fita suyi dare, nan babu wani wajen zuwan da har zasuyi dare a wajen, they should be home by now...."Momy ta matso ta rungume Mami kafin tace" Its Okay Mami I know they'll be home soon,.....
"Dammit dammit those boys will never change... Cewan Alhj Kasim cike da Ιacin rai, duban Barr Munir yayi kana yace" Keep on trying their numbers, daga haka miΖewa yayi ya fice zuwa waje...
"Su Salim kuwa basu suka shigo gidan ba saida suks tabbata kows yayi bacci, cikin sanΙa suka wuce sashensu, gaba Ιaya suka zube a parlor suna maida numfashi.
"Kaman daga sama sukaji an banko Ζofan an shigo... Daddy ne tsaye yana binsu da mugun kallo,
"Salim da Tariq kam tsoro ne Ζarara ya nuna a fuskarsu yayinda Labib ke binsa da mugun kallo shima.
"Where the hell have you guys been??? Dady ya tambaya fuska babu alamun wasa,...
"Labib ya miΖe yana Ιalle buttens Ιin rigarsa kafin yace" Uncle would Ζ΄ou pls stop, why ate you asking us like we are still kids, ya kamata ka gane mun girmafah yanzu we can decide our life.
"Daddy ya fuzar da iska kafin yace" I see, I see. Ya sauΖe dubansa kan Salim da yayi zuru kamanai tunani kafin ysce" And where is your engagement ring. Sai snn Salim ya duba yatsan sa yaga tabbas babu zoben da Kausar ta saka masa Ιazu wajen engagement. Ζan shafa kai yayi kafin yace" Com'on Dad I lost it. I'll by another one.
" We must talk gobe kunaji na, cewar Dad, daga haka sa kai yayi ya fice zuciyarsa na ci gaba da tafarfasa...
*Washe gari*
" Asubahin fari Hadiza ta fice ta nufi gidan Alhj Kasim, don izuwa lokacin itama ta soma shiga damuwa,. Hamma Habibu kam ko bacci bai sami zarafin yi ba haka ya kwana kuka, idan Kalmalu ya farka a bacci ya tayasa
"Securities kuwa sam sunΖi barinta ta shiga gidan, sai faman bambamin masifa take...."Anna dake tsaye ta back yard ta jiyo sautin Hadiza, aje bokitin hannunta tayi da sauri ta nufi gate..
"Hadiza na hangota ta nufota itama cikin sauri tana huci take faΙin" Wllhi kece, kece kikace tazo ki kaita ganin amarya, yun daga lokacin ban kuma ganinta ba. Annah ta riΖo hannunts kafin tace karkiyi magana haka, nida ke duk munsan tun jiya muka nemi Zubaidah wajen bikin nan, keda bakinki kikace gida ta tafi anyi haka ko ba'ayi ba. Snn naga kalan taΖura yarinyar da kikeyi, wnn kaΙai kan iya sa yarinyar ta tsere ma azabarki Ζila ta gaji da wahala da azabtar da ita da kike ne, ko gaban hukuma akaje dole ki bada wann statement Ιin... Haba nan fah Hadiza ta soma borin kunya musman dataji Annah na mata turanci,... Can kuma hawaye suka ciko idanunta ta dubi Annah tace don Allah ki taimaka min bansan yanda zan sameta ba.
" Annah ta sauΖe ajiyan zuciya kafin tace" Kinga yanzu Ζarfe shidan safiya masu gidan nan basu tashi ba balle nakai ΖoΖon taimakona garesu, Amma yanzu abinda zamuyi mubi layin nan muna tambaya muna nemanta wataΖila Allah zaisa mu dace. Babu musu Hadiza tabi bayanta suka bazama neman Zubaidah.
"Har Ζarshen layin suka isa babu ita babu alamunta, gashi basu haΙu da mahaluΖi ko guda ba balle su tambaya.
"Har zasu juya Annah taji kaman tayi tuntuΙe da mutum cikin ciyawa, aiko tana sunkayawa ta ganta kwance cikin bushesshen jini kaman an yanka dabba, gwiwoyin hannayenta da Ζafafunta gaba Ιaya ta kukkuje kai kace da kate tayi faΙa, Ζofan hancinta jini ne shima ya bushe, haka nan an Ιaure bakinta da farin Ζyalle, goshinta ma jini ya bushe alamun anji mata ciwo.....
"Annah bata san sanda ta durΖushe a wajen ba gamida fashewa da wani irin kuka wanda hakan yaja hankalin Hadiza,... Tana isowa wajen taga abinda Annah ta gani.
" Tsugunawa tayi a wajen dirshan, duk rashin imanin Hadiza da wulaΖanta Zubaidah da take yau saida taji tausayin Zubaidah...."Baki na rawa Hadiza ke faΙin " FyaΙe aka mata, sun mata fyaΙe.... Wani sabon kuka ya kufce mata.
"Annah tayi saurin saita kanta kafin ta cicciΙi Zubaidah da Ζyar, ta dubi Hadiza tace" Maza ki koma can gidan kice ni na aikoki ki kira min Ιana Jalal kinga ban fito da wayata ba,shi zai taimaka ya taho mana da Ζ΄an sanda don nasan da Ζyar asibiti su karΙemu babu jami'an tsaro, amma yanzu barin fara kaita asibiti don ceto rayuwarta. GyaΙa jai jawai Hadiza keyi hawaye na zuba idanunta, tana tunanin yau Habibu yaji ko yaga wann zance tabbas sai ya kusa mutuwa, cikin sauri ta juya yayinda Annah ta wuce bakin titi neman adaidaita.
" juyawan da Hadiza zatayi taji ta taka wani abu kan Ζarfe, sunkuyawa tayi ta Ιauko abin, shakka babu zobene size Ιin hanun namiji, kuma da gani yaji kuΙi zai tsada, sakawa bakin zaninta tayi ta Ζulle kafin ta soma tafiya.....
"A hankali ya sima buΙe idanunsa da suka masa nauyi, da Ζyar ya iya moΖewa zaune gamida dafe kansa da hannayensa guda biyu yana son tuno me ya faru a daren jiya.
" Juyawa yayi ya kalli abokansa da suke kan sharan bacci babu sallah balle salati...."A hankali komai ya soma dawo wa Jalal....a fili ya furta *"Zubaidah"* Kaman wanda aka zabura ya miΖe abubuwan da suka faru suka shiga dawo masa kwanyansa, ya tuno sanda ya riΖota, ya tuno shi ya fara kamata, ya tuno sanda Labib ya fizgeta daga hannunsa, ya tuna sanda Labib ya keta mata rigarta, ya tuno sanda suke wawa akanta kaman almajiri yaga abinci....." Jiri ya soma kwasan sa, Wani wawan Ζara ya sake wanda saida ya tashi duk wani mahaluΖin dake barci cikin gida.....
*"NOOOOOOOOOOOO"*
"Ya faΙi da Ζarfin gaske, gaba Ιaya suka miΖe babu shiri suna dubansa, Jalal ya Ιago rinannun idanunsa yana dubansu Ιaya bayan Ιaya, fuskan Labib yake kallo yana tuna sanda ya fara raba Zubaidah da mutuncinta dukda a lokacin yana ckin maye amma hakan bai hanasa ganin komai da fahimtar komai ba.... Tsalle yayu ya cikumo wuyan Labib ya shiga dukansa a ciki kaman Allah ne ya aikosa...yana faΙin" You raped her didn't you, you started it, you imbecile how dare you...... Da Ζyar Salim da Tariq suka Ζwaci Labib. Kukan kura ya kuma ya jawo Salim da hannu guda snnTariq da hannu guda ya daki Ζofar Ιakin ta buΙe ya nufo downstirs dasu haka ya ringa jansu a Ζasa kan stirs har saida ya fito waje........ Labib ya goge jinin da ya Ιata masa hanci kafin ya biyo bayansu a guje, daidai lokacin dasu Daddy su momy suka fito.......
0 comments:
Post a Comment