"Cikin sauri Labib ya miƙe yabi bayansu. Momy da Mami a balcony suka haɗu kowa ta fito daga ɓangaren mijinta don suma sunji ƙaran da Jalal yayi, a tare suka nufo downstirs... Curus suka tsaya suna bin Labib dake sauƙowa daga ɓangarensu wanda gaban singlet ɗinsa gaba ɗaya jini ya ɓata.... Mami ta nufesa a kiɗime tana faɗin" Baby me ya sameka, ina ja samo jini haka. Ɗan tareta da hannu Labib yayi sai sauri yake ya nufi parlor yana faɗin" Mami its nothing pls ku koma baccinku we can handle this, pls kar ku faɗawa wasu Dad...."Muryasa ya carke sanda ya jiyo muryar Dad daga waje yana falfawa Jalal ruwan ashariya da masifa, Ai Labib kaman zai kife ƙasa haka ya fice daga parlorn ya nufi waje don sauri. A tare Momy da Mami suka rufa mai baya.
" Barr Munir ya cafe zancen da faɗin" Ai dama tsiyan ka sake wa talaka kenan, yanzu Alhj ka duba yanda yaron nan yayiwa yaran nan snn kaji yanda yake mayar maka da magana tamkar wani sa'ansa..... Shiru yayi sanda ya hangi ƙanwarsa Hajiya Farha na fitowa waje,... Ƙarasow Momy tayi taga fuskan Salim duk a daddauje alamun an lakaɗɗesa.
"Boy who did this to you, Momy ta biɗa sanda take shafa fuskar Salim. Alhj Kasim ya dubesu itada Mami kana yace" Farha ku shige gida....." Idanun Momy ya sauƙa kan Jalal dake riƙe da sanda alamun shi ya jibga masu yara, ai a tamanin tayi kansa tana faɗin "Dama wnn shegen ne ya dakeku kuka ƙyalesa dashike ku saunaye ne....." Da sauri Dad da Barr Munir suka riƙota suka hanata ƙarasawa ga Jalal dake tsaye a wajen ko gizau baijiba da alama, banda huci babu abinda yake...
" Barr Munir ya jiyo ya dubi Jalal kana yace" Yanzu kai Jalal abinda zakayi kenan, mutanen da suka ɗaukeka tamkar ɗan uwa shine ka rasa sharrin da zaka laƙaba masu sai na fyaɗe, toh da kasan son yarinyar kake ai ba sai ka mata fyaɗe ba da nemanta da aure kayi da yafi maka.
"Jalal yayi murmushin takaici yana duban Barr Munir a hankali ya tako ya ƙaraso hat gabansa" Ido cikin ido suke duban juna kafin ya soma faɗin" Barrister bari kaji na faɗa maka, nafi ƙarfin na ɗaurawa su Salim sharri wllhi snn idanakwai waɗanda zan ƙulla masu sharri a wann rayuwa toh badai su Salim ba, sabida ƴan uwa na ɗaukesu inaga dukda dangantakar dake tsakaninku dasu nafika sonsu snn duk neman matan da mukeyi bazan musa maka ba a tare mukeyi snn da kake cewa son yarinyar nake shiyasa na mata fyaɗe kayi kiskure Barr sabida ni a tsarin bin mata na babu fyaɗe gasu nan ka tambayesu, snn koda zanyi fyaɗe ma bazanyiwa ƙaramar yarinya kamar Zubaidah ba, don haka Barr a matsayinka na mai hidima da kotu nasan kafini sanin hukuncin fyaɗe a ƙasar nan, kar ka dubi dangantakar ku kar ka dubi maysayin aikinka a companin iyaƴensu, ka dubi girman laifin a ƙundin tsarin mulkin ƙasa snn ka dubi girman laifin a al'adance snn ka duba a musulunce tunda nasan kai musulmi ne, ka shigar da waɗan nan azzalumai kotu ka ƙwato wa yarinya hakkinta, wnn shine kawai zai proving mana You are not a coward snn kasan aikinka snn kana hukunci da gaskiya......"Enough Barr ya daka masa tsawa kafin yaci gaba da faɗin" How dare kai har ka isa ka faɗa min abinda zanyi, wnn shi yake nuna dafinitely kai kayi raping nata....." Bai gama yin shiru ba suka jiyo muryar Salim yana faɗin"
"Toh kai Jalal da kake ta faman zare kanka kasan dai wann laifi tate mukayi sa, dukanmu huɗu mukayi raping nata so idan ma hukunci za'a mana harda kai....."Bai gama yin shiru ba su momy suka shiga tafe hannaye suna salati, Mami ta rungumo Labib ɗinta tana faɗin" wllhi bazai taɓa sakuwa ɗana ya karashe rayuwarsa a gidan yari ba, wllhi baku aikata ba, son pls tell me you are not involve..... "Barr ya fashe da dariya kafin yace" Hajiya pls kima daina ɓata hawayenki babu wanda ya isa ya ɗauresu don mune da ƙasa, idan kana kuɗi toh fah sai abinda kaga dama zakayi. Kan wata kucakar yarinya ƴar talakawa baƙauyiya kike tunanin za'a rufe yaran nan, ai hakan ba mai yuwuwa vane.... Ya ƙarashe maganar yana wani shafa haɓarsa.
"Jalal kuwa gyaɗa kai yayi kafin yace we shall see ya ƙarasa gabansu Labib ya dube fuskokin abokan nada kafin yaci gaba da faɗin" Da biyu kuka bani abinda zai bugar dani, kunyi hakan ne intentionally don ku aiwatar da mummunar kudirinku akanta, toh wllhi wllhi ku sani each and every one of you must pay..... Daga haka ya nufi hanyat fita......
"Cak yaja ya tsaya ganin mace ingarmiya wacce a tsaye ta kaisa tsaho tsaye a gabansa ga hawaye na bin ƙuncinta..... Su Dad ma gaba ɗaya suka maida dubansu ga matar. Yaya Hadiza kuwa kaman jira take tuni ta soma cire takalman ƙafafunta tana ƙoƙarin shan ɗammara take faɗin" Kune, wllhi kune ku kuka mata fyaɗe duk sau kunyi bayani...... Ta sunkuya tamkar taɓeɓɓiya tana shirin wawuran duwatsun dake a tsakiyar gidan cikin wani ruwa mai zubowa daga sama zuwa ƙasa.... "
"Oh my Lord! Shes crazy cewa Alhj Kasim, ya dubi Barr ya ce , Barr take care of her, kar a barta ta fice kasa gurd su kamata sƴ rufeta don wann matar ta fita da wann zance shukeɓan sunanmu ya ɓaci a duniya,... Barr ya gyaɗa kai yana murmushi kafin ya nufi kiran gurds, Alhj Kasim ya dubi Jalal dake shirin fita kafin yace" Dont do anything foolish boy ir you'll live to regret it, ya dubi su Salim kana yace ku wuce muje, babu musu suka bi bayansa kana ganin su kaga sangartattatun yara wanda basu san neman komai ba sede a basu.
"Kafin Jalal ya karasa wajen matar nan gurds sun kameta, yana da tabbacin matar nan tasan Zubaidah tunda gashi tana faɗi. Cikin sauri ya nufi gate, kai tsaye wajen da suka aiwatar da laifin ya nufa.
"Tsugunawa yayi a wajen sanda yayi tozali da bushesshen jinin dake malale kan ciyawar, take ya ringa tuno komai, komai ya shiga dawo masa, ji yayi ya kasa jure tsayuwar da yake tuni ya tsuguna a wajen zuciyarda na masa wani irin raɗaɗi tamkar zata fito waje, tunda yake a rayuwarsa bai taɓa nadama irin ta yau ba, bai taɓa danasanin shan giya ba sai yau, bai taɓa jin ya tsana kansa irin ta yau ba, yana wajen suka rabata da mutuncin ta and he didn't do anything to pretect her against them, infact shi ya fara riƙota ma ya damƙamasu ita..... Wani ƙara ya sake gamida kama gashin kansa kamar zai cizge, yasan bazai taɓa yafewa kansa ba, yanzu ina take ina zai ganta. Take matar ɗazu ta faɗo masa, miƙewa yayi cikin sauri, jin ya taka wani abu yasa sa tsayuwa, tsugunawa yayi ya ɗauka abin yana bi da kallo, ɗan hankacif ne data saƙawa Umar me flawowi a jiki, ..
"Jalal yabi Hankacif ɗin da kallo, a hankali ya manna hankacif ɗin a fuskarsa zuciyar sa naci gaba da zogi. Kaman wanda aka zabura ya soma tafiya....
"Likita ya dubi Ammi a karo na biyu kafin yace" Baiwar Allah magana ta gaskiya sede fah kiyi haƙuri don babu yanda za'ayi mu karɓi wann case ɗin ba tareda hukuma ba, kinsan yanzu laifin fyaɗe ya zama ruwan dare snn an saka tsattsauran mataki akan irin wnn case ɗin, a gaskiya kije kizo da hukuma don kinga dole a saka a cikin file na asibiti kuma gwamnati ta gani ni za'a kama tunda nine da duty.
"Ammi ta yarfe zufan da ya keto mata kafin tace" Haba likita taimako fa zakayi snn ka duba fah ka gani yarinyar nan tamkar bata numfashi don Allah ka taimaka idan yaso kar kasa case ɗinta cikin report ɗinku na yau har sai an san su waye masu laifin. Ka taimaka likita ka tuna idan ƙanwarka ce ko ɗiyarka a wan condition ɗin yaya zaka ji, nasan kai musulmi ne don Allah ka taimaka kar mu bari rayuwarta ta salwanta haka nan tunda su waɗan da sukayi laifin abinda suke so kenan, kaga hakan na nufin kaima ka goyi bayan ɓarna.
"Jikin Dr yayi sanyi da jin kalaman Ammi, fuzar da iska yayi kafin yace" Shikenan Hajiya zan taimaka mata, Godiya Ammi ta soma masa tana hamdala, tuni Dr yasa Nurses su shigo da Zubaidah ɗakin tiyata,
"Saida ya girgiza da ganin irin cin zarafin da akayiwa Zubaidah, tabbas wann ba don kwananta na gaba ba data tuni ta mace, Allah shi kaɗai yasan dalilinsa na barin yarinyar nan a raye, idan aka ce masa maza goma ne sukayi amfani da ita bazai musa ba, don kuwa sun mata kaca kaca, ta yanda ko dabba bazaiyi irin haka ba. A ƙalla ya samu ciwo a privaye part ɗinta sama da bakwai snn jini ya zuba sosao a jikinta. Tuni ya soma gudanar da aikinsa da taimakon nurses ɗinsa.
" Gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake,shi yama rasa wanne zaiyi sashen da yake tunani nan aka sauƙi Amminsa ya nufa, yana isa ya tarar bata nan ɗaki ya shige ya kulle kansa cike da naɗamar rayuwa.
"Hadiza sai wage baki take taji kuɗaɗen da ko a mafarki bata taɓa jin labarin irinsu ba, ta kuma duban Alhj Kasim dake hankince saman kujera kafin tace" Alhj barinyi sauri na ƙarasa asibitin kafin matar nan ta kira ƴansanda.
"Alhj Kasim yayi murmushin cin nasara kafin ya jawo drwer ɗin dake gefensa ya ciro bandir ɗin ƴan ɗari biƴar ya miƙawa Hadiza yace, ki fars taɓa wann, hannu na rawa Hadiza ta amshe kuɗin ta shiga sunsunawa tana wani lumshe idanu, a sittin ta miƙe ta nufi waje tana yashe baki kaman gonar audiga....
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:11] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
12
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*In Dedication to All Victims Of Rape. Never Keep Silence, Fight for Your Right. This is Not Something To Be Ashamed Of Your Self, Let the Guilty Ones Feel Ashamed Of Them Selves..... 🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾*
_Wannan Shafin naku ne Barr Asmie n Zainab ina ƙaunarku yanda kuke ƙaunata da labarai na, Allah shi bar ƙauna #1Luv...😘😍_
"Alhj Jamil ya rapka uban tagumi yana kallon yayan nasa, ɗan gyaran murya yayi kafin ya soma faɗin" Yaya kana ganin abinda muka yi munyi daidai, anya Yaya bazamu miƙa yaran nan ga hukuma ba......" Bai kai aya ba Alhj Kasim ya katse sa,...
"Jamilu kai har sai yaushe zaka soma tunanin irin ƴan adam, akan wata yarinya ɗiyar talakawa kake magana muyi risking rayuwar yaranmu, ka faɗa mun idan muddin muka bari maganar nan ta fito media shikenan sunan mi ya ɓaci, reputation ɗinmu ya ɓaci snn wa kake so ya gaje mu idan mu muka miƙa tilon yaran mu ga hukuma snn kana tunani Alhj Tahir zai yarda ya aurawa Salim ƴarsa Kausar ne, kai ƙarewa ma duk abokan hulɗanmu na kasuwanci sai sun guje mu, our company will go bankrupt (Kampaninmu zata samu kariyan tattalin arziki) dan haka bana sonjin wani magana daga gareka.
"Shiru Alhj Jamil kawai yayi yana duban ɗan uwan nasa wanda bashida abinda yafi masa kuɗi a rayuwarsa da kuma tilon ɗansa Salim.
"Barr Munir yayi wata murmushi kafin yace" S gaskiya Mr President shawarinka yayi daidai yanzu sai musan yanda za'ayi da wann yaro Jalal don nasan definitely yaron ka iya kawo mana cikas tunda dai mun gama da iyaƴen yarinyar. (Alhj Kasim Dasuki shine President na *Dasuki Holdings Of Company*)
"Alhj Kasim ya murmusa kafin yace ku bar min wann ni nadan yanda zanyi, Ya juyo ya dubi Mami da Momy da sukayi jugum suna kallonsu kafon yace" Farha kusan yanda za'ayi Kausar da Hajiya Raliya su rigamu isa Abuja...." Momy ta sauƙe ajiyar zuciya kafin tace " Dama Haj Raliya ta faɗa mun washi garin sakun rana zasu koma gaba ɗaya harda Alhj Tahir kasan very busy mutum ne, yau idan yayi sadaka a ƙofar gidansa gobe zasu wuce.
"Daddy ya jinjina kai amma har cikin ransa mamaki yake ya akayi Alhj Tahir bai sanar ɗashi ba, shashantar da zancen yayi dan yanzu babban ƙalubalen dake gabansa shine ya kuɓutar da ysransa. Jinjina kai yayi kafin ya dubi momy yace " Whete are the boys?? " Momy ta amsa masa da suna sama, kai tsaye stirs ya nufa Barr Munir na taka masa baya, Dad ɗin Labib kuwa ficewa waje yayi yana amsa call....
"Suna zazzaune kowa da abinda yake saƙawa Daddy ya turo ƙofa suka shigo hida Barr Munir, Kallo ɗaya Labib ya masu ya watsar yaci gaba da ɗunduma gefen fuskarsa yanda Jalal ya ji mai ciwo.
"Kallonsu One by one yayi kafin yace" Gobe gobe zaku bi jirgin safe ku wuce Abuja, babu wanda ya amsa sa duk cikinsu, ya dubi Tariq da har lokacin hancinsa bai daina zuban jini ba yace" Na kira Dad ɗinka nayi briefing nasa komai a waya don ya riga ya wuce Abuja yau da safen nan, kundai jini kar ku bari kuyi missing flight ɗin safiya, daga haka suka sa kai zasu fice Salim ya katse su da faɗin " Daddy what about Jalal,....." Bai gama rufe baki ba Barr Munir ya katse sa da faɗin " Kaci gidanku Salim, na maganar kuɓutar da rayuwarku kana maganan wani Jalal...." Baki Sal ya turo gaba like a spoiled kid kafin yace" But Uncle we cant leave without him, hes onr of us..... " Wata ashar Daddy ya watsa masa kafin yaci gaba da faɗin" Idan Jalal ɗin ƙanin ubanka ne sai ka jirasa ka tafi dashi, snn ku buɗe kunnuwanku da kyau kujini, babu ku babu Jalal, inace don kunga kuna rayuwa gida ɗaya ne dashi shiyasa kuke ganin kaman ku dashi ate equal ko, toh wllhi kukayi wasa koransu zanyi daga gidana daga shi har uwsrsa...Barr munir yayi saurin cews shikenn kuwa Mr Ptesident kaga kowa ya huta...
" Labib ya miƙe yana watsa masu mugun kallo mussaman Barr Munir don ya tsane sa ba kaɗan ba, don yana ganin shi yake saka Uncle ɗinsa yin wasu abubuwan snn yaga alama ƙoƙarin raba uncle ɗinsa da ɗinsa yake. cikin dakakkiyar murya yake faɗin " Uncle Idan ka kori su Jalal a gidanka zasu dawo gidanmu. So ba matsala bane....." Cike da mamaki Daddy ke kallonsu, anya Jalal bai asirce masu yara ba, bai kuma cewa komai ba sai karya babban gyaransa da yayi ya fice fuuuu Brr ma yabi bayansa da saurin gaske...
" Kasa zama yayi a ɗakin sabida ƙuna da ƙirjinsa ke masa, tausayin yarinyar ya saka gaba, ko runtse ido yayi sai ya tuno sanda suke rabata da mutuncinta, quiet alright ba sonta yake ba but tausayinta ya hanasa sukuni, jinta yake tamkar ƙanwarsa ji yake da ma ƙanwarsa akayi haka tabbas da sai yanda ƙarfinsa ya ƙare, mussaman kasancewarsa shi kaɗai wajarn mahaifiyarsa, tafiya yake baima san yanda zaije ba, shi dai yasan yana bin titi, hankacif ɗinta da ya tsinta kuwa yana nan damƙe hannunsa kaman mai tsoron kar wani ya wupce, duka lungun da Jalal yabi sai kaji ana yaba kyaun halittarsa babu mata babu maza, kar kuji nace haka, Jalal mutum ne wanda Allah yayi masa halittan kyau wanda harta ƴan uwansa maza suna yaba kyaun halittar sa.
"Ammi tana ganin fitowsr likita daga ɗakin tiyata yana share zifa tayi saurin miƙewa ta nufesa tana tambayarsa,
"Ɗan goge zufar goshinsa yayi kafin yace" Hajiya a gaskiya bazan ɓoye maki ba yarinyar nan ta sami mummunar rauni, sauƙin abin guda shine bata kamu da yoyon fitsari ba, amma tana tsananin buƙatar jini, yanzu abinda nake so dake kije ki nemo wani ɗan uwanta ko kuma kuɗin da za'a nemi jini a ƙara mata ....
" Ammi ta sauƙe ajiyan zuciya kafin tace" Toh likita ko za'a auna nawa. Ɗan jimm yayi kafin yace toh bbabu matsala idan kince haka, amma koda mun auna naki yayi daidai sai kinada wadataccen jinin da zaki iya ba wa wani kafin mu ɗiba, Ammi tace ta amkce, nan aka shiga ɗakin aunin jini da ita, unfortunately jinin Ammi baiyi matching na Zubaidah.
"Tagumi Ammi tayi tana tunanin ina Hadiza ta tafi, gashi batasan gidanta ba, bata san ina zata sameta ba, wata zuciya tace ki fita ki neme ta tunda ƴar uwarta ce ƙila a sami wanda jininsu zaizo daidai. Haka Ammi ta fice tana tunanin me ya hana Hadiza dawowa.
"Chan tsalleken titi ta hangesa sai faman tafiya yake, shaff ta mance da Jalal ma gaba ɗaya, hankalinta ya kaikaita wajen ceto rayuwar Zubaidah. Da sauri ta nufesa cike da mamKi take tambayarsa ina zaije haka.
"Ɗan shafa kai Jalal yayi kafin yace" Kawai dai ina kallon yanayin garin ne...... Zuciyar Ammi ya buga tayi saurin riƙo hannunsa suka tsallaka titi, Jalal dai sai kallonta yake gaba ɗaya da ganin Ammin tasa tana cikin damuwa....... Murya na rawa Ammi take faɗin Jalal babu dai wanda ya ganka ko, Jalal ka faɗa mun....."Da mamaki yake kallonta kafin yace" Ammi are you alright, meke faruwa, waima me kike yi a nan a daidai wnn lokaci.
"Sauƙeajiyan zuciya tayi kafin tace ba komai Jalal mije cikin asibitin sai na faɗa maka abinda ya fari,
"Asibiti kuma??? Ya maimaita a zuciyarsa, haka yabi Ammi kaman raƙumi da akala har suka shige cikin asibitin zuciyarsa na ci gaba da bugawa da sauri ɗa sauri.
"Cak ya tsaya yana kallonta sanda Ammi ta buɗe kofar ɗakin da take, itace dai ba gizo take masa ba, fuskanta na fiskantar sama, idanunta a lumshe tamkar mai bacci gashin kanta ya rufe pillow ɗin da aka mata mayashi dashi, hancinta pointed yana kallon sama ɗan lips ɗinta kaman wacce ta shafa jan baki, ga bandage ta ko ina duk yanda taji ciwo an rurrufe. Take yaji jiri na neman ɗibarsa, Ammi sai faman masa bayanin yanda ta sameta da abunda aka mata take Jalal kam ko saurarenta bai yi, abu guda da yaji shine shigowar likita da tambayar jinin da yayi.
"Juyowa yayi ya dubi Dr ɗin kafin yace" Dr ka yake my blood..... Kallonsa sukayi daga Dr ɗin har Ammi, Dr ya ɗanyi jim kafin yace " Amma sai mun auna munga ko........" Bai kai aya ba Jalal da tuni jijiyoyinsa sun tashi cikin ysananin ɗaga murya yace" *I said take mine,*
"Jiki na ɓari Dr Garkuwa yace Okay muje muje, Ammi kuwa kallo tabisu dashi har suka fice.
"Cikin sa'a jinin Jalal yayi daidai wa Zubaidah nan da nan aka ɗibi har leda biyu aka saka mata.
"Ammi ta shigo ɗakin da Jalal yake yanda aka ɗibi jininsa yana ƙoƙarin maida rigarsa, nan ta hangi tabon dake a bayan kafaɗansa wanda da gani ba sai ance maka shaida bace, ƙirjinta ya buga da ƙarfi, anya duk ranan da Jalal yasan ba ita ta haifesa ba anya bazai tsaneta ba, Juyiwan da zaiyi suka haɗa ido, murmushin ƙarfin hali ta sakar masa kafin tace "Son sannu da aikin alkhairi Allah ya biyaka.
"Ɗan mirmushi yayi ba yareda yace komai ba, su duka biyu kana ganinsu kasan akwai abinda ke damunsu,....
"Iyalle ta dubi Hadiza baki sake kafin tace" Ashe ke shasha ce, yanzu ɗan wann kuɗin har ya isa ya rufe bakinki, ai baki sani ba hanyar arziki ne Allah ya kawo maki a sauwaƙe, yanzu abinda za'ayi tashi zakiyi kije ki sami wann saunan mijin naki kita shera kuka ki faɗa masa abinda akayi wa ƙanwarsa daga nan ki ɗaukesa kuje asibitin ki koma can gidan kiyita masu bore da hauka, kinsan masu kuɗin nan basu fatan abinda zai ɓata masu suna, Snn kinsan anƴi baikon Zubaidah ce masu zakiƴi a al'adan garin nan duk macen da aka sameta ba budurwa ba tofah maido da sadakinta ake snn sunanta da na iyayenta ya ɓaci snn har ta mutu babu me aurenta, ce masu zakiyi saidai su aurawa yaransu ita, nasan bazasu yarda ba kinga dole su ksra maki kudi mai tsoka snn kice dede ku bisu Habuja don a nan tsangwamanku mutane zasuyi. Kinga idan kiks tafi Habuja kya min hanya nima na tafi, kinga muafah shikenn zamu fara neman kuɗi da gaske a can har muzo mu gine gida kalan nasu....... Hadiza tayi shewa ta miƙa wa Iyalle hannu suka tafe kafin tacr" Ƙawata shiyasa nake sonki yanzu bari kiga da zafi zafi ake dukan ƙarfe. Yawwa ƙawata cewsr Iyalle maza lalumo nawa kasoɓ ki bani ke ai tanzu kin zama hajiya.
"Hadiza ta zaro kuɗi ta danƙawa Iyalle kafin ta fice.
"Yanda Iyalle ta tsara mata kuwa hakan akayi, Hamma Habibu yasha kuka shaɓe shaɓe harda majina, tabbas yasan iyayensa bazasu taɓa yafe masa ba ya kasa riƙe masu amanar tilon ƙanwarsa, Hadiza harda hawayen munafunci take basa baki, kayi haƙuri Habibu ina nan tare da kai snn duk wanda yayi wann abu wa Zubaidah bazmu taɓa barinsa ba ko ɗan uban waye, sai an bi mana kadinmu, maza shirya muje asibitin, babu musu ya shirya suka nufi asibiti.
""Labib ne ya soma ƙarasowa yanda Jalal ke zaune kafin su Salim.suka karaso, murya kalan na masu nadama suka soma magana dashi, ko kallo basu ishesa ba ƙarshe ma tashi yayi ya bar masu wajen, ya ɗau aƙwashin ko yau ya koma Abuja bazai ci gaba da zama da Dasuki family ba, ya koyi darussa a rayuwa snn zai tashi ya nemi abun kansa duk wuya duk rintsi.
**************************
*Gombe Fada*
Wata matashiyar mata ce zaune saman Kujeru na alfarma, a shekare bazata gaza shekaru 40 ba, tana sanye cikin kaya na alfarma, fuskan nan nata ko kaɗan babu annuri, ido ta kafe hoton jariri dake manne a tangamemen parlron dashi, wani katutun baƙin cini ya kuma tokare mata maƙoshi, Idan akwai abinda tafi tsana a rayuwarta toh wann tangamemwn hoton ne wanda yake kaman ruhin mijinta Mai marta sarkin Gombe MODIBBO ALIYU MU'ALLAYIƊI.
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:11] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
13
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
"Gimbiya Zahida ce ta shigo parlorn cikin shiga shiga ta alfarma Alkebba fara ƙal sai ɗauke ido yake, daka ganta basai ance maka ga jinin sarauta ba, gefe da mahaifiyarta ta zauna fuskarta ɗauke da murmurshi kana tace" Barka da Hantsi Ummi na, da fatan kin tashi lafiya.
"Murmushi matar data kira da Ummi tayi kafin ta shafi gefen fuskar Zahida tace " Barka ɗiyar saraki jikar saraki da fatan kin wayi gari lafiya.
"Murmushi bai bayyana haƙwara Zahida tayi kafin ta riƙo hannun Ummi tace " Ummi kina sani naji kamar watarana zanyi sarauta idan kina koɗa ni haka.
"Ummi ta jawo Zahida cikin jikinta ta rungume kafin tace" Mai Martaba baida wani ɗa ko jika a doron ƙasa face ke, baida gudan jininsa a duniyan nan face ke ƴar lele na, meyasa kike tunani wataran bazaki mulki garin nan ba.
"Rausayar daidanu Zahida tayi kafin tace" Ummi a ina kika taɓa jin mace tayi sarauta a ƙasar nan, burina dai kawai shine na auri saraki nima don gaskiya idan ba jinin sarauta ba bazan yi aure ba.
" Ummi tayi wani dariya mai cike da ma'anoni idanunta suka sauƙa kan tangamemen hoton jaririn dake manne a tampatsetsen parlor kafin tace" Maza tashi muje mu gaida kakarki kafin ta fara mita.
"Babu musu Zahida ta miƙe Ummi na riƙe da hannunta bayi guda biyu ne ciki harda Jakadiya suka take masu baya snn suka nufi sashen "Madaki wato mahaifiyar mai Martaba.......
"Tunda ta buɗe ido tayi ido huɗu da lkitan ta ringa mimmiƙewa tana wani irin ƙara haɗi da ƙanƙame jikinta dukda azaban ciwon da takeji, babu yanda likita baiyi ba ya dubata amma abu yaci tura, kai duk wani mutum idan ya shigo muddin na mijini ne to ta rinƙa figita kenan tana wanu irin kuka mai wani irin sauti tana ƙanƙanme jikinta.....
"Daga can nesa ya tsaya yana kallonta sanda aka kira nurses sukai mata alluran bacci, wani irin tausayinta ne ya cika zuciyarsa, take yaji bazai iya kallon wann hali na ƙunci da wahala da take ciki ba, kaman wanda kwai ya fashe ma a ciki haka ya fito reception.
"Zama yayi a reception yana kallon Hamma Habibu dake ta faman share hawayen da ya wanke fuskarda gaba ɗaya, Jalal ya kuma jin tausayin waɗan nan bayin Allah sanda yaga Hamma Habibu ya kama wuyar rigarsa yana sharan majina dashi a hankali ya ƙarasa ga Hamma Habibu gamida da dafe kafaɗansa Habibu ya ɗago rinannun idanunsa da suka jiƙe da hawayr yana kallon Jalal kana ya soma faɗin"
"Bata da kowa sai ni, iyayenmu sun rasu sun bar min amanarta, gashi na kasa cika masu burinsu, na kasa riƙe amanar tilon ƙanwata, idan ta mutu bazan taɓa yafr ws kaina ba.... Kuka mai ƙarfi ya kufce masa sanda yake dukan kansa da duka hannayensa biyu yana faɗin" Bani da amfani, gaskiyar Hadiza ne banida amfani, banida amfanin komai.... Kalmar da ya ringa nanataw knn yana dukan kansa da ƙarfin gaske.
"Jalal da tuni hawaye sun ciko idanunsa, tausayin Zubaidah da Hamman ta ya cika zuciyar sa, Allaj sarki ashe marainiya ce babu uwa babu uba babu dangi sai Hamman ta wanda yake irin mitanen nanne masu maysalar ƙwaƙwalwa. Abu mai kaman wuya ne ke sa Jalal kuks, zai iya cewa tun yana yaro kai koda yakr yarinta duk tsananin abu bai yin kuka amma wann karan sai ji yayi ya kasa controlling kansa, tuni idanunsa sunyi jazur haka nan farin fatar sa ta koma ja, tsanar aminan sa ne ya cika zuciyar sa haɗi da tausayin Zubaidah da rayuwar da zata fuskanta...
"Annah ce ta bawa Jalal kuɗi ya sayo allura don babu wanda ake buƙata za'a mata a asibitin, cikin sauri ya amsa ya nufi waje, Annah ta karaso ga Hammah Habibu tana basa baki cike da tausayawa.
"A daidai ƙofa ya haɗu dasu, sun ɓadda kama basu ɗauko luxurious cars ɗinsu ba, Daddy ne sai Barr Munir... "Cikin sauri Jalal yayi niyyan wucewa Barr Munir yayi alama wa Gurd ɗinsu guda ɗaya da hannu, kan kace me an janye Jalal zuwa cikin wata mota mai baƙar glass.
"Fuzgewa Jalal ya shiga yu da iya ƙarfinsa daidai lokacin da Barr Munir da Daddy suka shigo, banda harara babu abinda Jalal ke masu, a hasale yake faɗin" Me kuke yi a nan marassa imani.
"Daddy yayi wata murmushi kafin yace" Relax boy, dont di anything foolish, magana ɗaya zuwa biyu zamuyi da kai, if you cooperate fine ka tsira, idan kuma ka ƙi..... Wata murmushi yayi jafin ya kalli Barrister.
"Barrister yayi gyaran murya kafin yace" Jalal, shin kana da shaida cewa su Salim su suka raping yarinyar nan, shin idan kana tunanin idan kayi gigin sbigar da ƙara kai zaka tsira ne, bazaka tsira ba , tunda dukanku kuna wajen sanda incidence ɗin ya faru, tabbas yarinyar ta ganku gaba ɗaya, babu mai cire ka cikin wnn mess ɗin, she'll admit dukanku ne kukayi raping nata, snn boy ina gani daga idanunka you are madly in love with her....."Da mamki kurum Jalal ke kallonsa.
"Barr yayi wata murmushi kafin yaxi gaba da zayanno kalamai masu ɓadda tunanin mutum irin nasu na lawyoyi " Ka sake tunani da kyau yaro, idan kayi confessing laifinku zaka tafi prison for the rest of your life don bakada mai tsaya maka, kar ka mance ƙasar nan idan kana da kuɗi babu mai ja da kai, su salim will be free kai ɗaya za'a bar cikin wann mess ɗin don kaine talaka, and poor mum ɗinka da bata da kowa saiki, ƙunci zai kasheta, snn wann yarinya bazaka taɓa kasancewa da ita ba, wataƙila itama depression ya kasheta, kaga ashe tainakon da kayi niyyan yi baiyi rana ba.
"Jalal ya zuciye tamkar zai jai mai naushi yake faɗin" Stop involving me a cikin mess ɗinsu, ban aikata ba n no one will force me to confrss something I never did, not even you Alhj Kasim.
"Murmushi sukayi su duka biyi, kafin Barr yace" I like your courage boy, amma dai ka duba maganar da nayi maka, and abu na karshe idan kana so kayi saving life ɗin yarinya ka aureta....
"Mun riga mun gama magana da likita gibe za'ayi discharging nata kai tsaye kuma Abuja zamu wuce gaba ɗaya including her and her family. So dabara ya rage naka Jalal, ka sani kai za'a bari a rana don mun sami amincewar uwar goyonta da likitan ta, kaga baka da shaida... Daga haka suka buɗe masa marfin mota ya fice jikin sa a sanyaƴe.
"Wai shin haka duniya ta koma, wai shin shi talaka bashida ikon gudanar da rayuwarsa yanda yake so, shin mutane haka suka zama, abin duniya ya gama rufe idanun kowa, kaico irin wann rayuewa da muke cikinta a yau.....
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:11] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
14
*©Sameena Aleeyou....✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
" Jiki a sanyaye ya tare mai mashin yana tambayarsa ina zai sami chemist mafi kusa don ba sanin garin yayi ba, basu wani tafiya mai nisa ba suka samu, nan ya sai alluran ya koma asibiti.
"To his greatest surprise wulgawan motar compnayn *Dasuki Hodlings* ya gani, kuma tabbas ɗazu cikin ta su Daddy suka zo. Toh me ya dawo dasu tambayar da yayi ma kansa kenn, sann babu mai basa amsar wann tambayar nasa yasa ya nufi asibitin kai tsaye.
"Shaye da mamaki Jalal ke kallon su Mommy da Mami, Annah ce ta hango shi tsaye ya kafe su da idanu,
"Jalal ƙaraso mana , Allah dai yasa an sami alluran, Annah ta faɗi daidau lokacin da gaba ɗaya suka maida kallonsu ƙofa, Mami Momy da kuma Yaya Hadiza.
"Momy ce ta miƙe gamida karɓan alluran hannun Jalal wanda ya koma tamkar gunki bai gama shan mamakin ɗan adam ba saida yaji momy na faɗin" Jalal abokan ka sun wuce sun barka har ina masu faɗan ina suka bari ka, ashe kai kam taimako ka tsaya... Da mugun mamaki kurum yaje binta da kallo sanda taci gaba da faɗin "
" Allah sarki Jalal yaron arziki, Allah dai ya biyaka kaida mahaifiyarka, irin wann raimako da kukayi ai mu ya kamata mu ringa yin irinsa, ta maida duvanta ga Annah daketa faman murmushi kafin tace" Habs Annah ai irin haka da wuri ake faɗi sai mubada kalan namu gudumawar, ƴanmatan da kaddara da tsautsayi na fyaɗe a auka masu haƙiƙa suna buƙatar taimako da kulawa don haka ne ma Alhj ya yanke shawarin taimaka masu itada familynta, gobe insha Allah zamu tafi Abuja baki ɗaya don hakan ne kurum zai mantar da ita wann mummunar ƙaddara da sameta, zamanta a nan zai ringa tuna mata abin, snn cannin wajen zama zai mantar da ita komai.
"Mami dai kallon Mommy kawai tayi tana mamakin yanda halin momy da Daddyn Salim yazo daidai, banda lugude da ƙirjinta keyi bata komai sau kallo, dan kuwa saida mijinta ya mata kashedi babu ruwanta a wann zalunci, toh ya zata yu tuɓda ɗanta na ciki, data rasa tilon ɗanta gwara ta biye masu kida hakan ka iya kawo matsala ga aurenta.
"Annah da yaya Hadiza godiya suka shiga, yaya Hadiza harda share hawayen munafunci tuni ta kaɗo kan Hamma Habibu yazo yayi godiya, bai kawo komai a ransa ba ya ringa masu godiya...
"Takaici da tausayi ya hanasa ci gaba da tsayƴwa a wajen, tuni ya fice zuwa farfajiayan asibitin.... Ƙasar wata bishiya a samu ya zauna gamida haɗe kansa da gwiwarsa, maganganun Alhj Kasim da Barr suka shiga dawo masa,
"Kalaman da yafi nanatawa shine *"You are in love with her, Ka aureta shine maka mafita...*
"Girgiza kai ya soma tamkar zararre, ko ɗaya ko kaɗan baijin abinda yake ji game da ita So ne ,shi bai taɓa yin soyayya ba balle yasan yaya take, abunda ya sani shine yana jinta tamkar ƙanwarsa snn yana tsananin tausayinta, snn ya ɗau alwashin tamaika mata har iya rayuwarsa.... A gigice ya miƙe ya nufi cikin asibitin sanda yajiyo wani irin karan da ta saki.....
" Mami dai jigum tayi a mota har suka isa gida, tana shiga parlon su ta tarar da Daddyn Labib zaune yana karanta jarida da alama isowarta yake jira.
"Kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki ta nufesa tanai masa sannu da gida, ko kallo bata ishe sa ba baƙƙe ya tanka ta. Sanin bazai mata magana ba yasata nufi sama.
"Daidai step na biyu taji ya kira sunanta, cak ta tsaya ba tare da ta jiyo ba.
"Saboda kin raina ni shine saida kika biƴewa Yaya da matar sa kuka je ha'intar waɗan nan bayin Allahn ko, kina cikin hankalinki kuwa Salma, na saka maki doka ki take......."Kamar me shirin kuka ta soma faɗin" Haba haba Jamil, me kake tunani, na bari inaji ina gani tilon ɗan nawa ya tafi gidan yari, bazan iya rasa sa ba idan kai baka damu dashi ba...."Mikewa yayi gamida ajjiye jaridar dake hannunsa kafin yace " Shi ya janyo ma kansa, shi ya saka kansa a ciki don haka babu hanuna a kare shi, kuma a yau na isa Abuja zan miƙa sa ma hukuma....."Ihun da Mami ta saki ne ya kaɗo hankulan sauran mutanen dake gida, kuka take kan rusawa tana fadin " Ita babu mai kai mata ɗata kurkuku....
"Alhj Kasim da Hajiya Farha a tare suja shigo, Mami ta karasa gabansu tana kuka take roƙon Daddy, Yaya dan Allh ka masa magana cewa yayi zai miƙa Labib ga hukuma, Yaya ka taimaka min ka hana sa....."Momy ta riƙo Mami tana lallashinta suka nufi upstirs....
"Wani mugun kallo Alhj Kasim ke waysa wa ƙanin nasa kafin yace" Jamilu wato baka daina maganar nan ba koh, bari kaji na faɗa maka dukda cewa kai ka haifi Labib baka isa ka min iko akansa ba, bari kaji na sake faɗa maka in case u forgotten "Wllhi wllhi babu mahaluƙin da ya isa ya shigar da ɗana prison muddin Naira na aiki a kasar nan, Jamil ga fili ga doki idan kayi shirin yin faɗa dani yayan ka. Kayi abunda kaga dama tunda yanzu har ni nake faɗa kake faɗa.... "Daga haka yasa kai ya fice fuuuu...
"Kallo Alhj Jamil yabi ɗan uwan nasa dashi, jikinsa yayi sanyi tabbas bazai so yaga rugujewar family ɗinsu ba hankali ya sulale gamida zama bisa sofa haɗi da zare faran tabarau na ƙarin ƙarfin gani dake idanunsa.....
*Washe gari*
"Tunda aka sallame ta bara ɗago ido ta kalli kowa ba, snn bata san duniyar take ko akasin haka ba, iyakacin abinda take tunawa shine dariyar su da shewan su sanda zasu rabata da mutuncin ta, haka nan idan ta buɗe idanun ta fuskokinsu take gani, motsi kaɗan idan tayi takan ji zafi zogo haɗi raɗaɗi daga ƙasanta, hakiƙa a galin yanzu tafu shiga sahun marassa ganjali, don kuwa tabbas bata san yanda hankalin nata yake ba, iyaka abinda ta sani shine duk na mijin da yazo kusa da ita takan fita hayyacinta takan koma tamkar mai ciwin hauka....
*Abuja*
"Batasan a ina take ba, itadai buɗe ido tayi ta ganta a wani gida na daban, mafarki take waɗann samaruka sun nufota da wuƙa tana ihu tana gudu, gabanta kuma Umar ne ya buɗe hannu alamun ta ƙaraso garesa, fuskarsa kaman ba nasa ba ashe shima wuƙar ne a hannu sa.. Da tsoro ta isa gareshi yana ƙoƙarin burma mata wuƙar knn ɗaya daga cikin samarukan nan ya ture Umar ya rungumeta.........
"A gigice ta saki wani irin ƙara gamida taƙurewa waje guda, .. Hadiza ce ta shigo gamida jan dogon tsaki jin Zubaidah na kiran sunan Umar,......Yaya na kazo ka ceceni kashe ni zasuyi,
"Ruwa cikin kopi Hadiza ta ɗebo gamida sheƙa mata..... Babu shiri ta buɗe ido firgit, ta yunƙura zata tashi taɓi zafi, hannunta dake ɗaure da bendeji yanda ta gurɗe taji ya shiga mata zogi alamun ta fama, a gigice ta fito daga ɗakin tana kallon yanagin yanda take, wani ƙara ta saki gamida durƙusawa waje...
"Labib dake tsaye ta windown ɗakinsa yake hangota, wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Salim.....
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:12] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
15
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
"Hello guy kana ina ne? Daga ɗaya ɓangaren Salim ya amsa
"Gidan su Kausar, what akwai wani abu ne.
"Okay mu haɗu a company things are getting outta control...
"Dont get u buddy, wau meke faruwa ne.
"Gajeren tsaki Labib yayu kafin yace" Salim its about that girl....
"You mean the Cow girl.
"Dama wacce yarinya nake maka magana aside from her, ka gane Uncle cant tackle this issue alone, we need to talk kafin abubuwa su caɓe wann matan yayan nata zata zame mana sabon matsala, nu banma san meyasa Uncle ya kwaso su ya taho dasu ba,..... "
"Miƙewa Salim yayi kana yace "Okay fine ka kira Taruq kace masa mu haɗu a company.. Daga haka yayi hanging.
"Fuzar da iska yayi gamida furta "Dmn dammit..!!!!
'Daidai nan Kausar ta ƙaraso riƙe ƙaramar tray a hannun ta... Da mamaki take binsa da kallo ganin ya miƙe ya ɗauki car keys ɗinsa.
"Ajiye tray ɗin tayi saman tabƙe kafin ta bisa da kallo.
"Ɗan murmushi yayi kafin yace" Sweetheart I'm so sorry but I really need to go.
"Ɓata fuska sosai Kausar tayi kafin tace" I dont get u, you mean you leaving right now, haba Salim wai meke damunka ne, this days you acting very strange, tun jiya fah ka dawo bakazo ka ganni ba as your fiancee na ɗauka ma da zaran ka iso zaka zo ka ganni, ko waya mukayi da kai bana gane kanka kwana biyun nan, tell ne pls is something bordering you???
"Ƙaƙaro murmushi yayi gamida ƙarasowa daf da ita hannayenta ya riƙe kafin yace" Sweetheart don't let those ideas to ur head pls. Babu abinda ke faruwa sai zallan soyayyar ki, Daddy ne ya kirani and its urgent, you know how business men are, always busy,
"Hannunsa Kausar ta kalla bataga zobensa ba, ɗago ido ta kuma yi tana masa kallon tuhuma kafun tace "And where is your ring.
"Ƙirjinsa yabada rasss, cikin sauri ya saita kansa kafin yace " Em na cire shi lukacin da zanyi wanka but ina zuwa guda zan saka.
"Cikin rashin gamsuwa da excuse ɗinsa tace " But that ring is a promise bazaka taɓa cire shi ko yaya,
"Ɗan fuzar da iska yayi sanda wayarsa ta soma ƙara, da sauri ya saka a silent kafin ya kalleta yace " For Allah's sake Kausar its just a ring, besides mu a nan ƙasar ba auren zobe muke ba, its obvious kin saba ɗabi'un turawan yamma, but its diff here kin gane, whats important is that I love you with all of my heart and I mean it, Ɗan kallan agogon hannunsa yayi kafin yace" Daddy is waiting for me, I'll give you a call, luv u take care daga haka ya fice sai sauri yake kaman zai kifa...
"Kallo ta bisa dashi har ya fice......
"Cikin gida Kausar ta wuce jiki a sanyaye, haka kurum take ji wani abu na shirin faruwa tsakaninta da Salim.
"Ƙura ma Yaya Hadiza ido tayi tana binta da kallon mamaki, she couldn't believe what shes hearing, hawayae na bin ƙuncinta ta sa bayan hannunta maras ciwon ta ɗan goge kafin ta soma faɗin"
"Meyasa, meyasa kika ɗauko ni daga mahaifata kika kawo nan wajen, meyasa baki bari na mutu ba, meyasa baki bari an bisneni gefen iyaye na ba, meyasa kika rabo ni da garin masoyi na, shin kina tunanin zanci gaba da rayuwa ne, shin kina tunanin ni Zubaida har akwai sauran rayuwa a gaba na, babu ita. Mutuwa a wnn lokacin yafiye mun komai....
"Tsawan da Hadiza ta daka mata ya jawo hankalin su Momy da Annah gaba ɗaya suka nufo sashen da aka sauƙe su Zubaidah. Janta Hadiza ta shiga yi tana faɗin babu yanda zaki tafi a nan zaki tsaya a nan zaki ci gaba da rayuwa.......
"A zuciye Zubaidah ta fizge hannunta daga riƙon da Hadiza ta mata, babu alamun tsoro a tattare da ita take kallonta, cikin ɗaga murya take faɗin"
"Is this all you can do for me, iyakacin abunda zaki iya min kenn? Ki amimce ki biyo waɗanda suka lalata min rayuwa suka durƙusar da rayuwar yarinyar da bata ci masu ba bata sha ba, shin idan kece Zubaidah hakan ta faru dake shin yaya zakiji,..
"For years kina azabtar dani kina wulaƙanta Hamma na sabida lalura na rayuwa da yake dashi, daidai da rana guda ban taɓa saɓa maki ba, shin abinda zaki saka min dashi knn....
"Da mugun mamaki Hadiza ke kallon Zubaidah ta canza gaba ɗaya ta koma tamkar ba ita ba lokaci guda, Huci ta soma tana bƙrin kunya....
"Ɗaga mata hannu Zubaidah tayi kafin taci gaba da faɗin" Kin kula.dani tun ina yarinya Allah saka maki da alkhairi da abubuwan da kika min, Allah ya biyaki na sani nida Hamma na duk muna ƙarƙashin kulawarki ne, Allah ya biyaki. Amma ki sani mutuwata a yanzu tafiye mun komai..... Da ɗingishi ta juya ta koma cikin ɗakin gamida rufe ƙofar.....
"Bugun duniya Hadiza tayi Zubaidah taƙi buɗewa. "Taƙurewa tayi can ƙuryan ɗakin tana kuka mai tsuma rai.
"Momy jiki a sanyaye ta koma sashen ta yayinda Annah ke tsaye a wajen tamkar gunki, abu guda da Zubaidah ta faɗi yayi muguɓ ɗaga mata hankali, *Kika kawoni wajen waɗanda suka lalata min rayuw* kalmar da Annah tayita nanatawa kenn, abinda ya ƙulle mata kai ta kasa fahimta. Jiki a sanyaye ta wuce ɓangarensu tana tunanin lamarin......
"Daga yanda yake tsaye ya gama jin komai yaga komai a gabansa komai ya faru, Zuciyarsa taci gaba da zogi da raɗaɗi, shin haka zai tsaya yanaji yana gani rayuwarta ta ƙarasa lalacewa,..."A fili ya furta no, no no cikin sauri ya juya ya nufi gate ya fice......
"A ƙofar *Dasuki Holding* suka haɗu su duka uku. Salim ne ya soma fitowa daga motarsa kafin su Labib da Tariq suka fito dama tare suke Labib ya biya ya ɗauki Tariq, Securities ne suka ƙaraso suka karɓi keys ɗin motocinsu suka ƙarasa da motocin parking space snn su kuma suka shige cikin companƴ ɗin wanda yake ko ta ina glass ne tamkar a turai kake.
"Guys gaskiya nifa na fara nadamar abinda mukayi don wllhi my Dad is totally mad at me, cewar Tariq yayinda suke ƙoƙarin shigewa cikin lift, Salim ya ɗanyi gajeren tsaki kafin yace nima dai abin ya soma damuna don Kausar ta fara tunanin I'm hidding something from het. Tsaki Labib yayi sanda suka isa floor ɗin Daddy kafin ya juyo ya dubesu yace" Thats precisely why we are here, to talk with our parents, they shouldnt have brought that girl here in the first place. Gaba ɗaya suka kaɗa kansu suka ce haka ne.
"Duk yanda suka wuce gaushe su ake *The Dasuki's* ba yara masu ji da kansu da ƙarfin arzikin iyayensu......
"Sakatariyan Daddy ta ɗan dubesu cike da rusunawa tace " Am sorry but Mr president is at the middle of a meeting right now, you cant see him now....
"Dmmit!!!!! Labib ya faɗi da karfi gamida buga tabƙe ɗinta wanda yasata zabura.
"kwanto da kansa saitin fuskarta yayi fuska a tamke yake faɗin " If you dont want to get self fired then go in right a way, and tell him we wanna see him right now.
"Da sauri ta miƙe kafin tace Ok ok sir right a way sir,ta wuce ta nufi Conference hall .....
"Ana tsakiya da meeting sakayariyar sa ta kawo masa saƙon, fuzsr da iska yayi cikin ransa yace " Those boys wunt kill me, excusing kansa yayi kana yayi alama ma Lauyan sa Barr Munir kan cewa ya biyo bayansa, babu musu Barr ya miƙe yabi bayansa...
"Babban parlon dake cikin Office ɗin suka ƙarasa, shigarsu yayi daidai da banko ƙofar wanda hakan ya ja hankalinsu gaba ɗaya suka kalli ƙofan. Cikin wani irin yanayi suke dubansa.
"Barr yayi saurin faɗin " How dare you barge in here, ku talakawa really have no manners.
"Daddy ya girgiza kai kafin yaci it is not his fault, I have to make it clear to those stupids securities that this filthy jark isnt my son, he cant just come in here inti this very company.....
"Alhj Kasim we need to talk for the sake of these spoiled brats ya ƙarashe maganar yana nuna su Salim da tuni sun sha jinin jikinsu....
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:12] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
16
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum....📖📚_
"Kallon mamaki suka bisa dashi, Alhj Kasim ya dubesu kafin yace "Excuse us, Labib ya kalli Uncle ɗin nasa kaman me son yin magana sai kuma yabi bayansu ya fice.
"Jalal ya dubi Barr Munir dake zaune saman ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da aka ƙawata parlorn dasu kafin yace" Kaifa Barr aren't gonna excuse us...."Dakatar dashi Alhj Kasim yayi ta hanyar ɗaga masa hannu kafin yace " Boy ko me zaka faɗa min ka faɗa min gaban lawyer na, nida shi babu wani shamaƙi a tsakanin mu so just go ahead and talk.
"Ƙarasowa cikin parlorn yayi gamida zama bisa kujera mai kallon na Alhj Kasim tuni idanunsa sun rine zuciyarsa ta shiga masa zafi sabida abinda zai faɗi, bashi da wani choice rather than it..."Barr ne ya katse masa shirunsa da faɗin " Jalal we don't have the whole day, Mr President is a busy man so kayi abinda ya kawo ka.
"Fuzar da iska yayi kafin ya ɗago ido ƴana dubansu kana yace" *Zan aureta* daga nan shiru yayi bai kuma cewa komai ba, sai faman murza hannunsa yake jijiyoyin jikinsa sunyi ruɗuruɗu haka nan idanun sa sun koma jawur....
"Surprisedly suke kallonsa...
"Fari'a ne ya cika fuskokinsu mission ɗinsu goes well wann na ɗaya daga cikin dalilin da yasa suka taho dasu, don sun san muddin Jalal ya aureta toh magana ta ruhu har abada babu abinda zai kuma tono ta.
" Kafaɗan Jalal Alhj Kasim ya shiga bubbugawa a hankali kafin yace" Now you proved to us you are capable of helping her, da kayi gigin kai report da shine ka cuceta ka kuma cuci kanka, don bazaku taɓa kancewa tare ba, you'll endup in jell and ita kuma she might commit suicide ko depression ya karta gaba ɗaya, and ƴour poor mother will loose her only son, Jalal you did the best thing.
"Har lokacin dai Jalal bai ce masu komai sai kallon gefe da yake yi.
"Alhj Kasim yayi ma Barr ido, check Brr ya ɗauko ya rubata mar kuɗi kafin ya miƙa masa yace" Ka je ka nemi hida sai ku yare gaba ɗayanku a can....." Bai gama rufe baki ba Jalal ya miƙe yana masa mugun kallo kafin yace" Bana son komai daga gareku, auren Zubaidah sji kaɗai na tambayeku sabida a halin yanzu ku kuke iko da ita tunda kuke iko da wicked sister inlaw ɗinta......
"Murmushin bossawa sukayi baki ɗaya kafin Alhj Kasim ya dubi Barr ya masa ido, Kallo suka bi Jalal dashi wanda tuni ya fice....
"A first parlor ya hangu su Salim suna zazzaune, Harara yabisu dashi ɗaya bayan ɗaya, Labib ne ya miƙe da sauri ya nufesa, saidai kafin ya iskesa ya tura sliding door ɗin ya fice.....
"Alhj Jamil da Alhj Maina Dad ɗin Tariq suka ƙaraso parlorn after the meeting don jin me ake ciki, Alhj Kasim yace kar su damu he can take care if everything.... "Kallonsa dai kawai sukayi amma sunsan Alhj Kasim zai iya yin komai to get rid of his problems.
"Alhj Jamil ya ajiye masa wasu documents saman table ɗinsa kafin yace
" Yaya our company its at risk of going bankrupt, we might loose some of our employees sabida fake golds da aka fitar zuwa NewZeeland,...
"A zabure ya miƙe yana kallon ƙanin nasa, tunu ya cire hular kansa ya shiga fifita duk da sanyin AC ɗin dake parlorn "
"Jamil yaya akayi suka gane Zinaren bogi ne, Jamil we can't go bankrupt you need to do something.... Gaba ɗaya kaman zaucecce yake maganar, Waya ya ɗaga ya kira sakatariyarsa yace ta masa scheduling meeting da *Marafa Group Of Companies* Barr da Alhj Jamil sai kallonsa suke yanda ya zauce lokaci guda.
"Kallon Alhj Jamil ya kumayi kafin yace " Ka kira duk wani bankin da ka sani ka karɓo aron kuɗi kafin business venture ɗinmu da Marafa group of companies ya bunƙasa, we cant loose our company brother, do as I said pls,...
"Alhj Jamil ya dubesa da mamaki kafin yace" Yaya bashin banki fah kake magana, kasan....." Bai ƙarasa rufe baki ba Alhj Kasim yace " Haba Jamil so kake mu rasa company ɗinmu, ko billion nawa ne kasa hannu ka karɓa idan yaso daga baya sai mu wanye dasu, amma yaya kake gani yau udan baba ya taso yaga company ɗin da yasha wuya akansa ƴaƴan sa his very own children sun kasa maintaining, pls brother just do as I said for the sake of our company, for the sake of *Dasuki Holdings* Fuzar da iska Alhj Jamiƙ yayi kafin ya riƙo hannun ɗan uwan nasa yace " Yaya zanyi yanda kace, daga haka ya miƙe ya nufi Office ɗinsa.....
"Yana ficewa Alhj Kasim da Barr Munir suka kwashe da dariya harda tafe hannu,.
"Barr yace " Mr president baka da kyau, Alhj Kasim ya murmusa yana karkaɗa pen kafin yace" Let him borrow the Money, with that I'll ruin him completely dariya suka kuma yi hadi da tafe hannu...
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*A Dukku fah*
"Inna wai har yau babu wanda zaice min ha yanda Zubaidah take, ya kuma tambaya a karo na biyu.
"Ajiye rariyan tankaɗen dake hannunta tayi fuska a tamke kafin tace" Baba Wuro (Haka take kiran Umar) Har sau nawa zan faɗa maka nima bani da taƙamammen masniyar yanda suka tafi, iyakacin jitajitan danaji cikin gari shi na faɗa maka, Zubaidah bada kanta tayi ma ɗaya daga cikin yaran masu kuɗin nan da suka zo, bayan sun gama lalatan su, suka tattara suka bisu garinsu wasu ma cewa suke da maƙudan kuɗi suka sayesu.....
"Girgiza kai ya shiga yi idanunsa jazur yake faɗin" Inna ni nasan ƙarya ake mata sharri ne, Zubadah na bazata taɓa bada kanta ma wani ba, bazata taɓa bin masu kuɗi ta barni ba, nasan tana sona......" Baffah ne ya fito daga kewaye ya tarar suna zancen....
"Ajiye butar hanunsa yayi gamida zubar da ruwan dake bakinsa kafin ya juyo yana ma Umar mugun kallo kana yace " Wato har yanzu bazaka daina maganar wann yarinyar ba ko, toh idan baka sani ba ka sani, maganar da mahaifiyarka ta faɗa maka gaskiya ne, idan da ba gaskiya bane ai da sun mana sallama kafin su tafi musamman ita Zubaidar tunda akwai baikon ta akan ka...
"Idanuwansa suka ciko ƙwalla, da sauri ya miƙe ya shige ɗaki gamida kulle kansa, da gaske ne Zubaidah ta barsa sabida wani, take ya yuna sanda tayi aikin wuni guda gidan Alhj Dasuki, ya tuna irin kallon da wani saurayi ne kyau yake mata, ya tuna yanda itama ta masa murmushi, tabbas ko wata mace zata iya barin masoyinta akan wann saurayin sabkda ya haɗa komai na rayuwa, ka kuɗi ga kyau,....."Share hawayen da suka zubo masa yayi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna, bazai iya barin Zubaidah ba, bazai iya rayuwa babu ita ba, dole ya fice ya neme ta dole ya dawo da ita gareshi don kuwa tabbas Zubaidah *Mallakin sa* ne......
"Iyalle ta dubi ƙanwarta shafa wacce ke mutuwar son Umar amma besan tanayi ba, tayi murmushi kafin tace" Shafah ki kwantar da hankalinki Ummaru kaman kin samu an gama, ni nan da kike gani ni na kitsa wa Hadiza yanda zata yi, bacin haka ina taga kwanyar yin wnn tunani, ni dai abinda nake so dake kisan yanda zaki saye zuciyarsa tunda naga har kusan mutuwa nikayi sanda yakai baikon Zubaidah.
"Shafa tayi wani murmushin jin dɗi, don yanzu jinta take tamkar sarauniyar mata tunda Zubaidah ta tafi kafin tace" Ai wllhi bakiji wani daɗin da nake ji ba, yanzu kika tabbatar min ke ɗin yayata ce, Umar kuma dole yaso ni tunda wancan me kama da aljanai ɗin tayi gaba.. Dariya suka kuma yi a tare harda kashe hannu....
*Gombe, Fada*
" Abba barka da war haka , cewar Zahida yayinda take ƙarasawa kusan mahaifin nata,
"Murmushi yayi mai fitar da ƙwarjininsa kafin yace "Barka Gimbiya ƙarasi mana, ya matsa mata gefe da tumtim ɗin da yaɗan kishingiɗa akai ta ƙaraso gamida zama daf dashi. Hannayenta ya riƙo gamida sunbatar su kafin yace" Allah ya miki albarka ɗiyata. Murmushi tayi tana mai kallon mahaifin nata wanda a kullum cikin tausayin sa take sabida damuwan da bar yau ya kasa mance ta sama da shekaru ashirin da huɗu.
"Ɗan gyaran murya Zahida tagi kafin ta kalli tapkeken hoton jaririn da duk wani parlor a gidan akwai hoton kafin tace " Abba meyasa baza a cire hotunan ba tunda naga ɗaga maku hankula yake musamman kai da Madaki, snn ya mutu Abba inaga ajiye hotonsa a parlor haka babu wani alfanu
"Girgiza mata kai yayi idanunsa naga hoton kafin yace "Zahida Yayanki bai mutu ba, ni inaji a cikin jikina bai mutu ba, nasan watarana Allah zai haɗani dashi, ina ganinsa kullum cikin mafarkina, snn Suhaima tana faɗa min cikin mafarki na ɗanmu yanada rai, snn ta bar min amanarsa duk randa na hafu dashi......."Baki Zahida ta saki tana kallon mahaifinta wanda ba don jinin sarauta dake yawo a jikinsa ba da sai tace tabbas kwanyarsa ta kusan samin matsala, a hankali ta miƙe da zummar barin wajen, don tasan mai martaba muddin ya soma waɗan nan batu toh a ranar haka zai wuni bai fita fada ba..
"Ummi dake maƙale jikin labule tana kallonsu, take taji zuciyarta na mata zafi, shin wnn wani irin yaro ne, shekara da shekaru yaci ace mai martaba ya mance sa shida uwarsa gashi har yau yana tunasu, gashi har yau bata cimma burinta na mallakan ɗa namiji ba wanda zai kasance magajin sarki.... Da wnn ƙunci ya juya ta nufi sashenta ba yateda ta shiga sashen mai martaba.
"Zahida kuwa tana komawa ɗaki wayatya ta kunna ta hau facebook don abokin hitarta knn sai amintattun bayinta guda biyu, kasancewar kullum a killace take a guda bata fita ko ƙofa.
"Hira ta soma yi da kawarta wanda basufi kwana biyu da haɗuwa ba, hura da yayi dadi sai aka koma waya daga chating...
*Abuja*
[1/23, 22:12] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
17
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*"Dasuki Mansion"*
"Matashin saurayi ne wanda aƙalla bazai haura shekaru 35 ba zuwa da shida ya shigo cikin parlorn cikin shiga irinta guards, baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa, idanunsa manne da ɓaƙar tabarau.
"Cike da rusunawa ya miƙa wa ogan nasa saƙon dake hannunsa. Alhj Kasim ya murmusa kafin yace " Good job Faisal, I trust you, I know I can always count on you, kaci gaba da aiki me kyau.
"Faisal ya kuma rusunawa haɗi da yin gajeren murmushi kafin yace " At your service Sir,
"Daddy yace " You can leave now,.
"Kuɗaɗene shirye cikin babban jakar wasu in dollars wasu kuma Naira, murmushi yayi sanda suka kalli juna shida Barr Munir.
"Barr ya shafi haɓarsa yana murmushi kafin ya jawo jakar ya buɗe, ..
"Documents ɗin dasuke cikin first folder ya ɗauko ya shiga buɗewa,.
"Murmushi yake yana kallon takardun kafin ya kalli Alhj Kasim yace" Everything perfect, gaskiya yaron nan bazamuyi wasa dashi ba yasan kan aikinsa, ka duba kaga yanda yayi copying signature ɗin Alhj Jamil tamkar shi yayi,....
"Alhj Kasim yayi wata murmushi kafin yace" Barr I know what I'm doing nasan irin mutanen da nake aiki dasu, Wann yaro Faisal is very talented bazamu barsa ya tafi haka nan ba, dole naja sa sosai a jikina, yanzu abinda nake so da kai yanzu kayi attaching attaching waɗan nan documents ɗin da wanda yayi signing na karɓan bashin banki, kaga idan akayi presenting a conference meeting babu wanda bazai yarda sa hanunsa bane, daga nan mission dina na mallakan *Dasuki Holding* ya kusa zama sucessesful... Dariya suka fashe dashi kaman ba manyan mutane ba....
"A tare suka miƙe suka nufi waje Barr na biye bayansa ɗauke da rapan en ɗari biyar rufe cikin envelop kai tsaye sashen su Jalal suka nufa...
"Annah na tsaye tana kwasan shanya taji sallaman su, cike da tsananin mamaki ta bar abinda take ta ƙaraso tana amsa sallaman, mamaki ma ya hanata gaishesu, da ƙyar ta lalumu kalamai tai masu sannu, suma sun lura da hakan.
"Har Annah tai masu iso suka shigo ta shimfiɗa masu darduma bata daina mamaki ba.
"Bayan sun gaisa ne Daddy yai gyaran murya kafin ya soma magana.
" Hannatu nasan zakiyi mamakin ganinmu a ɓangaren ki, Toh magana ta gaskiya its about your Son Jalal.....
"Ɗago ido Annah tayi tana dubansu kafin tace" Lafiya Alhj me ya sami Jalal.?
"Daddy ya ɗanja fasali kafin yaci gaba da faɗin" Jalal was at my office earlier, Yaje shi office ɗina on an a serious matter, bansan ko kin sani sabida naga tun da incidence ɗin ya faru kin yi iya ƙoƙarinki wajen kula da yarinyar, in short ke kikayi saving life ɗinta......
"Gaba ɗaya ya ƙulle kan Annah, ko kaɗan bata gane me yake nufi ba kokuma ina ya dosa.... "Murya cike da damuwa tace " Alhj saidai ban gane me kake nufi ba, what did this had to do with my son.
"Ko yayi maka wani abin ne....
"Daddy da Barr suka kalli juna kafin Barr yayi gyaran murya yaci gaba da faɗin"
"Tabbas bakida masaniya akan abinda ke faruwa amma yanzu ya zama dole ki sani tunda abin yakai ga aure, da alama Jalal ya ɓoye maki amma gaskiyan magana Jalal shi yayi ma yarinyar nan Zubaidah fyaɗe wanda hakan yasa Alhj taimaka masu tunda basuda kowa snn Jalal ma bashida kowa sai shi.......
"Kaman almara haka Annah take jin maganar, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske tasan Jalal manemin mata ne amma bata taɓa kawo zai iya yiwa wata yarinya fyaɗe ba..... Take hawaye ya shiga zarya a fuskar Annah.
"Alhj Kasim da damuwan munafunci ya nuna a fuskar sa yaci gaba da faɗin" Hannatu keda Jalal duka ƴan uwa muka ɗauke ku mussaman Jalal na ɗauke sa tamkar ɗa bazan gansa cikin matsala na ƙyalesa ba dan kuwa shida su Salim daidai na ɗauke su. Snn laifin da ya aikata yayi nada wann dalili ne yasa amincewa zai auri yarinyar su rufa wa junan su asiri.
"Barr ya ajiye kudin gabanta kafin Daddy yaci gaba da faɗin" Yau da dare insha Allah zamu ɗaura auren snn ga wann Jalal yayi amfani dashi don neman muhalli,..... "Kasa magana tayi har suka fice bata san sun fice ba.....
" Ido ta ƙura wa kuɗin har lokacin idanunta na hawaye, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un " Fyaɗe, Fyaɗe Jalal, Jalal, ɗinta shi yayi raping Zubaidah.... Hannu tasa ta goge hawayen, dukda ba ita ta haifi Jalal ba tana masa so irin wanda uwa keyi wa ɗanta, her whole life burinta Jalal ya zama ɗa na gari, amma sai ya kasance akasin haka, kaico kaicon irin wann rayuwa.
"Sai yanzu komai ya shiga dawo mata daki daki tun ranar bikin sakun rana Salim, ta tuna Jalal ya tambayeta sunan yarinyar da suke tare, ta tuna irin kallon da taga yana mata ta tuna yanda hankalin sa ya tashi lokacin da Zubaida ke asibiti wann a dalilin haka har rana me kaman ta yau bata gane kansa ba, ta tuna yanda yayi donating jininsa ma Zubaidah, ashe dama sabida yasan laifinsa ne dole ya damu..... Maganar Zubaidah na ɗazu ya dawo mata kwanyar ta yanda take faɗi wa Hadiza *"Kika kawo ni wajen waɗanda suka lalalta min rayuwa* tabbas da Jalal take, shine ma komai ya tabbatar mata shine tunda gashi su Alhj har sun sani, no wonder bai mata maganar ba, no wonder ya tafu kai tsaye ya sami Alhj ba tare da saninta ba. Durusawa tayi wajen zuciyarta na mata ɗaci......
" Suna fita daga sashen su Jalal suka nufi sashen da aka ba wasu Zubaidah su zauna.
"Har lokacin bata buɗe ƙofa ba tana rufe ƙuryar ɗaki tana kuka.
"Hadiza tana ganinsu ta miƙe tana washe baki tana gyara ɗaurin kwali, gaishe su ta soma yi har tana tuntuɓe wajen ɗaga masu kayan da Zubaida ta ringa watsi dasu.
"Gaba ɗaya suka sakar mata murmushi kaɗin suka tambayeta Zubaidah...
"Nan ta soma jero masu ƙarya da gaskiya na abinda Zubaida tayi da wanda bata yi ba. Barr ya fuzar da iska dan bai zaci yarinyar zata zame masu matsala har haka ba, Barr ya kuma tambayar Hadiza ina mijinta, ta bashi amsa da fadin" Sun fice ganin gari shida Kamalu
"Alhj Kasim ya murmusa kafin ya ciro wayar sa yayi dialing wani lamba ya ƙara a kunne. "Hello James ya kashigo cikin guda ina neman ka, Barr zaizo ya directing naka yanda nake, daga gaka ya kayse wayan.
"Jim kaɗan Barr da wani murtuƙeƙen mutumi sanye cikin baƙin kaya da baƙin tabarau , da gani basai ance maka guard dinsa bane suka shigo a tareda Barr.
"Daddy ya dubesa kafin yace " James nasan kanada makullin duka ɗakunan gidan nan, I want you to open this door right a way.
"Kames ƴa rusuna kafin yace " Considered it done sir.
"Kan kace me James ya buɗe ƙofar ɗakin da Zubaida ke ciki.....
"Aikuwa tana ganinsu ta saki wani ƙara ta shiga tattaro gaba ɗaya kayan jikinta tana rufe jikinta, manne wa sosai tayi ta taƙure can ƙuryan ɗakin jikin garu, banda rawa da jikinta keyi bata komai, sai faman cije bakinta take tana kuka maras sauti.
"Alhj Kasim yayima James Ido. Take James ya ciro ƙaramar bindiga a cikin suite ɗinsa yayi pointing bindigar a kanta cikin miryarsa mai cike da tsoro yace " Quittttttt....!
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:13] : 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
18
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
"Daɗa mannewa tayi jikin garu gamida runtse idanunta wanda suke a jiƙe da hawaye,
"Alhj Kasim ya durƙusa a gabanta gamida ƙura mata ido, hannu yasa ya ɗago fuskarta......
"Wani irin kyarma jikinta keyi jin hannunsa a jikinta, tamkar garwashin wuta aka ɗora mata haka take ji, ƙara ta saki gamida ƙanƙamewa waje guda,...." Murya a dake yace " Kalle ni nan...
"Bata kallesa ba sai runtse idanunta da tayi.
" James ya kwaɗa mata ƙasar bindigan a keyar wanda yasata buɗe ido babu shiri, da ƙarfin gaske James ya ɗago ta gamida riƙe hannayenta, jin bazata daina kuka ba yasa James ɗaure bakinta da wani farin ƙyalƙe, yana riƙe da ita ya ɗago ta tana facing Alhj Kasim...."
"Barr yayi wata silent murmushi kafin yace " Yarinya ki bada haɗin kai ki sami tsira, bata kallesu ba sai hawayen dake zuba daga idanun ta....
"A zuciye Daddy ya pinciko gashinta da ƙarfin gaske gamkda ɗago kanta, kallonsa kawai take da idanun tsana hawaƴe na bin idanunta.
"Daddy yaci gaba da faɗin" Idan kika bi umarni na kin tsira Shashan yayanki wanda ya kasa kula da rayuwarki ya tsira, ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji abubuwan da zan faɗa maki.
"Kukan azaba kwai Zubaida keyi riƙon gashinta da Daddy yayi na mata ciwo, haka nan raunukan dake jikinta basu gama warkewa ba.... "Daddy yaci gaba da faɗin
"Idan kika ƙi yin abu guda da zan umarce ki zan kashe ki snn na kashe ɗan Hamman ki kinga na tabbata wann sokon yayan naki wanda hankali bai ishe sa ba, idan ya rasa ki ya rasa ɗansa nasan baƙin cikin duniya zai taru ya masa yawa, bayan na gama azabtar dashi snn na kashe shi,..."Wani irin runtse idanunta tayi hawaye na bin ƙuncinta jin irin kalaman da yake faɗa mata.
"Zan aurar dake a yau ɗin nan ma wanda naga dama, snn wllhi wllhi kinji na rantse naji wann magana ya fita waje zanyi yanda na faɗa maki zan kashe ki na kashe ɗan Hamman ki na kuma azabtar da Hammanki, don haka kar naji kar na gani bakin ki ƙanin ƙafarki, maganan fyaɗen da aka maki ya zama tarihi... Kina jina ya ƙarashe maganar yana zungurin kanta da bakin bindiga.
"James ya kifa mata wani gigitaceccen mari kafin yace " Answer!!!!! Da ƙarfin gaske...
"Daɗa runtse idanunta tayi kafin ta gyaɗa kanta da ƙyar sabida azaba.
"Barr ya ajiye mata kuɗi bandir ƴan ɗari biyar a gabanta kafin yace " Amarya wann kiyi anfani dashi wajen sayayya don nasan amare ba a rabasu da sayayya.... Daga haka James ya suce mata baki gamida yin wurgi da ita tsakiyar ɗakin kafin suka fice.
"Yaya Hadiza dake laɓe bakin window ta gama ganin komai, dariya tayi a hankali gamida watsa wa Zubaida dake kwance helpless a ƙasa wani uwar harara kafin tayi saurin ƙarasawa yanda su Daddy suke.
"Murmushi suka sakar ma juna kafin Daddy yace " Kar ki damu kaman yanda na faɗa maki aurenta yau da daddare a parlor na ina fata yayan nata bazai zame mana matsala ba.
"Hadiza ta kuma murmusawa kafin tace" Yo ai Alhk kar kaji komai tunda kanada ni, wann shashashan kuma ai ba mutum bane don sai abunda nasa sa shi zaiyi,..
"Barr da Daddy suka kalli juna kafin suka sakar ma juna murmushi.
"Barr yasa hannu cikin jakar ya ciro rapan ƴan ɗari biyu ya miƙawa Hadiza baki har kunne tasa hannu ta amshe. Barr ya kalleta xike da jin daɗin yanda Hadiza ta kasance mace mai son kuɗi babu wuya yanzu sai ka saye imaninta.
"Hadiza sai ysallen murna take ta nufi cikin gidan, ɗakin da Zubaidah ke yashe a ƙasa ta shige...
"Tana nan kwance a kasa kukan ma baya fita, Allah sarki ƴar marainiyar Allah.😭.
"Harara Hadiza ta watsa mata gamida zama gefenta, ɗaukan kuɗin tayi ta maƙe a hammatar ta, take ta canza fuska zuwa kalan damuwa sai ka rantse har ranta ne.
"Tallafo Zubaidah tayi ta rungume gamkda goge hawayen munafinci kafin ta soma faɗin" Kiyi haƙuri Zubaidah ki amince ki auri wanda ya aminta da aurenki ki sani taimaka maki zaiyi don wllhi yanzu babu me yarda ya aureki ko Ummarun da yake waƙar soyayyarki muddin yaji abinda ya sameki ba aurenki zaiyi ba. Kuma bari na faɗa maki babban rufin asirinki shine rufuwar maganar nan din kuwa muddin kowa yasan abinda ya sameki haka za'a keta zancen ki ana nuna ki da yatsa, mutane zasu ƙyamace ki haka nan babu mai kallon da wata daraja baƙƙe kima.....
Sameeena ce👌🏾
[1/23, 22:13] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
19
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
"Toshe kunnuwanta tayi da ƙarfin gaske alamun bata son jin kalaman Hadiza, wani uban tsaki Hadiza ta buga kafin ta tureta daga jikinta ta faɗi ƙasa, idan kin ga dama kiyi yanda kika so tunda ke ba'a maki abin arziki, ai ba akan ki aka fara fyaɗe ba kuma wanda aka masu ma suna ci gaba da rayuwa, idan kin gama kukan munafurcin kinya iya tashi kizo ki min aiki don ba baiwar gidan ubanki bane...."Daga haka ta kaɗe sawayenta tayi ficewarta..
"Asmah ce ta shigo tapkeken parlorn da sallama cikin shiga irinta lauyoyi wato cooperate, har ta cire belt ɗin dogon takalminta Kausar dake zaune a parlorn bata sani ba, da alama tayi nisa duniyar tunani...
"Ɗago kai Asmah tayi tana dubanta kafin ta ƙaraso daf da ita ta dafata....
"A ɗan zabure Kausar ta kalleta kafin ta sakar mata murmushi...
"Ah Attorney yau har kun taso daga sch ɗin ne.
"Asmah ta murmusa tana mai ajiye tapkeken littafin ta saman tabƙe kafin tace" Ai na faɗa maki Law School ba kaman degree program bane ba lalle mu ringa jimawa ba... Asmah ta canza zancen da faɗin
"Ehen wai meke damunki ne, kwana biyu nan you dont seems your self, is anything bothering you?...
"Shiru Kausar tayi gamida ƙurawa Tv dake kan faman aiki idanu..
"Asmah ta matso daf da ita gamida dafa kafaɗunta kafin tace " Sis I'm here for you, you can talk to me may be I can help.
"Kallonta Kausar tayi still damuwa ne a face ɗinta kafin tace " Cousin bazan ɓoye maki ba its about Salim.
"Asmah ta gyara zama kafin tace " Ehen me ya sami Salim ɗin.
"Kausar ta ɗan rausayar da idanu wanda ɗabi'arta ne kafin tace " These days he's been acting very strange, gaba ɗaya tamkar bashi ba, I'm afraid he might be hidden something from me, and ɗazu yazo ya tafi sauri sauri wai Daddy na kiransa, ni the most abinda ya ƙuƙƙen kai ma shine rashin ganin engagement ring ɗinsa da banyi ba a hannunsa.......
"Dariyar da Asmah ta fashe dashi ne yasata cin birki, wani mugun kallo take watsa mata kaɗin tace " What, is it funny?
"Asmah ta ɗan tsaigata dariyar nata kafin tace" Wait hold on Kausar, you mean akan rashin ganin ring a hannunsa kika shiga damuwa haka, tabbdijam toh ai mu musulmai ba auren zobe muke ba, ke bari kiga naje na faɗawa Mumsy islamiya zamu shiga don wllhi turawan nan sun juyar maki da tunani...
"Harara Kausar ta kuma watsa mata har lokacin Asmah bata daina dariya ba kafin tace"
"Look at you jor, ce maki akayi ban sani bane, well I'm only used to it ne nothing more, nasan musulmai basa auren zobe you dont have to inmply anything, besides ni jikina ne ke bani something drastic is about to happen.... Miƙewa tayi ta suri car key ɗin Asmah gamida jan mayafi ta yafa."Asmah baki sake take kallonta.. "Wait ina kuma zaki.
"Kausar ta gama saka takalminta kafin ta juyo ta kalli Asmah tacd" Kinsan tunda aka sa rana na Mumsy bata so ina fita, so thats why zan fita da motarki don nasan bazata gane na fita, so kindly ina si ki miƙe ki wuce ɗakin ki, and help me close my door kafin one of those maids masu neman gidin zama wajen Mumsy su kai mata rahoton na fice.
"Asmah ta kalleta galala kafin tace" Aiko basu faɗa mata ba ni zan faɗa mata...
"Pls mana Attorney ,
"Murmushi Asmah ta ɗanyi kafin tace " But you've to be fast, sai kin dawi Allah ya tsare, hugging juna sukayi kafin Kausar ta fice cikin sauri.....
"Hamma Habibu yayi shiru yana duban Hadiza, harara ta kuma galla masa a kari na biyu kafin tace" Meye kake kallona haka, kamata yayi kamin godiya ba ka tsaya kana kallona haka nan ba tunda da taimakona ta sami mijin aure, bacin haka waye kake tunanin zai kwashi wnn ƙanwar taka sauran kan layi...
"Kallon Zubaidah dake matse cikin garu yayi har lokacin bata dawo daidak ba kafin ya maido da dubansa ga Hadiza, murmushi ya ƙaƙaro kana yace" Eh eh haka ne haka ne Hadiza, mun gode maki daba don ke ba da yanzu muna can garinmu anata zagar min ƙanwa.
"Ya kuma duban Zubaidah kafin yace " Kiyi haƙuri kiyi haƙuri ƙanwata kin sami me auren ki...... "
"Miƙewa tayi tana cije baki kallon tausayi tabi Hamman ta dashi kafin ta juyo tana duvan Hadiza,
"Murya na rawa take faɗin" Bazan aure sa ba wllhi ko waye bazan aure sa ba, bazan taɓa aure ba bazan ci gaba da wann rayuwar ba, da na auri wani ba Umar ba gwara mutuwa na, snn a halin yanzu banjin zan iya auren nasa,... Ta ƙarasa ta riƙe hannun Hamanta kafin tace " Hamma ka yafe min, ta shafi kan Kamalu dake bacci bisa tabarman kafin ta soma tafiya da baya da baya... Kan kace me ta fice a guje dukda ciwo da azaban da take fama dasu...
"A guje suka bi bayanta suna kiran sunanta, har suka fito haraban gidan wanda hakan yaja hankaƙin illahirin mutanen gidan...
"Daidai lokacin aka buɗe wa Kausar tangamemen gate ɗin ta kuwa shigo a guje wanda ita kanta bata san dalilinta na shigiwa a guje ba, kodayake tunanin da take ciki yasata yin hakan.... " Kowa dake wajen runtse idanunsa yay don kuwa daidai ƙarasawan Zubaidah wajen knnn.....
"Shigowarsa gudan knn yayi jifa da abinda ke hannuna ya nufeta gamida ƙwalla mata kira.....
"ZUBAIDAHHH..... Daidai lokacin da Kausar ta danna wani uban birki babu shiri, Jalal kuma ya rungumota suka zube ƙasa suka shiga juyi a ƙasa, ya tareta ta ko ina yanda bazata ji ciwo ba...
"Salim dake tsaye balcony ƙirjinsa ya buga da ƙarfin gaske ganin Kausar ce ta shigo, ai a talatin ya zura shkrt ɗinsa ya nufi downstirs...
"Buɗe idon da zatayi tayi ido huɗu dashi, fuskan da bazata taɓa mancewa ba, fuskan da shine mutum na farko da ya kai mata sura, ɗaya daga cikin fuskoki huɗu da bazata taɓa mantawa a tarihin rayuwarta ba, ɗaya daga cikin mutane huɗu da suka lalata mata rayuwa, farin fuskan da ya koma mata tamkar baƙin kumarci......."Wani irin kara ta saki don kuwa gaba ɗaya abinda ya faru da ita ya shiga yawo a kwanyanta...
"Tunda tayi wann ƙaran bata kuma motsi ba,... Hankali tashe ya shiga jijjigata yana kiran sunanta,.. Kausar ma hankali tashe ta shiga taya Jalal, gaba ɗaya sauran mutanen suka karaso Hammah Habibu kam durƙusawa yayi a wajen ya shiga shera kuka...
"Hadiza ta yaɓe baki take da baeinta kukayi ta mutu tunda abinda tafi so kenan, sekace akanta aka soma fyaɗe..... "Kausar ta ɗago tana duban matar dake magana kaɗin tace " You mean Rape???
"Daidai lokacin da Salim ya fito farfajiyan gidan... Dafe kansa yayi a hankali ya furta "Shitttttt! Cikin sauri ya juya ya koma cikin gidan.
"Mummy tayi saurin ƙarasawa ta riƙo Kausar ta faɗin " Daughter taso mu shige ciki...
"Kausar ta ɗan kalleta kafin tace " Mummy bari a sa mata ruwa ta farka, she panic nd then fainted......"Ido Mummy tayiwa Hadiza alamun su shige ciki....
"Kan su ankara Jalal ya sureta ya nufi ciki da ita, gaba ɗaya suka bisa da kallo.
"Hadiza ta gallawa Hamma Habibu harara kafin tace" Sai ka taso mu shige ciki ai me ƙanwa,... Kausar ta bisu da kallo har suka shige
Kafin ta juyo ta dubi mummy wacce itama kallon tabisu dashi.
"Suna haɗa idanu Kausar ta sakar mata murmushi da iayakacinsa fatar baki. Mummy ta rungumo kafaɗun Kausar kafin tace mu karasa Daughter.....
sameeena ce👌🏾
[1/23, 22:13] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
20
*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum... 📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape*
"Shiru Kausar tayi tana duban Mummy, a hankali ta furta "Jalal, so Jalal can rape someone....
"Mummy ta matso gamida rik'e hannun Kausar cikin nata kafin tace " Daughter ki bar D'anAdam yanda kika gansa, muma bamuyi zaton Jalal can do such thing ba, anyway they are getting married, at least sun rufa asirin junansu......
"Kallon Mummy ta kumayi da mamaki kafin tace " Mummy this is a very serious crime, why would you cover-up for him, let him pay for his crime, bai kamata a k'yalesa haka nan ba.
"K'irjin mummy ya bada dummm! Tamkar Wanda aka sauk'e mata guduma.
"K'ak'aro murmushi tayi kafin tace " Kausar the girl refused to talk, tak'i to shigar da k'ara tace duk wanda ya dameta da maganar shigar da k'ara zata kashe kanta, snn Jalal yayi nadaman abinda yayi ya nemi yafiyarta snn ya amince zai aureta so kinga gwara a barsu su sami Chance na kasancewa tare.....
"Jinjina kai Kausar tayi da jin hujjojin Mummy, on the other hand ta tsinci kanta cikin rashin gamsuwa da labarin da Mummy ta bata gameda Zubaidah, haka kurum taji tana son jin gaskiyar labarin, snn tana son kasancewa da Zubaidah don akwai abinda take so taji daga gareta.... bata kuma cewa komai ba har Mummy ta mik'e tana rangad'a kira wa Cook Jane don tazo tayi serving Kausar...
"Dafe kansa ya kuma yi a Karo na biyu yana hangen k'ofar parlorn....
"Ganin Mummy ta fito yasa sa k'arasasa da sauri... Wani uwar harara Mummy ta watsa masa kafin tace " Ni na gama nawa part d'in I made her believed Jalal was the one who raped the girl... Yanzu saura ya rage naku kai da Daddynka, yasan yanda za'ayi su bar gidan nan zuwa gobe kai kuma ka fara tunanin zama namiji for once, and stop being so Mama Boy...... Daga haka tasa kai ta wuce......
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin ya murd'a marfin k'ofan a hankali, zaune ya hangeta da gani tunanin wani abin take..
"Yayi saurin saita kansa kafin ya k'arasa yana fad'in " Baby kece a gidan namu, what a surprise..
"Mik'ewa tsaye tayi fuska babu walwala kafin tace " Mummy nazo gaisarwa don tun dawowarsu daga Dukku bamu gaisa ba ko a phone ne, and I'm leaving right now....
"Ohhh com'on baby so soon, at least mud'an gaisa mana...
"Hararansa take ba tare da tace komai ba ta suri Jakarta...
"Da sauri yasa hannu ya rik'e jakar kafin yace " What why the face, wai make damunki me huhm Sweetheart.
"Kallonsa take ido cikin ido kafin tace " Salim duk yanda akaga guda d'aya dole aga sauran ukun, what I Mean duk yanda aka ga Jalal dole a ganku kai, Labib and Tariq, don kuwa nasan bakwa rabuwa, Salim I perfectly well know you and your friends, nasan all of you are womanizers, now tell me the truth and when I said the truth I mean only truth, are you involved in that horrible crime?????
"Da mugun mamaki yake kallonta da k'yar ya iya lalumo kalamai saman harshensa kafin yace " Sweetheart I don't get you..... Which... Which crime are you talking about.
"Huci kawai Kausar keyi kafin tace " The crime your very own friend your childhood friend Jalal had committed, and still ka b'oye min baka dad's mun ba.
"Tattare naman goshinsa yayi gamida fuzar da iska kafin yace" For God's sake Kausar stop talking ridiculous, I swear to you I had nothing to do with that, Why must you accused me of such dirty crime, haba haba sweetheart I tought kinmin farin sani by now kinsan abinda zanyi kinsan wanda bazanyi ba, wllhi tun ranar da na d'aura idaniyana akanki ban sake kula ko wata mace ba, If I want zuwa zanyi na kama hotel na shek'e ayata da iya adadin 'yammatan da nake so without you knowing it ba wai na tsaya ina raping mere girl irin wann yarinyar ba, rashin fad'a maki kuma da banyi ba gani nayi wann ba abun fad'a bane abin takaici ne da Allah wadai... Jalal is my very good friend but believe me wllhi banda hannu kan abunda ya aikata, hasalima nida Daddy taimakonsu muke shida yarinyar su gina sabon rayuwa amma idan baki yarda dani ba fine banida choice..... Ya k'arashe maganar yana ware hannaye sai ka rantse gaskiya ya gama fad'i....
"Jikinta ya d'anyi sanyi amma har yanzu ba wai ta aminta bane. Gyara mayafinta tayi kafin ta d'ago kai tana dubansa snn ta soma fad'in" Salim zan iya zama da kowani irin mutmun a duniyar nan amma banda *Rapist* if I finds out kanada hannu ciki believe me I will not marry you and you can forget about me, excuse me.... Daga haka tasa kai ta soma tafiya....
"Dammit, dmmitttt, Ya fad'i gamida murza duka hannayensa biyu cikin gashinsa, da sauri ya bud'e k'ofar ya shiga kiranta yana binta da sauri......
"Daidai K'ofar da zai sadaka da haraban gidan ta had'u da Labib, kallo d'aya ta masa ta watsar don kuwa gaba d'aya haushinsu take ji...
"Ohhh our bride to be yau kece a gidan namu, Labib ya fad'i yana wani shi'umin murmushi....
"Gajeren murmushi tayi snn suka gaisa a tsaitsaye kana tace "Ita zata wuce gida,
"Labib ya kalli Salim dake tsaye bayansu yana muzurai kaman munafuki kafin ya ware idanu yace " Aww this is so soon though bansan time d'in da kikazo ba, gashi inaso muyi 'yar wata magana about your cousin Asmah, but anyway zamu zo gida nida abokina then we talk....
"D'an yak'e tayi kafin tace " That wud be much better, bye for now...... Wucewa tayi ta nufi motar, Labib yayi ma Salim ido alamun meke faruwa, ido ya masa kawai kafin yabi bayan Kausar da sauri.....
"D'an tab'e baki Labib yayi kafin ya nufi cikin gidan.....
"Har lokacin ya kasa motsa koda d'an yatsansa ne sai hawaye dake neman kufce masa....... Baki ya bud'e da k'yar da niyyan magana tayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin taci gaba da fad'in
. "Jalaluddeeen, ban tayar da kai ta hanyar banza ba, Allah shine shaida na, my whole life I've been struggling for you to have a better future, Why Why Jalal, meyasa ka zab'i ganin kukana, meyasa ka kasa rik'e amanar da Allah ya d'aura maka a matsayinka na d'an Adam. Meyasa ka lalata rayuwar innocent girl irin Zubaidah. Idan ka kubce wa Shari'an duniya ka sani bazaka kubcewa Shari'an mahaliccinka ba......
"I zuwa lokacin ya kasa rik'e hawayensa..... A hankali ya k'araso gamida d'aura kansa bisa cinyarsa ta, kuka yake kaman k'aramin yaro, babu yanda ya iya bashida wani zab'in da ya wuce d'aukan laifin da ba nasa ba, Alhj Kasim is very rich and powerful Man, he can destroy Zubaidah and her family muddin ya fad'i gaskiya so as Annah too, he needs to this for Zubaidah and Annah, take yaji zuciyarsa tana dad'a basa k'arfin gwiwa.....
"Kuka Annah keyi har lokacin kansa na bisa cinyarta, hannayenta ya rik'o a hankali yayi kissing nasu kafin ya soma fad'in"
"I hope one day you'll forgive me my Annah, yeah I was stupid and also a coward, I was drunk that I couldn't stop...."Burki yaja cikin ransa kuwa k'arasawa yayi da fad'in "I couldn't stop them, na kasa hanasu cin zarafinta......
"D'ago ido yayi yana kallon Annah kafin yace " I'll never ever forgive my self for what I did...... Wayarsa ne tayi k'ara gabansa yayi mugun fad'uwa ganin me kiran "Alh Kasim Dasuki ne. Jiki a sanyaye ya d'ago ido yana dubanta kafin yace " I'll Marry her Annah, I'll help her to live again, I'll stand by her to overcome this horrible experience, I'll help her to heel all the damages I caused her...... Daga haka ya fice cikin tafiyar da tafi kama da sassarfa.
"Annah ta bisa da kallo har ya fice, wani ikon Allah sanyi ne taji ya ziyarci zuciyarta, hak'ik'a Jalal yanada baiwa da wani babban Al'amari a tattare dashi wanda ita kanta bata isa tace ga abun ba......
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:14] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
21
*©Sameena Aleeyou.... ✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape*
*How painful it is... 😭😭😭 I barely slept well last night when I received the saddest story. Three girls were raped at a University in one night, and you know what frightens me the most, one of the victims was raped by three men just like ZUBAIDAH, she's now receiving treatments at a hospital ..... 😭😭😭*
*Shin har yaushene za'a daina yiwa mata cin zarafi ta hanyar fyad'e a k'asar nan, shin shuwagabannin mu basu ganin abinda ke faruwa ne, shin wai shi talaka bashida ikon rayuwa ne, Hak'ka yanzu nake jin k'warin gwiwar rubuta wann littafi kuma ina fata sak'ona zai isa ga jama'a mussam THE RAPISTS AND THE VICTIMS da kuma shuwagannimu, Dan Allah matasa aji tsoron Allah kar ka b'ata rayuwar da baka san yanda aka jima ana ginata ba Ka tuna idan baka haifah ba meyuwa ka haifa a gaba idan Allah beyi zaka haifah ba toh bazaka rasa 'yan uwa wanda nasan bazaka tab's so kaga wani yayiwa naka wann cin zarafi ba, Oh my Brother in Islam ka tuna whatever goes around comes around Dan Allah mu kiyaye......... , 'Yar uwa wanda wann mummunar tsautsauyi da k'addara ya apka maki kar kiyi fushi da lamarin ubangiji kar kice shikenan baza kicigaba da rayuwa ba kaman da although it's very difficult but don't worry Allah is with you, you'll never be alone, give your self a chance to live.. And Don Allah a ringayin gaggawar Sanar da hukuma idan irin haka ta faru don taimakwa wajen tsayar da b'arna....... "Ku kuma jami'an tsaro kuji tsoron Allah ku ringa hukunta masu irin wann aiki da irin hukunci da aka tanadar domin su, idan kun tawye hakkin 'yar wani ku sani Allah bazai barku ba don baya hukunci da zalunci....... Allah Ya kawo mana k'arshen wann musiba a doron k'asa.. Ameen*
"Jiki a sanyaye ya k'arasa cikin parlorn, ga mamakinsa Hamma Habibu ya gani zaune k'asa gefen Alh Kasim, daga gefe kuma saman kujera Lamin masallacin Alh Kasim ne gefe dashi kad'an Alh Jamil ne, d'aya kujera me kallon tangamemen glass door d'in dake parlorn kuwa Alh Maina ne Dad d'in Tariq da Barr Munir ne suke zaune akai...... Jalal yabisu da kallo One by one kafin ya k'arasa shigowa, Hamma Habibu kasa rufe baki yayi sai murmushi yake, gefensa ya muskuta yabawa Jalal,
"Jalal ya d'an sakar masa murmushi kafin ya zauna.....
"Zamansa keda wuya suka soma gudanar da abinda ya tarasu, Hamma Habibu shi yayi alwali wa k'anwarsa Zubaidah yayinda Jalal ya wakilta Alhj Jamil ya karb'a masa auren Zubaidah....!
"Cikin mintuna da basufi biyar zuwa goma ba aka d'aura auren *Jalal da Zubaidah* kan sadaki Naira dubu talatin tare da shaidu kaman yanda yake a tsarin musulunci....
"Hammah Habibu ya kamo bakin rigarsa yana share k'wallan da suka ciko idanunsa, tausayinsa ya hana Jalal motsawa daga yanda yake, kamo hannun Jalal yayi har lokacin na sharan k'walla kafin yace " Ka kulamin da ita bata da kowa a duniyan nan sai ni sai kuma kai a yanzu......"Bai iya ci gaba da maganar ba sakamakon rushewa da kuka da yayi..... "duk wani mai imani a wajen saida ya tausaya wa Hamma Habibu.
"Alh Jamil da Jalal suka rik'osa har haraban gidan, har lokacin Jalal kasa cewa komai yayi ba, dukda ba auren soyayya yayi da Zubaidah ba saida yaji canji a yanayinsa, har Hamma Habibu ya wuce sashensu bai sani ba.
"Kafad'unsa da yaji an dafa ne yasa juyowa da sauri, Alhj Jamil ya gani fuskarsa cike da damuwa.... "D'an bubbuga kafad'un Jalal yayi kafin yace "Jalal Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi..... Jalal bai iya cewa komai ba sai kallon da ya bisa dashi.... Har Alh Jamil ya wuce gidansa dake manne dana d'an uwan nasa Jalal bai daina kallonsa ba, A hankali kuma ya maida dubansa ga sashen su, Jiki a mace ya soma tafiya zuciyarsa ta shiga tambayarsa "Anya hukuncin da ka yanke kayi daidai, wata zuciyar ta shiga k'arfafa masa gwiwa kan cewa wann shine hukunci mafi kyau, Allah yaga niyan ka bazai barka haka nan ba , da wann tunani ya isa sashensu wato BQ..
"Zaune ya taddata ta had'a tagumi komai ya faru kaman a mafarki, komai ya faru all of a sudden, ta kasa gasgata lamarin wai Jalal d'inta yau yayi aure, tabbas abinda ta jima tana son gani kenn dukda ba wani girma can yayi ba.. Saidai auren yazo ba ta yanda tayi zato ba, snn a halin da ake ciki a yanzu batasan makomar auren ba....."Zaman da yayi gefenta ne ya katse mata tunaninta......
"D'ago ido tayi tabb k'walla tana kallonsa shima k'wallan ne a idanunsa..... "Bud'e baki yayi zaiyi magana Annah tayi saurin rungumesa, rungumeta shima yayi sosai gaba d'aya suka soma hawaye...
"You did the right thing son, Allah albarkaci rayuwar aurenku, maza tashi kaje kaci abinci....
"Mik'ewa yayi da k'yar tamkar maras laka a jiki da k'yar ya iya furta na k'oshi Annah wanka zanyi yanzu daga haka bai kuma cewa komai ba ya shige d'akinsa.......
"Yana tsaye jikin mirror bayan ya fito daga wanka , ya k'urawa tabon dake gefen cikinsa ido tunani iri da kala suna yawo a kwanyarsa, kaman daga sama ya soma jiyo hayaniyar mutane, babu shiri ya k'arasa jikin window ya d'an jaye labule kadan yana lek'ewa......
"Mummy da Hadiza ne rik'e da ita, Fuskarta a kod'e alamun taci kuka, da gani basai an fad'a maka dole aka mata ba, k'irjinsa ya shiga bugawa da sauri da sauri, juyawa yayi babu shiri gamida zama bisa katifarsa. Har lokacin k'irjinsa bata daina luguden da take ba......
"Annah ta fito domin tarbansu, Hadiza kuwa sai yab'a mata habaici da mugun kallo take, Mummy tayi saurin jan Annah uwar d'aki don tattaunawa.
"Ina d'an naki yake, ya fito ya kaimu gidan da zamu zauna, don nauyi ne sosai ya hau kansa, tunda ya iya danne d'yar mutane ya keta mata haddi na tabbata yayi girman ya d'auki d'awainiyar mutane da yawa....... "Jin wann kalamai na Hadiza yasa Zubaidah sakin wani k'ara gamida kame kanta, tak'urewa tayi can k'arshen garu tana kuka gamida k'ank'ame jikinta sosai, duk k'ok'arin dasu Annah suke abu na neman fin k'arfinsu, duk wanda ya nufota ihu take sakewa tana matsewa cikin garu..
"Daga d'akinsa yake jiyo kukan nata, dafe kansa yayi sabida zogi da yaji zuciyarsa na masa, cikin sauri ya fice daga gidan dukda dare ya d'an soma ja......
"Suna tsaye gate din gidansu Labib suna shirin tafiya gidansu Kausar suka hangosa, shima kallonsu yake daga yanda yake tsaye.......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:14] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
22
*©Sameena Aleeyou.... ✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape*
"Cikin sauri Labib yabi bayansa...
"Jalal pls mana let's talk Buddy, I promise I won't take much Of your time....."Hannunsa yasa ya rik'o hannun Jalal guda d'aya wanda ya hanasa ci gaba da tafiya....
"Kallon hannunsa yayi yanda Labib ya rik'e gam kafin ya d'ago rinannun idanunsa yana duban Labib, a hankali ya furta "Let go of my hand......
"Girgiza kai Labib yayi kafin yace " No Jalal, I won't let you go until we finally talk, for goodness sake Jalal we can't go on like this, I.....I know bamuyi daidai ba but please let's reconcile our friendship....."D'aga masa hannu yayi alamun dakatarwa, murmushin takaici yayi kafin ya soma fad'in"
"Labib Dasuki, You and I have nothing to talk about, I already made my decision and I didn't ask for Opinion.
"Kunyi abinda kuke so sabida kunada masu tsaya maku a wann rayuwar, kunyi destroying innocent soul, kun b'ata mata rayuwarta sabida bata da mai tsaya mata a rayuwa, kunyi amfani da k'arfin dukiyar da kuke dashi kun rufe bakin kowa, even the girl who's suffering right now bata da ikon kare kanta, sabida nasan Alh Kasim bazai tab'a bari tayi magana ba fine... Amma ka sani baku k'arfin Allah ba, And let make this clear to you,...."Dafa kafad'an Labib yayi kafin yaci gaba da fad'in" I didn't marry her because I wanna cover up for You, No! Na aureta ne to save her life, to help her continue living, and also to PROTECT her, Snn na rantse da Allah I'll never leave her side for as long as I will live.... Da d'an yatsansa yake nuni kan k'irjin Labib kafin yaci gaba da fad'in
"And let me give you this message ka isar ma sauran abokan naka da kai kanka and also to your so called uncle, Zubaidah is now mine, she's now my wife,....."Ya d'an ja fasali kafin yayi wata murmushi da bazakace ga nufinsa ba kafin yace " You don't Owe me any Explanation... Daga haka ya wuce ba tareda ya kuma cewa komai ba....
"Shafe fuskarsa Labib yayi da hannunsa gamida fuzar da iska.
"Sai sann Salim ya k'araso yana masa alama da ido kan me ya faru. Gajeren tsaki Labib yayi kafin yace " Let's get going Salim,...
"Kallonsa Salim yayi kafin yace " Wait just wait Labib, tell me what exactly you guys discussed, and... And ka fad'a masa kar yacewa Kausar komai gameda wann mess d'in in case she ask him? Huh? Com'on Salim say something.......
"Foz kawai Labib yayi yana kallon Salim cikin zafin nama yake bud'e hannayensa yake fad'in " Enough, enough of this Salim,, for God's sake be a man for the first time, haba haba I can't stand your attitude of always being Mama boy, be responsible for once, kai da anyi magana Kausar Kausar, Baka tunanin wann abun can also ruin our reputation so as our parents, you always think of your relationship with kausar, enough of this, kai wllhi na fasa raka ka ma, inaga nan gaba hiranma ni zan ringa maka...... A zuciye ya wuce ya nufi k'ofar gidansu.....
"Gajeren tsaki Salim yayi gamida dukan tayan motarsa da k'afa yana first shitt!!! Cikin gida ya nufa gamida cilla wa security guda d'aya car keys d'insa yace " Get my car in.....
"Sashen mummy ya nufa sai ture turen baki yake kaman.... Sak spoiled child.
*************************
"Gida ne d'an madaidaici mai d'auke da d'akuna hud'u sai brander a tsakiya, daga can gefe kuwa kitchen. D'aya d'akin daga can gefe yake tamkar d'akin samari.....
"Tun daga waje yake jiyo hayaniyar Hadiza ta yanda take shiga bata nan take fita ba,....
"Ke ki bud'e kunnuwanki da kyau kijini wllhi tallahi sai kinyi k'aura zuwa d'akin mijinki, uban me zaki zauna ki mana, kokuma raba yayan naki zamuyi nida ke,...... Iyakacin abinda ya iya jure ji kenn cikin sauri ya nufi d'akin Annah....
"Zaune ya tadda ta da alama taji komai itama, murmushi ta sakar masa kafin tace " Shigo Son. Babu musu ya shigo gamida zama gefenta. ....
*Manage this, zakujini later insha Allah...*
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:14] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
23
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum... 📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape..*
"Hannayensa Annah ta rik'o tana dubansa sanda suke jiyo kukan Zubaidah da yanda Hadiza ke azalzalansu ita da Hammanta....."À zuciye ya mik'e da niyan ficewa, da sauri Annah ta rik'o hannunsa tana girgiza kai kafin tace "
"Dakata Jalaluddeen.....
"Kallon Annah yayi da rinannun idanunsa kafin yace "Annah dan Allah ki barni naje na sami matan nan, ya kamata tasan a yanzu bata da iko da Zubaidah, she can't keeps on torturing her da kalamanta masu zafi...
"Annah ta jinjina kai kana tace haka ne Jalal, Amma a yanzu idan kaje ka sameta you will endup ruining everything thing, think of Zubaidah, how would she react idan ta ganka, komai sai a hankali Jalal...
"Shiru ya d'anyi yana nazarin kalaman Annah kafin ya jinjina kai yace hakane Annah, Zubaidah ta tsaneni kaman mutuwarta musamman da yanzu tasan nine mijin da aka aura mata.
"Sauk'e ajiyan zuciya Annah tayi kafin tace " Shiyasa nake so muyi magana nida kai.
"Gyara zama yayi sosai yana dubanta kafin taci gaba da fad'in"
"What are you planning Jalal, me kake shirya wa rayuwarka, kaga yanzu I'm not longer working for the Dasuki's, snn Kai baka da aikin yi, snn ga nauyin iyali da yanzu ya hau kanka. Snn wani hukunci ka yanke akan zamanka da Zubaidah.....
"Maganar ta na k'arshe yasa saurin d'ago kai yana dubanta, sadda kansa k'asa yayi kaman mai nazari, a hankali kuma ya soma fad'in"
"Annah idan zaki iya tuna wani aboki na Usman wanda kullum yake min nasihar na rabu dasu Labib....
"Shiru Annah tayi na d'an lokaci kafin ta jinjina kai," Na tunashi yaron kirki ne k'warai babu shakka.
"Jalal ya d'an fuzar da iska gamida had'e hannayensa yace " Toh ya sama min aiki a workshop d'insu yanda suke aikin kanikancin su tunda dama I already have the experience, snn wann gidan ma a wajen ogansu na amshi haya.....
"Murmushi Annah tayi kafin tace "Toh Alhamdulillah.... "Kaman wanda ta tuna wani abu ta tsagaita da fari'an nata kafin tace" Toh Jalal idan kud'in da Alhj Kasim ya baka ya k'are kanaga zaka iya ci gaba da biyan hayan....
"Hannunta ya rik'o cikin nasa don bayaso ta d'ago komai, don kuwa kud'in hayan ma Unman ne ya ranta masa don yayi alk'awari kwabon da ya fito daga Dasuki family bazai tab'a ba, Ya adana kud'in sabida akwai ranar maidasu ga Alhj Kasim.
"K'ak'aro murmushi yayi kafin yace "Annah insha Allah hakan bazata zama matsala ba tunda gashi yanzu na soma aiki...
"Hak'ik'a har cikin ranta taji dad'i wai yau Jalal ne ya zama very responsible mutum haka, Allah yasa ya rabu da bin matan banza da shan kayan maye kenn... kasa b'oye farin cikinta tayi wanda har saida Jalal yaji dad'in haka.
"Kaman yasan tunanin da take, Ya dafe hannunsa cikin nata yace "Annah Insha Allah duk wani hallayana marassa kyau na dainasu, ki ci gaba da min addu'a Allah yayi mana jagora.....
"Murmushi ta sakar masa kafin tace "Babu ranan Allah da zai fito ban maka addu'a be Jalal, kullum cikin blessings d'ina kake Allah shiyi maka Albarka ya kuma albarkaci rayuwar aurenka....
"Addu'anta na k'arshe yasa jin wani abu ya tsargar masa, shiru yayi gamida k'urawa ledar tsakar d'aki ido....
"Annah ta fahimce sa tsaf, a hankali ta dafe hannayensa kafin ta soma fad'in" Kar ka damu d'ana I'll look after her for you, zan kula da ita har zuwa lokacin da zata zama ta rabu da wann k'uncin dake damunta, nida kai Will make a great team wajen taimakata har ta dawo cikin farincikin data rasa....."Baisan sanda ya rungume Annah ba tausayin kansu ya rufesu.......
"Zaune ta sameta can k'uryan d'akin Hamma Habibu da Kamalu suna rarrashinta, Hadiza kuwa sai faman cin magani take.
"Annah ta ajiye flask d'in abincin dake hannunta kafin ta nufi yanda Zubaidah take.
"Hannu Hadiza tasa ta jawo kulan ta shiga k'ok'arin bud'ewa, wani uwar tsaki ta buga gamida tab'e baki kana tace "amma dai Allah sawak'e tsiya mutum ya baro shinkafa a garinsa yazo Habuja ma yanaci..... Wani tsakin ta kuma bugawa kafin tace "Allah sawak' naci abincin tsuntsu...Tasa k'afa gamida shure flask d'in....
"Annah bata ce komai ba sai girgiza kai datayi, gefen Zubaidah ta k'arasa ta k'ura mata idanu tana karantar ta, a hankali tasa hannu ta d'aura saman nata.
"Sai snn Zubaidah ta d'ago idanunta wanda gaba d'aya sun kod'e sun canza launi, Kallon Annah take wasu hawayen suna k'ok'arin ciko idanunta, don tabbas bazata mance ranar data fara gamuwa da Annah ba, daren da ya zame mata bak'in dare a tarihin rayuwarta dukda Annah was kind to her, amma bazata mance cewa harda d'anta cikin mutane hud'u da suka shafa wa rayuwarta bak'in fenti, suka mayar mata da farin cikinta akasin haka snn wai a yanzu shi aka aura mata a matsayin miji, take taji wani sabon kuka ya kufce mata, komai ya shiga dawo mata kwanyarta, ihunta a lokacin da suke k'ok'arin rabata da mutuncinta da kuma dariyarsu wanda sautinsa ya kasa b'ace mata daga kunnuwarta......
"Fizge fizge ta shiga yi tana Screaming...Wanda duk wani mai imani sai ya zubda k'walla idan ya ganta.....
"Rungumeta Hamma Habibu yayi yayinda Kamalu ma ya had'e ya rungumeasu, gaba d'aya suka shiga rera kuka........
"A fusace Hadiza ta shigo d'akin gamida watsa masu mugun kallo kafin ta janye d'anta, tana huci ta dubi Annah take fad'in" Baiwar Allah dan Allah ki tattara ta ki kaima wanda jin kukan ya zame masa dole, don nikam na gama nawa, naji da kula da wann hau d'in yayan nata ne ko kuwa da yarona zanji, ta k'arasa gamida finciko Zubaidah daga jikin Hammah Habibu ta hankad'ata k'ofa, da sauri Annah ta rik'e Zubaidah cikin jikinta tana watsa wa Hadiza kallon k'yama... Tama rasa kalma guda a bakinta a hankali ta rik'o Zubaidah dake d'ingishi suka nufi b'angaren d'akinta.
"Hamma Habibu ya mik'e zaibi bayansu Hadiza ta jawosa da bayan rigarsa ta zaunarsa k'asa kafin tace " Ka rufe min baki ka wuce ka wanko hannunka da na Kamalu kuzo kuci abinci.
"Banda felek'e da iyayi saikace kanta aka fara fyad'e a duniyar nan, kar Allah sa ta hak'ura suje can su k'arata.
0 comments:
Post a Comment