"Da k'arfin gaske ya tokari k'ofar saida ta bud'e, kwance Ya hangeta saman rug shame shame basai an fad'a maka a shaye take ba...
"Tsaki Ya buga Ya soma toshe hanci yana mai shiga d'akin, quite messy and untidy.... Kai dagaji ma d'akin warin amai na barasa take...
"Da k'afarsa Ya shiga shureta yana fad'in" Ke Ke tashi dalla, ki tashi nace....
"Bata tashi ba sai faman shure shure da take... A fili Ya furta
_"What a f**k"_
"Da k'arfin gaske Ya fincikota gamida d'aura mata lafiyayyar mari wanda yasata bud'e ido firgit babu shiri..
"Tun tana ganinsa duru duru har ta hangesa sosai yana tsaye gabanta sai huci yake kaman wani mayunwacin zaki... Bata tsamman zai dawo yau ba, cikin sauri ta soma fad'in" Dama zaka dawo, bansani ba I should have placed order for you.....
"Da k'arfi yace " Shut your trap you bitch... Bayani zaki min wani d'an iskan kika kawo min gida da bana nan....
"Zulaihat ta Saki murmushi kafin tace " Au Imam ne ba kowa ba....
"Jawota yayi Ya mak'ure yana fad'in" K'arya kike munfuka wancan wines masu d'an karen tsada uban wa Ya saye su, kinsan dai ni ba sha nake ba... Oya fad'a mun gaskiya wa kika kawo apartment d'in nan....
"Cikin k'ak'arin murya take fad'in" He's just a friend, I swear to you....
"I thought we made a deal with you... Ko ba ce min kikayi kin daina bin kowa ba... Witch nasan bazaki iya ba, ... You know I don't tolerate shits , you leaving my apartment right this very moment..... Ya k'arashe yana isa bakin sip Ya shiga watso kayanta...
"Rik'esa take tana fad'in" Haba Umar don't do this to me, haba kar ka mun haka, ina zanje idan ka koreni, remember you said you loved me...
"Fashewa da dariya yayi kafin yace " That was your thoughts babe, coz you're so naive so easy to manipulate.... I love only one girl, .... Well I was only using you... And you've done your part... Dole ki tafi ki bar min gida before you causes hell for me.....
"Rik'e rigarsa tayi tana basa hak'uri tana kuka ina ko kulata beyiba Ya shiga janyota downstairs... Har sun kusa sauk'a Ya tuna Ya ajiye kud'insa a bedside a cikin d'aki...
"Kamota Ya kuma yi kafin yace " Muje na duba kud'ina wllhi kabo yayi ciwon Kai ke zan kama....
"Aiko yana Bud'ewa $700 d'insa suka ce d'auke mu.... Whattt!!!! Ya furta da k'arfi kafin Ya mik'e Ya k'araso gaban Zulaihat yanda take durk'ushe tana kuka kafin yace " Where is my money...
"Bata amsa sa ba sai kuka..
"Shak'eta Ya kumayi yana tambayarta....
"Cikin kuka take fad'in " Wllhi Allah ni banma san da kud'i a ciki ba..
"Dariyar rainin hankali yayi kafin yace " Don't take me for a fool, I'm not in the mood to play such games, bani kud'ina tun muna mu biyu.....
"Kallon mamaki kawai take binsa dashi, how could someone be so ungrateful, after all what she's done to him, is that how he repay her....
"Girgiza kai kawai ta soma tana fad'in you are a monster, I shouldn't have believed you in the first place... You are my worse nightmare... Bayan duk abun da na maka abunda zaka saka min dashi kenan... Yeah you're right I was so naive and stupid, ba laifinka bane laifin soyayyar da nake maka ne.. But I promised you, you'll regret this, you'll come to me begging pleading and asking for my forgiveness.... You've no idea what I'm capable of....... Janyota Ya shiga yi da k'arfi yana fad'in "Get the heck out of my house you garbage.....
"Har waje Ya fitar da ita kafin ya dubeta yace " Babu abunda zaki iya mun, k'ark"arinta kice zakije bada shaida a kotu, fine kije, ni iyaka gaskiyata na fad'i, kefah??? Snn ba'a magana biyu a kotu, idan suka gane k'arya kikayi a baya they will have you locked up in jell..!! Oya fice daga nan.. And kud'ina da kika sata zan san yanda zanyi na amshe su... And remember babe "I'll be watching you..... Ya k'arashe yana nuni daga k'wayar idonsa zuwa Face d'inta...
"Tafiya ta soma yi ga uban dare, gashi har lokacin ana yayyafi kad'an kad"an.... D'an wani gefen kanti ta samu ta rakub'e ta shiga neman layin Imam...
"Sosai Imam Ya razana da ganin kiran Zulaihat at this hours, yana d'agawa ta fashe masa da kuka, cikin kuka tayi briefing nasa,
"Da sauri Ya mik'e Ya zira riga yana fad'in" Kar ki dam stay right there, it might be dangerous... I'll get you soon....
"Har lokacin kuka take tana tuna wulak'anci da cin mutuncin da yau Umar Ya mata, ko shine autan maza ta hak'ura dashi...
"Imam yace " Kiyi hak'uri kinga wann shine irin abunda nake ji maki, I've told you time without numbers ki daina wann low life d'in da kika d'auka ma kanki, be happy for who you are, ki koma gaban iyayenki ask for their forgiveness, kiyi aurenki, You are still young and beautiful son kowa kin wanda Ya rasa...
"Harara ta b'alla masa kafin tace " Yimin shiru as if I asked for your opinion... Wllhi bana barin garin nan until I take my revenge, I'll make him pay, na gode da nasihar ka da shawarinka kuma insha Allah I'm a changed person now... Happy..!! Ta k'areshe tana murmushi...
"Murmushi shima yayi kafin yace " Yeah happy.. Kiyi baccinki ni barinje d'akina, and feel at home, although gidan nawa babu komai, ba irin gidan da kika saba bane, kinsan ni d'in student ne kuma taxi driver....but kar ki damu akwai wata tsohuwa cikin d'akin nan zata baki breakfast...
"Kallon mamaki ta masa kafin tace " I thought you living alone...
"Murmushi yayi kafin yace " Yeah my grandma bata jima da zuwa ba,.... So have a goodnight.. Ya fadi yana murmushi kafin ya fice...
"Murmushi Zulaihat ma tayi gamida kwanciya bisa couch, tana mai mamakin wadatan zuci da godiyan Allah da saurayi mai k'aramin shekaru kaman Imam yakeda.......
*********************
"Har wajajen k'arfe bakwai na safe wayar Jalal ba'a d'agawa, k'arshe yama daina shiga gaba d'aya, I zuwa lokacin ba Zubaidah kawai ba, harta Annah ma hankalinta ya soma tashi, wayar Ansar suka kira suka sanar dashi halin da ake ciki..
"Ansar ne yazo ya ringa kwantar masu daehankula yana nuna masu akwai possibility na abubuwa, maybe wayar babu charge ko kuma wani abu makamancin haka, but yasan Jalal is very strong , su bari zuwa nan da 24hrs idan basuji sa ba sai suyi reporting to police station...
"Kallonsu kawai Zubaidah keyi amma bata tunanin zata iya kaiwa har nan da awanni ashirin da hud'u ba tareda tasan halin da Jalal ke ciki ba.....
********************
*Gombe*
"Shattima zaune gaban DPO yaci gaba da fad'in" Sir babu wani report na accident ko robbery da kuka samu, don ya tabbatar mun Ya fito a jiyan snn wayarsa tana shiga har da safen nan daga baya ta daina gaba d'aya....
"Dpo yace " Ranka shi dad'e bamu samu wani report da yayi kama da abunda ka lissafo ba daga jiya zuwa yau, snn tashan motoci ai an daina barin motoci suna tashi da dare sabida guje ma faruwan hadd'ura da kuma tabbatar da tsaro.... Amma we are going now, barin shirya yarana zamu bi hanyar snn zan kira station d'inmu na can su soma gudanar da bincike... Shattima Ya mik'e yana fad'in " I"ll go with you sir....
"Dpo ya kad'a Kai yace babu matsala.....
**********************
"Koda suka isa garin Dukku sun samu tuni polisawa sun soma gudanar da bincike, shugaban tashar motoci ya tabbatar babu motan da tayi tafiya daga Dukku zuwa Gombe a jiya, haka nan tashan motar garin Gombe Sun tabbatar babu motar Dukku datazo Gombe a jiya entirely.....
"Hanya suka soma bi jeji jeji suna nemansa, wani bend da suka gangara suka kalli k'afafuwan mutane dashike garin akwai damshi, k'afar suka ringa bi dukda basu san ko na masu noma bane.....
"Nan dpo ya tura yaransa ta ko ta ina suka soma hudanar da bincike.....
"Har sun firfito suna shirin tafiya don basu ga kowa ba, .... Can k'arkashin wata bishiya wani police officer ya danna intercom d'insa yana fad'in" Sir there is a body here, Direction bla bla bla.... Ya fad'i daidai wajen.....
"A sittin suka shige dajin yanda yayi directing nasu...
. "K'arasawa kansa Shattima yayi gwiwoyinsa duk a mace ganin irin dukan da kayi ma Jalal, jini duk Ya bushe a jikinsa, Shattima zai tab'asa Dpo Ya hanasa..... Intercom d'in hannunsa ya danna kafin ya soma magana, Nigerian Police station, we need an ambulance Direction bla bla bla... Yeah ASAP, ASAP... Okay.
"Gwaje gwaje suka soma yi yayinda Shattima Ya koma gefe ya durk'ushe baisan sanda hawaye suka shiga zubo masa ba.... Mintoci kad'an Ambulance ta iso likitoci suka shiga nasu aiki....
"Da sauri suka saka masa oxygen snn suka ciccib'esa suka sa a bayan ambulance bayan sun rufe hannayensu da gloves suna fad'in" He's breathing, let's go let's go....
"Jin ance na numfashi yasa Shattima saurin mik'ewa ya nufi nasa motar, su dpo ma suka haye nasu motan.......
" Babban asibitin garin Gombe aka nufa dashi yanda likitoci suka shiga k'ok'arin ceto rayuwarsa don kuwa dukan da aka masa ba Wanda hankali zai d'auka bane, da ba don Allah yasa nada sauran numfashi ba tabbas da ya jima da mutuwa....
"Gida Shattima Ya koma don sanar da iyayensa abunda Ya faru. Umma da Baba Waziri sosai hankulansu Ya tashi, oh wann duniya abin tsoro, har wani yayi yunk'urin kashe hallita irinsa wanda baisan yaya aka k'era ba,... Haka Umma ta ringa sunbatu idan Shattima yaji zata Saki layi sai ya d'an kalleta...
**********************
*Abuja*
*Dasuki Mansion*
" Cheers...!! Cewar Alh Kasim dake zaune a center gefe dashi Faisal ne da kuma Barr Munir... D'aga cups d'insu sama sukayi su duka suna amsa masa fuskokin su Ya cika da farin ciki..
"Barr Munir yace" Wnn alamu ne dake nuna mana nasara tana garemu....
"Dariya Alh Kasim yayi kafin ya mik'e Ya k'arasa gaban Faisal yana bubbuga kafad'unsa yake fad'in" Without you non of this would had happened, you did a great job boy..... You deserve the reward.....
"Faisal yayi murmushi kafin yace " I'm always at your service Boss...
"Suka kuma fashewa da dariya Alh Kasim yace " Ku tashi muje mu masu ta'aziya so that no one should suspect us.....
"Fitowar da zasu yi sukayi ido hud'u da Mummy hawaye tabb idanunta....
"Daddy ya d'an fuzar da iska kafin yace " Farha make faruwa wa Ya tab'a mun ke,.... D'aga masa hannu tayi sanda yake k'ok'arin k"arasowa gareta tana fad'in" I knew it, nasan you are behind all this.... Kuka ya kufce mata ta shiga dukan k'irjinsa tana fad'in" I hate you, you are nothing but a disaster to my life..... Da sauri Munir Ya k'arsa ya rik'eta yana fad'in" Calm down Farah, put your self together......
"Fuzgewa tayi tana fad'in let go of me, you are a snake Munir, I can't believe you are my flesh and blood. Kai kake saka sa duk abubua marassa kyau.. I hate you all... Kuma barin gidan zanyi bazan zauna da murderer ba..... Fizgota Alh Kasim yayi ya nufi upstairs da ita yae kulle kafin yace " Mujenku I'll deal with that idan mun dawo....
"Babu kunya babu tsoron Allah suka shiga har parlor yima Hajiya Raliya Ta'aziyya.
"Kausar dake duk'unk'une cikin bargo don tunda akayi rasuwar batada lafiya, jin ana cewa gasu Alh Kasim Dasuki sunzo ta'aziya yasata buga wani uban tsalle daga saman gadon ta duro k'asa, Asmah dake zaune saman rug rik'e da k'aramin Alqur'ani ta dubi Kausar dake zura hijabi tace " lafiya Sis ina zaki ...... Kausar bata amsata ba, sai zura slippers datayi ta nufi downstairs tana fad'in" I can't believe that Scumbag got some nerve to show his face here......
"Jin haka yasa Asmah saurin mikewa tabi bayanta....
.Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:25] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
63
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Ehen this spectacular chapter goes to you my dearest Sis Rally, thanks for the love and care 😍❤*
"Har gaban Alh Kasim Kausar ta k'arasa idanunta na fidda hawaye sai faman huci take..
"Da mamaki ya d'ago yana dubanta kafin ya sakar mata murmushi yace " Kausar yaya mukaji da hak'uri.....
"Murya a dake take fad'in" Don't act innocent....Get out of here you killer......
"Gaba d'aya mutanen dake parlorn kallo ya dawo kan Kausar, Mumsy ma kanta kallonta take cike da mamaki....
"Asmah ta d'an matso tana k'ok'arin janye Kausar a hankali take fad'in" Kausy let's go, don't make a sin here... Fizge hannunta tayi da k'arfin gaske ta k'arasa gaban Daddy sosai tana nuna masa k'ofa take fad'in" Ka fice nace kafin na kira maka police... I can't believe you have some guts to show your face here bayan duk abunda kayi...... "Barr Munir ne ya mik'e da sauri yana fad'in" Be careful with what you saying now.... Lafiyanki kuwa kinsan abunda kike fad'i.....
"Juyowa tayi tana duban Barr still tana hawaye kafin tayi magana saiji tayi Mumsy ta fizgota cikin tsananin fushi sun nufi stirs... Juyowa Kausar ta kuma yi dukda janta da Mumsy take bata fasa magana ba cikin kuka take fad'in" You murderer, you'll pay for what you did to my family, sai mun had'u a kotu coz I'll press charges against you.... Daidai sanda Mumsy ta jefata cikin d'aki had'i do d'auketa da lafiyayyar mari.....
"Wai tabarmar kunya da bori ake nad'e ta, ko minti biyu mai kyau basu k'ara a gidan ba suka kwashin manyan rigunansu suka fice, Alh Kasim sai faman muzurai kawai yake yana huci shi a dole Kausar taci mutuncinsa babban mutum kaman shi, wani b'angare na zuciyarsa kuma ta cika da shakku da mamakin k'arfin hali irin na Kausar.....
"Dafe k'uncinta tayi ta d'ago idanunta masu zuban hawaye tana kallon Mumsy wacce itama hawayen ne keta faman kwaranya a idanunta fuskarta cike da b'acin rai da takaici.....
"Baki na rawa Kausar ta soma fad'in" Mumsy zan iya rantsewa he's behind all this.... Yi mun shiru...!!!! Mumsy ta katseta cikin daka tsawa kafin taci gaba da fad'in" Kinyi hauka koh? Nace kinyi hauka koh..?? Ta k'ara fad'a cikin tsananin fushi.....
"A hankali Kausar take girgiza kanta har lokacin tana hawaye idanunta suna kallon k'asa, cikin rawan murya ta soma fad'in" Mumsy I just can't stand Man wllhi nasan wann duk aikinsa ne, but pls kiyi hak'uri.... I.... I just couldn't help it ne, I still can't believe my Pappy is gone...... Ta k'arashe cikin sheshshek'an kuka.....
"Rungumota Mumsy tayi kafin itama tayi bursting cikin kuka saida sukayi mai isansu kafin suka zauna bakin gado.....
"Mumsy ta rik'o hannayen Kausar kafin ta soma fad'in" Dear I know exactly how you feeling, but what you did lately was wrong, it doesn't suite you at all... Yau da Pappyn ki zai tashi yaga irin abunda kikayi bazaiji dad'i ba, snn nima banji dad'i coz I'm also suffering... Your Father was the great love of my life..... But I had to accept the fact that he's gone.... Ki kasance mai tawakkali Allah yana son masu hak'uri, snn duk wanda ya zalunceka a duniyar nan kaine a saman sa... Ki bari hukuma tayi aikinta wann ba field d'inki bane tunda they are already investigating the matter....
"Kiyi hak'uri kiyi hak'uri kinji Kausar kiyi ma mahaifinki addu'a shi kid'aine abinda yake buk'ata daga gareki a yanzu kinji daughter...... Gyad'a kanta tayi tana share hawayen idanunta da bayan hannunta kafin ta rungume Mumsy very tied kana tace " Mumsy pls stay here with me for a while.... Murmushin k'arfin hali Mumsy tayi tana shafa kanta kafin tace " I'll always be here for you sweetheart, together we will overcome this horrible tragedy.., Asmah dake tsaye bakin k'ofa ta goge hawayen da suka zubo mata, tausayin family d'inta yana ratsa ta b'argo da tsoka, she needs to be very strong, her family needs her now more than ever.....😪
*****************
"Sai faman masifa yake shi d'aya yana huci, lek'owa ta d'an tsakiyar mota yayi ya dubi Faisal dake front seat kafin yace " Faisal are you sure you did a clean job, na fad'a maka bana so wani suspicious yayi linking d'ina da abinda ya faru, coz I've had enough already, dealing with the issue of those kids ma ya isheni, bana so na sake fad'awa wani court case coz a halin da ake ciki yanzu our company is not financially stable....
"Faisal ya d'an karkato yana kallon baya kafin yace " Boss you don't have to worry about that, let them go ahead and press the charges, sune a rana, coz basu da wani evidence against you..... Dariyar da Barr yayi ne ya katse su.... Daddy ya karkato yana dubansa alamun yana jiran amsa yaji dariyar me yake.....
"Barr yaci gaba da fad'in" Ai a halin yanzu ba shigar da k'ara bane a gabansu, su samu su wanye da masu hannun jari a company d'insu, sabida idan wasu sunyi hak'uri wasu bazasu yi hak'uri ba, Alh Tahir was a very wealthy man, yanada hannayen jari a k'asashe daban daban snn yana banking da bankuna a k'asashe daban daban a duniya, a lokacin da mukayi Business partnership with his company Attorney na Company d'insu ya bani wasu documents duk wani breakdown na business dinshi was written on that document..... So I suggest mu ringa bin k'afafun Employees d'insa da kuma shear holders na company d'insa a hankali muna nuna masu muna influencing nasu muna persuading nasu muna nuna masu cewa lallai lallai kar su yarda, Hajiya Raliya sai ta fito masu da kud'insu da sukayi asara, daga nan mujasu a jiki su zuba kud'ad'ensu a company d'inmu tunda dama we are at risk of going bankrupt, so kunga basu da wani lokacin shigar da k'ara koda ace zasu san gaskiya ma, wancan issue d'in zaiyi distracting nasu.....
"Tunda ya soma magana Alh Kasim ke binsa da kallo lallai ya yarda Barr abokin tafiya ne.... Dariya ya fashe dashi harda cire hula kafin yace " You are just an incredible Attorney , wann yayi , you should start working on that right away, kayi copying document d'in a computer ka fara spreading nashi to their Emails....
"Wata silent murmushi Barr yayi kafin yace " You don't need to tell me what I should do, You can trust me on that.... Shigar da k'ara shine babban kuskuren da Haj Raliya da d'iyarta zasuyi....
"Ganin motocin police a k'ofar company d'insu ya basu shock dukda sun san hakan ka iya faruwa.....
"Motarsu tana gama parking securities suka shiga bud'e masu.... D'aya daga cikin securities d'in na company d'insu ya soma fad'in" Sir we got some police men here, they said they are here to interrogate you Sir.. Gyad'a kai yayi kafin yace let them in....
"Tambayoyi Police suka masa gameda k'onewar company d'in abokinsa da kuma mutuwarsa, snn suka ce zasu iya dawowa any moment, Daddy yace " You are always welcome, Im willing to cooperate with you duk lokacin da kuka dawo, what I can't take shine wann ridiculous acquisition d'in da 'yar marigayi take mun, I should hve press charges against her amma sabida zaman mutunci da kuma alkhairin da ya faru tsakani na da mahaifinta shiyasa nake d'aga mata k'afa.... But next time I won't tolerate such scandal...
****************
*Police station*
" Sunyi jigum suna jiran feedback,Ansar sai faman kai komo yake yayinda Zubaidah da Annah suketa faman bin mutanen dake shige da fice da kallo...
"DPO ne ya fito tareda Ansar, suna tafe suna magana, Detective Amir shine cikon na ukun su,..
"Zubaidah kam tunda ta hango fuskar Ansar ta cika da damuwa tasan tabbas something is definitely wrong, mik'ewa tayi zata nufesu Annah tayi saurin rik'o hannunta tace " Mu jirasu a nan Daughter...
"Kallon Annah ta d'an yi fuska cike da damuwa kafin ta koma ta zauna tana mai bin umarninta, Zuciyarta bai daina bugawa da sauri da sauri ba, ita kad'ai take dunk'ule 'yan yatsunta tana bud'e su tunani kalan daban daban suka shiga zayartan kwanyarta... Har Ansar ya k'araso wajen bata sani ba saida taji salatin Annah kafin tayi saurin d'ago kanta a zabure tana dubansu.... Ganin hawaye na fita daga idanun Annah ya kuma firgita Zubaidah...
"Kuka ta fashe dashi tana fad'in" Sun kashe shi koh, nasan bazasu k'yalemu ba.... Annah ina yake I want to see him, pls take me to him....... Sosai Annah ta rik'eta tana girgiza kai itama tana hawayen take fad'in" Basu kashesa ba Zubaidah, Jalal na nan a raye.... amma sunyi masa illa sunji masa rauni.....
"D'agowa tayi tana duban Ansar wanda ke nan tasye jugum snn tace "Where is he? ...
" K'ak'aro kalamai yayi ya d"aura saman harshensa ya soma basu labarin duk abunda ya faru according to yanda ya sami labarin, snn ne yake tambayar su ko sun san Shattima, nan Annah ta fad'a masa alak'arsu da Shattima.
"Ansar ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Gobe da safe insha Allah zamu wuce gomben, a halin yanzu police are investigating the issue, na fad'a masu main suspect d'inmu Alh Kasim Dasuki ne sabida shika da grudges against Jalal, zasu tafi suyi interrogating nashi right away.... "Ya d'an ja fasali kafin ya shafi sumar sa yace " Annah to be honest with you zamanku a Suleja is risky considering the situation, kunga irin abubuwan da suketa faruwa a kwana biyun nan, Alh Kasim is capable of anything. He's a a monster, he do not have a heart, who knows what he's up to, especially yanzu da idon duniya ta masa cha, mutane sun soma gane wanene shi...
"Annah ta sauk'e ajiyan zuciya takai dubanta ga Zubaidah wacce har lokacin hawaye take da alama bata tare dasu tayi nisa wani duniyan...
"D'agowa tayi ta dubi Ansar kafin tace " Barr ina zamuje wa muke dashi cikin Abuja....
"Ansar ya d'an Saki murmushi kafin yace " Haba Annah don't talk like that zaki sa naji kaman har yanzu nida ku bamu zama d'aya ba,
"Gidana wadacecce ne, zan iya komawa chan sashen baki sai na bar maku cikin gidan kuyi zamanku har zuwa lokacin da zamu kammala Shari'an mu.... Yanzu bari na kira Hafiz ya taho da mota idan yaso sai ya d'auko su Hamma, kuma sai muje ku d'auki duk wasu kayan amfanin ku for the meantime.....
"Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Hafiz gamida matsawa d'an gefe kad'an...
"Annah kam kallo ta bisa dashi cike da mamakin mutunci da karamci irin na Ansar, Allah sarki tausayinsa na rashin iyayensa da 'yan uwansa ya cika zuciyarta, tabbas yau da iyayensa na raye zasuyi alfahari da samun d'a kaman Ansar, Allah yaci gaba da karesa daga sharrin masu nemansa da sharri, Tabbas addu'an Alkhairi shine kurum zasuyi ma Ansar dun ko kusa bazasu iya biyansa abubuwan da yayi masu ba....
******************
"Tunda suka shigo gidan su Hadiza sai washe baki ake ana d'add'ana kujeru, Kamal ma ya tab'a wann flower vase d'in ya tab'a wancen, sai kalle kalle da d'an k'uyanci suke, Ansar ya nunnuna masu d'akuna da komai da komai, harta su kitchen su Store kayan buk'ata na abinci da sauransu, gidan nasa babu laifi ya wadace su ba tareda tak'ura ba.. Zubaidah kam kallonsu kawai take burinta bai wuce gari ya waye ta ganta a garin Gombe ba...
"Bayan ya gama nuna masu ko ina ya sauk'o downstairs ya nufi d'akin bak'i ya karkad'e ko ina ya shiga jera kayansa a wardrobe, yana cikin shirya kayan wayan Asmah ya shigo masa, " Bayan sun gaisuwa irin ta masoya ta cika sa da shagwab'a shiko sai biyeta yake yana lallashinta snn ne ya soma fad'a mata abubuwan da suke faruwa har kwaso familyn Jalal da yayi ya dawo dasu gidansa, da kuma maganar tafiyarsa Gombe a gobe idan Allah ya kai rai...
"Sosai hankalin Asmah ya tashi da jin abinda ya sami Jalal, oh when will all these end, ta furta a hankali....
"Cikin sanyin muryarsa taji yace "Soon insha Allah my Love, zamuyi auren mu cikin sabuwar duniya maras rikici da fargaba da izinin Allah......
"Haka kurum taji jikinta yayi sanyi, cikin sanyin murya tace " Allah yasa my Attorney, murmushi yayi gaimda lumshe idanu kafin yace " Ameen my Attorney, kiyi bacci I'll call da safe kafin mu wuce kinji.. ..
"Sallama sukayi kafin suka katse wayar.... ..
"Kwance take saman gado rungume da rigarsa, tunaninsa ya ringa yawo a k'irjinta, ko wani hali yake ciki...... Ta goge hawayen da ya zubo mata gamida k'ank'ame rigarsa, tayita tuno abubuwan da tayi masa a baya, ta tuna irin hak'urin da yi da ita, ta tuna irin fad'i tashin da yake don ganin rayuwarta ta inganta, ta tuna irin sadaukarwa yake kanyi duk a saboda ita.... Kai anya ta cancanci Jalal, anya bai cancanci sabuwar mace ba wacce babu wani Mahaluk'i da ya lalata mata rayuwa,.... Take taji gaba d'aya she's feeling ashamed tabbas ta yarda tana son Jalal, amma tana tunanin ranar da za'ace ta soma rayuwar aure da Jalal,...... Girgiza kai ta soma da sauri tana mai dad'a k'ank'ame hannayenta had'i da runtse idanu, don kuwa wann tunani ba komai ya haifar mata ba, sai gano fuskokin su Labib da take cikin idanunta.... A haka Annah ta shigo ta sameta, ta zauna gefe da ita ta shiga lallashinta tana nuna mata addu'a shi zaiyi masu maganin damuwarsu ba kuka ba.... Mik'ewa Zubaidah tayi ta nufi bathroom don yin alwala tabbas Allah shine maganin komai.....
"Washe gari Annah har ta tashi ta had'a masu breakfast. Ansar ya shigo cikin shiri yana fad'in" Wow daga ina wann aroma d'in ke fitowa, Murmushi Annah ta sakar masa kafin tace " Good morning, oya have a seat....
"Zama yayi d'aya daga cikin kujerun Annah ta shiga serving nasa tana jansa da hira....... "Jin yayi shiru baya amsawa yasata d'ago kai tana dubansa, k'walla ta gani tab idonsa ya k'ura ma abincin idanu....
"Kujera ta d'an jawo ta zauna chan gefe dashi kafin tace " Ansar are you alright....?
"D'an goge k'wallan idonsa yayi ya k'a'karo murmushi kafin yace " I'm fine Annah, it just that you remind me of my Mum,.... You sounds like her, and she cooks delicious food, I missed her so much, inama tana nan a yanzu nayi devoting entier life d'ina wajen kyautata mata, even though nasan bazan mata kwatankwacin sadaukarwar da ta min ba sanda nake yaro,..... I couldn't have chance to be with her, all of them ....
"Tausayinsa ya cika zuciyar Annah, wani sabon tsana Alh Kasim ya kuma wanzuwa a zuciyarta, a hankali ta soma fad'in" Ansar kai d'a na gari ne wanda ko wata mahaifiya zatayi alfahari da kai, nasan addu'an alkhairi da kake masu yana isa garesu, snn shi wanda yayi sanadinsu bazai tabbata a doron k'asa yana zalunci ba, da sannu Allah zai kawo k'arshensa....
"D'ago Kai yayi yana gyad'awa kafin yace " Hakane Annah insha Allah k'arshen Kasim Dasuki yazo snn zai girbe duk wani abinda ya shuka.......
"Hadiza dake lab'e a k'ofa jinjina kai ta soma cikin zuciyarta take fad'in" Kenan duk yanda akayi Alh Kasim nada sa hannu a mutuwar iyayen Ansar..... Murmushi ta soma a hankali cikin ranta taci gaba da fad'in" Kai haba ai biri yayi kama da mutum, shiyasa ya tsaya kai da fata ganin Zubaidah taci wann shari'a bayan ba biyansa ko tasi ake ba, idan kuwa hakane lallai zatayi amfani da wann damar,.... Ta k'arashe zancen zucin nata tana mai kai duvanta ga family pic d'in Ansar dake ajiye saman console a corridor d'in..... Jin k'aran tafiya alamun ana sauk'owa daga stirs yasata saurin saita kanta ta k'arasa cikin parlorn suka soma gaisawa da Ansar da kuma Annah, sai faman fari'a take uwa gonar auduga....
"Zubaidah ce ta sauk'o parlorn ciki shiri itama, tana sanye cikin red atampa mai touches d'in sea blue, ta d'aura sea blue hijab wanda yake daidai gwiwarta, tayi matuk'ar kyau duka she's looking pale, da gani kasan she had a sleepless night.... Annah ta sakar mata murmushi suna masu amsa sallamarta itada Ansar yayinda Hadiza ta bita da wani mugun kallo k'asa k'asa.... Bayan sun gaisa Ansar kam d'aukan abincinsa yayi ya koma cikin parlorn ya zauna yana ci, nan Hamma ma ya fito ya zauna tareda Ansar suka ci abinsu tare, sosai Ansar kejin dad'in hira da Hamma...
"K'arfe tara da wasu 'yan dak'ik'ai na safiya suka d'auki hanyan Gombe, har waje Hamma da Hadiza suka raka su gamida masu fatan alkhairi snn suka bada sak'on gaisuwarsu a isar ma Jalal...
"Ansar kuwa saida yaja kunnen danga security dake masa gadi sosai da sosai, yace ya kula da Al'amarin tsaro sosai...
. "Suna tafiya Hadiza tayi shirinta tsaf ta had'a Hamma da Kamal da kallon tashan gwaigwai na yara (cartoon) tace bari taje kasuwa ta sayo masu kayan miya na fridge ya k'are...
"D'aukan k'aramin hoton dake ajjiye saman console tayi ta b'oye cikin jakarta kafin tayi ficewarta......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
64
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*A Big Shout Out To All The Readers 😻*
"Zaune yake gaban Mai Martaba, Ya tattaro nutsuwarsa gaba d'aya ya had'e waje guda, kan nan nasa duk'e a k'asa, kallo guda zaka masa ka gane ramar da yayi.....
"A hankali Mai Martaba ke karantar canzawan da Shattima yayi a 'yan kwanakin nan, yana son Shattima yana jinsa tamkar d'an da ya haifa, ko kusa baison ganinsa cikin wann yanyi... Ajiye takardun hannunsa yayi saman makeken darduman Alfarma dake malale a parlorn kafin yayi gyaran murya ya kirawo sunan Shattima da ainihin sunansa had'i da jefo masa tambayar da yasa gaban Shattima mugun fad'uwa...
"Abdullah...... Shin akwai abunda ke damunka ne.???
"Shattima ya d'an daburce yama rasa me zaice, don kuwa magana ta gaskiya bazai iya fad'awa Mai Martaba son tilon d'iyarsa yake ba, toh ma ta ina hakan zata kasance bayan har an bayar da Zahidah..... Muryar Mai Martaba ya kuma jiyowa yana fad'in" Abdullah kai d'ana ne , ka fad'a mun idan akwai abunda ke damun ka, ko tafiya Kanon ne baka shirya ba...... Ai Mai Martaba bai kai aya ba Shattima ya soma girgiza kai yana fad'in" A'a Abba dama... Ya d'an ja aya.... K'irjinsa yaci gaba da bugawa sabida k'warjinin Mai Martaba ya wuce gaban ka masa k'arya. Take dabara ta fad'o masa ya tuna kan Ya shigo an masa waya ana nemansa a asibiti patient d'insa ya farka.... Nan Ya soma fad'in"
"Abba dama...emm dama akwai wani abokina da 'yan fashi suka taresa a hanyarsa ta zuwa garin nan suka masa duka to the point of death, yanzu haka yana asibiti yana receiving treatments..... snn bashida kowa a garin nan sai ni, toooh sun min waya daga asibitin sun sanar dani ya farfad'o.... Toh Abba dama inaso na biya na dubasa idan akwai wani abu sai nayi settling kafin nayi tafiyar......
"Subhanallahi.... Mai Martaba ya fad'i fuskar sa cike da nuna damuwa. Snn ya d'aura da " Haba Abdullah yaya baka sanar damu ba, bayan kasan duk ranar juma'a mukan shiga asibiti duba marassa lafiya....
"Kai a k'asa Shattima yace " Ayimin afuwa Abba, amma jiya ne ma abin ya faru shiyasa ban sami zarafin sanar da kai ba. ....
"Shiru Mai Martaba yayi haka kurum Ya rasa dalilin samun faduwar gaba da yayi a dalilin wann labari da Shattima ya basa... D'agowa yayi bayan wucewar wasu 'yan dak'ik'ai kafin yace " Kaje Abdullah snn maganar tafiya Kano mun janyeta cikin satin nan har sai Allah Ya bawa bak'on ka lafiya.... Snn a kula dashi k'ark'ashin kulawar mu har Allah Ya basa lafiya.....
_(Tabbas ba k'aramin Al'amari bane zaisa gaban Sarki fad'uwa)_
"Kai a k'asa Shattima ya ringa jero godiya had'i da addu'ar girma da arziki wa Mai Martaba kafin yayi masa sallama ya fice......
"A daidai hanyar sashen Mai Babban D'aki ya hange Zahida alamun sashen Mai Martaba ta nufa.... Cikin sauri kaman me shirin kifawa haka ya fice ya nufi motar sa......
****************
"Damn it.... Damn it, cewar Alh Kasim had'i da buga table d'in dake gabansa kafin yaci gaba da fad'in" Sun mayar min da company kaman ofishin 'yan sanda.... It's all because of that stupid girl... If only I could kill her with my own hands......
"Mik'ewa Barr yayi yana shafa kansa da hannaye biyu kafin yace " Calm down Mr President.....
"No.. Don't ask me to calm down, I'm sick and tired of everyone accusing me just like that, da abunda nayi da abunda banyi ba..... Cewar Alh Kasim cikin tsananin fushi
"Barr yace Alh Kasim, first we need to think of who could have possibly do that, muddin aka ce anyi attacking Jalal toh fah mune za'a soma zargi, duk wanda yayi attacking Jalal fansa yake nema akanmu tunda mune dole za'a soma zargi....
"Alh Kasim yayi shiru yana muzurai kafin yace " That must be Hajiya Raliya and her daughter, sune kurum suke neman revenge akaina, sune zasuyi haka don ace ni nake yunk'urin kashe Jalal....
"Barr ya fashe da dariya kafin yace " This is ridiculous Alh Kasim.... Ta yaya zakayi tunanin Hajiya Raliya would do something terrible like this, .... That woman and her daughter are not capable of murder..... It's clearly someone's wants to see Jalal dead.....
"Toh waye kenan.. Alh Kasim ya tambaya yana mai tsare Barr da idanu....
"Tafe hannu Barr ya soma yana wata muguwar murmushi kafin yace " It's Umar.... That jerk is really insane, I'm quite sure he won't stop har sai yaga babu me numfashi cikin su hud'un, Jalal, Labib Salim da kuma Tariq... Kar ka mance he shot Salim a wajen nan, kar ka mance yanda yayi reacting ranan he's eyes full of seeking for revenge. Zaiyi komai just to be with that girl.... "
"Gyad'a kai Alh Kasim yayi yana huci kafin yace " I won't let him drag me into his mess.....
"Murmushi kawai Barr keyi kafin yace " Come to think of it....... Alh Kasim you are already in the mess ko ince we.... Don't forget mu muka jawo shi cikin wann mess d'in from the very beginning, we can't get rid of him just like that, ni dai a gani na what we should do kawai mu kirasa mu sanar dashi mun san komai he's behind of what happened to Jalal, yayi laifi ya b'uya a inuwar mu tunda mune main suspect na police... " He should just obey us ko meye muka saka shi yi tunda shid'in abokin aiki ne, if not we would expose his little secret.. Ko yaya kace..???
"Dariya Alh Kasim ya fashe dashi kafin yace " Shiyasa nake sonka Barr wann moleliyar kan naka ba a banza ba, now just call the idiot right away don karma yayi tunani zai b'ace mana, we have eyes everywhere..
************
"Tun daga nesa Mum ke rakub'e rakub'e tana tunanin shiga d'akin.
"Dad ta hanga ta cikin glass yana zaune kujera Me kallon na Tariq. A hankali tasa hannu ta tura k'ofar d'akin....
"Me kike yi a nan Dad ya tambaya yana watsa mata mugun kallo....
"Dan Allah ka barni nagan d'ana na rok'i arzikin ka kar ka koreni pls....
"Get out of here, you've no right over my son. Bakiji kunyan zuwa nan ba, you should be ashamed of your self.... I hate you I hate you Karima...... Ya k'arashe yana zama bisa kujeran had'i da goge hawayen idanunsa..... Kaman wanda aka mintsili Tariq haka ya bud'e ido.... Da sauri Mum ta k'arasa wajensa tana fad'in" Son Tairq my So....... Bata kai aya ba ya shiga k'ok'arin tashi dukda bandage d'in dake d'aure a kansa da wuyarsa kasancewar ya sami internal injury anyi masa aiki..... "Cikin zafin nama yake fad'in" Me kike yi a nan,.... Get out I don't need you in my life, just go back to your lover or what ever you call him.... You are despicable Mum I hate you for good, just get outta..... Muryarsa ya sark'e sakamakon tari da yaci k'arfin sa..... Hankalinsu gaba d'aya Ya tashi ganin yanda Tariq ke tari kaman zai amai da kayan cikinsa.... " Mum tayi kansa a rud'e tana kiran sunan sa yayinda Dad ya fice kiran likita a guje, nan d'aya daga cikin polisawa masu tsaron Tariq yabi bayan Dad........
****************
"Fitowarsu kenan daga cikin company d'in sakamakon wayar da Jane ta masa ta sanar dashi Hajiya Farha babu lafiya...
"Daga can bakin company d'in ya hangi Hadiza..... Wata murmushi ya sake don yasan ba'a ganin Hadiza haka nan... Da sauri yace da driver d'insa su koma cikin company, nan yasa security guda d'aya ya shigo da Hadiza....
"Suna zaune a wani meeting room madaidaici shida Barr security ya turo k'ofar yace da Hadiza " You can enter Miss.... Kallonsa kawai Hadiza tayi gamida tab'e baki tayi shigewarta don bawai ta gane me yace bane...
"Tun daga nesa Barr yake sud'e baki don kullum yayi tozali Hadiza haka yake yi, ....
"Alh Kasim ya mik'e yana murmushi kafin yace mata bissmillah ya k'arashe yana nuna mata kujera.
"Zama tayi tana watsa wa Barr kallo ganin idanunsa k'yam akanta, ba tare da b'ata lokaci ba ta gabatar masu da abinda ya kawota....
"K'uri Alh Kasim yayi ma hoton data mik'a masa yanason gano fuskar mutumin jikin hoton...... Marigayi Alh Ma'aruf Kumo ya ambata cikin zuciyarsa tabbas shine ko shakka babu wann Alh Ma'aruf ne snn wann matarsa ce wanda sukayi dabi a kotu..
"Murya har na rawa Alh Kasim yake nuna ma Hadiza hoton kafin yace " In.... Ina kika san wad'an nan.... ??
"Hadiza ta juya idanu kafin tace kai zan tambaya ina ka sansu, koda shike nasan kai kayi ajalinsu da zalunci irin naka......
"Alh Kasim ya kafeta da ido kafin yace " Be careful with your language lady......
"Tab'e baki tayi kafin tasa hannu ta fizge hoton tayi masu nuni da d'an matashin yaron dake jikin hoton tace hala kun gane wann fuskar...??
"Barr ya matso sosai yana kallon fuskar yaron, it's looks quite familiar, a ina yasansa??
"A fili Barr ya furta " ANSAR KUMO....... Shitttt.... Ansar Kumo. Ma'aruf Kumo, shakka babu d'ansa ne.....
"Daddy Ya mik'e gamida cire hulan kansa yayi jifa dashi yana fad'in" Make shirin faruwa dani, bayan na gama da Ma'aruf Kumo da iyalansa ashe na kashe maciji ne ban sare kansa ba..... No wonder that imbecile is doing all his best to defeat us in court, but I won't let that happen, I'll finish him just like I did to his family..... He has no clue what he's getting him self into..... Kallon Barr yayi kafin yace " Get me Faisal right now... Daga haka yasa kai Ya fice sai huci yake tamkar kububuwa, gaba d'aya ji yake duniyar na neman juya masa.....
"Hadiza ta mik'e tana fad'in" Ni kazo ka sallame ni dun wallhi bana aikin banza...... Barr Munir yasha gabanta yana wani tand'e harshe uwa tsohon maye yake fadin " Relax I'll take care of you..... Muje mota na baki kud'in aikin ki..... .
"Babu musu Hadiza tabi bayansa tana narka masa wata uwar harara, don ko babu komai tasan Habibun ta yafi wann fasali, hasali ma ba don kyau da Allah yayi masa ba da bata aure sa ba sabida lalurar da yake fama da ita......
*********************
*Prison*
"Zaune yake yayi jigum akan gadonsa wanda yake tamkar na 'yan makarantar kwana..... Kallon yanayin wajen kurum yake kanyi da mutanen dake wajen, wanda ko a mafarkinsa bai tab'a hango kansa a wajen makamancin haka ba, kai ko karen gidansu d'akinsa yafi nan balle ma'aikata..... Wai yau shi Salim Dasuki ne yake rayuwa a irin wann wajen, it's all because of her, that filthy mere girl, bak'awyiya Me kiwo, wai yau a dalilinta yake experiencing wann horrible experience d'in... This is a nightmare...... K'walla masu zafi suka ciko idanunsa..... Da k'arfin gaske ya daki bunk d'in dake gefe dashi.....
"OgaChuna Ya bud'e ido a hankali kafin ya malmalo wata ashar ya watsa wa duk wanda ya tadashi daga baccinsa gashi yau ranar hutunsa ne....
"Salim kam a maimakon ya basa hak'uri sai zaginsa daya soma, AI wata wawan tsalle ogachuna yayi ya cakumo Salim Ya shiga kilansa uwa Allah ne ya aiko sa...... "'yan d'akim kuwa sai ele suke suna wasa ogachuna..... Shigowar Labib kenan rik'e da bokiti, a tamanin ya yar da bokitin ya shiga k'watan d'an uwansa yana bawa Ogachuba hak'uri..... Ina Ogachuna bayaji baya gani, fad'i yake, let me teach this spoilt brat a lesson, ba kana gadara kai d'an Kasim Dasuki ba ko shi Kasim d'in ne yazo nan da kansa dole yabi ogachuna a sannu, coz this is my palace, I rules here....
"Saida Labib yabawa Ogachuna hak'uri ya tabbatar masa da zaran sun fita daga prison d'in nan zaiyi masa hiring good lawyer wanda zaiyi handling case d'insa shima ya fice snn Ogachuna ya hak'ura ya k'yale Salim, bisa wann yarjejeniya, har wani dad'i ogachuna yake ji snn yabawa Salim hak'uri shi kuwa sai foffozewa yake, ga jikinsa bai saba da wahala ba duk Ya wani tattauje Ya sauya kamanni....
"Labib ya jawo Salim gefe yana fad'in" You're very stupid you know, how could you got Into a fight with that d'an fashi.... Hararansa kawai Salim yake yana goge jinin bakinsa don sai yanzu yake ganin duk laifin Labib ne, idan da ace basu biye nasa ba, da yanzu yana nan tare da Kausar d'insa.. He did that to ruin his marriage with Kausar......
"Labib yaci gaba da fad'in" Guy we need to put up with everything around this place na d'an wani lokaci ne, we will soon get out of here and take our revenge Ya k'arashe maganar yana marking sauran kwanakin da Ya rage masu a shiga kotu jikin wata 'yar kalandar dake manne gefen gadonsa....
"Hararansa kurum Salim yayi gamida kwanciya kan gadonsa zuciyarsa ta cika fam da k'unci......
***********
"Ana kiraye kirayen sallan magrib suke shiga garin ta Gombe.......
Sam sam..... Sameena ce 😍
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
65
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Bayan ya gama bawa Shattima labarin duk abunda ya faru, Shattima ma ya basa labarin yanda akayi suka samesa, dukda jin jikin da Jalal keyi bai hanashi yima Shattima godiya ba cikin muryarsa da bai fita sosai....
"Shattima ya girgiza kai kana yace ka daina min godiya haka pls Jalal, idan da inada ikon cire maka ciwon nan gaba d'aya da nayi.... This is the least I can bro....
"Murmushi Jalal ya d'anyi kafin yace okay bro, can you plz help me with a phone, I really need to call my family, inason jin halin da suke ciki coz nasan who ever did this to me kasheni yayi niyyan yi..... Snn nasan their lives might also be in danger.... I need to protect ZUBAIDAH... Ya k'arashe cikin rage sauti sabida rad'ad'i na ciwo da yake ciki......
"Tausayin Jalal ya cika zuciyar Shattima, gaskiya irinsu Jalal basuda yawa a duniya, despite his situation but he still thinks of his family, .... Sauk'e ajiyan zuciya Shattima yayi kafin yace " Jalal babu abinda ya sami family d'inka, according to police your family already knew about this.... Snn banida contact d'insu I should have called them.. Amma most important shine ka sami lafiya... Already 'yan sanda suna bincike, sun so suyi interrogating naka amma sabida yanayin jikin naka Dr yace a bari saiko zuwa gobe idan ka dad'a samun k'arfin magana....
"Shiru kawai Jalal yayi yana tunanin for how long zai zauna a nan waye zai kula da Zubaidah like he does, snn wani hali Annah ke ciki yanzu yasan for sure ta shiga tsananin damuwa....
"Muryar Shattima ya tsinkaya yana amsa sallama. Wata mata ce mai kama sosai da Shattima saiko wata 'yar budurwa wacce bazata wuce shekaru sha biyu ba....
"Shattima ya mik'e yana fad'in" Umma sannu da shigowa..... Umma kam bata iya amsa Shattima ba sai kallon data bi Jalal dashi, haka kurum taga tamkar tasan mai irin fuskar....
"K'arasowa sukayi itada Ameera suka zauna a wani coach dake gefe sunai ma Jalal sannu...
"Jalal ya d'an soma k'ok'arin mik'ewa yana son zama, Umma tayi karaf tace haba haba d'ana Don Allah kar ka tashi na yafe ka wllhi, sannu kaji sannu da jiki....
"Jalal na murmushi yake d'an amsawa da k'yar, nan Shattima yayi introducing Umman sa da k'anwarsa ma Jalal....
"Suka soma gaisawa shida Umma, sai faman jansa da surutu take sai ka rantse sun saba tun tuni,.... Abun har ya soma damun Shattima don likita yace Jalal kar yayi surutu sosai sabida aikin da aka masa, Yasan halin Umma idan ta ringa jero ma Jalal tambayoyi sai yasha kunya kafin ta basa kunya gwara ya katse zancen...
"Ya kai dubansa ga Ameera wacce ta sake baki da hanci tana kallon Jalal kafin yace " Little bazaki gaida abokin nawa bane...
"Ameera kam da baki bashida burki koda yake sak Umma ta gado. Bud'an bakinta sai cewa tayi " Mr Handsome yaya jiki...
"Murmushi kawai Jalal yayi kafin ya amsa mata.....
"Takaicin duniyar nan ya cika Shattima, ai tuni ya mik'e kafin a kuma b'anb'aro Wata yace " Umma tashi na rakaku kinga yanzu za'a kira isha kinsan Baba baison tuk'in" Malam Halliru da dare.....
"Harara kurum Umma ta watsa masa don sarai ta d'ago nufin Shattima baiso taji labarin 'yan fashin da suka tare su Jalal ne.... Mik'ewa tayi ba don taso ba ta shiga sallama da Jalal, shi kuwa harga Allah yaji dad'in company d'in Umma, haka yayita masu godiya had suka fice.
"Shattima na jan hannu Ameera ta kuma turo kai ta k'ofar tana d'agawa Jalal hannu tace " Allah k'ara sauk'i Mr Handsome....
"Jalal kam sosai yarinyar ta basa dariya kai family d'in Shattima sun burgesa da gani shida k'anwar nan tasa Tom and Jerry ne dukda ratan dake tsakaninsu a shekaru, ga Umman nasu kanta akwai barkwanci....
"Wata uwar rank'washi Shattima ya zuba wa Ameera bayan sun fito daga ward d'in kafin yace " Wato tsabagen kin rainani iskancin naki har ya tashi akaina ya koma abokai na.....
"Turo baki Ameera tayi kafin tace " Toh ba gaskiya na fad'a ba yaya wllhi yafika kyau..... Gajeren tsaki kawai yayi ya shiga jawota da kunne har jikin mota...
"Umma dake zaune a owners corner tab'e baki tayi kafin tace " Ai idan bakuyi ba baku had'u inuwa guda ba....
"Mal Halliru gaisawa suke da Shattima lokaci guda yana dariyan fad'an Shattima da Ameera.... Har saida yaga ficewar motar su daga haraban asibitin kafin ya sa kai ya koma cikin asibitin.... A daidai hanyar da zai sada ka da ward d'in ya hangesu.... Cike da mamaki yake binsu da kallo don kuwa tabbas ya gane Annah da Zubaidah, sai dai bai shaida namijin da suke tare dashi ba.... Cikin sauri Shattima ya k'arasa garesu...
"Annah ashe kuna tafe barkanku, barkanku da zuwa, sannun ku... Shattima ke fad'i sanda ya k'arasa gamida mik'awa Ansar hannu sukayi masabah... Tuni Annah da Zubaidah sun gane Shattima, gaba d'aya suka shiga gaisawa had'i da jajen abinda ya faru da Jalal. .. Jin Annah ta soma jero masa godiya yasa sa saurin cewa "Mu k'arasanku ciki, Jalal d'inma bai jima da farkawa ba.... Shattima ya soma yin gaba yayinda suka d'unguma gaba d'aya suka bi bayansa ..
"Yana kwance saman gadon idanunsa a rufe, kaman mai bacci, yana sanye cikin wata rigar ash color da ake sanyama duk wani patient a asibitin, jin an tab'a k'ofa had'i da sallaman su yasa shi Bud'e idanunsa a hankali..
"Da mugun mamaki yake binsu da kallo don kuwa bai tsammaci ganinsu ba, two women d'in da yafi so a rayuwarsa, his mum and the love of his life matar sa Zubaidah....
"Tun daga nesa idanuwan su suka cika da k'walla.... Jalal ya d'an soma yunk'urin mik'ewa Annah ta k'araso da sauri ta rik'esa tana girgiza kai alamun kar ya tashi ... Duk iya k'ok'arinta ganin ta maida kukan ta inaa saida kukan ya kufce mata.... Fuskarsa take shafawa tana fad'in" Meyasa suka maka haka bayan baka masu komai ba, why why....... My little boy, my son..... Kuka yaci k'arfin Annah.
"Hannunsa maras cannula ya d'ago snn ya shiga goge mata hawayen yana girgiza kai cikin murya na marras lafiya yake fad'in" Pls don't Annah, ki daina kuka kinji Annah na.. Mu godewa Allah basu cimma burinsu akaina ba....
"Annah ta rik'e hannunsa ta sumbata kafin tace " Allah Ya baka lafiya Jalaluddeen. Allah Ya shiga tsakanin ka da mugu... "Murmushi kawai Jalal yayi kafin yace " Ameen Annah nah.... Ansar ya d'an mik'o masa hannu sukayi musabaha kafin suka soma gaisawa... Jalal zai soma yima Ansar godiyar d'awainiyar da yake da family d'insa Ansar yayi saurin kawar da zancen da fad'in" Don't even start patient if not nasa Annah ta goge ka cikin 'ya'yan ta coz I'm her new son.. kasan anfi son sabon d'a.... Gaba d'aya suka murmusa idan ka d'auke Zubaidah dake rakub'e bayan k'ofa, gaba d'aya she's feeling guilty for what happened to Jalal, she feel responsible.
"Waige waige ya d'an soma yi da kansa, gaba d'aya Sun d'ago nufinsa, neman Zubaidah yake, tabbas idan bai b'ata gani ba, Ya ga wann fuskar da a kullum yake kwana yake tashi da ita....
"Shattima da Ansar suka fice suna hira tamkar sun saba da juna...
"Annah ta juyo ta kalli Zubaidah wacce fuskarta ke duk'e, ba sai ance maka hawaye take ba, juyowa tayi tana duban Jalal wanda ya kafe Zubaidah da idanu kafin tace " barin d'an zauna a reception ta fice tana d'an murmushi tana goge ragowar hawayen dake idanunta.....
"A hankali ta d'ago idanunta da suke jik'e da hawaye ta sauk'esu kan kyakkyawar fuskar sa.... Kallonta kawai yake babu ko kyafta idanu..... Takowa ta ringayi a hankali tana tuno tun farkon had'uwarsu da irin k'alubalen da suka fuskanta ko ince wanda suke kan fuskanta har rana mai kaman ta yau.....
"Cak ta tsaya gaban gadonsa ba tare da ta iya furta koda kalma ba.....
"Hannu Jalal ya mik'a ya rik'o hannunta...... A hankali ta soma fad'in" I'm sorry.... I'm sorry Ya Jay....... Kuka mai k"arfi ya kufce mata..... Kwanciya saman k'irjinsa tayi ta shiga rusa kuka mai tsuma zuciya....
"Dukda rad'ad'in ciwo da yake ji bai hana zuciyarsa yin sanyin dad'i ba..... Hannunsa maras cannula d'in yasa ya dafe bayanta a hankali ya d'an rungumeta ido a lumshe yana shak'ar k'amshinta. A hankali ya soma furta " Please Zubaidah...... Shiru ya d'anyi sabida har cikin b'argo da tsokarsa yake jin zogin kukan nata.... A hankali yaci gaba da fad'in" Pls ki daina kukan nan, it hurts kinji...... Tsit yaji ta daina kukan sai ajiyan zuciya da takeyi, sharkaf ta jik'a masa gaban riga da hawaye..... D'an dafe jikin gadon yayi yana k'ok'arin tashi.... Cikin sauri ta mik'e tana k'ok'arin taimaka masa had'i da goge hawayen idonta.... Kallonta kawai yake yana murmushi had'i da d'an ciccije leb'e sabida wajen aikinsa dake masa zogi....
"Pillow ta saka masa jikin garu ya d'an kishingid'a .... Kallonta yake kanyi yanda taketa faman goge ragowar hawayen... Hannu ya bud'e mata kafin yace " Come here....
"Babu musu ta k'arasa ta haye gadon gamida shigewa jikinsa, a hankali yake shafa kanta yana fad'in" Zubaidah bana so kina blaming kanki bisa duk abubuwan da suke faruwa, non of this is your Fault Miss Beauriful...... D'ago ido tayi tana duban fuskar sa na d'an wasu dak'ik'ai kafin ta sadda kan nata k'asa ta soma fad'in " But I don't wanna see you suffering, you don't deserve all this.... I'm sorry to say, but I already made up my mind..... I'm dropping the charges,....
"D'agota yayi da kyau yana dubanta kafin yace " You what?? No no Zubaidah you ain't going to drop the charges, Ko kin janye k'ara ko baki janye ba Alh Kasim Won't Leave us alone so as his children Labib and Salim.. ... Kallonta yake ido cikin ido kafin yaci gaba da fad'in" I won't allow to do that.... " But Ya Jay..... Bata kai aya ba ya katse ta yana girgiza kai yake fad'in" We can't make peace with those heartless until they all paid for their evil crimes.... Pls Baby don't give up kinji.... You're not doing this for your self alone, you're doing this for the entire ummah, akwai mata da yawa who are suffering from your experience, but they couldn't have chance to talk,..... Kinsan irin dad'in da suke tsintar kansu ciki lokacin da labarinki ya isar masu, I'm quite sure zasuyi farin ciki, and this is not a REVENGE it is your right your freedom, don't back down baby, you are not alone.... You have us all.....
"Kallon Jalal take soyayar sa da tausayin sa na ratsa zuciyarta, he's an Angel fad'awa jikinsa tayi ta rungume.... Ya d'anyi k'ara sabida ciwon sa data d'an fama..... Da sauri ta mik'e tana fad'in" Oh my I'm sorry, I'm sorry kaji, does it hurt.... Kallonta kawai yake da siraran idanunsa yanda duk ta daburce gaba d'aya..... Mak'aleta ya kuma yi da side guda snn ya soma fad'in" Hey relax is nothing serious...
"Ta d'an kallesa tace are you sure..?
"Gira ya d'aga mata dimple d'insa sai lotsewa suke kafin yace " Naji sauk'i tunda nayi tozali dake, oya tell me, what happened kika rame haka, dukda hijab ne jikin ki I can see that you lost weight....
"D'an turo baki tayi kafin tace ba ba kaine ba, I was afraid I might lose you....
"Cike da jin Dad'in kalamanta yake shafa 'yan yatsun hannunta kafin yace " Nothing will tear us apart kinji sweetheart oya give me a kiss ya k'arashe yana turo mata pink lips d'insa wanda suka k'ara jazir kaman fresh tomatoes.... Zaro ido waje tayi tana dubansa .... Kashe mata ido yayi kafin yace " Yeah a speedy recovery wishing kiss...
"Tafukan hannayenta tasa ta rufe fuskanta dasu.... Murmushi Jalal yayi kafin yace " I'm serious miss beautiful......
"Turo baki ta kuma yi kai a langab'e kafin tace " Pls Ya Jay.... Fah zan maka kuka...
"Okay sai na kira Dr Khaleesat ai... Kukan shagwab'a ta soma masa yayi saurin kwantar da kanta saman k'irjinsa kafin yace " Okay okay fine, but you I'm owing you a kiss ko bacci kike zan amshe kiss d'ina....
"Bacci ina zaka ganni bayan anjima kad'an zamu tafi masauk'in mu...
"Hannu yasa yana zame hijabinta yake fad'in " You must be kidding baby, ina kuma zakije after all kinzo jinyar mijinki ne.......Knocking d'in da akayi ne ya katse masu zancen nasu yayi saurin maida mata hijabinta snn yabada izinin shigowa, Zubaidah zata sauk'a daga gadon yayi saurin rik'eta yana rad'a mata stay right here baby....
"A hankali take fad'in" Ya Jay pls mana..... Daidai nan Dr ya shigo rik'e da files..... Murmushi ya sakar masu kafin Ya soma gaida Jalal, Zubaidah ma ta gaidashi cike da jin nauyin yanda Jalal ya hanata sauk'a a gadon.... Su Annah ne harma dasu Shattima suka take wa Dr baya....
"Wayyo wani sabon kunya ya mamaye Zubaidah, kaman gadon Ya tsage ta shige ciki, .Dr yace amma dai wad'an nan sabin aure ne...
"Ansar yayi karaf yace " Newlyweds ne ai Doc,
"Dr yayi murmushi yace I see..... Jalal dai murmushi kawai yake yi yana satar kallon Zubaidah... A hankali ta samu ta zame ta sauk'a daga gadon sanda Dr ya soma bayani wasu Shattima.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
66
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION (United we stand Divided we fall) 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*For All My Avid Readers 😻*
" Dole Shattima yak'i su Annah da Ansar suyi kwanan hotel. He keeps insisting saidai su kwana a gidan su tunda akwai wadataccen masauk'i ..
"Kai tsaye hotel d'in da sukayi booking d'in suka wuce suka d'auko kayayyakin su, Ansar bai damu ayi masa refunding kud'in sa ba..
"Saida suka biya asibiti suka ajjiye wa Zubaidah kayanta da d'an kayayyakin Jalal data taho masa dasu snn suka nufi gidan su Shattima..
"Ummah gaba d'aya ta rasa ina zata saka su sabida karamci, a tak'aice dai sun samu tarba mai kyau da dattako a gidan Baba Waziri wato gidan su Shattima.
"Ansar d'akin bak'i aka sauk'e sa wanda yake a kusa da d'akin Shattima yayinda Annah ta sauk'a a d'akin Ummah, Nan fah Ameera ta ringa zubawa Annah surutu musamman dataji tare suka taho matar Mr Handsome, gaba d'aya ji tayi ta k'agu taga Zubaidah. Saida Ummah ta shigo ta korata parlor kafin ta fice ta k'yale Annah, Baba Waziri na shigowa gida Shattima da Ummah sukayi iso masu Annah. Sosai yaji dad'in sauk'an su a gidan da Shattima yayi snn yayi masu jajen abinda ya faru da Jalal, Ya shaida masu ranar sati wato ranar juma'a shima zai duba Jalal d'in insha Allah. Dashike yana daga cikin tawagan Mai Martaba masu raka sa dubiyar asibiti duk bayan sauk'owa daga sallan juma'a..
"Sosai Annah tayi masu godiya da wann karamci nasu..
"Abincin Annah har uwar d'aki aka kai mata, Su Ummah ba'a sama ba'a k'asa sai jan Annah da labari take, Annah kuwa ganin irin sakewa da dattako na Ummah dukda ta lura tanada son jin k'wak'waf hakan bai hanata gaya mata duk abubuwa na iftila'i da suke fuskan ta ba musamman Zubaidah da Jalal.... Sosai Ummah ta tausaya masu musamman Zubaidah, harda d'an share k'wallan ta, gaba d'aya Ummah sai tayi sanyi, bayan wucewar d'an wani lokaci suka ci gaba da labarin su tamkar sun jima da sanin juna......
****************
"Tea ta gama had'a masa half cup snn ta k'arasa jikin gadon had'i da mik'a masa cikin tsanaki...
"Bai karb'a ba sai kafe ta da idanunsa masu rikirkita mata lissafi da yayi...
"Oh gosh ita fah bata jure wann kallon nasa ta fad'i cikin zuciyarta... Kaman yaji abunda tace ya koma ya kwanta had'i da lumshe idanu...
"Zaro ido waje Zubaidah tayi tana tambayar kanta " What's going on with him, kodai yaji zancen zucin nawa ne... Ko kuma dogging shan tea d'in yake son yi ba, wani b'angare na zuciyarta ya raya mata hakan....
"A hankali ta bud'e murya ta soma ambato sunan sa " Ya Jay ka tashi ka sha tea d'in it's done..... "Shiru ya mata still idanunsa a lumshe...
"D'an rausayar da idanu tayi kafin ta d'an d'ale gadon gefen sa ta kuma kirawo sunan sa... Ido a lumshe yake fad'in" I'm okay bazan iya sha ba...
"Ta d'an marairaice murya tace " But you heard what Dr said earlier, you need something in liquid in your system, oya pls tashi ka sha ko kad'an ne.....
"Mik'ewa ya d'an yi ta jera masa pillows ya kishingid'a kafin ta kuma mik'a masa mug d'in" Mak'e mata kafad'a yayi tamkar k'aramin yaro kafin yace ." Zatayi magana yayi mata nuni da hannunsa mai cannula kafin yace " Baby can't hold the cup,... Ya fad'i cike da shagwab'a...
"Okay fine, idan dai zaka sha zan baka a baki.... Ta fad'i sanda take kai cup d'in bakin sa.... Jalal kuwa kashe mata idanu yayi kafin yace " that will be even much better,.... Haka tayita basa a baki har saida yace mata ya ishe shi... Kwanto da ita gefen kafad'arsa yayi kafin ya soma tambayar ta school tunda yasan tana gab da rubuta jarabwan shiga makarantar gaba da sakandare....
"Kina karatun kuwa...? Ya tambaya sounding serious...
"Gyad'a masa kai tayi kafin tace" Na taho ma da books d'in you'll help me with mathematics koh...
"Shafa kanta yayi kafin yace " Good girl shiyasa nake k'ara sonki nasan you won't neglect your studies sabida tunane tunane, what about Dr Khaleesat, ta dawo kuwa...
"Girgiza kai tayi kafin tace " She's on vacation, tazo shekaran jiya tayi mana sallama akan yau zasu wuce Singapore da mijinta, and. And... We've talked alot.....
"Gyad'a kai yayi kafin yace " Yayi kyau,... Ya rik'o yan yatsun hannunta yana murzasu a hankali idanunsa a lumshe yake fad'in" Zubaidah thanks for coming into my life....
"Karkatowa tayi gamida k'ura masa idanu ba tareda ta furta koda kalma ba.... Sun jima a haka kafin ta d'an soma k'ok'arin zare jikinta... " Bud'e idanu yayi yana dubanta kafin yace " ina zakije..?
" Books d'inta dake saman d'an wani stool gaban couch ta nuna masa kafin tace " Karatu zanyi, you also need some rest, kaga wajen aikin ka har waje biyu ne nasan by now sun maka tsami, ka d'an jima kana zaune ai ya kamata ka kwanta haka nan, is getting late ma...
"Gyad'a mata kai yayi kafin yace " You're right sweetheart,.... Murmushi tayi ba tare da ta furta komai ba ta shiga gyara masa wajen kwanciyar.... Idanunsa akanta duk wani movement nata ya d'an rik'e yatsan ta guda yace " Ke a ina zaki kwanta....
"Nuni ta masa da couch d'in kafin tace " Don't worry it's okay by me, beside couch d'in wadacecce ne, ta jawo bedcover ta rufa masa kafin tace " Oya go to sleep, and if you need anything I'll be right here.... Ta k'arashe tana murmushi.... Har ta juya taji ya kuma rik'o hannunta.... Kallonta yake babu ko k'yafta idanu har saida ta kasa jurema kallon nasa ta sadda kanta k'asa.. " Daddad'an voice d'insa ta jiyo yana fad'in" Miss Beauriful can't I have a goodnight kiss...???
"Gaban Zubaidah yayi wani irin fad'uwa jin sigan da yayi maganar da ita da kuma irin murza yatsun hannunta da yake yi cikin tsanaki.... Sunfi minti uku a haka tama kasa d'agowa ta dubesa... D'an tasowa yayi ya kai bakinsa saitin kunnenta kafin yace " You owed me 2 kisses, oya je kiyi karatunki I'll be watching your beautiful face har nayi bacci..... A hankali ta janye hannunta tana murmushi har ta isa wajen karatun nata.....
"Idanunta naga book amma rabin hankalinta naga Jalal ne, idan ta d'an sata kallon sa saiko tayi sa'a shima ita yake kallo.... Kashe mata ido yake yi had'i da murmushinsa mai kashe 'yan mata... Murmushi kawai Zubaidah keyi kafin ta d'aga book d'in sama ta rufe face d'inta dashi....
"Can dai taga kaman yayi bacci don kuwa duk subansa da takeyi idonsa a lumshe take gani, a hankali ta bud'e jakarta ta ciro nyt wears d'inta yalwataccen riga da wando cottons ta nufi bathroom a hankali snn ta canza kayan had'i da rufa hijabinta.... Batasan duk akan idon Jalal tayi komai ba... Tana shirin kwanciya bisa couch ta tsinkayo voice d'insa yana fad'in" Baby pls can I ask a favor..??
"A d'an zabure ta juyo tana ware idanu kafin tace " Sure"
"Jalal ya murmusa kafin yace " Could you please sleep beside me... Please..... Ya k'arashe cikin salo na rage sautin voice d'insa...
"K'irjinta sai dukan uku uku yake, she can't say no to him.... A hankali ta soma takowa har gaban gadon sa kafin ta tsaya cak.... D'an mirginawa yayi kasancewar babu drip a hannun nasa, kunsan dai yanayin gadon maras lafiya yanda yake bashida girma, ta d'an d'ago idanu tana dubansa kafin tace " Ai zan tak'ure ka Ya Jay....
"Hannunta ya kamo kafin yace " Pls Baby I just want you here by my side, don't say no kinji...
"D'an murmushi tayi wanda iyakacinsa fatan baki kafin ta d'ale gadon k'irjinta naci gaba da bugawa da sauri da sauri, abune wanda bata tab'a yinsa ba kwanciya gado guda da namiji, gashi gadon tak'urarre wanda tasan dole jikkunan su Ya manne dana juna, haka ta kwanta cikin runtse idanu.... Ahankali taji yana zame hijabin dake jikinta, wayyo Allah Zubaidah ji tayi gaba d'aya ta soma shaking...... Cikin kunnenta yake rad'a mata "Calm down Baby I got you..... Ji tayi Ya sakalo hannunsa gamida rungumeta tsam cikin jikinsa ba tareda yayi la'akari da ciwon dake jikinsa ba.... Haka k'irjin Zubaidah ya ringa bugawa da sauri da sauri, gaba d'aya ji tayi baccin ya kasa zuwa mata... Shima Jalal abubuwa ne da dama sukayita ziyartan sa, a hankali yana shak'an daddad'an k'amshinta bacci ya soma d'aukan sa, cikin kunnenta Ya rad'a mata " Goodnight baby I love you"""
"Har cikin b'argo da tsokan ta taji kalaman nasa, a hankali ta kuma lumshe idanu gamida sakin murmushin da batasan daga ina ya bijiro mata ba... A haka bacci mai dad'i yayi awon gaba dasu....
_Nima Sameena nace "Asuba ta gari *ZubyJay*😘"_
**************
"K'arfe shabiyu na talatainin dare tana bugawa Tariq ya sauk'o daga saman gadon sa da k'yar, tabbas yasan by now polisawa masu tsaron k'ofar sa sunyi bacci , Hood sweater d'insa Ya d'auko ya saka a hankali sanda yaji motsin Dad d'insa a bathroom kafin ya sad'ad'o zuwa k'ofa cikin sand'a ya Bud'e k'ofar.... Yakai dubansa ga securities d'in ya tabbata bacci suke, a hankali ya d'aga kai sama yana duban CCTV Cameras, cikin sauri yaja hular sweater d'in ya rufe kansa da fuskar sa gaba d'aya kafin ya soma tafiya sauri sauri yana rirrik'e gefen cikin sa..... Yana ficewa daga corridor d'in Dad ya fito daga toilet, nan yaga wayam babu Tariq, a tamanin ya fito waje yana neman d'auki, ai a sittin polisawan nan suka ware idanun su, cikin sauri d'aya ya danna intercom d'in dake hannunsa ya sanar a gate, kafin suka fice gaba d'aya harda Dad.... Nan da nan asibitin ya kaure da k'aran security Alarm.......
"Ta k'ofar baya yayi niyan fita saidai ina securities sun samu labari, k'ok'arin tsere masu yake yana so ya haye garu saidai sabida ciwon dake jikinsa bazai iya ba,... D'aya police d'in kuwa fad'i yake pull right there, stop or I'll shoot.... Dad cikin tsananin tashin hankali yake fad'in" Tariq ka tsaya ka tsaya pls son kar su harbe ka..... Kan kace me sun capke sa.... Sai faman buge buge yake yana fad'in" Let me go, let go of me, I'm not a criminal, just let me goooo....
"Cuff him d'aya police d'in ya fad'i lokaci guda yana magana da ogan su da intercom d'in dake hannunsa..... Dad yanaji yana gani aka saka ma Tariq handcuffs... Nan Ya zube yana rirrik'e cikinsa wajen da aka mai aiki.... Nan da nan asibiti ta bada ambulance ba'a zarce dashi ko ina ba sai asibitin cikin prison.....
"Washi gari kan kace me labari ya baza garin Abuja.... Asmah ce take sanar da Ansar sanda suke waya suna kan hanyar su ta zuwa asibiti wajen Jalal.... Ansar ya jinjina lamarin kafin ya sanar dasu Annah da Shattima... Zancen suka ringa yi har suka isa asibitin......
"Jalal ma sosai ya jinjina lamarin, Zubaidah kam bata tofah komai ba, Jalal yanata santa kallonta don yasan dole mood d'inta ya canza tunda babu abunda ta tsana kaman taji labarin su, k'arshe ma ficewa sukayi ita da Annah ko breakfast d'in da suka kawo bata ci ba, dole ta d'aga Annah kan ta rakata su d'an zaga waje....
"Jalal kam yaji dad'i ficewar nasu don dama yana so su sami Time shida Ansar su tattauna, Shattima ma sallama ya masu don yanada uzuri...
"Ya rage daga Jalal sai Ansar, nan suka soma tattauna lamarin..... A haka wasu police guda biyu suka shigo don interrogating Jalal.......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
67
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION (United We Stand Divided We Fall) 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where are you my Shawty💕 this one's for you sweetheart.... 😍😘*
"Zaune suke saman d'aya daga cikin kujerun shak'atawa da aka k'awata asibitin dasu, jefi jefi mutane suke wucewa kasancewar wajen Amenity ne ba kowa da kowa ake kwantarwa ba kaman general...
"Zubaidah taci gaba da fad'in" Annah zan dropping charges d'in nan kurum kowa ya huta, ever since I pressed charges abubuwa suka dad'a rincab'e mana, I'm afraid Annah ... Nasan they Won't Leave us alone idan ba janye k'ara nayi ba....
"Hannayenta Annah ta rik'o kafin tace " Zubaidah Allah yana tare da mai gaskiya kar ki mance... Snn wann gwagwarmaya da kike yi bama kanki kurum kike ba, wa matan duniya kike yi, snn Alh Kasim ya zalinci mutane da dama wanda na tabbata ta dalilin wann sharia naki da ake yi Allah zai toni asirin duk wani muggan ayyukan sa... Kar ki damu daughter nasan you worried so much about Jalal, but he's doing this for us, ko kin janye k'ara ko baki janye ba The Dasukis Won't Leave us alone as they promised, kar ki mance yanda har cikin gida Labib da guards d'insa suka shigo sukayi cin kashinsu son ransu, Allah ma yace ka nemi hakkin ka, kinyi hak'uri da irin bak'in ciki da k'unci da suka jefa rayuwar ki, kinyi hak'uri lokacin da suka Aura maki mijin da ba zab'i ne a gareki ba... "Da sauri Zubaidah ta d'ago tana duvanta jin tace Mijin da ba zab'inki ba....
"Annah ta murmusa kafin tace " Na sani a yanzu shine zab'in ki, ina nufin a lokacin da abun ya kasance, a lokacin da bakisan wanene Jalal ba, a lokacin da baki gane duk duniyar nan bayaga Hamman ki bakida masoyi tamkar Jalal.... Annah ta d'an murmusa kafin tace " He has a big heart he's... just an incredible.....
"Murmushi kawai Zubaidah tayi tana duban Annah kafin ta hangi polisawa suna fitowa daga bakin ward d'in.... Mik'ewa sukayi gaba d'aya suka nufi d'akin Jalal d'in......
*****************
"No... No... No this can't be, Balele da gaske kake Baffah na babu.... Umar Ya fad'i sanda siririyar hawaye take gangaro masa...
"Daga d'aya b'angaren Balele yace " Umar itadai duniya budurwa ce amma ta wawa, babu abinda zan iya k'ara fad'i maka iyaka nace mun riga mun sallaci mahaifinka mun kaisa gidan sa ta gaskiya, don kuwa wasiyar sa ce cewa bai yarda ka sallaci gawansa ba, ni nayi nawa tunda na fad'a maka, kana iya zuwa idan kaga dama...... Daga haka ya katse wayar.....
"Gijiiff Ya zauna saman couch yana maida numfashi a hankali, wann wani irin rayuwa ce, shi bai sami albarka iyayensa ba, shi bai sami Zubaidah ba, uwa uba he's running out of cash.....
"Girgiza kai ya soma tamkar tab'ebb'e ya soma fad'in" No... No I won't let mutuwan Baffah ya b'ata mun plans d'ina ba... All that I planed... I won't back down until I take Zubaidah back, she's mine , tawace ni kad'ai babu wani mahaluk'in da ya isa ya mallaketa alhalin ina nunfashi, I'll take her back and kill them all one by one.... *Sune Sila* sune *Sanadin Rabuwar mu* *Su suka ja min* na rasata... They are all monsters, *Jalal* ya furta a hankali kafin yace " He's my biggest enemy, that coward must die...... Ya k'arashe yana hangan kwalbar giyan da Zulaihat ta bari a parlorn...... Cikin sauri ya k'arasa ya suri kwalban..... Ya jima yana juya kwalban yana tuno ranar shiga kotu ta farko da ya hangi irin kallon soyayyar da Jalal da kuma Zubaidah suke aika ma juna wanda duk iyaka zaman su da soyayyar da suka sha a baya bata tab'a masa ba....... Da k'arfin gaske ya finciki marfin yayi jifa da ita saida ta daki glass d'in window kafin ya d'aga sama ya soma kwankwad'a this is his first time don bai tab'a Sha ba... Wata uwar tsami yaji ta ziyarci saman harshen sa..... Runtse idanu yayi da k'arfin gaske Ya ringa kwankwad'ar barasan nan tamkar aikosa akayi..... Saida ya d'aga kwalba guda yana sunbatu shi kad'ai....... A haka bacci ta kwashe sa a wajen.....
_(Allah ka rabamu da bak'ar zuciya wanda zata kaimu ga aikin danasani... Ameeen)_
*******************
*Washe Gari*
"Alh Kasim dake tsaye gefen gadon Mummy da take ta d'irkan drip yayi tsaki a hankali kafin ya k'ara trying lambar Barr Munir still jinta yayi a kashe.... Da k'arfi Ya daki gefen gadon yana furta " Damn it... On your phone you idiot....
"zumbur Mummy ta bud'e idanunta tana kallon mijin nata, d'an matsowa kusanta yayi kafin yace " Farha kin tashi... Bata amsa sa ba sai cewa tayi " Salim.... Ina Salim yake, I want to see my boy, pls Call him for me..... Ta k'arashe tana k'ok'arin mik'ewa.....
"Wani tsakin Daddy Ya kuma yi kafin ya maidata ya kwantar yace " Farha wai bakiji abinda Dr yace bane, ki daina saka damuwa ma ranki wai ko so kike ki sami matsalan shanyewar b'arin jiki, idan kin kwantar da hankalin ki an kusa shiga kotu kuma na maki alk'awari this time around I won't let you down, zan kawo maki precious son d'inki har cikin gidan nan, I promise you that kinji Farha nah.....
"Gyad'a masa kai tayi tamkar k'aramar yarinya kafin tace "When's the heroine..???
"D'an jimm yayi kafin ya tsuguna ya rik'e hannayen ta yace soon my love, Salim zai dawo gida soon, and I'll make them pay...... Ya k'arashe yana furta Jalal I'll soon come for you, but sai na gama da incompetent Attorney d'in naku wanda baisan meke masa ciwo a rayuwa ba, Zaku san da waye kuke yak'i little brats...... A hankali duk yayi maganganun nasa wanda sai ka kasa kunne sosai kafin kaji.....
"Jane ce ta shigo da ruwa a glass cup saman d'an k'aramin plate ta gaida Daddy kafin ta ajiye gefen bedside.... Kallon agogon hannunsa ya kuma yi k'arfe 10:30am daidai, ganin Mummy ta koma bacci yasa sa zame hannunsa daga rik'on da tayi masa kafin ya fice zuwa parlorn k'asa ya shiga neman layin Faisal bugu biyu Faisal ya d'aga cike da rusuna...
"Faisal I want you to get me Attorney Kumo cikin awanni ashirin da hud'u, bana so a sami failure .... I confide this mission to you alone, ..... I repeat bana so a sami failure....
"Tamkar Alh Kasim na kallon sa haka ya gyad'a kafin yace " Mission accomplished Boss... Daga haka Alh Kasim ya soma katse wayar yana wani irin huci shi kad'ai..... Gama wayar keda wuya Attorney Munir ya kirasa..... Saida ya rakkaba uban tsaki kafin ya d'aga wayan yana fad'in" Where the hell have you been Attorney..??
. "Daga d'aya b'angaren Barr Munir yace " Calm down Alh Kasim, mu gaisa mana first....
"Tsaki Daddy yayi kafin yace " Ba wann bane a gaba na, get me that idiot right now, yanzu yanzu babu b'ata lokaci....
"Barr ya fuzar da iska kafin yace " I hear you, amma wani idiot kake magana...
"Umar Of course... Daddy yace cikin katse sa....
"Murmushi Barr yayi kafin yace " At your service Alh Dasuki, but first Yaya jikin k'anwata....
"Cike da k'osawa Daddy yace " da sauk'i sosai.... Sai na ganka, ina gida yau coz bazan fita company ba, apparently idon police yanzu na kan company d'inmu, irin wann had'uwar a gida ya kamata mu ringa yinsa.... Daga haka katse wayar yayi kafin ya mike Ya ringa zagaya parlorn shi kad'ai k'unci pal zuciyarsa......
**********************
" Whatt..! Kana nufin Barr Kumo baya gari, where the heck did he go..... Okay okay fine kazo gida Maitama straight, ..... Daga haka ya katse wayar yana tsaki... Juyowa yayi yana duban Barr da ya had'e hannaye biyu yana kallonsa kafin yace " I just can't believe this, dukansu biyu basa nan, ka sake kiran Umar ka fad'a masa bana wann game d'in dashi, idan yana son kansa da lafiya yazo gidan nan yanzu yanzu....
"Tab'e baki Barr yayi kafin yace " Ubansa ne fah ya mutu aiko kaga dole ya tafi ...
"Wani uban tsaki Alh Kasim yayi kafin yace " Uwar tasa ma ta mutu for all I care.. Lambar Umar Ya shiga latsawa lokaci guda......
*Kuyi hak'uri na rashin jina kwana biyu... Wllhi I'm pretty much occupied ne kwana biyun nan, you know how New Year is....biki everywhere, but just bear with me for the meantime, insha Allah I'll make it up to you by updating everyday..... Just stay tuned guys... 😍😘*
[1/23, 22:27] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
68
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Driving yake yana kuka tamkar yaro, he couldn't help it, zuciyar sa gab take da tawarwatsewa.... K'aran da wayarsa tayi ne yasa sa rage speed kafin ya duba, ganin mai kiran nasa yasa sa sakin wani mugun tsaki kafin ya ajiye wayar.... Kiran ta kuma shigowa, a hasale ya d'aga yana fad'in" Me kuke nema a wajena,...???
"Daddy Ya murmusa kafin yace " Where are you, ina son ganinka right now..
"Murmushi takaici Umar yayi kafin yace " I thought I have made my self clear, stay out of my life, Kai ka jawo na rasa mahaifina if only ban biye ma son zuciya irin naku ba..... "Katse Alh Kasim yayi da fad'in" Shut the hell up you idiot, on the contrary kai ka zab'i hakan ma kanka, .... Wait a minute, kar kace mun zaka giving up, well koma meye kake shiryawa a cikin zuciyar ka I have to remind you this.... You can't run away from me, how do times do I have to tell you, already kana cikin mess d'in nan, yanzu duk ba wann ba, abu guda nake so ka min, aikin da ka soma you must accomplish it, Apparently Jalal yana babban asibitin garin Gombe, kasan yanda za'ayi ka k'arasa aikin ka, what I mean finish him once and for all, kasan na riga da nasan little secret d'inka, so just go ahead and kill him... Sorry for your lost..... Daga haka ya katse wayar....
"Jifa da wayar Umar yayi kafin ya soma magana shi kad'ai.... " That imbecile is still alive, murmushi yayi mai cike da ma'anoni kafin yaci gaba da driving d'insa.....
****************
"Annah pls don't say no, Ya kamata ki koma gida, hankalina bazai tab'a kwanciya ba muddin nidake duka muka zauna a asibitin nan alhali bamu tare da Zubaidah, Annah ke kad'ai ce nasan zaki kula min da ita, pls kiyi hak'uri ku tafi bana so tayi missing jarabawarta sabida ni, just go pls kinji Annah na, don't worry about me, I'll be fine insha Allah, snn I'm not alone here, akwai Shattima da Family d'insa, pls kinji Annah.......
"Sauk'e ajiyan zuciya tayi tana kallon fuskar sa kafin ta shiga gyad'a masa kai a hankali tace " Shikenn Jalal zan tafi kaman yanda ka buk'ata but as soon as Zubaidah ta gama da jarabawan ta zamu dawo....
"Murmushi yayi kafin yace " Before then ma anyi discharging d'ina insha Allah... Ya rik'o hannayenta yana murmushi kafin yace " Always remember that I love you... You are the best Mum on Earth..... Rungume juna sukayi nan k'wallan da Annah take mak'ewa ya fito.... Shafa fuskar sa ta ringa yi tana masa addu'an samun lafiya....
"D'ago kai yayi ya kalli Zubaidah da kanta ke duk'e a k'asa, Annah ta kai duvanta ga yanda ya kafe idanunsa, a hankali tasa bayan hannunta ta share k'wallan ta kafin ta fice ta basu waje.....
"D'an sauk'owa yayi daga saman gadon yana d'ingisawa kafin ya k'araso gaban ta..... Bai iya ce mata komai ba sai rungumeta da yayi sosai cikin jikin sa.... Nan Zubaidah tayi bursting cikin wani irin kuka mai tsuma zuciya.... Hugging d'inta yayi very tied har saida yaji wajen ciwonsa na masa zogi kafin ya soma fad'in " Take care okay, just take care of yourself, always remember that you are my world, I love you ultimately kinji sweetheart.... Kar ki mance ko bamu sake had'uwa ba, don't give up kinji..... Ya k'arashe cikin rawar murya.....
"Kuka ta kuma fashewa dashi tana girgiza kai.... Fuskokinsu sunyi jajazir had'e karan hancinsu waje guda yayi ido a lumshe ya aika mata da light kiss kafin yace " I wish you success in your exams, and.. And when ever you thought of me, just say a word zaki ganni a gabanki... Ya k'arashe cikin sigan zolaya....
"Murya na rawa take fad'in" I won't let you down insha Allah, zan tsaya nayi exams d'ina da kyau kaji snn kullum zan rik'a maka addu'a.... Murmushi yayi mai bayyan dimples d'insa kafin yace " I know you will.... Oya come here, kukan nan ya isa haka....Suka kuma hugging juna, sun jima a haka kafin Ansar yayi knocking a k'ofa.....
"Jalal ya kuma damk'a wa Ansar amanar family d'insa kafin suka tafi cikin tsananin kewa da alhini da soyayyan junan su... A ranar haka Jalal ya wuni cikin damuwa da kewar iyalan sa dukda Shattima yana nan tare dashi wuni guda, yanzu Mai Martaba har hutu ya bawa Shattima sabida abokin sa dake asibiti.....
*************
"Dandatson mutanen da ya gani cike a k'ofar gidansu ya tabbatar masa cewa gaskiya ne mahaifinsa ya rasu.... Tun daga nesa mutane ke masa gaisuwa, kan ya isa cikin gida kuwa labari ya riske Innah, wani sabon kuka ya kuma b'alle mata musamman da ta tuna Ummaru shine sanadin ciwon mijin ta....
"Koda ya shigo ciki haka Mata suka ringa masa ta'aziya, wasu kuwa k'us k'us suka ringa yi suna Allah wadai irin arzikin sa wanda yayisu dare guda, wasu ma Allah wadai da haihuwan d'a irinsa suke, don kuwa labarin duniya baya b'uya, maganganu sunyita fitowa iri da kala bayan tafiyar sa....
"Innah ciki ciki ta amsa masa gaisuwar sa snn bayaga gaisuwa babu magana data kuma had'a su, haka ya fito waje ana karb'an gaisuwar dashi ba don yaso ba....
*************
"Wajajen yamma lis suka iso garin Abuja, Su Hadiza sai nan dasu ake sabida jinta take cikin kud'i, shari'a kawai take jira ayi ta tattari d'anta su gudu koda k'asar waje ne.... _(Allah sarki jahilci babu dad'i, da ta san cewa Check d'in bogi Alh Kasim ya bata da bata tsaya b'ata lokacin ta ba..)_
"A wann dare haka Zubaidah ta kwana cikin kewar mijinta, shima Jalal d'in hakan ne ta kasance dashi, ya tuno baccinsu a saman wann gado nasa, Ya tuna beautiful moments da suka kasance ciki, tabbas da ace zata zauna a wann asibiti har ya warke tabbas da ba zaiga jimawar sa ba ....
"Kwana uku aka gama makokin Baffah, Dole Umar Ya tikasta ma Inna saidai ta biyosa su tafi a cewar sa babu mai kula da ita, Innah ta k'ek'ashe k'asa tace fir bazata bisa ba, yaje chan ya k'arata da rayuwar sa... Magiya Umar Ya ringa mata yana nuna mata yayi nadamar duk wasu abubuwab da ya aikata a baya, kafin Innah ta d'an soma sauk'owa daga dokin fushinta, da sharad'in idan ta gama takaba zata bisa.... "Aifah fir Umar yak'i saidai ta bishi yanzu yanzu idan yaso tayi takaban nata a chan...
"Baiko bari tayi sallama da mak'ota ba ya d'auko Innah suka nufo Abuja....
**************
"Hankali kwance take rubuta jarabawarta, kusan kullum sai sunyi waya da Jalal, Ansar da Annah suke kaita su d'aukota, wata rana Ansar da Hamma wata rana kuwa Annah ita kad'ai...
"A kwana a tashi babu wuya wajen Rabbil Izza yau saura satittuka da basufi hud'u ba a koma kotu, ta ko wani b'angare suna k'ok'arin suga Sun had'a evidence d'in da zai kare su ya basu nasara a kotu....
"Yau tunda Ansar ya dawo gida ya had'a uban tagumi yanata faman research, Annah ta sauk'o parlorn k'asan ta samesa, tambayar sa tayi koda abinda ke damunsa, shiru kurum Ansar yayi don yama rasa da wanne zai soma mata.... Jin Annah ta sauk'a k'asa yasa Hadiza sad'ad'owa a hankali ta mak'ale jikin staircase...
"Ansar ya dubi Annah da kyau kafin ya sauk'ar da nannauyan ajiyan zuciya yace " Annah we are running out of time, komai ka iya faruwa a kotu, muddin bamu sami likitan da yayi treating Zubaidah ba Kotu bazata amince da mu ba, snn zata bayar da belin su Salim, yanzu haka daga Prosecution office nake, Prosecutors ya tabbatar min this is the only way for us to win, sai ko kuma su Labib sunyi confessing laifinsu... Annah I'm completely lost, I don't wanna fail Zubaidah and Jalal, in the next three weeks za'a sallami Jalal, what if I couldn't make it...... Ya soma girgiza kai shi kad'ai....
"Annah ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Ansar muna da hop guda d'aya, Tariq, Tariq zai iya confessing gaskiya, sabida a yanda naji yak'i bada had'in kai wa Barr Munir, snn su kansu The Dasukis and the Maina'a are not in good terms, so na tabbata they will go against each other k'arshe......
"Shiru Ansar yayi yana nazari kafin ya fuzar da iska yace " I must see Tariq , ina so nasan meye ke cikin mind d'insa, dukda nasan confession d'insa abune mai wuya don Alh bazai bari ba, he'll threaten his parents, I know that imbecile is capable of anything.... Amma insha Allah I'll do all my best, I won't rest until I see Kasim Dasuki spending his last day behind bars....
"Mik'ewa yayi yana duba agogon hannunsa kafin yace " Yanzu zan tura Hafiz Dukku, idan ma ministry of health zamuje duk zamuje a binciko mana that miserable Dr, amma kafin nan zan tafi prison na ga Tariq.....
"Annah ta gyad'a masa kai kafin tace " Allah Ya baka nasara Ansar, Allah d'aura mu bisa azzalumai..... Ameen Annahn mu... Ya amsa da fad'in haka kafin ya fice........
"Ya jima yana zaune wajen ganawa da mutane, har ya cire ran Tariq bazai fito ba sai gashi ya fito cikin uniform d'insa na prisoners, Ya jima yana k'arewa Ansar kallo kafin ya k'araso yanda yake.....
"Ansar ya sakar masa murmushi kafin yace " Bismillah zauna.... Babu musu Tariq ya zauna ba tareda ya furta koda kalma guda ba......
"Ansar yayi gyaran murya ya soma magana, still Tariq bai ce masa komai ba sai k'ura ma waje guda idanu da yayi...... Duk iya k'ok'arin Ansar na ganin Tariq ya masa magana Tariq bai yi ba, tunda ya zauna a wajen tamkar dutse baice k'ala ba, hakan ne take kasancewa dashi a duk lokacin da wani ya kawo masa visit..... Daga can Mum ta hangi Ansar zaune da Tariq k'irjinta ya yanke ya fad'i... Gudu gudu ta fice ta shiga neman layin mijinta wanda basa tare a yanzu.....
"Ba don yaso ba ya d'aya wayar nata cikin hasala, yana zaune cikin office d'insa dake Dasuki Holding..... "Cikin daburcewa take sanar dashi taga Lauyan Zubaidah da Tariq, ..... Ai bata kai aya ba Dad ya mik'e cikin tsananin tashin hankalk, don kuwa Dr ya sanar dashi Tariq ya sami minor tab'in hankali na rashin magana a dalilin accident d'in da yayi, Ya sami internal bleeding wanda duka sun masa aiki sun cire jinin, zai kwashi watanni kafin ya dawo normal....
"A guje Alh Maina ya nufo lift suka yi kicibus da Alh Kasim.... Take ya labarta masa abinda ke faruwa.....
"Cike da tashin hankali Alh Kasim ya shiga neman Faisal, a tare suka fice gaba d'aya daga company d'in cikin tsananin tashin hankali....
"Waya Alh Kasim yayi ma Barr Munir yace maza ya nufi prison and stop Ansar from talking to Tariq..... Shi kad'ai Ya ringa bubbuga car seat yana sunbatai kaman tab'abb'e.....
"Tun daga nesa Barr yake gudu kaman zai kifa da k'asa ya cakumo Ansar saida ya Mike tsaye babu shiri kafin ya soma fad'in" How dare you talk to my client you idiot.... Ansar ya fincike wuyar rigar sa daga rik'on da Barr Munir ya masa yana fad'in" Let go of me you good for nothing..... Nan hankulan gandurobobi ya dawo kansu suka soma k'ok'arin rabasu....
"Barr Munir yaci gaba da fad'in" Don't you ever let this imbecile come near my clients again or I'll press charges......
"Go ahead Attorney, ka shigar da k'ara idan ka isa, let me remind you this, wllhi Allah bazai barku ba, dukkan ku sai kun girbe abinda kuka shuka......
"Munir yana murmushi da gefen bakinsa yake fad'in " We shall see young Attorney..... Ficewa Ansar yayi daga wajen ganin tuni Tariq ya koma ciki....
"Barr Munir yaja gefe kafin yayi dialing lambar Faisal yace " Get your boys ready he's on his way right now..... Daga haka ya katse wayar yana wata mayaudariya murmushi.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:27] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
69
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Gudu yake kan falfalawa bisa kwalta ba tareda sanin wasu na biye dashi ba, saida yayi nisa sosai ya iso yanda babu mutane sosai kafin ya lura motar bayansa binsa suke.... A hankali ya soma rage speed yana k'ok'arin ciro wayarsa kwatsam sai ganin mota yayi ta sha gabansa.....
"Cikin sauri Ansar ya danna birki yana karanto innalillahi wa inna ilahirraji'un....
"Fuskokin su rurrufe da mask suka fito suna pointing d'insa da bindiga d'ayan ya jawosa ya fidda sa yana fad'in" Move.... "Ansar gaba d'aya ya rasa gane meke faruwa... Cikin dakewar murya yake fad'in" Me kuke nema a wajena.... Bai kai aya ba d'ayan ya danna kansa cikin mota yana fad'in" Shut up idiot... Da sauri suka saka masa Blindfold suka rufe masa idanu.... "D'ayan yace " Tony get his ride, Okay Boss Tony ya amsa kafin ya nufi motar Ansar.... "Cikin mintuna k'alilan suka bar wajen da gudun gaske uwa masu shirin tashi sama....
"What do you want from me, where the heck are you taking me to...??? Ansar ya tambaya cike da confidence...
"Shut your mouth you idiot, waya baka daman magana...? Cewar d'aya daga cikin su....
"Dukda idanunsa suna rufe yasan tabbas sun kwashi tafiya mai nisa....
"Suna isowa haka suka ringa hankad'asa suna fad'in" Move....
"Hannayen sa a d'dd'aure suka yasar dashi gaban Alh Kasim.....
"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Ku bud'e masa idanu, babu musu sukayi yanda yace...
"Ansar ya d'ago idanunsa da suka masa nauyi yana duban wajen da aka kawo sa da kuma mutumin dake make saman kujera a gabansa..... " Wani huci kawai yake ya yunk'ura zai kai capka wa Alh Kasim yana fad'in" You worthless imbecile....... "Da sauri d'aya daga cikin boys d'insa ya zaunar da Ansar ta hanyar kai mai naushi a ciki... "Babu yanda Ansar ya iya coz sun d'dd'aure mai hannu....
"Alh Kasim ya d'aga masu hannu alamun su k'yalesa... Takowa yayi har gaban Ansar kafin yace " ANSAR MA'ARUF KUMO, Am I right.... "Wani fincika Ansar ya kuma yi, komai ya shiga dawo masa, rasa family d'insa da kalan k'uncin rayuwa da Alh Kasim yayi sanadin shigar sa ciki.... Da kakkausar murya yake fad'in" Don't you dare call my fathers name again you miserable coward....
"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Gaskiya ne you're really his son... Saida ya d'an d'au lokaci kafin yaci gaba da fad'in" Attorney na kiraka nan ne mu samu peace nida kai..... "Hararansa kawai Ansar keyi ba tareda ya iya furta komai ba sai jini dake fitowa daga hancinsa.... "Yana huci ya soma fad'in" K'arya kake Alh Kasim bazaka tab'a samun peace da kowa ba, snn bazaka tab'a samun kwanciyar hankali ba until you paid for your damn crimes, you are a murderer, nasan ka kawo ni nan ne don ka kashe ni, go ahead and fulfill your mission, don na rantse idan ina numfashi sai ka tafi jell, and you'll spend the rest of your damn life there... Bai kai aya ba Alh Kasim ya wanka masa wata marin da saida jini ya tsattu daga bakinsa.....
"D'agowa Ansar yayi dukda galabaitan da yayi bakinsa bai mutu ba, yaci gaba da fad'in" I was even surprised da naga baka kashe ni ba tuntuni, coz you're not human, you're an Animal, a heartless being who doesn't...... Tasss...! Kake ji Alh Kasim ya kuma d'aukesa da Wata mari..... Kamo hab'an Ansar yayi yana huci yayinda Ansar d'inma ke huci .. Alh Kasim yaci gaba da fad'in" How dare you, you little brat, na gama da mahaifin ka ma balle kai, da ina son na ganka a mace da tuni ka mutu, but I don't wanna ruin my plans, I'm asking you nicely and politely withdraw the case, vanished disappeared get lost.... Zan baka duk wani dukiyar mahaifin ka da Ya rasa su a dalilina, zan baka huge amount of money ka tafi wani k'asar and start a fresh there...... Bai kai aya ba Ansar wanda zuciyar sa take kan faman tafarfasa ya tsatta masa miyau a fuskar sa... Cikin karaji yake fad'in"
"You are unbelievable Kasim Dasuki, you're the worst creature I've ever seen.. How dare you, har kanada gots da zaka kalli cikin idona ka gaya mun wad'annan magan ganu, you're an insane, tell me zaka iya dawo mun da mahaifiyata zaka iya dawo mun da mahaifi na, can you bring me back my two siblings.... Telllll meeee can youuuuu.....??? Ya k'arashe cikin wani irin murya mai firgitarwa idanunsa sunyi jazir sai zuban ruwa suke.... "Ansar yaci gaba da fad'in" Of course you can't... " Ba kowa bane irinka mai son kansa da son abun duniya, snn shari'ar Zubaidah bazan yi watsi dashi ba har sai mun kai bango, Allah zai had'a mu a kotu ranar da idon marassa gaskiya zai raina fata...... "Alh Kasim ya kuma d'auke sa da mari me kayu kafin yace cikin karaji... " You'll live to regret this Attorney, you've no clue who you really messing with, ... Ya kuma yin murmushi kafin yace " I'll see you in court Attorney, let's see who would win... Daga haka ya juya ya kalli boys d'insa kafin yace " Get him outta here..... Daga haka motarsa shima ya nufa....
"Kaman yanda suka d'auko Ansar ido a rufe haka suka fiddashi daga wajen, can gefen kwalta suka ajjiye mai motar sa snn suka jefar dashi gefen motar...
"Ya jima yana durk'ushe a wajen yana share jinin hancinsa kafin ya tashi da k'yar ya nufi motar, ko kad'an baiso su Annah su gane abinda ya same sa don kuwa hankulan su tashi zaiyi, don haka kai tsaye gidan su Hafiz Ya wuce......
**************
"Alhamdulillah, Zubaidah ta k'are jarabawar ta saidai fatan samun nasara, sosai kowa yayi mata murna ciki harda Hadiza dukda na ciki na ciki, hakan tayi daidai da saura sati biyu cif a koma kotu, snn washe gari ake saka ran sallaman Jalal daga asibiti, wani dad'i take ji maras misaltuwa, ji take she's ever ready to show her husband how she loves him, tabbas yanzu kam ta gama yarda she's into him irin totally d'in nan, fatan ta Ya dawo su gina rayuwar su snn mak'iyan su su sami abinda ya dace dasu, they will insha Allah finally have peace, .... Ita kad'ai take murmushi tana aikin gyara masa d'akin sa, a haka Annah ta shigo ta tadda ta suka ci gaba da aikin tare suna hira cikin annashuwa da jin dad'i gwanin ban Sha'awa.....
"Innah ki kwantar da hankalin ki tafiyar nan ba jinawa zanyi ba sann na fad'a maki oga na idan ban je ba zaiyi fushi dani, kinji ki kwantar da hankalin ki.....
"Innah ta sauk'e ajiyar zuciya kafin tace " Toh shiknn Baba Wuro, Amma kai shiknn bazaka ajiye iyali ba wacce zata ke dafa mana irin abincin da muka saba ci, kaga nidai ban saba da irin wad'an nan abinci na turawa ba, snn kaima ka girma da yawa ya kamata ka ajiye iyali nima naga 'yan jikoki nah......
"Take annurin fuskar Umar Ya d'auke cak don kuwa ba komai yake hangowa ba illa fuskar Zubaidah, all he was dreaming about shine ta haifa masa yara, Ya gina masu rayuwar su su biyu, but they ruined everything, all his plans...... Saida Innah ta buga kujeran da yake zaune akai kafin ya dawo hayyacin sa , gamida sauk'e nannauyiyan ajiyan zuciya....
"Innah ta girgiza kai kafin tace " Baka daina tunanin ta ba koh, na sanin tunanin Zubaidah bazai tab'a barinka kayi aure ba, har yaushe ne zaka gane Zubaidah ba taka bace, bazata tab'a zama taka ba, ka rungumi k'addara Ka nemi wata ka Aura, ga 'yammata kyawawa a gari sai....... Innah bata kai aya ba ya katse ta cikin tsananin d'aga murya yake fad'in" Noo no, she's mine, she supposed to be here with me, tawa ce ni kad'ai, nasan she still loves me, har yanzu nasan tana so na, and I'll take her back coz she belongs to nobody but me, me alone....... "Baki kurum Innah ta saki tana kallon sa tamkar zautacce, anya bai sami Tab'in hankali ba, itafah batama gane sunbatun da yake yi ba, tabass dai akan Zubaidah ne, _oh ni Fulera anya bazan bar barikin nan ba na koma gida na nema ma yaron nan magani ba kafin haukar tasa tayi tsamari.... "_ ta fad'i haka cikin zuciyar ta...
"D'an fuzar da iska yayi gamida tattare naman gishin sa kafin yace " Am am kiyi hak'uri Innah, yasa hannu a pantpocket d'in sa ya ciro kud'i kafin ya ajiyesu saman center table yace " Innah GA wann, tafiyar nawa bazai wuce sati guda ba, I'm quite sure wnn zai isheki, munyi magana da wani company masu bada contract na ma"aikata zasu turo yarinya guda wacce zatana kula dake, har girki ma zata ke maki, idan tuwon kike buk'ata ma zata maki.....
"Kallonsa kurum Innah take zuciyarta na raya mata d'anta ba kansa d'aya ba, k'ila shaye shaye ya soma, bacin haka miye wani constras (Contract) ." Magana ta soma masa ta harshen fillanci nan ya fayyace mata duk abinda yake nufi....
"Agogon hannunsa ya kalla kafin ya nufi upstairs ya tattaro abin buk'atar sa ya kuma yima Innah sallama don baiso ya makara kafin ya fice, Ya nufi Mercedes d'insa GLK 350 ,Da d'an banzan gudu ya fice daga gidan kaman mai shirin tashi sama..... Yana cikin driving kiran Alh Kasim ya shigo masa...
"D'agawa yayi gamida sawa a speaker kafin ya soma amsa wayar.
"Daga d'aya b'angaren Alh Kasim yace " Da fatan ka isa garin Gombe.....
"Murmushi rainin hankali Umar yayi kafin yace " Me kake ci na baka ke zuba Alh Kasim, ka kwantar da hankalin ka kaman tsumma a randa, Jalal will not show up in the Heroine, you have my word...
"Alh Kasim yayi wata murmushi kafin yace " Make sure you get the job done..... "Katse wayar Umar yayi lokaci guda yana hango fuskar Jalal.. A hankali ya furta " You must leave her for good, you Trap....
******************
"Sanye yake cikin bak'ar shirt wanda ya d'an kama jikinsa kad'an, farar fatar sa ta dad'a haskawa sosai, nininke kayan sa yake kanyi yana jerasu cikin luggage d'insa, fuskar sa fal fari'a kama daga kan likitoci yayi kan nurses kai har zuwa kan masu shara da goge goge na asibitin sun shaida irin farin cikin da Jalal ke ciki a yau, gobe War haka yana tare da princess d'insa by God willing..... Shattima da Ummah ne sukayi sallama a k'ofa .... "Da fari'ar sa ya Mike ya isa k'ofar yana masu iso....
"Sosai Ummah taji dad'in ganin yanda Jalal ya warke sosai, gaisawa suka soma yi gaba d'aya , Jalal da Ummah sun sake sosai tamkar sun jima da sanin juna... "Shattima ya jawo luggage d'in yana ci gaba da shiryawa yake fad'in" Patient you should have leave this to me ai, nazo na k'arasa ladana..... " Murmushi kawai Jalal yayi kafin ya dafi kafad'an Shattima yace " Bro you have done enough, Allah NE kurum zai biyaku all, banada bakin maku godiya...... " Ae ae pls don't even start patient, Ummah kinjisa koh zai soma.....
"Tab'e baki Ummah tayi tana kakkab'e slippers d'in Jalal wanda yake d'an zagayawa dashi take fad'in" Ni maza kuzo ku nemo min Dr Madi d'in idan za'a iya sallaman yau ai gwara a yi, don na dama masa fura na tarba.... Ta k'arashe maganar tana saka takalman cikin leda....
"Gaba d'aya saida Jalal da Shattima suka dara.... Shattima yace " Ummah kin manta Dr Madi yaje duba Mai Martaba kinsan baiji dad'i ba....
"Jinjina kai tayi kafin tace haka kuwa akayi, d'azu kafin Baba Waziri ya fice fada ya fad'a min, kunsan kwanyar nawa abubuwa sun masa yawa, ko damuwarka da Ameera sun isheni.....
"Shattima ya d'an tab'e fuska ba tareda yace komai ba... Jalal kuwa haka kurum ya tsinci kansa da fad'uwan gaba.... Tabbas yasan Dr Madi shine likitan Mai Martaba a iya zaman su, don kuwa shine case din Jalal ke hannunsa...
"Fatan samin lafiya Jalal yayi ma Mai Martaba duk suka amsa da Ameen, snn ya k'ara da gobe insha Allah kafin mu wuce gida sai mu biya na mik'a nawa gaisuwan.....
"Jinjina kai kurum Shattima yayi amma harga Allah baison duk wani abunda zai kaisa fada a halin yanzu, avoiding komai na fada yake sabida guje ma ganin Zahida musamman da yanzu ya rage saura sati biyu kacal bikinta da Khalifah, Umma kanta ta gane haka.... Ganin change d'in da ya wanzu a fuskokin su yasa jikin Jalal yin sanyi... Bai kuma tada maganar ba saida suka zo tafiya, Bayan Ummah ta fice yake tambayar shattima dalilin sudden change d'in... Shattima ya d'anyi jimm kafin yace " We would talk about it bro, zan dawo da dare... Cike da tausayawa Jalal ya gyad'a kai don yasan dole it must be something serious...
"Sun d'an jima a wajen Jalal kafin suka wuce don dama anguwa Shattima zai sauk'e Ummah suka biya ta wajen Jalal.....
****************
"Dr Madi ya kuma kallon tabon dake shimfid'e gefen kafad'ar Mai Martaba wanda bai tab'a gani ba sai yau, Ya tuna exactly tabon dake kafad'ar Jalal kenn ta bayan sa, Ya tuna Mai Martaba da Jalal have same blood group... Kai they have something in common aside from that akwai genetic signs da suke dashi......" Gyaran muryar da Mai Martaba yayi ne yasa Dr Madi saita kansa kafin yace " Ayimin afuwa Rankashidad'e..... "D'an murmushi Mai Martaba yayi kafin yace " Dr knn yaya jinin nawa ya sauk'a....
"Saida Dr Madi ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Allah Ya taimake ka jinin ka ya sauk'a amma lallai idan son samu ka rage yawan damuwar da kake,..
"Mai Martaba ya jinjina kai sanda Dr Madi yake gyara masa zamar rigar sa 'yar shara..
"D'an gyaran murya Dr Madi yayi kafin yace " Allah Ya taimake ka ina son sanin wata irin damuwa ce haka take damun ka, Ayimin afuwa idan na wuce hurumi na....
"Maiartaba yayi k'asaitaccen murmushi kafin yace " Likita sam baka wuce hurumin ka ba, tsakani na da kai ya wuce haka, Ko Dr Mansoor na K'asar Egypt bai kaika kusanci dani ba, na yarda da kai d'ari bisa d'ari kamar yanda na yarda da d'ana Shattima...
. "Dr Madi ya murmusa cike da k'arfin gwiwa kafin yace " Godiya nake Allah Ya taimake ka...
"Mai Martaba ya gyad'a kai lokaci guda yana kallon hoton jinjirin dake mak'ale a d'akin kafin ya soma fad'in" Shine damuwata, shine ke hanani bacci duk ranar dana tuna banga gawarsa da idanu na ba, ina ganinsa cikin barci na ya zama bababban saurayi magidanci, inama ace zan kuma saka sa a idanu na, inama zan gansa na mallaka masa duk wani abinda na Mallaka........ "Dr Madi dai kai dubansa yayi ga hoton da Mai Martaba keta magana dashi.... Gabansan ya yanke ya fad'i, a fili ya furta JALULDEEN, gyad'a kai ya shiga yi yana kallon Mai Martaba yake fad'in" Allah Ya taimake ka, shine wllhi shine, your long lost Son is here, wllhi Shine Jalal, wllhi yanada Tambari irin wanda kake dashi a kafad'ar ka...... Babu shiri yaga Mai Martaba na mik'ewa tsaye ba tareda ya iya furta koda kalma guda ba........
"Ummi dake tsaye jikin labule cikinta yabada wani irin k'ara wanda idan ba sa'a ba mutanen dake waje ka iya jiyowa, girgiza kai ta soma tamkar zararriya kafin ta fice da saurin gaske gudu gudu..
"Ward d'in Amenity tayi tsit tamkar babu kowa, Ya jawo abin rufe hanci wanda likitoci ke amfani dashi ya rufe bakinsa da hancinsa, gyara zaman labcoat d'in dake jikinsa yayi kafin ya shige d'akin da aka tabbatar masa shine na Jalal......
"Ya tada iqaman sallah knn yaji bindiga a kunkuminsa,... Umar Ya kwanto da kansa saitin kunnen Jalal kafin Ya soma fad'in" If you misbehave I'll kill you right here, now let's get going.. Kunkuminsa ya rik'e tamkar likita suka soma tafiya....
*Tom readers... Dan Dan Dan..... Kai I won't say a word..Just Find out in the next page.... 😜*
Queen Samy ce
0 comments:
Post a Comment