_Gaskiya wannam ba Rayuwa bace wani chan ya miki karya har kinji tausayin sa kika zauna kina kukan asara.Haba Kawata ba haka bane ki tsaya kiji mai yasa na tausaya masa ko ke kika ji labarinsa sai kin tausaya masa, Nam *Jawaheer* ta fada mata duk Abun da Nura ya sanar da ita ta karasa Maganar tana cewa kiji fa wani irin Rayuwa *Rahma* wanna wani irin sangwama ne haka?. Dan kawai 'yayanta yayiwa mahaifiyarta ciki ain haifeta shekenam ita bata da galihu kenam?. *Rahma* ta share hawayenta dan Labarin ya bata tausayi. Tace duk da haka *Jawaheer* bai kai kiyi wannam irin kukan ba ko dai kece da gaske *Sultanah* na sa?. Kika boye masa da mu kan mu da muke tare. Cikin Kuka *Jawaheer* tace ki yarda dani *Rahma* bani bace wacce yake fada nifa Haifeffiyar Abuja ce kinga ko mai zai hada ni da Sokoto?. Ta fada da sigar Tambaya. Dan haka kima cire wannam maganar a ranki ni kawai naji tausayin sa ne. To Shikenam *Jawaheer* Allah ya shige mana gaba nikam zan wuce dama kawai na shigo mu gaisa ne. To shikenam Kawa sai mun hadu gobe. Daga haka *Rahma* ta mike ta fita. Tana Mamakin kawar tata da sun saba in dai daya yazo gidan su daya sai sun raka juna har bakin kofar gidan su sannam ta juyo. Amma yau kuma babu rakiya koda bakin kofa ne. Gaskiya da Alamun Tambaya akan *Jawaheer* . Haka *Rahma* take ta Sake-sake har ta karasa gida su_
_" *Mujahit* suna shiga daki ya zube yana kuka sosai Abun gwanin ban tausayi. *Nura* abun tun yana bashi tausayi har yafara bashi haushi. Cikin fada yace Haba Mujahit wannam wani irin abune kana Abu kaman karamin yaro, ya kamata ya karfa daga wannam mayen mafarkin da kake haba dan Allah, Ta sanar dakai ba ita bace, bari kaji a duniya dan Adam yana da masu kama dashi har mutum 7 . Ya kamata ka fahimta wanda ya mutu ya riga ya mutu dan Bazai taba dawowa ba sai in an samu mai kama dashi haka ka yarda da kaddara maikyau ko Akasin haka. *Mujahit* ya goge hawayensa yace na yarda da maganar ka *Nura* kuma na yarda da kaddara maikyau da maras kyau Insha Allahu na rufe babin *Sultanah* a duniya Amma kuma bazan taba cireta a zuciyata ba insha Allah dan haka ina mai neman shawaranka ina so zan nemi soyayyar *Jawaheer* saboda ta maye min gurbin *Sultanah*. Nura yace haba *Mujahit* nasan in ka Aure *Jawaheer* Wallahi ba dan kaan sonta zaka Aureta ba sai don kamar da suke da *Sultanah* dan haka ka bar ma maganar hakan gwara muje wajen *Malika* zai fi. Dan ko ka Aure *Jawaheer* ba ita ka Aura ba *Sultanah* ka Aura dan komai da *Sultanah* zaka ke mata ko sunanta da *Sultanah* zaka kira. Kaga ko duk macen da tasan kanta baza ta taba yarda da haka ba duk hakurinta da Raunin zuciyarta. Ajiyar Zuciya *Mujahit* yayi yace na yarda da maganarka Nura kuma na Amince gobe sai muje wajen Malikar. Allah ya kai mu cewar Nura._
_"Lalle zaka ja mata wani abun a guri na dan ka sa na kara tsanata ma walla. Tana kanwata lalle ma Daddy Baka da han... Mubajjal yayi saurin rike baki dan ya kusa baran-barama haka ya wuni yana sake-sake har yamma da misalin karfe biyar Daddy yasa aka tara kowa na gidan a babban falo saboda zai yi babbar magana dasu. Bayan kowa ya hallara ya fara bude taron da Addu'a sannam ta cigaba da cewa na taraku a nam ne badan komai ba sai dan na fada muku kudiri ne dana dade ina rike dashi amma kuma dole sai mun fasa kwan da muka yi shekara da shekaru muna boyewa. Ba komai bane illah na hada *Mubajjal* da kuma *Nusaiba* Aure. Daga *Mubajjal* *Nusaiba,* *Yasmin,* *Yasir,* da kuma *Salma* Abun ya basu Mamaki. Dan shi *Mubajjal* ya gama tunanin Daddynsu ya haukace ma suko Hajiya Kaka da *Hajiya Babba.* Da kuma *Hajiya Karama* sai murmushi suke suna yiwa Daddy Godiya da wannam karancin davyayi musu. Musamman *Hajiya Karama* da tafi kowa farin ciki. *Daddy* ya ci gaba da ce zaku ji maganar kamar Rashin hankali to bari kuji. *Nusaiba* 'yata ce Amma kuma bani na haifeta ba haka ma Umminta ba ita ta haife ta ba. Maihaifiyarta tun ranar da ta haifeta Allah yayi mata rasuwa kuma yayace a wajen Umminku Wato Hajiya Karama. A ranar da Mahaifiyarta ta rasu Umminku ta karbe ki tace ita zata rikr ki kasam cewar bata taba haihuwa ba ta nemi shawarana kuma na Amince tun daga ranar kuma mukayi Alkawarin babu wanda zai sani.ko ke baza mu sanarwa ba. Sai gashi yanzu wani hadi da zanyi yasa sai na faitacewa kowa komai sanam komai zai tafi da kyau. *Mubajjal* tafe kanshi yayi. Dan ya manta da ba iyayensu daya da *Nusaiba* . Yasan ko Aurensa da ita ba gashi amma kuma yace sam bazai yarda ya Aure ya. *Daddy* ne ya katse masa tunaninsa da cewa kaji dai Abunda na yanke Allah ya baku zaman lafiya Allah ya kaimu lokaci kuma musha biki. 'Yan dakin ne suka amsa da Ameen in banda boyu daga ciki da suke duniyar tunani *Mubajjal* da *Nusaiba* . *Nusaiba* tunda aka fara take kuma sosai tana tuna yadda *Mubajjal* ya tsaneta. Amma ta yaya zasu zauna zaman Aure dashi to Allah gani gare ka Allah kasa ya *Mubajjal* ya karbe ni a matsayin matarsa dan nikam zan masa biyayya iya iyawata. *Daddy* ne yace mata. *Nusaiba* ya kika ce da fatan kin Amince. Cikin kunya tace na Amince *Daddy* tayi saurin mikecwavtana dan dariya. Shiko gogan wani haushinta yaji ya mamayesa da harara ya rakata. Hajiya Kaka ko wata guda ta rera tana cewa gaskiya wannam hadin yayi su Mubajjal za'a samu sauran Sado mai shago. Kowa na dakin sai da yaji ba dadi a maganar ta musamman ma *Hajiya Karama* nam Daddy yayi saurin Sallamar kowa dan yasan Hajiya Kaka babu rowanta komai ma zata iya fada. Shiko Mubajjal ji yayi kamarvya shaketa a wajen ta mutu. Haka ya mike yayi dakinsa._
_"Washe gari da misalin karfe 5:00pm *Mujahit* ne tare da *Nura* cikin shigar Wagambari mai shegen kyau Peach colour da hulansu zanna black da takalminsu sau ciki shima baki ga agogon fata dake makale a hannunsu sai tashim kamsu suke amma kuma *Mujahit* yafi *Nura* kyau nesa ba kosa ba. Haka suka shiga wata motar Mai colour peach kai sai wanda ya gani sai fara'a suke suka dauki hanyar gidan su *Malika* Suna tafiya suna hira kawai sai naga sun dauki hanyar gidan su *Jawaheer* wato *ZONE A NATIONAL Assembly*. Suma sunyi mamaki amma da suke duba Number gida jen basu gamsa a *ZONE A* ba *ZONE B* suka gansa 32 Nam suka dannam hot a katafaren gidan. Aiko mai gadi da sauri yazo ya wangale musu gate suka shiga bayan sun gaisa da Mai gadin nam suka sanar dashi wajen wacce suka zo. Da yake mai gadin yaro ne ya shiga da kansa ya sanarwa da Malika da kamar zata ce yaje yace bata nam sai kuma tace masa kace ina zuwa. Ya fita da sauri yaje ya sanar musu suka yi godiya ya kuma wajen zaman sa. Ta tashi ta shige daki ta kira wani karamin yaro taje kaje ka kai bakin da nayi dakin baki kace ina zuwa aiko yaron da sauri yazo ya same su suna tsaye yace ina wunin ku. Lafiya klao. Wai inji. Aunty Malika wai kozo na kaiku dakim baki tana zuwa La kune masu waka a Tv ko Aunty Malika tana son wakar ku musamman ma kai ya fada yana mai nuna Mujahit dariya suka sa baki daya dab yadda yaron yayi magana sai ya baka dariya nam suka bisa ya sadasu da wani daki babba wandacya kayatu da kayan more rayuwa. Mujahit yace miye sunan ka?. Sunana Shureem. Na tafi sai anjiman ku daga haka ya fice a guje dan dama Game yake ta taso sa suna zauneca waje wata budurwa daga gabi mai aiki cecta shigo shake da kayan mar mari a tire ta gaishesu tayi waje. Sai chan gimbiyar ta fito cikin shigar dogowar Rigar Kanti tasha kyau sosai ta shiga da Sallamarta suka Amsa mata cikin fara' ta zauna a Daya daga cikin kujerun tana mai gaishesu suka Amsa. Tana hada idanu da *Mujahit* sai da kirjinta ya buga tsabar kwarjini da ya mata ga uwa uba kyau gashi kuma Mawaki wanda take matukar son wakar sa. *Nura* ne ya katseta da cewa. Malama Malika Munsan zakiyi mamakin ganinmu saboda bamu sanar miki ba kuma baki sammu ba in ba dai kina kallon Tv ba. To ni dai Sunana *Nura* Shi kuma *Mujahit* . Ni rakiya nayi dan ga Uban gaiya nai aikin tuncranda ya ganki ya susuce akan ki Nam taji kanta ya kara hawa na jin kai. Kumm....... Haba *Nura* ka barni nayi magana mana sai surutu kake kamar Aku cewar *Mujahit* . Duka suka saka dariya *Nura* yace e dole kace haka tunda na rako ka ba barima kaga na tashi na fita na barku nima zan samun tawa bada jimawa ba daga haka yayi waje yana dariya suma dariya suke masa._
_"Yana fita *Malika* ta sun kuyar da kanta kasa tana wasa da dacdan yatsun hannunta. Ganin haka yasa *Mujahit* ya gyara zama tare da gyaran murya yace *Malika* kinki dai Abunda *Nura* ya fada miki tun randa na ganki naji na kamu da sonki shiyasa kika gammo a gidan ku dafatan zan samu fada a zuciyarki. Tunda ya fara Magana Malika taji irin muryarsa ta kara narke wa a cikin sonsa dan tun kan tasan wanda yake sontan tana ganinsa taji ya mana. Cikin Saririyar murya tace insha Allahu. Yace Masha Allah. Dafatan dai na miki ko?. Ya fada cikin sigar Tambaya. Cikin farin ciki tace wa zai ga guy kamar ka harvyace yana sonta taki ai ko hadu ta ko ina ton ganin farko naji kamin da ba kai kake so na ba da sai na tunka reka na fada maka insonka dan kamin sosai. Dariya yayi a zuciyarsa yana mamaki da tana jin kunya yanzu kuma ta ware to Allah yasa dai mu dace. Hakaa yake fadi a zuciyarsa. Nam suka fara hira kamar wanda suka shekara duk dacrabin hirar ta fishi surutu sosai kamar ba yau suka hadu ba. Sai ana kiran Sallar Magriba *Nura* ya shigo da Sallama yana cewa zanga ikon Allah tun haduwar Farko kun manta dani ina ko an daura Aure ina ga in kun ganni ma zaku ce kai kuma waye. Suka saka dariya baki daya. *Malika* tace da ina shirin baka Sister nah amma kuma na fasa tunda zaka kurar min Masoyi. A yi Hakuri Auntyn mu kai na bisa wuya na tuba nake a taimakan daman ban da masoyiya. To shikenam Amma kar ka kara. Tab yo in kika min hanya na samu Budurwa ina ma zaki ganni balle har na katse muku hira ai sai dai kowa tashi ta ficce shi. Suka kara sa dariya *Mujahit* da *Malika* suka yi musayar Number ya sanar mata zai kirata in har ya kuma gida. Ta karasu har bakin mota tana daga musu hannu suka fice ta shige gida cikin farin ciki na ta samu abunda take so.(Niko nace *Malika* baki zake da yawa ba kuwa?)._
_" *Hajiya Karama* tana mikeqa daga wajen taron dakin *Nusaiba* ta shiga ta sameta sai dariya take. *Hajiya Karama* ta zauna kusa da ita tace kai *Nusaiba* wannam irin fara'a haka mai ya faru. *Nusaiba* ta dago tana mai dariya sai kuma chan ta kuma kuka. *Hajiya* taji tsoro sosai tace haba *Nusaiba* miye kuma abun kuka ke da zakiyi farinciki kin samu jangwarzo. Cikin kuka *Nusaiba* . Tace *Ummi* Ashe bake kika haifeni ba Amma kin rike ni fiye da yarda zaki haifa. Haba *Nusaiba* miye to abun kuka dancAllah ki. Kwantar da hankalinki harvyanzu ke diya tace dama ban taba cire ki da ga yarana ba ko na haife su bare ma kamar bani da rabo a duniya cikin sauri tace karki ce haka *Ummi* insha Allah. Allah bai manta dake ba yana sane dake kuma zai baki da izinin Ubangiji. To Allah yasa *Nusaiba* . Ameen Ummi . Nam Hajiya tace *Nusaiba* kin dai ji abunda Daddynku ya yanke dafatan baza ki watsa masa kasa a idanu ba duk da naga shi *Mubajjal* kamar bai ji dadin hakan ba. Insha Allah Ummi bazan watsa muku kasa a idanu ba ko mai Ya *Mubajjal* zai min zan zauna dashi har'abada. Yauwa diyar Albarka Allah ya miki Albarka Allah kuma ya kaimu lokaci musha biki. Da Sauri *Nusaiba* ta rufe idanunta tana yar dariya. Ummi ya mike tana shirin fita sai ga Yasmin ta shigo. Ummi tayi ficewarta ta barsu. *Yasmin* ta haye gadon kusa da Nusaiba tace Kanwata kuma Aunty na gaskiya banji dadi ba da aka ce wai iyayenmu ba daya ba Amma kuma naji dadin wannam hadi fa akayi zamu sha biki nasan *Ya Mubajjal* yayi dacen Mata ta nunawa sa'a dan wallahi *Nusaiba* ba dai kyau ba. Cikin jin kunya *Nusaiba* tace kai Aunty *Yasmin* kyau kuma har na kaiki. Allah *Nusaiba* kin fini kyau nesa ba kusa ba Ya *Mubajjal* ne dai zaku kusa zama daya dan shima dai akwai kyau mu dai zamu sha biki. Duk da naga yayan Namu kamar bai so ba amma wataran zaiyi Alfahari da hakan. Nam Nusaiba ta fara hawaye tana cewa Tabbas Aunty Yaya bai so haka ba Amma koma yaya wallahi zan zauna dashi kuma tun lokacin da Daddy yace a bashi ya haifen ba naji na kamu da son yaya *Mubajjal* . Insha Allah zan zauna dashi duk rintsi duk wuta. Insha Allahu da kanshi sai ya furta miki kalmar so. *Nusaiba* tace Allah yasa Aunty Nam suka ci gaba da hiran su._
_Kuyi Manage_
*_NEXT PAGE IS LOADING........_*
_VOTES_
_COMMENT_
_08132761212_
*_MU[4/19, 7:22 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
_Kakana Hassan Atk tare da Husaini Atk_
*_Page 31&32_*
*★★★★★★*
_" *Jawaheer* tun randa taga *Mujahit* hankalinta yayi matukar tashi bata ci bare sha duk ta rame kamar ba ita ba tunani sun mata yawa sosai kullum cikin kuka take.(Niko nace wannan wani irin damuwa ce haka *Jawaheer* ?. Anya kuwa bake bace *Sultanah* ?. Masu karatu nima fa ina zargin wannam lamari). Yau ma zaune take a falo tana cin. Makaroni amma sam hankalinta baya tare da ita. Tana chan wata duniyar tunani. Wayarta ce ta fara ruri na naiman a gaji da kamar baza ta dauka ba chanda ta dauki wayar taga *Uncle Doctor* yana yawo a screen din wayar da sauri ta daga. Tare da cewa Ina Kwana Uncle. Yace lafiya tare da cewa *Jawaheer* wato yar yanzu baki daina wannam tunaninba ko?. Naji yanzu kin daina zuwa Hospital sai dai ki tura Kawarki ko?. Dan kawai kinga wani chan ki daurawa kanki damuwa to wallahi karki bari nazo na sameki baki fara zuwa aikin ki ba. Kin jinikam ko?. Cikin sanyin murya tace naji Uncle a gaida da su Aunty. Yauwa ko kefa yar kanwata ki daina saka damuwa a zuciyar ki ki cire komai ki kuma nata komai Allah ya miki Albarka. Ameen daga nam sukayi Sallama ya kashe tayi wani murmushi sai kuma ga wasu hawaye._
*★★★★★★*
_"Mubajjal yana fita ya nufi wajen aikin sa inda ya fara a wani Private Hospital yana aiki ne ta fannin mata. Yana zuwa ya fara aikinsa ba kama kafar yaro amma kuma wani gefe na zuciyarsa tana tuna masa Alakakan da aka hada shi da ita wai yanzu aurensa saura wata biyu da wannam ficiciyar yarinyar gaskiya zata ci Ubata wallahi. Wani murmushi yayi na mugunta tare da wani kwafa. Sai karfe biyar ya dawo gida. Yana shigo yayi fanninsa yana shiga ya fada toilet yayi wanka ya saka jallabiya dan yau yace babu inda zai fita. Ya kira Wayan Mommyn sa yace aka wo masa abinci dakinsa yau baya sha'awan ci da kowa. Tasan halin yaron nata ta amsa masa da cewa ana kawo wa. Tana kashe ta kira Nusaiba tace kizo ki kaiwa Yayanku Abinci yana dakinsa badan ta so ba ta amsa da to Mommy daga haka ta shiga kitchen ta hada masa komai sannam ta dauka ta nufi dakinsa kirjinta na bugawa sosai. Da Sallama ta shiga yana kwance a falo yana kallo ya amsa mata a ciki- ciki ta ajiye masa zata juya yayi saurin fin cikota ta fadi a ka ji kake tum. Ta saki wani kukan azaba shiko ko tausayinta bai jiba ya kama kunnenta tare da cewa mai nace miki?. Ba cemiki nayi karki sake zuwa inda nake ba. Ko ke kunnam kashi ne gareki?. Ita dai kukan azaba take dan goshinta ya bugu sosai. Dan Ubanki baza kiyi magana ba. ya fada cikin tsawa. Cikin Kuka tace dan Allah kayi hakuri bazan sake ba. Mommy ne tace na kawo maka. Yaja tsaki tare da cewa tashi ki bace min da gani Allah yasa ki kara zuwa inda na ke zaki ga abunda zan miki. Ta mike cikin sauri ta fita dan yanzu kam ya fara bata tsoro. Tana shiga falonsu ta shige dakinta da gudu ta saki wani kukan sai da tayi mai isarta wani bacci wahala ya kwasheta tun daga ranar bata kara bari sun hadu ba duk hanyar da tasan wani abu zai hada su sai ta rufeta har Allah yasa ta kammala makaranta ya kama bikinsi saura sati guda kenam amma har yau basu hadu ba kusan wata biyu kowa yana rayuwarsa.shirye- shirye ake sosai har yau jumma'a ranar daurin Aure kenam._
*★★★★★★*
_" *Mujahit* ya turo gidan su *Malika* Kuma an bashi Auren ta dan yanzu kowa yasan *Mujahit* a gidan su *Malika* . Ta harkar kasuwancin sa kuka sai dai muce Alhamdulillah. *Nura* ma ya turo iyayensa kuma an bashi shima. Yauma Kamar Kullum *Mujahit* ne da *Nura* suka Nufi *ZONE B* wato anguwarsu *Malika* kenam sun ci kwalliya sosai. Suna shiga gidan suka samu Malika ta fito da wani tire ta nufi inda suke hira dan yau kam ma *Mujahit* bashi da niyar zuwa hira amma ta sakashi dole sai yazo tana kallonsa ta saki kayataccen Murmushi suka karasa gaba daya falon nam suka samu *Ikram* tana gyara wajen. Suka hau gaisawa nam kowa yaja tasa suka fara soyewa. *Malika* ne ta shagwabe fuska na cewa sai anje ansha Icream aiko nam *Nura* ma yace sai anje *Mujahit* babu yadda ya iya yace to shikenam kafin su gama su *Nura* sunyi waje har sun hau Mota sun fita waje suna jiransu. Su *Mujahit* ne suka taso cikin so da kauna sukectafiya sai dariya suke suna fito wan. A dai-dai lokacin Motar *Jawaheer* ta shawo kwana tana daga idanu taga *Mujahit* tare da *Malika* sai dariya suke daga ganinsu soyayya suke wani jan birki tayi........_
_Kuyi Hakuri da wannam bana da charge in har sun kawo wuta zuwa anjima zan sake muku postin in naga Comment amma_
*_NEXT PAGE IS LOADING........_*
_VOTES_
_COMMENT_
_08132761212_
*_HAFSAT A GARKUWA CE_*🥰
[4/19, 7:24 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsa
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
_My Husband_
_Ina matukar alfahari da kai Mijina ka bani gudum mawarka sosai Allah ya barmu tare_
*_Page 33&34_*
*★★★★★★*
_" *Jawaheer* Wani Wawan Birki taja jika ke kir! Kir! Cikin firgici suka juyo suka kalli motar. *Malika* ta isa wajen tana cewa Jawaheer lafiyan ki kalao kuwa?. Cikin Karfin hali *Jawaheer* tace lafiya klao kai na ne kawai yake saramin. *Malika* yau ke na gani da saurayi. Keda bakya kula su. Yau kuma na ganki da wani. *Malika* tace wallahi da din ma ban samu wanda nake so bane sai yanzu shiyasa dan har an saka mana rana. Wani zare ido *Jawaheer* tayi tare da cewa an samuku rana fa kika ce?. Eh Nam da wata. Biyar za 'ayi Auren mu. Da Sauri *Jawaheer* ta figi motarta. Ta bat wajen gudu take sosai har ta isa gidan ta wanting. Hon ta buga wanda mai gadin yasan yaufa ba lafiya yayi hanzarin bude mata ta shiga saura kadan ta bige sa yayi saurin kaucewa. Tana Parking ta fito da gudu tayi cikin gida tana wani irin kuka ta zube a tsakar falo, kuka take sosai tana cewa Haba *Sultanah* mai yasa zaki cuci kanki?. Mai yasa zaki tsaya wata ta kwace miki Farin cikin ki?. Gaskiya gwara ki tashi tsaye domin ki kwato Abun Alfaharinki a hannunwa. Karki yi sake. Ta sake wani sakin kuka tana ta Sambatu. Da sauri ta dauki wayanta ta danna Number Uncle Doctor. Yana dagawa ta sake fashe masa da kuka cikin rikitar zuciya ce mai ya faru kike wabnam kuka?. Cikin kuka tace *Mujahit* ! Shikenam zan kara rabuwa da shi Har an saka masa rana da wata. Cikin kidimewa yace baza ki rasa saba *Sultanah* insha Allah *Mujahit* baki ne ke kai. Ina nam zuwa kiyi hakuri ki bar kuka. Daga haka sukayi Sallama taci gaba da wan kuka._
*★★★★★★*
_"A yau Jumma'a ne duban jama'a suka halacci daurin Auren *Mubajjal Hamza* da Amaryarsa *Nusaiba Kabir*. An daura aure akan Sadaki Dubu Dari da Hamsi. An daura Lafiya *Mubajjal* kowa Dariyar yake kawai yake yi *Mudan'sir* sai masa dariya yake shi kowa ya cika ya batse kamar bai tama dariya ba kafin wasu mutanen su gaisa dashi ya sa ki jiki ya bar wajen yayi bakin gidan su ya faka Motar yayi kwanciyarsa a ciki yana jin wani bakin ciki wai yau shi aka daurawa Aure da wannam yarinyar. Wai yau ni zan aure sauran Mai shago gaskiya anyi matukar cutata sosai. Yana cikin wannam tunanin yaji ana masa Norking. Dam kamar bazai bude ba ganin *Mudan'sir* ne yasa shi budewa. Yana shiga yace Haba Abokina ya ana gaisawa da kai kawai aka ne meka aka rasa?.Kai Malam dan Allah karka dame ni ka barni naji da abun da yake damuna. To Allah ya baka hakuri Ango cewar Mudan'sir yana yar dariyar Mugunta. Yace Yanzu zuwa anjima zamu shirya wajen Dinner ko?. Wani kallon Raini Mubajjal ya masa tare da cewa wai so nawa zan fada naka ni babu wani abu da zanyi a bikin nam to bari kaji na sake fada maka Wallahi Babu abunda zanyi na biki. Ya daka tsaki tare da mikewa ya tada Motar suka shiga cikin gidan. Yana fitowa aka fara rantaba guda aba masa tsiya shiko fuskar nam kamar bai taba dariya ba haka ya shige fuuu....! Kamar iska *Mudan'sir* ne yake amsa musu tare da ta yasu yi maaa tsiyar.Suna shiga ya zube akan Gadon sa Mudan ganin ba wanka zai shiga ba ne yasa cikin sanyin murya yace pls ka tashi ka shiga wanka kacshirya domin muje wajen Waliman nam kasan duk sun wuce mu ake jira. Babu yadda ya iya haka ya mike ya shirya cikincwani dakakkiyar Shadda Sky Blue shima Mudan shiryawa yayi sau daukan Kamshi suke suka fito suka tafi. A bangaren Amarya kuwa tunda aka Daura Auren jikinta ya mutu sosa dukctaji wani kasala ya shigeta duk sonta da Auren sai taji sam bata so. Amma fa Amarya tasha kyau sosai sai kyalli take zubawa. Su Yasmeen ne a gefenta sunata mata tsiya wai yau dai sai gidan Ya Mubajjal zata kwana bata so haka ba amma Daddy yace zuwa yamma za'a kaita gidan ta dake._
_"Arkillah Lowcos. Haka dai tayi zugum taba jin tsiyar da suke mata da wasu kawayenta biyu Rahina da kuka Sakinah. Ko Abinci ta kasa ci a ranar tana tunanin zaman da zasu fara da jan gwarzon ta. Da misalin Karfe 6:00pm na yamma na wannam ranar Wasu Motoci ne na fada a jiya suka shigo gidan su Mubajjal domin daukar Amarya aiko nam aka fara shiga aka fito da Amarya tana kuka sosai da kyar aka cireta daga jikin Hajiya babba da kuma Hajiya Karama suma sai da sukayi kuka. Hajiya Kaka ko dariyar ta take sha tare da cewa dole kije gidan mijinki! Nasan zaki sha walaha a wajen sa. Duk da saura zai dauka. Mutanen wajen sun jita ras amma babu wanda ya tamka mata dan sun san halinta ras. Ana ta shiga mota naga wata katowar mota aiko na kusa dan naga suwaye a cikin ta cikin Mamaki naga yan' grp din *Abinda aka gasa...! Paid Group* ne nace wadannam kuma ina suka san da wannam auren Basu samu damar gaisawa da kowa ba suka bi yan kai amarya dan kar a musu nisa basu san kuma gidan ba Gidan mutane kadan ne basu jeba dan suma iyaye ne shiyasa basu je ba Amma Hajiya Karama taje kai diyarta haka suka dauki hanba basu wani jima bacsaboda basu da wani nisa sosai tsakanin su. Nam naga sun faka a wani katafaren gida. Aka shiga da Amarya ta wagar *Abinda Aka gasa..! Paid grp* ma suka shiga su *Umm-Muhammad* sai ware ido ake yi anga gida kamar gidan Aljannah nam suka shiga falon gidan Babban falo ne da ya dau kayan more rayuwa Nam suka haura samma inda dakin Nusaiba yake kusa dana Gogan ta suna ajiye ta manyan ciki suka kara mata nasiha a tsatstsaye domin yanzu za'a mai dasu suka watse Su *Yasmeen* aka bari da kuma *Sakinah* da *Rahinah*. Domin su jira zuwan angwaye sai akai su dan kar a barta ita daya. Suna cikin hira suka ji Sallamar su Sis Nafisa yan' grp din Abinda Aka gasa...! Da Sauri Nusaiba ta mike domin ta gane su tace *Mom Haidar&Khairat* ! *Sis Nafisa* , *Ummu-Muhammad,* *Suleja,* *Maryam a tafida,* *Nana Khadii,* *mmn ibtisan,* *Ummu Eeman,* *Brr Husnah,* *Ummu suhaima,* *Mummy Jiddah,* *Halima,* *Zainab,* *Aisha Abubakar.* Lalle kun min karamci sosai wallahi nagode Allah ya bar zumunci *Mummy Jiddah* tace ba komai Kawa ai mun zama daya(Niko nace O ko yaushe ta santa har ta zama kawarta Ohoo Lol.). *Yasmeen* tace *Nusaiba* ina kika samu wadannam kuma?. Ta bada cikin sigar tambaya._
_" *Ummu-Muhammad* ne ta galla mata wani harara har da murguda baki(Kai Ummu Tambaya fa kawai tayi nima ai dole in tambaye ku yaushe kuka santa har kuka je bikinta). Nusaiba tace ke dai ki bari kawai wadan nam yan Amana ne a Grp Din *Abinda aka gasa...! Na Sister Hafsat A Garkuwa* muka hadu wallahi suna da mutunci sosai. Yasmeen tace aiko dai kam gaskiya muna godiya da wannam zumunci Nam kowa ya dauko abunsa ya kawo mata ya mika mata daga mai kudi sai mai kayan mata da dai sauran su. Su *Nana Khadii* iyayen Mako ne bata bada komai ba. Haka suka mike saboda driver yana jiran su a yau zasu koma. *Nusaiba* ha da dab kwallanta ta raka su har bakin kofa suna musu godiya suka rabu. Nam suka dauki hanya su sis Nafisa basu so subar gidan ba saboda gidan ya hadu sosai. Nam suka dauki hanyar kumawa. Su Nusaiba ko suka kuma suka zauna suna dan taba hira ganin fa Angwaye basu da niyar zuwa ne yasa Yasmeen tace bari dai na kira Ya Mubajjal dare sai yi take yi. Sakina tace gaskiya kam ta dauki wayarta ta kira sa sai da ta kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa mata tare da cewa Yaya Muna ta jiran zuwan ku amma har yanzu shiro... kafin ta kara yace dama ai ban ce kowa ta jirani ba dan haka ku kama hanya ku tafi ba yanzu zan shigo ba daga haka ya kashe wayar. Yasmeen ce tace to kunki dai abun da yace dama Hand-free ta saka nam suka mike suka mata Sallam tana kuka suna kuka suka rabu Yasmeen ta jasu a motar ta suka yi gida._
*★★★★★★*
_" *Malika* ta sake baki tare da karasawa wajen *Mujahit* yace wanchar kuma waye take so ta bige minke dariyar yake tayi tare da sanar masa yadda sukayi. Sai da gaban sa ya fadi a yanzu ya sake tabbatarwa wannam *Sultanah* nan sa ce. To mai yasa *Sultanah* zata masa haka kenam?. Mai yasa bata Mutu ba za'ace ta Mutu?. Mai kuma tazo yi nam garin?. *Malika* ne ta katse mata tunaninsa ta hanyar cewa muje mana dan anaci yana ta masifa nam suka shiga motar *Nura* yaja su yana mita suka nufi Halwa I Cream. Wajene babba nam suka ta jidar Icream sannam suka zauna *Malika* da *Ikram* da kuma *Nura* ne kawai suke sha amma *Mujahit* ko kallon abun bai yi ba tunani kawai yake yi. *Nura* nevya lura da haka yace Abokina wai meke faruwa ne haka?. *Mujahit* yace ba komai kuyi kusaha mu tafi akwai abunda zanyi yanzu jin haka *Nura* yace kawai mu dauka mu tafi dashi *Malika* bata so haka ba amma suka tattara suka shiga motar suka tafi suka ajiye su a kofar gidan suka yi sallama suka juya.su kuma suka shiga gida. Suna juyawa *Mujahit* ya sanar masa duk abunda *Malika* ta sanar masa ya kara da cewa *Nura* babu makawa *Jawaheer* itace *Sultanah* ta. *Nura* yace Lalle nima yanzu na yarda da haka amma kana ga wacce hanya zamu samu dan mu gane itan ce. Da akwai hanya *Nura* kaga yau da ta gammu ta shiga damuwa sosai in har ta ci gaba da ganinmu da kanta zata zo ta fallasa kanta. Dole naci gaba da zuwa hira wajen *Malika* kuma dai-dai lokacin da *Sultanah* zata dawo daga aiki mu futo waje dancta gan mu dan *Sultanah* tana da matukar kishi. Gaskiya haka za'ayi to in kuka ka gane itan ce ya zaka yi da *Malika* . *Nura* ya zanyi da ita kowa dole sai na aureta dan bazan yau dareta ba amma inhar *Sultanah* ce Wallahi Zata kwacewa *Malika* fadar ta a waje na dab dama ba wani sonta nake ba wallahi kawai dai na rasa wacce nake so ne._
_Kuyi Manage da wannam Ina matukar Alfahari daku fan's dina wanda na sani da wanda ban sani ba Ina kaunarku a ko da yaushe_
*_NEXT PAGE IS LOADING......_*
_VOTES_
_COMMENT_
_08132761212_
*_MUMMYN SEEYAMA CE_*
[4/19, 7:24 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
*_Ummu Suhaimah_*
```Ina jin dadin hot comment naki ina yinki irin sosai dinnam```
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
```My bestynah Hafsat Hafnan ƙaunarki daban take a jikinah bani da tamkarki kin nuna mun ƙauna sosai Allah Ubangiji ya barmu tare Allah ya ƙara mana ƙaunar juna.```
*_Page 35&36_*
*★★★★★★*
_"Haka *Jawaheer* taci kukan ta sosai Tana haka *Doctor* yazo yasameta da sauri ya ƙarasa wajen ta tare da cewa haba *Sultanah* mai yasa kike haka kefa kika roƙeni akan nayi nesa dake daga garinku amma gashi yanzu kuma kina kawo wani abun daban kuma. Haba mai yayi zafi haka Dan kawai kinga *Mujahit* shikenam kuma ki ruɗe. Kiyi hakuri karki tona sirrin nam Allah zai baki wani da danginsa zasu soki. Cikin kuka tace Uncle bazan iya hakuri da *Mujahit* ba ƙawata fa yanzu yake soyayya da ita gaskiya zan faɗa masa gaskiya. Dan ina son *Mujahit* sosai wallahi bazan iya rayuwa batare da shiba ada na haƙuradashi saboda bana ganinsa.amma yanxu ina kallonsa bazan iya haƙura ba. Jkin sa yayi matuƙar sanyi yace to shikenam Sultanah Allah ga baki sa'a Allah yasa ya dawo gareki. Ta Amsa da Ameen Nagode *Uncle* . Daga haka yayi mata sallama tare da fatan nasara yazo fita kenam ya haɗu da Rahmah kallonta yayi tare da cewa Rahma kin shigo kenam cikin dauriya tace Eh UnCle Ina wuni. Lafiya ƙlao ya mutanan gidan ku. Duna lafiya daga haka yayi waje ita kuma ta ƙarasa ta zauna kusa da Jawaheer ta na cewa ashe duk labarin da kika bani na ƙarya ne shine kika bani labarin Sultanah ashe shine labarinkin mai yasa kika ɓoye min?. Miye ribarki nayin hakan?. Mai yasa kika bar Mahaifiyarki kika dawo nam?. Mao yasa aka sanar da cewa kin mutu Alhali da ranki da kuma lafiyarki?. Haba Jawaheer. Cikin Kuka Jawaheer tace zan sanar miki da komai Rahma Amma kiyi hakuri zuwa anjima in munyi Sallar i'sha. Allah ya kaimu lokacin cewar Rahma tana buga Uban tagumi. Babu wanda ta kara magana a cikinsu har aka kira sallahr I'sha suka mike kowa ta ɗauro al'wala suka zo suma gabatar da Sallah kowa tayi ta zabga Addu'a barin ma Jawaheer .sanam Jawaheer ta fuskanci Rahma tana hawaye tace yau zan sanar miki *Abinda aka gasa..!* yau zaki san ya aka yi ban mutu ba yanzu kuma zaki san dalilinah na barin Ahalinah na dawo nam.ta fara da cewa._
```SHEKARU SHIDA BAYA```
_"Nam ta sanar da ita labarinta kaf fa ƙara da cewa a lokacin da Doctor ya shiga dani domin ya dubani yayi nasarar ceto rayuwata dama Numfashi nane ya ɗauke ya tsaya chak. Ina farkawa yace sannu baiwar Allah. Nace masa yauwa Doctor na gode da taimako. Yace ba komai yanzu ina ne ke miki ciwo?. Nace ba ko ina. Yace Alhamdulillah. Doctor dan Allah inaso ka min wani taimako._
_"Nam ya dawo ya zauna yace ina jinki.Allah yasa zan iya taimakonki. Insha Allah ma zaka iya na ƙara da cewa dan Allah Doctor in ka fita ka sanar dasu bana raye na mutu saka makon jinin dana bayar. Cikin firgici yace ke kuma miye ɗalilinki da zaki fadi haka. Cikin kuka nace saboda babu mai ƙaunata a duniyar nam, duk wanda ya sanni kuma yasan Labarinah sai ya tsane ni Alhali ba laifinah bane.Nam ta sanar dashi labarin rayuwarta ta kata ɗa cewa kaga in aka ce na mutu shikenam tsangwama da kyara ya ƙare.kaga zan bar garin zan kuma damu Mijin Aure dan Allah ka taimake ni. Share hawayensa yayi yace to in nace kin mutu ina zaki je?.kuma in za a sallace ki fa?.Duniya zan shiga har Allah ya hadani da mutane na gari, zancen gawa kuma nasan baza a rasa gawar da aka rasa danginta ba kaga shikenam an wuce gurin. Doctor yace zancen ki shiga Duniya bai taso ba, inhar kin amince akwai gida na da nake zaune da Matata aka min sauyin gurin aiki muka dawo nam mai aikin mu ce kawai a gidan a garin Abuja. In kin yarda zan kaiki chan ki zauna har Allah ya kawo miki miji, inhar kuma baki yarda ba nima bazan taimakeki da komai b a. Cikin kuka tace na Amince nagode Allah Allah ya saka maka da gidan Aljannah. Nam ya fita ya sanar musu. Tana jin yadda Mujahit yake kuka nima kuka nake sosai. Haka kuwa akayi aka dauko wata gawa aka mata wanka aka basu ita a maimakon nii. Aka kaita gidan ta na gaskiya. Sai dare tukun muka tafi da Doctor gidan sa Matarsa da taji labarina tayi kuka sosai a gidan na kwana, washe gari da safe muka ɗauki hanyar Abuja da Doctor da matarsa. Domin Aunty Aisha taki zama ita dole saita rakoni muna isowa banji mamakin ganin katafaren giɗan ba dan gidan da Doctor yake ciki nah Sokoto yafi wannam komai. Sallama mukayi muka shiga Baba Asabe wato mai aikin gidan ta amsa mana tana mana lalle marha bun._
_"Nam muka gaisa Doctor yayi mata baya ni ya kara da cewa zata zauna a gidan nam har Allah ya kawo mata Miji na gari. Baba Asabe tayi murna sosai dan dama bata son zama ita kaɗai ta nuna min ɗakin da zan zauna. Du Doctor basu tafi ba sai da ya siyomin duk abunda yasan zan buƙata tare da sayan kaya ya kaiwa tailer ya zo ya ganni tare da masa Alƙawarin nam da sati zai kawo min ɗinkin sannam suka tafi. A ranar na fara sabuwar rayuwa kullum ina cikin kukana rashin sanin halinda Umma nah take ciki, Baba Asabe tana bani kulawa tamkar ita ta haifeni kullum Doctor da Aunty Aisha sai sun kirani domin suji lafiyata kasan cewar ya sayamin waya kafin su tafi. Wata na. Biyu a gidan, Doctor ya juna min school jami'a da taimakon Allah tunda na fara ban samu matsala ba Samari ki nayi su kamar miye. A haka dai har na kammala na samu aiki a Hospital na kuɗi albashi na dubu talatin duk wata. A nam ne kuma na haɗu dake Rahma kika zama Aminiyata. Yanzu haka Baba Asabe watan ta ɗaya a garinsu taje ganin gida. Rahma wannam shine Labarina na ɓoye hakan ne saboda a Aureni da mutunci. Ba tare da wanda zan Aura yaji labari nah na gaskiya ba. Wallahi ina matuƙar ƙaunar mujahit kawai dai babu yadda zanyi ne nasan danginsa basa sonah. Ta fashe da kuka Rahma ma kuka take nam suka rungumi junah suka ci gaba da kuka mai sosa zuciyar mai karatu._
_"Tunda su Yasmeen suka tafi Nusaiba ta ke cin kuka sosai tayi kuka kamar ranta zai fitaSai karfe 12:00pm ya shigo tana jinsa tana kwance ta lullubu dan wani zazzaɓi ne ya kamata. Sai 1:00 sanna ya shigo ɗakinta. Yana shigowa ya sameta kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali. Wani wawan duka ya ɗaka mata da sauri ta mike tana mai......_
```Kuyi hakuri da wannam my fan's ina matuƙar Alfahari daku sosai ina jin dadin comment naku Allah yabar mu tare```
```NEXT PAGE IS LOADING.......```
_VOTES_
_COMMENT_
08132761212
*_MUMMYN SEEYAMA CE_*
[4/19, 7:25 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
```Wannam Page Sadaukarwa ne ga duk wani Maraya da suke fadin duniyar nam```😭😭😭😭😭😭
*_Page 37&38_*
*★★★★★★*
_"da sauri ta miƙe tana daka wani ƙara a zaton ta wani kwarton ne ya shigo mata wani tsawa ya daka mata tare da cewa ke ban son shashanci ba wannam wani irin hauka ne zaki sa makwafta suce ko yankaki nake yi. Maganar ta bata dariya sai dai kuma ba halin yin dariyar nam ta marairai ce fuska tace to Yaya Mai na maka? zaka min irin wannam ɗakar. Wani wawan mari yayi mata tare da cewa dan Ubanki ni kike yiwa wannam tambayar lalle ma kin raina ni. To wallahi ki sani baza ki taba zaman daɗi a gidan nam ba kin dinga fuskantar cin mutunci da barazana a gidan nam wawiya kawai. Daga haka yayi fice warsa tare da buga wani uban tsaki._
_"Abun ya bata mamaki bata ɗauka ƙiyayyan da yake mata ya kai haka ba sai yau gaskiya baza ta iya zama da shiba haka take ta magana ita ɗaya kamar zautacciya da taga dai kukan bazai kai taba taje da ɗauro Alwala tazo ta fata kai kukan ta wajen Ubanjigi. Sai da ta kai 3:00am sannam Ta zauna ta fara azkar har Assalatu Sannam ta gabatar da Sallah anan wajen bacci mai nauyi ya ɗauketa. Shiko tun daga fitarsa a ɗakin ya shiga ɗakinsa wanka yayi yazo ya zauna yana chart abunsa yana cin gasassaun kajin da ya siyo ko a jikinsa ya ma manta da wata amaryarsa yana gamawa yabi lafiyayyar gadon sa._
_Washa gari sai wajen 11:00 na rana Nusaiba ta tashi nam ma Wayar da aka kirata ne ya tada ta. da Salati ta mike ta ɗauki wayar Sister Yasmeen ta gani da Sauri ta ɗauka kafin tayi magana Yasmeen tace Auntyn mu kin tashi lafiya gamu nam zamu zo gidan ki dasu Sakinah zasu wuce yau. Cikin murna tace to Allah ya kawo ku lafiya. Ameen Amarya ya dai kike cikin murna ko dai Yaya jiya yayi aiki ne. Hawayen da take tarewa ne suka gangaro mata ta katse wayar Yasmeen bata kawo komai ba. Suka fara shiri. Itama wanka ta faɗa ta fito ta shafe jikinta da mayuka masu ƙamshi. Sannam ta ɗauko wasu Lace ta saka pink colour yayi matuƙar yi mata kyau sosai. Kwalliya ƙadan tayi sannam ta shiga kitchen tama rasa mai zata ɗaura musu. Nam ta tuna Yasmeen nason Sinasir da miyan kaji. Tana bude firji ta ga kaji guda uku ɗaya ancinye rabinsa cikin murna ta kammala komai tana cikin kaisu dinning ne sai ga Norking din su da sauri ta buɗe tana sakar musu murmushi._
_"Suna shigowa suka rungumi juna a murna nam suka zauna a falo suka fara gaisawa sai tsiya suke mata ita ko dariyar yaƙe kawai take musu dan ita tasan wani hali take ciki daga jiya zuwa yau. Dan yau kam ko ida nunsa bata gani ba. Yasmeen ce tace yanzu kam dai kinji abun da muka ji muma na aure shike nam nam da wata Tara zamu zo musha suna hawaye da take ƙuƙarin tarewa ne ya subuce nam dana idanunta suka cika da hawaye. Yasmen cikin ruɗewa tace haba Nusaiba lafiya?.mai yayi zafi haka. Kafin ta bata amsa ne Mubajjal ya sauƙo daga ɗakinsa cikin shigar ƙana nam kaya. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa a murtuke take. Yace ke Nusaiba zo nam daga haka ya shiga ɗakin da ke kusa da su. Da sauri ta miƙe yasmeen dai ido ta buɗe yadda taga Yayan nata yayi kamar bai san taba. Rahinah tace anya ƙalau suke kuwa?. Sakinah tace gaskiya ba ƙalau ba kam. Yasmeen ce tayi ƙarfin halin cewa aiko indai Yaya ne zakuce haka to bari kuji ƙalau suke zaune dama shi haka ɗabi'arsa take miskilin mutun ne. Sakinah ta taɓe baki tace to Allah ya basu zaman Lafiya. Duka suka amsa da Amin._
_"Nusaiba tana shiga da Sallama ta samesa zaune akan gado yana dannam waya. Dur ƙusawa tayi tare da cewa Ina wuni Yaya. Kamar bazai amsa ba yace Ƙalau. Daga nam shiri ya ratsa tsaka ninsu ita dai tana tsugune sai bayan mintina yace._
_"Mai kika sanar dasu dan gane da zaman mu jiya. Cikin Ƙarfin hali tace Babu abunda na faɗa musu Yaya._
_"To in kika sake naji wata magana kin sanar dasu wallahi zaki sha wahala a waje na. Insha Allah bazan faɗa musu komai ba. "Daya fi miki Alheri ki kawo min abinci na. "Ta amsa da To,daga haka ta mike ta fita kamar wanda ƙwai ya fashe mata a ciki. Shike da wata harara ya bita dashi._
_"Tana fita ta samu suna cin abinci dan Yasmeen ta gaji ta jiran fitowarta ne tace musu kawai suje suci abinci. Tace Yauwa Yasmeen dama ganzu zan zuba muku. Yasmeen tace to mu yau ina zamu tsaya jiranki kun maƙale a ɗaki. Nusaiba bata tsaya bata amsa ba taje ta hada masa komai da tasan zai buƙata sannam ta ɗauko ta fito ta shiga ɗakin da Sallama ta ajiye masa a gaban sa ta miƙe zata fita kenam yace ke dan Ubanki haka ake ajiye wa miji abinci ki dawo ki saka min. Jikinta na bari tazo ta saka masa ta juya ta fice tana goge ƙwallar da ta fito masa._
_"Su Yasmeen sun lura da halin da Nusaiba take ciki amma tambayar duniyar nam sun mata amma sam taki basu Amsa. Haka dole sukayi haƙuri. Mubajjal ko da ya fito a cikin fara'a suka gaisa Nusaiba tayi mamakin haka wato ni kaɗai yake yiwa wannam tsimewar. Haka da yazo fita ya ɗauki bandir ɗin yan dari biyar ya miƙawa su Sakinah yace suyi ƙuɗin mota._
_"Suka ƙarɓa tare da godiya bai bi ta kan Nusaiba ba yayi ficewar sa. Anam suka wuni har yamma Sannam Suka mata Sallah harda kukan ta dam sam bata son zaman gidan._
```Niko nace tun daga yanzu ai tunda kika yarda aka ɗaura Aure keda barin gidan nam sai mutuwa😹```
_"Haka taci gaba da rayuwa a gidan Ya Mubajjal kullum da abun ɗa yake mata na azaba kuma ko ɗaya babu wanda ta sanarwa yanzu Auren su Waya biyar kenam amma babu abunda ya taba shiga tsakaninsu shi a ban garen sa gani yake in har ya kusanceta babu abunda zai samu a gurin ta sai sauran Sado mai shago shi sam bai jin xai samu gamsuwa gashi kuma da shegen jaraba shi gani yake ma tunda yayi Auren Jarabarsa ta ƙaru amma sam bazai iya kwanciya da ita ba. Sai dai kawai ya ƙara Aure._
★★★★★★
_"Su Jawaheer sai da sukayi kuka mai isarsu sannam Rahma tayi ta bata haƙuri sannam tayi shiru. Nam Rahmah tace kiyi haƙuri insha Allah sai kin Auri Mujahit da yardar Allah. To Allah yasa Rahma. Ameen cewar Rahama tace miƙe tace sai da Safe Sultanah ki kwantar da hankalinki. Ba komai Rahma nagode ki gaida du Hajiya._
_"Daga haka ta fito tayi gidan su tana tausayawa Sultanah sosai tana kuma tunanin wacce hanya za subi dan ganin Mujahit ya fahimci Jawaheer itace Sultanah._
_"Tana wannam tunanin har ta isa gidan su Hajiyarta ta samu tana zaune tana jan charbi. Sai da ta kammala sannam ta ɗago tace ke ko a ina kika zauna haka?. Nam Rahma ta sanarwa da Hajiya duk abunda ya tsaida ta ta ƙara da cewa Wallahi Hajiya Jawaheer tana cikin damuwa sosai. Hajiya tace Allah Sarki wallahi na tausaya mata sosai Allah yasa Masoyinta ya dawo domin wallahi shi ya dace ta Aura. Dan shi mai rufe mata Asiri ne. Haka suka yi ta tattauna maganar._
_"Haka Mujahit yake zuwa wajen Malika babu randa bazai je shiga. Abun tun yana bawa Malika Mamakk har ya dai na bata dama ita kam tafi son kullum tana ganinsa. Yau kusan wata guda kenam Amma har yau bai sake haduwa da Sultanah ba. Kuma a dai-dai lokacin da take dawo wa daga gurin aiki suke fitowa sai sun jima a tsaye sannam yayiwa Malika Sallama ita dai bata kawo komai ba._
_"Yau ma Kamar Kullum Suna tsaye a bakin ƙofa tana sanar dashi yaushe zasuje hada kayan Aure domin Bikin Saura wata Uku ne. Mujahit yace ni ai kenake jira yanzu duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake._
_"To Sai muje Gobe ko?.Allah ya kaimu. Bai gama rufe baki ba sai ga Motar Sultanah ta shawo kwana. Malika tace yauwa ga ƙawata da nake nema zata hada min Kayan Sokoto dan naji tayi zaman Sokoto nam ta tsaida ta da kamar baza ta tsaya ba amma ta tsaya Malika ta ƙarasa tare da cewa kaga ƙawalliya kullum sai naje na samu bakya nam. Sultanah tace eh wallahi aiki kwanan nam yamin yawa kullum a chan nake kwana yau ne na samu na dawo. Nam suka gaisa take cemata dama maganar mu ne na maganin Sokoton nam Auren fa Saura 3month Da ram kirjinta ya buga tace What! Tare da zaro idanu. Malika tace Yeah! Sultanah bata tsaya ba ta figi motar._
_"Abun ya bawa Malika Mamaki sosai nam Mujahit ya sameta ganin tayi mutuwar kasko. Yace lafiya kuwa. Nam ta sanar dashi abun da yake faruwa ta ƙara da cewa na rasa mai yasa tun randa ta gammu tare ta sauyamin fuska ko dai ka santa ne?. Ta faɗa cikin sigar Tambaya. Yace to bana ceba kinsan mu ɗa jama'a ƙila ta sanni ni kuma ban santa ba. Nam ta sauke a jiyar zuciya suka yi Sallama yana shirin shiga mota Suka ji kira kamar daga sama ana cewa Mujahit! Mujahit! ka tsaya._
*_Wacece Malika_*
```Senator Bashir Ahmad Shine Sunan Mahaifinta Babban ɗan siyasa ne kuma dan Kasuwa ta fanni daban-daban. Senotor Bashir babu wanda bai sanshi ba yana da Mata Ɗaya Hajiya Naja'atu. Yaransu Uku Allah ya basu Malika itace babba Sai Kuma Ikram Sai kuma Ɗan ƙaninsu Shureem yaran sun taso cikin so da ƙauna musamman ma Malika dan iyayenta suna matuƙar ƙaunarta musamman mahaifinta ya sakaltata sosai bata da kunya ko kaɗan in dai tace zatayi abu to fa babu wanda ya isa ya hana ta inko tace baza tayi ba babu wanda zai iya saka ta haka kuma ba'a mata faɗa komai yinsa take tamkar bata da mafaɗi amma kuna a kwaita da ƙwalliya sai dai kuma har yau bata iya girki ba dan bata taba shiga kitchen da sunan girki ba sai dai ta ɗi ba Amma kuma akwai kyau komai na duniya ta haɗa sai kishi na masifa da ta ɗaurawa kan ta Ikram ita ko babu ruwanta salihar macece mai hankali da sanin darajar na gaba da ita komai da ake so mace ta iyasa ta fannin gida Ikram ta iya sa dan sam bata barin Binta mai aikin su ta shiga kitchen ita kaɗai in har tana gida tare zasu shiga shiko Senotor ba mazauni bane kullum baya gida yana wajen kasuwancin sa.```
*_WANNAN KENAM_*
```Zamu kuma Asalin Labarin```.
_Kuyi Manage da wannam Ina ƙaunar ku my Fan's Ina mai Baku haƙuri na rashin jina kwana biyu yachin banjin daɗi ne Hafsat A Garkuwa tana Ƙaunarku Over_
*_NEXT PAGE IS LOADING......_*
```Votes```
```Comment```
```please share```
0 comments:
Post a Comment