Su Ummy an dage wajen hada lefe na gani na fada, donma wannan coronar tahana fita waje da acan za'ayi sayayar Amma dukda hakan kayane ba gani na fada wanda kallo daya zakayi musu kasan anci uban naira.
6angaren daddy ma ba'a barshi abayaba don Kayan daki haddadu kayattatu yayi ordering har set biyu.
Ga shima ya hada mata nashi lefen na musanmman abinka da mai irin sana'ar.
Set daya na akwati wato akwati shidda maqare da kaya Nagani na fada yayima shalelenshi.
Niko nace anya be manta cewa auren na dan taqaittacen lokaci bane🤔
Bangaren mamy ma ba wasa, Kayan kitchen na musanmman take hadama angel dinta, abinka da ita kadai ce diyarta mace, Duk burin duniya ta Dora akan auren diyarta, sosai naira tayi kuka wajen hada Kayan kitchen din, shima Abba wato mijin mamy ba'a barshi abaya ba don dangin electronics wato su plasma, generator, deep freezer, ovens e.t.c
Duk shi yayi mata, abin dai zai😉
Su dangin mamy da Abba suma ba'a barsu abayaba don sosai suka bada gudunmawa dukda yanzu bawai kudi ke akwai sosai ba.
Sosai suke son Saudart saboda kirkinta da zumunci ga uwa uba girmama na gaba da son mutane.
Ataqaice dai kallo daya zakayima hidimar bikin kasan na yan gatane, yan gaban goshi kuma
Duk wannan haukan da'ake Daga amaryar har angon babu wanda yasan Anayi.
Kowa harkar gabanshi yake hankali kwance.
Don wani sa'in har mancewa da wani aure suke.
Bikin na sauran sati biyu mamy ta buqaci Saudart tadawo gurinta har zuwa bikin.
Alhaji shamsu be hanaba haka itama Saudart dadi taji sosai koba komai zata rage zaman kadaici tunda ga su Abdul.
Saida taje sannan tasan manufar mamyn na dawowarta nan, wato gyarata mamy zatayi ciki da bai.
Da farko taso qin yarda da Gyaran Amma da mamy ta tambayeta dalili Kasa amsawa tayi Dole t hqr ba don tasoba aka fara gyarata wasan zuciyarta kuma tasan asarar kudi kawai ake, Auren da na yan wattani ne?
Gyara sosai akema Saudart, abinka da yan Maiduguri.
Cikin yan kwanaki Saudart tafara riqidewa, ga dama yaya lfy giwa, dama can mai kyauce kuma tana bama fatarta muhinmmanci sosai take sheqi Amma yanzu tafi sheqi sbd dilkan da'ake mata ta musanmman.
Hakan a 6angaren Kayan mata da maganin Sanyi Duk ba'a barta abayaba.
Ingattatun Kayan mata da aka hada da fruits ake bata, ga yawan shan farfesu da ake sata tayi, gashi yanzu batada abinsha sai tattaciyar madara ko kindirmo.
Haka a bangaren lectures gameda auratayya, sosai mamy ta cire kunya ta zauna ta nusar da Saudart abubuwan da batasaniba gameda aure, tana kuma koyarda ita dubarun zama da miji, abinda wasu iyayen mata yanzu basu iyawa Wai kunya, qarshen kunya dai shine ki Tisa diyarki gaba ki bata Kayan mata, tunda itama tasan me kike bata da kuma amfaninsu tunda yanzu kai ya waye, a wajen karance karancennan ma wata Duk tasan komai.
So iyaye mata ba'a maganin mata kawai yakamata mu tsaya ba, mu nusar dasu miye auren da kuma abubuwan dasuka qumsa don dayawa yanmatan mu basusan ainahin menene auren ba sundai san in anyi aure ana tarraya tsakanin miji da mata, Amma basusan yadda zasu kula da mazajensuba dadai sauransu don ba'a koyamusu ba, Abu daya kawai aka koyamusu shine shan Kayan mata sai kiji har akwai mai suna, mallake miji, bita zai zai dade sauransu.
Babu abunda zaisa ki mallake miji yadawo tafin hannunki kamar biyyaya da tsantsan kyautatawa tunda zuciya tana matuqar qaunar mai kyautatamata.
Duk Kayan matan dazaki dirqa a banza don wasu sai sunason harkar zasu mutuntaka daka basu sun gama nan take suna iya sufkama rashin mutunci, Amma mace mai biyyaya da kyautatawa bazata ta6a wulaqanta ba awajen mijinta.
Tun Saudart najin kunyar mamy idan tafara mata ire iren lectures dinnan harta Bari don mamy ba ruwanta.
Su Abdul baseet sunji dadin dawowar Saudart gidan don sosai take debe musu kewa.
****************************************************
"What?! 5 million? 5million? Kam bala'i? Lallai kana wasa da wuta"
Afusace ya miqe ya nufi hanyar waje ko Dora suit dinshi dake rataye beyiba.
Kwankwasawa yayi a afusace ya murda ya bude batareda yajira anmashi isoba.
Dagowa Sadeeq yayi yana kallonshi sai huci yake kamar mayunwacin zaki.
"Toha, lfy ango kasha qamshi? Wannan dirar mikiya haka? Ai sai Kasa in arci na dog"
"Sadeeq ina wasa dakai?" Yafada cikin Fushi
"Ehh" yabashi amsa hankali kwance.
"Dan ubanka Kalla, Kalla nace" yafada yana shaqoshi yana nunamishi screen din wayar shi.
"To ai ta dauke mallam, Wai ya haka? Ka sakarmin wuya"
Sake Kunna wayar Ashraf yayi sannan yaqara haska mishi
"Ubanmi aka rubuta?" Injishi yana huci
"Anyi withdrawing 5million" Sadeeq ya amsa yana matse idanu sbd shaqarar da Ashraf yayimashi.
"Dan ubanka me kayiman da kudi har 5million? Daga cewa za'ayi project saika zaremin 5million? Dan ubanka ina project din?"
"T...to ka sakeni mana in amsa"
Sakinshi yayi yana galla mashi Harara.
"Aradu badan Kai ango bane daka gane kurenka, mugu kawai"
"Naji, ina kudina?"
"Na cinyesu nikam, Haba!"
"Kasan Allah saika fadamin uwar ne kayi dasu"
"Mtcheew, banza to na cire naqara wajen hidimominka, Shikenan?"
"Wane hidima!"
"Bansaniba! Mtcheew dalla ficemin office aiki nake"
Shaqoshi yaqarayi
"Kasan Allah? Saika fadamin"
"Mtcheew to cikani"
Sakinshi yayi yana huci.
"Dan ubanka nufinka su mamy zasuyi maka komai? Nabasu 3million suqara wajen hada lefe kingin kuma zan bugo I.v sai aba Amarya kingin as pocket money, saima ka qaro wata 5million din don akwai events daza'ayi kuma munada buqatar money, real money"
Galala Ashraf yayi yana kallonshi tunda yafara mgn har yakai aya.
"Wai tsaya, come again, kana nufin da kudadena akayi wadannan abubuwan?"
"To da danawa? Bakada hankali, to Bari kaji jiya munyi mgn da qawar Amarya basu shirya wani event ba sai walima ta mata wanda zasuyi a bangarenmu kuma Ummy naji tace zasuyi mother's eve, Kaga kenan Kowanne bangare zaiyi nashi to Bayan daurin aure sai Ayi dinner gabadaya kafin ka shilla da amaryarka"
Ya karasa zancen yana kashe mashi ido daya😉
"Kaga dole mu basu enough money dazasuyi hidimar walimar hankali kwance, so please we need another 5million"
Kutt.. Kasama magana Ashraf yayi na wucen gadi.
Sai Daga bisani ya tashi yanufi kofa
"Kuma wlh kafara biyan bashi kenan Tun Daga wannan watan, saika biyani kudina don bazanyi asaraba wlh"
Dariya Sadeeq ya fashe dashi yana cewa
"Ba komai, yanzu yaushe za'a qaramana 5million din?"
,"kazo ka qwata don ubanka "
Yafada yana ficewa cikin Fushi.
*****************************""""'
"Wai Ashraf meke damunka ne? Sbd kawai zakaje ganin amaryar ka saika wani dinga jamana tsaki kamar wata tsaka? Aida Tun acan kace Baka zuwa bawai kazo nan ka cikani da tsuwaba"
"You know what Sadeeq, wlh idan Baka fita harkataba zan mugu mugun sa6amaka, munafiki Kasa bansan Kaine ka hada makalkashiyarba? Idiot dan sa idon kawai, wlh kaji haushi Sadeeq, banza mai zubin ifritai"
"Naji mallam, hakan dai bazai hana kajeba, shure shure baya hana mutuwa, kayi sauri kana 6atamun time ko nafasa rakiyar, ehe"
Takaici yaqara qume Ashraf, kwafa yayi yacigaba da shiryawarshi cikin 6ata lokaci dukdan yaba Sadeeq haushi Amma ko ajikinshi.
Saida yagama feshe jikinshi da turarruka sannan ta Dora hular kube yawani kasheta a gaban goshi.
"Kai kai Kai!! Kaga ango bada Lanka asare kaje gida kace yafadi, wannan gayu haka? Duk dan aaburge Amarya ne? Gaskiya Amarya saita rude idan taganka, Wai ja ganka kuwa"
Tsaki yaja yafice yanacewa
"Kasameni waje idan kagama haukan"
"Yo ai hikenan" yafada yana maramashi baya.
Saida sukayima Ummy bankwana, ta basu wata Leda Wai suba Saudart kuma tana gaisheta, Sadeeq ya amsa yayinda Ashraf harya kai waje.
Binshi Sadeeq yayi da sauri yana cewa
"To? Duk zumudin ganin amaryar ne haka, atleast kajirani mana tunda ko sanin gidan bakayiba, kuji qagarrare"
Banza Ashraf yayi dashi ya shige mota, shima Sadeeq mazaunin driver yashiga yarufo sannan ya tada motar suka shilla...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Ka jiqan wadanda suka mutu sanadinta da dukkan musulmai da suka rigamu gidan gaskiya🤲
Ya Allah ka jabanci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
026
Zaune take ta tankwashe kafaffu sai shan farfesun da mamy tayimata take tana yatsina fuska.
Murda kofar da'akayi aka shigo yasata saurin dagowa tana kallon kofar.
Mamy ce tashigo tana murmushi.
"Wai haryanzu baki cinyeba Angel?"
Kwa6e fuska Saudart tayi tana turo baki
"Mamy wlh babu dadi"
"Mtcheew, shirmamma, Allah ya shiryaki yanzu tashi kidan watsa ki chanza kaya kuma kiyi sauri nabaki minti biyu"
Da sauri ta tashi dama ba son sha takeba.
Girgiza kai mamy tayi ta dauke bowl din farfesun ta fice.
A gaggauce ta warwatsa ta fito ta saka wata yaloliyar Riga ta fada kan gado tana Jawo wayarta tana danne danne.
Shigowar mamy yasake katseta.
"A'a? Meye haka? Baqi fa gareki kinwani kwanta, common change to something decent kizo ki fice"
"Baqi mamy? Su waye?"
"Bansaniba"
Tashi tayi ya chanza rigar jikinta da wata jallabiya jaa ta dora zumbulelliyar hijabi baqa akai wanda tsawonta yakai har idon qafa ta zura hannayen hijabin sannan tadan murza turare mai sanyin qamshi ta fito.
A falo ta tarda mamy zaune.
"Kiyi sauri dama kin 6atamusu lokaci, suna falon baqi, zan aiko Kamal da refreshment"
"Tou mamy" tace tana ficewa tana tunanin ko suwaye baqin.
Sallama tayi bakin kofar falon.
Saida taji an amsa sannan ta sanyo kafa ahankali tashigo kai a qasa.
Haka kawai taji gabanta yafadi batareda wani daliliba.
Kallo daya tayimusu na second daya ta dauke kai, hakan yasa tasan su biyune Saidai bata gane kosu wayeba.
"A'a? Gimbiya qaraso, lale sannu da fitowa sarauniya"
Jin muryar sadeeq yasa gabanta sake faduwa, to? Dama yasan gidansu? Shida waye?
Cikin nutsuwa ta isa kujerar dake facing dinsu ta zauna sai a sannan ta dago cikin nutsuwa ta kallesu.
Idanunta ne suka sauka cikin ba Ashraf dake maqale da waya a Kunne alamun waya yake.
Wani kallo ya watsamata wanda yasata saurin dauke idanu ta maidasu kan Sadeeq daketa yashe baki.
"Sannunku dazuwa, ina wuni"
Tafada cikin murmushi
"Lfy qalau gimbiya, ya hidima?" Inji Sadeeq yana dan take qafar Ashraf a fakaice alamun yabar wayar hakanan mana.
Yana jinshi yayi kamar besan abinda yakeba saima qara relaxing dayayi a kujera yana cigaba da amsa wayar shi cikin murya qasa qasa don ko Saudart batajin abinda yakecewa.
"Alhamdulilah" tafada tana ta6e baki cikin zuciyarta tana cewa, Masu hidima dai yakamata kayima ya hidima ba niba.
Kamaldeen yashigo da tray dake dauke da Kayan motsa baki da drinks da sallama a bakinsa.
Amsawa sukayi suna kallonshi, Qarasowa yayi ya ajiye saman centre table din sannan ya gaidasu a ladabce
Amsawa sadeeq yayi fuska asake while Ashraf yayi mashi murmushi kawai.
Juyawa yayi ya fita.
Shiru ne yadan ratsa falon.
Ganin wayar Ashraf ta iskanci ne yasa sadeeq miqewa.
"To Bari kuga yadda za'ayi"/yafada yana qarasawa centre table din ya dauki qaramin plate ya koda snacks ciki ya dauki robar hollandia daya yana cewa
" Ato, bari nabaku wuri Ku soye, kunsan masoya basu cika son shishigiba"
Yana kaiwanan ya fice ya koma garden ya zauna ka daya Daga cikin kujerun shaqatawa ya zauna, ya fara aika abinshi yana yi yana danne dannenshi a waya.
Tsit falon yayi yasake yin wani irin shiru sai qarar ac da akeji saikuma muryar Ashraf da ake danji qasa qasa alamun haryanzu be gama wayarba.
Itadai Saudart haryanzu kanta sunkuye yake don batama son sake kallonshi.
Sai tambayar kanta dalilin zuwanshi gidansu take.
Idan bata manta ba rabon data ganshi Tun wajen gathering, kusan wata daya kenan.
Shikau dakyar yagama wayar don dama sungama maganar dasuke kawai qara Jan mutumin da magana yake don beson ko kalma daya ta hadasu da Saudart, sai gashi mutumin ya kawo excuse na zaiyi attending din wasu.
Komawa yayi ya jingina da kujera yayi irin wannan shegen zaman dake bata haushi yacigaba da danne danne awaya.
Tsaki taja a zuciyarta ji yadda yayi wani balancing kamar yana dakinshi.
Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana ita kanta qasa tana wasa da yatsunta, shima kanshi saman waya yana danne danne.
Sun dade ahakan Amma babu wanda keda niyyar motsawa, dukda kowa ya gaji da zaman.
Saudart Jitake kamar ta tashi tayi tafiyarta Amma ta hqr atleast gidansu ne, su kwana haka.
Shima Ashraf da ba abinda yake awayar Saidai yashiga nan yashiga can jiyake kamar yabar dakin Amma jin kanshi yaqi bari don be iya ma tashi ya taka gabanta, Wai raini zai jamashi.
Haka sukaita zama kowa da abinda yasha mashi kai, sunfi awa daya ahakan Amma still babu wanda jinkai yabari yayi magana.
Yadda kasan kurame aka akai zaman.
Sadeeq dadai yaji shirun yayi yawa kuma dare qarayi yake ya miqe yana daukar plate daya rage snacks yan kadan ya taho.
Da sallama yashigo, ga mammakinshi yadda yabarsu haka ya taddasu.
Ga Kayan motsa bakinda aka kawo musu ko alamar anta6asu be ganiba.
Basarwa yayi ya qaraso yana murmushi
"A'a romeo and Juliet, wannan soyewa haka, naga fira yayi dadi ko niyyar kirana bakuda shiyasa na dawo"
Murmushi kawai Saudart tayi akunyace.
"To mallam romeo mujeko? Ko anan zamu kwana?"
Ta qasan idanu ya watsa mashi mugun kallo sannan ya miqe yana saka wayar shi aljihu sannan ya fiddo bundle din yan dubu dubu biyu ya ajiye saman table sannan yasa Kai yafice cikin takunshi ba qasaita.
Binshi da kallo Sadeeq yayi yana qumshe dariya.
'Shege da Baka badaba dana haddasa bomb yau tsakaninka da Ummy, marowaci kawai' Duk a zuciya yayi wannan zancen.
Shima tashi yayi ya Dora ledar da mamy tabasu shima da wrapper din #500 daya sannan yace
"To amarsu zamu ruga qauyanmu"
Da murmushi ta dago
"Ayyah, to Allah ya tsare. Agaida gida"
"Gida zaiji kwarai, mungode"
Nan ya miqe sannan ya fice.
Ajiyar zuciya tayi tana rolling dara daran idanunta.
Miqewa tayi itama tafice Bayan ta daidaici sun tafi.
A falo ta tarda mamy kamar dazu.
Amsa sallamarta mamy tayi sannan ta Dora dacewa
"Da harna fara shawarar zuwa kiranki, wannan zama haka?"
Ta6e baki Saudart tadanyi sannan tace
"Mamy Bari in hau"
"To, asauko lfy"
Ibrahim mamy tasa yaje ya kaikaye falon nan yadawo hannunshi dauke da Leda da kudaden da suka ajiye mata.
Ganin kudaden yasa mamy dan zaro idanu
"Wannan fa Ibrahim?"
"Kan centre table nagansu"
Amsa tayi tana jujjuya kudin sannan ta leqa ledar, Waro idanu tayi ganin abinda ke ciki, fiddosu tayi tana kallo, wasu haddadun turraruka ne hudu set, kallo data zakamasu kasan tsadaddune.
"Kiramin Antyn taku"
Da gudu ya haye sama itakuma ta cigaba da jujjuya Kayan hannunta.
Bayan yan mintuna saiga Ibrahim tareda Saudart sun sauko.
"Mamy gani"
"Saudart wannan fa?"
Sai lokacin ta tuna dasu don Duk taga sanda suka ajiye.
Su suka kawo, ba ledar Wai mamansu ta aikomin.
"Masha Allah, Amma kingode Amma kudin sunyi yawa da baki amsa ba"
Ta6e baki tayi a fakaice sannan tace
"Mamy ajiyewa fa yayi yawuce, bema saurareniba"
"Dukda hakan, Amma kau kingode, ki tabbatar kin kirashi kinmashi godiya most especially mamanshin don wlh idan kikaji kudin perfumes dinnan saikin riqe baki"
"Tou, zan kira"
Tafada deep down tana cewa Basai inada number dinshi ba?
Haka mamy taita santin Kayan kafin Daga bisani ta sallameta.
Wayarta tajawo ta Kunna data tahau WhatsApp
Kamar jira ake saiga message din baby na sticker din Daga hannu.
'Mayyar chatting' tafada cikin zuciyarta sannan itama ta tura mata sticker hyy.
"Aunty Duk yau baki hauba"
"Ni kece, kodayaushe kina online, ko wahala sub bakyaji"
Sticker din dariya baby ta aikomata
"Basai idan ni keyin sub dinma? Garori nake samu su cikamin waya da data"
"Allah ya shiryaki to, please kiyimin godiya wajen Ummy"
"Akan me?"
"Ina ruwanki? Ji gulma"
"Lol, kai anty Daga tambaya? Wai insan irin godiyar dazan matane"
"Babu ruwanki, kawai kiyimin godiya nace"
"To ko nabata kiyimata da kanki?"
Sticker din kallon kin rainani ko ta turamata sannan ta tura
"Ki kiyayeni baby"
Sticker din dariya baby ta turamata sannan ta rubuta
"Am sorry, zan gayamata, kuma Ku tanadarmin daki inanan tafe nanda kwana uku, saura sati biki kenan"
"Tofah, kiyi me? Bayan ana biki gidanku"
"Ai nanma gidanmu ne, idan dai ba son zuwana akeba"
"A'a me yayi zafi? Allah yakawoki lfy, kice zanyi babban baquwa"
"Kwarai kuwa don wlh ban zama nan lovely dinki yaita takurani babu gaida babu dalili, ya hanani rawar gaban hatsi"
"Kanku akeji, nikam zan sauka"
"To sauka lfy, sai kun ganni"
Sauka tayi ta kashe datarta sannan takoma tayi lamo akan gado tana tunani.
Wai yanzu dagaske aure za'ayi mata? Aure da wanda bataso kuma batajin zata ta6a sonshi? Auren da keda qayaddaden lokaci? Auren contract?
Ajiyar zuciya tasaki nannauya tana fadin Allah gani gareka...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
027
Abu sai matsowa yake, dama Duk Nisan rana idan Kasa zuwa zayayi.
Yau saura sati daya biki, gidan mamy yafara cika da Mutanen Maiduguri dama dangin Abba ma.
Saudart yau tana cikin farinciki sosai saboda wasu cousin dinta dasuka zo wato Nafeesa da mardeeya.
Qawayene sosai kuma yan uwa, Nafeesa diyar yayan mamy ce ita kuma mardeeya diyar kanwar mamy.
Tunda suka qaraso gidan yaqara hargitsewa, ihun murna Saudart taitayi data gansu don batayi tunanin Tun yanzu zasu tahoba don ko jiya sunyi waya sunce sai ranar Daren biki zasuzo Ashe plan suka shirya dukdan subata surprise.
Nanfa aka samu nayi tsokana kala kala babu wanda basuyi mataba, itama dayake bakin zaii yake kana mata fari zata maidama baqi, dama halinsu ne hakan, sunsaba.
Itama mamy a bangarenta ba sauki don Mamman mardeeya wato qanwarta itama tazo da ita za'a cigaba da shirye shirye kasancewar dama su biyune mata a family dinsu kingin Duk mazane.
Su shidda ne, maza hudu mata biyu.
Yayyan mamy uku, kawu bala, kawu Mamman da kawu shehu, sai mamy sai maman mardeeya sai auta kawu Yusuf.
Sosai suka hau hirar yaushe gamo sun wani baje a falo harda danginsu Abba don akwai kyakyawar alaqa tsakaninsu da mamy sosai, suna sonta sosai sbd kirkinta da faran faran dinta.
Shigowa Saudart tayi daure da qaramin towel a qirjinta iyakarshi cinya.
Ganin wayarta tayi hannun Nafeesa da alama bincike take mata.
Da sauri ta qarasa ta fizge tana danqara mata Harara.
"Uban me kikemin da waya?"
Dariya sukayi harda mardeeya dake tsefe kitsonta don gobe zasu wankin kai.
"Tofah, yaushe kika fara mana shamaki da wayarki?" Inji mardeeya tana taje inda ta tsefe
"Ato, ganemin hanya sis, hegiya Dama sonike inga dame akayi saving din surukin namu, Amma da alama babu number shi a wayar don sau uku kenan ina scrolling babu suna mai kamada nashi ko a call log banga makamancin sunan masoyi ba"
Harara Saudart Taqara lafta mata tana wucewa closet dinta tana cewa
"Ato, an gayamaku kowama baqauyene irin Ku? Yanzu qauyancine saving din contract din masoyi, real love shine ka hardaceta aka, sbd ire irenku Masu snatching"
Shewa suka dauka sannan suka kashe.
"Inyee? Kunji masoya, Wai snatching, uban wa zanyi snatching Bayan inada mukhtar dina dan sardidi son kowa qin wanda ya rasa" inji Nafeesa tana harararta
"Ato, wayasani Abu a duhu, wayasani ko naiman mararraba kike dashi, jira kike kiga handsome ki watsar dashi, mutum kamar dan chali chali qiris yake jira ka kalleshi ya 6arema baki Wai nan dariya yake, wannan kekam kin huta don ko Fushi yayi baki ganewa, tunda Maimakon ya hade fuska ke gani zakiyi kamar dariya yake miki. Sai kinji saukar mari sannan zaki gane Ashe ranshi a6ace yake"
Mardeeya saboda dariya har saukowa qasa take tana dafe ciki, Nafeesa ancika faam tashi tayi tanufo Saudart data gama saka Riga ta bita da gudu.
Zagaye dakin suka shigayi suna dariya.
Mardeeya tahau yin kida da tsinken tsifarta tana kuchasu mata kuchasu, kuchasu ba mai hanaku.
Suna cikin haka aka banko kofar dakin aka shigo, Duk Juyowa sukayi don ganin mai shigowa.
"Yeee! Antyna!!!"
Ta ruga dagudu ta rungume Saudart tana tsalle kamar wata yar yarinya, Saudart namata dariya.
Sukau Nafeesa sagale sukayi suna kallonsu, musanmman baby dabasu saniba, shigartama kadai zai saka sanin yar Masu kudine ga fatarta dake sumul sumul alamun Hutu.
"Wow! Antyna kinganki? Wlh kin hadu! Bari muyi selfie yau akwai status"
Tsaki Saudart taja tana tureta
"Kekam Allah ya shiryaki baby, ke kenan daukan pics da dorawa status. Nikam banso"
"Haba aunty please"
"A'a nikam"
"Wayyo Ummy, wlh anty kuka zanyi" tafada tana zaman yan bori kan gadon dakin tana kwa6e fuska.
Kallon juna Nafeesa da mardeeya sukai sannan suka maida kallon kanta.
"Please anty*
"Ok Amma kwara daya".
Ihun murna tayi ta taso taciro qatuwar wayarta ta kashe Masu selfie.
" wow! Wlh yaya ya iya za6e wlh kinma fishi kyau"
.tafada tana Dora hoton a status da caption din *me and my cute in-law*
Sai a sannan ta lura dasu mardeeya daketa kallonta, suna hada idanu suka janye idanu cikin basarwa.
"Laa, anty suwaye wadannan naga kunadan yanayi"
Murmushi Saudart tayi tana shafa mai tace
"Cousins dinane"
"Wow! Hyy" tafada tana Daga musu hannu fuska fall murmushi.
"Hyy" suma suka amsa suna mata murmushi.
"Kuna kama wlh Saidai Antyna tafiku kyau"
Yatsina fuska Nafeesa tayi tana cewa
"To kina buqatar spec sbd da alama biki kike gani, wannan ai itace hajiya munin cikinmu"
Baby nasamu abinda akeso, aka wani gyara zama sannan akace
"Wa? Ca6 in-law ai ta dabance, kyawunta kamar watane a Daren sha hudu, kuka jerama baza'ama lura dakuba saboda Tun Daga nesa zata dukkan daukan idanu"
Mardeeya tace
"Allah yasa ranace a qarfe sha biyun rana, wannan ai fari ya ceceta, da baqace da kau ba'a magana, cuss kenan"
"Atleast dai farin ya ceceta, wasu kau koda farinma ba kyau sukeba kullum ana cikin yima fuska kwaskwarima" inji Saudart tana Masu gwalo.
"Gayamasu dai anty, farar mace alkyabbar mata, wasu da makudan kudinsuma suke naiman farin, karshe atoye fuska a banza, Daga baya akoma multi colour"
"To kinga kenan kalar mu ce mai tsada, chocolate colour wanda baya saiduwa bare asiya, shi fari ana sayanshi baqifa?"
Haka sukaita cafta tsakaninsu, dayake baby batada baqunta tuni suka dinke yadda kasan dama sunsan juna.
Basu suka kwantaba sai sha biyun dare saboda fira.
Washegari da azahar suka fita dukkansu wankin kai, basuyi wani wahalar rabon iv ba saboda online invitation sukayi Basai anwani sha wahalar zirga zirga ba, anko ma Duk ta online aka turasu da dressing code din walima wanda Arabian gown ne baqa kowa zaisa, a dinner kuma kaya pink and blue za'asa.
A saloon din aka wankema dukansu kai, akayi musu stretching dinshi.
Zo Kaga santi wajen su baby da aka gamama Saudart, don hauka Wai shima gashin daukar shi hoto zatayi ta Dora status.
Dariya su Nafeesa sukaita yima diramarsu don dakyar baby ta hqr bata daukanba.
Nan aka musu manicure da pedicure, qunshi kuma sai saura kwana uku za'ayi.
Basu dawo gidaba sai gab da magrib don Saida suka biya shopping suka jidi Kayan amfani na biki wanda Duk baby ta biya.
Koda suka dawo Sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta don Duk a gajiye suke.
Washegari saura kwana biyar biki, ranar kuma za'a kawo lefe, tunda safe su Saudart suka fita kitso banda baby wanda tayi zuciya saboda tace tafison Saudart tabar gashin hakanan ita kuma taqiya shine tace bata rakiyar.
Da qarfe hudu na marece dangin A.A suka kawo lefe na gani na fada.
Set biyu shaqare da tsadaddun kaya da wata mota da aka sako Kayan ciki fara qall qirar Prado.
Sosai akayimusu tarbar mutunci da karamci kuma suka basu tukuici mai tsoka.
Baby kau sana'ar aka hau yi.
Hoto taita daukar Kayan da motar sai iyayi take.
Sai tsokanarta danginsu suke Wai tagudo gidansu Amarya ai datayi hqr har gida zatazo tasameta, ita taita biyemusu suna raha.
Yauma sai can magrib suka dawo sukaga gida haryanzu dinke da yan ganin lefe.
Jikin Saudart ne yayi Sanyi ganin akwatina baje tsakar falon, batace komai ba ta haye sama batareda tayima akwatinan kallo biyu ba.
Su kau mardeeya wuri suka samu suka zauna sunata duba lefen suna santi.
Koda Saudart tashiga daki kuka ya kufce mata ta toshe baki da tafin hannun damanta tana kuka.
Dagudu tafada kan gado tana kukan, Shikenan dagaske auren dai za'ayi mata.
Wayarta taciro takira daddy taita mashi kuka.
Sosai yaita rarrashinta, saida yasha wahala kafin yasamu tayi shiru.
Tananan kwance su baby suka shigo dakin, kamar hadin baki suka fada Mata ajiki.
Nanfa suka shiga tsokanarta baby na kareta, itadai Saudart banza tayi dasu don ba Sune gabanta ba.
Sai Daga baya baby tazame dankwalin Saudart taga kitson.
Nanma rudewa tayi don yau tamafi jiya rudewa.
Shikku akayi mata qananu an tamkesu da qaton ribbon ya sauko har wuya.
Nanma Wai hoton kitson zata dauka, dakyar ta hqr da daukar hoton don Saudart qin yarda tayi, su Nafeesa mezasuyi musu inba dariya ba suna musu ihun sunji Kansu.
Yauma sai kusan dayan dare suka kwanta, yayinda Saudart bata samu barci ba sai wajajen uku sbd yadda Taita juyi tana tunane tunane...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Ramadaan Ramadaan!! Ramadaan!!!
Watar alfarma Ramadaan
Wata mai cike da haske da ni'imomi Ramadaan
Watan da babu kamarsa Duk cikin wattani, Ramadaan.
To ya? Ko kun fara yima babban baqonmu tanaji?
Idan Baku faraba to Ku fara, mu dage mu kwashi gara6asar wannan wata mai albarka.
Mu nemi kusanci ga ubangijinmu mu kasance Masu yawaita istigfari, mu kasance Masu yawaita tilawar Al Qur'an mai girma.
Mu kwashi gara6asar wannan watan sosai don idan damar yin haka ya kufce mana ba lallai bane musake samun wata damarba domin babu mai tabbacin wani shekarar zai zagayo yanada rai.
Allah kabamu ikon yin tsarkakkaken ibada agareka a wannan wata mai alfarma🤲
Allah ka amshi ibadunmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
028
Yau saura kwana hudu biki, yau Saudart na gida bataje koina ba while su Nafeesa da la'asar sunje wajen tailornsu dasukaba dinki.
Zaman nata cikin kadaici yasata samun tunani da hasaso rikittaciya da 6audaddiyar rayuwar auren dazasuyi da wanda zata aura wanda a tarihin rayuwarta bata ta6a jin irin wannan auren yafaru awani wajeba.
Haka ta wuni zurr kwance dama ba tsarki garetaba so bata wani damu kanta wajen tashi ba, Saidai ta mirgina nan ta mirgina can, sam tarasa meke mata dadi.
Yauma da marece liss suka dawo kowa da shopping bag dinshi don shopping suka wuce Daga wajen dinki, itama Saudart sunmata nata sayayyar.
Nanfa aka dasa fira, uwar kaudi kau har gwada Masu irin rawar dazatayi take, kuma ba laifi ta iya rawa don sosai rawar tayimata kyau.
Nan ta zauna tana basu labarin qawayenta musanmman bestie dinta teema har tana cemasu karsu damu ai gobe zasu hadu a walima.
Haka sukaita hirarsu itadai Saudart na kwance tana jinsu idanu a lumshe, don abinda ya dameta ya daketa bata tasu takeba.
Washegari Tun goma nasafe mai qunshi wata yar Indonesia tazo gidan da ita da yaran aikinta biyu.
Nanfa suka kama aiki.
Ogan ita kema Amarya, yaran aikin kuma nama su yanmatan amaren.
Sai wajajen azahar aka gama.
Zokuga qunshi, ba irin jagwalgwalonmu ba🤣
Combination akayima Saudart jaa da baqi akayi mata wasu irin design kamar ba hannu yazanasuba.
Sosai qunshi ya hau da farar fatarta, suma su baby ba laifi nasu ma yayi kyau Saidai fa kunsan komai na Amarya yafi kyau.
Nanfa gida yafara dinkewa da jama'a yan walima dukda qarfe hudu za'a fara.
Su teema sai wajajen uku suka qaraso su biyar yan gayu yan kwalisa.
Nan suka hade aka fara 6arin iyayi, sai a sannan su Nafeesa suka gano dalilin kaud'in ta saboda Duk kusan haka qawayenta suke.
Nanfa daki ya hargitse da hayaniya kowa qoqari yake yafadi cikinshi, babu abinda ke tashi dakin sai shewa da surutu.
Da dai Saudart taga abin nasu azimun ne saita sulale tabar musu dakin takoma bedroom din mamy.
Wajajen qarfe 3:30pm saigasu maryam da Duk ma'aikatan bakery dinta mata.
Tafe suke da manya manyan robobi shake da snacks kama Daga cup cake, meat pie, doughnut, sausage roll, samosa, pizza, da dai sauransu.
Sosai Saudart tayi mammaki ganinsu da wadannan Kayan don kwata kwata batama Masu magana kwatankwacin hakaba.
Nan akayimusu maraba suma Duk sanye suke da baqar after dress wasu kuma Nada kwalliyar wasu kalolin.
Sosai Saudart tanuna jindadinta akan karamcin dasukayi mata wanda hakan ba qaramin dadi yayimusu ba.
4:00pm dai dai shaharrariyar malamar nan wato mallama wasila ta iso, izuwa lokacin harabar gidan dinke yake da mutane kowa cikin Arabian gown black.
Dayake harabar Nada girma sosai anan aka jera kujeru kowa ya zazzauna suna facing din inda mallamar ke zaune, itakau Saudart an tanadar mata mazaunin ta Daga gefen dama.
Saida komai ya lafa sannan aka fito da Amarya.
Wohoho nanfa kallo yakoma sama😳
Sanye take da atamfa Riga da skirt pieces Masu kalar jaa da fari saita Dora qatuwar alkyabba irinta ya'yan sarakuna fara qall mai aikin golden da zaiba , ta sanya hular alkyabbar wanda tarufe Rabin fuskarta.
Sosai akaita santinta saboda ta hadu iya hadewa, su baby Sune Masu tattare mata wutsiyar asoya dake Jan qasa harta samu ta qarasa wajenta ta zauna.
Nanfa akafara abinda ya tarasu, zikiri aka farayi mai ratsa zukata sannan aka dasa kirari mai sa jazaba don daidaikune wadanda basuyi hawaye ba Daga qarshe ta rufe musu da wa'azi mai ratsa jiki musanmman ga Amarya, tana gwada Mata nauye nauyen daya rataya akanta amatsayinta ba matar aure tana mata misali da Nana fadima da matan annabinmu Muhammad (s.a.w)
Sosai jikin Saudart yayi liqis, Kanta a duqe babu abinda take sai hawaye, don sosai wa'azin matar ya ratsa ga6o66in jikinta.
Sai wajajen shidda aka gama, nan aka shiga raba ledoji Masu dauke da sallaya ko doguwar hijabi da cazbaha hadeda snacks da akayi wrapping cikin irin wannan abun mai kyalkyali.
Anan na hango su tawagar yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP sun Kasa zaune sun Kasa tsaye kowacce burinta tasamu rabonta.
Can na hango ummu bilal ana ta miqa hannu za'a amshi Leda Bayan ga wata nan cikin qatuwar hijabinta sai kunbiya kunbiya take daita.
Dayan gefen kau sis hajara Nagani sai bin baby take kamar bindi Wai adole sotake su zama qawaye don tasamu hallatar dinner Bayan daurin aure.
Can gefe naga maman fateema da ummu arifullah suna leqa ledar juna don ganin me suka samu.
Itakau umman abdullra'uff ana gefe kan kujera sai gutsirar pizza ake ana tauna ana wani lumshe idanu (ba sabban ba🤣)
A can gefe kuma Mamman twins ce kamar tayi bindiga don bata samu komaiba, su twins sun hana🤣 basu tashi rikice mataba saida aka fara rabo, Maman twins fa ta kumbura, wazai kawo gudunmawar allura a saceta?🤣
Taro yayi taro inda aka hada malama wasila da shatara na arziqi, sai godiya take tana kwararowa auren albarka ana amsawa da amin.
Itakau Saudart dama ana gamawa tasamu ta silale daki ta kulle kanta tafada kan gado ko alkyabbar bata cireba sai kuka.
Sosai jikinta yayi Sanyi Jitake inama zata iya maida hannun agogo baya da kome daddy zaiyi da bata yarda da aurennan ba Amma inaa? Kin makara Saudart bakin alqalami ya buhe😏
Washegari kuma wato ranar Daren biki yayi daidai da ranar mother's Eve nasu Ummy.
Su baby amara qahon zuciyar biki don kau wannan Tawuce qirjin biki, shirya wa sukayi dukkansu suka wuce gidansu.
Babu yadda basuyi ba akan Saudart ma ta shirya sutafi tare Amma hausawa ma sunce shiru ma amsace don kwandon shara tasamu tasakasu ciki ta rufe.
Tafiyar su sukai suka barta ita kadai dama haka tafiso don taji dadin yin tunanin ta.
A gidansu A.A akayi mother's Eve din a garden dinsu dake can cikin gidan.
Sosai partyn ya qayattar, bawani chasu akayiba kawai zazzauna ake kowane table da kujeru hudu round dinshi ana zaune ana ci anasha ana fira ga wani sanyayan kida dake tashi a background.
A ataqaice sai 10:oopm su baby suka dawo gidan mamy kowacce agajiye liqis kuma kowa ce da burin data tanaddarwa gobe, wato ranar daurin auren.
*******************************************
Bankado kofar akayi da wani uban force kamar za'a qilleta.
"Gobene! Daga gobene fah! Gobene!! Gobene! Daga gobene haba! Gobene!"
Wani uban tsaki Ashraf yaja kamar bakin zai cire yana antayamashi wata uwa uban Harara.
"Waikai wane irin marar saiti ne zaka wani shigo na mutane daki bako sallama"
Yafada cikin Fushi
Daga hannuwa Sadeeq yayi alamun surrender yana dariya sannan yakoma bakin kofar ya kwala wata uwar sallama sannan yashigo.
Tsaki Ashraf yasake ja yana maida kanshi kwance yana cigaba da shafe shafen wayar shi.
"Ango! Ango!! Kaga ango wajen amaryar sa Saudatu tauraruwar mata, ango bada kanka asare kaje gida kacewa Ummy ya6ace, ango kasha qamshi, kana kuma cikin shan qamshi kuma zaka sha qamshi" ya qarashe zancen yana kashe mashi ido daya😜
Ashraf da tunda yafara 6a66atu yakeji kamar ya shaqeshi kowama ya huta ya juyamishi baya yana Jan tsaki.
"Ko tsakama datayi bataci ribaba, tsaki kamar wata tsohuwar karuwa, Nidai tashi su bash na falo don iskanci kawani zo ka qunqume uwar daka kamar wata sabuwar amarya"
"Bazan fitoba din! Kasan Allah Sadeeq? Wlh Allah zan mugu mugun sa6amaka, Wai ina ruwanka danine uhm? Dakai mayene dana kade har ganyena, wlh ka fita sabgata Tun kafin na shufkama rashin M"
"Tun yaushe kuma allaramma ango? Rashin m dinka ai harna saba dashi Kaga babu abinda zai tadamin hankali, oya miqe"
"Don ubanka miqar dani din" yafada cikin qulewa
"Wlh tsab kai kanka kasan ina iyawa Amma sbd kai angone Shiyasa nake ragamaka.."
"Dan ubanka karka ragamani, mtcheew dalla fita!"
"Yo ai hikenan, tunda hakan kakeso"
Yafada yana fita
Tsaki Ashraf yasake ja sannan yakoma ya kwanta, ba laifinshi bane don yaga nazo gidansu ne.
Be gama tunaninshi ba yaji ansake banko kofar, dagowar dayayi yaga su bash sunata shigowa sukai biyar da Sadeeq daya cika na shiddan.
Dafe kai Ashraf yayi yana komawa yana kwanciya, yasan yau tashi ta qare.
Nan kau suka hau tsokanarshi Tun yana Masu kumfar baki harya saduda don tsagerane suka hadu don wasu cikin su sunmafi Sadeeq qulluwa.
Haka ya zuba Masu idanu har suka gaji suka kyaleshi, shima saida yayi barcin qarya sannan suka shafamashi lfy, nan suka juya akalar firar zuwa na dinner gobe kowa na fadin albarkacin bakinshi.
Sai can wajajen dayan dare suka samu suka kwanta shikau Ashraf tuni dama barci yayi awon gaba dashi.
RANA BATA QARYA....✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu. Karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
029
RANA BATA QARYA......
Yau ranar jumu'a ce mai cike da tarihi a rayuwar wasu, jumu'ar da bazasu ta6a mantawaba.
Yau ne ranar daurin aurensu, AUREN KWANGILA.
Tunda ta farka ko matsawa Daga inda take batayiba, dama ba Sallah takeba bare ta tashi tayi.
Tana kwance ido lumshe kamar mai barci Saidai idanunta biyu tana sauraron Duk wani zirga zirga da hayaniyar mutane.
*yau ne* tafada cikin zuciyarta
*yau ba gobeba*
*yau zan zama matar aure*
*matar auren kwangila*
*matar mutumin da banajin ko digon sonshi daidai da qwayar zarra acikin zuciyata*
*matar aurenda nan da wani d'an lokaci zata zama baza wara*
*me kika yima kanki Saudart?*
*anya baki cuci kanki ba*
*anya daddy beso kanshi dayawa ba*
*inama ace mafarki ne*
*Allah yasa mafarki ne*
*Allah yasa ba gaske bane*
Hawaye suka silalo mata dukda idanun a rufe yake.
Wani nauyi taji zuciyarta nayi mata kamar an doramata qaton nutse a qirji.
Sosai hawayen keta silalowa batareda tayi wani yunqurin taresu ko sharesu ba.
Daidai nan mardeeya tashigo dama sunje amso dinkin anko dinsu ne dawowarsu kenan tabaro su baby qasa.
"Subhanalillah" tafada tana Qarasowa wajenta.
"Saudart" tafada tana dan jijjigata ganin idanunta haryanzu a rufe yake.
Banza tayi da ita Saidai hakan besa hawayen sun tsayaba.
"Sister menene? Dan Allah ki tashi, Meya faru?"
Nanma shiru saima juyamata baya datayi.
"Saudart kiyi hqr, nasan kukanki baya rasa nasaba da auren daza'a daura miki yau, Duk macen datasan ciwon kanta dole ta koka ranar aurenta ba don zata bar iyayenta kadaiba, don itama zata taka wani matsayi wanda bata ta6a takawaba a rayuwarta, nauye nauye zasu hau kanta wanda idan ba me dakkakiyar zuciya bace bazata iya dauke nauyin ba"
Kamo hannayenta tayi tariqe sannan cikin sigar rarrashi tace
"Sis kiyi hqr, Allah baya dorawa bawa abinda baya iyawa, ki kasance mai Neman tallafi a wajen Allah kuma ki kasance mai hqr, idan kinadashi ada ki Dora akai, darajar 'ya mace ke har namiji ma shine aure, ki kasance jajirttaciyar mace abun kwatance a fannin aure, ki zama abun alfahari ga mamy da daddy ke harma garemu gabaki daya, dukda aure rai gareshi idan ba'a mutu dashiba yakan mutu yabar ma'auratan don Allah aurenki yazama abin kwatance a family dinmu, babu yaji bare saki please, nafi kowa sanin yadda mamy ta kwallafa rai akan aurenki don sau ba adadi ina jinsu idan suna fira da ummina akan tanason kar aurenki yazama irin nata, tafison kiyi auren mutu-ka-raba, ya kasance yayanki duka nawajenki yadda zaki basu tarbiyya kuma su taso tare, please sister kicikama mamy wannan buri nata, ki jajirce sis, aure yanada dadi haka wani shafin idan aka bude yafi mad'aci daci, ki riqe Allah da manzonsa kuma ki riqe hqr.."
Shiru tayi ganin yadda kukan nata ya tsananta, shiru tayi tana kallon yadda take kukan, abinka ga ruwa ruwa sai itama taji digg digg hawaye sunfara digomata.
Nan aka rasa mai rarrashin wani cikinsu don hade kai wuri guda sukayi hannunsu cikin na juna sunata rizgar kuka.
Ita kukan Saudart ya Kasu kashi kashi, ga na fargabar aure da na barin iyaye gana fargabar yadda mamy zataji idan auren ya mutu.
Itakau mardeeya kukan tsantsar tausayinta take dama na mata gabadaya, wanda Daga inda kayi aure nauyi yahau kanka, gana miji, idan kuma aka hayyayafa gana 'ya'ya.
Ahaka su baby suka taddasu.
Turus sukayi abakin kofa suna kallonsu kowacce takasa motsi.
Baby ce ta fara takawa ta qarasa wajensu itama ta zauna ta rungumosu gabadaya itama ta bude nata muryar da Allah yabata tafara raira nata kukan.
Ganin hakan yasa itama Nafeesa tayi wajensu dagudu itama ta rungumosu sukaita kukan tare da wannan ya dauka sai wannan ya aje, da wannan ya aje sai wannan ya dauka.
(Nima ganin haka yasa nadan kauda kaina na matso guntun hawaye na😢 sannan na share da hanki)
Suna haka matar kawu bala tashigo, tana ganin yadda suka cure waje daya tafara sallalami tana tafa hannaye.
"Ni asiya mezan gani?"
Hakan yasasu dagowa Kowanne fuska jaga jaga da hawaye.
"Wannan wane irin sabon sakarcine zakuzo Ku cure waje daya kuna kuka? Meya faru?"
Nafeesa ta nunasu cikin muryar kuka tace "haka nisa baby mukazo muka tardasu suna kuka"
"Mtcheew Maimakon Ku rarrashesu shine kukayi joining? Ke mardeeya Meya sakaku kuka?"
"Haka nazo na isketa nima tanayi"
"Mtcheew, andaiji haushi Maimakon ki rarrasheta shine kika biyemata"
"Na rarrasheta taqi shiru"
"Mtcheew ni matsamin dalla"
Ta wuce ta kamo hannun Saudart da kanta ke duqe haryanzu tana hawaye.
"Ya isa haka baby, kiyi hqr kinji? Kowa haka yaji a lokacinshi, kiyi hqr, taho muje"
Tafada tana miqar daita tsaye suka nufi hanyar waje.
"Saura kuma Ku zauna karku tashi Ku shirya" tafada tana ficewa da Saudart.
Sun kusan mintuna goma zaune jigum jigum babu mai magana.
Can kamar an tsikari baby ta wani miqe tsaye tana kallon agogon hannunta.
"Guys har 11:30am yayi fa, Nidai bari kuga infada toilet, ato banmaga meye nawani kukaba Bayan ba aurena bane kuma ma aini farinciki yakamata nayi za'a rabani da dunqum"
Ta qarashe zancen tana Fadawa toilet.
Kallon Kansu sukayi Bayan sun rakata da kallo harta shige sai sukayi murmushi.
Bedroom din mamy anty asiya ta kaita don nan kadaine babu mutane.
Nan ta zaunar daita tanata yimata nasiha sannan Daga bisani ta hadamata ruwa mai dan gumi a jacuzzi tabata umarnin tashiga tayi wanka.
Ba musu ta shiga Bayan ta cire kayanta ta daura towel.
Ta dade sosai a toilet din sannan tafito tana tafiya kamar wanda Kwai yafashe mawa aciki.
Kayan data tadda kan gado wanda anty asiya ta fiddomata ta dauka tasa.
Doguwar rigace ta materials marar nauyi mai style din fish.
Sannan tadan shafa powder tasa kwalli a idanun ta kwanta don sosai kanta ke sarawa.
Can saiga anty asiya tasake shigowa da bowl hannunsu sai wata Leda.
Tada Saudart tayi wanda dama ba barci takeba ta tilastata shan farfesun da bread.
Saida tacinye Tass sannan tabarta Wai acewarta vazatabar diyarta da yunwa ba.
Paracetamol ta 6alla mata tasha sannan ta kwantar daita tafita ya rufomata qofa.
Dakinsu baby kau tuni yafara tashin hayaniya don su teema an iso.
Kowacce tasha anko dinta kowacce da irin daurin data kashe.
Baby ce tsaye gaban mirror ansha dinkin doguwar Riga mai budewa Daga qasa, dogon hannun rigarko Duk anyi raga raga ajikinshi wanda yaba farar hannunta damar fitowa cikin hudojin.
Fuska kau tasha simple makeup Wai sai ga dinner zatayi heavy makeup.
Ta wani kashe daurin ture Kaga tsiya.
Nanfa suka fara kashe selfie, Duk inda ka wulga flasher ce kawai ke wall wall akota ina kowa burinshi ya dauki hoton dayafi kyau, style din hotuna kam harda na hauka, haka sukaita yi ana dorawa a status, dp, pp e.t.c
*********************************************
"Wai Ashraf wannan wane sabon salon iskanci ne Wai, zaka wani shanya mutane waje kawani shige daki harda murza key? Ko bakasan qarfe nawa bane?" Inji Sadeeq afusace, yasha fararen dakkakiyar shadda da babban rigarta yar three quarter irindai ta gayun zamani yawani kashe hula gefen goshi.
Su bash suma cikin irin shigar zazzaune suna jiran tsammani Duk sun zubama kofar idanu.
"Baaam! Baaam!! Baaam!!!" Yasake bugun kofar cikin quluwa.
"Dan ubanka kafito kona kira Ummy yanzu yanzunnan!"
Tsaki Ashraf yaja yana daura agogon fata qirar apple a hannunshi sannan ya feffeshe turarrukanshi ya kaha hularshi akai, Duk cikin kwanciyar hankali yake hakan don yaqara qular dasu.
Saida yagama shan qamshinshi sannan yabude kofar yafito fuska a tamke.
Su Sadeeq dake jira ya fito sukusa cinshi danye suka Kasa motsi.
Hade yake cikin dakkakiyar shaddarshi milk colour mai aikin deep brown wanda yarufe kusan duka gaban babbar rigar sai hula kalar aikin Kayan takalmi da agogo ma hakan.
Ga fuskarshi datasha Gyaran fuska, dan siririn sajenshi sai walqiya yake.
"Tuff tuff, kuci kanku" yafada yana tuha Masu yawu.
Sai a sannan suka dawo Daga duniyar kallonshi.
"Wow! Wow!! Wow!!"
Haka sukaita fadi kamar wasu motocin yan sanda.
Tsaki Ashraf yaja yana cewa "idan kun gama jiniyar kusameni waje"
Kallon juna sukayi suka fashe da dariya
"Wooo! Tofah kunji, kuna 6atamishi time shi yayi gaba, he can't wait" inji wani mai suna Abbas's.
Nan suka fito sai tsokanarshi suke shikau ci kanku bece dasuba yashige wata farar motar ya danna lock yaba drivern umarni yaja.
Dariya suka sake kwashe wa dashi sannan suma suka hau motocin suka Mara mashi baya.
Unguwar ta cika maqil da mutane da manya manyan motoci, kallo daya zakayima taron kasan ana gudanarda gaggarumin abune.
2:30pm daidai aka daura auren ASHRAF AUWAL da SAUDATU SHAMSU KANKIYA.
Daurin auren daya samu hallatar manya manyan qusoshin gomnati da yan kasuwa.
Fuskar alhaji Shamsu kamar gonar auduga, yaudai burinshi yacika yazama surukin A.A
Nan akaita zomashi Allah yasa alhairi, a gefema Abba ne da tawagarshi shima sai barka ake mishi.
Can 6angaren angwaye ma abun ba sauqi sai Allah ya sanya alhairi ake zuwa yimashi, Shidai iyakarshi yaqe su Sadeeq ne Masu amsawa suna godiya.
Maroqa kau kasuwarsu ce tabude, nan suka baje kolinsu suna wasa ango da Amarya Dama abokan angon gabadaya, sunkau sha 6arin naira don su bash kamar basusan zafin nemaba haka sukaita watsa naira.
Masu daukar hotuna kau kowa burinshi ya dauka, Duk inda suka wulga Saidai sunji walai anata daukar su.
Ganin abun bana qarewa bane yasa Ashraf sulalewa ya fece.
Tunda taji sautin buda na tashi Duk ilahirin gidan gabanta ya tsananta bugu.
Sake cusa kanta tayi cikin bargo tana sakin wani marayan kuka wanda izuwa yanzu har idanunta sun gaji da tsiya yar hawaye, tausayin kanta yakamata nankau taita kuka kamar babu gobe.
Su baby anajin an daura tawani dale gado tana tsallen murna, Duk sai akaita mata dariya.
Wayarta ta kwace hannun wata safeena ta Danna ma Ummy kira tana rugawa toilet.
Ana dagawa tawani Danna ihu
"Ummy!!!"
"Ohh zaki kashe min kunne"
"Ummy finally, anty tazama family dinmu, finally yaya is married!"
"Yes sweetheart, mu gode wa Allah"
"Alhamdulilah Ummy zan sake kiranki"
Ta katse wayar ta fito waje ta tarda harsu teema sun fiddo mp dinsu sun Kunna anqure volume.
Aikau tayi joining suna rawar so na amana.
Sai wajajen 5na marece akazo daukar Amarya, zokaga kuka, ba Saudart ba ba mamy ba, dakyar aka samu aka 6an6aresu aka fito daita, Dama su yanmatan amare ana cikin mota an qame tundazu.
Fitowa akayi daita fuska lullu6e da lifaya aka sakata mota, tanaji tana gani aka shilla daita...✍
Toya? Wakeson acigaba yau? Koko abari sai gobe?
Adadin comments dinku zai bada amsa
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
030
Saida aka fara biyawa daita gidan daddy wato alhaji Shamsu, don suyi bankwana.
Nan ne mutane sukaga Ashe kukan datayi acan nafila ne bisaga na nan.
Sosai ta damke daddy tanata kuka, jikin daddy ne yayi Sanyi don yafi kowa sanin dalilin kukanta.
Ko dan nasihar nanma Kasa yimata yayi Saidai samata albarka dayaitayi.
Nanma dakyar aka 6an6areta Daga jikinshi Aka fita daita.
Cikin dalleliyar motar da'aka taho daita aka maidata sannan aka tada motocin sukayo layi sai gidansu A.A
Tun a harabar gidan aka fito tarbosu, sai 6uda dangin Ango suke, da wannan ta aje sai wannan ta dauka.
Ahankali Saudart tafito Daga motar Bayan an bude mata bakinta dauke da addu'a.
Ganin fitowar amaryar yasa budar qara yin sama.
Ummy nacan cikin falo da tawagunta wani farinciki ne ke sake ratsa ta jin yadda aketa callara buda.
Ahankali aka kamo hannunta aka wuto daita anata buda har suka shigo falo.
Mancewa Ummy tayi dawata surukanci ta tashi ta tarbota cikin fara'a hakan yasake Tunzura Masu budar suka qara volume.
Itadai Saudart kanta a qasa sbd matsananciyar kunyar datakeji.
Zaunar daita Ummy tayi tana mata lale marhabin sai kashe musu hotuna ake.
Haka akaita zuwa anamata sannu dazuwa itadai kanta qasa sai hawayen dake digowa diss diss saman hannunta
Kiransu baby dahar an tu6e za'a shiga wanka azo afara shirin dinner akayi tazo suka dunguma da Saudart dakin Ummy.
Nan akazo akafara mata shiri don dama bawani sallar dazatayi
Sukuma baby aka koma daki inda ke cike dasu yanmata hardasu Nafeesa ana shirin dinner.
Izuwa yanzu Duk wani fi'ili da iyayi nasu baby Nafeesa ma ta koya don idan tafara yadda kasan Dama can haka take
Itadai gwara gwara mardeeya ita abin nata da dan dama Dama.
Tofah gida ya kacame sai shirin dinner ake suma a 6angarensu ango hakan take.
Yanzu ma saida yagama shan qamshi sannan yashiga shiri.
Abokanan ango su shidda ango sukasha kamar dai dazu.
Sanye suke cikin wata dakkakiyar shadda sky blue babbar Riga da tan ciki.
Anyima babbar rigar aiki da zare dark blue, sun kashe hula wasu a goshi wasu a qeya.
Sosai suka bada kala don kallo daya zakayimusu kasan samarine Masu ji da kyau, kudi, dakuma wayewa.
Sanye suke da takalmi half cover farare Tass, saima kun gansu sun hadu👌
Yanzu ma saida ya qular dasu sannan yafito.
Yanzunma jiniyar suka dauka, don haduwar ta yanzu taci uban ta dazu.
Sanye yake cikin tsaddadar dakkakiyar shadda fara Tass babbar Riga da yan ciki wanda taji aikin sama na kalar sky blue, saiya kashe hula sky blue akai hannunshi daure da agogon fata qirar Gucci fara sai takalmi suma na company Gucci farare qarr.
Wow! Nima nayi nawa jiniyar, watakan nama Kasa magana ne, Saidai nabaku dammar hassasoshi da kanku don ya hadu qarhe👌
Nanfa aka hau yimashi kirari, Kowanne da irin kirarin dayake mashi ba shaqiyanci.
Abun nasu ya daina bashi haushi yanzu saima dariya, murmushi ya saki wanda yaqarawa kyanshi kyau.
Gabadaya suka dunguma sukayi waje abun gwanin sha'awa suka nufi motocin dake fake a waje.
Mota daya Sadeeq da Ashraf da bashir suka hau dayan kuma su abbass suka hau suka shilla sai gidansu A.A
Su baby Angama shiri cikin anko din dinner dinMaterials pink Ayi shafi da blue glass tapita.
Dukkansu anko din dinkin doguwar Riga sukayi mai wrapper 'o' a qasa, kowacce ta kashe daurin head sky blue, Duk an fente fuskoki da heavy makeup.
Sunyi kyau sosai sai kashe hotuna suke.
Can wajajen Bayan isha'i gida ya harmutse da buda.
Hakan yasa Duk aka fito don ganin Meya Jawo hakan.
Angwaye ne suka qaraso ga motocin kai mutane dinner Jere birjik waje, har mutane sunfara shiga, can Nagano maman twins Bayan wata mota tareda wata yar yarinya data taho daita wanda zatayi mata rainon su twins koda sun nemi yimata buqulu🤣
Cikin washe baki suka shiga cikin gidan Shidai ango iyakarshi murmushi dabe kai zuci ba.
Nan akaita tsokanarshi su sadeeq na kareshi Shidai nashi yaqe.
Har wajen Ummy aka rakoshi, da sauri ya qarasa ya rungumota yana lumshe idanu itama Ummy kankameshi tayi farinciki da kaunar danta na huda zuciyarta.
Sai daukar su hoto ake tayi ahakan don sunqi sakin juna.
Duk d'ari d'arin da baby keyiwa Ashraf ta daure ta qarasa itama ta rungumesu gabadaya hakan yasa akaita shewa ana daukar su hoto.
Sun dade ahakan sannan suka warware rungumar Kowanne farinciki fall fuskarshi.
"Yaya congratulations" inji baby tana mashi murmushi
Shima murmushin ya maida mata
"Thanks lil sis"
Sosai tayi farincikin sakin fuskar dayayi mata.
"Yaya, please selfie?... Please"
Murmushin gefen baki kawai yayi hakan yasa tayi saurin Ciro wayarta har kyarma take ta matso dab dashi suka dauka sai kuma ta dauki wani tareda ummy.
Ganin abun nasu bana qarewa bane yasa bash radawa Ashraf time na tafiya fa.
Hakan yasa suka miqe.
Yanmata Duk inda ango ya wulga saisun bishi da idanu, Nafeesa da mardeeya kau har kusan jalale sukayi Ashe dama haka angon Saudart yake?
Lallai tayi dace.
Shiga wasu sukayi dob fitowa da Amarya, izuwa yanzu jama'ar dakin Duk sun fita sun shige mota wasu har anfara tafiya dasu.
Fitowar Amarya yasa kallo yadawo kanta.
Yanzu fuskarta abude take, tasha heavy makeup wanda ya bayyana 6oyyayen kyawunta tsantsa.
Masha Allah mutane sukaita fadi don ba qaramin haduwa tayiba cikin farar wedding gown dinta da akayima ado da pink colour. Sosai rigar ta amshi qirar jikinta kamar a jikinta aka dinka.
Gashi anmata wani fitinannen daurin head pink kamar fanka don bazuwa.
Yanzu ma Ummy ce Taqara tarbota tana fadin masha Allah saboda kyawun datayi.
Itadai Saudart nata sinne kai sai murmushi datake a kunyace.
Nanfa aka kuma bude wani sabon babin daukar hoto, Duk abinda ake Ashraf be ko kalli gefen Saudart ba, itama hakan saida akace Amarya da ango su jera a daukesu tare.
Rasa wanda zaifara motsawa akayi cikinsu, ganin abun nasu nayine yasa wata abokiyar wasansu A.A ta kamo hannunshi ta jawoshi wajen Saudart ta Dora hannunshi a kafadar Saudart kamar irin yad'an rungumota dinnan.
Hakan yasasu jin wani vaqon al'amari a jikinsu wanda hakan yasasu saurin dagowa tare suna kallon juna.
Wall wall aka daukesu hoto suna kallon junan.
Saurin janye idanunsu sukayi Kowanne gabanshi na faduwa.
Qoqarin zame mashi take yaqara matseta yana dan harararta ta qasan ido
Hakan yasata janye dara daran idanunta tana kallon qasa Duk abinda suke ananan anata daukansu hoto saida sukayi mai isarsu sannan aka fara fita zuwa mota dama saura yan kadan su kingin sun tsufa acan.
Saida Ummy tayimusu nasiha mai ratsa jiki sannan tace musu sutafi Allah yayi musu albarka.
Tashi Ashraf yayi itakau Saudart tama Kasa motsawa, hakan yasa Ummy tayi mashi ido akan ya tadata.
Ba don yasoba ya duqa ya kamo tsintsiyar hannunta, hakan tasata dan razana ta dago ta kalleshi, kauda Kai yayi, tana shirin zame hannunta Ummy tace
"Ku tashi kuje daughter"
Babu yadda ta iya tamiqe still hannunta cikin nashi suka jera suka fita.
Saura motarsu kadai dama, Sadeeq ke mazaunin driver.
Yana ganinsu yayi saurin fitowa don budemusu kofa.
Ganin sun fito waje yasa Saudart kwace hannunta tana hade rai.
Ta6e pink watery lips dinshi yayi yana fadin "as if I care"
Banza tayi dashi ta kauda kai,
Qarasawa tayi tashiga motarda Sadeeq ya Budemata, saida Ashraf yasha qamshi sannan shima ya qarasa ya shiga yana Jawo kofar.
Zagayawa Sadeeq yayi mazaunin drivern yana girgiza kai, Shidai yaso ganin irin zaman da zasuyi.
Tada motar yayi ya shilla kan kwalta.
Babu mai magana acikin su har suka qaraso, nanma Sadeeq ya fito ya budemusu kofa.
Yanzuma saida yasha qamshi don har Sadeeq yafara hasala don dai kawai yana ganin Saudart ne da babu abinda zai hana ya balbaleshi.
Saukowa yayi ahankali yana gyara babbar rigar shi.
Itama Saudart fitowa tayi cikin nutsuwa ta tsaya Daga can gefe.
"Ehmm... Ango dan Allah ka kama hannun Amarya Ku shiga Ku kadai ake jira"
Harara ya watsa mashi ya dauke kai.
"Please Ku kadai fa ake jira, please"
Kamar bazaiyi ba saikuma ya matso dab da ita Saidai yakasa riqo hannun don beson yasake jin abinda yaji dazun daya riqe hannunta.
"Ashraf mana" inji Sadeeq cikin qosawa.
Tsaki yaja sannan ya kamo hannun ya riqe yana qara tamke fuska.
"Yauwa kutaho ahankali" inji Sadeeq yana yin gaba.
Cikin takun qasaita suka taho kafada da kafada dukda kowa da kalar abinda yakeji ajikinshi.
Ana ganin 6ullowarsu aka saki kidan ranarku ta umar m Sharif.
Nan yam rakiyar Amarya da ango aka fito aka jera bayansu
Ahankali suka qarasa stage din hannunsu cikin najuna, sukau yan rakiya sai rawar waqar suke suna maramasu baya har suka kaisu mazaunin su.
Sosai aka qawata mazaunin nasu da decoration sky blue and pink.
Zama sukayi ahankali Ashraf na taimaka Mata ganin tana Neman missing step.
Ta6e bakinta tayi don ba cika son ta6atan dayakeyi take ba.
Shima Ashraf ganin idanun jama'a yasashi tarota da babu abinda zaisashi tarota Saidai ta shekara tana faduwa.
Nanfa aka fara abinda ya tarasu.
Kowanne kagani a dinner ji da kanshi yake don dinner ne tsararre kuma na yan gayu don haka kowa ya aure wankanshi.
Bayan dan barkwanci da m.c yayi da yan surutansu dasuka saba aka kira wasu Afro dancer don su nishafadar da mutane.
Yan yara ne mata wa'inda basufi shekaru takwas takwas ba su hudu sanye cikin Riga pink da crazy jeans blue Kansu yasha bands blue da pink.
Nan aka kunnamasu waqar hiphop suka shiga yin rawa iri daya mai burgewa.
Sosai suka burge mutane abinka da yara, man akaita yimusu 6arin kudi, sai tafi akemusu.
Bayan nan abokan ango suka fito su shiddan Kowanne nasa6ar babbar rigarshi.
Nan aka sakamusu waqar EBEANO.
zokuga rawa wajen abokan ango, har wani baza babbar rigar suke suna shaku shaku sosai suka burge mutane sai tafi akemusu wasu harda fito don rawar tasu iri daya da alama sun dade ana training.
Bayan waqar taqare aka chanza musu waqar GIDODOGO nasu p-square da diamond
Nanfa Hall yadauki sowa ganin sun chanza salon rawar su.
Saudart da Ashraf Kansu Saida suka murmusa don rawa suke sosai gashi sai fama suke da babbar Riga abun gwanin dariya.
Waqar na qarewa suka bar stage din.
Nan DJ ya chanza waqar yasa ta lokaci ne na umar m Sharif.
Su baby suka fito suma su biyar
Suka fara rawar waqar.
Babu abinda ke tashi sai tafi su Nafeesa da badasu aka fitoba don basu iya rawar ba don musanmman baby ta hadu da qawayenta sukayi training din rawar sosai, su Nafeesa harda fito don sosai suka burge musanmman inda suka fara rawar jirgin so acikin waqar.
Sun burge sosai don bawai irin girgiza jikin haukarnan sukeba ahankali suke rawar cikin yanga kuma tayimusu kyau.
Nanfa suma akaita musu 6arin liqi basusan zafin kudinba.
Can Bayan waqar taqare suka sauka Daga stage nan aka fara shelar Amarya da ango suma su fito su taka.
Tofah nan akeyinta, ganin babu mai niyyar tashi yasa bash yaje ya tada Ashraf yana mashi rada a kunne.
Kamo hannunta yayi ya dagata ta tashi suka fito stage nan aka Kunna Masu waqar Hamisu breaker ta jarumar Mata.
Kama hannunta daya yayi, dayan kuma ya tallabo kuqunta.
Hakan yasata saurin dagowa ta kalleshi, dan harararta yayi yana mere baki.
Hakan yasa ta sadda kai.
Ahankali ahankali suka fara tattakawa yayinda suka burge kowa sai daukar video ake.
Ahankali ahankali akaita hawa stage din aka zagaye su ana Masu kiqi Ana dan tattakawa don waqar bata rawa bace irin ta haukannan ba.
Zokuga yadda kudi ke zuba qasa, liqe akemusu kamar yayyafin kudi akeyi.
Sun dade ahakan sannan aka rankaya wajen yanka cake, nanma cool music aka sakarmusu na DID YOU BELIEVE IN LOVE?
Hannunsu akan na juna suka yanka cake din tare sannan sukayi feeding din juna.
Daga qarshe aka saka waqa kowa yaita chashewa.
Duk bidirinnan da ake su hajiya maman twins dama sauran yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP basusan anayiba don tunda aka fara suka Tisa abinccicika kala kala sai handama suke musanmman maman twins acewarta saitayi qara'i wasu har a Leda zubawa suke Wai akai gida musanmman ummu sadik Mayyar shinkafar biki🤣
To Allah dai yasa kar ciki ya rude, ca6 da ba kanta, wayaga su maman Fatima ana yamutse fuska kan toilet🤭
Anyi dinner lfy antashi lfy inda ango dakanshi yaja motarsu da amaryar contract dinshi agaban mota.
Mutane sai dagamusu hannu suke har suka fice suka nufi sabon gidansu amatsayinsu na sabbin ma'aurata inda zasu fara gudanar da sabon rayuwa mai cike da chakwakiya...✍
Tofah fans yaya zaman nasu zai kasance? Ina Suzy? Zata dawo koko ta hqr? Zaku sami amsoshinku Bayan Sallah insha Allah.
Anan zamu tsaida littafin nan harzuwa Bayan azumi insha Allah.
Dan Allah ina mai Neman yafiyar Duk wanda nayima ba daidai ba acikinku, da sanina ko babu sanina,please ayafe.
Nima na yafe muku gabadaya.
Allah yabamu alhairin wannan wata mai alfarma.
Yasa mu kwashi garabasar dake cikinta
Muyi ibadunmu lfy mugama lfy.
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid 19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲
Happy edl- Mubarak🧚♀
Dafatan kowa yayi sallah lafiya, Allah kasa ibadunmu da addu'o'inmu kar6a6une🤲
To kowa yazo asa layi, yau duk sai anbani barka da sallah na, idan ba haka ba muci mutum tara😏
Afara layi gajeru agaba, dogaye abaya, qwailaye agefe🤣
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
031
Garin yayi tsit, yayi duhu saboda Daren yafara nisa, ga hadarin daya hadu Wanda yaqarawa Daren duhu, iska mai dadi sai qadawa yake.
Tuqi yake cikin normal speed yana sarrafa steering din gwanin burgewa.
Tsit motar kamar babu kowa aciki, kowanne da abinda yasha mishi kai babu Wanda yanuna yasan da wanzuwar Dan uwanshi.
Idanunshi da hankalinshi na kan kwalta ko gefenta yayinda itakuma take gefenshi lafe a kujera idanunta a lumshe.
Har yanzu takasa yarda wai ita Matar aurece, wata biyu dasuka wuce idan da wani zai gayamata warhaka tanada aure babu abinda zai hanata qaryatawa, amma sai gashi cikin Dan qanqanin lokaci labarin rayuwarta ya canza, acikin wata biyu tasamu miji har anyi auren saidai ba irin auren da aka saba yiba, aure ne na takaitaccen lokaci Wanda ke shimfide akan sharrud'a da tsari.
Ajiyar zuciya ta suke ahankali daidai Wanda taji ya dakatar da mortar yana horn.
Can kuma taji motar tacigaba da tafiya duk abinda ake idanunta na alumshe kuma batada niyyar budesu.
Direct parking space yanufa inda yake kwal babu mota ko daya kasancewar sabon gidane yau akafara amfani dashi.
Parking yayi sannan yakashe motar yakoma ya jingina da bayan kujerarshi yana lumshe hazal eyes dinshi.
Shiru motar ta dauka babu mai ko motsi, izuwa yanzu hadarin ya hadu sosai don iskar yaqara qarfi, sai walqiya da cida ake.
Hannu yasa cikin sanyi ya balle seat belt ya bude murfin motar batareda yako kalli gefentaba ya fita ya maida kofar yarufe, sannan yafara takawa cikin takunshi na qasaita yawuce.
Ajiyar zuciya ta sauke nannauya, ahankali ta bude idanunta Wanda tunda suka baro wajen dinner suke a lumshe.
Tacikin mirror din gefen motar tabishi da kallo harya shige ciki.
Ta6e baki tayi cikin takaici, ita tunda take bata ta6a ji ko ganin ango yabar amaryarshi amota ba ranar auren su.
Koda yake auren ma gabadaya bata ta6a jin irin nasuba don haka duk abinda yabiyo bayama ba komai bane.
Hannu tasa ta bude kofar itama sannan ta ziro kafaffunta ta sauko.
Qanqame jikinta tayi a tsorace jin anyi wata irin tsawa da walqiya, saurin maida kofar tayi tarufe tana qanqame net din data Dora akai Wanda iska ke baraxanar fecewa dashi.
Ahankali ta fara takawa itama tanufi hanyar dataga yabi hannu daya dafe da net din kanta dayan kuma ya tattaro qasan gown dinta dake sharar qasa.
Dakyar tasamu ta isa main door sbd wuyar tafiya da heels din kafarta kesata.
Hannu tasa a handle din kofar ta murda saigashi yabude, tura kofar tayi tashiga bakinta dauke da addu'o'i.
Wani sanyi da ni'imtaccen qamshi yaimata maraba Wanda saida ta lumshe ido don dadi.
Bin qayyatacen falon tayi da idanu tana jinjina 6arnar kudin da Dad yayi wajen zubamata kayan daki na gani na fada.
*Lallai dad* tafada acikin zuciyarta.
Haka taita bin falon da kallo tanata yan ta6e ta6en baki.
Jin tsayuwar ya isheta gakuma nauyin kayan jikinta yasata fara takawa tanufi matattakalar benen datagani daga gefen dama.
Ahankali taita taka mattatakalar harta kai sama.
Dakuna uku ke saman ajere.
Tsayawa tayi tana kallonsu tana tunanin wane ne nata.
Tsaki taja cikin takaici, wai ace Amarya ke Neman dakinta, kai gaskiya dad ya cuceta, kwata kwata ba haka ta tsara aurentaba, ta Dade tana qiyasta yadda rayuwar auren ta zai kasance, ta jima tana qiyasta yadda auren ta zai zama abun koyi da burgewa ga mutane da dama, amma rana daya an rusamata tsari.
Jitayi ankece da ruwan sama kamar dabakin qwarya.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tanufi dakin farko, tana murdawa taji gamm.
Tsaki tasake ja ta nufi ta tsakiyar, tana murdawa taji tabude.
Tsayawa tayi tana kokwanton shiga don bata fatan ganin fuskarshi nan kusa.
Fasa shiga tayi tanufi ta ukun ta murda taji itama gamm hakan yasata dawowa ta tsakiyar badon tasoba.
Tura kofar tayi ahankali sannan tashiga a darare.
Saida ta leqa koina ta tabbatarda babu kowa aciki sannan hankalinta yakwanta.
Maida kofar tayi tarufe harda saka sakata sannan tadawo cikin dakin
Nanma kamar falo an narkar da naira wajen qawatashi don Italy bed ne haddade da closet daya kusan cinye bango daya, sai mirror na bango ga saman dressing mirror din shaqe da mayyuka da turarruka kamar bana mutum dayaba.
Agefe gefen gadon bedside locker ne masu daukeda lamps
Daga haggu kuma koface Wanda ko ba'a fadamaka ba kasan toilet ne.
Agajiye tafara rage kayan jikinta, saida yarage daga ita sai undie sannan tanufi toilet din.
Nanma fadin haduwarshi 6ata time ne, dukda agajiye take hakan besata tsayawa qarewa toilet din kalloba.
Tara ruwan dumi tayi a jacuzzi sannan ta hada mayyukan wanka wa'inda duk yanzu ta fasasu cikin ruwan sannan tashiga.
Ta Dade cikin ruwan saboda dadinsu don harta fara gyangyadi sannan tafito ta jawo wani baby pink din towel dake gefe hange.
Tadaura sannan ta FASA sabon brush ta matsa MacLean tayi brush daganan tayi alwala tafito.
Wata doguwar night gown tasaka ta zura hijabi ta haye sallaya Wanda dama already a shimfide take a kusurwar dakin tayi nafila biyu.
Ta Dade zaune tana kwararo addu'o'i sannan ta shafa tamike ta cire hijabin tanufi gadon don bacci ke idanunta sosai.
Kashe fitilun dakin tayi ta kunna bedside lamp don bata iya kwana cikin duhu sannan tashige cikin bargo ta quddundune tana sauraron saurin saukar ruwan saman Wanda kesata nishadi.
Dama ita masoyiyar damina ce, tana bala'in son ruwan sama musanmman na dare, tana jindadin yin barci ana ruwan sama.
Bata wani Dade akwanceba wani nauyayyen barci mai dadi yayi gaba daita.
A bangaren ango kau dama yana shiga yacire babbar rigar don ba qaramin takuramashi tayiba.
Direct toilet yashige don wanka.
Koda yafi to kayan barci kawai yasa ya hada coffee da coffee maker dake dakin ya zauna yana kur6a hankali kwance kamar be baro diyar mutaneba awaje.
Yana cikin sha aka kece da ruwan sama sai a sannan tunaninta yafado mashi.
Ta6e baki yayi yacigaba dashan coffee dinshi har yashanye.
Yana gama yashige cikin bargo shima ya kwanta don shima yana son ruwan dare sosai.
Shima be jimaba barci ya daukeshi
Asuba tagari ma'auratan kwangila😴
Manage please🙏
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ja yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu🤲
Karka barmu dakanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
032
Kiraye kirayen sallar asuba ya tadata, bude idanunta daketa faman rufewa dakansu tayi tana hamma da alamu dai barcin be ishetaba.
Tashi tayi zaune tana miqa tana salati
Dafarko taso yin dimuwa don ta mance da inda take, tashi tayi tanufi toilet don dauro alwala.
Rakka'atainul fjr tafarayi sannan tayi sallar asuba.
Sannan tazauna tafara laziminta nasafe.
Ba ita ta tashi ba saida gari yafara haske.
Komawa tayi kan gadon ta dasa barcin don rabonda tasamu cikakken barci harta manta.
Sai wajajen qarfe goma ta farka dawata azabattaciyar yunwa.
Rabonta da abinci tun farfesun da Matar kawunta tasata ci jiya da hantsi, bataci komai ba darana da daddarema haka.
Miqewa tayi akasale ta sauko daga kan gadon tanufi bathroom.
Takusan mintuna talatin saigata tafito da daurin blue towel a qirji.
Dressing mirror tanufa tayi shafa Wanda daga lotion sai powder data bursinama fuska sai eyeliner datayi lining din idanu sai mascara data taje gashin idanu.
Gown din data cire jiya da jallabiyar datayi sallah yau ta linke ta bude closet tasaka sannan taciro wata doguwar Riga ta atampa mai kalar dark green da yellow tayi daurin kallabin turban.
Kalkade dakin tayi ta gyara zanen gadon sannan ta share dukda bawani datti tayiba sannan ta kunna burner bayan tasa turaren wuta mai qamshi.
Toilet tashige nanma ta gyarashi tsaf ta goge qasan da air freshner sannan tadawo dakin.
Zama tayi gefen gadon tana Dan dafa cikinta dake katsamata.
Yunwa takeji amma batason sauka don batason haduwa dashi.
Tadan jima kadan tana zaune taji ana danna doorbell.
Kasa kunne tayi taji ansake dannawa, shiru tayi taji kozai fito yaduba amma saitaji hanata dannawa.
Tashi tayi ta zari wata farar hijabi tasaka Tadan fesa turare sannan tafita.
Ahankali ta sauko zuwa falon Wanda duk azatonta yana ciki.
Ganin wayam yasata dakin ajiyar zuciya ta ida qarasawa ga kofar tana fadin
"Ana zuwa"
Koda tabude kofa wata budurwa tagani riqeda basket tanamata murmushi.
Itama maidamata murmushin tayi tana cewa "sannu, kishigo please"
"A'a aunty juyawa zamuyi ai, ina kwana"
"Lfy lau, ya kike?"
"Lfy lau dama hajiya tace akawo break" tafada tana miqamata basket din hannunta.
"Allah sarki, Ummi harda dawainiya? To mungode please kice muna godiya kuma muna gaidata"
"Insha Allah aunty"
"Ina baby?"
"Hhhh tanacan tana kumbure kumbure an hanata biyoni"
Dariya tadanyi
"Kai itama Ummy data barta tazo"
"Cewa tayi damunku zatayi saidai nan gaba"
Murmushi saudart tayi tace "to Allah yakaimu, ki gaidamana su duka"
"Insha Allah sai anjima" inji yarinyar tana juyawa.
Maida kofar tayi tarufe sannan tashigo da basket din falo.
Dining area dake daga gefen haggu tanufa ta Dora basket din saman table din sannan ta fiddo kayan ciki.
Flask ne shaqeda kunun gyada sai kulolo biyu.
Daya na dankali da kwai sai dayan na farfesun yan ciki.
Kallo daya tayi musu yawunta ya tsinke.
Maidawa tayi tarufe sannan takoma bakin kofa ta budeta ahankali tana leqowa.
Parking space ta hanga wayam Wanda hakan ke nufin yafita.
Komawa tayi falon tajawo kofar sannan tacire hijabinta tanufi kitchen.
Sakin baki tayi ganin dukiyar da aka narkamata a kitchen din, an cika kitchen din da kayan kitchen nagani nafada ga kayan electronic, su ovens, deep freezers, toaster dadai sauransu.
Jiki a sanyaye ta qarasa inda ake ajiye su plates, cups da bowls.
Wani bowl ta dauko mai kyau na tangaran da Kofi sai cokali da fork.
Wajen wanke wanke taje ta daurayosu sannan ta dawo dining din.
Kunun gyadan tazuba a kofin sannan tazuba farfesun cikin Dan bowl din sannan tafara ci.
Sosai abincin yayimata dadi don taci sosai musanmman kunun gyadan.
Koda tagama, tattara abubuwan data 6ata tayi taje ta wankesu ta maidasu ma'ajinsu sannan ta dawo falon Tadan kakka6eshi shima ta kunna burner ta hayewarta sama.
Tana shiga dakin wayarta daketa faman ringing na katsewa, da sauri tanufi wayar ta dauka taga har 5missed calls
Kafin ta duba masu kiran wani kiran yasake shigowa.
Da sauri tadaga cikin murna
"Dad.."
"Shalele?"
"Wayyo daddy na I missed you" tafara cikin muryar kuka
"Haba shalele you know I miss you too"
"Dad nidai kazo katafi dani please" tafada a shagwa6e
Dariya yadanyi kafin yace
"Shalele duka fa yau kwananki daya"
"Nasani Dad, nidai kawai kazo katafi dani please" tafada hawaye na taruwa a idanunta
"Shikenan zanzo kinji? Karki damu your dad is always with you okay?"
"Dagaske zakaxo?"
"Nayi alqawari, hope dai babu matsala?"
"Babu komai dad"
"Good, kicigaba da hqr insha Allah komai zai warware very soon okay?"
"Ok dad"
Nan suka Dan ta6a fira kafin suyi sallama.
Sunayin sallama ta lallubo number mamy datagani cikin missed call dinta.
Ringing biyu aka daga.
"Mamyy!!" Tafada da qarfi tana dalle gadon
Tsaki mamy taja fuskarta fall murmushi
"Zaki kashemin kunne ne?"
"Kai mamy bafa ihu nayi ba, kawai I miss you ne" tafada a shagwa6e
"Kyaji dashi, dama su Abdul ne suka addabeni saina kiraki sunmaki mgn, gaki gasu"
Nan ta miqamusu wayar, nanfa aka bude babin fira kowa da labarin dazaibata, itama tana biyemusu, daga qarshe suka cemata ta roqi mamy tabari suzo don tahanasu.
Koda mamy ta amshi wayar saudart ta gwada roqon mamy din tabari suzo taqi yarda tace takuramasu zasuyi da hayaniya sai nanda sati.
Sudan ta6a fira da mamyn inda a hikimance take fadamata yadda zata kula da kanta don ita a tunaninta jiya oga Ashraf ya kashe boss😂
Itadai saudart jinta kawai harta gama sannan sukayi sallama
Tana katse kiran kiran baby na shigowa.
Murmushi tayi ta jingina da kan gadon sannan ta dauka
"Halloo"
"Yee! Matar yayana!!" Tafada cikin ihu
Tsaki saudart taja
"Wuhh saikin dodemin kunne sannan?"
"Hhhh bazaki gane bane aunty, jiya na wataya gidan nan yauma haka, gaskiya Allah yabiyaki, kin rabamu da takuratu, Allah yaqara danqon love tsakaninku" tafada cikin sigar shaqiyanci
"Hmm Allah ya shiryaki baby, don kekam saida addu'a kuma ki qaddara a kunnenshi kikayi wannan maganar don saina gayamashi"
Zaro idanu baby tayi daga can bangaren
"Rufamin asiri aunty, karkija yace inzo inmaki zaman daki, ca6 Dana bar garin Allah"
Dariya sosai saudart tayi tace
"Kije ina?"
"Koina ma, ai yayi can tunda dai mun rabu lfy, nahuta da muguntarshi da punishment, ingayamaki akwai ranar da don mugunta yasani share backyard da tsirin hakkin tsintsiya uku.
Wlh na yini ina share wajen, quguna kamar zai cire"
Dariya sosai saudart tayi kafin tace
"Dagaske? Hakkin tsintsiya uku? Lallai"
"Wlh kau, ai kekam Allah ya kashe yabaki, aini kadai nasan halin yaya, kana kallon yar fuskarnan tashi uwa ta mage kamar bazai iya cizon yatsarkaba idan kasamashi, mugun mugunta ke cikeda qaramin kan nan, wlh mata masu binshi suna sonshi mammaki suke bani, basusan kyan Dan maciji ke gareshi ba ga kyau ga sari, ni kinmafi bani tausayi, kidaibi asannu kar wata rana muzo ziyara mu yadda Matar yaya na sare ciyawa da reza"
Dariya sosai saudart keyi harda dafe ciki don sosai tabata dariya
"A'a wannan saiku, ni saidai inbashi punishment badai yabaniba"
"Inyee! Kai Allah ya tsinewa love, soyyaya maida sarki bawa, mai maida mai taurin kai solo6iyo, gaskiya ina bayan ki aunty, ki murza kabunki dakyau, ki rarramamin muguntar dayayimin"
"Hmm yaushe zakizo?" Tafada cikin son canza aqalar maganar
Shagwa6ewa baby tayi
"Ba Ummy bace tahanaba? Wai zan takuramuku?"
"Kumafa hakane, Gwara karkizo yanzu takuramana zakiyi"
Waro idanu baby tayi
"Hakama zakice? Ba komai zan ramane"
"Zaki dai rame, bari in daga kiran wadannan mayyun kafin su lasheni"
"Laa su waye?"
"Qawayanki mana, yawuce su mardeeya?"
Dariya baby tayi tace
"To anty zan kiraki anjima"
"To Allah yakaimu agaidasu Ummy"
"Bazata jiba, idan kin matsu ki kirata ko kizo, bayan ta hanani zuwa kuma sai kiwani aikeni wajen ta, kifadawa wadda takawo muku breakfast din ta gayamata"
"Tofa? Haka akayi?"
"Eh din" tafada tareda kashe wayar tana dariya.
Dariya itama saudart tayi tana girgiza kai.
Kiran nafeesa yasake shigowa wayar.
Dagawa tayi tana cewa
"Tuff tuff kuci kanku, namana daci"
Ihu suka saka suna callara gud'a Wanda har saida Tadan kauda wayar daga kunnenta.
"Kunga amaryar handsome bada kanki asare Kije gida kice yafadi, amarsu ta ango, kinsha madara, kina cikin shan madara, zakisha madara" inji nafeesa cikin shaqiyanci.
Tsaki taja tace
"Kunga idan vakuda magana mai ma'ana zan ajiye waya kun dameni da kira kamar Wanda akaba ajiyar qodarku na dauka kuma zaku toshemin kunne"
"Inyee, amaryar baa? Irin anyi auren nan ba'a son wulaqanci ko?" Inji mardeeya
"A to, me yafi raina? Ai kuma kanku kunsan akwai banbanci" tafada cikin sigar tsokana.
"Mukau mukasan da banbanci tunda kema kinsha madarar lilo, wai yama naji muryarki garas? Ko yar shaqewarnan batayiba?" Inji nafeesa
"Uban me zai shaqeta to?"
"Ihu mana, jiya nasan ankira sunana wajen naiman dauki... Wayyo Allah nafeesa Dan Allah kizo ki ceceni, mardeeya! Wayyo yar uwa kizo ki kawomin dauki! Mamy! Wayyo Allah na! Kabarni haka yaya, zafi! Dan Allah kabari na tuba, akwai zafi, zan..."
Diff saudart ta katse kiran cikin tsananin kunya da takaici.
Lallai iskancisu nafeesa sai an hada da addu'a, kwafa tayi tana yin cilli da wayar tsakiyar gadon sannan tamiqe don dauro alwalar azahar Wanda har anfara kira.
Koda tagama Dan kishingidawa tayi ta jawo wayarta ta bugama yan bakery dinta, sundan Dade suna magana sannan sukayi bankwana.
Qarar doorbell miqewa, saida ta leqa ta windonta taga babu motar parking space sannan ta sauko, yanzu ma abinci aka aikomata daga wajen Ummy.
Godiya tayi ta amsa ta zauna ta take cikinta sannan ta haura da sauran sama.
Ataqaice haka tayini ita daya, saidai tayi game ta gyara dakin dukda ba datti tayiba don kwanciyar ta isheta, abunka da bata sababa.
Sai can wajajen taran dare taji dawowarshi.
Ta6e baki tayi tana cigaba da jera kayan ta a closet dukda ba'a yamutse sukeba, kawai Rashin aikinyi yasata fiddosu tasake musu sabon shiri.
Ba ita ta kwantaba sai wajajen goman dare...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan cuts (covid19)🤲
Allah kabamu zaman lfy a qasarmu🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
033
Washegari ma bata fitoba saida ta tabbatar da yabar gidan, sannan tafito ta samarma kanta abinda zataci ta gyara gidan ta goge Tass ta saka turaren wuta sannan tayi hayewarta sama.
Ba ita ta saukoba sai bayan azahar ta nufi kitchen ta Dora abinda zata sakama cikinta sannan ta gyare kitchen din ta tattara abincin tayi sama.
Yauma sai wajajen qarfe Tara ya dawo gidan, kamar jiya beko ni takan dakintaba yayi shigewarshi dakin shi.
Ataqaice dai haka sukaita wasan 6uya tsakaninsu, koko ince take wasan 6uya dashi don izuwa yanzu ta laqaici lokacin fitarshi da dawowarshi don haka ta rage zaman sama, tana saukowa qasa ta yini amma da tayi sallar isha'i kuma ita da saukowa sai Allah ya kaimu kuma.
Tanada kwana biyar su mardeeya su kazo harda baby don biyamusu tayi su kazo tare.
Ranar kau saudart taga ta kanta don tisata gaba sukayi da tsokana iri iri.
Tun tana maida martani harta haqura, ita kau baby wani sa'in ta shigarmata wani sa'in ta koma masu Nafeesa su tararmata.
Basu suka bar gidanba sai qarfe shidda da Rabi na marece bayan ta cikasu da kyauta na kayan kwalliya da snacks ta rakosu har wajenda motar baby take don aciki su kazo.
Jitake kamar tabisu don zaman kadaicin ya isheta gashi tayi missing din daddynta sosai dukda kullum cikin waya suke.
Ahaka sukayi bankwana cikin mararin juna saudart na musu addu'ar Allah ya tsare kasancewar su mardeeya gobe zasu koma Maiduguri.
Ba ita takoma cikiba saida taga fitarsu.
Bin harabar gidan tayi da kallo don yau ne karon farko data fito harabar tun zuwanta.
Bin wajen taitayi da kallo don ya qayatu iya qayatuwa ga trimmed flowers daya zagaye wajen gwanin burgewa.
Ta6e bakinta tayi ta jiya ta koma ciki don har anfara kiraye kirayen sallar magrib.
Yauma kamar kullum tana bata sake saukowa ba bayan isha'i.
Kwanci tashi yau kwananta sha bakwai a gidan.
A yanayin zamantakewarsu babu wani chanji don rabonda Susa juna a idanu tun ranar auren su.
Izuwa yanzu saudart tasake da gidan sosai babu inda bata saniba agidan.
Akwai komai agidan kama daga abinci da kayan more rayuwa.
Saidai tana cikin kadaici sosai, kullum ita kadai ke yini inba Allah yajefo mata wani baqoba, wani sa'in don debe kewa saita shiga garden dake bayan gidan don hutawa ko ta zauna falo tayi kallo.
Bakery dinta kau kullum tana samun bayanai akan yadda yake tafiya kuma alhamdullilah sai bunqasa yake.
Haka zalika kusan kullum sai sunyi waya da Ummy don izuwa yanzu tana Sakin jiki daita su danyi fira kasancewar Ummy batada matsala kuma tana sonta sosai don saudart badai hankali da nutsuwaba.
Wani sa'in idan kadaici ya isheta saita bugama Ummy ta roqeta akan baby tazo.
Duk zuwan da baby keyi bata yarda takai magrib take juyawa, saudart tasha yimata tayin kwana amma firr take qiyawa wai in taganta lahira kaita akayi.
A bangaren ashraf kuwa tuni yakoma bakin aikinsa, dama hutun sati daya ya dauka, shima saboda matsawar sadeeq.
Shi harga Allah wani sa'in mancewa yake da yanada mata, rabonda yasata a idanu tun awajen dinner.
Yasan haqqinshine yasan yaya take ciki dakuma kula da lafiyarshi amma bejin yana iya zuwa ganinta, aganinshi ai ba normal aure bane auren su, auren kwangila ne kowa da dalilinshi nayin auren kuma kowa da abinda yake targeting.
Jera abinci take bisa dining tanayi tana kada kai tana humming tana bin waqar datakeji ta earphones din kunnenta.
Saida ta shirya komai a table din sannan tayi sama tana Dan hadawa da tsalle tsalle Wanda duk acikin shauqin waqar datake jine.
Tana shiga tacire earphones din kunnenta ta fara tu6ewa don watsawa don yau garin badai zafiba, yadda akayi rana yau dakyar idan ba ruwan sama za'ayi ba. Tana gama ty6ewa ta dauki towel ta daura tashige toilet.
Horn yayi sau daya, nan aka shiga scanning din motar, bayan angama gate din ya wangale dakanshi ya kutsa kai yashiga.
A parking space yayi parking sannan yafito ya rufe kofar yayi locking din motar sannan yanufi cikin gida yana sassauta daurin necktie dinshi.
Murda handle din kofar yayi yashiga da sallama, kamar kullum, yauma wannan sanyayyar qamshin da harya fara kama dakin yayi mashi maraba.
Shaqa numfashi yayi ahankali sannan ya fesar, yau qamshin na dabanne don bayan na Wanda dakin yasabayi akwai wani kuma daban Wanda yakasa tantancewa.
Stairs yanufa cikin takunshi na qasaita yana hawa daya bayan daya harya isa sama.
Yauma kamar kodayaushe ko kallon saitin kofar beyiba ya bude kofar shi yashige.
Kasancewar tana toilet tafara wanka duk bataji shigowarshi ba, hasalima tasan lokacin dawowarshi don haka bata kawoma ranta dawowarshi yanzu ba.
Bayan yan mintuna tafito jikinta na digar ruwa, wucewa tayi closet direct don ga yadda ake zafinnan batajin zata iya shafama jikinta komai.
Budewa tayi ta tsaya hannaye riqeda kugu tana bin kayanta dake Jere gwanin kyau da kallo tana shawarar wanne yakamata tasaka.
Ta Dade tana ruwan ido kafin taciro wani three quarter din wando gari mai adon pink din zare a gefe gefen wandon sai mahadinshi wato armless pink vest mai zanen yar Tamar Barbie agaba sannan ta Parke gashinta tsakar kai tayi doughnut dashi sannan tasa wata farar hula marar nauyi.
Turare kawai ta fesa sannan tazura wasu pink baby shoes ta maida earphones dinta ta dauki wayarta tafita.
Harta zauna zata fara serving kanta taji tana sha'awar local lemu, tunawa tayi da lemun tamarin datagani dazu a group, ganin beda wuyar yi yasata tashi tashiga kitchen din don hadoshi.
Tana shiga yafito daga dakin cikin shigar qananun kaya ba Adidas.
Hannunshi daya cikin aljihu dayan kuma riqeda wayar dake kareda kunnenshi alamun waya yake.
A daya daga cikin qayyatatun kujerun falon ya zauna yayi irin balancing dinnan kamar wani Dan sarki ya Dora hannunshi dake cikin aljihu bisa kan kujerar yana cigaba da amsa wayar.
Cikin takunta tafito, hannunta daya riqeda wani haddaden jug, dayan kuma riqeda Glass cup.
Dining tanufa batareda takawoma ranta komai ba.
Serving din kanta tayi cikin plate sannan ta zuba drink din a glass cup tasaka straw aciki sannan ta zauna ta dauki spoon and fork tafara cin abincin cikin nutsuwa.
Tun fitowarta ya bar gane abinda ke wakana a wayar dasuke, da ido yabita tunda tafito har ta isa dining din.
Da farko kasa ganeta yayi, saida ta zauna tana facing dinshi sannan ya wayeta.
Kasa dauke idanu yayi akanta, duk wani motsi nata akan idanunshi, yadda kukasan anhada magnet tsakanin idanunshi da jikinta don kallonta yake bako kyaftawa.
Ita kau a bangarenta batamasan yanayiba don kwata kwata bata kawowa ranta da wani agidan bayan itaba, dukda tana jin alamun idanu akan ta amma bata maida hankali akaiba.
Ringing din wayarta yasata ajiye glass cup din datake tsotsar drink din ta dauki wayar tana duba mai kiran.
Ganin daddy ke kiran yasata katse kiran tana murmushi sannan tasake Kira.
Ta kara a kunne fuskarta fall murmushi sannan ta dauki cup din takai baki tana kur6a.
Kamar ance ta dago, sai caraf idanunshi suka hade.
Wani wawan zuwa tayiwa lemun abinka da tsamiya nan take tahaumata bisa kai tafara tari cikin fitar hayyaci Wanda har tana saukowa qasa...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan cuts (covid19)🤲
Allah kabamu zaman lfy a qasarmu🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
033
Washegari ma bata fitoba saida ta tabbatar da yabar gidan, sannan tafito ta samarma kanta abinda zataci ta gyara gidan ta goge Tass ta saka turaren wuta sannan tayi hayewarta sama.
Ba ita ta saukoba sai bayan azahar ta nufi kitchen ta Dora abinda zata sakama cikinta sannan ta gyare kitchen din ta tattara abincin tayi sama.
Yauma sai wajajen qarfe Tara ya dawo gidan, kamar jiya beko ni takan dakintaba yayi shigewarshi dakin shi.
Ataqaice dai haka sukaita wasan 6uya tsakaninsu, koko ince take wasan 6uya dashi don izuwa yanzu ta laqaici lokacin fitarshi da dawowarshi don haka ta rage zaman sama, tana saukowa qasa ta yini amma da tayi sallar isha'i kuma ita da saukowa sai Allah ya kaimu kuma.
Tanada kwana biyar su mardeeya su kazo harda baby don biyamusu tayi su kazo tare.
Ranar kau saudart taga ta kanta don tisata gaba sukayi da tsokana iri iri.
Tun tana maida martani harta haqura, ita kau baby wani sa'in ta shigarmata wani sa'in ta koma masu Nafeesa su tararmata.
Basu suka bar gidanba sai qarfe shidda da Rabi na marece bayan ta cikasu da kyauta na kayan kwalliya da snacks ta rakosu har wajenda motar baby take don aciki su kazo.
Jitake kamar tabisu don zaman kadaicin ya isheta gashi tayi missing din daddynta sosai dukda kullum cikin waya suke.
Ahaka sukayi bankwana cikin mararin juna saudart na musu addu'ar Allah ya tsare kasancewar su mardeeya gobe zasu koma Maiduguri.
Ba ita takoma cikiba saida taga fitarsu.
Bin harabar gidan tayi da kallo don yau ne karon farko data fito harabar tun zuwanta.
Bin wajen taitayi da kallo don ya qayatu iya qayatuwa ga trimmed flowers daya zagaye wajen gwanin burgewa.
Ta6e bakinta tayi ta jiya ta koma ciki don har anfara kiraye kirayen sallar magrib.
Yauma kamar kullum tana bata sake saukowa ba bayan isha'i.
Kwanci tashi yau kwananta sha bakwai a gidan.
A yanayin zamantakewarsu babu wani chanji don rabonda Susa juna a idanu tun ranar auren su.
Izuwa yanzu saudart tasake da gidan sosai babu inda bata saniba agidan.
Akwai komai agidan kama daga abinci da kayan more rayuwa.
Saidai tana cikin kadaici sosai, kullum ita kadai ke yini inba Allah yajefo mata wani baqoba, wani sa'in don debe kewa saita shiga garden dake bayan gidan don hutawa ko ta zauna falo tayi kallo.
Bakery dinta kau kullum tana samun bayanai akan yadda yake tafiya kuma alhamdullilah sai bunqasa yake.
Haka zalika kusan kullum sai sunyi waya da Ummy don izuwa yanzu tana Sakin jiki daita su danyi fira kasancewar Ummy batada matsala kuma tana sonta sosai don saudart badai hankali da nutsuwaba.
Wani sa'in idan kadaici ya isheta saita bugama Ummy ta roqeta akan baby tazo.
Duk zuwan da baby keyi bata yarda takai magrib take juyawa, saudart tasha yimata tayin kwana amma firr take qiyawa wai in taganta lahira kaita akayi.
A bangaren ashraf kuwa tuni yakoma bakin aikinsa, dama hutun sati daya ya dauka, shima saboda matsawar sadeeq.
Shi harga Allah wani sa'in mancewa yake da yanada mata, rabonda yasata a idanu tun awajen dinner.
Yasan haqqinshine yasan yaya take ciki dakuma kula da lafiyarshi amma bejin yana iya zuwa ganinta, aganinshi ai ba normal aure bane auren su, auren kwangila ne kowa da dalilinshi nayin auren kuma kowa da abinda yake targeting.
Jera abinci take bisa dining tanayi tana kada kai tana humming tana bin waqar datakeji ta earphones din kunnenta.
Saida ta shirya komai a table din sannan tayi sama tana Dan hadawa da tsalle tsalle Wanda duk acikin shauqin waqar datake jine.
Tana shiga tacire earphones din kunnenta ta fara tu6ewa don watsawa don yau garin badai zafiba, yadda akayi rana yau dakyar idan ba ruwan sama za'ayi ba. Tana gama ty6ewa ta dauki towel ta daura tashige toilet.
Horn yayi sau daya, nan aka shiga scanning din motar, bayan angama gate din ya wangale dakanshi ya kutsa kai yashiga.
A parking space yayi parking sannan yafito ya rufe kofar yayi locking din motar sannan yanufi cikin gida yana sassauta daurin necktie dinshi.
Murda handle din kofar yayi yashiga da sallama, kamar kullum, yauma wannan sanyayyar qamshin da harya fara kama dakin yayi mashi maraba.
Shaqa numfashi yayi ahankali sannan ya fesar, yau qamshin na dabanne don bayan na Wanda dakin yasabayi akwai wani kuma daban Wanda yakasa tantancewa.
Stairs yanufa cikin takunshi na qasaita yana hawa daya bayan daya harya isa sama.
Yauma kamar kodayaushe ko kallon saitin kofar beyiba ya bude kofar shi yashige.
Kasancewar tana toilet tafara wanka duk bataji shigowarshi ba, hasalima tasan lokacin dawowarshi don haka bata kawoma ranta dawowarshi yanzu ba.
Bayan yan mintuna tafito jikinta na digar ruwa, wucewa tayi closet direct don ga yadda ake zafinnan batajin zata iya shafama jikinta komai.
Budewa tayi ta tsaya hannaye riqeda kugu tana bin kayanta dake Jere gwanin kyau da kallo tana shawarar wanne yakamata tasaka.
Ta Dade tana ruwan ido kafin taciro wani three quarter din wando gari mai adon pink din zare a gefe gefen wandon sai mahadinshi wato armless pink vest mai zanen yar Tamar Barbie agaba sannan ta Parke gashinta tsakar kai tayi doughnut dashi sannan tasa wata farar hula marar nauyi.
Turare kawai ta fesa sannan tazura wasu pink baby shoes ta maida earphones dinta ta dauki wayarta tafita.
Harta zauna zata fara serving kanta taji tana sha'awar local lemu, tunawa tayi da lemun tamarin datagani dazu a group, ganin beda wuyar yi yasata tashi tashiga kitchen din don hadoshi.
Tana shiga yafito daga dakin cikin shigar qananun kaya ba Adidas.
Hannunshi daya cikin aljihu dayan kuma riqeda wayar dake kareda kunnenshi alamun waya yake.
A daya daga cikin qayyatatun kujerun falon ya zauna yayi irin balancing dinnan kamar wani Dan sarki ya Dora hannunshi dake cikin aljihu bisa kan kujerar yana cigaba da amsa wayar.
Cikin takunta tafito, hannunta daya riqeda wani haddaden jug, dayan kuma riqeda Glass cup.
Dining tanufa batareda takawoma ranta komai ba.
Serving din kanta tayi cikin plate sannan ta zuba drink din a glass cup tasaka straw aciki sannan ta zauna ta dauki spoon and fork tafara cin abincin cikin nutsuwa.
Tun fitowarta ya bar gane abinda ke wakana a wayar dasuke, da ido yabita tunda tafito har ta isa dining din.
Da farko kasa ganeta yayi, saida ta zauna tana facing dinshi sannan ya wayeta.
Kasa dauke idanu yayi akanta, duk wani motsi nata akan idanunshi, yadda kukasan anhada magnet tsakanin idanunshi da jikinta don kallonta yake bako kyaftawa.
Ita kau a bangarenta batamasan yanayiba don kwata kwata bata kawowa ranta da wani agidan bayan itaba, dukda tana jin alamun idanu akan ta amma bata maida hankali akaiba.
Ringing din wayarta yasata ajiye glass cup din datake tsotsar drink din ta dauki wayar tana duba mai kiran.
Ganin daddy ke kiran yasata katse kiran tana murmushi sannan tasake Kira.
Ta kara a kunne fuskarta fall murmushi sannan ta dauki cup din takai baki tana kur6a.
Kamar ance ta dago, sai caraf idanunshi suka hade.
Wani wawan zuwa tayiwa lemun abinka da tsamiya nan take tahaumata bisa kai tafara tari cikin fitar hayyaci Wanda har tana saukowa qasa...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka wanzar da zaman lfy a qasata qasarmu Nigeria🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
033
Wani irin zabura yayi, besan yaya akayi ba kawai sai ganinshi yayi tsugunne gabanta yana riqota batareda saninshiba.
Dukda yanayin datake ciki hakan be hanata jin wani Yarr daga kanta zuwa yatsan kafartaba.
Ganin yana qoqarin rungumo yasata kwacewa da karfi da kingin qarfin ta, taja baya tana cigaba da tarin.
Hannu tamiqa saman table din ta rarumo Goran ruwa ta 6alle murfin ta kafa Kai.
Ahankali ta sauke Goran tana kallonshi da jajjayen idanunta dauka fara d'urar ruwa sanadiyar qwarewa datayi.
Shikau mutuwar tsuggune yayi, ko kwakwaran motsi yakasa.
Yama rasa yadda akayi yazo har gabanta harma ya ta6ata.
Wani matsanancin kunya da takaici ya qumeshi kamar ya nitse a qasa.
Ganin yadda take kakkare jikinta yasashi binta da wani matsiyacin kallon up and down mai nuna alamun 'mezan gani anan' sannan yaja tsaki yamiqe yajuya, fuuu yabar falon dama gidan gabadaya.
Binshi da idanu tayi harya fita daga falon, zuciyarta inbanda aikin bugu babu abinda take.
Ta Dade a tsugunne batareda tadawo normal ba saida taji wayarta na ringing sannan tadan farfado.
Tashi tayi dakyar don haryanzu jikinta na Dan rawa rawa, ta dauki wayar a inda ta fadi qasa ta zauna saman kujera sannan ta daga.
"Shalele?"
"Dad.."
"Kin kirani na daga kuma ta yanke, nayita bugowa kuma babu amsa"
Shiru tadanyi tana qoqarin daidaita muryarta.
"Dad am sorry, baqi nayi shine nayi attending dinsu" tafada muryarta still na Dan rawa rawa.
"Ok, amma yanakejin muryarki wata kala? Are you okay?"
"Y..yes dad, kaina ke Dan ciwo"
"Subhanalillah, kinsha drugs, ko nazo nakaiki asibiti?"
"No dad, am okay, nasha Dana kwanta zanji sauqi"
"Ok Kije ki kwanta, zan bugo later akwai maganar dazamuyi"
"Alright dad"
Datse kiran tayi tana Sakin ajiyar zuciya.
Haryanzu takasa yarda da abinda yafaru dazu, wai yaushe ma yadawo gidan bata saniba?
Allah kadai yasan tun yaushe yake zaune yana qaremata kallo.
Ashe shiyasa takejin kamar ana kallonta.
*idiot* tafada cikin jin haushi da takaici.
Babu abinda yafi qonamata rai kamar kallon rainin daya bits dashi.
Tsaki taja ta tashi tana tattare plates din dining din don abincin ma kwata kwata yafita akanta.
Saida ta dauraye plates din data 6ata ta gyare saman sannan ta haye da niyyar ita da zama qasa kuma har abada saidai ta sauko tayi abinda zatayi ta haye sama.
Kwance take rigingine akan gado fuskarta na kallon ceiling saidai idanunta a lumshe suke amma ba barci take ba don duk abinda Beebah ke fadi duk a kunnenta ne.
Saida takai aya sannan ta numfasa ta kalli suzyn dake kwance tundazu kamar mai barci.
"Toyaya kikaji tsarin?"
Kamar bazata motsaba sai can ta saki ajiyar zuciya tana bude qananun idanunta akan fuskar Beebah sannan ta motsa la66anta dakyar tace
"Kenan duk wannan shirin da kike lissafowa duk inanan ina sagale da baki ina ganin su a tare za'ayi shi? You don't get me Beebah, banaso, vanason inwayi gari da tunanin my man tareda kowacce irin tsinnana, I want him for me, me alone, bazan iya jira harna tsawon lokacin da kike cewaba, na tabbata izuwa lokacin zuciya ta tariga da ta tarwatse"
Zama Beebah tayi bakin gadon kusada ita tana cewa
"Suzy, wannan itace kadai mafita, ya kike magana kamar batareda ke mukaje wajen ta ba, kamar bakiga yanayinta ba, yarinyar nan yar barikice, tasan takan barikanci, kalamanta ma sun nuna hakan, kawai zuru ne zaici zuru, ta hanyar data biyomana tanan muma zamu bida ita, ashraf nakine ke kadai, kisa wannan a ranki" tafada cikin qarfafa gwiwa.
Haka taita lallaminta harta samu nasarar bida ita hanyar datakeso, bata bartaba har saida taga ta dorata akan abinda sukeson cimmawa.
Yau kwana biyu da faruwar wannan al'amari tsakanin Ashraf da saudart.
Basu sake haduwaba don kowa yasake Jan baya da Dan uwanshi fiyeda da.
Ita tabar dadewa a qasa shi kuma yabar dawowa dawuri.
Don haryanzu kowanne cike yake da takaicin abinda yafaru ranar.
"Dad, I really need to get back to my work, I can't take it anymore, kullum ni kadai acikin gida kamar mayya? Nidai zanyi resuming on Monday, nagaji ai wannan deal din maku be shafi aikinaba, so am resuming" tafada cikin yanayin jin haushi don jitake kwata kwata ta tsani zaman gidan.
"Ban qi ta takiba shalele, it's normal idan kikayi resuming amma baki tunanin yakamata kiyi advancing din profession dinki? A matsayinki na Matar A.A be kamata ace kina zuwa bakery ba da sunan aiki, it's embarrassing"
Jim tayi tana sauraron daddy tana jin maganganun nashi wani bambarakwai musanmman *Matar A.A* daya ambata.
"I don't get you dad" tafada cikin Rashin fahimta.
Gyara zama dad yayi a bangarenshi yana murmushin samun nasara.
"Abinda nake nufi shine, tunda kinada bakery kuma kina iya gudanar dashi ko kina nan ko bakya nan, why not kisamu wani aikin daban da takardunki?"
Jimm tayi tana sauraron daddyn lokaci daya kuma kwakwalwarta na nazari akan maganarshi.
Katsemata tunani yayi da cewa
"Kinga zakifi samun kudi, ga na bakery ga salary, nima nan am trying my best, kinga saimu hadu mu hada qarfi wajen hada kudin mijinki mu biya a warware komai kowama ya huta"
Shiru tayi na yan daqiqu tana nazari akan shawarar Dad.
Eh hakane, wannan shawara ce, dukda bata cika son aikin office ba tana iya daurewa tayi kodan fita daga wannan vanzar deal din marar kan gado.
"Ya kikace shalele?"
"Deal, saidai ta ina zan fara?"
"Bakida matsala sweetheart, ba ganiba? Daddy zaiyi komai wa shalelenshi" yafada cikin fara'a.
"Awnn! Thanks dad, I love you"
"Love you more"
Tunda suka gama wayar yaketa aikin zabga murmushi.
"A.A, yanzu lokacina ne" yafada yana shafa gemunshi.
"Ummy please.. Zan kawota, I promised" yafada kamar zaiyi kuka
"Ni dalla tashi min, haka kake cewa kullum, sai yaushe zaka kawota din? Nida diyata ace sai an Mani rowarta? To wlh kaji na rantse gobe gobenan nakeson ganinta kaji ba gayamaka" tafada tana tureshi daga kan cinyarta.
Qin daga mata cinyar yayi, data tureshi saiya koma.
Itakau baby na daga can gefe akan kujera tana satar kallonsu tana ta6e baki.
"Wai bazaka tashi ba saika karya ni?" Inji Ummy tana qara tureshi
"Ummy please mana, wai me nayi ne?" Yafada yana qara komawa
"Mekayi? I told you I want to see her kana min rowa?"
"To ai Ummy magana tariga ta qare tunda har kinyi rantsuwa, you'll see her tomorrow, saiki cinyeta karki barmin ko kingi"
Rankwashi tabashi lafiyyaye
"Eh din zan cinyeta din, dagani"
Shafa kan yake yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka
"Kai Ummy wlh yanzu kinbar so na"
"Dama, ai yanzu nabar wayata yayinka, yanzu lokacin autata ce bakaiba godai godai dakai"
Kallon saitin baby yayi daketa Satan kallonsu tundazu tana qumshe dariya.
Ganin zai kallota yasata saurin kawar da idanu tana duba littafin hannunta a wayance.
"Ke jeki hadomin coffee" yafada yana tamke fuska.
"Bazata hadoba, kaje Matar ka ta hadamaka"
"Kai Ummy..."
"Ke tashi kiwuce sama kaima katafi gida ka baro diyar mutane ita daya"
Da sauri baby ta tashi tayi sama don dama tunda yace ta hado coffee take jinta kamar saman qaya.
Haka ta tisoshi gaba har wajen motarshi riqeda kunnenshi daya shikau sai qara yake saki qasa qasa, Kai kace ba A.A bane uban yan ji dakai.
Haka ta turashi mota ta rufe taja baya tana dagamashi hannu harya fice yana zum6urar baki...✍
No editing, kuyita hqr da mistake please🙏
0 comments:
Post a Comment