Yau Friday Wanda yayi daidai da ranarda akayi shara'a da mutanen Spain.
Anyi bincike anga basu kadai suka yaudara ba, sun yaudari mutane da dama ta wannan hanyar don haka aka yankemasu hukuncin zaman gidan yafi na tsawon shekaru goma bayan sun biya duk wadanda suka yaudara kudadensu, qarshe ma company dinsu akasa kasuwa aka siyar sannan aka ba kowa haqqinshi cikinsu harda su Ashraf.
Duk wannan bidirin da ake hankalin Ashraf be wajen sosai, duk sadeeq ne ya tsaya a komai don yakasa gane kan Ashraf, yakoma wani soo silent dashi, dama yanada dan miskilancinshi tou sai abin ya hade da damuwa sai ya kasance duk inda kaganshi zaune yake shi kadai yana qurama waje guda idanu.
Kwana hudu kenan rabonshi da ita, bata zuwa office, bata gida, bata bakery don kullum ne sai yaje bakeryn yayi parking daga nesa yana kallon masu shige da fice amma ko mai kama daita begani.
Har spy yasa Wanda zai zauna permanently wajen don ganin ko za'a samu akasi yana tafiya tazo amma duk amsar dayace, babu saudart.
A gida ma Ummy ta lura da yanayinshi dukda idan yaje yakan fuske yaita acting normal amma dayake uwa uwace ko yaya danta ya sauya koda ya 6oyemata saita gane, tasha tuntu6anshi akan abinda ke damunshi amma saiya waske da gajiya ce ko ayyuka sukai mashi yawa.
Dayake su Ummy ma sunada labarin yaudarar da akayi musu yasata ganin qila duk akan maganar ce, saidai har kawo yanzu basu ta6a sanin saudart na aiki a companyn shi a matsayin secretary ba bare Susan itace silar warwarewar wannan qulla qulla ba don ko wannan tafiyar dasukayi su a tunaninsu aiki yatafi da Matarshi don haka basuda masaniya akan komai bare su zargi komai.
***********************************************
*MONDAY*
Zaune yake a kujerarshi mai jujjuyawa, hannayenshi harde a Qirjinshi yayi balancing a kujerar idanu a lumshe sai jujjuyawa yake a kujerar kadan kadan.
Sanye yake da suit saidai tasaman na rataye a jikin wani hanger dake daga gefen office din, sai farar shirt da baqin wandon daya bari a Jikinshi, gashin kanshi kwance luff sai sheqi yake.
Kamar kullum yau ma tunaninta daya zaman mashi jiki yake, dama da ka ganshi haka shi kadai yayi zurfi a tunani to ba kowa ke maqale a zuciyarshi ba sai ita.
Tunaninta ke debe mashi kewa, hotunan ta ke sashi nishadi, don kullum yana maqale da wayarta yana kallon hotunan ta.
Yanzun ma tunanin inda zai ganta yake, koda yake baza'a ce besan inda take ba, hasalima yafi kowa sanin inda zai sameta saidai baya tunanin zai iya binta har wajen, bazai iya binta har can ba don aganinshi hakan ba qaramin zubda mutunci bane, hmm karkuyi tunanin soyyayar saudart ta chanza shi ko yayi laushi.
A'a he's still the proud Ashraf dakuka sani, haryanzu jin kanshi na nan, badan haka ba da tuni yabita har gidan daddy ya dawo daita amma gani yake hakan ba qaramin zubda class bane.
Yes yasan yana sonta amma hakan bazai sa yajawowa kanshi raini ba, shi yanzu kawai soyake tadawo, idan yasamu tadawo to komai zai tafi cikin sauqi, zaisan yadda zai cusamata soyyayar shi, yadda zai yimata mummunan kamu taji duk duniya babu Wanda take so saishi, shikuma sai yadan jamata aji sannan ya nuna yafara Sonta😒
Haka yaita wawwanawa a kujerar yana tsaka yana kwance wa akan yadda zai 6ulloma al'amarin.
Jin bubbugar kofa yasashi dagowa yana kallon kofar office din.
Sake bubbugawa akayi a Karo nabiyu hakan yasashi Jan guntun tsaki don ya tsani a dameshi yana cikin tunani musanmman ma irin wannan.
"Yes? Come in" yafada cikin harsh voice sannan yajawo wata takarda yana kallo fuska a daure.
Murda handle din kofar akayi sannan aka turota aka shigo sannan aka maida aka rufe.
Jin muryar sadeeq na sallama yasashi amsawa qasa qasa sannan ya dago da niyyar tambayarshi lfy?
Idanunshi basu sauka a koina ba sai cikin nata.
Cak bugun zuciyarshi ya tsaya, jinin Jikinshi ya daina gudana yakuma kasa ko kyafta ido akanta.
Cikin takunta Wanda nayau yafi na kullum ta qaraso gaban table dinshi.
"May I?" Tafada tana Jan kujerar gaban table din baya ta zauna batareda ta jira jin ko yabata izinin zamanba ko A'a.
Shidai binta kawai yake da kallo without blinking, maqoshinshi yaji ya bushe babu yawu ko kadan, be ta6a sanin yayi missing dinta har hakaba sai yanzu daya ganta, be ta6a jin abinda yakeji gameda itaba irin na yanzu, jiyake kamar Gwara lokacin da be ganinta, jiyake kamar yana narkewa ahankali, soyyayarta sai qara fuzgar zuciyarshi take.
Zama tayi ta Dora kafa daya bisa daya itama ta kalleshi.
Sanye take cikin doguwar rigar net baqa mai dan kamawa daga sama sai budewa daga qasa, hannun rigar dogone har qaurin hannu, kasancewar ba'a yiwa hannun lining ba yasa farar fatarta tayi reflecting tacikin raga ragan net din, kanta kuma nade da baqin gyale iya kafada sai qaton sun glass data kwamama fuska Wanda yakusan cinye Rabin fuskar, dan guntun bakinta kuma dauke da dark red lipstick Wanda yaqarama kyanta kyau.
"Have a seat Alhaji" maganar sadeeq ta katse Ashraf daga kallon qurrillar dayakema saudart yajuyo dan ganin dawa yake.
Alhaji shamsu yagani yana Neman zama a kujerar dake kusada ta saudart.
Binshi da kallo yayi harya zauna sannan ya maida kallonshi kan saudart data hade gabass da yamma na fuskarta yana mata kallon Rashin fahimta.
Tsit office din yayi babu mai niyyar motsawa kowa ya zubama dan uwanshi idanu kawai.
Ganin sun kusan 5mins babu mai niyyar magana yasa sadeeq dake tsaye still agefe yadanyi gyaran murya yace
"You're highly welcome Mr and Miss shamsu" yafada cikin fara'a.
Dawowa yayi gefen Ashraf dahar yanzu be dauke ido akansu ba sannan yacigaba dacewa
"Akawo coffee ko drinks?"
Murmushi saudart tadan saki tana kallon sadeeq
"No, mun gode da karramawa, amma ba zama yakawomu ba bare ayi maganar refreshment, we're here for *BUSINESS*"
tafada tana maida kallonta kan Ashraf dake kallonta still, zuciyarshi sai narkewa take ahankali soyyayarta na hudata ta koina.
"Business?" Inji sadeeq cikin Rashin fahimta sai kuma ya kalli Ashraf Wanda alamu sun nuna bemasan wainar da ake toyawaba.
Maida kallonshi yayi akansu sannan yace
"Ok, wannan wane irin business ne?"
Wannan karon Alhaji shamsu yayi magana yace
"Ba business bane, qarshen business ne, munzo ne mukawo qarshen business din dake tsakaninmu" yafada shima calmly
Gaban sadeeq ya fadi, dama ya zargi hakan tunda yagansu, dama abinda yake Gudu kenan.
Kallon Ashraf yayi da yanzu Alhaji shamsu yake kallo Wanda da alama shima yaji abinda yace din don shima wani kallo yake mashi mai wuyar fassaruwa.
Maida kallonshi yakuma yi gasu saudart yace
"Ban fahimceku ba, what do you mean by qarshen business"
"A tunanina business daya ke tsakaninmu.."
Katse ta sadeeq yayi da
"Yes and that was aikin ki anan"
Wani kallo ta jefeshi dashi
"That was then, I thought tun wancan satin na ajiye aikin"
"Da izinin wa? As far as I remember bamu sallameki ba kuma baki kawo resignation letter ba" inji sadeeq Wanda yanzu tsoron shi daya ne, rabuwarsu da Ashraf.
Dan guntun murmushi tayi sannan tasaka hannu a jakka tafido wata takarda a linke ta turamasu Gabansu
"Here, ga resignation letter din, nabar aiki"
"But why, meye dalilin ki na hakan" inji sadeeq, Ashraf kau ba baka sai kunne
"Dole saida dalili? A tunanina kamar yadda boss ke iya sallamar employee dinshi haka kawai shima employee na iya barin aiki haka kawai, yanada right din hakan"
"Amma kinsan baki ida one month ba? What about your salary?"
Dariya tadanyi tana sinne kai
"Salary? Me zanyi dashi?"
Shiru sadeeq yayi yana kallonta
"I don't need your salary Mr, saboda ba don shiba nafara aiki, you can keep it, zai qaramaku wani abun, nikam.. A'a"
"Bamucin gumin mutum, salary dinki guminki ne, so muma babu amfanin dazaimana"
Daga kafadunta tayi in an I don't care manner
Sannan ta maida kallonta kan Ashraf daya zama kurman qarfi da yaji
"As I was saying, munzo nan ne don qarashe business, I mean *THE CONTRACT*"
kallon daddy tayi shikuma ya doro wani akwati saman table din tareda budewa saiga kudade raw, dubu daya daya bundle bundle.
Bin kudaden Ashraf da sadeeq sukayi da kallo kowanne da irin kalan bugun zuciyarshi
"Mr A.A, a rana irin ta yau wata hudu dasuka wuce nazo nan don Neman taimakon ka na rancen kudade qimanin million talatin a wajen ka, kace naje nadawo bayan kwanaki biyu
Ranar da nadawo kuma ka sanar dani zaka bani rancen amma kanada sharadi"
Dan dakatawa yayi yana kallon Ashraf don ganin reaction dinshi, sai gani yayi still yana bin kudaden ne da kallo hakan yasashi cigaba dacewa
"Sharadin shine nabaka auren diyata bisa sharadin babu abinda zai shiga tsakaninku na auratayya kan idan na maido kudinka zaka sakarmin ita."
Nan ma dakatawa yayi yana kallonsu, sadeeq sai zufa yake dukda sanyin A.c din office din shikuma A.A is expressionless, baka iya gane yanayin dayake ciki.
Turamasu akwatin yayi yana cewa
"Yau gashi na maido maka da kudaden ka Mr A.A, dama wancan karon mu hudu ne, ni, kai, saudart sai kai Mr sadeeq"
"Now here is your money, give me my daughter" yafada yana tsaresu da idanu.
Itama saudart su take kallo zuciyarta na halbawa da sauri, wannan ne ranar data Dade tana dako, ranar da komai zai warware, kallo daya tayi musu ta ga mammaki da firgici dukda na Ashraf be nuna ba sosai, dama haka takeso, tayi taking dinsu in surprise, tayimusu dan baka zata, ta nunamusu ba dasu suka dogaraba.
Yau dai zata rabuda qaya, tunanin hakan ya hanata barci jiya don azaune ta kwana.
Tana murna amma kuma tana samun faduwar gaba Wanda batasan kota menene ba kuma bata damu tasaniba, all she know is yau zata rabu da allaqaqai and she's glad it's happening
A bangaren sadeeq kuma tashin hankali ne qarara a fuskarshi.
Tayaya zasu rabu yanzu, saudart is the perfect lady for Ashraf, ta dace dashi, idan ta su6uce mashi yayi babban asara.
Dama abinda yake Gudu kenan, dafarko beyi tunanin abin zai zama haka ba amma gashi abun na Neman juyemusu.
Kudaden yaqara kallo sannan ya kalli Ashraf da haryanzu su yake kallo fuska babu yabo babu fallasa amma shi kadai yasan badaqalar dake faruwa a zuciyarshi...✍
Ku bude next page da 200 comments, zan qilga idan baikai ba karku saka ran ganin wani page din nan kusa😏
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
Wow! Gaskiya jiya naga ruwan comments ta koina😄
Harda yan la6el duk anfito jiya anyi sharhi, gaskiya naji dadin comments dinku na kowanne group, amma mafi yawanku duk masu Allah ya qara ne ga A.A dinmu.
To afa kiyayemu ehe, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi🤔
To kudaibi sannu kar shalelen taku ta antayaku cikin kogin kunya🙈😆
057
Tsit kakejin office din kamar babu Abu mai rai aciki.
Wani irin shiru ke ratsa office din babu mai ko motsi bare akaiga magana.
Kallon kallo ake tsakanin juna kowanne na jiran dan uwanshi ya motsa.
Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji shamsu muskutawa kadan yace
"Ya kukayi shiru?" Yafada yana kallonsu
Sadeeq ne yayi qarfin halin bude baki yace
"Abin ne yazo mana a bazata... But.. Atleast.. Dakun fadamana munsan da zuwanka" yafada cikin kame kame.
Murmushin manya Alhaji yasaki sannan yace
"It's still don't make different, duk dayane, damu gayamaku kafin muzo damu gayamaku yanzu aganina duk dayane tunda a takardar contract din bamuyi yarjejeniyar sai mun fara fadamaku ba idan zamu maido, ko akwai?" Yafada yana tsareshi da idanu.
Ajiyar zuciya kawai sadeeq ya sauke don besan ta cewaba kuma.
Kallon Ashraf da tunda suka shigo kawo yanzu be furta Kalma dayaba yayi sannan yabude bakinshi dakyar yace
"Sir, they are here for the end of the contract" yafada yana kallonshi yana son karantarshi but he's blank.
Shiru office din yasake dauka duk idanu suka koma kanshi kowa na jiran reaction dinshi yayinda shi ko dago kai beyiba idanunshi haryanzu na kan akwatin gabanshi yana kallo amma a badini zuciyarshi takusan gama tarwatsewa.
Komai ganinshi yake kamar a mafarki, koda wasa be ta6a kawota ranshi zasu iya biyan kudaden nan nan kusaba, komai ya juyemashi ya zomashi a baibai.
Rabuwa? Rabuwa da saudart? Wannan shine Abu na qarshe dazai zomashi arai, Ada yake sanyo rabuwarsu a tunaninshi amma banda yanzu, no way, bazai ta6a yiwuwa ba.
Saida suka fara qosawa da shirun sannan ya janye idanunshi akan akwatin da yayima quri tundazu sannan ya dagasu ya zubamata su.
Wani kaifi taji idanun nashi sunyi mata ga wani kwarjini na musanmman dasukayi dan saida jikinta ya amsa wannan kallon, hakan yasata saurin janye idanunta tana sauraron bugun zuciyarta daya qaru farat daya
Kafeta yayi da sharp eyes dinshi babu ko kyaftawa Wanda hakan yasata jin ta ataqure matuqa, sadda idanunta tayi aqasa cikin zuciyarta tana godewa Allah ta sanyo sunglass babu yadda zai iya hango kwayar idanunta bare ya fuskanci halin dasuke ciki.
Ahankali ya motsa bakinshi kamar mai ciwon baki still idanunshi akanta yace
"Ina son ganin ki" yafada yana kafeta da idanu.
Kallon juna saudart da daddy sukayi sannan suka maido dubansu akanshi kuma
"Ganina?.... You mean yanzu baka ganina ne?" Tafada tana kallonshi tacikin glass dinta
Yanzun ma saida yayi kamar bazai yi magana ba sannan yasake motsa bakinshi dakyar
"Alone" yafada a ataqaice
Wani qululu ta tokareta, me wannan gayen ke nufi ne? Abinda ya kawosu daban abinda yake fadi daban, gashi sai wani shan qamshi yake kamar Wanda ake tilastawa yayi magana?
"Alone kamar yaya?" Tafada tana qoqarin danne 6acin ranta don yau ranar farinciki ne gareta, ranar da tadade tana jiran isowarta, ranar da ta shanye wulaqanci da cin mutunci saboda ita, batason mood dinta ya 6aci don yau ranar farincikinta ne
"I mean ke kadai... Zamuyi.. Magana ne" yafada yana kallonta
"Ka fadi koma menene anan din, inaji babu wani baqon fuska anan, idan P.A din nakane baka yarda dashiba kana iya sashi yafita" tafada tana kauda idanunta daga piercing eyes dinshi
"Eh zai fita amma tareda wannan ma" yafada yana nuna Alhaji shamsu
Haushi yakamata, wai wannan, daddyn natane wannan ma
"Karka damu shi wannan din is my backbone, idan bashi bani, kome kafada Mani kamar shi ka fadamawa, so feel free to say anything... Besides banga abun long story ba anan, wannan magana ce na signing da divorce, banga abun tsayawa na wasting din lokaci ba, as you can see munada ayyuka dayawa gabanmu Wanda zamuyi attending, can we please proceed with the signing Mr A.A?" Tafada tana jin kamar tayi exploding dan haushi
Shiru office din yasake dauka, Shidai sadeeq na gefe yana kallon ikon Allah, bashida tacewa don haka nashi idanu.
Dora hannayenshi yayi akan table din yadanyi leaning forward sannan yace
"Yes miss, nima banaso na 6atamiki precious time dinki nima na 6ata nawa, all I ask is five minutes of your time and mine, minti biyar kacal then komai saiya wakana"
"Wai minti biyar din me? Wace magana ce dole saimun ke6e?..."
Katseta yayi dacewa
"Look miss, wannan office ne ba kasuwa ba ok? Don't dare shout on me, wata hudu dasuka wuce, ke daya kikazo signing din contract din, daga ni sai ke, that's the same procedure we gonna take, five minutes kawai na tambaya and after that sai ayi koma menene" yafada shima cikin fada dukda wata zuciyar na kwa6arshi akan ba tahaka yakamata yabiba amma girman kanshi yahanashi sauraronta.
Saudart iya quluwa ta qulu, bude baki tayi zatayi magana daddy ya damke hannunta Wanda hakan yasata yin shiru ta juyo tana kallonshi.
Daga mata Kai yayi ahankali alamun ta amince kawai sannan ya maida kallonshi ga Ashraf dake masu wani kallo mai wuyar fassaruwa yace
"Five minutes ko? Ok munbaka, muda muka jira kusan five months, five minutes bazai bada matsala ba"
Yana kaiwa nan yamiqe tsaye ahankali sannan ya kalli saudart da kallo daya zakamata ka fuskanci ranta beso wannan hukuncin ba, yadan yimata murmushi sannan yafita.
Binshi dawani disgusting kallo Ashraf yayi harya fita don ya tsaneshi fiyeda yadda kuke tsammani, a duniya bayajin akwai Wanda ya tsana sama da wannan mutumin.
Sadeeq ma bejira komai ba ya nufi kofar fita yana addu'ar daidaito atsakaninsu, qasan zuciyarshi kuma fall take da takaicin ashraf, ya rasa irin taurin kanshi, shi a tunaninshi kwantar dakai zaiyi yabasu haquri asamu a warware komai amma gani yayi ma wani sabon wulaqanci ya tsiro dashi da girman Kai
Can gefen Alhaji ya zauna yana Satan kallonshi cikin zuciyarshi yana cewa
"Albasa batayi halin ruwaba"
**********************************************
Shiru office din yasake dauka, babu Wanda keda niyyar magana acikin su.
Ba yau suka fara ke6ancewa su biyu awaje dayaba amma yau yanayin dasukeji yasha banban Dana da.
Duk sai suka zama speechless, babu mai ko motsi atsakaninsu.
Sun kusan cinye mintuna biyu ahakan sannan Ashraf ya sauke ajiyar zuciya mai sauti Wanda hakan yasa tadan dago ta kalleshi, sai gani tayi yasa hannu ya dauki bundle daya cikin kudaden yana dan jujjuyawa a hannunshi.
Dagowa yayi ya kalleta still yana jujjuya kudin a hannunshi itakau ta kauda idanunta tana jinta duk a takure
"Sun cika?" Yafada still idanunshi kanta
"Ka qilga" ta amsa ataqaice without looking at him
Murmushin gefen baki yayi Wanda shi kadai yasan yayi abunshi yana maida kudin cikin sauran sannan ya kama zip din jakkar ya zuge
"Why the sudden change? Meyasa baki gayaman ba" Ya tambayeta yana maido dubanshi akanta.
Kallon Rashin fahimta tayi mashi Wanda shima besan tanayi ba saboda glass dinta daya kare idanun.
"I said why? You should have tell me" yafada calmly
"Tell you? Meyasa saina gayamaka?" Tafada tana mashi wani kallo
Ajiyar zuciya yasaki sannan yace
"Ok..ok..firstly inason yimiki godiya akan abinda kikayi mana, that shows you're loyal"
Mere baki tayi tana yatsina fuska
"Me kenan? I don't get you"
Murmushin gefen bakin yasakeyi sannan yace
"Kin taimaki al'umma da dama, da wadanda sukayimawa a farko damu dama wadanda zasu sake yimawa nan gaba da asirinsu be tonuba, thank you"
Ta6e baki taqara yi don ita bata wannan takeba
"It ok, besides ni don Allah nayi badon ayi appreciating dina ba, now back to business" tafada cikin qosawa da maganganun shi
Tsayawa yayi yana kallonta yana tunanin dama har haka ta tsaneshi? A qagare take ma ya sawwaqe mata don alamu sun nuna a matse take, zaman nan ma da maganar dasukeyi kamar an matsamata ne, kallo daya zaka yimata ka hango qiyayyar datake mashi Wanda hakan yaqara sagemashi gwiwa.
Jiyake kamar ya zube agabanta yaita bata hqr har ta haqura su zauna tare cikin aminci da soyayya, amma bazai iyaba, kar Allah ya gwada mashi ranarda zai zube gaban mace yana bata hqr, bazai ma ita misalta kanshi a wannan yanayin ba.
"Ok.. Back to business" yafada yana komawa ya jingina da kujerarshi yana kallonta
"Now me kikeso?" Ya tambaya yana bin kyakyawar fuskarta da kallo kamar yasamu mirror
"Me nakeso? Kafini sanin abinda nakeso" tafada cikin 6acin rai ganin kamar Neman raina mata hankali yake
"A tunani na zaku bari harsai mun cika 6months sannan mu warware komai, don't forget yanzu dududu watannin mu uku da auren, me kike tunanin duniya zata fada akanmu" yafada shima yana mammakin kanshi na maganar dayayi
Kallon mammaki saudart ta tsaya tana mashi
"Me duniya zatace? Ina ruwana da abinda zatace? It's my life Mr"
"Yes, it's your life, babu Wanda zaiyi questioning dinki amma mamy fa? Me zaki cemata idan kin koma gida bayan watanni uku a matsayin bazawara?"
Sosai maganar ta daki saudart har saida hakan yanuna a yanayinta.
Ganin hakan yasashi dorawa da
"Yes in so samune murabu din kowa ya kama gabanshi kowama yahuta, amma me zaki gayama mamy? Don't forget batasan komaiba gameda wannan auren ba, ya zataji idan labari ya risketa na kinfito bayan watanni uku da auren ki? Wane dalili zaki fadamata ya rabamu?" Yafada yana kallon yadda yanayinta ke qara chanza wa.
"D..don't worry, nasan me zan gayamata, wannan ba damuwarka bace" tafada trying to be firm
"Me zaki fadamata? Cewa dama auren contract ne auren mu?"
"Wannan be shafeka ba, uwatace ba takaba, babu abinda yashafeka"
"Nikau ya shafa miss, mezan fadawa Ummy idan muka rabu? Mezance shine silar rabuwarmu?" Yafada trying to convince her
"Look mubar wannan maganar, contract ne ya hadamu, kuma shi zai rabamu, babu ruwan wani da abinda zai fada don gamsar da mahaifiyarshi, besides aure nawa akayi? Normal aure, amma basuyi three months dinba auren ya rabu? Mutuwar auren mu a yanzu ba wani Abu bane it's normal, kana iya gayamata duk abinda kaga dama, I don't care" tafada firmly
Sa halshe yayi ya kashi qasan le66enshi ya tsaya yana kallonta ganin tarkonshi besamu danuwa ba
"Amma kinsan mutuwar aure saida dalili? Wani dalili zan bayar na rabuwa dake?"
"Dalili? Dama saida wani dalilin, atunanina kafi kowa sanin dalilin haduwarmu shi zai zama silar rabamu"
"Amma wannan ba hujja bace dazamu rabuba haka kawai, dole sai an samu kwakwarar dalili"
Tsayawa tayi sororo tana kallonshi
"What are you driving at wai?" Ta tambaya tana kallonshi unbelieving
Jan kujerar shi yayi dabaya sannan yamiqe tsaye ya nufi window din office din da labulen ke bude ya tsaya yana kallon waje hannunshi a aljihu itakau sai binshi da idanu take
"Dukda auren mu ba normal aure bane, auren yarjejeniya ne, hakan be hana asashi a jerin aure saboda shima shafamashi fatiha akayi kuma igiyoyin nan uku akwai su tsakanin mu, dan haka shima aurene kuma yana cikin auren da Allah yafada cikin *suratul thalaq*
Inda Allah (swt) yayi hani da saki batareda da qwaqwaran hujjaba, bayyananniya.
Saki yana daya daga cikin abinda Allah beso, Wanda awata ruwayarma cewa ake idan aure yarabu, al'arshi girgiza take saboda girman abun koda kuwa akwai kwakwaran dalili bare wannan Wanda bekai hujjar dazamu fake daita ba mu sa6ama mahallicinmu, idan mukayi hakan me zamu cewa mahallicinmu? Dame zamu kare kanmu?"
Saudart datayi mutuwar zaune tunda yafara magana kasa cewa komai tayi.
Wai meke shirin faruwa ne? Meya kawo wannan maganar kuma? A tunaninta izuwa yanzu sunmance da sun wuce wurin amma sai bullowa yake da abubuwa daban daban
"Look A.A ko mema kake? Meya kawo duk wannan wa'azin? Ohh dama duk kasan da wannan ka fara qirqiro maganar auren tun farko? Inajin kai ka faro komai ba wanibs, ina ilimin, ina sanin a lokacin? Koko sai daga baya duk kasan wadannan?
You force me into this marriage kuma yanzu kafara gayamin story? No way! Bazan ta6a zama dakaiba a matsayin miji, are you not ashamed? Just listen to yourself, bazai ta6a yiwuwa ba kanaji? I can't even stand you, bana jure zama na tsayin lokaci wuri daya dakai, shine kakemin maganar zaman aure, are you kidding me? Look Gwara kabar wannan kwalo kwalon naka and face the reality, this is just business and zai qarene a business! So wa'azinka bazai qareni da komaiba, ka Adana abinka zaifi yimaka amfani mallam" tafada cikin huci
Juyowa yayi yana kallonta tunda tafara har takai aya,
Takowa yayi cikin takunshi harya iso gabanta inda take zaune yana kallonta
"And who told you nima sonike na cigaba da zama dake din, I have no option ne, abinda nasani shine bazan qara tafka sa6oba kamar yadda nayi a bayaba, bazan sakeki batareda wata qwaqwarar hujjaba, final!"
Miqewa tsaye saudart tayi ba shiri
"What!" Tafada tana zare tabarau dinta, jikinta har rawa rawa yake saboda tashin hankali
"Look are you ok? What did you mean by bazaka sakeni ba? Me kake nufi? Na zauna da Wanda duk duniya babu Wanda natsana kamarshi? No way!" Tafada cikin qaraji, tashin hankali qarara a fuskar
Kalmar tsanar data ambata ba qaramin dukanshi tayi ba hakan yasa ya dago idanunshi dasuka fara chanza launi shima ya zubamata
"Nikuma bazan sakekiba! No way!" Yafada cikin 6acin rai
Kallo tabishi dashi na yan daqiqu sannan tasaki wata bushashiyar dariya Wanda daga ji iyakarta fatar bakin
"Wlh kayi kadan Ashraf, baka isaba, dolene ka sakeni! Saika sakeni wlh!"
"Nikuma bazan sakekiba! Aure yanzu aka farashi, sai kisani sakinki din!" Shima yafada a tsawace
"I hate you! You brat! I hate you!!" Tafada cikin qaraji hawaye na 6alle mata.
sai kuma tafara daukar files files din table din tana jifanshi dasu kamar sabuwar kamu tana nannata I hate you din cikin kuka sosai.
Be kare kanshi ba haka yatsaya yana kallonta zuciyarshi na bleeding, duk Kalmar ta daya na I hate you jinshi yake kamar sukar wuqa a zuciyarshi.
Saida tagama watsar da kayan table din sannan tadawo kanshi tana dukanshi da hannu tana kuka sosai sai nannata Kalmar ta tsaneshi take.
Sakin Jikinshi yayi tana dukanshi yana kallonta Yanajin kamar zuciyarshi zata tarwatse.
Jiyake inama zai iya yin kuka da yayi yarage rada din dayake ji a zuciya
Ganin abin nata bana qarewa bane yasashi Kamo kanta, yayi locking din la66ensu waje daya yashiga bata the hottest kiss ever...✍️
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
058
Waro dukkan idanunta tayi kamar zasu fado daga socket dinsu tana kar6ar the shock of her life.
Jikinta ya mutu nan take kamar Wanda aka zarewa lakka, tayi baya baya zata fadi ya sa hannu daya ya tarbota ta qugu yasake mannata da Jikinshi yana kissing dinta kamar kura tasamu nama Jikinshi har rawa rawa yake.
Sun kai minti daya ahakan, saudart kam bata iya misalta yanayin datake ciki don batama cikin hayyacinta.
Ashraf kam wani irin yanayi ya tsinci kanshi, having the extra soft lips of the love of his life in his mouth is undescribable.
Kissing dinta yake yana licking kamar yasamu tomtom shi kanshi yafara fita ahayyacinshi
Ahankali ya fara cire bakinshi daga nata yana kallon fuskarta daya koma jaa kamar tomato.
Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali tare kamar wadanda sukayi wasan tsere.
Dukansu sun kasa yarda da abinda yafaru yanzu.
Kallon juna suka cigaba dayi kowa na qoqarin daidaita numfashin shi.
Saudart takasa yarda da abinda yafaru yanzu, she can't believe yau tasamu first kiss dinta, kuma da Wanda duk duniya babu Wanda ta tsana kamarshi.
Wani ihu tafasa mai mugun qara Wanda saida Ashraf yasaketa babu shiri.
Jada baya tayi ta mannu da bango tana qara fasa wani Qarar Wanda yafi na farko, jikinta sai 6ari yake.
Nufota Ashraf yayi da niyyar yimata magana amma ganin ya tunkarota yasata taqarqarewa ta fasa wata Qarar Wanda saida ya toshe kunnuwanshi.
Banko kofar office din akayi, Alhaji yafado ciki kamar an jefoshi sadeeq biye dashi dukansu a giggice da alamun ihunta sukaji suka shigo.
Ganin saudart sukayi manne da bango tanata ihu shikuma Ashraf na daga can gefe hannayenshi Dade da kunnuwa.
Da sauri Alhaji ya nufi saudart ya riqota
Jin an riqota yasata fasa wata Qarar tana qanqame jikinta cikin fitan hayyaci.
"Shalele! Shalele!! Nine... Meya faru? Open your eyes and look at me.. Daddy ne..open your eyes!" Inji Alhaji yana riqeta gagaam ganin yadda take kiciniyar qwacewa.
"Shalele listen to me, daddy ne..daddy, please look at me" yafada yana rungumeta
Jin kamar muryar daddy yasata dagowa ta dubeshi ganin shine din yasata qara qanqame shi tana kuka kamar zata shige cikinshi
"Take me out dad! Ka fiddani daga nan" tafada cikin gunjin kuka.
"Shalele..."
"Please dad! Take me out" tafada tana qara qanqame shi
"Ok..ok" inji daddy da duk ya rikice suka nufi kofar still tana maqale dashi sannan ya bude suka fita.
Binsu da kallo sukayi har suka fita sannan ahankali sadeeq yajuyo yana kallon Ashraf, kallon tuhuma.
Shikau Ashraf cizon le6enshi na qasa yayi yana runtse idanunshi da qarfi zuciyarshi na mashi wani irin zafi.
"Me kayi mata?" Inji sadeeq yana cigaba da jifanshi da kallon tuhuma.
Bude idanunshi dasuka rine yayi yana sauke numfashi mai nauyi har kana iya ganin yadda qirjinshi ke sama da kasa tacikin rigar shi.
Jiyake inama zai iya kuka kamar yadda yaga saudart nayi yasan ko babu komai zaiji dan sauqi sauqi a zuciyarshi.
Yasan yanzu beda wani chance kuma, maimakon ya gyara abubuwa gashi ya ida lalatasu.
"Nace what did you do to her?" Inji sadeeq yana matsowa gabanshi.
Juyamashi baya Ashraf yayi tareda dafa desk dinshi da hannu biyu Yanajin kamar ya dauke sadeeq da mari don da yasan yadda yakeji da bazaima fara tanka mashi ba.
Abin ne yaba sadeeq haushi ganin magana yake mashi amma yawani juyamashi baya, hakan yasashi juyoshi da qarfi yana cewa
"Am talking you junk!"
Be qarasa maganar ba yaji an shaqeshi, kafin yasan meke faruwa harya mannashi da bango still shaqe da wuyanshi sai huci yake.
Waro idanu sadeeq yayi yana kallonshi not believing what is happening sai qoqarin kwatar kanshi yake amma yakasa.
Haryanzu qirjinshi sama da qasa yake sai motsa bakinshi yake amma wani Abu daya toshe mashi maqoshi yaqi barin maganar tafito.
"She is.. My.. Wife" yafada da daddaya kamar mai cutar asthma
Kusantoshi yayi har yana kusan hade fuskarsu
"So... Fuck off" yafada yana sakinshi sannan yaja dabaya yana dafe gefen qirjinshi daya dayake ji kamar ana hura mashi wuta awajen sannan yajuya yafita cikin sassarfa.
Sulalewa sadeeq yayi yana zama qasa yana murza wuyanshi don ba qarya ya shaqu, sai jujjuya wuyanshi yake don jinshi yake kamar ba nashi ba.
************************************************
Kasa gane kan saudart daddy yayi don tunda suka fito take kuka kamar ranta zai fita duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.
Dakyar yasamu suka isa motarsu yabude bangaren mai zaman banza ya turata ta zauna sannan yarufe shima cikin sauri ya zagayo yashiga mazaunin driver ya rufo ya tada motar yayi reverse suka fita daga company din gabadaya.
Akan hanyar ma bata bar kukanba muryarta harya fara shaqewa, baqincikin da take ciki bazai ta6a misaltuwa ba, bakinta sai zugi yake don ba qarya yasha tsotsa, duk zugi daya dazaiyi saiya tunamata da abinda yafaru, saiya tunamata she just kissed her worst enemy hakan ba qaramin tsimata yakeba hakan yasa takasa tsaida kukanta duk rarrashi da magiyar da daddy ke mata.
Daddy kau abin ba qaramin kulle mashi kai yayi ba, me Ashraf ya fadawa shalele daya rikitata har haka?
Shidai normal ya taddasu bare yayi zargin wani abun.
Kukanta ba qaramin rikitashi yakeba hakan yasashi qara speed ya nufi gidan shi direct.
Hannu dafe da qirji yafito yana tsoma qafarshi duk inda yaga dama harya samu yafito.
Motarshi ta nufa direct ya bude ya fada ciki ya rufo da qarfi ya maida kanshi kan seat din yana numfashi ahankali still hannunshi dafe da gefen zuciya.
Ya Dade ahakan, saida yafara jin sauqin abinda yakeji sannan ya miqe zaune ya kunna motar shima yabata wuta ya fice daga company din cikin wani mugun speed Wanda saida duk aka bishi da kallo.
Tuqi kawai yake amma badan kariyar Allah ba da komai na iya faruwa don tuqin ganganci yake sosai, zagi kau yashashi wajen mutane amma a banza don besan suna yiba.
Ahakan ya qarasa gida yayi wani irin parking a tsakar hanya ya sauko ya nufi cikin gidan yana hada hanya.
A falo ya zube qasa yana wani irin haki kamar zai mutu, hannunshi dafe da zuciya sai ambaton sunan Allah yake ko zaiji sauqin abinda ke damunshi
Abu daya yasani, son saudart jarabta ce daga Allah kuma wataqila cutar Sonta zaiyi ajalinshi don dukda halin dayake ciki, soyyayarta qara farashi take a zuciyarshi, wutar soyyayarta qara ruruwa take a zuciyarshi.
A bangaren saudart kau suna yin parking a parking space din gidan ta 6alle murfin motar tafito tayi cikin gidan dagudu.
Saurin kashe motar Alhaji shamsu yayi shima yafito ya maramata baya yana qwalamata kira.
Ina? Ko sauraronshi batayi ba ta haye sama ta bude dakinta tashige sannan ta maido kofar ta rufe harda saka sakata sannan ta sulale wajen ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana cigaba da kukanta cikin shaqaqqiyar muryarta.
Duk bugun kofa da magiyar da daddy yake mata akan ya bude besata ta motsa daga inda take ba, kukanta kawai take yayinda kanta ke saramata kamar zai rabe gida biyu.
Dakyar ya iya tashi daga inda ya jibge tundazu, hannunshi still a wuyanshi yana murzawa.
Tunda yake be ta6a ganin Ashraf acikin irin wannan yanayin ba, duk karfinshi kasa qwatar kanshi yayi Wanda yasan da zai kara minti daya be sakeshi ba da tuni ya margaya.
Nufar qofa yayi ahankali still yana jujjuya wuyanshi dayake jin dole yaje ganin mai gyara don Yanajin akwai qashin daya goce😆
Fita yayi shima yanufi motarshi dafeda wuya sannan yashiga ya tada motar yanufi gidan Ashraf don yasan yadda yafita cikin wannan yanayin dole asamu matsala.
Direct gidan yanufa, tun a yanayin parking din Ashraf yasashi tabbatar da hasashenshi.
Saurin kashe motar yayi ya sauko sannan yanufi ciki dagudu.
Afalo ya taddashi zube bisa rug din tsakiyar falon.
Dasauri ya nufeshi tareda dagoshi.
"Ya sallam" yafada jin jikin Ashraf rau kamar garwashi.
Ahankali ya taimaka mashi ya kwantar dashi akan three seater din falon sannan ya tsuggunna gabanshi
"Ashraf? Ashraf are you ok?" Yafada cikin tsananin damuwa
Dakyar Ashraf ya bude idanunshi wadanda sukayi nauyi ya kalleshi.
"Sorry ok? Zan kira doctor yanzu ok?" Yafada yana murza hannunshi daya
Ahankali Ashraf ya motsa bakinshi alamun zaiyi magana, hakan yasa sadeeq saurin matsowa saitin bakinshi
"She.. Hates me" yafada cikin wata iriyar murya
Wani mugun tausayinshi sadeeq yaji ya lullubeshi
"Shhhh it ok, bata tsanekaba kaji?" Yafada cikin sigar lallashi
"She do... Ta tsaneni" yafada yana lumshe idanu
"Shhh it ok, karka sake magana ok? Bari nakira Dr"
Nan yafiddo wayarshi yakira doctor din.
Cikin dan qanqanin lokaci Dr din ya qaraso, nan yashiga duba Ashraf sadeeq na gefenshi yana kallon amininshi cikin tausayawa.
Saida yagama dubashi sannan ya umarci sadeeq yakamashi sukaishi daki.
Haka suka kamashi su biyu suka kaishi daki suka kwantar dashi sannan aka daura mashi drip akayi mashi allurar barci sannan Dr ya rubuta ma sadeeq wasu magunguna yabashi akan su za'a bashi idan ya farka.
Kiran messenger sadeeq yayi ya bashi umarnin yasiyo magugunan dazaimashi text yanzu yakawo gidan A.A
Sannan yayi mishi txt din sunayen magungunan yakoma ya zauna gefen Ashraf daketa barci yana sauke numfashi ahankali ya kama hannunshi guda yana murzawa cikin tsananin tausayinshi...✍️
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
😆😆😆 gaskiya jiya kun bani dariya musanmman yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP.
Team S.S duk kurin da cika bakin? Yada saurin karaya haka?
Gaskiya bakuyiwa S.S adalci ba da kuke hijira kuna komawa A.A, tace agayamaku tana tsananin fushi daku😡 kuma zaku gane shayi ruwane biredi soso ne😠
059
Kiraye kirayen sallar azahar yasata dago kanta daga gwiwarta a inda take zaune bakin kofa tunda tashigo.
Ta Dade da barin kukan saidai na zuci datake.
Jiki ba kwari tamiqe tana dafa bango ciwon kanta na tsananta.
Da bin bango ta isa toilet ta daura alwala sannan tafito tana takowa ahankali.
Shimfida sallayarta tayi ta gabatarda sallar zuhr dinta sannan takoma ta zauna ta jingina da jikin gadon ta tareda lumshe idanu.
Abubuwan dasuka faru yau tun daga zuwansu company har yanzu yashiga dawomata a kwanya.
Wani murmushin takaici ya su6uce mata
Lallai saita gwadawa A.A ba kowa ake takawa kuma ya takuba.
Yayi kadan yayi controlling din life dinta, dolene yasake ta koda kuwa sai an hada da shari'a.
Bazata iya da irinshi ba, bazatama iya misalta hakan ba ko da wasa.
She hate him with passion don haka maganar zaman aure dashi ma bai tasoba kwata kwata.
Bubbugar kofar dataji ya katse mata guntun tunaninta.
Kallon saitin kofar tayi batareda tace komaiba
"Shalele?" Taji muryar daddy a tausashe
"Please open the door for daddy, ki bude kinji yar leleta?"
Shiru tayi kawai tana kallon kofar tanajin kanta cikin wani yanayi
"Kinga lokacin sallah yayi, please ki bude, ina cikin damuwa sosai, do you want daddy to be sad?" Yafada cikin sigar lallashi.
Girgiza mashi kai tayi kamar yana ganinta sannan ta yuqura ta tashi dakyar ta nufo kofar.
Jin motsinta kusada kofar yasashi dakatawa da rarrashi dayake mata yana kallon kofar.
Murda handle din yaji anyi sannan aka bude kofar saudart ta bayyana fuskarnan fayau.
Saurin shiga yayi yana rungumeta Itakuma kamar abinda take jira kenan saita fashe da kuka dakusashiyar muryarta.
Bubbuga mata baya yafara yi cikin sigar rarrashi yana cewa
"Shhhh ya isa hakanan, please stop crying kar wani ciwon yakamaki" yafada yana nufar gadonta daita sannan ya zaunar daita ahankali Itakuma ta Dora kanta a kafadarshi tana sauke ajiyar zuciya akai akai
"Am so sorry shalele, duk nine silar komai" yafada asanyaye
Girgiza mashi kai kawai ta iyayi hawaye na gangaro mata.
"Kiyi hqr ki fada min me yayi miki, please" yafada yana shafar kanta
Shiru saudart tayi tana sauke ajiyar zuciya ahankali, tasan ko giyan wake tasha bazata ta6a fadamashi abinda ya faruba.
"Kinji shalele ta, tell me please"
"Dad cewa yayi bazai sakeniba, wai babu hujjar yin haka, Dad I hate him, ko ganinshi banason yi" ta qarashe maganar tana matsar qwalla.
"It ok kinji? Babu Wanda zai tilasta miki zama dashi, abaya na tilasta miki yin hakan saboda son kai irin nawa amma yanzu hakan bazai ta6a maimata kanshi ba kinji? Kuma munada kwakwarar hujja na warware auren nan ko agaban kuliya ne, so relax, aurenan kamar anyi angama ne kinji?"
Qanqame shi tayi cikin farinciki tana kada kai cikin farinciki.
Haka yaita tausarta da kalamai har zuciyarta ta ida yin sanyi sannan ya tilasta mata tadanci abinci yabata magani tasha sannan yasata ta kwanta yajamata bargo tayi pecking dinta a goshi sannan yafita yabar dakin yana jawomata kofa.
A bangaren Ashraf kau bashi ya farkaba sai bayan la'asar.
Ahankali yafara bude idanu, tun yana gani Dishi Dishi har ganinshi ya washe idanunshi suka sauka a fuskar sadeeq dake zauna gabanshi.
Ganin ya bude idanu yasa sadeeq saurin gyara zaman shi yana mashi sannu murmushi a fuskarshi.
Yunqurin tashi yayi yana yatsina fuska, dasauri sadeeq ya taimaka mashi ya zauna yasamashi pillow a bayanshi don samun comfort.
"Sannu, ya jikin? Ina kema ciwo?" Inji sadeeq
Girgiza mashi kai kawai yayi Alamun babu tareda lumshe idanu
"Ok Bari na hadoma ko tea ne kasha sai kasha magungunan ka" yafada yana fita batareda yajira amsarshi ba.
Binshi da kallo yayi harya fita sannan ta sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Kallon hannunshi yayi yaganshi da cannula da alamun saida aka qaramashi ruwa.
Hannu yasa ya shafo kanshi yana furzar da huci
Abinda yafaru dazu yafado mashi arai.
Tunawa yayi da yadda yake sarrafa tausassan la66anta masu kamada auduga da wani scent din da bakin ke fiddawa na mint.
Murmushin gefen baki yayi yana cizon le6en qasa in a naughty way.
Tunawa yayi da lokacin daya cire bakinshi daga nata, irin kallon datake mashi, kallo mai cikeda shock da giggita.
Fararen idanunta data ware akanshi da guntun bakinta da yadan bude in shock.
Wani murmushin yasaki yanzu mai sauti yana daukar filon kusada shi tareda rungume shi aqirji
Kissing her feel soo good, damn good.
Tunawa yayi da yadda ta qanqame jikinta tanata rusa ihu, yar dariya yasaki yana cewa "matsoraciya"
Haka yaita zabga murmushi shi kadai kamar wani shabiyu sha uku har sadeeq yashigo besaniba.
"Inyee! Wannan washe haqoran duka menene?" Inji sadeeq cikin sigar tsokana
Dagowa yayi yana kallonshi tareda zabga mashi harara still fuskarshi dauke da murmushi.
Qarasowa yayi da tray din tea din tareda direwa a bedside locker ya zauna kusada shi yana cewa
"Wato ni inacan ina faman hada maka tea harda qonewa amma kai kananan kana dariya kai kadai ko? Tell me what's funny" yafada Yanajin dadin yanayin daya ganshi
"Am..in..love" yafada kamar mai koyon magana yana qara rungumar pillon
Waro idanu sadeeq yayi cikin mammaki, dukda yaga alamun son saudart a idanunshi be ta6a tunanin zai furta dawuri hakaba
Tsalle yayi yadawo kusada shi kan gadon
"Maimata inqaraji dan uwa, kamar ban fahimci zancenkaba" yafada cikin sigar waqar sambisa.
Murmushi Ashraf yasaki mai tsadan gaske yana dan mintsinin sadeeq Wanda har saida yadan saki qara.
"Yes am in love......I love her" yafada cikin shauqi
"Wayyo dadi kasheni! Dunkum din abokina is in love! Yeah! Oya Jo soapy soapy, tashi muyi rawar soapy, tashi muyi rawar soapy, soapy soapy!" Yafada yana miqewa Yana rawar soapy din.
Wurga mashi pillow Ashraf yayi yana dariya sosai
"Kai dan iska ne ko?" Yafada yanada dariya
"Yan iska ba, inyee gaskiya saudart ta ciri tuta, wannan washe baki haka? Rabon da naga kana irin wannan dariyar har mantuwarma ta mance"
Dariya Ashraf yasakeyi yana girgiza Kai
"Kaifa dan iska ne"
"Na yarda, wato shiyasa dazu aka kusan sheqeni ko? Haryanzu wuyana ciwo yake na rantse"
Dariya Ashraf yayi mashi yana cewa
"Maganin mai shiga sabgar mata da mijinta kenan"
Bude baki yayi yana toshe wa
"Inyee ni kake fadawa haka? Lallai Bari na koma gefe naita kuka"
Dariya Ashraf yayi kawai sannan yadan girgiza Kai yanayinshi na chanza wa
"Meye kuma?"
"Ta tsaneni" yafada cikin wani yanayi
"A'a bata tsaneka ba"
"Ta tsaneni kaima kasani"
"Amma ai kai k koyamata tsanar ka din, why not ka koyamata sonka?"
"How?"
"By showing her love tsantsa"
Girgiza Kai yayi
"Banjin zata saurareni"
"Zata saurareka mana, kawai all you need to do is ka sauke wannan shegen girman kan naka dabeda amfani ka yaqo zuciyarta"
Dariya Ashraf yayi yana shafa gemunshi
"Nikuma banason abinda zai ta6a Mani jin kai na, yaya za'ayi kenan?"
Harararshi sadeeq yayi sannan yace
"To saika cika form din wahala don kai dashi kun qulla abota kenan"
Dariya kawai yayi bece komai ba
"Yanzu sha tea din kasha magungunan"
Babu musu yaziro kaffafun kasa ya amshi tea din yana sha ahankali
"Ummy fa? Yakamata ta sani" inji sadeeq
Dagowa Ashraf yayi daga kofin bakinshi yana kallonshi
"No"
"No? Sokake taji abakin wasu?" Inji sadeeq
"Fushi zatayi kasan halinta, insha Allah ni dakaina zan gayamata amma sai komai ya lafa"
"Komai ya lafa kamar ya?"
"Sai saudart tadawo gareni"
"Amma baka gudun taji waje?"
"Wazai gayamata? Saudart bazata gayamata ba I know, tsohon ta ma bazai faraba, nima bazan fadaba saidai ko kai zaka fadi"
"Hmm to Allah ya kyauta, ga magungunan kasha ka rama sallolinka insamu inkoma gida."
Saida yasha magungunan shi sannan ya rama sallolinshi sannan yadawo ya zauna suka dan ta6a fira sannan sadeeq yatafi bayan yagama quleshi da tsokana.
Dawowa yayi ya zauna kan daya daga cikin kujerun falon yana kishingidawa murmushi kwance a fuskarshi.
*I love you*
*I love you so much... SAUDART*...✍️
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
060
Ranar zaune yakusan kwana, sai saqa da warwara yake na yadda zai 6ullowa saudart, wani abun har mammaki yake bashi don ko a mafarki be ta6a tunanin zai ware wani kaso cikin lokutanshi masu amfani ya asarar dasu akan tunanin mace ba amma gashi har hana idanunshi barci yake don tunanin yadda zai 6ullomata.
Washegari sai 11:00am yafarka saboda Rashin samun isashen barcin dabeyiba jiya Wanda saida yayi sallar asuba sannan barcin ya daukeshi.
A gaggauce ya fada toilet don yin wanka da brush.
Fitowa yayi bayan wasu yan mintuna ya shirya cikin wasu ash colour suit ya feshe Jikinshi da turare.
Fitowa yayi yana gyara necktie dinshi yanufi motarshi.
Shiga yayi ya tadata sannan yafice daga gidan.
Opposite din bakery dinta ya parka motarshi yana kallon mutanen daketa karakaina a wajen.
Ya Dade cikin motar yana kallon wajen batareda yasan me ya kamata yayi ba.
Can yaga wani yafito daga bakery din da alamun daya daga cikin ma'aikatan ne.
Saurin bude kofar yayi ya fito ya tsaya gefen motarshi yana kallon mutumin dake qoqarin ketaro titin zuwa bangaren da Ashraf yake.
Saida ya qetaro yana niyyar wucewa Ashraf yayi saurin dakatar dashi.
"Ehmm barka" inji Ashraf yana dakatar dashi
Juyowa mutumin yayi yana kallonshi da alamun Rashin ganeshi sannan yace
"Barka dai"
Hannu Ashraf yabashi sukayi musabaha sannan yace
"Erm madam nanan kuwa? I mean saudart"
Girgiza Kai mutumin yayi yana cewa
"A'a rabonta da Bakery dinnan tun Friday, lfy?"
Murmushi Ashraf ya sakarmashi
"No lfy lau, dama aikoni akayi wajenta ne, amma idan babu damuwa kozan samu number ta?"
Kallon Rashin yarda mutumin yashiga binshi dashi Wanda yasa Ashraf jin duk ya tsargu da kanshi.
"A'a banida numberta, idan order kukeso ko wani abun kana iya shiga ciki kasamu P.A dinta amma babu mai number ta" yana kaiwa nan yawuce yana waiwayenshi don hakanan yaji be kwanta mashi ba.
Shima Ashraf binshi yayi da kallo harya wuce sannan yasa hannu ya shafi kanshi yana hurar da iska.
"This is gonna be tough" yafada yana saka hannayenshi a aljihu yana qara kallon bakery din.
Ganin tsayuwar batada amfani yasashi shiga mota yabata wuta yabar wajen.
Direct company dinshi yawuce, anan yayi assigning din wani daga cikin guards dinshi kan ya cigaba da saka idanu a bakery dinta duk sanda yaganta yayi alerting dinshi.
Yakuma yi assigning din wani a unguwarsu akan yasaka idanu a gidansu saudart duk sadda yaga fitowarta yayi alerting dinshi.
Komawa yayi jikin kujera yana jujjuyawa ahankali yana jinshi empty, Yanajin kamar yarasa wani 6ari nashi mai matuqar muhinmmanci.
Ranar babu wani aikin dayayi bayaga tunaninta, abin har tsoro yake bashi don gani yake kamar qaramashi Sonta ake akowace daqiqa mai wucewa.
Wasa wasa kwana uku kenan da assigning din masu saka ido akan saudart amma babu wani labari mai dadi.
Kullum amsarsu daya ce, basuga fitowarta ba.
Ashraf yashiga cikin tsananin damuwa, damuwarshi dayace anya lafiyarta qalau kuwa? Idan yayi la'akari da yadda suka rabu a haduwarsu na qarshe sai yaga kamar ba lafiya.
Duk yabi ya susuce, kodayaushe wayace a hannunshi yana jiran akirashi ace anga fitowarta amma shiru, idan kuma yagaji shi yabuga amsar duk dayace, babu ita.
Duk wannan budirin da'ake sadeeq na gefe ya zuba mashi idanu, don shi abun ya daina bashi mammaki yanzu saima takaici.
Yaya za'ayi ace kana tsananin son ganin mutum kuma kasan inda yake amma ka kasa zuwa ganinshi saboda wani dalili naka na banza?
Hakan yasashi bude kwandon shara ya sakashi ciki ya rufe ya cigaba da harkar gabanshi acewarshi idan kaji ana rakani kashi to ba zawo bane.
Yau Saturday babu aiki don haka yau gidansu ya wuni yana hutawa.
Kwance yake yana waya murya qasa qasa da alamu da masoyiyarshi yake wayar.
Da sallama Ashraf yashigo looking so pale, kallo daya zakayi mashi kasan yana cikin damuwa don duk yazama wani iri, gashi nan dai.
Dagowa sadeeq yayi ya amsa sallamar sannan ya cigaba da amsa kiranshi hankali kwance.
Samun kujerar dake dakin Ashraf yayi ya zauna ya jingina da kujerar yana dafe kanshi dake dan Sara mashi.
Sadeeq na ankare dashi amma ya share yacigaba da wayarshi batareda ya kulashi ba, shima Ashraf bece komai ba sai lumshe idanun dayayi hannu dafe dakai yana sauraron wayar sadeeq.
Ada idan yaganshi yana waya irin haka has yake bashi yana yi mashi kallon marar aikin yi amma yanzu jiyake dama shine ke wayar da muradin ranshi, abar kaunarshi, Saudart.
Haka yaita jiranshi harya gama wayar batareda ya katseshi ba ko yanuna 6acin ranshi akan shareshin dayayi hasalima kalaman sadeeq din yake sauraro yana mammakin ina ya iya wadannan kalamai haka.
Dagowa sadeeq yayi yana kallonshi sannan yadan ta6e baki
"Ya dai? Naga you look pale"
Bude lumsassun idanunshi yayi ya kalleshi sannan ya maidasu ya rufe batareda ya tanka mashi ba.
"Mtcheew dan wahala kawai" inji sadeeq yana daukar remote zai kunna kallo
Bude idanunshi yasakeyi ya kalleshi sannan cikin sanyi yace
"Please banson hayaniya karka kunna"
Wani kallon uku saura kwata sadeeq yayi mashi sannan yace
"Dalili? Dakinka ko nawa? Kaji qarfin hali"
Sauke ajiyar zuciya Ashraf yayi yana dan rolling din idanu
"Sadeeq dama haka kake? Dama kai maqiyina ne bansaniba? Ni atunanina idan ina cikin damuwa saika fini shiga damuwar amma am mistaken"
Sadeeq da tunda yafara magana yake antayamashi harara yaja tsaki yace
"To ni me zan maka? Ashraf taurin kanka yasa nafara tantamar da irin qashin da'akayi namu kan akayi naka, kana wahala zuciyarka na wahala amma kasan yadda zaka kawo qarshen wahalar ka kasa, saboda wani banzan dalili naka can" yafada cikin jin haushi
"But am trying ko? Duk hanyar danasan zan ganta inabi kaima kasani" yafada kamar zaiyi kuka
"Nidai tawa ta sameni, dafarko ina zaman zamana hankali kwance banida damuwar komai amma tunda tashigo rayuwata ta sauya komai, gashi yanzu ta tafi tabarni da jinya gashi kai da nake tunanin zan dan samu sauqi a wajen ka kaima ka juyamin baya" yaqarashe zancen yana dafe Kai.
"Mtcheew kai ka siya ai, muddin bazaka sauke girman Kai ba bakaga komai bama, ita saudart din allurace da zata bace bakasan inda zaka ganota ba? Kasan inda zakaje ka ganta kawai baka shirya ganinta bane" yafada yana maida hankalinshi kan kallon dazai kunna
"I can't, bazan iya taka gidan mutumin nanba, zan iya zuwa koma inane inganta amma banda wannan gidan" inji Ashraf yana dan huci.
"Why? Ai ba wajen shi zakajeba, wajen Matar ka kaje, ni banga wani Abu aciki ba"
"Ni nagani, the first and worst mistake dina shine sanyota acikin deal dina, da bansata aciki ba da ko saninta banyiba bare har wannan masifar ta hayeni" inji Ashraf yana cije le6an qasa.
"Yes Ashraf, Allah ne ke nuna mana kurenmu, yakuma nuna mana aure ba abin wasa bane, dukda rama sharri da sharri ba haramun bane anfison a ramashi da alhairi, amma mu saimuka nemi ramawa fiyeda yadda akayi mana, muka kuma saka Wanda bata jiba bata ganiba kuma muka dauki abu mai martaba irin aure muka maidashi wasa shiyasa muka rufta aciki" inji sadeeq shima cikin sanyi.
"And you warned me, ka gargadeni akan hakan amma ni idanuna sun rufe fansa kawai nakeson dauka gashi yanzu muntashi ba wan ba qanin saima masifar danake ciki, wlh danasan yadda zan cire Sonta a zuciyata danayi hakan ko na huta, kullum kamar qaramani Sonta akeyi, with every passing minute, second, breath jinake kamar qara huramani wutar Sonta ake, am helpless, bansan yaya zan tunkareta ba, bansan Kalmar dazan yi amfani dashiba, bansan komai ba, all I know is I love her, I so much love her" yafada cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
Cikin tausayawa sadeeq ya dawo kusada shi ya zauna tareda dafa kafadarshi
"It ok bro, insha Allah komai zaizo da sauki, ka riqe addu'a kuma kaima kayi trying best dinka, ka ajiye komai kayi fighting for your love, insha Allah saudart alhairi ce a rayuwarka shiyasa tun farko ka sakota aciki, insha Allah zakayi dariya watarana.."
Ringing din wayar Ashraf ce ta katsesu.
Saurin saka hannu yayi ya fiddo wayar jin ringing tone din Ummy ne Wanda contact dinta kadai yasama tone din.
Janye hannunshi sadeeq yayi daga kafadarshi yana kallonshi yayinda shikuma ya daga ya kara a kunne yana sallama.
Ganin yanayin fuskarshi na chanzawa yasa sadeeq kuramashi idanu da alamun tambaya
"Ummy.. Lafiya?" Inji Ashraf cikin Rashin fahimta.
Bansan ko me ummin tace ba sai gani nayi wayar takawo haske alamun an katseta.
Ahankali ya sauke wayar daga kunnenshi fuskarshi dauke da ayar tambaya.
"Lafiya?" Inji sadeeq daketa kallonshi tundazu
"Ummy ke Neman mu" Ashraf ya amsa absentmindedly tunani kala kala na yawo a qwanyar shi.
"Meyasa?" Inji sadeeq
Miqewa Ashraf yayi
"Muje amma she don't sound normal".
Shima miqewan yayi ya Dora t-shirt akan singlet dinshi yasaka takalmi suka fita.
Sallama sukayima umman sadeeq dake falo akan zasu dan fita su dawo sannan suka fice da motar Ashraf.
A harabar gidansu Ashraf sukayi parking suka fito.
" sadeeq wani Abu na faruwa, inaji a raina something bad is happening" inji Ashraf yana kallon hanyar cikin gidan
"Babu komai insha Allah, mushiga nasan babu komai sai alhairi" inji sadeeq cikin qarfafa mashi gwiwa.
Haka suka jero kamar yadda suka saba sadeeq ya Danna door bell sukayi jigum suna kallon kofar.
Bayan yan daqiqu sai gani sukayi an murda kofar an bude.
Baby ce ta bayyana fuskarta adagule alamun something is happening.
Saurin qaqalo murmushi tayi tana kaucemasu tana gaishesu.
Yau babu Wanda yasamu halin amsawa saboda fargaba don haka shiga sukayi atare suna sallama.
A falo suka hango Ummy zaune kan one seater fuskarnan babu fara'a tadago tana amsa sallamarsu tana masu wani irin kallon daya kada hanjin cikinsu.
A sanyaye suka qaraso suka zauna qasan tsadadden rug din dake tsakiyar falon suka sunkuya kai.
Itama baby dawowa ciki tayi ta zauna kan kujerar dake nesa dasu ta zauna tana kallonsu
Tare suka gaidata cikin sanyi kallo daya zakayi musu kasan suna cikin fargaba sosai.
Kallo tashiga binsu dashi batareda ta amsaba hakan yasasu sunkuyar dakai kasa
"Ina matarka?" Ummy ta jefo masu tambayar a bazata.
Hakan yasa duk suka dago kai gabadaya suka kalleta sai kuma suka kalli juna.
Maida kallonsu suka sakeyi kanta sannan Ashraf cikin inda inda yace
"Ni?"
Batace komai ba sai tsareshi da idanu datayi Wanda hakan ba qaramin sanyaya mashi jiki yayiba.
Sunkuyar dakai yayi sannan ya bude baki yace
"Tana gida"
"Ka kirata tazo yanzu" tafada commandly
Dagowa yayi yasake kallonta yanason karantar yanayinta
"Ummy.. Wayarta a kashe.. Take"
Dan murmushi Ummy tasaki mai kamada na takaici sannan ta kalli baby tace
"Kirata"
Jiki a sanyaye baby ta Ciro wayarta ta kira number saudart sai gashi tashiga suna kuma ji saboda hands free tasata.
Har tayi ringing dinta tagama ba'a dagaba.
Maido kallonta Ummy tayi kansu sukayi saurin sunkuyar dakai.
"Ina matarka Ashraf!"
Gamm ya runtse idanunshi tashin hankali qarara a fuskarshi.
Tunda yake Ummy bata taba kiranshi da sunanshi ba sai yau.
Nan take zuciyarshi tafara bugawa abnormally gumi na tsatsafo mashi.
"Nace where is your wife!!" Ummy ta daka mashi uban tsawar da bata ta6a yi musu ba.
Nan take baby tafashe da kuka tana toshe bakinta shikuma Ashraf yadago yana kallon Ummy idanunshi sunyi jajur.
"Ummy.."
"Shut up!" Ta katse sadeeq din a tsawace
"Kabari nadawo kanka tukun" tafada a fadace
"Now answer me, ina matarka?" Ta maida akalar tambayar kan Ashraf.
Bakinshi yabude zaiyi magana amma yakasa sai 6ari da bakin keyi.
Be Ankara ba yaji an wurga mashi takardu a fuska sun watse a gabanshi
"What is this?! Nace meye wannan!" Ta tambaya a tsawace
Bin takardun yayi da kallo nan take Jikinshi yadauki rawa...✍️
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Aslm fans🙋🏻♀️ sorry kunjini shiru kwana biyu, wayatace tasamu mtsl😟 amma yanzu komai yayi daidai.
Masu cigiya, masu kira da masu text duk nagode da qauna😍😇
Allah yabar zumunci🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
Bin takardun yayi da kallo nan take jikinshi yadauki rawa.
Shima sadeeq takardun yake kallo fuskarshi fall mammaki zuciyarshi na bugawa.
"Nace meye wannan!!" Suka sakejin muryarta tsakar kansu.
Kasa dagowa Ashraf yayi daga kallon takardun sai binsu yake da kallo kamar yau yafara ganinsu.
"Ummy... we can explain.." inji sadeeq cikin kwantar da murya
"Explain? Kenan wannan gaskiya ne?" Tafada cikin sanyin murya tana kallonsu most especially Ashraf daya kasa dagowa, idanunshi sun kada sosai
"Yes ummy...amma.."
"Ya sallam!" Inji ummy tana komawa dabaya ta zauna akan kujera jagwab tana dafa kai, tashin hankali qarara a fuskarta.
Da sauri Ashraf ya rarrafa gabanta yana kamo hannunta data dafe kanta dashi
"Ummy?.. ummy am sorry, am so sorry"
"Sakarmin hannu" tafada cikin sanyin murya.
Qara qanqame hannun yayi yana cewa
"No ummy, Dan allah kiyi haquri ummy, please" yafada muryarshi na rawa rawa, jiyake kamar yafashe da kuka ko zai samu sauqi.
Idan akwai abinda ya tsana duniyarnan to 6acin ran ummy ne, kullum cikin taka tsantsan yake wajen ganin ya faranta mata rai amma yau tashin hankali da 6acin ran dayake hangowa a idanunta yasashi jin kanshi so guilty.
Baby kau na gefe tana sheshekar kukan dataci, bata ta6a ganin ummy da yaya a wannan yanayin ba, hakan yasata jin wani iri ga baqin labarin da hankalinta yakasa dauka daya riskesu.
Shima sadeeq rarrafowa yayi kusada ashraf cikin sanyin jiki.
"Ummy munyi kuskure amma Dan allah ki sauraremu, please" yafada shima kamar zaiyi kuka.
"Let go of my hand" ummy tasake cewa in a cool mode wanda hakan yaqara tada hankalin Ashraf
"Ummy.."
Fizge hannunta tayi a fusace daga riqonshi sannan ta miqe tsaye tana nuna masu kofa da yatsa.
Tashi baby tayi tayi sama dagudu tana toshe bakinta cikin qoqarin hana kukan daya kufto mata fitowa.
"Out!!" Tafada a tsawace.
Kasa ko motsawa Ashraf yayi daga kneeling position dinshi, jikinshi yayi liqis jiyake kamar babu sauran lakka ajikinshi.
"Nace kufita and never come back again! Get out!" Tafada cikin qaraji.
Hakan yasa sadeeq saurin tashi don yasan halin ummy idan ranta ya 6aci, dawuya kaga 6acin ranta amma idan ranta ya6aci batada kyau.
Kamo ashraf dake durqushe haryanzu yayi dakyar suka miqe.
Dago kai ashraf yayi ya kalleta da idanunshi dasuka yi jaa, siraren jijiyoyi jajjaye duk sunfito akan farin idanun.
"Ummy am.."
Daga mashi hannu tayi sannan ta nunamashi kofa.
Babu musu suka juya su biyun kowanne kamar zakaran da aka tsoma cikin ruwan zafi suka fita.
Komawa ummy tayi ta zauna tana dafe kai zuciyarta a jagule.
Cikin mutuwar jiki kowannensu ya kama murfin motar yabude yashiga.
Tada motar sadeeq yayi sannan yabata wuta suka fita daga gidan.
Tafiya suke amma babu mai cewa uffan kuma babu mai niyyar maganar, kowanne da tunanin daya addabi ruhinshi.
Ahaka suka isa gidan Ashraf din, ko gama daidaita parking din beyiba Ashraf ya 6alle murfin motar yafita.
Binshi da kallo sadeeq yayi sannan ya ida gyara parking din shima yafito.
A falo ta taddashi kwance bisa kujera two seater, kanshi akan hannun kujera daya kaffafuwanshi akan daya sun sauko qasa, hannu daya dafe da kai yayinda idanunshi ke a lumshe.
Dauke kai sadeeq yayi yawuce dining area, yabude fridge din wajen taciro gorar ruwa da cups yadawo cikin falon.
Zama yayi kan kujerar dake gefen ashraf sannan ya tsiyaya ruwan a cup sannan yayi tapping din kafadar ashraf.
Bude idanunshi yayi dakyar ya dago ya kalleshi yaga ruwa yake miqomashi.
Maida idanun yayi ya rufe batareda yako motsaba.
"Kasha Ashraf, you'll feel better" inji sadeeq a tausashe.
Shiru yayi kamar bazai motsaba saikuma ya bude idanu ya miqe zaune ahankali ya miqa hannu ya amsa cup din ruwan ya kafa kai.
Saida yashanye sannan yasake miqama sadeeq ya amsa yasake cikawa yabashi ya amsa yaqara sha sannan ya ajiye cup din kan stool din gefen kujerarshi yakoma ya kwanta.
Ajiyar zuciya sadeeq ya sauke sannan yace
"Ashraf?"
Banza yayi dashi
"Ashraf katashi, we need to discuss this"
A kwancen dayake batareda ya bude idanuba yace
"Babu abun tattaunawa anan sadeeq"
"Ofcourse akwai, dole musan wa ya gayawa ummy wannan abun"
Murmushin gefen baki yayi wanda shikadai yasan yayi abinshi
"Ni dakai munsan wanda yafada, meye na wahalarda kanmu? Bansan har haka tadauki abinba, telling my mother without my consent?"
"Saudart? No bazata iyaba" inji sadeeq
Shiru ashraf yayi besake cewa komaiba
"Ashraf.."
"Dan allah kayi haquri ka kyaleni, please.. i need to be alone..please" yafada yana dafe kanshi.
Shiru sadeeq yayi yana kallonshi, yasan yadda yakeji kuma ya tausayamashi, komai sai juyemasu yake from normal to abnormal.
Yasan yadda suke da ummy, yasan dole abin yayi affecting dinshi sosai.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miqe yana cewa
"Ok, zanje gida amma please take it easy on yourself"
Bece komaiba kamar yadda be bude idanunshi ba.
Dafa kafadarshi yayi yana dan murzawa
"Be strong" yafada cikin qarfafa gwiwa sannan yajuya yafita.
Ahankali ya bude idanunshi bayan yaji fitarshi ya saukesu a p.o.p din falon
Yau ummy ke fushi dashi? Yau ya 6atawa ummy rai? Garin yaya be ta6a tunanin wadannan abubuwan zasu bayaba tinda farko? Yana iya jurar komai amma banda fushin ummy, bazai iya jurewaba samm.
********************************
Driving yake tunannuka kala kala na yawo akanshi.
Haryanzu yakasa yarda cewa Saudart zata iya gayawa ummy komaiba, yanaji ajikinshi ba ita bace.
Karya motarshi yayi awani round about ya dauki hanyar gidansu Saudart.
A opposite din gidan yayi parking sannan yafito yana kallon gidan.
Tsallakawa yayi yazo bakin gate din yafara bubbugawa.
Saida ya bubbuga sau hudu sannan yaji motsi daga ciki.
Tsayawa yayi yana kallon yadda karamar kofar gate din ke motsi alamun budewa akeyi sannan kofar ta bude fuskar maigadin ta bayyana wanda kallo daya zakamashi kasan buzune.
Murmushi sadeeq yayi yana miqamashi hannu yana mashi sallama.
Shima miqamashi hannun yayi yana amsawa yana mashi kallon rashin sani.
"Erm.. dan allah ko madam nanan? Saudart nake nufi"
"Eh yananan, lfy?" Inji buzun cikin gur6attacciyar hausanshi
Murmushi sadeeq yayi
"Eh lfy lau, dan allah kamin sallama daita, kace sadeeq ne, abokin mijinta"
Kara karemashi kallo buzun yayi sannan daga bisani yace
"To..to, amma ki tsaya nan bari na fadamashi, ki tsaya" saiya rufe kofar sannan yashige ciki don sanarda madam saudart.
Zaune take a falo kan one seater ta doro kaffafunta a kan kujerar tana filing din akaifunta na hannu, kanta dauke da earphones dinnan da ake dorawa akai tana sauraron cool music cikin low volume.
Kallo daya zaka mata kaga tadan fada, ga hasken data qara wanda hakan yaba fatarta damar fitowa sosai cikin blue black din roba gown din dake jikinta.
Sallamar maigadin dataji yasata dagowa daga abinda take.
Amsawa tayi cikin fara'a, duk kwakwarka baka iya gane damuwarta don allah yayita mai fara'a da yawan murmushi.
"A'a? Sannu mallam audu, kina lfy?" Tafada cikin sigar tsokana.
Washe baki yayi yace
"Wlh lfy lau hajiya, barka da hutawa"
"Barkanmu dai, wani abu kikeso?" Tasake tambayarshi cikin yanayin maganarshi fuskarta daukeda murmushi.
"A'a hajiya, kayi baqo ne"
Dan daga gira daya tayi
"Baqo? Waye?"
"Wai abokiyar maigidanki ne, wai saddiqu"
Dan ware idanunta tayi
"Sadeeq?"
"Eh"
"Shi dawa?" Ta tambaya still idanunta aware.
"Nidai ita kadai nagani"
Ajiyar zuciya ta sauke
"Yana ina yanzu?"
"Tana shan waje aradu, cewa nayi tajira in fadamaka"
"Ok..ok, kagane? Kaje kashigo dashi ganinan tafe"
"To angama" yafada yana fita don aiwatar da yadda tace.
"Sadeeq? Meya kawoshi?" Tambayar datayiwa kanta kenan.
Tashi tayi ta tattara tarkacenta ta haura sama tana cire earphones din kanta.
Doguwar hijabi kawai tazira ta zura takalmin soso sannan ta dauki wayarta tafito tana addu'ar allah yasa takardarta yakawo mata.
Tun daga nesa ta hangoshi zaune kan farar kujerar roba kusada parking space wata empty kujerar na facing dinshi.
Dauke kai tayi ganin shima ya dago yana kallonta ta qaraso wajenshi ta tsaya daga dan nesa dashi tana mashi sallama.
Cikin fara'a ya amsa yana cewa
"Sannu da fitowa *Mrs A.A*"
Jin sunan tayi wani banbarakwai amma saita basar tace
"Yauwa sannu"
Nunamata kujerar gabanshi yayi yana cewa
"Bismillah mana"
Itama kallon kujerar tayi kamar yanzu tasan daita sannan ta dauke kai tana cewa
"No need, hakanma am ok"
Miqewa shima yayi yana cewa "in that case nima bari na tashi yadda zamufi fuskantar juna"
Kauda kai tayi batareda tace komaiba
"Kin wuni lfy?" Yafada yana pocketing din hannunshi
"Lfy, yes? How may i help you?" Tafada tana kallonshi
Murmushi yadanyi yace
"Magana nazo muyi *Mrs A.A*"
Kallonshi tayi kafin tace
"Idan ban manceba, ba ta6a warning dinka akan dagantani da wannan sunan"
"Why? Ba sunanki bane? Ko ba matarshi bace"
Guntun tsaki taja
"Now get to the point, kazo da sign dinne ko da takardar?"
"Takarda? Tame?"
"Kafini sani" tafada tana kauda kai cikin son danne 6acin ranta
"Nazone don in tambayi dalilinki na aikawa ummy da takarda don nasan bake kikajeba dakanki"
Kallon rashin fahimta tayimashi.
"Takarda? What are you talking about?"
Ganin kamar bata ganeba yasashi cewa
"Kin gayawa ummy komai, dont you? Why zaki aikamata bayan kisan wannan is between us, mu kadai"
Tsayawa tayi tana kallonshi na yan sakanni sannan taja tsaki.
"Look, basan akan me kake magana ba, i thought kazo da takardata ne shiyasa kaga nafito tun farko.
Batun kaima ummy takarda ba aikina bane, why should I? Koda aika takardar zanyi to ta sammaci zan aiko maku ba kotu don am taking this issue down to court, it's better kaba abokin naka shawara akan mu warware komai a tsakaninmu salin alin ko kotu ta taimakamana wajen warwarewa"
"Court? Kinsan me hakan ke nufi? Zaku tonama kanku asirine a idanun duniya da kanku, kinsan abinda zai biyo baya? Kinsan abinda duniya zata fada akanku?" Yafada cikin ayar tambaya
"I dont care, as far as zan rabu da wannan mutumin duniyar ta dade bata fadi koma menene akaina ba" tafada in an I-don't-care manner
"Amma kinsan hakan zaiyi tarnishing din image dinku ko?"
"Yadaiyi tarninshing din image dinshi, am independent and not that famous, shifa? Kana ambatar A.A kowa saiya waigo don sunanshi, sunanshi zai 6ata a banza, zai shafama kanshi baqin fenti a bugamashi tambarin zalunci wanda bazai iya taimakon naqasa dashiba saiya nemi wani abu in exchange.
Court zata tuhumeshi da bribery, corruption and harrassment, labari zai yadu a duniya akuma wajen abokan huldarshi, zai samu karaya fiyeda tunaninka, now tell me waya kwan aciki?"
Ajiyar zuciya sadeeq yasauke sannan yace
"Saudart, why did you hate him that much? Allah nason bayinsa mai gafara, ki tuna koshi Allahn daya hallicemu muna mashi laifi mu nemi yafiyarsa yakuma yafemana" yafada cikin sanyin murya
"Shima Allahn dakace sai mun nemi yafiyarshi yake yafemaba, tell me.. is your friend sorry?"
"He is, na rantse, you need to see yadda yakoma, yayi nadama sosai kuma yana cikin damuwa plus ga ummy na fushi dashi, idan kin ganshi dole ki tausayamashi"
"Mtcheew, story for the gods, look ban damu da nadamarshi ko damuwarshi ba don banma yadda yayi din ba.
All I know is yabani takardata, tun farko shiya faro komai don haka he must end it.
Ka fadamashi nabashi daga nan zuwa monday ya aikomin da takardata idan ba hakaba, wlh kaji na rantse? Zan kai wannan issue din court, idan yanajin yafi qarfin kowa ai befi qarfin shara'a ba, daga yau zuwa monday inba hakaba yaga sammaci.... Have a wonderful day"
Tajuya tabarshi tsaye anan.
Binta yayi da kallo harta shige sannan yasa hannu yashafi kanshi cikin damuwa.
"Ya allah take control" yafada ahankali sannan yajuya yanufi hanyar fita jiki a sanyaye.
Da sauri ta haye sama tashige dakinta ta maido kofar ta rufe ta jingina daita tana numfashi mai nauyi
"Ummy? Ummy tasan komai?" Tambayar datayiwa kanta kenan.
Qarasawa gaban gadonta tayi tana cire qatuwar hijabinta tana fiffita da hannu saboda zafin dataji yana suromata takoina.
Tasan idan ummy taji dolene zata kira mamy ta tambaya.
Ya sallam! Bazata iya kiyasta tashin hankalin da mamy zata shigaba idan taji labari. Tasan she's doomed kawai.
"Ya allah kasa barazanar danayimasu yayi tasiri akansu, allah karabani da wannan bawa naka lfy" tafada tana kallon sama tareda daga hannayenta tafukanta abude.
"Allah kasa sai komai ya warware sannan mamy zataji, Allah mun tuba ka yafe mana" tashafa sannan ta dago kaffafunta saman gadon ta rungume tana dora kanta akan gwiyagunta, zuciyarta fall da fargaba...✍️
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
Jiya na mance banyi numbering din page ba, na jiya is page 61 yau kuma 62
062
Haka yadawo gidansu jikinshi a sa6ule, duk abunda ke faruwa beyi blaming din saudart ba, tanada gaskiya ta kowane fanni, Ashraf was so rude and cruel to her, yamata abubuwa kala kala wanda dolene ya fice mata akai, mance abubuwan dayayi mata ba abu bane mai sauqi ba.
Saida ya gabatar da sallar asr sannan yasake fitowa da niyyar sake leqa Ashraf, ahalin yanzu mugun tausayi yake bashi don abun duk ya hargitse mashi, tsawon lokacin dasuke tare be ta6a ganinshi acikin irin wannan yanayin ba.
Saida yabiya wani restaurant dake kan hanya yayimusu takeaway don yasan haryanzu beci komaiba sannan yawuce gidan.
Sa6anin dazu, yanzu a bedroom dinshi ya iskeshi zaune akan sallaya ya jingina da jikin gadonshi da alama be dade da gama sallah ba.
Dagowa yayi ahankali ya zubama sadeeq daya shigo da sallama ido sannan ya amsa ciki ciki wanda ko kadan sadeeq bejishi ba yadaiga bakinshi ya motsa.
Be damuba ya qaraso ciki riqeda ledar hannunshi ya dorata a mirror sannan yasake ficewa.
Maida kanshi yayi ya lumshe idanu yana dorawa daga inda tunaninshi ya yanke.
Jiyayi ansake bude kofar hakan yasa yasake bude idanun yadan dago yana kallon sadeeq daya dawo da plates da cups tareda cokula.
Batareda yace mashi komaiba ya dauko ledar ya zauna bisa rug din dakin yana facing din Ashraf sannan yafara ciro abubuwan dake cikin ledar.
Jujjuyesu yayi a plate, jollof rice ce dataji kayan lambu sai qamshi take sai gassashiyar kaza da robobin yoghurt.
Saida ya zizzuba kowanne a inda yakamata sannan yasaka spoons ciki ya tura tsakiyarsu.
"Oya bismillah" yafada yana gyara zama.
Ganin beko motsaba yasashi dagowa ya kalleshi saiya tsinci idonshi cikin nashi wanda hakan yanuna dama shi yake kallo.
Gira daya ya daga mashi alamun lfy? Dan murmushi yayi kawai still yana kallonshi.
"Oya muci, favourite dinka ne" yasake fada yana kallonshi
Babu musu shima ya tashi zaune shima yana takwashe kaffafunshi kamar dai sadeeq cikin zuciyarshi yana alfahari da abotarsu da sadeeq, sadeeq yacika amini kuma danuwa agareshi, duk tsanani duk wuya yana taredashi, duk cikin abokanshi sunfi shaquwa don yafi iyawa dashi, dukda wasu halayen nasu ya banbanta amma hakan yake haquri dashi suna jallaftawa a hakan.
"Wai ya? Kawani yi sakale kana kallona, nufinka nizanyi feeding dinka?" Yafada yana antayamashi hararar wasa.
Murmushi kawai yayi ya dauki spoon ya debi abincin yakai baki.
"Atoh don ba sweetie dinka bace" inji sadeeq shima yana kai loma.
Haka sukaci abincin sadeeq na janshi da fira duk na barkwanci duk don yasaki jikinshi yaci abincin sosai.
Babu laifi yadanci don yaci fin rabi sannan yakora da kakkaurar yoghurt din yakoma yadan jingina bayanshi da gadon.
"Daga gidansu saudart nake" inji sadeeq yana kai cup baki.
Dagowa Ashraf yayi dasauri ya kalleshi saidai yakasa cewa komai, koyaya aka ambaci sunanta sai jikinshi da zuciyarshi sun amsa.
Yana sane yaqi qara cewa komai ya maida hankalinshi kan abincin dukda yanajin idanun ashraf akanshi.
Cigaba yayi da kallonshi yanason ya tambayi me yajeyi kuma ya ya taddata amma yakasa sai idanun daya zubamashi kawai.
Saida yagama kwalailaitarshi da tsantsani sannan yarufe plate din yasha cikin zuciyarshi yana ayyana mai hali baya ta6a chanza halinshi. Yasan a qagare yake yaji komenene amma girman kai ya hanashi magana wai ahakan ne wai ya saduda.
Dagowa yayi ya kalleshi yaga still shi yake kallo amma yana iya hango 6acin rai cikin idanunshi dukda be nunaba a fuska.
'Baka buguba' inji sadeeq cikin zuciyarshi sannan yamiqe da niyyar tattare kwanukan wajen wanda hakan ya tunzura Ashraf sosai.
Wannan wane irin salon wulaqanci ne kafaro magana kakuma yi shiru?
"Ehen? Me kajeyi wajenta bayan abinda tayimana?" Yafada cikin 6acin rai dayaga beda niyyar magana.
Dariya ce takusa su6ucewa sadeeq yayi saurin dannewa sannan yadago yana kallonshi da plates a hannu.
"Perdon? Me kake magana akai?" Yafada cikin waskewa
Wani malulu ta tsayawa Ashraf a wuya, lallai ma sadeeq.
Tsaki yaja yamiqe a fusace ya dauki sallayar ya linke ya ajiyeta a ma'ajiyarta sannan ya haye gado ya kwanta.
Dariya sosai yaba sadeeq hakan yasashi saurin fita da kwanikan yana dariya marar sauti, wani sa'in Ashraf yayi wani abun kamar qaramin yaro.
Saida ya kimtsa komai sannan yadawo saman ya taddashi still kwance yaba kofar baya.
Murmushi yasaki sannan ya qaraso shima ya haye gadon da qarfi yana rera yar waqarshi ta beginning to fall in love yana jawo wayarshi.
"Duk yau banji muryar rabin rai ba wlh" yafada yana scrolling a wayar da niyyar lalubo numberta.
Fitt.. yaji an fige wayar hakan yasashi saurin dagowa.
"Nan ba gidanku bane kuma ba dakinka ba, kabari saika koma gidanku sannan kayi koma me zakayi" inji Ashraf cikin jin haushi.
"Ikon allah, daga kira?" Inji sadeeq yana danne dariyarshi
"Koma menene, this is my house don haka inada iko dashi" yafada ahasale
"To naji, yi haquri bani bari nakoma falo nayi don gaskiya bazan iya jure rashin jin muryar ruhin ba na tsawon yini daya"
Haushi yaqara qumeshi
"Saidai katafi gidanku kayi wlh dama va gayyatarka nayiba, now out" yafada yana nunamashi kofa
"Iyee? Ni kake kora Ashraf?"
"Eh gidanka ko nau?"
"A'a nakane, yanzu ashraf ni kakema rashin M? Babu komai nina kawo kaina" yafada yana juya kai gefe
"Rashin M har yakai naka? Marar mutunci kawai"
"Ni me nayi to?"
"Bansaniba!"
"Dan allah gayamin, haka kawai kawani sauya lokaci daya kamar mai iskokai, dazunfa hirarmu muke"
"Guguwa gareni qarewar iskokai, mtcheew" yasake juyamashi baya
"To yanzu yi hqr, gayamin meya faru rigimatu"
Tsaki yaja batareda yajuyoba, jiyake kamar ya shaqureshi, wai tayaya mutum zai faro magana kuma ya manta?
"Kaji?"
Wani tsakin yasake ja sannan yace
"Don iskanci saika faro magana kuma kayi shiru?"
Danne dariyar dake cinshi yayi yana kallon bayan ashraf daya juyamashi
"Magana? Wace magana?" Ya tambaya kamar gaske
Wani dogon tsaki yaja sannan kamar bazaiyi magana ba yace
"Ta yarinyar mana, mtcheew" yafada cikeda takaici
Dariyar da sadeeq keta dannewa tundazu yasaki harda bubbuga katifar.
Juyowa ashraf yayi yana kallonshi sannan ta girgiza kai
"Madness on point" yafada cikin borin kunya.
Shidai sadeeq bece komaiba sai dariyar dayake hakan yasake tunzura ashraf yakai mashi bugu yayi saurin matsawa baya don ya kauce sai yajishi qasa kasancewar dama bakin gado yake, hakan yaba ashraf dariya sai yadan murmusa yana kada kai.
Miqewa sadeeq yayi yana dan tsagaita dariyarshi don ba maganarshi damar fita.
"Wace yarinya?"
Jifanshi ashraf yayi da pillow yana cewa
"Bansaniba dan air kawai"
Dariya sadeeq yasakeyi sannan yadawo yazauna kan gadon yana cewa
"Gakanan babban dan air? Wlh ka rage wannan shegen girman kan naka marar amfani, idiot nazaci bakada bakine wlh da saidai nafasa fada"
"Mtcheew kanka akeji" inji ashraf yana juyamashi baya
"Hmm wlh ina tausaya maka yaro, wlh ka ajiye girman kai ka yaqo soyyayarka kafin kayi asararta gabadaya, did you know she's taking this issue to court? Kuma wlh dagaske take"
Juyowa yayi bashiri yana kallonshi a galale
"Court?"
"You heard me right ai, to wlh makaka kotu zatayi a warware komai kuma kasan zancenan yaje kotu wlh an warware angama ne don tanada evidence kuma sunanka ne zai 6aci abanza"
Kasa koda motsi ashraf yayi sai idanun daya zubamashi kamar dolo
"Court? Is she crazy?" Yafada unbelievingly
Daga kafada yayi kawai yana jingina da kan gadon
"Ni bama wannan ba, inason sanin wanda yagayawa ummy ne, don da alamu ba ita bace batama san hakan ya faruba, maganar gaskiya ashraf you have to fight, tun kafin komai ya ta6ar6are"
"No, zan rabu daita kawai" yafada a sanyaye
"What!" Inji sadeeq yana waro idanu
"Yes she hates me, bazata iya zama daniba kuma bazan iya tilastamata ba, son kai din zaiyi yawa"
"Mtcheew amma bakada hankali, meye na saurin karaya?"
"Duk abinda zan mata bazata ta6a saurarata ba"
"Ka gwada? Eh? Dukfa abinda ake ko sau daya baka ta6a nunamata kayi danasani ba bare akaiga ka nemi yafiyarta. Maganar gaskiya ashraf you're so annoying, durkusawa wada ba gajiyawa bane, kayi mata laifi meye aciki don ka nemi yafiyarta? Kasan wani tasiri neman yafiyarta zaiyi a rayuwarka? Mtcheew gwanin takaici wlh" yafada yana saukowa daga gadon tareda ficewa.
Binshi yayi da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kanshi ahankali yana antayawa cikin kogin tunani.
A bangaren saudart kuwa haka tawuni sukuku kamar marar lfy, jiran dawowar daddy kawai take.
Sosai ta birkicewa daddy bayan yadawo, kuka kawai take tana tsoron maganar nan takai kunnen mamy.
Sosai daddy ya damu yanajin duk shine silar faruwar komai, yanajin duk shine mai laifin.
Dakyar yasamu yashawo kanta hankalinta yadan kwanta amma can qasan zuciyarta fargabace da tsoron yadda abin zai kaya.
Tunda yakoma falo beqara shiga dakinba don yavashi haushi sosai.
Yananan har aka fara kirar magrib.
Daya daga cikin toilets din falon yashiga ya daura alwala.
Fitowarshi yayi daidai da saukowar ashraf shima wanda shima da alama masjid zaya.
Jerowa sukayi batareda suncema juna uffan ba suka nufi masjid din.
Basu suka fitoba sai bayan isha'i
Cikin gidan suka koma sadeeq yanufi parking space.
Binshi da kallo ashraf ta tsaya yayi harya bude motar dazu zai shiga.
Takowa ashraf yayi wajen yana cigaba da kallonshi.
"Ina zaka?"
Banza sadeeq yayi dashi
"Look am sorry, nifa bada nufin ba 6atama rai nayi maganarba"
Wani mugun kallo sadeeq ya watsamashi
"And wayace ranshi ya6aci?"
"Idan ba fushi kakeba meye na tafiya?"
Shigewa yayi cikin motar ya rufo sannan ya kalleshi ta window yana cewa
"Gidanmu zani dare yayi"
"I thought nan zaka kwana"
Harara ya 6allamashi
"Bakada hankali, gidan auren naka zan kwana? Mtcheww"
Ashraf beqara cewa komaiba sai dan jada baya dayayi ganin ya tada motar, hakanan yakejin va dadi har cikin zuciyarshi, shi kowama fushi yake dashi, saudart,ummy, yanzu shidinma dayake dan kwantar mashi da hankali yayi fushi.
Bama motar wuta sadeeq yayi sannan yafice daga gidan bayan ya dage glass din motar yabar ashraf da binshi da kallo.
Yadan dade anan tsaye feeling soo empty sannan yasoma takawa yakoma cikin gidan a sanyaye yanajin komai na duniyarnan namashi ba dadi.
Sama ya fara haurawa ahankali hannayenshi zube cikin aljihu kanshi a qasa harya qarasa sama.
Tsayawa yayi tareda dagowa ahankali ya zubama kofar dakinta ido tunani kala kala na zarya a ranshi.
Ahankali ta taka yanufi kofar yana kallon kofar.
Hannu yasa yakama handle din ya murda ahankali dukda yasan a kulle take.
Ga mammakinshi sai yaji ta bude, hakan yasashi tura kofar yayi stepping ciki ahankali yana qarewa dakin kallo.
Yaune karo na farko daya ta6a shigowa dakinta, tsarin dakin ya burgeshi sosai don komai a tsare yake in a tidy way sai dan qura qura da dakin yayi na yan kwanakin dayayi bega gyaraba.
Takowa yayi ahankali cikin dakin yana bin koina da kallo kamar mai inspecting yanajin wani irin feeling gameda ita.
Ahankali ya qarasa bakin gadonta dayake liss kamar ba'a hawa yadan kakka6e saman gadon ya zauna ta jingina da kan gadon yana sakin nannauyan ajiyar zuciya.
Lumshe idanunshi yayi ahankali yana tariyo duk abinda yafaru dasu tun farkon haduwarsu har ixuwa yanzu.
Yasan yayimata laifi kai laifukama dayawa, tsawon rayuwar dasukayi tare be iya tuna abu daya datayimashi wanda ba daidai ba, duk shi kemata.
Bata ta6a bude baki da nufin yimashi rashin kunya ko zagi ba dukda abinda yake mata saidai ko tabashi amsa daidai datashi ko ta basar tanuna vataji haushi wanda shikuma hakan ke quleshi a lokacin.
Gani yake jijji dakanta yayi yawa ita ba kowan kowaba amma sai shegen girman kai hakan kesa yaqara yimata wani abun dazai qonamata rai.
Ajiyar zuciya yasaki yana kamo le6enshi na qasa yana dan cizawa
"Will she ever forgive me?" Tambayar dayayiwa kanshi kenan
*kata6a nuna danasaninka gareta bare akaiga ka nemi yafiyarta?*
Maganar sadeeq na dazu ta dawo mashi.
"No" yafada ahankali
Duk haukan dayakeyi batasan yanayiba, batasan yayi nadama ba, batasan irin qaunar dayake mata.
Duk meyasa? Ya sake tambayar kanshi
*Girman kai* wani sashen zuciyarshi yabashi amsa.
*is better ka ajiye wannan girman kan naka marar amfani kafin wuri ya quremaka*
Maganar sadeeq ta kwanaki tasake dawo mashi.
*saudart alkhairice agareka ashraf, karkayi kuskuren barinta ta su6uce maka*
Maganar sadeeq tasake dawomashi
*Son, ina alfahari dakai da matarka, samun suruka da mata irin saudart zaiyi wuya a wannan zamanin, ka godewa allah don samun mace tagari shine dadin zaman duniya*
Maganar ummy data ta6a yimashi watarana dayaje gidan tadawomashi.
Tunawa yayi da tashin hankalin daya hango qarara a fuskar ummy dazu.
She's scared, tsoro take ta rasa suruka irin saudart, tana jiyemashi tsoron rasa mata kamarta, tana jiyemashi tsoron rasa abokiyar rayuwa tagari kamarta.
Amma tambayar anan shine shi yanajin tsoron rasata?
"Yes, am scared" ya amsa ahankali.
To meyasa bazai yunqura wajen ganin ya mallaketa na har abada? Meyasa yakeson girman kanshi yakaishi yabaro? Meyasa?
Haka yaita juyi shikadai yana saqa da warwarewa, ganin hakan ba mafita bane yasashi miqewa yashiga toilet dinta ya daura alwala sannan yadawo ya bude closet dinta dake a tsare sai qamshi kayan keyi ya ciro sallayarta yarufe ta shimfida yahau yashiga jera nafiloli.
Akan sallayar barci ya sadado ya daukeshi...✍️
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
063
Yau ya makara wajen tashi sakamakon rashin samun isashen barcin dayayi.
Tashi yayi yashiga toilet din dakin ya daura alwala sannan ya kabbara sallar asuba kasancewar har bakwai nasafe tayi.
Saida yagama yayi addu'o'inshi sannan ya fito daga dakin yakoma nashi yaqara komawa kan gado don kwata kwata barcin be isheshiva.
Sai wajajen 11 saura yasake farkawa yashiga bathroom yayi wanka ya fito sannan yashirya cikin wasu qananun kaya dasuka qar6eshi sosai suka kuma qara fiddo mashi qirarshi na qarffafen namiji.
Makullan motarshi kawai ya dauka sannan yafito daga dakin ya sauko qasa sannan yafita waje.
Parking space yanufa ya bude daya daga cikin motocin wajen yashiga ya fita daga gidan.
Direct gidan ummy yanufa cikeda fargabar abinda zai tarar.
Saida yayi parking sannan yafito ya kulle motar sannan yanufi hanyar cikin gidan.
Danna door bell din yayi yana kallon kofar yana tunanin yadda zai fuskanci ummy yau, sosai yakejin kunyarta dakuma shakunta.
Budewa akayi fuskar mai aikinsu ta bayyana.
Saurin russunawa tayi tana gaidashi a ladabce tareda kaucewa gefe don yasamu damar shiga.
Da hannu ya amsa mata sannan yashigo yana qarewa falon kallo.
Can ya hango baby lafe bisa kujera tanata faman danne danne awaya.
Jin sallamarshi yasata saurin dagowa tana gyara zamanta tana amsawa.
"Yaya sannu dazuwa" tafada cikin murmushi
Saida ya zauna a kujerar dake facing daura daita sannan ya amsa yana jingina da kujrar
"Ina kwana yaya?" Injita
"Lfy" ya amsa a taqaice
Shiru palon ya dauka nawani lokaci sannan yadago ya kalleta
"Ummy fa?"
"Tana sama" ta amsa a sanyaye.
Be sake cewa komaiba yamiqe ya haura saman baby tabishi da kallo.
Saida yayi knocking sau uku sannan yaji muryar ummy daga ciki tana cewa
"Na'am, come in"
Ahankali kamar marar gaskiya ya murda handle din kofar ya tura sannan shima yashiga bakinshi dauke da sallama.
Dagowa tayi daga bisa sallayar datake zaune wanda alamu sun nuna bata dade da gama sallar walha ba ta dubeshi sannan ta kauda kai tana amsa sallamarshi.
A darare ya qaraso ciki yana kallonta sannan yasamu can dan nesa daita ya zauna qasan rug din dakin.
Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana, ita tana cigaba da jan cazbin hannunta shikuma yana satar kallonta.
"Ummy ina kwana?" Ya gaisheta cikin sanyi
Kanta kawai ta dagamashi batareda ta ko kalleshi ba hakan yaqara sanyaya jikinshi.
Hakan sukaita zaman kurame na kusan minti shabiyar.
Ashraf jinshi yake so akward, sosai cold attitude din ummy ya dameshi gashi taqi bashi fuskar yayi magana.
Saida tagama laziminta sannan ta miqe zata nade dardumar yayi saurin amsa yana nademata.
Batace mashi komaiba ta wuce ta rataye cazbinta ta cire hijabinta itama ta adanata sannan tanufi hanyar toilet.
"Ka sauka kaje kaci abinci" ta umarceshi daidai zata shige toilet din sannan tashige tarufo.
Bin kofar yayi da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya cikin jindadin maganar datayi mashi koba komai tadamu dashi, fushinta be hana ta lurada beci komaiba.
Tashi yayi ya fita yajamata kofa sannan ya sauka.
A falo ya qara tadda baby wannan karon waya ke maqale a kunnenta da alamun wayatake.
Tana ganin saukowarshi tayi saurin yin sallama da wanda suke wayar ta sauke wayar.
Zama yayi a inda ya tashi dazu sannan yadago ya kalleta.
"Serve me food" yafada yana lumshe idanu.
Tashi tayi babu 6ata lokaci tawuce dining area zata kwaso kayan karin dake sama.
"No bari naqaraso" yafada yana tasowa.
Dining din yaqaraso yaja kujera ya zauna sannan tace
"Yaya tea ko kunu?"
"Kunu" ya amsa yana danna wayarshi
Kunun gyadan dayaji madara tayi serving dinshi sai fried plantain kamar yadda ya buqata sannan tajuya da nufin tafiya.
"Wait.."
Juyowa tayi tana kallonshi
"Dawo kizauna fira zamuyi" yafada yana kai kofin a baki.
Dawowa tayi ta zauna tanajin abun wani banbarakwai, shi dake korata idan zaici abinci yau ita zata tayashi fira?
Cigaba yayi da karyawarshi itakuma ta nutsu sai jujjuya wayar hannunta take tanajinta duk a takure.
Saida ya cika cikinshi sannan yadago ya kalleta yana goge bakinshi da tissue sannan ya jefa a waste basket din dake can gefe.
"Ya school?" Taji ya tamvayeta
"Lfy lau yaya" ta amsa tana mammakin sudden change dinshi cikin zuciyarta.
"Kinadai karatu ko? Idan naga C.O a result dinki saikin gane kurenki ne"
Murmushi tadanyi
"Kai yaya, tunda kake ganin result dina ka ta6a ganin C.O? Am trying hard yaya"
"To try harder" yafada yana danna wayarshi.
"Insha allah" tafada tanajin dadi wai yau suna fira da yaya babu tsangwama ba harara.
Shiru wurin yadan dauka kasancewar babu mai wani abun dazai sake fadi, can sai ashraf ya ajiye wayar hannunshi yadago yana kallonta in a serious mode ganin hakan yasata sadda kai.
"Baby" taji yakirata
Hakan yasata dagowa tana kallonshi itama.
"Tell me, waye yazo jiya? Waye yazo yasami ummy jiya yabata wannan takardun" yafada yana kafeta da idanu.
Shiru baby tayi tana sadda kai qasa cikin tsoro.
"Tell me ok? Don't get scared" yasake fada ahankali
"Suzy.."
Dan ware idanunshi yayi
"Wanene?" Yasake tambaya cikin mammaki
Hawaye taji suna taranmata a idanu
"Suzy ce yaya"
Shiru yayi yana kallonta don harga allah inba yanzu data kira sunanta ba harya mance da wanzuwarta a duniyarnan.
"Suzy? How?"
Sniffing tayi ahankali sannan tace
"Muna zaune bayan mungama lunch mukaji doorbell na ringing, Asabe taje ta bude sai gashi sun shigo tareda ita tayi shigarnan nata na rashin dacewa.
Nayi mammaki dana ganta har cikin falonmu amma sai banyi maganaba muka bita dakallo nida ummy hartazo tanemi wuri tazauna ta dora qafa daya bisa daya tana taunar chewing gum.
Nice nace 'mallama lfy zaki shigo gidan mutane babu ko sallama and ki zauna vatareda an baki iziniba?'
Kallon banza ta watsamani sannam tace
'Save it, ba wajenki nazoba wajen kakar da ko diyata nazo, so mind your damn business'
Shiru mukayi muna kallonta cikin mammaki don babu wanda ya fuskanci inda ta dosa.
Kallon ummy tayi tace 'barka da warhaka hajiya, fatan kina lfy?'
Karfin hali ummy tayi tace 'lfy lau, wacece ke?'
"Surukarki nan gaba insha allah kuma uwar jikanki nan bada dadewa ba"
Kallon juna mukayi nida ummy sannan na miqe a fusace ina cewa
'Look mallama tashi kifita! Rashin ajin naki haryakai kibiyo mijin wata har gidansu don rashin zuciya..'
Ummy ce ta katseni ta hanyar dagamani hannu sannan ta kalli suzy da ko ajikinta saima kallonmu sheqeqe datake.
'Baiwar allah, vamu fahimci bayananki ba'
'Ok ina nufin ni karuwar danki ce Ashraf mai dauke da danshi ko diyarshi a marata, yanzu kin gane?'
Abin ya dakemu sosai dagani har ummy.
Bansan sadda nakai wajenta ba sai gani nayi ummy na kiciniyar rabani daita.
Dakyar ta banbareni jikinta tanamin fadan meye haka nakeyi.
'Ummy qarya takeyi, tana daya daga cikin yan iskan dakebin yayane tun kafin yayi aure, ganin be aureta ba shine zata yimashi sharri, nasanta ummy nasanta farin sani' nafada ina huci
'Kin sanni amma bakisan yayanki ba, idan ni yar iskace to yayanki dan guguwa ne don shi ya koyamin iskanci yafake da auren bogi don azaci kamili ne a zahiri bayan yana tsula tsiyarshi a 6oye'
Kalamanta sunyi mugun 6atamin rai hakan yasa na nufeta again ummy tayi saurin kamo hannuna sannan takalli suzy
'Kinsan dawa kike magana? Kinsan kan wa kike magana? Kinsan abinda zaki iya jama kanki akan wannan qazafin?' Inji ummy da alamun itama ranta yafara 6aci.
'Ba qazafi bane hajiya ban taho nanba saida sheduna, ashraf auren bogi yayi, tsararren aure yayi da wannan yarinyar don wanda itama tayishi ne don tarufama kanta asiri...'
Cakumota nayi wanda hakan yayi sanadiyar katsewar maganarta nafara bugunta takoina hakan ya fusata ummy ta juyoni da qarfi ta daukeni da mari wanda yasani dawowa hayyacina, nan taita man fada inda take shiga batanan take fitaba sannan tajuya kan suzy tace ta zauna ta gayamata komai dalla dalla.
Zama suzy tayi sannan tacigaba dacewa
'Nida Ashraf masoyane tun a school, shine saurayina na farko kuma shine yafara kawarmin da virginity na' saita fashe da kuka.
'Shi ya lallatani nikuma saboda soyyayar danake mashi yasani biyemashi, bayan yagama karatunshi yadawo nigeria yafara aiki nikuma yabarni can ina kammala karatuna, lokacin kuka takuramashi kan batun aure shikuma ni yakeson aura nikuma family na sunce bazasu aurar daniba saina kammala karatu na.
Hakan ya tada hankalina sosai..dafarko harnaso bijirewa akan saina kammala karatun don inasonshi sosai don hakanma yabashi damar yin amfani da son danake masan ya lallatani.
Ana hakan yazo qasar wanda dama al'adarshine daya fita qasar waje da sunan business trip wajena yake gangarowa muyita masha'ar mu.
Nan yaita rarrashina ganin yadda duk nadamu yacemin yasamo mana mafita wai akwai wata yarinyar dazasuyi auren kwangila daita.
Cikin mammaki na tambayeshi Auren kwangila kamar yaya?
Sai yace wai itama yar hannuce wato tasha mu'amala da maza to shine takeson yin aure amma tana tsoron kar asirinta ya tonu don a zahiri tana pretending ita kamilace kuma nitsatsiya wanda a badini kuma karuwace, shine tazo mashi da tayin ya aureta na yan wattani saisu rabu yadda zatayi aurenta a matsayin jawara babu wanda zai zargi komai, suka yanke wannan shawarar akan babu abinda zai shiga tsakaninsu har su rabu wanda lokacinda zasu rabu kuma zaiyi daidai da nagama karatu sai muyi aurenmu'"
Shiru baby tayi tana sheshekan kukan da tundazu tafarashi, shikau ashraf kamar statue yakoma sai binta da kallo yake babu ko kyaftawa.
"Yaya wlh bakaji yadda najiba alokacin, zuciyata kamar ta tarwatse, nasan karya take yaya, sharri take qulamaku kaida anty hakan yasa natashi nasake nufarta ina bugunta ina kuka ina cewa karya take wlh sharri take muku.
Itadai ummy batace konaiba, she's shocked to death don tama kasa motsawa.
Dakyar suzy ta kwaci kanta ta tureni nafadi sannan ta watsamana wasu takardu tana magana cikin qaraji wai muduba idan qarya take don harda shaidu gasunan.
Duqawa ummy tayi ta tattara takardun tana dubawa nan mukaga takardar comtract ne na auren kamar yadda tafada ga sa hannunka 6aro 6aro gana aunty ga kuma na sadeeq na hudun kuma tace natane.
Mun shiga rudani sosai don sosai hankalinmu yatashi.
Dayar takardar kuma na gwajin juna biyu ne nata na wata biyu sai hotuna dakuke tare.
Ahankali ummy ta dago ta kalleta sannan ta sake kallon hotunan taga eh ita dince tareda kai.
'Juna biyu gareki?' Ummy ta tambaya
'Eh ummy kuma nashine wlh' ta amsa tana matsar hawaye
'To meyasa kika tonaku bayan ba haka kukayi dashi ba?' Ummy tasake tambaya
'Saboda yanason tilastamin zubarwa ne kuma ni ina tsoron aikata kisan kai, dana gayamashi yace to ku in zubar ko intafi can nida cikin kar in alaqantashi dashi don ba shirya zubewar mutuncinshi ba, nikuma naji haushi nafara masifar be isaba don tun farko shiya lallatani ba wani ba, shine yayiman mugun bugu yakuma ce yafasa auren kuma karna sake nanuna nasanshi.
Ganin ban iya facing din family dina da wannan abin kunyar yasani tahowa nan don a warware komai asamamin mafita'
Tashi nasakeyi ina qaryata cikin kuka
'Ummy qarya take wlh, son yaya take da aure shikuma yaqi saurarenta shine tabiyo ta wannan hanyar tayaya za'ace anty saudart karuwa ce? Tayaya yaya zaiyi zina? Wannan sherrin editing ne'
Dagaman hannu ummy tayi sannan tace ma suzy ta tafi zata nemeta saita tashi ta tafi.
Zuwa nayi kusada ummy nayita mata rantse rantse cewa qaryane, sharri ne
Batace mani komai ba sai shirun datayi na wani lokaci sannan ta umarceni na kira aunty saudart.
Kira biyar nayimata lafiyayye amma bata dagaba hakan yasa ta kiraka tace kuzo.
Saigashi kuna zuwa kuka gasgata abin"
Ta qarashe tana kifa kanta a dining table din.
Tsitt wurin ya dauka bakajin komai sai kadawar a.c dake wajen
Idanunshi sun kada sosai kamar gauta yayinda numfashinshi ke fita da nauyi har kana iya hango yadda qirjinshi ke sama da qasa.
Motsin dataji yasata dagowa daga kifa kan datayi taga shine ya miqe.
Sosai yanayinshi ya tsoratata hakan yaqara bugun zuciyarta.
Juyawa yayi batareda yace komaiba ya fice daga dining din dama falon gabadaya yanufi parking space cikin wani irin taku nashi wanda ban ta6a ganiba saiyau.
Wayarshi yaciro yana dailing din number yana bude motar.
Ba'a dagaba harta tsinke hakan yasa yasake bugawa lokacin harya shiga motar ya tadata.
Sai a kira na uku aka daga, lokacin harya fara reverse
"Fuck you! Ina kake!" Yafada cikin wani irin murya
Bansan kome aka fadamashi ba saiya sake cewa
"Damn you! Nace where the hell are you before I straggled you to death!" Yafada tsakankanin haqora, qirjinshi sai sama da qasa yake alamun zuciya
Bansan kome akace ba sai gani nayi yayi tilli da wayar seat din baya sannan ya bama motar wuta yafice daga gidan kamar zai tashi sama...✍️
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
064
Tsit dakin yayi bakajin komai sai qarar a.c dake aiki.
"Kutt... amma anyi tsinnaniyar yarinya, ciki? How and when?" Inji sadeeq cikin tsananin 6acin rai
Cize le6enshi na qasa Ashraf yayi yana kalkada kafa daga inda yake zaune, shikadai yasan abinda yakeji acikin zuciyarshi.
"Lallai dolene akoyama yarinyarnan lesson, ni wlh nama manta da ita ashe tananan tana bibbiyarku, abu mafi daure kai anan shine ina tasan cewa auren contract kukayi? There is something fishy here" yafada yana zagaye dakin
"I can't believe ummy kallon mazinaci takemin a jiyan nan, kallon me lallata yanmata, ni... ni Ashraf" yafada cikin wani yanayi
"Dolene mu nunamata kuskurenta Ashraf wanda nan gaba ko wuqa akasamata a maqoshi bazata qara gigin yima wani qaxafi ba, qazafin zina ba qaramin abu bane musanmman ma akan Saudart kamilar mace... baiwar Allah, allah kadai yasan yadda zataji idan labarin nan ya risketa"
Shiru dakin yasake dauka kowa da kalar tunanin dayake.
Ringing din wayar sadeeq ne ta katse musu tunaninsu.
Zaro wayar yayi ya duba sannan ya dago ta kalli Ashraf daya lumshe idanunshi.
"Ashraf.. ummy ce" yafada yana maida kallon ga wayar kuma
Bude idanunshi yayi yazuba mashi kawai batareda yace komaiba.
Ganin kiran zai tsinke yasashi saurin dagawa yakara a kunne.
Sallama yafara yimata sannan ya gaisheta a ladabce.
Bansan kome tacemishi ba saiya dago ya kalli Ashraf da shima kallonshi yake yace
"Eh gashinan ummy"
Magana aka sakeyi tacan 6angaren sannan yace
"Insha allah ummy"
Katse wayar yayi ya maido kallonshi ga ashraf dake kallonshi haryanzu.
"Ka tashi mutafi"
"Ina?" Ya tambayeshi ahankali
"Ummy ke nemanmu tace takira wayarka ba'a dagawa" inji sadeeq yana nufan closet dinshi don zaro rigar dazai daura bisa singlet din jikinshi.
"Ban iyawa, bazan iya fuskantar ummy ba ahalin yanzu" yafada yana dafe kan dake saramashi
"Meyasa? Yanzu ne the right time dazamu fahimtar da ita komai tun kafin abu ya girmama, yau zatasan komai so stand up dalla" inji sadeeq yana dora shirt saman singlet din.
"Allah kadai yasan kallon datakemin yanzu, i swear sai suzy tayi nadamar zuwanta duniya" yaqarashe yana huci
"Ai fadi ma 6ata baki, she really need to learn the lesson of her life, tashi mutafi"
Jiki asanyaye ashraf yatashi, besan yadda zekuma qara facing din ummy bayan yagama sanin kallon datake mashi.
*************************************
Zaune suke gabanta qasan rug kamar dai jiya kowanne kanshi sunkuye.
"Ina kiranka baka dagaba" inji ummy tana kallon Ashraf daya kasa hada idanu da ita
"Am..sorry, na..barota a mota ne" yafada kanshi still a qasa
"Wacece wannan?" Tafada tana turomashi wani pics gabanshi.
Dagowa yadanyi yana kallon pics din.
Hotonshi ne da suzy tadan shige mashi ajiki tana dariya shikuma yadanyi murmushi
Bazai manta ranar dasukayi hoton ba, ranar suna school ba'a dade da gama sheqa ruwan sama ba, garin yayi shar mutane sun fito waje sai daukar pics suke.
Saukowa shima yayi hannunshi riqeda wani qaton littafi shima yatsaya yana kallon students din
"My.." yaji an kwala mashi kira abaya.
ko be juyoba yasan itace
Qarasowa tayi gabanshi tana haki, binta yayi da kallo yadda kayan jikinta suka dan jiqe gashi tawani tsuqe cikin jumpsuit (biri da wando) babu ko mayafi sai yar hular datasa akai.
"Please muma muyi hoton..please" tafada zata riqe hannunshi.
Dan zamewa yayi yana harararta
"Look at you, wai bakijin sanyi ne kam?" Ya tambaya yana binta da kallo cikin kishi
Itama kallon kanta tayi sannan ta kwa6e fuska
"Am sorry zan chanza yanzu, please mu dauka ko dayane"
"No" yafada firmly yana juyawa zai tafi.
Bunshi tayi tafara mishi magiyar ya bari ko dayane suyi, ganin bazata barshiba yasashi hqr ta tsaya ta fiddo wayarta ta matso jikinshi kadan, bece mata komaiba don aqagare yake tayi din yatafi.
"Please kayi murmushi mana wannan hade ran dukna menene?" Tafada a shagwa6e
Tsaki yaja sannan yadanyi yaqe ta daukesu sannan yadan tureta daga jikinshi yana cewa
"Ai shikenan ko? Am going to the library, see yah" yajuya yatafi.
"Nace wacece wannan?" Muryar ummy tasake maidoshi daga duniyar tunanin daya lula.
Ajiyar zuciya yasaki sannan ya bude bakinshi dakyar
"Tsohuwar budurwa ta ce"
Shiru dakin ya sake dauka.
Rintse idanunshi yayi snnan yacigaba dacewa
"A school muka hadu kuma muka fara soyyaya... saidai tafiyarmu batayi wani nisaba muka rabu don kwata kwata batada kamun kai, ga shigar datakeyi anyhow dukda ina nuna mata rashin dacewar haka amma bata dauka..."
Shiru yasakeyi idanunshi still rintse yana sauraron bugun zuciyarshi.
"Mun..mun rabune ranar dana..."
Shiru yasakeyi hoton yadda ya taddata suna musayar hot kiss dawani qaton arne a wani class na dawomashi a qwanya.
"Sadda na.. naganta dawani suna.." sai yayi shiru yakasa idawa.
Ummy kallonshi take tunda yafara magana kuma haryanzu bata daina kallonshi ba
"Ummy na rantse ban ta6a zina ba, ko zanyi bazanyi da qazamiyar yarinyarnan ba, bansaniba.. bansan abinda aka fadamaki kenan ba, yes aurenmu da Saudart AUREN KWANGILA ne amma babu wata yarjejeniya makamanciyar wadda ta fadamaki a tsakaninmu da saudart, she's innocent.. hasalima..bada son ranta akayi auren ba, believe me ummy.. kinfi kowa sanin halin danki..."
Ya qarashe maganar muryarshi nadan rawa rawa.
"Ummy suzy shaidaniyace, sharri ta qullamasu saboda daga baya tadawoma ashraf yaqi sauraronta shiyasa ta buyomashi ta wannan hanyar, ummy ni aminin ashraf ne tare muke akoda yaushe, ko alokacin dasuke soyyayar ban ta6a ganin ya riqe koda dan qaramin yatsanta ba, hasalima bawani sonta yakeba duk ita taita cusa kanta gareshi" inji sadeeq
"Hakane ummy, nima nasan suzy farin sani, qawayenta kawai zaki kalla kisan ko ita wacece, tasha cusa kanta gareni don tasamu shiga awajen yaya akaro na biyu, tasha tazo taita rarrashina akan nabata number yaya amma naqiya, ga sa bikin su yayama saida suka fito qarara suka nuna baqincikinsu, magangannu kala2 babu wanda basu fadaba, ummy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba suzy qarya tashiryama yaya do n tasamu a liqamashi ita" inji baby itama fuskarta bayyane da 6acin rai.
Shiru dakin yasake dauka, kan ashraf haryanzu aqasa zuciyarshi na bugawa yanason jin wane hukunci ummy zata yanke.
Ajiyar zuciya ummy tasauke mai sauti sannan tace
"Kalleni Ashraf"
Shiru yayi yakasa dagowa, bejin zai iya dagowa su hada ido daita, wani irin nauyinta yakeji
"Nace ka kalleni"
Ahankali yadago ya kalleta saikuma yayi saurin kauda kai ganin ta kafeshi da ido.
"Nasani, nasan qarya take kuma sharri takemuku tun alokacin datake maganar, nasan cikinku babu wanda zai iya aikata abinda tace kun aikata, nidama ban zargeka ba ban kuma zargi daughter ba cos I trust you both"
Ajiyar zuciya ashraf yasauke mai sauti yanajin kamar ana lifting din wani qaton dutse a qirjinshi.
"Wacece saudart? Meya hadaku? Meye silar wannan auren naku na contract?"
Tambayar ummy tasauka a dodon kunnensu.
Kowannensu shiru yayi zuciyarsu na bugawa.
"Magana nike" tafada tana binsu da kallo.
"Ummy.."
"Shhhh.. barshi yayi magana, dashi nake ba kai ba, ka gayamin komai ashraf karka saki ka 6oyemin komai" tafada tana kallonshi.
Shiru falon yasake dauka, sai motsi yake da baki amma yakasa magana, yarasa ta inama zai fara.
"Saudart diyace ga SHAMSU KANKIYA...Tsohon aminin Abbu" yafada yana lumshe idanu.
Ware idanu Ummy tayi tana kallon Ashraf unbelievably
Bakinta na rawa tace "Shamsu qolo?"
Kada kai yayi zuciyarshi na suya.
"Nafara ganin appointment letter dinshi ne wattanin baya dasuka wuce, akan yanason rance don farfado da company dinshi dake neman collapsing... ina ganin sunan naga tabbas kamar nasanshi wani wuri, hakan yasa babi diddigin qundinshi ta internet anan naga shidinne bawani ba... nan take tsohon raunin dayaimana a zuciya ya motsa naji na tsaneshi fiyeda yadda na tsaneshi da, dafarko sai naso qin taimaka mashi amma sai wata idea ta fadomin, mezai hana inyi ramuwar gayya nima in dandana mashi abunda ya dandana mana?
Saina amsa buqatarshi nabashi ranar dazamu hadu sannan nakoma naita bin diddiginshi daga kan iyalanshi zuwa abokan aikinshi dakuma abinda ya tara da abinda ake binshi bashi.
Saura kwana daya mu hadu na gayawa sadeeq plan dina, dafarko yaso hanani yacemin inbarshi da allah kawai mai yiwuwa sakkayar allah ce yake gani tun yanzu amma sainaqi saurararshi don alokacin *WUTAR FANSA🔥*(littafina ba gaba insha allah) ke ruruwa azuciyata, na nunamashi bansan zancenba acewata don indauki fansa yasa allah yaturoshi wajena..dakyar nayi convincing din sadeeq ya amince min shima.
Ranar farkon dayazo...."
Nan yashiga bata labarin zuwan Alhaji shamsu nafarko company dinshi da yadda suka kaya sai kuma zuwanshi da biyu da yadda ya gabatarmashi da sharaddinshi dakuma amsar daya bayar na zaije ya shawarta.
Yakuma gayamata zuwan da saudart tayi da abinda yafaru tsakaninsu wanda hakan yaqara 6atamashi rai dakuma qara jin lallai saiya aureta donya koyamusu hankali gabadaya.
Yabata labarin yadda alhaji yaita fadi tashi har yasamu saudart ta yarda dakuma yadda aurensu yakasance har izuwa zaman aurensu ya gangaro zuwa fara aikinta a companynshi da abubuwan dayaita mata na muzgunawa ya gangaro zuwa tafiyarsu spain da zamansu acan dakuma yadda ta taimaka mashi wajen kama mayaudaran mutanen dasukaso karyashi har zuwa lokacin dasuka dawomashi da kudinshi da niyyar kawo qarshen contract din da abinda yafaru aranar dukda ya 6oyemata kissing dinta dayayi sannan ya gangaro har zuwan da sadeeq yace yayi gidansu jiya da barazanar makashi kotu datayi.
Shiru yayi yana sauke numfashi ahankali saboda doguwar maganar dayayi.
Dakin yayi tsit babu mai ko motsi yadda kasan babu kowa ciki.
"Na aureta ne badon komaiba saidon in rama abinda yayimana ko fiyeda hakan, nabashi rancen ne bisa tsarin zanyi shige da fice yadda komai nashi zai lallace yakasance babu uwar kudi ba riba ga kuma uban bashi.
Nikuma lokacin sai in nuna bansan zancenba saiya biyani inhar yanason diyarshi, sonake ya talauce shima yakoma bayada komai shima ya dandana abinda ya dandana inyaso shima zuciyarshi ta buga ya fadi mattac..."
Tasss! Sautin dayaji a qunnenshi ya hanashi qarasawa.
Kafin ya tantance meyake faruwa tasake daukeshi dawani zazzafan marin a dayan kumatun
Dafe duka kumatun yayi ta dogo da sauri yana kallon ummy daka tsaye sai huci take idanunta sun chanza launi.
Toshe baki baby tayi da hannu biyu tana ware idanu, tashin hankali qarara a fuskarta.
"Da hankalinka?" Ummy ta fada tana nunashi da yatsa manuniya.
"Nace da hankalinka da iliminka ka aikata wannan abin da ko jahili bazai aikataba?"
Kasa koda motsi yayi daga tsugunnen dayake hannayenshi dafe da kunci yana kallonta
Yakasa yara yau ummy ta dora hannu akanshi da sunan duka abinda bazai iya tuna when last tayimashi va tsawon rayuwarshi
"Fansa haukane?! Aure? Aure ka maida abin wasa? Abun daukar fansa? Ka rusa rayuwar yarinya da future dinta duk akan fansa?" Ta tambaya cikin zaremashi idanu.
"Ummy don alla.." katseshi tayi ta hanyar qamtsamashi nashi qason marin
"Yimin shiru! Harda kai? Atunanina kafishi hankali ashe taron zamuce ta tadda muje?!"
Dafe kuncinshi shima yayi yana sadda kai qasa
"Kaiga sarkin zuciya? Mai zuciyar qarfe dabakasan kabar mutum da allah ba? Akan banzar daukar fansarka ka janyo wanda bata jiba bata ganiba kana neman lallatamata rayuwa?! Kana..."
Kasa idawa tayi ta juya kawai ta dafe kanta kasancewar ta mai zuciya idan ranta yayi mugun 6aci maganama gagararta yake.
Ganin hakan yasashi saurin rarrafowa yana riqemata qafa.
"Ummy am sorry, am soo sorry"
Fizge kafarta tayi da karfi taja baya.
"You're not but you will be, kutashi kufita! Kutashi nace!!"
Tafada tsakankanin abinda ya toshemata maqoshi.
Saurin tashi sadeeq yayi amma ashraf ko gezau
"Kutafi nace kuma kai.."
Ta nuna ashraf
"Gobe kamar yanzu inason ganinka anan gidan da takardar saudart, banaso ko igiya daya ta rage atsakaninku"
Agigice ya dago yana kallonta yayinda zuciyarshi tayi wani mugun bugawa.
"Kaji nagayamaka! Ke tashi kitafi dakinki!"
Ta dakama baby tsawa.
Dagudu ta tashi tayi sama aguje.
Itama bin bayanta tayi tahaye sama batareda tasake kallonsu ba.
Dafe kanshi ashraf yayi cikin tashin hankali wanda tunda yake beta6a shigaba yayinda zuciyarshi ke bada wani hucin zafi kamar a oven....✍️
*WAYE ASHRAF?*
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
065
*WANENE ASHRAF?*
*AUWAL MUHAMMAD* Haifaffen garin wudil ne dake jahar kano.
Su shidda ne awajen iyayensu *MUHAMMAD JARIRI* wanda akafi sani da *MAMMAN* da matarshi *AMEENATU*
Yayansu shidda, maza hudu mata biyu.
Auwal shine d'a nafarko, sai ibrahim dake bimishi sai Nuradeen, sai Jamila, sai Zaharadini sai auta Halimatu wanda watanta uku a duniya ta rasu.
*MALLAM MAMMAN* manomine wanda ya riqe noma amatsayin sana'arshi, yanada rufin asiri daidai gwargwado don cikin noman yake samun abinci dazasuci harkuma su sayar.
Duk cikin yaranshi babu wanda yayi boko don lokacin ba'a wani bama karatun boko muhinmmanci ba.
Iyakarsu makarantar allo sai suwuce gona idan sun tashi don taimakawa babansu.
Jamila nada shekaru sha shidda akayimata aure dawani d'an abokin Mallam Mamman dake qauyen kakumi.
Auwal tun tasowarshi yakasance yaro mai hazaqa da zuciyar nema, duk yafi sauran yan uwanshi kazar kazar da qoqarin aiki.
Shiyasa sukafi shaquwa da Mallam Mamman don sosai yake taimakamashi a gona.
Auwal da kingin yan uwanshi sunada hadin kai ga girmama na gaba dasu suk qarantar taxarar dake tsakaninsu kau, hakan yasa zaman lfy, girmama juna da hadin kai ya wanzu a ahalin.
Koda sukadan qara tasawa sai suka amshi ragamar nomar yakasance mallam mamman ya sakarmusu komai yakoma yana hutawa.
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a wannan ahalin har watarana wani abokin mallam mamman dake zaune cikin garin kano yakawo mashi ziyara.
Anan su Auwal suka taddasu lokacin sun dawo daga gona, saida suka gaishesu sannan suka shiga cikin gidan.
Bayan sun shige ne abokin mallam mamman wato *MALLAM SANI* yayima mallam mamman tayin mezai hana yabashi daya daga cikin yaran yabishi kano ya hadashi da d'anshi sudinga aikin tuqin dayake.
Dafarko mallam be yarda ba, dakyar mallam sani yashawo kanshi yace zai shawarta.
Sai bayan isha'i sun zaune tsakar gida kamar yadda suka saba, samarin na zagaye da tray din abinci sunaci yayinda iyayen ke gefe.
Anan ne mallam mamman ya tada maganar da abokinshi sani yazomashi daita.
Nan take Auwal yanuna ra'ayinshi nason bin mallam sani don sosai yake sha'awar fita wani wurin nema.
Da farko mallam yaqi yara don ganin duk yafisu himma da qoqarin noma gashi shine babba amma ganin babu mai ra'ayin zuwa cikin qannen yasa ya yarda shima saida Auwal yadan sha wuya wajen shawo kanshi.
Cikin dan qanqanin lokaci suka shirya, ranar da mallam sani zai koma kanon yabiyo suka wuce da Auwal din.
Acan kanon mallam sani ya hada auwal da danshi mai suna Lawal wanda shima tsarar Auwal dinne suna daukan kayan gwari a mota suna kaiwa garruruwa.
Tun Auwal nabin Lawal a mota amatsayin karen mota har shima ya qware da tuqi shima aka bashi mota.
Alhamdulillah yana samu bakin gwargwado don duk qarshen wata idan zai ziyarci wudil yana zuwa masu da alhairi bakin gwargwado.
Suma su Nura suna itakar qoqarinsu a harkar nomansu idan kuma auwal yashigo garin yazo hutu wanda duk yawanci kwana hudu yakeyi haka zasu hadu sutafi gonar gabadaya.
Cikin dan qanqanin lokaci Auwal yayi suna, masu bada mottoci haya suka sanshi saboda gaskiyarshi da riqon amana.
Tun yana daukan kayan gwari har yakoma daukan kayan smuggeling irinsu shinkafa, man olga dadai sauransu.
Sosai yake samu da wannan sana'ar dob harya gyaramasu gidansu dake wudil dukda ba rusheshiba yayi akayi saboba saidai duk ya gyagyarashi an chanza sabon rufi na kwano sa6anin ba karare saikuma shafe da akayima gidan both qasa da bango.
A 6angaren qannenshi kau suma suna samun cigaba sosai don Ibrahim yabude dan shago yana siyarda kayan masarufi wanda yake hadawa da noma.
Nura kuwa yakama kiwo na dabbobi daban2 wanda shima hakan be hanashi nomanba.
Shikuma Zaharadini daga baya Auwal yatafi dashi kanon don sudinga aikin tare.
Auwal cikim tafiye tafiyenshi ba tuqin mota watarana yaje garin yola ya hadu dawata kyakyawar bafulatana mai suna *FATIMA* wanda ke kawo tallar nono da wara a inda suke sauke kaya.
Wasa wasa suka shaqu dajuna soyyaya tashiga tsakaninsu, ya kasance dik sadda yashigo garin suna tare kofar qaton shagon dasuke sauke kayan suna fira kamar karsu rabu hartakai yafison daukan kayan yola don haduwa da sahibarshi.
Ahaka suka qulla shekara daya suna soyyaya .
Awani dawowa hutu dasukayi wudil mallam mamman da yafara tsufa ya tarasu ya nemi kowannensu ya fidda mata yayi aure musanmman Auwal da Ibrahim kasancewar sune manya.
Anan ibrahim ya bayyana cewa shi dama akwai wacce yakeso mai suna *Raliya*, yarinya nitsatsiya babu wanda besantaba a garin wudil.
Sosai sukaji dadin za6in nashi nan aka maido akalar tambaya akan Auwal.
Shima beyi qasa a gwiwa ba ya bayyanamasu soyyayar dake tsakaninsu da Fatima yar yola.
Dafarko Aminatu (inna) taso taqiya acewarta saidai yasamu mata ansn cikin wudil ta aura amma daga baya ta amince bayan mallam mamman ya fahimtar daita shi aure rabone kuma matar mutum qabarinsa.
Nanfa magana takaiga manya, suma can 6angaren fatima sunso qiyawa amma daga baya sai suka amince aka saka rana lokaci daya dana Auwal da Ibrahim din.
Gaggarumin biki akayi a garin wudil.
Mallam mamman baqi yaqi rufuwa ana bikin yara har biyu yan gaban goshi.
Jamila itama ta halarci bikin alokacin 'ya'yanta uku.
Sosai akasha shagalin biki inda anan qauyen aka kawo fatima saida sukayi sati sannan suka koma cikin garin kanon awani madaidaicin gida daya kama haya.
Kwanci tashi asarar mai rai.
Haka Auwal yacigaba da harkarsa ta tuqi Allah na sanyamashi albarka yana kuma qara budamashi har ya tara kudi shima yasiya mota daya dukda da second yafara don gangar jikin motar yafara siya sannan ahankali ahankali yacigaba da hadata harta zama cikkakiyar mota nan shima yabadata haya ga qanninshi Zaharadini yayinda shima yacigaba da nashi tuqin, saiya kasance ana bashi haya shima yana bayarwa kuma hakan ba qaramin budi ya qaramashi ba.
Ana cikin haka suka hadu da *SHAMSU ABUBAKAR* wanda akafi kira da *SHAMSU QOLO* d'an qauyen kankiya dake jahar katsina shima yashigo kano ne cirani.
Sun hadune wani zuwan da shamsu yayi zai sari jarkokin man olga sai aka hadoshi da motar Auwal suka taho alokacin shamsu na aiki ne awani qaton shagon kayan masarufi aqarqashin wani.
A wannan tafiyar suka qulla abota kasancewar shamsu mutum ne mai saurin shiga rai ga iya tsara kalamai ga raha.
Cikin dan qanqanin lokaci suka zama aminan juna don sosai suke qaunar juna har takaiga indai auwal nacikin gari to zakagansu jone koda wane lokaci, hakan yasa kowa yasan da abotarsu.
Shekara daya da aurensu Auwal Allah yayima Mallam mamman rasuwa, mutuwae data girgiza mutane dadama don bawani jinya yayiba, amai da zawo yayi na yini daya ya sheqa.
Babu shiri su Auwal suka tarkato sukayo wudil.
Suna wudil har akayi sadakar bakwai.
Cikin masu zuwa masu gaisuwa harda Shamsu qolo don shi tun ranar kwana biyu yazo saida akayi addu'ar uku yajuya washegari.
Bayan addu'an bakwai su Auwal na shirye shiryen komawa kano Raliya matar Ibrahim ta haihu kasancewar dama da tsohon cikinta akayi rasuwar.
Ta haifi danta namiji tubarkallah babu wata wata aka maida sunan margayi mallam mamman sai aka dinga kiranshi *Mallam*
Sai bayan suna sannan su Auwal suka koma kano.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, ahankali ahankali Allah yaita budama Auwal yaqara siyan mota yaqara badata haya itama wanda hakan besashi barin tuqinba.
Haka yacigaba tun yana sayan tsoffafi yana hadawa harya fara siyan sabbabi dall zuwa lokacin arziqi ya zaunamashi sosai don harya ginama kanshi gida mai kyan gaske.
Yakumu rushe ginin qasan gidansu ma wudil yayi na zamani ya zuba kayan more rayuwa a gidan musanmman dakin inna wanda babu yadda beyi ba daita kan yamaidota kano taqiya wai gwara ta mutu a mahaifarya.
Haka zalika bebar qannenshi ba, yana taimakamasu bakin yinshi donshi mutum ne mai yawan kyautaa dukda suma basu rasa komaiba sunada rufin asiri daidai gwargwado.
A 6angaren abotarsu da shamsu qolo kau sai abinda yaci gaba don izuwa lokacin shamsu shima ya bude nashi qaton supermarket wanda babu abinda mai siyar na kayan masarufi.
Tun yana order a garruruwa har aka fara kawomashi daga qasashe daban daban wanda harda cotonou inda ake kawomashi shinkafa mottoci mottoci wanda duk yawanci motoccin Auwal ne, hakan yaqara danqon zumuncinsu ya kasance kansu a hade yake.
Saidai matsalar Shamsu daya, had'ama da son kudi, dik inda ta qyallo zai samu saiya kutsa yabi yasamu, hakan yasa yake hadawa da ha'inci a al'amuranshi.
Auwal yasha yimashi fads akan wannan halin amma yakasa dainawa don tun farko betashi ta wata isashiyar tarbiya ba na iyaye saina malamin makarantar allonsu wanda sunmashi yawa baya iya controlling dinsu duka.
Ana haka wata shekara Auwal ya tilastama Shamsu dole suka tafi aikin hajji tare wanda da ason ran shamsu ne bazaijeba don shi be qaunar abinda zai zazzagarmashi da account dinshi.
Bayan dawowarsu Alhaji Auwal da Alhaji shamsu, Alhaji Auwal ya tadda labarin farincikina na samuwar juna biyun Fatima wanda shekararsu ta uku kenan da aure.
Farincikin da Alhaji Auwal dama makusantanshi sukayi baya misaltuwa don sadaka yaitayi yana godewa allah da kyautar dayabasu.
Nanfa suka dauki son duniya da kulawa suka dorawa cikin, ba Alhajin ba ba zaharadini qannanshi ba ba fatima ba.
Haka fatima taita samun kylawa ta musanmman suka raini cikin cikin tsantsan kulawa har allah ya sauketa lfy ta sum6ulo qaton d'anta mai kama daita sak masha allah.
Farincikin da Alhaji Auwal yashiga alokacin 6ata bakine.
Kan kace me? Mutanen wudil harsun iso lokacin har ansakama Nura mai bima Ibrahim biki.
Suma yan adamawa yan ywan fatima ba'a barsu abaya ba da jamila yar kakumu haka suka garzayo kano don taya wannan ahali murnar samun qaruwa.
Ranar suna d'a yaci sunan kakanshi wato Muhammad ana masa laqani da *ASHRAF*...✍️
0 comments:
Post a Comment