A 6angaren Alhaji shamsu kau abin ba'a cewa komai don shima ba qaramin kudi yakashe ba don har ragunan da aka yanka shiya siya bayan kayan jarirai da lasa lasai dayaba mai jego.
Haka dai akayi sunan aka watse, kowa yakoma inda yafito.
Anan Fatima tacigaba da wankanta Auwal yasamomata wata dattijuwa dake qasan unguwarsu tana zuwa kullum tana wanke jariri.
Haka suka cigaba da kula da dansu cikin so da qauna, kan kace me yaron ya girma yayi bul bul kamar irin 'ya'yan turawan nan ga wayau kamar me?
Yanada wata biyar suka tattara sai wudil bikin Nura.
Shima babu laifi ansha shagalluluka kala kala, Ashraf kau saboda farinjini fatima har rasa hannun wa yake don beda qiwuya ko kadan da yaga saiya 6angale mashi baki yana miqo hannu alamun yanason adaukeshi, hakan yasa Fatima bata ganinshi sai ya buqaci abinci sannan za'a kawoshi ta shayar dashi akoma dashi.
Saida sukayi sati sannan suka juyo kano wanda tun washegarin biki Alhaji Auwal dama yayi gaba sukuma saida suka zagaye dangi sannan suka taho.
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa.
Ashraf ya taso cikin gata da soyyaya tako wane 6angare saidai duk gatan dayake samun hakan be hanashi samun inganttaciyar tarbiya ba don duk yadda suke dashi idan yayi ba daidai ba suna tsawatar mashi kuma suyimashi nasiha.
A 6angaren arziqin Alhaji Auwal kuwa sai abinda yayi gaba don yanzu yabar tuqi yakoma harkar shinkafa kawai, mottocinshi basu qilguwa kullum cikin busy yake yazama babban dan kasuwa.
Tun bayan haihuwar Ashraf *Ummy* kamar yadda Ashraf ke kiranta bata qara haihuwa ba sai 6arin datakeyi akai akai wanda sunyi maganin amma a banza.
Da farko Alhaji Auwal (Abbu) yaso ajuya mahaifarta saboda wahalar dayaga tanasha amma saita qiya acewarta abarta ahaka haka allah ta tsara mata.
Ashraf nada shekara biyar Abbu tabiyama inna, inna Raliya, ummy, inna jamila da zainab matar Nura hajji suka dunguma sukaje suka sauke faralli.
Bayan dawowarsu da yan wattanni akasama Alhaji shamsu biki dawata shuwa Arab ta garin borno.
Acikin wannan lokacin ciwon zuciyar Inna yatashi sosai babu wata wata Auwal ya daukota takawota asibitin kano aka cigaba da bata kulawa saidai dayake lokacinta na kusa kwana biyar tayi tana jinya ta rasu.
Sosai mutuwar ta girgizasu don sunyi kuka marar iyaka.
Haka suka dauki gawar suka juya wudil don Inna tabar wassiya idan tamutu koma inane a maidota wudil arufe don tafison arufeta a mahaifarta.
Bayan sati biyu suka dawo kano rayuwa tacigaba da tafiya.
Izuwa yanzu ansaka Ashraf makarantar primary ta private kuma allah yayimashi qwalwa da basirar daukar abu don shike ciwo nadaya a ajin duk qarshen term
Ba'a dadeba bikin Alhaji shamsu ya matso nanfa sukaita shirye shirye babu kama hannun yaro.
Duk tare suke komai da Alhaji Auwal don bawani dangi ke gareshiba sosai sai tarin abokan arziqi da abokan kasuwanci.
Gaggarumin biki akayi nagani na fada inda babu laifi ansha shagulgula sosai sannan aka kawo amarya khadija dakin mijinta.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya Ashraf sai qara girma yake da wayau, arziqin Abbu sai qara hauhawa yake allah nasa mashi albarka hakan yasa yakeda maqiya da mahassada masu hassada dashi a6oye batareda yasaniba.
Bayan shekara daya da aurensu Alhaji Shamsu sai Allah ya azurtasu da samun diya mace kyakyawa sak uwarta.
Alhaji shamsu baki yaqi rufuwa don murna, ranar suna na zagayowa aka radamata sunan *SAUDATU*
bayan haihuwar da 'yan wattani su Alhaji shamsu da matarshi khadija suka fara samun matsala atsakaninsu sanaddiyar sata dayayi acire mata mahaifarta wai diya daya ta ishesu acewarshi 'ya'ya talauci suke jawowa.
Firr khadija taqi yarda acewarta bazai sata ta kashe kanta da rai ba, tun suna abin a tsakaninsu har yakai kunnen Abbu kasancewar Khadija tagayamashi ko zata samu yanunama Alhaji shamsu daidai.
Abin yaba Abbu haushi sosai saiyaje yasamu Alhaji shamsu har company dinshi yayimashi magana shikuma sai abin ta hassalashi sosai ganin wai khadija takai qararshi wajenshi kamar wani ubanshi.
Nanfa Alhaji shamsu yafara zazzaga bala'i ta inda yake shiga batanan yake fitaba, aranar dakyar Abbu yafito company din rai 6ace abinda beta6a faruwaba a tsakaninsu.
Shikuma Alhaji shamsu yana komawa gida yarufe khadija da fada ta inda yake shiga batanan yake fitaba yace kuma cire mahaifa dole ayi muddin tanason cigaba da zama dashi.
In taqaice muku dai saidai auren yamutu da abu yaqi dadi wanda hakan ba qaramin 6ata ran Abbu ba yayi.
Wannan karon har gida Alhaji Auwal ya tadda Alhaji shamsu sukayi tatass inda daganan abotarsu ta shekara da shekaru ta watse.
Ummy sam bataji dadin hakanba amma ya suka iya?
Kan kace me? Har labarin 6atawarsu ya zagaye koina da aka sansu, mutane sai jimamin abun suke yayinda wasu suke farinciki akan haka.
Shekara daya da faruwar wannan al'amari Ummy tasake samun juna biyu lokacin shekarar Ashraf takwas kenan.
Sosai cikin yabata wahala sannan tasamu ta haifeshi bayan tasha baqar wahala tasamu diya mace sak Ashraf saidai bata ida kamoshi a haskeba.
Zokaga murna wajen Ashraf don sosai yake sha'awar qane ko qanwa dama.
Ranar suna na zagayowa akasamata sunan margayiya Inna wato AMINATU amma ana kiranta da *Baby*
Ana haka bikin zaharadini yataso inda ya auri yar kano suka tare a gidanshi da shima yagina a unguwar.
Kwanci tashi ba wuya, baby anfara girma don harta shekara biyu wanda yayi daidai da shekarun ashraf goma da wattanni.
Har a lokacin Abbu basa ga maciji da Daddy, sun watsar da zumuncinsu don ko labarin juna basaji.
Ana haka watarana Abbu na zaune cikin iyalanshi zaharadini ya bugo mashi waya kome yacemishi oho? Saiga Abbu ya zabura zaune har yana qwarewa da abinci
Cikin sauri ummy ta bashi ruwa suna jeramashi sannu ita da yaran.
Saida tarin ta lafa sannan ta tambayeshi lafiya? Yace ba lafiya bari yaje yadawo.
Haka ya fice be ida qarasa abincinba wanda itama ummy kasa ci tayi sai barosu ashraf datayi a dining tadawo falo tazauna tana addu'ar allah ya jiyardasu alhairi.
Acan kau Abbu yashiga tashin hankali marar misaltuwa don duka mottocinshi jami'an custom suka kame da abinda suka dauko.
Babu yadda beyiba wajen ganin an sakarmashi su amma abu yaci tura kai daga baya ma har gidanshi jami'an sukazo suka watsamashi komai suka 6alle store dinshi suka kwashe shinkafa ko taci basu bariba.
Wannan cin zarrafin baqaramin qonama Abbu rai yayiba don gani yake wannan cin fuskane babba.
Be ida shiga tashin hankaliba saida yaji cewa tsohon abokinshi kuma amininshine ummul aba'isan faruwan wannan lamarin.
Sosai abun ya dakeshi wanda har saida yakwanta ciwo.
Alokacin zaharadini ne yake taimakonsu dana magani don yadda kasan daukewar ruwa hakan komai na arziqin Abbu ya qare.
Magani akema Abbu amma kamar qaramashi ciwon ake.
Kullum cikin ambaton sunan Shamsu qolo yake yana hawaye.
Sosai su ummy dama kingin danginshi suka shiga tashin hankali akoda yaushe ummy da ashraf dashima yafara sanin komai cikin kuka suke saiya kasance Ashraf yakasa mance sunan da abbu ke yawan maimaitawa yana hawaye. Abinka da yaro saiya riqe sunan gamm a kwakwalwarshi yayinda yakema mammalakin sunan tsana wacce bata misaltuwa.
Saida Abbu yayi sati biyu sannan Allah ya dauki ranshi, mutuwar da ta girgiza jama'a da dama kar ummy ma taji labari.
Haka dole akamashi sutura jama'a takoina ancika unguwar danqam suka rakashi aka kaishi gidanshi na gaskiya.
Su ummy basu tashi gane kurensu ba saida duk aka watse nan fa talauci ya kunnomasu kai.
Gashi dama zaharadini yake dan taimakawa to shima yanzu babu mota hannunshi kuma kamar hadin baki kowa yaqi bashi dukda kau mutuncin da mutanen keyi da margayi Auwal dayake raye.
Hakan yasa yakoma kasuwa yana tsaron shago wanda abinda yake samu bewani taka kara ya karya ba.
Ganin haka yasa ummy ta tuntu6i zaharadini akan asiyarda gidan dasuke ciki su siya qarami kingin kudin saisu jujjuya.
Saida zaharadini ya tuntu6i yayyanshi na wudil saboda hadin kai irin tasu suka kauyi maraba da hakan don suma basujin dadin halin da iyalan dan uwan nasu yake ciki kawai don basuda halin taimakawa ne.
Kan kace me? Har an saka gidan kasuwa aka kau siyeshi da daraja, zaharadini ya samarmasu dan qaramin gida a unguwarsu suka zauna ya miqamata kingin kudin inda taqi amsa tace yaje yaita jujjuyawa kawai.
Shima qin yarda yayi har saida magana taje gasu Kawu ibrahim nan shima kawu ibrahim yayi na'am da shawarar Ummy kan zaharadini ya juyasu tunda shima kusan beda sana'a yanzu tsayyaya albashi sai aba ummy wani kaso acikin kudin itama tafara business.
Hakan kau akayi, zaharadini yaje ya sari kayan kitchen da kudaden yayi hayar shago acikin kasuwa itakuma ummy tafara sana'ar saida kayan humra da turrarukan wuta wanda Allah ya dubi maraicinsu yasamasu albarka aciki.
Ashraf da tuni ancireshi daga makarantar kudi don yanzu tafi qarfinsu aka maidashi ta gomnati yazana common entrance dinshi yakau fito da result mai kyau yasamu admission awata makarantar gomnati ta secondary.
Ashraf yanada hazaqa sosai kasancewar yasamu good background a makarantar primary dinsu kasancewar private ce.
Ahankali yafara suna don ashraf akwai qoqari da saurin fahimta don shike topping din class dinsu duk term.
Bayan haka ga baiwar kyau da Allah yabashi don kallo daya zakamashi kasan ya hada jini da fulani.
Ganin yadda ake sonshi ake kuma lilliqemashi yaja ashraf tsirowa da halin jinkai da miskillanci.
Yaga daman kana mashi magana saiya mula yasha iska sannan ya amsa a dage.
Haka yan aji ke fama dashi musanmman masu liqemashi ya koyamasu karatu, bazaiqi koyamusu ba amma saiya wanasu son rai ya shamusu qamshi sannan ya koyamasu hakan kuma be 6atamasu rai don su shan qamshinshi ma burgesu yake don komai yake kyau yake musu.
A ss1 suka hadu da *SADEEQ UMAR* the mathematician kamar yadda aka samashi suna a school din.
Duk aji daya aka sasu kuma ga lokacin basusan junaba don sadeeq transfer akayi mashi yayi junior waec a school din, sai ya kasance dukkansu sun hadu a commercial class.
Da farko gaba da kishi suka farayi dajuna kasancewar kowa na taqama shi genius ne.
Ashraf yafishi qoqari a sauran subjects din irinsu biology, english, business studies da dai sauran subjects din da babu calculation saidai sadeeq ya dokeshi a calculation don yadda kasan aljani haka ya iya lissafi hakan baqaramin 6ata ran ashraf yakeba don yasaba shine agaba a komai.
Hakan yasashi yin kishi da sadeeq musanmman idan yaga students naxuwa wajenshi solving din lissafi.
Shima sadeeq lura dayayi da yadda ashraf kemashi wani gani gani yasashi kama kanshi yanuna besan da wanzuwarshi ba.
Haka fa akacigaba da competition tsakaninsu kowa nason gwadawa dan uwanshi iyakarshi.
Saida suka shiga ss2 suka shirya shima sadeeq ne yanemi suyi abota don harga allah ashraf na burgeshi.
Kamar yadda yasaba saida yasha qamshi yana hura hanci sannan ya amince dukda can qasan ranshi murna yake don shima sadeeq na burgeshi don sadeeq badai raha da barkwanci ba, kwata kwata beda saurin fushi saidai idan aka quleshi beda kyau sa6anin ashraf da kamar akan wuya yake abu kadan ke hasalashi.
Ahaka suka qulla abota mai qarfi duk inda kaga daya sai kaga dayan har takai babu wanda besan da abotarsuba a fadin makarantar.
Alokacin allah yasama sana'ar kawu zaharadini albarka sosai don harya canza shago ya kama babba yana cigaba da sana'arshi ta kayan kitchen ashraf na dan kama mashi da tsaron shago duk sadda beda wani aikin yi.
Ahakan suka qarashe secondary school din lokacin baby ana primary.
Baby ta taso yarinya mai rigima da iyayi ga baki zai kamar parrot, rawar kanta yasa basa shiri kwata kwata da ashraf don kwa6darta yake idan tayimashi ba daidaiba babu abinda ya dameshi saidai yana sonta sosai.
Bayan result dinsu yafito ne suka samu daddadan albishir na scholarship da aka bada a school dinsu na mutane biyar qasar waje wanda ciki harda ashraf da sadeeq.
Farincikin ranar har rawa saida suka taka.
Cikin dan qanqanin lokaci aka gama shirin komai suka lula UK karatu.
Acanma bata sauya zaneba suna zuwa ba'a wani jimaba sukayi fice a school din saboda qoqarinsu ga hadin kai don kodayaushe tare suke dukda kamar kaji suke kodayaushe cikin fada suke donma sadeeq nada haquri.
Nanfa akaimasu caa don lokacin sun zama samari masu jida kyau da gayu dukda sadeeq ba fari bane amma baqinshi mai kyau ne ga uwa uba fara'a dake qarawa mutum kyau dayakeda ita.
Kan kace me yanmatan school din sukai musu caa dukda vasu cika tunkarar Ashraf ba don ba qaramin kwarjini yake musuba gashi fuskarshi ba wasa kullim a dinke take.
Sa6anin sadeeq da ba ruwanshi idan mace ta tinqareshi saiyace yanada aure harda 'ya'ya biyu qauye idan kuma tanason yayi nabiyu daita ya kaita qauye to.
Haka yake samu su rabu lfy dasu batareda ran kowa ta 6aci ba.
Ana haka kwatsam yaga ashraf na soyayya da suzy wata yar nigeria wanda itama karatu yakawota qasar saidai batada kamun kai ko kadan ga shiga ta fidda tsiraici.
Da farko yaso nisarda ashraf aibunta anma saiyaga kamar yana sonta sosai saiya qyaleshi saigashi basu wani yi nisaba suka rabu inda sukayi wani gaggarumin fada a filin makaranta sadda yaganta suna kissing da wani bayahude mai suna chris james
Daya nuna 6acin ransa akan haka saita fara bala'i wai bawani matsiyacin da zai hanata sakewa a school donma sun samu an biyamusu scholarship da a ina zasu ganta bare har raini yashiga tsakani?
Sosai abun ya6atawa ashraf rai don dakyar sadeeq ta janyeshi daga filin wanda yacika danqam da yan ganin qwam.
Tun daga lokacin kowa yakama gabanshi babu mai kula dan uwanshi har suka kammala abinda yakaisu suka dawo nigeria.
To anan ne zaharadini ya maidomasu dukiyarsu duka ganin ashraf ya mallaki hankalin kanshi.
Nan ummy taqi yarda suka amshi kudin kawai suka barmashi ribar dayaita juyawa hakan kuma ba qaramin dadi yayimasuba kuma hakan yaqaramata qima a idanun dangin mijinta.
Ahankali ahankali shima ashraf ya shiga harkar kasuwanci kasancewar shi dama ya karanta.
Nan sukayi hadin gwiwa da abokinshi kuma dan uwanshi sadeeq suka fara da kadan kadan har allah yasaka masu albarka suka bude tanqamemen company dinsu wanda suka samashi suna A.A ENTERPRISES LTD
wanda ahankali ahankali sukayi rassa a qasashe daban daban, talauci ya qaura a wannan ahalin suka koma kamar koma ince fiyeda yadda suke da.
Ashraf shima babanshi yabiyo a kyauta shiyasa kaf family dinshi babu mai kukan babu don babu babu din.
*CIGABAN LABARI*
sainaga ruwan comments tukun, naga alamun kwana biyu kun danyi sanyi🙁
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu nigeria🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
067
*CIGABAN LABARIN*
Wani matsanancin ciwon kai ya saukoma Ashraf nan take yayinda jikinshi har tsuma yake saboda tashin hankali.
Ummy is requesting na ya datse igiyoyin dake tsakaninshi da Saudart duka kuma she mean it don ya hango dagaske take acikin qwayar idanunta.
Jiyayi an dafa kafadarshi ta dama.
Ko be dagoba yasan sadeeq ne hakan yasashi lumshe idanunshi dasuka chanza kala yana sauraron bugun ziciyarshi.
Har lokacin sadeeq na dafe da kafadarshi saidai yarasa kalmar dazaiyi amfani dashi wajen kwantar mashi da hankali don shima hankalin nashi atashe yake don shima bega alamun wasa ko sassauci atareda ummy ba.
Sun dade ahakan sannan sadeeq yayi qarfin halin jawo hannunshi sama alamun yataso sutafi.
Babu musu yatashi dakyar suka juya suka bar falon sadeeq na janye da hannunshi shikuma yana biye dashi kamar raqumi da akala.
Zama ummy tayi bakin gado tana dafe kanta da hannu daya.
This is unbelievable, takasa yarda da abinda Ashraf ya gayamata.
Saudart? Diyar shamsu? This is super shocking.
Ya akayi takasa hango kammaninta dana mahaifiyarta? Dama kullum idan ta kalleta saitaga kamar ta ta6a sanin face din awani waje.
Ya akayi takasa ganewa duk tsawon wannan lokacin? Kenan da khadija suke waya lokaci bayan lokaci?
Ya akayi takasa gane muryarta? Ya akayi su kawu ibrahim suka kasa gane shamsu lokacinda sukaje nemama Ashraf aure?
Qarar budewar kofa dataji yasata dagowa daga dafe kan datayi tana kallon mai shigowa.
Baby ce tashigo idanunta jawur alamun taci kuka.
Kallonta tacigaba dayi harta qaraso kusada ita ta zauna qasa.
Shiru dakin ya dauka kafin baby ta dago a raunane.
"Ummy?.." sai kuma tayi shiru tana hawaye.
Itama ummin shiru tayi saidai batabar kallonta ba
"Ummy don allah karki raba yaya da aunty..please karki 6ata komai ummy, ki gyarashi instead" tafada cikin muryar kuka.
Nan ma shiru, ummy batace uffan ba.
"Ummy.."
"Get out" inji ummy ahankali
"Ummy please..."
"Out!!!" Ta daka mata tsawa wanda babu shiri ta miqe tanufi hanyar fita tana toshe baki.
Komawa ummy tayi ta jingina da kan gadon, tunanika kala kala na kai kawo azuciyarta.
********************************************
Zaune saudart take a garden din gidansu ta kafe waje guda da idanu .
Tunda tasamu labarin ummy tasan komai hankalinta yaqi kwanciya.
Koda yaushe cikin fargaba take na kar mamy taji lbr don tasan idan taji to ta kade har ganyenta.
Wayarta ce tasake daukar ringing a karo na ba adadi.
Duba takai ga wayar tana kallon sunan mai kiran yayinda takejin wani iri cikin ranta.
Baby ce, tun shekaran jiya take matsamata da kira da massages kala2 tana magiyar tayi picking din call dinta.
Sosai takejin ba dadi har cikin zuciyarta don harga Allah tana qaunar baby fiyeda tunanin mai karatu don ta dauketa ne kamar qaramar qanwar da batadashi.
Haka taita kallon kiran harya tsinke sannan tasaki ajiyar zuciya ta dauki wayar ta kasheta gabadaya don Allah yasani ko zata shekara tana kira bazata iya dagawa ba, to ta daga tace me?
Komawa tayi ta jingina da resting chair din tana lumshe idanu tana tunanin hanyar daya kamata tabi don kawo qarshen wannan qaddararren auren.
Kafin su iso wani zazzafan zazza6i ya lullu6eshi, jikinshi yayi rauu.
Ganin haka yasa sadeeq juya akalar motar zuwa gidansu don bazai iya barinshi ta kwana shi kadaiba acikin wannan halin.
Dakyar ya taimakamashi yakaishi dakinshi ta kwantar dashi sannan yafito yana amsa tambayar ummy daketa tambayarshi lfy?
Amsamata yayi da zazza6i yakeyi sannan yayi saurin fita saboda gudun ta jegomashi wata tambayar.
Tunani umma tafarayi to idan zazza6i yake ina matarshi dazai kawoshi nan?
Hakan yasata daukar wayarta tashige daki don kiran unmy taji ko lfy?
Be dadeba sai gashi yadawo hannunshi dauke da ledar magunguna yashige dakinshi.
Cikin bargo ya tadda Ashraf yashige ya qudundune sai rawar sanyi yake.
Remote din a.c ya dauka ya kashe a.c din dakin sannan ya haura kan gadon yana dan yaye bargon.
"Ya sallam" tafada jin hucin zafin daya dakeshi, ahankali yakai hannunshi a saman goshinshi yajishi rauu.
"Sorry friend" yafada cikin tausayawa
"Bari na amsomaka abinci kaci kasha magani kaji ko?"
Shidai be bude idaninshi ba bare ya amsa.
Tashi sadeeq yayi ya bude kofar yafita don samarmasu abinci.
A falo ya tadda umma zaune da alamu ma tayi zurfi a tunani, jin takunshi yasa ta dago tana kallonshi harya qaraso.
Sosa qeya sadeeq yayi yanadan sinne kai alamun rashin gaskiya sannan yace
"Umma akwai abinci?"
Nuna mashi dining tayi batareda tayi magana ba tana tunanin to meke faruwa haka wanda Hajiya Fatima tace maganar bata waya bace saidai tazo?
Fatanta dai allah yasa lfy.
Wucewa yayi dining din ya dibarmusu abincin sannan yayi sama yana sauke ajiyan zuciyar sa'ar dayaci ummy bata tambayeshi komaiba.
Dakyar yasamu ashraf yaci abinci don har saida umma tasa baki sannan yadanci yasha magani yakoma ya kwanta yana rufe jikinshi gabadaya da bargo.
A ranar dai barci rabi da rabi yayi marar dadi saidai alhamdullilah zuwa safe jikin yadanyi sauki zafin jikin ya rage sosai saidai har lokacin kanshi nadan sarawa.
Yanzu ma bawani breakfast din kirki yayiba yatashi tashiga wanka yafito yabude closet din sadeeq ya ciro wasu qanannun wanda da alamu sabbi mane ya fara shiryawa.
Fitowa sadeeq yayi daga wanka shima ya tsaya yana kallon Ashraf dake taje sumarshi gaban mirror.
Qarasowa yayi shima wajen mirron yana daujan wani lotion ya matsa a hannu yafara murzama jikinshi.
"Ina zuwa haka?" Ya tambayi ashraf dake taje kanshi
"Ummy" yabashi amsa a taqaice
"Ok bari nima na shirya na rakaka"
"No katafi company kawai"
"Why? You need me, don't you?"
"Yes, amma company yafini buqatarka, katafi kawai nima zanzo bekamata ace daga ni harkai ba wanda yajeba" yafada yana daukan turaren dudduba turarrukan sadeeq yanason ganin wanda yakamata yafesa don babu kalar nashi anan.
"Ok but take care, uhm?"
"Sure" yafada yana ciro daya daga cikin turrarukan ya feffesa sama sama don duk basuyi mashi ba kawai manage yayi.
"Bani key" inji ashraf yana saka wayarshi a aljihu.
"Kafini sanin inda suke" inji sadeeq dake cikin closet tana za6an kayan dazaisa.
Guntun tsaki ashraf yaja yanufi bedside locker yaja ya dauki daya daga cikin keys din ya maida ya rufe.
"Natafi" yafada yana nufar qofa.
"Take care" inji sadeeq.
Koda yafito babu kowa falo sai wata mai aiki dake goge centre glass table.
Saurin russunawa tayi ta gaisheshi bako kalletaba yafice yanufi hanyar parking space yana danna dan botton din dake maqale a key din hannunshi motar tayi tsuwa.
Yaje ya bude motar yashiga ya tada yafice daga gidan.
A parking space din gidan ya tadda baby zata tafi makaranta.
Jira tayi yayi parking yafito sannan ta gaisheshi ya amsa ba yabo ba fallasa yawuce.
Binshi tayi da kallo cikeda fargabar ko sun rabun da saudart din, jitake kamar takoma ciki tajiyo amma saita haqura kawai tashiga bayan motar driver ya tada suka fice.
Ya dade zaune a falon saidai babu ummy babu alamunta dukda ya aika wata yar aiki ta sanar daita zuwanshi.
Ganin zaman yafara isarshi yasashi tashi yanufi saman.
A kofar dakin ya tsaya yafara knocking ahankali.
Shiru... hakan yasa yasake knocking nanma shiru.
Saida takusan minti daya yana knocking sannan yaji muryarta a kausashe tana tambayar waye? Bayan yasan tasan ko waye don tasan kalan knocking dinshi.
Ajiyar zuciya yayi sannan yabude baki ahankali yace
"Nine ummy" yanajin wani banbarakwai don besaba ba.
"Kaine wa?" Tasake tambaya in the same husky tone.
Shafa kanshi yayi ahankali yana murmushi, lallai ummy kenan bata gane muryarshi ba take nufi.
"Ummy Danki ne Ashraf"
Tsaki yaji taja
"Ehen lfy?"
"Lfy lau ummy"
"To ya akayi?"
Shiru yadanyi yana kallon kofar da mammaki
"Bakomai ummy" yafada a sanyaye.
Shiru ya ratsa hakan yasashi cewa
"I want to see you ummy, please ki bude"
"Kazo da takadar?"
Gabanshi ne yafadi hakan yasashi yin shiru yana kallon ruffafiyar kofar.
"A'a" yafada ahankali
"Then leave my door karka sake dawowa saida takadar kaji nagayamaka"
"Ummy..."
"Leave!!" Tayi mashi tsawa daga ciki.
Babu yadda ya iya hakan ya juya jiki a sa6ule yabar kofar yasauko qasa yana jinshi wani iri.
Komawa yayi ya zauna inda ya tashi ya zubama hanyar stairs din ido yana kallo.
Ya dade ahakan amma babu alamun saukowar ummy.
Sosai yakejin ba dadi har cikin zuciyarshi.
Yasan yanada laifi amma saka sharri da sharri ai ba haramun bane.
Kuskurenshi daya shine sako wanda bata jiba bata ganiba a abun.
And now gashi abun ya rufta dashi, shi be cika burinshi na daukar fansaba, gashi allah ya jarabceshi da mugun sonta bayan mugun tsanar dayasan tayimashi ga kuma ummy na fushi dashi.
Tunawa yayi da abinda suzy tayimashi, koyaya saudart zataji idan tasan qazafin da akayi mata?
Sai jiyai be kyauta ba, na farko ya tilasta mata aurenshi ga wulaqanci da cin mutunci dayaita mata kala and to top it all ga mummunan qazafin zina da akayimata duk don ta dalilin shi.
Daga kai yayi ya kalli agogon dake manne a bangon falon yaga har shabiyun hantsi ta wuce.
Tashi yayi yagyara zaman t-shirt din jikinshi yaqara kallon hanyar stairs sannan yanufi hanyar kofar fita.
Motarshi yabude yafada ciki sannan yarufe ya tada ta fita daga gidan.
Tuqi yake in a normal speed har yazo ya parka bakin kofar gidansu.
Tsayawa yayi yana karewa kofar gidan kallo yanajin wani iri a zuciyarshi.
Ya dade ahakan sannan dakyar ya bude murfin kofar yaziro kafarshi wajen ahankali kingin gangan jikin suka fito ya maida kofar ya rufe yana qarewa gidan kallo.
Ahankali ya zagayo yana zube hannunshi cikin aljihu harya qaraso bakin gate din sannan yasa hannu yana bubbugawa ahankali.
Saida yayi bugu uku sannan yaji motsi daga ciki haka yasa yadanja baya yana kallon kofar.
Qaramar kofar gate din aka bude sannan fuskar buzun ta bayyana.
Tsayawa yayi yana qaremashi kallo shima ashraf hakan take awajenshi.
"Lfy?" Inji buzun yana dan leqen motar bayan ashraf
"Lfy lau, barka"
"Barka dai" buzun ya amsa.
Dan sa hannu ashraf yayi yana dan sosa kai
"Erm s..Saudart nanan?"
Qara qaremashi kallo yayi wanda har hakan yafara kule ashraf.
"A'a tafita, lfy?"
"Lfy" ashraf ya amsa sannan yajuya yanufi motarshi yana jan guntun tsaki.
Binshi buzun yayi da kallo harya bude yashiga ya tada yatafi sannan ya ta6e baki ya maida kofar ya rufe.
Tuqi yake amma yarasa inda kuma zai nufa, anya ma buzun nan gaskiya ya fadamashin batanan din? To mema ya hanashi tsayawa confirming?
Tsaki yasake ja, he can't believe yau yaje kofar gidan babban maqiyinshi haryasa hannu yayi knocking din kofarshi.
Karya corner yayi ya dauki hanyar bakery dinta yana addu'ar allah yasa tanacan.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Zaune take kan kujerar office dinta hannunta riqeda pen jujjuyashi take a paper.
Haka kawai taji yau tana sha'awar zuwa bakery din, tagaji da zaman kadaici da yawan tunani shiyasa ta yanke shawarar zuwa bakery din ko zata samu sauqi amma tunda tazo bata iya komaiba sai zaunen datayi tana jujjuya pen tana karanta wasikar jaki.
Yau ne wa'adin data dibarma sadeeq yacika, amma babu alamun nasara.
Yanzu ya zatayi? Tasan ko giyar wake tasha bazata iya kai case dinnan court ba don kamar ta kwancema kanta zane a kasuwa ne.
Bakowa takejiba sai mamy, koya ta tuna daita saitaji zuciyarta tayi rawa saboda fargaba.
Sosai take cikin damuwa dukda tana qoqarin dannewa ko don daddy daya fita shiga damuwa yake kuma blaming din kanshi a koda yaushe.
Knocking akayi a kofarta hakan yasa ta saki nannauyan ajiyar zuciya takoma ta jingina da kujerar.
"Yes? Come in"
Ahankali aka turo qofar aka shigo.
Maryam ce sanye da apron fari hannunta riqeda da littafi da pen.
"Unhun?" Inji saudart tana lumshe idanu.
"Ma'am kinyi baqo"
Tsaki tadanja, itafa bata cikin mood din ganawa da baqi
"Ok su shigo but please duk wanda tasake zuwa ace banzoba ok?" Tafada tana dan dafe kai.
"Ok ma'am" tafada tana fita daga office din.
Jimm kadan aka sake bubbugo kofar.
Tsaki tadanja
"Come in"
Maryam ce tasake shigowa da mutum biye a bayanta.
Saida mutumin yashigo sannan tajuya tafita.
Dagowa tayi daga rubutun datafara kafin su shigo tadan kalleshi ta maida idonta kan littafin tana cewa
"You are welc..." cak maganarta ta tsaya da wani abu yazo mata a brain.
Saurin dagowa tasakeyi cikin rashin gasgata da mammaki bayyananne.
Dumm.. gabanta ya yanke yafadi ganin shi dinne jingine da kofa ya harde hannunshi ya zubamata piercing eyes...✍
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
068
Mutuwar zaune tayi tana kallonshi idanunta adan ware alamun mammaki qarara a fuskarta.
Binshi tayi da kallo daga sama har qasa.
Sanye yake cikin qananun kaya, tsadadden jeans trouser da top ash mai quntun hannu wanda ya tsaya daidai damtsenshi sai hular da rigar kedashi daya saketa baya, sosai packs dinshi suka bayyana tacikin rigan kasancewar rigar tadan kamashi.
Yar sumar kanshi a kwance luff sai qyalli take, sosai yaqara mata kwarjini da haiba
Shima a 6angarenshi kallonta yake yana jin wani irin shauqin dabe ta6a jiba na dibarshi yayinda qaunarta ke qara hauhawa acikin birnin zuciyarshi.
Jiyake kamar ya saceta ya gudu don kwana biyun nan dayai beganta ba gani yake an chanzata.
Sanye take cikin baqar Arabian gown datasha stones agaba kanta yane da gyalen rigar, fuskarta daukeda simple makeup daya qara fiddo ainahin natural beauty dinta.
Ita tafara janye idanunta akanshi tana blushing sanadin tunawa da abinda yafaru tsakaninsu a haduwarsu ta qarshe.
Nan take ranta yaqara dagulewa, ranta na 6aci.
Maida hankalinta tayi ga rubutun datake wanda ayanzu batamasan me take rubutawa ba.
Dagowa yayi daga jinginar dayayi da kofar yana kallon yadda taqara tamke fuska tana cigaba da rubutunta.
Takowa yayi ahankali cikin usual takunshi na qasaita harya qaraso gaban table dinta.
"May I?" Yafada yana kama kan kujerar dake facing din table dinta.
Bata dagoba haka zalika bata ansaba amma hankalinta kacokan na kanshi tana sauraron duk wani motsi nashi.
Murmushi yasaki sannan yaja kujerar baya ya zauna ya jingina daita hannayenshi harde a faffadan qirjinshi yana zubamata idanunshi masu mugun takurata.
Jinta tayi duk atakure don sosai idanunshi ke piercing har cikin zuciyarta don har rawa rawa hannunta datake rubutunda ma bata san nami takeba keyi amma haka ta daure taqi dagowa dukda tanajin yawon idanunshi a fuskarta.
Binta fuskarta yake da kallo yana inspecting every part of the face, jiyake kamar yau yafara ganinta.
Baya tunanin yata6a ganin macen data kaita komai.
She's just too perfect, damn perfect.
Jin kallon nason yin yawa yasata dagowa at last ta kalleshi.
Sarqewa idanunsu yayi waje guda wanda saida hakan ya haifarmata faduwar gaba sai tayi saurin janye idanun nata gefe tana tsuke fuska.
"Yes? How may i help you Mr?" Tafada in a harsh voice.
Murmushi yayi mai sauti wanda hakan yasata kalloshi takuma kauda kai.
"Good Afternoon ma'am" yafada in a cool voice yana kafeta da idanu.
Wani banbarakwai taji wanda hakan yasa tasake dagowa ta kalleshi.
Yau ita A.A ke gaisarwa? Harda wani *ma'am*?
Hmm wani sabon salon wulaqancine da izgilanci halan? Anyway koma mezaiyi ko zece bazai dameta ba itadai burinta ta rabu da alaqaqai daganan yaje ya rungumi transformer for all she care.
"Yes? Get straight to the point, as you can see am busy" tafada avoiding his gaze.
Guntun murmushin nan na gefen baki yayi.
Bata chanza ba, she's still the proud cute princess, the angry bird.
"Am sorry" ya furta ahankali.
Dagowa tayi ta kalleshi again cikin mammaki.
Wait kodai a make yake? Tambayar datayima kanta kenan.
"Am so sorry...very sorry" yasake fada wanda kallo daya zaka mashi kasan har cikin zuciyarshi yake fadin haka.
Shiru tayi tana kallonshi batareda ta iya cewa komaiba tana wondering acikin zuciyarta anya A.A data sanine wannan? The proud rude A.A?
Ganin yadda ta kafeshi da idanu yasa yayi dan murmushi wanda yaqara mashi kyau sosai
Ya miqa hannu ahankali ya amshi pen din hannunta yajawo file din gabanta yana dubawa.
Galala tabishi da kallo kamar wata doluwa tana kallon the amaziest thing she've ever saw.
Juya file din yayi baya inda ke blank babu rubutun komai akai ya dora pen asama yanadan cije qasan le6enshi.
"Am sorry.. for everything" yafada yana kanshi aqasa yana rubutu itakau saudart ta maidashi t.v ko kyaftawa batayi.
"For coming into your peaceful life... for not releasing how worthful you are... for the harrasment and tough time i made you went through... for everything.
Words can't express how sorry I am... hope you'll find it in your heart to forgive a helpless soul... hope you'll give me another chance" ya tsayar da rubutun still idanunshi nakan file din yana kallon rubutun dayayi wanda duk maganar dayayi ne ciki.
Ajiye pen din yayi saman file din sannan ya dago a tsanake ya kalli saudart dako kyaftawa batayi daga kallonshi, hankalinta yakasa daukar abinda ke faruwa.
"Mafarki nake?" Tambayar datayima kanta kenan.
"No" ashraf ya amsa mata don afili tafada batareda ta saniba.
"Ba mafarki bane ba, dagaske ne, am here... seeking for your forgiveness *SAUDARH*, nasan ni mai laifine awajenki, inajin wani iri... wani iri idan na kalleki, am shy, am sorry" yafada yana lumshe idanu yayinda zuciyarshi ke gudu.
Tabbas wani irin yakeji don tunda yasan kanshi bezai iya tuna sadda yazauna yaba mutum haquri kamar hakaba, wani abu yakeji a zuciyarshi kamar kunya kunya kamar ya6ace daga office din ya huta.
Itama saudart din wani iri takeji.
Wannan ba A.A din datasani bane, bawanda tasaba dashi bane, the rude, proud, wicked peacock.
Sam bashi bane.
Shiru office din ya dauka kowanne feeling awkward, babu wanda ya iya magana acikinsu don basusan abinda zasu sake cewa ba.
Saida suka kusa mintuna biyar ahakan sannan saudart da tundazu ke kallon yatsunta tana wasa dasu ta dago ta kalleshi shima daidai ya dago sai suka hada idanu.
Kauda kai tayi tareda sakin silent ajiyar zuciya sannan ta muskuta ta fara bude wani file dage daga gefen table din shikuma yabita da kallo cikin tsantsan qaunarta.
Zaro wata farar takarda tayi qall wanda babu komai aciki ta turomashi a gaba ta dauki pen din gabanshi ta dora akai.
Binta yayi da kallo saikuma ta kalli takardar da pen din sannan yadago yasake kallonta yaga itama shi take kallo.
"Let's end this" tafada ahankali.
"Ka kawo qarshen komai sai in yafemaka" tafada tana kallonshi.
Shiru yayi yana kallonta batareda ya iya cewa komaiba don yadda zuciyarshi ke gudu.
Kenan tana still kan bakanta? Kenan she still hate him dukda yayi stooping low yabata haquri yakuma nemi yafiyarta?
"Ka rubutamin saki na then I'll forgive you Mr A.A" tafada tana dan janye ido ganin yadda ya kafeta da idanu.
"Did you still hate me?" Ya tambaya cikin wani yanayi.
Kallonshi tasakeyi sannan ta kauda kai
"Ba maganar hatred mukeba"
"Tell me, kin tsaneni ko? Kinaji kamar ki kasheni ko?" Ya tambaya mood dinshi na canzawa.
"Why? Nina halliceka dazanji kamar in kasheka? Am talking about contract dake tsakaninmu ne not hatred, I want to be free again, inason jina yadda nake ada"
Shiru Ashraf yayi yana kallon takardar gabanshi sannan yadauki pen din yariqe sannan ahankali yadora kan takardar yafara rubutu.
Wani gauron ajiyar zuciya tasaki tana fesar da iska daga bakinta, farinciki na bayyana akan fuskarta.
Bewani dadeba yagama rubutun ya linke takardar ya turamata agabanta yana dora pen din akan takardar yakoma ya jingina da kujerar yana kallon fuskarta that is litted with happiness.
Ajiyar zuciya tasake saukewa sannan tasa hannu ta dauke pen din ta ajiye gefe sannan tadauki paper din tafara warware linkin fuskarta dauke da murmushin da batasanma tanayiba shikuma ashraf ya kafeta da ido yana kallon yadda fuskarta ke fitarda annuri just because yabata takarda.
Dama har haka ta tsaneshi? Tambayar dayayima kanshi kenan yayinda tausayin kanshi ya lullu6eshi.
Ahankali fara'ar fuskarta tafara gushewa ganin abinda aka rubuta sa6anin abinda tayi tunanun gani.
Cikin tsarraren handwriting taga an rubuta:
*I CAN'T LIVE WITHOUT YOU😢 PLEASE GIVE ME ANOTHER CHANCE👏SECOND CHANCE..*
Qara gwala idanu tayi tana qara karantawa unbelievable
Dagowa tayi tana kallonshi in shock.
"Yes.. i need a second chance" yafada yana kallonta
"Second what? Meye kake magana akai?" Ta tambaya still in shock plus 6acin ran daya fara tasomata daga qasan zuciya.
"Second chance to prove my *love* to you"
"What!"
"Yes, *I love you* *I so much love you*"
***************************************************
"This is unbelievable!" Inji umma cikin mammaki
"Hmm kema kya gani Hajiya zainab, haryanzu nakasa dawowa daidai wlh" inji ummy tana sauke ajiyar zuciya.
"Allah mai iko, ji yadda ya hadaku kuma ta hanyar baku ta6a zatoba, tabbas ashraf yayi kuskure be kamata ya saka sharri da sharri ba, amma abinda yayi bekai girman wannan hukuncin da kika yankemashi ba don yayi nadama kuma ai shima a wani 6angaren yanada gaskiya, shifa yayi sanadiyar mahaifinshi dole ya tsaneshi, idanma laifinne ai sadeeq ne me babban laifi tunda maimakon yabashi shawara ya nusardashi saiya biyemashi, zai dawo yasameni ne" inji umma tana kwafa.
"A'a hajiya zainab babu laifin sadeeq, koda bebashi goyan bayaba saiyayi abinda yayi niyya nasan halinshi sarai, kuma batun aurensu dolene ya rabu don idan nabari abin ya dore banyi adalciba, kobe fadaman ba nasan ba qaramin abu yakema saudart ba, nasan halin ashraf, idan ya tsani abu yana tsanarshine da dukkannin zuciyarshi. Nasan tasha wahalarshi dukda nasan ba dukkan abinda yaimata ba yafadaman, bata sonshi tayaya nikuma zan jajirce akan dorewar auren? Ita zata cutu dole, ga wahalar datasha abaya and at the end taqare da baqinciki? No badaniba" inji ummy tana girgiza kai
"Amma sai inga gwara abarsu Hajiya fatima, Allah kadai yasan dalilin dayasa ya hadasu kuma"
"Hajiya zainab inason saudart, ina sonta kamar yadda nakeson baby, bazanso wani abu ya cutar daita ba.
Dukda sanin diyar wanene hakan be rage son danake mataba daidai da kwayar zarra, bazan ta6a barin tayi zaman dazata cutuba"
"Hmm dukda haka dai mubi sannu, tsakanin ma'aurata sai allah, kar kizo kiji kunya aqarshe" inji umma tana dariya.
Murmushi ummi tadanyi sannan tace
"Inason naje gidan khadija, inason ganinta"
"Hakanma yakamata"
"Please ki gayawa Abbansu sadeeq yabarki ki rakani gobe, i really need to see her"
"Insha allah zan gayamashi amma kinsan gidanta ne?"
"A'a amma baby tasani, saita kaimu"
"To allah yakaimu lfy"
Da ameen ta ansa sannan suka cigaba da tattaunawa akan lamarin...✍
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲
Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
069
Galala tayi tana kallonshi babu ko kyaftawa yayinda kalamanshi kemata amsa kuwa akunne.
Shima kallonta yatsaya yi yanason ganin reaction dinta.
Ga mammakinshi saiyaga tasaki murmushi mai sauti ta janye idanunta daga ksnshi tana chuckling don ita nothing make sense to her, this is total madness.
Murmushi mai ciwo yayi ganin yadda take dariya qasa qasa.
Wato ga mahaukaci, kodayake duk wanda yasan yanayin zamansu ada yakuma ji abinda yakecewa yanzu saiya yimashi daukan mahaukaci.
"Is it funny?" Ya tambaya yana kallon yadda dimple dinta ke lo6awa.
"Very funny" tafada cikin dariya.
Murmushin nan nashi yasakeyi
"It may sound funny amma am not joking..am serious"
"Yes, it's a joke, a cheap joke" tafada murmushi akan fuskarta
"Saidai yanzu ba lokacin barkwanci bane, we're discussing a serious issue, magana ta hankali" tafada tana gimtse fudskarta daga murmushin datake.
Ajiyar zuciya ya sauke, dama yayi tsammaci hakan ko fin hakan ma
"Am damn serious *SAUDARH*, nasan bata haka yakamata in fadamakiba, wataqila I sound straight forward or non-romantic...amma ki yarda dani, abinda nake fada yana zuwane from the bottom of my heart.
Saudart I love you, I love you so much.. i can't deny it anymore" yafada emotionally.
"Really? Yaushe? Kuma tayaya?" Tafada cikin izgili tana mashi wani kallon sama sama.
"I don't know... bansan how and when ba.. all i know is Ina sonki"
"Mtcheew, look Mr man, kamar yadda kagani ina busy lokacin daka shigo, inada aikin yi dayawa so karka nemi rainamin hankali.
This damn thing should come to an end now! It ought to...nagaji!" Tafada fuskarta nayin jajaja don 6acin rai.
"Saudart..."
"Enough!" Ta katseshi tana numfashi ahankali ahankali, idanunta na forming din ruwa.
"Kai kafaro komai, now end it!" Tafada cikin cracking voice
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take kokowa wajen ganin ra tare hawayen dasuka cika idanunta daga zubowa.
Yasan yadda takeji, she's in pain, kallo daya zaka mata kagane hakan.
Cikin kwantar da murya wanda yafi kama da rad'a yace
"Saudart I can't... bazan iyaba, nasan sonki jarabtace daga ubangiji, bansan sadda nafara kuma banajin akwai ranarda zan bari.... wannan hannun..." yafada yana kallon tafikan hannunshi
"Bazasu iya rubutamaki abinda kikeso ba, yatsuna bazasu iya riqe pen ba dasunan datse abinda yayi bonding dinmu..am sorry"
Dafe kanta tayi cikin tsananin takaici da baqinciki ta sadda kanta.
"Saudart i know kin tsaneni, kibani dama...second chance don na nunamiki soyyayar danake miki, second chance don goge baqin fenti nawa acikin zuciyarki.. Let me love you"
Hawayen datake dannewa ne suka kufcemata suka gangaro kan kumatunta.
Jin kowanne kalma nashi take kamar digar darma a kunnuwanta.
Tarasa meta tsaremashi, wane laifi tayimashi daya za6i quntatawa rayuwarta.
Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da rinnanun idanunta dake sheqin hawaye, ziciyarta na zafi.
Shima kallonta yake yanajin kowanne digar hawayenta harcikin zuciyarshi, idanunshi suka fara chanza kala yanajin kamar shima yafara zubda nashi hawayen.
"Why?" Ta tambaya cikin rad'a
Lumshe idanu tayi taba hawayen dasuka cika idanunta damar gangarowa sannan tabude tasake kallonshi
"Who are you?" Tafada muryarta na rawa.
"Dama ka sanni ne? Na ta6a maka wani abu ko? You're purnishing me right?" Tafada tana lumshe idanuwanta tana shesheqan kukanta marar sauti.
Kamo tender hannayenta dake kan table yayi ya riqe yana kallonta shima zuciyarshi na zafi.
Bude idanunta tayi ta kalli hannayenta dake cikin nashi wanda jitake kamar rushin garwashine jikin hannun sannan tadago takalleshi batareda tayi qoqarin janye hannunta ba.
"Ka tsaneni ko? Ka tsani ka ganni cikin farinciki da walwala ko? Tell me" tafada muryarta nadan siezing.
"No, never! Bazan iya tsanarkiba... ban ta6a tsanarkiba" yafada almost cikin rada yana kallonta da idanunshi dasuka kada.
"Then..why are you...hunting my life? Me..nayimaka?" Tafada wasu sabbin hawayen na gangarowa daga idanunta.
"Babu.. babu komai, nine dai nayimaki...am sorry for coming into your life" yafada softly still hannunshi riqeda nata.
Sadda kai takumayi tana dan shesheqan kukanta marar sauti tanajin duk duniya babu wanda zata yiwa tsana kwatankwacin wannan datakema ashraf.
Murza hannunta yayi ahankali yana jin shesheqanta harcikin ranshi.
"Saudart please stop crying, nasan you hate me, nasan kin tsaneni, please kibani dama na musanya wannan qiyyayar zuwa soyyaya..please"
Dagowa tayi ta kalleshi da jiqqaqun jajjayen idanunta
"Dagaske?...dama kasan na tsaneka?" Ta tambaya tana kallonshi
"Yes saudart, kinsha fadamin kuma nasha hangowa acikin qwayar idanunki...dan allah kiban wata damar, please"
Kada kai take ahankali tana hadiyar abinda ya tokare mata maqoshi
"Zaka iya misalta adadin qiyyayar danake maka?" Tafada tana kafeshi da jajjayen idanunta.
Shiru yayi yana kallo yadda ta kafeshi da idanu
Girgiza kai yayi ahanksli kamar yayi kuka
"A'a" yafada helplessly a raunane
Itama girgiza kanta tafarayi wasu sabbin hawaye na 6allemata.
"Nima haka... baxan iya misalta qiyyayar danake makaba ada.. saidai yanzu ina iya cewa...qiyyayar danake maka ada batakai kaso daya cikin kaso goma danake makaba yanzu.
Ashraf I hate you! I hate you so very much! Ban ta6a tsanar wani mahalukiba yadda na tsaneka kuma banajin zan ta6a tsanar wani kamar haka... i hate you more than death itself. I hate you!!!" Taqarashe cikin kuka mai sauti sosai ta sadda kanta kan table tanayi da dukkanin zuciyarta.
Lumshe idanunshi yayi ahankali wani zazzafan hawaye ya gangaro kuncinshi yanajin kamar ya cire zuciyarshi ya huta saboda radadin datake mashi.
Sakin hannunta yayi ahankali jikinshi na rawa rawa yana sauraron sautin kukanta yana kallon yadda take jujjuya kanta akan table.
"Leave, banason ganinka! Please leave!!" Tafada cikin ihun kuka.
Rufe fuskarshi yayi da tafikan hannu yana tamke idanunshi yanajin dama shima zai iya kukan da babu abinda zai hanashi 6are nashi bakin yafara shar6a nashi.
Tashi tayi da sauri ta shige toilet din office dinta aguje cikin kuka sosai ta rufo kofar.
Maida kanshi yayi shima kan table din yanadan jujjuyawa yana ambaton sunan Allah acikin zuciyarshi don jiyake kamar zata tarwatse.
Wajen sink ta qarasa dagudu ta dafashi tana gunjin kukanta.
Ashraf yazame mata qarfen qafa, yazame mata alaqaqai, yana naiman karta lokacinta beyiba.
Yazatayi dashi? Yazatayi ta rabu dashi? Wannan wace iriyar qaddarace?.
Yadade ahakan yana ambaton sunan allah a zuciyarshi harya samu tayimashi dan sanyi sanyi.
Tashi yayi ahankali yana dafa kanshi da ciwon kai yadawomashi sabo yajuya yanufi hanyar fita dafe dakai.
Bude kofar yayi yafita batareda yama iya rufo kofarba ya ratsa tacikin mutanen daketa hidiman gabansu harya samu yafito waje.
Kamar dan qwaya haka ya qaraso wajen motarshi ya bude yashiga sannan yarufo ya saka key hannunshi nadan rawa rawa ya tada motar sannan yawani figeta yabar harabar wajen da wani irin speed.
Tuqi yake amma har wani biji biji yake gani sanaddiyar saran da kanshi kemashi.
Wayarshi yaciro da hannu daya ya kunna yashiga contact yayi dialling din number sadeeq yana cizon le6en qasanshi da qarfi.
Saida takusan tsinkewa sannan aka daga.
"Hello?" Inji sadeeq daga can 6angaren
"Sadeeq she hates me, ita dakanta tacemin bata iya misalta qiyyayarta agareni ba...sadeeq I want to..die" yafada cikin cracking voice.
Miqewa sadeeq yayi daga zaunan dayake a office ba shiri jin yanayin maganar ashraf.
"Ashraf! Menene? Ummy ce? Talk to me!" Yafada a gigice yana daukar keys din dake kan desk dinshi yana nufan kofa.
"Saudart ce sadeeq, i love her...she hate me...zuciyata zafi" yafada still yana tuqin
"Subhanalillah! Ashraf kuka kake? Tell me ina kake?" Inji sadeeq yana nufan elevator dagudu.
Hannu ashraf yasa yashafo kumatunshi ya kalla saiyaga lema alamun kukan yake.
Be amsaba sai katse wayar dayayi yajefata bayan motar yaqara speed kamar zai tashi sama.
Jin wayar ta tsinke yasashi saurin qara bin jiran amma bata shiga hakan yasa hankalinshi qara tashi.
Hannu na rawa ya danna last floor elevator din yabude yafada ciki yana addu'ar allah ya tsare ashraf don beta6a jinshi cikin irin wannan yanayin ba.
"And nagayamashi zan rakashi amma yaqiya, ai ga irintanan" yafada restlessly yana dan zagaye zagaye a elevator din yanajin kamar va tafiya yakeba.
Elevatorn ba tsayawa yayi saurin fitowa yayi parking space dagudu ya bude motarshi yashiga ya kunnata yayi reverse.
Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta dago ahankali ta kalli mirror din jikin sink din tana kallon yadda fuskarta tayi jaa ta kumbura.
Kunna fanfon tayi ta tara hannunta ta debi ruwa ta wanke fuskarta sannan tajawo hand towel dake rataye awajen ta tsane fuskarta sannan tafito tana dan layi saboda yadda kuka yayi exhausting din qarfinta.
Jakkarta kawai tabude ta watsa wayoyinta aciki sannan ta zage ta ratayeta tasaka sunglass dinta wanda yarufe asirin kumburan da idanunta sukayi tafito don batajin zata iya qara koda minti dayane a bakery din.
Haduwa sukayi da maryam data fito daga wani office
"Ma'am fita zakiyi?" Injita tana kallonta.
Kanta kawai ta iya kadamata ta fice da sauri itama ta bude motarta tashiga ta kunna itama tafice daga bakery din...✍
Manage please👏
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Happy edl-mubaraq fans🧚🏻♀️
Fatan anyi sallah lfy, fatan kuma ba'ayiwa nama cin rashin mutunci ba😏
Kodayake ai ko kunyima zai rama ne😆
Am back again, masu cigiyata ngd, masu kira kudos🤙🏻 Ashaanty loves you😍
070
Tuqi yake amma yarasa inda zai nufa, besan inda zai fara nemanshi ba.
Fatanshi daya shine Allah yasa kar yace zaiyi driving acikin wannan halin.
*saudart ce sadeeq, I love her... she hate me... zuciyata zafi*
Maganar Ashraf tadawo mishi.
Kenan sun hadu? Definately sun hadu, yabama kanshi tabbaci.
Karya motarshi yayi yakama hanyar gidansu saudart.
*wannan hannayen.... bazasu iya rubutamaki abinda kikeso ba*
*yatsuna bazasu iya riqe pen ba dasunam datse abinda yayi bonding dinmu ba*
Cize le6enta naqasa dasukayi jaa saboda kuka tayi tana lumshe idanu don ba hawayen dasuka qara forming a idanunta damar gangarowa.
Zafi takeji a zuciyarta marar misaltuwa, she can't believe yau itace abin wasa, abin toying.
Ita zai nunama isa da iko? Dama yace zai nunamata koshi wanene, dama abinda yake shiryawa kenan?
Dama burinshi ya daqilemata duk wani farinciki nata?
Burinshi ya ganta cikin dawwamammen qunci?
Bayan hannu tasa ta sharce hawayen fuskarta ta cigaba da tuqin wanda allah allah take ta isa gida don tuqin ma yafara gagararta.
Jin motsin mutum na kusanto gate din yasashi tsagaitawa da knocking din yana kallon ruffafen gate din.
Qaramar kofar gate din aka bude fuskar maigadin ya bayyana.
Ganin sadeeq yasashi washe baki don be manceshi ba kuma ranan dazai tafi saida yaimashi alhairi.
"A'a? Kaine?"
Shima sadeeq cikin fara'a yace "nine wlh, barka da warhaka"
"Barkanka dai, ya aiki?"
"Alhamdulillah" yafada yana gyara tsayuwarshi
"Erm... tananan?" Ya tambaya
"Wlh kau yau kayi rashin sa'a, yau tunda safe hajiya tafita, dazunma wani yazo nemanta saidai tafiya yayi"
Dan daga gira sadeeq yayi
'Wani? Could that be Ashraf?'
Uban horn din da aka danna ta bayanshi ya katse mashi guntun tunaninshi.
Tare suka waiga shi da maigadin don ganin wanene ke shirin dodemasu kunnuwa.
"Yar halaq gatanan" inji maigadin yana komawa ciki da sauri don budemata babban kofar gate din.
Bin motar sadeeq yatsaya yi da kallo na yan daqiqu sannan yatako a nitse ya nufo motar.
Gab da zai karaso ta sake tada motar ta figeta tashige cikin gidan kasancewar har anbude gate din tana badeshi da kura.
Bin motar yayi da kallo yadan girgiza kai sannan shima ya maramata baya.
Sadda yashigo harta fito daga motar.
Kallo daya zaka mata kasan ba lafiya ba.
Zuwa tayi zata giftashi ta wuce batareda tanuna tasan an dasashi awajenba
"Miss saudart.." yafada ganin zata wuce
Ko iskan daya kwasoshi bata kallaba tacigaba da tafiyarta.
Binta yayi yana cewa
"Good day miss saudart.. please listen to m..."
Kasa qarasawa yayi ganin ta tsaya cak daga tafiyar datake kamar wanda aka tsaida da remote.
A nitse ta juyo ta kalleshi ta cikin sunglass din idanunta sannan ta kalli saitin gate ta kwalawa maigadi kira cikin muryar da bata ta6a yimashi amfani dashi ba.
Da sauri maigadin ya iso wajensu yana dan russunawa cikin girmamawa.
"Wayace ka dinga shigo da kowacce shara agidan nan?" Ta jefa mashi tambayar cikin tsuke fuska.
Dan dagowa maigadin yayi ya kalleta a mammakince don wulaqanci ba halin saudart bane shi shaidane.
"Ayi haquri.. gani nayi.."
Katseshi tayi ta hanyar daga mashi hannu.
Sannan ta nunashi da car key din hannunta.
"Kasake barin irin wadanan gabbages din shigowa gidannan... believe me abincinka yaqare a gidannan, now ka gwadamashi hanyar fita"
"To..to hajiya insha allah" inji maigadin a sanyaye.
Juyawa tayi zata wuce saikuma ta tsaya daga takunta tana dan cije le6en qasa.
Juyowa tayi a nitse ta kalli sadeeq dashima ita yake kallo expressionless.
Cikin sanyin murya mai shige da rada tace
"Zan gwadamashi... zan gwadamashi mata ma suna suka tara, zan gwadamashi ba kowa zaka iya takawaba kuma ya taku... he's playing with fire and he'll get burns. I'll made life a living hell to him.... *mark it*"
Tana kaiwa nan tajuya tawuce.
Binta da kallo sadeeq yayi harta shige sannan ya dauke kai daga barin kallonta yana sauke ajiyar zuciya.
Maigadi dake tsaye haryanzu yace
"Kayi hqr amma wannan ba halin hajiya bane, qila 6atamata rai akayi waje"
Kallon maigadin sadeeq yayi sannan yadan saki murmushi
"Ba damuwa ai" yafada yana saka hannu cikin aljihu ya fiddo kudi yaba maigadin.
Qin amsa maigadin yayi dafarko saida sadeeq ya 6atarai sannan ya amsa yana kwarara mashi godiya sannan yarakashi haryaga tashin motarshi sannan ya maida gate din yarufe.
Ahankali take taka stairs din kanta qasa harta kai qarshe sannan ta isa bakin kofarta tasa hannu cikin sanyi ta murda yabude tashiga.
Maida kofar tayi ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sakin jakkar hannunta a wajen tareda lumshe idanunta dasuke mata yaji yaji tsabar zubda hawaye.
Wannan wacce iriyar qaddarace? Ashraf qaddarartace tasani, tun shigowarshi arayuwarta tarasa walwalarta da farinciki.
Tasan qar6ar kowacce iriyar qaddara yana cikin cikon imani amma bata tunanin zata iya qar6ar wannan qaddarar.
Bazata iya zama cikin qunci ba tsawon rayuwarta ba, bazata iya zama da wanda ita kanta batasan iya tsanar datake mishiba.
Wannan be dauki dan adam a bakin komaiba, wanda besan darajar iyaye ba.
Zata iya rungumar kowacce qaddara amma banda wannan, banda wannan baqar qaddarar.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Tuqi yake amma kallo daya zaka mashi kaga damuwa qarara a fuskarshi.
Wannan wacce iriyar qaddarace? Tausayi suke bashi dukkansu, yasan they are having tough time dukkansu.
Kofar gate din gidan yatsaya akayi scanning dinshi sannan ya shiga.
A mammakince yake kallon motar dake tsaye a passage wanda ko arxiqin a qarasa da ita parking space bata samuba.
Saurin tsaida motarshi yayi yafito yanufi motar.
Kasancewar tinted ne glasses din motar be hangen naciki hakan yasashi bubbuga glass din 6angaren driver ahankali.
Shiru... hakan yasashi qara bubbugawa nan na tsit.
Duqowa yayi yana leqe ta baqin glass din kozai iya hango mutum ciki.
Hangowa yayi dishi dishi kamar mutum hakan yasashi sake bubbuga glass din.
Zaune yake cikin motar kanshi kife da sterring din motar.
Dakyar yasamu yakawo kanshi gida inda ko qarasawa parking space yakasa ya tsaya anan.
Duk bubbugar glass din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka.
"Ashraf...Ashraf open up" inji sadeeq yana bubbugawa yana leqenshi at the same time.
Shiru ashraf yayi don be iyawa, da yana iyawa da be dauki tsawon lokaciba a zaune haka ba.
Ganin beda niyyar motsawa yasa sadeeq miqewa yanufi cikin gidan da sauri, shi tsoronshi ma kar ace asume yake.
Dakin ashraf yashiga ya nufi locker dayake aje keys dinshi.
Kwasosu yayi batareda ya tsaya dubawaba yayo waje cikin sassarfa.
Agefen drivern yakoma ya saki keys din qasa yashiga lalluben spare key din motar.
Dakyar yagano key din sannan ya tashi ya zira a motar yabude.
Gabanshi ne yafadi ganinshi zaune kanshi kife da sterring.
"Subhanallilah! Ashraf?" Inji sadeeq yana dagoshi.
Kamar marar lakka haka ya fadamashi ajiki yana sauke numfashi mai nauyi.
"Ashraf? Are you ok?" Inji sadeeq yana nishi dakyar a dalilin nauyin da ya sakarmashi.
Shiru kuma be bude lumsassun idonshi ba.
Ganin haka yasashi qoqarin fiddoshi a motar.
Dakyar ya fiddoshi ya ratayo hannunshi a wuyanshi yana qoqarin gyara tsayuwarshi.
Sake tamke idanunshi ashraf yayi saboda ranar dake hasko saitin fuskarshi wanda hakan ke qaramashi sarar da kanshi kemashi.
Dakyar sadeeq yasamu yakaishi falon ya kwantar dashi kan three seater ya dora kaffafunshi sama tareda zaremashi takalmin kafarshi sannan yadawo saitin fuskarshi ya zauna ya riqo hannunshi cikin tausayawa, ganin kamar yanajin sanyi yasashi daukar remote ya kashe A.C din dakin yadawo kusadashi yana dan murza hannunshi.
"A.A are you ok?"
Shiru..
"Bari nakira doctor" yafada yana zaro wayarshi.
Ahankali ashraf yashiga girgiza kai idanunshi still a lumshe, shi kadai yasan abinda yakeji.
"No ashraf kana buqatar doctor" inji sadeeq yana laluban number wayar Dr.
Bece komaiba sai hawayen dasuka sulalo ahankali daga rufaffen idanunshi suka gangaro mashi.
Babu abinda ke yawo kuma yake amo a kwanyarshi sai kalmomin saudart na daxu.
Ganin hawayen ashraf yasa hankalin sadeeq ida tashi.
Rungumoshi yayi sosai jikinshi cikin tausayawa
"Ashraf please take it easy..insha Allah komai zaiyi daidai please" yafada cikin karyayar murya
Shidai ashraf be tankaba yananan yadda yake sai hawayen dake zuba daya bayan daya.
Suna haka Dr yazo.
Da taimakonshi aka kamashi suka kaishi daki, izuwa yanzu jikinshi yayi rau kamar garwashi.
Kwantar dashi sukayi sannan Dr yashiga dubashi sadeeq na gefe yana kallonsu cikin mutuwar jiki.
Drip ya daura mashi yayimashi allurar barci sannan ya rubuta masu magunguna.
Zaune sadeeq yayi gabanshi yana kallon cute face dinshi, tunda yake beta6a ganin ashraf cikin makammanciyar damuwa irin wannan ba, jiyake kamar ya daukemashi abinda yakeji ya maidoshi jikinshi.
Qara kiran wayar ummy yayi karo na uku amma ba'a dagaba kamar sauran.
Ajiyar zuciya yayi ya ajiye wayar ya zabga tagumi yana kallon sleeping ashraf kamar mirror.
A taqaice dai ranar takasance ranar qunci garesu, damuwa qararra ya bayyana a rayuwar wadannan bayin allan,
Dakyar sukaga wayewar garin.
WASHEGARI
Jin bubbugar bata hankali bane yasata katse lazumin nata tamiqe da sauri ta nufi kofar tabude.
Baby ce ta fadomata ajiki tana kuka sosai.
Saurin dagota ummy tayi tana kallonta
"Meye haka? Lafiyarki kuwa?"
Cikin kuka baby tace
"Ummy... yaya ashraf" saikuma tafashe da kuka
"Wai menene? Meya sameshi?" Inji ummy hankalinta na dan tashi
"Beda lfy... yanzu haka suna hospital" tafada cikin kuka sosai.
Shiru tayi saidai kallo daya zaka mata kasan hankalinta atashe yake.
"Ummy please muje...karya mutu" tafada cikin kuka sosai
"Jeki shirya maza" inji ummy tana komawa ciki itama don shiryawa.
Hankalinta yatashi matuqa.
Ita bazata iya tuna rabon ashraf da kwanciya asibiti ba.
He's always healthy and energetic, ba qaramin abu zai kwantar dashi ba.
"Ya rahman.. take control tafada tana daukar purse dinta tayo waje suka hade da baby suka nufi waje cikin sauri.....✍
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
071
Zaune yake jigum ya zubamashi idanu yana kallon yadda yake sauke numfashi ahankali na barci.
Sosai jiya cikin dare ya tsoratashi don giggicewa yayi da ganin yanayinshi.
Tunda Dr yayimashi allurar barci be tashiba sai wajajen takwas na dare.
Lafiya lau ya tashi yaci abinci ya rama sallolinshi yasha magani sannan yakoma ya kwanta.
Shima sadeeq ganin hakan yasa hankalinshi kwanciya har yasamu damar kwanciya shima.
Can cikin barci yaji sautin tari babu qaqqautawa wanda hakan yasashi watsakewa ba shiri.
Ashraf yagani zaune yana tari tafin hannunshi dafe da qirji yanata tari babu qaqqautawa.
Bashiri ya duro daga gadon ta zagayo wajenshi yana riqeshi ganin yadda jikinshi ke rawa.
Sosai hankalinshi ya tashi nan yaita jeramashi sannu.
Ganin tarin yaqi tsayawa yasashi sakinshi ya nufi dan qaramin fridge din dakin yaciro ruwa ya tuttula a cup yadawo da sauri ya samashi abaki yasha ko tarin zai lafa.
Cikin ikon allah sai tarin ya lafa sai sauke ajiyar zuciya dayake dakyar idanunshi sun kada sun tara ruwa.
"Sannu Ashraf" inji sadeeq kamar zaiyi kuka
Dagowa yayi a kasalance ya kalleshi batareda yace komaiba yakoma ya jingina da kan gadon.
"Sannu Allah yabaka lfy" yasake cewa cikin tausayawa.
Lumshe idanu kawai ashraf yayi yana sauke ajiyar zuciya
"Meke damunka yanzu?" Inji sadeeq.
Bude kod'add'un idanunshi ashraf yayi ya kalleshi sannan ya dafa saitin zuciyarshi yana dan shafawa
"Za..fi" yafada ahankali cikin muryarshi da baya fita sosai
Kamo hannun daya dafa qirjin dashi sadeeq yayi yana dan murzawa cikin tsananin tausayinshi.
Idan da wani zai ta6a gayamashi abokinshi kuma dan uwanshi zai ta6a fadawa cikin irin wannan halin saboda mace da ya qaryata amma gashi yana gani da idanunshi.
Shi shaidane, iya zamanshi da rayuwarshi da ashraf yasan komai gamedashi.
Ashraf mutum ne da idan yanason abu yana sonshine da dukkanin zuciyarshi haka zalika idan yaqi abu yana qinshine da dukkannin zuciyarshi ataqaice dai be iya son abu ba, be iya qallafar abuba haka allah yayishi.
"She... hate..me" ashraf ya katsemashi guntun tunaninshi
"Nima...na... tsani...kaina" yafada yana sake lumshe idanunshi
"No ashraf, please kabar wannan maganar, you're ill"
Bude jajjayen idanun yasakeyi ya kalleshi a gajiye
"Na cancanci tsanarta, don't I? Kullum saina sata kuka..."
"It ok ashraf, nace kabar magana" sadeeq yasake katseshi
"I want..to die" yafada yana sake murza qirjinshi dake mashi zafi kamar ana hura wuta.
"Ashraf please kabar magana nace, haba? Kanason..."
Tarinshi ne ya katseshi wanda yasake tasomishi yacigaba dayi babu qaqqautawa wannan karon ruwa be lafarmashi dashi ba.
Hankalin sadeeq yakai qololuwar tashi.
Ganin abun nayine yasashi kiran Dr wanda saida yajeramashi kira biyar kafin ya daga kasancewar cikin darene don har uku ta gota.
Cikin daren Dr din yafito yazo gidan suka dauki ashraf dayayi matuqar galabaita suka sakashi mota sai hospital.
Dakyar suka samu suka shawo kanshi sai gab da asuba barci ya figeshi sanadiyar allurar barci da aka sake danna mashi.
Sai a sannan sadeeq yasamu hankalinshi yadan kwanta yaje yayi sallar asuba, gari na ida wayewa yakira baby ya gayamata.
Ringing din wayarshi yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula.
Dauka yayi ya daga ganin ummy ke kira.
Gaisheta yafarayi a girmame, saida ta amsa sannan ta fadamashi gasunan hospital din yazo yashigo dasu.
Tashi yayi yafita don shigowa dasu.
A reception ya taddasu tsaitsaye kallo daya yayima baby yasan tasha kuka don fuskarta ma ta isa ta baka amsa.
Sake gaida ummy yayi sannan yayimasu jagora har zuwa dakin da ashraf ke kwance yana barcinshi peacefully.
Dagudu baby ta qarasa bakin gadon tana toshe bakinta don hana kukanta fitowa tana kallon yadda fuskar yayan nata yayi so pale.
Ahankali itama ummy ta qaraso dayan gefen gadon tana kallonshi tanajin wani abu na ta6amata zuciya.
Kallon fuskarshi take datayi fayau tana hango dan fadawar dayayi na kwana biyu.
Ahankali tasa hannu tashafi lallausan gashin kanshi cikin tausayi da qaunarshi.
"Me Dr yace ke damunshi?" Inji ummy batareda ta daina kallonshi ba.
Sadeeq dake gefe tundazu ya sauke ajiyar zuciya yace
"Damuwa... cewa yayi yana stressing din zucuyarshi da damuwa ne" yafada shima yana kallon sleeping ashraf din.
Kafin wani yasake magana acikinsu kofar dakin ta bude Dr yashigo.
Juyowa sukayi dukkansu suna kallonshi, ganin ummy yasashi qarasowa yana murmushi.
"A'a Hajiya? Yaushe kuka zo?"
Janye hannu tayi daga shafamashi kan datake tana maida mashi martanin murmushin nashi tana cewa
"Yanzu wlh... ya aiki?"
"Alhamdullilah Hajiya antashi lfy" yafada cikin girmamawa
"Lfy lau.. ya mai jiki?"
"Alhamdullilah, as you can see tarin ya lafa, yasamu barci, insha allah lokacin da zai tashi everything will be ok" yafada yana qarasawa wajenshi yana dafa kanshi.
Gwaje gwaje yadanyi mashi sannan ya gyaramashi drip dinshi sannan ya buqaci ummy tabiyoshi office zaiyi magana daita.
Babu musu ta maramashi baya suka fita.
Bayan fitarsu sadeeq ya dago ya kalli baby dake gefen ashraf tana matsar qwalla.
"It ok angel... everything will be ok" yafada a tausashe cikin sigar rarrashi.
Dago watery eyes dinta tayi ta kalleshi sannan ta saddasu tana saka bayan hannunta tana share hawayenta.
"Hajiya gaskiya damuwace tayima danki yawa, dagani wani abune yasa aranshi har yake neman illata mashi zuciya don sosai yake stressing din zuciyar... yakamata a kula please, seems he have a tender heart wanda abu kadan zai illatata if care is not taken, yanzu munsamu komai yadawo normal, munmashi allurar barci kuma munasaka ran lokacinda zai farka zaiji sauqi zamu riqeshi a hospital mucigaba da kula dashi harya warware gabadaya insha allah"
Ajiyar zuciya ummy daketa sauraronshi tundazu tayi sannan tace
"To Dr mungode qwarai"
"Yanzu yakamata asamarmashi abinda zai dan ci idan yatashi don zai buqaci hakan and please aguji 6atamashi rai hajiya, adinga kwantarmashi da hankali yadda zamu samu ya ida warkewa sumul"
"Insha allah doctor" inji ummy tana kada kai.
Dakin suka sake komawa inda suka tadda su sadeeq kamar yadda suka barsu saidai yanzu zaune baby take kan wata plastic chair kuma tabar hawayen.
Umarni ummy taba baby kan taje su hadamashi break su kawo nan ta fadama sadeeq shima yaje gida ya huta hakanan ita zata zauna dashi.
Da to duk suka amsa suka fita inda sadeeq yawuce da baby gida.
Jawo kujera ummy tayi ta zauna kusada gadon tana kallon dan nata abubbuwa namata yawo a zuciya tana tuhumar kanta na tsauraramashi.
Tasan yadda Ashraf ke taka tsantsan da gudun 6acin ranta, koyaya ra chanza fuska saiya shiga taitayinshi.
Irin wadannan yaran ne da suke tsoron 6acin ran iyayensu ko yayane, basu qaunar suga 6acin rai a tattare dasu komai qanqantarshi.
Wataqila she's so harsh on him, wataqila ta tsauraramashi dayawa.
Amma kuma ko menene tayimashi shi yaja, tasan yanada kwakwarar hujja na daukar fansa kan Alhaji shamsu saidai bataga hujjarshi na hadawa da innocent diyarshi ba.
Bataga dalilin dayasa zai jata a abinda batada masaniya akai ba, ya lallatamata rayuwa da wani banzan dalili nashi.
Ta tausayawa halin daya shiga amma hakan bazaisa taso kanta dayawa ba, bazata ta6a bari sucigaba da zaman cutarwa ba, bazata tilastawa saudart zama dashiba koda kuwa hakan na nufin zai wahala fiyeda haka.
Tasan yafara sonta, tun a reaction dinshi sanda ta nemi ya kawomata takardarta.
Tasan be iya son abuba kuma yana matuqar wahala idan ya kwallafama abu rai besamu ba.
Saidai hakan vazai sa taso kanta ba ta tauye haqqin diyar wasu.
Yadda takejin son nata dan da tausayinshi haka suma iyayen nata sukeji koma fiyeda hakan.
Ajiyar zuciya tasake saukewa tana qara kallon face din ashraf zuciyarta na saqa da warwara....✍
Manage🙏
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
072
Ahankali yafara bude idanunshi dayaji sun qaramashi extra nauyi.
Dishi dishi yafara gani dafarko sannan yafara ganin clearly.
Bin dakin yashiga yi da kallo yanason gane a ina yake.
Idanunsu suka sarke dana Ummy dake kallonshi shima.
Gabanshi ne yafadi wanda hakan yasashi yunkurin tashi da sauri.
Saurin tashi ummy tayi itama tana dafashi.
"Easy, kabi sannu you're still weak" tafada cikin kulawa tana jingina mashi pillow abaya don ya jingina.
Ahankali ya jingina da pillon yana bin ummy da kallo kamar yanason tabbatarwa kanshi ita dince.
"Ya jikin?" Tafada softly
Gyada kai kawai yayi yana kallonta
Shafa kanshi tayi tana dan murmushi
"Allah ya qara sauqi kaji? Bari nakira Dr" ta tashi tanufi waje yabita da kallo harta fice.
Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar anyi lifting wani qaton dutse daga saman qirjinshi.
Bin dakin yashigayi da kallo wanda ya tabbatarmashi hospital yake.
Ajiyar zuciya yasake saki yana komawa ya jingina sosai da pillon dake bayanshi yana tuna abinda yafaru jiya.
Shi kadai yasan abinda yakeji jiyan nan don qirjinshi inbanda zafi babu abinda yake, jiyake kamar ana iza wutane a qirjinshi amma yanzu alhamdullilah yarage sosai sai dan abinda ba'a rasa ba.
Bude kofar da'akayi yasashi dagowa yana kallon kofar.
Baby ce tashigo riqeda basket din abinci abayanta kuma sadeeq ne cikin wasu kayan da alamun yayi wanka ne riqeda qatuwar leda dake shaqe da kayan itace.
Da sauri baby ta qaraso bakin gadon ta ajiye basket din ta kamo hannun ashraf murmushi fall fuskarta.
"Yaya you're awake?" Tafada cikin murna
Guntun murmushi kawai yayimata yana dan lumshe idanu.
Qarasowa shima sadeeq yayi yana fadin
"Inyee gawa taqi rami? Ai harna fara cinikin gero shine dan baqinciki ka tashi?" Yafada shima yana ajiye ledar hannunshi kan locker dake kusada gadon ashraf.
Murmushi kawai ashraf yayi don haryanzu beda kuzari sosai.
"To saika fasa don yayana ko turwa ta shafa mashi lfy a taurin rai, sai yafara shan naka gumbar kafin asha tashi" inji baby tana murgudamashi baki.
Dan waro idanu sadeeq yayi yana rufe bakinshi da tafin hannu
"Iyee? Dama fatan dakike mani kenan? Kodayake ke zaki kwan ciki, kizama bazawara nabarki da maray..."
Waro idanun da baby tayi yasashi saurin sakama zancenshi full stop yana wulwulga idanu cikin rashin gaskiya.
Ashraf dai kallonsu yake kallon tuhuma, ganin haka yasa baby saurin duqawa ta ciro flask din cikin basket din tana yaqe.
"Yaya bari ba hadamaka tea" tafada tana dorawa kan dayan lockern dake dayan 6aren
"Nikuma na hadama fruits" inji sadeeq yana satan kallon baby dake antayamashi harara qasa qasa yana qumshe dariya.
Shidai ashraf bece komaiba sai binsu kawai dayake da kallo
Suna haka kofar ta bude ummy da Dr suka shigo.
"A'a? Tare kuka dawone?" Inji ummy tana qarasowa
"Eh wlh, zuwa nayi nai wanka na shirya nakoma na daukota" inji sadeeq yana dan sosa qeya.
"To yayi, tea kike hadawa?" Ta tambayi baby dake riqe da mug din shayin tana jujjuya tea din da spoon
"Eh ummy" tafada tana kallon Dr dake duba Ashraf.
Saida yagama yan gwaje gwajenshi sannan ya ciromashi magungunnanshi yace abashi yasha idan ya karya sannan ya ciremashi empty drip din yafita.
Bowl aka fara kawomashi yayi brush aciki don beda qarfin dazai tashi yaje toilet sannan aka bashi tea din don yasha.
Kauda kai yayi kawai yana satan kallon ummy qasa qasa.
Itama kauda kai tayi don tasan abinda yake nufi.
Ganin haka yasa jikinshi yin sanyi ganin kamar still tana fushi dashi.
Dagowa yayi yamiqa hannu zai amshi mug din ummy tarigashi amsa taja kujera ta zauna gabanshi ya debo a spoon tadan hura sannan takaimashi a baki.
Dagudu ya bude bakin yana bin fuskarta da kallo, harara ta gallamashi tana sakamashi spoon din abaki, murmushi ya su6ucemashi yayi saurin sunkuyar dakai yanayi.
Agefe kau baby sai antayama sadeeq harara take shikuma yana dariya marar sauti harda gwalo.
Haka ummy taita feeding dinshi harya qoshi sannan ta dago dan cewa sadeeq yabata magungunnan sai gani tayi yanata dariya marar sauti kamar sabon kamu.
Kallon baby tayi ganin direction dinta yake kallo taga ashraf ma ita take kallo wanda itama saida taga ummy zata waigo tayi saurin maida kallonta kan ashraf din.
Maida kallonta tayi ga sadeeq daya nutsu yanzu sai muzurai yake.
"Kaikuma lafiyarka?" Ta tambayeshi
Dan sosa kanshi yayi a kunyace
"Lfy lau ummy" yafada yana satar kallon baby dake qumshe dariyarta
"To allah yasa, miqomin magungunnan kekuma miqomin ruwa"
Duk juyawa sukayi su aiwatar da abinda tace baby sai danne dariyarta take.
Ballar mashi magungunnan tayi tabashi yasha yanajin sanyi a zuciyarshi don abubuwan datake mashi sun nuna tabar fushi dashi.
Excusing kanshi sadeeq yayi ya fita waje yana hararar baby ta gefen idanu itakuma tamashi gwalo ta gefen baki tana murmushi.
Juyowa dazatayi suka hada idanu da ashraf tayi saurin kauda kai gabanta na faduwa.
Ta6e baki kawai yayi shima ya janye idanunshi.
Riqesu akayi asibitin ganin yanayin rashin qarfin jikin nashi.
Da yamma saiga matar kawu zaharadini da shi kanshi kawun nashi sunzo ganinshi.
Anan ne suka ke6e da ummy tabashi labarin komai.
Yayi mammaki shima matuqa don shi rabonshi dajin ko labarin shamsu qolo tun suna mutunci da margayi Alhaji Auwal.
Saida suka tattauna sosai sannan suka tafi can gab da magrib.
Saudart kau a 6angarenta abin yayi affecting dinta itama sosai.
Takoma wata shiru daita ranta kodayaushe a jagule.
Duk yadda daddy yaso wartsakar daita yagaza don wannan karan takasa controlling din kanta.
Haka zata wuni a daki ba uhm ba uhm uhm, abinci saidai abiyota dashi kuma dakyar yake samu taci.
Idan ya takuramata da tambayoyi sai taita mashi kuka.
A cikin kwana biyu duk ta chanza tafita hayyacinta.
Saida yayi kwanaki uku sannan aka sallamashi daga asibiti, lokacin yaji sauqi sosai.
Direct gidan ummy suka wuce.
Sosai Ashraf ya wartsake saidai haryanzu cutarnan ta son Saudart babu abinda ya ragu saima abinda yaqaru.
Kwana daya da sallamoshi Kawu ibrahim ya diro garin kano don shima tuni labari yakaimasu a wudil.
Sudai su baby basusan dalilinshi nazuwa ba amma sunsan baya rasa nasaba da case din Auren Ashraf.
Ranar sun hadu da Kawu zahradini da ummy da kawu ibrahim sunyi heart-to-heart discussion akan yadda zasu 6illowa al'amarin.
*WASHEGARI*
Bayan azahar suka shirya dukkansu wato Kawu ibrahim, Kawu zahradini, Ummy, baby da Umma suka nufi gidan *MAMY*
💖💖💖💖💖💖💖💖
Jin ringing din doorbell yasa su dagowa daga cin abincin dasuke.
"Habeeb, jeka duba" inji Abba yana sipping din juice.
Ajiye fork din hannunshi yayi yana goge bakinshi da tissue sannan ya sauko daga dining din yanufi kofar.
Budewa yayi yayi tozali da maigadi
"Baba Audu" inji habeeb yana murmushi
"Na'am habibullahi" shima ya amsa yana washe baki
"Kashigo" yafada yana matsawa
"A'a dama baqi kukayi"
"Baqi? Ina?" Yafada yana leqa bayanshi.
"Suna can garage, suna neman iso ne" yabashi amsa
"Ok inazuwa" yakoma ciki yafadawa su mamy.
"Baqi? Jeka ka shigo dasu" inji mamy
"No, kaisu falon baqi seems harda maza tunda kikaga sun fara aikowa" inji Abba.
Wucewa habeeb yayi don aiwatarda yadda yace din.
Tare suka tafi da maigadin har parking space din.
Ganin baby cikinsu yasashi washe baki yana qarasawa wajensu da sauri
"Laa aunty?" Yafada yana washe baki
Shafa mashi kai tayi tana murmushi
"Sheikh habibullah" tafada cikin sigar tsokana kamar yadda tasaba kiranshi a dan zamanta gidan lokacin biki.
Murmushi yayi sannan yajuya gasu ummy ya duqa har qasa yana gaidasu.
Amsawa duk sukayi cikin jindadi ummy na kallonshi tana hango kammaninshi da saudart sosai.
Iso yayi musu suka bishi har falon baqi suna tafe baby na tsokanarshi shikuma yana murmushi don dama shi becika maganaba ko a lokacin data zauna gidan idan ta tsokaneshi saidai ya sunkuyar dakai yana murmushi hakan yasa take kiranshi sheikh ko ustaz.
Saida suka zauna sannan yajuya yafita, chan saiga aminullah yashigo da kayan motsa baki.
Shima yadda habeeb ya gaidasu haka shima yayi amma banda baby sai harararta dayayi yana murmushi.
"Inyee lallai ka riqu, ni bazaka gaidani ba?" Tafada tana harararshi don dama shine abokin fadanta.
Gwalo yaimata yafice da sauri ganin tayi kamar zata tashi.
Duk dariya sukasa don sosai yaran suka burgesu.
Ana haka sukaji sallamar Abba, hakan yasa suka maida kallonsu a qofar dukkansu suna amsa sallamar.
Cikeda nutsuwa da dattako Abba yashigo Mamy abayanshi suka shigo suna sakeyin sallama.
Amsawa duk suka sakeyi suna murmushi.
Saida suka zazzauna sannan aka shiga gaishe gaishe cikin girmamawa.
Sai anan Mamy ta lura da baby lokacin da itama ta zamo tana gaidasu.
"Laa kamar baby" inji mamy
Murmushi baby tayi
"Nice mamy"
"A'a wata sabon gani, yau kece gidanmu?" Tafada cikin raha tana bin kingin mutanen da kallo tana mammakin su wanene? Agefe guda kuma gabanta nadan faduwa.
Ummy kau tunda Mamy tashigo take binta da kallo don sosai take hango kammaninta nada dukda ta chanza sosai, gashi kammaninta sak na saudart sai mammakin yadda takasa ganin kammanin ada tayi.
Saida suka gama gaishe gaishen cikin raha da dariya sannan aka nutsu don tattauna abinda yakawosu.
Ganin hakan yasa baby miqewa ta barmusu dakin tashige cikin gida....✍
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
073
"Hajiya khadija, ashe rai kan ga rai?" Inji ummy cikin murmushi.
Itama Mamy murmushin take mayar mata sai kallonta take don she looked familiar
"Aikaudai yaudai allah yayi mun hadu, munata saka ranar zuwa gashi kun rigamu zuwa" mamy tafada cikin fara'a
Murmushi ummy taqarayi ganin haryanzu bata ganeta ba.
"To yaya bayan rabuwa? Ban ta6a tunanin zamu sake hadewa ba, gashi Allah yasake hadamu a matsayin in-laws"
Sai alokacin mamy tafara mata kallon rashin fahimta don bata gane abinda take nufiba, su dai du Abba nasu ido.
"Erm... sorry, dama munsan juna ko?" Inji mamy tana kallonta sosai tana qoqarin gano inda ta ta6a sanin fuskar.
Murmushi mai sauti ummy tayi tana kada kai
"Sosaima, nasanki kema kin sanni wataqila dan an dade ba'a haduba shiyasa kika kasa ganeni, shekaru Ashirin ai ba wasaba"
Kallon juna Abba da Mamy sukayi sannan suka maida kallonsu kanta
"Fateema ce, matar aminin tsohon mijinki Shamsu... Matar Alhaji Auwal"
Tsit dakin ya dauka, kowa yazuba masu idanu yayinda ita mamyn tazuba ummy idanu babu ko kyaftawa tanason tuna inda ta ta6a jin wannan sunan.
"Auwal aminin mijinki dakika sameshi lokacin dakuka fara samun mtsl da tsohon mijinki" ummy taqara fada ganin mamy ta antaya kogin tunani.
Ahankali mamy tafara ware idanu tana kallon ummy daketa murmushi yayinda take nunata da yatsa bakinta na rawa
"Ummyn muhammad?!" Tafada tana ware manyan idanunta sosai
Murmushi kawai ummy tayi tana kada kai.
Dasauri mamy tanufi wajen ummy suka rungumi juna
"Ummyn muhammad? Kece or am dreaming? This is unbelievable" tafada cikin alhini.
Murmushi duk mutanen dakin sukayi suna kallonsu.
Nanfa akayita firar yaushe gamo, haryanzu mamy takasa yarda ummy ce surukarta, jinjinama ikon Allah takeyi, ko a mafarki bata ta6a tunanin zata sake ganinta ba sai gashi cikin ikon allah sun sake haduwa kuma wannan karon da strong bond atsakaninsu.
Sun dade suna fira suna dariya suka dan ta6a kayan motsa baki da aka kawomusu sannan suka nutsu suka dawo serious don tattauna abinda yakawosu, ummy sai kallon mamy take tana jin badadi don tasan dole hankalin mamy yatashi idan taji dalilin zuwan nasu.
Ciki hikima da iya tsara zance Kawu ibrahim ya gabatarmusu abinda yakawosu wanda saida yafara basu labarin abota da amintar dake tsakanin margayi Auwal da Shamsu sannan ya gangaro zuwa yadda suka samu matsala dajuna suka koma basa ga maciji da juna zuwa yadda aka kame mottocin margayin da yadda labari ya iskesu nacewa aikin tsohon amininshi ne sanadi harzuwa jinyar dayayi wanda sanaddiyar girgizar dayayine dajin cewa tsohon abokinshi ne sanadin karayarshi wanda wannan jinyarce sanadinshi.
Ya gangaro kan yadda rayuwa ta sauyamusu da yadda suka siyarda gidansu suka samu allah ta tallafamusu zuwa inda Ashraf yasamu scholarship yayi karatunshi a Uk xuwa inda yagama yabude company na A.A ENTERPRISES.
Tsit falon yayi, kowa shiru kamar ruwa ya cinyesu, mamy kau idanunta sun kada sosai mood dinta ya chanza
Abba kau he is expressionless, baxaka iya gane awane yanayi yake cikiba.
Ajiyar zuciya kawu ibrahim ya sauke sannan yacigaba daga inda yatsaya yafara magana akan abinda ya tarasu.
Tunda yafara magana mamy takafamashi idanu tana kallo babu ko kyaftawa harya kai aya.
Daga mamy har Abba rasa mai kwakwarran motsi akayi, they're all dumbfounded.
Kwakwalwarsu kasa daukar zancenshi sukayi.
"I don't understand, i don't really understand" inji mamy tana girgiza kai hawaye na taruwa idanunta, kallo daya zaka mata kasan hankalinta yayi matuqar tashi.
Kama hannunta ummy tayi kasancewar dama kusada ita take asanyaye tace
"Khadija, nima i was shocked danaji wannan zancen, it's unbelievable banta6a jin makamancin wannan yafaruba ko a tatsuniya amma it's real" tafaxa asanyaye.
" *AUREN KWANGILA?* contract marriage? Dama akwai irin wannan auren? Am confused" tafada kaida gani kasan she's not herself.
"But how? Tayaya Saudart da hankalinta zata yarda da irin wannan shirmen? This is unbelievable" inji Abba shima cikin alhini
"He forced her, bada son ranta bane, shiya tilasta mata" inji ummy
"Shiya tilasta mata?! Ni meye amfanina? Why can't she come over to me and tell me! Daqiqancinta harya kai takasa confiding in me as her mother?.... dama nafada! Babu yadda banyiba akan kar amayar mashi daita tun farko akaqi saurarata, ga irinta nan, ya siyar daita akan kudi, ya musayata da kudi! Kagani ko Alhaji? Kaga abinda nake fada? Allah kadai yasan me da me yakoyamata, Allah kadai yasan tarbiyarda ya dorata akai, ya maidamani yarinya cash worm..." kuka ne ya kufce mata ta toshe bakinta tanayi sosai.
Rungumota ummy tayi asanyaye tana rarrashi.
"But how come tun farko baku ganeshi ba dakukazo?" Inji Abba da duk jikinshi yayi sanyi.
"Alokacin nida Nura mukazo tareda yan uwan ummy, lokaci yaja gashi dama ni sau daya nata6a ganinshi lokacin rasuwar mallam, shi zahradini daya sanshi sosai bayanan lokacin yayi tafiya, kuma munyi bincike mun samu gamssashiyar shaida gamedashi tun kafinma muzo din" inji kawu ibrahim.
"Innalillah waina ilaihi rajiun, wannan abu beyi dadiba samm" inji Abba yana girgiza kai.
Dagowa mamy dake kuka haryanzu tayi tareda cewa
"Dama nasani, that greedy man can do anything don yasamu kudi, gashi greediness dinshi yaja zai lallatama diyata future, koko ince yama lallata tunda gashi itama saboda kudin ta yarda tayi auren"
"No mamy, he forced her ne" inji umma da tundazu batace komaiba.
Kallon umman mamy tayi tace "bawani forcing, nasan saudart ciki da bai, idan batayi niyyar yin abuba babu wanda ya isa yasata, besides baganiba? Ni meye amfanina idan bazata iya gayamin damuwarta ba? Am her mother for goodness sake, dama i smell something fishy gameda auren nan don everything come all of a sudden ne, now yayi nasarar maida diyata kwadayyaya irinshi" tafada bitterly.
Rarrashinta akai tayi don kuka take sosai, banda zafi babu abinda zuciyarta keyi.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya kalli su kawu ibrahim dakyau ya bude baki calmly yace
"Now meye abin yi? Aikin gama dai yariga da yagama, sai samun solution yarage, yanxu ku me kuka yanke?"
Kawu zahradini da shima tundaxu beyi maganaba yadan muskuta sannan yafara cewa
"To yanxu dai two things are involved, na farko case din shamsu nabiyu kuma auren nan.
Mudai bamu riqe shamsu araiba akan abinda yaima margayi, wannan tsakaninsu ne da margayi da Mahallicinsu, Allah zaima kowa sakayya daidai dashi.
Batun aure kuma Ashraf yanuna yanason matarshi kuma ya janye contract din tsakaninsu, idan so samune sucigaba da zama a matsayin ma'aurata saidai wani hanzari ba gudu ba.. *saudart!*.... dole yadda tun farko auren yarjejeniya ne a tsakaninsu yanxuma yarjejeniya zamansu zai zama, ma'ana dole saida amincewar dukkansu, bazamuso mu cutar da daya ba don farantama dayan. Idan saudart ta amince zata cigaba da zama dashi to fallilahil-hamd don muma bazamu so yankewar wannan alaqar tamuba, munason saudart kamar yar cikinmu, abinda mahaifinta yayi can baya bazai ta6a shafanta ba don kwata kwata babu kamanceceniyar hallaya tsakaninsu, saudart yarinyace mai nutsuwa da tarbiya wanda samun irinta ayanzu yayi wuya, ladabi da biyyayarta yasa tunfarko ta yarda da qudurin babanta wanda ita tausayamashi tayi ganin halin dazai fada idan bata aminceba, saudart macece mai amana da zuciya mai kyau don ba don itaba da yanzu company don A.A ya fuskanci mummunar asara da karaya, muna sonta amma hakan baxaisa idan taqi yarda da cigaba da zama dashi mu tilastata tayi zaman cutuwa ba"
Ummy itama ta dora da "tun farkon haduwarmu da saudart tashiga raina, nasan she's the best wife for my son, she's a girl with a pure heart, ina jinta araina fiyeda yadda nakejin baby araina, bazamu ta6a mata dole zama da Ashraf ba, haqurin datayi dashi da farko ma ya isa, i know yamata abubuwa don ni nasan waye dana idan yanaqin abu, wataqila cin zalinta dayaitayi batareda haqqintaba yasa allah ya jarabceshi da sonta lokaci guda don dama ance idan qiyyaya tayi yawa takan zama soyyaya daga baya, yana sonta fiyeda tunaninku yanzu amma hakan bazai sa a tauyema saudart haqqinta ba, cigaba da zamansu da rabuwarsu will depend on amsarta ne"
Shiru dakin yasake dauka sai can Abba ya sauke ajiyar zuciya yace
"To yanzu abinda za'ayi shine zamu zauna dukkanmu harda Alhaji shamsu da saudart dashi kanshi mijin natan a yanke koma menene, aganina hakan zaifi? Koko?" Yaqarashe zancen yana kallonsu kawu ibrahim
"Masha allah, hakanma yayi"
"Yanzu zanma shi Alhaji shamsun magana inyaso duk yadda muka yanke zanyi informing dinku insha allah"
"To allah ya yarda yakuma mana jagora" inji kawu ibrahim
Duk amsawa da amin sukayi har lokacin mamy batabar hawaye ba.
Haka dai suka tafi kowa zuciyarshi babu dadi.
Mamy tayi kuka kamar me? Sai blaming din alhaji shamsu take da lallatamata rayuwar diyarta.
Shidai abba inbanda rarrashi babu abinda yake don shima har zuciyarshi beji dadin abinda yafaruba don shima yanason saudart harcikin zuciyarshi kamar kingin yayan cikinshi.
Aranar dai haka suka wuni cikin damuwa da bacin rai.
A 6angaren Ashraf kau tunda suka dawo yakasa xaune yakasa tsaye don fargaba, jiyake zuciyarshi zata iya tarwatsewa idan yaji mummunan sakamako, dama tunda suka tafi yaketa addu'ar allah ya dorashi akansu allah yabashi nasara don rashin saudart daidai yake da rasa farincikinshi a rayuwa.
Duk up and down din dayakeyi ummy na hankalce dashi tayi banza dashi kamar batasan me yakeba.
Sai kai komo yake a falon yaji ko zata kirashi amma tayi banza dashi daga baya ma zama yayi a falon yana kallo yayinda dukkan hankalinshi ke kan duk wani motsi da ummy zatayi.
Haka yasha zamanshi daga qarshe ummy ta tashi ta hayewarta sama tabarshi nan zaune.
Babu yadda ya iya haka ya tashi shima jiki a sanyaye yakoma part dinshi zuciyarshi namashi saqe saqe.
Zaune take a garden bisa wata plastic chair ta rungume hannayenta tana kallon waje guda babu ko kyaftawa wanda hakan ke nuna cewa tayi nisa cikin tunani ne
Tun ranar dasuka rabu da ashraf bakery dinta wurin yazama wajen zamanta, bata qara marmarin fitaba tun ranar, kullum anan take zuwa ta zauna ba uhm bare uhm uhm sai tunani wanda yazame mata jiki.
Kallo daya zaka mata ka hango fadawar datayi sosai, duk takoma shiru daita kamar ba active saudart ba.
Ringing din wayarta ya maidota daga duniyar tunanin data lula.
Ahankali ta kalli wayar sannan cikin rashin kuzari ta jawo wayar ta duba.
Maryam ce hakan yasata yatsuna fuska sannan ta daga.
Sudan jima suna magana akan abinda yashafi business dinta wanda yanzu rabonta da leqasu tun ranar nan, akasalance taita amsamata suka dan tattauna sannan sukayi sallama.
Tana niyyar ajiye wayar wani kiran yashigo wayarta.
Tsayawa tayi tana kallon sunan dake yawo a screen din wayar batareda ta iya dagawa ba yayinda takejin qaruwar bugun zuciyarta.
Kasa dagawa tayi har kiran ya tsinke, babu 6ata lokaci wani kiran yasake shigowa again.
Limshe idanu tayi ahankali tayi ta bude tana kiran sunan allah.
Cikin rawar hannu tayi picking din call din ganin zai qara tsinkwa ta kara a kunne atsorace....✍
Ummin fasihu ce🧚🏻♀️
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
074
"Aslm alaiki" tafada ahankali zuciyarta fall fargaba
"Wslm Amaryar contract, ya kike?" Taji anfada daga dayan 6angaren
Dumm! Gabanta ya yanke ya fadi, ahankali ta sauke wayar daga kunnenta taqara kallon screen din don qara tabbatar da mai kira din.
Maidawa tayi a kunne tafara magana ad'an daburce
"M...mamy? Mamy ina wuni?" Tafada bugun zuciyarta na qaruwa
"Save your greetings don bana buqata, banida wannan matsayin awajenki so hang it" inji mamy
Hankalinta ne yatashi wanda har saida tamiqe tsaye bakinta nadan 6ari tace
"M...mamy... mmm..meya faru please" tafada yayinda wasu hawaye suka fara kawo mata.
"Mefa? Just call to hear from you dukda bawani matsayi nakedashi awajenki ba"
"Mamy..." saikuma tayi shiru tana toshe bakinta don kuka ne ke neman kufcemata.
"Bye" mamy tafada a dayan bangaren zata tsinke kiran
"No mamy please don't hang u..."
Ding... taji an katse kiran.
Sakin wayar tayi takoma kan kujerar tana dafe kanta da hannaye bibbiyu tafashe da wani irin kuka.
"No..no" tafada tana kuka sosai.
Saurin duqawa tayi tasake daukar wayar data yar qasa tana kuka tashiga re-dialling din number mamy, hannunta sai rawa suke.
Takira yafi so biyar amma ba wanda aka daga.
Wani kukan tasake fashewa dashi tana cillar da wayar.
Dama tsoronta kenan, kullum fargabar datake kenan, shikenan tafaru taqare.
"Am doomed!" Tafada tana daura hannu aka kamar wanda aka kawoma saqon rasuwar uwarta.
Wayar tasake dauka tanufi cikin gida tana kuka sosai tashiga dialing din number Daddy.
Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hayyacinta.
Ringing biyu daddy ya daga.
Kukanta dayaji ya katsemashi sallamarshi wanda hakan yasashi zabura amiqe.
"Shalele?"
Zubewa tayi qasan falo don harta shigo falon tana kuka sosai wayar kare a kunnenta.
"Shalele menene? Talk to me" inji daddy cikin rawar baki.
"Nashiga uku daddy, daddy am doomed!" Shine abinda kawai ta iya fadamashi cikin kuka.
"Subhanallilah! Shalele what happened? Meya sameki?" Yafada yana laluban car key dinshi kan table
"Daddy kazo... zan mutu" tafada cikin kuka sosai
Kafin yasamu damar yin wata maganar harta katse wayar.
Bashiri yayo waje hankalinshi a matuqar tashe.
Zaune yake jigum, yarasa meke mashi dadi.
Tagumi yabuga da hannu bibbiyu yana bin screen din laptop dinshi da kallo wanda ke dauke da hotonta daya fito tarr wanda duk ya turasu akan laptop dinshi daga cikin wayar databar mashi
Ahankali aka bude kofar dakinshi baby ta leqo.
Ko dagowa beyiba don bemaji budewar kofarba
Qarasa shigowa tayi da sallama wanda hakan ya fargar dashi yayi saurin dagowa.
"Yaya?... yaya wai ka sauko muyi dinner" inji baby ahankali
Komawa yayi ya jingina da kujerar dayake akai yana sauke ajiyar zuciya
"Go... banajin yunwa" yafada ahankali.
Jimm tadanyi kamar bazata wuceba saikuma tajuya tafita.
Can saigashi tasake dawowa.
Dagowa yayi yakalleta kawai batareda yace komaiba
"Yaya wai kawu yace kazo"
Lumshe idanunshi yayi ya bude
"Ok" yafada ataqaice
Saida tadan jima da tafiya sannan shima ya tashi ya dora shirt saman singlet dinshi yafito.
A dining ya taddasu duka, a ladabce ya gaidasu kai a qasa.
Kawu ibrahim kawai ya amsa ummy ko ko kallo be ishetaba.
"Zoka zauna babana" inji kawu ibrahim yana nunamashi kujerar gefenshi
A natse ya qaraso ya zauna baby tayi serving dinshi
"Now eat" inji kawu ibrahim
Ba musu yadauki spoon din yafara cakula abincin don bawani cin kirki yayimashi ba sai jujjuya spoon din dayake aciki.
Haka suka gama in silent sannan suka fara tashi daya bayan daya yarage saura kawu ibrahim da Ashraf.
Goge bakinshi kawu ibrahim yayi shima yatashi
"Kasameni a garden" yafada tareda ficewa.
Haka kawai yaji gabanshi yafadi ya kasa kai kofin ruwan a baki.
Ajiyewa yayi yana sauke ajiyar zuciya.
Tunda suka dawo yake kasa kunne yaji ki zasuyimashi magana amma shiru gashi yanzu ammashi din amma jiyake beda courage din jin sakammakon daza'a gayamashi.
Ya dade zaune awajen yana saqa da warwara kafin daga baya ya miqe dakyar ya fita zuwa garden din kamar kazar da kwai yafashe mawa aciki.
"Shalele kiyi hqr please, kibar kukan hakanan" inji daddy daya gaji da rarrashi
Zaune take jan gadonta cure wuri guda ta hade kanta da gwiwa tana kuka cikin muryarta dabaya fita tsabar kukan datasha.
"Shalele, am sorry, duk nine silar komai, ki gafarceni 'yata" yafada shima kamar zaiyi kukan
Ko dagowa batayiba haka zalika batabar kukanba hakan yasashi jawota ajikinshi cikin sigar rarrashi.
"Shalele kiyi hqr, nasan yadda kikeji, please kibar kukan haka, ni da kaina zanmasu bayyani kinji? Nina jawo komai kuma ni yakamata inga consequence dinshi, please kibar kuka please"
Itadai batace komaiba sai kukan datakeyi qasa qasa, sosai zuciyarta kemata zafi gawani sara da kanta keyi agefe daya jitake dama tamutu ta huta.
Dakyar daddy yasamu ya lalla6ata tasha tea tasha magani ta kwanta.
Ya dade sosai dakin har saida yaga tayi barci sannan ya lalla6a yafita don karya tadata.
Saida taji alamun yafita sannan ta bude kumburarrun idanunta ta miqe zaune ahankali, hade kai da gwiwa tayi tacigaba da hawaye tana kukan zuci.
Daddy a 6angarenshi shima kasa rintsawa yayi, sosai yake danasani marar amfani.
Danasani yake sosai na halinshi, yasan yanzu tuni dan kingin mutuncinshi yarigada yazibe a idanunsu mamy
Sosai yakejin kunya, sai yanzu yake mammakin yadda acan baya idanunshi suka rufe yakasa hango abubuwan dazasu biyo baya.
Alokacin shidai kawai abinda zai qaru dashi yake hange, be ta6a hangen abinda zai ragu dashiba.
Gashi yanzu ya tsunduma 'yarshi kwaya daya, mai son farincikinshi cikin qunci da bakinciki.
**********************************
Fada sosai kawu ibrahim yayimashi kan abinda ya aikata, ta inda yake shiga batanan yake fitaba.
Sosai jikin ashraf yayi sanyi don tunda yake beta6a ganin kawunshi cikin irin wannam 6acin ran ba.
Sai daga baya yafarayi mashi nasiha mai ratsa zuciya wanda ya ida kashe jikin ashraf.
Saida yaimashi nasiha sosai sannan ya gayamashi yadda sukayi dasu Abba, ya dora dacewa
"Yanzu dai dorewar aurenku ya danganta ne da amsar da yarinyarnan tabada, bazamu so kanmu dayawa ba, bazamu bari ayi zaman cutuwa ba, idan ta amince zata cigaba da zama dakai to fallilahil hamd, amma idan ta nuna akasin haka bazamu tilasta mataba, saidai muyima dukkanku fatan allah ya hada kowa da mafi alhairi"
Bayan haka ya sallameshi.
Tashi yayi jiki amace, yabi ta hanyar baya yashiga cikin gidan ya haye sama kamar marar lakka.
Ahankali ya zauna gefen gadonshi ya jingina kanshi da jikin gadon ya lumshe idanunshi da suke a rine.
Yasan shikenan, shikenan sun rabu da saudart sun gama.
Tun yanzu yasan matsayar aurannan, dama mai neman kuka ne aka jefa da kashi.
She hate him so much, ta tsaneshi ta tsani ganinshi burinta su rabu, meye to amsarta bayan anbata za6i yanzu na cigaba da xama dashi ko rabuwa dashi?
Ofcourse rabuwa ce, yasan bazata tsaya dogon tunaniba zata za6i rabuwa dashi.
Ahankali hawaye suka gangaro daga ruffafun idanunshi yanajin tausayin kanshi.
Yasan rabuwarshi daita daidai yake da rabuwarshi da farincikinshi.
Yasan rabuwarshi daita kamar bude sabon shafin kunci ne arayuwarshi.
His last hope was gone, yanzu baida sauran wani hope, kawai yariga yarasata yagama ne.
Adaren babu wanda ya rintsa acikinsu daga Ashraf da saudart har Alhaji Shamsu daya tsangwami kanshi yake ganin shine umul abaisan faruwar komai.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Washegari da zazzafan zazza6i saudart ta tashi.
Sosai Alhaji shamsu ya rude don jin jiki take sosai kuma taqi yarda akaita hospital saidai aka kira family doctor dinsu yazo hargidan.
Ranar wuni yayi tareda ita bekosan motsawa daga gefenta, duk motsin dazatayi saiyayi mata sannu, he's feeling guilty, yanajin duk shine silar komai, hqr kau har saudart tagaji dajinshi abakinshi. Haka ranar tazo tawuce masu dukkansu cikin qunci.
A 6angaren ashraf kau sai abinda yayi gaba.
Haka shima yawuni sukuku, saidai kaganshi zaune ya kafe waje daya da idanu yana tunani.
Baya fita gidan sai yaga lokacin sallah yayi sannan yafita masjid, daga nan kuma sai dakinshi.
Idan kuma ya sauko qasa to ankirashi ne ya sauko yaci abinci wanda ko kwata beci zai tashi wai ya qoshi daganan kuma yakoma daki ya dasa daga inda ya tsaya.
Ganin tunane tunanen bazasu amfaneshi dakomai ba yasashi tashi ya daura alwala misalin shabiyu na dare yahaye sallaya yaita nafilfili yana addu'ar allah yabashi haquri da juriyar rabuwa daita yakuma yayemashi sonta kamar yadda ya doramashi don shi yarigada ya fidda rai da kasancewa tareda ita.
Saida tayi kwana biyu kwance sannan tadanji sauqi.
Damun daddy tayi da kuka akan ita gidan mamy zata don tasan tana fushi daita.
Ganin bata ida warwarewaba yaso hanata dafarko amma ganin ta burkucemashi yasashi yarda akan tayi hqr zaikaita dakanshi washegari.
Haka ta haqura badon yasoba.
Washegari sukuku ta tashi, fargabar haduwarsu kawai take da mamy don tasan haduwarsu won't be funny at all.
Haka ta shirya jiki amace kallo daya zaka mata kasan atsorace take.
Daddy ne yaita kwantarmata da hankali ganin yadda duk ta tashi hankalinta.
Haka suka fita daga gidan suka dau hanyar gidan mamy kowanne da irin fargabar dayake....✍
Sorry for the short chappy🙏
Please sai kun dinga hqr dani yanzu, wlh bansamun zamane kamar da.
Da ace yadda nake samun lokaci ne kamarda da yanzu book dinnan yaqare.
Yanzu typing dinma kanshi wahala yakebani don am always busy.
Please bear with me, yanzu ba kullum zaku dinga jinaba, amma duk ranarda am less busy zan dinga yimuku mai yawa🙏
Nagode da qaunar dakukemani da littafin nan.
Masu cigiyata da masu kirana duk nagode, Allah yabar qauna da zumunci, Allah yabarmu tare har abada💖
Ashaanty loves you so much😘💖💖💖💖💖
0 comments:
Post a Comment