DA WA NADACE ?
(Yaya Abnee ko Yaya Fu'ad)
(Love story)
1 & 2
NA
SUWAIBA MUHAMMAD GOMBE
(Mrs Yarima)
?PEN WRITES ASSOCIATION
Real Mrs Yarima WhatsApp 08178287947
GODIYA:
Godiya tatabbata ga Allah subahanahu wa ta'ala! Tsira da aminchin Allah sutabbata ga fiyeyyen halittu Annabi Muhammad S.A.W da sahabbanshi da iyalenshi.
FATAN ALKHAIRY:
Fatan alkhairy gareku iyayena, Allah yasaka muku da mafificin alkhairy amin.
JINJINA:
Jinjina gareka Mijina uban ya'yana A.D yarima, Allah yasa kafihaka amin.
GARGADI:
Ba'ayarda wani ko wata yacanja wani'abu daga cikin wannan littafin ba, se da 'izinin marubuciyar arubuce, akiyaye.
SADAUKARWA:
Nasadaukar da wannan littafin nawa me suna DA WA NADACE wa 'iyalaina.
GAISUWA TA MUSAMMAN:
Gaisuwa ta musamman ga aminaina
Hajiya Hafsat Sudan(Mamna Affan) da
Hajiya Sofiyya Abuja(Ummu Samha) da
Hajiya Sakina Ethiopia(Ummi Suhaima) da
Hajiya Suwaiba Cairo(Mamna Yasmeen)
DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI!
Tafe suke cikin nutsuwa! Fitowarsu daga lectures kenan, inda 'aka tanadar domin 'ajiye motoci sukanufa! Motace kirar 406 one door sukabude suka shiga, ayayin da daya daga cikin matasa biyun ta zauna awajen zaman driver ta tada mortar sukafice.
Han'yar daze kaisu unguwar Nasarawo sukadauka! Hirarsu sukeyi 'irinta aminan juna, adede kofar wani gida sukatsaya, cikin zolaya takalli matashiyar datakawosu tace Yasmeen bade kina nufin kindena shiga gidan namubane.
Ayyah Halee kiyi hakuri tace na'isa nadena shiga, ayko domin Umma nashiga tace tana yar' dariya, ayayin data karasa maganarta da cewa maybe gobe insha Allah zanshigo, kigaida Umma, idan Adda Fanna ta'iso kisanar dani ta waya.
Sannan kuma kice 'inamata barka da zuwa zanzo nakarbi Humrata kuma, dariya sukayi gabadayansu tare dayin sallama da junansu, sannan tatada mortar ta kama han'yar daze kaita gidan nasu dake unguwar Low cors dake cikin birnin bubayero.
Gidane mekyau da tsari, tun daga harabar gidan zakasan cewa 'antara naira acikinshi, saboda komai yaji 'acikinshi 'irin kuma nazamani da masu akwai.
Daga 'isarta bakin gate megadi yabude matah gate tashigye, tana parking tafito 'asanyanye, wanda tatsanane acikin kwanakin nan tafarayin four eye dashi.
Ido yatsura mata ko kiftawa bayayi!, yayin da 'ita kuwa ta dauke kanta, tafe take kamar wacce take jin tausayin kasar, cikin 'isa da yauki 'irin tatah take tafiya, komai nata acikin sanyin jiki takeyinshi, wanda hakan yasa 'ake ganin yangarta dayawa.
Masu aikin gidan ta tarar aparlourn kasa, hakan yasakata wucewa sama, dakinta tabude tashiga tare da rufo kofar, tana fadin wash nagaji.
Guntun tsaki taja tare da ajiye handbag din dake sakale ahannunta, cikin nutsuwa takarasa inda akatanadar matah domin karatu adakin ta'ajiye takardun dake rungume ahannunta, fridge din dake dakin natah tabude tadauko drink tanasha, tare da bin dakin natah da kallo tamkar yau tafara shigarshi.
Komai nadakin pink and milk, color din da tafiso kenan, dakin yayi matukar kyau da tsari, ankuma zuba naira acikinshi.
Se da tagama shan drinks din sannan tawuce bathroom dinta tawatsa ruwa, riga da siket tadauko tasaka na English wes marassa nauyi, akan makeken gadonta tamike tare da lalubo wayarta tadanna sannan takara akunnenta tanadan murmushi tamkar tana gaban masoyin natah.
Ringing daya yadauka yana fadin hello Dear inata neman wayanki inakika shigene haka, cikin sanyin muryarta medadin sauraro tace kamantane ay yau 'ina da lectures, toh ya kike yakatseta dacewa gaskiya nayi kewarki dayawa, nima haka Yayana tace.
Sannan tacigaba dacewa sati daya jinakeyi kamar mun shekara bama tare, wai yaushene Abba zedena turaka garuruwan nan, nikam Yaya nagaji, kamata yayi kadinga aiki anan, cikin yanayin shagwaba tacigaba dacewa Yaya ko kafison tafiyar.
Nide inajin tsoron kar watah takwacemin kai 'acan, aah Dear yace yanayi matah dariya wanda har tana jiyo sautinsa tawayar, sannan yace ni nakine kekadai kamar yanda kike tawa, babu wacce ta'isa tasha gabanki kinjiko My Dear.
Asanyaye takatseshi da cewa, Yaya kakira Abba kacemar zakadawo toh, don gaskiyi nayi kewarka da yawa.
Aah Yasmeen yace ay nakusa dawowa, domin nan da five days insha Allah nakammala abin dayakaini, haka sukacigaba da hirarsu 'irinta masoya tare kuma da nunawa junansu kulawa.
Husna ce tashigo da gudu tana ihu! Al'ameen ne biye da 'ita wai zedaketa, tana'isowa taboye abayan Yasmeen din tanafadin Adda Yasmeen kinganshiko wai zedukeni.
Itade kam YasmBahakanin tarude, domin babu abin dayake saurin rudad da 'ita kamar hayaniya, ganin haka yasashi juyawa, sannan Husna tafice da gudu, kai tadafe tanafadin hayaniyarku tafara 'isata agidan nan.
Adede lokacin da mahaifiyar tasu wacce suke kira da Ammi taturo kofar dakin tashigo, gyefenta ta zauna tanacewa yaushe kika dawo?
Ammi ay nadan dade da shigowa tace tana dan murmushi, tacigaba dacewa naji kamar kinyi bakine, kekuma bakyason jama'ah ko! Ammi takatseta dacewa.
Bahaka bane Ammi, hakane man Ammi tasake katseta dacewa, sannan tacigaba dacewa nide bansan lokacin da zakiyada wannan dabi'un nakiba Yasmeen, ace mutum shi bayason jama'ah, cike da kulawa ta kalleta tace kinci abinci kuwa ma?
Banajin yunwa Ammi tace nasha malt yanzu, amma ay malt ba abinci bane Yasmeen, kinsanfa banason zama da yunwa.
sundan taba hira da mahaifiyar tatah, sannan tasanar da ita muhimmin al'amarin dake tafe da ita, wanda kuma mahaifinnasu yasa asanar da itah.
Ganin numfashin diyar tatane yana neman daukewa gabadaya yasakata shiga cikin tashin hankali da rudani, sakamakon maganar datagaya matah.
Cikin hanzari tanufi parlourn megidan natah tana kwala kira Alhaji!Alhaji!! Alhaji!!!
Fu'ad ne yatareta cikin hanzari yana fadin Ammi lafiya? Meke faruwa?? Dakin Yasmeen kawai tanunamishi, dakyar ta'iya furta Yasmeen zata mutu Fu'ad daga bakinta.
Beyi wata-wata ba yanufi dakin da gudu! Cikin tashin hankali yakarasa 'inda take kwance.
Ganin konmotsi batayi yayi matukar tayar mishi da hankali, betsaya bata lokaciba yasureta yafice! Adede lokacin Ammi da Abba suka'iso kofar dakin, Abba natambayar Ammi meyasameta.
Alhaji daga sanar da 'itafa kawai naga tashiga wannan tashin hankalin Ammi tace wa Abba, cikin kankanin lokaci tunin Fu'ad yagama sauka daga kan staff's da ita, tamkar wanda yadauko yar baby.
Ahanzarce yanufi harabar gidan da 'itah batare da yasaurari ma'aikatan gidan dasuke faman tambayar lafiya ba.
Cikin hanzari yatada mortar yafice, Muhseen Clinic yawuce da 'itah dake nan 'acikin low cors, cikin gaggawa akashiga da itah (emergency).
Hankalin Fu'ad yayi matukar tashi! Tsaye yake abakin kofar, banda sakar zuci babu abindayake, tabbas Yasmeen bata sona! Abnee take SO" baniba, Yasmeen meyisa zakiso Abnee ba ni ba, why Yasmeen! Yabazaki So ni ba.
Jin da yayine andafa kafadarshine yafarga daga zurfin tunanin dayayi, Dr ne tsaye, asanyaye yabishi har zuwa office dinshi.
Kujerar datake kallon ta Dr yaja yazauna, cike da kosawa yakalli Dr yace Dr batade mutu ba ko? Dr kace ehh mana yasake cewa, cike da kosawa yacigaba da cewa bansan yazanyiba 'idan narasata, wallahi bazan taba gafartawa kaina ba idan har Yasmeen ta mutu adalilina.
Calm down Dr yace! Sannan yacigaba da cewa bata mutu ba, suma tayi sakamakon firgita datayi, amma tafarfado zaka'iya ganinta, sede akulafa my friend yasake cewa adena tayar matah da hankali, bejira Dr yagama maganaba yafice daga office din.
Cikin hanzari yanufi dakin da take tare da tura kofar yashiga, zaune yatarar da 'ita akan gado, Ido hudu sukayi da junansu, cikin muryar kuka tafara magana.
Yaya Fu'ad katemakeni shinake SO"! Inasonshi, don Allah karoki Abba yajanye wannan auren! Don Allah Yaya Fu'ad kayiwa Abba magana yajanye, kuka tacigaba dayi mefitar da sauti! Ayayin dashi kuwa yakaraso inda take yazauna agabanta asanyaye.
Magana tacigaba dayi kamar wacce tazauce, Yaya Abni kadawo gareni za'arabamu, Abba yadauramin aure da wanda bayasona! Wayyo Abba meyisa zakamana haka bakasan Yaya Fu'ad bayasona bane Abba!!!!!
Jin datayi anrufe matah bakine yasakata yin shuru! Ido yatsura matah yana kallonta, itama shitake kallo! Sede kuma 'idanuwanta sunkasa jure kallonshi, gabadaya yacika matah 'ido, wani 'irin kwar jini yake matah.
Jikinta yabi da kallo! Cike da mamaki yake kallonta, waidama haka Yasmeen dina take yace 'acikin ranshi, watah yar' rigace ajikinta, wanda yafitar matah da surar jikinta, dukiyar fulanin dake cike da kirjinta kuwa tamkar suna neman sufito waje, saboda 'irin kankantar rigar da kuma shape dinta.
Siket din dake jikinta kuwa yayi matukar kamata, wanda hakan yasa bayyanar hips dinta sosai, babu dankwali akanta wanda hakan yasa bayyanar kitson dake kanta kanana tamkar ba hannu bane yayishi.
Kitson yabi da kallo wanda ya sauko har gadon bayanta, irin kallon dayake matane yasatajin kun'ya, ganin kuma 'irin suturar dake jikinta, hakan yasatayin yan' waige-waige kozataga wani abun domin ta rufe jikinta.
Hannunta yakamo yahada danashi! Sannan yafara magana cikin nutsuwa, Yasmeen kikwantar da hankalinki, ya'isa haka dena kukan, waye yagayamiki banasonki 'iyye Yasmeen, kefa yar' uwatace kuma ay ni da Abnee duk dayane.
Kai takada, sannan tace badaya bane, domin Yaya Abnee shine masoyina bakai ba, wani 'abune yasokeshi akirji sakamakon jin maganarta dayayi.
Ahankali ya tallabo fuskarta suna kallon junansu yace! Ki kalleni kice bakya SO"na Yasmeen.
Idanuwanta talumshe tana kokarin furta 'abinda yace, jin datayine yayi kissing din lallausan labbanta (Sumba) yasakata bude 'ido cikin sauri.
Gabadaya kamanninshi sun canja, cikin kausassiyar murya yace ni nasan bazaki taba kinaba Yasmeen, domin nine Yaya Fu'ad dinki ba Abnee ba.
Karar wayar shine yakatse shi daga maganar dayake! Asanyaye ya ansa da hello Abba gamunan dawowa babu watah matsala insha Allah, sannan yakatse wayar yamaida kallonshi gareta yace muje gida ko Baby.
Akun'yace tamike dakyar saboda kayan dake jikinta! Ganin haka yasashi mika matah hijab dinta tasaka, hannunta yakamo sukafito, jitake kamar tazame hannunta daga nashi amma kuma setakasa hakan
Se da suka'isa bakin mortar sannan yabude matah tashiga tazauna, sannan shima yashiga yatada mortar sukanufi gida, zuciyarta cike take da fargaba da kuma zullumi ayayin da maganganun mahaifiyar tatah suke dawo matah acikin kunnuwanta.
Wai shin da gaske Ammi take andauramin aure da Yaya Fu'ad, hawayene suka wanke matah fuska mecike da damuwa da kuma tunanin masoyin nata, jin datayine mortar yatsaya yakatse matah tunanin datake tare da jan dogon numfashi.
Dakinta tanufa ko takalma babu 'akafarta, tanashiga ta turo kofar tare dasaka key! Hawayene yacigaba da kwaran'ya a'idonta 'ayayin datajingina da kofar dakin, tunanin masoyin natah kawai takeyi! Ayayin da kuka mefitar da sauti ya subuce matah wanda hakan yasakata durkushewa awajen.
Se datayi me'isarta sannan ta tashi tanufi bandakinta tadauro alwala tafara gayawa ubangiji domin neman sassauci acikin lamarinta.
WASHE GARI: Kwana tayi tana zullumin wannan al'amarin, gashi kuma tanemi wayoyinta gabadaya tarasa, hakan yasakata neman laptop dinta domin sanar da masoyin natah abin dake faruwa ta yanar gizo, amma shima batasamu ba, lamarin yayi matukar bata mamaki, domin 'itade tasan babu meshigowa dakinta, sannan kuma su Husna basataba kayanta kwata-kwata.
Tadade atsaye tana nazari akai amma kuma takasa samun mafita, hakan yasatanufi dakin Ammi.
Zaune ta tarar da 'ita akan carpet, da'alama ta'idar da sallar walaha ne, cikin nutsuwa takarasa ta zauna tare da yimatah barka da safia cikin shakakkiyar muryarta me'alamun tayi kuka har tagaji.
Ido tatsura matah, tadan fada cikin wuni daya kawai, se kuma tausayin diyar tatace yakamatah, tace Yasmeen 'inaso kiyi hakuri da wannan lamari, haka Allah yaso, munsan da cewar kinfi shakuwa da yayaku Abnee akan yayanku Fu'ad, amma wannan bazehanaki zama da yayanku Fu'ad 'amatsayin miji ba.
Kukane yasubuce matah don jin maganganun Ammi, cike da kulawa Ammi tadinga rarrashinta tare dayimatah yan' nasihohi! Asanyaye tadago kai takalli mahaifiyar tatah tace Ammi 'ina wayoyina da laptop dina bangansuba.
Ammi 'inaso nasanar da Yaya Abnee 'abindake faruwa, Ammi kar Yaya Abnee yagalefina.
Kallonta kawai takeyi don tasan babu wanda ze aikata daukan wayoyinta da laptop se Fu'ad, domin tasan yana da tsananin kishi da saka ido sosai akan abun da yadamu dashi.
Duk da cewar Abnee da Fu'ad duk daya suke awajen diyar tatah amma kuma tayi matukar tausaya matah, domin ganin 'irin SO" da kuma shakuwar dake tsakaninsu tun tasowarsu.
Ganin da tayi Ammi batace komai ba ne yasakata cewa, Ammi ko sunagurinkine? Batare datasake kallon indatake ba tace kije kitambayi mijinki.
Cike da tsoro ta zaro ido tana kallon Ammi! Ayayin da zuciyarta kuwa take bata sawarar hakura dashi ko da kuwa shidinne yadauka.
Jikinta asanyaye takoma dakinta tana neman mafita akai tare kuma da tunanin masoyin natah, domin tasan tabbas Abnee besan meke faruwa ba, da kuma yasani da tunin yadawo gida, kai takifa tana kuka mefitar da sauti.
Jin datayi ne anturo kofar dakin 'anshigo batare da'annemi 'izininta ba yasakata dagowa cikin sauri!!!
Adda Fanna tafurta ahankali, Dadan gudunta takarasa ta rungumeta tana kuka mefitar da sauti, cike da mamaki takamo hannunta zuwa bakin gado tazaunar da 'itah.
Adda Fanna yar' aminiyartace Halee Sa'eed, kuma tamkar yar' daki take awajen Ammi, zumuncinsu kuma yasamo asaline tadalilinsu Abba, domin babansu yaron Abba ne tabangaren kasuwanci, hakanne yayi sanadiyyar kulluwar zumuncinsu.
Sunyi matukar shakuwa da Yasmeen duk da cewa 'ita ba'agarin Gombe take aure ba, cike da kulawa takamo hannunta tace ya'isa haka Yasmeen gayamin mekefaruwa?
Hawayene yacigaba da kwaran'ya afuskarta! Hakan ya kara tabbatarwa Adda Fanna da cewa ba lafiya ba, Yasmeen mekefaruwa ne? Tasake cewa cike da kosawa.
Nashigo yanzu Ammi takesanar dani jiya andaura aurenki, memakon nazo nasameki cikin farin ciki se kuma ga sabanin haka, bayan wannan lokacine dakika dade kina jiran zuwarshi, bamake kadai ba har duk wani masoyinki.
Haba Yasmeen meye damuwarki? Bayan kuma burinki yacika, ko kinmanta da cewa kindade kina bani labarin wannan ranar da kuma irin farin cikin dazakinuna, idanuwanta tadago takalli Adda Fanna! Wanda tunin sun canja launi zuwa ja tafara magana cikin muryar kuka.
Adda Fanna jiya Ammi tasanar dani andauramin aure da Yaya Fu'ad bada Yaya Abnee ba, wani sabon kukane yasake subuce matah! Gabadaya ta kullewa Adda Fanna kai da maganganunta, hakan yasakata kada baki tace toh wai wayeneshi Yaya Fu'ad din da kuma Yaya Abnee??
Ido tatsurawa Adda Fanna tamkar tana kallon wani sabon 'abu, se kuma tayi dan guntun murmushi ayayin datah tuna masoyin natah sannan tace Yaya Abnee shine masoyina wanda nake burin kasancewa tare dashi har iya tsawon rayuwata.
Akagare Adda Fanna tasake cewa toh waye shi? Kuma waye Yaya Fu'ad?? Nima Mrs Yarima jin hakan yasakani karasowa domin jin 'ansar dazatabawa Adda Fanna.
Asanyaye tatashi tsaye kamar menazarin wani abu! Cikin sanyin muryarta tafara magana.
Yaya Abnee da Yaya Fu'ad dukkansu yan'uwan junane, Alhaji Usman Abnee shine da' na biyu 'awajen iyayensu Malam Auwalu da Gwaggo Meramu, Baba Muhammadu shine babba, sannan Alhaji Usman Abnee, se kuma Baba Iro da Gwaggo Hadiza da Gwaggo Zainabu.
ASALINSU:
Asalinsu fulanin Mambila ne (Taraba) amma tunsuna yara iyayensu sukadawo Yola da zama, sun taso cikin son junansu da kuma riko da al'adarsu ta Fulani, haka kuma boko besa sun yada abinda akasansu dashi ba, wato noma da kiwo.
Duk da cewa babu me zurfin karatun zamani acikinsu kamar Usman Abnee, kasancewar yanason karatu sosai hakan yasashi medahankalinshi gabadaya akai, wannan yasa ko maganar aure bayayi har kannenshi duk sukayi aure, ganin haka yasa iyayensu nema mishi auren yar'uwarshi Hauwa.
Yayi matukar farin ciki da zabin iyayen nashi, domin damah abinda yadadene yana SO" ne! domin Hauwa macece me matukar kyau da kuma nutsuwa, duk da cewa sumah ba bayabane afagyen kyau.
Haka akayi bikin Usman Abnee da Hauwa cike da kaunar junansu, ganinshi dan boko kuma wayayye hakan yasashi kaita makaranta domin cigaba da karatunta, don kuma gudun samun yawan banbanci azamansu na aure.
Kasancewar itama tana ra'ayin hakan yasamu goyon bayanta, tsawon shekaru biyu Usman Abnee da Hauwa basusamu haihuwa ba, ganin haka yasa Baba Muhammadu bashi danshi nafari Fu'ad, adede kuma wannan lokacin matar Baba Iro tasake haihuwar da'namiji, Nanfa sukayiwa Usman Abnee takwara (maisuna) wanda suke kiranshi da Abnee.
Usman Abnee da Hauwa suna matukar jida Fu'ad da Abnee, wanda hakan yasasuka dora musu SON" duniyar nan, tamkar su suka haifesu, duk da cewa shi kam Abnee ba'ahannunsu yake ba, amma kuma duk rabi acan yake wuni.
Suna kuma tafiyar da rayuwarsu cikin jindadi da rufin asiri, domin Allah yayiwa Usman Abnee arziki da kuma albarka acikin kasuwancinshi, kasuwanci yake har kasashen waje.
Bayan Hauwa takammala karatunta na N.C.E Usman Abnee yanemi sukoma birnin Bubayero (Gombe) da zama, awannan lokacin Fu'ad yana da shekaru shida da aihuwa 6 years, Abnee kuwa kwata-kwata shekarunshi hudu ne aduniya 4 years.
Haka Alhaji Usman Abnee yahada Fu'ad da Abnee suka dawo garin Gombe, yakuma rikesu tamkar shiya haifesu, domin inba angayama ba zakace ya'yan shine nacikinshi.
Fu'ad da Abnee suntaso cikin jindadi da kwanciyar hankali, babu kuma abin da suke nema surasa najin dadin rayuwa dede gwargwado, kasancewar Alhaji Usman Abnee yana da tarun dukiya.
Rayuwa sukeyi irin ta yaran man'ya, haka yasakasu amakarantu masu kyau boko dana islama, sede ayarintar Fu'ad da Abnee akwai sabani sosai, wanda hakan yasasu rashin jituwa, domin shide Fu'ad yarone marar son magana, haka kuma kwata-kwata bayason hayaniya.
Abnee kuwa duk inda hayaniya da harkar magana yake tohfa yananan, wannan yasa tasu batazuwa daya da Fu'ad, domin shi miskilin yarone, Fu'ad da Abnee suna dan' iban kama, domin duk kansu kama suke da iyayensu maza, gashi kuma iyayensu auren dangi sukeyi bisa al'adar zuriyarsu, hakan yasa duk yaran gidansu (family) suna kama da junansu.
Sede shi Fu'ad bayida jiki kamar Abnee, domin Abnee yana da garin jiki sosai, kuma Fu'ad fatarshi farine sol, shikuwa Abnee yadanyi yellow.
Fu'ad yafi Abnee kwazo takowane bangare, wannan yasa Alhaji Usman Abnee kudirin bawa Fu'ad dama domin zurfafa iliminshi, sabanin Abnee da yasa wasa acikin ranshi.
Kallo daya zakayiwa Fu'ad da Abnee kasancewa Fulani ne na'asali kuma yan'uwan juna, gashi suna da matukar kyau, wanda hakan yasa mutane ke dangantasu da larabawa.
Bayan shekaru shida Fu'ad ya gama karatunshi na matakin primary, nanfa yacigaba da secondary dinshi anan cikin G.H.S shikuwa Abnee yana daf dagama tashi primary din duk 'anan G.H.S din.
Kwatsam Hajiya Hauwa tasamu ciki! Murna wajen Alhaji Usman Abnee ba'amagana, bayan watanni tara ta'aifi diyarta kyakykyawar gaske, wacce taci suna Yasmeen.
Yasmeen tana da matukar kyau tun daga jariranta, gashi kowa yaganta seyasota, murna wajen yan'uwa da abokan arziki ba'acewa komai! Anyi shagalin suna nakece raini, irin kuma na gidan man'ya masu akwai, domin ankashe naira.
Tunda aka haifi Yasmeen yazamana Fu'ad ne merenonta, domin Fu'ad yarone meson yara sosai, hakan yasa 'idan ba makaranta yajeba tohfa yananan 'agida yanayiwa Yasmeen wasa, sabanin Abnee kuwa da sede yadagata ya'ajiye.
Haka Yasmeen tafara wayo babu wanda tasaba dashi kamar Fu'ad, wanda hakan yasa 'idan Fu'ad yana gida tohfa batayadda da kowa seshi, don hatta mahaifiyarta wacce suke kira da Ammi bata yadda da 'ita.
Duk wanda yake gidan yasan shakuwar Yasmeen da Fu'ad, kwata-kwata Fu'ad bayason yaji kukan Yasmeen, haka kuma ko bacci tayi dakyar yake zamewa yatafi nashi dakin, inko tabude ido taga bayanan tohfa rigima tatashi, haka kuma bata bacci se ajikinshi.
Tun Ammi tana hana Fu'ad har tagaji tabarsu, domin tana matukar tausaya mishi narashin hutun dayake samu idan yana gida.
Bayan shekaru biyar Fu'ad yakammala karatunshi na Secondary, nanfa Abba yasamamishi makaranta acan kasar U.S, nan 'akahaushiri domin tafiyar Fu'ad makaranta.
Ranar da Fu'ad zetafi Yasmeen tayi kuka sosai, domin 'irin shakuwar dasukayi tawuce misali, shikanshi Fu'ad sedayayi kwalla don dekawai zabin Abba ne fitar tashi wajen, domin shide besoyayi nisa da Yasmeen ba.
Haka aka banbareta dakyar 'ajikin Fu'ad, tamkar wacce ake cirewa wani bangare ajikinta, kuka takeyi sosai, suna kallo 'ita da Amminta jirginsu yatashi zuwa kasar U.S, wannan rabuwa se datasaka Yasmeen zazzabi, saboda irin sabon datayi da Fu'ad, komai kuma nasu tare sukeyinshi.
Haka gidan yazame matah tamkar babu kowa acikinshi, satin Abba daya acan kasar U.S yabaro Fu'ad yadawo gida Nigeria, haka Fu'ad yafara karatunshi cike da kewar kanwartashi Yasmeen, haka 'itama Yasmeen din anata bangaren, tafara karatunta na matakin nursery.
BAYAN WANI LOKACI:
Yasmeen tana kammala nursery tashiga matakin primary a'inda yayanta Abnee yake nashi karatun, haka rayuwar Yasmeen tacigaba da tafiya, tun basa jituwa da Abnee har sukafara jituwa, hakan yazama komai natah tare da Abnee sukeyinshi, tun 'ana fada ashirya.
Sede kullun Abbanta yana kira matah yayanta Fu'ad awaya suyi magana sosai, tun tana damun Abbanta har tafara wayo tasaba da rashinshi, kasancewar kuma rayuwarta tafara canjawa, domin tafara sabawa da yayanta Abnee sosai.
Shekarun Yasmeen shida aduniya Ammi tasake aihuwar Al'ameen, cikin ikon Allah Al'ameen yana da shekara daya aduniya tasake haihuwar Husna, shekarun Husna biyu tasake haihuwar Arfat, sede awannan karon tasha wahala sosai, wanda hakanyayi sanadiyyar lalacewar mahaifarta gabadaya.
Hakan yasa tsayuwar haihuwar kuma gabadaya, haka rayuwar Yasmeen tacigaba da tafiya tare da yan kannenta cikin jindadi da kwanciyar hankali tare kuma da kulawar iyayensu.
Haka kuma abangaren Abba yana yawan zuwa kasar U.S domin yaga Fu'ad da kuma abokinshi Alhaji Jamilu Shinku dake zauna acan, domin Fu'ad dinma agidan abokin Abban yake zaune tare da iyalenshi, kuma yana samun kulawa sosai awajensu.
Kwance tashi babuwuya awajen Allah, har Fu'ad ya kammala karatunshi na digiri afannin engr Amma betaba zuwa gida Nigeria ba, domin Abba yace baseyazoba yayi karatunshi kawai, nanfa wani company yanemi yayi aiki tare dashi acan U.S, don ganin 'irin kwazonshi.
Amma kuma fir yaki amincewa, Alhaji Jamilu dakanshi yakira Abba yashedamar, domin shide Fu'ad yanaso yadawo gida yayi aiki acikin kasarshi, babu kuma abun da yakeson gani illah yarkanwarshi.
Duk da cewa basayin waya yanzu, atunaninshima de yanzu kam tamanta dashi, tunda rabonshi da ita tun tana karama, sede shikam yana rike da kamanninta na yarinta duk dayake andau shekaru, tayiyu tacanja kamanni, ganin 'irin wannan cigaba yasa Abba tilastawa Fu'ad dole yayi aiki tare da company koda kuwa nadan wani lokacine, wannan yasa Fu'ad hakura yacigaba da zama akasar U.S yakuma fara aikinshi.
BAYAN SHEKARU GOMA DA TAFIYAR FU'AD KASAR U.S:
Abnee yakammala karatunshi nagabada secondary acan A.T.B.U har yagama bautar kasarshi N.Y.S.C, kasancewar business man ne shi yatsaya abangaren harkokin kasuwancin Abba nanan gida Nigeria.
Yasmeen kuwa takammala karatunta na secondary tazama budurwa sosai, kyanta yakara fitowa gashi kuma dama kyanta 'irin me daukan hankalin nanne.
YASMEE:
Doguwace fara tass, kanaganinta kaga diyar Fulani gaba da baya, tana da dara-daran idanuwa masu shape mekyau kuma da daukar hankali, ga dogon hancinta wanda yakarawa dan faffadar fuskarta kyawu, bakinta kuwa dan madedecine.
Tana kuma da gashi mesilbi da taushi irinna Fulani, wanda hakan yasa koda yaushe zakaga tayi parking nashi, saboda wahalar kitsuwarshi, kallo daya kayi matah saikasake kallonta, saboda tsantsan kyan da Allah yayi matah.
Abba ne yasama matah admission a G.S.U (Gombe state university) nanfa tafara karatunta na Mass com, Duk ranar datake da lectures Abnee ke kaita makarantan kuma yadaukota, haka kuma bayabarin driver yakaita sedefa 'idan baya garin, domin Abba yahanata driving.
BAYAN SHEKARA DAYA:
Soyayyace mai karfi takullu 'atsakanin Abnee da Yasmeen, wanda hatta 'acikin danginsu ansan da soyayyarsu (family), Yasmeen da Abnee sunyi matukar shakuwa da junansu, hatta 'iyayensu sunsan da hakan.
Zaune take ababban parlourn fake kasa (main parlour), chart take da wayarta, da 'alama tanajin dadin yanayin garin, Abba ne yasauko sanye yake cikin farar shadda kal, yadora farar hula da farin takalmi, hatta agogon dake sakale ahannunshi fari ne, yayi kyau sosai da shi se kamshi yake.
Ayayin da Ammi kebiye da shi domin yimar rakiya, ido tabita da shi, sanye take cikin atamfa ta exclusive koriya (green color) dinkin riga da zani, takafa daurin dankwali wanda yadace da halittar kayinta, kamshin turarensune yagauraye parlourn me dadin shaka ahanci, wanda hakan yahana gane aynihin color din turaren da sukayi amfani da shi.
Kallo daya zakayi musu kasan cewa jini daya ne su, parlourn sukakaraso ayayin da Abba yakalleta yace diyar Abba yaufa yayanki yana hanya insha Allah, saboda haka kishirya mishi abinci namusamman, saboda nasan bakida matsala awannan bangaren yace cike da zolaya.
Ammi ce takatseshi da cewa Alhaji kadena koda diyar taka dayawa, dariya kawai sukayi gabadayansu, itade Yasmeen ido tazubawa mahaifin natah, itakam atunaninta batada yayan dayawuce Abnee, gashi kuma yananan agarin babu inda yaje.
Muryar Abba ne takatseta da cewa kobakyajine, nace kishiryawa yayanku Fu'ad abinci yau zedawo.
Waishin meye Abba yadamu da wannan mutuminne dasuke kiranshi da yayanmu taraya acikin zuciyarta, tabbas naga alamafa Abba yadaukeshi da muhimmanci sosai tasake rayawa aranta.
Ammi ce takatse matah tunanin datakeyi wanda yahanata jin 'abin da Abba yace, waibadake akebane Yasmeen kinsanfa banason wannan kyaliyar taki.
Cike da yanayi irinta shagwaba tace don Allah Abbana kayi hakuri banjibane, kai kawai Abba yakada, domin yana mamakin yanayin diyar tashi wani lokacin.
Asanyaye tacigaba da cewa Ammi bansan 'abindazan dafabane, kinsan matasan nan idan sunga sunfita kasashen turawa se ahankali, harara Ammi tawatsa matah, sannan tace toh sannu marar kun'ya, toh kode bazeci ba dolene ki girka, kinsande kina gidan nan bazan shiga kitchen don nagirka mishi abinda za'atarbeshi ba, kuma yafi karfin 'abar masu aiki kawai suyimar abinci.
Abba ne yakatse Ammi da cewa ya'isa haka, ayayin dayamaida kallonshi ga Yasmeen dake faman zumburar baki yace karkidamu diyar Abba, zeci duk abinda kika girkamar, domin nasan da'na bayi da matsala.
Su Al'ameen ne suka shigo da gudu cike da murnansu sunafadin Adda Yasmeen wai yau akace Yaya Fu'ad zedawo!!!! Tsawa tasakar musu wanda yajawo hankalin iyayen nasu yadawo kansu.
Tunin itade Husna kam takoma kusa da Amminta, saboda ta tsorita da ganin yanayin Addan nasu, Ammi ce tace banaso Yasmeen kidena tsoritarmin da di'ya, ayayin dasuka fice gabadayansu daga parlourn.
Talura da cewa duk gidan nan kowa yana sonshi, wani haushin shine da kishi kuma yakamata, domin gani takeyi yana nema yakwace matah kujerarta awajen Abbanta, dole yasa ta tashi tashiga kitchen badon tasoba.
Tadade atsaye batare datasan abinda zata girka ba, can kuma tayanke shawarar dafa komamiyene, idan bazeci ba yabari, tunda itade ba Cook dinshi bace, dogon tsaki taja hade da murguda baki tamkar yana kallonta, azuciye takira Ramatu mai aiki tasakata fere doya tadora awuta.
Tana dafuwa tasakata tadaka sakwara mekyau ta kuma nade tasaka akula, miyar edika-ikon tayi wanda yasha kayan hadi me rai da motsi, se kuma pepper soup na naman rago datayi, takumayi fish nurgghet da hadadden pineapple drink.
Ramatu tasaka tagyara kitchen din takuma wanke komai tashare, ita kuma tashirya dinning room (dakin cin abinci)! Agajiye tawuce sama, domin rabonta da irin wannan aiki meyawa tun dawowar yayanta kuma masoyinta daga bautar kasa.
Bathroom dinta tafada tayi wanka tadauro alwala sannan tagabatar da sallar la'asar, kasancewar agajiye take tamike amakeken gadonta, baccine menauyi yadauketa cike da kwanciyar hankali.
0 comments:
Post a Comment