Shigowar Husna da Arfat ne yatada ita daga baccin dayadauketa, cike da murna Husna ta kalleta tace Adda Yasmeen kinga yayanmu nakasar U.S kuwa, kamar balarabe kuma sunadan kama da Yaya Abnee, cike da doki tacigaba da cewa Adda bakiganshi ba wallahi suna kama sosai da Yaya Abnee, sede wannan yafi Yaya Abnee kyau da haduwa!!!!!
Marin da Yasmeen din tayi matane yasakatayin suru daga maganar datakeyi, wanda hakan yasakata ficewa daga dakin, cikin sauri Arfat yabi bayanta, ayayin da taja dogon tsaki tana mamakin yanda kowa agidan yakeson wannan yayan nasu, wani irin haushin shine yakaru matah hade da kuma tsanarshi.
Fridge dinta tanufa dake dakin azuciye domin shan abumedan sanyi, tadade atsaye tana mamakin Husna da kuma irin yanda aka damu dashi, jin gidan yayi tsitt ne tamkar babu kowa acikinshi yasakata saukowa kasa.
Ahankali take taka kan staffs din tamkar batason saukar, ido yazuba matah ko kiftawa bayayi cike da mamaki, sanye take cikin riga da wando na Pakistan dede jikinta, parking din gashinta kawai tayi wanda yasauko matah har kafadanta, fuskarta fayau take babu kwalliya, tabbas wannan itace Yasmeen dina yace acikin ranshi, gaskiya tahadu dayawa yasake rayawa acikin zuciyarshi.
Amma daga ganinta zatayi tsiwa dayawa, sede kuma zatayi shagwaba dason jiki yasake rayawa acikin ranshi, ayayin dasukayi ido hudu da junansu, nantake taji wani abu yadaki kirjinta, wanda ita kanta batasan ko menene ba.
Dole su Husna suce balarabene tace acikin zuciyarta, amma gaskiya yagama haduwa, duk yanda nake ganin Yaya Abnee yahadu amma wannan yafishi tasake rayawa acikin zuciyarta, gaskiyar Husna datace suna kama da Yaya Abnee, sede daga ganinshi miskiline tasake cewa acikin ranta.
Kanta tadauke tamkar batasan yana kallonta ba, se da takusa isowa indayake se kuma zuciyarta taraya matah 'anya kuwa wannan yanajin harshen Hausa, saboda yanda taga yanayinshi, hakan yasakata canja harce ayayin datakaraso inda yake.
Cikin sanyin muryarta medadin sauraro tayi mishi barka da zuwa cikin harcen turanci, (ur welcome), murmushi yasakar matah wanda yasa bayyanar wushiryarshi dake karamishi kyau, sannan yamayar matah cikin harcen larabci.
Cike da mamaki takalleshi, saboda azatonta yajuye turawane, murmushi yasakeyi yace kina mamakine, banyasar da yarena ba ay, awannan karon da harcen Hausa yayi maganar.
Tabbas cike da mamaki take amma kuma se tabasar, tace yaza'ayi nayi mamaki hade da yatsina fuska, ayayin data wuce store batare datah sake kallon inda yake ba, cike da mamaki yabita da kallo, domin yalura tana matukar ji da kanta, lallai yazama dole nacanja salo, domin kar yarinyar nan tarenani yace acikin zuciyarshi.
Katon din drinks tajawo har zuwa parlour tare da kwalawa Ramatu me aiki kira, Abnee ne yashigo parlourn, ganinta tsaye da katon din drinks agaba yace my dear lafiya kuwa? Cikin yanayin shagwaba tare da langabe kai tace yayana fridge dina ba'asamin drinks ba aciki, kuma nakasa daukanshi da nauyifa dayawa takarasa maganar tare da dan zumbura baki ashagwabe.
Dariya yake matah cikin sigar tsokala, saboda yasan halinta sarai na shagwaba, shide Fu'ad dake kwance cikin kujera ido yazuba musu cike da mamaki.
Tunin Abnee yakwashi drink's din yahawar matah dashi sama, sannan yadawo parlourn yazauna tare da yiwa Fu'ad barka da yammah, cike da yauki irin natah itama takaraso parlourn tazauna akujerar dake kusa datah Abnee.
Hirarsu sukafarayi tunin sun manta da Fu'ad dake kwance agyefensu, Yasmeen kam se faman murmushi takeyiwa masoyin natah, wanda kuma yake kara matah kyau, ayayin dashi kuwa Abnee kefaman kyakyata dariya domin jin dadin labarin datake bashi na wani littafin datah karanta mesuna NI DA ASWAD! na Suwaiba Muhammad Gombe (Mrs Yarima).
Fu'ad kuwa wani abuyaji yatokaremishi awuya wanda besan ko menene ba.
Kiran sallar magrif ne yatadasu gabadayansu daga parlourn, ayayin dasu Abnee suka wuce masallacin dake cikin gidan, ita kuwa tanufi dakinta domin gabatar danata sallar.
Se karfe takwas 8:00pm kowa yahallara ababban parlour domin yin dinner kamar yanda sukasa ba, amma kuma shuru Yasmeen batafito ba.
Abnee dayaga haka tunin yadubata online, nanfa yaganta, bebata lokaci ba yatura matah dasako kamar haka, Hey my dear! Bakiduba time bane, banganki akasaba har yanzu, ko sarautarne tamotsa.
Murmushi tayi datah karanta sakon nashi sannan itama taturamishi da cewa banajin yunwa, yace OK! Se anjimato zamuyi magana.
Fu'ad kuwa jiyakeyi gabadaya wajen bayamar dadi dabega Yasmeen ba, saboda bayagajiya da kallonta, duk da cewa kuma bawai hira sukeyi ba.
Abba ne yakaraso dinning room din, ganin bega Yasmeen ba yace da Husna mazatahau sama takirawota ayi dinner, kwance ta tarar da ita tana chart a laptop dinta, bataso tashi ba domin tasan ko tace takoshi tohfa Abba ze'iya hawowa yasameta da kanshi.
Dan mayafinta na Pakistan dake jikinta tajawo ta rufe kanta dashi tabi bayan Husna zuwa parlourn, kusa da Abba tasamu tazauna, ganin haka yasa Ammi cewa kinzo kinsa mutane agaba ko gaisuwa babu ko kallonki mukazoyine, asanyaye ta mike domin tamanta da itace takeyin saving nasu aduk lokacin dazasuci abinci.
Sunci abincin sosai tare kuma dayaba matah, Fu'ad kam yayi mamakin yanda ta'iya girki haka, sede kuma yadake kamar baya santi, ayayin da Abnee kuwa se faman santi kawai yakeyi, saboda baya boye damuwarshi, cike da kulawa ya kalleta yace Dear wai a'ina kike koyo irin wannan Special Delicious ne haka? Kode kin canja cors ne bansani ba??
Dariya kawai su Arfat keyimar, Abba ne yakatseshi da cewa junior Abnee natabbatar da santi kawai kakeyi, Yasmeen kam taji dadin yanda masoyin natah yaji dadin girkin natah sosai, tatabbata idan sunyi aure zatadinga burgeshi har abangaren girkima, wanda hakan yasakata sakar mishi murmushi har se da dimples dinta ya lotsa tace yayana bancanja cors ba, duk girkin dakaga inayi a SUWAIBA MOHD GOMBE GROUP ake koyarwa, saboda yatara man'yan matah kuma kwararru abangarori daban-daban, hmmmm! Bamah girki ba harma da gyaran fata dade sauransu.
Ammi ce takatseta da cewa ayba karamin kokari sukeyi ba, domin suna temakawa yara mata sosai, Fu'ad kam ido yatsura matah, yakuma lura da batason cin abinci, domin tun zamansu bataci abincin dayakai spoon biyar ba.
Shiyisa batayin jiki yace acikin ranshi, muryar Abba ne takatse mishi tunaninshi da cewa dan' Abba kaga Nigeria wani iri ko? Murmushi yayi wanda yazamemishi jiki sannan yace Abbana Nigeria babu wani cigaba, saboda baza'ahadata da kasashen turawa ba, kasan turawan nanfa Abba sunfimu kishin kasarsu.
Abnee ne yakatsesu da cewa mukam 'ay munhadu da azzaluman shuwagabanni ne kawai, domin aymuma munada arzikin kasar dasuke takama dashi, kawai de rashin kishin kasa ne, haka sukacigaba da hirarsu, sede ya fahimci Abnee haryanzu yananan dashegen surutun nan tashi becanja ba, yana mamakin kuma yanda akayi har suke dedetawa da Yasmeen, domin yalura kamar batada yawan surutu.
Muryar dayake jin dadin saurarone atsawon wunin yau yaji takatsesu da cewa, Abbana gobenefa bikin kawata Mufida danake gayama, kuma agoben ake family and friends dinta, shizansamu zuwa don sauran kwanakin ina da lectures.
Dawane lokacine Abba yace? Karfe uku ne 3:00pm race, ashagwabe tacigaba da cewa Abbana account dina yayi low dayawa, kuma ina bukatar naje da motor, saboda bikin babbar yarinya za'ayi Abbana, murmushi yayi sannan yace toh diyar Abba, zanyimiki transfer zuwa account naki anjima, maganar motor kuma kije kisamu yayanki Fu'ad zekaiki, cikin shagwaba tace Abba de!!!!!
Hannu yadaga matah, alamun bayason tace komai, sannan yacigaba da cewa daga yau kuma duk wani abinda kike bukata kije kitambayi yayanku Fu'ad, zemiki duk abun da kike bukata.
Maganar Abba yadaure matah kai, Abnee shima beji dadin hakan da Abba yace ba, domin atunaninshi shine yafi da cewa yakula da duk wani al'amuran Yasmeen bawai Fu'ad ba, se kuma yaji beji dadin wannan maganar da Abba yayiba.
Fu'ad kuwa cike yake da farinciki fal! Don jin irin hukuncin da Abban yayanke, don ko babu komai nasamu damar dazan kula da kanwata yace acikin zuciyarshi, tashi tayi ta wuce dakinta don rashin jindadin maganar Abbannata, shikam Fu'ad se kuma yaji beji dadin tafiyar taba adaya bangaren kasar zuciyarshi, domin bayagajiya da kallonta da kuma jin dadin muryarta, shima Abnee tashin yayi yanufi nashi dakin tare dayiwa iyayen nasu se da safe, don yasan yaude babu wani hirar daze samu daga wajen gimbiyar tashi.
Kwance take akan makeken gadon natah, kirar Italian bed, ayayin da take tuno maganganun Abba da kuma irin sharudan daya gindaya matah, wai yanzu Abba yana nufin wannan miskilin mutumin zandinga tambaya abu, gaskiya bazeyiyu ba tasake cewa acikin ranta, ayayin dataja dogon tsaki, duk yanda taso tasake ranta amma takasa hakan.
Acan bangaren Abnee kuwa tunin yabasar da abun, domin yafahimci kawai Abba ya yanke wannan hukuncinne don Fu'ad shine sama dasu.
WASHE GARI:
Mufida ce tabugo sammako, amaryar da ake bikinta yau, jin kawar tatah tayi mata waya baratasamu halarta bikin natah bane yasakata zuwa, domin zuwanta yana da muhimmanci sosai awajenta, don itace babbar kawar amarya.
Dakin kawar tatah tawuce kaitsaye, akwance tatarar da ita tana kwasar baccinta, tsalle tayi akan gadon tare da saka ihu, wanda yasakata tashi afirgice zata gudu, tace ina kuma zakije sarkin tsoro tana dariya.
Jin haka yasakata tsayawa, Mufida meye hakan kuma tace, kinyiwa mutane sammako kamar wacce take bin bashi, ke Yasmeen banda sharri, karfe 9:00am shine nayi sammako, saboda ke sarkin bacci ba.
Toh ya shirye-shiryen biki takatseta da cewa? Gaskiya Yasmeen jiya banji dadi ba hakan ne ma yasakani zuwa naji ko Ammi ce tahanaki zuwa senaje naroketa.
Baki tatabe sannan tace babu wanda yahanani, kawai rainane yabaci Mufida, acewai don zanfita se wani yakaini, wayeshi Mufida takatseta da cewa akagare?
Wani brother dinmune Mufida, dan girman kaine, gashi kuma miskili, ko don yaga daga outsider yadawo oho.
Mufida ce takatseta da cewa toh waye zenunawa bude ido da kasashen waje, kawata ay naga kema kinzagaya babu lefi, idan kuma miskilanci yakeji dashi ay gidanta yazo, kuma ay Abba dama yabaki basekidinga juyashi kamar driver ba muga karshen girman kan.
Allah kawata tace ayayin dasuka saka dariya gabadayansu, sundan taba hira sannan tayi matah rakiya tagaida Ammi, seda tarakata har bakin motor ta sannan sukayi sallama, da tunanin maganganun Mufida takoma cikin gida, sede kuma tundatafara ganinshi taji yacika matah ido, anya kuwa zata'iya medashi driver kamar yanda Mufida tace, guntun tsaki taja tare da sauke dogon numfashi.
Haka tawuni tana sake-sake acikin ranta, se karfe hudu 4:00pm tashiga wanka sannan tayi zaman yin kwalliya, tabata lokaci sosai awajen kwalliya, abinka da dama me sanyin jiki.
Tafesa kwalliya irin ta zamani wanda kuma yakara fitar matah da kyanta, har tadauko doguwar rigarta ta les zatasaka Husna ce ta turo kofa tashigo rike da leda ahannu tamika matah, batare datah karba ba tace namiye kuma?
Ammi ce tace wai nakawo miki kisakashi idan zakije wajen family and friends din Adda Mufida, fuska tadan yamutsa tare da duba ledar tana cewa Ammi nikam dakinbari nasaka wanda nayi niyyarsakawa, ayayin da kuma acan cikin zuciyarta take matukar yabawa mahaifiyar tatah irin yanda take basu kulawa.
Materials ne dinkin riga da siket da kuma gyalenshi me matukar kyau da tsada, yasha ado sosai, blue color and Golding, kayan sunyi matukar yi matah kyau.
Ita kanta kayan sunburgeta sosai gashi kamar angwadata, haka Husna tadinga santin kayan tare da yabawa.
Takalma tadauko da jaka suma Golding color, sannan tasaka sarka da yankunne duk Golding color, sewani sheki take zubawa kamar 'itace amaryar, gawani kamshi datakeyi namusamman.
A parlour tatarar da Ammi tare da kannenta, cike da murmushi tace Ammi nayi kyau? Kinga kamar tailor yagwada ni, gaskiya ya'iya dinki, nagode sosai Ammi, Allah yakara arziki tasake cewa cike da ladabi.
Ido Ammi ta tsura matah tana mamaki, domin batada masaniya akan kayan da Husna takai matah, Husna takalla dake gyefenta, wacce take faman dariyar da basusan ma'anarta ba, tabbas Husna tana da masaniya akan kayan nan Ammi tace acikin ranta, sannan ta kalli Yasmeen dake tsaye tace kinyi kyau sosai diyar Abba, Allah yakiyaye hanya.
Husna takalla tace kije kicewa Yaya Fu'ad nashirya, batadade da fita ba ta dawo tace yace kijira yashirya, dogon tsaki taja tace ga irinta nan ay Ammi, kawai zebatamin lokacine!
Ke Yasmeen yaushe wuyanki yayi kwari haka Ammi tace, lallai bakida kunya, Yayan naku kikefadawa haka Yasmeen, ko kin dauka driver ne daze zauna yana jiranki, toh baki'isa ba.
Ammi fa yasan da zuwana bikin tace tana dan zumbura baki, ehye!! Sannu ishashshiya Ammi tace, tohbaki kai nan ba daze zauna yashirya yana jiranki, idan bazaki iya jiraba ayse kifasa fitar tunda bake kika ajiyeshi ba.
Kwallane yacika matah ido saboda takaici! Tsanarshi takeji acikin ranta, se karfe biyar da rabi 5:30pm yashigo parlourn, batare da yakalli indatake ba yace Ammi zamufita se mundawo ayimana addu'ah.
Toh Allah yatsare Ammi tace, yajima da fita bata tashi ba, Ammi ne takalleta tace Yasmeen ki kiyayenifa, kinsan banason irin wannan halin, kinsan baki da niyyar fitar kikabari yashirya, toh kitashi tun kafin raina yabaci!!
Azuciye tafice tana hararar Husna da take faman yimata dariya, tunin har tashiga motor, Motor ce kirar Land Crouse's baka, se yanzu takula da kayan dake jikinshi, takuma fahimci dariyar da Husna takeyi matah.
Wato wannan mutumin ne yabawa Husna kayan nan takawomin ba Ammi ba, lallai Husna zatagane kuranta tasake cewa acikin zuciyarta! rigar jikinshi irin kayan jikintane wato Material, ammishi dinkin Pakistan irin ta maza, se kuma wandon jeans da yasaka blue color, haka takalman dake kafarshi suma blue color da kuma agogon dake manne atsintsiyar hannunshi.
Yayi matukar kyau tamkar wani ba'indiye, cikin yan' seconds takare mishi kallo, sundade ahaka shuru batare dayata da motor ba, kamar meyin rada ahankali yace Yasmeen kidawo gaba.
Wani abune yadaki kirjinta nantake, bata taba jin wanda ya'iya furka sunantaba kamarshi, ko kuwa wayewace kawai da boko irin tashi.
Asanyaye tabude gaban motor ta zauna, sannan yatada motor suka fice, hanyar daze kaisu Jewel suit yadauka batare da ya tambayeta ba, kasancewar 'acikin garine basuyi wani tafiya menisaba suka'iso, sunashiga sukatarar da waje ancika makil.
Har amarya da ango sun'iso anashirin farah programs, Yasmeen kam tayi mamakin ganin ango da abokanshi yanda sukayiwa Fu'ad cha kowa na magana, da alamun sunsan juna sosai damah.
Ya'akayi yasan mutane sosai shi da ba'a kasar ya girma ba tace acikin ranta, ango ne yakaraso inda suke tare da amaryarshi, ganin yanda suka rungumi junane yatabbatar matah da cewa badon ita yazo bikin ba, don daga gani kasan yana daya daga cikin man'yan abokan ango, don gabadayansu abokan angon shigarsu irina Fu'ad ne.
Sadik ne yanunawa Fu'ad amaryar tashi yace Fu'ad wannan itace Mufida, ayayin dayamai da kallonshi ga Mufida yacigaba da cewa Mufida wannan shine Fu'ad da kuke gaisawa awaya, tare mukayi karatu dashi acan kasar U.S, cikin zolaya yacigaba da cewa sedeshi yanzu yazama dan U.S, don turawa sun kwaceshi.
Dariya sukayi gabadayansu, Mufida kam kallon kawar tatah tayi, saboda batasan shine brother din natah datake bata labari ba, Fu'ad ne yakatsesu da cewa Sadik wannan itace Yasmeen, kai kawai Sadik yadaga yana dariya, sannan yace ay friend tunin naganeta danaganta.
Itade Yasmeen tayi matukar mamaki, domin batasan Fu'ad yasan Sadik da Mufida ba, tohma wai a'ina Sadik yasanni da har yake cewa yaganeni, bamu taba ko haduwa dashi ahanya ba balle yace yataba ganina tace acikin zuciyarta.
Kawayen sune sukakaraso wajen kowacce tana ji da kanta, Yasmeen sukafara yiwa tsiya cikin zolaya, se yanzu ta'iso don jin kai, can watah kawarsu Nabeela Ishaq takalli Fu'ad da tunda suka'iso wajen yadauke kai tare da tsuke fuska tace kawata Gaskiya kin'iya zabe, saboda kun DACE da junanku, harara Yasmeen din tawatsa matah, ayayin da ita kuwa tayi dariya tace tohmiye ay gaskiya nafada, ko kishi kike saboda nafadi haka.
Bataji dadin maganar kawar tasuba kwata-kwata, se da sukayiwa amarya da ango rakiya har zuwa wajen da akatanadar musu domin zama, sannan kowannensu ya koma yanemi waje ya zauna.
Jidatayine mc yana kiran babbar kawar amarya Yasmeen Usman Abnee tare da babban abokin ango watoh Fu'ad Muhammad gabanta yafadi cike da fargaba.
Gabadaya wajen yayi tsit sukadai ake jira domin siyiwa baki barka da zuwa tare da bayar da tarihin amarya da ango atakaice.
Fu'ad ne ya'iso inda take zaune cikin nutsuwa, domin takasa tashi ganin yanda aka zubo matah ido, hannunshi yamiko matah, ayayin datah bi hannun da idanuwanta rana kallo tamkar tana kallon wani abu aciki, batare datasani ba taji natah hannun acikin nashi, amma kuma seta tsinci kanta da kasa kwace hannunta daga cikin nashi hannun, ahankali yakaraso daf da kunnenta yace muje ko.
Cikin nutsuwa sukakarasa harzuwa gaban mc din, ayayin da mc yamikawa Yasmeen abin magana domin yiwa baki barka da zuwa, ta dade atsaye batare da tace komai ba.
Fu'ad ne yadawo daf da ita yace, kanwata tsoron waye kikeji haka da har zehanakiyi abinda yadace, kanta tadago sukayi ido hudu da junansu, ayayin dayadan daga matah girarshi yana murmushi, se kuma tatsinci kanta itama da sakar mishi murmushin.
Cikin sanyin muryarta medadin sauraro tafara magana, magana takeyi tamkar me koyon yin magana hade da yanga irin natah, cikin harcen turanci tafara da cewa!
Hello Lady's and gentlemen's, I Welcome's all to this of occartion, hare with us the joy and happiness of weeding ceremony, I want also reconies the present of all king personality especially (so and so), I welcome's u wants again to this important occartion, thank u all.
Fu'ad tamikawa abin maganar yafara bada tarihin ango atakaice cikin harcen larabci, sannan itama tabadana amarya cikin harcen Hausa, nanfa waje yadau tafi.
Fu'ad yasake kamo hannunta sukadawo suka zauna, awannan karon waje daya suka zauna, Yasmeen kam cike take da mamakin Fu'ad, yanda taji yana larabci kamar harshen dayake magana dashi ko da yaushe, haka akacigaba da hidimar biki.
Tunda Fu'ad yafahimci duk inda Yasmeen tashiga anafaman yimata magana yake like da ita, ita ko hakan bakaramin takurata yayi ba, sede kuma wani irin kwarjini yake yimata aduk lokacin datayi yinkurin yimar magana, wanda hakan kuma yasa takasa cemar komai.
Se kusan karfe takwas 8:00pm suka kama hanyar gida, se da yawuce dasu Mr Biggs yakwasar wasu Husna Ice cream da kuma sneaks sannan sukayi gida.
Wayarta ne tayi kara alamun anakiranta, kamar bazatayi magana ba datah ansa wayar! Ahankali tace Hello yayana, nayi kewarka dayawa yau, wani abu Fu'ad dake gyefenta yaji yadoki kirjinshi yatokareshi.
Adaya bangaren kuwa Abnee ne yace My Dear kina'ina yanzu nima nayi kewarki sosai yakarasa maganarshi da cewa yau bansamu ganinki ba, murmushi tayi kamar yana kallonta sannan tace Yayana kenan ay kasan nima ina ishir ruwan ganinka sosai, har jinakeyi kamar bani da lafiya.
Cikin sanyin muryarta tacigaba da cewa kana gidane? Ganinan awajen shan iska, takatseshi da cewa toganinan My Only, guntun tsaki yaja batare dayasan fitowarshi ba, wanda jinshi yasakata kallonshi cikin sauri, ido yazuba matah yana kallonta, ayayin da zuciyarshi take cike da takaici.
Jin motor arufe ne yasakata kai hannu zata cireshi daga key din dake gyefen kujerarta, hannunshi yadora akan natah hannun, atsorace tadago idanuwanta masu daukan hankali ta kalleshi, ahankali yakira sunanta tare da zuba matah manyan idanuwanshi!
Sannan yace banaso kisake ansa waya agabana, inaso kuma kidauki hakan amatsayin umurni ba shawaraba, cike da mamaki ta kalleshi, jinyayi shuru besake cewa komai ba yasa tafice daga motor.
Wai miye yake nufi da hakan ne, ay kuma abinda bazeyiyu ba kenan, yama renamin hankali tasake cewa acikin ranta, ko cikin gida batashiga ba tawuce wajen shan iska dake cikin gidan.
Abnee ta tarar zaune acikin flowers yana jiranta, murmushi sukasakarwa junansu irin ta masoya.
Hirarsu sukafara cike da dokin ganin junansu, ganin agajiye tadawo yakalleta yace Dear mujeko naga kamar kingaji dayawa, yakamata kije kihuta, murmushi sukayiwa junansu, yariko hannunta sukabi ta kofar cikin gida.
Fu'ad dake rabe jikin flowers ne yana kallonsu ya runtse ido ganin Abnee yajawo hannun Yasmeen yayi kissing nashi (Sumba).
Wani irin haushin Abnee ne yakamashi, wanda yagwammace begansu ba, bayansu yabi zuwa cikin gidan shima, rike take da ledar Ice cream din su Husna ahannu.
A parlour ya tarar dasu suna kallo yaraba musu, Husna ce tace Yaya Fu'ad ina na Adda Yasmeen? Kasan tafi kowa agidan nan son ice cream, Ammi ce takatseta da cewa tunda kekam kinsamu naki kisha mana naji yarinya da kalan magana.
Murmushi yayi sannan yace natah 'ay dabanne Husna tunda tare mukasayo, lahh yaya ashe nima idan munje nawa zefima na Adda Yasmeen, jin maganarta yasasu dariya, Ammi ce tace nikam banason wannan rashin wayon naki Husna ya'isa haka.
Yajidadin maganar Husna, domin ko bakomai yau yafara sanin abubuwan da Yasmeen dinshi keso, na hannunshi yamikawa Husna yace kaimata wannan, bedade da fita ba tadawo da shi tana dariya! Ammi tace ya'akayi diyata?
Ammi wai cewa tayi batasha, toh ku'ajiye a fridge kuyi ta sha Ammi tace, domin tasan damah zeyi wuya takarba.
0 comments:
Post a Comment