Agurguje tasauko sanye take da doguwar riga ajikinta baka, tayi rolling da gyale red color, hakama jakar dake sakale ahannunta da takalman dake kafarta masu dan tsayi suma red color, kasancewar tadan fara makara.
Harabar gidan tafito bayan tayiwa mahaifiyar tatah sallama, waige-waige takeyi ko zata hango masoyin natah, can nesa tahango Abnee yafito domin kaita makarantar.
Cikin hanzari Fu'ad yakaraso inda take tsaye, sannan yace gacan driver wuce kije yakaiki makarantar, ganin babu alamun wasa atattare dashi tunin tawuce tana zumburar baki! Adede lokacin kuma Abnee yakaraso inda suke yana cewa My Dear ya'akayine ko kingaji da jirana ne?
Fu'ad ne yakatseshi da cewa daga yau kar kasake kai Yasmeen makaranta bamah makaranta ba hatta unguwa, saboda ba aikinka bane, idan kuma baka kiyaye ba toh ranka zeyi mummunar baci acikin gidan nan.
Magana Abnee yake shirinyi! ganin yanda Fu'ad din yadaga mishi hannu alamun bayason jin watah magana daga gareshi hakan yasashiyin shuru, Fu'ad besake magana ba yawuce yabarshi cike da mamaki.
Ayayin da ita kuwa Yasmeen din tunin tashiga motor, driver ne yashiga yatayar suka fice, zuciyarta cike da haushin Fu'ad.
Shikam Abnee yana mamakin irin wannan abu, ko don yaga shine sama damu yace 'aranshi! Guntun tsaki yaja don rashin samun mafita akai, tun daga wannan ranar yazama duk lokacin datake da lectures sede driver yakaita yakuma daukota, idan kuma sunga Fu'ad bayanan se tashiga motar Abnee yakaita.
Kasancewar Fu'ad din yafara aikin kwangila anan cikin gari, sede tafahimci Fu'ad din yana sakamata ido sosai acikin tan kwanakin nan.
BAYAN WATA DAYA:
Sanye take cikin English west na riga da siket brown and milk color, tayi kyau sosai acikinsu, duk da cewar batayi wani kwalliya ba, Powder tashafa afuskarta oil control se dan lipglow data shafe lallausar labbanta dashi, Parking din gashinta tayi.
Dan mayafinta tadora akanta wanda yasauko matah har kan kirji, gawani kamshi datake zubawa medadin shaka ahanci me kuma sanyaya zuciyar duk wani masoyi.
Cike da yauki hadi da yanga irin natah tasauko kasa rike da key din motor dinta ahannu, domin tasan yau Abba baya garin, hakan yasakata shirin fita da motor, gashi kuma yau weekend bats da lectures.
Babban parlour tanufa danufin zuwa wajen Ammi donyi matah sallama zata gidansu aminiyar tatah wato Halee.
Karon datayine da tukunyar flowers dake gyefen parlourn yasakata zamewa, kasancewar takalman dake kafarta masu matukar tsayine kuma ga santsin tayis, cikin tashin hankali tatafi idanuwanta arintse saboda tsananin tsoro.
Jinta datayine ajikin mutum yasakata bude ido tare da dena karar datakeyi! Lamoh tayi ajikinshi tamkar watah yar baby, ayayin dashi kuwa yakara mannata akirjinshi yarike.
Godiya yakeyiwa ubangiji dayakare mishi ita bata fadi ba, ido suka zubawa junansu suna kallo tamkar yaune sukafara ganin junansu kuma cike da yanayi irin ta kauna.
Karar saukar marin datajine yasakata firgita tazame daga jikinshi, Fu'ad ne tsaye agabansu rai abace! Cikin yanayi irin na fushi yanuna Abnee da dan yatsarshi wanda yake dafe da kumatunshi sakamakon marin da Fu'ad din yamishi yace, Abnee ashe damah abinda kakeyi kenan da yarinyar nan bansani ba.
Cike da yanayi irin na bacin rai yanunashi da dan yatsa yacigaba da cewa, kakiyayeni idan bahaka ba zanyi mugun batamaka rai.
Kallon Yasmeen yayi wacce ke rabe agyefe cike da tsoro, tunin tasha jinin jikinta tawuce parlourn Ammi, sakamakon kallon da Fu'ad din ya watsa matah.
Asanyaye Abnee yafice yana tunanin sa ido irin na Fu'ad! Domin yalura tun dawowarshi kasar nan yatakura wa rayuwarsu, shide yasan Fu'ad batarbiyya yafisu ba balle yace zasu lalace yasake cewa acikin ranshi! dogon tsaki yaja kawai domin yarasa meye Fu'ad yake nufi dasu fice
Shi kuwa Fu'ad bayanta yabi zuwa main parlour din, ido Ammi tazuba musu don data ganinsu tasan akwai abin dake faruwa, sede kuma batashiga lamarin ya'yan natah, hakan yasakata kau da kai domin cigaba da harkarta.
Sundade azaune batare da kowannensu yace komai ba, karar TV kawai kakeji acikin parlourn, kasancewar akunne yake, cikin yanayi irin ta mekama da wanda yake cikin damuwa yace kihadamin tea yanzu ina bukata, ayayin dayakarasa maganar shi yanafita batare da ya kalli inda take ba.
Kamar meshirin yin kuka ta juya takalli Ammi dake zaune tace Ammi anguwafa zani, saboda Allah duk masu aikin dake gidan nan amma se ni da zan fita.
Ko kallo bata ishi Ammi ba tace ayse kisameshi kigayamar bani ba, azuciye tanufi kitchen din tahada tea din, cike da takaicinshi fal cikin ranta tanufi dakinshi.
Tadade abakin kofar dakin tana bugawa batare dayayi ko gyaran murya ba, hakan yasakata tura kofar tashiga domin ajiye mishi tea din, wani irin sanyayyen kamshi ne yadoki hancinta me kuma dadin shaka ahanci.
Komai nashi tsaf, gaskiya ba lefi yana da tsafta sosai, dole yadinga rena kazamin mutum tace acikin ranta.
Cikin nutsuwa takarasa inda yake zaune atsorace ta'ajiye mishi tiren da take dauke da shi, saboda ganin gabadaya yanayinshi yacanja.
Tana ajiyewa tajuya cikin hanzari zata fice har ta'isa bakin kofar dakin batare daya kalleta ba.
Muryarshi ta tsinta yana cewa kidagamin tea din yayimin zafi da yawa, ko kuwa damah soyayya kawai kika iya ta rashin kunya.
Tsaye tayi agurin da take rai abace! Mamaki takeyi yau itace Yasmeen wani yake juyata har yake kokarin gaya matah maganar da yaga damah, afusace tajuya da tsiwa irin natah!
Gaskiya wannan abin yafara isana ko kuwa angayama ni yar' aikinkace, dazaka dinga gayamin abinda kaga dama, ko sabida kaga su Abba suna goyama baya, tobazan iyaba tasake cewa.
Kai tadaga sukayi four eye da junansu! Wani mayatatcen kallo yasakar matah, nan take taji wani abuyadoki kirjinta, wanda batasan ko menene ba.
Wani irin kwarjinin shine yacika matah ido, jinta tayi kawai tana dagamishi tea din, tadade tana dagawa, jin nauyin cups din yaragune ya'ankarar da ita takalli cups din dake hannunta.
Babu komai acikin cups din, gabadaya tajuye mishi ahannunshi! Abinka da farar fata nan take yatashi yayi jajir, ido ta zaro cike da tsoro! Nan da nan har tafara kwalla saboda tsananin tsoro, bata ankaraba taji yafizgo gashin kanta hade da dan gyalen dake yane akan yana huci!!!
Idanta tarintse tana sauraron abun da ze biyo bays, ga mamakinta kuma setaga yakasa matah komai ya tsaya kallonta, sundade ahaka batare dayace da ita komai ba, illah kawai numfashinsu dayake haduwa, saboda yanda sukayi kusa da junansu.
Kwallar dayacika matah ido ne yafara kwaran'ya akan lallausar kumatunta saboda tsoro, cikin wani irin yanayin datakasa fahimtarshi yakai bakinshi dede kan hawayen tare da tallabo fuskarta da daya hannunshi.
Cikin murya kasa-kasa yace I love u Yasmeen, I still love u and I will love u forever!!!!!!!
Ido tazaro cike da tsoro take kallonshi tare da girgiza kanta alamun aah, ayayin daya cigaba da cewa saboda na mari Abnee shiyisa kika konani ko kuwa saboda ni bakya sona??
Afirgice tasake kallonshi, ayayin da jikinta yafara rawa! Bakinshi yakawo dede kunnenta yasake rada matah!!!!!
Ina sonki Yasmeen fiye da yanda nake son kaina, idonta ta runtse ayayin da jikinta yacigaba da rawa, inda box dinshi dake dakin yanufa domin duba inda ya kone, ayayin datah fice cike da tsoro tanufi dakinta.
Maganganun shine suke dawo matah akunnuwanta, I love u Yasmeen! I still love u!! and I will love u forever!!! Saboda namari Abnee shiyisa kika konani!!!! Ko kuwa saboda ni bakya sona!!!!! Ina sonki Yasmeen fiye da yanda nakeson kaina!!!!!! Kanta tadafe, saboda batason tuna kalaman nashi, ayayin datah rintse idanuwanta tamkar meshirin yin bacci.
WASHE GARI:
Tunda gari yawaye takejin babu dadi, asanyaye tasauko kasa domin yin breakfast (karin kwamallo), Abba ne yace da ita taje takira Fu'ad, abinda yafaru tsakaninsune yadawo matah, cike da tsoro ta'isa dakinshi.
Wani irin haushin kantane kuma yakamata, jitakeyi adaya bangaren ranta kuma Abba beyiwa masoyinta Abnee adalci ba, nayanda yanuna mishi al'amuranta ga wani daban bashiba.
Ahankali ta tura kofar tare da yin sallama, kwance yake akan makeken gadonshi, tausayin shine kuma yakamata ganin yanda hannunshi yatashi yayi jah, ahankali takarasa kusa dashi ganin bargon dake rufe dashi yana tabamar ciwo, hannunta yarike tare da yin kissing nashi (Sumba).
Ido ta tsuramar tamkar yau tafara ganinshi, bargon dake jikinshi ya janye tare da zuro kafafuwarshi kasa, ganinshi dagashi se dan boxes ajiki yasakata kau da kai.
Murmushi yayi ganin haka yace, ashe kinajin kunyata kikeyimin tsiwa jiya, asanyaye tace wai kazo inji Abba tafice tare da ja mishi kofar.
Murmushi yayi mekama danajin dadin ganinta sannan yamike yashiga bathroom dinshi don watsa ruwa, tun daga wannan lokacin Yasmeen bata bari suhadu da Fu'ad, sede shi yaganta batare datah ganshi ba, domin duk wata hanyar dazesa suhadu tadatse, don hatta wajen cin abinci tadena zuwa, sede taci natah adaki ko kuma a parlourn sama.
Wanda kuma iyayen nasu sunyi matah magana harsun gaji na rashin cin abincinta acikin yan uwanta.
Abangaren Fu'ad kam yadamu matuka da rashin ganin natah, duk da cewar bawani magana takeyimar ba, amma kuma yanajin dadin ganinta sosai, domin yana samun nutsuwa.
ASALIN LABARI:
Adda Fanna ta juya ta kalla wacce ke saurarontdomin da tafara magana, tace Adda Fanna tun daga ranar da Yaya Fu'ad ya furta kalmar SO" agareni narasa gane tunanina, naso ace na aure Yaya Abnee domin shine zabin zuciyata.
Burina na auri wanda nakeso yake sona, aganina zamufi bawa junanmu hakki na sure, nasan kuma Yaya Abnee yana matukar sona, amma kawai jiya nafito danufin shiga parlourn Abba naji muryar Abba, wanda tasakani tsayawa cak batare dana kara taku daya ba!!!!!
Da'alama shi da Yaya Abnee ne da kuma Yaya Fu'ad zaune a parlourn, domin Yaya Abnee yadawo daga tafiyar dayayi, sede bamu haduba tunda yadawo.
Abba naji yacigaba da cewa, tun lokacin da Fu'ad yatafi kasar U.S nadau alkawarin aura mishi Yasmeen, se kuma akayi sa'ah bayan tafiyarshi na fahimci yana sonta, tunin nabar wasiya ko da ta Allah zata kasance Fu'ad shine mijinta, domin yafi DACEWA da ita.
Saboda haka Abnee banaso kadauki dan'uwanka da watah manufa, ga mamakina Adda Fanna, kawai senaji yaya Abnee yafurtawa Abba yahakura dani tunda Abba yayi abin da yadace.
Cike da girmamawa yacigaba da cewa, damah Abba tunin nafahimci Yasmeen tafi DACEWA da yaya Fu'ad bani ba, kawai de nazubawa sarautar Allah idone, kuma nafahimci yaya Fu'ad yafini sonta, domin shi yafara sontane tun tana karama.
Abba yace toh Allah yamuku albarka! naji dadin maganarka junior Abnee, kuma ka tabbarmin da cewa kai da'ne nagari kuma me biyayya!!!
Tabbas yazama dole kibi umurnin iyayenki Adda Fanna tace, ayayin datacigaba da cewa Yasmeen yazame miki dole ki karbi Fu'ad amatsayin miji, kiyi hakuri da soyayyar Abnee datayi zurfi acikin zuciyarki, kukane yasubuce matah tace Adda Fanna zan zauna ne kawai dashi badon inasonshi ba, saboda zuciyata yaya Abnee take SO" kuma dashi tasaba, domin nafisabawa dashi akan kowa yanzu! Toh yama za'ayine na zauna da wanda babu watah soyayyarshi acikin zuciyata, kuma amatsayin miji!!
Kuka ne yasake subuce matah, ya'isa haka Adda Fanna tace, sannan tacigaba da cewa ahankali zakisaba dashi fiyema da yanda kika saba da Abnee, domin shi zaman aure zakuyi, zaman aure kuma yafi kusanci da damah, kuma nafahimci Fu'ad yana matukar sonki Yasmeen, kishine kawai yake sashi yimuku wani 'abun ke da Abnee, haka Adda Fanna tacigaba da bata shawarwari tare kuma da rarrashinta.
BAYAN KWANA BIYU:
Jiki babu kwari tafito tamkar wacce bata da lafiya, dakin Ammi tanufa tasanar da ita zataje gidansu aminiyarta Halee daga nan kuma zata karasa gidan kawarsu Mufida, domin tun da 'akayi bikinta bataje ba.
Ammi cewa tayi aybani zaki tambaya ba, ko kin manta da cewar yanzu ke matar aure ce, saboda haka duk 'inda zakije seki tambayi mijinki, kalaman Ammi sunyi matah nauyi sosai, se kuma taji abin wani iri.
Yanzu Ammi tana nufin idan zanfita sena tambayi wannan mutumin tun kafin akaini gidanshi tace acikin ranta, ganin muhimmancin fitar natah yasakata hakura tabi yanda Ammi tace din badon taso ba.
Kofar dakin tatura tare dayin sallama, karar ruwan datajine yasanar matah da cewar yana bathroom dinshi, durowar dake jikin gadonshi tajawo (bedside) tadauko takarda da biro tayi mishi dan note sannan ta'ajiyemar akan bed.
Da hanzari tajuya zata fice, ganinshi datayi ne agabanta daf da ita daure da towel yasakata ja da baya cikin sauri, domin bataji fitowarshi ba, ido kawai yatsura matah yana kallonta, tarame sosai, duk da cewar damah bawani kiba bane da ita.
Kasa tayi da kanta, cikin rawar murya tace damah Ammi ce tace nazo na tambayeka zani gidansu Halee da Mufida!!! hannunta ya riko batare dayace komai ba yajanyota jikinshi ya rungume.
Wani abu taji ajikinta! Wanda hakan yasakata kokarin kwacewa, amma yariketa kyam! tamkar zeshigar da ita cikin jikinshi, wani irin ajiyar zuciya yakeyi, ayayin da yakaita jikinshi ya rungume, ahankali ya tallabo fuskarta suna kallon juna yace!!!!!
Kar kidamu babu abun da zanyi miki! Meyisa kikejin tsorona haka, kamar meshirinyin rada yacigaba da cewa tsorona kikeji Yasmeen dina, ninefa yayanki, nine yayanki Fu'ad, meyisa kika manta da ni.
Cikin rawar murya tace Yaya Fu'ad kayi hakuri kabarni natafi!!!! Jin datayine bakinta acikin nashi yasakata yin shuru, se da yasha son ranshi tamkar wanda yasamu wani sweet.
Ahankali yakai bakinshi dede kunnenta yace ina kewarki dayawa awannan lokacin, nadade ina jiran wannan lokacin, lokacin dazaki zama mallakina, kina iya tina lokacin danake yimiki tsarabar ice cream nake baki abaki, kin manta ko, shi kadai kawai yake magana bedamu datah bashi ansa ba, saboda baya tsammanin hakan damah daga gareta.
Sundade ahaka yana rungume da ita ajikinshi, sannan yalura da kayan dake jikinta, doguwar riga ce ta atamfa, anmishi dinkin fitted gown yabi dukkan 'illahirin jikinta yafitar matah da shape dinta sosai, gyalene color din kayan tadora akanta wato sky blue, wanda behana ganin gashinta da yasha gyara ba.
Wani irin kishine yataso mar, cikin wata irin muryar da bata sanshi da ita ba yace babu inda zakije ahaka, kidubi kayan jikinki, ke kin manta da cewar ke matar aure ce yanzu.
Kwallane yacika matah ido, nan take yafara kwaran'ya afuskarta! Kasa tazame ta durkushe don rasa abin cewa, cike da kulawa ya durkushe agabanta yace Baby Yasmeen ashe haryanzu kina nan da saurin kukan nan.
Hannunshi yakai yafara share matah hawayen dake fuskarta, ayayin da yacigaba da cewa banason ganin wannan hawayen, dena kukan haka idan kinaso nabarki kije! hawayen tafara sharewa cikin hanzi wanda ganin haka yasashi yin murmushi, cikin hanzari yabude durowa yadauko kayanshi yasaka.
Wani trolleys yabude, kayane na mata cike acikinsu, masu kyau da kuma tsada, wasuma irin wanda yabawa Ammi da su Husna ne tsarabarsu ta U.S, Laffaya yadauko (Sari) yabata yace, kinademin jikinki dashi, saboda inada kishi sosai musamman akanki.
Asanyaye takarba tayi yanda yace din, key din motor yadauka yana yacewa muje nakaiki da kaina, bayanshi tabi badon taso ba har zuwa motor.
Tun dasuka fara tafiya babu wanda yayi magana, tayi mamakin yanda akayi yasan gidan su Halee, ganin yanda yakama hanyar gidan batare kuma da yatambayeta ba, wai meyasane yake bibiyar duk wajen da yasan ina zuwa tace acikin ranta.
Se da yayi parking akofar gidansu Halee sannan yajuyo yakalleta yace kikulamin da kanki sosai, idan anyi sallar la'asar zanzo nadaukeki da kaina, saboda haka kijirani.
Betafi ba se da yaga tashiga gidan sannan yaja motor shi yatafi, wuni tayi agidansu Halee suna tattauna matsalarta tare da aminiyar tatah.
Anayin sallar la'asar Fu'ad yadawo daukarta, awannan karon har cikin gidan yashiga yagaisa da Umman su Halee, hakan yatabbatar matah da cewar ba wannan bane zuwanshi nafarko gidan ba, domin yanda taga sun saba sosai da Umman su Halee.
Gidan Mufida yawuce da ita, kasancewar gidan abokinshine shima yayi zamanshi sukasha hirarsu da Sadik din, ayayin da ita kuwa Mufida tajata suka shige natah parlourn.
Tayi mamakin sanin aurenta da Mufida tayi sosai! ashe harma Sadik yaje daurin auren nata, yahana Mufida sanar da itane, se dare sukabar gidan, yabita kusha shagalinku yasimata ice cream ita da su Arfat sannan sukawuce gida.
BAYAN SATI DAYA:
Kasancewar sunyi hutun makaranta koda yaushe tana gida, sede talura acikin yan' kwanakin nan Fu'ad yasaka matah ido sosai, domin duk inda tazagaya acikin gidan seta ganshi, Abnee kam gabadaya yacanja matah, bemacika hira da 'ita ba ko acikin kannenta.
Yakikuma barin duk wata kofar dazasu kebe suyi magana, gabadaya jitakeyi batajin dadin gidan, ga wani irin mayatatcen kallo da Fu'ad keyimata aduk lokacin da sukahadu, wanda kuma yake matukar razanar da 'ita.
YAU 'ASABAR:
Tunda safe gida yakacabe da hidimar biki, gida yacika makil, abinka da ya'yan dangi kuma yan'gata, amarya tasha kaya kam awajen Abbanta.
Abba ne yayi matah kayan aure (lefe), domin yace Fu'ad kar yasiyi komai, yan'uwa da abokan arziki duk sun hallara, mutanen Adamawa dana Taraba duk sunzo tun jiya, har ma da wasu daga cikin yan'uwansu na Mambila suma sunzosu, domin cewa akayi bikin duk na Abba ne, saboda haka ayishi anan Gombe, da'acewar Abba Adamawa za'atafi ayi bikin acan.
Nanfa nahango wasu daga cikin members din REAL MRS YARIMA HAUSA NOVELS GROUP suma sun halarci wannan kayatatcen biki, can nahango su Maman Haneef da Mrs Suleiman Sokoto, dasu Namesake (Suwaiba Adamawa, Mrs Kabeer Sokoto anata hidimar biki.
Amaryafa se sheki takeyi takara kyau sosai, kwanan Adda Fanna biyar agidan tana gyarawa amarya jiki, tun daga gyaran jiki har kamshi se datayi matah irin na amare (kamshin Amarya), abinka da shuwa arab.
Nanfa tadinga bata sirrika namusamman irin nasu na shuwa, sannan tayi matah zanen fulawa irin na amare, amarya tafito ras da ita, se kamshi take zubawa, kyanta yakara fitowa sosai, sede tarame sosai saboda tasaka damuwa acikin ranta.
Itade har yanzu takasa sakewa, akoda yaushe bata da tunanin da yawuce na masoyinta Abnee, don tasan kawai yahakura da itane don babu yanda zeyi, kwallane sukacika matah ido ayayin da Halee da Mufida sukashigo dakin tare da wasu daga cikin kawayensu.
Nanfa sukafara tsokalarta, bata ankaraba taji kwallar dake cike a'idanunta ya wanke matah fuska, Halee ce tadawo kusa da 'ita tace yade sister? yanaganki haka? Cikin yanayi irinta damuwa tace Yaya Abnee! Halee inason ganin Yaya Abnee yanzu, kitemakeni Halee.
Haba Yasmeen kin mantane da cewa yanzu za'akaiki gidan miji, hannunta takama tace nasani Halee, nasan kece zaki'iyamin wannan temakon, inaso kije kisamu Yaya Abnee kisanar dashi inason ganinshi yanzu, muhadu awajen shan 'iska.
Amma Yasmeen bakyajin tsoro wani yaganki, karkidamu zanbi ta kofar baya babu wanda zeganni, duk wanda ya tambayeni kice ina bathroom, ayayin datakarasa maganarta da cewa kitemakeni Halee please, hannun Halee takamo suka fito ta kofar baya.
Ganinshi kwance agurin shan iska yasa Halee juyawa takoma ciki, ahankali takarasa inda yake tadurkusa agabanshi, kallonta kawai yakeyi batare dayace komai ba.
Cikin muryarta me'alamun tayi kuka har tagaji tafara magana, Yaya Abnee meyisa kayimin haka, meyisa kacewa Abba ka hakura da ni, bayan kasan kaifa nakeso ba Yaya Fu'ad ba, meyisa kamin haka Yaya Abnee! Kukane yasubuce matah mefitar da sauti, ayayin da tacigaba da cewa Yaya Abnee katina shakuwar damukayi da junanmu, ko kamanta da alkawarin da mukayiwa junanmu ne, kamanta da burinmu ne, Yaya Abnee da kainafi DACEWA bada Yaya Fu'ad ba, hawayene sukacigaba da kwaran'ya afuskarta.
Cikin rawar murya me alamun kuka tace kamin magana mana Yayana kozansamu sauki acikin zuciyata, kuka tacigaba dayi mefitar da sauti me kuma ratsa zuciyar duk wani masoyi!!!
Asanyaye yatashi ya zauna daga kishingiden dayayi, su na fuskantar junansu sannan yace dena kukan haka kanwata inasonki har yanzu, inaso kizama meyadda da kaddara, kiyi biyayya wa iyayenmu, banaso kibijire yanda nima ban bijireba kinji ko.
Cike da rarrashi yacigaba da magana, inaso ki fahimceni, nahakura dake ne kawai ba don bana sonkibane, illah don kawai na farantawa Abba rai, saboda banason ran Abba yabaci Yasmeen, cikin yanayi irin na wanda yayi zurfi acikin SO" yacigaba da cewa! Yasmeen ina matukar kaunarki, babu wacce nataba SO" se ke, banajin zanso watah mace kamar yanda nasoki arayuwata.
Agabanta shima yadurkushe tamkar wani karamin yaro! Yacigaba da cewa nazo nazauna anan ne kawai don ko zan samu sauki acikin zuciyata, sannan kuma banaso naga anfita dake ankaiwa yaya Fu'ad ba ni ba, duk da cewa ni da shi duk dayane.
Se de kuma nayi matukar farin ciki da Allah yabaki Yaya Fu'ad amatsayin miji! Idanuwanta tadago ta kalleshi wanda suka kada sukayi jajir saboda kuka, cikin muryar kuka tace meyisa kace haka? Babu yanda za'ayi nasowani bayan kai Yaya Abnee, kai da shi kuma badaya bane, domin kai nakeso bashi ba.
Nafahinceki kanwata yace, amma inasanar dake cewa Yaya Fu'ad yana sonki fiye da ni, afirgice ta kalleshi don jin furucin dayayi, kai takada tare dayin murmushi mekama da yake, alamun bata gamsu da maganar tashi ba!
Sannan tace Yaya Abnee kar kace zaka kwantarmin da hankali da wannan kalaman domin baze yiyuba, hannun shi yadaga da nufin kama natah hannun, se kuma ya tuna da yanzufa ita matar wani ne.
Cikin sanyin murya yace kina sona har yanzu Yasmeen? kai tadaga tace ehh, yacigaba da cewa nakai matsayin dazan nemi wani abu awajenki kiyimin?? Kakaimana yayana tace, babu abinda zakanema awajena karasa sede idan yafi karfina.
Ido yatsura matah yana kallonta, tamkar wanda yake nazarin wani abu, ahankali yakira sunanta! Wanda hakan yasakata kallonshi ido cikin ido, saboda tasan aduk lokacin dayakira sunanta maganace me muhimmanci zeyi matah.
Sannan yacigaba da cewa tabbas Yaya Fu'ad yana matukar kaunarki, ina rokonki alfarma da kiso Yaya Fu'ad kamar yanda kike sona, ko ma ki SO" shi sama da yanda kika SO" ni, kuma ina rokon alfarma da ki zauna dashi lafiya, tamkar da ni kike zaune, idan da gaske kina SO" na toh kidaukarmin alkawari za ki zauna da mijinki lafiya.
Gabadaya yadaure matah kai da maganganunshi! Cikin muryar kuka tace Yaya Abnee idan har hakan dakace shine ze tabbatar ma da cewa ina kaunarka har yanzu toh nayima alkawari, zan kuma yimar duk kan biyayya, kamar yanda nake mafarkin yima agidanmu na aure Yaya Abnee, amma kasani bayida wani gurbi acikin zuciyata.
Ido suka tsurawa junansu tamkar karsurabu da juna, karar motor ce ta'ankarar dashi daga kallon da yake matah, yace nagode kanwata tare da sauke ajiyar zuciya, muje ko narakaki yace, gacan motocin abokan angonki sunfara isowa, kar anemi amarya arasa, nasha mari yau awajen Yaya Fu'ad, kinsan bai da sanya awajenki, harararshi tayi yana dan dariya ta tsokala, wanda hakan yasakata yin dan murmushi itama.
Asanyaye tamike yamata rakiya ta kofar baya tare da yimata fatan alkhairi, har tashige cikin gida tana wai wayenshi, ayayin da shi kuwa yake daga matah hannu cike da murmushi a fuskar shi.
Karfe bakwai na yammah 7:00pm aka rufa amarya aka kaita gidan mijinta dake nan acikin unguwar Abuja quarters dake birnin Bubayero, tayi kuka sosai, irin kukan da kusan kowace mace keyi alokacin daza'akaita dakin mijinta, sede ita nata ba narabuwa da iyaye bane kawai, har da kukan rabuwa da masoyinta.
Karfe takwas 8:00pm akafara shirin zuwa dinner party kuma, wanda abokan ango suka shirts, nanfa amarya takafe tace babu inda zataje, juyin duniyar nan akayi amma fir tace ita kam barataje ba, ganin kowa yashirya sukadai kawai ake jira Fu'ad yashigo dakanshi gidan, nanfa kawaye suka dinga yimar tsiya.
Gabanta yakarasa yatsaya, kallo daya zakayimar kasan cewa babu wasa afuskarshi, ga kuma wani irin kwarjini da yakeyi.
Ledar da yashigo da shi medauke da kaya aciki yamika matah sannan yace se kitashi kishirya kisaka wannan kar kuma kibata mana time, ko kuwa zakinunawa duniya cewa auren dole akayimiki, kofar dakin ya tura ayayin da kawayen natah suka koma parlour.
Ganin bai da niyyar fitane yasakata shiga bathroom tasaka kayan, inda tabarshi anan tatarar dashi tsaye.
Daya daga cikin kawayen ne tashigo tayi matah kwalliya (makeup), sarka da yan kunne da abin hannunta tasaka color din materials din dake jikinta Lemon green and Golding color, tasaka takalma da hand fan sumah Golding color.
Shadda ce ajikinshi mekyau toties din Materials din dake jikinta, wato Golding color, takalmanshi da agogon dake manne atsintsiyar hannunshi sumah duk Golding color, hulace akanshi color din head dinta lemon green wanda yakaryata gyefe daya, se farin glass dake manne a idanunshi.
Sunyi matukar kyau sosai, se wani irin kamshi suke zubawa namusamman, hannunta yakamo har zuwa parlour, su Halee ne da Mufida tare da sauran kawayensu sukadau tafi, kunyane yakamata ayayin da shi kuwa Fu'ad ko ajikinshi yakara janyota jikinshi sukafice.
Motor Sadik suka shiga kirar LEXUS! shi da Mufidar shi agaban motor sukakama hanyar zuwa SHAGALINKU MALL! ayayin da sauran kawaye da abokan Fu'ad din sukamara musu baya acikin motor tinsu.
Sun tarar tunin DJ da MC sunfara aikinsu, sautine kawai yake tashi, waje kam yacika makil, ga yan'uwa da abokan arziki duk 'an hallara, anata shagalin biki.
Abokan Fu'ad ma sunzo da dama, harda wa'yanda sukayi karatu dasu acan kasar U.S, wasu daga cikin suma duk turawa ne.
An kayatar da wajen sosai, abinka da bikin man'yan yara kuma yan boko, komai kuma yaji awajen, domin ankashe naira, can naji ankira ango da amaryarshi, domin sununa farincikinsu, Fu'ad kam jikinshi yayi sanyi sosai, ganin yanda amaryar tashi kefaman kuka alokacin da Abnee yafito yanayi musu liki, fuskar nan tashi cike da farin ciki.
Jiki babu kwari yaja amaryarshi suka koma suka zauna, domin yasan kullalliyar soyayyar dake tsakaninsu, har aka tashi tana zub da hawaye, shikam de Fu'ad beji dadin wannan yanayin ba.
Anbar amarya da angonta akayatatten gidansu dake unguwar Abuja quarters, gida kam ya kayatu da kayan alatu, anyiwa amarya komai na dakinta da parlour Orange and milk color, ayayin da komai na kitchen natah kuma aka samata lemon green and white color! bakaryafa iyayenta sun kashe naira da dala, kuma sun nuna matah gata sosai.
Ga kuma jeran kayan kamshi da Ammi ta bawa Adda Fanna tayiyo matah, tun daga kan Humra fara da bakar, ja da kuma koriya, ga kuma turarukan wuta masu kyau da dadin kamshi, ko ina agidan se kamshi yake zubawa, Adda Fanna kam bata tafiba se da tabi ko ina na gidan lungu da sako ta turareshi da turarukan wuta masu dadin kamshi.
Yasmeen tun da taga kowa yawatse tashiga dakinta tayi kwanciyarta, abangaren Fu'ad kuwa, betsaya bin wata al'ada ba yataho gurin amaryarshi, nanfa su Sadik sukadinga yimar tsiya, domin yaki yarda da rakiyarnan da akeyi na ango, yace shide babu ruwanshi da wannan al'adar tunda ba sunnah bace ta manzon Allah S.A.W.
Jin kofarta arufe kyam ne yasashi wucewa nashi dakin ya kwanta, sede kuma yakasa bacci, juyi kawai yakeyi, fuskarta kawai yake gani a idanuwanshi, ahankali ya jawo pillow dake kusa dashi ya rungume, tunanin kyaukykyawar fuskar nan tatah yakeyi, wanda yake dauke da murmushi ko da yaushe, wanda yakesa bayyanar dimples din dake kumatunta, ahaka bacci barawo yayi awun gaba da shi.
WASHE GARI:
Se karfe goma 10:00am yatashi, kasancewar besamu bacci sosai ba jiya, har yayi wanka yafito parlour bata bude kofar ta ba, se zuwan su Husna ne tare da Ramatu me'aiki yasa tabude kofa, Ammi ce ta aiko musu da abincin karyawa (breakfast).
Tunin suka jera musu komai akan dinning, sanye take cikin doguwar riga baka yar' Dubai dede jikinta, wanda tasha ado da duwatsu, asanyaye tafito daga dakin ta tarar dasu a parlour tare da Fu'ad.
Cikin sanyin muryarta tadurkusa ta gaishe shi, fuskarshi asake ya ansa tare da tambayarta gajiyar biki.
Husna ce takatsesu da cewa, Lahhh! Adda Yasmeen yanzu kika tashi? Adda Muhseena tace wai dolenki yanzu kam kidena wannan baccin naki na shagwaba, wai ko danma Yaya Fu'ad!!!
Harara taswatsa matah tare da kai matah duka, cikin hanzari tayi bayan Fu'ad tana cewa kaganta ko yaya, kuma bani nafada ba Adda Muhseena ce tace, ayayin da ita kuwa Yasmeen din ke kokarin dukanta.
Dariya yake musu ayayin da yake tareta domin kar ta daki Husna, yana cewa Husna ashe gulmar matata kukeyi ko, toh ya'isa haka yace kuxo muje muyi breakfast.
Lahhh, Ammi tace muna ajiye muku mubaro muku gida, idan ba haka ba baramu kara zuwa ba Husna tace, dariya kawai Fu'ad yakeyi saboda yasaba da surutun Husna, yace to ku gaida Ammin bari nazo namai da ku, ay tare da driver muke tace ayayin dasuka fice suna yimusu se anjima, ido yabisu dashi yana murmushi me cike da jin dadi.
Kallonshi yamayar ga Yasmeen dake tsaye agyefenshi yace Husna fa badama asurutu kamar Muhseena, inaga shiyisa tasu tazo daya sosai, baki kawai tatabe batare da tace dashi komai ba, muje dinning ko yace ayayin da yake kokarin wucewa.
Karo sukayi da junansu, kasancewar kanta na kasa, ayayin da shi kuwa ya juya baya zewuce, cikin hanzari ta ja da baya.
Kara kuma tasaka! Wanda hakan yasashi juyowa afirgice ya janyota jikinshi yana cewa lafiya? Me yasameki?? Kasa magana tayi ganin yanda gabadaya ya janyota jikinshi ya rungume.
Ganinta dafe da gyefen kumatuntane yasashi lura da kunnenta, yan' kunnen tane ya kama jikin rigarshi ya makale, sakamakon karon da sukayi da juna, murmushi yayi ganin irin karar da tayi, ashe haka take da tsoro da raki yace acikin zuciyarshi.
Da dabara yacire matah, jiyake tamkar su zauna ahaka, asanyaye tazame jikinta daga nashi ta nufi dinning room.
Tun da suka zauna ya fahimci takasa cin komai, hakan yasashi bata da kanshi, amma kuma firr taki karba, tunin ya lura da duk matsawan da yayi kusa da ita kara matsawa takeyi, hakan yasashi janyota jikinshi, se kuma tafashe da kuka, wanda kuma hakan yakara tayarmar da hankali matuka.
Magana yafarayi cikin nutsuwa, Yasmeen kiyi hakuri kici abinci, kar kice zaki horar da kanki da yunwa, yakamata ki hakura haka, karfa ki manta da cewa ni dan 'uwanki ne kamar Abnee, kuma ina miki SO" irin wanda Abnee bayamiki, domin nafishi sonki.
Ahankali tazame jikinta daga nashi ta nufi daki, kukane yadawo matah sabo jin ya ambaci sunan masoyin natah, se da tayi me'isarta sannan tayi shuru, magana tafarayi tamkar wacce take gaban masoyin natah.
Yaya Abnee meyisa kabarni! Bayan kasan kai nakeso ba Yaya Fu'ad ba, ya zakayimin haka, Why? Ko kadena sona ne, nasan kana kaunata Yaya Abnee tasake cewa, amma meyisa kabarni, kasadaukar da soyayyata ga Yaya Fu'ad, bayan kasan da kainafi DACEWA!
Fu'ad ne dake tsaye abakin kofa yakaraso daf da ita yana cewa saboda ya fahimci nafishi sonki shiyisa ya hakura, ido ta tsura mar don jin kalamanshi, don atunaninta maganar zuci takeyi, jikinshi ya janyota tare da rungumeta, yana sauke ajiyar zuciya.
Ahankali yafara magana kamar meyin rada, kiyi hakuri zannemi Abnee muyi magana dashi, ina shi kike SO" ba ni ba? Kai kawai tadagamar, alamun ehh, wani abune yaji yasokeshi akirji, sakamakon 'ansar databashi! Jiki babu kwari yacigaba da cewa to muje kici abinci senaje nasamu Abba domin 'asan yanda za'ayi.
Asanyaye ta tashi tayi gaba yabita yana murmushi me cike da takaici, sedaya tabbatar taci abincin sosai takoshi sannan ya fice.
Ammi yayiwa waya driver yadawo dasu Husna, nanfa suka wuni matah har dare, amma Fu'ad shuru be dawoba har suka tafi gida.
0 comments:
Post a Comment