By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
Marubuciyar, *tawa kaddarar* da *uwata* 😜😜😜
Page :1🌹
Bismillahir rahmanir rahim, WA sallallahu ala nabiyyir Kareem
Saurin nake tayi in ƙarasa wanke2n da nake yi don inje in ɗebo ruwa nasan yanzu mama ta kusan dawowa daga yawon ta kuma duk irin hidimar nan da nayi mata a gidan ta ba lallai ne ta gani,
Khadija ce ƙanwata wacce take bina suka fito daga ɗakin mu ita da maryam cikin uniform ɗin islamiyya,
"yaya haryanzu baki gama ba, zaki makara ma yau kinga jiya sai da aka miki dukan latti"
"hmmm kudai tunda kun shirya ku wuce ku tafi karku makara ni ba lallai bane inje" alamar tausayi na gani a fuskar ƙannan nawa
"me yasa" suka haɗa baki
Tashi nayi ina goge hannu na da riga ta ina kaɗa su don in ba korar su nayi ba ba lallai ne su tafi ba sai suma su makara, wucewa sukayi dukkanin su rai a jagule ni kuma na dawo na ƙarasa aiki na
ko dana gama na ɗau botiki na fara ɗebo ruwa sai da cikawa mama robobin ta tas sannan na samu na huta, ba ita ta dawo gidan ba sai karfe 5:30 yadda ba yadda za ayi nace zanje mkrnt don lkcn tashi ya kusa
tana shigowa sai ga ƴaƴanta sun biyo ta ko da yaushe suka fita oho ni dai nasan lkcn da suka dawo daga schl ita kuma ta daɗe da ficewa
"sannu da zuwa mama" ko kallo na batayi ta hankaɗa labulen ɗakin mu tai shigewar ta
A ƙofar ɗakin dai na cigaba da zama don banga alamar sakin fuska a tattare da ita, *zainab* naji an ƙwala min kira da manyan harufa
"na'am"
cikin ɗakin na shiga asukwane ta cire kayan jikinta daga ita sai zani ga ƴaƴanta nan a zaune a ƙasa suna cin gyaɗa, ɗakin da na gama shan wahalar gyaransa
"to uwar munafunci baki ga alamar na dawo bane baza kizo ki karɓi abinda zaku dafa bane don tsabar kinibibi kina zaune kina kallo na ko ni zan dafa muku" ta faɗa a hasale
Bance komai ba "ɗauki garin kwakin can kije ki tuƙa eba sai kije kasuwa ki siyo ewedu kiyi miya tunda muna da dage dage" too kawai nace na ɗauka na fice
sai da na tuƙa ebar na kwashe sannan na shiga ta bani kuɗin ewedun da daddawar, ina fitowa na ci karo da su khadija har sun taso,a tsatsatsaye nayi musu magana sannan na wuce don kasuwar ba laifi da ɗan nisa
kasuwar agege naje kasancewar tafi kusa da mu na siyo, inda magariba ce ta shigo dani gida ina shigowa sai da na ɗaura miyar sannan nayi alwala na shiga ɗakin mu, bayan naa idar na ƙarasa miyar ewedu ta na sauke ɗakin mu na shigar da abinci inda na tarar da mama da yaran ko shirin tashi sallah basu ba saboda suna kallo kai Allah ya kyauta baga uwar ba baga ƴaƴan ba
ana sallar isha muka ci abinci su khadija suakyi wanke wanke mukayi shinfiɗa a nan falon mu muka kwanta gajiyar da ke jikina baisa ma naji dawowar bbn mu.
************
sunana zainab mahaifina ɗan gezawa ne dake garin kano, mahaifiyata wadda muke ce mata iya Allah yayi mata rasuwa shekara tara kenan da suka wuce mu uku ta mutu ta bari, ni sai ƙannena biyu khadija da kuma maryam, sannan baba ya auro wata bazarawa me wacce muke ce mata mama ita kuma ta haifa masa yara huɗu maza uku sai auta mace
a agege muke da zama a unguwar ruwa haya muke yi a gida me ɗakuna barkatai inda muke cikin ciki da falo, mama ta hana mu shiga ɗakin ta ko da wasa yasa muma iyakacin mu falo ba abu namu da ke cikin ɗakin, baban mu mutun ne mara zuciya ko kaɗan be damu da harkar mu balle ya kula da rayuwar sana'ar kayan gwari yakeyi a kasuwar gatan kowa, amma sai ya shafe sati be kawo komai gida ba don muci sai yace wai ba kasuwa, ita kuma mama a nata ɓangaren Allah yai ta masifaffiyace don in ƴen abinta suka motsa har wajen gidan mu ana iya jiyo su da baban mu barin ma in ta tashi bata da ko sisi kuma babu abinda zamu sa a bakin saƙatin ranar baba yana da bomb ɗin kamawa da hannunsa
ko kaɗan bana jin haushin abinɗa mama take yi mana da ƙannena don nasan cewar ko me tayi mana laifin babanmu, kuma duk jarabar mama bata taɓa barin mu da yunwa ko baba bai kawo ita sai tasan yadda ytayi muka ci muka ƙoshi wannan dalilin ne yasa nake ɗaga mata kafa
mama Allah yayi ta me shige shige ce gidajen mutane don haka kullum sai ta fita ko babanmu ya sani ko be sani ba ita dai oho shima baya damuwa idan ya dawo be ganta be wani nuna damuwa ko kaɗan
***********
Tun kiran farko na asuba na tashi kasancewar yau mune da wankin vandakin gidan kuma ni nake wankewa in turn ɗin mu ya zagayo tun mutanen gidan suna ƙorafin mama bata wankewa saini har suka haƙura tunda mama ba mutum bace da zaka taɓa ta ta kyale, da sauri na zundimi ruwa nayi banɗaki na fara wankewa amma ikon Allah kafin in gama har a cika a ƙoafar banɗakin a a layin shiga
haka na gama na futo wasu ma har sun ƙagara sun fara mita, ni dana wanke komawa nayi gefe na zauna don banga ranar shigana ba, sai da gari yai shaaa sannan aka ragi ya rage sauran iya temitope ce kawai a layi sai ni komawa nayi ɗaki na taso kannena suka fito
Sai da tabbatar da sunyi wanka sannan nima na shiga nayi wankan nawa muka zo muka shirya mama haryanzu bata buɗe kƙfar cikin ɗaki ba ragowar ebar nan na dumama mana muka ci sannan na jaa kƙoar falo muka kama hanyar schl Wacce ta kasance ta gwamnati ce dake unguwar dopemu a ƙafa muke zuwa kullum sannan in an tashi ma mu dawo a ƙafar
k
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By mmn walid nd walida(mrs aliyu)
Page: 2🌹
Shekara tana ta tafiya muna ƙara zama ƴan mata lamarin baban mu ba sauƙi don kuwa haryanzu be canza sai ma ƙara taɓarɓarewa da yayi, don yanzu sai yai wata be kawo komai gidan ba wai don muci mama ma on d other hand lamarinta na nan, amma ita tana ƙoƙari sosai damu in dai banda zagi da gorin da muke sha a wajen ta to gaskiya bata da matsala
A yanzu nayi graduating daga secondary amma babu maganar ci gaba yo ina ci gaban abinda har yanzu banje na karbo result ɗin da ya dade da fitowa ba saboda tsabar babun da baban mu ya ɗorawa kansa, don haka ne ma na kama sana'ar taimakawa wata maƙociyar mu sai da abinci
Iyan amina muke ce mata yar ghana ce da ke zaune a lagos ita da mijinta da kuma ƴaƴanta biyu shapi'u da kuma amina, tana saida wance (abincin ƴen ghana wake da shinkafa wadda ake ci da tankwa, zaku ga wance din baƙi amma sai daɗi)
Da kuma dukunu shima kamar tuwo ne na ghana wanda ake yinshi da masara sannan a naɗe shi cikin ɓawon masara, kullum take biyana wannan ba ƙaramin taimaka mana yayi duk wasu ƴen ƙananan matsololin mu ni da ƙannena ina iya biya mana, mama ma wani lkcn in abin yai mata yawa takan sakar min ciyar da mu nida ƙannena, haka rayuwa take ta ci gaba sai godiya Allah
Kullum ni nake zuwa kasuwa inyo cefanen girkin da muke siyar wa, sannan inna dawo in haɗa girkin in ɗora, duk wannan abinda nake yi bai hanani aikin mu haka zan haɗa aiki kamar wata jaka, in su khadija suna nan sukan taya ni amma idan basa nan sai godiyar Allah
************
Bayan shekara biyu
Rayuwar dai bata canza ba ɗan cangin da aka samu shine yanzu baba yana kawo kayan abin sai dai kuɗin cefane sai ankai ruwa rana da shi, shima kayan abincin bai fara kawowa ba har sai da mama ta gaji tayi yaji da yaga abin ba daɗi sai ya dawo da ita tare da alƙawarin zai dinga kawo kayan abinci haka kuwa ake yi har yanzu
Su khadija a yanzu suma sunyi candy tunda dama shekara ɗaya ne tsakani na da khadijar, mun zo mun haɗu mu ukun muna zaman gida su suna yin aikin gidan ni kuma ina sana'ar sai da abinci, wanda yanzu ba laifi nima ina samu sosai
Baban mu ya tara mu yace dukkan mu mu fito d miji aure zai mana, abinda nake gudu kenan don ni tunda nake zan iya cewa ban taɓa yin saurayi ba, gwanda ma khadija akwai wani hadi shine yake son ta amma yana da mata don dai matar tasa bata taɓa haihuwa ba ne
Bayan mun keɓe ne nake cewa khadija "kiyi wa hadi magana ya fito mana tunda naga da gaske yake" ta kalle ni ido rau rau kamar zatayi kuka
" yaya ke fa" murmushi nayi na dafa ta nace "khadija kowa lkcn sa na aure idan yayi zai yi, kinga ke yanzu Alƙah ya haɗa ki da wanda yake sonki ki yi auren ki kawai kin huta da wannan rayuwar da muke ciki mara tabbas"
ba irin lallami da ban bakin da banyiwa khadija ba amma ƙiri2 tace fafur bata yadda ba ita dai in ban riga ta ba to sai dai muyi tare ba yadda na iya da ita don na san inna na matsa mata sai ta sa min kuka
sai da bari dare yayi hadi ya zo zance sun daddage suka zuba soyayya na je nayi musu sallama suka amsa khadija tana ganina ta sha jinin jikinta sai naga ta haɗe rai, ban kula ta ba na koma wajen hadi nai mai bayanin komai da ake ciki, ya nuna jin daɗinsa sosai sannan ya ce in shaa Allah yana komawa zai yiwa magabatansa magana akawo kuɗi ina ganin khadija sai zumɓurar baki take tayi ni dai na bar su na koma gida abina su ƙarata
hadi kuwa kamar yadda yai alƙawari haka kuwa ya aiko da magabatansa suka kawo kuɗi inda aka sa ranar wata biyar, kuɗin hannuna da nake tarawa wanda nake samu a wajen siyar da abinci shi na ba khadija muka je tare ta siyo ƴen kayan kitchen wanda muka ɓoye a ɗakin iyan amina don in mama ta gani ba lallai bane ta bari baba yayi mata wasu ba
Bikin khadija yana gabatowa inda ni kuma a ɗayan ɓangaren nake shan habaici a wajen mama wai nayi kwantai na rasa mijin aure, shima a ɓangaren baban mu ba sauƙi sai kace nice zan bawa kaina miji, wannan hali da na shiga yakan ɗaga wa khadija hankali don wani lkcn har kuka zaka tsince ta tana yi, na kan ɗige da bata haƙuri, ince mata kowace mace da irin yadda rayuwar auren ta yake farawa
************
Da bikin khadija ya zo Allah ya taimake mu baba yai mata gado dama auren lagos mace gado kawai zata tare da shi sai kayan kitchen duk ragowar hidimar gida su gyaran falo da komai duk na miji ne, munyi shagalin biki lfy mun gama ƙalau sai dai fatan Allah ya basu zaman lfy, flat aka kai khadija duk da dai ba ita kaɗai bace akwai kishiyar ta kowacce ta ɗauki ɗaya shima mijin ya ɗau ɗaya,
Da bikin khadija Allah ya haɗa jinin maryam ɗin mu da wani cousin ɗin hadi mai suna sadiq, shima kamar yawancin matasan agege ɗan chanji ne, haka shima mijin khadija chanji yake yi
Soyayya suka dinga zubawa sun so ma suyi aure kasancewar maryam akwai rawar kai amma baba yace har yanzu be huta daga auren khadija ba gani ni ma har yanzu ba wani motsi,
haka ta haƙura, suka zubawa sarautar Allah ido nidai in don ta nine ban ƙi a aurar da maryam ɗin ba amma baba ya ƙi, khadija bata daɗe ba ta fara laulayi, kafin kace me sai haihuwa, ta haifi ɗan ta namiji kyakkyawa kamar ubansa,
Ansha shagalin suna inda hadi ya ɗauko ƙanwar mmnsa daga kwatano tana kula da mai jego, hadi ya kashe kuɗi sosai a wajen sunan khadija inda ɗanta yaci sunan baba sa ibrahim ana ce masa khalil, haihuwar khadija ce ta taso da zancen auren maryam, inda iyayen sadiq suka samu baba da zancen har da kuɗin zancen su da na sa rana baba baiyi wata wata ba ya karɓa aka sa musu rana
kawo kuɗin maryam ya sa na kuma takura a gidan ba wanda yake tausaya min sai ma wulaƙanci da musgunawa danake fuskanta daga kowane ɓangare na naƙi kawo miji nayi kwantai,
ni dai ba abinda nakeyi sai miƙawa Allah kuka na akan ya zaɓa min na gari, sallah dare nake tashi nayi amma randa mama ta ganni inayi har safiya tana mitar wai ina tashi ina son in asirce mijin wata da daddare, haka ina ji ina gani na daina ko kuma inyi a ɓoye,
da bikin maryam ya gabato sai aka haɗa da na ƴaƴan mama wanɗanda ta haifa a gidan ta na fari su uku duka mata dama ƴaƴa huɗu ta haifa acan ta aurar da ta farin ta, kuma duk kayan ɗakin da aka kai su da shi babanmu ne yayi musu gaba ɗaya da maryam ɗin
na so harga Allah in samu miji ko da bikin maryam ne amma hakan be yuba haka na dawo na cigaba da ruwata ina ta miƙa roƙona ga Allah ubangiji (swt) akan ya dubeni da lamarina
Mijin maryam sadiq irin mutanen ne masu sakin hannu, don kullum in dai yaga ƴen gidan mu a gidan sa to da saƙo na musamman da zai ba akawo mana, don haka mama take kiran shi da ɗan albarka, bata sati cikakke sai ta je gidan shi kuwa baya gajiya da hidima saɓanin miji khadija, itama maryam ɗin in ta tashi zuwa haka zata zo da kaya ciye ciye lodi lodi, baba kuwa yai ta sa mata albarka hmmm iyayen zamani
ko da lkcn da maryam ta haihu mama ce da kanta take zuwa har gidan maryan ɗin don kula da jariri da kuma mai jego, nidai tunda naje barka sau ɗaya ban koma ba, sai ƴar autar mu amina da aka kaima ta wai ta taya ta aiki don anga mijinta da ɗan maiƙo
ana gobe suna mama ta koma gidan wai saboda aikin miya, ban yi niyyar zuwa sai da khadija ta biyo min sannan ta sani a gaba muka je, wai don kar ace inayi wa maryam ɗin baƙin ciki
a gida aikin miyar maryam na sha habaice habaice kusan agege da sa ido tun ina danne wa ina nuna ban san dani ake har abin ya dame ni na koma uwar ɗakin ta nai ta kuka na khadija ce kawai ta san halin da na shiga har ta iya lallashina ita kuwa me jego ba abinda ya dame ta hidimar ta kawai take yi
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By mmn walid nd walida (mrs aliyu)
Page :3🌹
Ranar suna ƴa taci sunan kakarta mmn sadiq hafsat wdda za a dina ce mata farhana, sa da rago sadiq ya yanka banda iyayen kuɗin da ya kashe na hidimar suna, ban so na tsoma kaina a harkar sunan maryam ba don yadda naga mama komai idon ta na kai amma da khadija ta ja ni gefe ta min magana sai na zage na fara rabon abinci nima
An sha hidima sosai da sunan mama bata koma gida ba ranar ma ni kaɗai na koma da kayan suna wanda na kaiwa bbn mu saƙon mama,
Kashegarin suna ina kwance har goma kasnacewar gajiyar da yi a gidan suna yasa nace yau ba inda zani wajen ƙarfe sha ɗaya na safe ina ta juyi ina shirin tashi in san abinyi sa ga khadija
"kai yaya kar kice baki shirya ba" gira na ɗaga mata alamar ban gane me take nufi ba,
" yanzu yaya si yaushe zamuje gidan suyan naman" ohhhh yooo ni ba na manta da wani suyan nama ba,
azalzala ta khadija tayi muka shirya muka fita gidan suyan nama amma ga mamakin mu kafin mu je gida ya cika danƙam kamar yau ne sunan mama ta gayyoto mutane bila adadin wai a taya ta suyan sa da rago sai kace shanaye ya yanka, ba wacce kalle mu itama knta me jegon si wani shash shan ƙamshi take yi wai bamu zo da wuri ba, a zuciyata na ce maryam ni ban ma yi niyyar zuwa ba da badan khadija ba ma da bazaki ganni ba
Mu dai ni da khadija ba wani abin arziƙi muka yi a gidan suyan nan ba don mutanen mama sun yi kane kane da naman sai muka zama kawai ƴen kallo kar dai ace bamu zo ba
ranar suyar ma mama bata koma gida sai kashe garin suyar nama da daddare sai gata da kayan nama, nidai aka bani nawa a farar leda na karɓa nace Allah ya raya na cinye a take,
na mama nama ne botiki guda har wani cewa take yi ƴata ce tace in ajiye in taci a hankali, mama ta ci gaba da zuwa gidan maryam tana yi mata wanka ita da jaririyar ta,
randa maryam ta cika kwana 30 cif da haihuwa su mama an shirya kenan za a tafi gidan ƴar albarka sai ga ƙanwar mijin ƴarta nan ta zo
Bayan sun gaisa take cewa mama ai iyami ta haihu, toooo inji mama yaushe
"yau da asuba"
"a gida ko asibiti"
"a gida nurse aka ɗauko mata"
"ai kinji irinta nan ba za akai yaeinya asibiti ba likita ya duba ta sosai sai ace wata nurse tooo Allah ya raya, nidai yanzu da kike ganinan na shirya ne zan tafi gidan maryam in mata wanka ita iyamin sai kije gidan bbn ta ki faɗa sai a samu me yi mata hidima daga can" mama ta ƙare zancen ta tana gyara mayafin ta
"ai naje shine suka ce inzo in faɗa miki ba me zama a wajenta" juyiwa tayi "ban gane ba ni ba ƴar mijina bace nake mata hidima don kara amma ni a rasa me karanta min akan tawa ƴar"
Ita dai ƴar aike tai tsuru tsuru, "to ku a dingin naku shi ɗan uwan nakin ba zai nemo me zama masa da matar sa ba har sai ni uwar ƴa naje" nan ma shiru tayi ba amsa
Tausayi mama ta bani yasani tsoma musu baki "mama ki barshi da zuwa gidan maryam ɗin kaeai ni naje ke kije ki ga iyamin"
" a a ke kije gidan iyamin ni na tafi gidan maryam" tana faɗin haka ta juyawarta tayi tafiyar ta
mamakine ya kama ni, wai mama wace irin macece ne, barin tunanin nayi na jawo ƙofar ɗakin mu na kama hanyar gidan iyamin don inga abinda zan iyayi
ko da naje na tarar me jego batayi wanka ba haka zalika itama ƴar ba wanka na rasa abinda zan musu dole na fito daga gidan na kama hanyar gidan maryam don inje on tattago mama don bansan abinda zan musu ba
a zaune na tadda ta ta harɗe ƙafa tana kwasar farfesun kayan ciki da bread da shayin ta me kaurin gaske, ko da ta ganni sai ta haɗe ranta "lafiya" ta tambaye ni
bayani nayi mata sosai halin da me jego take ciki nayi amma ga mamakina sai ta ja wani dogon tsaki
"ƴar iskar yarinyar sai da nace mata kar ta auri yaron nana amma gashina nan abinda nake gude mata, yaro da shegiyar tsiyar kamar ɓeran masallaci ace matar ka ma ta haihu amma an rasa me kula da ita don kowa yasan cewar sai dai shi ya saka nasa aljihun a harkar gidan ka ba kai a more ka ba, tunda ta auri yaron nan ƙwandaƙar ta ban taɓa gani sai dai ma intazo wajena in bata kullum shi cikin babu, kamar shi ya yankewa tsiya cibiya, Allah dai ya kyauta bari in gama sai muje tare"
to kawai na bita da shi maryam tai mun tayin abinci amma sai nace na ƙoshi ko da mama ta gama da muka tashi tafiya sai da ta cewa maryam wai tayi abincin rana da ita don zata dawo
ita kima maryam ɗin sai tace ai mama ba sai kin dawo ba yunda yanzu na iya wankan kuma na iya yiwa farhana gashi iyami ya haihu hidimar ai sai tayi miki yawa ƙiri ƙiri mama tace bata yadda ai tayi wa bbnmu alƙawarin sai maryam tayi arba'in sannan zata daina zuwa
daga ganin fuskar maryam ba haka ta so ba amma sai tayi shiru, tun a gidan maryam mama take zagin mijin iyami tana mitar auren nasu har muka je gidan, inda cikin ikon Allah muka tarar da yayar mijin na tan ta zo tayi komai ko da mama ta ga haka ko zama batayi ta koma wai ta baro maryam ita kaɗai, ido kawai muka bita nida iyami ko yaushe mama ta zama haka ohooo
Ni na dinga jigiƙar zuwa gidan iyami taya ta aiki sai yar mijin ta da take zuwa safe da dare tana yi mata wanka da ɗan babyn ta, gaskiyar mama ne lamarin mijin iyami sai a hankali sam bai damu da ita ba balle abinda aka haifa wataran haka zai fita bai bata komai ba sai dai in naje da kuɗin da yake hannuna da shi zamuyi abinda zamu ci
nima yanzun samun nawa sai ahankali don iyan amina tana masu taimaka sosai ƙannanta ne suka zo daga ghana don haka yanzu gaskiya ina shiga cikin matsalar kuɗi sosai khadija kawai tasan halin da nake ciki kuma itace kawai take taimaka min da ɗan abin da zan kashe, kuma itama ba kasaifai ta fiya aikomin da shi ba, wataran kuma idan ta aiko min sai ince ɗan aiken ya maida mata da abinrmta don itama nasan halin da take ciki hadi ba wani basu kuɗi yake ba, shi komai na fnfanin gidan sa yake siya ya ajiye don hka ɗan kuɗin da yake basi ba wani abin ya taka kara ya karya bane
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
Page:4🌹
Mun shiga sunan iyami lfy lau inda ko ƙeyar mama bamu gani tun randa ta zo, na ci gaba da zuwa taya iyami aiki har sai da ta yi sati uku sannan na daina,
Rayuwa taci gaba da tfy muna ƙara girma yanzu ina da saurayi me suna salisu irin ƴen ci ranin nan ne ɗan sokoto, yan zuwa zance duk da dai ba wani son shi nake yi ba amma kuma yafi ka zauna ba aure, baba ya tare shi akan ya turo magabatansa, ba ƙaramin daɗi yaji ba
Tun ina lissafin dawowa salisu daga sokoto don zuwa ya sanar da magabatansa har na hakƙura don yanzu kusan watan shi ba lbrnsa, kamar an aiki bawa garinsu
Ko da ya dawo yazo gidan mu diraect yace wa bbn mu wai shi bbn shi yace wai ba zai auri ƴar bariki ba wayyo Allah na ranar na sha zagi wurin bbn mu kamar me harda kwaɗeni wai dama iskanci muke yi da salisun shiyasa bbn sa yace bazai aure ni ba, shi kuma salisu a nasa ɓangaren yana nufin lagos ai kamar bariki ce shiyasa ban wani ƙullace shi ba
Yau da sassafe khadija ta aiko wai don Allah inje, ban san ko menene ba amma ban fita ba sai da naga komai sannan na kama hanyar gidan ta, ko da naje akwance na same ta ba lfy, "ohhhh khadija jikin ne" ya mutse fuskar ta tayi ta kasa magana kasancewar miyan da ya cika mata bakinta, wan ya tabbatar min ciki ne da ita
Ohhh Allah ƙanwata zata yi na biyu ni ban ma yi auren ba Allah ka dubi lamarina, khalil yana ta rigima ɗaukar shi nayi nai masa wanka na shirya shi na goya sannan na dawo ɗakin nata bacci takeyi don haka sai ban tashe ta sai na hau gyara mata ɗakin nata
sharar da nakeyi ce ta tada ta, "sannu yaya" mmm kawai nace na ƙarasa, tashi tayi zaune
"yaya dama yaye shi zanyi shine nace bari inkira ki ki tafi da shi idan yaso bayan kwana biyu kya dawo shi"
"kin gayawa bbn sa"
"shi ma yace in kira ki in ce ki ɗauke shi na kwana biyu, amma ni so nake ya kwana uku kinga kafin nan na huta"
"to shike nan bari in tafi da shi ɗin bana son ina daɗewa a gidan ki kinsan halin mama" to shike nan dubu biyar ta bani wai inyi masa siyayya ƙin karɓa nayi sai da ta rantse min da Allah cewar hadi ne ya bayar a bani sannan na karɓa, na haɗa masa kayan sa na fito kenan muka ci karo da maryam ko daga ina take ohooo
" a a a awata sabon gani yaya dama ba a ganin ki a ko ina sai gidan khadija, ni kun ware ni kamar ba ƴar uwar ku komai sai dai kuyi tare ba ni"
"haba dasooo" na bata ansa dayake haka nake ce mata idan ina cikin nishaɗi
"wallahi khadija ce ba lfy tace min inzo in ɗauki khalil in yaye shi, shine fa kika ganni yanzu ma na zo kuma kin ganshi nan a baya na zan juya don bana son ƙananan maganganun mama"
"yaya khadija" ta faɗa ta karfi tana dafe kirjin ta "ciki na biyu, bari inje inyi mata tsiya ita me cewar sai nan da shekara uku" ta faɗa tana shigewa tare da jan hannu na zuwa cikin gidan "yaya yaushe rabon da mu haɗu tare har muyi hira yaudai Allah ya bamu dama baki isa ki koma gida da wuri ba sai munyi hirar zumunci" ba yadda na iya haka na bita zungwi zungwi
mun sha hira sosai da ƴen ƙannena sai yau nasan cewar nayi kewar su sosai har sai bayan la'asr sannan mu tashi muna shirin tafiya ne maryam tace
"yauwa dama sunday me zuwa ne bikin cika shekara 10 da auren uban gidan bbn farhana don haka za ai celebrating a beach shine nace bari in gaya muku ko za ku mara min baya don kune kaɗai ƴen uwana" kallon kallo muka tsaya yi ni da khadija, har maryam ɗin ta tsargu bama son zuwa
"gaskiya maryam nidan ina fama da kaina bana tuanin zan iya zuwa wani hayaniyar party" inji khadija
"ni ma gaskiya baba bazai barni zuwa beach ba, yanzu ma ya aka cika yana cewa na zama ƴar iska balle yaji naje beach" rau rau maryam tayi da idon ta
"yanzu ace ni bani da wanda zai karanta min ku da nake ganinku a matsayin ƴen uwana amma bazaku rufa min asiri ba shike nan Allah ya bamu alkhairi" tana faɗin haka ta sunkuci jakar ta azuciye
"a haba abar sooo me yayi zafi da zaki tafi" na kamota ina faɗin haka
"to me kuke so in muku tunda yanzu kun tsane niiiiii" ta karashe zancen nata da kuka
"to yanzu ya kiko so muyi abar soo" na faɗa da sigar lallashi
"ba komai daga ke har khadijar baku da lkcn da zaku rufa min baya alkcn da na gama yiwa mijina kurin zan gayyato ƴen uwana su taya ni aiki kuma muje gurin partyn tare"
"to shike nan karki damu zamu zo mu taya ki, ita khadija sai ta gayawa hadi sai su tafi guri partyn tare ni kin ganni nan idan kika gayyace ni wurin party yanzu kunya zaki ji don ko kayan da zan sa inje banni da shi"
Sai alkcn khadija tai magana "indai kayana ne zan baki, dama akwai wata, doguwar rigata ƴar dubai da na siya tai min tsayi sosai sai ki sako" harara na banka mata wacce ita maryan ɗin bata lura ba
"to kinji yaya don Allah ku zo muje,ƙila acan ma Allah ya haɗa ki da nagari" ta faɗa a zolaye amin thumma amin inji khadija, muka gama tsara yadda tafiyar tamu zuwa partyn zai kasan ce amma maryam ta roke ni da kar in gayawa mama don ta san halin ta sai tace zata je
dariya miua dinga yi mata nida khadija don soyayyar nan da ta ƙullu tsakanin mama da maryam sai Allah, bamu muka bar gidan khadija ba sai da mukayi magariba bayan mun gama tsara komai
ko dana je gida haka natarar da mama ta cika tayi fam wi naje na zauna a gidan khadija banzo na ɗaura abinci ganin khalil a bayana yasa ta tambayin daliln zuwana da yaron, na faɗa mata maryam ce ba lfy shiyasa tace mi in yaye shi
"haka dai za a kare sai dai aita ganin ƙannen suna haihuwa ke kuwa kin zama uwar mata sai in sun kuma samin ciki a kira ki abaki yaye ke kin fasa auren ke nan si dai ki ta rainon ƴaƴa to Allah ya bada sa a" tai ta mita nida ɗakin mu kawai na shige na ɗauko kayan girki na zo na ɗaura na dare ina mamakin abinda nayiwa mama haka da yawa da yasa ta tsaneni
ko dana gama da wuri muka kwanta nida ɗan yaye na amma abin baƙin ciki, cikin dare yari ya tashi yai ta tsala kuka kamar me na rasa abinda zan masa baba ne ya fito yai ta min bala'i a kaina ga kukan yarioga bala'in bbn mu har gorin nayi kwantai sai da yai min wai nima kaina na zame masa jaraba gashi na je na ɗauko yaro ya zo ya ishe su da shegen kuka sai kace ba jikan sa ba
ya ƙaraci bala'in sa ya koma cikin ɗaki mama dai bata ce komai ba sai dai uban tsaki da take ta ja kamar tsaka ahaka muka kwana da sassafe baba ya tashe ni alkcn na ɗfaa gyangyaɗi ya nan ya tasa min kwandon bala'il ba irin zagin da bansha wai na hana shi bacci,in fito da miji inyi aure naƙi sai yawon gidan ƙanne ko kunya bana ji ranar nayi wan iabu wai shi kuka har na gode wa mai duka
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By mmn walid nd walida (mrs aliyu)
🎁 *Nasibi writers association*🎁
In dedication to all nasibi writers 😘
Page:5🌹
Da ƙyar baba ya yadda khalil yai kwana biyu sannan ya jaaa min kunne akan kar ya dawo ya same shi, sai da na gama duk wani abinda nake yi da la'asar sannan na mayar da shi,
Mun ƙara tsara yadda zamu haɗu a gidan maryam ran lahadin don taya ta aikin da kuma partyn sai magariba sannan na fito na koma gida, munyi da khadija akan zata zo ranar sunday da niyyar zan raka ta asibiti daga nan zamu kasuwa, indan kuma na fice sai baba ta gani yo wayasan lkcn tashi daga wurin partyn
Ban gaya wa mama akan partyn ba don nasan halinta sai tace zata, ranar sunday ƙarfe bakwai sai ga khadija a ƙofar ɗakin mu tana mana knocking,
ni na buɗe mata sai ga baba ya fito daga ɗakin "waye wannan da safen nan" ganin khadija ya sa shi wangale bakinsa
*khadija* lfy kika zo mana da sassafen nan" ya faɗa yana zare ido, jin sunan khadija ya sa mama fitowa daga ɗakin ta da zanin a hannun ta ytana ƙoƙarin ɗaurawa "lfy" itama ta tambaye ta, nima tashi nayi ina zare idin ƙarya kamar bansan komai ba
"ba fa komai baba dama bani da lfy ne, shine hadi yace min inje general hospital na cikin lagos in ga likita sosai shine na biyo yaya ta rakani ko ta riƙe min khalil inna ta tashi shiga" ta faɗa kamar gaske
Tsaki mama taja tayi wucewarta ɗaki shi kuma baba sai ya hau mita "da ba sai ki kirata taje can ta same ki ku tafi ba,amma kin tashi kin doko mana sammako sai kace wani abinne ya faru"
Kallon inda nake yayi "sai ki tashi tunda kin zama sai in ƙannen ki ba su da lfy su dinga futowa daga gidan mazajensu kina raka asibiti, Allah ya bada lfy" ya faɗa wa khadija
Tashi nayi jiki ba ƙwari banji daɗin abinda baba ya faɗa min amma ya zanyi, "bari inyi wanka"
" a a yaya ba sai kinyi wanka ba wanke fuskar ki kawai, ai daga asibitin kasuwar ikko zaki rakani" ta faɗa da ƙarfi don baba yaji ilai kuwa
"kuce yau kawai yawo zakuyi,to ki tabbatar na dawo na same ki a gida" ya faɗa yana shigewa ɗakin
fuskata kawai na ɗauraye na saka hijabi na ja musu ƙofar falon muka kama hanna, ni na karɓi khalil na goya don naga khadija ƙarfin hali kawai take yi
Gidan maryam a A p yake don haka sai muka hau keke napep don da yar tafiya, bakwai da kwata muka isa inda muka tarar madam ɗin an tashi ana ta hidima, mmmmm wayaga su maryam
"sai yanzu kuka zo" ta faɗa tana zunɓurar baki
"au sai yanzu nema, da asuba kike son mu zo ko me"
"ni dai ku zo mu fara don tun bakwai na aiki bbn farhana kasuwa yayo mana siyayyan abinda zamuyi amfani da su" binta mukayi inda ta lissafa mana abinda da zamuyi, springrolls, meat pie, doughnut, sai cup cakes kowanne 300 pieces ,
Zaro ido nayi "maryam jakai ne mu"
"akwai masu taya mu ai" ohhho
"yauwa sai kuma kunun gyaɗar nan da kike yi me farar shinkafa, kinga har na jiƙa gƴadar da shinkafar, ya siyo robobi na yoghurt in mun gama sai mu ɗura a ciki ko ya kikace"
" eeeeeeh hakan ma ya bada ma'ana, muga gyaɗar" nuna min gyaɗar tayi dayawan ta, sannan muka je ta nuna min farar shinkafar da ta jiƙa wuuuuuuu nace ina zare
"maryam me za ai da dawannan uban shinkafar ke da ake sa ƴar kaɗan don ta ɗaure kunun, amma ba komai ayi waina da ragowar"
" waina kuma yaya partyn ƴen gayu kin taɓa ganin waina"
"ko ma partyn uban waye bazan bari ai asarar uban shinkafar nan, ina masu taimaka nan su zo suje suyo mana cefanan waina"
Maryam bata soo yin waknar nan ba amma ba yadda ta iya ni kuma gani nake yi in aka bar shinkafar lalace wa zatai don cikin botikin penti ne ta cika shi dam da jiƙaƙƙiyar shinkafa, masu taya mu aikin suka zo muka basu sautjn sannan muka fara hidimar aikin
ƙarfe 2:00 dai dai mun gama komai hatta da wanka jira kawai muke yi sadiq yazo mu tafi, shima ko da yazo yaga wainar nan sai da yayi ta mitar abin ƴen gayu me ya kai waina, sai da nace musu in ba za aje da waina ba ni ma bazan je ba sannan ya Haƙura aka zuba kaya a boot ɗin mita muka shiga
sabuwar doguwar rigar da khadija ta bani ita na saka ajikina, irin rigunan ƴen india ne me buɗewa sosai daga ƙasan, rigar tai kyau sosai samanta a tsuke yake inda ƙasan ya buɗe sosai don sai inayi ina tattaro ta indai zan hauwuri me tudu ko zan sauka, sai yaba min kwalƙiyar suke yi ni ko kunya ce ma ta kama ni don duk kyan nan nawa na rasa me taya ni ohhhh ni abu
lekki beach muka wuce direct tunda anan ake partyn ko da muka je ƙin ɗauko min waina ta suka yi sai ni na koma da kaina na ɗauko abata da miyar ta da ta sha bogo (ƙashi me taunuwa 😋😋) da kuma pkomo sai nama, na je inada ake jere abincin na ajiye, har anfara shagali kowa yana ta son ya nuna bajintarsa awajen celebrants ɗin ta fannin ko abinda aka kawo na ci ko na sha kona kyauta wato gift, sun yi kyau suma celebrants ɗin wato alh musa sosai inda suka ci kayan su iri ɗaya su da ƴaƴnsu guda huɗu
ganin lkcn sallah yayi yasa na ɗan yi nisa daga wurin partyn don in samu in gabatar da farilla, na ɗau lkc me tsawo ina addua sannan na naɗe sallayata na koma gurin partyn tun daga nesa nake jiyo hayaniyar ƴen partyn, nace lallai duniyar tayi wasu daɗi
Y
ƙaraswa nayi don inga menene yake sa mutane wannan hayaniyar ashe akan waina ta da maryam da mijinta suka ce kauyancine ake ta wannan wasoson, ana so can na hangon babba abokin alh musan da kuƙar wainae a hannun sa ya ɗora ta a sama nkansa mutane suna ta binshi ta basu, dariya nm abin ya bani sosai
sai ga kuma sadiq shima yana ta wani washe baki suna magana shi da alh musan daga gani zuba santi yake yi, matar aƙh musan ce ta matso kusa da mijin nata ta masa magana, sai naga ya juyar da plate ɗin da wainar take ciki a lkcn da ita ta kai hannun ta, ban san lkcn da tintsire da dariya wato yau wainar ta ma tasa masoya faɗa
bayan an gama wasoson wainar sai kuma aka ci gaba da hidimar partyn, abin nasu ya ƙawatar sosai da sosai, sai da la'asar tayi sannan na kuma fita na gabatar da tawa ni ko me akeyi bana barin sallah ta wuce ni haka nake, bayan na dawo naga salon partyn ya canza wai couples dance toooo
couples za a zaɓa su zo su danceee a filin wurin bayan sun gama sai su ma su zaɓo wasu an ɗan jima ana haka sai kuma akea ce ance dance dance dance, sai naga kowane ɗan miji yana jan matar sa suyi rawa saurayi yaja budurwar sa ƴar iska khadija itace har da kawo min khalilkarɓar shi kawai nayi na bar wurin don inna tsaya sai zuciyata ta buga
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By mmn walid nd walida (mrs aliyu)
🎁 *NASIBI WRITERS ASSOCIATION*🎁 we shine with the smile ☺ 😊😊☺ of our readers, so keep smiling while we keep shining ND entertaining u with amazing story love y'all mua Mua 😘😘😘😘
Page :6🌹
can daga nesa daga wurin partyn na samu wuri a yashi na zaina ina kallon yadda ruwa yake yo anbaliya ya na koma wa tekun ba tare da wani wani matsala ba ko wani takura khalil na zaunar akusa da ni don in samu inyi tunanin rayuwata sosai, dama nima zan zama kamar ruwan nan in ta sha'anina batare da damuwa ba ohhh Alƙah ka kawo min ba don halina ba na ɗaga kai sama ina roƙon Allah a ziciyata
kamar an jeho mutum haka naji an zauna kusa da ni haki, a ɗan tsorace na juyo inda mukai huɗu da wani balarabe, balarabe ne sosai ba wai kamar labarawa yake ba kana ganin shi kaga jinin larabawa a tattare da shi, ƙura mai ido nayi ina ƙarewa ƴar kyakkyawa fuskar shi kallo wanda kallo ɗaya zaka gane tsabar kyan da yake ɗauke a fuskar tasan
"Baby kallon ya isa haka, zan ɗan dade a kusa da ke" ƙara sakin bakin nayi ga hausa kuma raɗau abakin ɗan balaraben mintsinin kaina nayi kodai mafarkin nayi yana magana,ƙara katsemin tunanina yayi da cewar "baby am talking to u" baby kuma sai a lkcn na dawo hayyacin na inda na zunburar masa baki nace "baby kuma, wace babyn ka, ko ka zo da babyn kane ka ɗauka nice"
Murmushi yayi wanda ya ƙara fidda masa da tsantsar kyan sa, "am talking to u" ya ƙara faɗa juyawa nayi ko zanga wata a kusa dani ganin babu kowa yasa na tabbatar dani yake
"excuse mr man am not ur baby........... Bai barni na ƙarasa zancen nawa zancen nawa ba ya ɗora da cewar "wasu ƴammata tun ɗazu suke ta bina shine ni kuma nace musu da matata nake suka ƙi yadda shine kawai ganin ki a zaune ke kaɗai ya sani garzayowa don in ɗan lape kafin su gaji su tafi,"
Harara na banka masa ina ƙoƙarin miƙewa ya ma rainani, "noo babay karki ƙoƙarin tashi ya kamata ki juya ki kalli yadda suke binki da kallo" ni har yanzu ina mamaki hausar da take fita daga bakins, zama nayi sannan na kalle shi "a ina suke"
"kalli hannun daman ki zaki gansu su huɗu"
juyawa nayi a wayance wasu ɗima ɗima matan lagos na gani kowacce sai zare min ido take kamar zasu cinye ni, bansan lkcn da juyo na daina kallon su ba, dariya naji yana min "kinga in kika tashi Allah ya haɗa ki da waɗancan ko ƙashin ki baza a gani ba"harara na banka masa tare da murguɗa masa baki
"baby ba a harara ta don dai ni nakawo kaina amma ni mutum ne da bana ɗaukar raini" wata hararar na kuma doka masa na juyar da kaina
wayar sa ya ɗauko yana ta ƴen wayoyin sa inda khalil da ke tsakiyar mu ya fara yi masa gwarancin sa ni shap ma na manta da yaron kawai sai ji nayi ya ɗauke shi yana mai wasa ban kula su don san duk abinsa ina zaune de baze sace yaron ba
wayar sa ce ta fara ringing ya ajiye khalil sannan ya ɗau wayar
"ɗan uwan ya kwana biyu ya garin da jikin hjy kuwa" shiru yayi daga dukkan alamu ɗan uwan nasa yana ansa tambayoyin da yayi masa ne, sun ɗan taɓa jira irin tasu wadda su suka san ko akan menene sannan naji yana cewa "haka tace hjyr, to kace ta kwanta da hankalin ta Allah ya amshi addu'ar ta don gani ma yanzu ga yayar taka"
jin haka yasani tunani waye daga cikin ƙannena,
" a a ai ka bari kawai sai kazo lagos ɗin sai ku gaisa" aka kuma magana daga can ɓagaren
"a haba wannan karon ba ƙarya nake yi ba ɗan uwa, gata akusa da ni" muhawarace kamar yadda na fahimta ta kaure tsakaninsa da ɗan uwan nasa akan sai yayi magana da wadda yace yayarsa ce daga ƙarshe dai aka kada ɗan balarabe, juyo wa yayi ya kalle ni inda ni kuma na haɗe rai
"baby don Allah ga ɗan uwana zaku gaisa"
"a wane dalilin na faɗa ba tare da na kalle shi"
"a dalilin in baki karɓi wayar ba zan tashi in barki da zakunan cen da suke ta kallon ki da tsana har yanzu" ya faɗa yana kare zancen nasa da dariyar mugunta
fusge wayar nayi daga hannun sa na kara akunne na tare da sallama
" wa'alaikis salam yayata ya garin lagos ɗin, ya mutanen gidan" lfy na ansa atakaice
"yayata kece ta farko da ɗan uwa ya fara gabatar mana amatsayin wacce yake so dan Allah ki riƙe mana shi amana, har Allah ya kaimu lkcn da zaki zama tashi kinji" tooo kawai na iya cewa
hira sosai ya dinga min akan mahimman cin ɗan uwan nasa wanda ni kuma wasu in gane wasu in bishi da too kawai,
"ya sunan yayata tawa ne" ya jeho min tambaya kallon inda balarabe yake nayi inda hankalinsa yake kan khalil suna wasa kamar baya sauraren mu
"ka tambayi ɗan uwaan naka mana sai ya faɗa maka"
"to shikenan ga hjyr mu kinga yanzu ta tashi daga bacci bazan bari wannan ɗaɗɗadan zancen ya huce ba ungo ku gaisa"
sai da ɗan ji ɗan jim sannan naji sallama cikin wata kamilalliyar murya, na ansa sannan na gaishe ta addua tai ta doka min akan in kular mata da ɗanta amana, wayyo Allah ni ban san mutum ba amma ƴen uwansa suna ta bani amanarsa to kawai nake binta da shi da kuma in shaa Allah ɗuk ilahirin jikina yai sanyi
"ya sunan ƴar tawa naji tace, bazan iya yi mata musu ba yasa ni nace zainab, Maa shaa Allah babban suna Allah yayi wa tarayyarku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba amin nace yo dan Allah me zance
"ina ɗan nawa" ta tamabaya miƙa masa wayar naiy ya karɓa jin wacce ke maganar ne yaga ya ɗan nutsu sai wani shagwaɓa yake kamar wani yaro har da wani cewa baya iya bacci saboda basa kusa da shi
ya ƙaraci dai shagwabaraa sannan ya miƙo min hjy tace zakuyi sallama, karɓar wayar nayi sal da ta ɗan ƙara yi min nasiha mai shiga jiki sannan mukai sallama bashi wayar suka ƙarasa sallamar sannan ya ajiye
shiru ne ya biyo bayan haka ba wanda ya kuma tanka wani daga cikin mu ni ina tunani n hrar mu da baiwar Allah nan shi kuma yana danne danne a wayar sa
hayaniya na jiyo a bayan mu kamar ana kokawa wanne ne yasa muka juya atare da shi don ganin ko me ke faru, hasken camera camera ne kawai yake ana walƙiya afuskokin mu kasancewar duhu ya farayi *shit* kawai nahj yace ya sunkuci khalil ya riƙe mun ya fara jana muka fara gudu inda masu cemerar suke binnu suna.ci gaba da ɗaukar hoton su
kasancewar yashine a ƙasa don haka bashi da daɗin yi gudun a kai wannan ya bawa masu ɗaukar hoton daman samun hotunana namu sosai duk da naga akwai masu karesu da hana su ƙarasowa wajen mu, haniniyar doki kawai naji a bayan mu wanda wannan ne ya bamu damar tsayawa ya wuce sai naga nakan dokin ya sauko ya miƙawa balarabe linzamin ya kama ya hau hannu ya miƙo min na noke
"ya zakiyi da waɗannan vultures ɗin da suke binki" juyowa nayi na ci karo da mutane sunfi biƙa adadin da suke bin mu a guje da camera sasu kuma da abin magana a hannu dats mic daga gani ƴen jarida ne bansan lckn da na miƙa masa hannun ba yai sana dani sai kan doki ya karɓi khalil daga hannu mutumin nan, ya zaburi dokin tuni mukai gaba ba abinda kake gani sai haken camerar tana ɗaukar hotuna too shi wannan ɗin waye shi haka da ƴen jarida suke ta binshi 🤔🤔🤔
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁nasibi writers association🎁
Page :7🌹
Wani keɓantaccen waje muka nufi inda muka shiga ni dai har yanzu jikina bai daina rawa ba
"ke da kuka zo, don in san inda suke in kaiki"
"da ƙanwata da mijinta"
"kawo wayar ki sai in kira su" ɗauko wayata nayi wadda ta sha jiki, kallon wayar yayi sannan naga yana ƙoƙarin buɗe ta ciro sim ɗin yayi sannan yai wurgi da wayar tasa wayar ya cire sin ɗin ya samun nawa,
"wane suna zan kira" ya tambaya bayan ya gama daidaita wayar
"maryam" na amsa atakaice, sanin cewar ba kuɗi awayar ne ya sani kau da kai aikuwa yana dannawa yaji ba kuɗi sai ya ja tsaki
"jira ni anan bari in siyo credit naga wayar taki ba ko asi"
Ficewa yayi na bi bayan shi da kallo a tsaye yake me ƙirar ƙarfi irin waɗanda ake cewa giant ga tsayi ga faɗi oohh wannan matar shi zata more irin waɗanda idan sun rungume mace ne zata ji kamar babu wata damuwa a rayuwa lif zata lafe a faffaɗan ƙirjinsa
Bai daɗe ba sai gashi kiran maryam yayi tayi mai kwatance sannan ya ɗauki khalil muka ƙarasa har wajen motar mu ya raka ni
ko bayan da muka shiga wayar tashin ya miƙo min tare da cewa "sai munyi waya" juyawa yayi ya ɓace cikin duhin daren nan kamar walƙiya ajiyar zuciya na saki wanda sai alkcn na fahimci ashe duk waɗan da ke motar hankalin su na kaina zunɓurar baki nayi na ce "menene"
"a ina kika samu wannan yaya" inji maryam ba irin tambayar da basu yi min ni dai bance musu komai hankalin khadija ne yaje kan wayar sa da ya bani
"wannan kamar iphone 7 latest version ko" gefe sadiq ya faka da motar ya karɓa
"ai kuwa ita ce, a ina kika san shi" oho kawai na iya faɗa
"kinsan nawa wayar nan kuwa yaya tana fa kaiwa dubu 350" zare ido na nayi ina kallon wayar da zata kai wannan kuɗin wai a hannuna dariya na ɗan yi ku china ce
dariya suka dinga min wai basu taɓa jin iphone china ba sai a wajena ni dai har ni dai ban kula su har gida su kaini na ɗauki saƙon mama na kayan snacks nai ciki
ko dana koma baban mu bai dawo ba don haka kawai sai na ba mama bata tambayeni ina na samo ba nima ban damu ba sallolina nayi na kwanta amma kuma sai na kasa bacci tunanin ɗan takari ne ya faɗo min to ɗan takari mana muma ƴen uwan mu idan suka je garinsu takari ake ce musu to muma ba dole muce musu takari ba ( har na tuno littafin makawa, ki ci gaba da gashi lbrn nan yana ƙawata mu)
da asuba na tashi da wuri sakaka haka na wuni ba abinda yake min daɗi ko abinci kasa ci nayi abi kaɗan kuma sai induba wayata ko zanga ankirani shiru kakeji
da daddare bayan sallahar isha mun zauna muna kallo har da su baba sai ga breaking news an rubuta da manyan harufa *ajaban caught off guard with wife nd son* sai ga hoton mu da ɗan takari danɓarere akan akwatin tv
baba ne ya fara magana "wannan kamar zainab ko dai ido nane" shiru nayi
"itace mana baha khalil nan ba ɗan wajen khadija"
ni dai bance komai ba sai ga news an ci gaba "a jiyane muka samu daman samun hoton matashin yaron nan me multi billion dollars shipping, company da yayi ƙaurin suna suna a dunuya wato mr ajaban da kuma me ɗakinsa tare da ɗan ƙaramin ɗan su wanda suka je shaƙatawa a beach, rahotanni sun nuna cewar mr ajaban ya daɗe da aure inda ya ɓoye wa ƴen jarida da duniya kasancewar baya san iyalinsa su shiga cikin hayaniya, sao jiya Allah yasa muka samu daman ɗauko hotonsa sai asha kallo lfy"
kamar afilm haka naga abin namu da yadda muke gudu ƴen jarida suna bin mu abin gwanin sha'awa Allah nidai kam ya birge ko don ban saba ba be ohho
saukar mari ne ya dawo dani hayyacina ashe baba yana ta magana banji ba babu yadda ybaiyi ba in faɗa masa ko waye nayi shiru ba urin zagin da ban sha har cewa yayi in ban fidda miji ba cikin satin nan gezawa zai kaini ya bada ni sadaka
Ya gama bam bamin sa ya shige ɗaki ita ma mamahaka kwanciya nayi ina tunanin to wannan wanene shi wane irin suna ne *ajaban* a haka bacci yai awon gaba da ni
kashe gari da sassafe bayan na idar da sallah ina zaune sai naji wayata tana ringing kamar kar inɗau amma sai na daddage na ɗauka a lkcn ta kusa tsinkewa sallamar sa naji wanda ko bacci nakeyi naji muryarsa zan gane na amsa ga drivwr kiyi masa kwatancen gidan ku too kawai nace
drivern ya karɓa nayi masa kwatance sosai yace ya gane sannan ya kashe wayar murna naji ko ba komai zai zo zance, ko yaushe zaizo na tambayi kaina ima murmushi
komawa nayi na kwanta ina tunanin ɗan takari na wani daddaɗan bacci me ya fafa kwasata, kamar a mafarki naji ana buga mana ƙofa kamar za a karya a firgice na tashi wanda yai dai dai da fitowar bbn mu daga ɗakin yana mitar waye
buɗe ƙofar yayi yaci karo da wasu ƙarti su biyu cikin baƙaƙen kayan su da baƙin glass
"sainob in ko" wato ina da zainab
Hannu baba yana rawa ya nuna ni da yatsa
kirawo ƴen uwan su suka yi akan gani nan wasu mata ne suma cikin irin shigar mazan suka shigo suka kama ni suka fara ja zasu fita da ni bbnmu na ruƙo ina kuka, doke min hannu yayi nina aike ki ya faɗa muryar sa tana rawa daga gani atsorace yace
a haka suka jani har waje duk ƴen gidan mu sun fito ganin wannan ikion Allah nikuma sai kuka nake yi ina ihu na a taimake ni amma ba wanda ya kawo min a gaji
a tsakiyar layin mu sukayi parking motocin su waɗanda suka kai kusan guda goma duka baƙaƙe sai ƙyalli suke yi a ta tsakiya suka saka ni suka rufe nayi nayi in buɗe ƙofar amma na kasa sai kawai na saki wani sabon kukan
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By mmn walid nd walida mrs aliyu
🎁nasibi writers asso🎁
Page:8🌹
Kuka nakeyi ina yin gunji sannan muna tafiya a hankali, tsaki naji an ja min wanda yai min nuni da cewar ba ni kaɗai bace a motar ba waigowa nayi don inga ko waye hmmm "ɗan takari" na faɗa da karfi da kuma mamaki
"ɗan takari kuma kinga nayi miki kama da takari ne"
"oho maka naga in ƴen nan sunje garin ku takari ake ce musu to muma in kun zo garin mu ba dole muce muku takari ba"
Useless kawai najo yace ya juya ya ci gaba da danna laptop ɗinsa
"me yasa ka sato ni" na tambaya be kalle ni yaci gaba da abinda yake yi ba irin tambayar da ban masa amma ko ƙala baice min ba har muka isa inda zamu,
Parking na ga anyi
"ki fito"
"walƙahi ba inda zan je sai ka gaya min me nayi ma ka sato ni" be kula ni can sai naga waɗannan ƙattin matan nan sun zo sun kuma kamoni ina ihuna ina komai naga mu nufi wani jirgi da yake gaban mu
Nutsuwa nayi donni in akwai abinda da tsana yabi bayan jirgi tun wani haɗarin jirgi da na gani nake tsoronsa
Juyowa nayi na kalli ɗaya daga cikin matan nan mausu jana na fara mata yarbanci akan don Allah kar ta sani cikin jirgin nan mutuwa zanyi, kamar ba da mutum nake
tun ina kuka da roƙon a sanyaye har na fara zunduma ihu za a kashe ni a jirgi kasancewar private plane ɗinsa ne yasa ba mutane sosai muna ƙara dosa jirgin naganshi wani tanƙameme da shi da zuciyata ta buga sai na wani luuuuu zan faɗi ni ban yadda ba na suma cak naji ɗaya daga cikin matan ta ɗagani sama ta ci gaba da tafiya ganin suman nawa na ƙarya bazai min ba yasa ni na wani miƙa sai gani sauran kaɗan in suntumu a ƙasa da saurin ta ta taro ni suka ƙara riƙe ni ita da ɗaya
a matattakalar benen hawa jirgin ma sai da akayi artabu da ni inda daga ƙarshe de sai ɗaukata akayi ina ihu iya ƙarfina, ko da muka shiga jirgin sai na nutsu don gani nake yi kamar idan nace zanyi kokawar sai in ruguza jirgin cikin jirgin ya sha kujeru na aƙfarma har wani bar ne acikin sa inda ake jera lemuka kala, kamar falon wani hamshaƙin me kuɗi sam beyi kama da cikin jirgi tunda a film mun saba gani cikin jirgi kujerunsa a jere suke kamar a class wannan kuwa a zagaye yake kamar kana falo tsayawa nayi kawai ina kallo amma yanzu ba lkcn ƙarewa cikin nan
zaunar dani matar tayi ta ɗaura min belt sannan tayi gaba, ɗan takari ne naga ya fito daga wata ƙofa a jirgin ya doso ni yana murmushi duk da firgice nake amma hakan bai hanani gani kyan da yayi ba
"naga alamar kina tsoron shiga jirgi ko, to da fatan dai baza ki kayar mana da jirgi ba da kokawar nan taki ba idan mun tashi" zare ido nayi alamar tsoro ne tattare da ni, murmushi naga yayi sannan ya juya ya wuce tunda na zauna bani na tashiba har sai da muka sauka ko ƙwaƙƙwaran motsi bana yi don kar in kada jirgin sukuwa sai wani kaiwa da kawowa suke yi ko a jikin su
kasancewar na gama tsorata yasa ko da muka sauka ban wani yi taurin kai ko ma dai ina za a kaini yanzu munyi nisa da gida kokawa ya ƙare,
mota ɗaya aka kuma samu da ɗan takari wannan karan ko kallan inda yake banyi ba har muka isa masaukin mu, fitowa nayi nan ma na bi bayan matan inda muka doshi wani tafkeken gini kamar ba mutun ne ya gina shi ba
door bell ta danna inda wata mata again ta buɗe suka gaisa sannan ta nuna mata ni tai wuce warta ni kuma na tusa kaina ciki
tsayawa faɗin tsaruwar falon nan ƙauyanci, tafkekene na faɗa inda aka sa ma kujeru kusa set 7 a kowane angel inda ba wata kujera da take kusa da ƴar uwarta ga ƙofofi nan barkatai ba iyaka
tafiya mukayi muka ɗan wuwwuce wurare da dama kafin mu zo wata takekiyar kofa buɗewa tayi inda turaren da aka sa ya doki hancina na lumshe ido don tsabar ƙamshin sa ɗaki ne pink komansa pink ne gado, kwaba komai dai na ɗakin pink ne
come in naji tace binta nayi har ciki ta buɗe wata ƙofa nan ma muka shiga sai na banɗakine tafkeke shima ba abinda babushia kamar ɗakin komansa pink ne
wani tafkeken Jacuzzi tub ne a tsakiyar toilet ɗin da girman sa wanda ya gani cike yake da ruwa da red flowers da aka watsa a cikin ruwan sai wsu ƴammata da suka kewaye ruwa su shida ko wacce da uniform a jikin ta
bath her" kawai naji tace, kut tana nufin su min wanka yau fa ake yinta na faɗa araina ruƙunƙume jiki na nayi sai gasu gaba ɗaya sun doso ni kamar wasu karnuka kokawar cire kayan muka dinga inda daga ƙarshe wacce ka ta kawoni tace su ƙyaleni
ko da suka sake ni da murmushinta ta matso kusa da ni
"madam they r going to help u take a bath nothing more"
"no i can bath my self i have being taking my bath since when i was born" dariya tayi
"indeed" ni nama manta ashe sai mutun ya girma yake fara yiwa kaansa wanka
"ok here's how we will do it they will help u nd u Will do d rest okey" gyaɗa mata kai nayi
wani towel ta bani na cire kayan jikina na ɗaiur shi sannan na shiga cikin jacuzzi ɗin ruwan yai daɗi dai dai yanayi, fara massaging ɗina sukayi
wayyo me kwance min kai tanayi me gyaramin ƙafa tanayi me min gyaran hannu kowacce dai ta kama aikin da ta ƙware akai, mun kusan awa anayi min gyaran jiki ga matsa da nake sha akai a kai sai da suka gama sannan suka canza min ruwa suka fita suka barni inyi wanka na
da ƙyar na iya wankan na fito don tsabar daɗin ruwan da nake ji ko da na fito daga toilet ɗin wasu saitin ƴanmatan na kuma gani masu irin uniform ɗin waɗancan suna jirana nan suka jani suka fara aikin su a kaina me gyaran gashi me kwalliya sai da suka ga nayi tsab da ni sannan suka ƙyale ni inda suka ɗauko min wata strapless armani gown na saka daa ganin rigar nan taci kuɗi nan na kalli kaina kamar wata tauraruwa haka na ganni na yi kyau sosai murmushi wanda ya kara min kyau sosai
jagora sukai min zuwa dining room don inyi breakfast sai lkcn na tuna ko break fast ban ba abinci aka shiga jera min kamar abin arziki na kai hannu zan buɗe kenan sai matar da ta karɓe ni tun bayan shigowata wato linda kenan naji ta doke min hannu da bulalar da ke hannun ta *auch* nace na juya na kalle ta tare da zubɓuro mata baki
sawa tayi ƴammatan da ke wajen suyi serving ɗina breakfast ikon Allah, wato ba wani abin arziki a cikin abin,
fruits ne kala kala akai masu wani irin decoration me kyau shi aka fara turo min, hannu na daga zan ɗauka nan ma naji bulalar Linda ƙwal a hannuna *auch* njena faɗa da ƙarfi tare da sosa wajen fork ta nuna min na ɗauka sama sama naci fruit ɗin don ni yunwa kawai nake ji ba kwaɗayi ba
ko
da na ture sai aka kawo min main breakfast ɗina aikin banza na faɗa araina ƙwai ne guda ɗaya jal aka soya wanda ba a kaɗa ba don kana iya ganin ƙwaduwar a tsakiyar sa, sai fatan wake shima baifi cokali biyu ba sai kuma, timatir wanda aka akayi slicing ɗinshi sa bread slice ɗaya, sai tea rabin kofin tangaran
kallan abincin nayi wanna idan na daddage gabaki ɗayan abincin zan kwaso su in musu loma ɗaya a lkc ɗaya amma wai shine breakfast kallan linda nayi inda tayi min nuni da fork nd knife tooo faaa yau ake yin ta wa ya iya cin wai abinci da fork da wuƙa
ɗauka nayi na fara ci bazan dai faɗa muku yanda na ci abincin ba amma na sha bulala ya fi a ƙirga ina gamawa aka kawo min soup na sha shi wannan bashi da matsala don da spoon kawai na sha bayan na gama ne tasa wasu ƴammata suma na daban su fita da ni nasha iska aikin banza mutun be ƙoshi ba amma an sa shi zagayawar dole tashi nayi na bisu ko ba komai na ga guri
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page: 9🌹
Mun sha zagaye sosai a cikin gidan inda ƙara ganin girman gidan, tanƙameme ne sosai garden suka kaini inda ya sha shuke shuke masu ƙayatarwa launi daban daban masu kyau da ƙamshi
ga table da kujerun sa daga gefe na zama sai swimming pool wanda kusan guda uku ne kowanne da shape ɗin da aka yi masa, can daga gefe kuma wani fountain ne da akayi masa shape ɗin tukunyar ƙasa inda ta saman ta ke zubar da ruwa cikin ta ƙasan, gurin yai kyau sosai
wuri na samu na zau a kan grass carpet ɗin daya zagaye ko ina yai kore shar da shi ga shi kuma yai lif lif da shi daga gani yana samun kulawa sosai
fruits aka kawo min da juice sai kuma ruwan roba ga snacks nan abin dai sai kace mutane goma ne zasu don tsabar yawan sa, wanda inda ace hankalin mutun a kwance yake sai kaci iya cin ka amma ya za ayi in zauna in ci bayan ban san dalilina na zuwa gidan na ba
kuka na saka me sauti sosai wanda ya janyo hankalin masu kula da wurin da ƴammatan da suka rako,
"madam do u need anything" naji wata tace
Abin takaici bama Hausawa ya haɗa ni zama da su ba ƙabilu ne, harara na doka mata
"where is ur oga" na faɗa in me shaƙar wuyan rigar ta
shaƙar da tajine yasa ta kakari wanda ya janyo hankalin mutane suka zo agajin ta, ko da aka ƙwace ta daga hannu sai na fara zunduma ihun
"take me to ur oga" shine kawai abinda nake faɗa ina ihu, ƙattin matan nan ne dai suka zo sukai ciki da ni sai ɗakin da aka sauke ni da farko garam naji an rufe ƙofar tare da sa key
zaman daɓaro kawai nayi a ƙasan ɗakin ina ci gaba da rafsar kuka na wanda ban san ranar denawa ba ƙila sai ya mayar da ni gida,
sai 1:30 sannan na tashi na gabatar da sallah azahar ban idar ba naji an buɗe ni linda ce
"is time 4 lunch ma'am" naji tace
kau da kaina nayi lunch ɗin banza da wofi bayan ba lallai bane su bani abinda nasa ci ba, ganin alamar bazan tashi bane yasa ta juyawa ta tafi, haka na zauna banci na rana ba haka ma da dare
wajen ƙarfe takwas da rabi sai sai ga linda
"time 4 ur bath" kallo bata ishe ni ba na ci gaba da kwanciyar da nake akan sallayata,
matsowa tayi kusa da ni kizo kiyi wanka don kiji daɗin bacci kuma acire miki wannan make up ɗin na fuskar ki, tayi ta banbamin ta ta gaji ta fita ta ja min ƙofar, wani sabon kuka na kuma saki a hankali wannan karon ina tunaningurin da nake kwanciya a gida wai yau nice a wannan kayataccen gidan amma sam ban san dalilina na zuwa wannan gidan ba
Ina tunanin na ban san lkcn da wani wahalallaen bacci ya kwashe ni ba, sai ƙarfe goman dare sannan na tashi inda naji cikina kamar an min satar kayan ciki
Gaba na ne ya bada dam kar dai mutanen sun kwashe min kayan ciki ne na faɗa ina yamutsa cikin, alamar yunwa naji atattare da cikin wanda hakan yasa na tuna cewar na daɗe rabona da abinci tun wanda na ɗan tsakura da safe
Sakkowa nayi daga gadon na murɗa kofar ɗakin inda na same ta a buɗe, buɗewa nayi na shiga ɗan corridor ɗin da zada ka da falon na tarar da falon nayi dining room ɗin, dining table ɗin tsap yake an goge shi kamar ba a taɓa cin abinci akan sa ba
kitchen ɗin na shige shima a gyare yake na samu wuri na tsaya ina kallon ikon Allah tun da nake ko a film ban taɓa gani tsaruwar kitchen irin wannan ba, shi kanshi gas ɗin saman shi glass ne ba bu wurin sa ashana tsayawa nayi ina ƙarewa gas ɗin kallo
*maxi flameless cooker* naga an rubuta wannan ya tabbatar min da irin gas din nan ne da ba a ganin wuta sai da kawai aita girki, danne danne na nayi tayi a jikin wurin da naga kamar nan ne wuri opperating ɗin gas ɗin har Allah ya taimake ni na kunna
Tukunya na ɗauko na ɗaura ruwa na dafa indomie ta wadda na gani a cikin store ɗin wanda don girman sa da kuma kayan abincin da ke ciki kai sai ka ɗauka wani kanti ne a singa
ina gamawa na kashe sannan na sauke tukunyata a ƙasa na zauna na daki abata juice na duba fridge na ɗauka na share na gode wa Allah, na koma store nayi guzurin snacks ɗina na ciki leda da cake na zuba aleda na kama hanyar ɗakina na adana kayana na kwanta sai bacci.
**********
Lagos
tun bayan da motocin da suka zo suka yi masa awon gaba da ƴarsa ya doka wa ƴen uwanta kira suka zo, haka aka taru ana ta jajanta masa inda in banda kuka ba abinda baba yake yi, su khadija da maryam ma kukan kawai suke yi
har wurin sakin hausawan lagos akaje amma babu abinda da zai iya yi musu kasncewar ba a san wanda yazo ya sace tan ba
haka suka dawo gida jiki a sanyaye suna mai roƙon Allah ya bayyana ta amma abin da mamaki har cikkn mutane azo a ɗauke maka ƴa Allah ya kyauta, masu faɗan alkhairi nayi masu faɗan sharri nayi don wasu har cewa sukai wai matar ajaban ce ta sa a sace ta
*************
*ajaban resident*
Yana zaune ya gama kallon ta ta camerar dake kitchen ɗin yadda ta dafa indomie ɗin, tun da linda tayi masa waya akn taƙi cin abinci sai yaji ba daɗi a ransa, ya kunna security cam ɗin dake ɗakin ta yana ƙare mata kallo da nazarinta daga ganinta tana jin yunwa dakiya ce kawai irin tata, sai kuma yaga ta tashi ya ɗauka guduwa zata yi sai yaga ta nufi kitchen wannan yasa ran shi nutsuwa wato yunwa take ji kenan,
ta camerar yake kallon yadda take cin indomie ɗin tata kamar tana cin wata duniya shi baiga meye abin daɗi a indomie ba abincin yara ko dayaga taje ta kwanta
bawai na kawo ki bane don in takura k na kawo ki ne don in tserar da ke daga sharrin mutane da wannan haniyar ta hotunan ta kwanta zan maida ke gaban iyayenki ya faɗa yana mai ƙare mata kallo, da sauri ya kashe don shaiɗan har ya fara masa kiɗa a kan sa
************
ko da safe da suka gayyace ta wanka bata ƙiba don tanasan matsan nan da ake mata a jikin ta, ta shiga akai mata wankan ta shirya da taimakon su amma da aka gayace ta cin abinci sai tace ta ƙoshi, babu yadda linda batayi ba daga ƙarshe da ta dameni ma sai na juya mata baya
"sai oganku yazo ya maidani gida sannan zanci abinci" na faɗa
ba yadda ta iya haka ta juya ta tafi tana fita na bita na kulle ƙofar leda ta naɗauko na zauna naci abuna na ƙoshi naje banɗaki na ɗaɗɗaki ruwana na gyara wajen na koma na kwanta
duka abinda yake faruwa akan idon sa da ƙin cin abincin nata da tace wa linda da cin snacks ɗin nata tana lumshe ido abinma sai ya dinga bashi dariya wai ita jaruma
ko daya fito zai tafi office ma'aikatan gidan suna ta kwasar gaisuwa yana ansa musu da fara'ar sa, aguje ya ga linda ta taho
"sir tun jiya madam bata ci abinci ba at dis moment zata iya suma fa" ta faɗa hanklinta a tashe
"dont worry linda ba abinda zai same ta"
tsayawa tayi tana kallon uban gidan nasu tasan mutun ne me tausayi amma ga mamakin ta wai yace a kyale wannan da mamaki har ya shiga mota sai taga yana kiran ta ƙarasawa tayi
"daga yanzu a dinga yin snacks different veriaties ana ajiyewa a kitchen musammamn da daddɗe bana son inga kitchen ɗin nan babu snacks da daddare kinji ni ko" ya faaɗa yana jan kunne sa gyaɗa kanta tayi alamar ta fahimta yana murmushi yace wa driver lets go
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
I dedicate dis page to u all
Page:10🌹
Yau kwana na goma sha biyu a gidan, har yanzu ina nan kan baka na na bazan ci abinci ba sai an mai dani gida, linda kullun idan ta shigo ɗakina sai tayi kamar za tai kuka don tausaya min inda ni kuma zaki ganni ina langwaɓewa ina ƴen nufarfashi ni ban yadda ba yunwa tana galabaitar dani
Ban fasa shiga kitchen ba kullum da daddare sai naje na ɗebo abinda zanci, sannan in dafa indomie ta Allah bai taɓa sa wata ma'aikaciya ta kama ni ba,
kwance nake akan gado, linda ce a gefe na tana ban bakin akan in haƙura in fara cin abincin, ni kuma si wani botsarewa nake yi,
"ni fa sai ya mai dani gida" na faɗa a shagwaɓe
"ya za ayi ya maida ke gida ba kya jin maganar sa, sir bazai taɓa cutar da ke ba akwai dalilin sa na kawo gidan nan, kuma da yaga condition is ok zai mai da ke, just trust me"
"how can i trust u wen i don't even know u" na juyo ina kallon, shiru tayi
"ok just have faith dat he wil never harm u" shiru nayi kawai na rasa abinda zance, ganon nayi shirun ne yasata ci gaba da lallashina, ni ma kuma on d other hand ina buƙatar lallashin don na gaji da cin indomie da daddare da snacks ɗin da nake ci da safe da rana kawai basarwa nake yi da jan class
Sai da na jaaa aji na sannan na ce mata na haƙura, murmushine fal fuskar ta
"nasan sir will be very happy, let me set d table i will be right back" tashi tayi ta fita
Ko da ta gama tazo ta kira naje to my surprise tuwon dawa na samu tare da miyar ewedu sai dage dage, ai kuwa na zauna na daki abuna ohhhh yaushe rabon duniya da ayyaraye, ko da na gama ranar har zagaye gidan nayi ba kamar da ba da nake akulle kullum
**********
*kano*
hjy ce a kwance a gadon asibiti daga ganinta tana jin jiki sosai,
"sannu hjy" inji aliyu ajaban, juyowa tayi ta kalle shi da mamaki don bata san ya zo, harara ta jefa wa tj wanda yake kusa da aliyun tasan shi zai gaya masa bata da lfy shi da yace kar a faɗa masa
"me likitocin sukace" ya tambayi tj, kanshi a ƙasa
"da sauƙi"
"da sauƙi magana ce meke damunta"
"ciwon kai ne kawai" ya faɗa yana sosai ƙeya
ya buɗe bakinsa zaiyi magana sai hjyr ta katse shi
"yaushe kazo" Juyowa yayi ganin tayi masa magana
"da la'asar ya jikin naki, muna miki processing visa sai mu fita da ke a duba ki sosai"
"hmm aliyu kenan ni dai da zaka min abu ɗaya da nafi son shi akan fita wajen nan, tun da wannan ciwon ba lallai bane in tashi ba"
"hjy me kike so ki faɗa ko a ina ake siyarwa zan siyo miki don Allah hjy ki faɗa" ya faɗa da ƙwalla taf idon sa saboda tausayin baiwar Allah da yake ji ita ce komai nashi yau idan akace ba ita ya zaiyi
"kayi aure aliyu naah, tunda yanzu ka samu wadda kaga tayi ma duk da dai banganta ba amma nasan zatayi hali na gari" zuƙar iska yayi tare da fesar da ita da ƙarfin lallai hjy kin kawo babban zancen, in akwai abin da aliyu ajaban ya tsana bai wuce ace mai yayi aure
"kar ka damu aliyu nidai kawai alfarmar da nake so kaimin ke nan kafin in mutu inga auren ka" tare suka fashe mata da kuka shida tj wai ta daina faɗan hakan
"hjy duk abinda kike so za a yi, zan sa aje a tambayo yaushe kike son ayi bikin"
"ran jumma'a ta sama,"
"an gama hjy Allah ya kaimu"
"yauwa ɗan albarka Allah yai ma albarka da kai da zuri'ar ka" addu'a tai masa sosai shida tj ɗin sannan ta bisu da nasiha mai sanyaya jiki
"zansa ayiwa su mlm magana sai muga yadda za ayi ko" to anan gizon yake saƙar don idan akwai abin da aliyu ya tsana a rayuwar sa to bai wuce yaji an anbaci *dangin sa* ranshi yakan ɓaci zuciyar shi tai mai kunci, amma ya zai yi hjy ce ba yadda zai yi da ita
"shike nan ka tafi kawai duk yadda mukayi da su mlm ɗin kaji a wajen tijjani" ta faɗa, to kawai ya iyace mata ko sallama kasa yi mata yayi don idan ya buɗe bakinsa sai ya ji wani ƙululun baƙin cikine a maƙogoronsa wanda yake hana shi maganar, itama fahimtar yananin da ya shiga ne adalilin ambaton *dangin sa* da tayi ne ya sa bata kuma ce masa komai ba har ya bace,
tj ne ya rako shi har gurin parking space, shima ba abinda yace masa kawai shiga motar sa yayi yai gaba a guje
"Allah ya sauke ka lfy ɗan uwana" ya firta a fili🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
I dedicate dis page to u all
Page:10🌹
Yau kwana na goma sha biyu a gidan, har yanzu ina nan kan baka na na bazan ci abinci ba sai an mai dani gida, linda kullun idan ta shigo ɗakina sai tayi kamar za tai kuka don tausaya min inda ni kuma zaki ganni ina langwaɓewa ina ƴen nufarfashi ni ban yadda ba yunwa tana galabaitar dani
Ban fasa shiga kitchen ba kullum da daddare sai naje na ɗebo abinda zanci, sannan in dafa indomie ta Allah bai taɓa sa wata ma'aikaciya ta kama ni ba,
kwance nake akan gado, linda ce a gefe na tana ban bakin akan in haƙura in fara cin abincin, ni kuma si wani botsarewa nake yi,
"ni fa sai ya mai dani gida" na faɗa a shagwaɓe
"ya za ayi ya maida ke gida ba kya jin maganar sa, sir bazai taɓa cutar da ke ba akwai dalilin sa na kawo gidan nan, kuma da yaga condition is ok zai mai da ke, just trust me"
"how can i trust u wen i don't even know u" na juyo ina kallon, shiru tayi
"ok just have faith dat he wil never harm u" shiru nayi kawai na rasa abinda zance, ganon nayi shirun ne yasata ci gaba da lallashina, ni ma kuma on d other hand ina buƙatar lallashin don na gaji da cin indomie da daddare da snacks ɗin da nake ci da safe da rana kawai basarwa nake yi da jan class
Sai da na jaaa aji na sannan na ce mata na haƙura, murmushine fal fuskar ta
"nasan sir will be very happy, let me set d table i will be right back" tashi tayi ta fita
Ko da ta gama tazo ta kira naje to my surprise tuwon dawa na samu tare da miyar ewedu sai dage dage, ai kuwa na zauna na daki abuna ohhhh yaushe rabon duniya da ayyaraye, ko da na gama ranar har zagaye gidan nayi ba kamar da ba da nake akulle kullum
**********
*kano*
hjy ce a kwance a gadon asibiti daga ganinta tana jin jiki sosai,
"sannu hjy" inji aliyu ajaban, juyowa tayi ta kalle shi da mamaki don bata san ya zo, harara ta jefa wa tj wanda yake kusa da aliyun tasan shi zai gaya masa bata da lfy shi da yace kar a faɗa masa
"me likitocin sukace" ya tambayi tj, kanshi a ƙasa
"da sauƙi"
"da sauƙi magana ce meke damunta"
"ciwon kai ne kawai" ya faɗa yana sosai ƙeya
ya buɗe bakinsa zaiyi magana sai hjyr ta katse shi
"yaushe kazo" Juyowa yayi ganin tayi masa magana
"da la'asar ya jikin naki, muna miki processing visa sai mu fita da ke a duba ki sosai"
"hmm aliyu kenan ni dai da zaka min abu ɗaya da nafi son shi akan fita wajen nan, tun da wannan ciwon ba lallai bane in tashi ba"
"hjy me kike so ki faɗa ko a ina ake siyarwa zan siyo miki don Allah hjy ki faɗa" ya faɗa da ƙwalla taf idon sa saboda tausayin baiwar Allah da yake ji ita ce komai nashi yau idan akace ba ita ya zaiyi
"kayi aure aliyu naah, tunda yanzu ka samu wadda kaga tayi ma duk da dai banganta ba amma nasan zatayi hali na gari" zuƙar iska yayi tare da fesar da ita da ƙarfin lallai hjy kin kawo babban zancen, in akwai abin da aliyu ajaban ya tsana bai wuce ace mai yayi aure
"kar ka damu aliyu nidai kawai alfarmar da nake so kaimin ke nan kafin in mutu inga auren ka" tare suka fashe mata da kuka shida tj wai ta daina faɗan hakan
"hjy duk abinda kike so za a yi, zan sa aje a tambayo yaushe kike son ayi bikin"
"ran jumma'a ta sama,"
"an gama hjy Allah ya kaimu"
"yauwa ɗan albarka Allah yai ma albarka da kai da zuri'ar ka" addu'a tai masa sosai shida tj ɗin sannan ta bisu da nasiha mai sanyaya jiki
"zansa ayiwa su mlm magana sai muga yadda za ayi ko" to anan gizon yake saƙar don idan akwai abin da aliyu ya tsana a rayuwar sa to bai wuce yaji an anbaci *dangin sa* ranshi yakan ɓaci zuciyar shi tai mai kunci, amma ya zai yi hjy ce ba yadda zai yi da ita
"shike nan ka tafi kawai duk yadda mukayi da su mlm ɗin kaji a wajen tijjani" ta faɗa, to kawai ya iyace mata ko sallama kasa yi mata yayi don idan ya buɗe bakinsa sai ya ji wani ƙululun baƙin cikine a maƙogoronsa wanda yake hana shi maganar, itama fahimtar yananin da ya shiga ne adalilin ambaton *dangin sa* da tayi ne ya sa bata kuma ce masa komai ba har ya bace,
tj ne ya rako shi har gurin parking space, shima ba abinda yace masa kawai shiga motar sa yayi yai gaba a guje
"Allah ya sauke ka lfy ɗan uwana" ya firta a fili
sai dare sannan yaji zai iya magana, ɗauko wayar sa yayi ya kira tj akan ya same shi a hotel ɗin daya saba sauka, ba a wani ɓata lkc ba sai ga tj nan ya zo sai bayan da suka ƙara gaggaisawa ne sannan suka shiga abinda ya haɗa sun
aliyu ne yai wa tj bayanin halin da ake ciki na sace zainab ɗin da yayi, tj yai mamaki sosai amma kuma sai be ce komai ba don yasan halin ɗan uwan nasa
"to yanzu yaushe zaku lagos ɗin" inji aliyu
" gobe zan tafi in shaa Allah don dole zanje in samu ɗan uwan hjy dake agegen mu samu mu gyara wannan ɓaran ɓaramar da ka tafka"
harara aliyun ya bishi da shi, amma kuma yasan maganar tj gaskiyace, don haka sai bece komai ba
"ka zaɓi gida guda a cikin gidajena na agegen a bashi don bana son aje neman min auren mata a inda suke a raina ni" ba ce komai ba suka ci gaba da tattaunawar yadda bikin zai kasance daga ƙarshe sukayi sallama akan sai tj ɗin ya dawo zai kira shi yai masa bayanin yadda ta kaya
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Huguma grp 😘
Safiya huguma congrats on your completely ur amazing novel *da'iman* I hope u r going to blast us with yet another jzk sis
0 comments:
Post a Comment