Page :11🌹
*Lagos*
Ko da tj ya je lagos direct gidan ɗan uwan hjyr ya wuce daga na suka wuce sai gidan su zainab da taimakon kwatancen drivern sa,
Sun samu baba sun masa bayanin kansu, kasancewar akwai ƴar sanayya tsakanin ɗan uwan hjyn wato alh idris da baba yasa ba su wani kai ruwa rana sosai ba suka shawo kansa
"to wai ma don me yasa aka sacen ta shine ban sani ba kuma nake neman ƙarin bayani"
"wato shi yaron nan da ka ga hoton su tare da ita babban mutum ne, to kasan duk manyan mutane dole ne bazasu rasa maƙiya ba, don haka duk wanda yake tare da ajaban dole a bashi tsaro na musamman barin ma da akace matar sa to wallahi za a iya halaka ta, gaji dalilin sa na ɗauke don ya kare ta daga halaka, don an taɓa kwatanta haka wata yarinya ta fito tace wai ita zai aure Allah yarinyar nan sai gawar ta, to gudun kar hakan ta sake faruwa yasa shi aikata hakan"
jikin baba sai yai sanyi
"amma duk da haka da sai yayi bayani ba ba wai yazo da dakarai ba ya sace min ƴa"
"ƙuruciya fa" inji alh idris
ran baba ya ɓaci sosai ace sai da ƴar sa ta kwana sha huɗu sannan akazo aka ce masa wai don tsaron ta aka sace ta, ranshi ya ɓaci sosai daga baya dai ya sauko kuma ganin irin bada haƙurin da suke yi
Sai bayan da baba ya sauko ne sannan suka gabatar masa da zancen auren nata da za a zo a ɗaura ran jumma'a me zuwa inda hali, nan ma baba sai da ya ɗan yi ɗan karamin hauka kana daga baya ya sauko ya fahimtar da su shi bai tanadi komai na aure ba, inda suka shaida masa basa buƙatar komai su za suyi komai har abinda za a ci da bikin,
"to ai shikenan ita zainab ɗin yaushe zata dawo"sosa kai tj yayi
"ai baba sai nan da wata uku in shaa zaka ganta kafin nan komai ya lafa"
"meeeeeyeeee ƴar tawa sam ban yadda ba na sanima ko siyar min da ita kuka yi wannan zamanin da ba gaskiya" wannan karon alh idris ne yayi magana
"haba haba haba shi in baka san shi ba ni ai kasan ni ka san gidana ka san komai nawa na ɗauka har ƴar ka ce take auren ɗan aminina (maryam), ya za ayi kace zamu sai da maka da ƴa, wallahi da alkhairi muka zo ba sharri" sai da yayi baba dogon turanci na lallami da ban baki sannan baba ya sauko ganin cewar ko savce tan zasu yi a yanzu dai yasan wanda zai bi don fara binciken inda yar tasa take
"to shike nan Allah ya shige mana gaba" gabaɗayan su suaka ansa da amin , tj ne ya gabatar masa da gidan nan ma baba ƙin karɓa yayi sai da ƙh idris yasa baki sannan ya karɓa, sun masa bayanin cewar suna son ayi bikin a gidan, inda angon zai gyara musu gidan su tare kafin jumma'ar
Bayan doguwar shawara an tsai ds tarewar su ranar laraba ana jibi ɗaurin aure,suka buƙaci baba da yazo aje aje ganin gida wani maƙocin sa ne ya rakashi don ganin gidan wanda ya kasance a unguwar daji dake agegen
Four bedroom Duplex ne gidan, yai kyau sosai sai dai ɗan alamar an daɗe ba kowa a ciki amma da ya ɗan sha kwaskwarima zai fito fes da shi, sun zazzaga cikin gidan daga bisani suka dawo da su baba gida tare da yi masa alƙawarin zuwa kashegari don akai shi ya zaɓi irin kayan da yake so ai mai gyaran gidan da shi
ko da baba ya koma gida yai mama bayani da farko ta ɗauka wasa yake yi sai da taga takardun gidan nan fa hankalinta ya tashi wai ita ce zasu koma gidan kansu a unguwar daji ma, mama ranar kwana tayi batai bacci ba burin ta gari ya waye ta je gidan ta gani sannan ta fesa wa ƙawayen ta masu zama a fƙat suna mata kallon matsiyaciya, ko misƙaƙa zarratin bata damu da abinda zainab ɗin baban yace ta shiga ba ita kawai taje gidan ta gani
kashegaɗi baba ne ya kira su maryam suma suka zo aka sake ɗora zancen daga farko, gaskiya hankalkn sj ya tashi sƙsai barkn ma da suka ji maganar gidan shike nan baba ya sai da yaya
ko da baban yai musu bayanin wanda ya zo da zancen sai hankalin su ya kwanta don sun san alh idris kuma sun san halin sa
sun je sun ga gida mama ce ta zaɓi irin furnitures ɗin da za a gidan sannan tj ya sallami baba ta ɓangaren kayan abinci da kuma ƴen hidomomin bikin, store ɗin su taf aka cika musu da shi, nan suka shiga hidimar bikin ƴar sa zainab sai dai muce Allah ya kaimu
*abuja*
*ajaban recidence*
yana zaune yana tunanin wai gobe za a ɗaura masa aure da wata shi a rayuwar sa bai taɓa kawowa wai zaiyi aure saboda fassara mata da yayi akan basu da tausayi da imani a ziciyar su, a kullum idan ya tuna ƙuruciyarsa sai yace to me zanyi da mace a rayuwata amma yanzu gashi hjy tai masa shigar sauri matar da baya iya musu da ita ta haɗa shida aure, ko yama za ayi auren da shi oho
tashi yayi ya ƙarasa haɗa kayan sa da zai sa a cikin ƴar trolley ɗin tasa ɗinki da tj ya kawo masa ya ɗauka yana Allah sarki ya za ayi in iya rayuwa ba kai, shi sam ma ya manta wai ango sabon kaya yake sawa da badan tj ya ɗinka masa ba da saidai yaji kunya
kwanciya yai da safe yana da flight don ma sai goma zasu zo kasancewar yace a bar sabon private plane ɗin nasa a kano idan ya ɗauko tj sai su zo su kwashi shi, tsohon kuma a ɗauko ƴen ɗaurin aure, kwanciya yayi don bayasa ya makara
ina can akwance bansan wai nar da ake toyawa a kaina ba, nima bayan na gama komai na na kwata saba'ul khair
***********
*lagos*
ranar lahadi da ƙarfe da ƙara sha biyu dai dai aka ɗaura aure wanda ya tara dubban mutane daga ko'ina naɗin duniya, duk abokanan ajaban ne, shagali aka sha sosai ba ga ɓangaren amarya ba baga na ango don tj be ɗauki auren ɗan uwansa da wasa ba, reception ya haɗa musu sosai na gani na faɗa wanda sukayi bayan ɗauri auren acikin garin lagos,
a ɓangaren mama ita ma ba sauƙi a lamarin nata duk da guturi tsomar da akeyi akan anyi aure ba amarya wannan bai hana mama haɗa gagarimin yinin ta ba don itama ace ta faso
ɓangaren ƙannena ma hankalin su akwance suka gudanar da sha'anin bikin kasanceqar alh idris ya kira su ya kuma yi musu bayanin dalilin ɓoye nin da aka yi kuma sun gamsu sosai. ko da daee yayi babu batun kai amarya don haka sai kowacce mace ta kama hanyar inda ta fito mudai sai dai muce Allah ya bada zaman lfy
***************
yana kwance akan gadon ɗakin da ya kama a hotel yana hutawa yana hutawa bazai iya komawa abj ba yau don a ajiye yake tiƙis, bayan duk sun sallami ƴen ɗauren auren da suka zo da badan tj ba da baisan ya zaiyi da mutane ba don wasu ma bai gayyace su bai ma san inda suka samu lbrn auren nasa ba ya manta cewar he is d famous *ajaban*
bugun ƙofar ɗakin yaji kamar za a ɓalla a hotel ɗin ake irin wannan bugun ya faɗa ranshi a ɓace don har ya fara bacci, a gajiye ya sauko ya buɗe yai mamakin ganin tj ne, kuka tj yakeyi sosai kamar ƙaramin yaro, girgiza tj ɗin yayi tare da tambayarsa lfy
"hjy ce Allah yai mata rasuwa yanzu nan"
shiru aliyun yayi duk wani service ɗin shi ya ɗauke
"wace hjyr" ya tambaya idon nan nasa yai ja jijiyoyin jikin sa sun tashi fuskar sa ma tai jajawur
"hjyr mu ɗan uwa uwar mu kuma kakar mu yau Allah yai mata rasuwa"
"tj kenan da magaribar nan fa sai da mukayi waya da ita tace min jikin nata da saukƙiya zaka kawo min zancen banza wai ta rasu"
Tj ne ya ƙara fashewa da kuka yasan sam dama aliyun bazai taɓa yadda ba in ba gani yayi ko kuma ji, wayar shi ya ɗauka ya kira ƙanwar mahaifinsa wadda itace take jinyar hjy ya sa a speaker, da kukan ta ɗauka
"tijjani ka gaya aliyun kuwa hjyrsa ta rasu " shine kaɗai kalmar da ji don ragowar bai ƙarasa jin zancen ba service ɗinsa gabaɗaya ya ƙarasa ɗaukewa
wai hjyrsa ce ta rasu to shi ya za ayi ya iya rayuwa babu ita matar da duk wani neman sa da faɗi tashin da yake yi don ita ne yanzu da ta mutu ta barshi da wannan uban dukiyar me zai yi da ita wa zai kashewa, wani irin kuka ne me ƙuna ya kwace wa aliyu wannda tunda yake bai taɓa yi irin sa, wayar sa kawai ya ɗauko ya kira pilot ɗin
"prepare d plane we r flying to kano"
"yes sir" inji pilot ɗin
tj ne ma ya iya haɗa musu kayan nasu don shi gogan tuni yai waje yana kuka sosai me ƙona zuciya yana tafiya yana kiran sunan hjy ta bai damu da yadda mutane suke binsa da kallo ba shiɗdai burin sa ya isa yaga ta farfaɗo har suka shiga jirgi ya ɗaga zuwa kano yana kukan sa me sauti tare da tausayi
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Dis page is 4 u mmn farida 😁😁😁
Page :12🌹
Har suka je kano aliyu bai daina kuka ba direct tafkeken gidan sa na sharaɗa uuka wuce inda anan hjyr take zaune tare da tj da matar sa babban gida ne, a cike gidan yake taf ba masaka tsinke don kuwa hjyr ajaban ta rasu, har an mata wanka an haɗa ta an ajiye ta tun da mutuwar dare tayi sai da safe za ayi jana'iza ta,
Mace me mutunci da sanin darajar ɗan adam wai itace yau babu Allah ya jiƙanta, a zaune aliyu ya kwana tare da ƴaƴanta da kuma tj, ba wanda bai tausaya aliyu ba ganin halin daya shiga don ba wanda baisan tsakanin su da hjyr ba,
Kashegari da ƙarfe takwas na safe aka kai wa hjy jana'iza inda mutane suka dinga ɗurowa daga ko ina kamar gayyatar su aka ohhh duniyar nan sai kallo ko da aka binne hjy aƙiyi ne kawai ya tsaya akan kabarin nata da tj bayan kƙwa ya watse ya kasa tafiya wai hjyr sa a nan, ya shafe kusan awa biyu akan kabarkn kafin daga bisani tj ya ja shi da kyar suka koma don tabbas za a dinga zuwa yi musu gaisuwa
Tun a mota aliyu ya ba tj atm card ɗinsa
"gashi a dinga yin cefanen abincin sadakar ba sai an dinga tambaya ba, pls kuma a dinga yin wanda mutane zasu iya ci"
"akwai kuɗi a hannuna ai"harara ya dokawa tj ɗin wanda baisan lkcn da ya karɓa, ya za ayi yace tj ya yi cefanen gidan nan bayan Allah ne kaɗai yasan irin mutanen da zasu dinga zuwa bayan tj ɗin shi yayi hidimar bikinsa tas da kuɗin hatta da lefe shi sai a gidan bikin ma ya gani don ya ma manta da batunsa, kuma ya san a ƴaƴan hjyr babu me cewa zai yi wani abun shi zasu zubawa ido to don me zai ɗaurawa tj ɗin
"kasa a ɗauko masu dafa abinci daga hotel ɗina don tun jiya na kira manager ɗin nace ya ya rufe hoteƙ ɗin saboda masu zuwa daga nesa sai su dinga sauka a can sai su kuma cooks din su dinga yi mana abinci dan nasan mutanena zasu dinga zuwa ban Son a kawo min abinda zanji kunya"
"to wane irin abincin za a dinga fitowa da" tj ya tamabaya
"ko menene ma ban damu ba amma a tabbatar anyishi kala kala"
"tom in shaa Allah"
a cike ƙofar gidan take taf kamar ɗaurin aure ake ba masaka tsinke hango fitowar aliyu daga motar ne yasa mutane suka yuuuu kansa kowa so yake yi yayi masa gaisuwa kuma a san ya zo, ansawa kawai yake yi amma baya ma iya gane komai, wurk ɗaya ya samu ya zauna ya ci gaba da karɓar gaisuwa
zaman makokk akayi wanda sai wanda ya gani abinci ne ake fitowa da shi kamar ba a san darajar kuɗi, kullum sai anyank sa da raguna huɗu banda iyayen kaji
mutane sai cicciɗowa kawai suke yi daga kowane ɓangare taf gidan yake cika har waje gurin zama har kaɗan yake yi, ko da akayi sadakar uku tj ya so ya cire canopies ɗin da aka kafa a wajen gidan amma ganin yawan mutanen da suke zuwa gidan ne daga ance agri ya waye ne yasa aliyu yace a ɓarsu haka aka ci gaba da ciyar da mutane
ran da ta cika kwana shida ana gobe sadakar bakwai aƙiyu ya kira pilot ɗin sa yace masa ya shirya zasu tafi saudiya kashegari da daddare yes sir kawai yace
ranar sadakar bakwai kamar biki akeyi saboda tsabar cika abin har ya bawa tj haushi yawancin su ba mutuwar bace a gabansu ba sudai suci su ƙoshi shikenan, ana sallah isha aliyu yai wa tj sallamar da cewa ya tafi saudiya, aliyun yana tafiya, tj yasa aka kwashe canopies ɗin da tabarmin wurin an tashi daga zaman makoki
kashe gari da sassafe sai ga wasu alarammomi da malun malun ɗin su wai sunyi wa aliyj magana cewar zasu dinga zama suna yiwa hjy addua har sai tayi arba'in, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa tj rai yayi ba tabarmi ya basu suka shinfiɗa a waje aka fara karatu, kafin kace me wurin ya kuma cika ba masaka tsinke wasu ma akan talkalman su suke zaune a cikin rana, ko ƙala baice musu yayi fice warsa
to rana fa ta ke hantsi ya fara duban ludayi alarammomi da ƴen zaman makoki aka fara jin yunwa tun suna sa ran akawo musu har suka ga la'asar tayi ba aɗɗa'am ba alamar sai suka fara zamewa da ɗaya da ɗaya kafin biyar wurin nan kamar anyi shara ba komai ko da tj ya dawo yaga sun watse sai yayi murmushi ba baiyi musu haka ba ana arba'in ɗin ma sai suce sak ta shekara kuma tsab aliyu biye musu zai yi wannan ke nan
**********
*saudiyya*
ko da aka sauke shi direct madina ya je kwanan shi uku sannan ya baro ta don ya samu ya gabatar da ummara, tun daya shigo makka yake hawaye daya tuno zuwan su ummarar su ta ƙarahe shi da hjy, yai ummarar sa sannan ya samu wuri a haramin yai zaman sa ko hotel ma bai bi ta kamawa ba
daga shi rigar jikinsa sai wayar sa sai master card ɗinsa ya taho da shi, a masallaci yake kwana yana ibada tare da kashe wayar sa gabaɗayan ta, shi gani yake yi komai da yake nema na hjyr sa ne kullum ya tashi burin sa ya farantawa hjyrsa wai yau ace bata nan, shi to neman me zai yi gwanda kawai yayi zaman sa anan yai ta ibadar sa har shima tashi ta same shi tunda wacce yake ganin ta yana jin daɗi yana nema dare da rana ba ita to kuma yanzu neman me zai yi don wa zai nema
a cikin haramin yake komai ɗinsa sai dai in yaji rigar da ke jikinsa ta dame shi ne sai ya fita ya samu shagunan da ke jikin haramin ya siya ya canza ya bada sadakar wacce ya cire ɗin, haka ya koma yana rayuwa shi kaɗai har taimakwa ma'aikatan cikin haramin yakeyi idan zasuyi shara ko moping shima yanayi tun basu saba da shi har suka saba da shi sosai suna ganin shi kamar wani ɗan uwansu kasancewar yadda yake shiga cikin su yayi aiki sosai da iya ƙarfin sa ga kyauta da yake musu akai akai wanda hakan ya tabbatar musu da cewar wani babba ne ƙila ko matsala ya samu shine ya gwammaci ya keɓe kanshi har ya manta ba abinda basu kawo amma basu samu ansa ba kasancewar baya magana ko aiki yake yi zaka tsince yi yana tasbihi sa, ga bashi da san jiki ko kaɗan aiki zaka ganshi yana yi ba kama hannun yaro, duk ya canza ya rame sosai ga uban ƙasumba da ya tara afuskar sa wanda hakan ne ya sa kamannin sa suka canza wanda inba ƙwaƙƙwaran sani kayi masa ba sai ya wuce ka wuce baka gane shi ba
***********
*kano*
yau watan aliyu biyu bashi ba labarin sa, ba inda ba aje don duba shi ba amma shiru tj sau biyu yana zuwa saudiya amma baya ganin sa ba irin luxirious hotel ɗin da bai duba ba amma ko mai kama da shi bai gani ba gashi wayoyin sa duk a kashe, dole haka ya haƙura yasa su dinga cigiyarsa ko za a ganshi ko ya zasu iya gane shi yadda ya canza oho
dole ya dawo abj ya ci gaba da kula da dukiyar sa don baza abarta ba mai kula da ita ba, sai yanzu tj ya fahimci irin wahalar da aliyun yakeyi wajen kula da dukiyar nan tasa lallai ba ƙaramar wahala yake sha dukiya ce da inba ido kasa sosai ba sai a barka cikin ta hamma wato an washe ka,
Duk sati sai jiragen aliyu na ruwa manya manya guda ashirin sun fita da baƙin mai cike taf a cikin su zuwa ƙasashen da suke sarar man nijeria, sannan kuma duk satin sai wasu jiragen sun shigo da kaya kafin wasu su tafi wasu sun dawo haka tj yake wannan hidimaɗ sai yanzu ya fahimci dalilin daya sa aliyun ajiye private yau kana wannan garkn gobe kana wancan ba daman hutawa rabon shi da kano tun lkcn da ya fahimci aliyun ya gudun, ko abinci saboda tsabar hidima watarana mantawa yaƙke yi baici ba sai dai in yai yunwa zatai mai illa sannan zai nema
yaje gidan aliyun sau biyu ga zainab ɗin kuma ya yaba da hankalin ta ganin kaɗaicin yana mata yawa ne ya shi ya sai mata waya ko ta dinga gaisawa da ƴen uwanta baisan cewar bata da number kowa ba, ko daya koma yaga yanayin nata dai bai chan ja ba sai ya yanke shawarar ɗauko mata iyalin sa shima kuma on d other hand yana kewar matar tashi don wani lkcn ko lokacin yi mata waya baya samu
ɓangare guda aka gyarawa salma matar tj ɗin a gidan aliyu inda part ɗin ya koma gurin yinin zainab don ba ƙaramin daɗin ganin ƴar uwatar bahaushiya tayiba kuma gata me faran faran da sakin jiki, salma tana da yar ta ɗaya me suna islam sunan hjy taci wato furairat aka saya ana ce mata islam
duk wani ɗawainiya islam zainab ce take yin sa ganin hakan ne yasa salmar ƙara sakin jiki da zainab ɗin kunsan ance me ɗa wawa, tj yajawa salma kunne sosai akan kar ta faɗawa zainab ɗin cewa an ɗaura mata aure da aliyun abin ya bawa salmar mamaki sosai amma kuma da yake macece me kau da kanta akan abinda babu ruwan ta yasa ta ja bakinta tayi gum 😶😶😶
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Dis page is 4 u mmn farida 😎
Hankalin tj ya kwanta sosai ganin cewar yanzu zainab ɗin hankalin ta ya kwanta, amma duk da haka kullum sai yayi tunanin in ɗan uwan nasa ya shiga, wannan abun yakan damu tj sosai da sosai
Ita ma zainab ɗin yanzu ta saki jikin ta fiye da daa, ganin salmar a gidan, ga kuma islam da koman ta zainab ɗin ce itama yarinyar hankalin ta ya kwanta sosai da zainab ɗin don in ba yunwa take ji bata damu da mmn ta ba
*************
*saudiyya*
Yau da wuri ya tashi ya fara share sharen na cikin masallacin tare da ma'aikantan inda yawan su suna yin aikin ne suna surutu saɓa'in shi daya duƙufa yana yi yana tasbihin sa gaba ɗaya yau baya jin daɗin jikin nasa, don haka ya gama ya nemi wuri da ba mutane sosai ya kwanta don ya huta don through out jiya baiyi bacci ba kasanceqar kwana da yayi yana ibada
ya kwanta kenan ya fara sai yayi mafarkin hjy, tana zaune ta sha kwalliya da wasu fararen kaya sai sheƙi taki yi tai kyua sosai sai murmushi take yi ga yara nan a gaban ta suna zuwa ɗaya bayan ɗaya tana shafa musu kai,
Da sauri sa ya ƙarasa wajen ta ya tsugunna da nufi shima ta shafa mai kan nasa amma ga mamakin sa si yag ta miƙe ta bar wajen,
binta yayi yana kira hjy hjy, juyowa tayi duk fara'ar dake fuskar nan tata babu ita jikin shi ne yai sanyi, ya ƙarasa gaban ta
"hjy kin tafi kin banni bayan in mutuƙar buƙatar ki a tattare da ni, kin barni ni kadai a cinkin wannan duniyar me cike da ƙunci da ƙyashi, kuma gashi yanzu na gani ina murna amma kuma kin juya min baya" ya faɗa yana ƙare zancen sa da kuka
kamar baza tayi magana ba amma kuma sai tace masa
"aliyu baka godewa ba" a tsorace ya ɗago ido yana kallan ta
"kafin Allah ya ɗauke maka ni ba yabaka wdda zata maye ma gurbi na, amma kayi facali da kyautar da Allah yayi maka ka watsar ka gudu daga ni'imar ubangiji tayaya zakayi tsammanin zan tsaya kula, kaji tsoran Allah aliyu yarinyar amana ce a wajen ka Allah ya baka, ka riƙe ta da kyau don Allah ka ji" ta ƙarashe zancen nata da sigar lallashi
jikin shi ne yayi sanyi sosai
"ka shirya ka koma ga iyalin ka da ƴen uwan da kuma mutanen da suke ci da kansu da iyalen su ta dalilin ka kaji aliyu na" ta faɗa tana me shafa masa kansa
kansa yana ƙasa kuka kawai yake yi yana gunji, girgiza yaji ana yi
"ya akhi ya akhi maa ha dathaa"
buɗe idon sa yayi yaga wani balarabe yana tambayarsa
tashi yayi zaune jikin sa yana rawa
"maa yusibuk" Ya kuma jeho masa tambaya, be kula shi yaci gaba da kukan da yarasa dalilin yin sa kuma ya kasa dainawa
"laaa tabki, ya akh, sa a tika bil ma'a"
ya faɗa yana miƙe wa tare da nufar coolers ɗin da ake ajiye ruwa na cikin harami, ruwan ya ɗebo ya kawo masa
"kuz wash rab" ya faɗa yana miƙa masa ruwa, karɓa aliyu yayi fara sha, sai daya shanye ɗan ƙaramin kofin nan tas sannan ya ajiye
"iɗɗaje was tareh" ya faɗa, kwanciya yayi kamar yadda balaraben ya faɗa masa, ganin haka yasa balaraben tafiya
ko da ya ga balaraben ya tafi sai ya fara tunani mafarkin hjyr da yayi nan wani sbon kuka ya kuma kwace masa mara sauti,
ganin kwanciyar bazata yi masa bba ya sashi tashi ya fara ɗawafi yana yi yana kuka yana roƙon gafarar ubangiji tare da yiwa hjy addua, sai da ya gama yaje yayi sallah raka' biyu wacce ake bayan anyi ɗawafi a bayan maƙaman Ibrahim yaje ya sha zam zam sannan yaji ɗan sanyi aransa
zuwa yayi gurin ma'aikatan da yake taya su aiki, sallama sosai yayi musu akan zai koma garin su, sosai sunji ba daɗi a ransu ganin yadda yake taimaka musu sosai ba kaɗan baamma kuma ya zasu yi dama ɗabi'ar baƙo ce in yazo wataran dole ya tafi
direct air port ɗin jidda ya nufa siyan ticket yayi kuma yai sa a jirgin da zashi nigeria zai tashi a daren amma kano zai sauka, bai damu ba shi dai burin sa ya ganshi a nijeria
rabon da aliyu ya shiga commercial flight har ya manta, don haka sai da samu taimakon flight attendance ɗin sannan ya samu wurin zaman sa kasancewar vip tickets ɗin an siyar sai commercial sit, a takure yai wannan tafiyar har aka iso nigeria bai sake ba, da asubar fari jirgin nasu ya dira a ƙasar mu wato nigeria
ko da aka sauka naija directly ya wuce wurin siyan domestic flight tickets ya yanki ticket ɗin zuwa birnin tarayya amma wannan karon ya samu vip sit ɗin
a flight ɗin har wani bacci wahala yayi kafin su ƙarasa abj ɗin
**********
*abuja*
Ko suka sauka directly ya wuce office safiya don haka yace bari ya fara biyawa office ɗin yaga abinda yake ciki kafin ya wuce gida, taxi ya tara don ta kai shi office ɗin, a get ɗin office ɗin nasu sukayi parking ya fito,
"bari in karɓo ma kuɗin ka"ya faɗawa ɗan taxi ɗin, bai jira ansaba ya nufi get ɗin kanshi tsaye ya ƙwanƙwasa, me gadin ne ya zo ya buɗe, ganin mutum da ƙasumba ya sa shi tsayawa yana ƙare masa kallo
"malam inuwa ya aiki"mutumin da kira da mlm inuwan ya tsaya yana kallon wannan baƙo me ƙasunbar da har ya san sunan sa
"don Allah ko kana da 2000 in biya me taxi ɗin nan idan na shiga sai in baka"mlm inuwa bai ce komai ba don shi gani yakeyi ma me ƙasunbar nan ya rai na shi wai ya bashi kuɗi
" mlm ina ganin ɓatan hanya kayi don ni ban san ka ba" murmushi aliyun yayi
"mlm inuwa nine fa yallaɓai" ya faɗa yana murmushin da ba'a iya ganin lebɓansa na sama saboda tsabar gashin da ya rufe su
kallon sama da ƙasa yayi masa, sannan ya mai da get ɗin garam ya rufe, don ma ya raina min wayo zaice wani yallaɓai ne yallaɓan da kayan sa kullum tsab tsab suke a goge yana tashin ƙamshin turare amma shi wannan yazo da wata doguwar rigarsa da ta yamutse sai ya sha kokawa ga wani uban ƙasunba da ya tara, zaice min wani wai yallabai ne ko da dai daga ƙauye na zo ai ba dabba bane ni ko a cikkn mutane million naga yallaɓai zan gane shi ya faɗa yana mita
kada aliyun yaga abinda me gadin yayi sai kawai ya juya gurin me taxi ɗin
"mlm mu je atm ɗin da ke kusa in baka kuɗin ka" haka kuwa sukayi ya zari kuɗi a atm machine ya biya sannan ya kama hanyar favourite restuarant ɗinsa yaci ya ƙoshi sannan ya koma office ɗin, samun wuri yayi yazauna yana kallon ikon Allah har lkncn da Allah ya kawo tj a mota
ya gane motar tj tun lkcn da ta karyo layin don haka sai yaje ya tare shi a ƙofar get ɗin, tj be ankara ba kawai sai ganin mutum yayi a gaban motarsa kamar an jehoshi daga sama ga uban ƙasum ba ya tara da sauri ya taka birki ya fito ranshi a ɓace
"mlm lfy kazo ka sha min gaba na ina cikin tafiya idan da na taka ka fa
"ba sai kayi jinyata ba dan ubanka" ya maida masa a zolaye
kai tsaya wannan muryar bata aliyu bace ya faɗa a ransa, ƙarasawa yayi kusa da me ƙasunbar nan ya ƙare masa kallon lallai ba shakka ɗan uwansa ne, rungume shi yayi ya samasa kuka shima aliyun kuka ne ƙwace masa
sai da sukayi me isar su sannan ya sake shi
"ɗan uwa ashe zaka ƙara gudu ka barni ba kayi min alƙawarin baza ka ƙara tafiya ka barni ba" haƙuri aliyu kawai yake ba tj ɗin don yasan ya bata masa rai ba kaɗan ba
"mu shiga daga ciki ɗan uwa kowa yasan ka dawo"
"mlm inuwa kuwa zai barni in shiga don ɗazu na zo ya kore ni" dariya tj ɗin yayi zo muje sai ka ƙara gabatar masa da kanka
ko da suka je mlm inuwa yai mamakin da tj yace masa yallaɓai ne, sai haƙuri ya din ga ba aliyun , ko acikkn office ɗin ma ma'aikatan office ɗin sun yi murna sannan sunyi mamakin yadda suka ga ogan nasu ya koma,
basu wani daɗe ba suka kama hanyar gida nan ma ma'aikatan sunyi mamakin ganin yadda oga ya koma amma ba damar cewa komai tunda dai bai basu fuskar wasa ba, ya wuce part ɗin sa dirdct don ya gyara kansa
a cikin gidan zainab ce zaune tana yiwa islam kalba akanta suka ji shigowar tj
"ɗan uwane ya dawo" ya faɗa, kallon rashin fahinta nayi masa wanda hakan ne yasa shi yi min bayanin wanda yake nufi,murna ce nima ta rufe ni ganin ko ba komai ƙila in koma gida wannan ke nan
************
sai da ajaban yayi kwana biyu ssnnan su tj suka fara shirin komawa gida, gaskiya banso ba, randa zasu tafi har bakin motar na rako su riƙe da islam a hannuna ina ts sharɓan kuka sabo tirken wawa,
ganin kukan nawa yai yawa ne yasa tj ɗin yace min ko a bar miki islam ne in yaso in an kwana biyu sai inzo in ɗauke ta ban san lkcn da na share hawayen nawa ba ina gyaɗa kai
aliyu da ke gefe kawai binta yake yi da kallon mamaki wai zainab ɗin ce ta zama,rabon da ya ganta tun kafin hjy ta rasu amma dubi ɗan canzawar da tayi a ɗan ƙanƙanin lkc, haka sukayi sallama da kowa suka kama hanyar kano ta dabo tunbin giwa sai dai muce Allah ya kiyaye hanya
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*opps na manta bansa page number a last ɗin ba sorry page 13 ne hope u will enjoy reading love y'all*
Page:14🌹
Har su tj suka tashi su zainab na tsaye a wajen get ɗin suna kallon motar yadda take tfy a hankali, ajiyar zuciya zainab ɗin tayi wanda hakan ne ya jawo hankalin aliyu kansu, ta na rungume da islam ita kuwa yarinyar tayi luf a jikin ta, wannan yanayin na su ya ba aliyu sha'awa sosai sai yaji dama islam ƴar sa ce yacce sukayi masa mutuƙar kyau har ya kasa ɗauke idon sa daga kansu,
Wai sai yaushe shi zai fara samun nasa zuri'ar waɗanda zasu kasance jinin sa waɗanda akulum zai kallah ya ji daɗi a ransa waɗanda zai kira su da *dangin sa* ƙara kalon inda su zainab ɗin suke yayi ga mamakin sa kallon sa take rai ɓace
"sai yaushe zaka gaji da ajiye ni a gidan ka, ka mayar da ni gida, ko kuma a haka zan ƙaraci rayuwata ina cikin kulle a gidan ka" ta faɗa rai aɓace,
be ce mata komai ba sai ma gyara tsayuwar sa da yayi yana fuskantar ta sosai tare da rungume hannayen sa a qirjin sa, ido ya zuba mata wanda ita hakan da yayi ya ƙara fusata
"me na tare maka a rayuwa ne da ka kawo ni gidan ka ka kulle ba tare da ka kuma waiwayena ba ka raba ni da dangin na da ƴen uwana ka kawo nan a wane daliin" ta kuma tambayar sa, wannan karan ma baice mata komai kawai si ya wuce yai part ɗin sa ranshi a ɓace
Kuka ta saki me tsuma rai wanda hakan ne ya jawo hankalin islam gareta itama ta fara kukan, ganin islam na kuka ya sa zainab ɗin yin shiru ta fara lallashin ta, ko da taga islam ɗin tayi shiru kawai sai ta kama hanyar part ɗin ta itama
Lallai ma yarinyar nan wai auren nawa ne bata ɗauka da dajara ba kome da har zata ce wai bata san zaman me take yi ba, bata san yana ciki da ita ba yau kusan satin sa ɗaya da wani abin da dawo wa amma bata taɓa zuwa ɗakin sa a matsayin ta na matar sa ba sai yau zata zo tare da wani zancen banzan ta wai ya kai gida
tsaki yaja har yanzu bata san halina ba ta ɗauka irin mazan nan ne ni masu bin mace tana wulaƙantasu, mu zuba ni da ke maa ga me gaji ya faɗa yana tsaki
bai yi niyyar fita ba ranar amma ganin yadda zainab ɗin ta ɓata masa rai ya sashi faɗawa banɗaki yai wanka ya shirya yai ficewarsa,
ba shi ya dawo gidan ba sai 11:30 na dare, wanka kawai yayi ya nemi wuri ya kwanta, amma ga mamakin sai sai bacci yaƙi zuwa maganganun zainab na ɗazu ne kawai suke dawo masa lallai ma yarinyar nan ta raina ni ya faɗa aransa, tashi yayi ya buɗe ƴar computer ɗin gidan sa wacce take ɗauko masa duk wani ilahirin gidan tare da taimakon ƴar ƙaramar camerar da ke manne akowane ɓangare na gidan
directly ɗakin zainab ɗin yayi searching don yaga ko ta kwanta koda kuwa ta ɓata masa rai dole ya duba lfyr ta tunda amanace a hannun sa, tayi ɗai ɗai tana baccin ta cikin rigar baccin nata kalar ruwan madara wato milk, net ce rigar amma me taushi don haka komai na jikin mutin ana iya gani
ya subhanallah ya faɗa a ransa tun da yake be taɓa ganin mace a haka ba kamar ya rufe sai ya tuna ai matar sa sai ya ci gaba da kallon nata, rigar iyakacin ta gwiwa amma kasancewar a kwance take yasa rigar ta ɗage mata da kƴar ma ta rufe mata mazaunanta yana iya hango white pant ɗin
wani irin miyau ya haɗiya *maƙwat* har da zooming don ya ji daɗin kallon ta, ya kwashe lkc yana kallon ta tana sharar baccin ta peacefully inda daga ƙarshe shima baccin ya kwashe shi cike d mafarkai iri iri na zai zainab ɗin ta kawo masa kanta wannan ke nan
************
Ɗakin zainab yanzu ya zama nan ne film ɗin aliyu yini yake yi yana kallon duk wani mƙtsin ta in dai yana gida idan kuwa dare yayi kusan computer ɗin tasa akunne take kwana yana kallon duk wani shige da ficen ta, ya riga ya saba da kallon ta kullum wannan ɗabi'ar sa ce tasa yai developing feelings 4 her amma shi sai yake gayawa kansa cewar kawai dai yana kula da amanar Allah ne ba komai ba, yana kallon yadda take kula da islam daga ganin ta tana da son yara sosai, in ma taƙi kawo masa kanta don ra'ayin kanta zai iya maida islam ɗin gidan su sannan ita kuma yace mata idan tana da ra'ayin ƴaƴa nata na kanta, ta iya kawo kanta gareshi ko Allah zaisa ta samu, wani ɗan murmushi yayi da ya hango ta ta faɗa tarkon nasa ta kawo masa kanta yana sarrafa wannan ɗanyan jikin nata da yanzu sai dai ya kalla a computer
tafiyace ta kama aliyu zuwa lagos inda har gidan su zainab ɗin yaje sun sha hira sosai da babanta har yake cewa baban ai bai daɗe da dawowa ba, ya buƙaci ya gaisa da ƴen uwan zainab ɗin inda baban yaiwa su maryam waya ai kuwa sai gasu kamar dama suna kusa,
sunyi masa ƙorafin rashin kiransu da zainab ɗin takeyi inda suka buƙaci number ta daga wajen sa nan fa yai zuru zuru wayarsa ya ɗauko ya basu wata tsohuwar numbersa da bata yi suka kira a kashe ba yadda suka iya haka suka haƙura sai da ya tashi tafiya ne ya nemi khadija ta bashi number ta inyaso idan yaje sai ya kira ƙila zainab ɗin ko bata da numbers su ne
kashegari da wuri ya je gidan inda ya ɗauki baba ya kaishi ƙaton shagon da ya buɗe mai a oshodi mrket baba kasa godiya yayi sai kuka
da murnar sa ya dawo abuja don gani yake yi yanzu ya samu damar yiwa zainab ɗin magana dama da rashin sanin abin faɗa ne yasa shi bai doshe taba, don kar tace ya yada girman sa a matsayin sa na namiji
linda ya kirawo ya shaida mata yau a part ɗin zainab ɗin zaiyi dinner don haka tayi setting table ɗin da shi, yes sir kawai ta iya amsawa,
ina kwance gab da magariba Tunanin da nakeyi ne de kullum shi nake yi yanzu naji an turo ƙofar, linda ce ta turo ƙofar
"madan is time 4 ur bath"
ta faɗa miƙewa nayi ina rage kayan jikina
"linda a haɗa min ruwan wankan kawai amma banason ganin kowa a toilet ɗin"
"yes mam" ko da suka gama ta zo tace min
"ma'am d water is ready"
"ok linda tank u"
shiga cikin jacuzzi ɗin nayi na kwanta inda ruwan ɗimin wanda ba abinda yake tashi sai ƙamshi a cikin sa yake ratsamin ko ina na jikina ina jin daɗin yadda ruwa yake gasa min jikina sosai, sai da gaji don kaina sannan nayi wanka na fito inda na tarar ɗda masu kwalliyata suna jirana, kwalliya sukai min kamar wacce zata wani shahararran diner
closet ɗina na shiga da kaina don yau ni nake da ra'ayin ɗauko kayan da zansa da kaina shi kanshi closet ɗin nawa gidan wani ne don tsabar girman sa, inda ɓangare komai daban yake har spa gare ni a cikin closet ɗin nawa kaya kiwa kusan kullum sai an kawo sababbi an zuba, matsala ɗaya ce da closet ɗin nan nawa wato ba kayan mu na hausa daga english wears gown sai abaya of different designs
wata pink armani gown ce taja hankali na daga gani sabuwa ce don acikin ledar ta take a jikin hanger nayi murmushi nace wannan
ko da nasa rigar tai min kyau sosi sai anci mutunci yadin sosai don gabaki ɗaya bayan rigar a kwaye yake sai da aka kai rigar saman duwawu sannan aka barta anan ga gaban rigar shima a buɗe duk rabin boobs ɗina suna waje sai wani shegen yanka da aka ɗauko tun daga saman cinya har izuwa kasan rigar inda in mutun zaice zaiyi tafiya to gabaɗaya kafarsa ta hagu tun daga cinyar sa har ƙasa a waje zai kasance
wannan wace irin riga ce na tambayi kaina,
" d dinner table is set ma'am" inji ɗaya daga cikin yaran
"ok" na faɗa ina yin gaba wannan wace irin rigace na kuma faɗa araina ganin yadda ko ya na motsa sai tasa jikina motsi
direct dinner room ɗin namu na nufa ina kallon kaina wannan riga ai ba ta irin mu bace ina gama cin abincin cire ta zanyi, karo naji munyi da mutun inda nayi ƙasa zan faɗi, yayi yunƙurin kamoni amma kuma na riga nayi ƙasa shima sai yayi losing balance ɗinsa ya faɗo kaina, inda lips ɗin mu suka haɗe waje ɗaya, tsotsan lips ɗin nawa naji yana yi wanda hakan ya jefani a cikin wani yanayi wanda ban taɓa shiga ba
mun shiga cikin wannan yanayi inda hannayen sa suke dumu dumu akan boobs ɗina yana massaging ɗin su wanda hakan yasa tsigar jikina gabaki ɗaya tashi nayi losing control gabaɗaya na, deep down in me nasan abinda yake min be dace ba amma i cant stop him he is too darm good
shaiɗan shaiɗan wannan shine kalmar da zuciyata take faɗa bansan lkcn da ƙarfi ya zo min ba na hankaɗe shi daga kaina na tashi a guje nayi ɗakina na rufe ƙofa har da sa key ina haki ina maida numfashi haka kurum bazan bari ya cuceni ba na faɗa a raina dinner da banyi ba kenan a ranar na kwanta da yunwata
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :15🌹
Kasa tashi yayi, duk ilahirin jikin sa a mace yake, sai da ya ɗan nutsa sannan ya samu ya miƙe tare da taimakon bango da yake dafawa,
part ɗinsa ya wuce ya faɗa toilet ya sakar wa kansa ruwan sanyi ko yaji daɗi a ransa, ruwan ya daɗe ya zuba a kansa inda duk wani da ya faru ɗazu da shi da zainab ɗin yake faɗo masa aransa, *shit* ya faɗa tare da dukan bangon tiles ɗin da ke toilet ɗin, tun da ta fito daga ɗakin natan yake ƙare mata kallo wanda wannan ne yasa ya kasa ɗauke idon sa daga gare ta har ya matso kusa da ita inda ita kuma ta faɗi
Sai da yaji ya nutsa duk wasu jijiyoyin jikin sa da suka tashi don bada action sun kwanta sannan ya cire kayan jikin sa ya fito ɗaure da tawol,
Directly wurin computer tasa ya nufa ya kunna ta don yaga a wane hali zainab ɗin take ciki, tana tsaye dai dai saitin camerar har yanzu nishi take yi wanda hakan ne yasa boobs ɗin ta suna ɗagawa suna komawa 😳😳😳 ido kawai ya ƙwalalo yana kallan kayan gabas ba damar taɓawa
a guje ya koma toilet ɗin ya kuma sakar wa kansa ruwa don yaji jijiyoyin nasa sun fara harbawa again ko da ya fito bai iya kallon computer ba sai kawai ya rufe ta ta baya ya shiga shiryawa, sai da ya gama abinda yake yi tas sannan ya ɗauko computer ya ɗaura a kan bedside kusa da shi ya kwanta yana kallon ta tana ta sharar bacci ta peacefull
Daina fita nayi ya kasance komai a ɗaki nake yi hatta abinci sai ince a kawo min ɗaki dƙn bana son abinda zai kuma haɗa mu da wannan bawan Allah da ya kawo ni kuma yake son ɓata min rayuwata don kawai yaga bamni da gata ubana bashi da abin duniya
yau garin an tashi da ruwa, garin ya ɗanyi sanyi sanyi haka na tashi duk jiki na ba daɗi burina in ɗan motsa shi ko naji daɗi tun da yanzu bana fita balle in ɗan taka, shawarace ta faɗo min na ɗauki wayata inda na kunna kiɗa na fara tiƙar rawa ai shima exesice ne kuma zai ɗan motsa min jiki
ganin bana ganin abin ciki wayar sosai ya sa na kira linda akan taimin connecting wayata da tv ɗin ɗakin don in dinga bin mawaƙan muna taka rawar tare
"madan today u r in a good mood oooh"ta faɗa tana dariya
"yess ooooh linda come and join me"
"aah noooo am busy" ta faɗa ko da gama ta fice sao na rufe ƙofa ta harda key don kar wani ya shigo min
doguwar rigar da ke jikina ita na cire don inji daɗin yin rawa ta ya kasance daga ni sai ɗan pant da bra, na shiga rawa ta ina kwaikwayan mawaƙan
wata waƙar ariana grande ce ta shigo me suna side by side, ina son wakar sosai don dana fara ganin ta har tsalle sai dana yi kafin in fara bin salon nasu, slow music ce sai sexy moves da ake yi, inda aka nuno su suna tuƙa keke ni kuma sai na dafe gado na ina juya ɗuwawu, ina bin kiɗan
babu wani move da na bar ya wuce, ko da waƙar ta ƙare si na sake dawo da ita baya don waƙar tai min daɗi sosai, haka na dinga rawa ta har na gaji na kwanta ina maida numfashi
ya zaune a gaban computer tasa yana kallon duk abinda take yi, ƙanƙara ce sukutum da guda ɗinta akan ɗan gajeran wandon nasa don in haka yayi ba sai hakimar tasa ta tsere 🏃🏼♀ ta tafi gurin zainab
wai ita wannan wace irin yarinyace bata san cwwar ana kallon ta ba ko kuma yana kallon ta zata dinga irin wannan abin mai tadawa da mutum hankali bayan ba wani kulawa yake samu daga garea ta ba, iska ya fesar da ƙarfin sa kana ya tashi ya faɗa banɗaki dole yana buƙatar wanka da ruwan sanyi sosai duk da dai sanyin ake yi amma yau ya cancanci wankan da na sanyi
************
bayan kwana biyu na saki jiki na saosai na manta abinda ya shiga tsakanin mu da aliyu hidimata kawai nake yi kamar banida wata matsala, islam tana ɗebe min kewa sosai da sosai duk da yarinyar ƙarama ce amma tana wayo sosai don haka sai nake jin daɗin zama da ita sosai
kamar kullum yau ma na gama komai na shirya islam na kwantar da ita har tana fara bacci nima nayi abinda ya kamace ni na kwanta sai na kasa bacci don haka sai na ɗauko waya ta na shiga whatsapp,
grp ɗin da nake na shiga na wata shahararriyar marubuciya wato mmn farida, grp din ta na samun wuri ina duba wa ko ta aiko da cigaban littafin ta na samun wuri ɗin amma kamar yadda nayi tsammanin haka bata aiko da shi ohhh mmn farida akwai shiririta na na faɗa a raina, wani saƙo ne ya ɗauke min hankali,
saƙo ne akan breast cancer yadda mace zata gane cewar cancer ta fara zuba ƴaƴanta a cikin maman mutun don ayi saurin ɗaukar mataki kafin abin ya ɓaci, saƙon ya ɗau hankalina sosai inda akace ya kamata mace ta dinga bincikar breast ɗinta a kullum to ensure she is safe
zata dinga checking nonuwan taji idan akwai ɗan ƙullutu ƙullutu, idan akwai to ta garzaya asibiti idan kuma babu to she is safe, wannan ne yasa zainab ɗin yin zunbur ta miƙe daga gadon da take kwance akai tayi wajen madubin ɗakin, inda saman madubin ƴar munafukar camerar ɗakin take
cire ƴar rigar baccin tawa nayi na tsaya ina kallon boobs ɗin nawa kafin daga bisani na fara checking ɗin nasu out for lumps kamar yadda suka ce inayi ina ɗan ɗaga idanuna sama alamar ko zanji wani abun🤔🤔🤔
jin alamar cewar banji komai bane yasani na ɗauki rigata na maida na koma na kwantasai da nagama ƴen karance karance na sannan nai mana addua na kashe fitilata, bacci me daɗi ya sure ni
yana zaune agaban computer tasa kamar an dasa shi duk jikin shi sai da ya yi paralyzed na ƴen sakwanni kafin su dawo su cigaba da aiki, kallon ta kawai yake yana ƙarawa ji yake yi inama shine yake checking mata ƴen abebaɗan nata, ya rasa zai yi da yarinyar nan kullum sai ta fito da sabon salon da zai sa ta rikita masa lissafinsa, kai amma ganin tan nan da yayi yau ba zai iya haƙura ba sai yaje yau ko ta halin ƙaƙa an bashi haƙƙin sa, haba ace mutun kusan wata nawa da aure ba wani cigaba kullum sai dai ta tayar min da hankali sannan ta barni da wanka da ruwan sanyi too yau da sake don yau haƙƙina nika karɓa
da ƙwarin gwiwarsa ya nufi part ɗin nata amma kuma sai dai kash ɗakin natan a rufe yake ta ciki ɗan handle ɗin kofar ya dinga murɗawa da ɗan ƙarfi yana ɗan ƙwanƙwasa kofar ko Allah zai sa taji ta buɗe yana yi yana waiwaye don baya son ma'aikatan da ke part ɗin nata su fito su ganshi ai girma kuma ya faɗi ya faɗa aransa, ni kuwa nace mlm aliyu bata matse bata matse ka bane da ta matse ka baza ka kawo komai a ranka ba
zainab na kwance tana bacci taji kamar ana ƙwanƙwasa ƙofar gabanta ne yai mugun faɗuwa inda tatashi taga da gasken ƙofar ɗakin ake niyyar buɗewa harda murɗa handle ɗin ƙofar Allah ya taimaketa tana kullewa da Allah ne kaɗai yasan mutumin da yake son shigo musu da kuma wace irin mugunta da ya zo da ita, tashi tayi a hankali ta ɗauki islam ta nufi cikin closet ɗin ta, can ƙarshen closet ɗin taje ta rakuɓe tana mai kiran sunan ubangiji ya kawo mata ɗauki tare da kuka mara sauti
ko da yaga taƙi buɗewa haka ya haƙura don kansa ya koma part ɗin nasa tare da yin abinda ya saba yi wato wanka da ruwan sanyi sannan ya kwanta haushin da ta bashine yasa ko buɗe computer ma bai yi don yasan sarai tana jinsa
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: .🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:16🌹
Ko da ya tashi da safe be bi ta kanta ba don ba ƙaramin haushinta yake ji ba, office kawai ya shirya ya wuce ya mitar wace irin yarinya ce
Shi a yadda ya ɗauki mata wasu ababe ne da basu san darajar da Allah yayi musu ba ashe har yanzu be san karatun mata ba, yana mamaki yadda yammata da suke kawo masa kansa suna rushing ɗin sa yana wulaƙantasu amma wannan ƴar ƙaramar yarinyar tana neman rikita masa lissafi mita ya dinga yi har ya isa office ko ɗan fara'ar da yake yi wa ma'aikatan nasa ma yau basu samu ba
Sai da naga gari ya waye sannan na iya buɗe ƙofa linda na gani ashe ta daɗe tana bugawa kasancewar ina cikin closet ɗin yasa ban ji ba
"madam are u ok" ta tambaya
"ina fa ok jiya wani ya shigo yana neman shigar min ɗaki" na faɗa mata atsorace, kallo na tayi alamar bata yadda
"baki yadda bane"
"no ma'am but am sure na rufe ƙofar falon nan, ƙila ko mafarki ne"
"mafarkin me abinda na gani da idona"
Na faɗa ina zare mata ido
"ok ma'am zan gayawa oga zai san yadda za ayi" ta faɗa tana mai ƙarasowa cikin ɗakin
Ta dudduba ko ina bata ga wani abin da ba dai dai ba don haka sai tace "bari in kira oga inyi masa bayani, ki shirya ki fito 4 breakfast" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin
yana zaune a office yana tunanin yarinyar nan da take rena masa sense ɗin sa wayar sa ta ɗau ƙara, linda ya gani don haka ya tabbatar wani abin ne ya faru
"hello linda"
"hello sir dama madam ce take complain ɗin ana ƙwanƙwasa mata ɗaki sannan" shiru yayi abinda zata yi asa kenan kuma yanzu ta faɗa wa masu aikinta yana zuwa ɗakinta
"sir y r u quite"
"ba komai abin ne nake tunani, tasan wanda yake buga matan"
"no ita dai kawai tace taji knocking, ni a tunanina imagination ɗinta ne kawai" ajiyar zuciya yayi ganin cewar bata faɗa musu shi ne ba
"ok just assure her cewar she is sfe ba komai"
"yes sir"
"emmm linda prepare today's dinner with me i will be dinning with her"
"yes sir"
Ta faɗa daga nan sukayi sallama, ko da taje ta faɗawa zainab ɗin cewar ba komai, zainab ɗin dai bata yadda ba amma ta sha alwashin koma waye sai ta kama shi
ko da lkcn cin abinci yayi linda ta gayyace cin abincin, jeans ne ajikin ta da ƴar ƙaramar body hug wacce ta tsaya mata iya cibiyar ta sai parking ɗin gashin ta da tayi a tsaki kan wanda jelar ya ɗan saukar mata yana lilo
fitowa nayi don zuwa wajen cin abin cin
"linda ina islam take"
"tana dining room ɗin"
"ok bari kawai inje sai in bata abinci acan"
su islam wasan ne kuma har dinning room yarinyar akwai ƙiriniya sosai gata bata zama wuri ɗaya so full of energy,
ko da naƙarasa cikin dinning room ɗin a zaune na ganta a kan kujera tana cin abincin ta
"ohh har kin fara baki jiran ni ba ko" Na tanbayeta ina ɗan dariya
tsoro naji ashe da mutun a ɗakin ban ganshi ba da shigo don yana gurin bar yana tsiyayowa kansa lemo
"bismillah zauna muci abinci tun ɗazu nake jiran ki" ya faɗa tare da ja min kujerar zama
rasa abinda zanyi nayi ga kayan jikina ga kaina ba ɗan kwali duk sai ƙare min kallo yake yi, juyawa nayi da niyyar guduwa ban ankara ba naji ya kamo ni ya haɗa ni da jikin sa yana sauke numfashi da sauri da sauri
ƙoƙarin ƙwace kaina nayi amma ina ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane
"relax relax kawai naji yana furta min a kunne na inda maganar sa tasa jikina yin shiruda kuma daina kokawar kasanceqar tasirin da tayi a jikina da gaɓoɓina
kuka na sa masa shi kuma ya shiga lallashina tare da shafe ilahirin jikina yana wani irin numfashi
"4 God's sake zainab wat do u want" ya tambaye ni
"ni ka kaini gida"
" gida kike so nan ba gida bane me yasa bazaki saki jikin ki da niba" azzalimmi in saki jikina ka cuce ni na faɗa araina
"ni dai don Allah ka dubi girman Allah ka maidani gida gaban iyayena" na kuma faɗa
"to shike nan kije zan yi tunani tukun na" ya faɗa yana sakina
a guje na kama zan bar ɗakin ƙara kamoni yayi yan ƙara mannani aqirjinsa tare da kissing ɗin wuyana sannan ya sake ni
"ki zauna kici abincin ki ni zan fita inci a waje naga alamar nine ba a son gani" ya faɗa yana yin hanyar waje
wanda ni kuma hakan yai dai dai da tsugunna wata ƙasa tare da dasa wani sabon kukan, in da naji islam ta hau kaina itama tana nata kukan, dole na share hawaye na na lallasheta sannan na zauna na ci gaba da bata abincin ta
tun daga lkcn na tsiri yawo da hijabi ko ina in dai zan bar ɗakina to da hijab ɗina a jikina, ban san cewar duk aikin banza nake yi ba shi ta ɗakina ma yake shan kallon sa ya more, mun sha cin karo da shi sai in zura a guje inyi ɗaki in barshi anan
rasa yadda zaiyi da ita yayi ta zauna ma suyi maganar fahimta taƙi da ta ganshi kamar taga wani dodo sai gudu ga wani hijabi da ta tsiri sawa duk yasan don shi takeyin hakan bosho ke nan ya faɗa
yana zaune a ɗakinsa yana tunanin ta yadda zai ɓullo mata ko ta saurare shi
"khadija khadija" shine abinda da iya faɗa, lallai ya ƙura yarinyar tana da saukin kai zata iya shawo masa kanta, wayar sa ya ɗauka ya lalibi number khadijan ya kira sai da ta gama ringing ta tsinke ya kuma kira sannan ta ɗauka da sallamar ta
"khadija ce" ya tambaya bayan ya ansa sllamar
"e ni.....ce......" Ta faɗa tana ɗan jan harufan alamar mamakin jin muryar namji ya kira ta
"ok aliyu ne mijin zainab"
"laaaaa ina wuni" ta faɗa da fara'ar ta wadda yana iya gane wa ne ta yadda tayi magana
"lafiya ƙalau ya gidan da me gida"
"lfy lau, ina yayar tun da ka tafi muke tasa ran ta kira mu amma shiru"
"wallahi khadija yayar nan taki ce ta matsa sai na kawo ta gida ni kuma gaskiya banni da ra'ayin haka"
"kash amma yaya bata kyauta ba"
"shine nake cewar idan kinga ba damuwa ko ku zaku iya zuwa ku ganta kinga ƙila idan taganku wataƙila hankalinta yafi kwanciya ko"
"to shike nan bari in kira maryam sai inji yadda zamuyi in zamuje sai mu sanar da mazajen mu inyaso zuwa magariba zan kira kaji duk yadda mukayi" godiya ya dinga zankaɗa mata har yasa ta jin kunya sannan sukayi sallama
oohh yaya ban sanki da wannan hali ba,wayar ta ta ɗauko ta kira maryam inda suka tsaida shawarar kowacce ta tambayi mijinatan, haka akayi kuma cikin sa a kowacce mijinta ya yarde mata
ko da aliyun ya kira khadijar ta shaida masa yai murna sosai sannan yace mata akwai flight gobe da ƙarfe 11:30 na safe lagos zuwa abj in zasu biyo yasa ayi musu booking
"to shi ke nan Allah ya kai mu" ta faa ta kira maryam ta shaida mata tafiyar tasun gobe da safe ce
ƙarfe goma dai dai na safe aliyu ya turo da driver ɗin sa na lagos ƙofar gidan maryam tare da taimakon ta wajen yi masa kwatance, a shiye suke tsap don har maryam ma tazo suka shiga suka kma hanyar airport tare da rakiyar mijin maryam, sun biya ta gidansu sunyi bbn su sallama inda mama ta dinga faɗan ba a gaya mata ba aida ƙafar ta ƙafar su, shidai baba cewa yayi da sun sauka su kirashi, da haka sukai salama
A airport ɗin duk aka gama duk wani abinda za ayi suka hau jirgi ya ɗaga da su birnin tarayya
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page: 17🌹
Khadija bata ga wautar su ba sai da sukayi kane kane a jirgi sannan wani abu ya faɗo mata, to in banda ma rashin tunani irin nasu tun da yayar nan ta tafi babu wanda ya taɓa ganin ta ko jin labarin ta, sai dai shi mijin, amma daga zuwa yace musu wai taƙi sakin jikin ta kawai sai su kuma suka kamo hanya suka taho ganin ta, oh Allah kasa ba ajalin mu yake kiran mu ba
juyawa tayi ta kalli maryam wacce take ta ƴen kalle kallen ta ga farhana a hannun ta tana ta bacci, ita ta baro khalil a wajen mama kasancewar yanzu cikin ta ya fito sosai don haka bata yawo da shi
suna sauka ta kunna wayar ta sai ga kiran aliyu nan
"na turo driver ya ɗauke ki na bashi number ki don haka zai kira ki, ni na shiga meeting ne sai dare" To kawai ta iya cewa jiki a sanyaye
"Allah yasa ba meeting ɗin siyar da mu ya shiga ba"
ilai kuwa sai gashi driver ɗin ya kira ta, tai masa kwatancen inda suke ya ƙaraso tare da ɗaukar kayan su zuwa wurin motar, wata baƙar continue discussion ce suka dosa glass ɗinta duk tinted ne baka ganin na ciki (ta wata tace *ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba* 🤣🤣🤣🤣
cikin khadija ne ya ƙara ɗurar ruwa shike nan su tasu ta zo ƙarshe ta faɗa tare da yin bismillah tana shiga motar tare da yiwa Allah addu'ar ya tsera tar da su
ko da suka je gidan ma khadija ganin irin girman gidan yasa ta kasa hakuri
"maryam nifa tsoro nake ji"
"tsoron me" inji maryam ɗin wacce hankalinta gabaɗaya yan ga kallan kataferen ginin da suke ƙoƙarin shiga
"yaya khadija don Allah dubi irin gidan da yaya take rayuwa acikin sa"
lallai har yanzu maryam ba nazari a lamarin ta wato ita kyawun gidan ma take hangowa ba irin hatsarin da suke shirin shiga take yi ba yanzu idan aka garƙame ka awannan tafkeken gidan ko tokar ka a ganine
share maryam tayi ta ci gaba da addu'a suna shiga cikin kataferen gidan kamar na shugaban ƙasa, sai da suka ɗanyi tafoya a cikin a cikin farfajiyar gidan, sannan suka samu sukayi parking
Ƙofar motar aka buɗe musu wani mutun ne sanye cikin bakaƙen suit da gilasin sa baƙi ya bude musu tare da cewa "welcome" a cikin muryar nan tasa kamar a shaƙe shi
maryam ce ta ansa da fara'ar ta ita kuwa khadija fitsari ne kawai be zubar mata, kai duba tayi taga farfajiyar cike take da maza tiƙa tiƙa duk sanye cikin bakƙaƙen kaan da glass ɗin abtsaye ƙiƙam kamar an dasa su
wawuro maryam tayi "mun shiga uku maryam gidan yankan kai aka kawo mu" itama maryam ɗin da jikin ta ya fara sanyi ganin waɗannan ƙattin yasa itama yin shiru
"dis way pls" ya faɗa tare da nuna musu hanyar da zasu bi da hannu sa, bin shi sukayi a baya duk jikin su yayi sanyi
sunyi tafiya ta kai ta kusan minti goma kafin su ƙaraso wata ƙofa daga ganin ta ƙofar falo ce, door bell ya danna aka buɗe masa,
"they r here" ya faɗa tare da juyawa, matar da ta karɓe su me ɗan fara'a ce ba kamar mazan ba
"do come in pls" tace musu haka suka shigo jiki yayi sanyi, tsayawa sukayi suna ƙarewa ƙayataccen falon kallo
"pls wait here let me call madan"
"ok" suka ansa a tare
ina kwance ina game ɗina rebecca ta shigo
"madam u have guest"
"guest kuma tell them am sleeping" na faɗa na cigaba da game ɗina, ni wacece a gidan na da zanyi guest, ko kuma waye ma nawa yasan inda nake da za a ne mi, ƙila baƙin aliyu ne yace a kawo su in yi entertaining ɗin su ko a wane matsayin oho, ci gaba nayi da game ɗina hankali kwance
ko da ta fita taje ta sanar musu sai jikin su yayi sanyi, anya yayar da suka sani ce, maryam ce tayi karfin halin cewar
"go and tell her, her sisters from lagos maryam and khadija are here to see her" tsayawa tayi tana ƙare musu kallo tana tunanin taje ko kar taje
riƙe hannunta khadija tayi
"pls pls pls and pls i take God beg u call her 4 us" ganin iɗin roƙon da suke mata ne ya sa ta tausaya musu
"ok lemme go again but if she say she will not come out now u will have to wait oooh" ok suka bata ansa
ina kwance ni nama manta da wata rebecca ta zo
"madam"
"ooooooo..... Wat again"
"they say i should tell u dat ur sisters from lagos morya and kadija are here"
jin an anbaci sunan ƙannena yasani sakkowa daga gadon aguje nayi falon ban dai gaskata abinda tace ba amma ai ance gani ya kori ji
sune kuwa atsaye ƙiƙam, a guje naje na rungume su ina kuka ashe zanga ɗan uwana, suma rungume nin suka yi muks ci gaba da kukan mu, sai da muka yi mai isar mu sannan muka nutsa
"ku zo muje ɗakina" na faɗa ina jan hannayen su
"rebecca Kawo musu kayan su ɗakina, na faɗa ina yin gaba da hannun ƙanne na
"ya akayi kuka san inda nake"na tambaye su
"mijinki mana, shi yace mu zo"
"mijina kuma waye kuma mijina" na tambayesu, tsayawa sukayi suna kallon juna
a lkcn ne rebecca ta shigo musu da kayan nasu,
"ina linda tayi"na tambaye ta
"bata dawo daga kasuwa ba"
"ok haɗo musu ɗan abin sawa abaki"
ko da ta fita ƙara matsowa nayi kusa da khadija
"waye mijin nawa, yaushe aka ɗaura min aure" tsayawa sukai suna kallon juna
"yaya da gaske baki san kina da aure ba" gyaɗa musu kai kawai nayi don wannan lamarin ya girmi tunani na, ina da aure to me yasa miji bai taɓa zuwa inda nake ba
"to me gidan nan yaya aliyu" kamar in gwaɓe wa maryam baki wai wani yya aliyu, harara na bita da shi na kuma fuskantar khadija don ita a lamarin ta ba ta waasa
"Allah yaya me gidan nan ne mijiki, ke da tun zaman da kike yi a gidan baki san zaman aure kike ba" kaina ne ya kuma juyewa
"yaushe aka ɗaura min auren ban sani ba"
"kusan wata bakwai ke nan ko maryam"
neman maryam mukayi muka rasa ashe ita tuni tayi cikin closet ɗina
"yanzu yaya duk wannan kayan naki ne" muka jiyo muryar ta, kamar inje in rufe ta duka hka nake ji don haushi, wai ina da aure da kuma aliyu duk yaushe hakan ta faru na kuma tambayar kaina
ƙara dawo da hankali nayi ga khadijar wadda itama hankalinta yana kan kayan da maryam ta fito da su daga closet ɗin tana nunawa
"yanzu khadija wa ya ɗaura min ba tare da sani na ba"
"baba ne " ta faɗa a taƙaice
hawaye kawai naji yana zubar min ashe baba sai da ni yayi shi yasa bai taɓa nema na ba, wayar khadija ce tayi ƙara ko da ta ɗauka baban ne
"eee gata" kawai naji tace ta miƙo min wayar
kunne na na kai wayar inda muryar babana ta daki dodon kunne na, yaushe rabon da inji muryarsa har na manta, a mutunce muka gaisa sannan ya dinga bani labarin irin hidindimun da mijina yake mas harda ceqa ɗan al barka ne ki bishi sau da ƙafa kin ji, to kawai nake cewa
"ga maman taku" ta karɓa muka gaisa ita ma ɗin dai ce min takeyi wai inyi masa godiyar hidimar da yakeyi da su, ko da muka gama khadija ce ta karɓa sukayi magana da ɗanta sannan sukayi sallama, wannan shine fa ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :18🌹
Naji daɗin zuwan ƙannena gidana inda duk abinda ban sani ba sai da suka sanar dani, na sha mamaki sosai, shima aliyun ya samun daman sake wa da ni son ransa, ba yadda na iya haka na dinga sakar masa jiki a gaban su amma da mun keɓe sai zancen ya canza, ya kan yi haƙuri da ni yace bazai yi rushing ɗina ba
kwanan su khadija shida suka fara shirye2 tafiya, muna zaune a tsakiyar ɗakina munbaje muna hira, su kuma suna haɗa kayan su,duk abinda da suka gani nawa sukace suna soo basu nake, sun haɗa kayan su tsab sai shirin tafiya
"yaya bazamu zaga gari ba kafin mu tafi tun da muka zo muna gidan nan bamu fita ba"inji maryam
Tsuru tsuru nayi nayi don gaskiya naga dacewar ace sun zaga ɗin amma rashin sanin hanyar da zan bi in faɗawa aliyu yasa ni na basar
"ai kuwa maji daɗi idan mun zaga muma muce mun zo birnin tarayya" khadija ta faɗa
"to shikenan ku bari idan aliyu ya dawo da daddare sai in faɗa masa
ko da ya dawo da daddare naje part ɗin sa na same ya fito daga wanka daga sai towel a ɗaure a jikinsa duk sai kunya ta kamani, gashin kan nan nasa sai ɗigar da ruwa yakeyi inda yake ɗiga a faffaɗan qirinsa,
"bari inje inka shirya na dawo" na faɗa ina juyawa
"no ba komai shigo kawai ai kasya kawai zan sa" Tsayawa nayi ƙiƙam ni ban shiga ba ni kuma ban fita ba, har sai da yazo ya jawo ya zaunar da ni akan cinyarsa
"ma kike so" ya tambaye ni, kasa magana nayi kaina na ƙasa ina wasa da ɗan zoben azirfar da ke hannu na
"kin zo ne kawai ki ganni"ya tambaya yana murmushi,girgiza masa kai nayi
"oooh akwai wani abu da kikesoo ne" na gyaɗa kaina
"ok ina jinki"
"dama su khadija sukace sunaso kafin su tafi su zaga gari, shine nace bariin faɗa ma kozamu samuaron mota"
"duk motocin da ke gidan nan ai naki ne, ki zaɓi duk wan da kuke son fitaaciki ta sai driver ya kai ku kinji" gyaɗa masa kai nayi alamar naji
"ga atm card ɗina nan daga nan ki kai su shopping don karsu koa gida ba tsaraba ko" ɗagowa nayi na kalleshi da fra'a ta kamar yasan abinda ke zuciyata
ko da na kai hannu na zan karɓa sai ya ɗauke abinsa
"ai ba kyauta zan baki ba, sai kin biya" yafaɗa, ƙwalalo ido nayi don bansanda me zan biya ba
"karki damu kiss kawai zakiyi min card ɗin ya zama naki" ya faɗa rasa yaddi zanyi nayi,
Rufe idona nayi nakai lips ɗina saman kanshi amma to my surprise ashe akan lips ɗin sa na sauka, it was great, bani card ɗin yayi
"ayi siyayya lfy, kema kina iya zaɓar kayan mu na nan naga baki da su ko" gyaɗa masa kai nayi
"ok a siyo masu kyau don aji daɗin kwalliya da su" ya faɗa yana kashe min ido ɗaya 😉
Ko dana koma na faɗawa su maryam fitar mu kashegari ba ƙaramar murna suka yi
Kashegari ƙarfe 11:30 na safe muka fita, mun zaga gari sosai babu wanda na sani don haka yawo kawai muka dingayi parks sannan muka je wni restuarant muka ci abinci daga nan muka wuce shop rite, da farko ƙin sakin jiki sukayi sai da suka ga ina kwasar wa su mama da baba kaya sannan suma suka ɗaɗɗauka
sai yamma lis sannan muka dawo tare da kaya niƙi niƙi ni ban ma san ko nawa muka kashe ba amma nasan mun yi ɓarna ni kaina kayan da na siyawa kaina ba kaɗan bane
da daddare naje maiyar masa da card ɗin sa sai yace in riƙe kawi a hannuna, gidiya nayi maisosai sannan na koma ɗaki na
kashegari sai 12:00 sannan su maryam suka tafi kamar in bisu amma ba hali haka na haƙura na dawo, ko da na tashi kwanciya sai duk kewar su ta kamani na kira su daya bayan ɗaya muka sha hirar mu sannan na iya bacci
************
Tsakanina da aliyu kuwa mun koma ƴar gidan jiya, don yanzu ko ya zo inda nake haɗe rai nake yi ni har yanzu banga dalilin da zai sa ya aure ni ba ba tare da izini na ba,
Ina zaune naga missed call ɗin maryam wai khadija ta haihu nai mamaki yau watan su guda da sati biyu da komawa amma ta haihu sam cikin ta ba alamar ya tsufa na faɗa araina, tashi nayi tsam na kama hanyar part ɗin aliyu don ina son ayi sunan da ni
yana kwance yana kallon ceiling ɗin ɗakin nasa na shiga da sallamata daga gani yayi nisa a tunanin nasa don ko jin sallamar tawa baiyi ba sai da na ɗan taɓa shi, sannan ya juyo ya ƙura min ido kamar yana neman wani bayani a fuskata
"kamar kinsan tunanin ki nakeyi yanzu, zo ki kwanta kusa da ni" ya faɗa yana me matsa min wuri
ban musa ba na kwanta kamar yadda ya umarta rungume ni yayi tare da yin ajiyar zuciya, nakan jiyo bugun zuciyar sa sosai kamar zata fasa ƙirjin nasa ta fito, mun ɗan jima a haka sannan ya ɗan sassauta min ruƙon
"kina buƙatar wani abun ne" ya tambaya, har na buɗe bakina zan yi magana sai wani abun ya faɗo min wato ni bana zuwa pary ɗinsa sai buƙatata ta taso, kunya ce ta kamani na kasa magana
"sweetheart just tell me ko menene"
"dama khadija ce ta haihu" na faɗa da ƙyar
"maa shaa Allah, yaushe"
" ɗazu an sami namiji"
"maa shaa Allah, Allah ya raya kina son zuwa suna ne" gyaɗa masa kai nayi
"wannan ba komai bane muma tazo ta ziyarce mu dole ne kije, amma bakya ganin kema kafin ki tafi muma mu gwada ƙila ki tafi da ɗan abinki a nan" ya faɗa yana shafa min marata
"bana sallah"
"ohh ba komai ai akwai ƴar dabarar da mata suke yi idan basa sallah kin iya" shiru nayi masa don wannan zancen ya girme ni
ganin nayi shiru yasa shi fara wasa da jikina, ni a ganina bani da abinda zan bashi don haka me zai sa in zauna ina ɓata masa lkc don haka sai na tashi na yi ficewata ina jinsa yana ƙwala min kira amma ban kula shi ba
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :19🌹
Shirye shirye tafiya nekeyi ba kama hannu yaro, aliyu ya kaini shopping na kayan jariri da mai me jego muka yo musu siyayya sosai, inda wani less ya ɗauki hankalina na siyo mana shi mu uku don muyi anko, na kai ɗinkunan, na so tahowa da islam amma aliyu yace amaida ita gida don gaskiya iyayen sun mana kara, kuma haka ne gaskiya sunyi kara, haka inaji ina gani muka rabu da islam bayan shaƙuwar da muka ɗanyi
sai da da khadija tayi kwna huɗu sannan na kama hanyar lagos tare da aliyu a private plane ɗin sa, ko da muka je a hotel ɗin da yake suka muka, sai da muka kwana ɗaya sannan muka je gidan me jego don yi mata barka, sun yi mamakin gani na sosai
Inda duk inda nabi sai an bini da ido har mamakin mutane nayi wai nice yau na zama abar kallon su,
Ranar suna yaro yaci sunan baban mu abubakar wanda zamu dinga ce masa sadiq, an sha shagalin suna sosai, tun da aliyu ya ajiye ni ban kuma neman sa ba ta ina zan neme sa bayan banni da numbersa, hidimata kawai nake yi har nayi sati biyu da zuwa ba wanda yake takura min balle a tambayi yaushe zan koma
**********
*abuja*
yana zaune a ofice ɗinsa yau kusan kwanan sa biyar kenan kullum sai ya wuni da ciwon mara wata ran ma har hana shi bacci yake yi, na yau na fi na kullum don yau hatta zuciyarsa wani irin bugu take yi kamar zata faso ƙirjin sa
ya kamata in koma china a ƙara duba min zuciyar nan tawa ya kuma faɗa, zazzaɓi ne ya rufe shi wanda hakan ne ya sa shi kashe ac ɗin da ke office ɗin tare da ƙudundune kansa akan couch ɗin da ke ɗakin daga nan bai san inda kanshi yake ba kuma again
Farkawa yayi ya ganshi a gadon asibiti, tare da ƙarun ruwa a hannun sa, ko da yayi yunƙurin tashi sai ya kasa duk jikin sa ciwo yake masa gashi har yanzu zuciyar tasa batai masa yadda yake so ba, ƙara kwanciya yayi ya zubawa ceiling ɗin ɗakin ido wasu hawaye suna zuba da idanun sa,
turo ƙofar yaji anyi tare da sallama , tj ne ya shigo da kaya a hannun sa ya nemi wuri ya ajiye su, rufe idon sa aliyun yayi kamar yana bacci
"har yanzu baka tashi ba" ya faɗa, komawa yayi kan kujera ya zauna yana mamakin ya baiga zainab ba, ɗauko wayarsa yayi don ya kirata yaji lfy bata zo ba mijinta a kwance a asibiti, nasan halin ta tsab ƙila wani abinne ya hana ta zuwa
**************
*lagos*
ina kwance a ɗakin khadija muna hira da maryam da me jegon, waya ta tayi ringin sunan tj nagani don haka nai saurin ɗauka ina murmushi
"nayi fushi sai yanzu ka iya kirana ka ce min ƴata taje gida ko" na faɗa
"yi haƙuri yayata wallahi na ɗauka salmar ta kira ki ne" ya faɗa, ba haka na saba jin muryar tj ba idan muna waya, magana zanji yana yi kamar zai tsaga min kunne amma yau naji shi a sanyi sa don haka sai na sha jinin jikina
"lafiya ko tj naji ka kamar akwai wani abin"
"kina ina yanzu" ya tambaye ni
"ina lagos ƙanwata ce ta haihu nazo suna, amma in shaa Allah na kusa dawo wa"
"baki son mijinki ba lfy ba, gashi akwance a asibiti" jin an anbaci asibiti yasa ni tashi zaune ba shiri
"me ya same shi lfy lau muka rabu da shi"
"tun jiya da yamma aka tsince a asibiti a sume aka garzayo da shi asibiti" shiru nayi, na rasa abinda zan faɗa, dama bashida lfy ne be faɗa min ba na faɗa araina
"ban sani ba amma bari kaga yanzu zan haɗa kaya na inyi airport, Allah yasa in samu flight"
"in kinsamu sai ki kira ni sai in samu driver ɗin da zai ɗauko ki daga airport ɗin in kin iso"
"ok"
sallama mukayi inda sai da muka gama sannan na fahinci gabaɗaya hankalin su yana kaina
"lfy yaya, me ya faru waye ba lfy" duk suka jejo min tambaya
"aliyu ne akwance a asibiti ba lfy"
"subhanallahi"
"tafiya zanyi yanzu Allah ysa in samu jirgi"
"muje in raka ki airport ɗin"inji maryam
minyi sallama da khadija sannan muka kama hanyar sai da naje gida don haɗa kayana nan muke sanar da mama ita ma tace da ita za a je airport ɗin ni dai sauri kawai nake yi, ƙanina ne ya kaimu wanda yake bin maryam ɗan wajen mama, don haka na dinga azalzalar sa ya yi sauri
ko da mukaje airport ɗin na barau da kwaso min kayana ni kuma na tafi counter ko Allah zaisa in samu, luckily 4 me kuwa akqai jirgin da zashi abj a lkcn boarding ma yake yi don haka na biya
"madam babu commercial sit sun ƙare" ta faɗa haushi ne ya kamani yanzu take cemin flight ɗin yana boarding yanzu kuma sits sun ƙare,
"sai dai in kina iya biyan vip" ta faɗa ayangance, harara na daka mata
"ke ni ko kusa da pilot ɗinne saka ni" na faɗa mata ai kuwa nan da nan ta ciri kuɗin su a atm card ɗin dana bata ta cike min na karɓa nayi gaba abina
Naje wajen su mama na karɓi kayana mukayi sallama sannan na kama hanyar hawa jirgi ku sai ku ɗauka vip ɗin wani abin arziki ne mtss nai tsaki babu wani banban ci kawai dai kujerun sunfi ɗan girma ne da kuma ɗan space tsakanin su
tj na kira na faɗa masa na taso yai mamakin samun jirgin da nayi da wuri hakasannan yace min kafin in ƙaraso zan tadda driver na jiranamu kai sallama na kashe wayata sai fatan Allah ya sauke mu lfy
*************
*abuja*
mun sauka lfy inda na tarar da driver yana jirana, na shiga muka kama hanyar asibitin, ko da na shiga ɗakin yana zaune akan gadon da bowl na abinci a gabansa, yai mamakin ganina inda naga ya juya ya doka wa tj harara daga gani yayi warning ɗinsa na kar ya gaya min, shi kuma tj ɗin sai yayi kamar bai gani ba, ya rame sosai sai fari da yayi fayau haka
ƙarasawa nayi kusa da shi ina yi masa sannu tare da zama akan gadon na ɗauko bowl ɗin ind naci karo da farfesun kayan ciki, fara bashi nayi, da farko kamar bazai karɓa ba amma da yaga na tsire shi ido kuma naƙi sauke hannu na sai ya bude bakin sa ya karɓa, cokali buyi yayi naji yace
"wasshh Allah na" tare da dafe ƙirjinsa
"sannu" muka haɗa baki nida tj
"ƙirjin ne again bari inje in kira likitan yazo ya kuma duba ka" tj ya faɗa yana fita, na ci gaba da bashi farfesun kaɗan ya kuma karɓa yace ya ishe shi, ajiye wa nayi na ɗauko hanky na ɗan gyara masa bakin sa sannan na ɗauki bowl ɗin don in mayar inda hakan yai dai dai da shigowar dr. ɗin da tj
"sannu ya jikin" dr ya faɗa yana buɗe file ɗin da ya shigo da shi
"ina ne yake ma ciwo" ƙirjin shi ya nuna dai dai in da zuciyarsa take
"sannu ai na baka pain reliever amma ina ƙara tuna maka ana sallamar ka kaje a ƙara duba maka zuciyar nan taka, cikin ya hdaina ciwo"
"zan je in shaa Alla ya daina"
"ok shiike nan ba wani matsala da ka ɗan ƙara warware wa sai a sallame ka" Inji dr
"ok dr mun gode" muka haɗa baki
ko da dr ɗin ya fita sai tj ya ƙara matsawa kusa da aliyu
"ɗan uwa me yake damun zuciyar taka" ya tambaye shi, nima abinda nake son ji kenan don haka sai na mai da hankalina akan aliyun inji me zai ce, ɗagowa yayi muka haɗa ido wanda hakan ne ya sani sauke nawa idon ƙasa
"ba komai kar ka samu damuwa, zuciyar tawa ce wani lkcn sai ta dinga bugawa fiye da yadda ya kamata"
"tun yaushe" ya kuma jeho masa da tambayar
dafe ƙirjin nashin da yayi ne tare da kiran sunan Allah yasa tj ɗin daina masa tambayoyin da yake masa
"tj ɗan kwantar da ni in huta na gaji da zaman, ita ma ka kaita gida ko ta samu ta ɗan huta tunda daga tafiya take"
ni da kaina naje na kwantar da shi sannan nace wa tj ka tafi kawai zan cigaba da kula da shi, kallo na aliyun yayi baice komai ya lumshe idon sa sai bacci, gyara masa kwanciyar nayi sannan na koma gefe na zauna tj yayi mana sallama shima ya tafi ni kuma na hau tunani na
kar dai ace ni na sawa mutumin nan ciwon zuciya, kai yama za ayi ace ni na sa masa yaushe muka haɗun da zan sa masa wani ciwo, to wai me yasa a zuciyar sa haka har ya kamu da ciwo kana da kuɗi me zai dame ka na faɗa arai na nai ta wasuwasi na har nima baccin ya kwashe ni ban daina tunanin me yake damun aliyu ba
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :20🌹
Kwanan mu 15 a asibitin sannan a ka sallame mu ya samu sauƙi sosai kuma zuciyar tasa ta daina masa ciwon, amma duk da haka likita yai masa tunin na cewar ya koma ya kuma ganin likitan sa, inda sai daga baya ya faɗa mana cewar shekarun baya ne yayi fama da ciwon inda yake ganin likita a china,
a irin jinyar da nake yi na fahinci cewar tsabar sha'awr da tayi wa aliyu yawa ce ta haddasa masa ciwon cikin wanda shine ummul aba'isin tada ciwon zuciyar tashi, rasa abinda zance nayi da dr ɗin yayi min bayani lkcn da naje office dinshi karɓo takardar sallama, na kuma kuɗiri niyya a raina in shaa Allah in dan tanine Mijina bazai kuma ciwon zuciya ba, babu yadda banyi ba mu saba da shi tun a asibitin amma ƙiri ƙiri yaƙi sai ko ya tsiri baccin ƙarya har na gasken ya tadda shi ko kuma dai ya ɗauki qur'ani ya tsiri karatu
Ko da muka koma gida direct ɓangarensa muka nufa sai da naga ya kimtsa yai wanka ya sha magani ya kwanta sannan nima na wuce part ɗina don inɗan kimtsa
a gare na tadda da shi kamar da mutun nasan ta wannan ɓangaren bani da matsala ɗan watsa ruwa nayi ajikina sannan na shiga yau so nakeyi inyi wa mijina abinci da kaina
Tuwon semo na tuƙa masa da miyar egusi wacce na soya egusi ɗin da ƙwai yadda egusi ɗin zai duddunƙuƙe sannan ya kakkama ragowar kayan da ke cikin miyar, sai farfaesun catfish, sai zoɓo naji ance zoɓo ma magani ne
tun da nazo gidan ban taɓa ganin anyi mana abincin mu na gargajiya ba sai na bature, don haka yau na canza salon da kaina, ko dana gama wanka nafaɗa inda sai da na shafe kusan minti talatin dani da yi masu yimin kwalliya don in fito fes da ni
wata yellow strapless riga na ɗauko wacce iyakacin ta rabin cinya na saka, bata hannu, sai zip a bayan ta, ta kamani sosai tai min ɗam kamar dama jikina aka gwada aka yi rigar, suma sai yaba min suke yi yadda nayi, a zuciyata nace balle kuma shi wanda akayi domin sa
a back yard garden ɗin mu nasa suka jera min abincin sannan na shiga don inga ko ya tashi, yana zaune akan sallaya daga gani ya idar da sallah ne, samun wuri nayi na zauna kusa da shi har ya idar muka shafa tare
"ka zo muje kaci abincin ka" na faɗa ayangance
"ok ganin nan zuwa bari in ninke sallayar na" karɓar sallayar nayi na fara ninkewa
ko dana juyo zan masa magana sai na tsince shi yana kallona, kau da kansa yayi tare da yin gyaran murya
"muje ko" ya faɗa, noƙe kafaɗa ta nayi tare da zunɓuro baki
"ni dai sai ka ɗauke ni" na faɗa ashagwaɓe, murmushi yayi tare da kauda fuskar sa gefe
"in banda abinki kina ganin banni da lfy kice in ɗauke ki"
"to zaka ɗauke ni knka warke" na faɗa tare da matsawa kusa da shi har ƙirjina na shafen sa, murmushin ya kuma yi
"muje muci abinci yunwa nake ji"
hannun shi naja muka ƙarasa garden yai mamakin yadda nasa aka tsara wajen yai kyau sosai har kasa shiru yayi sai daya tanka
"welcome back party na haɗa maka" na faɗa masa a cikin kunnen sa wanda sai danayi ɗage sannan na faɗa, ɗan janye jikinsa ya ɗanyi daga nawa sannan ya samu wuri ya zauna, ko dana zuba mai abinci nan ma naga mamaki tab fuskar sa amma baice komai ba
malmala biyu yaci sannan ya sha zoɓo sosai, kana ya gode wa Allah
"daga ji yau ba abincin cook na ci ba" ya faɗa da fara'a a fuskar sa
"girkin matar ka" na maida masa da martani
"gaskiya yai daɗi kin cancanci kyauta, yaushe rabon da cin abincin gargajiya mai daɗin wannan tun hjy na da rai" jikina ne yayi sanyi
"hjyr ka da muka yi waya da ita a beach itace ta rasu"kallon mamaki ya binki da shi
"baki sani ba" girgiza masa kai nayi da alamar tausayi a fuskata, nan ya shiga bani labarin mutuwar ta da ɗaurin auren mu da guduwar da yayi, ta tausaya masa sosai wai ace mijina ne ya shiga wannan halin amma ban sani ba, koda yake ba laifi na bane duk rashin sani ne ya kawo haka, amma in sha Allah na sha alwashin sai na zama mace me shayar da mijin ta daɗina faɗa araina
ƙara tausar shi nayi tare da bashi haƙuri akan rashin hjyrsa
"haba ba komai ai yanzu ya zama tsohon zance" ya faɗa, shiru ne ya biyo baya, ganin shirun na naiman yin yawa ya sani na ce
"kace zaka ban tukwicin girkin" na faɗa ina karyar da kaina
"nawa kike so faɗi" rufe ido na nayi na ɗora hannuna akan lips ɗina tare da cewa
"guda goma" shiru naji kmar ba mutum a kusa da ni hakan ne ya sani buɗe ido na, yana zaune bai motsa yana kallona,
"baka ce komai ba ko bazaka bada tukwicin ba" murmushi yayi ya jamin hancin na taer da miƙe wa ya kama tafiya, binshi nayi ina shagwaɓar kaifa kace zaka bani tukwici har muka shige ɗakinsa ina yi masa mita shi kuwa ko ƙala baice ba sai ma ban ɗaki da ya shiga wanda ni kuma na samu wuri a gadonsa na kwanta
da daddare bayan na gama komai na koma ɗakin nasa don in kwanta, a kwance na same shi inda nima naje na kwanta kusa da shi, ban daɗe da kwanciya ba ya tashi ya shiga banɗaki, da alwalar sa ya fito ya tada sallah, tun yana yi ina ƙirga raka'a nawa yayi har bacci ya kwashe ni be idar ba, sai ji nayi ana cemin ki tashi an kira assalatu
tashi nayi ina yin magagi don zuwa toilet nan naci tuntuɓe da shinfiɗar sa wato kenan ma a ƙasa ya kwana kenan ko na faɗa araina, raina bai min daɗi ba me yasa yake min haka na faɗa araina, toilet na faɗa nayo alwala ta na fito na tada sallah, har na idar nayi lazimi na tare da azkar bai dawo ba don haka kawai sai na ɗan gyara gadon tare da kwashe shinfiɗar tasa nai part ɗina don haɗa mana breakfast
*************
wasan saurayi da budurwa muka koma yi nida aliyu inda sam baya wani sakan min fuska sosai ba kasa fai ba ma ya fiya magana sai dai in nayi abu yayi murmushin nan nasa, babu wani irin technich da ban bi ba don ganin na jawo hankalinsa kaina a banza wai an shuka dusa, kai da ƙarshe ma daya ga abin nawa ba na ƙare bane sai ya tsiri azimi da sallah dare, ina shigowa ɗakin in ya tsiri sallah har sai na yi bacci yake dainawa ga idon nawa da shegen son bacci kamar na kasa, azimi kwa kullum kusan yana cikisa wai irin azimin annabi dauda yake son yi
Yau ta kama monday an tashi da sanyi sosai kasancewan ruwan saman saman da aka kwana ana tafkawa, kuma har yanzu anayi don aliyu ko masallaci baije ba don ruwa a ɗakin sa mukayi tare, ko da muka idar na yi lazimina tare da azkar na idar sai nazo gaban sa yana jan carbi
"yallaɓai me zaka karya da shine yau inje in haɗa maka da wuri"
"jekiyi kwanciyar ki yau azimi nake yi"ƙwalalo ido nayi yau monday fa"
"to menene ba a ai ranar monday, azimi me falala ma da ma'aiki (saw) da kansa yace muyi, ai banga me zai sani ƙinyin azimin yau ba" girgiza kaina nayi lallai ma mutumin nan na faɗa araina, jiya fa yayi lahadi amma shine yau ma ya tsiri shi
tashi nayi naje na ɗibo ruwa afrigde na zo zan wuce kenan nayi tintiɓe ruwa ya ɓare tas a kan shinfiɗar malam aliyu sarkin azimi da ƙiyamul layli, baice min komai ba ganin haka ne ya sani kwasar shinfiɗar nayi tafi don in shan ya masa
haushin daya bani yasani shanya masa kayan shinfiɗar tasa aruwa, nima garin mugunta ƴar nightie ɗin da ke jika na ta jiƙe, cire ta nayi na ɗaura zani na kwanta, ko daya tashi kwanciya yaje yaga a inda na shanya masa kayan sai ya dawo
"matsa can ƙarshen gadon zan kwanta" naji yace, bance komai ba na matsa sosai har ina ɗan takure kaina da jikin bangon don kar jikin mu ya haɗu, lallai ma wannan mutumin in kasan wata ai baka san wata ba na faɗa rai na
kwanciya yai tare da jan bargo ya rufe kanshi, bai daɗe da kwanciya ba aka doka wata irin tsawa wacce tasani wurgi da zanin da ke jikina na shige cikin bargon nasa tare da maƙalƙale shi
"lfy" naji yace
"tsoro nake ji" na bashi ansa
"tsawa ce ba komai koma wuri ki" ƙara maƙalƙale shi nayi tare da sa masa kuka
"ni tsoro nake ji" kuma wallahi ba qani tsoron tsawa da nake ji
"shhhhhhh its ok" ya faɗa yana ɗan shafamin bayana alamar lallashi
"wait tsaya ba kaya a jikin ki" ya faɗa, ƙara rushe mai nayi da kuka tare da kara shige masa jiki
"sshhhhh nace ya isa haka ko ai gani akusa da ke ba inda zanje" ya faɗa tare da cigaba da shafe min jikina wannan karan bada sigar lallashi bane
nidai bansan hawa ba ban san sauka ba sai dai kawai jinayk minkna ya maida ni cikakkiyar mace thank u thank u thank u shukran shukran kawai yake faɗi duk kunyar shi sai ta kama ni, ko da muka ɗan nitsa sai naji ya jaa min hancina
"auch, da zafi fa"
"naughty girl kin karya min azimina" kunya ce ta kamani na ƙara shige wa jikin sa, shi kuma ya ƙara rungumeni tare da zuba min ruwan kisses😘😘😘😘😘
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*ya muka ji da alamar shigowar sanyi Allah ya sa mu wuce lfy, mata sai a tanadi kayan harka😜😜 don kuwa maza in akace sanyi yayi abin sai a slow da fatan zamu dinga kula da tsaftar jiki Allah yasa mu wanye ƙalau*
0 comments:
Post a Comment