Zainab tana zaune duk abin duniya ya ishe ta bata taɓa ɗaukar cewar zata daɗe haka ba ba tare da ƴaƴan ta ba amma gashi yanzu kusan watan ta ɗaya har da sati, kullum ta tashi matse nonon ta takanyi kukan yaushe Allah zai haɗa ta da ɗan ta,
Ita shap tama manta cewar ita ce ta ɓoye kan ta duk laifin ɗorashi take yi akan aliyu, kuka ne ya kwace mata tana me tausaya wa kanta, Allah ya taimake ta ma iya bata nan ta tafi biki ita kaɗai ce aɗakin
ganin shirun yayi yawa yasa ta ɗauko wayar ta da tun ran da ta bar gidan aliyu ta kashe ta bata kuma kunna ba ta kunna don ta shiga watsapp ko zata ga abinda zai ɗebe mata kewa ta daina tunanin don kar ta haifar wa kanta wani ciwon
Saƙon ni ne sosai suka dinga shigo min waya kamar zasu tsaga wayar yawanci na grps ne sai kuma na ƴen uwa da suke ta tambayata ina na shiga, ashe aliyu ya je gidan mu ke tunda gashi ance mijina na nemana
banda lkcn sa na faɗa, saƙin mimma ne ya ɗauke min hankali sosai tambataya take ƙfy ta kuwa kwana biyu saƙon sun fi ɗari duk na tambayar ina na shiga ne
ɗaukar wayar nayi na danna number ta don inkira ta, don gaskiya ina neman wanda zanyi magana da shi in ji daɗi, ni ƴar adam ce don haka dole at stage ɗin da nake i really a shoulder to lean on an cried ma heart out,
kun san wani lkcn baka san mutum ba amma zaka ga u can talk to him musamman ma yanzu social media freinds some will love u honestly kuma zasu iya baka shawarar da zata fidda ka cikin tashin hankali don haka mimma na ɗauke ta kamar irin mutanen da ban sani ba amma zata iya bani shawarar da zata kwantar min da hankali
ringing biyu ta ɗauka tare da cewa
"ma za hadatha laki, ma hadatha li jawwala tiki, ai na dakalti,"
kuka kawai na sakar mata don gaskiya i really need to cry ina bala'in son yi kuka sannan in samu me rarrashina, bata hanani kukan ba sai da nayi me isa ta sannan na yi tare da cewa
"good day mimma"
"how dy, habibti"
"fine" Na ansa shiru ne ya biyo baya daga ni har ita
"habibti will u like to talk about wats rong wit u" ta tambaya
na shiga rattabo mata yadda mijina yake da matsala da da *dangin sa* da yadda matsala ta juye kaina, na faɗa mata komai bata katse ni ba har sai da taji na yi shiru alamar na gama sannan ta fara
Mimma ji tayi kamar zainab ɗin ta fama mata wani mugun ciwo da har yanzu yaƙi warkewa acikin rayuwarta, har gobe idan ta tuno da ɗanta daya rasu, sai tayi kuka duk rashin hankali da ƙuruciya da yasa ta tafiya ta bar ɗanta a hannu wanda bata sani har yayi sanadiyyar rashin ɗan, har gobe gani take yi da bata bar ɗan ta ba da ƙila yana nan yana rayuwar shi kamar kowa, hawaye ne taf idon ta zuciyarta tai mata ɗaci kamar zainab ɗin tana tariyo mata tarihinta ne da labarin da take bata sai da ta ɗan nutsa sannan ta fara magana don gaskiya bazata bari yarinyar nan ta tafka kuskuren da ita ta tafka ba wanda hanyanzu yake bibiyarta, ya ƙi kyale ta har gobe tana mafarkin ɗan ta
"habibti da farko dai baki kyauta, tayaya ɗan ki zai shiga tsakanin faɗan ki da mijinki" faɗa sosai mimma tayi min kamar ta ari baki tana yi kuma muryata na rawa kamar wacce zata yi kuka
mimma tayi faɗan ta dosai wanda ba abinda nake yi sai shesheƙar kuka inda itama kaga jin yadda take maganr kamar kuka take yi
"kuma abu na ƙarshe da zan faɗa miki shine ko ki koma gidan mijinki ko kuma ki sa aɗauko miki ƴaƴanki ki riƙe kayan ki, don banga zaman me kike yi ba babu ƴaƴan ki a kusa da kesalam" ta faɗa tare da kashe wayar
jikina ne duk yayi sanyi duk kalmar da mimma ta faɗa gaskiya ne uwa da tausayi aka santa, to yanzu ya zata yi, zata koma ne ko kuma zata sa aɗauko mata ƴaƴan ne
kai komawa gidan aliyu ba option bane bani da niyyar komawa zaman gidan sa har sai ya sauko daga fushin da yake yi da *dangin sa* sannan zan saurare shi ta faɗa a ranta
To yanzu wa zansa ya ɗaukƙ min ƴaƴan nawa, na tambayi kaina, su linda da rebecca ba zasu taɓa kwaso min ƴaƴan nan ba don kuwa tsoron aliyu suke ji, na fi son in samu wanda baya shakkar aliyu ko kaɗan
tj ne ya faɗo min a raina ina rawar hannu na ɗauko wayata na danna number sa lallai tj ne kawai zai iya taimaka min a wannan harkar don shine kawai baya tsoron aliyun kuma aliyun be isa yace zeyi masa barazanar sa ba na faɗa
tj yana zaune a falon gidan aliyu tun da suka dawo daga lagos ya kasa tfy don ya fahimci aliyun yana cikin tashin hankalin rashinganin zainab ya san daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba, ko kuma yace don ƴaƴan sa amma daga ganin sa ba acikin kwanciyar hankali yake ba
Kusan kullum yaran basu da lfy barin ma haidar kusan kullum da zazzabi yake kwana mohd de nashi da ɗan sauki sosai tunda yanzu gudawar da sauƙi sai dai amai da yake akai akai wanda kuma ba laifi be wani ji jiki ba kasancewar yana shan ruwan gishiri da sugar, ya tausaya wa yaran sosai faɗan iyayen yaran ya shafe sun bashi tausayi sosai
wannan ne dalilin daya sa shi kasa komawa kanoya ɗan zauna ko dan yaran, wayar shi ta fara ringing, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya kai hannu ya ɗauko ta
ganin harafin *yayata* akan screen ɗin ya sa sji daga wayar jikin shi na rawa
"ina kika shiga" shine kawai abinda tj ya iya faɗa
kuka na saka masa tare da yi masa bayanin halin da nake cikinsa na son ganin ƴaƴa na
lallashina yayi tare da neman sanin inda nake, sai da na sashi yai min alƙawarin ba zai faɗawa aliyu ba kumabtare da min alƙawarin zai kawo min ƴaƴana sai na faɗa masa ina gidan iya
tj yayi mamaki sosai sannan yace mata yana abujan ya faɗa mata irin halin da yaran suke ciki ya kuma roƙe ta tadawo, kuka sosai na sakawa tj tare da roƙar sa ni dai kawai ya kawo min ƴaƴana, babu irin rarrashin da tk be yi min ba amma naƙi daga ƙarshe dole ya haƙura akan zai kawo su mukai sallama da niyyar zai taho kano yau da su
daɗi naji sosai tare da godewa Allah da kuma tj ɗin da zai kawo min ƴaƴana bayan na ɗauke tsammanin ganin su kusa
tj ya sa su hannatu haɗa masa kayan yaran sannan ya kama hanyar kano a jirgi shi kanshi hankalin sa zai fi kwanciya idan yaga ya sada ƴaƴan dabuwar su, don ta aliyu me saƙi ne duk lkcn daya sauko ya so su shirya ya kai kansa
magariba ce ta kawo tj kano, direct jakara ya wuce ya samu zainab ɗin tare da bata ƴaƴan ta, yai mamakin yadda yaga haidar ya wani kwanta a jikin na ni kuma ina shafa shi yadda nake idan zaibyi bacci kan ace meye wannan kuwa tuni bacci ya kwashe shi, shi kanshi mohd ɗin da yake ɗan ƙarami lub yayi ajikina kamar yasan abinda yake yi
na tausayawa ƴaƴa na daga gani ba ƙaramar rashi na sukai ba, tj faɗa ya dinga yi min akan in dinga haƙuri da ɗan uwan sa jin sa kawai nake yi amma aliyu yana buƙatar me koya masa hankali
yanzu hankali na akwance yake yake ganin gani ga ƴaƴa na babu abinda yake gabana yanzu daya wuce a ƙarasa min ginina in tare, kun san ance inda kuɗi kasha kallo to lallai tabbas na yarda da wannan kari maganar don kuwa mutanen nan ginin suke yi kamar ba mutum ne yake yi ba
ba abinda nake yi sai jiran a gama mu tare da bin dare ina gaya wa Allah buƙatata ta ya karkato da hankalin mijina gare ni tare da kawo ƙarshen wannan gabar da ya ke yi da *dangin sa*
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*wannan abu na kishi da mata muka ɗauka muka ɗorawa kanmu don Allah don annabi mu rage, kishi halak ne amma kuma ba irin wannan kishin matan ƙwarai suka yi*
*sannan na biyu masu yaɗawa kuma kuji tsoron Allah a kodayaushe an fi son mutum ya yaɗa alkhairi ba sharri ba, hadisi ne ingantacce ma'aiki (saw) yace "fal yakul khairan auli yas mut``` to kuwa in haka ne don me za a dinga yaɗa abin yake ba alkhairi, don Allah mu daina, don tun ana yaɗa gaskiya har a zo ana yaɗa abinda yake ƙarya, mutane sun manta shap cewar idan ka yaɗa abinda yake ba dai dai akan ɗan uwan ka musulmi ka ɗau haƙƙin sa*
*don haka don Allah abar zancen nan ya wuce abar ita wacce tayi abin taji da abinda yake gaban ta ba mutane sun ƙara mata stress ba, Allah yasa mufi ƙarfin zuƙatan mu*
*wallahi abin nan ya kashe min jiki don haka yau typing ɗin sai kunyi haƙuri da abin da ya samu na shiga vibration, duniya tazo ƙarshe, Allah yasa mu wanye ƙalau*
page 42🌹
ko da aliyu ya dawo gida ya tamabayi yaran sai aka gaya masa tj ya ɗauke su, sai yaji sanyi aransa, amfanin ɗan uwa kenan in bashi ba wa zai masa haka, ko ba komai yaran zasu fi sakewa gidan shi don ita ma salmar uwa ce zata san abinda yaran suke so
Aliyu yana kwance tun da safe ya kasa yin komai, yau yaran sa kusan watan yaran sa ɗaya da tafiya amma tj be taba kiran sa ba wai ko don ya gaya masa ya suke, shi kuma hidima sun masa yawa
ya san yaran sunanan lfy tunda ance inka ji shiri to lfy ce amma ai ya kamata a ce tj ya kira shi ko so ɗaya, shi fa tj ba wani hankali gare shi sosai ba be san abinda ya dace ba da wanda bai dace ba,
ɗaukar wayar sa yayi ya kira tj ɗin don yaji ya yaran suke, ringing ɗaya tj ɗin ya ɗauka
"ɗan uwa ka manta ni" inji tj
"kai fa ba hankali gare ka ba ace mutum kwana nawa da ka kwashe min ƴaƴa amma baka taɓa kira ba" ya faɗa da ɗan faɗa
"ban gane ba, ai ni ƴaƴan ka basa hannu na" Ran aliyu ne ya ɓaci
"ban ga ne me kake nufi ba, na ɗauka tun randa ka tafi akace kai ka tafi da su yanzu kuma kace basa hannu na"
"yayata ce ya kira ni tana kuka wai don Allah in kawo mata ƴaƴan ta ni kuma gani yanda yaran suke ciki yasani kai mata su"
"kana nufin zainab ta kira ka ka kai mata ƴaƴan tashine ka kwashe min ƴaƴa ka kai mata ba tare da shawara ta, me ye haɗin ka da zainab ɗin ba ni bane ɗan uwanka ba amma sai ka koma ka bi bayanta bayan ta guje mu"
aliyu ya ci gaba da faɗan sa wai tj ya ci amanar sa ya kwashe masa ƴaƴa bayan yasan sune kaɗai makamin sa na sawa zainab ɗin ta dawo ko bata so, yai faɗa sosai kamar zai ari baki daga ƙarshe yace
"sai kaje ka dawo da ita kuma wallahi baka dawo da ita ba sai na saɓa maka ba kaɗan ba".
tj dariya ce kawai take cin sa don daga dukkan alama ɗan uwan nasa ya fara missing zainab ɗin in shaa Allah burin su shi da zainab zai biya don zasu yi amfani da wannan damar na ganin sun shirya aliyu da *dangin sa*
zainab tana zaune a tsakar gidan iya ana ta hira da mutan gidan yanzu ko babu komai hankalinta ya ɗan kwanta don gata ga ƴaƴan ta kuma mutan gidan ba ƙaramin so suke nunawa yaran natan ba
kafin ta tashi tayi musu wani abin har an riga anyi musu don haka hutawar ta kawai takeyi sai kuma ginin ta da take jira a ƙarasa, tj garesu ya zama ɗan halak don duk abinda suke buƙata kafin ta fidda kuɗi ta siya ya fitar ya siyo musu don haka hankalin ta akeance shi kan shi aliyun tana ɗan jin labarinsa awajen linda kuma yana nan ƙalau don haka itama sai ta kwantar da hankalinta
pls kuyi haƙuri da wannan hankalina gabaɗaya yau ba ajikina yake ba
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*na gode sosai da tambayar da kuka dinga yi min na ko lfy, wallahi lfy ƙalau jiki da jini ne kawai, da masu yi magana ta prvt da ta grps tanks sosai, ni nayi mamakin ma yadda aka san number ta🤔*
Page :43🌹
A yanzu an gama min gini na, shirin tashi kawai muke yi mu koma, in da ragowar kayan aikin na ce ayi wa iya gyaran ɓangaren ta, iya na bawa jari tana saro icce da gawayin coal, ana sama mata su a ɗakin soro
Ciniki take yi sosai babu kama hannun yaro, don duk mutan gidan nan da maƙota a wurin iya ake siyan icce da coal, sana'ar ta amshi iya sosai har tana kurin ita ba hayen sana'ar sai da icce tayi ba daga wajen mijinta ta gada, idan tana faɗin hakan takan bani dariya🤣 dama agado ne awajen miji
ko da na gama haɗa part ɗin nawa rana ɗaya na saka muka koma, ɗan tsakar gida ne, sai falo da kitchen a ciki sai ɗakuna biyu, kowanne da banɗakin sa
aunty bilki cevta rakani na sissiyo kayan da na saka na gyara part ɗin nawa sosai, ganin unguwar babu wuta ya sa na haɗa mana solar inverter, a gidan don mu rinƙa samun wuta tunda gaskiya ni bana son ƙaran inji, ban san solar haka take tsada ba gaskiya nayi barnar kuɗi sosai wajen haɗa solar amma kuma daga ƙarshe sao gashi ko ima a gidan sun samu wuta
duk zama na agidan babu wanda yasan cewar guduwa nayi sai iya kaɗai kuma ta kwaɓe kar in faɗa wa kowa sai muka barshi da cewar aliyun yayi tafiya ne, a haka nake zaune ba tare da kowa ya san dalilin zama na ba
ganin wuta available ya sani nima na fa siyar da kunun aya duk da dai ina da kuɗi sosai a account ɗina amma ina neman abinda zai ɗebe min kewa sosai wannan ne ya sani fara sana'ar sai da kunnun ayan
Hankalin aliyu yanzu a kwance yake ganin cewar ƴaƴan shi suna wajen zainab amma duk da haka yana son ganin su, don haka sai ya kira tj
"kai ɗan iska sai yaushe zaka kawo min iyalina ne, kana zaune lfy da iyalin ka ni kuma ka kwashe min nawa" shiru tj ɗin yayi don bashi da ansar da zaiba aliyun
" wai baka ji bane yaushe zaka dawo da ita"
"yayata fa tace sai dai ka tako da ƙafar ka kazo biko sannan zata saurare ka"
"bangane ba ba nace ta dawo ba"
"to ai in mace ta bar gidan mijinta dole sai mihin yaje biko, don haka sai ka shirya ka taho kano biko"
Allah tj ka mayar dani sa'an ka, in zaka kaɗo min ita ka kaɗo ta in kuma raina min hankali zaku tsaya kuna yi da kai da itan Allah ya baku sa a" ya faɗa yana kashe wayar sa
tj yana son raina masa wayo yasan zainab tana gidan sa shi yasa aliyun be damu ba don yasan ba inda zata je da ya wuce gidan tj ɗin, to amma yai mamaki da tj ɗin ya baro kano suka je lagos neman zainab ɗin kokuma sai daga baya ta koma gidan tj kai wannan munafuncin nasu ya fara isar sa
wayar sa ya kuma ɗauka ya tura wa da tj da saƙon cewar ya dawo masa da matar sa in ba haka ba sai yayi mugun ɓata masa rai ya tura masa tare komawa ya kwanta
ko da tj ɗin ya ga text ɗin be yi ƙasa a gwiwa ba sai ya kama hnayar jakara, yaje ya faɗa wa zainab ɗin mijinta fa ya dame shi da ya dawo da ita harda nuna mata saƙon da aliyun ya turo
"tj kace masa idan yana son ganina sai dai ya tako ya zo inda nake" tj ne ya ɗauki wayar ki kuma kiran aliyun
"ɗan uwa gani ga yayata tace sai dai kazo da kanka"
"ban gane ba nace mata ka dawo da ita shine zaka zo min da wani zancen banza, kawai ka ce mata ta dawo in ba haka ba zan kwashe ƴaƴa na"
tj ya faɗawa zainaba abinda aliyu yace, ita zainabɗin ta maida nata martanin
"kace masa yanzu ba da bane yanzu na waye" tj ya isar da saƙon zainab
haka suka dinga musayar magana da zance tun ana yin me ɗan dama dama har kowannen su zuciya tayi zafi shidai tj da yaga abin na neman zama faɗa sai ya cewa aliyu
"kasan number zainab ɗin"
"wannan wane irin zancen banza ne"
"to ka kira ta ku tattauna don na gaji naga alamar daga kai har ita ɗin babu me niyyar ɗaga wa ɗan uwan sa ƙafa ka kira ta sai ku shirya"
"zan maka rashin mutunci tj ba kai kazo ka ɗauke min ƴaƴa na ka kai mata ba, da ba ka kai mata ba zata dinga min abinda take min ne na faɗa maka ka kawo min matata, tun kafin mu raba hanya da kai don duk randa nazo da kaina kanon nan Allah sai ka gane baka da wayo"
"to ni ya zan yi ne tunda ban isa ince ta koma ba tunda tace sai kazo ba sai kazo ba kawai, ai ba a kanka aka fara zuwa biko ba ko"
"bikon yaci uwatar bazan zo ba kuma wallahi ka dawo min da ita"ya faɗa yana kashe wayar sa
tj yau yaga ikon Allah shi fa lkcn da akayi faɗan nan be sani ba amma yanzu ya zama shine ma me lefin, ɗaukar yaran yayi a hoto tare da turawa aliyu ta whatsapp, sannan ya shiga tausar zainab ɗin ko zata haƙura ta koma abujar
Zainab ƙiri ƙiri tace fafur ba zata koma ba sai dai aliyun ya tako ya zo da kansa sannan zata saurare shi ta faɗa kanta tsaye da tj yaga itama babu wani abinda zai mata da zai canza mata ra'ayin ta sai ya kama hanyar gida shi abun su ya fara isar sa kowa yana ji da girman kai kai Allah ya kyauta
ko da aliyu ya buɗe whatsapp yaga pics ɗin da tj ya turo masa ya ga yadda ƴaƴan sa suka koma gwanin ban sha'awa sai yaji duk hankalin sa ya tashi burin sa kawai ya ganshi da ƴen ƴaƴan sa ƙagu sosai ya ganshi cikin iyalin sa amma a gaskiya ba zai iya bin zainab ba ai ya yada girman sa na namiji wai biko to shi tarihi zai fara kafa sunan shi akan namijin da baya biko ya faɗa a ransa
wayar shi ya ɗauka tare da turawa tj da saƙon
"iyalina nace ka dawo min da su ba pic ɗin ƴaƴa na ba kuma idan baka dawo min da su ba zan ɓata maka rai"
ko da tj ya ga text ɗin sai ya turawa da zainab ita kuma zainab ɗin ta turawa da tj reply ɗin "bazan dawo ba sai dai ya tako ya zo inda nake da ƙafar sa"
ta turawa tj, tj yana ganin saƙo ya turawa aliyu, aliyu yana ganin reply ɗin yasan daga zainab ne sai ya rubuta sabon saƙo ya turawa tj ɗin
"sabida ke baki san darajar miji ba shine nace ki dawo zaki ce sai dai in tako koo" ya turawa tj, shi kuma tj ya turawa zainab ɗin
Ko da zainab taga text ɗin nan sai ta rubuta "ka manta lkcn da kore ni ina kuka ka rabani da ƴaƴa na, yanzu in kana son ganina sai dai ka tako da ƙafar ka" ta turawa tj shi kuma tj ya turawa aliyu
ko da aliyu yaga reply sai ya kuma turawa tj wani saƙon inda shima tj ɗin turawa zainab ita ma ta turo masa da reply ya isar da shi ga aliyu
haka suka dinga yi shidai tj ya zama shine middle man inna ya saƙon da be dace ba sai ya ɗan gyara ya tura wa wanda akayi saƙon domin sa, ya so su shirya amma ƙiri ƙiri sai kowannan su ya kuma fusa ta daya gaji da wannan baƙl ɗin da suke yi da shi sai ya turawa aliyu
"in kana son matar ka ta biyo ka, to ka neme ta a number ta na gaji" sannan ya turawa zainab da
"in kina son mijin ki ya biyo ki ki kirashi a number sa na gaji" yana gama wa ya kashe wayar sa gaba ɗaya don yau sun chaja masa ƙwaƙwalwa
aliyu ranshi ne ya ƙara baci yaji haushin yadda zainab tayi musu da shi, da ba haka take ba amma yanzu ta chanja sosai yana mamakon ko a ina ta samu wannan ƙwarin gwiwar yi masa musu da shi
tj ya ci gaba da turawa da aliyu da hoton ƴaƴan sa sai dai in baije inda zainab ɗin yake ba hakan ba ƙaramin farantawa aliyu rai yake yi ba, ta wani ɓangaren kuma yana jin haushin zainab da taƙi dawowa tace sai dai ya zo da kansa
rannan da tj ya turawa da aliyu pics ɗin sai yaga aliyun be buɗe last pic ɗin ba sai yayi mamaki don haka sai ya ɗauki waya ya kira ɗan uwan nasa amma wayar sa akashe take, ya haƙura, haka ya dinga trying kullum sai ace switched off yayi mamakin hakan aliyu baya taɓa kashe wayar sa don haka sai ya shirya ya kma hanyar abuja ko ya duba lafiyar ɗan uwan nasa
ko da yaje yayi mamakin da akce masa aliyun yana kwance a asibiti kusan sati kenan, asibitin ya wuce direct don ganin ɗan uwan nasa
me yasa ɗan uwan sa bashi da lfy amma ya ƙi faɗa masa ko kuma laifin zainab ɗin ne ya shafe shi, yana shiga ɗakin da aliyun yake kwance a zaune ya samu ɗan uwan nashi a zaune yana shan fruit,
ko da tj ɗin ya shiga da sallamar sa aliyun ansa shi kawai yayi tare da kau da kan sa don tj ɗin ba ƙaramin bashi haushi yake ba, ya ƙi dawo masa da matar sa
kusa da ɗan uwan nasa ya samu wuri ya zauna
"ɗan uwa ashe baka ji daɗi ba" be kula tj ɗin ba ya ci gaba da cin fruit ɗin nasa, ya rame sosai daga gani yana jin jiki
"ɗan uwa me nayi haka da zafi da kake jin haushina har baka da lafiya amma ka kasa faɗamin"ya kuma tambayar sa
"me kake so ince maka tunda kaƙi ka dawo min da iyalina gashi har ciwo ya kamani saboda rashin su"
"ɗan uwa tace bazata biyo ni bavya zan yi"
"ba sai ka kore ta daga gidan ka ba in taga bata da inda zata ai dole ta dawo gidan ta koo"
"ɗan uwa ai zainab bata gidana, haba da tana gidana da tuni na kaɗo maka ita"
juyowa aliyu yayi yana kallon tj
"ban gane bata gidan ka ba tana ina kake nufi" sai da tj ya ɗan ƙara gyara zaman sa sannan yace
"tana jakara gidan iya"
hankalin aliyu ne ya kuma tashi me zainab take nufi da zata tafi gidan mutanen da baya ƙaunar ko jin sunan su ta zauna ita da ƴaƴan sajuyowa yayi wajen tj yace
"tun yaushe take gidan ko kana nufin dama tun can tana can gidan shine baka faɗa min ba ka bar min ƴaƴa na gidan da nafi tsana a rayuwata" shidai tj shiru yayi kawai don daman yasan idan aliyu yasan cewar zainab tana jakara yasan sai anyi ɗan ƙaramin yaki da shi saukowa yayi daga kan gadon yana neman hanyar fita tj ne yayi magana "ɗan uwan ina zaka je ne"
"zan je in dawo da iyalina ne don bazan bar su su zauna awannan gidan ba" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗakin tare da bugo ta da ƙarfi tj ya bishi a baya yana kiran ɗan uwa ɗan uwa amma aliyu ko juyowa be yi ba babu yadda ya iya haka ya bi bayan sa shima gwan da ya bishi don daga dukkan alamar aliyun ranshi ya baci sosai da jin zainab ɗin tana jakara
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:44🌹
Duk irin kiran da tj yake yi wa aliyu be kula shi tafiyar shi kawai yakeyi yana hanyar fita daga asibitin, wata nurse ce ta zo da zunmar dakatar da aliyun amma irin kallon da yayi mata yasa ta kaucewa
"malam dr. be sallame ka ba" ta faɗa da ƙarfi
ko kula ta be yi ba sai nine na ƙarasa kusa da ita nace mata
"ki ce dr. ɗin patient ɗin sa ya sallami kansa ya tura bill ɗin office ɗin aliyun za ayi settling, gyaɗa kanta kawai take yi don tana mamakin wannan patient ɗin wai ya sallami kansa shida dr. ɗin yace case ɗin sa is serious it can even call for theater amma shine ya fice
Aliyu kasa jiran suje airport ma yayi yace wa tj kawai su tafi a mota, sai da suka biya ta gidan shi aliyun inda tj ɗin ya ɗan haɗa masa kaya, wand aliyun yai ta mita shi ba zama zaije yayi a kano ba ya na zuwa ya tattaro kan iyalin sa abuja zasu dawo
Suka kama hanyar kano wanda aliyun yake bayan motar sa crv, inda tj yake driving tare da rufe duk gilasen motar da sakin Ac dai dai yadda mutum ze sake, babu abin dabyake tashi face sautin ƙira'a na shaikh mahir al mu'aiqely aliyu yana son ƙira'ar bawan Allahn nan don haka sai yaji nutsuwa tana saukar masa ahankali duk wani baƙin ciki da yake ciki yaji yana yayewa a hankali tuni wani bacci me nauyk yayk awon gaba da shi
har suka iso garin kano karfe 11:15 na dare aliyu yana bacci ba magariba balle isha, tj directly gidan sa ya nufa da shi, don duk son dawo da iyalin sa be isa ya shiga gidan mutane da wannan daren ba,
ko dabya tsayar da motar yai mamakin da har a lkcn aliyun baccin sa yake yi hankalin sa akwance daga ganin ba ya samun bacci, tausayin ɗan uwan nasan ya kama shi sosai, ɗan tattaɓa shi sannan aliyun ya farka, ganin shi a gidan tj ya fara faɗa
"ce maka nayi ka kawo ni gidanɓka ka kaini can inda zainab ɗin take ayau zan kwaso su kuma mu koma abuja a yau ɗin"
"to duk dai abinka ka haƙura ka duba lkc ko inkaga ya dace ka ke gidan a wannan lkcn ga mukullin motar nan ni dai bazan kaika"
Tj ya faɗa masa tare da miƙa masa keys ɗin amma aliyun be karɓa ba sai ma duba agogon sa da yayi, yai mamakin ganin yadda lkc ya wuce haka, ko da yake da yamma suka baro abujar, fitowa yayi daga motar tare da bin bayan tj ɗin inda shikuma tj ɗin yayi masa jagora zuwa inda zai kwana
Wanka kawai ya shiga yayi yaji daɗin jikin sa sosaia kasancewar ya daɗe rabon sa da yayi wani baccin kirki, ko da ya idar da sllah a kan sallayar wani baccin ya kuma kwashe shi, in da tj ya kawo masa shayi don yasan atsarin aliyu baya cin abinci bayan 10:00, ko daya kawo masa sai ya tarar da ɗan uwan nasa ya bacci don haka sai ya ɗan ƙaro masa sanyin ac ɗin tare da lilliɓe shi ya ja masa ƙofa
kashegari da safe tun daya yai sallah asuba ya koma bashi ya tashi ba sai karfe 11:25 na safe gaskiya yayi bacci rabon shi da wannan baccin har ya manta duk sai yaji wani nauyi da yake ji a jikin sa ya ragu, wanka yayi inda yana fitowa ya tarar da tj ya shigo da break fast, be iya cin komai ba sai ɗan tea da slice bread guda ɗaya, sannan suka kama hanyar jakara da niyyar yana zuwa zai kwaso su su koma abj
a daidai inda ake parking a nan tj ya parker don mota bata shiga lungun su iyan da ƙafa suka ci gaba da tafiyar tasu, aliyu yai mamakin har yanzu unguwar ta nan yadda yasanta shekara 20 tun lkcn da ƴaƴan hjy sukai masa wulaƙancin nan, sai kuma in ya zo ganin hjyr sa aɓoye
yana ratsa cikin unguwar amma duk wasu memories na ƙuruciyarsa yana dawo masa kamar a lkcn abin ya faru, sai ya ji ya kuma tsanar unguwar da mutanrn cikin ta don babu wani memory na ƙuruciyar sa da yake tunawa ya ji daɗi duk na ɓacin rai, dake zuciyar sa kawai yake yi amma can ƙasan ran shi gabaɗayan sa aƙunci yake
suna karyo kwanar gidan iyar duk a tunanin shi zai ganshi a rakyakkyaɓe amma ga mamakin sa sai ya ga gidan ya fi kowane gida haskewa, tj kamar yasan tunanin da aliyu yake yi sai yace masa
"kaga gyaran da zainab tayi musu" harara kawai aliyu ya bishi da shi wato da kuɗin shi tazo tana yi musu burga ko to ko ma dai menene daga yau ya ƙare, ya faɗa a dai dai lkcn da suke zuwa ƙofar gidan
Iya ce a tsaye a soron gidan wandabyanzu ya sha fenti suna ciniki da me man ƙuli haidar a goye a bayan ta, tun da aka kawo su kullum in dai ze yi bacci sai iya ta goya shi haka ta saba masa don haka ko bacci yaji sai kawai ya ɗauko zani ya taho wajen iya, ita kuma bata gajiya sai ta saɓa abinta abaya tai ta hidimar ta,
Aliyu yai mamakin ganin haidar a bayn iyar ba haka yayi tunanin zai samu iyalin nasa ba, tj ne ya fara sallama, iya ta juyo zata ansa amma sai taci karo da fukar aliyu, mamaki ne cike taf a fuskar ta amma sai ta dake kasancewar ta kasa karanta halin da yake ciki
"ahmadu kune tafe da ranar nan" iya ta tambaya
" mune iya mun biyo matar mu ne" tj ya faɗa da niyyar ya ƙona wa aliyu rai ai kuwa ya ci karo da wata muguwar harara
"ai kun kyauta" inji iya
Aliyu ne ya ƙarasa bayan iya don ya karɓi ɗan sa, amma abin mamaki sai haidar ɗin ya noƙe kafaɗarsa tare da ƙara shigewa cikin iyar, tj ne yace
"ai wannan in iya ta ɗauke shi babu wanda ya isa ya raba su sai don ganin kansa"
Janye hannun sa aliyu tare da ɗan basarwa,
"amadu ka raka shi mana wurin abun ko kuma tsaye anan ga zafi ga rana"
"to iya ai da wai mufara gaisawa da ke ko, ina wuni" inji tj
"lfy lau kun zo ƙalau" tj ya ansa Allah Allah yake aliyun ya gaida iyar amma sai yaji shiru, can kuma sai yaji aliyun yace
"ina yuni ya muka same ku" kamar baya so haka yayi gaisuwar
Iyar ta ansa da fara'ar ta tare da tambayar shi hanya, ya ansa ba yabo ba fallasa, sannan tj yayi masa jagoran cikin gidan
Tas tsakar gidan yake shima ya sha gyara da siminti wanda akayi masa gyara bayan an gama min, kowacce mace tana ɗakin ta kasancewar zafin da ake tafkawa ga babu wuta, sai solar da aka kunna inda kowacce ta gudu ɗaki ko tana kallo da iyalan ta tana shan fanka ko kuma dai sina shan fankar kaɗai
Ko da su aliyu suka shigo gidan a share yake tas ba kowa don haka directly bangaren zainab ɗin suka wuce wanda aliyun yai mamakin ganin ita ma wai bangaren ta daban
Zainab tana zaune a falo ta gama girki kenan ta ci tana jiran kiran sallah tayi ta ɗan kwanta, gaskiya yau ana ƙwalla rana sosai
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin naji wanda hakan ya dawo dani daga tunanin zafin da ake dokawa
"waye"
"yayata nine"
"lallai tj yau an kawo mana ziyara ne gaskiya baka gajiya Allah ya saka da alkhairi, da ɗan uwan nan naka zai ga yadda kake kula da iyalinsa da ya wulaƙanta da ..................."
Maƙwat na haɗiye ragowar maganar da zanyi ganin aliyu a bayan tj lkcn dana buɗe kofar, duk sai naji kunya, matsa musu nayi suka shigo, tj dariya ce take son suɓuce masa ina kallon shi yana toshe baki tare da kallon aliyu wanda shi kuma ya haɗe rai daga gani be ji daɗin maganganu ba
Suka shigo kowa ya nemi wuri ya zauna
"tj ina wuni ya salmar ta daɗe bata leƙo ni ba" na faɗa da ɗan borin kunya ta
"Tana nan tace ma in gaishe ki"
"ina wuni" na juya na gaida gogan wanda gabaɗayan hankalinsa yake kan mohd wanda yake dabo yanzu
Tashi yayi yaje ya ɗauko ɗan ɗan nasa tare da rungume shi daga gani yai missing ɗin shi sai ya bani tausayi, shin shina shi kawai yake da sunbatar sa duk sai na tsargu na raba wannan soyayya, tashi nayi tare da shiga kitchen na haɗo musu abinci
Ko da na kawo sai da tj yayi wa aliyu magana sannan ya sauko ya fara ci don gabaɗaya hankalin sa yan kan mohd
Saukowa yayi ya zauna tare da taƙwashe ƙafar sa ya fara cin abinci tuwon shinkafa ne da miyar kuka wadda ta sha wake sai tantaƙwashi ga kuma man shanu wannan ne yasa aliyu babu abinda yake yi da ya wuce loma
Sai da suka ci suka ƙoshi sannan na kwashe kayan, aliyu ya so bayan sun gama cin abinci tj ya tafi, Amma tj sai ya gyara zama ya fara hira da zainab
Tun be lura ba har ya lura da kallon da aliyun yake masa kan ya fita don har nuni yake masa da kai inda yake nuna masa hanyar ƙofa amma sai tj ya yi kamar be san me aliyun yake nufi ba
Ai har yanzu ban gama wana ka ba, tj ya faɗa a ransa, sam ban san wainar da suke toyawa ba don hankalina gabaɗaya yana kan tv, na kan dai ji dariyar tj akai akai, ashe kunna mutumin yake yi
Kiran sallahr azahar ce ta katse mana hirar tamu
"sai ka tashi mu tafi masallaci" inji aliyu
Miƙewa sukai yi,
"yayata bari muje muyi sallah sai mu dawo don yau agidan nan zan ci na dare" tj ya faɗa a zolaye ban gane zolayar aliyu yake ba amma naga dai bayan ya gama maganar tasa ya sa dariya, ban kawo komai ba suka fice
Ko da suka fi sai da aliyu ya kai wa tj harbi da ƙafar sa,
"haba ɗan uwa me kuma nayi"
"dan uban ka baka ganin lkcn da nake maka signa ka tashi ka tafi, ka zo ka tsare mutane da surutun ka na banza, har da cewa wai anan zaka ci na daree wallahi muka idar da sallah baka kama gabanka ba sai nayi mugun saɓa maka" ya faɗa yana yin gaba, dariya ce sosai take cin tj amma sai ya dake tare da nuna shi be ma san me yayi
Ko da suka idar da sallah sai suka shiga sabgogin su, basu koma gidan ba, sai bayan sallah isha sannan aliyu ya samu kansa don duk wata kadara tasa ta kano sai da tj ya nuna masa ita, kuma duk da haka basu gama,
Karɓar motar yayi a hannun tj inda ya wurgar da tj ɗin a hanya wai ya nemi hanyar gidan sa don shi be iya cin ƙwan makauniya ba, yj sai ɗan adai dai ta sahu ya ɗauka ya kama hanyar gida tare da murnar shiryawar ɗan uwan sa da matar sa
Har ya kama hanyar gida sai ya ga bazai shiga haka salin alin ba don haka sai ya karkata akalar motar yayi wajen yahuza suya, ya siyo musu tsire da kuma gasashshiyar kaza sai youghurt me sanyi, har ya kama hanya sai kuma ya dawo yace a sake masa irin haɗin da ya siya
Sai ƙarfe tara na dare ya shiga gidan yana nan dai tsakar gidan shiru, ɗakinɓiya ya shiga direct inda yaci karo da ƴen uwan baban sa
Sun gaisa amutunce sannan ya zauna kowanne sai ya rasa abinda zai ce don ba sabawa suka yiba, da aliyun yaga shirun yayi yawa sai kawai ya ɗauko ledar yahuzar guda ɗaya ya miƙa wa iyar
"ga wannan kici" ya faɗa atakaice
"an gode Allah yayi albarka, ya ƙara buɗi"
A ciki ciki ya ansa amin ɗin, ya miƙe yai musu sallama tare da fita daga ɗakin ya nufi ɓangaren zainab ɗin
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*wannan page na wata me ƙwadayi ne da tace zata ciii yahuza suya kin san kanki ko sai na kama suna*
🍗🍗🍗🍖🍖🍗🍗 *ba a samu yahuza ba amma ga wannan*
*F. B* da ke nake 👈🏻😉
Page :45🌹
Tun bayan azahar nake sa ran dawowar su amma sai naji shiru, bayan la'asar na tashi na ɗarao na dare, ko dana gama na kintsa komai Wanka nayi na shirya sosai, don nasan yau ba sauƙi iya ta kawo min haidar bayan yayi bacci na haɗa shi da mohd na kwantar da su, don bana son su ɓata mana hirar mu ta yau
ba su suka dawo ba sai ƙarfe 9:10 na dare nayi mamakin dana aliyu shi ka ɗai, ko daya shigo sai nayi masa tayin abinci, sai yace sai ya fara wanka
ruwan wankan na haɗa masa tare da gayyatar sa toilet ɗin, ya shiga ya watsa ya fito, sannan ya canza zuwa ɗan gajeran wando sai ƴar vest kasancewar zafin da ake yi, don ma da wuta
gabatar masa da abinci nayi tare da tsarabar da ya kawo yaci ba yaba sai ya ce
"naman ai na siyan baki ne kin ga ban isa in ci ba sai da yardar ki" kunya ce ta ɗan kama ni wai siyan baki
tura masa plate ɗin nayi gaban sa
"muci tare"
"ni na isa yanzu inna ci wayasan ina za akuma guduwa" Ya faɗa a zolaye ɗan murmushi nayi, duk na kasa sakewa sai kace ba aliyun da sani ba duk ya wani rikitani
"ai nace kaci ko ba inda zan kuma tafiya"na faɗa kaina a ƙasa
"ban yadda sai dai a bani a baki" wata sabuwa inji ƴan caca
rasa yadda zanyi na yi ƙatse min tunanin yayi
"to kinga alamar da naci da na ciwo wa kaina kenan tunda gashi kinƙi ki bani da kanki"
gutsuro tsokar naman nayi na kai masa bakin sa, riƙe hannuna yayi wanda hakan ya sa na kalle shi cikin idon sa
"pls habibti kar ki ƙara guduna kinji, u r my everything u nd d kids r all i have"
gyaɗa masa kaina kawai nayi hawaye taf idona
"i really miss u dat it really aches here" ya faɗa yana kai hannuna me naman zuwa wajen zuciyar sa, sakin naman nayi don sai in ɓata masa rigar sa
"pls stay by my side am not perfect buh i will try my possible best nd be a good husband to u"
"i miss u too" na iya furtawa daga ƙarshe, kalmar ta dake shi sosai don ya nuna jin daɗin sa da na faɗa haka
"really den show me how much.............."
Ban barshi ya ƙarasa ba na kai lips ɗin bakinsa inda na barshi ya ƙarasa ragowar aiki
Cak ya ɗauke ni sai bedroom, yahuza da bamu ci kenan, ni kuma mmn waleed da kwaɗayi sai na zauna cin kayana abinda da za suyi a ɗakin matsalar su ne ni dai inyi kwaɗayi na ko da yake bani kaɗai bace can na hango *FAIZA BABA* leƙowa ta taga wulla mata tsoka nayi na cafe da baki oohhh su fa'iza da kwaɗayi
Mun sasanta sosai da ni da mijina inda duk wani bashi da ke kaina ban yi wani yunƙura kasa biya ba tas na biya sai dai sam barka, soyayya muka shiga zubawa ni da ɗan mijina yanzu babu laifi yana kula *dangin nasa* sosai matsalata ɗaya itace shin mahaifiyar sa tana da rai ko kuma bata da rai
Ina son tambayr shi amma sai na ɗan ja ɗan lkc ganin bamu daɗe da shiryawa ba komai a hankali za ayi shi, aliyu be nemi in bishi abuja sai dai yakan je in ya samu lkc kuma ya zo, har da tsaraba yake zuwa da shi ai ta rabo a cikin gidan
Yaran gidan har sun san bbn haidar don in aka ce yana kano, to haka zaka ga gidan cike da kayan ciye ciye ina jin daɗin yadda yake kula da *dangin sa* duk da dai daga gani har yanzu be gama sakin jikin sa da su ba, don baya zama yayi hira da su
Daya dawo ya shiga ɗakin iya suka ɗan gaisa idan ya fito ya dawo part ɗin na baya kuma fita sai masllaci ko kuma in tj ya zo zasu fita shine yake fita, duk ƴen samarin gidan da basu da sana'a ya kwashe su ya basu abin yi, wannan ne yasa mijina ya zama zakaran gwajin dafi,
Yau na tashi gabaɗaya ba na jin daɗi jikina, sai na ɗauka ko yau da gobe ne kun san ance tafi ƙarfin wasa, amma ga mamakina tafi tafi sai abin ya zame min jiki bana jin da daɗin komai sai kwakwa ga miyau da yake yawan tarar min wannan ne ya tabbatar min na kuma samun passenger a tare da ni
Shiru nayi ban faɗawa aliyu ba ko da yazo yai ta dai mitar nayi kyau nayi ƙiba nayi freash ni daɗi na nake ji a kano shi kuma yana abj yana cin kwakwa(wahala)
Duk da nasan ba wani kwakwa da yake ci kawai dai mita ce irin ta ɗan adam yai mamakin ganin yadda nake cin kwakwa ta, sai yace
"ashe bani nake cin kwakwa ba ke kike cinta"
Ko kaɗan ban so y fahici ina ɗauke da ciki don haka sai na bishi da cewar lkcn ta ne shiyasa nake sha'awar ta, ganin yadda nake cin kwakwar nan ba dare ba rana ga miyau ya sa shi ɗauka ta ya kaini asibiti wai ko banda lfy ne, har da cewa
"dauɗar ciki yake damun ki, ke da kika taso cikin yarbawa ya kamata ki din ga shan magani jedi jedi don shan zaƙin ki yayi yawa"
Har muka je asibiti yana lissafo min magungunan dauɗar ciki daya sani, ni dariya kawai yake bani yadda ya daddage da dauɗar cikin nan ko ya zai yi idan yaji dauɗar cikin nawa babyn sa ne
har cikin consultation room ɗin muka shiga tare, dr. ya rubuta sunana da shekaruna sannan ya ɗago ya kalle ni
"hjy me yake damunki" kallon aliyu nayi don ni ba bu abinda yake damu kawai tattago ni yayi ya kawo ni asibiti
"ni dr. babu abinda yake damuna kaga wanda ya kawo ni nan"
Dr. ɗin ya kalle ni da mamaki sannan ya kalli aliyu, sai aliyun yace
"dr. Ƙyale ta dauɗar ciki take fama da shi tai ta tara miyau ga kuma cin kwakwa ba adadi, ni ina tsoron kar tuƙar kwakwarbtai mata illa ne"
Murmushi dr. yayi tare da tambayata last dana ga period ɗin, wannan ya nuna min dr. ɗin ma ya harbo jirgin nawa
Na faɗa masa ya fara ƴen rubuce rubuce sa sannan ya bamu test da scanning, muka je nayi a wajen scanning ɗin ne nace wa aliyu ya biyo ni muje scanning room ɗin
Macece tayi mana scanning ɗin don haka a sake nake ko da ta zo daidai wajen da babyn yake wanda be fi sati 12 ba sai tayi pause din monitor ɗin tare da nuna shi
"alh ga babyn naka" ta faɗa wa aliyu
Shi aliyun da ke gefe har yanzu be san me ake ciki wai shi duk a tunanin sa abinda yake sani zubda miyan ake nema
"baby faa kika ce" ya faɗa da mamaki
"yes kusan 12weeks babyn yake" ta kuma faɗa
Ƙara matsowa yayi kusa da monitor ne amma ba'a iya gani komai sai wani hatsa hatsa don haka sai dabya kai fuskar sa har gaban monitor sannan yace
"ni fa babu abinda nake gani sai wani hatsa hatsa" ya faɗa kuma kalƙon monitor
"alh ai ba a gani sosai kaga har yanzu babyn ba wani fara halittasar akayi ba"
"ok kin dai tabbatar da ba dauɗar ciki bace baby ne" murmushi tayi tare da gyaɗa kai
Ya juyo ya kalle ni h
"habibti kinga ashe ba dauɗar ciki yake damun ki ba baby na ne", shafa min ciki yayi tare da kissing lips ɗina tare da ce mi "thank u 4 everything"
Har muka koma gida yana cewa
"dama nace ba lallai bane dauɗar ciki bane amma ban taɓa kawo cewa ciki gare ki ba" kallon shi kawai nayi kamar ba shi kaɗai yai ta mitar dauɗar ciki gare ni amma wai yanzu kuma ya canza zancen
A hanyar gida ya tsaya ya siya min kwakwa ta wannan karon harvda dabino ɗan agadas don kwakwa da dabino ba dai daɗi ba ga daɗi a baki ga aiki a jiki 😉
Mun koma normal life ɗin mu amma yanzu gabaɗaya zaman garin kanobya fita raina don haka ko wannan zuwan da aliyu yayi sai na tuntuɓi ko yana sha'awar mai da mu abuja
Rungume ni yayi sosai wanda har sai da naji ɗan zafi a rungumar tasa daga gani in ya tafi yana kewar mu ba kaɗan ba
Ana gobe zamu tafi muna zaune a falo duk na gama haɗa duk wani kayana yara ma sun yi bacci muna ɗan kallo aliyu yana zaune ni kuma ina kwance akan cinyar sa sai nace
"habibi ina da wata alfarma ɗaya"
"anything 4 u habibti"
Kamar bazan yi magana ba sai kuma na buɗe baki na
" ina mahaifiyar ka" shiru yayi kamar yana nazari
"wallahi ban san inda take ba"
" baka ganin ya kamata mu neme ta"
"kina son ganin ta ne" gyaɗa masa kai nayi
"in shaa Alƙah zan nemo ta ko don ke, amma ganin ta zai yi wuya tunda bansan komai nata ba sai sunan"
"ba komai in shaa Allah zan taya ka"
"no sweetheart just concentrate on dis" ya faɗa yana dafa min ciki na
"Ok buh promise me to look 4 her soon"
"in shaa Allah habibti"
Muka ci gaba da hirar mu har lkcn bacci muka koma ɗaki muka kwanta sai da safe
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:46🌹
Kashegari da wuri muka fara shirye shiryen tfy ƙarfe 8:00am muna airport, domin hawa jirgen da zai kai mu birnin tarayya abuja, aliyu ne ɗauke da mohd inda ni kuma na riƙe hannun haidar, tj ne ya rako mu airport, sai tsokanar aliyu yake yi
"ɗan uwa nan gaba in aka kuma daka maka yajin nan gidana zan kawo yayata in ɓoye ta" shiru mayi banɓtanka musu ba don maganar ba tawa bace
Shima aliyu be tanka masa sai ma cigaba da yayi da anfani da wayar sa wacce take hannun sa tun da muka shiga motar ko me yake yi da ita oho
mun hau jirgi lfy mun kuma sauka birnin tarayya ƙalau muka kama hanyar gida, Alhamdulillahi na je na samu gida kamar yadda na barshi tsab da shi, sai ma ƙarin gyara daya samu
Hankali na a kwance na ci gaba da tafiyar da hidimar gidana ba tare da wani matsala ba muna waya da su iya sosai ina jin halin da suke
idan akwai wani taimako ko wani sabga ta tashi suna faɗa min zan faɗawa aliyu shi kuma sai ya aika musu da abinda ya samu
gaskiya aliyu ya canza ba laifi don ya fi da, matsalata ɗaya dashi yanzu na rashin ƙara yi magana akan neman mahaifiyar sa
ko da irin nayi masa magana akai sai yace shi ya ki kyautata zaton ta mutu, amma ina ƙara ƙarfafa masa gwiwar akan ya neme ta
rannan muna zaune aka kira shi a waya cewar an samu me irin sunan mmn nashi, sai yasa aƙara bincike sosai akanta
amma abin mamaki sai aka gano ba ita bace, na ɗauka zanga hankalin shi ya tashi ko be ji daɗin abin sai na gan shi je ia very calm kamar ba abinda ya faru wannan abun ya bani mamaki don haka sai na tunkare shi in dalilin shi na nuna ko in kula
"habibi kamar bakayi baƙin ciki daya kasance ba ita ce mmn ka ba ko" murmushi yayai ya juyo ya kalle ni
"na rantse miki da Allah ko kaɗan bana son haɗuwa da ita"
"me yasa"
"saboda ita ma ɓa ƙauna take yi ba"
"ya akayi kasan hakan"
juyowa yayi sosai ya kalle tare da riƙe min hannuna
"habibti matar da ta yarda ni ta gudu ranar da ta haife ni kina ganin zata kuma biɗa ta, kin san me yasa ta yadda ni"
girgiza kaina nayi don ni a labarin daya bani kamar ƙuruciyace take ɗawainiya da ita a lkcn
"ta yarda ni ne don ta manta da ni da kuma mahaifina, inda ta yarda ni ko don wani abun ba wannan ba ya kamata ko so ɗaya ne ta neme ni amma ko da wasa bata taɓa tunanin in ɗan jaririn dana ajiye ba" maganar shi akwai ƙamshin gaskia
Fisabilillahi abinda mijina ya faɗa gaskiya ne amma tunda sulhu nake neman yi da shi da mahaifiyar sa sai na kaɗe baki nace
"Akodayaushe ka kasance me yiwa ɗan adam uzuri, ina lefin mu neme ta in ta nuna da gaske so take yi ta manta ka ɗin is fine by us in kuma wani uzurin sai muyi mata ko"
Kina ganin akwai uzurin da zai sa mace taƙi neman abin da haifa har zuwa shekara 30+ kina ganin akwai irin wannan"
Rasa bakin magana nayi don gabaɗaya maganar shi tafi tawa gaskiya haka na haƙura na sakko tare da cewar ni dai don Allah kawai ya neme ta don ni, yai min alƙawarin zai neme tan don amma idan ta nuna bata son mu'amala da mu bazan ƙara tada zancen ta
Na amince sannan yace min zai sake sa waɗan su su kuma bincika masa ita, godiya nayi masa sosai inda ya katse min tare da cewar
"kede kiyi fatan kada Allah yasa ta watsa miki ƙasa aido in kun haɗu"
"amin kawai nace tare da rungume ni
*****************
Tafiyace ta kama aliyu china inda ya nemi mu tafi tare ni kuma na nemi alfarmar in ɗauko ƴar autar mu mu tafi tare saboda da yara zamu ni kuma in fama da kaina
Aliyu be musa min ba yace mu tafi da hannatu ma ta dinga taimakawa aminar kula da yaran
Mama na kira na shaida mata tafiyar da zamuyi da amina, murna a wajen mama kamar me, ta haɗa amina ta hankaɗo min abuja, passport akayi masu ita da hannatun muka shiga neman visa barin ƙasa
Tun da amina tazo sai ta shaƙu da yaran sosai komai itace take musu tare da taimakon hannatu, kullum zaka tsince su ita da hannatun a tare ko a kitchen ko a ɗakin yaran wannan ne ya sani sakin jikina
Visar tamu bata fito ba ko ince tasu amina don tamu ta fito tun yaushe, aka aiko wa da aliyu gayyatar bikin ƙarasa sanin juna na masu manyan jiragen ruwa na duniya, tare da haɗin gwiwar masu manyan kamfononi na duniya, kasancewar ɗaya baya iya ci gaba da sai taimakon ɗaya
Taro akan sanin juna tare da sanin kan abinda ya dace ayi tare da gina kyakkyawar mu'amalat tsakanin masu company da masu yi musu dakon kaya zuwa garuruwa wanda sai kana da babban matsayi sannan za a gyace ke
A england za ayi, a garin man city, yaron aliyu na can ya kira shi don an bada iv ɗin har da aliyu kasancewar an san shima yana da manyan jiragen da suke shige da fice da kayayyaki
Ko da aliyu yaji saƙon sai yace wa da yarin nasa shi ya wakilce shi don shi bazai iya zuwa ba zai je china
"sir wannan harkar fa ta manya ce, manya manya ne na ƙasashe zasu taru, wannan zai bada damar ka haɗu da manya kaima ka ƙara bunƙasa taka harkar"
"shiyasa nace kaje"
"sir ai wannan dole sai kai, kasan manyan nan sun fison su haɗu da mutum in person"
"in son zanje china ne ni da iyalina faa"
"haba sir tun yaushe kake wannan harkar, wannan ai kamar dama ce muka samu, tun yaushe muke wannan harkar amma bamu taɓa samun daman irin wannan ba, kaga wannan damar zata sa ka ƙara bunƙasa sunan ka da kuma harkar tamu, muma adinga dama wa da mu" shiru aliyu yayi amma shi san zuwa england ɗin nan beyi masa be
Duk da duk abinda peter yake faɗi gaskiya ce ze kasance dama ce gare shi ya ƙara faɗaɗa harkar sa, barin ma ya haɗu da masu manyan kampononi kala kala, tunda yanzu iyakacinsa, ya kai ɗanyan mai china da america, ya ɗebo kaya daga china, america, thailand, saudiyya sai dubai
Amma hanyan zu be samu chance ɗin da jiragen sa zasu dinga duniya da kaya ba duk da dai cewar yana da jirage masu girma da ingancin da zasu dinga iya zaga duniyar tare da kwasar kaya ko a ina da kaisu duk wani loko da saƙo da duniyar
"ok peter make the preperation i will be there in shaa Allah"
"inn jaaa Allah" inji peter
"i will be coming with my family and my wife's sister so look 4 a comfortably hotel 4 us"
"yes sir"
Ko da aliyu ya kashe wayar sai ya gayawa zainab cewar sai sun fara biyawa ta england domin ya halacci meeting ɗin kafin su wuce china
Da farko bata so hakan ba don ita bata da wani buri daya wuce ta gansu a china don aliyu ya je ya kuma ganin dr. sa don tana lure da shi yana fama da zuciyar sa kawai ɓoye mata yake yi, amma tasha farkawa da daddare ta ganshi a zaune riƙe da ƙirjin sa yana salati
Sam ita bata san wannanɓhali irin na mijinta ba, ace mutum yana ciwo amma ba zai je asibiti ba shine ma dalilin da yasa ta ce zata bishi chinar amma in ba haka ba me ze kaita birnin sin da wannan cikin duk da dai har yanzu be fi wata uku ba
Si da aliyu ya rarrashe ta tare da faɗa mata kwana goma kacal zasu yi a england ɗin sannanɓta sakko, sai kuma mimma ta faɗo mata,
Ai mimma tace a england take lallai kuwa in haka ne in shaa Allah in taje zata neme ta
Dole aliyu ya canza akalar neman visar su zuwa england, cikin ikon Allah suka samu sai shirye shiryen tafiya,
Ta lagos zamu tafi don haka nayi murna sosai ko ba komai zan ga gida, ana sauran kwana biyar mu wuce england aliyu ya barmu muka tafi lagos
Mun sha yawo sosai a lagos sannan Allah ya kawo mu lkcn tafiya,
Aliyu ya zo har gidan mu sun sha hira da baban mu sosai inda yayi musu alƙawarin kujerar makka da shi da mama da khadija da maryam
Baban mu harda hawayen farin ciki don be taɓa kawo ba, ko da yake naji su maryam suna cewa tunda na auri me kuɗi sunji mama tana cewa mijina zai kai su hajji ita da baba basu san har da su ba
Ni kaina ban san da tafiyar ba sai naji aliyu ya kuma shiga raina na kuma godewa Allah daya bani miji irin sa, mama har da rawa kun san idan aka ce mutum al'adar bayarabe ta shige shi doe sai an masa uzuri, ni ma nayi masa godiya sosai su maryam ma suka kira shi taka nas su kai masa godiya
Ran da zamu tafi har airport su mama suka rako mu mama sai rawar kai take yi ƴar ta zata tafi turai, muka yi sallama muka kama hanyar shiga jirgi sai turai ɗin gaske
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:47🌹
mun sauka lfy garin man city sannan muka kama hanyar hotel ɗin da peter ya kama mana, five star hotel dake kan titin neil lane, babban hotel ne me bene 95, inda peter ya kama mana presidential suite ɗin hotel ɗin
Suite ne me ɗakuna barkatai kitchen dining area, har da ɗan garden ƴar varender da ke kusa da living room, gaskiya ya ansa sunan shi presidential suite don komai me tsada ne
Unparking kayan mu kawai muka yi, ni da aliyu muka ɗauki master bedroom, amina ita da hannatu ko wannan ya ɗau ɗaki ɗai ɗai sai akar bar wa yaran ɗakin ɗaya, wanda yake kusa da na amina
ina cikin gyaran kayan aliyu ne naci karo da wasu pics daga gani na da ne, wata balarabiya ce ɗauke da ciki da wani ɓakin mutum kusa da ita ya rungume ta ta baya, ko wannen su ɗauke da murmushi, matar tana bala'in kama da aliyu kana ganin ta kaga mahaifiyar sa
Tausayi ya bani daga gani yana kewar ta sosai don dai bazai faɗa bane, amma yadda yake yawo da su ko ina har cikin wallet ɗin sa ma na taɓa ganin pic ɗin don de kamar baya son in sani ne ya sa nima nayi shiru
Pics ɗin kusa kala goma kala kala, ɗaukowa nayi tare da dawowa kusa dai
"habibi, su waye waɗan nan" na tambaye shi, sai da ya fara kissing ɗina, yakan yi kissing ɗina ne idan na tambaye shi magana me ɗan wuyar bada ansa
"ƴar ƙauye iyaye na ne"
"kuna kama da mmn ka sosai" hanci na ya ja min har na ɗan yi ɗan ƙara
"ki kalla sosai i resemble my innocent father"
"Allah habibi kunfi kama da mmn ka"
"shhhhh taya ma za ayi inyi kama da ita, am a photo copy of my papa" na san jin haushin abinda mmn tayi masa ne yasa baya son yace yana kama da ita
na kau da maganar don ko ɗan ƙaramin yaro yaga aliyu yaga mmn shi yasan sun yi kama ba kaɗan ba,
"i suppose wannan na cikin kai ne ko" na nuna cikin mmn shi daya fito sosai
"yep ɗat happens to be meee" ya faɗa da murmushi a fuskar sa
"do u miss her"
"no i never miss her, ban san ta ba bansan halin ta ba ban san komai nata ba ta yaya za ayi in missing abinda ban sani ba"
"i mean wataran kana cewa dama tana nan ko"
"no i never wish for 4 dat" ya faɗa yana tashi
"lets end d conversation here its boring" ya faɗa yana haɗa pics ɗin tare da yi musu ɓuya sosai
" na taho da su nedon kince sai na cigiyo miki ita don haka am going to use dis pics in shaa Allah, dont even think other wise"
sarai na san baya son hirar iyayen sa ne ko me yasa oho kai Allah ya kyauta na faɗa a raina
mimma na kira na shaida mata muna england a man city tai mamaki sosai don bamuyi da ita zan zo ba, dama naso ne onyi surprising ɗin ta, tai min alƙawarin zata zo, ni kuma nai mata kwatancen hotel ɗin da muka sauka
kashegari kuwa ta kira ni akan nayi expecting ɗin ta around 2:00 na ji daɗi sosai, da yake turai ya shige ta sosai ƙarfe 2:00 dai dai sai ga call daga reception wai ina da guest,
nace a barta ta shigo, minti biyu ne da ɗan sakons ya kawo ta suite ɗin mu, ina buɗe mata na rungume ta ban taɓa ganin ta ba sai yau
Kissing ɗina tayi a gefen fuskata duka biyun tare da ƙara rungume ni,
"ai nal aulad, where r kids" ta tambaya
Ƙwala wa hannatu kira nayi nace mata ta kawo su haidar,
Kawosu tayi, mimma ta dinga ɗaukar su tana kissing ɗin su sam ta kasa a jiye yaran ta taɓa wannan ta taɓa wancen, har ƴar ƙwalla sai da na gani a idon ta, wanda ya ke ɗauke da glass irin na likitoci,
Kallon mimma na dinga yi kamar na san kamar na san fuskar ta, amma shap na manta a ina na san ta, ko dai ban santa ba gaskiya na san wani me kama da ita, medicated glass ɗin da ke fuskar ta ne ya sani kasa tantance a ina na san fuskar ta, ko kuma a kalle kalle na na film ɗin larabawa ne oho ni dai nasan fuskar nan tata
"Mimma me za a kawo miki" na tambaye ta
"am full habibti"
"no mimma at least ko ba yawa ne ki ɗan ci kaɗan"
Gabaki ɗaya hankalin ta yana kan yaran, na sa akawo mata abinci da ɗan abin sawa a baki daga kitchen ɗin hotel ɗin
Da ƙyar ta iya ajiye haidar taci abinci ɗan kaɗan shima, pics ta dinga ɗaukar yaran, naso muyi hira da ita sosai amma sam hankalinta yana kan yaran,
Ba wani hira mukayi ba sosai sannan tace zata tafi duk da dai sai da ta kai kusan 5:20 sannan ta tashi nayi mata laƙawarin zuwa gidan ta
Ta bani address ɗin ta a liverpool take, na duba address ɗin nasu gidajen su na turai bashi da wuyar gane wa ba kamar namu ba nai mata alƙawarin zuwa gidan nata kafin mu tafi
Roƙo na ta dinga yi na don Allah in zo in kuma taho da su haidar na ansa mata da too
Har reception na rako ta anan ne ma muka ɗan tsaya muna hira kasancewar an tafi kira mata cab,
Aliyu ne ya shigo ya tarar da mu a reception ɗin yai mamakin ganina, sai na gabatar masa da mimma, yakan ji hirara ta a wajena sosai
"habibi ga ka yau ga mimma ta" na faɗa ina nuna masa ita
Da murmushin sa ya ƙaraso kusa da ita, amma abin mamaki suna haɗa ido sai naga fuskar shi ta canza, tsayawa yayi yana mata kallon mamaki kamar ya santa
Sai da nayi masa magana sannan ya dawo hayyacin sa
"habibi kasanta ne" na tambaya
"ta ina zan san ta" ya faɗa rai a ɓace
"ina jiran ki idan kin sallame ta"
Jikina duk yayi sanyi yadda yayi wa mimma sam ban ji daɗi ba ina laifi ta bar abinda take yi tazo kawai don tagan mu amma irin tarbar da zai mata kenan ohhh ni abu zan ga ran da mijina zai shiryu
Jiki a saɓule na raka ta itama bata ji daɗi ba amma kuma bata ce komai ba bayan ta tafi na dawo don yau aliyu yana da bayanin da zai min na wulaƙanta baƙuwata da yayi
"Habibi me kayi wa baƙuwata kenan" na faɗa lkcn da na shigo ɗakin mu wanda na tarar da shi a kwance yayi rigingine yana kallon ceiling
"habibi kasan mimma ne da yasaka yi mata wulaƙanci bayan ta zo daga liverpool kawai don ganina da yaran amma shine kake wulaƙanta ta"
Tashi yayi zaune
"a ina kika santa" ya faɗa ba tare da wasa afuskar ba
"so nawa zanɓfaɗa maka a yadda muka haɗu da ita"
"just tell me for GOD's sake" ya faɗa da tsawa
Na faɗawa aliyu yadda muka haɗu da mimma, shiru kawai ya yana saurare na, ko da na gama sai yace min
"ki rabu da ita Hippocrate ce"
"huuuh 🙊 subhanallah, abu haidar a ina kasan ta da har zaka kira ta wannan sunan"
"just shut up an leave me alone" ya faɗa haushi naji na tashi gaba ɗaya na bar ɗakin, a cikin abinda yake yi kamar ya san mimmar amma me yasa baya son faɗa min ko wacce ce ita
ban kuma kula shi ba da magana mimma ba, gashi nayi mata alƙawarin zuwa ko ya za ayi inje, na faɗa araina
Bayan kwna biyu sai gashi ya zo da rana yana shiryawa, tashi nayi na je wajen sa tare da tambayar sa ko ina zashi don yai mana alƙawarin zai kai mu zaga gari da yamma
"habibi yaushe zamu fita ganin garin"
"sorry habibti ba yau ba kinga peter ya haɗa min dinner da wani mutumin ɗan ƙasar saudiyya, wai yana da kaya sosai da za ai masa shipping, shine yace pls inje gidan sa muyi dinner da iyalen sa"
"ohh cikin garin nan ne"
"noo liverpool ne, akwai train da zai tashi zuwa liverpool nan da 00:30 mins idan nayi sauri zan samu"
Jin an ambaci liverpool ya sani miƙewa,
"don Allah habibi zani"juyowa yayi ya kalle ni
"are u sure" ya tambaya, gyaɗa masa kai nayi
"ok hurry up and get ready we have a train to catch" da sauri na tashi na fara shirya wa in shaa Allah sai naje gidan mimma
"yaran faa" na tambaye shi
"ohh barsu kawai ai dinner ce kawai bana son yaran su kawo wani matsala, kin san official meeting ne"
"ok kawai nace
Cikin shadda ta greenish blue me ɗinkin fitted gown wacce ta sha surfani tun daga sama har ƙasa na sako tare da ɗauko pendants ɗina silver wanda ya shi sosai da kayan
Mayafina na ɗauko wanda yai dai dai da kayan sannan na ɗauko stiletos hill ɗina na saka sai na fito kamar wata tauraruwa
muka fito muka kama hanyar station ɗin mun yi sa ar samun train ɗin on time mukai boarding muka fara tafiya zuwa liverpool tare da burin zuwa gidan mimma in dai muka je liverpool ɗin
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: [11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: Page: 48🌹
Lfy muka isa liverpool a train muka sauka sannan muka hau cab tare da ba driver ɗin address ɗin gidan da zamu, ƴar purse ɗin da ke hannu na na ɗauko na fito da address ɗin mimma
"Habibi don Allah in mun fito daga dinner sai muje ko" hankalin shi gabaɗaya yana kan wayar don haka be kalli ƴar paper da na bashi ba, sai cewa yayi
"wa kika sani a liverpool da zaki gidan sa"
"gidan mimm ne nayi mata alƙawarin zanje"
"stop dreaming dear babu inda zaki" ya faɗa
"kamar yaya" juyowa yayi sosai har ina iya jiyo nunfashin sa dake sauka akan fuskata
"sweatheart ba nace u should 4 get about her ba, i dont like dis relationship"
"amma ................"
"no amma just do me a favour nd stop talking about her u aint going any where, i hate d sight of her"
Oh my goodness wai sai yaushe mijinta zai bar halin sa ne,
Tafiyar 00:30 mins ne ya kaisu gidan da za suyi dinner, ran zainab a ɓace yake don haka kallon ma batayi ita da take cewa in suka fita zata yi using oppurtunity don ƙarewa garin kallon amma tun bayan ɗan faɗan su da aliyu ta cushe fuskar ta tare da juyawa gefe ta share shi
Ko da suka zo gidan ya biya me cab ɗin sannan suka ƙara ƙofar gidan inda suka dan na door bell ɗin
Wata yarinya ce ta zo ta buɗe daga gani bata fi sa ar zainab ɗin
"u r welcome" ta faɗa
shiga suka yi inda tayi musu jagora zuwa sitting room inda iyayen su suke,
"mr aliyu its a pleasure seeing u in my home u r highly welcome"
"the pleasure is all mine" aliyu ya faɗa suna musabaha da me gidan
"i believe this is ur wife" ya faɗa yana nuna zainab wacce ita kuma take ɗan murmushi
"yes she is zainab"
"oh wat a nice name, nice meeting u mrs aliyu"
"nice meeting u too" na maimaita
"yusra habibti tell ur mum our guest r here" ya faɗawa ƴar sada ta buɗe mana gidan
"yes dad" ta tashi ta fara hawa bene
Me aikin su ya kira ta kawo mana ruwa da lemo, ni dai gabaɗaya raina a ɓace yake abinda aliyu yayi, mmn tasun ta sauko tana maganar ina baƙin, to my surprise mimma
da murna ta na ƙarasa wajen ta tare da rungume ta,
"mimma" na faɗa
"habibti" ta faɗa tare da ƙara rungume ni
Nayi murnar ganin ta, ƙarasowa tayi cikin living room ɗin don su gaisa da aliyu, haka ya ansa gaisuwar tata fuskarsa babu yabo ba fallasa,
jana tayi zuwa kitchen
"zo muje mu haɗo wa boys ɗin mu ɗan snacks" binta nayi ina jin daɗi duk da dai ina feeling guilt na yadda mijina yake mata amma ita sam bata damu ba
A kitchen take tambayar yaran sai nace mata ai ban san nan zamu zo ba, Bata kawo komai ba ta yadda da abinda na faɗa
Muka haɗa ɗan snacks wanda yake a cikin leda ne a fridge kawai reheating muka sake yi a micro wave sannan muka ɗauko muka fito
Ajiyewa mukai agaban su sannan muka zauna muka fara hira, bamu daɗe da zama ba wani ya zo ya hankaɗo kofa ya shigo, gabaki ɗayan mu hankalin mu ya koma kanshi
Mimma ce tayi masa magana
"hisham come and say hi to our guest" ta faɗa masa, kamar ba ze zo ba sai kuma ya zo
miƙawa aliyu hannu yayi suka gaisa ni kuma ya min sallama, daga nan sai yayi sama, mu kuma muka koma hirar mu, sam ban ga tarbiya a tattare da yaron da mimma ta kira da hisham ba kanshi a tsaye yake daga gani kan nashin yana hayaƙi
cook ɗin su ta gayyace mu dinner ta gama muka tashi muka tafi, kowa ya nemi wuri ya zauna, inda mijin mimma yake zaune kan kujerar da take kallon ta mimma sai ni kuma na zauna kusa da aliyu,
Aikawa tayi a kira yaran gidan su zo muyu dinner, matan ne kawai suka sakko amma ban da hisham ɗin, mun ɗan jima kafin mijin yace kawai muci abinci ƙila hisham ɗin ya ƙoshi ne
Muka fara dinner sai ga hisham ya sauko a gadarance ya samu wuri kusa da bbn shi zauna, fara cin abinci yayi babu ko bismillah mun lura gabaɗayan mu, mimma ce tayi masa magana
"hisham baka yi bismillah ba"
"ina ruwanki da ni ko plate ɗin mu ɗaya ne" ya faɗa a wulaƙance
Abun ya bani mamaki ɗaga ido nayi na kalle su naga kowa babu abinda ya dame shi kamar dama sun saba
"ƙyale ta ta fiya sa kanta akan abinda da babu ruwanta, acting lika mother" inji ɗayar
"its ok kids, lets just eat we have guest today, salma behave ur self" shine abinda mijin yace
Mamaki ne ya kama ni, wannan rashin mutun ci ƙiri ƙiri amma abinda zai ce shine suyi shiru
Yarinyar da ake kira da yusra ne tace
"salma pass me d salt" tsayawa nayi ina kallon su
gabaki ɗaya babu tarbiyya a tattare da yaran salma ma suke ce mata kansu tsaye, itama mimmar sai ta share yusrar bata miƙa mata ba
"salma am taking to u"
"kinsan abinda ya kama ta kice kafin in baki salt ɗin"
"kina nufin in ce miki pls" Gyaɗa mata kai mimmar tayi
"da ince miki pls gwanda kar inci abinci" ta faɗa tana miƙe wa
"yusra habibti zauna lemme pass u d salt" inji yayar tatan, ƙin zama tayi ta shi ta miƙe ta hayewar ta sama
wani kallone uban ya bi mimma da shi wanda ƙiri ƙiri ya nuna itace me lefi
" ki daina yin abu kamar wata uwa a wajen mu, in tarbiyya kike son yi kije kiyi wa mataccen ɗan ki ba mu ba" hisham ya faɗa yana mike wa shima
yau naga ta kaina na kuma faɗa, ita ma yayar yusrar sai ta tashi har da cewa wai mimma ta sa loosing appetite ɗin itama ta bar wurin, kamar inyi mimma kuka haka neji, kanta yana ƙasa baza ka iya ganin fuskar ta don haka ba za iya faɗin mood ɗin da take ciki ba amma daga gani bata ji daɗin abinda ƴaƴan mijin ta suka yi mata ba
sai ya rage mu kaɗai tun marasa kunyar yaran sun fita
"so aliyu kace maman ka ƴar saudiyya ce, a wane garin" inji mijin mimma
"oh ban sani ba don ban ma santa ba, bamu taɓa haɗuwa da ita"
"me ya same ta"
"she died the day i was born" ɗago kaina nayi ima kallon aliyi shi da yace mmn shi tana da rai amma yanzu yace ta mutu
"oh am so sorry may her soul rest in peace" in mijin mimma ita ma mimma sai tayi wa mmn aliyun addua
"amma baka tambayi bbn ka lbrn ta ba"
"ya mutu kafin a haife" sosai suka nuna tausayin sa
"amma gaskiya kaga rayuwa, ka rasa iyayen ka lkc ɗaya, lkcn da kake mutuƙar buƙatar su"
"haka Allah ya ƙaddara"
"do u miss dem"
"no babana kawai nake missing, ita kuma mmna lefin ta na gani da ta iya barina a wannan cruel world ɗin ta tafi without looking back how selfish of her"
"bata da zaɓi ne shi yasa alkcn mutuwa mutum bashi da zaɓi" Inji mijin mimma
"ba wai zaɓi ne bata da shi ba son kai ne kawai, ƙiri ƙiri tasan banni da wani bayan ita, amma duk da haka saboda selfishness irin ta da rashin imani da rashin tausayi ta iya barina a lkcn"
Daga maganganun aliyu kana ji kasan akwai baƙin ciki a tattare da su, riƙe masa hannu nayi alamar lallashi, juyowa yayi ya kalle ni yayi murmushi
"but who cares yanzu Allah ya haɗa ni da wacce ta fita a rayuwa so bana ji komai" Ya faɗa yana kallona
Murmushi nayi masa tare da shafa gefen fuskar sa wanda hakan yasa shi lumshe idon sa
"am soo sorry to hear dat, a wurin grans dinka ka tashi"
" no its a pity da babu wanda yake son ɗauka a lkcn da aka haife ni don ƙiri ƙiri tun kafin a haifeni babu jituwa tsakanin mum ɗina da inlaw ɗinta, amma yet bayan ta haife ni ta iya barina bata yi tunanin wa zai kula da ni ba, dats y i said she is selfish"
shiru duk muka yi maganar sa akwai tausayi sosai, kukan mimma kawai muka ji, ajiye table napkin ɗin da ke hannu ta tayi ta tashi da gudu ta bar table ɗin, binta muka yi da kallo sai da ta ɓace sannan mijinta yace
"kar ku samu damuwa ita ma ɗan ta ne ya mutu yana baby a hannun kakar sa shi yasa in taji lbrn baby ya rasa ɗaya daga cikin parents ɗin sa sai ta tuna ɗan"
"hypocrite" na kuma jin aliyu ya kira da shi, juyowa nayi na daka masa harara ,yaushe mijina ya ɓaci da zai dinga kiran mijina da hypocrite
tausayi ta bani sosai don haka sai nace
"bari inje in lallashe ta" aliyu ne ya riƙe min hannu na tare da zaunar dani,
"ba hurumin ki bane, kinga shima mijin daya ajiye ta be damu da ita ba sai ke uwar shishigi" ya faɗa da hausa yadda mutumin ba zai fahimci me muka ce
komawa nayi na zauna suka ci gaba da tattaunawa akan harkokin su, ganin na gaji da zama gashi ina son sanin halin da mimma take ya sani cewa don Allah a nuna min rest room
me aikin su ya kira yace ta kaini guest room, barin su nayi suka ci gaba da maganganun su na business ni kuma na bi me aikin nasu, sai da muka bar gurinsu sannan nace mata ta nuna min ɗakin mimma wurin ta zanje, tayi min kwatancen ɗakin na haura sama
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: A hankali na tura ƙofar ɗakin tana zaune a gaban mudubin ta tana kuka, kus da ita naje na dafa ta
Sai da ta goge fuskar ta sannan ta juyo da murmushin
"y r u crying" na tambaye ta
"lbrn mijiki ya sani tunowa da nawa ɗan"
"am sorry kin ce ya mutu ko" gyaɗa kanta tayi
"Haƙuri zaki yi ki tayi masa addu'a, shi kawai yake buƙata"
" ya za ayi ɗana ya yafe min" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka
"ni na jawo ya mutu very innocent of him amma ya haɗu da uwa dat is full of childish, i just cant forgive my self for d death of my innocent baby"
Kuka ta kuma ci gaba da yi ina ta bata haƙuri, sai da ta ɗauki lkc sosai sannan ta haƙura bayan na tabbatar mata da cewar a kodayaushe ƴaƴa sukan yafe wa iyayen su balle nasan ɗan ta yana aljanna don haka bazai wani holding grudges against her ba
A hankali ta ɗan sakko har muka fara hira dai, irin na yadda ta zam successful likitan yara tace saboda son da take yi wa ɗan ta ne da dana sanin mutuwar sa da tayi ne yasa ta zama likitan yara
Na jin jina mata daga gani tana kewar ɗan nata sai dai muce Alƙah ya jiƙan sa, wani hoto ne ya ɗauke min hankali a kan mudubinta na ɗauko shi,da graduation gown a jikin me hoton tana dariya, tsaya wa nayi ina ƙarewa pic ɗin kallo, wannan kamar pic ɗin mmn aliyu
Juyowa nayi nace mata
"mimma wacece wannan" zuwa tayi kusa da ni ta karɓi pic ɗin
"nice lkcn graduation ɗina" ta faɗa da alamar alfahari
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un mimma ce mmn aliyu, kuma ya sani amma, ya subhanallah, ko shi yasa akan dining yake ta faɗa maman shi tana son kai don ya cusguna mata,
Hawaye ne ya cika idon na goge shi a don bana son ta gani, me yasa mijina baya son ya sanar da mmn shi ya nanan a raye, wayyo wannan wace irin ƙaddara ce ɗa yana son rama abinda mahaifiyar shi tayi masa da ƙuruciyar sa
Futowa nayi daga ɗakin inda naga aliyu yana nema na zamu tafi mimma har ƙofar gida ta rako ni mukayi sallama gaba ɗaya jikina a yayi sanyi ganin wannan irin relation ship ɗin nasu muka kama hanyar man city ni da miji kowanne mu zuciya ba daɗi, ni ina tunanin me yasa mijina zai yi wa mmn sa haka shi kuma Allah ne kaɗai ya san abinda ke ransa
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :49🌹
*na Sadauƙar da wannan page ɗin ga dukkan masoya na gidan aure da waɗanda suke shirin yi Allah ka barmu da mazajen mu ka ƙara musu son mu ka rufe musu idon su daga ganin aibin mu ka buɗe musu idanuwan su don su dinga ganin alkhairan da ke tattare da mu, masu matsala a gidan aure Allah ya kawo musu sauƙi, masu zaman lfy Allah ya kuma zaunar su lfy waɗanda suke shirin aure Allah ya sada su da nagari waɗanda har yanzu basu samu ba Allah ya haɗa da nagari, Allah ya barmu da masu son mu yau ina cikin murna*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
Sai 12 :40am na dare sannan muka shiga gida, kowannen mu zuciya cike da tunani, ɗakin yara wuce direct don in duba su, baccin su suke hankali a kwance ga amina ma a kan kujera
Tashin ta nayi nace ta koma ɗakin ta sannan na kuma yi musu addua tare da kashe musu fitila na fice, ko da na shiga ɗaki aliyu yana toilet, kaya kawai na cire na zauna ina jiran ya fito
Wanka yayi don ya fito gashin kansa yana ɗigar ruwa, tashi nayi nima naje na yi wankan sannan na fito na shirya na kwanta kusa da shi
"habibi yau me kayi a gidan su mimma kace mmn ka mutu"
"she is as good as dead to me" ya ansa
"ba nace ka daina wannan abun ba, wai sai yaushe zamu zauna ne ba tare da ka kawo mana wani problem bane, wat u did to dat innocent woman is unfair"
"unfair me na mata da ya zama unfair don kawai na faɗi tahirin rayuwata"
"labarin naka kamar kasan zai ƙona mata rai ne shi yasa ka dinga faɗin shi haka, did u intend ta hurt her"
"why will i hurt her wen i dont even know her"
"ranar da ka fara ganin ta ka kira ta da hypocrite wannan ya nuna ka santa"
"less stop dis conversation here bacci nake ji kinsan gobe akwai partyn da zamuyi attending kuma kin san ba nigeria ba ne don haka babu african time, we have to be there on time" shiru nima nayi aliyu baya son ya faɗi wani abu, amma ina da tabbacin mimma ce maman sa na so mu ci gaba da conversation ɗin amma ba hali
Bacci ne ya kwashe ni don na gaji, cikin dare na ji nishi a kusa da ni, farkawa nayi naga aliyi yana murƙususi riƙe da qirjin sa
Ohh my goodness zuciyarsa again na faɗa tashi nayi na dafa shi sai naji ya ce
"magani na pls" tashi nayi na ɗauko maganin nasa na ɓallo su dai dai yadda dosage ɗin yace miƙa masa nayi tare da bashi ruwa
Da ƙyar ya iya karɓa ya sha, cikin minti biyu bacci ya kwashe shi amma kafin yai bacci ya bani tausayi sosai daga gani yana fama da zuciyar nan tasa don har kuka sai da yayi
Gyara masa kwanciya nayi don ya ji daɗin baccin sai na ci karo da pics ɗin mimma na wajen sa, ohhh my goodness mijina ya gano mmn sa amma ƙiri ƙiri ya ƙi nuna mata cewar har yanzu yana a raye
Cuzguna mata yake son yi amma on d other hand shima he is suffering, gwanda ma ita bata fama da matsalar zuciya amma shi fa, zuciyar sa bata da lfy yet duk da haka ya hana ta ta samu sassauci kullum ƙara danƙara mata ƙiyayyar mutane yake
Sai yanzu na fahimci dalilin daya sa mijina ya samu ciwon zuciyar nan sabida gabaki ɗaya rayuwar sa ya taso cikin ƙunci da cuzgunawa daga mutane don haka zuciyar mijina babu komai a cikin ta sai ƙiyayya
Zuciyar da ke cike da soyayya na ba kowacce take lafiya ba balle ta mijina tun yana yaro ya cika zuciyar sa da tsanar *dangin sa* ya za ayi a samu lfy a tare da zuciyar da tun tana ƙarama babu abinda ke cikin ta sai ƙiyayya
Shi aliyu be fahimta bane shine maganin zuciyar sa inda zai dena ƙiyayyar da yake da ya zauna ƙalau amma burin shi yanzu naga alamar ya ƙuntatawa mahaifiyar sa, bayan kuma na san koda zai ji daɗi ya ganta a halin ƙunci yet shima a ƙasan zuciyar sa sai yaji ciwon nan kasancewar mahaifiyarsa don an ce blood is thicker than water, no matter stage ɗin da ɗa ya kai wajen resenting iyayen sa dole deep down in him dole a samu ɗan tausayi ko da ƙalilan ne na iyayen
In haka ne kuwa aliyu kenan be san cewar ɓacin mimma ba shima ɓacin ransa ne, kallon shi nayi baccin sa yake yi peacefully nace araina, bazan barka da wannan halin ba dole i have to tell mimma u r her lost son ko a kawo ƙarshen wannan abin don faɗa mata kamar jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne
Ita a ɓangaren ta zata daina blaming kanta na mutuwar ɗan ta kaima ka samu sauƙin zuciyar nan taka, haɗa pics ɗin nayi na ɗora akan bedside so nakeyi idan ya tashi da safe ya gane cewar nasan abinda ya sashi ciwon zuciyar, na koma na kwanta
***************
Kashegari ras ya tashi ba dole ya tashi ras ba tunda ya bar zuciyarsa ta huta, da wuri ya fita tare da faɗa min sai dare zai dawo in tabbatar da na shirya kafin ya dawo,
Yana fita nima na shirya tare da amina muka tafi shopping don banni da kayan da zani partyn,
Mun samu wani boutique a ƙasan hotel ɗin, muka shiga daga gani boutique ɗin na masu hannu da shuni ne ganin yadda ake nan da mu
Na faɗa musu "dinner gown"
"wane irin dinner ne" inji attendant ɗin
"well kamar businee dinner ne"
"mostly cocktail aka fiyi in dai business dinner pls come with me" binta nayi muka je inda cocktail gowns suke, amma to my surprise kusan duk babu wanda musulmai zasu saka
Don haka sai na faɗa mata ni musulma ce, sai tace min in zaɓi wanda nake so za a iya gyara min yadda zaiyi covering ɗin na
Wata armani gown na ɗauka gabaki ɗaya bayanta sa kwashe yake, sai wasu zare da akayi kwalliya da su abayan ta, gaban ta kuma stones ne akayi kwalli da su, sai satin da aka belt da shi tai kyau sosai
Bayan na ɗauka sai muka wuce, ware house ɗin su inda anan tailor ɗin su suke, wai lallab bature ya ci gaba, gida gudane ware house ɗin nasu baka gani komai sai kekuna, baka jin komai tsit kawai kamar ba kekuna ne suke aiki ba
Gurin wata muka je ta gwada ni tare da nuna min yadda rigar zata koma, babu abinda za a taɓa a wajen rigar, cikin ta ne kawai za a saka material da zai rufe jikin mutum, rigar baƙa ce amma sai suka ce zasuyi amfani da silver material a ciki, wanda zasu sa masa kƴalli yadda zai dinga ɗaukar ido ta ciki
Nidai kawai binsu nayi da to sai nace musu suyi min ɗan himar wanda zan yane kaina da shi, nan ma suka amince na biya su kuɗin su inda suka ce min in zo da daddare du shirya ni
Wato bature yana da wayo irin waɗannan designers ɗin idan ka sai kaya a wajen su da wuya su barka ka shirya da kanka instead sai suce kazo su shirya ka ba don komai ba sai don indan suka shirya ka zasu ma yadda duk inda kabi sai an yaba saboda kiran costomers, don in an yaba za a tambayeka a ina ka siya kunga sun kuma samun costomers ke nan
Nai musu complain ɗin rolling ɗin himar ɗin duk suka ce suna da expert kawai inzo har da kwalliya duk zasu yi
Mukai total har da kuɗin shirya ni na biya su na kama hanyar hotel ɗin da muka sauka inda na bar su amina boutique ɗin suna siyayya ko da naje sun gama don haka na biya muka koma sama
_you are light, the guide of our life, you are the essence of beau...........ty, the best mankind,for ever you'll be, the source of truth, peace be upon u ohhh muhammad(saw) even though i cant see ur face, ur presence is always all around me, ur names on my mind, every single day peace be upon u oh muhammad (saw)_ *kar ku damu ina rubutu ina jin waƙar nan ne yasa nace bari in rubuto ta tayi min daɗi sosai by mahir zain*
Sai da nayi sallah magriba sannan na na shiga wanka ina fitowa kawai na saka kaya sannan na sauka boutique ɗin don nasan yanzu sai inga aliyu
Kwalliya sukai min sosai don ma ina hana a saka min wani abun ne ɗan ciki na daya fara turowa sai akai wa wurin ciki wani design a jikin rigar baza ka ɗauka ciki bane
Aliyu ya kira ni Nace masa ya same ni a boutique ɗin ko da yazo na fito be gane ni, har na zo gaban sa yana ta kalle kallen sa dariya ya bani na ƙarasa kusa da, kallon ɗaya yayi min ya ɗauke kansa alamar be gane ni
"r u looking 4 some mr" be kalle ni ba sai ma canza hanya da yayi har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya dawo ya ƙura min ido
Dariya kawai nayi,
"wow na zo ne in ɗauki matata zata rakani dinner, amma bari kawai inyi kidnapping ɗinki, muyi sauri mu bar wurin nan kar matata ta ganni"
ya faɗa yana jan hannu na, binshi nayi da murmushi don fahimci da gaske da farko be gane ni ba, buɗemin ƙofar yayi na shiga sannan ya zagaya ya shiga ɓangaren sa na driver ya ja muka tafi
Mutumin nan yana driving amma kusan rabin hankalin sa yana kaina,
"sssshhhhhh hhhhhh, mutumin nan u r very cheap"
"am speecless ne, irin wannan kyau haka na kasa magana ma"
"to amma me yasa baka yaba ba da farko sai kawai kayi kidnapping ɗina"
"i was soo shoked ne shi yasa u really took my breath away, zainab ina ƙaunar ki a kullum ban san yadda rayuwa zata kasance min ba in babu ke pls ba don ni ba ki daure ki ci gaba da haƙuri da ni nasan kina yi amma don Allah ki ƙara, na kasance maraya tun daga ranar da aka haife ni ban taɓa samun soyayya ba sai a wajen hjyta wacce na bar gaban ina da shekara13 don kawai gudun ɓacin rai da gori na sha wuya sosai a rayuwata, da rayuwa kawai nake yi babu purpose kullum jiran randa zanji ance yau zan mutu nake yi,amma tun da haɗu da ke na zama ɗan adam wanda bashi da buri a kullum da ya wuce ya rayu, wallahi da idan akace wane ya mutu har cewa nake yi dama nine, amma yanzu wai nine nake roƙon Allah ya bani doguwar rayuwar duk saboda ke, don Allah ki so ni ba don halina ba ko be kai kamar yadda nake son ki ba ni is ok by me indai zaki zauna da ni am ok"
ya ƙarashe zancen sa muryar sa tana rawa
"i love u to the moon and back, nima am not any better than u amma kuma ka zaɓe ni kake zaune dani duk da fault ɗina don haka i love u sooo much my one and only ɗan rigima"
Murmushi yayi min "wannan maganar taki ta sai miki ticket na zama ke kaɗai" a dai dai lkcn muka ƙaraso inda za ayi partyn, parking yayi sannan ya ɗauko wani ɗan ring box a aljihun sa,
"wannan ring ɗin da zan samiki shine yake da license ɗin nace cewa da ke kaɗai zan zauna iyakacin rayuwata babu ke babu kishiya" rungume shi nayi tare da godiya muka fito a tare kamar wasu taurari 💖💖💖💖
*yau nishaɗi nake ji don haka ga wata waƙar maher zain*
```i praise Allah 4 sending me u my love, u open my heart I was always thinking that love was wrong but everything was change when u came along ohhhh, there are couple words I wanna say
for rest of my life I'll be with u I will stand by ur side honest and truth to d end of my time I'll be loving u..... Loving u
for the rest of my life to days and nights I will thank Allah for opening my eyes now and 4 ever I will be with you deep in my heart 🎼🎼🎼🎼🎼🎼🎼
I feel so blessed when I think of you and I ask Allah to bless all we do, u r my wife nd my friend and my strength and I pray to be together in jannah```
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
page:50🌹
Cocktail party ne kamar yadda me boutique ɗin nan tace, kowa a tsaye yake sai waiters da ke zagayawa suna raba drinks da kuma snacks,
Kowa ya samu wanda ya sani suna tattaunawa, muna shiga peter yayi mana iso sannan ya raka aliyu gurin waɗansu turawa wai suna ta jiran shi,
Mun gaisa da su inda sukai ta yabon kyau na duk sai naji babu daɗi kasancewata musulma kwalliyaya ga mijina kawai zata tsaya
Barin wurin nayi na koma ladies rest room ɗin hall, wanke fuska ta nayi sannan na ɗan saka ƴar powder na fito don nasan mijina da kishi
Ko dana fito ya ganni ba make up sai na ga ya kuma washe baki alamar yaji daɗin abinda nayi
nayi mamakin yadda turawan nan suke so suyi magana da mijina, peter ne yin introduction yawanci hirar tasu akan business ɗin su ne, so it was boring to me don ni ba gane wa nake ba
Mun ɗan daɗe da zuwa kafin mc ɗin ya ƙaraso kowa ya gyra tsayuwar sa aka fuskanci stage, yayi introducin kanshi da ragowar manyan da ke wurin
Nayi mamakin da naji sunan mijina akan shine ya fi kowa jigilar kaya a africa, aka kira shi ya fita yayi ƴen bayanan sa da ban fahinci komai ba
Bayan ya gama aka bishi da tafi raf raf raf raf raf raf raf raf raf ni dai ban gane me suke yiwa tafi ba kawai na biye musu ne don mijina na ne
Ko bayan da aka gama intro ɗin sai aka ce kowa yayi enjoying partyn, nan fa naga mutane kowa so yake yi yayi wa mijina magana amma kasancewar akwai peter sai ya ce duk wanda yake son magana da shi ga peter nan
Wannan abin da mijina yayi ya shafa masa lfy inda ya haɗa peter da ƙwallan mangwaro, muka koma gefe, can na hango mimma ita da mijinta suna ƙarasowa gurin mu
Mimma na faɗa tare da rungume ta
"hello habibti ya kika je gida" mimma ta tambaya
"lfy"na ansa mata sannan na juya muka gaisa da mijin ta
Ina lure da aliyu sai yayi kamar be ga mimma ba, ita ma sai bata damu ba, muka shiga hirar mu kowa da ɗan uwansa,
Mijin mimma ne yace wa aliyu
"mr aliyu ni da matata muna shirin zuwa boat trip jibi ko zaku biyo min da matar ka it will be fun, kwana biyu kawai zamu yi"
"oh yi haƙuri muma in shaa Allah jibin zamu bar gari" na ansa shi
"no habibti ki bari muje muga teku mana, mr muktar i will really apriciate dat, in shaa Allah zamu zo" aliyu ya ansa
"yauwa kai naji daɗi sosai" inji mr muktar ɗin
Tsayawa kawai nayi ina kallon sa,
"mr muktar amma zaka taho da ƴaƴan ka ko, don it will be much fun with dem"
Washe baki mr muktar wato mijin mimma yayi,
"ai babu komai if dey r available zamu zo da su, i really hope ba kallon ɗaya daga cikin ƴaƴana kake yi don babu ruwana kai da matar ka" ya faɗa a zolaye
"no no no kawai de dey r fun to be around" ya faɗa yana sosa ƙeyar sa wai yaji kunya, haushi ya bani na riƙe hannun sa tare da kai masa mintsi ni
Duba na kai ga fuskar mimma wanda hakan da aliyu yayi yasa bata ji daɗi ba har hakan ya nuna a fuskar sa, wanda shi kuma aliyun ya kalle ta yayi murmushin mugunta
Sai yanzu na fahinci dalilin daya sa aliyu cewar ze bi mr muktar boat trip ɗin shi, wato so yake ya kuma ganin yadda ƴen iskan yaran zasu wulaƙan ta masa ƴaƴa uwa ko, ohhh Allah naah wannan miji nawa, ɓacin ran mahaifiyar ka ya kai mijina ɓacin ranka ne baka sani ba na faɗa a raina
"zo muje muyi rawa" naji ya faɗa, binshi nayi ba tare da nace komai ba, kasancewar slow music ne sai kawai na kwanta a jikin sa, don gaba ɗaya ba a cikin hayyaci na nake ba
Da wuri muka baro dinner don duk na gaji sai aliyu yace kawai mu tafi, a mota ne nace masa
"me yasa kace wa mijin mimma ya taho da ƴaƴan sa"
"kar dai kina nufin kin yadda son ɗaya daga cikin su nake yi"
"ko ɗaya ai nasan duk cikin su babu type ɗin ka don ba kunya gare su"
"yes rashin kunyar tasun nake son gani" ya faɗa da murmushi a fuskar sa
"kana nufin kana jin daɗin rashin kunyar da suke wa mimma"
"more than everthing i really enjoy watching her suffering"
"me yake damun ka, me matar nan tayi maka, baka tunanin kana ɗaukar hakkin ta, randa muka je gidan ta ka sa ta kuka u insulted her in directly yanzu kuma zasu boat trip da mijinta ka sa ya zo da ƴaƴan sa don kawai kaga suna wulaƙantata me ta tare maka"
"sweatheart dont worry ta chanchanci abinda ya fi haka ma saboda abinda tayi abaya"
"kana nufin na ajiye kan da tayi ranar da ta haife ka ta tafi" juyowa yayi ya kalle ni sauran kaɗan mu buge wani don haka sai ya koma gefe yayi parking, tsayawa yayi sosai yana kallona
"how do u know"
"yanda kake yi mata ne yasa ni na fara tunananin ƙila ka san ta kuma Allah sai ya taimake ni naci karo da pic ɗinta a ɗakin ta sak irin wanda kake da shi a lkcn na fahimci daliliɓ da yasa kake mata haka wai ka rama abinda tayi maka, ina tunanin ka yake, da har kake son ɗaukar fansa aka wacce ta kawo duniya"
Na faɗa ido na cike da ƙwalla don gaskiya yanzu abin aliyu tsoro yake bani
"yanzu meye na kuka kina ganin abinda nake mata ban kyauta bane"
"mahaifiyarka ce kake mata haka"
"me tayi min da zai nuna ya kamata in bata matsayin ta na uwa"
" ta kawo ka duniya, wannan be isa ba"
"ko kaɗan be yi min ba, matar da ta gudu ta barni ranar da ta haife ni kike son in kula ko me, ni ko kaɗan bana jin ta a raina"
"Aliyu duk abinda yake samun ka kaine kake jawo wa kanka" murmushin takaici yayi
"wato laifi nane ma yasa mahaifiyata ta gudu ranar da ta haife ni ko" girgiza kaina nayi
"ba wannan nake nufi ba matsalar zuciyar ka da kashe kanka da kake son yi saboda takurawa kanka da kake yi da sawa zuciyar ka ƙiyayyar mutane, ka taɓa tunanin wane hali zamu shiga ni da yara idan muka wayi gari zuciyar ka buga mun rasa ka, ko kana son yaran ka suyi maraici kamar yadda kai kayi, idan kana abun ka na san kai kana samu a cikine ko kuma kawai burinka ka ɗau fansar wanda ya ƙuntata maka, babu yafi a lamarinka ne ko menene" a wannan halin kuka ne kawai ya kubce min wanda hakan ne ya sani yin shiru
Rungume ni najo yayi wanda ni kuma na dinga kokawar ya sake ni ammabina da ƙarfi ya rungume nin
"aliyu tsoron ka nake ji yadda kake yi wa mutane idan sun ɓata maka kar nima wataran in ɓata maka ka guje ni, don Allah ka sawa zuciyar ka salama ka cire duk wasu ƙiyayyar ɗan adam a zuciyar ka ko ka zauna lfy, bana son rasa ka i really love u sooo much dat it ache me" na ƙarasa da kuka
"habibti am urs and will 4ever be amma mamana ta wulaƙan tani tun randa aka haife ni ta gudu ta barni baki ganin nima ya kamata in rama ita ma taji abinda naji througout those years i spent alone"
"talk to her don Allah kayi mata magana kaji dalilin ta na rabuwa da kai don Allah kayi mata magana" na faɗa ina haɗa hanne na tare da murza su a salon roƙo 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
"babu ita a cikin tsarin rayuwa ta abinda take fuskanta yanzu a gidan ta sakayya ce"
"i know na sani don Allah kayi mata magana ita kanta she is suffering, cant u see, she thought u r dead"
"ta sa aranta cewar am dead ne shiyasa cant u see bata so na tunda har zata iya yin ƙarya dan da ta haifa ya mutu bayan ita ta gudu ta barshi yet kina son kice min in yi haƙuri in mata magana, pls let's stop here is ok"
"habibi.................."
"shhhhhhhh mu daina musu akan hakan ya isa da mun gama abinda muke a nan zamu wuce nigeria mu man ta da ita, kuma kema ina son ki yanke duk wata hulɗa da ita, don bata buƙatata ta shi yasa ta ce na mutu let me just act as dead ɗin kamar yadda take so"
"pls pls plsssssss"
"zainab, can u pls stop it" ya faɗa da ƙarfi wanda har sai ɗan da ke ciki na ya motsa saboda tsawar daya daka min
Shiru nayi na kifa kaina tare da sakin sabon kuka, wayyo yau Allah ya haɗa ni da wani murɗaɗɗaen miji ya zanyi
Har muka koma gida babu wanda ya kuma kula ɗan uwansa ina shiga ɗaki kawai na shiga na kwanta ban daɗe da kwanciya ba bacci ya kwashe ni ko sallah isha ban yia ba
Cikin dare aliyu ya kuma tashi na da ciwon zuciyar sa tashi nayi na dinga yi masa kuka yadda ƙiri ƙiri yake son kashe kansa don kawai ya ɗauki fansar abinda mahaifiyar sa tayi masa alkcn ƙuruciya
Maganni na bashi ya sha Allah ya taimake shi bacci ya kwashe shi salla na tashi nayi na daɗe a sujjada ina gayawa ubangiji buƙatuna na Allah ya sanyaya mijina zuciyar sa da wannan halin nasa
Nai kuka nai majina duk wajen kaiwa ubangiji kukana, sai gab da sallah asuba sannan na sallame
Fes na jini don haka sai na tashi na shiga kitchen na ɗan haɗa ɗan abinci na ci sannan nayi niyyar ɗaukar azimi don a gaskiya lamarin aliyu yanzu tsoro yake bani
Da zazzaɓi ya farka don haka sai na koma jinyar sa ko kaɗan ban yi masa tunin abinda ya faru jiya ba
Na ce masa muje in raka shi asibiti ya ƙi sai kawai na saka masa na mujiya 👁👁, haka ya wuni yana ta nurƙususu a gado in ciwo ya ci yai ta salati tare da kuka yana kiran sunan Allah ko ta kanshi ban bi iyaka cin dak nace masa
"idan Allah yayi maka rasuwa dana fita takaba aure na zanyi" ya bani haushi ne iyakar bani haushi
Be kula ni sai ma kulle ƙofar ɗakin da yayi bayan na fita, sai la'asar ya fitƙ daga gani zuciyar tasa tayi sauƙi, be min magana ba kawai ya fice ni ma sai nayi kamar ban ganshi ba
Har ƙarfe 11:00 na dare be dawo ba kiran wayar shi nayi
"ina ka shiga ne har yanzu baka dawo ba"
"ina ruwanki ke da idan na mutu aurenki zaki yi ai se kije kiyi yanzu ma na barki"
"am sorry in shaa Allah kai kaɗai ne mijina duniya da ƙiyama"
"wannan cin hanci ne ko me"
"ni dai kawai ka dawo"
"to ya zanyi tunda na riga na mallaka miki zuciyata"
"a wannan zuciyar taka tana buƙatar wanki, in da gaske ka mallaka min ita to ka barni in wanke ta"
"tayi dauɗa kenan" ya faɗa
"bance ba ni dai kawai ka dawo"
"too shiken gani nan tun ance in dawo"
Be daɗe ba sai gashi, muka a jiye differences ɗin mu muka raya sunna a daren sai dai in ce sai da safen ku readers
*ina godiya sosai ga masu miƙo min addu'a Allah ya biya mana buƙatun mu na yau da kullum da ku da ni*
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page 51🌹
*wannan shafin naki ne ke kaɗai mummy rabi ta grp ɗin dangin sa, Allah ya biya miki buƙatun ki, adduar ki tana kashe min jiki na gode jazakilla bi khair Allah ya barmu tare*💖💖💖💖💖💖💖
Kashegari da safe da wuri muka shirya, suma su amina muka sa suka haɗa kayan su dana su haidar don baza mu bar su su kaɗai a gidan ba
Manchester muka fara zuwa gidan wani abokin aliyu me suna junior sukka( *tawa kaddarar* ) da matar sa fatima da ƴen ƴaƴan sa masu kyau masu kama da ƴen korea
Sun mana iso sosai, sannan muka keɓe da fatimar macece me mutuƙar kirki sosai mun sha hira da ita, na yadda take juya mijinta sosai kome tace sai yayi ta rawar kai yana yi
Abin ya bani mamaki ban yi nauyin baki ba na tambayeta irin wannan hidimar da mijin ta yake yi da ita haka
Murmushi tayi tace kafin in zo nan junior babu irin kukan da be sani ba har ƴaƴan mu na fari ya kira da shegu amma kinga da nayi haƙuri yanzu ya zama labari,
Don haka kema kiyi haƙuri shi aure akan haƙuri ake gina shi, na so ta bani lbrn auren ta amma sai tace min yanzu babu lkc sosai in bari indan mun sake haɗuwa zaki ji lbrna
*idan da me son jin lbrn auren fatima da junior ya nemi littafin TAWA KADDARAR*
Sai bayan azahar sannan muka bar manchester muka kama hanyar liverpool, sai dare muka je, hotel muka kama muka kwana don sai kashegari zamu wuce gidan mimma, fatana de kawai shine Allah yasa marasa kunyar ƴaƴan mijinta bazasu ba
Kashegari da wuri muka fita muka je gidan mimma acen ma mukai breakfast, sannan muka kama hanya da ƴaƴan mr muktar amma matan kaɗai banda namiji ko ba komai an rage iri na faɗa
muka kama hanyar bakin ruwan inda zamu shiga jirgin domin zuwa trip ɗin, muka hau muka fara tafiya, ɗaki uku ne a jirgin sai kitchen wanda akwai cook sai kuma masu tuƙa jirgin su biyu suma a ɓangaren su, muka ɗau ɗaya mimma ma suka ɗau ɗaya sai marasa kunyar ƴaƴan su suka ɗau ɗaya
Da rana muka fito ɗan farfajiyar jurgin domin cin abinci, table akai setting duk muka zauna muka fara cin abinci ina lure da mimma duk wani abun da zai haɗa ta da yaran nan tana gudan sa
Muna cin abincin hana wacce take yar yusra ce ta ce wa mimma
"yau salma lfy kike acting kamar wata saliha" yusra tayi dariya
"ƙila bata son embarrassing kanta ne"
"ku kuma da kuke lacking manners baza ku iya gani kuyi shiru ba" na faɗa, daga aliyu har mr muktar duk sai suka ɗago suka kalle ni shiru nayi na ci gaba da cin abinci na kamar ba ni na faɗa ba
Shiru suka yi na sha alwashin muddun a wannan tafiyar suka ce zasu yi wa mimma rashin mutunci sai na rama mata da su da uban su suji inda daɗi
Babu wanda ya kuma cewa komai har muka tashi, mr muktar da aliyu suka koma gefe suka fara kamun kifi wai da shi zamuyi dinner wanda zasu kamo ɗin
Su yusra suka koma ɗakin su don sun lura da irin kallon da nake musu na rashin M
muka zauna ni da mimma muna ta hirar mu yawanci jirar su haidar ne take tambayata ina bata ansa dai dai abinda nasa ni, tai min alƙawarin idan na haihu zata zo har nigeria ganin baby
Nayi murmushi na kalle ta a zuciyata na ce Allah sarki shi yasa kike son su haidar ashe su jininki ne ya za ayi in iya faɗawa matar nan cewar mijina ɗan ta ne
Zuwa dare cikin ikon Allah sun kamo kifin da zai ishe mu dinner amma tare da taimakon cook ɗin, grilled fish da potatoes sai kidney sauce akayi mana dinner, sai lemon curd a matsayin dessert,
Mun ci nan ma lau babu faɗa na fahimci su yusra matsoratan ƙarya ne, da wuri muka kama hanyar ɗaki don a gajiye nake bacci nake ji sosai
Da safe ba da wuri muka tashi ba, sai da muka makara, mun fito mun tarar da pancake wanda akai masa cream me strawberry flavour, ƙamshin pancake ɗin ma ya isa ya sa mutum ƙoshi sai cafe latté,
Ban taɓa shan café latté ba amma yau danayi tasting ɗin shi na fahimci dalilin daya sa mutane son shi, zaki ne haɗe da ɗaci wanda yake fitar da wani aroma me daɗi, ko daɗin aroma ɗin cafe ɗin ma ya isa ka sha shi, na ci pancake ɗin nan sosai, taste ɗin strawberry ɗin da ke cikin cream ɗin shi ya ja ni na ci dayawa ban sani ba, har aliyu yana tsokana ta
"habibti ko da cook ɗinnan zamu koma nigeria ne, yada naga kina cin pancake ɗin nan ban taɓa ganin ki kina cin abinci haka ba"
Ban kula shi don shiru ma magana ce, da rana aka kawo mana bufferlo chicken wings, da braised chinise rice wacce aka mata irin dahuwar fried rice, amma ita ta ɗan fi fried rice yin laushi, sai pasta salad
A ɗaki na zauna na ci abinci na don bana son fita inci karo da waɗancan ƴen iskan, muna cikin cin abincin ne naji hayaniya har na tashi aliyu yace in zauna in cigaba da cin abinci na shi bari yaje yaga menene,
Fita yayi amma maimakon inji shiru sai naji muryar hana tana faɗa da ƙarfi harda zagi, wannan jarababbiyar kuma ita da wa na faɗa ko kafan ban kawo a raina cewar mimma take zagi ba
Jin muryar mr muktar nayi yana cewa duk ba ke kika jawo suka raina ki ba, kukan mimma naji ai ban san lkcn da na fita a guje ba, na doshi inda suke amma kafin inƙarasa sai na hango mijina a durkushe riƙe da ƙirjin sa yana ta kakari kamar ya kasa numfashi ko kuma numfashin ne yake neman ɗauke wa
a guje nayi wajen sa ina kiran sunan sa *ALIYU* jin kiran sa da nayi ya jawo hankalin su ko kafin in ƙarasa inda yake jikin shi ya saki ya daina nunfashin gaba ɗaya ma
Da gudu na isa wajen sai ga su mimma, itace ta ƙaraso ta janye shi daga jikina da na rungume shi don ni a tunanina ko ya mutu ne taɓa pulse ɗin shi tayi taji yana nunfashi sai ta kwantar da shi a ƙasa tace duk a ɗan matsa sabida iska
"ki toshe masa hancin sa ki hura masa iska ta bakin sa" ta umarce ni, hakan nayi, ko bayan da iskar ta shige shi ita kuma sai ta fara danna masa kirjin sa don zuciyar sa ta fitar da iskar dana ɗura masa
haka muka dinga yi babi abinda nake yi sai kuka, wannan abun da aka yi yaƙi yi don haka mimma ta sa aka ɗauke shi sai cikin daƙin mu
wayar wuta ta ɗauko ta sa masa a ɗan yatsan sa babba ko wanne, tsirarar wayar kana ganin ɗan ƙarfen nan na ciki, sai da ta tabbatar da komai ya zauna dai dai sannan tace in matsa daga kusa da shi
matsawa nayi sannan ita ma ta koma gurin switch ɗin ta kunna sai gashi wayar ta fara shocking ɗin sa yana girgiza, kuka na saka sosai wai mijina ne wannan
sakon ɗaya sai ta kashe ta zo ta duba shi be dawo ba ta kuma komawa ta kuma kunnawa tana kunna wa ya fara tari sauri kashewa tayi tare da zuwa ta kwantar da shi ta cire masa wayar a hannun sa can sai gashi ya dawo hayyacin sa rungume shi nayi na saka kuka me ƙarfi
Asibitin su ta kira tayi reportig abinda ya same shi, a wayar suka dinga gayamata abinda zata yi masa, nima ta tanbaye ni a game da ciwon sa na faɗa mata an taɓa masa aiki a china, ta faa musu a binciken da sukayi sun gano ya samu heart attack ne kuma it is very serious don haka mu juyo don a kwantar da shi
Magani ta bashi ya karɓa ya shi sai bacci ita kuma ta fice daga ɗakin, abin mamaki cikin aljihun aliyu hoton mimma ne, nayi mamakin dana ga haka
sai yanzu na fahimci abinda ya sa shi heart attack ɗin nan wato jin zagin da hana take wa mahaifiyar sa ne yasa shi haka kuka na saka gaskiya lkc yayi da mimma zata san komai
tashi nayi na fita daga ɗakin zuwa ɗakin ta, ƙwanƙwasawa nayi muryarta a dashe tace min in shigo, idon ta ya kaɗa yayi jajir daga gani kuka tasha
gaban ta naje nace "mimma me ya saki kuka, me yasa baza ki bar mr muktar ba kije kiyi rayuwar daban da su, irin wannan abinda suke miki watarana sai ki kamu da ciwon zuciya ke ma rana ɗaya a rasa ki kinga kin jawowa masoyan ki" murmushi tayi
: "babu wanda zai yi missinga ɗina idan bana nan, more over kinga duk wannan abun da nake yi alhakin ɗana ne yake bina shiyasa duk abinda su hana zasuyi min bana cewa komai nasan cewar alhakin ɗan ƙaramin ɗana ne"
"mimma baki ganin ya kamata kije ki nemi ɗan ki yanzu" murmushi tayi
"zainab my son is dead" na ta shiga rattabo min tarihinta kamar yada aliyu ya faɗa amma ita daga ƙarshe sai tace bayan wata guda da tafiya sai iyayen ta suka ce ta zo ta ɗauki ɗanta
Ko da tazo gidan iya sai ɗan iyar yace mata ɗan ta ya mutu don yunwa don babu nonon da zai sha, anan sai kawai ta kuma fashe wa kuka, sai a yanzu na fahinta Allah sarki ba laifin ta bane kamar yadda aliyu ya faɗa ta dawo sharrin ɗaya daga cikin kawun sa ne
"mimma ɗanki be mutu ba" ma faɗa
"what" tace
"mijina shine ɗan ki da kike tunanin ya mutu"
A firgice ta kalle ni me kike nufi, hoton da ke cikin aljihunsa na ɗauko na miƙa mata, karɓa tayi hannun ta yana ta kalli hoton, wannan ai sune pics ɗin da sani ya haɗa musu cikin kayan da zasu nigeria da shi wanda suka bar wa buhari ya taho musu da shi
Kuka ne ya kubce mata nai mata duk baya nin da nasani game da aliyi ban gama ba ta tashi a guje tayi ɗakin mu, binta nayi naje na tarar ita akansa tana kuka
"Pls kar ka barni, na rasa ka kana jariri don Allah bana son in rasa ka so biyi u have to be strong don Allah ka tashi don ka rama abinda nayi maka ko sau nawa zaka rama indai zan ganka da lfyr ka i will be ok" ɗago ta nayi na rumgume ta alkcn ne mr muktar ya shigo yana tambayar me ya faru
Faɗa masa nayi sai naga yayi shiru kuma jikin sa yayi sanyi ya fice, mimma ko kuka ta ɗinga yi nima shi nake yi
Sai cikin dare muka iso bakin shore inda muka tarar da ambulance tana jiran mu ɗaukar shi akayi, sannan aka fara duba shi tun a cikin ambulance ɗin aka saka masa oxygen a hanncin sa don ya taimaka sa numfashi
muna shiga asibitin directly theater room aka shiga da shi, mu kuma muka tsaya a wajen duk ran mu a dagule daga ni sai mimma inda mr muktar ya tafi kai ƴaƴan sa gida
Har asuba sannan likitoci suka fito, bin ɗaya muka yi wanda daga ganin su shine team head ɗin su, office ɗin shi muka bishi, ya zauna ya ɗauko wani file ya gama ƴen rubuce rubucen sa, ya dube mu
"ku kwantar da hankalin ku abinda zan faɗa muku ba a kanshi aka fara ba kuma idan ya samu treatment zai warke" hankalina gaba ɗaya baya jikina burina kawai inji me zace, sai kawai naji yace
"zuciyar sa ta buga, ta tashi daga aiki, yanzu mun sa mana machine ne wanda yake taimaka mata take ɗon functioning, don haka yana buƙatar heart transplant" suman zaune kawai nayi
Subhanallahi ya Allah shi ne kawai na iya faɗa
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
0 comments:
Post a Comment