Service ɗina ɗaukewa yayi kasancewar wannan mummunar lbrin da nake ji ya samu mijina,
mimma naji ta dafa ni juyowa nayi na kalle ta
"zo muje mu ganshi" tashi nayi na bita amma gabaɗaya ba a cikin hayyaci na nake ba
Yana kwance a gadon marasa lfy sai oxygen da aka saka masa sai kuma wasu wayoyi da akayi connecting zuwa babban ɗan yatsan sa duka biyun, sannan kuma wasu abubuwa da aka manna masa a ƙirjin sa
Duk sai yayi wani fayau ya ramew sosai, kuka ne kawai ya ƙwace min ina yi mimma nayi mun rasa me share mana hawaye
Mimma ce ta fita ta barni ni ɗaya tausayin kaina ne ya kamani wayyo Allah ya tashi kafaɗar mijina ga ciki ina da shi fa mijina yana buƙatar zuciya ko tawa zan bashi ne inyaso sai a cire min cikin
Tunani ne ya dinga faɗo min a raina ni kaɗai, shigowa ɗakin ne ya dawo dani daga tunanin nawa, mimma ce ta shigo
"an samu zuciyar da za a saka masa"
"alhamdulillah na faɗa" ashe samun zuciyar ma babu wuya
"mimma ta musulmi ce" gyaɗa min kai tayi sannan ta koma kusa da aliyu kissing ɗin shi tayi sosai a goshin sa, sannan naga hawaye suna fitowa daga idon ta suna ɗiga akan fuskar sa
"pls 4 give me, don Allah ka yafe min zan so ace inyi ma bayanin dalilina na barin ka amma hakan bazai yuwu ba,
don Allah idan ka farfaɗo kayi rayuwa me daɗi na yafe maka a matsayi na uwa, kaima ina roƙon ka ka yafe min" mimma ta rinqa rokon Aliyu ya yafe mata tana kuka,
Ni na rasa dalilin da mimma take cewa bazai tashi ya same ta ba, dr. ne ya zo ya kira mimma sai naga ta kuma sunbatar aliyu sannan ta fita, me mimma take nufi da hakan
Fita nayi na bi bayan su, wani ɗaki suka shiga sun ɗan jima si gasu sun fito dr. ɗin yake cewar result ɗin zai fito gobe
Murmushi tayi masa sannan tazo inda nake sai nace
"mimma wane result ne zai fito kuma"
"am donating my heart to him"
"no no no and no u r not" na faɗa ina kuka
"mimma u cant donate ur heart, aliyu ba zai so zuciyarki ta kasance a jikin sa, mutumin da yayi missing ɗinki all of his life kice shi zaki bawa zuciyarki, tayaya kike tunanin zai yi rayuwa idan ya fahinci kin rasa rayuwar kine saboda shi, mimma idan kika bawa aliyu zuciyar ki kin kuma kashe shine don zai zauna iyakacin rayuwar sa da tunanin kin kashe kankine saboda tayaya kike tunanin zai rayu da wannan guilt ɗin pls mimma ki bari muje 4 donation mu samu zuciya pls ba taki ba he really need u by his side"
"zainab ya kike tunanin zan bari in rasa ɗana 4 d second time in my life da farko na rasa shi yanzu ma so kike yi in kuma rasa shin, ba zuciya ba ko komai na jikina aka ce inba ɗana zan bashi"
"pls mimma kar kiyi haka"
" na riga na gama magana in shaa Allah gobe result zai fito in yaso sai kawai ayi ni dai fata na ki riƙe min shi amana"
Kuka ne ya ƙwace min sarai na san halin aliyu ya za ayi mutimin nan ya tashi yaji cewar zuciyar mahaifiyar sa ce a qirjin sa ya za ayi ya iya rayuwa da wannan ko nice ake ansa wa zuciyar wani nawa dole in tausayawa wanda aka kashe don kawai a rayani balle shi da ba abinda ya taɓa yi wa mahaifiyar shi sai rashin kyautatawa tun da ya gane ta,
Don Allah ya za ayi mijina ya zauna da wannan guilt ɗin wannan kamar an kashe shi ne amma kuma yana rayuwa haka zai rayu da wannan guilt ɗin,komawa nayi ɗakin yana ta bacci kuka ne ya ƙwace min ɗa na tuno irin rayuwar da zaiyi nan gaba da zuciyar mahaifiyar sa aqirjin sa
Tj na ɗauki waya na kirashi na faɗa masa halin da aliyin yake ciki da kuma abinda ya dace ayi masa da kuma hukunci da mimma ta yanke
"wacece kuma mimma" shiru nayi sai yanzu na fahinci
ashe tj be san anga mmn aliyu ba
"mahaifiyar aliyu ce mun gano ta a nan"
"noo baza ta bashi zuciyarta ba aliyu will kill himself"
"nima haka nace, don yanzu zancen da nake maka ma an yi mata duk wani bincike da za ayi mata na cire zuciyar"
"no koma dai menene kice mata sai nazo kar a sake a taɓa min ɗan uwa sai na zo in bahaka ba sai na maka ta a kotu"
Ya faɗa da zafi tabbasa nasa cewar ciwon aliyun ne yasa tj ɗin hakan amma tj shi me sanyi ne, muka gama waya yace za ɗauko private plane ɗin aliyi ya taho a ranar don be sani ba ko akwai flight ɗin da zai zo nan liverpool ɗin a ranar mukai sallama ni da shi
Ko da dare yayi sai wata nurse tace min mu tafi gida don ba a kwana, muka fita amma ni sai na ƙi zuwa gidan mimma don bana son ganin waɗannan ƴen iskan yaran, mimma ta raka ni na kama hotel sai da taga nayi settling sannan tayi min sallama ta tafi
Kashegari da wuri mimma ta zo ta kawo ɗan abinda baza a rasa ba na jinya na riga ta zuwa don ni da sassafe na zo, wata takarda ta bani wai idan aliyu ya warke in bashi
Hannuna yana rawa na karɓa idona taf da hawaye na faɗa mata abinda tj yace murmushi tayi "ba komai duk abinda ya kamata ayi za ayi" ta faɗa tana shigewa office ɗin ɗr. ɗin
Jimawa kaɗan sai gata ta fito idon ta cike da ƙwalla binta nayi na riƙe ta mimma lfy
"wai dr.yace my heart is weak ba za a iya bawa aliyu ba he need a strong heart" kuka ta fashe da shi babu abinda nake yi sai hamdala don nasan mijina ba zai so ya rayu da zuciyar mmn shi ba
Tj be ƙaraso ba sai dare asibitin ya wuto direct, nan ya samu halin da ɗan uwansa yake ciki shima keɓewa yayi da dr. yace wai a cire tasa a sawa aliyun tooooo😳😳😳
Shima dr. ɗin yace ba za a cire tasa ba don he is very healthy kuma basa cire zuciyar lafiyayyen mutum su sawa mara lfy don ba shi da 100% na surviving bayan opperation ɗin, sukan fison zuciyar mutumin da yayi accident kuma aka fidda ran shi amma mutumin da yake da rai basa wannan gangancin
Sai alkcn na fahinci kenan hakan ne amma yayi wa mimma ƙarya, cakumar wuyar rigar shi mimma tayi tace
"ka cire min zuciyar da ke jikina ka sawa ɗana gwanda in mutu shi ya rayu, bazan iya rayuwa babu shiba pls pls pls" sai ta sa kuka
dr ɗin ya basu haƙuri tare da cewar ai samun zuciya ba wani abun bane kullum sai an mutu don haka kawai suje donation office su cike form the earlier the better
Tj ya faɗa masa cewar "mu musulmai ne zamu fi buƙatar zuciyar musulmi"
"dont worry if u r lucky u can find a muslin dying" ya faɗa yana fita
Donation dept ɗin muka je muka cike form, sannan suka ce mana muje idan an samu za a yi mana magana, da daddare bayan mun fito daga asibitin muka wuce manchester muka ɗauko yaran anan nake faɗawa junior abinda ya samu aliyun ya tausaya mana sosai sannan yace akwai abokin sa a nan asibitin manchestan zai yi masa magana ko za a samu zuciyar"
Godiya mukai masa sosai sannan muka fito da yaran, mama na kira na faɗa mata halin da aliyun yake ciki har da kukan mama, na ce mata zan turo su amina can har da su haidar su zauna a wajen ta har sai abinda hali yayi
A ranar su haidar su kar england kuka kawai nakeyi ina tausayin ƴaƴa na yanzu idan aka ce ba uban su ya zasu yi duk da de dukiyar da aliyu ya tara tafi ƙarfin ace ta ƙare nan kusa ko da juyata akeyi amma kuma uba kuma faaa Allah ka tashi mijina kasa a samu zuciyar nan
a daren muka koma liverpool ɗin, muka koma da sassafe muka je asibitin muna zuwa akai mana albishirin an samu zuciya murna kamar me amma kuma ba ta musulmi bace, nan fa murna ta koma ciki
*****************
yau kusan watan mu biyu a asibitin aliyu yana dai kwance a gaskiya innace a kwanciyar mu ba a samu zuciya ba nayi ƙarya don har wani aka kawo shima da irin matsalar aliyu amma ana samun zuciya aka biya aka yi masa dashen tunda shi kafiri ne, zuciyar musulmi tayi wuya sosai kasancewar ba garin musulmai bane
Kuma da in bari a sawa mijina zuciyar wanda ba musulmi ba gwanda in barshi a haka ƙia yanzu idan ya mutu ya wuce aljanna wacce haka muke fata amma idan aka saka masa ta kafiri fa ya zo yana kafirci bayan shekaru ɗari ya mutu ya shiga wuta fa ai ba ƙaunar sa nake yi ba
Tj da mimma sun so a saka masa kowacce ce amma ni na dage akan bazan yadda ba, bawai ba sa ƙaunar sa ba amma suna tuananin yadda zasu ne idan baya nan, mimma tana ganin Allah ya haɗa ta da ɗanta don haka bazabta bar shi ya mutu ba shi kuma tj yana ganin ba zai iya ba in babu ɗan uwan sa, inda na biye musu da tuni anyi aliyu aikin nan amma naƙi, naga gabaki ɗayan su hankalin su ba a jikin su ba don haka ni kuma sai na zama jaruma dole a cikin mu a samu jarumin in ba haka ba sai yadda hali yayi
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:53🌹
Bayan zaman asibitin ya ishi dr. ɗin aliyu ya ga babu wani cigaba ganin munƙi yadda da kowane zuciya indai ba ta musulmi ba, dr. yai mamaki sosai wai ne yasa bama son kowace zuciya, nai masa bayani zuciya ita ce mutum hadisi ne guda da ma'aiki saw yake cewa "akwai wata tsoka a jikin ɗan adan idan ta gyaru komai na jikin sa ya gyaru idan kuma ta ɓaci komai na jikin sa ya ɓaci" idan kuwa haka ne don me zan bari a sawa mijina zuciyar kafiri, bayan wnnan tsokar da ma'aiki (saw) yake magana ba kowacce bace face zuciyar ɗan adam
Don me zan bari a sawa mijina zuciyar da take ba a gyare ba, ko kaɗan dr. be fahimta ba, a zuciyata nace tayaya zaka fahimta tunda ba imani gare ka ba
"to yanzu zaku so kuga ɗan wanku ya mutu bayan ga zuciya," murmushi nayi tare da gyaɗa kaina
"in dai har haka ƙaddarar sa tace zan barshi ya mutu a matsayin sa na musulmi zan fi son haka akan in bari a saka masa zuciyar kafiri"
Sam dr. kasa fahimtar mu yayi don haka sai ya kawo mana shawarar mu canzawa aliyu asibiti wai akwai wani dr. Shima cardiologist ne tare sukai karatu kuma musulmi ne a ƙasar musulmai yake mu koma can ko Allah zai sa mudace amma zaman da mukr yi anan kamar zaman jiran mutuwar sa muke tun da babu wani hope
Nayi murna sosai ko ba komai akwai chances ƙila aliyu ya samu zuciya, a saudiyya cardialogist ɗin yake dr. ɗin namu yai masa magana tare da tura masa duk wani halin da aliyu yake ciki, ƙasancewar aikin sa ne nan da nan yace mu taho
Ƴ
Muka fara shirye shiryen komawa saudiyya, garin ta'if da ke ƙasar saudiyya anan asibitin yake, akan babban titin shiga garin yake kafin ma ka shiga cikin gari, ƙaton asibiti ne, wanda kamar branch ne na asibitin amri hospitals wani asibitin aikin zuciyane a india
Kana ƙarasowa zaka ga sunan asibitin wato *amri hospitals (annex)* muka shiga da shi wanda tun daga airport ɗin jidda ambulance taje ta ɗauko kasancewar aliyu bazai iya ci gaba da numfashi ba in dai babu oxygen don haka dole ne sai da medical practitioner kusa, duk da dai mimma pediatric ce amma ba za ayi bata kulawa da shi ba kasancewar mahaifiyar sa ce
Muna shiga da shi aka shiga da shi theater again don sai sun sake duba shi, sun daɗe don kusan awan su takwas da shi a theater inda daga ƙarshe suka fito
Binsu mukai gabaɗayan mu inda muka damu dr. Hisham shi kaɗai a office ɗin sa, wurin zama ya nuna mana muka zauna sannan shima ya zauna tare da ɗauko file ɗin aliyu
"a binciken da muka yi ya nuna aliyu is in a critical condition, ya buƙatar urgent heart transplant, don haka dole muyi yadda zamuyi don samun zuciyar don kuwa nan da 2weeks in bai samu zuciyar ba komai ze iya faruwa"
Ya faɗa da confidence a tattare da shi, shiru kawai mukai dukan mu, mun rasa ma me yin magana a cikin mu wai sati biyu, nice ma nayi ƙoƙarin yin magana
"yanzu kana ganin nan da sati biyun zamu iya samun zuciyar"
"ya dangan ta, amma akwai chances na za a asamu tunda kullum mutuwa ake yi a duniya, in shaa Allah yau na daka team akan su ne mo mana zuciya a kowane asibitin in shaa Allah za a samu"
Anan ma sai da mimma tace a saka masa zuciyar ta dr. Hisaham dariya yayi, yace mata mu musulmai ne wannan abinda ya samu ɗan uwan naku ƙaddara ce, ba abinda ya kamata da ya wuce muyi masa adduar Allah ya bashi lfy,
Amma ina kuka taɓa ganin an cire zuciyar lafiyayye don a sawa mara lafiyar da chances na survival ɗin sa is not stable, ku bari kawai mu duba yadda muka saba ba yau na fara wannan aikin ba, kuma in shaa Allah zai warke, ɗan uwanku bashi da wata matsala da ta wuce ta zuciyar sa mun duba duka organs ɗin jikin sa they are ok and fit don haka daga anyi transplant ɗin in shaa Allah shike nan"
Allah ya sa muka ansa baki ɗaya sannan dr. Hisham ya sallame mu,aka fara neman zuciya
Kullum sa rai muke yi ko zamuji an damu zuciya abin takaici yawancin mutanen da ake kawo wa zuciyoyin na da matsala, ko ace hayaƙin taba yayi wa zuciyar illa ko kuma dai wani matsala na daban ga kuma lkc kullum ƙara wucewa yake yi
Kuma jikin aliyu a kullum ƙara tsanan ta yake, inda dr. Hisham yake shaida mana cewar da lkc ya cika zai cire wa aliyu abinda yake taimaka maka bugun zuciyar, don shima yana da lkcn expiring
Ko kaɗan kasa fahimta nayi sai na tanbayeshi to idan ka cire masa kuma yaya zai yi, shiru likitan yayi sannan yace
"shi wannan abun da kike gani akwai lkcn da yake aiki, idan zuciyata ta kai certain point na weakness to barin abun a jikin mutum ya fi cire shi haɗari, don me makon ta taimaka masa sai ta kashe shi so gwanda a cire in dai har lkcn ya yi"
"to in aka cire kana ganin zai daɗe har mu damu zuciyar"
"a yadda zuciyar mijinki take yanzu in aka cire masa zai iya yin awa sha shida, amma daga nan sai yadda hali yayi bazan muku guarantine zai ci gaba daga nan ba" shiri kawai nayi ni yanzu ma bana kuka idan naji halin da ake tunanin mijina nan gaba don kullum sai ka ƙara jin wani matsalar
Yau ana saura kwana biyu appointment date ɗin cirewa aliyu abinda yake sa shi bugun zuciya yayi, ya tashi tun da muka zo saudiyya sai yanzu ya farka, yayi fari ya wani ɗashe kamar ba shi ba
Zuwa nayi kusa da shi na tashe shi a daidai lkcn tj da mimma suka shigo don sunje neman zuciya amma daga ganin fuskokin su an san ba a dace ba
"ɗan uwa ka farka"
"gyaɗa masa kansa yayi amma be ce komai ba" kira likita mukai yi ko za a iya bashi wani abun yaci, amma likitan yace kar a bashi komai nurses ɗin su zasu masa preparing abinda zai ci
Aliyu ya gyara zaman sa sosai inda mimma ta zauna kusa da shi tare da dafa shi ya kalle ta yayi murmushi nayi mamakin da ya canza na ɗauka idan ya farka ya ganta zai haukace amma sai na ga saɓanin hakan
"pls ki yafe min da duk abinda nayi miki..................." bata bari ya ƙarasa ba ta rufe masa bakinsa, ta fara kuka tana bashi haƙurin itace ya kamata ta roƙi gafarar sa
Nima sai suka bani tausayi, aliyu sai ya fara barin wai wasiyya................ Hmmmm babbar magana
"tj don Allah idan na mutu ka auri zainab ka riƙe min ƴaƴa na" ya juyo gare ni
"naso ace na zama uba da miji da jigo gare ku ke da ƴaƴa na amma ban ga hakan na shirin faruwa ba don Allah ki kular min da ƴaƴa na kuma ga ɗan uwanan ki aure shi shi kaɗai ne zai iya kular min da ku" kuka ne ya kwace min inda tj ya matso har kusa da aliyun sannan yace
"ni ban karɓi wannan amanar taka ba idan zaka tashi ka kula da iyalinka ka tashi idan kuma baza ka tashi ba shike nan ni dai ban karɓi wannan amanar ba" yana gama faɗin hakan ya fice sosai na ga alamar kuka a tattarebda shi daga gani baya son yi ne a gaban mu
Mimma da bata san abinda yake faruwa ba ta tambayeni na faɗa mata ita ma kukan take yi
"haba ya za ka faɗi haka na rayu akan rashin sanin kana raye yanzu na ganka kace kuma zaka kuma barina, tayaya kake shirin inyi iya rayuwa babu kai, ada ina da ƙuruciya shi yasa na iya jurewa amma yanzu i cant do wihtout u"
Kuka duk muka sa inda aliyun yake ƙara jaddawa mimma ta kular masa da mu ita kuma tana girgiza kai, muna cikin wannan halin ne zuciyar aliyun ta kuma motsawa wayyo Allah dai kun tausaya masa yadda yake yi gaba ki ɗaya lkc ɗaya ya fita hayyaci sa switch ɗin da ke kusa da gadon sa na danna nan da nan sai ga likitoci sun danno suna zuwa kora mu waje sannan suka fara aikin sun babu kama hannun yaro
Fitar mu ke da wuya sai ga wata mata ta shigo tana rusa ihu wai a taimaka mata ihu take yi iya ƙarfin ta, nurses ɗin asibitin ne suka fito da gudu sai ga shi an shigo da wani akan wheelchair duk jikin sa jini barin ma kansa an ɗaure kan da wani ƙaton bandage amma duk da haka jinin zuba yake, theater aka wuce da shi directly
Basu jima ba sai ga dr.hisham ya fito daga theater room ya doso wajen matar, da larabci naji yana mata magana don haka ban ganr me yake cewa sai kukan ta kawai na kuma ji sai ta bani tausayi
Lallashin ta ya dinga yi sannan ya ce wata nurse ta kawo masa file matar ta sa hannu ko da aka kawo file ɗin mema kon matar ta sa hannu sai kawai ta fara ihu tare da tsalle kamar ana dukan ta
Abin ya bani mamaki ban gama mamaki ba sai ga dr.hisham ya zo wajen mu
"mr aliyu kinga waccr matar da take kuka" gyaɗa masa kai nayi,
"ɗanta mutuwa zai yi nan da yen mintina don haka naso ta sa hannu a cire zuciyar sa idan ya mutu kafin zuciyar ta daina bugawa amma kamar bata fahinta ba amatsayinki na mace ko za ki iya yi mata magana aka...............
Be gama bayanin nasa ba na warce file ɗin nayi wajen matar me ihu, sai da na fara lallashin ta da turanci kasancewar tana ji dai da naga zuciyarta ta nutsa sannan nayi mata maganar signing
Aikuwa kamar na kuma tursasata sai ta kuma zunduma uwar ƙara wai za a kashe mata ɗa ne, babu yadda ban yi ba, tun ina yi ni kaɗai sai ga mimma ma ta shigo taji halin da ake ciki
Mimma har durƙusawa matar nan tayi akan ta sa hannu amma matar nan ƙiri ƙiri ta shafe wa idon ta rashin M, da anyi mata maganar sai ihu
Tun likitocin suna tausaya mata har suka gane bata son bayar wa ne, wani dr. ne ya fito daga theater room ya zo yayi wa dr.hisham magana a kunne nan da nan naga hankalin dr. Hisham ɗin ya tashi
Karɓar file ɗin yayi yaje kanshi tsaye yace mata ɗan ta ya mutu ɗin hakabta sa hannu a cire zuciyar tasa, wallahi matar nan sai ta fara abu kamar me bori, tana ihu tana tumuwa a ƙasa tana abu kamar na mahaukaciya
Ɗaga ta nayi ina kuka ina cemata don Allah ta dubi girman Allah ta bamu zuciyar nan ko bata bamu don komai ba ta dubi cikin da ke jikina ta ba mijina zuciyar ɗan ta ko na haihu abinda zan haifa ya ga uban sa amma matar nan ƙiri ƙiri ta ƙi
Can zuwa anjima sai ga wannan dr. ɗin ya kuma fitowa ya kuma faɗawa ɗr.hisham magana again a kunnen sa, kawai sai naji dr.hisham ya ce mata
"zuciyar ɗanki ta daina harbawa i hope u are happy 4 not helping those in need" wulla mata takardar yayi a fuskarta yayi gaba
Zama nayi a gaban matar nan ina kallon ta ina kuka ita ma mimma haka dai naji kamar wannan itace damar mu ta ƙarshe amma matar nan ta nuna rashin imani a tattare da ita
Tashi nayi da naji dr.hisham da wasu likitocin suna guje gujen shiga ɗakin aliyu don na'urar dake ɗakin sa ce take alarming ```ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit``` alamar danger muna zuwa kusa da ɗakin aka dakatar da mu
Kuka kawai nake yi sun jima sosai sai ga su sun fito inda dr.hisham ya buƙaci ganin mu, muka bishi office ɗinsa, sai daya zauna sannan ya fara magana
"a bisa binciken da mukayi mun gano cewar gaskiya aliyu inbai samu theater nan a yau ba in shaa Allah gobe zamu cire masa duk wani ƙarfe na jikinsa don yanzu a haka ma they not helping him, but hurting him don haka in shaa Allah gobe da ƙarfe 12:00 na safe zamu cire daga nan kuma sai yacce hali yayi" kasa kuka nayi don nasan bashi da amfani
"dr. ya shi aliyun yake"
"well am sorry to say he is not helping at all, zan iya faɗa muku a halin yanzu aliyu is not fighting 4 his life he has already given up, don haka yanzu kawai sai yadda hali yayi, kunsan wataran idan mutum yana da burin ya rayu to sosai yaka taimakawa likita amma aliyi yanzu ko kaɗan baya taimaka ya riga ya losing hope na rayuwa don haka sai haƙuri"
Jikina a sanyaye na fito daga ɗakin, directly ɗakin aliyu na nufa ina kallon sa gobe iyanzu bamu da tabbacin kana raye ko ka mutu ko na faɗa,
Ko da tj ya dawo da daddare mimma ce ta iya faɗa masa kasa cewa komai yayi sai hawaye kawai, kasancewar bama kwana a asibitin yasa da dare yayi tj da ƙyar ya lallashe mu muka tafi ni da mimma
Tunda muka je ɗakin da muka kama na hotel sai muka kasa duk muka zauna mukai jugum jugum nice ma na gaji daga ƙarshe na tashi na ɗauro alwala na fara gabatar da sallah don in roƙi Allah ya kawo mana sauƙi a wannan lamarin, ita ma mimma sai ta bini ta fara sallahr
Ƙarfe biyu dai dai muna cikin ibadar mu naji wayata ta fara ringing ƙirrrrrrrrrrrrr innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine kawai abinda na faɗa
Ko da na duba wayar number tj na gani, wayyo Allah na kawai na iya faɗa na je gurin mimma na rungume ta na san yau ta aliyu ta ƙare
Ruƙunƙume juna mukai ni da mimma muna kuka, wayar ce ta kuma ringing again wannan karon tsorata mu tayi ni da mimma inda muka ƙara manne wa da juna
Ko da tayi ringing a karo na uku sai mimma tayi ƙarfin halin ɗaukar wayar ta doka ta da ƙasa ni kuma nabi ta ina tattaka ta don nasan ƙarshen alawa ƙasa ne irin yadda jikin aliyu ya rikice a yau ɗin nan amma ko kaɗan ban kawo zan rasa mijina yau ba
Kuka sosai muka dinga rusawa ni da mimma ni na rasa mijina uban ƴaƴa na ita kuma ta kuma rasa ɗan ta wayyo Allah na
Tj ne tsaye a gaban gawar yana ƙare masa kallo buɗe ɗan mayafin da aka lulluɓe shi yayi yana kallon sa tare da binsa da addua
"abinda kayi mana Alƙah yayi maka Allah yasa mutuwar ka hutu ce a gareka, Allah ya jikan ka ya duba bayan ka" rufe shi yayi sannan wasu suka tura gawar zuwa mortuary don a adana ta kafin safiya sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai baki ɗaya
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:54🌹
Tj yana tsaye a bakin theater room ɗin sai safa da marwa yake yi tare da roƙon Allah yasa ayi aikin nan cikin sa a,
Tun kusan ƙarfe 01:00 na dare yana cikin sallah yaji hayaniya a cikin asibiti ko da ya idar sai ya fita don yaga ko menene, sai yaga alamar jini a ƙasan alamar anyi hanyar theatet, bai daɗe ba sai ga dr.hisham ya fito ya doshi reception in da mutanen da suke jira suke
Can sai gashi ya dawo da wasu likitoci directly ɗakin aliyu suka nufa sai gashi an fito da shi komai da sauri sauri suke yi ko dana tsayar da su in tambayi ko menene sai likita ɗaya yace an samu heart,
Sujjada nayi shukuriyya ga Allah daya kawo mana wannan zuciyar a lkcn da muka fidda tsammanin samu, sun ɗan jima a theater room sannan sai gashi an turo gawar an fito da ita
Tj ne ya tsayar da waɗanda suka fito da gawar sannan yai masa addua tare da godiya da zuciyar da ya basu duk da dai baji ze yi ba sannan aka rufe aka wuce da shi mortuary,
Tun daga lkcn ya koma kusa da theater room yana ta roƙon Allah yasa ayi aikin nan cikin sauƙi, su mimma ya tuno don haka sai ya ɗauki wayar sa ya kira zainab don ya faɗa mu su abinda ya faru, yai mamakin da suka ƙi ɗauka ko bacci suke yi ya faɗa
Ya kuma kira amma ga mamakin sa sai tana fara kira taji a number busy, daya kuma kira kuma switched off, tooo Allah dai yasa lfy ya faɗa
Basu suka fito daga theatet room ba sai ƙarfe takwas na safe, likitocin duk suka fito fuskar su ɗauke da fara'a wannan ya nuna min alamar aiki yayi kyau kenan
Adaidai lkcn ne wata nurse tazo tace za a ɗauki gawar jiya sai yanzu ma na tuna cewar banyi wa wanda yayi mana signing aka bamu zuciyar godiya ba
Don haka sai na bi bayan dr. Hisham, wata dattijuwa ce zaune da tasbaha a hannun ta idon ta yai ja sosai daga dukkan alama tayi kuka amma idan ka ganta a nutsen ta take, daga gani imani ya ratsa ta sosai
Har gaban ta naje na durƙusa ina kuka ina gode mata da turanci, murmushi tayi min tace min ince wa ɗan uwana ya kular mata da zuciyara ɗanta
Daga haka sai ta fice, bin bayanta nayi da kallo yadda take tafiya da nutsuwa gaskiya indai wannan mamacin yayi halin wannan baiwar Allah to tabbas ɗan uwa yayi sa ar zuciya na faɗa
Gurin dr. Hisham na je nace ko zan samu address ɗin matar sai yace min a madina suke daga nan ma madina zasu wuce ayi jana'izar ɗan nata, sai ta bani tausayi ita kaɗai ce zata tafi da gawar a ambulance, gaskiya dole ne in bita don inga inda take nasan idan ɗan uwa ya tashi dole ne ya so ganin wacca ta taimaka masa
Tambayar ɗan uwan nawa nayi inda dr. Hisham yace ba wanda zai ganshi sai gobe da safe kasancewar ya wahala sosai kafin aikin don haka sun kai shi ɗakin hutu sai gobe zasu fito da shi
Jin hakan ya sani bin matar nan da gudu har motar ta fara tafiya na bita da gudu suka dakata sannan na shiga, kamar yadda nayi tsammanin kuwa haka ne ita kaɗai ne ce a bayan ambulance ɗin tare da gawar ɗan shiga nayi tare da yi mata sallama ta amsa da fara'ar ta
"me kake yi anan kaje ka kula da ɗan uwanka"
"sai gobe da safe zai farka in shaa Allah, kuma wannan ma ɗan uwana ne tunda zuciyar ɗan uwan ne a jikin sa don haka bazan rabu da shi ba har sai naga ya kwanta cikin kabarin sa in shaa Allah"
Bata ce komai ba sai murmushi kawai da da tayi muka fara tafiya, ko da muka zo bakin get sai na faɗa wa me guard idan su mimma suka zo ya faɗa musu na tafi madina jana'iza,
Tafiya ce me nisa sosai daga ta'if zuwa madina,
Mun sauka lfy nai mamakin da naga babu wanda ya zo tarar mu, harami muka wuce da shi directly ni na tsaya a matsayin ɗan uwan sa a lkcn da ake masa sutura, duk da dai ya kasance balarabe ni kuma baƙi 🙍🏻♂🙍🏿♂
sai da aka gama na fito zan kira baiwar Allahn nan sai naga wata yar matashiya da hijab a jikin ta, sai kuma wan yaro da bai wuce shekara uku ba
Matar nan ta gabatar da matashiyar nan a matsayin matar mamacin shi kuma ɗan ƙaramin ɗan ɗansa ne, ɗaukar yaron nayi me suna al amin na sunbace shi
Allah sarki Allah ya haɗa qaddarar mahaifinka dana ɗan uwana dole sai mahaifinka ya rasu sannan ɗan uwana zai rayu
Raka su nayi suka ganshi tare yi masa addu'ar sannan ya rako su cikin masallaci wajen ɓangaren mata suka zauna
Tare da faɗa musu bayan janai'zar zai zo ya kaisu gida, sai da aka sallaci sallahr la'asar sannan aka sallaci yahya, ba abinda zamuce sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai
Bayan an idar ya zo ya samu su ya ƙara yi musu godiya sannan ya nemi daya yana son ganin gidan su, amma ummu yahya sai taƙi tace masa ita don Allah ta taimaka musu ba don komai ba
Faɗa mata yayi wanda ta ba zuciyar yana da mata da uwar sa yana son kawo sune suyi mata godiya amma ƙiri ƙiri sai taƙi tace kawai ayi masa addua
Babu yadda zai yi haka ya wuce ta tafi sai ya samu wuri ya ɓoye don yasan idan ɗan uwan sa ya farka yaji be san mazaunin donors ɗin sa ba kashe shi kawai ba zai yi ba
Ko kuma ƙila aɗan uwan sa ya canza koooo? tunda yanzu ba zuciyar da gare shi ba, binsu ya dinga yi a baya tafiya ce me nisa amma suka yi ta aƙafa ya tausaya musu daga gani basu da shine
Sunyi tafiya kusan ta minti 20 sannan suka zo wani gida ɗan ƙarami a wani ɗan lungu suka shiga, sai da ya tabbatar da nan ne gidan nasun sannan ya wuce,
Ko da ya koma ta'if dare yayi sosai, don haka sai ya wuce hotel ɗinsa ɗirectly yai mamakin da wunin ranar beji daga zainab ko mimma, don haka ɗakin su ya wuce directly
*****************
Mimma da zainab kwana sukai basuyi bacci ba,ko da gari ya waye sai suka ƙi fita, sai da suka ga azahar tayi sannan suka fita asibitin suka je, a bakin get suka ci karo da me guard ɗin da tj ya barwa saƙo ya faɗa musu ya tafi jana'iza madina zainab kusan faɗuwa tayi dabadan mimma da ta riƙe ta ba suka shige ciki don su ga abin a zahiri
A maimakon su ƙara tambaya a cikin asibitin sai suka ƙi sukai ta shashancin su, su a tunanin su ya rasu tj ya ɗauki gawar zuwa madina don aliyu ya bar wasiyya in ya mutu a nan a binne shi a madinar, fara haɗa kayan su sukayi sannan suka fito
Reception suka wuce don closing biƙl ɗin amma sai receptionist ɗin tace sai dr.hisham yazo don haka su saurare shi, zazzaɓi ne sosai a jikin zainab don haka sai mimma ta ce bari ta kaita gida in yaso sai ta dawo
Komawar su gida yayi dai dai da dawowar tj, a wajen hotel ɗin suka ci karo shi, zainab tana ganinshi ta fashe da kuka, mamaki ne ya kama shi, ya ƙaraso wajen su
"yayata lfy me kuma ya faru"
Wani kukan na ƙara fashe wa da shi, mimma ce ma ta iya magana
"me yasa ka binne shi ba tare da mungan shi ba" sam se be gane me take nufi ba
"me yasa zaka binne min ɗana ban ganshi ba" ta kuma faɗa da ƙarfi,
"mimma aliyu be mutu ba, wanda ya ba aliyu zuciya ne naje jana'zar sa"
Da sauri muka ƙaraso wajen tj
"kana nufin an samu zuciyar, to ina aliyu yake" tambayoyi muka cika tj da shi shi kuma ya ƙi ansawa sai kawai murmushi da yake yi, tas tj ya larabta mana yadda akayi nayi kuka nayi murna na godewa Allah sosai sannan nayi wa yahya adduar Allah ya jiƙan sa
cikin hotel ɗin muka koma don munji sai da safe zasu bari a ganshi, a daren ranar kasa bacci nayi don kawai ina ɗokin gari ya waye inje inga mijina
ana idar da sallah asuba muka kama hanya amma ko da muka je asibiti sai dr.hisham yace sai 08:00 na safe zamu ganshi don ya ma tashi amma sai ya cika ƙa'idar lkcn daya dace zamu ganshi
koya zanga aliyu na faɗa araina, murna nida mimma kamar me,muna cikin wannan halin ne aka kira tj daga nigeria wai salma tana naƙuda, murna a wajen tj har yana cewa indai namiji ne to in shaa Allah sunan ɗan uwana zan saka
sai ƙarfe takwas muka shiga naga mijina a zaune yana ta murmushin sa a guje naje na rungume shi duk da dai cikin da ke jikina ya hana ni rungume sosai wanda yanzu nake cikin watan haihuwa
Mimma ma rungume shi tayi sannan suka gaisa da tj murna sosai nake ji har na faɗa masa matar tj tana naƙuda
"ɗan uwa ka shirya ka koma nigeria don tara ɗan jariri tunda kaga na warke"
"in shaa Allah ɗan uwa zan koma ko yau ko gobe"
har bayan la'asar shiru shiru salma bata haihu ba hankalina gaba ɗaya ya tashi shima tj ɗin daga gani kawai daurewa yake, in ya kira sai ace masa har yanzu dai, sai magariba sannan sai ga waya a lkcn aliyu yayi bacci
ko da tj ya ɗauka da fara'ar sa
"me na samu" ya faɗa da murnar sa, a maimakon inga yaci gaba da murna sai naji yace
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un, salmar ta mutu" jikina ne yaɗau rawa, kashe wayar sa yayi ya saki kuka
rasa abinda zan masa nayi nima sai na saka kuka ko ba komai na san salma sosai kuma jinyar mijina Allah yayi bazasuyi bankwana da mijinta ba
kuka wiwi tj yake yana tausaya wa kan sa da ƴar sa islam nima ina taya shi mimma ce ta lallashe shi sannan tace sa ya tashi ya kama hanya Allah yasa ya samu jirgin da zashi nigeria a ranar
har bakin asibitin muka rako shi mukai sallama tare da ƙara yi masa ta'aziyya har ya tafi sai ya dawo
"don Allah kar ku gaya wa ɗan uwa salma ta rasu ku bari idan ya warke sai a faɗa masa"
gyaɗa kaina nayi nima dama hakan naso yi muka ƙara sallama ya kama hanya babu abinda zamuve sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai baki ɗaya
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:55🌹
*ina murna sannan da ban godiya ga mmn farida da ta kammala littafin ta samun wuri duk da dai da sannu sannu aka tafi amma dai an kai ƙarshe babu abin da zamu ce sai Allah ya ƙara basira*
*Sannan ina miki murna da fara sabon littafin ki faccala da fa'iza ƴar baba, Allah ya bada ikon gamawa lfy sannan da fatan ba za ai mana tafiyar hawainiya* 🦎😁😁😁
Ko da aliyu ya farka ya tambayi tj sai nace masa ya tafi nigeria, ya nuna jin daɗin sa da matar ɗan uwan sa zata haihu har da addu!ar Allah ya sauke ta lfy na amsa da amin
Sai da tj ya sauka lfy sannan ya kira ni na ƙara yi masa gaisuwa tare da tambayar abinda aka samu sai yace min bata ma haihu ba Allah ya karɓi abar sa, wayyo na tausaya masa sosai
Ya tambayi jikin aliyu na ce masa da sauƙi yana ma ta tambayar sa, yai masa fatan samun lfy sannan mukai sallama
Aliyu ne ya matsa min na kira tj yayi masa ta'aziyyar ɗan kasancewar na faɗa masa ɗan be zo da rai ba amma ban faɗa masa rasuwar salmar ba don yanzu neman hanyar da zuciyar da aka dasa masa ta warke muke yi
Aliyu yana da sati 3 a asibitin na tashi da naƙuda anan asibitin Allah ya sauke ni lfy na samu saurayi na kyakkyawa fari tas da shi duk yafi ƴaƴa na fari har shi ma aliyun ya fi shi haske
Mimma da aliyu sukai murna da wannan ƙaruwar da muka samu a donga waya ina faɗawa mutane ƙaruwar da muka samu, aliyu ne ya kira tj ya faɗa masa, tj yai masa murna da kuma alƙawarin zai zo
Ko da ranar suna ta zagayo aka saka wa ɗana suna *yahya* sunan wanda ya bawa aliyu zuciya mimma ce ta ce a saka sunan nima da aka faɗa min sai naga dacewar hakan don babu abinda zamu iya ce masa sai dai muce Allah ya jiƙan sa
Watan aliyu biyu aka sallame mu, muka koma makka inda dangin mimma suke ta gabatar da da aliyu a matsayin ɗanta da aka ce mata ya ɓata, da ni kuma a matsayin matar sa
Sun sha koke koke sun kana gada ƙarshe aka kaimu masauƙin mu, dangin mimma babban dangin ne sosai a cikin garin makka, mun zazzaga su kana daga bisani muka koma ainihin gidan mimma wanda ta gada a wajen mahaifin ta
Sai da na kusan arba'in sannan tj ya zo duk ya rame kamar ba shi ba sai a lkcn ya sanar da aliyun mutuwar salma, kuka ne kawai aliyun be yi na tausayawa ɗan uwansa da yayi tare da kuma ƴar ta da ta bari
Sai da tj ya nutsu ne sannan aliyu yace masa yana son ya raka shi gidan ummu yahya zai mata godiya, tj ma ya yadda da hakan don haka sai muka fara shirin zuwa madina gurin ummu yahya,
Da sassafe muka shirya muka kama hanyar madina, bamu isa ba sai azahar don haka directly masallaci muka wuce inda tj ya tafi kama mana hotel
Sai da muka sallaci isha'i sannan muka koma hotel ɗin da aka ka mana wanda bashi da nisa da haram ɗin, wanka nayi kawai na hau gado sai bacci, ina jin aliyi ya shigo yana min mitar
"matar nan tun da akai min aikin nan na fahimci gudu na kike yi yanzu ma dana gama budgeting in mun zo madina muyi honey moon shine kafin ma in shigo har kin yi bacci ko"
Ban kula shi ba bacci na kawai na cigaba da yi don bacci ne sosai a kai na, kyakkyawar runguma naji yayi sannan shima baccin ya kwashe shi
Kashegari sai da azahar sannan muka koma harami sai da mukai la'asar sannan muka fito don zuwa gidan ummu yahya, wani kanti muka fara tsayawa tj yai musu siyayya sannan muka kama hanyar gidan, ɗan tafiya ne babu laifi sannan muka zo, inda mukai parking mota muka fito, gangarwa za a yi a shiga wani lungu don haka sai tafiyar ƙafa
Su aliyu suka samu wasu yaran suka ɗau musu kayan sannan muka kama hanya, gida na uku a layin muka tsaya inda tj ya ce mu shiga ni da mimma muyi musu magana
Ƙwanƙwasa ɗan ƙyauren gida mukai, wata ƴar dattijuwa ta zo ta buɗe da fara'ar ta, muka gaisa sannan tace bata gane mu ba, tj ne ya matso ko da ta ganshi sai ta ɗan tsorata don ta san bata nuna masa gidan ba
Hanya ta buɗe mana muka shiga gidan, ɗan ƙaramin gida da ɗan tsakar gida sai ɗakuna guda uku da banɗaki ɗaya da kitchen a cikin gida sai kuma uban shirgi daga wani lungu can ƙarshen gidan
Ɗakin farko tai mana izinin mu shiga, muka shiga da sallama, babu komai a ciki sai dadduma sai tv akan tv stand ɗinta da wani yaro yana zaune yana kallon cartoon
Ko da muka shiga yaron kawai bin mu yayi da kallo tj ne yace
"al amin ta'al" da ɗan gudun sa ya taho ya faɗa jikin tj yana dariya tare da ce masa abbu,
"ɗan yahya ne wannan" inji tj, wayyo Allah na sai naji tausayin yaron har ƙwalla ta cika min ido, aliyu ne ya miƙa hannu ya ɗauke be ƙiba shi ma aliyun sai al amin ya kira shi da abbu
A daidai lkcn ummu yahya ta shigo da tray da lemu da ruwa akai inda naji tana yi al amin larabci, mimma ce ta tanka mata, inda daga baya mimma take faɗa mana wai ummu yahya tace al amin kar ya ƙara kiran mutane da abbun sa ba ta faɗa masa abbun sa yayi tafiya ba
Aliyu ne ya gyara zama sannan ya kalli ummu yahya ya tambayeta tana jin turanci, da murmushin ta ta gyɗa kai
"daga yanzu nine abbun yaron nan, don zuciyar abbun sa a jikina don haka babu abinda ya baban tani da abbun sa, baƙi idan kin ce masa kar ya kira wasu da abbun sa ba amma ni abbun sa ne"
Hawaye taf ya cika a idon ummu yahya inda take faɗa mana tunda mahaifin yaron nan ya rasu duk wanda ya gani sai ya kira da abbun sa
"to kar ka samu damuwa ga abbun ka ya dawo kaji al amin" aliyu ya faɗa yana shafa kan yaron kamar al amin ɗin yana ji
Tj ne ya ɗan tambayi matar yahya inda ummu yahya tace tana wajen aiki,
"aiki kuma, ai bata fita takaba ba"
"addini ya halatta mace ta nemi abinda zata rufa wa kan ta asiri koda tana takaba" ummu yahya ta faɗa
Haka ne amma ummu yahya ina dangin ku" inji mimma, sai da ummu yahya ta ɗan nutsa sosai sannan ta fara magana
" mu mutanen syria ne yau shekarar mu uku kenan a nan yaƙi ne ya koro mu daga syria, inda muka rasa duk wani dangi namu a cikin yaƙin yayana wanda ya kasance mahaifin nadia matar yahya kenan da matar sa da ƴaƴan sa, a gabana aka harbe su ina laɓe ya hana ni fito wa
Mijina uban yahya shima aka kashe shi a kan idon na don haka sai mukai ƙaura da ni da yahya da nadia muka taho da taimakon wani ɗan uwan mahaifiyar nadia wanda yakan sance yana taimakawa mutane suna tsira daga tashin hankalin nan
Tunda muka zo nan na ɗaura wa yahya da nadia aure don bana son in tafi in barsu su kaɗai ba tare da aure ba amma kunga inda aure a tsakanin su bazan ji komai don Allah ya ɗauki raina ba nasan na bar su a matsayin ma'aurata" ta daka ta
"daga yanzu ni zan ci gaba da kula da ku ni zan maye gurbin yahya in shaa Allah" inji aliyu
ummu yahya ƙi tayi sai da su mimma suka ba ki sannan ta yadda har da kukan ta,mimma ce ta ɗauki baby yahya wanda muke kila da mu'allim ta bawa ummu yahya
"ga yahya mun kuma samu, matar aliyu ta haifa" da hawaye a idon ta ta karɓe shi tayi kissing ɗin shi sannan ta rungume shi,
mun jima acan inda aliyu da tj suka fita suka barmu
ni nayi wa ummu yahya girki, sai kusan shida sannan nadia ta dawo, mun gaisa sosai da inda inda ummu yahya tayi mata bayanin mu muƙa ɗan taɓa yar hira sannan su aliyu suka zo muka tafi
Satin mu biyu muka koma nigeria mimma ma nigeria ta bimu, ashe ta kashe auren ta bamu sani ba wai dama rashin aliyu ne yasa ta zaman auren amma yanzu taga ɗan ta baza kuma rayuwa babu shi kusa da ita ba
Bamu daɗe da komawa ba su mama suka zo da su maryam suka zo duba aliyu, inda aka dawo da su haidar
Ko da suka tashi tafiya sai aliyu yace amina ta zauna, mama taji daɗi sosai da aliyi yace zai riƙe amina, ko da suka tashi tafiya aliyi yayi musu kyauta sannan ya kuma tuna musu da tafiyar su hajjin su
Aliyu ya ɗora tj akan kula da su ummu yahya, komai suke so da komai na al amin tj ɗin yayi musu
Nima naje kano nayi wa ƴen uwan salma gaisuwa tare da ɗauko islam ta dawo hannun na don naga sai pasin pasin akeyi da ita tj yaji daɗi sosai aliyu ma ya dawo da tj aiki nan kusa da mu a abuja inda ya gina musu gida kusa da juna shi da mimma wanda yake ƙasan jikin namu
Kowannen gida part biyu akai masa mimma tayi ta mita wai ita gidan da aka gina mata yai mata girma sosai don haka sai aliyu ya bata haidar da mohd su koma wajen ta duk da haka gidan part ɗaya kawai take anfani da shi
lkcn tafiyar hajji yayi su mama suka tafi mu kuma muka bi ta international muka je hajji ban ma san dani za ayi ba mun yi aikin hajji lfy mun gama sannan muka dawo, muka je madina domin gaisawa da ummu yahya
[7:47PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: [12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed💖: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:56🌹
*last page in shaa Allah tank u sooo much 4 ur support babu abinda zance sai shukran gare ku masoyan dangin sa yau Allah ya kawo ƙarshen littafin da fatan kun ji daɗin sa*
*ina fatan zaku saurare ni a sabon littafina me sunan*
💐💐 *RABO NACE*💐💐💐
*ana mugun tare*🤝
[12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed💖: Mun je gidan ummu yahya inda muka same babu lfy sosai amma kuma tace an sallame ta ne ma daga asibiti, aliyu yai ta faɗan tj be faɗa masa amma sai ummu yahya tace ai shima be sani ba itace ta faɗawa nadia kar ta faɗa don kar hankalin wani ya tashi
Karɓar mu'allim yahya tayi a hannuna tana shinshinashi tare da sunbatar sa ina iya hango wasu hawaye a idon ta amma si tayi koƙarin mai da su nima sai nayi kamar ban gani ba
Aliyi ne ya matsa kusa da ita
"ummu yanzu kema fa uwa ce gare ni don me zakice kar a faɗa mana ciwon ko gaskiya ban ji daɗi ba"
Haƙuri ta dinga bashi, muka tambayi nadia da al amin ummu yahya tace sun je kasuwa don kuwa nadia ta fita takaba, mun ɗan jima sai ga nadia ita ma aliyu yai mata faɗan cewar kar ummu ta ƙara ciwo bata kira shi ko tj ta faɗa ba
Kanta a ƙasa ta ansa, sai magariba sannan muka tashi tafiya sai ummu yahya tace
"Aliyu zamu koma syria ni da nadia da al amin mun gode sosai da ɗawainiyar da kake yi da mu"
Daga ni har shi ɗin bamu san lkcn da muka dawo ba daɓar haka na zauna a ƙasa
"ummu yahya syria me zakiyi a syria yanzu"
Murmushi tayi sannan tace
"bana son in mutu in bar nadia ita kaɗai sai wannan ɗan yaron shiyasa nake son maida ita cikin dangi, ko da de babu na kusa amma ai bazamu rasa dangi ba"
Kuka na saka mata
"don Allah ummu yahya karki koma syria ya za ai al amin ya tashi a syria a wannan tashin hankalin da ake fama da shi a syriar zaki kai yaron da bai son tashin hankali ba can, don Allah ummu yahya ku zauna anan"
Aliyu ne ya katse min maganata
"nima gaskiya hankalina be kwanta da zaman da kuke yi ku kaɗai anan ba, amma kuma syria ba gurin zuwa bane, me zai hana ku bimu nigeria sai ku zauna da mu tunda mun ruga mun zama ɗaya" aliyu ya faɗa
Kallon kallo muka tsaya muna yi inda daga ƙarshe ummu yahya tace ita bata yadda ba tunda take bata taɓa zama liability ba kuma in shaa Allah da tsufanta baza ta zama ba
Babu yadda bamu yi ba amma ummu yahya ta riga ta kafe sai sun koma syria haka muka tashi muka koma masauƙin mu ni dai zuciyata gabaɗaya bata kwanta min da tafiyar nan syria ba garin da kwata kwata basu da zaman lfy
Ko da muka zo kwanciya na so imu ƙara maganar amma sai aliyu ya hana ni yace da safe zai ƙara komawa wajen ta in shaa Allah
Da gari ya waye aliyu be samu damar zuwa gidan ummu yahya ba sai ni naje na same su suna ta haɗa kayan su wai ƙarshen watan nan zasu koma
Ɗaki na shiga kusa da ummu yahya na zauna akan tafiyar na cigaba da yi mata magiya amma sai tayi murmushi tace
" zainab na riga na gama yanke shawara, kuma in banda abinki in muka biku a wane matsayi muke a wajen ku"
"aliyu yace zai auri nadia" kawai naji baki ya furta
Ɗagowa tayi ta kalle ni sosai taga a magana ta babu ƙarya duk da dai ƙaryar nake yi, don Allah ya za ayi in bar ɗan yaron da zuciyar uban sa take ƙirjin mijina shiga cikin tashin hankalin bayan nasan cewar ƙaddarar uban sa ta haɗu da ta mijina in ban taimaka masa ba ai na zama butulu ban gode wa Allah ba ƙenan
Ajiya zuciya ummu yahya tayi sannan tace
"Zainab kin gani auren nadia da yahya ni na haɗa su ba wai son take yi ba amma saboda ni nawa tunanin ya bani cewar wannan shine mafita bata so haka na haɗa, yanzu kuma kice in kuma tursasata ta auri mijinki saboda wai mu je mu raɓu kusa da mu wallah bazan iya ba, amma kuma bazan hanaki tambayar ta kije kiji inta yarda ni banni da ta cewa"
Fita nayi na samu nadia tana haɗa kayan su al amin yana wasa kusa da ita zama nayi na zayyano mata ban ɓoye mata komai ba amma sai na ɓoye mata cewar ni na nemi auren
Shiru tayi kamar bata yadda ba sai dana ƙara nuna mata illar komawar su syria ko ta yadda zai shafi rayuwar ɗan ta sanna da ƙyar ta aamince tana kuka ban san ko kukan me take yi ba amma daga dukkan alamu tana tuna tsohon mijin ta ne
Ɗakin na koma na faɗawa ummu yahya murmushi tayi sanna tace maa shaa Allah
Sai da aliyu ya dawo gida da ddare sannan na faɗa masa ɓaran ɓaramar da naje nayi kamar ya rufe ni da duka haka yai ta min faɗa ni dai shiru nayi ina kallon ikon Allah be haƙura ba har sai da na kira mimma na faɗa mata itama tace hakan shine dai dai sai da tayi masa magana sannan ya sauko ya yadda
Oh Allah ni abu naga ta kaina wai macen da za ayi wa kishiya zaka ganta ana lallaɓa ta amma banda ni wai ni nake lallaɓa mijin na nayi abu kaɗan sai yace
"wallahi kika ɓata min sai ma ince na fasa auren" sai in bishi da ban haƙuri
Dole na danne kishi na na ci gaba da lallaɓa mijin nawa wanda aka saka ranar ɗaurin sa sati biyu masu zuwa, na kira tj na faɗa nayi mamakin da naji kamar be yi murna ba amma kuma sai na share don tunda salma ta rasu tj ya koma wani salihi
Aliyu ya tubure shi ƙwandalar shi ba za tai ciwon kai ba a auren ni dana ɗauko auren sai in yi masa, haka na zage dantse don ma su nadiar sunce basa son komai na bidia kawai a bada sadaki amma kuma dole ayi wa amarya sutura, don haka kullum sai na fita kasuwa don siyowa amarya lefe
In na dawo gogan ko ta kaina baya bi sai dai kawai yai ta cewa aikin sa kai nake yi don haka bana buƙatar sannu sai kace in na aura masa ita ni zan more ta, don Allah ƴen uwa ba daga ya shiga wannan babban ɗakin ya kwashi roman damokaraɗiyyar da ke tattare da ɗakin ba ba kuma sai a hankali ba, namiji fa duk inda yake namiji ne daga an buɗe masa wannan ƙofar ya shiga ya ji abinda ke ciki shike nan an gama zance, amma dubi yadda yake min
Ana gobe ɗaurin aure ne muna zaune da shi yana kallon news ni kuma ina ƙara haɗa kayan mu don ana gama ɗaurin auren zamu koma nigeria
"habibi na ɗauka tj zai zo"
"me ze zo yayi miki" ya tambaya ba tare da ya kalli inda nake ba
"auren ka mana ya kamata ace yana nan"
"auren dolen de da kike son yi wa mijin ki, ni wallahi ban taɓa ganin mace irin ki ba wai da yiwa miji aure" ya faɗa yana yatsine fuskar sa, taɓe bakina nayi don banni da ta cewa
Wayata ce ta fara ringing dubawa nayi naga number nadia, ɗauka nayi da fara a ta
"our bride to be in shaa Allah" na faɗa a zolaye murmushi tayi sannan ta gaishe ni
"dama number abu haidar nake"
"zakiyi masa magana ne" na tambaye ta
"eeeh ina son magana da shi ne"
"ok gashi ma kusa da ni" miƙa masa waya nai sannan na tsokane shi
"amaryar ka tana son jin muryar ka" ƙin karɓa yayi da farko sai da na tashi daga inda nake na zauna akan ƙafar sa sannan na kara masa wayar a kunne sa, sai da naji ya ansa sallama sannan na sakar masa wayar na bar wurin don kar zuciya ta kwashe ni
Sai da ya gama sannan ya shigo ɗakin da fara'ar sa daga gani ta faranta masa ne, kusa dani ya zauna
"habibti ga wayar ki, ashe yarinyar nan haka take kai gaskiya na gode da kike son haɗa ni da ita hmmmm *rangaɗi* gaskiya ta haɗu"
Wani ƙululun bakin ciki ne ya tokare min wuya sai nayi kamar banji shi ba, surutun shi ya dinga yi dana gaji kawai sai nahaɗe bakin da nashi don bana son in furta komai don in dai nace zanyi magana to kuwa kuka ne zai biyo baya
Tuni na canza wa mijina lissafin sa yana lissafin maths ya koma english ```don Allah waya taɓa jin lissafin english, ko da yake wannan karatun na masu aure ne```😜😜😜
Kashegari da wuri ya fita sai ɗoki yake yi na rasae nadia ta faɗa masa da ya saka shi jin daɗi haka ana gama ɗaurin auren ya dawo na tambaye shi da fara'ar shi yace aikin gama ya gama
Wasu hawaye ne waɗanda nake ta ɓoye su, aliyu ne ya share min su sannan yace
"zainab har gobe babu wata mace a zuciyata sai ke kuma baza a kuma ba in shaa Allah, ke kaɗai ce har abada babu wata bayan ke ke kadai nake jin daɗin keɓewa da ita ke kaɗai nake kalla naji daɗi a raina din haka don Allah kar ki kuma anan gaba kice zaki kuma haɗai ni da wata, ke kaɗai ce bazan iya haɗa ki da wata ba" ya ƙarashe zancen sa tare da rugume ni
"abu haidar yanzu wannan zancen na da ne yanzu mun zama mu biyu dole ka koyi danne zuciyar ka don ka zama adali a gare mu don kar ka cutar da nadia ba zanso inga hakan ba"
"baki tambayi me nadia ta faɗa min jiya ba" mintsinin shi nayi don naga so yake yi ya sani kuka again
" to shi kenan tunda abin naki ya zama harda mugunta na fasa faɗa miki, ki haɗa kayan ki gobe zamu bar gari zuwa nigeria, su nadia ma na saka su haɗa kayan su"
"kace sai ƙarshen watan nan zasu koma"
"ke ina kika taɓa ganin an bar amarya tana jira" ya faɗa azolaye, duka na kai masa aƙirjin sa sannan na saka masa kukan shagwaɓe
Ɗauka ta yayi sai gado, ina ta kokawar ya sauke ni amma ina sai da ajiye ni akan gado sannan yace
"bari in kwashi don Allah ne kaɗai ya san lkcn da zan dawo wajen ki gwanda in more kafin mu koma a fara sharing kooo"
Haushi ya bani na hankaɗe shi amma kasancewar yana da ƙarfi sai beji ba kokawa muka dinga yi inda shi in banda dariya babu abinda yake min, kukan gaske na saka masa
"to menene kuma abin kuka, ba ke kikai min auren ba kuma wai yanzu ba kya son inyi maganar auren" wa'azi ya shiga yi min akan mace me gudun miji babu yadda na iya haka na sallama masa
Kashegari da wuri muka shirya a gida mukaje muka ɗauke su nadia taci laffayar sai ƙamshi take yi haushin ta ne kawai ya kamani kamar in kai mata duka, wai don Allah dama haka kishi yake
Aliyu naji kusa dani
"uwargida don Allah a rage kishin nan mana kinga yadda kike dokawa nadia harara" ya faɗa yana min dariya, ban kula shi ba nayi wajen su muka gaisa jikin ummu yahya da sauki don haka sai muka kama hanyar airport don ta madima zamu wuce
tunda muka shiga jirgin na wuce ɗan ɗakin dake cikin jirgin kasancewar private plane ɗin aliyu ne ze mayar da mu don ummu yahya suna da kaya sosai
tunda na shiga ɗakin na kulle ko ƙaunar ganin nadia bana yi wani haushin ta ma nake ji kawai daurewa nake
[12/7, 7:21 PM] Mmn Waleed💖: Lfy muka sauka nigeria kuma abuje directly gida muka nufa nai mamakin dana ga an kai nadia gidan da tj yake wanda yake kusa da gidan mimma ita kuma ummu yahya zata zauna a ɗayan part ɗin dake gidan mimma tunda dama n part ɗaya take anfani da shi
Har ɗakin aliyu na bishi na same shi
"me yasa ba za ka haɗa mu a gida ɗaya ba"
"habibti naga alamar idan na haɗa ku wataran sai dai in dawo in ga kin mata duka" ya faɗa da dariya a fuskar sa
Ƙarasowa nayi kusa da shi ina taimaka masa cire button ɗinrigar sa
"kana ganin zan iya dukan ta don tana matar ka"
"kinga irin hararar da kike aika mata kuwa, ko ni kika aiko min da wannan hararar shiga taitayina zan yi balle nadia" shiru kawai nayi na fice
Banyi niyyar girki ba don a agijiye nake don haka saina aika part ɗin mimma tasa ayi abinci da mu, ko da aka gama sai ta aiko amina ta kawomana
Ƴar iskar yarinyar ni tunda na dawo sai yanzu ma na ganta tana part ɗin mimma ita da islama da su haidar can suka koma, ko da nace ta dawo part ɗina sai tace wai part ɗina bavu daɗi haka na haƙura na ƙyale ta acan
Da daddare na tafi part ɗin aliyu don in raka shi gidan amarya nai mamakin dana ganshi a azaune ko shiri be yi
"yanzu abu haidar sai yaushe zaka je gidan amarya"
"oooh wannan matar tawa muguwar ƴar ƙauye ce wai ke har yanzu ɓaki fahimci tj ne ya auri nadia ba ba ni ba" kuka na saka masa tare da zuwa gurin shi ina dukan sa
Dariya ya dinga min, yana ƙyaƙyatawa
"shine baka faɗa min kasa nake ta jin haushin baiwar Allah"
"so nawa na tambaye ki kina son ji abinda nadia ta faɗain sai kika ce bakya sonji" sai yanzu na fahinta
"me tace maka" na tambaya a ƙage
"oho" ya ansa
"au oho ko bari ka gani" sai na fara yi masa cakulkuli, dariya ya dinga yi sannan yace yayi surrender zai faɗa min
Ashe nadia da tj sun riga sun haɗe kansu tinda ta fita takaba tj ya nuna mata yana ra'ayin ta itama kuma taga ɗan fulanin bauchi yasa bata wani ja aji ba sai ta yadda suna cikin soyayyar sune ummu yahya ta kawo zancen barin su madina nadia taso ta faɗawa tj don ya faɗawa ummu yahya ke kuma sai kikai shigar sauri kika ce nace zan aure ta
Ana gobe ɗaurin aure ummu yahya taji nadia tana kuka suna waya ita da tj shine bayan ta gama sai tace ta kira ni ta faɗa min gaskiya tunda taga alamar nima ba son ta nake yi ba shi ne ta kira ni, wallahi nai farin cikin sosai dana ji ni na tsira sannan zan bawa ɗan uwana abinda yake so kinji yadda abin ya kasance
Kwanciya nayi sosai a jikin mijina tare da godewa Allah ubangiji (swt)
***************
Babu abinda yake faruwa a cikin gidajen mu sai alkhairi aliyu ya bawa ummu yahya al amin da mu'allim bayan na yaye shi don kar ta zauna a wurin ta babu hayaniya, inda su haidar suke wajen mimma ita kuma islam ta koma wajen nadia, a gidan ni kaɗai ce banni da ɗa 😞😞😞😞 innai magana sai aliyu yace wai in dage in ƙara kawo wani be san ina na ɗauke da ɗan passenger ɗina ba
Ummu yahya tacewa aliyu tana son ta buɗe islamiyya a cikin gidan ta tunda akwai ɗakunan da babu kowa a ciki don ta dinga karantar wa tunda dama can aikin ta ne,
Gini sosai aka fara yi na ɗauka ƴar islamiyya zai baɗe mata dana ji yace ta bari zai ga yadda zai ashe gini zai yi
Babbar makarnta ce wacce taci sunan *yahya memorial islamic scl* aliyu ya ɗauko ma'aikata da malamai sannan yai wa ummu yahya maganar an kammala ko da taje taga ginin har kuka sai da tayi ta dinga godewa aliyu ciki lck ƙanƙani akayi launching makarantar aka fara karatu
Ita ma mimma ta koma asibitin national hospital dake abuje ta cigaba da aiki itama aliyu ya buɗe mata pediatric hospital babu abinda ake yi a asibitin sai kula da yara da duba matsalolin su ya samo mata specialist akan harkar yaran da nurses ya cika asibitin da su, sannan ya aurar da ƙanwata amina zuwa ga pA ɗin sa al mustapha suka tare a lagos don yanzu al mustapha yana lagos gurin kular wa da aliyun sifirin jiragen sa wanda shi kuma aliyu suke yin zuwa in lkcn yayin zuwan yayi shi da tj
*BAYAN SHEKARA 10*
Alhamdulillahi yanzu gidan mu ya cika don bayan mu'allim sai Allah ya azurtani da mace me sunan hjyr aliyu wato furairat amma muna kiran ta da walida sai namiji me sunan bbn mimma wanda muke kiran shi walid sai mata guda biyu wato yen biyu masu suna fatima da kuma rabia
Itama nadia tana na tana da ƴaƴan ta guda huɗu wanda ta haifa da tj ɗin mata biyu maza biyu babu abinda zamu ce sai dai ince Allah ya ƙara bamu zaman lfy da mazajen Allah ya ƙara bamu haƙuri da juriyar zaman tare
*tammat bi hamdulillah*
*ina miƙa godiyata sosai da jinjina ga masu karanta wannan littafin nawa na gode da soyayyar ku da adduar ku gare ni Allah ya biya mana buƙatun mu na yau, da kullum ya haɗa mu a aljannar fiddausi baki ɗaya*
*don Allah mu dinga kuƙa da zuciyoyin mu mudinga sauke wa zukatan mu nauyin da muke ɗara musu na baƙin ciki ko hassada ko kuma ƙullatar mutane mu zama masu yafiya ko da mutum ya tambayi a yafe masa ko bai tambaya ba kai dai ka kasance me yin afuwa hakan ne kawai zai sa mu zaunablfy da zuƙatan mu, mu cika zuƙatan mu da soyayyar ma'aiki (saw) babu abinda zaka cika zuciyar ka dashi daya wuce wannan ya kasance zuƙatan mu babu hassada babu ƙyashi babu baƙin ciki, YA ALLAH KA KULAR MANA DA ZUƘATAN MU BA DAN HALIN MU*
SALAM ALAIKUM
Taku ce akullum mmn walid nd walida ce (mrs aliyu) a kullum 🤝 ana tare
0 comments:
Post a Comment