Tana fita bata sharce ko ina ba sai shagon shamsu, bayan sun gaisa tace don Allah ya bata garin tuwo anjima zata kawo mashi, yace gaskiya bazan bayarba, raihana tace miyasa don Allah idan na tambaya baka bani laifin mi nayi maka don Allah,?"" yace haka nan bazan bayar ba, murmushi raihana tayi sannan tace to Allah ya sawaƙe, bai sake magana ba, saboda haka raihana ta juyo tayo gida..............................
Bayan ta dawo ta tadda badiyya ta kawo mata wankin da tace zata aiko, kuma sauƙi ɗaya an aiko mata da kuɗin wanki , don haka ta karɓa ta tura yaron ya siyo mata gari da kulili, ya karɓa ya tafi, ita kuma taci gaba da wankin kuma har yanxun bataci komai ma cikinta ba,
Bayan wani lokaci ya dawo ya kawo mata, ta jiƙa garin, ta kwaɗa , umma takai ma umma tace ita bata cin garin kwaki, raihana tace umma kiyi haƙuri kici don Allah abunda ya samu ai dashi ake aiki a rayuwa, umma tace kai gaskiya bana ci, haka raihana ta zauna ta shafe garin tatas ta bulbili ruwa a jarka tasha, fitowa tayi taci gaba da wankin ta, don yinin ranar haka ta yini tana wanki, harna badiyya duka ta haɗa ta wanke fess , bata gama wankin ba sai bayan salƙar isha"i, Allah ka raba mu da wahala duniya da lahira ameen,,,,,,,,
Lokacin da ta gama wanki wanka tayi , tana kwanciya don hutawa gwaggo tace ai lallai sai ta fito tazo ta aiketa, raihana bata da yadda zatayi saboda baba yana nan haka ta fito, a tsakar gida gwaggo ta nuna mata wani rabin buhun gero tace wai ta ɗauka takai ma ladi aminiyarta,
Raihana tace to banda abinki gwaggo ina ni ina ɗaukar wannan?"" gwaggo tace iye?""" lallai sannu ɗan wanke kinfi ubanki kinfi uwarki, to udan baza ki iya ɗauka ba sai ki raba biyu idan kinje kin dawo sai kikai sauran, raihana tace indai samu yara sukai kawai sai inbi bayansu idan mun dawo in biyasu, gwaggo tace wallahi babu yaron da zaki ɗora ma yaje ya gudu da geron nan,
Baba dai baice komai ba, saboda haka gwaggo tace duk ubanda ya tsaya mata lallai ta ɗauki geron nan takai shi, wasu hawayen baƙin ciki ya zubo mata, matsawa tayi ta ɗauki wata katuwar rober ta rage geron ta ɗaure sauran ta ɗauka ta tafi,
Saida takai geron sannan ta dawo ta kwashe sauran takai , bayan ta dawo gida , har zata shiga taga yusufa tsaye a ƙofar gida, ko inda yake bata kalla ba, har zata shige gida yace raihana ina magana, cikin fushi tace ji nan malam fita harkarta ina kuma kada in sake gani ƙafarka a ƙofar gidan nan idan ba haka ba saina sa an kulleka,
Dariya yayi sannan yace haba raihana miye yayi zafi haka don Allah?"" raihana tace kawai idan kana so mu daidaita dakai kada ka sake zuwa nan gidan harsai na neme ka?"" yusufa yace to babu damuwa ina jiranki, tace yawwa sai kaji ni, ta shige gida shima ya juya ya tafi...............,,,,,,,,,,,
Tana shigowa gida gwaggo tace taje ta siyo mata maganin sauro, raihana ta karɓa ta fita, a ranta ita kaɗai tasan yanda take ji, wannan wace irin rayuwa ce?"" komai itace zatayi kuma dan ɗaukar alhaki aikenma baza a haɗa mata ba sai guda guda kamar ƙaramar yarinya?""" lallai idan har haka *zawarci* mara galihu yake baiyi ba,
Sallama tayi ta shigo gidan, bayan ta bawa gwaggo maganin sauro har zata shiga ɗaki gwaggo tace rahanatu, nace "yar uwarki bushira tana can babu lafiya yanxu aka zo aka faɗa man idan Allah ya kaimu ai sai kije ki zauna kwana biyu kafin ta samu sauƙi,
Raihana tace miyasa saini zanje?"" gwaggo tace to waye kullenki?"" tunda baki da aure ai sai kije """"" raihana tace to bazanje ba, idan ciwon yayi tsanani a dawo da ita gida.........
Baba dai yana zaune a gefe baice nasu komai ba, raihana ta shige ɗaki gwaggo kuma taci gaba da mita.....................,,,,,,,,,
****
Da safe misalin 9:30am raihana ce take ta faman haɗa kayan wanki data wanke tana kulleqa kiwa nashi, haka duk ta haɗasu ta ajiye ma kowa nashi gefe ɗaya,
Wata yarinya ce ta shigo ta kawo murji taliya, raihana ta karɓa, sannan tace anjima ta dawo ta karɓa, yarinyar tana fita raihana ta fara murhe taliyar, bayan ta gama ta ɗauko wankin kayan baba da gwaggo tace ta wanke tun jiya,
Tana gama wanki ta tafi ɗaki ta kwanta don huta ma rayuwarta,
*T*ana kwanciya abinda ta fara tunani shine, a gidan Aminu bata wanki saidai yakai a wanke mata amma yau itace take wanke kayan wasu , Allah sarki rayuwa da tayi haƙuri ta zauna mijinta yana santa amma ita sai wulaƙanci take mashi yanxun ga yanda takaita, sai tayi wahala sannan take samun abinci taci, sannan kuma wani lokaci sabulun wanka tsaye yake mata, idan tayi wanki kuma ta samu kuɗi dasu take samu taci ɗan abu mai ɗan text, abunda take tunani shine yanxun kuma da a gidan haya suke ko ya zasu ƙare?"""
Lallai wato duk inda Allah yakaika shi hakuri nasara ne na rayuwa, duk da tayi haƙuri lallai da bata kai wannan matakin ba, hawaye ya zubo mata daga idonta, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace yanxun kuma ko waye zai aure ne?"""""" shin yana da kirki?"" zai soni kamar aminu?""" gidan rufin asiri ko akasin haka?"" tayi ta jero ma kanta tambayar da babu amsa,
Allah sarki da banda mahaifiya a gidan nan lallai da bansan yanda rayuwata zata kasance ba, wai ance ana sallama da raihana!""" maganar wani yaro ne ya katse mata tunani.!!!""" daga ɗaki raihana tace je kace waye?"""" ba"a daɗe ba yaron ya dawo yace wai ance *honoravel* ne, da aauri raihana tace je kace tana zuwa,
A gaggauce raihana taje tayi wanka ta fito taci kyau cikin wani lallausan material ta haɗu iya haɗawa, sannan ta ɗauko turare ta feshe jikinta dashi kamshi yace salama alaikum, ita kanta da ta kalli kanta a madubi kasa gane kanta tayi, saboda haka tayo waje,,,,,,hhhhhhhhhhh
*zawarci*
*A* zauren gidansu tana ƙoƙarin fita taji yace barka da war haka gimbiyar mata!"""" kallo ɗaya raihana tayi mashi sannan ta ɗauke kanta, tana ƙoƙarin fita daga zauren ya sake magana bata sake bi takanshi ba tayi waje...............
Fitar ta ƙofar gida ta ware idanuwanta iyakar ganinta bata ga kowa ba, haka ta haƙura ta dawo, tana shigowa ciki zata wuce yace ranki ya daɗe ai nine na aika a kiraki!!!
Kallonshi raihana tayi ta sake kallonshi ƙasa da sama sannan tace kaine waye?"" yace honarabil tsaki raihana tayi sannan tace to ya akayi?"" murmushi yayi zai fara rattafo sirrin zuciyarshi raihana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, saurara yanxun fita zanyi ka bari wani lokaci ka sake dawowa , tana faɗin haka ta ƙutsa kanta tayi cikin gida,
Tana shiga cikin gida tace Allah ya isa ɗan iska nama ɗauka honorabil ɗin gaskiya ne, shege na ɓata gugar kayana na ɓata turare na a banza, tsaki tayi sannan ta sake tuno ma yanda ta ganshi
Ƙutuƙutu yake kamar an tono shi daga cikin rami, tace ɗan iska baka da arziƙin takalmi mai kyau sai silifas, tsaki tayi sannan tace wato idan dai kai *zawara* ne shara da bola sai yazo wurinka, da sauri ta shiga ɗaki ta cire kayanta, tana ma honarabil Allah ya isa...............,,,,,,,,
*** ***
*Y*au gidan su *raihana* babu kwanciyar hankali saboda ɗiyar gwaggo tayo yaji, babbaf ɗiyarta, mai suna *fiddausi* tunda fiddausi taxo ta faɗa ma gwaggo abun ya ɓata mata rai sai safa take da marwa a tsakar gida tana tsine ma mijin fiddausi, lallai yaufa an taɓo gwaggo abun babu daɗi,
Ƙorafin da fiddausi take mijinta baya bata abinci sannan kuma sai yayo shaye shaye yayi mata shegen duka, ga neman mata kuma ƙarshen wulaƙanci a gidan ta yake kawo su, yau abinne yaci tira saida yayi mata shegen duka ita kuma ta tattaro "ya"yan ta ta taho gida,
Ita kuma gwaggo tace tunda an wulaƙanta mata ɗiya baza ta riƙe ɗan uban kowa ba, ita kuma fiddausi tana cewa itama babu mai rabata da yaranta,
To gasu nan dai koya zaman zai ƙare tsakanin gwaggo da fiddausi da kuma raihana da yaranta?"""
Raihana dai tana cikin far gaba saboda fiddasi bata da mutumci bata da ragowa, ga san abun duniya sannan kuma ta kware wajen iya bariki,............
Kam cakwakiya kenan, wannan zama nasu koya zasu yi shi ne?"""
Ku kasance tare dani, *Ameenci writer's association* ke maku fatan alkairi ni *meelat* nake cewa ku kasance tare dani!!!
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*Page* 1⃣4⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT* 🌹
*T*o koda baba ya dawo ya tambaya lafiya yaga fiddausi a gida?"" gwaggo tace ta kashe auren nan dan ta gaji da iskanci, baba yace abinda baya yuwuwa dole ta koma ɗakin mijinta, amma gwaggo tace babu gidan ubanda zata je, ta ƙara da cewa aiga raihana nan itama tana zauniyar ta sai neman kuɗi take abinta, duk inda baba ya shiga gwaggo tace fiddausi baza ta koma ba, dole ya haƙura,
****
*S*ati ɗaya da dawowar fiddausi gwaggo da kanta ta shiga maƙota duk inda ake kawo ma raihana wanki tace su daina kai mata ga fiddausi ta dawo kuma da kyau take wanke wa suyi fesss,
*R*aihana kwance a tsakar gida ga yunwa ta isheta ta rasa inda zata saka ranta, ita baƙin cikinta ma kuɗin da zata siyi pard take nema, bata da ko sisi, tana kwance fiddausi ta kwaɗa mata kira, ke raihana?"" raihana tace na"am, zo maza ɗauki usman kiyi mashi tsarki yayi kashi,
Raihana tace to, miƙewa tayi ta nufi wurin da fiddausi take zaune, ta duƙa ta ɗauki yaron taje tayi mashi tsarki ta dawo mata dashi, har ta ajiyeshi zata tafi tace jeki ɗakin gwaggo ki tattaro kayan fitsarin shi ki wanke , kuma ki gyara ɗakin, raihana tace to amma don Allah ki bari inci abinci yunwa nake ji,
Fiddausi ta buɗe baki sannan tace lallai yarinya nuna man kin balaga, duk ina nan zaune harsai kin gama uzurinki zakiyi man nawa?""" raihana tace ba haka bane wallahi duk yau banci komai ba, fiddausi tace to ni na hana kici?"" raihana tace ban samu ba, suna maganar akai sallama wani yaro ya kawo wanki, raihana tace kawo, yazo gabanta ya ajiye mata wanki sannan ya bata kuɗin, ta karɓa fiddausi tace kawo nan mu gani!!""" raihana tace kuɗin wanki ne, fiddausi tace to ki bani dan uwarki, miƙa mata tayi kuɗin, ta karɓa sannan tace to ki wanke kayan mana,
Raihana tace to, ɗaukar kayan tayi ta matsa dasu ƙofar ɗakinsu ta ajiye sannan ta shiga ɗakin umma tana shiga ta zauna kusa da umma ta fashe da kuka,
Umma tace lafiya?"" raihana tace Umma wannan ai cutane tunda fiddausi ta dawo gidan nan nice nake komai da komai inyi nata inyi na yaranta, dan kuma rashin imani duk abinda zasuci a gabana sukr ci basa bani, yanxun an kawo wanki zanyi ta kwace kuɗin kuma wai in wanke kayan, bazata bani ko sisi ba,
Umma tace kiyi haƙuri, raihana tace inyi haƙuri da yunwa umma?"" Umma tace to idan baki haƙuri ba mi zakiyi?"" raihana tace nidai gaskiya zanzo in fara sana"a ko abinci siyarwa ne inyi ina kaiwa waje ina siyarwa, amma bazan iya wahalar banza ba inyi wanki ta kwace kuɗin kuma duk wahalar yaranta a kaina zai ƙare,
Umma tace to kiyi abincin siyarwar Allah yasa ma neman albarka raihana tace amin,
Naira hamsin umma ta bata tace taje ta siyo shinkafa da wake taci, kuɗin ta karɓa sannan ta fita daga ɗakin, tana fita umma tace Allah ya sawaƙe, shi yasa idan ka samu inda ka raɓa ake so kayi haƙuri, Allah dai ya baki miji na gari raihana,
Ina kuma zakije?"" fiddausi take tambayar raihana inda zataje, raihana tace zanje in dawo ne, tace babu inda zakije kixo ki wanke kayan mutane mana, raihana tace zan wanke zanje in samo abincine in dawo, to kiyi sauri dan bana so ki ɓata man lokaci, raihana tace to sannan ta fita daga gidan,
Bayan taje ta siyo abincin ta dawo, ɗakinsu ta shiga taci, sannan ta fito, ta fara wanki, saidai ta wanke kayan fess kamar wata inji sannan taje tayi wanka,
Gwaggo tace ta ɗauki niƙa takai mata, raihana tace gwaggo duk ga yara nan ki aike su mana, fiddausi tace anƙi a tura yaran mana sai sunje sun zubar da masarar anjima uwarki zamu ci muyi bacci?"" tsaki raihana tayi sannan ta duƙa ta ɗauki kwaryar ta nufi shagon yusufa,
Lokacin da ta isa wurin cike yake yana niƙa, raihana ta ajiye ta samu wuri tayi tsaye kamar wata sojanya, saida ya gama niƙa wani niƙa ya hangota,, ya yashe baki yace baiwar Allah kece?"" raihana ta ɗaure fuska shiko sai fara"a yake wai yaga masoyiya, ina niƙan naki yake ne?""" raihana ta nuna mashi ya ɗauka ya niƙa mata danshi ya ɗora mawa yace yakai mata gida, kuɗin ta ajiye mashi don idan ta bashi baya karɓa, tana ajiyewa tabar wurin, dariya yayi sannan ya ɗauki kuɗin ya saka a aljihu,
Lokacin da raihana ta dawo gida, gwaggo sai faɗa take wai ta ɗora ma yaro niƙa ya zubar mata, ko inda take raihana bata kalla ba ta wuce ɗakinsu,
Tana zuwa ta buɗe kayanta, wani less ta ɗauko mai tsadar gaske, ta saka a leda , sannan tace ma umma sai ta dawo, umma tace to,
Raihana tana fita, maƙota ta shiga gidan wata dillaliya, ta bata less in, tace zata siya dubu goma, raihana tace haba hajiya ki ƙara don Allah tace ai hakanma na zura jikina da yawa, raihana tace duka so ɗaya na taɓa sakawa wallahi , hajiya tace ai su gwanjo babu ruwansu da so nawa ka saka, idan kin siyar a haka in bayar idan baki siyar ba to in baki kayanki, raihana tace to kawo,
Hajiya ta shiga ta ɗauko mata kuɗin ta bata, tana karɓa, ta nufo kasuwa, dan siyp cefane da abinda zata buƙata wurin abincin siyarwa, ta haɗo duk abinda zata buƙata ta nufo gida,
Tana dawowa fiddausi tace ina kika shige ne "yan mata?"" raihana tace taje kasuwa, fiddausi tace kawo muga abinda kika siyo tace ba nawa bane, tana faɗin haka ta shige ɗakin su............
Fiddausi tace tou pha yau naga munafinci tsurarshi yarinya ina magana bama tada lokacina, ita dai raihana bata sake magana ba, haka umma bata yi magana ba, haka sukayi ta jarabarsu a tsakar gida ita da gwaggo har suka gaji sukai shiru dan kansu..................,,,,,,,
****
*D*a safe raihana ta fara aikinta, fiddausi da gwaggo suka fito suna tambayar ko lafiya?"" raihana tace zata fara siyar da abinci ne, haka taci gaba da aikinta, au fiddausi suna kallon ikon Allah,
Koda baba ya fito zai tafi kasuwa gwaggo tace Allah ya hutashshe ka ɗiyarka ce zata riƙa ciyar da kowa a gidan nan tayi kuɗi ubanta ya huta,
Raihana dai batace komai ba, saboda haka baba gwaggo ta hana shi ya bayar da ɗan abinda yake bayarwa saboda haka yasa kai ya fita daga gidan,
Koda raihana ta gama haɗa komai nata, gwaggo tazo da ƙaton wuri ta kwashe abinci kafff, raihana tace yana ga haka kuma?"" gwaggo tace ya kuwa baza kiga haka ba?"" ai gida bata ƙoshi ba baza akai daw ba, dan haka sai kowa yaci ya ƙoshi sannan,
Baƙin ciki ya ishi raihana saboda duka abinci gwaggo ta kwashe shi, doƙe ta haƙura ta kina ɗaki, da tace ma umma yau sai taci uwar kowa a gidan umma tace tayi haƙuri kada ace tana zaune gida tana faɗa da matar babanta, umma ta ƙara da cewa kuma ko aurenki aka zo nema haka za"ayi ta faɗa ace baki da ragowa, haka raihana tayi haƙuri ta tashi a tutar babu, duk miye yaja mata??""" *zawarci*
Umma to yanxun miye ya kamata in fara siyarwa kuma?"" umma tace sai ki nemi aiki a gidaje, raihana tace kai haba Allah dai ya sawaƙe, nje inyi ma wata ƙatuwar banza aiki, umma tace to Allah ya kawo mafita raihana tace amin..................
*B*ayan kwana biyu, mijin fiddausi yaxo biko, gwagho tace baza ta koma ba, raihana kuwa addu"a take Allah yasa ta koma ita kuma ta samu ta huta .................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*Page* 1⃣5⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
````MEELAT``` 🌹
*G*waggo ta bushe fitalar ido tas tace fiddausi baza ta koma gidan mijinta ba, shi kuma daya fi su iskanci ya tattara dukan yaranshi har na goyen bai bari ba, ya tafi dasu kuma yace bazai saketa ba,
*F*iddausi keta fama kiran raihana, ita kuma raohana tana kwancd babu lafiya, shirun da fiddausi taji raihana tayi yasa ta tashi ta taho ɗakin a fusace,
Ita kuma raihana tana kwance sai rawar sanyi take, idonta sai fitar da hawayen wahala yake, fiddausi tace ubanmi ya sameki?"" cikin yanayin wahala tayi magana tace banda lafiya, fiddausi tace ai nasan baki lafiya nake tambayar abinda yake damunki raihana tace masassara da ciwon kai,
Fiddausi tace Allah ya sawaƙe, idan kina da 100 bani zanyi amfani da ita, tsaki raihana tayi cikin ranta sannan tace kaji wani zancen banza idan ina da ɗarin ni da banje ko cemist ba?"""
Fiddausi tace ina magana kinma mutane shiru, raihana tace banda su, tsaki tayi sannan ta fita daga ɗakin,
Umma ce ta shigo ɗakin ta cire hijabin jikinta tana ma raihana sannu, tace ni banma samo kuɗin ba, raihana tace to umma babu komai , Umma tace wane babu komai kin kwanta da ciwo ba magani kuma duk yau bakici komai a cikinki ba?"" raihana tace shin,
Fiddausi ina zakije ne?"" gwaggo take ma fiddausi magana amma ko inda take bata kalla ba, haka ta fece tabar gidan,
Yinin ranar haka raihana ta yini babu zuwa asibiti umma duk buga bugarta ta rasa ina zata samu kuɗi kuma ciwo sai ƙara tubirewa yake, dan raihana sai wani farfar da idanuwa take, hankalin umma ya tashi sosai, saboda haka ta fito take gayama gwaggo, tare suka shigo ɗakin ganin halin da raihana take ciki gwaggo hankalinta ya tashi sosai,
Ta kalli umma tace an ajiye ɗiya a gida ciwo babu magani?"" umma tace nidai banda kuɗi kuma duk yinin jiya da yau bata samu taci abinci ba, har gari ta siyo gashi can ta kasa ci,
To Allah ya sawaƙe, to yanxun ya za"ayi?"" kafin gwaggo ta rufe bakinta, raihana tayi wata irin ajiyar zuciya, lokacin da suka maida kallonsu wurinta wani kumfa yake fita daga bakinta, tana kakkafafewa, umma tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, gaba ɗaya suka matsa kusa da ita, lokacin da suka ɗaga raihana babu nunfashi, gaskiya gwaggo taji babu daɗi da gudu ta fita , tana fita mijin badiyya ta gani jikinta yana karma tace mashi ka taimaka mana raihana babu lafiya
Har ta suma, yace to suje su ɗaukota akaita asibiti, da sauri gwaggo ta koma ita da umma suka kamo raihana a motar shi aka sakata, suka nufi asibiti,
A asibiti ana kai raihana likitoci suka fara gwaje gwaje don gano abinda yake damunta, bincike sosai akai likita ya tabbatar masu da raihana ciwon yunwa { ulcer } sannan kuma tana da damuwa sai kuma ta rage amfani da ruwa sosai idan ba haka ba, limonia tana neman kamata,
Duk kuɗaɗen da aka kashe a asibiti mijin badiyya ne ya biya, sannan yayi ma su umma fatan samun sauƙi, sannan ya tafi,
Kwanan raihana 3 a asibiti aka rubuta masu sallama , suka dawo gida, duk zaman da raihana tayi a asibiti fiddausi ko leƙe bata leƙa ba,
Yusufa yazo yaga raihana yace baisan bata lafiya ba, sai yau ake faɗa mashi, yayi mata sannu , tare da mata addu"ar samun sauƙi,
Hankalin raihana ya tashi, wato banda mijin badiyya lallai da bata san yadda zata ƙare ba, saboda basu da kuɗi, lallai *zawarci* da matsala, shi yasa idan ka samu inda Allah ya ajiyeka kayi haƙuri ka zauna wata rana sai labari,
Fiddausi kuma zaman gidansi ya fara isarta, dan babu ma mata wanki bare ta samu ɗan kuɗin kashewa, dama raihana ce take wanki ita kuma ta kwace kuɗin, to yanxun ta daina wanki saboda asibiti ance ta rage yawan amfani da ruwan sanyi dan inganta lafiyarta,
Fiddausi ta gaji da wannan zaman ita ba zawara ba ita ba mai aure ba, saboda haka yau ta ɗauki alwashin komawa gidan mijinta, gwaggo tayi juyin duniya karta koma amma fur fiddausi tace tafiyarta zata, saboda haka ita ta tattara yanata yanata tayi gidan ta..................,
Lallai itama raihana abun duniya ya dameta saboda haka tayo ɗamarar duk wanda yazo zata aureshi dan gaskiya ta gaji da wannan wahalar,
Yanxun an hanata wanki, dama dashi takd samu ta ɗan rage zafi, kuma girman kai ya hanata aiki gidaje, kuma ita babu ilimin boko mai zurfi bare ta fara aiki,
Sallama badiyya tayi ta shigo gidan nasu, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin fushi, fankam fankam haka ta nufo ɗakin su raihana, babu ko sallama ta yaye labuƙen ƙofar ɗakinsu, ta fara cewa,
Ai dama duk abinda zakai da marar amana sai yaci amanarka, dan kutumar uwarki ina tausaya maki amma ashe ke ƙoƙarinki ki auri mijina?"" to daga yau na karajin labarin kinyi magana da mijina ko kinzo man gidan sai naci durin uwarki, kafin raihana tayi magana tuni badiyya ta fita dag gidan,
Baki raihana ta saki tana kallon umma, umma tace ai dama haka ne, idan dai baka da aure duk yanda kake da abokiyarki dole sai tayi nisa dake sabida kada ki aure mata miji, raihana tace ko waye yaje kuma ta haɗa wannan faɗan?"" umma tace Allah dai ya sawaƙe,
Bayan badiyya ta fita haka ta shiga gidan maƙotansu tana cewa ayi hankali da raihana aure take so, kuma duk mijin wanda ta riƙe tofa lallai yayi ta kanshi, saboda haka yanxun kowa ya fita harkarta,
***
Raihana ko fita tayi idan taga mace tayi mata magana bata ko kallon inda take, danma kada taga fuska tace zata zo gidanta, suma matan yusufa sunji labari, saboda haka sun shiga sun fita sun raba mijinsu da ita, dan ance idan har ta auri yusufa duk waje za"ayi dasu, to babu wanda take san *zawarci* duk wanda ta kama riƙewa take bata yanda ta sauka saboda rayuwa ,,,,
Raihana abun duk ya isheta saboda yanxun babu maiyi harkarta,
Ga baba ya kunno mata wuta ta fiddo miji tayi aure,
Kuka raihana takeyi gaban umma tace ita wallahi tama rasa ina zata saka rayuwarta, umma tace haƙuri zaki kawai ki fitar da miji kiyi aure, raihana tace umma ai babu mai sona, kuma a unguwa haka ake cewa wai bana aure sai nai kuɗi, jiya naje shagin shamau a gabana ake gulmana wai naƙi aure sai karuwanci nake a boye, inba ina iskanci ba, wai zan zauna har yanxun banyi aure ba, umma tace masu maganar suda Allah,
Kafin raihana tayi magana taji anacewa sallama alaikun raihan tana nan?"" raihana tace muryar waye nake ji kamar farida?""" tace nice, da sauri ta fito ta rungumeta sannan sukayo ɗakin umma,
Farida suka gaisa da umma sannan umma ta tashi ta fita daga ɗakin, tana fita farida ta fashe da kuka, raihana tace mi aka maki ke?""" tace ƙawata yaji nayo, amma gida har na fara fuskantar matsala kannena iskanci suke man idan nayi magana sai mamana tace ai rashin haƙurina yaja man gani nayo yaji har yanxun miji baizo biko ba, wallahi ko sabulun wanka mama ɗauke abinta take, amma lokacin ina gidan aurena baki ga yanda ake baki girma ba a gidanmu, raihana tace to duk miye yayi zafi haka?"" farida tace bari in faɗa maki abinda ya haɗani da mijina...........................
Raihana tace ina saurarenki,👂🏻
Kafin farida ta fara bada labari tace wallahi mata kuyi haƙuri ku zauna gidan mazajen ku dan *zawarci* ba ƙaramar fitina bane,
Sai yasa ka faɗa da mutane sannan kuma duk wanda yake ganinka da mutumci idan kana zaune gida saiya rainaka, Allah ya kara mana haƙuri ya uma ƙara mana ƙauna tsakaninmu da mazajenmu,
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣6⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
````Meelat```
*Ƙawata Asmeenat Xeeyan Allah yasa damuwarki ubangiji ya yaye maki abinda yake damunki*
*Allah ya baki lafiya Halima Yahya Allah ubangiji yasa zakar jiki ne, Allah kuma ya baki ladar jinya*
*R*aihana tace inajinki,
Farida ta fara:• ke aure zaiyi ni kuma na tambayeshi dalilinshi na aure yace man saboda yana ra"ayi, tun lokacin daya faɗi man zaiyi aure na daina kwanciya ɗaki ɗaya dashi kuma na daina girki, na daina shara, duk abinda nasan baya so, shi nakeyi wanda nasan yana so kuma na daina,
Haka na shiga keta ma danginsa rashin mutumci, bana jin sauƙi a raina, kullum kamar ana balbala man wutar rashin mutumci a raina,
Irin abinda nake yasa ya zaunar dani yayi man nasiha, amma yanda kika san yana ƙara hayaƙani haka nakeji, dan nasihar kwata kwata bata shiga cikin jikina,
Idan kuma ya nemeni zaiyi kwanciyar aure dani sai ince yaje can wurin wanda zai auro tayi mashi tunda ni banda rana, da ina da amfani da baice zai sake aure ba,
Wannan abun yasa ya shiga maƙota gidan wata mata da muke gaisawa da ita, ya faɗa mata taxo taman nasiha,
Tazo tace man in rufa ma kaina asiri inyi haƙuri, wai miyasa mu mata bamu da adalci, duk wanda ta samu ta auri namiji bata yadda ya sake aure wannan wace irin rayuwace?"" idan ba"a aure ni an auro ni?"" ni banma gamsi da abinda take cewa ba, saboda haka na rufe idanuwa na, na cancara mata rashin mutumci, tunda ta tafi banma sake ganin ƙeyarta ba,
Muna cikin haka wata rana *safara'u* taxo, wata ƙawarsu ce, da taxo gidana na ganta ta zama "yar gayu ga makullin mota a hannunta ga ɓarka ɓarkan wayoyi, nace mata ƙawata ina kike aure yanxun?""
Dariya tayi safara,u sannan tace haba idan ina aure kin ganni haka?" aini nayi ban kwana da baƙin cikin namiji, jin wannan maganar da safara"u tayi yasa farida ta zayyano mata matsalar da take ciki,
Koda na gama gaya mata tace ni naso, in tattara inyi tafiya, idan yazo biki ince bazan koma ba, idan na rabu dashi zan su wanda yafi shi, ni kuma ina cikin wutar kishi, saboda haka shawarar da ta bani naga daidai ce, ta kuma ɗora da cewa ita gata babu aure amma tanajin daɗinta, ga motar ta kuma komai tace tana so za"a mata, tace yanda nike da kyau ina rabuwa dashi zan samu wanda yafi shi, wannan shawarar itace taman daidai, bayan safara,u ta tafi, na fara parking kayana, mai gida yana dawowa nace saiya sakeni,
Yace bazai sakeni ba, haka nayi ta bala"i ina masifa, amma ko inda nake bai kalla ba, dana ga haka kawai na tattara abinda zan nema a gida nayi tafiya na,
Tace raihana lokacin dana koma gida, har daɗi naji yanda aka nuna man ƙauna,
Hmmm ina yin sati ɗaya na fara ganin canji, wulaƙancin dai iri iri, wallahi wata rana ma idan ina buƙatar abu saidai inyi haƙuri, na gaji, kuma idan na kirashi a waya baya ɗauka, raihana tayi ajiyar zuciya tace gaskiya daɗi ya maki yawa, ina ruwanki da matar da zai auro?"" kima gode ma Allah bai sakeki ba, farida tace yanxun miye abinyi?"""
Raihana tace murje idanuwanki zaki kawai ki koma ɗakin mijinki, tace haba raihana ai babu aji kuma?"" raihana tace aji tun yaushe kika barshi a baya?"" farida tace kuma kinsan Allah har cewa nayi idan na tafi sai yaxo gidanmu yana haɗani da Allah bazan koma ba,
Raihana tace to kuma kin faɗa mashi wannan maganar miye dalilin da yasa kika kirashi?"" tace wallahi rashin tunani ne, tsaki raihana tayi sannan tace to ita safara"un ta san kin dawo gida?""
Farida tace ta sani mana, tunda data zo na faɗa mata halin da nake ciki sai tace zata haɗani da wani babban alhaji dama ai ba"a zama haka dole sai an ɗan nemi maza dan sune marufar asiri, wai har dubu ɗari zai bani, nace mata toni mijina na sunna ma na hanashi haƙƙinshi sai wani ƙaton banza, dariya tayi sannan tace man ai dama ɗan banzan wayanmu yake hanamu mu more rayuwarmu,
Bayan wani lokaci kuma na kirata nace mata nifa har yanxun mai gida baizo biko ba, tace man wai in shirya ta rakani wurin wani malami , haka na shirya mukaje wallahi raihana na kashe kuɗaɗe da yawa yace man zai kirani, bai kirani ba, saini na gaji na kirashi amma bai ɗauka ba ,
Raihana tace kinji wata matsalar kuma?"" nidai shawarar da zan baki kawai ki koma, idan ma yaxo ya taddaki a gidan kice mashi kawai kin dawo, farida tace gaskiya babu aji,
Raihana tace ai dama abinda yake ƙwararmu kenan matan malam bahaushe, wai ke girman kai kike ji, amma kinje kin kare kuɗinki wajen malamai amma basui maki komai ba,
Farida tayi shiru, raihana tace kixo gobe ni zan raka tunda har kikaga bai sakeki ba yana sanki, sannan kuma abinda yasa baizo biko ba, kila yana ganin kamar zaki mashi wulaƙanci tunda a haka kuka rabu,
Amma idan muka je Office ɗin nasu gobe idan Allah ya kaimu, abinda zakice mashi ,muna zuwa kawai kice ya baki makullin gida, kila zaice mi zakiyi?"" idan ya tambaya kice akwai wasu kayanki da zaki ɗauka ne, daga nan sai mu saurara muji abinda zaice, idan ya bada makullin sai muje gidan daga nan sai mu samu mafita,
Farida tace to Allah ya kaimu, raihana tace ai dole idan kina san zaman lafiya dole ki aje girman kai, idan ba haka ba, zakisha baƙar wahala, ni miye yaja man?"" gani nan ina zaune na rasa mai sona, ameenu kuma yana can ya samu tafi da gidanka, baki ga yanda akace take kula dashi ba, ina nan ina haukan banza, ni yanxun ma banda ubanda yake so na,
Wata rana ma hodar shafawa wahala take man, saboda haka ina baki haƙuri kawai kiyi haƙuri kixo ki koma ɗakinki tunda baizo ba bai aiko wani ba, duk maganar malamai ki barta duk ɓace hanya ce,
Farida tace babu damuwa Allah ya kaimu lafiya, haka sukai ɗan fira daga baya kuma farida ta ce zata tafi sai Allah ya kaimu raihana tayi mata rakiya sannan ta dawo gida,
***
Da daddare gwaggo tace ma raihana tazo takai ma ladi kuɗin adashen ta, raihana ta karɓa ta tafi,
Lokacin da ta isa gidan ta tadda ɗiyar ladi wanda take auren ameenu tsohon mijinta, bayan sun gaisa da ladi ta bata kuɗin, ita kuma ɗiyar ladin lokacin ta fito, ta ɗauki ɗanta ta fita saboda Ameenu yazo ɗaukarta,
Ita kuma lokacin raihana ta miƙe, tayi ma ladi saida safe, tana fitowa waje taga ameenu yana cikin motar zaune, ta matsa kusa dashi tace ranka ya daɗe ana ganin ka?""" kallon sama da ƙasa yayi mata, sannan ya kalli inda matarshi take, ita kuma taɓe baki tayi sannann tace malama ya akayi ne?"" abun yayi ma raihana ciwo saboda haka bata sake magana ba taja saɓa tabar wurin,
Tana tafiya sukazo suka wuce ta fuuuuuiiiii a mota, raihana ta matsa da sauri saboda ji tayi kamar aminu zai bigeta, lokacin da suka wuce raihana tace ikon Allah ashe aminu ba sona yake ba?"" har in ganshi in zuwabar da ajina inyi mashi magana amma ya basar dani,
Uhum Allah ka zaɓa mana alkairi haka kawai raihana ta faɗa a bayyane,
Lokacin da raihana ta iso gida, ta tadda an dawo da baba babu lafiya, duk su umma suna kusa dashi suna mashi sannu, itama raihana wurin taje tana mashi sannu,
Gwaggo tace raihana anshi maza kije ki sawo mashi maganin ciwon kai da masassara, tace to, gwaggo tace kada ki daɗe, raihana tace to, haka ta tafi taje ta siyo maganin ta dawo, baba yasha ya kwanta bacci,
****
Da safe baba yaji jiki da sauƙi abinka da ciwon talaka yace bara ya lallaɓa yaje kasuwa, haka ya lallaɓa ya tafi...............,,,,
Da rana misalin 1:34pm farida taxo, raihana itama taci shirin ta , tayi kyau sosai, saboda haka suna shirin tafiya *Office* ɗin mijin farida, niko nace lallai *zawarci* yayi zawarci tunda har mata zasu biko!!!
*A* madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ni ```meelat``` nake cewa ku kasance tare dani,
📚✍🏻
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣7⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELART* 🌹
*T*are suka fito daga ɗaki farida da raihana Umma tana zaune a tsakar gida, raihana tace Umma sai mun dawo, umma tace to Allah yasa ku dawo lafiya ita dai umma bata san inda zasuje ba
Amma raihana tace mata ganin marar lafiya zasuje,
Suna fita daga gida suna tafiya kafin su isa wurin titi su samu abun hawa, duk inda suka wuce sai an nuna raihana , ga *zawara* uwar san banza ke wuta ƙaninki ɓarawo, dan a unguwar cewa suke ita a dole mai kuɗi take so bata aure sai mai kuɗi,,,,,
Ita kuma raihana kwata kwata ba haka bane a wurin ta, amma mutane sai fassarata suke, wai ita ba kowan kowa ba galadiman kashi, ita ɗiyar talakawa amma baki aure sai gidan masu kuɗi,
Lokacin da suka isa bakin hanya sun ɗan dade sannan suka samu mai napep farida ta kwatanta inda za"a kaisu, saboda haka suka hau sai office in mai gida,
Lokacin da suka isa wurin aikinsu tun a bakin get in shiga, ƙawayen mijin farida aka fara ah ah ah, madam yau da kanki?"" farida saidai tayi murmushi, kafin su isa cikin office in mijinta har an mashi waya cewa ga madam nan zuwa,
Allah sarki sha"anin miji da mata sai Allah, lokacin da suka shiga cikin office in cikin mutumci ya karɓe su, sannan ya basu wurin zama, bayan sun zauna raihana ta gaishe shi ya amsa cikin mutumci, ita kuma farida sai wani basarwa take,
Shine yace madam barka da rana, ko inda yake bata kalla ba, murmushi yayi lokacin daya miƙe, ya nufi wurin da frig yake, ruwa da lemo ya ɗauko ya ajiye a gabansu,
Sai kallon farida yake, bayan ya zauna raihana tace ranka ya daɗe key muka zo a bamu aro don Alƙah zamu ɗan ɗauki wasu kaya a gidanka,
Murshi yayi sannan yace wane irin kaya zaku ɗauka?"" farida tace nawa, kallonta yayi sannan yace da kanki?"" farida tace Eh, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace to ki bari idan na tashi office sai muje tare mana, farida tace a,a, ka bani idan mun gama zan dawo maka dashi,
Raihana tace Eh ka bamu dan sauri muke akwai inda zamuje kuma abinda zamuyi amfani dashi yana gidan naka, yace to, gashi, raihana tace ma farida karɓo mu tafi, ita kuma tace kedai ki ƙarɓo,
Dariya yayi sannan ya miƙe tsaye ya nufo inda suke zaune, miƙa ma farida makullin yayi, yace karɓi, ta miƙa hannunta da niyyar amsa, ya haɗa da makullin da hannunshi da nata ya rige, raihana tana ganin haka ta miƙe ta fita daga office ɗin,
Tana fita inda ta tashi a wurin ya zauna, ya jawota jikinshi, yace bakijin magana, wato yaji ko?""" farida tayi shiru, yaci gaba da cewa wato dan ranshin ta ido harda wani zuwa karɓar makulli zaki je ɗaukar kaya ko?""
Nan ma shiru tayi, yace hmmm yau kwananki nawa baki nan?""" nan ma batai magana ba, yace kin tafi ke zafi kishi kin bar mana gida duk yayi datti, kin barni yunwa ta kamani bana iya cin abinci bana iya shara sannan kumanidan dare yayi bana iya bacci, ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓa tare da jan hankali,
Kallon farida yayi sosai yaga duk ta rame tayi baƙiƙƙirin duk dai ta koma wata iri, sai yaji tausayinta, yace kinsan wani abu?"" kanta ta girgiza alamar a,a, yace zan baki makullin gida a bisa sharɗi guda biyu!!!""" kin yadda?"" ɗaga kanta tayi alamar Eh,
Yace yawwa na farko zaki gyara gidan kuma kiyi man girki, sharaɗi na biyu kuma zan faɗa maki shi ina nan zuwa bayanki bada daɗewa ba, sannan ya saki hannun ta, ta miƙe jiki a sanyaye babu kunya simi simi ta fice daga office ɗin,
Tana fita yayi dariya, yace "yar rainin hankali, kafin kibar gidan zan rutsa ki, yau jikinki saiya baki labari,
Lokacin data fito ta samu raihana, harta tseda masu napep, saboda haka suka shiga suka tafi sai gidan farida.....................,
Bayan sunje gidan, a farlo suka zauna, farida ta sauke ajiyar zuciya, hawaye suka biyo mata fuska tace haƙika na gode ma Allah da kika bani shawara kinsan Allah babu gidan ubanda zan tafi ina nan gidan idan ya dawo yace ban tafi ba?""" zance mashi ai nayi aiki na gaji anan zan kwana da safe na wuce,
Raihana tace ai mu mata wani lokaci muna da matsala, lokacin da muke da ƙima da daraja a idon namiji sai muyi ta iskanci muna wulaƙanci shi kuma namiji duk lokacin da kike wulaƙanta shi kike mashi rashin mutumci kullum sanki raguwa yake a ranshi,
Ke kuma harda wani horashi da hana shi haƙƙin sa, wannan duk haukace kikayi, yanxun da ɗan wulaƙancine wallahi dasai ya ƙare mana rashin mutumci a office ɗinshi, tashi farida tayi ta shiga ɗakin ta, tana ta leƙe leƙe a gidan kamar wata baƙuwa, tace Allah sarki wallahi raihana wani lokaci ko ruwan da zanyi wanka sai mama tace wai naci ka ɓata ruwa, kuma anan gidan ya saba man da shan ruwa faro, kai wallahi naci ubana a gida,
Raihana tayi dariya sannan tace ai yanxun saiki rufa ma kanki asiri, farida tace ina ai yanxun na tuba, suna cikin maganar wayar farida ta fara ringing, tana dubawa tace ke mamana ce take kirana, raihana tace ɗauki kiji abinda zata ce!!!!
Sallama tayi bayan ta ɗaga wayar, mama tace ina kika shige ne?""" kashe wayar tayi, sannan ta faɗa ma raihana, dariya raihana tayi sannan tace kawai kice mata kin dawo ɗakin mijinki, a daidai lokacin da wayar mama ta sake shigowa, farida ta ɗauka, mama tace dan ubaki bakiji ina magana ne?""" shine kika kashe man waya?""" nace kina gidan uwar wa?""" farida tace ina gidana""""" mama tace gidanki ubanwa?"" farida tace na dawo ɗakin mijina,
Mama tayi salatai sannan tace dan ubanki baki bari sai yaxo biko?""" farida tace ai na jira har yanxun baizo ba, mama tace dan ubanki maza maza ki dawo gida shegiya kafin yaxo ya taddaki ya rainaki, farida tace tou , kawai ta kashe wayarta,
Tana kashe wayar tace ma raihana kinji wai inyi maza maza in dawo gida, raihana tace to yanxun komawa zaki?"" farida tace keda Allah rabu da ita, dariya raihana tayi, a daisai lokacin da sukaji ƙarar buɗe get, wato dai mai gida ya dawo,
Raihana tace tashi muyi kamar muna haɗa kaya, farida tace to, da sauri suka tashi suka nufi bedroom, suna shiga suka fara sauko kaya, shi kuma lokacin ya shigo cikin bedroom ɗin ,
Sallama yayi ya shiga ciki, raihana tayi mashi sannu da zuwa, tace ranka ya daɗe har ka dawo bamu tafi ba""" a gidan ƙin buɗewa yayi, daƙel muka samu ya buɗe, dariya yayi sannan yace ai babu damuwa, ita kuma farida tace saka man wannan kayan a cikin can, yace ina zakije kuma da kaya?""
Farida tace bikin ƙawarmu muke shine nazo ɗaukar kaya, murmushi yayi sannan yace da izinin wa zaki fita?"" dan shima tafiyar farida gaskiya ya jigata kawai haƙuri yake amma kullum dare cikin taƙura yake kwana,
Farida tace ban gane da izinin wa zan fita ba?"" yace Ey inda raihana take tsaye ya kalla yace hajiya muje in sauke ki a gida, raihana tace to ita kuna ƙawar tawa fa?"" yace ta dawo gida,
Farida tace wane na dawo gida?"" so kake ace banda kunya na dawo ɗakin mijina babu ɗan rakiya?"" yace ai dan baki da kunyar kika dawo kuma abinda kika zo amsa zan baki, da sauri raihana ta fita daga ɗakin, ita kuma farida irin kamar bata san zaman nan ta fara cewa bani hanya,
Yace babu fa inda zakije, cikin shagwaɓa ta faɗa kan gado yanda tayi abunne yasa yaji wani iri, shima wurin gadon yaxo yace yarinya yanda kika haye wannan gadon nima in rama mashi bara dai inyi ma raihanar rakiya in dawo , mu fara sabon lissafi daga inda aka tsaya,
Lokacin daya fito ita raihana tuni ta ɓace, danma kada inyi ƙarya da nace yanxun takai gida............,,,
Dawowa yayi yace farida ƙawarki fa tayi tafiyarta Allah dai yasa ba fushi tayi ba?"" dariya tayi tace barta zanje gobe, yace ke babu fa inda zaki ƙara fita na faɗa maki,
A daidai lokacin daya zauna kusa da ita, daga nan karatun nasi ya fara nisa, nidai babu ruwana bara inbi raihana baiwar Allah,............,
Raihana lokacin da taji mijin farida ya fara naganganu tayi dariya, tana fitowa, tace a ranta wannan bari in basu wuri, fita tayi ta samu abin hawa tayo gidansu,
Cikin farin ciki ta dawo gida, Umma tace mata ina kikaje kika daɗe haka?"" tace Umma gamu dai, tana faɗin haka ta shige cikin ɗaki,
Tana shiga ɗaki kayanta ta cire ta saka wanda take zama dasu a gida, kwanciya tayi tana tunanin farida tace shi mijin naki ma mai sauƙin kaine, ita fa dama so ɗaya take zuwa a rayuwa ya kamata mu riƙa haƙuri , dan wallahi idan har mace ta fita a ran namiji ta gama tasiri a rayuwarshi, gyara kwanciyarta tayi ita kuma tana addu"ar Allah ya zaɓa mata miji na gari,............,
***
Jikin baba yayi tsanani sosai dan yanxun ma baya gane wanda yake kanshi ciwo sosai, saboda haka duk "ya"yanshi sunxo maza da mata duka "ya"yan gwaggo sun haɗu,
Lokacin da suka zo suka ɗauki baba suka kaishi asibiti, ciwo baya buƙatar komai sai kuɗi, dan haka sunyi tsaye gam suna nemar wa baba lafiya,
Tom satin baba biyu a asibiti yace ga garinku nan,
Kai bazan iya tsayawa faɗa maku irin halin dasu raihana suka shiga ba, ita dai mutuwa kowa yasan tana da ciwo, amma haƙuri ake Allah ya bamu kyakkyawan karshe ubangiji kuma yasa mu cika da imani idan ajalinmu yaxo...........ameen,
Bayan rasuwar baba da wata ukku, "ya"yan gwaggo suka fara maganar rabon gado, baba baya da komai sai wannan gida dasu raihana suke ciki, saboda haka kuma sunce gidan nan bazasu raba shi ba, amma zasu sa ayi ma gidan kuɗi sai su fitar da umma,
Umma tace ita dai ko ɗaki ɗaya ne a bata , yayan su raihana shine babban ɗan gwaggo yace wannan gida babu abinda za"a bata a ciki saboda ɗiyarta ɗaya, sa"a ma taci za"a bata kuɗi,
Umma da raihana sunaji suna gani duka abinda aka basu dubu ishirin , kuma ranar da aka basu kufin ranar gwaggo tace su tashi su bar mata gida,
Allah sarki haka raihana sunaji suna gani suka tattara yanasu yanasu suka bar gidan.....................,,,,,,,
Cikin unguwa suka samu wani gidan haya wanda ɗakuna ne sunkai 20 a gidan nan suka kama haya, ɗaki ɗaya kuma a gidan kewaye biyu ne,
Ranar dai raihana tayi kuka kamar ranta zai fita, ga kukan maraici da wulaƙanci da aka masu ga kuma kukan *zawarci* toi wannan zama nasu ya zai kaya ne?"""
Ku kasance tare dani , a madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻 ni *meelat* nake maku fatan alkairi,
💋
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣8⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*T*o a gidan dasu raihana suka kama haya, kowa dai yasan yadda rayuwar gidan haya take bare kuma ance ɗakuna ne sunfi 20, kuma toilet guda biyu ne, ga matan aure ga mazan aure ga yara ga tsofaffi ga kuma zawarawa ga "yan mata,
****
*T*unda safe gidan ya yamutse ba babba ba yaro layine kowa ya jera bakin toilet masu san wanka su tafi kasuwa sunayi masu san fitsari ko bayan gida duk dai gasu nan sun haɗu, raihana kashine ya dameta amma hankalinta ya tashi dan ta hango kawai saura kusan mutum 11 a gabanta,
Kuma abun nasu da gayya sukeyi dan idan kana jin haushin wanda yake binka layi idan ka shiga baka fitowa da wuri,
Wani matashi ne wanda yayi auren farko bada daɗewa ba, bayan wata mata ta fito daga toilet, ya ɗauki bokitin ruwanshi ya shiga, da alama wanka zaiyi saida ya daɗe sosai bayan ya gama wanka ya samu wurinshi yayi zauniyarshi,
Su raihana suna nan tsaye suna bin layi saiga "yar matarshi da bokitin ruwa tazo ta karkatasu ta shige, mutane marasa haƙuri suka fara magana, wannan ai zalinci ne ɗaukar alhakine in banda iskanci sai ka gama abinda kake ita bata bin layi saidai kawai taxo ta shiga wanka?""" a daidai lokacin da mijin ya fito daga toilet in yace, ai layi nabi?"" saboda haka du wanda ya isa ya leƙa mashi mata tana wanka,
Wani yace kaidai ɗan iskane wallahi , kai danma bakajin kunya kana wanka har waccan yarinyar taxo ta ganka bakajin kunya?"" dariya yayi sannan yace gani kuma har nawa?"" taga wanda yafi wanda ta gani yanxun, da gani dai ɗan duniya ne saboda haka ya shiga rattafo magana marar amfani,
Raihana dai dukar da kanta tayi ƙasa , haka yaci gaba da batsarshi, a ran raihana kuwa cewa tayi tou pha dama shi gidan haya yake?""" Allah ka rufa mana asiri da haya, ina ma amfani?"" haka yayi ta iskancin shi har matarshi ta gama wanka ta fito, ya dafa kafaɗarta suka wuce ɗaki,,,
Haka layi yaci gaba da ja, har yaxo kan raihana ta shiga tayi abinda zatayi ta fito ta nufo ɗakin su,
Tana shiga ɗaki ta samu umma zaune ta zabga tagumi tace umma , umma ɗago kai tayi ta kalleta ba tare da tayi magana ba, raihana tace gaskiya wannan zaman baya yuwuwa ki tashi umma mu nemi mafita?"""
Dariya umma tayi sannan tace raihana har kin gaji?""" kuka raihana ta fara tace umma naga ta kaina na rantse da Allah ko kashin da nayi a leda nayi na jefe masai kamar wata inyamura,
Dan wallahi wannan masan bana iya hawanshi umma ji nayi idan na hau kamar zan faɗa, don girman Allah kawai mudai mu koma gidanku,
Umma tace kinga rufa ma kanki asiri zaman gidanmu baya yuwuwa wurinki, dan nima ina da yayye wanda basu aure kuma ɗaki ɗaya ne gara muyi haƙuri kizo mu nemi mafita wato sana"a don mu samu abinda zamu riƙa biyan haya,
Zama raihana tayi , sannan umma tace naga tunda gidan nan yana da yawa shawara ɗaya muyi ƙoƙari mu riƙa tashi tunda sassafe muyi abinda zamuyi kafin su tashi, raihana tace to, yinin ranar dai haka suka yini suna tattaunawa dan ganin samun mafita a rayuwarsu,
****
kwanan su raihana ukku da komawa gidan haya suka fara sana"a dan biyan kuɗin haya da kuma samun abinda zasu ci ,
Da safe umma tanayi koko da kosai haka ake shigowa cikin gida ana siye, da rana kuma tayi shinkafa wake da mai da yaji, raihana take fita dashi anan ƙofar gida tayi talla, babu laifi gaskiya ana siye sosai dan duk abinda ka gyara na sana"a to insha Allah zai samu shiga,
Raihana zaune a wurin siyar da abincin ta, tayi jugum tana tunanin rayuwa, taji ana ta magana ta ɗago kanta, dan ganin maiyi mata magana, raihana tace sannu murmushi tayi sannan tace da gani dai baki ganeni ba raihana?"" murmushi raihana tayi sannan tace ai naga kamar nasan fuskar amma ta shige man,
yaron da take riƙe dashi a hannun ta ne yake cewa mama don Allah ki saiman abincin nan, raihana maida kallonta tayi wurin yaron da yake maganar, ita kuma tace to zan siya maka jira, raihana ta kalleta tace don Allah ɗan bani haske mana,
Tace mata zulaiha ce, raihana tace wace zulaiha?""" tace baki gane ni ba?"" nice fa zulaiha sani, idanuwa idanuwa raihana ta zaro tace zulaiha kece haka?"" innalilillahi wa"inna ilaihir raji"un, da sauri ta miƙe ta zuba ma yaron abinci ta bashi ita kuma zulaiha ta sauko na goyen ta ajiyeshi suka fara cin abinci,
zulaiha ta kalli raihana tace gaskiya ƙawata ki gode ma Allah ke kina cikin rufin asirin rayuwa, raihana tace to Alhamdulillah, amma a ran raihana cewa tayi hmm yarinya baki san yadda nake raɓe ba da baki wannan maganar ba , ni zama ma babu miji ya isheni, zama ba aure shine damuwata duk macen data san ciwon kanta tana can ta rungume ɗan mijinta suna rufa ma kansu asiri, amma ni hauka da ƙuricciya yasa na maida kaina *zawara* danma ban ni wata rayuwar aure bata shiga tsakanina da aminu ba, bare in ƙara tantance daɗin aure da rashin sa,
Maganar zulaiha ta katse mata tunani , zulaiha tace raihana baki cewa ya kika ganni nan?"" raihana tace aini kinsan babu ruwana da rayuwar kowa tawa nake yi kuma inda zan samu mafita nake nema,
zulaiha ta fara kuka tace baki cewa ina mijina?"" raihana tace nasan yana nan lafiya qalau, zulaiha tace ai kina gani na kinsan banda aure, tunda ke kanki gashi kin kasa ganeni"""" raihana tace dan ban ganeki ba sai kawai akace baki da aure?"" kika san ko kyau kika ƙara ?"" dariya zulaiha tayi sannan tace lallai kinma raina man hankali, raihana tace to Allah ya baki haƙuri,
Zulaiha tace raihana ina cikin matsala ina cikin damuwa ina cikin tsananin rayuwa ina cikin bala"i ina cikin masifa, subahanalla raihana tace duk miya kawo kike jawo ma kanki wannan mugun al,kaba"i a rayuwarki, ko wane lokaci bawa ya riƙa dan gana alkairi da rayuwarshi duk yanda kika ga kina cikin aƙuba ta rayuwa wallahi wani yafiki,
zulai wani maƙoƙo yazo ya to kare mata zuciya tace wayyo Allahna na bani na lalace ni zulaihatu, bakin san baƙin cikin da nake ciki ba, da baki ce wani yafini ba, raihana tace ki rufa mana asiri don Allah a bakin titi muke kada ki tara mana mutane,
Duk wansa kika gani a duniya kowa yana da matsala, saidai ta wani tafi ta wani amma idan kowa yace zai fito yayi kuka haƙiƙa kukan mutane da yasa duniya ta rikice,
zulaiha tace ke rufa ma kanki asiri duk faɗin duniyar nan nafi kowa shiga cikin masifa, zulaiha ta ƙarashe maganar tana kuka, baki raihana ta saki tana kallonta, ita abun ma dariya yaso ya bata, amma ta kanne, zulaiha tace saboda haka abokin kuka shi ake faɗa ma mutuwa, yau ina nan sai abincinki ya ƙare muje gidanku ina san magana dake, murmushi raihana tayi sannan tace to,
suna nan zaune har abincin raihana ya ƙare sannan suka tattara suka tafi gida,
suna shiga ɗakinsu raihana wata yamutsatstsiyar tabarma ta shinfida masu suka zauna,
Umma ce ta shigo ɗakin bayan sun gaisa da zulaiha tace zata shiga maƙota tayi masu barkar aihuwa, raihana da zulaiha sukai mata fatan dawowa lafiya,
sannan ta fita daga ɗakin, zulaiha ta sake matsowa kusa da raihana tace a inajin alhakine yake bibiyata, bari un baki labarin gidan aurena, raihana ta matso kusa da ita sannan tace ina saurarenki,
Zulaiha ta fara magana, a *Abuja*
Ku kasance tare dani danjin wani hali zulaiha take ciki wanda yasa take ganin duk duniya tafi kowa shiga cikin damuwa,
a madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻 masoyana nake maku fatan alkairi sau kunji ni........................💋
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣9⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Wannan page sadaukarwa ne gareku Ameenci association, tare dake ƙawata ASMEENAT XEEYAN saboda kinsan kia raina bana mantawa dake ko wane lokaci ƙawata*
*Halima Yahya Allah ya baki lafiya ubangiji yasa kaffara ne, Allah ya tokari kafaɗa, muna maki addu'ar samun sauƙi ko wane lokaci, Allah ya baki lafiya ameen*
*****
*A* Abuja gidana ƙayataccen gida ne, babu abinda na nema a gidan mijina na rasa, mijina kullum baya da buri wanda ya wuce yaga ya kyautata man baida burin daya wuce yaga ina cikin farin ciki,
Mutumne mai rufen asiri kuma yana da ƙoƙari wurin ganin ya fidda haƙƙin iyalinsa,
Kinsan wani lokaci mu mata muna da namu halin da zarar munga mun wadatu iskanci sai abinda yayi gaba amma bance kowa ba, nidai zulaiha haka tawa rayuwar ta kasance shi yasa wasu mazan ke cewa idan daɗi yayi na mace yawa take abinda taga dama,
Zuwana abuja duk lokacin da mijina ya dawo daga aiki zai ɗaukeni ya ɗan zagaya dani inga gari saboda nace mashi ina san abuja tana burgeni, wannan dalili yasa yake fita dani dan nima inga yanda duniyar abuja take,
Zama muke mai daɗi dashi , wata rana nace mashi zan ɗan riƙa shiga maƙota dan idan ya tafi kafin ya dawo inayin kewa sosai kasancewar shi mutumne mai haƙuri da kuma ƙoƙarin ganin ya fita haƙƙin iyalinshi yasa ya amince da buƙatata,
Gidan wata hajiya sakina wanda naga duk yawancin matan anguwar a gidanta suke zuwa saboda haka nima ina fita gidanta na fara shiga, lokacin da naje na tadda gidan cike da mata kamar ana koya masu darasi , saboda haka nima sallama nayi na shiga, bayan gaisuwa na gabatar da kaina a wurin hajiya,
Ta nuna man jin daɗinta, ni kuma na ɗan zauna na wani lokaci, saida na tashi zan tafi hajiya ta tashi ta shiga ɗakinta ta ɗauko man wani maganin mata tace man ga wannan, nace to godiya nake tayi man bayanin duk yanda zanyi amfani dashi ta kuma ƙara da cewa idan har na riƙe wannan na wuce ƙarfin wulaƙanci a wurin miji na, haka nayi godiya sannan na dawo gida............
Ina zuwa yanda hajiya taman bayani haka na aiwatar da maganin nan, aiko magani naga amfaninshi, gari na waye wa na koma gidan hajiya nayi godiya, sannan kuma nace nawa ake siyarwa?""" ta faɗa man nace to aini bani da kuɗin siye saboda da yawane kuɗin ta faɗa man, dariya hajiya tayi sannan tace ai da wannan zaki kama mijinki duk matar da kika ga tana hawa ƙatuwar mota tana jin daɗinta wannan shine mutumcinta a gidan aure,
Hajiya tace zauna ayi lecture yau dake, abinda karatun hajiya yake nunawa mace idan har mijinta yanajin daɗin kwanciya da ita haƙiƙa ta riƙa ja mashi aji, sannan kuma saima ya biya kuɗi,..
duk wacce take san zama *kasaitacciyar mace* wanda take so a dama da ita a duniyar ƙasaitaccin mata ta nan zata samu itama ta fito,
Maimakon hajiya ta koya mana abin arxiƙi sai ta koya mana abun da zai wahalar da rayuwarmu, """ niko nace ai duk abinda zai zamar maka alkairi kasanshi kuma ido ba mudu ba yasan kima"""""
Karatun hajiya kullum ya za"a samu a ƙwalƙwalo kuɗi a wurin miji, haka shine huɗubarta ,
Wannan hali na ɗaukeshi kafff a kaina kinsan duk abinda aka koya maka sai kayi zarra, wanann huɗubar ta zauna man kaff a cikin kai saboda haka , a gidana shi kanshi mijina yasan na canja, sannan ga wani yawo dana gane, sai naci gayu na sannan zan ɗauki mota in fita, in fita lokacin da nake so in dawo lokacin dana ga dama,
Wannan abu ya damu mijina lokacin daya zaunar dani yaman nasiha abinda nace mashi nan bariki ne saboda haka kuma tunda ya kawo ni saidai yayi haƙuri,
haka naci gaba da kutsawa cikin abuja kullum idona ƙara buɗewa yake iskanci sai abinda yayi gaba,
Ganin haka yasa yace man in shirya muzo gida, anan neman mu, na tattaro na biyo shi, dan yace duk abinda nasan zan buƙata in ɗauka saboda zamu daɗe bamu dawo ba, nace to, haka na tattara duk abinda nasan inaso, mukayo gida,
Bayan mun zo gida na shiga , na samu bbanmu yana nan, dan haka ya shigo suka gaisa, sannan ya zaro takadda daga gaban aljihunshi yabawa baba , sannan yace ga zulaihat nan na dawo da ita bisa dalili kaza da kaza, kada taje ta shiga cikin wata rayuwa kuma ace nine sila, baba ya bashi haƙuri yace ah ah shi kaɗai yasan yanda yake zaune dani, """ sannan ya tashi yayi tafiyar shi,
Ni kuma huɗubar hajiya na riƙe, ina da kyau da diri zan samu wanda yafi shi komai koda an sakeni, baba ya nuna rashin jin daɗin shi amma nace yayi haƙuri insha Allah saina samu wanda yafi shi komai da komai,
*****
Sati na biyu a gida duk abinda nake taƙama dashi wanda nazo dashi daga abuja ya ƙare rashin kuɗi da rashin abin wanki da wanka ya fara damuna, yayana yana kiyon kaji sai sharar ɗakin kaji da wanke masu abun shan ruwa ya dawo kaina saboda tsabar babu da talauci yana bani naira hamsin idan na wanke mashi,
*zawarci* babu daɗi na shiga cikin fitina da musiba dan haka wani yana zuwa neman aurena babu bincike babu komai kawai nace ya turo,
hawaye ya zubo daga idon zulaiha tace raihana naci ubana, raihana dai batayi magana saboda kawai tana kallon zulaiha bata da hankali, zulaiha tace duk wannan aƙubar dana sha a gida bayan nayi aure,
Wannan wanda na aura yana da rufin asiri wanda ci dasha baifi ƙarfina ba, shi kuma abinda ya haɗamu,
Yafi kuka da rashin tattalina dan idan na toya dan kali ko nama man zubar dashi nake, idan nayi wanka da sabulu so ɗaya bana ƙara amfank dashi saidai in buɗe saboda , iskanci dai iri iri,
A haka dai muka daddafa har na haihu ɗaya, bayan na haihu iskanci yaci uban na da, idan ya kawo man pampers sai in ɗauka in siyar ga shige shige maƙota, bana zama gida wannan abun yana mashi ciwo , ga rashin kunya da rashin gurmamawa ,
Tsakani na da "ya"yanshi sai zagi sai tsunuwa yana nuna man rashin jin daɗin hakan amma dan nasan baya so kullum sai na nayi ,
Muna cikin haka ne, wata maƙociyarmu ta kirashi tace mashi taga yana ƙokarin kyautata man amma bana godewa saboda haka yazo ta bashi ɗiyarta, ta ƙara da cewa ai duk macen da ƙoshi yai mata yawa iskancin da take baya kalluwa, shi yasa maza da dama suke tafiya su auro yar ƙauye , duk abinda zata ba miji saita rusuna sannan kuma ga biyayya amma su matan binni sai raini da girman kai suka iya,
tace ka auri ɗiyata ina da yaƙinin zata maka biyayya, kuma ni bazata fito cikin unguwa ta wulaƙanta ka ba, ko a cikin gida baza tayi maka ba, bare har ta fito a idon duniya ta maka rashin kunya,
Haka ya amince da buƙatar ta, haka aka tsayar da lokacin aure , aka ɗaura mashi aure da ita, haƙiƙa nayi tashin hankali nayi bala"i nayi masifa amma a banza, tana shigo babu sanya taci gaba da kyautata mashi
Ladabi biyayya aka barni da haukan banza, ina da ciki na biyu, na kama matarshi nayi mata shegen duka yana dawowa shima na rufe shi da masifa, haka ya gaji da bala"ina ya sakeni saki ɗaya, nace mashi saina samu wanda yafi shi yace man baya baƙin ciki, Allah ya bani inma auri shugaban ƙasa baya man hassada,
Haka na dawo gida ga mahaifiyata babu rai, matar babana baba yace mata tunda abun iskanci ne abuna inji baba miyar gidan nan kada a sake kaɗata da gishi sai naci ubana tunda dai *zawarci* na zaɓa, raihana wahala ta isheni na rasa inda zan saka rayuwata, ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace kema banda abinki sai a sakeki kuma sai ki kwaso "ya"ya jagal jagal ki taho?
wannan rayuwar babu wanda yake san ɗan wani, shawara ɗaya da zan baki yaran nan ki mayar dasu wurin ubansu, kima ji da kanki ko Allah ya fito mana da mazaje muyi auren mu,
zulaiha tace to zan mayar dasu, raihana tace to yanxun shi ina tsohon mijinki na abuja?"" zulaiha tace yana can , kuma har yanxun baiyi aure ba, raihana tace miya sa baza ki koma wurin shi ba?"""
tace ai baya kirana, raihana tace kina da number shi?""" tace banda ita, raihana tace yanxun dai ki fara maida yaran nan wurin ubansu tunda duk maza ne sai musan mafita, zulaiha tace , to
haka sukayi ta "yar firarsu daga baya ta tashi ta goya yaronta ta kama hannun ɗayan tayi ma raihana sai anjima, a bakin zauren gidansu raihana ta rakata sannan ta dawo,
Raihana ta dawo gida tana ta nunanin wannan urin hauka na zulaiha, tsaki tayi sannan taje tayo alwalla don an kira sallar magrib,
hmmm Allah dai yasa mu dace,
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 2⃣0⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*****
*R*aihana tana shiga ɗaki zama tayi a gefen katifa, hawaye yaci gaba da ambaliya daga cikin idanuwanta, kuka take sosai tana addu"a Allah ubangiji ya bata mijin tayi aure wannan musifa ta isheta, shin wai da tana da ƙanne ya zatayi?"" lallai da ba ƙaramin raini zasuyi mata ba,
Kanacin gashin kanka amma ka dawo gida sai abinda aka kasa aka baka, wannan wace irin rayuwa, amma ita zulaiha Allah ya bata dama amma tayi sakaci, kuma ta tashi ta kwaso yara jagal jagal to banda hawanta inama zata wuce a so ta?"" hawayen ta goge sannan ta miƙe ta fara sallah,
Raihana tana cikin sallah ta jiyo gida ya kiɗime, wasu na salati wasu kuma suna cewa gara da akai haka, wasu kuma kamar dai suna ɗan kuka kuka, raihana ita kuma tana gama sallah ta dawo bakin ƙofar ɗakinsu ta cikin labule ta laɓe don tabbatar da abinda taji gaskiya ne?"""
Lallai kunnen gaskiya ya jiyo mata, wato an siyar da wannan gidan da suke ciki kuma ga wanda ya siyi gidan tsaye a tsakar gida yana cewa yaba duk wanda take cikin gidan nan notices daga yanxun zuwa gobe da safe duk wanda takai la"asar a gidan nan tou pha zataga abinda zai biyu baya,
Ajiyar zuciya raihana tayi sannan taja jikinta ta koma saman katifa, *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un* kwai take iya faɗi, raihana a bayyane tayi magana tana faɗin wannan wacd irin rayuwa ce?"" amma lallai bari Umma ta dawo dole gidan gwaggo zamu koma saidai duk bala"in da za"ayi ayi dan basu da inda zasu zauna,
Taci gaba da cewa gashi nan munma fara "yar sana"ar mu muna samun abinda zamu rufawa kanmu asiri, wayyo Allahna ya Allah kaji ƙaina ka rufa man asiri dan matsayin manzan Allah S. A. W, ka taimakeni ka bani miji inyi aure wallahi nayi hankali in Allah ya yadda nayi aure ko bansan mijin wallahi zama zanyi Allah ka yaye man haka nan, ta sake farkewa da wani irin kuka, sannan tayi magana ƙasa ƙasa tace Allah ka taimaka man kada in mutu banyi aure ba,
Umma ce tayi sallama ta shigo ɗakin da sauri raihana ta goge hawayen idonta tunda ɗakin da duhu umma bata san raihana tana kuka ba,
Umma sannu da zuwa, umma tace yawwa raihana tace kin daɗe baki dawo ba, umma tace wallahi, raihana tace kinji kuma abinda aka zo mana dashi?"" umma tace miye?"" hmmm umma wai an tada kowa na gidan nan, umma tace bisa wane dalili?""" raihana tace mai gidan ya siyar wanda ya siya kuma yace kada wanda takai mashi la"asar a gida, ajiyar zuciya umma tayi sannan tace Allah yasa haka shine alkairi,
Raihana tace haba umma wand alkairi kuma don Allah a tashe mu kina cewa Allah yasa alkairi ne, Umma tace haba raihana da ilimikin da hankalinki ya kike abu irin na jahilai?"" duk abinda kika ga ubangiji yayi a rayuwa yana da sila, jin umma zata fara wa,azi ita kuma tana cikin zafi dan haka kawai tace shikenan,
yanxun ina zamu koma?"" umma tace mu bari da safe sai musan nayi, raihana tace Allah ya bamu aron rayuwar, umma tace amin, anma fara kiran sallah muje muyi sallar, raihana tace ita tana da alwalla buta umma ta ɗauka ta fito tsakar gida donyi alwallah,
****
*G*ari na waye kowa fidimar gabansa yake masu fita da kayansu dan mutanen gidan sunce alhaji baya da mutumci, dan haka gara su tafi kafin a wulaƙanta su, raihana tace ma umma kodai mu koma gidan gwaggo, umma tace haba raihana sai kace dai karnuka?"" tunda an koremu ai sai muyi haƙuri mu matsa gaba ko Allah yasa mu dace, raihana tace to, umma ce tace bara inje in cigita mana gida ko mun samu dan wannan ɗaukar alhakine ace an bayar da notices daga jiya zuwa yau, taka dai ta fita daga ɗakin tana mita, dan yau ko abincin siyarwa basui ba,
haka kowa yaci gaba da kwashe kayanshi yana fita, raihana kuma tana ɗaki kwance tana baccin da bayada ma"ana, umma kuma tunda ta tafi har harxun bata dawo,
Raihana tana ɗaki kwance tana bacci bata san gidan kowa ya gama kwashewa ya fita ba, ita kaɗai a ɗaki kwance tana bacci,
alhaji ne ya shigo gidan dashi da rundunar shi, ganin ɗakin su raihana cikin fushi ya yaye labulen ɗakin ya leƙa, hango raihana yayi kwance tana bacci yace kam lallai amma wannan yarinyar tama raihana mana hankali, wani ya kalla sannan yace waccan matar waye?"" yace ranka ya daɗe bata da aure,
tsaki yayi sannan yace waye ubanta, aka ce mashi ɗiyar marigayi mai wankin takalmi ne, alhaji yace shirmen banza maza hau sama ka kware man rufin ɗakin,
raihana na kwance tana bacci, taji ƙarar kwano sama dan ya fara cire kwanon ga kuma rana tana ɗan hasko ta haɗi da ƙasa data fara zubowa, raihana da sauri ta miƙe tana faɗin lafiya?"" daga waje "yan kwarakon alhaji suka fara cewa mai gidane yake iko da abunshi
Raihana tace to miyasa ake cire kwanon ɗakin?"" alhaji yace saboda nawa ne, raihana ta fito daga ɗakin ta kalli alhaji tace "yar laɓai miyasa sai kwanon ɗakinmu za"a cire?"" tsaki yayi sannan yace gyara za"a, raihana tace okey to bari in kwashe kayan in mayar dasu wancan ɗakin, ta nuna wani ɗaki da hannunta, alhaji yace ke nan gidan bakuda wurin zama kowa ya tashi gidana zansa a rusa man, murmushi raihana tayi sannan tace ai babu komai zamu zauna a haka idan an kawo maka kayan aiki dani da ummana sai mu riƙa kular maka dasu kuma ma basai ka bayar da kuɗin kula dasu ba,
Alhaji yaga lallai raihana tana neman raina mashi hankali don haka yace a shiga ɗakinsu a fiddo kayansu waje road dasu, raihana tace haba bawan Allah dan matsayin annabin rahama kayi haƙuri wanda ya shiga ɗakin nasu ta kalla tace idan har kana san Allah ya kyautata lahirar ka kada ka tona mana asiri a cikin unguwa jira kallon alhaji tayi sannan tace Alhaji ka rufa mana asiri kada ka bari a wulaƙantamu a idon duniya,
dan Allah ya baka arziki bai kamata ka wulaƙanta wanda baya dashi ba, hawaye ya zubo daga idonta, taci gaba da cewa tunda kai Allah ya baka kayi haƙuri ka tausaya ma wanda baya dashi, ka rufa mana asiri kaima sai Allah ya rufa maka, zamu tashi kada kasa a watsa mana kaya ummana tun safe ta tafi nemar mana gida har yanxun bata dawo ba nasan bata samu ba, kayi mana wannan alfarmar sai kaima Allah yayi maka, ka rufa mana asiri sai Allah ya rufa maka ,
idan ka koremu anan bamu da inda zamuje, ka bamu aron gidanka mu zauna na lokacin da muka samu, alhaji duk abinda ka samu anan ka sameshi kuma anan zaka barshi babu abinda kowa yaxo dashi kuma duk abinda ka sama anan babu idan zaka je dashi, arxiki kuma da Allah ya baku dan ku taimaki wanda baya dashi idan ka barmu mun zauna a gidan nan babu abinda zamu rage shi, taimako da tausayi shine halin girma,
tunda ta fara magana taƙi tayi shiru bare taji abinda Alhaji zaice, sai taci gaba da cewa kayi mana alfarma dan baka san abinda gobe zatai ba, murmushi tayi sannan ta kalli alhaji tace kayi haƙuri insha Allah zuwa gobe zamu tashi,
umma ce tayi sallama ta shigo, ta gaishe dasu alhaji sannan tace ma raihana an samu gidan, raihana tace alhamdulillah, raihana tace alhaji kaji ma mun samu to mun gode Allah ya ƙara arxiki, umma wannan shine ya sayi gidan kiyi mashi Allah yasa alkairi, umma tayi ma Alhaji addu"a Allah yasa alkairi ubangiji kuma yasa yawancin rai akaimaw, alhaji ya kasa magana, komi yasa Oho,
haka su raihana suka fara cire kayansu dan babu wasu abun arxiki a ɗakin daga wata lasarsar katifa sai kayansu na sakawa da tabarma, haka suka ci gaba da ɗaukar kayansu har suka gama raihana ta sake ma alhaji godiya, suka fita daga gidan,
Suna fita alhaji yace ma wani bisu kaga inda zasu koma, yace to sannan ya fita daga gidan,
raihana da umma sunyi "yar tafiya sosai tsakaninsu da gidan da suka tashi sannan su isa ƙofar gidan da suka koma, sallama sukai sannan suka shiga,
wanda yake binsu ta baya yana ganin inda suka shiga sai ya juyo ya dawo gidan daya bar su alhaji,
Su kuma suna shiga, da sallamar su, matar gidan ta fito tana ma su umma sannu, bayan sun shiga sun zauna, sai matar gidan tace wannan fa?"" ta nuna raihana, umma tace ɗiyata ce, matar tace kai gaskiya wanann nana zankaɗaɗiyar bana zama da ita, wannan ai sai ta kashe man aure, umma tace ah ah baza ta kashe maki aure ba, tana da hankali itana ta taɓa aure, matar ta zaro ido tace *zawara* ce?"" umma tace Eh matar tace kam maima illar kenan wallahi na ɗauka ke ɗaya ce amma gaskiya bana zama da zawara taje ta aure man miji ko kuma ina can sake da baki tayi ta man lalata da miji, umma tace *subahanallah* raihana ba haka halinta yake ba, matar tace ɗan yau ai baka shedarshi tunda ba tare kuke fita ba,
Macen data san daɗin namiji kuma lafiyayyar mace kamar wannan ance maki dutse ce ita da bata buƙatuwa?"" ke tsohowa wallahi ban zama da zawara, kiyi haƙuri, raihana tace kedai zamu bawa haƙuri, amma a ko wane lokaci ka kyautata zato ga mutum, dan ance maki ni *zawara* ce sai akace maki ni karuwa ce?"" kiji tsoron Allah kuma kiyi sauri ki tubar ma Allah sannan kuma ki nemi gafarana in yafe maki, dan ita shedar zina girma gareta, amma daga gani na sai kije zanje inyi ta lalata da mijinki?"" kawai dai kice bayan tafiyarta kin sake shawara bazaki zauna da ita ba,
matar tace to naji bazan zauna da ita ba, ai gidana ne bana uban wani ba?"" kuma shima mai gidan ba nashi bane nawa ne ni na siya dakai na shima na raɓa shi, raihana tace Allah ya baki haƙuri abin duk baikai na zagi ba, Kallon inda umma take zaune tace tashi muje, umma ta miƙe jiki a saɓuƙe tabi bayan raihana suka fita daga gidan,
haka suka ƙusa suka ci gaba da tafi basu ma san ina zasuje ba, ga kuma magrib ta karato, raihana tace umma kiyi haƙuri kawai mu nufi gidan ku,
umma tace baza ki gane abinda nake nufi ba gidanmu baki iya zaman shi, raihana tace zan iya, ajiyar zuciya umma tayi sannan tace muje, suka fara tafiya raihana tace kinga idan mukaje sai mu nemi wani gidan da zamu koma ko?"" umma abun ya kasheta saboda haka bata sake kula raihana ba dan ita kaɗai tasan matsalar da take gidansu raihana ita kaɗai tayi ta magana ba tare da umma tana bata amsa ba har suka isa gidan su umma,
Suna shiga da sallama umma duk bata jin daɗi dan gidan ya haɗa da mutane iri iri, lokacin da sukai sallama suka shiga wani ɗan yayar umma ne kaɗai a gidan zaune da gajeren wando babu ko singilet ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana shan sigari,
Umma ta fara mashi magana yace sannu , ku kuma daga ina kuke haka kamar "ya sansanin gudun hijira, ke kuma kin ɗauko wannan lasassar katifar ko ƙyanƙyanmin ta bakya ji?"", umma dai batayi mashi magana ba, sannan tace ma raihana su shiga daga ciki, shima tasowa yayi ya biyo su yana cewa *raihan* babbar yarinya, kusa da raihana yaje ya zauna sannan ya miƙa mata hannu alamar su gaisa, ko inda yake bata kalla ba, don haka ya tashi ya fita daga ɗakin,
Yana fita daga ɗakin, umma tace kinga ɗaya........................,,,,,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
*Page* 2⃣1⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Jinjina gare ku ameenci writer's bisa namijun ƙoƙarin da kuke Allah ya ƙara basira da zagin hannu ubangiji ya ƙara lafiyar ido da ƙwarinsu,*
*wannan shafin nakune ameenci fans, kuma Allah ya ƙara maku lafiyar idanuwa dan kuji daɗin karatu,*
*Ƙawata Asmeenat Xeeyan ina tare dake a kowane lokaci alkairin Allah yakai maki haɗ sakoton shehu*
*****
*R*aihana ta kalli umma sannan tace ai ban bashi hannun ba, umma tace baki san halin kabir ba , dan ɗan iskane jigunanne saboda haka sai kin kama kanki sosai sannan kuma kada ki kuskura ki sakar mashi fuska, wannan shine dalilin daya sa nace maki zaman gdan nan bayayuwa wurin, raihana tace to umma munje mu kwana saman titi?"" umma tace Allah dai ya sawaƙe ina gaya maki magana ki a kawo man shirmen banza,
Shiru sukai na wani lokaci sannan umma tace bara inje inyi alwalla, raihana tace to, umma ta ɗauki buta ta fita, bayan tayo alwalla ta dawo itama raihana ta fita danyo alwalla,
Kabir yana tsaye tsakar gida sai sigari yake zuƙa yanda yake ɗaga bakinshi idan zai fita da iskar sigarin tun daga nan zaka gane tataccen ɗan iskane, raihana ta wuce kangal kangal zata nufi bayi, shima bayanta yabi, juyowa tayi taga ita yake bi,
Kaucewa tayi gefe ɗaya don bashi hanya ya wuce, kallonta yayi da idanuwanshi masu jan tsiya, raihana ta sake ja da baya dan gani take kamar hanyar bata isheshi ba, inda ta raɓe shima wurin ya koma lokacin daya sake sanya karan sigarin a bakinshi ya ja, sannan ya busa mata hayaƙin, tsaki raihana tayi ta nufi bayi ta shige ta kulle, saida ta gama abinda take sannan ta fito, tana buɗe ƙofar ta ganshi tsaye tace malam bani hanya kaji,
Cikin maganar yan iska yace nayi farin cikin ganinki fa, ke bakiji daɗi da kika ganni ba?"" raihana tace bara in gama abinda nake sai muyi magana, kabir yace ai kin gama yanxun, tace sallah zanyi, kabir yace wace sallah kuma ga umma can tana maki basar kawai ta sammaki ladar, raihana ta wuto zata wuce ya sake shan gabanta, yace an mata ana nan ana hutawa shi yasa kika ƙi aure ko?""
Raihana tace da Allah gyara man hanya in wuce, yanda tayi maganar babu alamar wasa kabir cikin maganar tashanci yace keji yarinya waini zaki ma fuska?"" uhum bara dai anjimar tayi, tunda muna tare in daina zumiɗi, raihana dai bata sake magana ba ta raɓa shi ta wuce,
alwallah tayi sannan ta shige ɗaki danyin sallah,
suna nan zaune ita da umma sukai magrib suna wurin har aka kira isha"i suyaka yi, bayan sun gama raihana tace umma wai miyasa ita umma halima ta rufe wancan ɗakin?"" ai sai ta buɗe mana dani dake mu shiga ciki, umma tace ai sai kije ki faɗa mata,
dariya raihana tayi sannan tace Allah ya baki haƙuri, umma bata sake magana ba,
bayan wani lokaci raihana tace umma idan kina da kuɗi kawo inje in samo mana ko gari ne mu jiƙa ni wallahi yunwa ma nake ji, umma tace banda su, raihana dai ta kula umma cikin fushi take saboda haka ta tashi taje ta kwanta saman wani gadon ƙarfe da yake cikin ɗakin, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauketa dan ta gaji sosai, ita kuma umma hankalinta ya kasa natsuwa dan haka ta kasa kwanciya tana nan zaune kuma ɗakin babu fita ɗakin dumm yake da duhu,
Raihana bacci take sosai , saboda haka cikin bacci taji umma sa"a na cewa wanda ta isa ce ta hau man gado sauko, umma ita kuma tana cewa wai ku duk ina kuka shiga sai yanxun zaku dawo gida don Allah?""
umma sa"a tace neman kuɗi muka je, umma tace neman kuɗi kuma kamar wasu mazaje?"" tsaki tayi sannan tace wai mima kuka zo yi nan ne?"" umma tace a gidan da muke haya ne aka tashe mu, zamu zauna nan kafin mu samu wani,
umma sa"a tace amma baki da hankali fatima, in banda hauka kinsan nan gidan ɗaki ɗaya ne, sai kuma ki kwaso saboda Allah ki taho , ita raihanar aikin mi takeyi ne da baza taje wurin masu santa su baku wurin zama ba, to miye amfanin *zawarcin* nata?""
raihana dake kwance taji abun yaƙi ƙarawe ta tashi ta sauka daga saman gadon kusa da umma ta koma ta zauna sannan tace umma sa"a ina yini, umma sa"a tace wane ina yini?"" ina amfaninki raihana?"" da kyanki da ɗirinƙi da sigarki babu namijin da zai ganki hankalinshi bai tashi ba, ina ni"imar da Allah yayi maki dan baƙin ciki sai ki zauna bahagguwa dake duk masu sanki sai kice su baki gidan zama ,
amma sai ku kwaso dake da uwarki kuyo mana nan?"" mu a ina zamu ajiye ku?"" ki dage ki more rayuwarki raihana ki samar maku "yanci har muma muzo cin arxiki,
umma sa"a, yayar umma ce, idanuwanta sun bushe saboda ita tana da san abun duniya sannan kuma tana da san kai ita kullum yaranta tana ƙoƙarin ɗorasu kan turba ta gaskiya, amma ɗan wani duk inda zata turashi ga halaka kullum ƙoƙarin neman haryar take, amma ita ga "ya"yan ta nan duk basujin magana ,
*zawara* sunkai biyar a gidan su umma idan hada raihana da umma mutum bakwai kenan wansa basu da aure,
raihana dake nake magana , kina jina kin wani man kamar baki sna ina magana ba, cikin sanyi raihana tayi magana tace umma naji,
umma sa"a tace to banda abinki ke fatima ina zamu kwana, kinsan babu wuri a ɗakin nan, yanxun ina zaku kwanta?"" kabir daga waje cikin maganar ƙauraye ga sholisha yana murzawa yace umma ita raihana ai sai mu kwana ɗaki ɗaya da ita, tunda ita muharrama tace, umma tace kai da Allah rufe mana baki , umma sa"a tace to fatima miye?"" dan kabir da raihana sun kwana ɗaki ɗaya miye?"" tunda abun duk gidane ai sai a haɗu a rufa ma kai asiri, ke raihana ki kwana a ɗakin kabir ɗin ita kuma fatima sai muyi sikwacin nan da ita,
dariya raihana tayi sannan tace umma sa"a kenan wannan kasafin naki yayi, amma huɗubarki ta farko itace na ɗauka zanje yau cikin daren nan in samo mana gida, umma sa"a tace ah ah ki bari sai goben, kabir yace ke "yar rainin hakali ummata zaki fara gayama magana?"" ni ban ɗaukar iskanci idan dai aka taɓo man ummata, raihana tace yi haƙuri banzo wurinka ba, da yar uwata nake magana,
kabir ya taso daga inda yake zaune cikin layi ya shigo ɗakin gaban raihana ya tsaya sannan yayi magana cikin muryar daba yace shegiya *zawarar* banza iskancin ki zai tsaya akan uwata ne,?"" wata tagulla ya fito da ita daga cikin aljihunshi sannan yace kinga wannan?"" ina iya aika ki lahira da ita,
murmushi raihana tayi da gefen bakinta, sannan ta ɗago ta kalli kabir ta jinjina kanta, yace ni kike cewa zakici uwata?"" raihana tace ai ban zagin uwarka saboda uwarka uwata ce saida in lalata maka fata da duka, dan bari ganin umma sa"a tana magana kana neman raihana ma mutane hankali raihana zafi ne da ita, dan idan na sadda kaina ƙasa ni nafi guguwa bala"i, daka taɓoni gara kaje ka rungumi transfomer, ɗaure fuskarta tayi sosai sannan tace umma kwanta,
Umma tabi raihana da kallo da tasan raihana ba magana tasha mata kaiba, ita kuma raihana ta ɗauri aniyar duk wanda ya sake taɓota bata mashi sauƙi tunda ba"a tausayinsu, kuma yanxun babu inda zata je, anan zasu kwana,
umma ki kwanta nace, umma tabi raihana da kallo, ita kuma miƙewa tayi taje wurin kayansu ta buɗe jakar kayanta ta fiddo wani wandon jeans ta saka ta ɗaure gamm sannan ta dake cinyarta tace dani dakai duk wanda ya fasa yaci uwashi , tana gama maganar ta koma ta haye saman gadon umma sa"a, tace umma sa"a, kezo nan muyi sikwacin, maganar data faɗa ma ummarta ta rama mata,
Umma sa"a tace ma kabir jeka, haka umma sa"a taci gaba da mitarta, daga bayan taje ta raɓa kusa da raihana ta kwanta, sda guda guda haka zawarawan gidan su umma suka ci gaba da shigowa, ko ina suke zuwa ohon masu, dan ita dai raihana tuni bacci yayi gaba da ita,
*****
Da safe kowa ya tashi lafiya, raihana koda safe batayi ma kowa magana ba,
Kowa shine yakd siyen kalancin shi da kanshi, umma ta bawa raihana kuɗi itama taje ta siyo masu koko, taje ta siyo masu koko da alewa ta dawo gida, bayan sun gama kalaci kowa ya fara wanka dan fita,
itama umma shiri tayi dan tafiya nemar masu gida, da zata fita tace na raihana ta kula da rayuwarta, dan kabir bayada mutumci raihana tace to umma, bayan taja mata kunne ne ta fita tabar gidan , haka kowa yayi ta fita ɗaya bayan ɗaya,
gida ya rage daga raihana sai kabir..........................................
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦
💦💦💦
*Page*2⃣2⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*****
*R*aihana ta fito daga ɗaki taxo taja ruwa, bayan ta gama jan ruwan ta koma ɗaki taje ta cire kayanta ta ɗauro zani ta ɗauki hijabi ta saka , kwandon wanka ta ɗauko tayo waje, tana zuwa ruwa ta ɗauka ta nufi bayi,
Kabir yana ganin raihana ta shiga bayi shima ya fito daga cikin ɗakinshi ya nufi ƙofar bayin ya fara kwankwasawa, gamgamgamm bambambamm, raihana saidai tace Ehem Ehem, yaci gaba da kwankwasawa, raihana tayi masji banza, yace raihana buɗe zan shigo bayan gida zanyi, raihana tace wai kai wane irin tantirin ɗan iska ne?"" tun ina maka gyaran murya kasa nayi magana a bayi, ai kaga na shiga wanka banda iskanci duk da bama ce zaka shiga bayin ba sai yanxun?"" yace to ki buɗe mana yanxun na matsu, kinayin wankan ki nima sai inyi nawa uzirin,
Raihana tace ina wanka zaka shigo?"" kabir yace to miye nifa da zaki ganni nima?"" raihana tace bana buƙatar ganin ka, kabir yace buɗe ƙofar dan kutumar ubanki, raihana tayi mashi banza taci gaba da wankanta, zaninta da ta ɗaura saman ƙofar ya janye ya riƙe a hannunshi yace shegiya yau kin fito tsirara inga abinda kike boyewa, wani banza ma can ya ganki bare ni, ina ɗan uwanki muharramin ki, dan na ganki miye a ciki to?""
Wani irin salati raihana tayi ganin lokacin da kabir ya janye mata zani daga saman kware, kallon rufen bayin tayi sannan ta kalli ƙofar kwaren, tace kam lalla kabir ɗan iskane, wato kila da babu rufe zai iya shigowa ta sama, da kuma saman kwaren zai iya shigo dasai yabi ya shigo, tace Allah yasa kada ya dauko wani abu ya taka ya leƙoni,
Shi kuma zama yayi ya riƙe zanin gam, yana cewa dan uwarki yau saidai ki kwana a bayi na faɗa maki,
Gaban raihana ya faɗi tace kai wannan anyi ɗanyen ɗan iska, hawaye ya zubo mata daga idanuwanta tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, duk zawarci yaja man, hannunta tasa ta goge hawayen idon ta sannan tace kai Allah ka rufa mana asiri, shi yasa haƙuri yake da riba a rayuwa, lokacin da akd bani haƙuri in zauna ɗakin mijina gani nake kamar ba kauna na ake ba, gashi yanxun ina haƙuri da ƙaton banza,
Tana cikin wannan tunanin ne taji kabir yana cewa, shehiya danma za"a rufa maki asiri ga magani har gida an hutashshe ki fita, shine sai kin tsaya kina wani jama mutane aji, ki fito ki anshi rabonki ko kin samu na bacci rana,
Raihana tace subahanallah, ita dai ta kasa magana dan ji take kada ta sake magana ya ɓalle ƙofar ya shigo, raihana tana cikin bayi sai kuka take tana da nasin ta zuwa gidan nan, ji take ina ma da zata dawo yanxun data gyara zaman ta da ameenu, tace Allah ka bani miji ko a gidan hayane, wallahi ko baiman ba sai na zauna,
lallai zanje in samu farida inma faɗa mata ta ƙara zage damsti ta kula da mijinta dan samu tsira duniya da lahira, wato idan kana zawarci gani ake kai ɗan iska ne, tsaki tayi sannan tace Allah ya tsine ma kabir albarka,
Maganar shi ta sake jiyowa yana cewa na rantse da Allah idan wani ya shigo gidan nan baki fito sai naja maki sharri, raihana tace kaji ɗan iska kuma ko?""
ita dai tayi shiru tana addu"ar Allah ya tsallaketa, tun tana zaman bayi na marmari ha zaman ya fara isarta, tun tana kukan zuci har ta fara mai ƙarfi, shi kuma kabir sai maganar batsa yake, raihana tanajinshi amma ta kasa magana,
Har aka kira azahar kabir bai fita ba kuma bai dawo mata da zaninta ba, kam wasa sabon fari, tana cikin bayi har yanxun tana kuka, tana tsine ma kabir albarka, tana nadamar zuwanta gidan nan tare da nemar ma duk macen dake faɗin duniya Allah ya rabata da *zawarci* duk inda ka samu ka raɓa kayi haƙuri wata rana sai labari, idan kuwa kace zawarci zakai lallai yanxun ka fara ganin wulaƙanta, dan baka da mutumci da kima da daraja a idon kowa raihana tace yanxun da ina da aurena mima zai kawoni gidan nan har inyi wanka?"" koma nazo nayi wankan ai bai isa ya wulaƙantani haka ba, wani irin ihu raihana tayi kamar mai shirin hawa bori, kabir dake zaune yaji ƙarajin data yi, yace kiman alkawari idan zaki ban insha nono, raihana tace Allah ya tsine maka albarka wallahi banƙi yau an gitta gawarka ka mutu ba, kabir yace ban mutuwa wallahi harsai na samu abinda nake so a wurinki, ina samun abinda nake so yauma in mutu banajin komai,
Kiran sallar la'asar raihana taji an fara, wayyyo Allahna na shiga ukku na lalace nk raihana, kabir dan matsayin manzan Allah S. A. W ka bani zanina dan girman ubangiji kasa sai kiran Allah nake a cikin bayi, ka rufa man asiri, kabir yace yarinya dani kike zance, baƙin ciki yasa raihana tayi shiru, ta koma kuka ƙasa ƙasa, ga ta gaji da tsayuwa amma babu damar ta zauna cikin bayin dan tsikar jikinta ma a tashe take,
tana cikin kuka taji anyi sallama, gabanta ya faɗi tace Allah kasa ba umma bace, lokacin da hawaye ya sake zubo mata daga idon ta , gaishe da kabir tayi sannan tace don Allah raihana tana nan?"" kabir yace bata nan, daga cikin bayi raihana tace zulaihat ina nan ƙarya yake rufa man asiri kada ki fita daga gidan nan don girman Allah, kasan cewa zulaiha ba ita ɗaya bace taxo, su ukku ne, itama ɗaga muryarta tayi sannan tace kina inane?"" raihana tace gani nan a bayi shiga ɗakin ki ɗauko man kayan sawa, har zata shiga ɗaki kabir yace bar munafika gafa zanin nan ta bani riƙo da zata shiga wanka, anshi ki miƙa ma baƙar munafika kusa dashi zulaiha ta matsa ta karɓi zanin ta miƙa ma raihana ta ɗaura ta sako hijabinta sannan ta buɗe bayin ta fito,
tana fitowa da gudu taje ta rungume zulaiha ta fashe da kuka tace Allah ka raba kullihin musulmi da zawarci, ƙawayen zulaiha suƙa amsa da amin bakin ɗayansu, kabir kuma sai hararar raihana yake, alwalla tayi sannan suka shiga ɗaki baki ɗayansu,
suna shiga raihana ta fara sallah ko gaisawa dasu bata tsaya yi ba, saida ta gama sallah sannan ta shirya ta saka kayanta, ta kalli zulaiha tace yau kin ceci rayuwata, ta kwashe kaf abinda ya faru ta faɗa masu, ƙawar zulaiha tai dariya tace ke ai mai sauƙi ne, shi yasa kin ganni nan na rufa ma kaina asiri dana fara zawarcin nan mijina yana shaye shaye mutane suka matsa man in kashe aure na, na kashe auren na koma gida, sai gashi ni ƙanin kishiryar mamana zaiman fyaɗe,
tsaki raihana tayi tace Allah dai ya sawaƙe, kawar zulaiha tace idan dai kana zawarci wulaƙanci iri iri sai ka fuskance shi, ni wallahi dana ga mace tana halbe halbe a gidan mijinta sai nace ta rufa ma kanta asiri, tayi haƙuri tayi zaman ta,
raihana tace gaskiya aini yanxun idan nayi aure ko mijina ya ƙoreni babu gidan ubandaa zanje, bare ma insha Allah bazan mashi abinda zai ɓata mashi rai ba, tarairayarshi zanyi in kula dashi bazan bashi abu daga tsaye ba, zan girmamashi sai yaji daɗin aurena wallahi, dariya sukai baki ɗayansu, raihana tace bansan wulaƙanci fa, dukansu sukai dariya baki ɗaya,
raihana tace zulai waye ya faɗa maki ina muna na gidan?"" tace dana je gidan da kuke haya baku nan sai naje na tambayi gwaggo tace tanajin kina gidan ummanki, raihana tace ashe tasan muna nan?"" zulaiha tace Eh, raihana tace ina yaranki ne?"" tace hmm na maiyar dasu kamar yanda kika ce,.ke raihana matarshi kinsan bata taɓa aihuwa ba, ko?"" to tace bata riƙe mashi "ya"yanshi, tayi yaji tana gidansu, yau yazo gidanmu yace ma baba ayi haƙuri yana biko,
Raiha a tayi dariya, sannan tace kinji ita kuma banzar zatai ma kanta, mu mata muna da matsala dasai ta kama yaran ta riƙe to miye a ciki?"" zulaiha tace baƙin ciki zaki man?"" kibar banza ta tafi ai duniyar sai wani ya rasa wani yake samu, raihana tace ba baƙin ciki bane, gaskiya ce, dake da ita babu wanda ya kawo wani kiyi haƙuri kuyi zaman ku, zulaiha tace kr barta can ita ta sani,
Raihana tace to yanxun ya aka ƙare zulaiha tace da aka kirani maganar komawa cewa nayi gaskiya bazan koma ba, raihana ta taɓe baki tace shegiya dama ni na samu damarki wallahi da komawata zanyi dariya zulaiha tayi sannan tace ke jan ajin nan ne, su duka suka kwashe da dariya, raihana tace wane aji yarinya?"" ai aji cikin gida ake janshi , bari ki shiga daga ciki sannan kina shi, idan yaga zaki raina mashi hankali saiya haƙura dake kinsan suma mazan da nasu halin, amma ki lallaɓa kawai ki koma tunda dama ta samu kafin ta wuce, zulaiha tace insha Allah, hada ceman ai laifinki yasa na ƙara aure tana kwaikwayon maganar mijin nata, duk suka sake sheƙewa da dariya,
zulaiha tace kai ku tashi mu tafi idan muka biye raihana anan zamu kwana kinga har an fara kiran sallah magrib, lokacin da suka tashi baki ɗayansu,
hijabi rainaha tasa danyi masu raki, tunda tace su tsaya suyi sallah amma sunce sai sunje gida,
bayan ta raka su ta dawo, bata shiga gidan ba, ƙofar gida ta zauna, tana jiran wanda zai shiga gidan, tana nan zaune ƙofar gida babu alamar wanda zaizo, kabir ne ya fito daga cikin gidan, ya kalleta sannan ya wuce, miƙewa tayi da sauri ta shige gidan tana shiga ta kulle ƙofar, shi kuma yana ganin ta shiga ya fara bubuguwa, raihana tasa ko masu gidan ne suka fara dawowa, tana zuwa tace waye?"" yace ubanki ne, buɗe mana gida tunda ba gidan ubanki bane, raihana tace anƙi a buɗe sai masu gidan sun dawo, yace na ranste maki idan na biyo ta sama kashinki ya bushe, raihana tana jin haka da sauri ta ɗaga kanta dan ganin kantangar ganin zai iya shigowa yasa ta yanke shawarar buɗe mashi amma sai ta koma ƙofar gida, tana magansr zuci taji yace baki jina ne dan kutumar ubanki?"" da sauri raihana ta buɗe ƙofar tana ƙoƙari fita yana ƙokarin shigowa, da sauri ya riƙeta, ya lallatsa mata nono tace wayyo Allahna na shiga ukku matse ta yayi jikin bango da ƙarfin bala"i shi ƙoƙarinshi ya rufe gidan ita kuma sai yage baki take tana jama"a ku kawo ɗauki, daɗe mata baki yayi da hannushi yace shegiya sai kin tara mana mutane, ni ban taɓa ganin wanda baisan arxiki irinki ba, ana ƙoƙarin rufa maki asiri ke kuma kina so ki tona ma mutane ko, hannunshi ya sake kaiwa saitin mamanta da sauri ta zame, tana ƙoƙarin fifa dan ƙafarta ɗaya harta taka sumintin ƙofar gida, ya jawo mata wuyan hijabi ƙiyyyyyyy ya dawo da ita ciki, dukiyar fulaninta ya sake kai hannunshi kafin ya ƙara taɓawa raihana tayi kukan kura takai bakinta saitin hancin shi tayi mashi wani irin cixo, shi kuma lokacin da yaga ta buɗe bakinta ta nufo fuskarshi tunaninshi kisss zatai mashi saboda haka ya saki baki,
lokacin daya ji cizo kundai san hanci baya san a taɓa shi kabir jinshi yayi a duniya yake ko a lahira, tana ganin ya rufe idonshi yana ihu tayo waje da gudu, tana fitosa suka haɗu da umma..................€€
💦💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦
*Page* 2⃣3⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*jinjinar ban girma ameenci fans, wannan page in nakune , Asmeenat Xeeyan tace a baku shi*
*****
*U*mma ganin raihana ta fito da gudu ta tsaya tana tambayarta lafiya?"" bata gama rufe bakinta ba, saiga kabir ya fito cikin 360 yana cewa yau sai kinci ubanda ya haifeki,
Ganin umma yasa ya tsaya, umma ta fara tambayar lafiya?"" da gudu raihana taje ta faɗa saman kafaɗar umma tana kuka tace umma muje bana san gidan nan mu tafi don Allah, tana sake farkewa da kuka,
Hankalin umma ya tashi tace miye wai?"" hannu raihana ta shiga girgizawa tana cewa muje umma mu tafi don Allah,
Umma ta kalli inda kabir yake tace lafiya kabir?"" kabir kallon raihana yayi raihana tace umma muje muje don Allah na tsani gidan nan, mu tafi kada mu dake komawa gidan nan,
Umma tace wai miye ne?"" kai kabir laifi tayi maka ne?"" kabir yace umma zagina tayi, da sauri raihana ta ɗago daga saman kafaɗar umma ta kalli kabir, umma kuma tace miya haɗaku?"" kabir yayi tsuru tsuru dan baisan amsar da zai bawa umma ba, umma tace ummmm Allah ya kyauta dai,
Raihana cikin kuka tace umma kin samo mana gdan?"" umma tace ban samu ba, raihana tace ina kika je kika daɗe?"" umma tace inacan neman gidan , umma tace muje ciki, raihana tace wallahi bazan sake shiga gidan nan ba,
Umma tace to ina zamu?"" raihana tace ki zauna gidanku nima zan tafi gidanmu, tana faɗin haka ta fara tafiya, umma tace raihana zo nan!"" raihana ta tsaya ba tare data juyo ba, umma tace raihana ina ne gidanku?"" raihana tace wallahi gidan gwaggo zanje, umma tace to kije da safe ki dawo ina nemanki, raihana tace to, sannan ta wuce daga wurin,
Umma na ganin tabar wurin tace kila halin nashi ne yayi mata, bawar Allah ubangiji ya baki miji na gari ubangiji ya kawo maki sauƙin wannan *zawarci* mutum ya rasa inda zai raɓa, ajiyar zuciya tayi sannan ta shige gida, shi kuma kabir wuri ya samu ya zauna yana tsine ma raihana da maiyi abinda yasa ransa yayi ba,
raihana tafiya tayi sosai kafin ta iso gidan gwaggo, lokacin data iso ƙofar gida suka haɗu da gwaggo da alama daga unguwa ta dawo, raihana tace gwaggo daga ina haka?"" gwaggo tace daga unguwa nake, raihana tace nazo gaisheki ne, gwaggo tace to, ta buɗe gidan suka shiga, ɗaki raihana tabi gwaggo suka shiga, suna shiga raihana tace bara tayi sallah gwaggo tace to, buta ta ɗauka ta fita, bayan tayo alwalla ta dawo tayi sallah, data gama suƙa sake gaisawa da gwaggo sun ɗan daɗe suna fira, daga baya gwaggo tace ma raihana ki tashi ki tafi gida dare ya fara, raihana tace ina nan yau anan zan kwana, gwaggo tace saboda mi zaki kwana anan?"" raihana tace haka kawai nayi ra"ayi, gwaggo tace idan uwaki ta nemeki fa?""
Raihana tace ai nace mata na dawo nan gidan kwata kwata da zama, harsai Allah ya bani mijin aure, ido gwaggo ta zaro tace nidai ban zama dake raihana tace ai bake zaki zauna dani ba nice zan zauna dakai, gwaggo tace baki isa ba, raihana gado ta tashi ta haye, bayan ta kwanta tace gwaggo da safe ko waye zaije can gidan ya anso man kayana?"" gwaggo tayi ma raihana shiru , duk maganar da raihana tayi gwaggo bata , bata amsa, baki raihana ta taɓe, sanan tace gwaggo kenan,
Raihana gyara kwanciyarta tayi sannan ta fara tuno abinda ya faru tsakaninta da kabir, ajiyar zuciya tayi sannan tayi addu"ar Allah ya tsare na gaba, haka dai tayi ta tunani iri iri har bacci ya ɗauketa,
****
*G*ari na waye wa, gwaggo ta tashi ta ɗora dumamen tuwo, lokacin da raihana ta farka, dan sallahr asuba tayi ta koma bacci, to lokacin data farka jikinta ta wanke ta shirya dan tafiya wurin kiran da umma tace da safe ta dawo,
tsakar gida ta fito tayi ma gwaggo sai ta dawo, tace kada ki dawo gaskiya nidai kiyi zamanki can, raihana ta juyo ta kalli gwaggo sannan tace gwaggo kiyi haƙuri don girman Allah kada ki manta ada wannan gidan ba naki bane, mahifinmu yake dashi baki taɓa zaton zaki sameshi ba, ita rayuwa hawa da sauka ce kiyi man alfarma dan Allah in zauna na wani lokaci kafin mu samu gidan zama, bance da umma zamu dawo ba ni kaɗai zan zauna, taci gaba da cewa gwaggo kefe mai riƙeni ce yanxun da maifiyata bata da rai haka zaku barni inyi ta tangariri a duniya?"" hawaye ya zubo daga idon raihana tace kiyi haƙuri rayuwa juyawa take sai kiga wata rana na gaba ya koma baya, amma duk abinda akai haƙuri dashi sai ya zama labari,
gwaggo cikin sanyi tace to ai kema ki fito da miji kiyi aure amma kin tsaya ruwan ido , raihana tace ba ruwan ido nake ba Allah har yanxun bai kawo man wanda zai aureni ba, dana samu zanyi aure kiyi haƙuri, ki barni in zauna tare dake kada wannan raɓe raɓen da nake yasa ni faɗawa cikin wani hali,
Jikin gwaggo yayi sanyi raihana ta bata tsauyi, tana tunani taji raihana na cewa ki taimaka man don girman Allah ko yau muka samu gida dani da ummana bama zan dawo ba, amma idan bamu samu ba zan dawo ki taimaka man ko a tsakar gida sai in riƙa kwana, gwaggo tayi shiru,
raihana taci gaba da cewa nayi imani da "ya"yanki ne a wannan rayuwar zakiji tausayinsu duba kiga jarawar da Allah ya ɗora man ya kamata a tausaya man gwaggo duniyar duka guda nawa take?"" baki da tabbas ma idan na fita zan dawo da rayuwata kila kuma saƙon mutuwa ta zaizo maki, ki taimakeni gwaggo yanxun nake buƙatar taimako don Allah
gwaggo tace tsaya kici tuwo, raihana tayi murmushi sannan tace na ƙoshi, gwaggo tace mi kika ci ne?"" raihana tana cikin tashin hankali sai yanxun ta tuna rabonya da abinci tun ruwan kokon data sha jiya da alewa, tanajin yunwa sosai amma tunda gwaggo dama tun baba yana raye bata san taci abincin gida yasa ta haƙura ta matse yunwarta tace umma ta ajiye man kalaci,
sai na dawo gwaggo, gwaggo tace jira in baki mabuɗi guda ɗaya ko kinxo bana nan sai ki buɗe, raihana tace ah ah barshi idan nazo baki nan zan jira a waje harsai kin dawo,
tana faɗin haka tayi waje, tana fita take magana a ranta tace muda gidan gadonmu amma ƙarfin ya cinye mana, hawayen daya zubo mata a idonta tasa gefen hijabinta ta goge, haka ta daɓi sayyada har gidansu umma,
Lokacin data isa a ƙofar gida ta tsaya ta samu yaro tace ya shiga yace a na sallama da umma fati, bayan wani lokaci yaron ya dawo yace gata nan zuwa, godiya raihana tayi mashi sannan ta samu wuri ta zauna tana jiran fitowar mahaifiyarta ,,,,,
ba"a wani ɗauki lokaci ba, umma ta fito, inda raihana take zaune taje ta zauna , bayan ta zauna raihana ta gaisheta, umma ta amsa sannan ta kalli raihana tace kuka kikai?"" murmushi ta ƙaƙaro dan tana cikin damuwa, sannan tace ma umma mi kika gani?"" umma tace naga idonki yayi ja, wasu sabbin hawaye suka zubo ma raihana wadda ta kasa maida su, ta kalli umma tace nidao zanje ince ma yusufa ya aiko idai zai aure ni, umma ta zaro ido tace mata haba raihana kiyi haƙuri tunda ya daina zuwa wurinki saiki barshi, kiyi fatan Allah ya baki wani wanda yafi shi alkairi,
raihana tace umma haƙuri na nidai bama ƙarewa yayi ba mutuwa yayi ta sake ɓarkewa da kuka umma taji tausayin raihana sosai, ita umma tunanin ta raihana abinda yasa take so tayi aure kila dan ta taɓa auren ne ko tana buƙatar namiji a kusa da ita,
Ita kuma a ɓangaren raihana tana so tayi aurene saboda ta rasa mataɓa, dan ita babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninta da wani namiji, dan ko aminu daya aureta duk zan da sukai saidai ya ɗanyi wasanni da ita,
Umma ta kalli raihana sannan tace to tunda kina ganin haka ne mafita kiyi ma yusufan magana kiji, tayi ma raihana hakane dan kada taje ta saka rayuwata a wani halin ,,,,
Raihana ta kalli umma tace umma kinyi kalaci ne?"" umma tace ni ɗan kuɗaɗen nawa ma an sace, raihana tace subahanallah""" garin ya?"" umma tace nima wallahi ban sani ba , raihana tace to mi kikaci yanxun?"" umma tace ba komai, raihana tabi mahaifiyarya da kallo cikin tausayi
Umma tace ke ban maki albishir ba, raihana tace nami?"" umma tace na samu aiki wani gida, gaban raihana ya faɗi, tace haba umma, sai ki tafi kina aiki aje ayi ta ɓata maki rai?"" ni wallahi bansan aikin gidajen nan, tace ke wannan basu da wulaƙanci wallahi mutanen kirki ne, raihana tace to Allah ya tsare ,
Umma tace ameen sannan tace to ya kuka ƙare da gwaggon?"" raihana ta ɓoye ma umma dan kada ranta ya ɓaci, tace gwaggo tace wai hadake mu dawo gidanta, dan tasan umma baza ta koma ba, raihana taci gaba da cewa nace mata ah ah, nidai kaɗai zan zauna ke kince baza kixo ba, umma tace kwarai kuwa ko babu sauran gidan zama a duniya,
Dariya raihana tayi sanann tace umma bani kayana kinji inje inyi wanka gidan farida zanje, umma tace wane iri zan ɗauko maki, raihana tace masu kyau zaki bani kala biyar dan saina kwana biyu ban sake dawowa ba, umma tace to,
tashi tayi taje ta ɗauko mata kayanta sannan ta kawo mata, raihana tayi mata bankwana sannan ta tafi,
raihana tafiya take a galabaice yunwa ta isheta har bata ganin gabanta saboda azabar yunwa, daƙel ta iso gidan gwaggo lokacin data iso ta samu gwaggo ta fito zata fita, gwaggo tace har kin dawo ne?"" raihana tace Eh gwaggo tace to ga mabuɗin gidan raihana tace a,a barshi kije ki dawo, gwaggo tace saboda mi?"" raihana tace ai nima gaba zanyi, gwaggo tace to sai kin dawo, raihana ta miƙe da "yan kayanta tayi gaba,
a ranta take magana tace yanxun in anshi makullin gidan nan gwaggo tana iya cewa na sace mata wani abu, a fili tayi magana tace tunda ina san zama zan kiyaye abincinko da makullin gidanki dan in zauna lafiya,
Tafiya take har ta iso wurin wata majalissa suka fara kaɗa mata taken nata, *zawara uwar san banza ke wuta ƙaninki ɓarawo* haka sukai ta faɗi har ta wuce wurin ta isa bakin titi, napep ta tsayar ta faɗa mata inda zata kaita, sukai ciniki sannan ta shiga sai gidan farida,
suna zuwa tace mashi ya jirata ta karɓo mashi kuɗin shi, tana zuwa tayi ta nooking shiru, haka taci gaba da bugawa, wata maƙotarsu ce ta leƙo, suka gaisa tace mata don farida fa?"" tace ai farida sun daɗe basa nan!""" raihana tace ina suka je ne?"" tace sun tafi umara , kuma dama kamar tasan zakizo tace ga saƙo a baki,
shigo , raihana tace to, ciki suka shiga, a farlo ta zauna tana jiran fitowarta, ta ɗan daɗe sannan ta fito, da wata ƙatuwar leda ta ajiye a gaban raihana tace ki duba komai yana ciki, tace taxo gidanku baku nan , gidan a kulle,
Godiya raihana tayi sannan ta miƙe tayo wurin mai napep, ta shiga tace suje, suka dawo, a ƙofar shagon shamsu ya ajiyeta, kayan sawarta data ɗauko daga gidansu umma taba shamsu tace don matsayin manzan Allah S. A. W ka riƙesu ka bani ɗari biyar, dariya shamsu yayi sannan yace kai gaskiya kinajin garin nan, raihana tace kaidai ka sani, karɓar kayan yayi sannan ya bata kuɗin mai napep taje ta bawa ɗaru ukku sannan ta ɗauko ledar da farida ta bada a bata, sannan ta nufi gidan da ake siyar da abinci tana zuwa tasa aka zuba mata na ɗari da hamsin dukanshi ta shafe shi kafff sannan ta anshi amsin ɗin ta fito daga gidan , tana tafiya taga wani yaro yana tallar ruwa ta siya tayo ƙofar gidan gwaggo ta zauna,,,,
tana zama ta duƙar da kanta ƙasa taci gaba da kuka........................
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦
💦💦💦
*Page* 2⃣4⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*Gaisuwa ta musamman a gareki Hafsat Isa Mamman Katsina, ina maki fatan alkairi, alkairin Allah ya taddaki har binnin katsinar dikko ɗakin ƙara*
*Allah sarki ƙawata Asmeenat Xeeyan ina maraicinkin sosai Allah ya dawo man dake lafiya kema alkairi ya iskoki har sakoton shehu*
*Wannan shafin naku ne ameenci fans Allah ya ƙara mana kaunar juna, muna tare*
******
*K*anta yana ƙasa sai kuka take tare da addu"a Allah ya kawo mata ɗaukin wannan rayuwa da take ciki,
Raihana ta ɗago kanta sannan ta goge hawayen idonta, ledar gaban ta data zo da ita daga maƙotan farida data bada a ajiye mata ta jawo, buɗewa tayi ta fara dubawa, turamen atamfa ne kala ukku da gyale sai mabar riga da hijabi biyu, sai talami kala ɗaya, da kwalin waya ƙirar L9plus , ajiyar zuciya tayi sannan tace Allah sarki idan mutum yana sanka yana kaunar ka, Allah ya ƙara maki kisanci da mijinki ya baki haƙurin zama dashi kiyi haƙuri kiyi zaman ki farida zawarci babu daɗi kixo kiyi ta raɓr raɓe,
ƙarshe ma abinda zakaci yaxo yayi maka tsaye, sannan baka da mutumci da kima a idon kowa, haka tayi ta magana sai kace tana ganin farida,
Atamfofin ta fiddo ta fara dubawa ɗaya bayan ɗaya tana dorawa saman cinyarta, saida ta gama fitowa da kayan duka sannan daga ƙasa taga takarda , da sauri ta jawota, ta buɗe, kuɗi ne ciki 5k, a jikin takardar kuma anyi rubutu kamar haka,
```Assalam ƙawata da farko dai ina godiya sosai dan banma san da bakin da zan gode maki ba, naxo gdanku a rufe , naxo maki bankwana ne, munyi tafiya saudiyya, wannan saƙon kuma mai gda yace a baki, kuma shima yana godiya sosai, insha Allah zan maki addu"a sosai kema Allah ya baki miji na gari, daga mai ƙaunar aminiyarki farida ahmad```
Hawaye ya gangaro daga idon raihana tace Allah sarki rayuwa, wallahi naji maki daɗi Allah ya ƙara ma duk macen duniya haƙuri da juriya a gidan mijinta, dan idan kayi haƙuri a gidan aurenka shidai aure ibada ne, idan kuma mutum ya zalinci wani Allah dai shine mai sakayya,
Goge hawayenta tayi sannan ta maida kayan a leda tace bara inje inkai ma umma baiwar Allah kila ma har yanxun bata ci komai ba,
Bayan ta gama maidai kayan kaff ta ɗauki ledar ta nufi shagon shamsu ta bashi kuɗinshi data ranta, ta amso kayanta , bakin titi ta nufa dan hawan abin hawa wai tunda ta samu kuɗi bara ta more su tunda idan suka tafi tana shan wahala kafin ta samu,
Abin hawa ta hau tayi ma gidansu ummarta tsinke, lokacin data isa ta samu umma ita kuma tana fitowa daga cikin gida a ƙofar gida suka haɗu,
Umma tace lafiya kika dawo?"" dariya raihana tayi sannan tace lafiya fess umma, kusa da ita umma ta matsa, wuri raihana ta samu ta zauna itama umma zaman tayi, kallon raihana tayi sannan tace gwaggon ƙoroki tayi ne?""
raihana tace a,aa abun arxiki na samu, tana magana tana fiddo kayan tana miƙa ma umma, umma sai yashe baki take tana cewa waye kuma ya baki?"" jikin raihana yana ƙarma ta fiddo wayar ta miƙa mata , tace umma kalli harda waya, umma tace ni sai nuna man kaya kike faɗa man wanda ya baki, dariya raihana tayi sannan tace kamar lefe ko umma?"" dariya umma tayi sannan tace gaskiya ke yanxun yanda kike zawarcin nan kika samu kamar wannan ai kinyi goshi, dariya sukai gaba ɗayansu sannan raihana tace wallahi farida ta bani,
umma tace farida taki?"" raihana tace farida tawa kau, kinga kuɗi nan, saboda haka muje mu kama haya umma kema kibar wannan gidan don Allah, hannu umma ta miƙa ta karɓi kuɗin sannan tace itama tana da 1k saboda haka akwai wani gda nan kusa da gidan gwaggo sai muje mu kama ko?"" raihana tace wannan gaskiya ne,
haka dai sukayi ta firarsu cikin tausayi da kuma hali na damuwa, bayan wani lokaci raihana tayi ma umma sai anjima, umma tace zata shigo idan Allah ya kaimu zata shigo dan suje su biya kuɗin hayar, raihana tace to sukai ban kwana umma ta shige gida raihana ta nufo gdan gwaggo,
a ƙofar gida raihana tayi zaune har yanxun gwaggo bata dawo ba, tana nan zamanta tana jiran zuwanta, tun daga nesa ta hango zulaiha ta tun karo wurinta sai yage baki take kamar ƙefen sakara, tana tafiya kamar ana ingixo ta,
da ɗan gudu ta iso tana zuwa takai ma raihana duka , tace banza albishirin ki?"" kallonta raihana tayi sannan tace miye, zulaiha tace naje gidansu umma tace man yanxun nan kika taho, kinsan abinda ya faru?"" raihana tace ah ah sai kin faɗa,
Zulaiha tace an saki kishiyata, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un raihana tayi tare da zaro idanuwa cikin tashin hankali taci gaba da salati, tana cewa kam amma na tausaya mata wallahi,
zulaiha tace ke bar "yar iska, raihana tace haba kiji tsoron Allah kinyi *zawarcin* nan kinji yanda yake kinsan wahalar da take cikin shi da yamutsi sai kiyi murna dan an saki wata?""
Zulaiha tace wallahi nayi, raihana tace duk miye yayi zafi haka?"" zama tayi kusa da raihana sannan ta fara cewa,
ke tunda kika bani shawarar in mayar mashi da yaran shi na maida su, tace ita Allah ya kasheta bata zama da su, yace tayi haƙuri tace wallahi bata zama da wa"an nan tsinanin "ya"ya dan ita ba ɓautarsu taxo ba, idan ya zama dole sai sun zauna saidai ya dawo da uwarsu,
yace mata shi bazai maidoni ba, tace to wallahi bata zama dasu , saidai ta tafi gidan ubanta itama, haka dai sukayi ta tashin hankali idan ta dafa abinci bata basu da sunyi abu sai zagi sai duka, idan yace mata yaro saida lallashi sai tace ba yara bane iskanci ne sunsan abinda suke,
wannan saɓanin ne dai yasa har aka rabu, raihana ta sake salati tace lallai amma tayi hauka , matsalarmu mu mata wani lokaci bamu da lissafi, in banda hauka ka nuna ma namiji baka san yaranshi?""
kama so su wace Allah cika?""" kuma idan ta girka abinci ta basu ina zata ragu?"" ai duk macen da bata san yaranka kaine bata kauna, yanxun kinga ita wanna haukan yaja mata sanadin mutuwar aure?""
keda kika raɓa kici arxiki?"" kuma da nata ne yaran idan taso tazo dasu *agolanci* idan yace baya rigewa sai kiga kuma ta nuna damuwa, don Allah mata mu riƙa haƙuri da "ya"yan miji duk abinda zakai kayi tsakaninka da Allah komai kayi Allah yana kallonka baka da tabbas kai zaka rayu da naka idannka ci zalin na wani, idan babu rabuwa akwai mutuwa , duk abinda kayi a rubuce yake baya canjawa dole wani abun sai mu riƙa danne zuciyarmu dan sama ma kanmu salama, Allah yasa mu dace ameen,
raihana ta kalli zulaiha da take ta faman rawa, girgiza kanta tayi sanann tace ai dama haka duniya take sai wani ya rasa wani yake samu, amma ita dai wannan rashin haƙuri yaja mata,
zulaiha tace ke banza ranar juma"a za"a ɗaura mana aure ,idan na shirya sai in tare haka yace, raihana ta kalleta tace in baki shawara?"" zulaiha tace bani aike baki bada shawarar banza, murmushi raihana tayi sannan tace kada ki yanda sai wani lokack ki tare ana ɗaura aure a ranar ki rufa ma kanki asiri kiyi gidan mijin ki,
sannan kin ɗanɗana kinji abinda yake cikin *zawarci* yanzun saidai kiyi ma wasu nasiha, idan kin koma kuma kici gaba da haukan da kikai a baya, zulaiha dariya tayi sannan tace haba ai ɗan ba ƙari godiya da kwanan garke, idan na koma kinsan abinda zanci da safe?"" raihana tace a,aa zulaiha tace wallahi shayi zansha da wainar kwai, wata irin munafikar dariya raihana tayi sannan tace shegiya shi kike yunwa ne?"" zulaiha ta ɗaure fuska tace kema matsalarki iskanci wallahi raihana tace Allah ya baki haƙuri,
zulaiha taci gaba da cewa wallahi rabon da insha shayi kinsan Allah ba wasa ba har mantuwa ta manta, kai ai idan naje akwai abubuwan da zanma yaushe rabo, tsaki tayi sannan taci gaba da cewa bira"uba babu a gida babu a maƙota,
Gaskiya raihana *zawarci* baiyi ba, kema Allah ya baki naki kije kindan raɓa, murmushi raihana tayi cikin sigar tausayi sannan tace aini kila ma ban sake aure, zulaiha tace saboda mi?"" raihana tace to ai har yanxun ma na rasa wanda zaice yana so na, bare azo maganar aure , ni wallahi gani nake kamar hada alhakin Aminu, na samu yana kauna na, da nayi haƙuri nayi zamana duk da abun baikai haka ba,
zulaiha tace ba komai Allah yana tare da mai haƙuri duk abinda yayi tsanani sauƙi yana nan tafe, kiyi haƙuri wata rana sai labari,
raihana tace Allah ya nuna man ranar nan in ganni a gidan mijina ɗakina ni ɗaya inci abinda nake so inyi wanka da sabulu, danni tuni na koma wanka da omo dan yafi auki idan na siyo na 20 sai yayi man sati ina ɗan lallaɓawa, mai ma man gyaɗa nake amfani dashi idan na siyi na 100 yaman wata ukku,
zulaiha tace Allah dai yasa mu dace, idan kana zaman tun kana burge iyayenka har ka fita a ransu, miƙewa tayi tace bari in tafi dare ya gabato don Allah ki shigo gobe sai muga abinda ya kamata muyi, dan yau idan yaxo zan faɗa mashi ranar da aka ɗaura aure a ranar zan tare, raihana tace haka yayi , tare suka miƙe da raihana da zulaiha , zulaiha ta dafa kafaɗar raihana tace kinsan fa yaga canji dan yanxun idan yaman abu godiya nake sosai kamar wata "yar maula, kinsan namiji yana san yayi maki abu kina godewa tare da mashi addu"ar Allah ya ƙaro mashi buɗi daɗi suke ji har a ransu wallahi, raihana tace to ai duk abinda kasan zai fishshe ka sai kayi dan zaman lafiya, haka suka ci gaba da "yar tafiya saida tayi mata rakiya sosai sannan ta dawo ta zauna ƙofar gida tana jiran dawowar gwaggo,
ta ɗaɗe sosai dan har an gama sallar magrib sannan ga gwaggo ta ɓullo, raihana tayi mata sannu da zuwa sannan gwaggo ta amsa, makullin ta bata tace ta buɗe masu ƙofa yau akwai labari, raihana tace labarin mi?"" gwaggo tace kedai buɗe gida mu shiga kiji ikon Allah, raihana tace to, da sauri tayi ta buɗe gida suka shiga,
suna shiga rainaha tayi alwallah dan gabatar da sallah magrib , bayan ta gama sallah gwaggo tace , ashe ɗiyar ladi sata take ma mijinta?"" idanjwa raihana ta zaro tace wace ladin kuma?"" gwaggo tace wace kika sani?"" raihana tace ai ladi da yawa, gwaggo tace ladi aminiyata, tana nan gida mijin ya maidota, amma auren bai mutu,
tsaki raihana tayi sannan tace su suka sani, in banda hauka da taɓewa mi yakaika yima miji sata?"" ai yima namiji sata ba ƙaramar lalacewa yake sa mace tayi ba, kuma ko ba komai idan ka fita da tambarin sata wane namiji zai aure ka?"" tsaki tayi sannan tace Allah dai ya rufa asiri, gwaggo tace ameen,
miƙewa raihana tayi taje ta sako alwallah , tana tunanin irin halin gwaggo wato ɗiyar aminiyarta wanda take auren mijin daya saki raihana, tace umm kada ince wani abu kuma taje ta ƙarani, miƙewa tayi sanann ta nufi ɗakin gwaggo tana zuwa tayi sallahr isha"i, tana gamawa a wurin da tayi sallahr anan ta kwanta, bata daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita,
Allah yasa mu dace ubangiji ya ƙara mana haƙuri a gidan aurenmu idan bakayi haƙuri don Allah ba sai kayi dan banza, hausawa sunce wanda bai share masallaci ba ya share kasuwa, Allah ka zaunar da kowa a gidan mijinta lafiya, ameeeeeeeeeeen,
da haka nake cewa ku kasance tare dani, 💋💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 2⃣5⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Wannan shafin naku ne ameenci writer's association, ƙungiya mai haɗin kai da kaunar juna, kullum ƙoƙarinsu ganin sun kyautata wa juna Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, ubangiji ya ƙara basira da hazaƙa , Allah kuma ya ƙara lafiyar idanuwa, abinda muke rubutawa wanda mukai daidai Allah ya bada ikon amfani dashi inda mukai kuskure Allah ya yafe mana , ku kuma masoyanmu muna maku fatan alkairi ubangiji ya barmi tare*
*Asmeenat xeeyan har yanxun ba zan daina maraicinki ba, saboda kina cikin babban birni zuciyata* 😜
*Hafsat isa maman katsina ta dikko ɗaƙin kara muna godiya sosai bisa ƙaunar da kike ma aminci writer's mun gode sosai da kulawarki alkairin Allah yakai aki har cikin bargon baccinki dan nasan yanxun dai baki tashi ba,*
*****
*G*ari na wayewa raihana bayan tayi sallah bata koma bacci ba, suna nan zaune da ita da gwaggo suna ɗan taɓa fira, har hantsi ya fito, gwaggo ce ta tashi ta fita daga ɗakin dan sarrafa abinda zata bawa cikinta,
Daga tsakar gida ta kwaɗawa raihana kira , tana cewa fito ki siyo man alewa, raihana ta fito daga ɗaki tana miƙa, da hijibin ta rataye a kafaɗa, naira 10 gwaggo ta bada ta siyo mata alewa, raihana tace wai mi zakiyi da itane?""
Gwaggo tace kunun tsamiya zanyi, idanuwa raihana ta zaro sannan tace banda abinki waye zaisha kunun tsamiya da alewa?"" gwaggo tace ni, raihana tace haba kiyi haƙuri a siyo maki sugar kona ishirin sai ki ɓalɓaɗa, gwaggo tace ƙarshen canjinta kenan, dariya raihana tayi sannan ta anshi kuɗin ta fita daga gidan,
Ita kuɗin ta suna hannun umma data siyar ma gwaggo sugar nan , tsaki tayi sannan tace Allah yayi mana tsari da talauci, niko nace ameen ,
Tafiya take sosai har ta isa shagon shamsu, akwai layi dan haka ta samu wuri ta raɓe, saida aka rage sannan ta miƙa mashi kuɗin , bayan ya riƙe kuɗin a hannunshi ne kafin ya ɗauko mata alewar ya fara cewa raihana jiya anxo binciken halinki amma nidak Allah ya sani na bada shedar halinki ikar wanda na sani amma ina nan naji shehu yace aike alashe money ne baki auren talaka sai mai kuɗi sannan kuma duk kinbi kin gama barbaɗewa saman titi, shekara ukku kina zawarci kada ya kuskura ya yayo ma kanshi jaraba,
Amma kiyi haƙuri ba faɗa maki wannan dan ranki ya ɓace ba kiyi haƙuri idan kinsan kina da wani hali wanda bai dace ba ki gyara, kamar yanda kike haƙuri akan rayuwa ki ɗaure kuma ki dage da addu"a, dan duk tsanani yaa tare da sauƙi,
Ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace shi a gabanshi nayi iskancin ne?"" shamsu yace wallahi banda ni kima tambayi duk wanda kike so, zai faɗa maki dan cewa yayi wai kwalba kika samu idan kika kama mutum ki fara aske mashi arxiki wahala take sa ya gudu da kanshi , kina jiran mai kuɗi yaxo ki aureshi,
Raihana tace to shida Allah, kuma idan lokacin aurena yaxo wallahi bai isa ya hana ba, idan kuma ina rabon hutawa haka shima bai isa ya tare man samuna ba,
taci gaba da cewa tunda yayi aure ya aihu shima wata rana anyi ma nashi, daga nan bata sake cewa komai ba, har shamsu ya bada alewar ta fito daga cikin shagon ta nufo gida,
Tana tafiya tana tunanin wanan sharri, tsaki tayi lokacin data wuto majalissar da ake janta suka fara , ko ka gane mana *zawara* uwar san banza ke wuta kanenki ɓarawo, suka fara sheƙewa da dariya, suka ci gaba da cewa nifa ban taɓa ganin zawarar gdan talauci ba wai ita can mai kuɗi take jira don Allah kalleta, sai su sheƙe da dariya hhhhhh *zawara* haka sukayi ta mata iskancin , ita kuma raihana hawayene kawai yake bin idonta rugawa tayi da gudun tsiya, tayi cikin gda, gwaggo tana bakin murhu tsugunne taji raihana ta shigo da guda,
da sauri ta miƙe tana tambayar lafiya?"" raihana da gudu ta faɗa cikkn jikin gwaggo ta rushe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, gwaggo ta fara salati tana cewa wai miye don Allah,
raihana tace wai gwaggo har takai idan anzo tambayar halina a anguwar nan ace man waini "yar iska ce, wai bana aure sai mai kuɗi, ni wallahi miji ko daga kauye yazo wallahi aurenshi zanyi, ni banma san mai kuɗi talaka nake so muyi zaman mu, in rufa ma kaina asiri, yanda take kukan tana ƙara ɗaga murya, abun yasa gwaggo taji tausayinta,
raihaina taci gaba da cewa ama barni da abinda Allah ya jarabeni amma sai ayi ta jaman sharri?"" to wallahi ni tunda nake ban taɓa iskanci ba, kuma duk wanda yaman sharri na barshi da Allah wallahi,
gwaggo taji tausayin raihana don haka taci gaba da rarrashinta tana bata haƙuri , raihana tace ba komai Allah zai saka man, tana cikin magana wani yaro ya shigo yace ance raihana taxo, ɗago jajayen idon ta tayi sannan cikin maganar kuka tace waye yake kirana?"" yaron yace ummarki ce, murmushi raihana tayi sannan tace ma gwaggo ina zuwa,
Tana faɗin haka tayi waje da gudu, tana fita a ƙofar gidan da zasu kama haya ta hango umma tsaye saboda haka da gudu ta isa wurin umma tana ta kuka, umma tace mi akayi maki kuma?"" raihana ta kwashe komai ta faɗa mata,
Har a ran umma bataji daɗi ba, amma dan tasa raihana taji natsuwa tace to miye?"" aidai ke kinsan baki iskanci ko?"" to duk wanda yai maki barshi da Allah, raihana tace haba umma sharri babu daɗi , umma tace mai sharrin zai isko maiyin da izin Allah,
ta kauda maganar ta hanyar cewa na biya kuɗin na wata ukku na bayar, yau zanje in kwaso kayanmu, raihana tace to, umma tace ki shiga kiga ɗakin, raihana tace umma basai na gani ba, ina sauri ne inje in shirya zulaiha tana jirana a gdansu,
umma tace to kije ki shirya ki tafi, raihana tacd umma kinga waya, nayi chargy ashe ma hada layi ta saka man, umma tace to Allah ya tsare , raihana tace amin, sannan tace ummana ki bani ₦20, inje in siyo ko koko insha,
Umma tace to sannan ta bata kuɗin, ta juya tayi gidan da suke siyo koko, ta siyo a leda sannan tayo gidan gwaggo,
tana shiga ta samu wuri ta juye kokon, babu sugar babu alewa, ta bara sha, gwaggo tace miyasa kika siyo?"" gashi nayi dake, raihana tace ai yau koko nake ra"ayi, gwaggo tace tou fa,
ita kuma raihana tayi haka ne dan zaman lafiya dan idan dai kana san zamanka da mutum yayi nisa dole saika nisanci abunshi, idan kaga mutum yana san abunshi tayashi sanshi sai ka zauna lafiya,
tana gamawa wanka taje tayi, kayan da taxo dasu dagan su umma ta saka , taci uban kyau idan ka kalli raihana sau ɗaya baka iya sauke idon ka, dan gaskiya raihana tana da kyau , kuma kyau mai ɗaukar hankali , tana da siga da diri mai ɗaukar hankalin duk wanda ya ganta, amma daka ganta kasan bata da wadata, danshi ƙoshi daban yake, kana kallonta zaka gane tana cikin damuwa,
haka ta gama shirinta tsaff ta fito, tayi ma gwaggo sai ta dawo, gwaggo tayi mata Allah ya tsare hanya,
tana fitowa ta ibi hanya sai gidansu zulaiha, haka tayi tafiya mai ɗan nisa sannan ta iso gidansu, a ƙofar gida ta samu zulaiha, suna gaisawa da wani abokin mijinta wanda shine zai kaisu inda zasu je, zulaiha da sauri ta iso wurin raihana ta rungumeta kawata kinfa haɗe, dan ba haɗuwa kikai ba haɗewa kikai wallahi, raihana tayi dariya, sannan zulaiha tace *K"B* ga ƙawata, sunan ta raihana,
kb ya kalli raihana sannan yace sannu raihana tace kaima sannu, ya tsareta da idanuwa sai kallonta yake, zulaija tace muje ciki,
suka shige ciki gida, suna shiga wata ƙanwar zulaiha ce ta fara cewa wallahi yaya zulaiha shine kika shafa man janbaki na?"" zulaiha tace janbakin banza, yarinya nida aka kawo ma lefe,
kanwar tace lefenkin banza ina ruwana dashi, zulaiha tace rashin kunya zaki man ne?"" wannan ba baƙuwa bace a wurina, tana nuna raihana tace da Allah wuce muje bar raihana bar banza,
babu kunya yarinyar nan tace gaki ƙatuwar banza, wanda kika kasa haƙuri da mijinki irin halin da kikai mashi ya koro ki kkke so muma nan kixo ki raina mana hankali tomu bamu barin takwana,
raihana tacd ikon Allah zulaiha tacd ke bar banza nan mi kika gani?"" ai nan ba"ai komai ba, muje ciki lokacin da take jan hannunta suka shiga cikin ɗaki,
Ita kuma kanwar zulaiha haka taci gaba da ɗago murya tana zungurawa uwar zulaihat zagi amma daga raihana har zulaiha babu wanda ya sake magana, suka fara buɗe kayan lefe,
akwati shidda hada wata katuwar jaka, an kashe kuɗi gaskiya akamar lefen budurwa, ga kaya masu tsadaɗ gaske, komai dai na aji ne aka sako mata tsayawa faɗin abun ɓata lokaci ne, raihana taima zulaiha fatan alkairi,
zulaiha tace nace mashi ranar da aka ɗaura aure zan tare ,yace to babu damuwa kuma ko kayan ɗaki da duk abinda zan buƙata shine yayi man, raihana tace masha Allah haka ake so ai,
bayan sun gama ganin kayan zulaiha tace suje kabir yana waje yana jiransu haka suka taso sukayo waje, suna fitowa kabir ya kwashe su suka biɗaɗa duniyar gayyar ƙawayensu,
haka suka yini suna gayya, amma ba kowa suka gayyata ba sun gayyaci ƙawayensu na kusa da kusa, sannan sukayo gidan su zulaiha , k"b yace to zulaihat bari inkao ƙwarki gda, raihana tace ah ah nidai ajiyeni anan , zanje dakai na, yace wallahi sai nakaiki,
zulaihat ta fita, shi kuma yace ma raihana ta dawo gaba, raihana ita tunda take bata taɓa shiga gaban mota ba, saboda lokacin data auri aminu baya da mota,
Raihana taƙi tashi , ya sake mata magana amma ta kasa motsawa, zulaihat tace haba ƙawata miye haka don Allah wannan babban mutum zai zama drivern ki?"" zo kiji, ta matso kusa da raihana tayi mata raɗa, bansan abinda sukace ba amma naga raihana ta tashi ta koma gaban mota,
tana shiga zulaihat ta rufe masu ƙofa, k"b yaja suka bar ƙofar gidansu zulaiha,
Lafiya suke babu wanda yayi ma wani magana, k"b ne yace muga wayarki, raihana ta miƙa mashi, amsar wayar yayi ya ɗan jujjuyata sannan yace wanne wayar kike riƙewa?"" raihana tace Eh, tsaki yayi sannan yace haba ai abun kunya ne ina tare da mai kyau kamarki kina riƙe wanann ƙaramar wayar,
saboda haka zan kawo maki waya mai kyau idan Allah ya kaimu gobe, raihana tace ai wannan sabune, yace nidai batai man ba gaskiya, raihana tayi shiru, haka yaci gaba da maganarshi wata ta bashi amsa wata kuma tayi mashi shiru har suka iso ƙofar gidansu , bayan yayi parking ne , yace ma raihana yana zuwa, fita yayi daga cikin motar yaje ya buɗe but, ya ɗauko wani abu, sannan ya dawo ya miƙawa raihana,
Nidai bansan ko miye ba, amma wani ɗan ƙaramin kwaline, raihana ta karɓa tayi godiya,, sannan tayi mashi saida safe, saida ta shiga gidan da suka kama haya yaga inda ta shiga sannan ya tafi,
Sallama raihana tayi sannan ta shiga, uma daga ɗaki ta amsa mata sallamar, raihana ta shiga, umma tayi mata sannu da dawowa, raihana tace yawwa daidai lokacin da take cire gyalen jikinta, ta raye a saman ƙofa, zama tayi dan ganin abinda k"b ya bata, umma tana cewa miye wannan ?"" raihana tace nima ban sani ba, amma bara mu buɗe mu gani,
Bayan ta buɗe ɗan ƙaramin kwalin daga umma har raihana zaro idanuwa sukai da sauri umma ta miƙe tsaye ta dafe girjinta dan ganin abinda ta gani , itama raihana gabanta sai faɗuwa yake, umma ta fara cewa raihana yaushe kika canja hali? Yaushe kika koma rayuwar da ba taki ba?"" wane irin rayuwa kika zaɓawa kanki haka"??""" ina kikaje kika samo wannan kuma?"" waye shi da har zai ɗauki wannan ya baki?"""kuma raihana cewa take wallahi umma bansan ko miye a ciki ba haka ya bani da nasan hakan ne ai da bazan karɓa, na ɗauka biscuit ne, umma tace keda yunwa ta ƙare maki ko?"" raihana tace umma ba haka bane, umma tace rufe man baki aikin mi kikai masji da zan ɗauki wannan ya baki??"""" wato kin fara halin da ake zarginki dashi ko?"" raihana ta fashe da kuma tace haba umma ki kyautata man zato don Allah wallahin banyi duk abinda kike tunani ba, idan kuma zatonki haka ne wallahi umma ki dubani na yadda kiga idan nayi iskanci, tunda nake wallahi ban taɓa zuna ba, tsaki umma tayi sannan tace faɗa man abinda kikai mashi ya baki wannan iyayen kuɗin...........................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
0 comments:
Post a Comment